DOGUWAR HANYA CHAPTER 12

Advertisements

_____

*Bayan kwanki biyar*

   Har akai kwanaki biyar Lawuri bata cikin nutsuwar ta sam, komai baya mata dad’i ga yawan yin mafarkai da mahaifiyarta, mafarkin datayi yau yafi komai firgitata, sabida mafarki tae da mahaifiyarta an cinna mata wuta tana ihu tana neman taimakonta amma ita ta gagara zuwa ta tallafeta, ganin haka ya sanya ta soma tunanin lallai tabbas iyayenta basu samu wanda zasu bayar matsayin sadaukarwa ga abin bauta ba,kuma tabbas an kashe su. A bayan gidan take zaune ita da kuyangarta Barbo furanni da ‘yan shuke shuke dake gun suna d’ebe mata kewa, Kuka takeyi na abubuwa kala kala, na farko tunda suka dawo bata k’ara sanya mutanen uku a idanta ba dukansu, tarasa to zamanme take ne, ga wannan yarinyar da wannan tsohuwar ma yaransu sukejiba ga rayuwar takura su a jejin dasuke ko rijiya babu a kogi suke ebo ruwa, a jeji suke kashi, amma wannan komai ya sauya komai basu iyaba hatta yanayin cimarsu daban da tasu, bakinta be saba ba sam! Kallonta barbo tae cikin kulawa tace

“Lawure shugaba ya dace mu koma gida fa, yanzu nasan K’uru da k’uruwa suna cikin damuwa kamar yanda kema kike ciki yanzu” 

“Barbo wataqil ma an kashe su fa, idan fa basu samu sadaukarwa bafa sune za’a kashe, anya Barbo na kyauta kuwa” sadda kanta k’asa tayi

Advertisements

_____

“Nasan Baki kyautaba amma ni inaga kaman zuciyanki kika bi, kuma akwai abinda kikeso agun mazan garin nan” D’agowa tae suka kalli juna

“Inaso insan halinda Iyayena suke ciki, amma banso na koma cen, so nake nasan menene ake ciki bansan ya zan ba” Barbo batace komai ba sega Abu Sufyan akansu, murmushi d’auke a fuskar sa ya kallesu

“Sanunku” shine abinda ya fad’a yana kallonsu, ganin yana murmushi ya sanya ta sakar masa murmushin itama, cikin ido ta kalleshi tana share k’wallan idanta, da hannu ya mata alamar tambaya akan menene yana b’ata fuskar sa akan menene yake sanyata kuka, nanma take ta fahimcesa dan haka da kanta ta masa alamar ba komai lokci d’aya k’walla yana kwaranya daga idanta, b’ata fuska yae yashiga nodding kansa alamar bayaso ta dena, bayan hannunta ta sanya ta share k’wallan daya silalo tana k’ok’arin sanya murmushi a fuskar nan, da hannu ya mata alama akan tabiyo bayanshi, haka suka rankaya har babban parlor gidan, zama yae ya nuna mata da hannu akan ta zauna, zama tae ya nunata da hannu sannan u

Yakai hannunsa  a bakinsa alamar cin abinci yana tambayar ta ko taci abinci? Lokaci d’aya ta fahimci meyake nufi ta shiga gyad’an kanta alamar taci, jinjina kansa yae ya mayar da dubanshi akan TV yana jiran k’arasowar Dawood dakuma Abu huraira yau an sallamaeshi a asibiti mommy ce kawai basu sallama ba acewar su jinin keda sauqin hawa amma saukar se’a hankali, suna nan jigum jigum har sukaji sallamar su, zamanta a gidan na kwanaki biyar ta fahimci cewar idan Akayi wannan maganar shigowane za’ayi haka harta soma haddace yanda suke amsawa dan haka kafij yae aune harta furta

“Amin wa Alaikumussalam” da sauri dukkansu suka kalleta suna mamakin dukda kalmar tayi wani iri abakinta yanda ta iya furtashi, yaushe tazo harta iya ansa sallama hakan nan rad’au a bakinta, Mik’ewa tsaye tayi tana kallon Abu Hurairah tana zuba masa murmushi, kallonsu take shida Dawood har suka k’araso acikin tsakiyan palon, seda tayi jim kantace dasu “Sannunku” kamar yanda Abu sufyan yace dasu d’azu, sannan yanda taga Cyama da Hanifer suna gayarda Baba ladi kullum shine itama tace

“Ina kwana Baba ladi” a zatonta duka gaisuwar ce har Baba ladi, yanzu kam dariya dukkansu suka saka mata suna jinjinawa Hikimomin Allah yanda ya halicemu da magana amma kowa da yarensa dayakeji, Dawood ne yace mata cikkn yarensu dashima akwai banbanci

“Ina kwana, shine ainahin gaisuwar Baba ladi, sunan matar dasuke gayarwa kenan baya cikin gaisuwar kamar ke ai sunanki Lawuri ko?” Gyad’a masa kanta tayi alamar eh yace

“Yauwa to idan zan gayar dake senace “Ina kwana Lawuri” idan fa da safe ne kenan, idan kuma da rana ne ko yamma sena

“Ina wuni Lawuri? Kingane ko?” Murmushi tae tace dashi

“Tokai menene sunanka?” Yana murmushi yace

“Ni sunana Dawood” ya nuna Abu Sufyan da d’an yatsansa yace “wannan kuma sunan Abu Sufyan”, ya qara Nuna Abu Hurairai yace ” Wannan kuma sunansa Abu Huraira”  Jinjina kanta tae cikin gamsuwa tana me k’ok’arin nanata sunayen a bakinta cikin dabaru dan basui daidai ba zaka ka gane dai

“Menene sunan wannan mtan to?” Kallon sufyan yae yace

“Matan nan gidan take tambayar sunansu, wakenan ne?” Numfashi sufyan ya sauke cikin yanga yace

“Cya ne da hanny ko?” Se yaran qanana inaga” kallonsa ya mayar zuwaga reta

“Cyama kenan d’ayar kuma Hanifer” yamutsa fuska tae

“Sunanku wahala ne dashi, yaushe zan koma gidanmu ne” kallon mamaki ya mata amma seyace da ita

“Se sanda kika yarenmu yanzu dai ba inda zaki” batace dashi komai ba se zama datayi a saman kujerar tamkar wata er koyo sanye da jar atamfa d’inkin doguwar riga tayi kyau sedai kanta ba d’ankwali, gashin kan har yau yana nan jiya iya yau

“Yau mamanmu zata dawo fa, yadace dai asan abinyi” Abu sufyan ya fad’a

“Dama Mom batasan komai ba kenan game da abinda ya faru da wannan yaran?”

“Ba abinda na sanar mata sabida banason ta tashi hankalinta sedai ta dawo ta gani, amma me zamuce mata?” Dawood ne ya sharb’e zancen da cewa

“Ba abinda zamuce mata se gaskiya, idan muka damu kanmu akan hakan ai bamu godewa Allah kuma ai daddy yana nan ko, shima ze iya mata bayani da kanshi” jinjina kansu sukai cikin gamsuwa da bayaninsa

Hanifer ce tazo ta sauri taje ta hugging yayanta Hurairah, cikin d’okin ganinsa

“Oyoyo swt bro na, i really really missed u” D’agata yae daga jikinsa

“Halin ya motsa ne se yaushe zaki girma ne wai, yanzu gand’a memiya dake sekizo kina tab’ara anan hadda wani rungumeni ko” ya furta cikin kafeta da manya manyan dara daran fararen idansa, Turo baki tae tahau doddoka k’afa a k’asa

“Allah yaya nifa bana tab’ara, koda kadawo asibitin ma gunka se Yaa sufyan ya hana inje ma ance kana zazzab’i kuma shine kum…..” Shiru tae ganin k’afarsa a d’aure da sauri taje k’asa gaba d’aya ta dafe k’afar a hankali

“Subhanallah bro menene a k’afanka haka” Cikin zafi Abu sufyan yace

“Hanifer please mana, karki ishemu da surutu kaman aku, badai gashi kinga yaji sauk’i ba ki godewa Allah, sabida da abin yazo da tsautsayi se mutuwa kurin ba ajali se rabon shan wahala harbin b’arayi sukayi a gun” Anan ta zube tanata faman kuka duk rararrshin duniya sunyi tak’i tae shiru

“Seda fa nagayawa yaa Huraira ni Banson tafiyar nan sam, na sanar masa hankalina be kwanta ba” ganin haka ya sanya Sufyan ya mata masifa sosai seda tabar parlon hurairah murmushi kawai yae aranshi yana mamakin K’aunar da Hanifer ke masa irin wannan idan da agaban saurayinta tae aita taro match….Lawuri kuwa fuskar nan ta sauya setaji haushin wannan Hanifer ma meye na wank zuwa ki dinga kuka anan koda batajin me suke fad’a ta fahimci lallai zancen dai akan raunin k’afarsa ne take kuka to meye hakan?…..

*************

  Murna sosai ake agidan, ga Abu Huraira ya dawo ga kuma mom ta dawo, General ma yana gidan anyi girke girke kala kala, zakasha mamakin yanda ma akai aikin har wanka da kwalliya yaran gidan sukai idan ka gansu zaka d’auka wani bikinne ya tashi, mazajen sune suka d’akko mahaifiyarsu daga asibiti, Abu Hurairah kam tunda ta ganshi  crouches hankalinta ya nemi tashi

“Menene ya sameka haka ban saniba Na fari?” Ta tambaya tana kallonshi cikin ido, murmusawa yae  cikin nuna ba komai bane

“Mom calm down mana bafa komai bane ba, gogewa nae a k’afa ga gocewar qashi shikenan ne, bakiga nazo d’aukan ki da kaina ba?” Dukda bata yarda ba amma bata tankaba se “Allah ya tsare na gaba” kurun data iya furtawa cikin muruwar jiki.

Kallon wannan Family kurin zakayi ka tammabatarwa kanka cewan lallai suna ciki  tsantsan farin ciki, sedai mom ta k’asa tsayae da zuciyarta gu d’aya akan wannan matan data gani takuma rasa waye ma zata tambaya game dasu, seda ta kalli cyama da hanifa bayan sun kammala cin abinci tace dasu

“Kuje da bak’in nan ciki zamuyi magana da yayyunku” Ba musu suka ja hannunsu zuwa ciki, anan mom ta nemi sanin su waye, abu hurairah shine yae jarumtar gaya mata tundaga farkon maganar har k’arshen sa, Koda ya gama kuka sosai takeyi na tausayawa halin dasuka shiga ciki, gefe d’aya tana godewa Allah akan ni’imar sa na kub’utar da yaranta daga hanun azzalumancen da sharrin jeji, haka aka dinga jajantawa juna sedaga bisani ta kalli Abu huraira tace

“Wannan yaran dakuka saki jiki suka biyoku, ina kuke tunanin zaku kaisu, acikinku wayene ze mayar dasu ga iyayen su, a duk labarin wannan *doguwar hanyar* dakuka d’auka banaji kunzo da hankulanku a yayin dawowa yaya ma zaku daddage ku kwaso mana *maguzawan jeji!!* alhalin bakui tunanin ainahin dalilin dayasanya suka biyoku ba? Kokuma ku dalilin daya sanya ku kuka kwaso mana annoba ba, kai Na fari sarai kasan halina bana d’aukar  ire iren wannan haukan wannan yaran dakuka kwaso sekusan nayi dasu, danni bazan bari ku bisu su koma garin suba bakuma zan lamunci su zaunamun a gidana ba ehe”  kallonta General yae dama yasan a rina yasan halin zafin ta gata itama ta iya kafiya akan hukuncinta

“Ba’ayi haka ba adama, ni ina ganin haske musulunci ne ya janyo yaran nan, itace fa ‘yar sarkin garinsu wannan baiwar tace, kinga alamar zata wuce 16 yrs ne ko’a haihuwa? Batada alamar wayau ma, idan mukai musu rashin mutunci irin haka sesu d’auka addinin mu ba tausayi” idanta harya k’ada yayi ja sanda take kallonsa tace cikin takaici

“Sunsan addini ne? Matsafa ne fa General, kanada dalilin mayar dasu gida ai, ka sanya a d’aukesu da jirgi me saukar angulu a mayar dasu inda suka fito danni dabadan dare bane  ko kwana bazasuyi agidana ba, kanaji fa har ruwan mugun zakin gawar safa suka baiwa sufyan nawa wlhy suda Allah” General dasu sun rasa bakin nata hak’uri duk yanda suka so su d’auki abun da sauki mom ta kafe, se turjiya takeyi me ban mamaki dankuwa basu zata hakan zatayi ba.

**************

   *Washe gari*

Mahaifiyar Dawwod ma kafewa tae akan lallai sesun bar gidan, shi kuma General da asuba yabar gidan kwata kwata yama bar garin zuwa sokoto akwai aikin dasuke da shi acen sokoton, sun yanke shwara korar yaran dazaran su Sufyan suka saki jikinsu akan zasu barsu, tunda sunyi ta lalama abun ya faskara, haka suka nuna wa sufyan kaman ba komai, Abu Huraira dake da ciwon k’afa ma haka ya d’aukesu a mota harsuka isa salon na gayarn gashi da k’afa, a mota yajira seda yaga an gyare Lawuri tsaf! Har baiwar ma ba laifi kud’i sosai aka cake sa dankuwa ko farce basa yankewa, k’afan uban datti, koda ta fito dukse ya soma hangowa hasken fatrata da kyau, yana murna ya mayar da ita gida, kowa yasha mamakin kyawun datayi daganan suka sake wanka ta sanya jallabiyan dake jikinta, washe gari suka shiga sabgoginsu tunda shima k’afar tayi sauk’i alhamdulillah yaji garau, mom kuwa dama shirinta kenan, da driver ta had’asu tace seyayi nisa yabar cikin garin Abuja dasu an yanki jeji ya ajiyesu su k’ara gaba yanda zasu fita harkar gidanta har abada!!!!

*Ni kaina tuna nina ya tsaya cak akan wannan al’amarin! Bana fahimtar yaren mom, anya bata nemi tarwatsa mana farin cikin mu ba kuwa? Ko shakka banayi mun qara lulawa ne wata *Doguwar Hanya* mara b’ullewa………*

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

WA GARI YA WAYA BY MARYAM IBRAHIM LATEE

Advertisements _____ : WA GARI YA WAYA Rubutawa MARYAM IBRAHIM LITEE (labarin zaman kishin mata …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *