RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Advertisements

_____

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun bakin ciki haka nake ji a lokacin da naji Abban Nusrah na ta shafani wanda nasan mai hakan ke nufi,tun kafin nayi bacci bai neme ni ba sai yanzu,ban motsa ba dan har ga Allah bazai samu abinda ya keso har ya gamsu ba,sai dai shi kadai yayi kidan sa yayi rawar sa duk da ba abinda ya shafe shi ko baccin nake idan yayi ra’ayi ko ban bashi hadin kai ba zai juyo dani ne ya samu biyan bukatarsa.

Ina Jin lokacin da ya rabani da zanin dana dora a saman t shirt din dake jikina,a madadin ya juyo dani sai naji ya rungumeni ta baya,ya fara k’ok’arin neman hanya da jikinsa dan tsawon zamana dashi ban wani san dan aike ba balle har wai a motsa min sha’awa,shi dai burin sa kawai ya shafani sama sama ya samawa kansa nutsuwa,inda naji Yana k’ok’arin yi yasa nayi saurin janye jikina,sai a lokacin na motsa na juyo Ina kallon sa cikin mamaki,shi kuwa idonsa a kankance ya kara jawoni,sai na juyo a rigingine dan ya samu abinda yake so dan Ina tunanin dan ta gefe yasa yayi hanyar da ba haka ba,sai dai a madadin ya hau kaina sai naga ya Kara juyar dani ya kankameni da hannu daya ya sa hannu daya ya Kara danna jikinsa wajen da yasa na Kara janye jikina da bala’in sauri na Mik’e zaune cikin mamaki Ina kallonsa.

K’ok’arin jawoni yake na janye jikina Ina “Lafiya kuwa Abban Nusrah mai haka”?

“Wane irin tambaya ne wanan Sajeeda bangane mai haka ba ki matso na samu nutsuwa ki koma baccin ki”

Advertisements

_____

“To ai kai din ne bangane ba Kai ma kasan ba wajen nutsuwar ka nufa ba bayana naji kana k’ok’arin shiga”

Tsaki yayi ya Kara jawoni da k’arfi Yana “Ta bayan yafi dadi bari kigani”

Da karfi naga Yana Neman tura jikinsa bayana

Da k’ok’awa na fusge jikina cikin tashin hankali da mamaki na sauka daga gadon na nufi wajen haske na kunna na zuba masa ido kamar yanda shi ma ya zubo min ido, tamkar an like min baki haka naji dan tsabar mamaki na ma kasa magana,shekarar mu Ashirin da biyu da Aure bana Jin da gani har shi bakine a wanan fagen balle ince sani ne bai yi ba shi yasa yake k’ok’arin nema na ta baya har Yana cevmin yafi Dadi.

“Abban Nusrah anya a hayyacin ka kake kuwa”?

Mik’ewa yayi ya nufo wajen da nake tsaye yayi kasa da muryarsa yana “Sajeeda a hayyacina nake nasan zaki ji wani iri amma ki taimaka ki ba ni hadin kai ina so na gwada ta bayan nan ance yafi dadi”

“Allah ya kiyaye Kabiru Allah ya kiyaye ni zaka nema ta baya ta Inda ake kashi,kabiru Anya Kaine kuwa?waye yace ma ka nemi matar ka ta baya, idan Wanda ya baka shawara bashi da ilimi kai ina ka Kai naka ilimin bayan kasan haramun ne, bazan iya ba Kai ma da ka yi tunanin kayi gwajin ka fara istigifari”

Kasa ya Kara yi da murya cikin rarrashi ya matsoni Yana “Sajeeda yanzu baza ki iya taimaka min ba ki bari nayi sau d’aya sai muyi istigifari an dade ana kwadai ta min ta bayan nan haba matata”

Ya fara k’ok’arin rungumoni na ture shi da iya karfina dan zuwa yanzu ma sai naji tsoron uban yayana ya kamani,gani nake kamar bashi ba

“Kabiru Ina ga ba’a hayyacin ka kake ba a tsawon lokacin da nake tare da Kai nasan baka shaye shaye ballantana nace ba’a hayyacin ka kake ba,a iya sani na ka na da ilimin ka daidai gwargwado ka san abinda ya ke daidai da wanda yake haramun, bazan tab’a maka biyayya na Sabawa Mahallicina ba Ina mai rokon ka idan a hayyacinka ka ke wani ne ya baka shawara ka zo ka neme ni ta baya,ka gaggauta rabuwa da koma waye dan so ya ke ya Kai ka halaka”

Daga haka na nufi Kan gado na na dauki zanina na daura nayi hanyar fita daga d’akin ya hau kwalla min kira Yana

“Sajeeda Sajeeda karki sake ki bar d’akin Nan

Ko juyawa ban yi ba har na bar d’akin har lokacin ban daina mamakin sa ba.

Koda na fito dan karamin palon namu fitila na kunna idona ya sauka akan agogo naga karfe uku na dare na zauna akan kujera tare da dafe kaina jikina har rawa yake bansan tunanin ma da ya Kamata nayi ba.

Na kasa yarda da abinda ya faru yanzu a daki,na kasa yarda mijina uban yayana da shekarar mu Ashirin da biyu da aure da arzikin Yara biyar har mun aurar da Yar mu ta fari Nusrah shi ne yau dare daya zai nemeni ta baya wai ya dade yana san yayi gwaji an ce Masa yafi dadi har waye zai ce wa Kabiru ya gwada abinda Allah ya haramta.

Sosai na zurfafa a tunani bansan tsawon lokacin da na d’auka Ina saka da warwara ba,sai Kiran sallah ne ya katse min tunanin da na tafi.

Mik’ewa nayi na koma d’akin.

A kwance na ganshi Yana dan girgiza kafarsa da alama ba Bacci yake ba idonsa biyu.

Bandaki na shige na daura alwala na fito har lokacin Yana kwance bai motsa ba,nasan fushi yayi,da ace wani abin na Masa da har zai yi fushi dani da sai na bashi hakuri,amma ni nasan ba laifin da na masa bazan tab’a masa biyayya a sabon Allah ba ba muyi haka tun kuruciya ba sai yanzu da muka Manyan ta,tsawon zamana dashi ban tab’a hana shi hakkin sa ba Koda kuwa fada mu ke amma dai yau na bijire masa dan bazan iya Sabawa Allah ba,
tsigar jikina har tashi yake idan Ina hararo yanda wai zai sadu dani ta baya.

Sallah nake amma na kasa yin sa a nutse sabida tunanin da ya dankare min zuciya.

Har na sallame Yana kwance zuwa yanzu sai naji kamar canzo kabiru aka yi bashi bane dan iya sani na baya Wasa da Sallah fushi dani bazai saka wai yak’i fita massallaci sallah ba.

Kasa hakuri nayi da carbina a hannu na Mik’e na zagaya ta wajen da ya kwanta Ina “Abban Nusrah “Abban Nusrah yau ba zaka yi sallah bane”?

“Dama can ke kike saka ni nayi Sallah”?

“Bani nake saka ka kayi sallah ba amma dai bai dace idon ka biyu kana Jin ana sallah ka k’i tashi kayi akan lokaci ba”

Tsaki yayi ya juya min baya.

Zuwa yanzu bazan iya fadan kalar mamakin da nake na sauyawar halin mijina dare daya ba,ga nemana ta baya ga k’in sallah.

Bai tashi ba sai da gari yayi haske ya shige bandaki ya dauro alwala yazo ya tada sallah Yana sallamewa ya fice daga d’akin.

A ranar sukuku na wuni na rasa mai ke damuna dan tunda Abban Nusrah ya fice daga gidan bai Kara dawowa ba.

Har karfe hud’u na yamma Ina zaune zuciyata fal da tunanin muryar Yasmeen ya katse min tunanin da na tafi “Umma ko dai magani zan d’auko miki ki sha”?

Girgiza kaina nayi na aro murmushi na yafa a fuskata sam bana so ta fahimci Ina cikin damuwa,dan nasan sai ta fini ma shiga cikin damuwar, kallonta da nake fuskar kanwata nake gani a fuskarta Margayiya Nuratu damuwar da nake ciki yasa naji hawaye na zubo min.

“Umma kuka kike”?

Share hawayena nayi Ina “ba kuka nake ba Yesmeen na tuna kanwata ne kawai Allah ya gafartawa Nuratu”

“Bata amsa ba illa idon ta da naga ya ciko da kwalla shekara goma kenan da rasuwar kanwata da ta kasance mahaifiyar Yesmeen.

Ruk’onta ya dawo hannuna Ina balain kaunar yesmeen tamkar yanda nake kaunar yayan cikina,
Yesmeen ta Kara siye zuciyata ne daga lokacin da rukon ta ya dawo hannuna,tana da bala’in biyayya da hankali duk wani abu data san ina so bata Wasa dashi bata da burin daya wuce taga ta faranta min ko Yaya ta gani a cikin damuwa itama tayi ta damuwa kenan.

Ko yanzu ma nasan ba lailai taci abinci ba sabida ta gani a cikin damuwa.

“Jeki d’auko mana abinci mu ci dan nasan baki ci abinci ba.

Tura abincin kawai nake ba wai dan Ina gane dandanon sa ba,na daure na hadiye damuwar da nake ciki dan Kar na Kara dagawa Yesmeen hankali.

Koda muka gama cin abincin daki na shige na cewa Yesmeen zan dan kwanta dan itace take yin aikace aikacen gidan Kamar yanda ta Saba kafin Nusrah tayi Aure tare suke aikace aikacen gidan,dan su biyu ne kawai Mata kannen Nusrah duka maza ne,Saifullahi Fahad Hamza da Annur.

Sosai na tsinci kaina a cikin damuwa dan tunda nake da Abban Nusrah bai tab’a fita Yana fushi dani ba dan muna samun sabani zamu shirya,duk da Yana da zuciya nasan hanyar da nake bi na shawo kansa,amma jiya abinda ya b’ullo min dashi ya girmama tunanina bazan tab’a iya barin sa ya neme ni ta baya ba sai kace wasu jahilai.

Karfe goma Sha daya ya shigo gidan fuskarsa a bala’in hade ina zaune a palo Ina jiran dawowar sa dan har yara duk sun yi Bacci.

Ko sallama bai yi ba ballantana ya kalli Inda nake, d’aki ya shige batare da ya amsa sannu da zuwan da nake masa ba.

Da ido na bi bayan sa Ina Kara mamakin fushin da ya ke dani na rashin gaskiya har ga Allah mamaki da al ajabi nake ,mik’ewa nayi na d’auko farantin da na jera abincinsa na bi shi d’akin.

Ko da na shiga a gefen gado na gan sa a zaune yana duba wani abu kamar a takarda ban dai san mai yake dubawa ba”

Na ajiye farantin a gefen teburin dake gefen gadon Ina

“Abban Nusrah Sannu da dawowa”

Bai dago ba ya cigaba da duba takardar Hannun sa

“Abban Nusrah mai na maka kake fushi dani?a iya sanina ba abinda na maka Abban Nusrah wani bak’on al amari ka zo min dashi wanda ni nasan kasan haramun ne,dagani har Kai ba yara bane,ga ta hanyar da Allah ya hallata ma ka neme ni ka samu nutsuwa dani,amma dare daya Abban Nusrah kace zaka neme ni ta baya ta Inda Allah ya haramta kaga dan na k’i bin umarnin ka bai Kamata kayi fushi dani ba dan babu biyayya a sabawa Allah,bansan waye ya baka wanan gurguwar shawarar ba,iya sanina duk wayanda kake mu’ammalla dasu ba mutanen banza bane bansan waye ya ce ma ka gwada ta baya zaka ji dadi ba,taya wajen da ake kashi yayi dadi Ni dai kayi hakuri zan iya k’ok’arina dan na gamsar da Kai amma ban da ta baya”

Sai a lokacin ya dago ya kalleni ya ajiye takarda a gefen pillo Yana “Sajeeda duk abinda nake yi Ina sane tsawon zamana dake Ina ga baki tab’a ganin na neme ki ta baya ba,gwaji ne kawai nake so nayi naji abinda ake ji ba wani abu ba,amma tunda kin nuna bakya so shikenan ba zan Kara nema ba,na dauka duk abinda nake so matsawar bai fi karfin ki ba Zaki iya min”

“Wanan yafi karfina ne Kabiru shi yasa bazan iya ba abinda akace haramun ne ban ga dalilin da zai saka kace zaka gwada ba mu fa ba Yara bane idan muna raye ma wani shekara zaka gan mu da jika”

“Ya isa haka Sajeeda Kinga na Kara neman naki ne yanzu”!?

Shiru nayi Ina kallon sa yaja siririn tsaki ya kwanta ya juya min baya.

Nace masa ga abincin sa yace bazai ci ba.

Wasa Wasa mijina ya fara fushi dani dan naki bari ya nemeni ta baya Wanda zuwa yanzu lamarin nasa ya fara bani tsoro ko Yaya na shawo kansa asan na faranta Masa rai, a madadin yayi ta hanya da ya dace sai naga Yana neman tura jikinsa bayana.

Halin nan daya bijiro min dashi ya matukar daga min hankali dan kullum cikin fada mu ke.

Gashi mu ba Yara ba ballantana nace wani Zan nemi shawarar sa Wanda ni nasan mu ya Kamata ma mu ringa hana wasu ba dai mu ba.

Ko a yanzu da ido nake bin sa har ya gama shiryawa bai ce min komai ba ya fice daga dakin na sauke ajiyar zuciya ina tunanin mafita Kiran Nusrah daya shigo wayata ya katse min tunanin da nake.

Ina dagawa muka gaisa kamar yanda muka saba Inda take sanar min zuwan ta anjima na ajiye mata dambu na saki murmushi Ina sai ta zo.

Na Mik’e nayi waje dan na fadawa Yesmeen zuwan Nusrah duk da nasan kila ma sun yi waya.

Ina fitowa naga Abban Nusrah a zaune a doguwar kujera duk a tunanina Yama fita ashe fitowa yayi ya zauna a palon.

Yesmeen kuma na tsugunne a gabansa tana hada mi shi shayi.

Fitowa ta yasa ta dago tana “Umma Ina kwana”

Zama nayi a gefen shi fuskata d’auke da faraa na hau amsa gaisuwar ta ko kad’an bana so yarana su fahimci wani abu.

Tana gama hada masa ta mike tana bari ta d’auko kofi ta hado min shayin na girgiza mata kai akan ta bar shi sai anjima.

KABIR

Da ido ya bi Yesmeen din har ta shige d’aki ya d’auki shayin ya fara kurba a hankali har ya shanye Yana Jin idon Sajeeda a kansa.

Yana dire kofin ya mik’e yayi waje batare da ya tsaya Jin mai Sajeeda ke cewa ba.

Yana fita ya haye machine din sa bai zame ko’ina ba sai wani hadadden gida da fadar haduwar sa bata Baki ne.

Mai gadi ya riga da ya gane shi hakane yasa ya bude masa ya shige da machine dinsa kansa tsaye ya nufi d’akin saukar baki dake farfajiyar gidan.

Kamar yanda yayi tsamani a zaune ya tarar da Alhaji Rabiu a cikin dakakiyar shaddarsa dake ta kyalli kamar madubi.

Sai da Kabiru ya sama wa kansa wajen zama.

Alhaji Rabiu yace “An dace kuwa”?

Sai da Kabiru ya sauke ajiyar zuciya yace “wlh ba’a dace ba duk ta inda kake tunanin zan biyo mata na biyo mata wlh tak’i bani hadin kai”

Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana “Na fa san irin su haka suke da balain taurin kai Amma idan tasan wata ai bata San wata ba ka tashi muje wajen shugaba mu masa bayani”

Ya mik’e Yana k’ok’arin yin hanyar waje.

Kabiru yayi saurin dakatar dashi yana “Rabiu Ina kaunar matata tunda na yarda zan yi harkar nan zuciyata take cike da fargaba da tsoro ko bacci bana iya yi dan Allah muje wajen shugaba ka fada masa ya duba min ko zan iya yi da wata na samu biyan bukatata ba sai Sajeeda ba.

“Ikon Allah toh wa zaka samo”?

“Akwai yar kanwarta da nake rike da ita da ita nake so na samu biyan bukatar tawa”

“Bani da ta cewa muje daga can muji ko zai yu……

Hmmm

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

WA GARI YA WAYA BY MARYAM IBRAHIM LATEE

Advertisements _____ : WA GARI YA WAYA Rubutawa MARYAM IBRAHIM LITEE (labarin zaman kishin mata …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *