RUFAFFEN SIRRI CHAPTER 2 BY SADNAF

Advertisements

_____

Kabiru har suka je Suka dawo bai iya magana ba sabida kasan zuciyarsa cike take da tsoro,ji yake Kamar ba zai iya ba dokokin da Abubuwan da akace yayi sun masa yawa da tsauri,a hankali ya Kai dubansa wajen Alhaji Rabiu da ya kasance abokinsa tun primary da a lokacin ya fi shi k’ok’ari nesa ba kusa ba dan shi yake zuwa na karshe ma a ajinsu da kuwa suka gama primary bai Kara saka shi a idonsa ba,bai Kara jin labarin sa ba sai a shekara biyu da suka wuce ya had’u dashi,sai da yayi da gaske ya gane shi sabida yanda ya dawo fari kal sabida yadda hutu da Jin dadi suka zauna masa tashin farko,kyautar dubu dari ya Masa,ya hada da bashi lambarsa,duk kalar rayuwar da yaso tun Yana karami na rayuwar Jin dadi shi yake gani a wajen Rabiu.

Gashi ya girma zai iya cewa ya d’auko tsufa tunda Yana dab da aurar da ‘yar cikin sa duk bai samu cikar burin nasa ba.

Tuni yaji ya kwadaitu da san yayi kudin fiye ma da da hakane yasa ya makalewa Alhaji Rabiu ko zai taimaka Masa ya sama mi shi aiki irin nashi da shi ma zai samu kudin.

A haka Alhaji Rabiu ya ringa masa yawo da hankali Yana kasuwanci yake yi sai da yayi dagaske Rabiu ya fito ya nuna masa ta hanyar da ya samu kudin sa,idan har yaga zai iya.

Advertisements

_____

Tsayuwar motar Alhaji Rabiu a wani tamfatsatsen gidansa da matarsa ta uku take ciki ya katse tunanin da Kabiru ya tafi.

Yayi horn Mai gadi ya bud’e masa.

Tun da suka shiga gidan Kabiru ya saki baki da hanci Yana kallon Aljannar duniya,maganar shugaba na dawo Masa a kunne,”zaka yi kudi, idan nace ma kudi,Ina nufin kazamin kudin da zai saka duniya ta san ka zaka ji dadin rayuwar ka zaka bar wa yayanka tarin dukiya ka tabbata baka tsallake duk sharuddan da aka gindaya ma ba daga yanzu kafin wata ukun zaka fara dandana arziki amma ka iya takun ka”

“Sauko mu Shiga daga ciki ka gaisa da Aseeya”

Muryar Alhaji Rabiu ya katse Masa tunanin da yake.

“Rabiu anya zan iya wlh bansan mai yasa nake Jin bazan iya ba gani nake za’a iya gano ni da wuri bazan iya yiwa Sajeeda haka ba”

Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana “Tunda na iya yiwa Sakeena Yar uwata haka Kai ma zaka iya bafa kasheta zaka yi ba,a cikin kankanin lokaci Kai ma zaka zama kamar ni,kayi amfani da abinda kake dashi ka samu cikar burin ka,kar ka karaya abokina muje dai daga ciki indai Muka bi komai a yanda Muka tsara wlh baza’a samu matsala ba”

Kabiru gyada Kai yayi duk da a kasan zuciyarsa gani yake bazai iya ba.

Yabi bayan Alhaji Rabiu yana karewa gidan kallo,hararo kansa kawai yake a matsayin Rabiun ya mallaki irin wanan gidan,ya ginawa su Saifullahi manya manyan gida daidai da Nusrah ma sai ya mallaka Mata gida da mota, tuni yaji ya Kara kwadaituwa da ya samu kudin,a lokacin da suka Shiga palon da Kamar a kasar waje suke da suka shiga.

A lokacin kuwa daya zauna kalle kalle ya cigaba da yi Alhaji Rabiu ya haye Sama minti biyar a tsakani sai gashi ya sauko ya zauna.

Kafin kace me masu aiki sun cika gabansu da kayan ciye ciye.

Alhaji Rabiu kuwa sai murmushi yake dayaga yanda Kabiru ke hadiyar yawu.

Takun takalmin Aseeya matar Alhaji Rabiu dake saukowa daga saman benen yasa Kabiru maida hankalin sa wajen benen.

Yarinya ce bata fi saar Nusrah Yar sa ba ko zata girmi Nusrah bazai fi da shekara biyu ba,kyakyawa ce ta ajin karshe tamkar ita tayi kanta fuskarta d’auke da murmushi,har ta karaso gefen Alhaji Rabiu ta zauna ta fara gaida Kabiru da ya hau washe baki kasan ransa Yana ta mamakin yanda yarinya karama ta yarda ta auri sa’an mahaifinta.

Bayan sun gama gaisawa ta mik’e ta koma sama,

“Rabiu yanzu Wanan Yar yarinyar ka Aura”?

Murmushi Alhaji Rabiu ya saki ya zuba Lemo a kofi sai da ya kurba ya ajiye ya kalli Kabiru Yana “Shekara uku kenan da Auren mu Kuma ta wajen nan da matarka ta hana ka ta wajen nake neman ta”

Ido Kabiru ya zaro waje Yana “Kuma sai ta yarda”?

“Kwarai kuwa ba Ina da kudi ba,a yanzu da kake ganin ta bama tasan Inda zata Kai kudi ba kaga kuwa ko dan su dole ta yarda da bukatata dan sai da na tabbata Iyayenta irin talakawan nan ne sosai,dan a garin talla ma na hadu da ita,na cikata da kudi na cika Iyayenta da kudi, basu da gidan kansu kafin na aureta yanzu kuwa har yayyenta maza ba Wanda ban siyawa gida ba tana morata a zahiri Ina morarta a badini”

Sai yayi kasa da murya

“Tana samun ciki take b’ari na riga na bada mahaifarta”

Ni kuwa Ina nan da yayana bakwai suna jin dadin su a waje”

Kabiru mamaki ya sa ya kasa ma magana dan sai a yanzu ya gane da rabon amaryar kudin sa ke Kara hab’aka uwar yayan sa kuma ta masa silar kudin.

“Rabiu dama nima na auri wata ta zama silar kudin bana so na tab’a uwar Yayana da mu ka Sha wahala tare da ya Kamata ace a yanzu taji dadina shugaba ya bani wata uku ya bani Abubuwan da zanyi har zuwa matakin karshe,tunda Muka baro wajensa wlh jikina a sanyaye yake gani nake bazan iya ba”

Wani irin mugun kallo Rabiu yabi Kabiru da shi yana “Ka ga idan baza ka iya ba ka tashi ka bar min gida ka Kuma dawomin da kudadena da na baka,kudin nan idan kayi ni zaka bawa ko me ana ta nuna ma hanyar arziki kana baudewa,duk uban wahalar nan da ka ringa bani dama baka tsayar da zuciyar ka ba abu kad’an sai kace baza ka iya ba dalla tashi ka bar min gida kasan Kuma baa yiwa kungiya haka indai ka fasa wlh sai an tab’a ka”

“Ba abinda nake nufi ba kenan Rabiu ba fasawa zanyi ba sharrudan yanzu sunfi bani tsoro ina tsoron na kuskure a samu matsala”

“Ka kwantar da hankalin ka kasa a ran ka zaka iya Sajeeda da kake ta fadi ba fa kasheta zaka yi ba balle,dadin ma da ita za’aji gefe guda Kuma idan an kwana biyu zaka iya auren Mata uku kayi ta more rayuwar ka abokina kana Jin dadi,yayanka ka gan su fes,ni kasan gabad’aya yarana suna kasar waje,shawara daya dai Zan baka duk yanda muka tsara ka bi zaka Sha mamaki kila.ma.ka fini himma wajen bada abin arziki kudi suyi ta hauhauwa ai ba dawwama zamu yi muna yi ba zamu Yi iya yin mu kudin ya Kai mana yadda muke so sai mu tuba muyi ta istigifari Allah Mai yawan afuwa da gafara ne zai yafe mana duk shekara muna d’akin sa muna neman yafiya fa wanan ba wani abu bane”

“Hmmmm toh shikenan Allah yasa duk Kar na samu matsala Ina Addu’a Allah yasa Kar Sajeeda ta tab’a rafkoni dan tana da balain wayo da san tabi kwakwafi”

Da haka suka cigaba da hirarsu wajen laasar Alhaji Rabiu ya Kara tsara masa duk yanda za’a yi ya d’auko kudi ya bashi mai yawa ya raka shi ya tafi.

Sajeeda

Idan naga yarana gabad’aya a gabana ji nake kamar banida wani matsala a rayuwata, zuwan Nusrah yasa na manta da damuwa da hawan jinin da Abban Nusrah ke neman saka min,Ina zaune a tsakiyar su duk mun baje a tabarma ana ta hira, wayarta ya hau ringing tak’i d’auka ganin Kiran ya Kara shigowa nace “Wai ba za ki dauki wayar ki ba ko ba kiran ki ake ba”?

“Umma Ahmad ne fa na san cewa zai yi na dawo ni Kuma na fi so na gaisa da Abba kafin na tafi na ga kowa ban dashi bazan ji dadi ba idan ban gan shi ba”

“Sai ki Kira shi a waya ku gaisa maza tashi ki tafi gidan ki bana San shashanci dama mijin ki ke ta Kira kika k’i d’auka”?

“Umma dan Allah ki bari na Kira Ahmad nasan bazai hana ni jiran Abba ba”

Sai da na ga ta kira mijin ta ya amince ta jira Abban ta kafin na yarda ta zauna duk da har a kasan raina ba gajiya nayi da ganin ta ba gani nake kamar jiya na haifeta sai gashi cikin ikon Allah da ran mu ta girma tayi, aure duk Wanda ya ganta yasan tana d’auke da karamin ciki,a tunanin da nake na tuna halin da mahaifinta ya bijiromin dashi,take da girmana da komai nabi sauran kannenta da kallo da duk sun ma fi Nusrah girma Annur da Fahad ne kawai basu fita girma ba,mutane da yawa sun d’auka saifullahi yayanta ne da yake girman yazo da zamani har wani saje da gemu ya ajiye, ba Mai yarda ta girme shi,
Shigowar Larai da sallama yasa Mu ka mai da hankalin mu wajen k’ofar tare da amsa sallamar da tayi,Larai yar aiki ce a wani gida dake bayan layin mu na riga da nasan da zuwan ta tunda hajiyar ta kirani akan zata turo ta ta kawo min kayan aiki.

Buhun hannun ta ta fara ajiyewa kafin ta sauke kayan dake Kan Almajirin dake biye da ita a baya ta zauna muka gaisa

Tana “ga kayan nan Hajiya tace ki duba abinda babu sai na karbo”

Kayan na duba naga duk abinda na bada list Ina bukata akwai hakane yasa na dago Ina “Karfe uku ne taron ko?

“I karfe uku ne idan Allah ya kaimu”

“Toh ba damuwa gobe karfe daya da rabi kizo da kulolin zuwa lokacin na gama in sha Allah”

Mik’ewa tayi ta min sallama ta tafi,

“Umma dan Allah ki daina wanan aikin wahalar wlh har ga Allah bana so sabida ke nake so na nemi kudi ki huta”

Cewar Faisal yana hade rai.

Saifullahi ya karba da “Abin nan na cimin tuwo a kwarya wlh nima bana san aikatau dinan da take karba kudin ma ba wani Mai yawa ba a gaskiya lokaci yayi da Zaki daina wanan aikin umma”

Murmushi na saki Ina “Ina ga tunda kuka taso kuka same ni da sana’ar nan, ni kadai nasan kalar rufin asirin da wanan sana’ar yamin bani kadai ba har daku tunda kunsan aikin baban naku ba wani mai kwari bane idan na daina ku kan ku zaku Sha wahala a yanzu idan ta biyani kudi na gobe shine zan samu kudin registration din jamb din ka”

Yana k’ok’arin magana Abban Nusrah ya shigo da sallama hannun sa d’auke da ledoji niki niki.

Tuni yaran Suka mimike Nusrah ta riga su isa wajen sa tana “Abba oyoyo tun dazu nake jiran dawowar ka sannu da zuwa”

Washe baki yayi Yana “Kin dade da zuwane”

“Kana fita nazo Abba”

“Ai da kin kirani a waya ai da na dawo da wuri ya kike ya maigidan naki”

A kunyace Nusrah ta ringa amsawa Bayan ta ajiye ledojin.

Daya bayan daya suka ringa Masa sannu da zuwa fuska a washe ya ringa amsawa sai da ya juyo muka hada ido ban kawo zai min kallon arziki ba naga ya sakar min murmushi take na saki murmushi Ina Jin dadi a raina na Masa sannu da zuwa a daidai lokacin da Yesmeen ta d’auko masa ruwa ta ajiye a gabansa.

Ganin su Saifullahi na k’ok’arin mik’ewa yasa yayi saurin dakatar dasu sai da suka zauna ya kalli Saifullahi Yana “Ni nawane ma kudin registration din ka”

Washe baki Saifullahi yayi Yana “Abba na dan yi aikin lebura na tara dubu goma yanzu ciko nake nema”

“Nawane cikon”

“Dubu goma Sha biyar ne”

Hannu yasa a Aljihu ya d’auko wrapper Dari biyar biyar,na gwallo Ido Ina kallon sa tamkar yanda duka yaran suma suka zaro ido suna kallon kudin,ya kirgo Dubu ashirin dan dani aka kirga kudin ya mikawa Saifullahi Yana “gashi nan kaje kayi registration din”

“Na gode Abba Allah ya Kara arziki”

“Ameen”

Ya kalli Faisal yana “nawane kudin jamb din naka”

Shima baki a washe ya fada masa ya kirga ya bashi zuwa lokacin farinciki da mamakin Inda ya samu kudi Mai yawa hakane ya cikani dan iya sanina yanzu ba lokacin samun kudin sa bane

Dan aikin nasa sai lokacin zafi sosai idan ya samu su gyaran freezer haka Ac franker da sauran su.

Mamaki bai Kara kasheni ba sai da naga daidai da Annur sai da ya tambaye shi matsalarsa ya kirgo kudi ya bashi ko Nusrah bai bari a baya ba ya kirgo Dubu goma ya bata har ga Allah kasa motsi nayi dan a lissafin da nayi ya bada wajen dubu sabain,Ina ya samu irin wanan kudin mai yawa haka yadda ya bawa Nusrah dubu goma haka ya bawa Yesmeen da bakin su ke washe suna ta zuba Mai godiya da Addu’a sai amsawa yake bakin sa shi ma a washe.

Sai a lokacin yacewa Yesmeen ta d’auki ledar kajine a ciki ta wanke ta dora sai yarana suka Kara haukacewa da murna har Nusrah na wlh sai ta tsaya an gama ta tafi dashi.

Sai da duk Suka watse ya juyo ya kalleni yana “Hajajju yau nima na dan yi abin kwarai rabon da na yiwa yaran nan abu da kaina har na manta baki ji dadin da naji dana ga farin ciki a fuskarsu ba”

Murmushi na saki Ina “Allah ya Kara arziki ya Kara budi ni da adashe na ma Zan dauka na bawa Saifullahi yayi registration din sai Kuma Allah yayi ikon sa ka samu kudi”

“I Allah kuwa yayi Ikon sa Alhamdulillah ke ma ai ga naki siyayyan nan na miki”

Ya turo min daya ledar gabana

Baki a sake na bud’e ledar naga less ne guda biyu sai atamfa da wani bakin mayafi duk da ba wani sanin kaya masu tsada nayi da gani kayan masu tsada ne”

“Abban Nusrah a Ina ka samu kudi mai uban yawa haka”

Kabiru gyada kansa yayi dan yasan zaa rina indai Sajeedar daya sani ne sai ta tambaya

“Haduwa nayi da wani tsohon abokina ya zama mugun mai kudi,shi yamin kyautar kudin nan bai tsaya iya nan ba yace zai taimaka min na samu aiki”

“Wane abokin naka ne dan Kamar duk nasan abokanan ka”?

“Aa baki san wanan ba primary Mu ka yi tare”

“Allah sarki Allah ya saka Masa da alheri ya biya Masa bukatunsa na alheri yadda ya faranta mana Allah ya faranta masa”

“Ameen ya Allah”

A ranar tare duk Muka ci abinci cikin tsananin farin ciki su Annur a kudin da aka basu har da siyo sababin takalma.

Abban Nusrah ma zan iya cewa rabon da naga farin ciki haka a fuskarsa har na manta.

Bayan sallah isha mijin Nusrah yazo Suka tafi.

Addua kawai nake a raina Allah yasa Abban Nusrah ya cire wanan mumunan abin a zuciyar sa har ga Allah naji dadi da naga baya fushi dani bana san abinda zai Kara sawa na mu yi fada.

Ko da muka kwanta a ranar bai neme ni ta baya ba ta hanyar da Allah ya hallasta miji ya nemi matar sa ya neme ni bayan ya samu nutsuwa ya bani hakuri akan na kwantar da hankalina bazai Kara tunanin nemana ta baya ba sai a yanzu ma ya ringa nadama da yayi tunanin gwadawa.

Har ga Allah naji Dadi rumgume da juna muka yi Bacci.

3am

Kabiru a hankali ya leka fuskar Sajeeda yaga tayi nisa a bacci.
Ya zare jikinsa daga nata ya sauko a hankali sabida Kar ya tasheta daga bacci.

Gefen gadon ya duba a hankali ya d’auko pant din ta ya kudundune a hannun sa cikin sanda ya fice daga d’akin yayi waje.

Yana zuwa yayi bayan gida ya d’auko tukunyar kasar da ya shigo dashi da ba Wanda yasan ya shigo dashi,ya saka pant din a ciki ya fara surutan da aka ce yayi a hankali Yana waige waige duk da Yana da tabbacin ba Mai ganin sa dan a sharrudan ance Kar ya sake ya yarda a gan shi.

Yesmeen.

Bata da nauyin bacci ko kad’an ko ya taji motsi sai ta farka.
Motsin k’ofa yasa ta bude idonta.

Kafin taji Kamar takun tafiya a ta Bayan dakinta Inda ta mik’e zaune tare da dafe kirjinta cike da tsoro.

A hankali ta Mike ta leka ta window……….

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

WA GARI YA WAYA BY MARYAM IBRAHIM LATEE

Advertisements _____ : WA GARI YA WAYA Rubutawa MARYAM IBRAHIM LITEE (labarin zaman kishin mata …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *