WA GARI YA WAYA BY MARYAM IBRAHIM LATEE

: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter One

Sai da ƙarfe ɗaya muka shiga kaduna,
kayan kwalliyata na ciro na kuma gyara fuskata,
Na goggoga turaruka a jikina.
Ina nuna ma direba hanya muka isa har gidan,
Horn direba yayi,ina niyyar sanar ma shi ba maigadi ya saurara,
aka wangale get ɗin,
wani wanda ban taɓa gani ba sai a yau,
shi ya buɗe,
ya kuma iso wurin yana tanbayar wurin wa muka zo.
Ni na yi mishi bayani,
haƙuri ya shiga bani kafin ya soma gaishe ni.
Motar ta kunna kai cikin gidan,
Maigadin ya biyo mu da sauri,
na fito ina kallon yanda aka ƙara gyara gidan,
taɓe baki nayi
ƙila sanda zai yi amarya ya yi gyaran.
Direba ya shiga fito min da kayana,
maigadi ya kira Garba me wanki wanda shi na bari kafin tafiyata Lagos.
Kuɗi na ciro babansu laila ya bani
da naje yi mishi sallama,
ya ce ba lallai ina da kudin nan ba, in riƙe za su yi min amfani.
Nayi ma direba alheri na sallame shi,
Maigadi da Garba suka biyo ni da kayana,
Knocking nayi a ƙofar main falon, daga ciki aka bada izinin shigowa,

Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi
yasa mazauna falon maido hankalinsu inda nake,
Zaune suke a kujerin da suka yi wa falon ƙawanya dukkansu har megidan.
Maigadi da ke bayana
ya tanbayi inda za a ajiye min kayan,
Ƙofar ɗakina na nuna masa,
Zama nayi ɗaya daga cikin kujerun,
kowace da irin kallon da take min,
kafin suka soma min sannu da zuwa,
nayi mamakin canzawar su,
mun gaisa na gaida megidan,
suka bi ni da kallon ita ɗin ce koko wata aka canzo bayan na miƙe zuwa ɗakina.
Key na fiddo cikin hand bag ɗina,
na buɗe dakin
ina cusa kai mamaki ya rufe ni dan ko ina a gyare yake tsaf yana tashin ƙamshi,
Ba alamar an daɗe ba a yi amfani da shi ba.
Jakata na ajiye na cire takalmi,
na koma kofar daki na shigo da jakunkuna na
Basma ce ta shigo abinci ta miƙo min,
na ƙarba tare da godiya cikin wani bala’in mamaki da ya kara rufe ni game da matan na Tahir,
Na dai ajiye nayi alwala nayi sallah,
da na idar na ji cikina yana bukatar abinci,
amma zuciyata bata nutsu in ci wanda aka kawo min ba
dan ni dai ina ta mamakin canjin nasu.
Wani danbun nama da laila ta sanyo min cikin kayana na ci sai na sha ruwa,
canza rigar jikina nayi zuwa wasu riga da wando masu santsi
na koma bisa kujera na miƙe ina latsa wayata.
Tahir ya shigo,
Zaune na tashi ina ƙara gaishe shi ban samu amsawar shi ba illa faɗan da ya lullube ni da shi,
Mutum shi da iyalin sa an nuna masa iyakar shi,
ana ma shi iko da matarsa.
Shiru nayi ina sauraren shi,
zuciya na kawo min wuya,
kamar in ba shi amsa sai na kasa,har ya ƙare
wai kuma sai yana faɗa min ni zan yi girki yau,
komawa nayi na kwanta
Na ce “Gaskiya a gajiye nake ka bar me girki ta kare girkinta in ya zagayo kaina sai in yi”.
Wani kallon mamaki ya kafe ni da shi,
“Saboda me?
“Saboda ba yau zan tare da kai ba”
ba tare da na dube shi ba
na ba shi amsar
wata iska ya furzar me bayyanar da takaici sai ya mike ya nufi hanyar fita,
“Ki tabbatar kin shiga ɗakina kin gyara girkin ba dole bane,
zan zo da take away”.
Daga haka ya fice,
ban ko bi shi da kallo ba dan wani ƙullutun bakin ciki da ya tokare ni,
wannan ita ce marabar da ta dace in samu a wurin mijina, bayan shafe tsawon watanni biyu bana nan.
Na miƙe zan shiga bed room kiran Aunty Kulu ya shigo amaryar kawun Tahir ce wanda ya riƙe shi,
na ɗauka da murmushin karfin hali a fuskata,
ta ce “Mutanen waccan kasar,tun jiya nake neman layin yaki shiga”.
na ce “Ban canza sim ɗin ba Aunty”.
na soma gaisheta,
tayi min fatan Allah yasa an yi karbabbiya.
Na ce “Aunty na ga akwatunana,
an kuma gyara min ɗakina, ƙamshin da naji yana yi na tabbatar da hannunki a gyaran”.
ƴar dariya tayi
“Na zo Kaduna,
ganin Sodangi yana kadunan saboda karatun shi yasa na taho maki da kayanki, gyara kuma ni na ce idan akwai key ya bayar a gyara maki ɗakin,
sai na sa masu aikin gidan malam na nan suka taya ni muka yi gyaran.
“Na kuwa gode Aunty, Allah ya ƙara girma”.
ta ce “Da zan tafi bamu haɗu da Sodangi ba, sai idan Malam zai zo zan ba shi key ya zo maki da shi”.
na ce “To Aunty”
Mun jima muna fira hakan ya mantar da ni damuwar da na shiga daga dawowata.
Ina ɗakina ban fito ba,
sai bayan an yi sallar isha’i sai ga shi ya shigo,
Wai ba zan fito in ci abinci ba?
na ce”Zan fito”

Kowace da ledar ta a gabanta, soyayyar taliya ce da kaza, gamawata sai na miƙe, da niyyar in koma ɗaki,
dakatar da ni ya yi ya ce
“In zauna a yi fira”
suna firarsu ina nazarin maganganunsu, ina kuma ta tambayar kaina ko bayan yin amaryar matan suka samu hadin kai haka, ban dai yarda na sanya masu baki ba.
Goma dai dai nayi masu sai da safe na wuce abuna,key na sanya ma ƙofata, nayi shirin kwanciya na kwanta.

Tunda ta bar wurin hankalinsa ya koma kanta, sai dai ganin idon sauran matan na shi yasa ya ci gaba da zama yana aikin shi a system ɗinshi, duk da ba wani gane aikin yake ba, dan kacokan hankalin sa ya koma kanta.
Basma ta soma tashi,
Halima ce ƙarshe,
ganin shigewar su shima ya miƙe,
har ya ƙare shirin kwanciya ba ummulkhairi ba alamar ta,
wayarshi ya dauko ya lalubi lambarta a rufe ya ji ta, ya yi wurgi da wayar bisa gado,
ya kwanta dafe da goshinsa yana tunanin mafita,
dan zuciyarsa na ba shi shawarar ya share ta kawai ya shiga barcinsa,
Sai dai wata kuma na zuga shi da kwaɗaita masa matar tasa da kewarta da ya yi.
Ya daɗe yana juyi amma barci ya kasa nasarar sace shi zuciyar shi ke azalzalar a samo mata abinda take muradi.
Ganin ba shi da zabi yasa ya mike ,
silifas ya zura
sai ya sauko ƙasa inda ɗakunan matanshi suke,
a hankali yake takawa dan gani yake kamar cikin matan nashi wata za ta fito ta gan shi,
sanin ba wacce yake bi sai dai ki kawo kanki,
amman kuma ya makara dan Basma da Halima mutanen da kishin kwanan da zai yi da ummulkhairi ya hana su barci, musamman ganin yanda ta canza ta waye ta goge kamar wacce ta shekara ƙasar Turai.
A hankali yake ranƙwashin ƙofarta,
gaba dayansu kowace ta leƙo Halima da ke da window ta inda za ta riƙa hango shi ta ɗaga labulan,
Basma kuma ƙofarta ta buɗe kaɗan ta fito.
Tun yana yi a hankali har ya zage yana bugawa,
amma ba alamun za a bude,
cikin matuƙar bacin rai ya juya dan komawa wurinshi,
A sittin Basma ta faɗa dakinta ta rufo ,
sai Halima da ta sha gabansa,
duk da rashin wadataccen haske bai hana shi gane ta ba,
Sun aika ma juna wani bahagon kallo,
dan yasan tsayuwarta nan baya nufin alheri,
yayinda ita kuma wani bakin kishi ya tokare mata kirji.
Zai ratse ta ya wuce ta sha gabansa ta ce
“Lallai wasu matan rako wasu suka yi, ta yamutsa baki.
“Adalci kenan? wace macen ka taba bi dakinta, koko sai ita da yake nata abin na gwal ne”
Murmushin takaici ya yi
“Duk a maganganunki babu karya, wata ko da kanta ta kawo maka sai dai kayi kan dole”.
daga haka ya ture ta daga bake baken da tayi masa a hanya ya wuce.
Wani uban ihu haɗe da kuka ta fasa,
duk wanda ke wurin ya ji sai dai me nauyin barci,
Basma da ke lekensu ta saki labulen tana tsaki,
da itama tayi gigin tunkararsa tare zai gasa masu maganar da za ta hana ta runtsawa,
gara ma Halimar ita kaɗai yake daure wa tsiyar ta,
In ita ce bata san iya abinda zai mata ba.
wata shegiyar kwafa tayi ta sulale bisa gadonta.

Tahir yana wuce Halima saman shi ya hau ya rufe ƙofar, dan yasan wannan bakar maganar da ya yaɓa wa mata bata barinta,
zama kawai yayi ya rasa wane ma irin tunani zai yi.

Ina kwance naji fasa kukan Halima, nasan labarin gizo bai wuce ƙoƙi,sanin zafin kishinta.
Maida kaina kawai nayi na kwantar,
na rufe idona da ƙarfi a fatan da nake barci ya ɗauke ni.

Ina idar da Sallar asuba duk da gajiyar da nake ciki kitchen na shiga,
gudun ƙara wa kaina laifi,
dan abinda na wa Tahir
a daren jiya ban san hukuncin da zai yanke min ba,
ina cikin aikin me masu aiki ta shigo ba Ade bace wata baƙuwar fuska ce a gare ni.
Ita ta kama min bayan ta gaishe ni da girmamawa,
sai da na shirya komai kan dinning,
kafin na wuce ɗakina,
wanka nayi me kyau
na zauna na gyara jikina,
turaruka na musamman da mahaifiyar su laila ta saya mana nayi amfani da su wanda na san Tahir na shaƙa sai ya sukurkuce.

Saƙon ƙamshin da na aika masu yasa su juyowa,
zaune suke matan biyu kan dinning,
sai dai ban san me ya hana su fara ci ba,
kowaccensu kamar dole ta amsa gaisuwar da na haɗesu nayi masu, kamar yadda na yi hasashen zaman nasu ma kamar dolen ce ta sasu yin shi,
Basma na latsa wayarta,
Halima tayi tagumi kawai
fuskarta kamar hadari.
Takun saukowar megidan yasa kowaccen mu gyara zamanta,
kallo ɗaya nayi masa na maida kaina ƙasa na sunkuyar,
dan yadda na ga ya haɗa fuska kamar gobara.

Maimakon ya zauna wurin karyawar,
hanyar fita ya nufa
ban san na shagala
wurin bin bayan shi da kallo ba cike da alhinin wannan cin fuska da ya yi min a gaban kishiyoyi,
sai da naji tashin shewar matan biyu,
wa’anda abinda aka yi min ya yi matukar kayatar da su.
A fakaice na dube su
kafin na maida idona kan kayan abincin zubawa nayi na soma ci kamar bani da wata mas’ala,
alhali ji nake kamar zuciyata za ta fashe,
Basma ta zuba itama ta fara ci,
kammalawa ta sai na miƙe zuwa ɗaki inda nayi ta zubar da hawaye tare da ƙudiri kala kala na yanda zan rama abinda Tahir ya yi min.
Cikin kunci na wuni wanda na lura su kuma ɗanyan ganye suke abinda ban san basma da shi ba dan girman kanta ba ya barinta sakin jiki da kowa.
Megidan dai bai kuma shigowa ba har sai da aka yi sallar isha’i,
Ina ji matan nashi na tanbayar inda ya shiga,
ni kam kokowa nake tayi da zuciyata me cewa in share shi saboda wulaƙancin da ya yi min,
sai kuma me rarrashina da cewa auren kenan
cike yake da ƙalubale,
hakuri shi ne kawai.
Da haka na samu ta rinjayi me min zugar in share shi.
Na fito na karɓi jakar da ya shigo da ita ,
na ratsa saman shi na ajiye ma shi,
sai da na haɗa ma shi ruwan wanka sai na sauko,
ban tsaya inda suke ba
ɗakina na wuce kamar inyi wanka sai dai na miƙe bisa sopa dan wata kasala da naji ta rufe ni.
Hannuna na sa na dafe goshina idanuwana suna lumshe,
Muryar Halima naji a kaina tana shaida min in fito in basu abinci,
da to na amsa mata na tashi zaune ina bin bayanta da kallo,tare da jinjina girman tseguminta,
miƙewa nayi bakina ɗauke da addu’a,
dan faɗuwar gaban da ta
sanyo ni gaba
dan nayi imani ba tsakani da Allah Halima ta shigo ɗakina tana neman in zo in basu abinci sai dan sha’awar ganin wane irin tozarci Tahir zai min yanzu kuma.
Na fito jikina a mace
sun hallara sai megidan ne babu,
wanda kafin in kai ga zama ya soma takowa step ɗin benen,
cikin jallabiya yake me guntun hannu
ƙamshin turarenshi ya cika wurin,
ya zauna na zuba ma shi
sosai ya ci ya dora da jus ɗin da na haɗa masa
wanda na san sosai yake san shi.
Gaban system ɗinshi ya koma ya umurce ni in ɗauko masa phone ɗin sa a daki,
ko da na kawo zama kawai nayi ina danna wayata,
gyaran murya yayi wanda yasa kowaccen mu ƙara shiga nutsuwarta,
“Idan Allah ya kaimu gobe amaryata za ta tare”
Ko da ban sani ba
a tare gabanmu ya faɗi,
dan kallon da kowaccen mu tayi saurin aika masa,
Ba kuma wacce ta furta komai illa Halima da ta yi saurin miƙewa ta wuce zuwa ɗakinta,
Basma ma bata ɓata lokaci ba ta bi bayanta ni nayi saura a wurin,
goma na bugawa kamar jiya na miƙe sai na nufi ɗakina.

Yana ganin ɓacewarta ya janyo wayarshi,
Amarya Latifa ya kira,
Bugu guda tayi picking
tare da fara masa salo da gwalangwaso,
sai da ya gama saurarenta,
ya ce “Idan Allah ya kaimu gobe za ki tare”.
Farin ciki tare da faɗuwar gaba suka ziyarce ta a lokaci guda,
ga koshi ga kwanan yunwa,
jin shirunta ya yawaita ya ce “Ba ki ji na in kashe wayata?
tayi saurin daidaita kanta,
Ina ji Darling, na gode sai dai….
Sai dai me sarkin complain?
“Kayan ɗakina ban gama biyan me kayan ba”.
“To yanzu ya kike so ayi?
“Ka temaka min darling”.
dan guntun tsaki ya ja
“Ba abinda zan baki,
duk kuɗaɗen da nake baki me kike da su?
idan kuma ba za ki tare ba Allah ya bamu alheri”
Kit ya kashe wayar
ta cire ta a kunnenta,
jikinta sai tsiyayar gumi yake
ta kira shi ya ki ɗagawa
ta san ba zai daga ba
Sai tayi mashi txt
ta ba shi hakuri da cewa za ta taren.
Miƙewa tayi ta yayumi mayafi sai ta bar gidan makota ta shiga wurin kawarta, sai dai maman kawar ta shaida mata bata nan
ta tanbayi yaushe za ta dawo ta ce bata sani ba,
tayi mata sallama ta koma gida.

ɗakinta ta shiga ta rarumo wayarta ƙawar tata ta kira sai dai har ta katse ba a ɗaga ba,
sai da tayi kira shida aka daga cikin masifa ta ce “Dan ubanki ina ta kira kin ki ɗagawa dan baƙin wulaƙanci”.
cikin wata irin murya ta ce “Da kika ga ban ɗaga ba da kin ƙyaleni ƙawata”
mugun tsaki ta ja
wallahi dan b……
daga can ta katse ta
“Ko za ki bari sai gobe,
idan na dawo sai muyi maganar?
cikin ƙaraji Latifa ta ce
“Wai kin san cikin masifar da nake?
To wallahi ko da wane ƙato kike, ya saurara maki ki saurari matsalata,
yanzu Tahir ya kira ni,
ya ce “Gobe in tare kin san shi kuma kaifi ɗaya ne, ni kuma ban da komai,abinda zan karya da shi da safe ma bani da shi”.
daga can ɓangaren ƙawar ta ce
To da kika rasa komai buƙata bata biya ba, ga shi yau da bakinsa ya ce ki tare,ai komai ya zo da sauƙi ki bari in dawo da safe.”
tsaki Latifa ta ja
“Wai wane jarababben kike tare da shi, da ba za ki dawo yanzu ba?
dan murmushi me sauti tayi “Ki dai yi hakuri zuwa safiya ƙawata”.
kan dole suka ajiye waya
ba dan latifa ta so ba.

Haka ta kwana kai kawo ta kai gwauro ta kai mari,
tana tunanin inda za ta samu kuɗin kayan ɗaki.

Gari na wayewa ta dosa kiran wayar kawarta Fadila,
sai goma ta diro,
shima daga inda ta kwana ko gidansu bata shiga ba a ɗakinta ta same ta sun aika ma juna kallo,
Latifa duk tayi wani iri
dan zullumi da fargaba da ta kwana ciki,
Fadila kuma cikin kwalliya take ta wani dakakken less sai tashin ƙamshi take.
Bakin katifar dake yashe tsakar ɗakin ta zauna
“Wai meye haka kika bi duk kika tashi hankalinki
ki zauna muyi shawara”
Latifa ta dofana ta zauna
“Ya ba zan tashi hankalina ba,
cikin kishiyoyi fa zan shiga bani da ko katifar da zan jefar a ƙasa”.
Akwai zaɓi guda biyu latifa”
Fadila ta faɗi tana taunar cingam,
“Faɗi muji”
Alh Yahya har yanzu bai haƙura da ke ba,
jiya da abokinsa muke tare, na faɗa mishi matsalarki ya ce ki same shi yanzu zuwa azahar kun gama abinda za ku yi,
ki je ki zaɓi kayan gadon da suka yi maki”
wani kallo latifa tayi
mata “Mu je zaɓi na biyu”.
rafar dubu daya ta ciro cikin jakarta
“Ko in ba ki waɗannan sune gudummuwata muje ki sayi katifa da zannuwan gado,
kayan abinci gidan Tahir ba matsala bane shi ke sayen komai,
kinga ba ƙatuwar da za ta ɗaga maki hanci”.
Latifa ta sosa ƙeyarta da ke mata ƙaiƙayi
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter Two

Da auren Tahir a kaina ba zan iya ba wani kaina ba,
tunda na ɗandana zumar Tahir kowane namiji fanko nake kallonsa,
ba zan iya haɗa jiki da kowa ba.
Muje kasuwa in zabo katifar,
wuyarta dai in samu shiga gidan,
shi yasa na zaɓi ƙarar da duk abinda na mallaka in kaiwa malamai dan su samo min kan Tahir
taɓe baki Fadila tayi
Gayen nan dai ba karamin tafiya ya yi da imaninki ba, mu dai in dai kana da masu gida a rana magana ta ƙare.
Kin sanar wa su mama ko?
girgiza kai ta yi
“Tashin hankalin da na shiga ya mantar da ni muje in faɗa mata
tare suka mike dan gayowa mahaifiyar Latifa batun tarewarta a yau wadda suke ga daki ga daki.

Ina shiga ɗakina bathroom na shiga wanka nayi
dan tun wankan safe ban kuma ba,
gamawata na fito ɗaure da tawul a ƙirjina,
zama nayi gaban dressing mirror ina mulka mai ta jikin mudubin na zura ma cikina ido wanda yake a shafe ba alamar akwai wata halitta kwance a ciki,
tunanin yin shiru da maganar cikin kar in gaya wa Tahir har sai ya bayyana kanshi na yawo a ƙwaƙwalwata.
Turo ƙofar da akayi yasa ni saurin jan tawul ɗin dan suturce jikina da yake waje,
tare da jin takaicin wanda ya yi min wannan aikin,
tsaye yake idonshi fes bisa kaina
“Ina jiranki”.
kalmomin da ya furta min kenan sai ya juya,
ban ko samu bin shi da kallo ba dan wani takaici da naji
tagumi na rafka da hannu bibbiyu,
Me mutumin nan ya mayar da ni,
shashasha ko sakarai?
“Ba ko ɗaya illa hakan shi ne auren”
zuciyar ɗazu ta dawo
ta kwaɓe ni daga zugar da ɗayar ta fara min
Biyayya ga miji ai wajibi ne ga duk macen da ke so ta tsira,
ba ki faɗi ba, ke ce a ƙasan shi,
fito na fito da miji da miji ba inda zai kaiki face halaka.
Har na gama shirina tsaf zuciyar nan tawa tana ta jero min da kalmomin haƙuri da biyayya,
har na miƙa wuya na zaɓi kai kaina ga Tahir
duk da nake tunanin bai cancanci hakan ba,
ganin irin tarbar wulaƙancin da na samu daga gare shi,
wani ƙarin wulaƙancin ma
bai tashi sanin amaryar shi za ta tare ba aure wajen watanni nawa har sai da na dawo.
na gama zura rigar barcina zan ɗora hijabi kiran Aunty laila ya shigo wayata,
sai da na zauna bakin gado sai na amsa kiran,
da murmushi a fuskata,
“Amarya ba kya laifi ta faɗi da sigar zolaya,
wani malalacin murmushi na saki,
“Ki dai gyara kalamanki
ka da amaryar gaskiyar ta ji ki”
dariya tayi ta ce
“Kina raina duk wunin yau,sai yanzu na samu na kira ki”.
muka shiga fira tana bani
labarin yanda suka kasance bayan rabuwata da su.
Kiran Tahir da ke shigowa yana yankewa
yasa hankalina rabuwa biyu,
har ta fahimci ban tare da ita sosai,
ta ce “Ko na shiga lokacin ogan ne?
murmushin yaƙe nayi “Me kika gani?
“Babu komai,mu kwana lafiya”.
Ta katse kiran.

Murmushi nayi na kashe wayar gaba ɗaya,na ajiye ta,sai na zura hijab ɗin,
rufe ƙofata nayi, na ratsa falon har lokacin matan biyu suna zaune wanda na ƙaddara zaman nasu a gulma dan nasan sun riga ni wucewa to me kuma ya dawo da su?
sun bi ni da wani Irin kallo kafin kowacce ta miƙe zuwa ɗakinta cikin matsanancin kishi.

Taɓe baki nayi tabbatar da zargina, dama abinda ya zaunar da su kenan.

Ban same shi falo ba sai na wuce bedroom,
ɗakin ba wadataccen haske,
sai dai ya ɗauki sanyi ƙwarai
ina ƙoƙarin zare hijabina
na jiyo sautin sa cikin wata galabaitacciyar murya
“Ki bani ruwa Please”
jin muryar ya bani tsoro,
dan haka sai na ƙarasa na kunna fitilar ɗakin,
take ya gauraye da haske,
dafe yake da mararsa,
ruwan nayi saurin ɗaukowa na ƙarasa gabansa na miƙa masa
ina tanbayarsa abinda ya same shi,
mararshi ya nuna min,
maganin da na gani a hannunsa ya sha ya bi da ruwan ya koma ya kwanta,
na maida ruwan na dawo na zauna ina jera mishi sannu,
mun ɗauki wani lokaci a haka
kafin barci ya kwashe shi ,
tagumi nayi na zura masa ido har na soma gyangyaɗi,. gyarawa nayi na ɗan kishingiɗa barci yayi awon gaba da ni.
Cikin barcin na riƙa jin nishin shi, tashi nayi da sauri ina ta ma shi sannu
ya ce in yi masa addu’a a ruwa nayi na ba shi ya sha,
to ba laifi ya samu sauƙi har muka yi barci,
fara kiraye kirayen sallar asuba ya farkar damu,
Alwala ya ɗauro ya shiga ibada,
rashin samun isasshen barci ya sa na kasa tashi,
sai da aka tada sallah
na farka na ga yana haramar fita,
daurewa nayi na miƙe na ɗauro alwalar na bada farali.
Ina azkar ya shigo na gaishe shi tare da tanbayar shi jiki
ya ce “Alhamdulillahi”
Na tanbaye shi abinda zai ci ya ce bai sha’awar komai zai dai ɗan kwanta zuwa takwas da rabi zai shiga makaranta.
Na ce “Asibiti ya kamata ka fara zuwa ya ce
“Kar ki damu idan na fito makarantar zan shiga Hospital ɗin”
Da ya kwanta zama nayi na tasa shi,
har ya tashi ya yi wanka ya shirya,
ya yi min kyau ƙwarai cikin shigar ƙananan kaya ga farin glass ɗin shi na rai da rai ya manna,
wurin motarshi na jira shi da ya shiga wurin matansa,
sai da ya shiga ya zauna na zagaya na ajiye masa jakar laptop ɗinsa,
cikin ido ya dube ni
“Ki gyara min ɗakina pls Ummuna”
saukar da idona nayi nayi masa a dawo lafiya sai na koma ciki.

Dakinsa na koma na shiga gyarawa ina mita a zuciyata zai tare da amarya ni zai sa in gyara masu wuri,
ban sa ganda ba ko ganin ƙyashi na gyara ko’ina fes na sanya ƙamshi,
har bathroom na gyaro na wanke boxers ɗinsa na shanya,
na so shiga gidan kawu Attahiru mariƙin Tahir
sai dai na ce bari in bari sai gobe yau in yi masa danbun nama,
ɗakina na koma na gyara jikina da ɗakin,
sai da Halima ta gama girkinta ta fita sai na shiga,
ina aikin danbun naman ina girkin rana na ji ana knocking gane ba kowa kusa yasa na fito na buɗe,
Mata biyu na gani suna kitimillin shigo da katifa
sai namiji ɗaya da ke temaka musu.
Sannu nayi masu
suka ce sun zo shirya ma Latifa ɗaki ne ,
duk da faɗuwar gaban da naji sai na basu hanya tare da yi masu izinin shigowa na nuna masu ɗakin,
ajikinsu suka fito da key suka buɗe suka shiga,
na koma kan aikina,
na fito shirya dinning na samu Halima jikin fridge tana shan ruwa kusa da dinning,
taɓe baki tayi idanuwanta na kan ɗakin amarya,
tsaki me ƙarfi naji ta ja
“Aikin banza ai indai sana’ar mutum kwashe kwashe ba abinda ba zai jajibo ba,
yau kuma me zuwa daga ita sai katifa ya kwaso,
gayyar na ayya”.
Ta kuma jan wani mummunan tsaki,
Ni dai ban ɗago ba ballantana har in gwada na ji abinda ta ce
har na gama abinda nake na wuce ta tana cigaba da maganganunta.

Yamma liƙis amarya ta iso da yan rakiyarta,
kamar yanda lokacin da aka kawo ni ba wadda ta ce mana mu ci kanmu haka suma ba wadda ta yi masu maraba,
har suka ƙare arerewarsu suka tafi.

Waya yayi min ya ce in temake shi inyi girkin dare,
ban ƙi yi ba nayi,
sai dai abinda ya ban mamaki ana fara zaman cin abinci waya kawai ya yi mata sai ga amarya tsagal ta fito idanuwanta fes kan kowa,
ta zauna aka ci abinci da ita.
Wata doguwar mace fara mara jiki,
sai dai tsawo kamar daren sallah.
A raina nake faɗin wani aiki sai namiji,
itama ba yarinya ba ce,
kamar yadda Halima take tsararsa,
nayi imani wannan ma
ba wata tazara me yawa ce a tsakaninsu ba.
Da muka kammala ya zaunar damu yayi mana nasihar zaman lafiya,
lokacin tashina nayi nayi masu sai da safe na wuce ɗakina.

Washegari ban shiga gidan kawu Attahiru ba
dan rashin ganin Tahir wanda yayi sammakon fita makaranta da ya dawo ma wani shirin ya sake yi ya fita,
ya buɗe motarsa
zai shiga kenan
wani mutum da megadi ya buɗe wa gate ya ƙaraso wurinshi yana masa sallama,
musabaha suka yi
ya ciro takarda a aljihunsa ya miƙa wa Tahir,
tanbayar shi vayi ta mece ce
“Sammaci ne yallabai”.
bai ko tsaya sauraren ƙarin bayani ba ya buɗe takardar,
ya shiga karantawa,
ƙarar Halima aka shigar ana bin ta bashin wasu maƙudan kuɗaɗe.
Zufa yaji tana keto masa,
ya sallami mutumin ya rufe ƙofar motar sai ya koma cikin gidan,
amarya Latifa kawai ya samu a falon, ya wuce ta zuwa ɗakin Halima,
daga bayansa take cewa
“Bata nan”
juyowa ya yi,
ya faɗa kan ɗaya daga cikin kujerun falon,
ya dafe fuskar shi da hannayensa,
Latifa da ke tsaye kansa
ta gama kisisinarta
dan taji damuwarsa amma yayi mata banza,
wata kujerar ta zauna dan tayi ma kanta alƙawarin sai taji tushen
matsalar.
Shigowar Halima yasa shi ɗagowa
“Daga ina kike?
ya tanbayeta cikin fushi,
yamutsa fuska tayi
“Unguwa naje”
Ƙwafa ya yi
“Yayi kyau, da izinin wa?
shiru tayi ya jefo mata takardar ta faɗa kan jikinta,
ta ɗauka tana dubawa
gabanta ya faɗi,
ta kalli inda Latifa ta zubo mata ido,
wuce ta yayi zuwa saman shi,
ta mara masa baya,
Latifa ta bisu da kallo har suka shige,
sai ta mara musu baya,
laɓewa tayi tana sauraren yanda Halima ke kuka da magiya kan Tahir ya rufa mata asiri,
shi kuma yana bambamin ya gaji da halinta na cin bashi,
yau har ta kai ga a kawo mishi sammaci,
ta ina ya rage ta da har za ta jefa kanta a masifar ciwo bashi.
Ina take kai abinda yake bata?
sai da Latifa ta gama saurarensu sai ta bar wurin tana taɓe baki
ita kuma ta ta masifar kenan ta cin bashi,
Allah shi kyauta an kuwa tafka asara.
Ɗaki ta koma tana tir da wannan bala’i da Halima ta tarkato a ranar kwananta,
kamar yanda ta zata tunda suka gama da Halima ya fito ya bar gidan,
bai kuma shigowa ba
sai da kowa ya nabba’a a makwancinsa.
Tana ta kai kawo a ɗakinta da taji motsi ta leƙa window,
sai sha daya ya shigo ta ba shi wasu mintoci
kafin ta kare shirinta
na zuwa turaka.
Kwance ta same shi
fuskarshi na duban sama
ya yi matashin kai da hannayensa,
idanuwansa a rufe suke amma ta san ba barci yake ba,
haka yake idan ransa ya ɓaci.
A hankali ta hau gadon gabanta na faɗuwa,
sai tsine wa Halima take a zuciyarta
ita ta taɓo zuciyar mazan
tun jiya take banka ma cikinta magunguna
a matse take ƙwarai amma wannan ƴar sherin ta lalata mata daren.
Ta daɗe amma barci ya gagara daukar ta a buƙace take,
ganin ya juya sai ta mirgina ta haɗe jikinta da nashi,
duk da ya ji abin a matsayinsa na lafiyayyen namiji
sai ya ture ta,
ƙara matsawa tayi ta manne masa
tsaki ya yi ya fara magana cikin fushi
“Look Latifa ki bar ni please”
ya ƙara ture ta
“Ba burinku kullun ku gan ni cikin damuwa ba?
ta fashe da kuka tana faɗin ita meye laifinta
me tayi masa?
Shiru ya yi yana sauraren ta,
a ransa yana jin bai yi mata adalci ba,
laifin wani bai shafar wani,
a hankali ya kai hannu ya ja ta ta lafe jikinsa,
sai dai abinda take son bai samu ba
har sai da ya dawo sallar asuba,ta ja hankalin sa har ya shafa’a da fita duba sauran matansa.

Har nayi wanka na shirya
ban ji Tahir ya shigo ba,
na duba agogo ƙarfe goma.
Na zauna ina duba wayata sai ga shi,
muna gama gaisawa ya fita
har nayi mamakin fitar shi daga shigowa,
ina son tanbayarsa zan shiga gidan kawu Attahiru,
lilliɓina na zura na ɗauko
mazubin da na zubo danbun naman da nayi na fito na rufo ƙofata,
na tako cikin falon,
can jikin ƙofar da za ta fitar da kai cikin falon
idona ya gano mini abinda ya sanya ni juyawa zan koma inda na fito.
“Ina za ki kuma”
Muryar Tahir wanda ke tsaye latifa na gaban shi
kamar za ta faɗa jikinshi,
a kallon da nayi masu sanda na riske su cikin
shauƙi suke
abinda yasa nayi mamakin yanda aka yi har ma ya gan ni,
ƙafata kamar ba za ta ɗauke ni ba, ƙirjina na mini wani zafi saboda kishi.
na isa inda suke,
“Ina za ki?
ya tanbaye ni yana ƙare ma yanayina kallo,
Dama na fito ne in tambayeka zan shiga gidan kawu in gaishe shi”.
wani kallo me kama da harara ya min da idanuwansa masu rikita ni,
“Haka dama ake tambayar unguwa sai an fito?

 

 

 

 

 

 

 

 

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA

Daga

Marubuciyar

CANJIN Ba ZATA

MARYAM IBRAHIM LITEE

*RASHIN SANI AKA CE KE SA KAZA KWANA KAN DAMI Ai LALLAI RASHiN SANi SHi ZAI SAKA WUCE LABARIN NAN BAI KARANTA BA, KO DA KUDINKA SAI DA RABONKA, TAFIYAR TA DABAN CE HAKA MA SALON NA DABAN NE. KARANTA LABARIN
zaman kishin
mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)
AKAN NAIRA 300
Dan biyan kudin karatu
2208124716 Maryam nasir UBA bank
Dan nuna shaidar biyanka 07033400612*

Free fage

Chapter three

Marairaicewa nayi na ba shi haƙuri
“Sai kin dawo” ya faɗi yana harɗe hannayensa a ƙirji, gifta su nayi na wuce har kuma na isa gidan raina a ɓace yake,
Haj Hajara uwargidan kawu Attahiru ta tarbe ni ta kaini wajenta muka gaisa na bata danbun naman da jallabiya da darduma da turare da nayo ma kawun tsaraba na ce a ba Kawu,
ita kuma doguwar riga da darduma.
Ta ce In zo muje in gaishe da kawun,
Sallar walha ya idar
na gaishe shi cikin nutsuwa,
ya amsa yana ta sa mini albarka
ya ajiye kayan ya buɗe cooler ya yi arba da danbun naman,
ya maida ya rufe
ya ce “Adana min naman nan da kyau Haj”.
tana ƙoƙarin ɗauka Tahir ya shigo
ya ce “Na gani zan ci Baba dama na rabu da ganin ka da shi,
ya ce “Dama saboda irinku nake cewa a adana min, daga me kawo min bata nan ina za ka gan shi, iyalinka ta kawo min kuma mu cinye tare da kai”.
Kallon mamaki Tahir ya juyo yana min, dan har ga Allah bai taɓa sanin ni ke kawo wa baban nashi danbun nama ba.
Kawun yana nuna mishi tsarabar da na kawo masa Ni kuma sai
na miƙe na koma sasan Haj, duk da zaman kuramen da muke na gwammace in zauna wurinta da in koma gida.
Sai yamma sosai na koma shima Tahir ne ya kira ni ya ce ba zan dawo ba hala can zan kwana.

Sai da amarya ta kammala kwanakinta wanda har aka so ayi fitina dan Uwargida Halima dagewa tayi da ba wasu kwanakin da amarya latifa za tayi a cewar ta auren da aka ɗaura wata da watanni shi ne sai tayi wasu kwanaki tun yaushe suka tare.
Halima ta karɓi girkin sai Basma da ya zo kaina sai na kaima Tahir tsarabar da nayo masa,
Jallabiyoyi da agogo sai turaren da yake sawa,
gyara sosai nayi wa ɗakin dan abinda na lura da shi yanzu babu me gyarawa,
na wanke boxers dinsa a laundry na sake zanen gado na saka ƙamshi.
Muna kwance dare ya soma nisa wasanninmu muke yi yana gab da cimma burinsa sautin wata ƙara ta ya shiga kunnuwanmu,
Tahir wanda ya kasa barin abinda yake
na raɗa masa “Ba ka ji anyi ƙara ba?
Ƙyaleni ya yi ya cigaba da abinda yake har zuwa lokacin da aka kuma ƙwalla wata,
ba shiri ya raba jikina da na shi ya sauka gadon jallabiya ya lalubo ya zura da sauri sai ya bar ɗakin.
Cikin kasala nima na sauko kayan barcina na mayar tare da hijab sai na bi bayansa,
saukata kasa na fahimci daga dakin basma karan ke fitowa mun kalli juna da Latifa wadda ta fito ita ma a lokacin,
tare muka shiga ɗakin
a dakin barcinta muka same ta Tahir na riƙe da ita tana fizgewa, idanuwanta a rufe da dafe hannunta a kanta tana fadin “Kaina”
matsawa nayi kusa da su ina addu’a ina tofa mata,
ganin ihun nata ya soma sauki shima ya fara addu’ar yana shafa mata.
Da hannu ya yafito Latifa
wadda tun shigowarmu ta maƙale a jikin kofa
ya ce ta zo ta riƙe masa
ƙafafuwanta
hannuwanta da kanta gaba daya ta karkada ta ce ba za ta iya ba tsoro take ji.
bai ce komai ba
umarni ya bani inje saman shi in kawo mishi zamzam,
da azama na fita na dauko sai da na biya kitchen na ɗauko kofi
cikin kofin na juye mishi ina riƙe da kofin yana addu’a a zamzam din,
ya kafa mata kofin da karfin tsiya ya dura mata ba laifi ta sha,
ba kuma a dauki wani lokaci ba ta bingire a jikinsa,
saukar numfashinta ya bamu tabbacin ta samu barci, sai dai ko ya ya Tahir ya motsa za ta kankame shi.
Latifa ta taɓe baki daga inda take tsaye sai kawai ta juya ta bar ɗakin,
maimakon ɗakinta ɗakin Halima ta wuce tana ranƙwashin kofar taji daga ciki tana tanbayar waye
“Ni ce Latifa”
Ta bata amsa a ƙagauce
“Shigo” ta bata izni
zaune ta same ta kan kujera,
“Hala ba ki ji meke faruwa a gidan ba?
a yatsine ta dube ta
“Me kika gani?
“Na ga ba ki fito ba”
Baki ta taɓe
“Me zan fito yi musu su ƙarata can”
ita ma bakin ta taɓe
“Kin hutar da kanki ganin kayan takaici”
kallon da Halima tayi mata ya bata tabbacin ƙarin bayani take nema,
dan haka sai ta gyara zama ta bata labarin ilinbon da Basma tayi dan san kasancewa da Tahir,
anan suka dau lokaci suna la’antar Basma tare da jin dadin bata ma ummulkhairi wannan daren, kafin Latifa ta fito tayi ɗakinta.

A wannan daren zan iya cewa sam bamu rintsa ba ni da Tahir muna tare da Basma ina taimaka masa.
Asubar farko ya nemi temakon megidan da ke makotaka da mu muka wuce da ita Hospital,
Asibiti ce me zaman kanta
ƙwararrun likitoci suka rufu kanta karshe sun tura mu wurin likitan ƙwaƙwalwa dan dama shi ke dubata dan tana fama da wani ciwon kai me tsanani sai dai yana jimawa bai tashi ba.
a gwaje gwajen da likitoci suka yi sun gano ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta wadda suka ce a guji abinda duk zai bata mata rai dan shi zai tayar da ciwon.
Ni da Haj Hajara muke wurinta idan na wuni ita kuma sai ta kwana,
tun ina saka ran ganin yan’uwanta har na cire
sai ranar nan naji Tahir na waya ƙarshe na gane yayan Basma ne abokinsa,anan na fahimci basu gari shi da mahaifinta da matar mahaifin nata dan mahaifiyarta bata raye.

Sai a ranar su Latifa suka shigo Hospital din,
tunanina gaishe da Basma suka zo
ashe wai ganin likita Latifa za tayi,
sai da suka gaishe da Basma Latifa ta fita ganin likita,
fitarta ne Halima ke fadin wai ciwon ido Latifa ta ce tana yi shi ne za ta ga likita,da alama akwai tsegumi me yawa a bada labarin nata.
Kafin Latifa ta gama ta zo har ta ƙosa da zaman ta sallame mu ta tafi,
sai da Latifar ta gama sai ga ta jin Halima ta wuce yasa ta canza fuska daga ƴar fara’ar da ta shigo da ita
bata ɓata lokaci ba Ita ma ta wuce.

Wucewarsu Tahir ya shigo ƴan kwanakin nan
har tausayi yake bani dan yanda yake a tsaye da ɗawainiya me yawa akan
ciwon Basma,
kunun gyada me kyau wanda na daure da shinkafa na tsiyayo masa yana tururi,
ban jima da dawowa daga gida ba, nayo mana girkin sai na damo kunun,
na miƙa masa idan sa na kan Haj Hajara da ta miƙe za ta fita yana ƙara mata godiya kan dawainiyarta,
ya maido dubansa kaina bayan fitar ta
dan murmushi yake min
hannunsa ɗaya kan sumarshi yana shafawa
“Anya kuwa Ummulkhairi zan iya saka wani abu a bakina?
kalaman ban hakuri nayi tayi masa har ya yarda ya karɓa ya kurɓa a hankali yake kurɓa muna fira wadda duk akan ciwon na Basma ne,
shigowar likita yasa na ƙara gyara lilliɓina
sun yi musabaha da Tahir sai na gaishe shi
Sabon bill na makudan kuɗaɗe ya miƙo masa
dan gaskiya a yan kwanakin nan da Basma take kwance ba ƙananan kuɗaɗe ake cajinshi ba.
Na dube shi cikin tausayawa yayinda yake jifana da murmushi
Mug din ya miƙo min
ya ɗauki mukullan motarsa
“Bari inje in sauke Haj a gida ta samu ta ɗan huta, daga nan ina musu transfer kuɗin”.
gyaɗa masa kai nayi
na kuma bi shi a baya har wurin motarsa sai da ya ja motar suka bar wurin sai na koma ciki
wurin Basma wadda kodayaushe cikin barci take.
Zamana ba daɗewa aka turo kofar
wata hamshakiyar mata ce ta shigo biye da ita wani attajirin dattijo ne sai wani matashi da ba zai wuce tsarar Tahir ba
biye da su.
Ba tare da sun kula da sannun da nake yi masu ba suka rufe gadon da take kwance,
hankalin mazan tashe yake kwarai,
cikin mintocin da banyi zaton Tahir zai je gida ya dawo ba sai ga shi ya dawo ban raba ɗaya biyu
ya samu labarin zuwansu ko kuma dama yasan da zuwan nasu,
a take kuma na fahimci su ɗin ko su waye
Mahaifin Basma ne da matar mahaifinta sai yayanta abokin Tahir
Cikin matuƙar girmamawa Tahir ya shiga gaishe su,
mahaifinta ya shiga faɗin rashin jin dadinsa da aka bar masa ƴar sa anan kwance tun soma ciwon ba a yi ƙoƙarin fita da ita da ita waje ba,dan haka ya ce su je ya ga likitan da ke dubata in ta kama ya ɗauke ƴar sa.
Fitarsu aka bar ni daga ni sai matar sai Basma wadda bata ma san sun zo ba,
ganin kamar zamana ba shi da amfani yasa na miƙe na wa matar sallama wadda ke matuƙar ji da kanta
ta amsa da ƙyar,
na fito asibitin na tari me daidaita sahu zuwa gida
mun kusa isa kiran Tahir ya shigo wayata,
tanbayata ya yi inda na shiga na ce “Na tafi gida”
Ya ce Amma ame na tafi
kuma me yasa na tafi ban sanar masa ba.
na ba shi hakuri sannan na ce keke napep na hau.
Faɗa ya fara me yasa ban jira direba ba wani haƙurin na kuma ba shi
ya ce me zan yi a gida bayan ban daɗe da dawowa ba,
na ce na ga yan’uwanta sun zo
ya ce “Haka ne”
Sai ya kashe wayar
nima na mayar da tawa jaka.
Bayan na sallami dan adaidaitan kwandon da na kwaso kwanonina na ɗauka zuwa ciki
na wuce ina amsa gaisuwar megadi da direban da dawowar nan tawa na samu ya ajiye yana kai matansa unguwa,
na zo shiga ƙofar da za ta shigar da kai main
falo muryar Halima da maganar da naji tana yi yasa ni tsayawa haɗe da saurarawa
“Ai in faɗa miki ƙawata wai hidimar da yake da waccan ta kwance a asibitin itama Latifa ta ƙirƙiri ganin likita a asibitin saboda tana fama da ƙaiƙayin ido,
maimakon ta nufi Eye centre a’a wai ita ma can za ta dan asibitin tsada ce da shi ta fitar hankali”
Muryar ƙawar naji ta ce
“Musamman da aka ce abin ya haɗa da ƙwaƙwalwa dole za a ji naira, to wai shi dama mahaukaciya ya kwaso?
Wata dariyar mugunta Halima ta saki
“Oho masa tana can dai kwance ana illata aljihunsa, ita kuma Latifa ta nemi a yanka mata Glass duk da gaya mata da aka yi ciwon idonta
bai kai tayi amfani da Glass ba”
“To ke kuma fa?
ko zama za ki yi ki zuba ido sun zo bayanki suna cin arziki ke an bar ki ƴar kallo”
Haliman ta amsa da “Kin san kuwa waccan matsiyaciyar har ta samu ta sawo labulaye
cikin muryar mamaki waccan ta ce “Wai kina nufin ko labulai bata zo da shi ba ?
Haliman ta ce
“E mana, amma fa ni ki bar ƴan wahala ni ba ta hanyar ciwo zan karbi nawa ba, kai tsaye zan fito mishi ya bani rabona”
Shewa ƙawar ta saki
“Hakan ya yi ta wajena”
Jin kamar suna tahowa ya sa ni shiga da sallama, kawar ce ta amsa suka raka ni da ido
Sannun ku na ce musu na wuce ciki.

Na daɗe kwance a ɗaki ina juya zancen Halima da kawarta game da ciwon idon Latifa,
Text ɗin Tahir da ya shigo
yana gaya min in karɓi girki ya sa ni miƙewa zuwa kitchen a yanda na fahimta ni kaɗai ce a gidan, sai yamma sosai suka dawo Halima ta fara shigowa can sai ga Latifa wadda ta sha Glass ɗinta banda firar su Halima da na saurara zan ɗauka na gayu ne kawai dan ba karamin armashi ya ƙara ma fuskarta ba.

Ana idar da Sallar isha’i Tahir ya shigo,
mun hallara gaba ɗaya muka ci abinci
ina lura da shi ba wani me yawa ya ci ba
hasalima ba shi da walwala da ka dube shi za ka san akwai damuwar da take damun sa yana kuma kammalawa miƙewa ya yi riƙe da mukullansa sai ya fice,bin shi da ido nayi
cike da tunanin damuwar
da ke damun sa.
Ban koma daki ba a falon na cigaba da zama tare da Halima da Latifa,
sai ƙarfe goma ya shigo
nayi masa duk abun da ake masa kafin ya kwanta, yana shan black tea da na haɗa masa idonsa na kan TV Latifa da Halima da ke zaune shiru Halima ta gyara zamanta
“Idan ka kammala ina son magana da kai”
ta fadi sai ta miƙe zuwa ɗaki,
ni da Latifa muka bi ta da ido
shima ya miƙe ya bi bayanta.
Jin shiru shiru raina ya soma ɓaci ganin wannan ai cin fuska ne aka yi min,girkin nawa ya tsallake ni su shige daki a bar ni shanye da baki a zaune, wata zuciyar nata zuga ni da in yi ɗaki
in datse ƙofata
wata kuma na bani haƙuri,
da na saci kallon Latifa sai na rasa wane hali take ciki ita ma kishin ke mintsininta koko murna take da abin da aka min.
Jin tashin muryar Halima yasa mu maida ido wurin
Tahir ya fito a fusace ya haura saman sa,
na miƙe dan zuwa in yi shirin barci Halima ta fito tana cigaba da bambanci
“Wallahi ban zama ka mayar da ni sakarai dan rashin adalci waccan tana kwance kana kisan kuɗi,wata ma ta ƙirƙiri ciwon idon ƙarya dan ta tatseka duk baka damu ba sai ni dan na nemi ka bani kuɗi in kashe matsalar gabana shi ne za ka gaya min bani da tunani to za ka san ban……
Dirowar Latifa gabanta cikin masifa ta katse ta
“Idan kina neman bala’in ki Halima ki kiyaye ni,
ni nan da kika gan ni ba kanwar lasa ba ce,
dama saka ma ciwon idon nawa idanu kika yi?
kina baƙin ciki an mini magani,
to sai dai wallahi ya kashe ki”
Nan suka dirar ma juna
kamar za su cinye kansu
ni dai da na gama shirina
tsayawa nayi jiransu su gama dan kar in je in samu ya rufe kofa
dan yanda na ga ya fusata,
ba zan rasa wadda za ta yaɓa min baƙa ba na je turaka miji ya rufe kofa.
Ganin basu da niyyar dainawa na zo gabansu ina basu hakuri ba wadda ta saurare ni kamar yadda na zata
maganar da Halima ta faɗi ma Latifa ita ta raba faɗan
An zo tsiya tsiya ba dole a kirkiri ciwon karya a samu na sayen kayan ɗaki,
ga shi nan har an fara samun na labulai.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *WA GARI YA WAYA**

Daga

Marubuciyar

*CANJIN Ba ZATA*

MARYAM IBRAHIM LITEE

*RASHIN SANI AKA CE KE SA KAZA KWANA* *KAN DAMI, Ai LALLAI RASHiN SANi SHi ZAI SA KA WUCE LABARIN NAN BA KA KARANTA BA*,
*KO DA KUDINKA SAI DA RABONKA, TAFIYAR TA DABAN CE HAKA MA SALON NA DABAN NE. KARANTA LABARIN*
Zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta).

AKAN NAIRA 300
Dan biyan kudin karatu
2108124716 Maryam nasir UBA bank
Dan nuna shaidar biyanka 07033400612*
a chapter 3 na yi mistake wurin sa No Account dan haka ga yanda take nan yau na gyara

Free fage

CHAPTER Four

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

 

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

 

Ɗauke wuta kawai Latifa tayi ta juya zuwa ɗakinta ta rufo ƙofar da karfi,
na wuce a hankali na haura sama.

Kamar yanda nayi zato ya kashe duk fitilun wurin sai hasken bed side lamp ita taimaka mini na hango sh gefen
gado ya yi tagumi da duka hannayensa.
Ina shirin zama wayarsa tayi ƙara
ya kai hannu ya ɗauka
cikin dakusashshiyar murya ya soma magana
“Kana ji na Usama? al’amarin Halima yana neman sha mini kai,
ina duba mata saboda ganin al’amuran da muka keto ni da ita har muka zo yau.
Amma ita bata sani ba
gani take isarta ke sa ni kyaleta”.
ya yi shiru ya ɗan saurara
kafin ya cigaba
“Wallahi nake gaya maka
bayan fama da nake da ciwon Basma
Latifa ma na fama da ciwon ido, wai ciwon shi ya zama abun kishi wurin
Halima, yanzu ta tsare ni ta nemi in
bata wasu ubannin kuɗaɗe tun da ina kashe kudi kan matana.
Ta bar ni ma in ji da damuwar da nake ciki
yau tun isowar mahaifin Basma yake nuna mini gazawata kan ciwon ƴarsa”.
Shiru ya yi ya cigaba da saurare
sun ɗauki lokaci yana bayyana ma wanda suke wayar damuwar da yake ciki,
a raina ina ta tunanin ko ya manta ina dakin.
Da ƙare wayar tasu ajiyeta ya yi ya koma ya rafka tagumi tashi nayi daga inda na lafe gabana na harbawa zuwa inda yake ƙirjina na haɗa da bayansa sai na rungume shi, cikin sanyaya murya na riƙa ba shi hakuri.
Mun ɗauki wani lokaci a haka ba tare da ko motsi ya yi ba, har na sare na janye hannayena zan koma inda na taso in kwanta, na ji ya waiwayo gaba ɗaya sai ya rungume ni, kwanciya ya yi ina maƙale a jikinsa sai ya ja mana bargo.
Zuwa safiya nayi duk abin da zan yi dan ganin na rage mishi damuwar sa kuma sosai na samu nasarar hakan.

Da zai fita sallar Asuba ma umartata ya yi da kar in koma ɗakina
nan na zauna bayan na idar da tawa sallar,
nayi azkar da karatun Alkur’ani har gari ya soma haske.
Da ya shigo kwanciya muka kuma yi da nayi yunkurin zare jikina in tashi dan in je in haɗa abin karyawa sai ya kuma maƙale ni dole na haƙura,
sai tara da rabi muka tashi kofin shayi guda ya ce in kawo masa sai ƙwai cikin sauri na kammala na kawo masa dan ban ga alamar zai sauko ba, su ma matan ban ga kowa ba,
Haɗa mishi nayi na daidaita mishi zafin hada danbun naman da nayi na haɗo masa.
Sai na koma kitchen
su ma mutanen gidan ruwan zafi na dafa musu na soya kwai na jere komai bisa dinning.
Ɗakina na wuce wanka nayi na gyara jikina ina ƙamshi, doguwar riga ta atamfa da ɗinkin ya zauna mini dam a jikina
na saka nayi ɗauri me kyau sai na fito
Latifa na hango zaune a dinning tana break past
na ƙarasa ina mata ina kwana ban tsaya ba na wuce dan yanda na ga tana bi na da kallo,
saman na haura na samu Tahir yana aiki a system
ɗinshi,murɗa ƙofar da sallamar da nayi yasa shi ɗago kai ta cikin farin Glass ɗinsa yana kallona
tafukan hannayena na sa na rufe fuskata, neman wurin zama nayi ba tare da na yarda mun haɗa ido ba ta wutsiyar ido na saci kallonsa karaf idanuwanmu suka haɗu
tsadadden murmushinsa yake jifana da shi.
Nima murmushin nayi dan tsantsan kyan da ya mini ya sha wanka cikin jallabiya me guntun hannu, mun jima zaune shiru shi yana aikinsa ni kuma ina famar ƴan tunane tunanena na dalilin da ya hana masa zuwa asibiti yau dan sammako yake yi,
kamar in masa maganar zuwa asibitin dan makaranta ba kullun yake shigaa ba,
sai dai na ja bakina.
Ƙarfe sha biyu na sauka dan ɗora abincin rana
a kitchen ɗin ya same ni
ya ce mini zai leƙa asibiti,
nayi masa fatan dawowa lafiya tare da yi ma me jikin addu’ar samun sauƙi.
Bai shigo ba sai da aka yi sallar Isha’i gidan daga ni sai Latifa muka wuni wadda na lura cikin nishaɗi take, a kuma ƴan wake waken da take
na fahimci zaman ɗakin da Halima take a yau ya yi matuƙar yi mata daɗi.
Yana cin abinci ya ce mu shirya ni da Latifa muje asibiti mu duba Basma,
take annurin da ke kan fuskarta ya ɓace ta yamutsa fuska sai dai iya bariki irin nata sai tayi saurin daidaita kanta.
Kowaccenmu ɗakinta ta shiga dan shiryawa,
duk da takaicin da abin ya bani fitowata da na samu Latifa ta kame gaban mota kuma girkina sai da na kusa dariya,yanda ta shafa hodar garin sauri a zo a faɗa gaban mota
dan tsayawa nayi,
da wani irin kallo ta dube ni tana taunar cingam ɗin da baka raba ta da shi, ta gyara zaman Glass ɗinta
“Lafiya malama kika tsaya mini a kai?
Ikon Allah na faɗi a raina bari ka ga matar nan
shiru shiru fa ba tsoro ba ne gudun magana ne
sai da na rama kallon banzan da ta mini na ce
“To ina ruwan kallo da gajiya?
har da buɗe baki tayi dan da alama ta ji mamakin mayar mata da nayi,
“Amma dai kar ki ce rashin kunya kike so ki mini? ta faɗi cikin hayayyaƙowa.
“Rashin kunya kuma?
na tanbayeta cike da mamaki
ta ɓalle murfin za ta fito
muka ga fitowarsa,
“Ke fa lafiya ba ki shiga ba?
ya tanbayeni da ya iso
“Ba komai yanzu zan shiga”.
na ce ina kama murfin bayan motar
sai da na shiga na zauna
shima ya zagaya ya shiga,
ko zama Latifa bata bari ya gama yi ba
cikin faɗa ta ce
“Darling ka ja wa yarinyar nan kunne ta fita harkata”
da mamaki ya dube ta
“Wace yarinyar kenan?
za ta fara bambami
ya ce “Look malama
meye a fuskarki?
cammon ki koma ki goge
abin da kika yaɓa”
wani kallo ta dalla mishi kamar me shirin fashewa da kuka,
ta ɓalle murfin ta fita ta buga shi da ƙarfi kafin ta wuce ciki kamar me shirin tashi sama.
Mun zauna kusan minti goma ba Latifa ba labarinta, ya kira wayarta bata ɗaga ba
Ƙwafa ya yi ya ce mini
“Dawo gaba”
ba bata lokaci na koma sai ya ja motar muka bar gidan, muna tafiya bisa hanya babu mai magana da wani sai radiyon motar da ya kunna ya tsaya a hanya ya sayi
kayan marmari.
Mun shiga ɗakin da Basma take,
zaune muka same ta tana shan wani abu a mug
wata mata da ta fara shiga shekarun girma ke tare da ita, ita ɗin ce kuma tayi mana maraba
dan Basman daga ni har ogan ba wanda ta amsa sannunsa,
mun jima Tahir ya tafi office ɗin likita
sai da ya dawo muka yi musu sallama.

A hanya mun kusa gida na ji tambayar Tahir
“Me ya haɗa ki da Latifa?
Ban tunanin jin tambayar ba dan haka na so daburcewa
sai da na daidaita nutsuwata sai na mishi
bayanin yanda muka yi da ita,
tsaki ya ja “Ba na so kina biyewa ke ma ana mini faɗa a gida”.
haƙuri na ba shi,
mun samu falon ba kowa
Latifa uwar iya yau dai ba zaman gulma tana ɗakinta.

A ranar ko da na kwana turaka ban leƙo ƙasa ba
Mai aiki nayi ma waya na ce ta samar musu abin karyawa,
dan Ogan ya ce min yana azumi kuma ranar ma ba zai shiga makaranta ba.
Ina zaune yana shiri zai fita muna ɗan taɓa fira
turo ƙofar a kayi,
gaba daya muka kai duban mu ga ƙofar,
Latifa ce tayi ɗaurinta na ture ka ga tsiya tana famar taunar cingam ɗinta na fama,
baki na taɓe yayin da ogan ya dube ta cikin hasala
“Lafiya za ki fado wa mutane wuri ba sallama ba neman izini”
Noƙe kafaɗa tayi irin nasu na ƴan duniya
“Magana nake son yi da kai”
Shi ne ba ki haƙuri in fito
daga kin san akwai wata a ciki, ko na taɓa fita ban shiga ɗakin wata ba?
“To ai magana nake son yi da kai ina ruwana da wata ko……
“Stupid Latifa”
ya faɗa da ƙarfi
wanda har ni sai da yan hajina suka kaɗa,
Ki fita kuma kika sake gwada mini irin haka matakin da zan ɗauka kanki”
ya yi ƙwafa
ta juya fuu!
ya bi bayanta da mugun kallo.
Tashi nayi na soma gyara wurin na wanko toilet,
kasa na sauka zuwa ɗakina, wanka nayi zuciyata cike da tunanin wannan rikice rikice na wannan gida,
sai da na ƙare shirina sai na koma falona na kunna TV na kwanta,
murɗa ƙofar da aka yi yasa ni daga kai
Tahir ne bai shigo ba
sosai yana daga tsaye
yasa hannunsa aljihu
kuɗaɗe ya ciro masu kauri ya ajiye min a hannun kujera,
godiya nayi masa sai ya juya na bi shi da A dawo lafiya.

Halima ce ke da girki a ranar sai uku na fito dan yunwar da ke sakaɗata
ganin wayam teburin yasa na gane bata girka komai ba,
kitchen na wuce
Latifa ma ciki na gan ta
sai mai yin aiki Indo,
ko da nayi sallama bata amsa ba,
a yanda na gan ta na gane daga unguwa
ta dawo kuma da alama tana tare da shegiyar
dan sai masifa take wa Indo, me yasa da Halima bata fito ba ita bata girka
komai ba, ita dai sai haƙuri take bayarwa.
Indomie na dafa
da ƙwai biyu na juyo a
flate, kallonta tayi sai ta ja tsaki raina ya sosu amma sai na danne na sa kai na bar kitchen ɗin,
a dinning na zauna
ina kallon wani frogramme da ake gabatarwa a tashar Arewa 24 a ƙatuwar flasmar da ke falon.
Latifa ta fito da nata abincin a hannu
ɗakinta ta wuce ni
ma da na kammala nawa ɗakin na koma txt na tura wa Tahir zan shiga gidan Kawu Attahiru
shi nake so in gaido dan
ya shigo garin duba Basma.

Washegari da safe ina gama karyawa ɗakina na gyara nayi wanka da kwalliya cikin wata doguwar riga mara nauyi
sai na bi lafiyar gado,
barci me daɗi na shiga yi
har ina mafarki.
Kukan wayata da na riƙa ji yasa ni kai hannu na lalubota a hankali na buɗe idanuwana,
sunan maman ummi matar yayan Tahir kuma wadda muka fi shiri lokacin da na zauna gidan su Tahir da na gani kan screen ɗin yasa ni yunkurawa ina ɗaga kiran, bayan sallama gaisuwa ta biyo baya
da tambayar jama’ar gida
ta ce “Yanzu fa za mu ɗauko hanyar garinku”
ɗan murmushi nayi
“Lafiya?
ta ce “Za mu zo duba kishiyar ki ne”
na ce “Allah ya kawo ku lafiya, kuna da yawa ne?
ta lissafa mini su shida ne,yayyen Tahir biyu sai matan yayyensa dan kowa an ɗauko matarsa ɗaya.
Kai na gyaɗa “Tahir kuwa ya san da zuwan”.
“A’a kam dan an ce ba a samu wayar tasa ba”
nayi masu addu’ar Allah ya kawo su lafiya”.
Muna ajiye wayar sai na nemi barcin da nake ji na rasa, miƙa nayi sai na fito zuwa kitchen ban samu kowa a falo ba sai Indo tana daɗa gyara shi,
ina shiga kitchen din
sai ga ta ita ma ta shigo
“Haj za a taimaka miki ne?
ta tambaye ni da girmamawa,
kallonta nayi “E jama’ar gidan su oga ne za su zo”.
dan murmushi tayi
“Ya kamata kam a shirya musu abincin tarba”
Fridge na buɗe ina kallon abin da ke ciki nama ne nau’i daban daban sai fitar da sanyin raɓa yake.
Naman kaza na shiga fiddowa wanda kafin ya ƙare ake daɗa lodo wani
su ma dai ƴan’uwan mai gidan bari in dafa musu
su ci yau ɗaya su ma su dangwali arziki,
ba sai waɗannan matan da ya tara ba ya kawo kullun su ci su na ma jama’a kallon banza.
Indo na umurta ta ɗora jallof me ƴan ciki da kayan lambu ni kuma na ɗora pepper chicken.
Cikin sauri muke aikin
dan in samu mu kammala cikin lokaci,
ɗaki na koma nau’in maggi da nake amfani da su curry wanda na riga na bare,
sai kayan ƙamshi da nake haɗawa citta da karanfani da kimba da tafarnuwa,
ina amfani da su wurin girkina ba ƙaramin ƙarawa girkina ƙamshi da daɗi suke ba
su na ɗauko,
Aunty Kulu ta bani wannan dabarar ta ce kar in yarda kishiyoyina su san da kalar kayan dandanon da nake amfani in bar su ranar girkina in haukata su da dandanon girkina.
Na koma mun ci gaba da aikin, muka tsinkayi muryar Halima
“Indo aikin kika soma ban fito ba, me kike yi
haka gida duk ya……..
haɗa idon da muka yi yasa ta hadiye sauran maganar,
sai ta ƙara tamke fuskar
dan ita kullum cikin tsare gida take.
Bata amsa sannun da nake mata ba illa illa Indo da ta duba
“Wa ya ce ayi mini girki ban fito ba?
shiru muka yi duk kan mu
“To aji a sani duk wata kankanba da mutum zai yi ya tsaya iya kan wanda ya kwaso shi”
Tsayuwa na gyara
“Da yake ma mutum ɗin ba shi ake wa girkin ba,
ko kuma isar har ta kai
kitchen ɗin ma a hana
mutane shigowa?
gaba daya ta taso mini kamar za ta sa duka
“Kar ki ce za ki yi mini
wallahi duka zan miki”.
Idanu na buɗe “To!
duka?
ta ce “Me kike nufi?
shiru nayi ta cigaba da bambaminta kafin ta fita fuu! ɗakinta ta zarce ta kira Tahir kan ya ja min kunne me ya kai ni shiga
kitchen ina mata girki a ranar girkinta.
Hakuri ya bata ya ce
“Kila taimaka miki tayi ta ga matsayinki na babba”
To ban bukatar taimakon ka gaya mata,
kuma sai na ji ba’asin
rashin kunyar da tayi mini d…….
Tsawa ya daka mata
“Kar ki kuskura ki koma wurin yarinyar nan indai kin kawo ƙara wurina dan ina gaba da ku”.
Kit ya katse kiran
gane ɓacin ransa ya sa ta kasa komawa kitchen ɗin,
tsaki ta ja ta cillar da wayar ta zauna tana huci.

Shi kuma wayata ya shiga kira sai dai har ta karaci rurinta ta katse ba a ɗagawa, ransa ya ƙara ɓaci na san rashin kunyar da na wa Halima shi yasa na ƙi ɗaga kiransa.
Ƙwafa ya yi
“Zan koya miki hankali”

Mun kammala girkin ya yi mini yanda nake buƙata
bayan babbar cooler da na cika musu da pepper chicken,na kuma cika wata madaidaiciya wadda nufina zan bai wa maman ummi ta kai ma mahaifiyar Tahir.
Duk wani drinks da ke gidan sai da na daukar musu kalarsa
Indo ta fitar mini zuwa wurin mota,
Daki na koma na gyara kaina na fito cikin dogon hijab me hannu, wayata sai sannan na ɗauko ta a ɗaki ban ko tsaya duba ta ba na jefa ta jaka,
Indo na wurin motar har lokacin sai da tayi mini fatan sauka lafiya sai ta koma ciki, tana me murna a ranta yau Allah ya ceceta da zama da yunwa dan girkin Halima kowa sai ya ji jiki kafin ta gama gara mata girkin Latifa duk da ba daɗi,
dan sam bata iya girki me daɗi ba a ƙalla za ta gama cikin lokaci.
Basma kuwa ita take sakarwa girkin duk da sanin da tayi mai gidan ba ya so
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *WA GARI YA WAYA*

Daga

Marubuciyar

*CANJIN Ba ZATA*

MARYAM IBRAHIM LITEE

*RASHIN SANI AKA CE KE SA KAZA KWANA KAN DAMI* *Ai LALLAI RASHiN SANi SHi ZAI SA KA WUCE LABARIN NAN BA KA KARANTA BA, KO DA KUDINKA SAI DA* *RABONKA, TAFIYAR TA DABAN CE HAKA MA SALON NA DABAN NE. KARANTA LABARIN*
Zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta).

AKAN NAIRA 300
Dan biyan kudin karatu
2108124716 Maryam nasir UBA bank
Dan nuna shaidar biyanka 07033400612*
A chapter 3 na yi mistake wurin sa acc no to ga yadda take

Free page

Chapter five

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1020959516678

 

Mun shiga Hospital ɗin,
a ɗakin da Basma take sai yayyen Tahir na samu Yaya lawal sai Baban Ummi,
na gaishe su da girmamawa kafin na
gaida me jikin da masu jinyar ta.
Su yaya lawal su ka ce mini matan ai har sun shiga mota,
direba ya shigo da abincin da na kawo musu
n ce “Ai kuma ga abinci na kawo maku”
Yaya lawal ya kira matarsa a waya
ya ce su dawo na zo,
sai ga su da murnar su
muka tari juna wurin da suka yi sallah muka koma suka zuzzuba abincin aka zuba wa mazan matar yaya lawal sai fadin irin canzawar da nayi take yi da a hanya ta haɗu da ni me wuya ta yarda ni ce.
Sun gama suka yi harama da maman Ummi muka jero zuwa mota take ce mini
“Ba ƙaramar lada kika samu ba ummulkhairi dan da da bakar yunwar mu za mu koma, saboda yanayin hanya muke tsoron tafiyar dare.
murmushi nayi na damka mata cooler na ce ta kai wa Hajiyar su Tahir na ƙara da cewa ya aka yi Tahir bai zo ba?
ta ce sai da suka zo aka kira shi ya ce baya kusa ya je kaciya in muka ce kuma a tsaya jiransa dare zai yi mana.
Sai da duk suka zauna
na ajiye musu 10 thausand na ce su sha mai sai godiya suke na juya,
ban koma wurin Basma ba inda direba ke jirana na isa da shigata ya ja motar sai muka bar
Asibitin.

Sai dare Tahir ya dawo
ina ɗakina ko abincin daren Halima ban fito ci ba, waya nake tayi da ƴan’uwana da su laila da ƙawata Hafsat
Latifa ta leƙo ta ce mini
ana kirana a falo.
bin bayanta nayi da kallo bayan ta fice kafin na miƙe hoda na murza na fesa turare sai na fito,
Halima ana zaune ana kaɗa ƙafa Latifa ma na zaune haka zalika Ogan.
Gaishe shi nayi ya amsa cikin dakewa dan haka a hannun kujera na ɗofana mazaunaina,
kallona ya yi “Me yasa dan Halima tayi miki maganar abinci sai kika ɗauke abincin gidan yau aka wuni da yunwa”,
faduwar gaba na ji jin zancensa,sai nayi shiru ina kakkaɓin jin wani rainin hankali da za a yi mini, cikin ƴar hasala ya ce “Ba ki ji ina miki magana”
kawai sai na ji hawaye sun cika mini ido tausayin kaina ya kama ni, kallonsa nayi sai muka haɗa ido
hawayen suka gangaro mini ban damu da in share su ba na ce
“Ni dama ba abincin gida
nake yi ba, ƴan ƙanƙara da za su zo nayi mawa
Kuma ina gamawa na kai musu Hospital”
lura nayi jikinsa ya yi sanyi su kansu matan sun yi laƙwas.
Shiru falon ya dauka wayarsa ta dauki ƙara
ya ɗauka cikin girmamawa ya soma magana “Haliyata”
a yanda na fahimci wayar ta su labari take ba shi na aiken naman da nayi mata, ko
ta nemi ya bani wayar
ne sai ya miƙo mini
godiya tayi ta mini da sa albarka bayan na gaisheta,
muna gamawa na miƙe na ajiye mishi wayar kusa da shi na wuce ɗakina ina ta kakkaɓin wulaƙancin da aka so yi mini cikin kishiyoyi.
A daren na daɗe barci
bai ɗauke ni ba ina ta tunanin irin wannan zama da kuma ƙalubalen da ke cikin auren nesa
yanzu da a garin mu nake inda iyayena da ƴan’uwana suke da gari na wayewa sai in tafi gidanmu ko gidan daya daga cikin ƴan’uwana
na san dai ko ban faɗa masu damuwar da ke
damuna ba a ƙalla za su sanya ni cikin farin cikin
da zai mantar da ni damuwata.
Hausawa suka ce ya kamata auren na gida ko
ba ka ci ba ka ga uwarka.
Rashin samun barci da ban yi ba sosai yasa ni makara daga sallar da nike tashi a karshen dare
ina yi inda nake raka’a biyu, a sujadar karshe ina karanta (LAILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN)
Sau 41 sai in faɗi bukata ta in dago in yi tahiya in sallama.
Gari na wayewa kuwa na kira Babana da mamana
na gaishe su
Tahir na shigowa na roke shi in shiga gidan Kawu Attahiru,
Sha daya nayi na fito na
tafi sai da na fara gaida kawun sannan na koma wurin Haj,
na dai zauna ne kawai daga ita ba magana take ba, sai mai aikinta da ta shigo muka yi ta hira.
Wuni nayi zungur har aka yi sallar magrib,
na idar da sallar isha’i Hajiyar ta leƙo ta ce in fito in ci abinci a kasa na zauna bisa carpet na kusa kammala cin abincin muryar Tahir da naji ta sa ni daga kai fuskarsa haɗe take kamar hadari maida kaina ƙasa nayi
gaishe da Haj Hajara ya yi sannan ya dube ni
“Zaman me kike yi har yanzu?
ƙara sunkuyar da kaina
nayi ina shirin tashi
Hajiyar tayi magana
“A’a Sodangi ka bar ta ta ci abincinta, nan ma ba gida bane?
Bai yi magana ba
illa harɗe hannayensa da ya yi a kirjinsa,
kallon da yake bi na da shi yasa jikina ɗaukar rawa na san ran ƴan mazan a ɓace yake,
na kai kwanukan kitchen na dawo,
sannan nayi mata sai da safe har na fice ban ga tahowarsa ba.
Ga mamakina da shigata falon matan na samu duk kan su hada Basma wadda bani da labarin dawowar ta ina tunanin bayan fitata aka dawo da ita,
gaishe ta nayi tare da yi mata ya jiki
ta amsa da yanayinta na kodayaushe, na wuce zan shiga ɗaki naji muryar shi
“Ina za ki zo kema ki zauna”.
dawowa nayi na nemi wuri na zauna
shi ma zaman ya yi ya dafe kunci da hannu bi biyu, ya dauki mintoci kafin ya ɗago
“Na tara ku ne domin na ja wa kowaccen ku kunne,in kuma jaddada muku zaman da kuke kuna zama ƙarkashina ne,
dan haka dole in sa doka a bi, ba wadda ta fi ƙarfina duk kuma me son zama da ni dole ta bi umarnina.
Ba zan lamunci ci mini zarafi a cikin gidana ba,
ba kuma zan dauki yawan faɗa ba,
dole kowacce ta zauna da ƴar’uwarta lafiya.
Sannan wace hujja ce tasa ba a kai wa Basma abinci ba alhali kun san daga asibiti ta dawo bata da lafiya?
duk kan mu shiru muka yi
har Halima me nuna gadarar ita isashshiya ce yau shiru kake ji kamar ruwa ya ci ta.
Da na fahimci ya ƙare fadan sai na ba shi hakuri,
miƙewa ya yi ya haye saman shi,
nima tashi nayi na shige nawa ɗakin.

Halima ke juyi bisa gadonta maganar barci ma ya ɗauke ta ma bata taso ba a yau,
wani tururi ke tasowa
a kasan zuciyarta,
wai ita Tahir zai tara
wadannan kucakan da yake ganin mata ya tara
ya wulaƙanta ta,
Kullun cikin kashe kudade take amma har yau malaman sun kasa
mata maganin matsalolinta,
zaune ta tashi kirjinta na cigaba da suya
“Wallahi ba zai yiwu ba,
ba ƴar iskar da ta isa”
ta buga kanta jikin gado
sai kuma ta dafe kan,
sai gabanin hudowar alfijir barci ya yi awon gaba da ita abin da ya ja
mata muguwar makara.
Tana farkawa
toilet ta wuce
ta dauro alwala,
a gurguje tayi sallah ta fita zuwa kitchen
zuciyarta na bugawa ka da Tahir ya ci zarafinta
a gaban matansa.
Indo ta samu a gefe ta gama gyara kitchen tana jiran me girki dan doka ce daga me gidan bai yarda me aiki ta girka abin da zai ci ba,
gaishe ta tayi sai suka soma aikin.
A daidai nan Ogan ya fito
fita yake son yi, ganin dinning wayam yasa shi
yin ƙwafa har yau Halima bata gama sanin shi ba,
dakin basma ya fara shiga suna zaune ita da me kula da ita suna
break fast,
ya gaida matar wadda take ƙanwar mahaifin Basma tana shirin fita
Ya ce “Yi zamanki ba daɗewa zan yi ba”
bata yarda ba,
kwanonin da suka yi amfani da su ta shiga tattarawa ta ce
“Ai na kammala zan miƙa
su kitchen ne”
sai da ta fita ta ja musu ƙofar,
ya dubi Basma
“Ya jikin?
a hankali ta ce “Da sauƙi”
“Daddy na ya yi ta neman wayarka ta ƙi shiga shi ne ya kira ni yana tambayata lafiya”
ya ce “Ok bari in kira shi”
hannunsa yasa aljihu ya ciro wayar
“Wa ya kawo muku abinci” ya tambaya
dan ya yi mamaki ko shi me gidan ba a ajiye nashi ba, amma su suna ci.
kamar bata son maganar ta ce “Ummulkhairi ta kawo”
Ummulkhairi?
ya ambaci sunan cikin mamaki.
Lokacin kuma aka daga wayar da ya kira cikin girmamawa ya soma gaishe da surukin nasa
sai da ya amsa ya ce
“Jiya ba mu haɗu ba”
Tahir ya ce “E wallahi mun samu saɓani ne”
ya ce “To dama na so mu zauna kan Basma ina so in kafa sharadi kan zamanta,
wajibi ne zamanta da matanka a guji abin da zai bata mata rai kamar yadda ka sani ɓacin rai ke tada ciwon ta dan nayi nayi mu wuce Abuja ta ƙi
kamar yadda ka ki raba mata gida da matanka.
Ga Hajjo nan yar’uwata ce za ta zauna da ita dan taimaka mata.
Duk yanda Tahir yaso
ya yi magana kasawa ya yi dan wani ɓacin rai da ya taso ya tokare kirjinsa
har surukin nasa ya kashe wayarsa.
Bai bi takan Basma ba
wadda tun daga ganin canzawar yanayinsa ta gane ba me daɗi Daddynta ta fada masa ba.
Fitowarsa da Latifa ya ci karo wadda ya nufi ɗakinta wucewa ya yi ta bi shi a baya tana fadin
“Ni dai wallahi na gaji da horon yunwar da matar nan take mana a ranar girkinta.
Ina dalili har 10 mutum bai yi break fast ba”
Shi dai bai ce komai ba har suka shiga ɗakin nata.
Bai jima ba ya fito ya bar ta da takaicin ɗakinta ne kawai ya shiga baya jimawa,kome yake yi dakin sauran? tayi ƙwafa bari ka ga ya shiga ɗakin waccan munafukar yarinyar da ta lura yana ba matsayi na musamman, dan Halima ko da take tsula tsiyar ta
ba ko wane lokaci yake ƙyale ta ba.
Miƙewa tayi ta bi shi ta ga sa’adda zai fito.

Da ya shigo ɗakina zaune ya same ni
ina karyawa,
dan yanzu saboda cikin jikina bana juriyar yunwa.
Na fito na ga ba alamun Halima sai na shiga kitchen din dan na taimaki kaina.
Na soma aiki kenan
matar ƙanwar mahaifin Basma ta shigo,
cikin mutunci muka gaisa,
“Dan Allah ruwan zafi nake so in dafa wa mara lafiyar yunwa take ji,
ko tea ne in hada mata.
Murmushi nayi na ce
“Ba damuwa bari in dafa mata”
Godiya ta mini ta koma
ta dawo ɗauke da flaks,
Lifton na sa da kayan ƙamshi, sai da ya tafasa sosai sai na juye mata,
ta amsa tana ta godiya.
Kunun gyaɗa na dama
me kyau sai nayi farfesun kaza,
na kai wanda zai ishe ni daki kafin na dawo na
kwashe sauran zuwa dakin Basma,
da na ƙwanƙwasa matar ce ta bude, sai da na gaishe da Basma sannan
na miƙa musu,
nan ma matar ce tayi godiya.
Sai da nayi wanka na gyara jikina, cikin wani material fari me zanen manyan fulawoyi, ɗinkin doguwar riga da tayi kyau a jikina,
na zauna zaman karin ne
ya shigo.
Ya bi ni da kallo kafin ya
sauke kan abin da nake ci, “Ya kike cin abinci
a daki bayan za a ci gaba ɗaya?
kai na langabe “Ba na juriyar yunwa yanzu shi yasa na shiga kitchen din”
“Ya yi kyau”
abinda ya faɗa kenan sai ya zauna,
“Ina kwana?
Na soma gaishe shi
sai da ya amsa na tambaye shi yaushe zan tafi gida?
“Nan ba da jimawa ba”
amsar da ya bani kenan
ina cin abincina
amma a takure nake dan mayun idanuwansa
da ke cikin farin Glass ɗinsa na rai da rai
da ke kaina suna tasiri a jikina, shigar kananun kaya ya yi duk hassadar ka dole ka yabi Tahir,
dan wani kwarjini da Allah ya ba shi
ga cikar zati da iya ado
na mazan da suke ji da kansu a wannan zamani.
Na miƙe dan samun wurin zama,taku ɗaya
nayi ana biyun ƙafata ta bigi tashi wadda na fahimci da biyu ya yi
dan na tafi zan kifa ya taro ni na faɗa kan jikinsa, gaba ɗaya ƙamshin turarensa ya mamaye ni.
Wata ajiyar zuciya yake fiddawa yayin da hannunsa ke yawo cikin jikina
wai har yanzu ban yi ajiya ba?
ya fadi cikin lumshi
hannunsa na kan cikin yana shafawa,
ganin yana kokarin danne ni kan kujerar da muke yasa ni soma kwatar kaina, ina tuna mishi ba ni ke da wannan alhakin ba,
hannayen nawa ya kama da hannu ɗaya
ya cigaba da sha’aninsa.
Sai dai kofar da aka buɗe gaba ɗaya ta sa ni kwace
hannayena jikina na rawa.
Latifa ce tsaye kanmu
tana huci dan duk yanda
taso daurewa kishi yasa
ta gwammace
koma me Tahir zai mata
sai dai ya yi mata
amma sai ta ga abin da ke sa shi daɗewa a dakin
wannan shegiyar yarinyar da tafi tsana a duk cikin
kishiyoyin nata.
Kuma ga shi ta tabbatar da zargin ta.
“Daga kin shigo kin ga abin da kike son gani
sai ki fita ki bani wuri”
Tahir ya faɗa ba tare da ya ɗago ba,
duk kuma ture shin da
nake ban samu nasarar ture shi a jikina ba.
juyawa tayi ta fita tana gunjin kuka,
ni ma sai sannan na samu ture shi na gudu
Bedroom ɗi na na sa key.
Shi ma miƙewa ya yi sai ya fice, dakin Latifa ya koma wadda ya samu kwance tayi rub da ciki
tana sharbar kuka,
tsawa ya daka mata ya ce ta tashi zaune
tilas ta tashi ta zauna,
mugun kallon da yake watsa mata yasa ta hadiye kukan.
“Wannan ya zame miki na ƙarshe da za ki yi
mini laɓe,
ko sai ina tare da wata ki fado sai ka ce rayuwar wasu arna ko marasa addini.
Abin da nayi nayi ne dan in tabbatar ko kina laben da kika saba, kuma sai kika tabbatar mini da zargina kika shigo.
Na ƙara kama ki sai kin bar mini gidana wallahi”
Ya juya ya bar mata ɗakin.
Rantsuwar da ya yi za ta bar mishi gida idan ta ƙara mishi laɓe, ya firgita ta, dan ta fi kowa sanin waye Tahir.

Yana fita Halima ya gani suna shirya dinning ita da me aiki, kallo ɗaya ya yi musu ya haura sama.
Wasu kayan ya sauya
yana sa turare ta shigo
“Abinci ya sauka”
ta fadi tana duban sa,
ganin yana neman rabe ta ya wuce yasa ta shan gaban sa,
“Wai me yasa kake son yi min wulaƙanci?
wani shegen kallo ya mata,
“Matsa ki bani hanya malama, kuma ban ce ki
daina gama abinci lokacin da kika ga dama ba, ki yi tayin hakan
sai dai har yau ba ki gama sani na ba,
ba kuma ki san dalilin da yasa nake raga miki ba.
Ina ganin wannan karon
sai na tura ki gida,
kilan kya koyi hankali”
Ya fice ya bar ta kamar an dasa ta,
Ai kam ba babban tozarci irin ace Tahir ya kore ta,
da wane idon za ta dubi yan gidansu?
Ina jin kai da takamarta,
idan ta dawo ya za ta dubi kishiyoyinta.
Zabura tayi ta sauko sai dai tana saukowa yana tashin motar ba kowa falon kamar ta aiki Indo ta mika wa su Basma abincin girman kai ya hana, ita ma takaici bai bar ta ci ba.

Latifa ma ta dade kwance ba abin da ke mata yawo a ido sai halin da ta ga Tahir da wannan yarinyar,
cikin wani shauƙi yake wanda ko yana me gaba ɗayan da ita bata taɓa ganin shi hakan ba.
Can sai ta tuna fushin da ta gani a idonsa bata san irin matakin da zai dauka kanta ba.
Miƙewa tayi tuna dabarar da za ta fishshe ta.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: [2/11, 4:14 PM] Maryam: WA GARI YA WAYA

Daga

Marubuciyar

CANJIN Ba ZATA

MARYAM IBRAHIM LITEE

*RASHIN SANI AKA CE KE SA KAZA KWANA KAN DAMI Ai LALLAI RASHiN SANi SHi ZAI SAKA WUCE LABARIN* *NAN BAI KARANTA BA, KO DA KUDINKA SAI DA RABONKA, TAFIYAR TA DABAN CE HAKA MA SALON NA DABAN NE. KARANTA LABARIN*
Zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta).

AKAN NAIRA 300
Dan biyan kudin karatu
2108124716 Maryam nasir UBA bank
Dan nuna shaidar biyanka 07033400612*

*Free fage na dab da karewa*

*CHAPTER Six*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849

Gidan Kawu Attahiru ta nufa, ganin motarsa a harabar gidan yasa ta jin dadi.
daga ƙofar falo suka yi kacibis da Haj Hajara, kukan da take rusawa ya tashi hankalin Hajiyar, tana tambayar lafiya.
Nan ta hau rattafo mata Tahir yana ɗaukar kwanan su yana kai wa
Ummulkhairi.
Sauran maganganun da take ba sakaye cikin su,
yasa Kawu Attahiru wanda ya taso dan jin ihun da ta ke rafkawa,
bai kai ga karasowa
ba ya tsaya turus.
Hajiyar ma nauyi zancan yai mata,
ta dai yi ƙarfin halin bata
hakuri, har ta juya ta koma inda ta fito.
Falon ta shiga ta samu Kawun ya yi jugum ga tagumi ya rafka hannu bi biyu, yana kakkaɓin wannan mata da Tahir
ya auro, anya akwai ƙamshin tarbiyya cikin lamarin ta.
Wayarsa ya janyo ya kira
Tahir kan idan yana gida
yana son ganin sa.
Ya ce “Ya fita yanzu sai dai bai yi nisa ba”
Juya kan motar ya yi zuwa amsa kiran uban goyon nasa.
Nasiha sosai da wa’azi ya yi mishi, kan zama da mace fiye da ɗaya, da wajabcin adalci a tsakanin su.
Ba kaɗan suka ratsa Tahir ba ya yi mishi godiya ya fito ya ja motarsa, yana tafe yana tunanin abinda ya kawo wannan nasiha da baban ya yi mishi.

Da rana ya kira ni ina zaune cikin takaicin zaman da ake a wannan gida,gaba ɗaya zaman gidan ya ishe ni.
Cewa ya yi in shiga kitchen in yi girki daga Basma bata gama wartsakewa ba.
Da wuri na shiga kitchen din na soma aiki, ina gamawa ɗakina na koma ina shiryawa na bar Indo tana gyara kitchen din.
Kwalliya nayi cikin atamfa ɗinkin doguwar riga mai aljihu, na kashe dauri na fito ina tashin ƙamshi.
Halima da Latifa na zaune wuri ɗaya, ni ma wuri na samu na zauna dan doka ce jiran Ogan ya fito sai a ci abincin gaba ɗaya.
Sai da aka kammala cin abincin ya aiki Latifa ta kira mishi Basma, fitowa tayi tana takawa a hankali, dama kuma ita ɗin me nutsuwa ce.
A fakaice na kalli matan biyu kallon da suka jefa mata suka dauke kansu,
yasa na ƙara tsinkewa da al’amarin kishi.
ta samu wuri ta zauna megidan ya ce mata ya ƙarfin jiki ta ce da sauki, ni ma na ce mata megidan ya yi gyaran murya, “Abin da yasa na ce ina son magana da ku Asabar me zuwa za a ɗaura auren ƴaƴan yayyena su biyu, mace da namiji.
Ina so mu tafi da ke Halima da ummulkhairi, na so muje da ke Latifa da ba ki taɓa zuwa ba,to ga ciwon Basma ba zai yuwu mu tafi mu bar ta ita daya ba, so sai wani lokacin kenan.
Hamdala nayi a zuciyata wani daɗi ya kume ni,
jin zan tafi gida in ga family na.
Latifa ya umurta ta miko mishi wasu ledoji da na lura da su tun fitowata.
Ya umarci Halima ta zaɓi daya, ta miƙe ta dauka sai Basma,sannan ni Latifa da ta dauka ƙarshe kamar ta fashe.
Ni dai nayi mishi godiya, su kam sai dai kowacce ta gyara zama.
“Wannan kayan na kwalliyar biki ne, akwai kuɗi a ciki sai ku yi amfani da su”
Nan ma godiyar na kuma mishi.
Basma ta mike da ledarta zuwa ɗaki, ni dai na ƙara zama dan idan nayi girki na kan zauna.
Kitchen na shiga na ɗauko wa Ogan kunun aya, da nayi mishi tanadin shi.yana kurɓa a hankali Basma ta fito, gaba ɗaya muka bi ta da kallo, na lura ita dai tana son yin shigar da za ta bayyana jikinta, ko kyan surarta ke ruɗinta?
Wani abu naji yana taso min ganin Tahir yana bin ta da kallo, su ma sauran hakan ne dan har a fuskokinsu sun nuna.
Wata yalolon riga ta saka da bata ɓoye komai na halittarta ba, a kasa kuma bata saka komai ba sai dan kamfai.
Sama ta wuce muka raka ta da ido, dan kowa yasan ni nayi girki.
Ai nan fa ji nayi kamar ba zan iya daurewa ba, dan ƙirjina da ke sama da kasa.
Latifa ta ja tsaki “Aikin banza dama ya maida ita wata macen kirki, za a yi mana salo”.
Halima ma tsakin ta saki,
miƙewa kawai nayi zuwa ɗakina,ina shiga na fara hawaye, wannan wane irin kalar wulaƙanci aka yi min?.

Tahir na haurawa ya samu Basma tayi ɗaiɗai bisa gado, fuskar shi ɗaure ya ce “Wai meye wannan abu da kika yi?
ke da ba ki da lafiya me ya kawo ki nan ɗin?
Cikin ido ta dube shi”Ai na warke kuma na ji zan iya karɓar girkina”
Wani kallo ya watsa mata, “Amma za ki iya girkin me ya hana ki fitowa ki yi, sai da wata tayi sai ki fado dakin, ba ki kyauta ba”.
Wani kuka ta fasa tana dafe kanta, ita Tahir zai wulaƙanta.
Tunanin dokar likita kan ciwon ta yasa ya ce “Shi kenan, ki yi shiru ki kwanta” Ya juya zai fita ta ce “Ina za ka kuma?
Kamar ba zai mata magana ba, ba tare da ya juyo ba ya ce “Zan ma ummulkhairi magana, dan kin san ba a kyauta mata ba”.
Ɗauke kai tayi.
Ya sauka ganin falon wayam ya ba shi mamaki, TV ya kashe ya wuce ɗakina.
Kan gadona ya same ni zaune, na dogare gwiwoyina kamar me jin sanyi.
“Lafiya ummuna? ko jikin ne” ba shiri na dube shi dan jin ummun shi da ya kira ni dan rabon da in ji ya kira ni hakan, tun ina Lagos. Gira ya ɗaga min “Kin hada ni da kunun aya za ki zo nan ki takure” wani kallon ka raina min hankali na jefa mishi “Da yake wadda ka baro ita ma tana da abin, za ta baka ai”
idonsa ya gwalo “Wai da gaske Ummuna ce me sakin zance haka?
ƙara daure fuska nayi, ganin ya kasa shawo kaina yasa ya ci serious.
Gadon ya hau ya tallafo ni, ƙwace jikina nayi ina ture shi.
“Ki bari kar in ji miki ciwo” daga haka ya kara jawo ni ya haɗa da jikinsa, shiru nayi yi ina
zubar da hawaye.
“Ki yi hakuri ban san za ta ce za tayi girkin ba na ce ki yi, ki yafe min ki yi haƙuri.
Ganin yanda yake bani haƙuri na ce ya wuce.
Ya ce “Kin yafe min?
na daga kai, “To tashi ki yi shirin barci”
Yana nan sai da ya ga nayi shirin kwanciya na kwanta, hada su min addu’a, sai ya min sai da safe ya ja min ƙofar.

Yana fita na tashi zaune, humm namiji kenan ƙanen ajali.
Na daɗe zaune kafin na ba kaina magana,
na kwanta ina ta kiran sunayen Allah da neman dauki zuwa gare shi, Har na samu barci ya yi nasarar kwashe ni.

Tahir na komawa ɗakin ya yi shirin kwanciya, nesa da inda Basma take kwance ya hau ya kwanta, ya juya mata baya.
Juyowa tayi ta dube shi, wasu hawaye ta ji sun taho mata, zaune ta tashi, jin saukar numfashinsa yasa ta gane ya samu barci.
Sai kallonsa take ta raba dare a haka, sai gabanin asuba barci ya ɗauke ta.
Dan haka ko da ya yi ta tada ta tayi sallar asuba kin tashi tayi, ya yi shirinsa ya fita masallaci. Ko da ya dawo sai da ya yi mata jan ido sannan ta tashi, anan tayi sallar ta koma ta kwanta. Ya dade zaune yana azkar, kafin aka kira wayarsa kan harkokinsa ne, wanka ya yi ya shirya cikin wani yadi ɗinkin iya gwiwa da yayi matukar hawansa, sai ya manna Glass ɗinsa, yana feffesa turarukansa wayarsa tayi kara, aljihu ya jefa ta sai ya bar ɗakin.
Yana saukowa kallon ƙofofin matansa ya yi,
Tsaki kawai ya ja sai ya bar wurin.

Basma ta shari barcinta, yunwar cikinta ta tashe ta, bata ga alamar Tahir ba, ganin lokaci ya yi nisa yasa ta gane ya fita
hamma tayi ta mike ta bar ɗakin.
A ɗakinta ta samu Gwoggonta Hajjo ita ma tayi tsuru ita ma yunwar ta gallabe ta, bata iya gaishe ta ba sai ita ta tambaye ta jikinta, yamutsa fuska tayi.
“Wannan yarinyar bata kawo abinci ba?
Kallon mamaki ta bi ta da shi “Amma ke kam Basma sai a bar ki, ke wane irin tunani ne da ke? wa ke sauraren mu ya biyo mu da abinci dakin nan idan ba ita ba, amma kina dan jin ƙarfi da me za ki saka mata sai za ta karbi girki, ki ce ke za ki yi. Ai kin ja mana sai ki fita ki nemo mana abin da za mu ci”
Ba yanda Basma za ta yi, fitowa tayi ta ce Indo ta kawo mata ruwan zafi, dan ko kwai ba za ta iya hakurin a soya ba.
Haka nan suka sha tea.

Karfe biyu Tahir ya kira wayarta yana tambayar ta ta gama girki, ga shi nan zuwa, dan yunwa yake ji. Hankalinta ya tashi ta fita neman Indo, bata gan ta ba, kuma girman kanta ba zai bar ta tambayar wata ba.
Yankewa tayi ta koma daki komai ta fanjama fanjam, ai yasan bata da lafiya zai ce sai ta ba shi abinci.
Yana isowa dakinsa ya shiga, ya sauya kayan jikin shi zuwa jallabiya,sai ya sauko ganin danning wayam saman shi ya koma, ya kira ta a waya, sai ga ta tana yauƙi ita ala dole yunwa take ji.
Ya ce “Ina abincina?
Dan kauda kai tayi, “Ban yi ba” Dalili? Ya tambaye ta, “Ka san dai bani da lafiya”
Shat up my friend” ya da ka mata tsawa.
“Kin san ba ki da lafiya, kika karɓi girkin?
Wayarsa ya janyo Ummulkhairi ya kira, lokacin ina kallon wani shiri a tashar Afrika TV 3, sai da ya saurari gaisuwar da nake mishi, kafin ya ce “Zan samu abincin da zan ci a wurin ki”.
Dan jim nayi kafin na ce “E” “To ki ajiye min a dinning kafin in fito”.
Ya kashe wayar.
Shiru nayi “Me kenan hakan? na tambayi kaina, An kwace min girkin kuma yana batun in ba shi abinci.
Kamar in kira Aunty laila in ne mi shawarar ta,sai kuma dai na ga in adana sirrina kawai,
miƙewa nayi na sauko.

Abincin da na tanada in ci da dare na ɗumama mishi, na shirya a trey na ɗauka zuwa falo, na tarar Halima da Latifa sun fito,na wuce su zuwa dinning muryar Latifa na tsinkaya. “Wasu dai Allah ya yi musu neman cusa kai, ni dai ban ga rashin zuciyar da ta aike ni in yi girki a karɓe mijin, kuma in zauna ina musu abinci suna cinyewa.
Ko da yake dan an maka abinda kake yi bai kamata ka ji haushi ba”.
Halima ta ce “Kamar ya?
“To idan a girkin da ba naka ba, kana kebewa da miji,dan an maka haka ai ba ka ji haushi ba”
Halima ta amshe cikin fushi, “Ai kuwa ba a haifi ƴar ba, ran girkina ta raɓi miji”.
Wata shewa Latifa tayi “Na nawa kuma? ai sai dai kar a kuma”
Halima ta zaburo za ta yi magana suka ga ogan a kansu.
Raɓa su ya yi kamar ma bai gan su ba, ya je ya zauna ya soma cin abincinsa,
Juyawa nayi na koma ɗakina.

Basma ta sauko, jin ƙamshin girkin cikinta ya soma ruri, yana tuna mata ba a ba shi hakkinsa ba.
Kujera ta ja ta zauna suna fuskantar juna, yana cin abincin tana ta kallon sa, tunaninta zai ji tausayinta ya rage mata, sai ta ga ya tashi flate ɗin,
Ya dauki tattacciyar abarba da na tsiyaya masa a Glass cup ya sha, ya goge bakinsa, sai ya fice falon.

Ganin ba sarki sai Allah
Basma ɗakinta ta koma, kuɗi ta dauko ta fito zuwa harabar gidan, direba ta kira ta aike shi ya yo mata take away. ta juya Tahir da ke kallon abin da ke faruwa, ya kira direban, da saurin sa ya iso kiran uban gidan nasa, tambayar sa ya yi abin da Basma ta ce mishi, ya yi mishi bayani, “Ka mayar mata kudinta”
ya fadi da dakewa,
Ba yanda direba zai yi,
dole ya kama hanya ya yi sa’a bata kai ga shigewa ba, ya ce “Mai gida ya ce a maido miki kuɗinki”
bata damu ba, dan tunaninta zai bayar a sawo mata ne.

Ɗakinta ta koma tana zaman jiran tsammani, ga Gwoggonta me lalurar ulser, jin shirun ya yawaita yasa ta tashi ta fito, sama ta hau ganin ba Tahir sai ta koma harabar gidan.
A kebabben wurin da yake motsa jiki ta same shi ya haɗa gumi kashirban,
shagala tayi da kallon sa, dirarren namiji da ko wace mace za ta yi ma kanta sha’awar a ce nata ne kirjinsa ta zura wa ido, har jikinsa ya ba shi ana kallonsa, waiwayowa ya yi sai Basma ya gani tsaye.
“Lafiya” ya ce yana dubanta.
Ina abincin? ta tambaya kai tsaye, “Abinci kuma wane abinci?
Bata fuska tayi “Ba ka aiki direba ya sawo min abinci ba?
Cigaba ya yi da abin da yake kamar ba shi da wata mas’ala, “Magana fa nake maka”
ta fadi kamar za ta fasa kuka.
“Akwai abin da babu ne na nau’in abinci a gidan?
ya tambayeta.
Turus tayi, gane ba za tayi magana ba yasa ya ce “Ki shiga kitchen ki dafa, kuma dokar da nasa duk me girki ta ba jama’ar gidan abinci kika taka zamu gauraya.
Ina daga miki kafa saboda lalurarki”
Ya yi ƙwafa, ganin ya tunkarota yasa ta tunanin ko mangare ta zai yi, sauri tayi ta juya.

Daga shi sai guntun wando ya shiga falon, Halima da Latifa da ke zaune har lokacin kowacce tana tunanin takurar da take ciki na zaman me gidan a gari ba halin fita sabgar gaban su.
Sun dube shi a tare shi kuma ya dubi ƙofar ummulkhairi.

 

 

 

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *WA GARI YA WAYA*

Daga

Marubuciyar

*CANJIN Ba ZATA*

MARYAM IBRAHIM LITEE

*RASHIN SANI AKA CE KE SA KAZA KWANA KAN DAMI Ai LALLAI RASHiN SANi SHi ZAI SA KA WUCE LABARIN NAN BA KA KARANTA BA, KO DA KUDINKA SAI DA RABONKA, TAFIYAR TA DABAN CE HAKA MA SALON NA DABAN NE. KARANTA LABARIN*
Zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta).

*AKAN NAIRA 300*
Dan biyan kudin karatu
2108124716 Maryam nasir UBA bank
Dan nuna shaidar biyanka 07033400612
A chapter 3 na yi mistake wurin sa acc no to ga yadda take

Free fage

CHAPTER SEVEN

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1020959516678

*Bismillahir Rahmanir Rahim)

Chapter Seven

Yana son dubata, amma tsegumin da hakan zai janyo yasa ya wuce sama, ruwa ya watsa ya yi alwala sai ya wuce zuwa masallaci sallar la’asar.

Sai da ya dawo sallar magrib ya shigo, dakin Latifa ya fara shiga sannan ɗakina.
Ina zaune inda na idar da Sallah ina azkar, gabana ya tsuguna, ya kafe ni da mayatattun idanunsa da ke cikin glass ɗinsa na rai da rai, sau daya na dube shi, sai na maida kaina ƙasa gaba ɗaya ya dabuta ni, sannu da zuwa nayi mishi ya yi min ya gida da tambayar ba wata damuwa, har yana ce min “Me yasa ba ki son fita ana fira da ke?
Murmushi kawai nayi mishi, ledar da ya shigo da ita ya miƙo min, “Tashi to ki ci”
Mikewar nayi, na karbi ledar “Ki ci yanzu tunda zafi”
Ban ƙi ta tashi ba, budewa nayi gasashshen naman rago ne me zafi.
Na sa hannu na soma ci, dagowa nayi na dube shi na ga ni yake kallo,maida kai nayi na ce
“Dan Allah ina son zuwa dalilin”.
Ban yi tunanin zai yi saurin amincewa ba, sai na ji ya ce “Ki shirya gobe, sai in fita da ke”
na ce “Na gode daga nan ina son miƙa ɗinkin da ka kawo mana”.
ya ce ok”. Ya miƙe tare da ce min sai da safe, dan na ce ba zan fita ba barci nake ji, dan ni dai na tsani wannan zaman da ake yi na tsurku da faɗa wa juna magana a fakaice.
Yana fita ledar da ya kawo mana na dauko, ɓacin ran da na shiga yasa ko tunanin dauko ta ban yi ba, Atamfofi ne super guda biyu, sai shadda daya less daya.
Zura musu ido nayi ina tuna kuɗaɗen da aka yi wa ta’adi kafin a mallake su.

A dakin Halima da ya shiga daru suka kwasa, dan sun shirya ita da Latifa duk wadda ya shiga ɗakinta ta zage ta nuna mishi ɓacin ranta, kan yasa doka kan girki, ga shi Basma ta taka dokar ta ƙi yi, kuma bai yi komai a kai ba.
Latifar dai da ya shiga nata dakin, bata yi maganar ba, sai ma kwarkwasa da ta yi ta mishi, dan ɗaukar hankalinsa.
Halima dai ta kira shi mara adalci, kuma kalmar ta taɓa shi,
sun yi baran baran ya ajiye mata nata naman ya fita.
Ya kai ma Basma hada na gwaggonta, itam ma fushi take da shi, dan yasa ta ta shiga kitchen, dole tayi musu abinci wanda ta cika ma yaji, saboda yunwa dole gwaggonta ta ci, tana kwance kirji ya dame ta,
Basma ta ci naman ta koshi ta ɗora fresh yogurt, Gwoggonta dai fresh yougourt din kawai ta iya sha, ta koma ta kwanta, tana kallon Basma na shirin zuwa turaka, ta ja mata ƙofar ta wuce.
Latifa ce kaɗai a falo wai kallo take, tana ganin Basma ta haura sama, ita ma ta kashe komai ta wuce ɗakinta, cike da kishi.
Wanka ta samu Ogan nayi, dan haka wuri ta nema ta kwanta, ya fito yana share ruwa a kansa,har ya gama shirin kwanciyarsa tana kallonsa, ya zo ya raba ta ya kwanta.
Ganin ba shi da alamar kulata yasa ta mirgina ta haɗa jikinta da na shi, kamar jira sai wayarta da ke gefe ta dau ƙara, yi tayi kamar bata ji ba, dan takaicin me kiranta a wannan lokaci da ya kamata.
“Ba ki ji ne? ta ji maganarsa, kan tilas ta raba jikinta da nasa ta dauko wayar, Gwoggonta ce tana ɗauka ta ji tana cewa, “Basma ki zo ki kaini asibiti, ƙirjina Basma”
Sauka tayi kan gadon, yana tambayarta abin da ya faru,tayi mishi bayani
cikin hanzari ya mike ya saka jallabiyarsa.
Yana tafe tana biye da shi har ɗakinta, inda suka samu Gwoggonta ba yanda take dan ulser da ta taso mata.
Da ƙyar ta tashi suka yi mota da ita, sai asibiti.
Cikin gaugawa suka ga
Likita, ya dubata aka basu magunguna, sai ɗaya da rabi na dare suka dawo gida, Tahir ya ce Basma ta zauna wurinta ta kula da ita.
Da safe ta tashi da sauki, da kansa Tahir ya sanya Indo wacce ashe jiya kwance ta wuni sakamakon zazzaɓi da ya rufe ta.
Ta yi ma Gwoggon abin karyawa, ta dan ci ba laifi, ta sha magungunanta sai ta kwanta.

Ya shigo wurina mun gaisa, yake ce min in shirya da wuri, dan haka karfe goma saura na fito cikin kyakykyawar shiga, Indo kawai nayi wa sallama, dakin Halima a rufe yake haka ma na Latifa, Basma na shiga na gaishe da Gwoggonta na shaida mata zan fita.

Wata dalleliyar motarsa muka fita cikinta, muna tafiya ina kallonsa ta gefen ido, dan sosai ya mini kyau cikin wata tsadaddar shaddar da ta kwanta lub a jikinsa, ga hularsa da ke ta sheƙi ya ajiye ta a sha tara,
Ƙamshi me daɗi ke fita cikin motar.
Muna tafe shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa, har muka isa wani wuri, can cikin rabah road, daga irin galla gallan motocin da ke fake wurin za ka san wurin zuwan masu hannu da shuni ne.
Ya faka muka fito, cikin girmamawa da haba haba ma’aikatan wurin suka tarbe mu.
Sai da na zauna ya ce “Idan an kare min, in kira shi”.
Gyaran jiki aka yi min, kafin na zauna zaman kunshi da kitso wanda aka yarfa min, ni kaina
sai kallon kaina nake.
Tahir ma jin shiru ya kira ni, wai me ake min har yanzu, ba a gama ba?
Na ce “Gyara” tsaki ya ja, “Wane irin gyara ne har la’asar ta kusa?
Na ce “Ka taho an kammala, dama ina shirin kiranka sai ga naka kiran ya shigo”
Yana isowa kudinsu ya biya su, sai muka fito, jikin wurin muka shiga na bayar da dinkunana,sun bada sati guda a zo a karba.
Mun shiga mota, Fadila ƙawar Latifa da ta zo gyaran kai, ta kuma duban motar, Tabbas! mijin Latifa ne. Lallai gayen nan naira na faɗa mishi ƙarya, bayan mata huɗu reras da ya ajiye ina kuma zai kai wannan?
Wayarta ta ciro ta soma kiran Latifa, wadda shigowarta kenan, tun fitar Tahir ta sa kai ta bar gidan, tana ɗauka ta ce
“Wai ke mijinki mata basa isarsa a……
Katseta tayi “Wannan wane irin wulaƙanci ne, ki kira ni kina zagin mijina?
“Maida wuƙar ƙawata, yanzu na gan shi da wata santaleliyar baby, wallahi in ba ku yi da gaske ba, duk sai ta karɓe muku shi, Dan tayi ba karya.
K…… “Ki saurara min dan Allah Fadila”
ta katse ta cikin hasala dan kirjinta har wani ɗagawa yake, dan azabar kishi.
“A ina kika gan shi?
Kwantar da murya Fadila tayi ta yi mata kwatance,
da gaya mata har yanzu bai tashi motar ba.
“Ki ɗaukar min pic din motar Please”
Wata yar shashshekar dariya tayi “Kina ganin kamar zan miki karya?
ina zuwa”
Ɗauka tayi daidai yana ribas sai ta tura mata ta WhatsApp.

Kin tada motar ya yi tsayawa ya yi yana min wani kallo, me ɗauke da ma’anoni ƙwayar idonsa ta canza kala.
Hannuna ya kama yana murzawa, kafin ya janyo ni na fada kansa, dankwalina ya zame yana shafa hadadden kitson da aka zauna aka yarfa min.
Mun dade a haka kafin ya cire ni a jikinsa, ya tashi motar muka harba titi.

Daga get ya ce in sauka zai ga wani abokinsa a layin gaban mu.
Ina shiga a harabar gidan na hango Latifa tsaye kamar tana jiran wani, na wuce ta bayan nayi mata sannu, sallar la’asar na fara gabatarwa sai na sauya kayan jikina da doguwar riga mara nauyi, kafin na isa kitchen.
Tuwon shinkafa na fara daurawa, sannan na shiga haɗa miyar gyada, Indo ta shigo tana taya ni, farfesun naman kai na ɗaura karshe, kiran sallar magrib mun kammala, muka shirya komai a dinning Indon na ba ta kai wa gwaggon Basma da megadi.
Daga nan na wuce dakina, nayi sallah ina idarwa sama na wuce, falon Ogan ba laifi, dan bai yi wani datti ba, amma dakin barcin sai a hankali, komai da ya yi amfani da shi yana nan inda ya bari.
Na kwashe komai na kintsa wurin na wanki nasa cikin Landry kayan sawar shi masu datti na hada su wuri ɗaya, na cire zanen gadon na canza wani, kafin na share ko’ina na goge na fesa air freshener,
Toilet ne ƙarshe na wanko shi tas.
Tunda na dawo na lura matan yanzu sun sa kyashin gyaran dakin megidan, kowacce na kyashin ta gyara wata ta shiga, ni kuma ban ga dalilin da zai sa in ji kyashi ba, daga ba dan wata zan yi ba, zan yi dan mijina ne.
Sanda na fito ana ta sallar isha’i, wanka me kyau na shiga nayi, na zuba turarukan da Aunty Kulu ta bani.
Ina gaban mirror, nima har mamakin yanda na koma nake, rashin zaman lafiya da ake a gidan bai hanani yin kyau kamar ka sure ni ka gudu.
Ina bukatar mijina, dan haka bani da bukatar doguwar firar da ake a falo, turarukan da Aunty Kulu ta faɗa min sai za ni turaka zan yi amfani da su, dan muddin namiji ya shaƙe su, ba zai kara zama lafiya ba, gaba ɗaya zai sukurkuce.
Na dauko na goggoga na sanya wasu riga da wando masu masifar kyau da muka saya a Saudiyya, sun kama ni daidai jikina, na yane kaina da gyalensu,
takalmi na zura na fito falon.

Duk kan su sun fito har Basma, sun bi ni da kallon kishi, an hau dinning da alama Ogan ake jira, jin taku daga sama yasa ni kai idona, shi din ne shirt yasa da gajeren wando, idanuwanmu suka shiga na juna, nayi saurin janye nawa.
Yau tsakanin Latifa da mutumniyarta Halima yar harara ce, Halima take banka ma Latifa, dan ta gane shigo shigo tayi mata.
Ita kuma Latifa ba nan tunaninta yake ba, hankalinta tashe yake kuma ya rabu biyu, shin wadda Fadila ta ce ta gani da Tahir tana zargin Ummulkhairi ce, koko wata daban?
Shiyasa ta kasa zama tayo waje dan ta ga shigowarsu, amma sai ummulkhairi ta gani ita kadai ta shigo, idan kuma wata daban Tahir ke nema wace ce ita?
Kafin ta shigo gidan Basma take hange za ta zame mata matsala, sai da ta shigo ta gane bambancin ta da babu a gidan ba shi da yawa.
Halima kuma amfani take da ita, duk abin da ya kamata tayi sai ta ingiza ta ita tayi.
Wannan yarinyar kuma nema take ta zame mata dan hakin da ka raina,
kashe kuɗi take dan ta mallaki mutumin nan amma kamar bata yi.
Nasara ɗaya ta samu, ita ce auren Tahir Sodangi,
tun kafin ta shigo tayi iya yinta dan nakasa rayuwar yarinyar, wadda tana dab da samun cikar burinta, na mallakar Tahir ya subuce mata ya auro yarinyar.
Sai dai ita ta shigo a ta karshe.
Da suna shiri da Halima ita za ta bari da aikin, dan Halima na jin labarin fitar za ta firgice.
Tashi nayi na matsa sosai kusa da Ogan na zuba mishi abincin, ya shaki daddaɗan ƙamshin da ke fitowa jikina sai ya lumshe ido.
Ya soma cin abincin, wanda ya yi matuƙar yi mishi daɗi.
Matan duka ba wadda v
dadin girkin bai ratsata ba, amma wani kishi ya zo ya tsaya musu a wuya.
Basma ce kadai ta ci ta yi nak.
Na miƙe zuwa kitchen ya saci kallona, idon matan biyu na kanshi wani kishi ke taso musu, har na dawo ɗauke da jug, wannan karon ya shafa’a shi da suwaye zagewa ya yi yana aika min kallon tsananin bukatuwar sa a kaina.
Isowata ya ankarar da shi inda yake, ya yi saurin saita kansa, sai ya sha mur, ya maida idonsa kan farfesun da yake sha.
Na tsiyaya mishi zobon da nayi sai na ga ya mike,
“Gobe idan Allah ya kaimu babban abokina, da muka yi secondary tare, zai kawo mana ziyara shi da matarsa.
Tunda muka kare secondary ɗinmu ya tafi turai karatu,
tun kuma tafiyarsa bai zo ba dan bayan kare karatunsa aiki suka ba shi a can, dan likita ne.
Shekaru biyu da yin aurensa, wanda shi ma anan aka daura sai dai aka tura mishi matar.
Cikin satin nan ya dawo,
ina so ayi musu tarba ta musamman, abin da duk babu na cefane a duba sai ayi min list”.
Kowaccen mu gyada kai tayi, dubana ya yi “Ki kawo min abin nan sama, zan kwanta mura ke damuna”
Ya ture kujera ya wuce,matan suka bi shi da kallo galala, yaushe ya fara barci karfe tara?
Lallai yarinyar nan ta zo da sabon salo.
Ɗaukar jug din nayi na bi bayansa, ina murɗa ƙofar na ji an janyo ni, zan fasa ƙara ya haɗe bakina da na shi, ajiyar zuciya me ƙarfi na sauke.
Ya jani zuwa kujera, sai mutsu mutsu nake na ce “Ka bari in zuba maka”
Wani malalacin murmushi ya saki
“Yarinya kenan, ni na ce miki na taɓa shan wannan abin”
Ya daɗe yana jagwalgwala ni, ina maƙale da shi, amma ina mishi korafin ban yi isha’i ba.
Da ƙyar na samu ya sake ni, zan fita ya ce dawo ki yi anan. da mamaki nake dubansa, amma dai ban yi magana ba, na shiga na dauro alwala, ina fitowa zane da hijab na samu a bakin gado.
Bata fuska nayi, ko ya gane ba zan ɗauka ba ya ce “Ba na kowa bane, imma tunaninki kenan, ke ce ta farko da za ki yi amfani da su”
ɗauka nayi ina jin wani dan kishi kishi na taso min”.
Inda sallayar ke shimfide na isa na kabbara, da na idar da sallar addu’a nayi sai na miƙe, zan zare hijab ɗin na dubi inda yake kwance, ya yi daidai a gadon daga shi sai guntun farin wando.
Na dubi kirjinsa da gashi ya kwanta sai na ji tsigar jikina na tashi, sunkuyar da kaina nayi
“Zan je ɗaki in sa rigar barci”
Oya malama jan ran ya isa kya sanya tawa”
marairaicewa nayi na ce
“Ban rufe ƙofata ba”
Ya ce dan tsaki ya ja “Minti biyu na ba ki ”
A gurguje na sauko rigar da na tanada dan daren na zura, sai wani magani a wata yar roba, cikin wadanda maman Aunty laila ta saya mana a Saudiyya na dauko na shanye, na rufe ƙofata.Mun raya wannan dare cike da zunzurutun kauna me tsayawa a rai.

Da safe da wuri na fito, na samar da abin karyawa ga jama’ar gidan, sai na shiga aikin taran bakin Indo na tsaye gefena tana taya ni.
Main falo ma tare da ita muka gyara shi na bade shi da ƙamshi me sanyaya rai.
Babu wacce ta leƙo taya mu kamar yanda Ogan ya nemi ayi.
Cincin na fara yi wanda zamu tari baƙin da shi.
Sai na yi dambun shinkafa, wanda ya ji kayan ciki da kayan lambu.
Cake nayi karshe wanda nayi nufin ba bakin idan sun tashi tafiya.
Ina haɗa coconut milk pudding, Ogan ya leƙo kitchen din.
Sosai ya min kyau cikin wani yadi ɗinkin South South.

 

 

 

MARYAM lITEE
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *WA GARI YA WAYA*

Daga

Marubuciyar

*CANJIN Ba ZATA*

MARYAM IBRAHIM LITEE

*RASHIN SANI AKA CE KE SA KAZA KWANA KAN DAMI Ai LALLAI RASHiN SANi SHi ZAI SAKA WUCE LABARIN* *NAN BAI KARANTA BA, KO DA KUDINKA SAI DA RABONKA, TAFIYAR TA DABAN CE HAKA MA SALON NA DABAN NE. KARANTA LABARIN*
*Zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta)*.

AKAN NAIRA 300
Dan biyan kudin karatu
2108124716 Maryam nasir UBA bank
Dan nuna shaidar biyanka 07033400612*
A chapter 3 na yi mistake wurin sa acc no to ga yadda take

Free fage

CHAPTER Eight

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

 

Key ɗinsa yasa a kunnensa yana dan sosawa, “Madam sarkin aiki” murmushi nayi, “Ni zan dan fita, zan dawo kafin isowar baƙin”
daga haka ya juya na bi bayansa, ina mishi a dawo lafiya. Sai da ya shiga motarsa sai na juyo, ban lura da Latifa da kawarta da ke zaune akan fararen kujeru, a can kusa da wasu Flowers, sun zura mana ido tun fitowar mu, sai da na iso daf da su sannu na musu, sai dai ban san ko Latifa ta amsa ba, wadda suke tare dai ta amsa hada gaishe ni.
Miƙewa Fadila tayi hada buɗe baki, Latifa ta kamo ta ta zaunar, “Ke meye?
Ajiyar zuciya ta fidda, “Wai Latifa me nake shirin gani ne?
da sauri ta ce “Me kika gani?
“Wace ce wannan da ta wuce? matsiyacin tsaki ta ja, “Ita ce nake bi a gidan Tahir”
Ido waje Fadila ke dubanta, “Kina nufin kishiyarki ce?
tsaki ta kuma ja bata yi magana ba.
“To wallahi ita ce na gani jiya tare da Tahir ɗinki”
Wani kishi ne ya soki kirjin Latifa, har ta gwammace wata macen ce ta waje aka ga Tahir da ita. “Sai kin dage Latifa, yana da irin wannan a gida lafiyayyar mace maka malam, da ko wane namiji zai so ta kasance kusa da shi.
In ma banda tarangahuma irin ta ɗa namiji, me kamar wannan har ya ƙara ganin wata macen ya ce zai dauko ya karo cikin gidansa. Ko da yake mijin naku gwarzo ne, mata hudu reras ka…..
“Idan kin gama zagina Fadila, sai ki tashi ki tafi”
Latifa ta katse ta cikin fushi, kama hannunta tayi “Yi hakuri ƙawata, amma dai gaskiya sai kin dage, tunda kin ce ita waccan ta Abujan bata da power a gidan.
Ni wannan ina ce ita ce kika ce min yar ƙauye ce”
Baki ta taɓe “Yar ƙauye ce mana, an zo birni an sha jar miya sai a ka kile”
Fadila za ta kara magana Latifa ta daga mata hannu “Na fa san ki Malama, kada ki ce min jarabar taki ta rasa inda za ta tashi sai kan kishiyata”
Baki ta lasa “To mu bar wannan maganar, akwai wani magani da na kawo miki, yana da matukar kyau, sai dai tsada, samun maganin ba ƙananan kuɗaɗe na karɓa a hannun alhazan birni ba”.
Sai sannan Latifa tayi murmushi “Yawwa yanzu na ji batu, muje ki bani”
ciki suka shiga riƙe da hannun juna, sun ratsa falon da basu samu kowa ba zuwa dakin Latifa, ta bata maganin tare da bayanin yadda za ta yi amfani da shi.
Ta nemi ta bata kudin maganin, transfer tayi mata, ta taɓa kafadarta
“Muje falon nan naku ƙawata, ban gajiya da ganin sa, kana cikin sa kamar kana ƙasar waje, ba fa ƙaramin dace kika yi da samun gayen nan ba, ga shi ya haɗu ga masu gidan rana ya tara”
Cije lebe tayi “Ke dacen kawai kika hango, ba ki tuna bakar wuyar da na sha kafin in samu nasarar shigowa in amsa sunan matar sa”
tafawa suka yi “Haka ne fa dan ni ba ma zan iya ba, ba dan namiji guda aka yi ni ba”
Lumshe ido Latifa tayi “Ba za ki gane ba ƙawata, gwarzon maza ne ogana, ban taba samun namijin da ya shiga raina irin sa ba, namiji ne da zai sa ki manta sunanki, ya iya tarairayar mace ya jiyar da ita daɗi”
Fadila za ta yi magana txt ya shigo wayarta ta soma dubawa sai suka fito.
Suna zaune ina ta hada hadar shirya abinci, duk na bi na tsargu saboda mayataccen kallon da kawar Latifa ke bi na da shi, dama tunda na gan ta hankalina bai kwanta da ita ba, bata yi kama da masu kamun kai ba.
Ban da wani banzan ɗinki da ta sa har sarƙa na gani a kafarta, ga gashin doki da ta yarbatsa a kanta.
Ina samu dai na kammala sai na wuce su zuwa ɗakina.
Latifa ma miƙewa tayi “Ke gidan fa yau manyan baki za mu yi, wani babban abokin Ogan ne da ke zaune a Abroad zai zo da matarsa, bari in shiga in shirya kar a raina ka cikin kishiyoyi”
Ita ma miƙewar tayi
“Shi kenan nima bari in ƙarasa, akwai wanda muka yi alkawarin haduwa”
Ta taka mata sai ta dawo ta wuce ɗakinta dan shiryawa, tare da ƙara jaddada kudirinta na kulla abota da matar abokin ogan nasu.

Ita ma Halima a nata fannin kudirinta kenan kulla alaƙa da matar abokin ogan dan haka shiri take tayi ita ma.

Saɓanin Basma da ke kwance bisa kujera tayi ɗaiɗai, bata ma da niyyar shiryawa, kallon Gwoggonta take wadda ke zaune tana cin abinci tana fadin “Kai wannan yarinya akwai baiwar iya girki, kana ci kunnenka na motsi, ga ta kuma yar albarka ita kadai za ta yi girki ta aiko min da shi har daki, girkinta ne kawai kuma za ka ci abinci me daɗi”. Basma da ke kallon Gwoggon ta ta cikin fushi ta ce “Haba mana Gwoggo kishiyar tawa kike ma wannan yabon?
Kallonta tayi “To ai ni dai kin san in gaskiya ta zo bani boye ta, fadin ta nake”
Cikin kumbura baki ta soma kunkunai “Ni dai ba a kyauta min ba wallahi”
“In ma zagina kike kin dade sai na fadi gaskiya”
Juya mata baya Basma tayi dan ji take kamar ta tashi ta shaƙe ta.

Sallah na fara yi kafin na shiga wanka na fito na zauna gaban mirror, nayi shafe shafena, wata hoda da muka saya a Saudiyya ni da Aunty laila na mitstsika nan take fuskata ta ƙara wani irin kyau da sheƙi, na zizara jam baki, na gyara girata.
Wajen kayana na koma kayan da muka lafto a Saudiya nake ta duba wadda zan sanya,idona ya tsaya kan wata abaya me masifar kyau, wadda kai da ka gan ta ba sai an gaya maka ita ɗin me tsada ba ce, na ciro ta na sanya, ɗan kunne me kamar awarwaro na sanya sai agogo na fata na daura a hannuna, na soma fesa turare, wayata tayi kara alamar shigowar sako, na kai hannu na ɗauko ta ina dubawa, daga megidan ne yana shaida min isowar baƙin, kan gadon na maida wayar, na janyo takalmi, me tsini ne da ya shiga da rigar, na yane kaina da gyalen abayar, sai na fito na rufo ƙofar.

Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi yasa jama’ar da ke zaune falon kai dubansu inda nake, Halima kwalliyar shadda aka sha Latifa kuma less, baƙon da matarsa na zaune cikin two sitter sai namu Ogan da ke zaune a kujrerar da ke kusa da abokin nasa.
Na ƙarasa ina musu sannu da zuwa, sai da muka gaisa da mijin kafin matar wadda ta ke me fara’a ce da matuƙar wayewa, ta dubi Tahir
“Wannan ita ce amaryar taka?
Mijinta ya duba “Ka ji matarka ko? ba ga ki ga su nan ba”
Noƙe kafaɗa tayi “Na ƙi wayon, kai za ka faɗa min”
Na miƙe tsam na wuce kitchen, cincin na zubo musu da coconut milk pudding na kawo, an dauki lokaci ana fira cikin raha, kafin na gayyace su cin abinci, sai mamakin Latifa nake yanda ta zake wurin yin saving din bakin kamar ita ta dafa.
Shiru kake ji sai ƙarar cokula ke tashi, kafin abokin me suna Muhammad ya dubi Tahir, “Gaskiya abokina ka samu duniya, bayan nasarar mallakar mata har huɗu, ga kuma daddaɗan abinci ana shirya maka”
Flate ya yi saurin kanga masa “Ya kamata in maka waigi dan na lura santi ke ɗawainiya da kai”
Cokalin da ya debo dambu ya zuba bakinsa, ba zan musa maka ba wallahi, in ma ka ce santin nake, gimbiyata za ta zo koyon abin nan har ma da cincin ɗin da na ci”
Tahir ya ce “Dambun kake ce ma abin nan?
Ya ɗan bude ido “Kai mutumina wannan daddaɗan abincin ne dambu?
Su Latifa da Halima na saci kallo, kowace yaƙe kawai take, matar tashi me suna Asiya ta yi murmushi “Wai ina ɗaya matar ba hudu bane?
Tsit aka dan yi kafin me gayya me aikin ya ce
“Da yake bata jin daɗi, ba ta dade da fitowa daga Hospital ba”
Addu’ar samun sauƙi suka yi mata, Ogan ya miƙe “Bari in dubo ta”
A kwance take kan sopa, Gwoggonta na zaune kan carpet tana gyangyadi, jin motsin sa yasa ta bude ido sai ta miƙe ta shiga ciki bayan ya gaishe ta,
duban Basma ya yi ta cikin farin glass dinsa, ganin ya ki magana yana kafe ta da mayun idanuwansa, yasa tsoron shi ya fara rufe ta.
“Meye hujjar ki na zama a daki? bayan na shaida muku za mu yi baki”
Shiru tayi dan bata da wata hujja, har ya ƙare fadansa tana sauraran sa hakuri ne dai ba za ta iya bayarwa ba, ya juya ba tare da ya waiwayo ba ya ce “Ina jiranki, kuma kar ki sake ki ce za ki fito min a yadda kike”
Kyabe baki tayi tana kallon rigar jikinta, tsaki tayi sai ta miƙe, wata doguwar rigar ta canza
ta kama hanya ta fita cikin daure fuska,kamar yanda take kullun ba fara’a.
Da fara’a mata da mijin suka tare ta, sai dai sam ta ƙi sakin fuska, hannuwanta ta dogare a saman cushion, suna kuma gama gaisawa ta juya ta koma ɗakinta.
Asiya ta dan ƙara matsawa kusa da mijinta “Allah honey abin nan fa yana ta ban mamaki, wai wannan hand some ɗin shi ne da wadannan manyan matan har huɗu kuma duk matansa ne”
Murmushi ya yi “Kin raina mu kenan? shiru tayi dan ganin Halima na kallon su, tana gudun kar su ji,
Latifa da Halima dai sai
jan Asiya da fira suke, ni dai ina zaune ina sauraren su har sai in Asiyar ta jeho ni cikin zancan.
An kwala kiran sallar la’asar Tahir da Muhammad suka fita zuwa masallaci, ni ma na miƙe na dubi Asiya “Bari in shiga in yi sallah”
Ita ma miƙewar tayi “Muje ni ma in yi”
Halima da Latifa da aka gyara zaman shan fira da bakuwa, suka raka mu da mugun kallo.
Muna shiga ita na fara cewa ta shiga tayi alwalar sai nima nayi,
muna idarwa mun yi addu’a ta dube ni “Ina shigowa gidan nan na gan ki na ji kin min, sunanki Ummulkhairi ko?
Na daga mata kai ina murmushi “Uwar alkhairi kenan ta fada ita ma tana murmushi “Kuma na gane wannan daddaɗan abincin da muka ci har sweetyna na santi ke kika yi shi”
nan ma murmushi na kuma yi mata, “To yaushe za a fara koya min?
Na ce “Duk sa’adda kika shirya”
Ta ce “To shi kenan, ki bani lambarki”
na faɗa mata ta sa sai ta kira ta shigo, nima sai nayi saving.
Muna ta fira ta faɗa min gidansu na nan a millennium City, sai da mijinta ya kammala ginin sa sannan suka dawo”
na ce Allah sarki, mu ma namu ginin anan unguwar yake yin sa”
ta ce “E na ji suna maganar layi biyu ne a tsakani”
mun yi fira sosai da ita dan bata da wuyar sabo, har sai da Tahir ya leƙo “Ina kuke ne?
Na tsinkayi muryar sa, fitowa nayi ina faɗa mishi “Ga mu nan” sai da ya kalle ni sai ya ce
“Ya za ki riƙe baƙuwar a daki? na ce “Mun yi sallah ne” ya ce “To ta fito za su tafi”
Na ce “To” na koma ciki na shaida mata, sai da ta gyara fuskarta ta fesa turare, na dauko wata humra nayi mata kyautarta,sai muka fito.
A fuskar matan za ka karanci canjin da suka samu, dan takaici ne ƙarara a fuskarsu, gaba ɗaya muka fito dan musu rakiya, sai da suka zauna cikin mota na bude bayan motar na ciro kwalin da nake sunne da shi cikin hijab na cake din da nayi musu na ajiye shi, suna godiya muna yi suka ja motar su suka tafi.
Sauri nayi na riga su wucewa zuwa ciki na shiga kitchen, tuwon semo miyar kuka da ta ji wadataccen nama da kayan ƙamshi nayi saboda Ogan, a sanin da nayi shi din me san tuwo ne, da muka kammala muka shirya komai da Indo ɗakina na wuce nayi sallah sai na sake kwalliya da wata riga doguwa kalarta danyen kore, me guntun hannu, ta kamani dam a jikina , sai na yane kaina da wani dan siririn gyale, ina zura takalmi sai na fito kitchen na shiga cake din da nayi na raba na ba Indo ta kai wa matan, na haura sama dan ajiye wa ogan na shi.
Na fito na zauna ba daɗewa ya shigo tare muka haura saman na hada mishi ruwan wanka, saukowa ta na samu matan dukan su sun fito, Latifa ce kawai ta ce min sai ga cake an kawo, sauran ba wadda ta tofa.
Sai da ya fito aka ci abincin wanda kowa ya gane ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba, ranar an yi fira har goma da rabi.
Mun yi shirin kwanciya har na soma barci na ji hannun mutum jikina,
“Ya kamata in miki tausa, ta ban gajiyar aikin da kika sha a yau”
Ya tallafo ni jikinsa ina kokarin ƙwace jikina in kwanta na ce “Ni ban gaji ba, barci kawai nake ji”
al’amuran da yake min yasa dole na watstsake na biye masa, sai da komai ya lafa ina maƙale jikinsa na ce “Ya kamata a ce mun soma shiri na tsarabar da za a kai wa mutanen gida”
dan tsaki ya ja “Ni bana wata tsaraba” na ce “Shi kenan idan muka je, sai ka basu kuɗaɗe su sayi abinci, dan ka san ba lokaci me wahala a wurin mutanen mu na gida irin wannan lokacin na damina, abinci ya koma gona”.
Daga haka nayi shiru, shi ma shirun ya yi.
Duban ta ya yi ganin har ta soma barci, miƙewa ya yi ya shiga bathroom wanka ya yi ya tsaftace kansa sai ya fito gindin window ya tsaya idanunsa na kallon harabar gidan, “Kwarai tun yana yaro ya san ba lokacin da ake shiga kaka ni ka yi irin lokacin damuna a karkara, amma me yasa tunaninsa bai taba ba shi ya maida hankali wurin taimakon ƴan’uwansa a irin wannan lokacin?
har sai da wannan yarinyar ta tunasar da shi.
Ya dade tsaye cikin tunani kafin ya ja ƙafarsa zuwa gado ya kwanta.

Da safe bayan fitar megidan makaranta, kwanciya kawai nayi sai da na sha barcina kafin na fito nayi musu abincin rana, na fita girki kenan, Latifa ta karba sai rawar ƙafa ake, ana kai da kawo, aka shirya abinci ga kwalliya an caba,
an zauna zaman cin abinci dan rashin dabara ganin idan nayi tuwo ogan na ci sosai yasa ta ita ma yin tuwon, ni tun a ido da na kalla girkin bai bani sha’awa ba,na dai zuba, lomar farko da na kai na tsame hannuna dan wani amai da ya taso min.
Ashe bani kaɗai ba ce ogan cewa ya yi “Latifa wannan wace irin miya ce?
Mur ta sha kamar yanda shi ma ya sha, “Miyar har daban daban ce?
Dan tsaki ya ja “Ai sai ki sha ki ji”
Halima ma ta taɓe baki
“Hala ba ki dandana ba?
Shiru tayi musu sai ta debo ta kai baki dan ta ji dalilin wannan tozarci da ake mata, rashin kan gadon miyar ta ta yasa ta ji kamar ta maido ta, amma tilas ta tauna ta hadiye.
Sai tayi ta yan duniya
“Meye to a cikin miyar?
“Daga ba komai ai sai ki ci” Tahir ya bata amsa yana tura kujera, sai ya bar wurin zuwa saman shi, matan ma da ɗai ɗai da ɗai ɗai suka zare aka bar ta da tulin abinci a gaba, kamar ta fasa kuka.

Basma na shiga ɗaki ta samu Gwoggonta ta tasa abincin tayi jugum, ganin Basma yasa ta miƙe “Wallahi gobe gida za ni, ban zama gidanki yunwa ta kashe Ni”
Bata yi magana ba sai juyawa da tayi kitchen fresh yougourt ta ɗauko da glass cup, ta dire gaban gwoggon ta ta, gorar ta galla wa harara
“Wai shi zan sha in kwanta? ina fama da ulser? Ni lariya na kawo kaina”
Da kukanta share share ta kira baban Basma, ta ce ya turo direba gobe ya tafi da ita yunwa za ta halaka ta.
Ran mahaifin Basma ya yi matuƙar ɓaci ya katse kiran, ya shiga lalubar lambar Tahir.

 

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter Eight

Key ɗinsa yasa a kunnensa yana dan sosawa, “Madam sarkin aiki” murmushi nayi, “Ni zan dan fita, zan dawo kafin isowar baƙin”
daga haka ya juya na bi bayansa, ina mishi a dawo lafiya. Sai da ya shiga motarsa sai na juyo, ban lura da Latifa da kawarta da ke zaune akan fararen kujeru, a can kusa da wasu Flowers, sun zura mana ido tun fitowar mu, sai da na iso daf da su sannu na musu, sai dai ban san ko Latifa ta amsa ba, wadda suke tare dai ta amsa hada gaishe ni.
Miƙewa Fadila tayi hada buɗe baki, Latifa ta kamo ta ta zaunar, “Ke meye?
Ajiyar zuciya ta fidda, “Wai Latifa me nake shirin gani ne?
da sauri ta ce “Me kika gani?
“Wace ce wannan da ta wuce? matsiyacin tsaki ta ja, “Ita ce nake bi a gidan Tahir”
Ido waje Fadila ke dubanta, “Kina nufin kishiyarki ce?
tsaki ta kuma ja bata yi magana ba.
“To wallahi ita ce na gani jiya tare da Tahir ɗinki”
Wani kishi ne ya soki kirjin Latifa, har ta gwammace wata macen ce ta waje aka ga Tahir da ita. “Sai kin dage Latifa, yana da irin wannan a gida lafiyayyar mace maka malam, da ko wane namiji zai so ta kasance kusa da shi.
In ma banda tarangahuma irin ta ɗa namiji, me kamar wannan har ya ƙara ganin wata macen ya ce zai dauko ya karo cikin gidansa. Ko da yake mijin naku gwarzo ne, mata hudu reras ka…..
“Idan kin gama zagina Fadila, sai ki tashi ki tafi”
Latifa ta katse ta cikin fushi, kama hannunta tayi “Yi hakuri ƙawata, amma dai gaskiya sai kin dage, tunda kin ce ita waccan ta Abujan bata da power a gidan.
Ni wannan ina ce ita ce kika ce min yar ƙauye ce”
Baki ta taɓe “Yar ƙauye ce mana, an zo birni an sha jar miya sai a ka kile”
Fadila za ta kara magana Latifa ta daga mata hannu “Na fa san ki Malama, kada ki ce min jarabar taki ta rasa inda za ta tashi sai kan kishiyata”
Baki ta lasa “To mu bar wannan maganar, akwai wani magani da na kawo miki, yana da matukar kyau, sai dai tsada, samun maganin ba ƙananan kuɗaɗe na karɓa a hannun alhazan birni ba”.
Sai sannan Latifa tayi murmushi “Yawwa yanzu na ji batu, muje ki bani”
ciki suka shiga riƙe da hannun juna, sun ratsa falon da basu samu kowa ba zuwa dakin Latifa, ta bata maganin tare da bayanin yadda za ta yi amfani da shi.
Ta nemi ta bata kudin maganin, transfer tayi mata, ta taɓa kafadarta
“Muje falon nan naku ƙawata, ban gajiya da ganin sa, kana cikin sa kamar kana ƙasar waje, ba fa ƙaramin dace kika yi da samun gayen nan ba, ga shi ya haɗu ga masu gidan rana ya tara”
Cije lebe tayi “Ke dacen kawai kika hango, ba ki tuna bakar wuyar da na sha kafin in samu nasarar shigowa in amsa sunan matar sa”
tafawa suka yi “Haka ne fa dan ni ba ma zan iya ba, ba dan namiji guda aka yi ni ba”
Lumshe ido Latifa tayi “Ba za ki gane ba ƙawata, gwarzon maza ne ogana, ban taba samun namijin da ya shiga raina irin sa ba, namiji ne da zai sa ki manta sunanki, ya iya tarairayar mace ya jiyar da ita daɗi”
Fadila za ta yi magana txt ya shigo wayarta ta soma dubawa sai suka fito.
Suna zaune ina ta hada hadar shirya abinci, duk na bi na tsargu saboda mayataccen kallon da kawar Latifa ke bi na da shi, dama tunda na gan ta hankalina bai kwanta da ita ba, bata yi kama da masu kamun kai ba.
Ban da wani banzan ɗinki da ta sa har sarƙa na gani a kafarta, ga gashin doki da ta yarbatsa a kanta.
Ina samu dai na kammala sai na wuce su zuwa ɗakina.
Latifa ma miƙewa tayi “Ke gidan fa yau manyan baki za mu yi, wani babban abokin Ogan ne da ke zaune a Abroad zai zo da matarsa, bari in shiga in shirya kar a raina ka cikin kishiyoyi”
Ita ma miƙewar tayi
“Shi kenan nima bari in ƙarasa, akwai wanda muka yi alkawarin haduwa”
Ta taka mata sai ta dawo ta wuce ɗakinta dan shiryawa, tare da ƙara jaddada kudirinta na kulla abota da matar abokin ogan nasu.

Ita ma Halima a nata fannin kudirinta kenan kulla alaƙa da matar abokin ogan dan haka shiri take tayi ita ma.

Saɓanin Basma da ke kwance bisa kujera tayi ɗaiɗai, bata ma da niyyar shiryawa, kallon Gwoggonta take wadda ke zaune tana cin abinci tana fadin “Kai wannan yarinya akwai baiwar iya girki, kana ci kunnenka na motsi, ga ta kuma yar albarka ita kadai za ta yi girki ta aiko min da shi har daki, girkinta ne kawai kuma za ka ci abinci me daɗi”. Basma da ke kallon Gwoggon ta ta cikin fushi ta ce “Haba mana Gwoggo kishiyar tawa kike ma wannan yabon?
Kallonta tayi “To ai ni dai kin san in gaskiya ta zo bani boye ta, fadin ta nake”
Cikin kumbura baki ta soma kunkunai “Ni dai ba a kyauta min ba wallahi”
“In ma zagina kike kin dade sai na fadi gaskiya”
Juya mata baya Basma tayi dan ji take kamar ta tashi ta shaƙe ta.

Sallah na fara yi kafin na shiga wanka na fito na zauna gaban mirror, nayi shafe shafena, wata hoda da muka saya a Saudiyya ni da Aunty laila na mitstsika nan take fuskata ta ƙara wani irin kyau da sheƙi, na zizara jam baki, na gyara girata.
Wajen kayana na koma kayan da muka lafto a Saudiya nake ta duba wadda zan sanya,idona ya tsaya kan wata abaya me masifar kyau, wadda kai da ka gan ta ba sai an gaya maka ita ɗin me tsada ba ce, na ciro ta na sanya, ɗan kunne me kamar awarwaro na sanya sai agogo na fata na daura a hannuna, na soma fesa turare, wayata tayi kara alamar shigowar sako, na kai hannu na ɗauko ta ina dubawa, daga megidan ne yana shaida min isowar baƙin, kan gadon na maida wayar, na janyo takalmi, me tsini ne da ya shiga da rigar, na yane kaina da gyalen abayar, sai na fito na rufo ƙofar.

Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi yasa jama’ar da ke zaune falon kai dubansu inda nake, Halima kwalliyar shadda aka sha Latifa kuma less, baƙon da matarsa na zaune cikin two sitter sai namu Ogan da ke zaune a kujrerar da ke kusa da abokin nasa.
Na ƙarasa ina musu sannu da zuwa, sai da muka gaisa da mijin kafin matar wadda ta ke me fara’a ce da matuƙar wayewa, ta dubi Tahir
“Wannan ita ce amaryar taka?
Mijinta ya duba “Ka ji matarka ko? ba ga ki ga su nan ba”
Noƙe kafaɗa tayi “Na ƙi wayon, kai za ka faɗa min”
Na miƙe tsam na wuce kitchen, cincin na zubo musu da coconut milk pudding na kawo, an dauki lokaci ana fira cikin raha, kafin na gayyace su cin abinci, sai mamakin Latifa nake yanda ta zake wurin yin saving din bakin kamar ita ta dafa.
Shiru kake ji sai ƙarar cokula ke tashi, kafin abokin me suna Muhammad ya dubi Tahir, “Gaskiya abokina ka samu duniya, bayan nasarar mallakar mata har huɗu, ga kuma daddaɗan abinci ana shirya maka”
Flate ya yi saurin kanga masa “Ya kamata in maka waigi dan na lura santi ke ɗawainiya da kai”
Cokalin da ya debo dambu ya zuba bakinsa, ba zan musa maka ba wallahi, in ma ka ce santin nake, gimbiyata za ta zo koyon abin nan har ma da cincin ɗin da na ci”
Tahir ya ce “Dambun kake ce ma abin nan?
Ya ɗan bude ido “Kai mutumina wannan daddaɗan abincin ne dambu?
Su Latifa da Halima na saci kallo, kowace yaƙe kawai take, matar tashi me suna Asiya ta yi murmushi “Wai ina ɗaya matar ba hudu bane?
Tsit aka dan yi kafin me gayya me aikin ya ce
“Da yake bata jin daɗi, ba ta dade da fitowa daga Hospital ba”
Addu’ar samun sauƙi suka yi mata, Ogan ya miƙe “Bari in dubo ta”
A kwance take kan sopa, Gwoggonta na zaune kan carpet tana gyangyadi, jin motsin sa yasa ta bude ido sai ta miƙe ta shiga ciki bayan ya gaishe ta,
duban Basma ya yi ta cikin farin glass dinsa, ganin ya ki magana yana kafe ta da mayun idanuwansa, yasa tsoron shi ya fara rufe ta.
“Meye hujjar ki na zama a daki? bayan na shaida muku za mu yi baki”
Shiru tayi dan bata da wata hujja, har ya ƙare fadansa tana sauraran sa hakuri ne dai ba za ta iya bayarwa ba, ya juya ba tare da ya waiwayo ba ya ce “Ina jiranki, kuma kar ki sake ki ce za ki fito min a yadda kike”
Kyabe baki tayi tana kallon rigar jikinta, tsaki tayi sai ta miƙe, wata doguwar rigar ta canza
ta kama hanya ta fita cikin daure fuska,kamar yanda take kullun ba fara’a.
Da fara’a mata da mijin suka tare ta, sai dai sam ta ƙi sakin fuska, hannuwanta ta dogare a saman cushion, suna kuma gama gaisawa ta juya ta koma ɗakinta.
Asiya ta dan ƙara matsawa kusa da mijinta “Allah honey abin nan fa yana ta ban mamaki, wai wannan hand some ɗin shi ne da wadannan manyan matan har huɗu kuma duk matansa ne”
Murmushi ya yi “Kin raina mu kenan? shiru tayi dan ganin Halima na kallon su, tana gudun kar su ji,
Latifa da Halima dai sai
jan Asiya da fira suke, ni dai ina zaune ina sauraren su har sai in Asiyar ta jeho ni cikin zancan.
An kwala kiran sallar la’asar Tahir da Muhammad suka fita zuwa masallaci, ni ma na miƙe na dubi Asiya “Bari in shiga in yi sallah”
Ita ma miƙewar tayi “Muje ni ma in yi”
Halima da Latifa da aka gyara zaman shan fira da bakuwa, suka raka mu da mugun kallo.
Muna shiga ita na fara cewa ta shiga tayi alwalar sai nima nayi,
muna idarwa mun yi addu’a ta dube ni “Ina shigowa gidan nan na gan ki na ji kin min, sunanki Ummulkhairi ko?
Na daga mata kai ina murmushi “Uwar alkhairi kenan ta fada ita ma tana murmushi “Kuma na gane wannan daddaɗan abincin da muka ci har sweetyna na santi ke kika yi shi”
nan ma murmushi na kuma yi mata, “To yaushe za a fara koya min?
Na ce “Duk sa’adda kika shirya”
Ta ce “To shi kenan, ki bani lambarki”
na faɗa mata ta sa sai ta kira ta shigo, nima sai nayi saving.
Muna ta fira ta faɗa min gidansu na nan a millennium City, sai da mijinta ya kammala ginin sa sannan suka dawo”
na ce Allah sarki, mu ma namu ginin anan unguwar yake yin sa”
ta ce “E na ji suna maganar layi biyu ne a tsakani”
mun yi fira sosai da ita dan bata da wuyar sabo, har sai da Tahir ya leƙo “Ina kuke ne?
Na tsinkayi muryar sa, fitowa nayi ina faɗa mishi “Ga mu nan” sai da ya kalle ni sai ya ce
“Ya za ki riƙe baƙuwar a daki? na ce “Mun yi sallah ne” ya ce “To ta fito za su tafi”
Na ce “To” na koma ciki na shaida mata, sai da ta gyara fuskarta ta fesa turare, na dauko wata humra nayi mata kyautarta,sai muka fito.
A fuskar matan za ka karanci canjin da suka samu, dan takaici ne ƙarara a fuskarsu, gaba ɗaya muka fito dan musu rakiya, sai da suka zauna cikin mota na bude bayan motar na ciro kwalin da nake sunne da shi cikin hijab na cake din da nayi musu na ajiye shi, suna godiya muna yi suka ja motar su suka tafi.
Sauri nayi na riga su wucewa zuwa ciki na shiga kitchen, tuwon semo miyar kuka da ta ji wadataccen nama da kayan ƙamshi nayi saboda Ogan, a sanin da nayi shi din me san tuwo ne, da muka kammala muka shirya komai da Indo ɗakina na wuce nayi sallah sai na sake kwalliya da wata riga doguwa kalarta danyen kore, me guntun hannu, ta kamani dam a jikina , sai na yane kaina da wani dan siririn gyale, ina zura takalmi sai na fito kitchen na shiga cake din da nayi na raba na ba Indo ta kai wa matan, na haura sama dan ajiye wa ogan na shi.
Na fito na zauna ba daɗewa ya shigo tare muka haura saman na hada mishi ruwan wanka, saukowa ta na samu matan dukan su sun fito, Latifa ce kawai ta ce min sai ga cake an kawo, sauran ba wadda ta tofa.
Sai da ya fito aka ci abincin wanda kowa ya gane ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba, ranar an yi fira har goma da rabi.
Mun yi shirin kwanciya har na soma barci na ji hannun mutum jikina,
“Ya kamata in miki tausa, ta ban gajiyar aikin da kika sha a yau”
Ya tallafo ni jikinsa ina kokarin ƙwace jikina in kwanta na ce “Ni ban gaji ba, barci kawai nake ji”
al’amuran da yake min yasa dole na watstsake na biye masa, sai da komai ya lafa ina maƙale jikinsa na ce “Ya kamata a ce mun soma shiri na tsarabar da za a kai wa mutanen gida”
dan tsaki ya ja “Ni bana wata tsaraba” na ce “Shi kenan idan muka je, sai ka basu kuɗaɗe su sayi abinci, dan ka san ba lokaci me wahala a wurin mutanen mu na gida irin wannan lokacin na damina, abinci ya koma gona”.
Daga haka nayi shiru, shi ma shirun ya yi.
Duban ta ya yi ganin har ta soma barci, miƙewa ya yi ya shiga bathroom wanka ya yi ya tsaftace kansa sai ya fito gindin window ya tsaya idanunsa na kallon harabar gidan, “Kwarai tun yana yaro ya san ba lokacin da ake shiga kaka ni ka yi irin lokacin damuna a karkara, amma me yasa tunaninsa bai taba ba shi ya maida hankali wurin taimakon ƴan’uwansa a irin wannan lokacin?
har sai da wannan yarinyar ta tunasar da shi.
Ya dade tsaye cikin tunani kafin ya ja ƙafarsa zuwa gado ya kwanta.

Da safe bayan fitar megidan makaranta, kwanciya kawai nayi sai da na sha barcina kafin na fito nayi musu abincin rana, na fita girki kenan, Latifa ta karba sai rawar ƙafa ake, ana kai da kawo, aka shirya abinci ga kwalliya an caba,
an zauna zaman cin abinci dan rashin dabara ganin idan nayi tuwo ogan na ci sosai yasa ta ita ma yin tuwon, ni tun a ido da na kalla girkin bai bani sha’awa ba,na dai zuba, lomar farko da na kai na tsame hannuna dan wani amai da ya taso min.
Ashe bani kaɗai ba ce ogan cewa ya yi “Latifa wannan wace irin miya ce?
Mur ta sha kamar yanda shi ma ya sha, “Miyar har daban daban ce?
Dan tsaki ya ja “Ai sai ki sha ki ji”
Halima ma ta taɓe baki
“Hala ba ki dandana ba?
Shiru tayi musu sai ta debo ta kai baki dan ta ji dalilin wannan tozarci da ake mata, rashin kan gadon miyar ta ta yasa ta ji kamar ta maido ta, amma tilas ta tauna ta hadiye.
Sai tayi ta yan duniya
“Meye to a cikin miyar?
“Daga ba komai ai sai ki ci” Tahir ya bata amsa yana tura kujera, sai ya bar wurin zuwa saman shi, matan ma da ɗai ɗai da ɗai ɗai suka zare aka bar ta da tulin abinci a gaba, kamar ta fasa kuka.

Basma na shiga ɗaki ta samu Gwoggonta ta tasa abincin tayi jugum, ganin Basma yasa ta miƙe “Wallahi gobe gida za ni, ban zama gidanki yunwa ta kashe Ni”
Bata yi magana ba sai juyawa da tayi kitchen fresh yougourt ta ɗauko da glass cup, ta dire gaban gwoggon ta ta, gorar ta galla wa harara
“Wai shi zan sha in kwanta? ina fama da ulser? Ni lariya na kawo kaina”
Da kukanta share share ta kira baban Basma, ta ce ya turo direba gobe ya tafi da ita yunwa za ta halaka ta.
Ran mahaifin Basma ya yi matuƙar ɓaci ya katse kiran, ya shiga lalubar lambar Tahir.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter Nine

Tahir wanda ke kwance
bisa gadonsa, idonsa
yana kallon sama ya
tada kai da hannayensa,
a zahiri za kayi tunanin kyakykyawan rufin dakin
nasa yake kallo, amma a
baɗini tunani me zurfi ya faɗa.
Matan da ya tara,
kowacce da irin
matsalarta, saboda
rashin dace da samun
me aikin da ta iya girki,
yasa shi saka dokar kin
amincewa da ƴan aiki su
girka abincin da zai ci.
To matan nasa ma, Basma da Latifa sai
godiya, abincin suka
kwabo maka shi, sai dai
ka ci kar ka mutu,
ummulkhairi da Halima
ne kaɗai ya dace ta
wannan fannin, Halima
tunda ya auro Basma ta
ga ta zo da me aiki, a rashin dabara irin nata
sai ta watsar, ta bar yi ita ma.
Idan ya nemi ta yi masa wanda zai ci sai ta ƙi,
idan ya nemi hukuntata. sai ta ce dan ita ba diyar masu kudi ba ce shi
yasa.
Dan da za a kawo Basma
ta taho da me yi mata
aiki, yawan gutsiri tsoma
daga Halima yasa dole
ya tattara me aikin Basma ya sallame ta,
yasa a ka kawo ta gida
duka, Halima mace me
matuƙar tsafta da gyara,
shi ma zuwan Basma
kasantuwar ta mace me dan banzan ganin kyashi
ta watsar da ko kauda tsinke a cikin gidan.
Cikinsa da ke kuka ya dawo da shi hayyacin sa,
ba shi da zaɓi, dole miƙewa ya yi, dan ko
abincin rana bai ci ba
Makaranta ya shiga da ya tashi ya tafi duba harkokinsa, flaks din da ake zuba mishi Black tea
ya ɗauko ya tsiyaya,
Cake din da ummulkhairi ta kawo masa ya dauko ya hada yana sha, ya
kusa kammalawa Latifa
ta fado dakin, kallo ɗaya
ya yi mata ya maida
kansa ya cigaba da abin
da yake, duk da uban kishin da ta ji, ganin yana
cin cake din nan, haka nan ta jure, tana ta mishi kwarkwasa har ya gama
duk abin da zai yi suka
kwanta.

Bayan me aukuwa ta auku, Latifa har ta shiga
barci, sai minsharinta ke
tashi a dakin, dubanta kawai ya yi ya ja tsaki, jin sabon al’amarin da ya bakunce shi yasa shi miƙewa, wanka ya yo ya dawo ya kwanta, sai dai ina, al’amarin da ɗa gaba yake, duka ya ɗaɗa mata wadda ta yi ɗaiɗai kamar wadda za a yanka, zafin dukan yasa ta farkawa duk da nauyin barcin ta.
“Sweety lafiya? ta fada tana mutsutstsuke ido,
ƙara tamke fuskarsa ya yi, “Me kika sa a gabanki?
ya haddasa min ƙaiƙayin gaba da zafi”.
Faduwar gaba ta ji, tare da saurin watstsakewa
“Ni kam me zan sa? ni ban sa komai ba”
Shiru ya mata yana jin al’amarin na ci gaba, sun kai wani lokaci tana rantse rantsen ita bata saka komai ba.
Gajiya ya yi ya bata wuri, alwala ya dauro ya shiga sallah, tun tana sa ran zai gama har barci ya sace ta, cushion ya koma ya kwanta.
Yana dawowa sallar asuba Dr Muhammad ya kira, ya shaida mishi abin da ya same shi, ya ce ya same shi gida.
Har ya gama shirin sa ya fita Latifa na barcin ta,
haushin ta kuma da yake ji ya hana shi tashin ta, sai da ya zagaye ɗakin matan nasa kafin ya fice,
yana tashin motar wayar mahaifin Basma ta shigo, wanda tun jiya yake neman wayar bai samu ba dan a rufe take, bai kula da gaisuwar da Tahir yake masa ba cikin izza ya soma fadin
“Wane irin riƙo kake wa ƴata har gwoggonta za ta zo zama da ita a bar ta da yunwa, to ba zan lamunta ba,
har Basman zan turo direba ya ɗauko min su.
Dole sai mun yi zama na musamman, na gindaya sharadi kan zamanta”.
Shiru Tahir ya masa har ya ƙare maganganunsa ya kashe wayar, ɓacin ransa ne ya nunku kan wanda yake ciki.
Ɗora kansa ya yi bisa sitiyari, ya jima kafin ya ba zuciyarsa magana, ya tashi motar, sai ya bar gidan.
Latifa bata tashi ba sai bakwai, rashin ganin Tahir yasa ta shiga neman sa, gane ya bar gidan yasa ta saukowa zuwa ɗakinta, sai da ta kintsa ta shiga kitchen da taimakon Indo ta hada abin karin, suna yi tana bugun cikin Indon dan ta ji yanda ummulkhairi take haɗa abincinta, da kalolin maggin da take amfani da su, sai dai duk yadda ta kai da bugun cikin ta kasa fahimtar komai, gane ba za ta gane komai ba yasa tilas ta hakura, tana kara ɗaura mummunar manufarta kan ummulkhairi.
Mun fito mun karya, ni dai na ci abincin ne kawai dan tsoron saba umarnin megidan, wanda na san su ma haka ne.
Shigowar kosassun matan su biyu ya samu zuba ido muna kallon su,ba su yi ma kowa magana ba, sai Basma da ta miƙe ta nufe su tana fadin “Anty kune da safiyar nan?
Wadda ke gaba ta taɓe baki, sai a sannan kuma na gane ta, matar babanta ce da na taɓa gani a asibiti,
“Ba dole mu yi zuwan safiya ba, daga gidan naku an koma zama da yunwa”
gaba dayan mu zuba mata ido muka yi jin zancenta, suka wuce ciki zuwa dakin Basma, sun samu Gwoggon na shan tea, dan daidai da kwan da Latifa ta soya ta ce bata ci, sama sama suka gaisa matar baban ta dubi dakin, “Ya baku haɗa kaya ba?
Cikin rashin fahimta Basma ta ce “Wane kaya za ta haɗa ban da na cikin jakarta”
Fuskantar Basman tayi “Babanki hada ke ya ce min in zo mishi, dan ba zai lamunci zama da yunwa ba”
“Yunwa kuma? Basma ta tambaya cikin haɗa rai ƙawar Auntyn ta kama haɓa “Ga gida dai har gida, kai ba za ka taba tunanin na ciki zai san wani abu yunwa ba”.
A fakaice Basma ta harare ta, “Ni gidana ba yunwa, duk wanda ya ce ma akwai yunwa karya yake”
Gwaggon ta dauki salati ni ke miki karya Basma sai ta fara fyace hanci “Ni ban ce ba abinci ba, amma matan gidan ba su iya ba, ni kuma ba zan iya ci ba”
ta nufi wurin jakarta ta ɗauka, “Ku mu kama hanya Hajiya usaina”
Antyn ta ce “Basma ki shirya mu wuce dan hada ke mahaifinki ya ce min” tura baki tayi “Ni ba inda za ni, haka kawai mijina bai min komai ba a ce sai na tafi”
Nan fa suka kada suka raya amma Basma ta kafe, wayarta ta ciro ta kira mahaifin Basma dan shaida mishi abin da kenan, ya nemi a bata wayar, sai ta ruga da gudu ta hau gado tana kuka, tilas ya ce su rabu da ita.

Dan ɓacin rai Tahir bai dawo gidan ba sai yamma likis, ya sha mamakin ganin Basma dan shigowar sa ya yi daidai da fitowar ta kitchen ta dauko ruwa,
sun kalli juna kafin ya wuce ta zuwa ɗakinta, sai ga ta “Me kika zauna yi a nan? ba ki bi umarnin mahaifinki ba”
Bata yi magana ba, baƙaƙen maganganu ya gaigaya mata tana ta kuka, a zatan sa ita ta kai karar sa gidansa ana zama da yunwa, har ya karaci maganganun sa ya fita kuka take tayi.
Kiran matan nasa ya yi gaba ɗaya, faɗa ya yi da sa musu doka kan kula da girkin gidan da kuma wajabcin ayi me daɗi.
Su fa dama masu kudi dole ana musu alfarma”
maganar Halima kenan take fadi ƙasa ƙasa “Me kike cewa?
Tahir ya tambaye ta, “A’a cewa nayi daga masu kudi sun zo gidan nan suna yada maganar gidan nan ana zama da yunwa, ka ga ai baka ga laifin ƴar su da ta ɓata ka ba, sai mu da aka raina aka sanya mu riƙa wa ƴar gwal abinci me daɗi.”
Glass din idonsa ya zare,
“Ni Halima ni kike faɗa wa magana haka kai tsaye irin wadda tayi miki daɗi?.Baki ta murguda “Yo ƙarya nayi”.
nan suka shiga sa in sa abin ba ko tsari a gaban mu, Basma da Latifa babu wadda ta tanka sai ni na bada hakuri, wani ashar ta lailayo ta danna idan na kara sa mata baki.
Dan haka tsam na miƙe nayi ɗakina, ganin missed call a wayata yasa na duba Asiya ce, baki na rufe dan na ji kunya, kira nayi tana ɗauka na soma bata hakuri ta ce ba komai, ni da na damu da ke ba ga shi na kira ba, na dafe kai “Dan Allah ki dubi girman sa ki yi min uzuri, kina raina ina ta son kiranki Allah ne yasa sai an yi hakan” ta ce “Shi kenan, ya gidan ya na bar ku?
Na ce lafiya lau” mun shiga fira har muna dariya ta ce “Yaushe za ki zo min yini? Na ce sai na tambayi ogan ina za ta gan ni” ta ce “Meye sirrin humrar da kika bani”
na ce “Sirrin kenan abin da kika gani” muka yi dariya ta ce “Na yarda ta sirrin ce, ina so a min hanya zan saya”
Na ce “Kuma idan kika ga Aunty Kulu za ki dara”
ta ce “Kwarai kam dan na ga alamun hakan”
muka yi dariya, mun sha fira kafin muka yi sallama, jin hayaniya har lokacin yasa ni bude kofa, Halima ce ke kuka, Tahir yana tsaye yana fadin wallahi yau sai ta bar masa gida, dan wallahi ya gaji da zama da matar da bata ganin girman sa. Haj Hajara ita ma iyakar karfinta take ba shi hakuri, ganin abin ya ci tura yasa ta kira Kawu Attahiru a waya, shi kuma ya ce ta ba Tahir wayar, dan baya Kaduna ya koma Lagos.
Ta waya ya yi mishi magana, tsallake su ya yi ya haura sama, Haj Hajara ta kama ta zuwa ɗakinta, tana kara gaya mata girman miji.

Washegari maigidan na fita Halima da Latifa suka take masa baya,
sai dai kowacce da inda ta nufa, Latifa unguwar su makeran kakuri gidan su kawarta Fadila tayi wa tsinke.
“Za su haukata ni! Za su haukata ni! Za su haukata ni Fadila”
Kalmomin da take ta maimaitawa kenan yayin da ta daga labulan ƙofar ɗakin kawar ta ta, Fadila da ke kwance kan luntsumemiyar katifar da ke yashe tsakar ɗakin nata ta tashi zaune.
“Lafiya ƙawata? “Ina fa lafiya, na rasa inda zan tara waɗannan ƴan iskan kishiyoyin ko ogan kansa,
ban shiga da niyyar barin kowacce shegiya ba.
Amma yi nake kamar ba nayi”. Ta ƙarashe zancan tana fashewa da kuka. “Ki zauna ƙawata mu yi magana, me ya faru?
Zaman tayi tana lissafa mata irin matsalolin da take fuskanta.
Na rasa yanda zan yi in yi girki ya gamsar da me gidan, in yi a ce ba daɗi, dan sheri har gwoggon waccan shashashar Basman wai ta kasa zama dan ana yin abinci ba ta iya ci,
shi kuma ogan ya zo yana mana bala’i.
Ke kuma maganin da kika amsar min uban kuɗaɗe, mun kwanta da shi, ya tsare ni sai na faɗa mishi abin da nasa ya haifar mishi da ƙaiƙayin gaba da zafi”
Fadila ta zaro ido “Ni ba ta garin nan ba yaƙi ya ci kwartuwa, to ni dai wallahi salin alin duk wanda nasa mawa sai san barka”.
Ta ja mummunan tsaki, “Ai duk ke kika ja, muna zaman zaman mu, muna murza rayuwa kika haukace kan gayen nan ke sai kin aure shi”
Latifa ta share idonta ni dai ki bar wannan maganar, mu nemi mafita”
Fadila ta gyara zama
“Yawwa za mu shiga kasuwa, duk wani littafin girki ki tabbatar kin mallake shi, haka nan daga kin ji kin gani dole ki zage dantse, sannan akwai wani sabon malami a sabon kawo za mu kai mishi ziyara.
Maganin mata kuma ai ba dainawa za ki yi ba”
Saurin girgiza kai Latifa tayi “A’a ba yanzu ba tukuna, mutumin nan shu’umi ne, ganewa zai yi” sun jima suna kullawa da kwancewa kafin Latifa ta dubi agogo,
“Wucewa zan yi Fadila, sai dai gobe, yau zan yi girkin rana”.
Taɓe baki Fadila tayi “Girki dai girki dai! haka kawai ki takura rayuwarki, ban iya zama namiji guda na juya ni”
Miƙewa Latifa tayi tana daukar gyalenta “Shekaru sun fara ja Fadila, gwara kayi wa kanka faɗa kayi auren, tun ba a kare yayin ka a bariki ba” wani uban tsalle Fadila ta daka “Wa! wallahi yanzu na fara bariki , ko tatata ban fara ba a bariki rarrafe nake”
Latifa ta gyaɗa kai “Shi kenan, muje ki rakani suka fito, sai sannan Latifa ta ga mahaifiyar Fadila sun gaisa suka yi waje. Wani yaro da bai wuce shekaru bakwai ba ya ce “La! Aunty Latifa”
diban su suka kai inda yake “Taye ina za ka? maimakon ya maida mata da hausa sai ya amsa mata da yarensu.
Sun wuce shima ya ruga cikin gidan su dan fadin ya ga Latifa, dan ƙanwarta ne da ke zaune gidan su tana zawarci, “Ba za ki shiga gidan ku ba? Fadila ta tambayi Latifa, “Sauri nake ba zan shiga ba”
Nafef suka tare Latifa ta shiga ita kuma ta juya.

Ban samu zuwa karbo dinkunana ba sai da aka kwana takwas, dan na roƙi Tahir zuwa gidan Asiya, da direba muka fita sai da ya fara kai ni na karbo dinkunan wadanda suka yi matuƙar kyau, sai muka karasa gidan Asiyar.
Kyakykyawar tarba na samu daga gare ta, sai fira muke kafin daga bisani muka shiga kitchen, girke girke masu kayatarwa muka yi.
Da rana da Muhammad zai dawo sai ga su shi da Tahir, sun jima har bayan la’asar da za su fita ya ce in zo mu wuce gida, amma sai Asiya ta shiga rokon sa ya bar ni zuwa dare akwai girkin da za muyi kan dole ya bar ni.
Sai da nayi sallar isha’i ya zo muka taho, bayan Asiya ta faɗa mishi akwai friend ɗinta da ta haihu za ta zo muje suna tare. Tahir ya ce “Za dai ki buɗe wa matata ido ta san gari”
dariya tayi ta ce “Ni dai zan zo” ya ce “Sai kin zo”.

Yana gaba ina biye da shi muka shiga falon, duka matan suna zaune da alama zaman ganin shigowarmu suke ina riƙe da ƙatuwar ledar dinkunana.
By

 

 

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter Ten

Sama ya wuce Halima ta bi shi a baya dan ta samu ya sauko ya daina fushin da yake da ita, ita ke da shi kuma a yau take son tambayar sa kuɗaɗen da za ta yi amfani da su kan tafiyarta gida.
Shiyasa ta danne bala’in da ke cin zuciyarta na fitar da ya yi da ummulkhairi suka kuma kai dare. Tayi mishi iya abin da za ta yi masa sai ta sauko inda ta samu Basma da Latifa, zama tayi suna yar firar su da Latifa, “Wai ina labarin kudaden da abokin Sweety ya bamu ranar da suka zo da matarsa?” Latifa ce ke tambayar Halima,
Wani duba Halima ta mata “Wane abokin Sweety kuma?
Dan murmushin kin raina min hankali Latifa tayi, kuɗaɗen da ya ajiye da za su wuce kin san ko kowa bai gani ba ni na gani kuma ba yarda zan yi ba sai an bani hakkina”
Cikin hasala Halima ta taso “To ba za a bayar ba”
Nan fa suka kaure ka ce na ce, na fito zan shiga kitchen na wuce su suna tayi, ba su san da zuwan ogan ba sai tsawar da ya daka musu ita ta sa kowaccen su shiga cikin nutsuwarta, ya kuma ce duk wadda ta kuma magana yau sai dai ta kwana gidan su.
Halima ta fara wucewa ɗakinta kafin Latifa ta bi bayanta. Latifa na shiga ɗakinta ta buga tsalle ta faɗa kan katifa, “Ko dai ban samu kuɗin ba na bata mata daren” ta fadi cikin farin ciki.

Nima na fito na wuce ɗakina ina tunanin wannan rashin zaman lafiya na wannan gida, kamar nan aka fara zaman kishi.
Na daɗe zaune barci bai ɗauke ni ba tunanin farkon haɗuwa ta da Tahir da rayuwata ta baya na gilma min a cikin ido.

Zawarci bai yi ba! Ita ce kalmar da ta subuce a fatar bakina, yayin da na zauna dabas kan wata tabarma da na samu a shimfide a barandar gidan mu.
Hannuna na kai kan goshina na share zufar da ta tsatstsafo min,
Mahaifiyata da ke fitowa daga kitchen ta dube ni cikin kulawa, “Har kin dawo ummulkhairi?
“E Amma” na bata amsa ba tare da nayi fara’ar da kowa ya san ni ya san ni ma’abociyar ta ce, “Hala ba ki samo kuɗaɗen naki ba?
Ƙara bata rai nayi ina turo baki “Ina fa Amma sai bakar tafiyar da na sha da uwar ranar da na kwaso, Allah daga yau na haƙura da sai da ƙwan”.
Wani kallon mamaki ta bi ni da shi, sai dai kafin ta kai ga magana gwoggo Rabi abokiyar zamanta ta fito daga ɗakinta, “Anya ummulkhairi, me zai sa ki daina? kina dan samun abun biyan bukatunki na yau da kullum.
Gwoggon ce tayi maganar na ce “Allah Gwoggo Balarabe me shayin ne dan rainin hankali, sai ya yi ta wahalar da ni.
Yasa ni in ta jerangiya bisa hanya.
Sun ci gaba da maida zancen, wanda duk lallashi na suke da nuna min alfanun sana’a komai kankantarta.bani da niyyar yarda da cigaba da saida kwan, dan haka miƙewa kawai nayi na wuce daki hijab din da na shigo da shi na sauya zuwa na makaranta, na fito nayi wa su Ummanmu sallama,
“Ba za ki tsaya ki ci abinci ba ummulkhairi an kusa saukewa? na ɗan yamutsa fuska, “Nayi latti Umma idan na dawo na ci” da damuwa a fuskarta ta ce “Shi kenan sai kin dawo”
Na sa kai na bar gidan.

Ƙarfe ɗaya da minti biyar aka tashe mu, sanawiyya nake ina shekarar ƙarshe, maimakon in wuce gida sai na shiga wurin ƙawata Hafsat mijinta shi ke da makarantar,
na samu tana sallah dan haka wucewa nayi na dauro alwala na kabbara tawa sallar kusa da ita.
Tana idarwa miƙewa tayi ta shiga kitchen ɗinta ta fito daidai ina kammala addu’o’ina, ɗauke take da wani tray me faɗi ta dire shi gabana, gaisawa muka yi kafin ta kafe ni da ido, na san me take nufi dan haka sai na shiga buɗe kwanonin ina cewa “Ƙawata Sarkin girki me aka girka mana?
ƴar harara ta bani “Sai ka ce ci take” siririyar dariya na saki”Ina ci mana”
Waina ce shar shar da tayi matukar bada sha’awa a ido, sai kwanon miyar miyar taushe ce da ta ji wadataccen tantaƙwashi, na karshen farfesun yan ciki ne sai kunun aya shi na tsiyaya na sha kafin na zuba waina biyu ta ce ban isa ba sai na kara na kara biyu farfesun ma kadan na zuba da na kammala ci na kara kunun ayan sai na rufe komai na koma kan kujera na miƙe, ba tare da na damu da kallon da Hafsa ke min ba. Ta gaji ta ce “Ƴar rainin wayau ki rasa wa za ki yi wa fulatanci sai ni, komai na kawo maki ki ci sai ki ƙi ci”
ƴar dariya nayi “Iyakar cikina kenan, wa zan yi wa fillancin ke?
Ta ce “Yawwa Baban Ramlah na neman ki, tun jiya ya bar min sallahu, ya ce in kin shigo in shaida miki”
Ido na buɗe na tashi zaune “Lafiya dai ko? Malam ke nemana, me ya faru? kafadarta ta noƙe “Bai faɗa min ba, amma na san yana hanyar shigowa”
Sallamar sa muka ji littafin da ke a riƙe a hannunsa yasa na gane daga makaranta shi ma yake, kujera ya samu ya zauna, cikin nutsuwa na gaishe shi, kamar yanda shi ma yake a nutsen.
Cikakken ustaz ne wanda jama’a suka shaida tsantseninsa da gudun duniyar sa, a takaice malami ne me matuƙar tsoron Allah an shaide shi kan rashin hulda da mata, ko ni da yake yarda mu zauna har muyi fira saboda na kasance ƙawar Hafsa da bata da wata kawa sama da ita, tun muna yara har girmanmu, shi ɗin malaminmu ne ya koyar da mu muna yammata, lokacin ya dawo karatu daga Misra.
Yin aurensu ba daɗewa ya sayi tafkeken fili ya gina gida hada masallaci da islamiya, a hankali makarantar ke bunƙasa, har ta zama tana daga cikin makarantun da ake ji da su a garin namu Dutsinma, saboda koyarwarta.
Gama gaisawar mu ya ce “Hafsa ta fada miki sakona? Kai na daga mishi tare da cewa “E”
Ya ce “Yawwa dama muna neman malami ne, da zai riƙe mana aji biyu na ɗaliban safe, shi ne na ce bari in tuntube ki ko za ki yi” wani farin ciki na ji ya lullube ni, ƙara nutsuwa nayi “Zan yi malam” ya ce “Yawwa daga yau muna Laraba idan Allah ya kaimu Asabar sai ki fara”
Na ce “Allah ya kaimu malam na gode”
Tashi ya yi ya wuce dakinsa, Hafsat ta bi bayan sa, zuwa can sai gata ta same ni tsaye cikin shirin tafiya “Har za ki yi me?
Ta tambaye ni “Wucewa zan yi Hafsa, ke ko ai na daɗe Umma tana can tana zuba ido ta ga ta inda zan ɓullo”. muka yi murmushi ta rako ni nan nake bata labarin shawarar da na yanke ta daina saida ƙwai, na kara da cewa”Kina jin mu da malam?
ta ce “Na ji kin zama Malama, Allah yasa daina saidawar shi ya fi alheri” na ce “Amin” .

Na nufi gida, inda na shaida ma su Ummata koyarwar da na samu, su ma murnar suka taya ni dan hukumar Saudiyya ta san da zaman makarantar, dan haka akwai albashi me kauri ga malaman makarantar.

Washegari babu makaranta dan haka sharar tsakar gida nayi kamar yanda na saba, sai na zubo koko na matsa Ummata ta zuba min suga na zauna na sha, gamawata kayan wankin mu ni da Ummata na haɗo na wanke su tas, sannan nayi wanka kwalliya nayi sama sama sai nasa atamfata, farin hijab na saka sai na ɗauki pos ɗi ta, na gaya wa Umma zan karbo kuɗaɗena wurin Balarabe.
Inda na saba tsayawa nan na tsaya na aika yaro ya min magana da shi, sai ga shi da saurin shi, sai kallona yake na tambaye shi kuɗina, ya buɗe baki zai soma gaya min in yi hakuri in dawo na tsaida shi ta hanyar daga mishi hannu, “Ya isa Balarabe, wannan shi ne zuwana wurinka na ƙarshe, matuƙar baka bani yau ba to ka riƙe na haƙura, ba za ka sake ganina da niyyar zuwa karɓar kuɗi ba”
Ƙara zuba min ido ya yi
“Na ji amma me zai hana ki bani dama in zo ƙofar gidan ku? kin fi kowa sanin irin son da nake miki, haba wai so ya taɓa zama laifi?
Ya ƙarashe maganar yana wani marairaicewa.
Taɓe baki nayi “Son ne yasa kake wahalar da ni?
idan aka kawo maka kwai sai in yi sati kana wahalar da ni, ina famar gantali a hanya.
Ƙara kwantar da murya ya yi “To ya kike so in yi idan na zo gidan ku wannan yayan naki ya hanani ganin ki, in ba hakan nayi ba ta yaya kike gani zan samu in gan ki?
Miyau na haɗiya “Indai wannan ne damuwarka ya kusa tafiya karatu, sai ka zo abin ka”.
Farin ciki ne ya mamaye fuskarsa “Ki ce Allah?
Wani busashshen murmushi na sakar masa “Zan maka karya ne?
Hannu yasa a aljihu ya ciro kudade ya kirga sai ya miƙo min, na ga karin dubu biyu kan kuɗina, na dube shi murmushi ya sakar min “Ki sayi hoda” na ce “Na gode”
Muka rabu ni da shi kowa cike da farin ciki, shi na jin yayana Mustapha zai tafi karatu ya samu ya rika zuwa wurina zance kamar yanda na tsara shi. Ni kuma ina murnar zare zaren da nayi na karbi kuɗaɗena, me kama da ni ma ba sake gani zai ba.
Fara saida ƙwai na ya samo Asali ne bayan mutuwar aurena, akwai yayata sana’ar ta kenan, sai mijinta ya yi sabon gida suka tashi, shi ne ta shawarce ni ko zan cigaba da kai wa costomominta, shi ne fa shi yana ƙyalla ido akaina sai ya ɗafe min shi dole so na yake yi.
Ranar da ya fara zuwa ƙofar gidan mu da sunan ya zo tadi yayana Mustapha ya kore shi, ni kuma ya kwakwkwara min zagi wai ni wawuya ce da ban san kaina ba, kowane tarkace sai ya kwaso jiki ya ce ya zo zance wajena karshen lalacewa hada wani me shayi.

Ban shiga gida ba sai da na biya wani shago na sayi yadikan hijabai kala uku dan su nake fatara, sai takalma su ma kala uku masu sauƙin sakawa, ban shiga gida ba sai da na shiga gidan su Hafsa wurin mahaifiyarta, muka yi fira.
Fara koyarwata ya rage min wahalhalu idan aka bani albashi na kan sayi yan kayan bukatuna na mata.

Wata ranar Asabar da ba zai yiwu in mance ta ba cikin tarihin rayuwata, na nufi makaranta cikin sauri dan makarar da na zabga, tun daga get na ɗaga likab dan ajin yammata nake, kuma doka ce ta makarantar su daga likab, saboda kama wani da aka yi cikin matan ya sanya hijab da likab.

Ganin akwai malami ajin mu yasa jikina sanyi kar ya hana ni shiga, cikin sanyin nayi sallama, juyowa ya yi yana dubana baƙon malami ne wanda ban taɓa gani a makarantar ba sai yau, idanuwansa suka yi min kwarjini sai na sunkuyar da kaina.

Daga ina haka sai yanzu ake zuwa makaranta?
Muryarsa ta ƙara jefa ni cikin wani yanayi, sai da ya ƙara tambayata nayi ƙarfin halin ba shi amsa da cewa “Daga gida nake”
“Amma kin san kin yi latti ko?
Ban yi magana ba sai ma kara sunkuyar da kaina da nayi, “A’a ɗagowa za ki yi ki dubi agogo”
Dole na dubi agogon, “Na yi latti a yi haƙuri” a raunane na faɗa dan yadda duk na bi na muzanta da zuba min ido da ƴan ajin suka yi.
“Shi kenan zan haƙura amma bisa sharaɗi, ni sabon malami ne da zan riƙa ɗaukar ku darasin matanin risala asabar da Lahadi, kun yi girman da ba sai an an riƙa dukan ku ba, dan haka duk wanda ya yi laifi zan mishi tambaya ne kan karatun da a kayi.
Dan haka yanzu kun tsaya wane babi ne?
Na ce “Mun gama babin zakatul fiɗr mun soma babun fil hajji wal umra.
“Da kyau” ya faɗi yana gyaɗa kai,
“A yanzu za ki gaya min inda mutanen kasar Sham da Misra da magrib, da juhaifa, da mutanen Iraqi da Yaman suke ɗaura niyyar su?
Ban ko yi gargada ba na jero mishi su, ya sallame ni ya ce in je in zauna.

Sabon malamin nan ya cigaba da ɗaukar mu darasi a ranakun Asabar da Lahadi, sai dai zuwan sa ajin namu sai ya dauki wani sabon salo game da yammatan ajin, basu da wani zance sai na shi, idan ya shigo ajin ya kan rasa nutsuwarsu, surutun da suke barkewa da shi ya kan sa shi fita ya bar musu ajin, wanda su kuma ba haka suke so ba suna yi ne dan ya san da su, dan wai ai ranar da ya fara shigowa lattin da nayi yasa ya yi min tambayoyi kuma tun daga ranar da ya shigo ajin ni ce dai yake wa magana.

Ranar wata Laraba na tashi dalibaina na fito, malam Mas’ud mijin Hafsa na gani zaune da bakon malamin nan, wanda har sai da na ji mamaki dan tunda ya soma koyar da mu, bai taɓa zuwa in ba ranakun Asabar da Lahadi ba.
Na shige su zuwa cikin gidan, shanya na samu tana yi ta tsame hannunta tana min murmushi, “Har kun tashi?
Na daga mata kai sai na shige ɗakinta, mug na gani saman fridge ɗinta dauka nayi na ce “Zobo akayi kenan? saurin cire shi a bakina nayi ina yamutsa fuska, “Ashe ma tsimi ne”.
Karɓa tayi ta shanye “To ya ba ki sha ba? wani kallo na mata “Dalili da me kuwa zan sha, ni ba miji ba ba kwakwkwaran farka ba”.
Dariya muka yi ta ce “Kina tsaye ba ki zauna ba duk satin nan ma sai cigiyar ki nake ba ki shigo ba.
Na ce “Da an tashi gida nake wucewa, yanzu ma sauri nake wanki gare ni, kin san ranar Asabar za mu tafi suna Katsina na Aunty Rahma”. Baki ta rike”An ko yi haka, amma ya kamata ki fitar da miji mu kuma sai mu sha biki zaman ya isa haka”. Na ce “Sai ki taya ni addu’a, dan duk masu zuwan ban gane kansu ba”
ƴar dariya tayi “Dama mazan kawuna ne da su?
Muka yi dariya.
Jin gyaran muryar malam ya sa mu shiga nutsuwarmu, sallama ya yi sai ya shigo na gaishe shi ya ce “Sai sauri nake in shigo kar ki fito, son ki ake ummulkhairi, shi ne aka biyo ta hannuna”. Shiru nayi ina sauraren sa. Ya cigaba “Aikin hajji muka yi ni da shi mun shaku matuka, a Kaduna yake zaune duk da yake haifaffen ƙanƙara ne, zai zo ku daidaita, ya damu in nema mishi izni a gidan ku”
Ba tare da na ɗago ba na ce “Allah ya kawo shi”
Ya ce “Amin mutumin kirki ne abokin nawa, matansa biyu sai dai bai taba haihuwa ba” Saurin haɗa ido muka yi da Hafsa, “Mata biyu kuma Hafsa ta fadi cikin damuwa.
Ni kuma na ce “Tsoho ne kenan abokin naka malam?
Dan murmushi ya yi Wa ya ce miki tsoho ne? idan ya zo za ki gan shi”
Ya fadi yana ficewa daga dakin. Dariya muka yi tayi ni da Hafsa dan shiririta muka ɗauki abin wace ila ni kam ta kai ni auren me mata biyu?
Hafsa ma haka ta ce.

 

Rike
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter Eleven

Tun komawata gida na manta da batun, sai shirin tafiya suna Katsina nake, matar yayana ce ta haihu sosai yayan nawa yaso in je in zauna har sai tayi arba’in, karatuna da kuma koyarwar da nake ta hana ni tafiya.
Na samu dai daga makaranta an bar ni in yi sati, ranar sunan muka tafi, can yan sunan suka baro ni, sai da nayi sati na dawo.
Washegari Lahadi na koma makaranta, da aka tashi ina ta sauri in wuce gida,dan ko gidan Hafsa ban yi niyyar shiga ba, a gajiye nake kwarai, dan tun da na je gidan jegon ban zauna ba.
Wani dalibi ke kirana “Malama na tsinkayi kiran, ya karaso inda nake “Malam ya ce ki zo”
“Wane malam? na tambaye shi da mamaki
Shiru ya yi wanda ya bani tabbacin bai san sunan malamin ba, “Yana ina? na kuma tambayar sa “Office din malam Mas’ud” ya faɗi yana nuna min da hannunsa.
Na juya zuwa can da tunanin shi ke kirana da sallama na tura ƙofar, tsaye yake ya juya baya fitinannen ƙamshin turarensa da a kullum ya shiga zai fita ya bar mu da shakar daddaɗan ƙamshin nasa, ya fallasa min gane waye, gaba ɗaya ya waiwayo bakon malaminmu ne, sanye yake cikin fara kal din jallabiya idonsa sanye cikin farin glass, wanda tun soma ganina da shi ban taba ganin shi babu shi ba, sumar kanshi ya shafa idanuwansa na kaina, sauri nayi na soma gaishe shi, ya amsa a hankali, yana nuna min wurin zama da hannunsa, na ɗosana mazaunaina kan daya daga cikin kujerun Office din. Kafe ni ya yi da idanuwansa da suka yi matuƙar tasiri a jikina, dole na sare na sunkuyar da kaina. “Me ya hana ki zuwa makaranta tsawon sati guda? Muryar sa ta ratsa dodon kunnena, mamaki ya kama ni jin tambayar ta sa ya aka yi yasan sati daya ban zo makaranta ba? shi da yake zuwa karshen mako kaɗai.
Na dai daure na ce “Haihuwa aka yi mana a Katsina”
“Shi ne sai a tafi har tsawon sati?
Shiru nayi cike da mamakinsa.
Na daɗe zaune ba tare da ya bani umarnin tashi ba, sai ni nayi ƙarfin halin tambayarsa izinin tafiya, shiru ya min sai da aka kara wasu mintunan ya sallame ni, na fito cike da takaicinsa.

Da daddare muna shirin kwanciya Umma ta ke ce min malam Mas’ud ya yo ma wasu dattawa jagora sun zo neman iznin fara neman aurenki” wani banbarakwai na ji ina bazawara wai sai an tambayi neman aurena, taɓe baki nayi, ganin na ki cewa komai yasa ta tambaya ta na ce “Matansa fa biyu me ya ja min faɗa wa mata har biyu?
Kabli da ba’adi tayi ta kawo min, ni dai nayi mata shiru har barci ya kwashe ni.

Ranar da malam ya ce Abokinsa zai zo ina koyarwa a aji yasa aka kirani, na fita na same shi ya ce “Ya kika zo makaranta ummulkhairi?
nayi zaton za ki zauna a gida dan yin kwalliyar taron baƙon naki” murmushin da yake zaton zan yi ban yi ba, cewa nayi “Ina ganin har mun tashi malam”
Ya ce “A’a yana hanya, ki je gida kawai zan sanya a riƙe miki ajin”
Na ce “To” gidan na wuce bayan ya bani wata leda me ɗauke da gororin ruwan faro da su maltina
da Hollandia, ya ce in ba baƙon. Ina shiga gida Umma ta ce “Ya aka dawo tun lokacin tashin bai yi ba?
Turo baki nayi “Wai yau bakon da Malam ya ce,
zai zo”
faɗa ta rufe ni da shi na kin faɗa mata ranar zuwan na shi da nayi.
Da kanta ta ta je ta share dakin yayana da nake bi mawa da kanena me bi min, ta gyara ta saka turaren wuta, ni dai sai dubanta nake ta gama ta zo ta ce “Ba za ki yi wanka ki ɗan gyagygyara ba? na ce “Nayi wanka kafin in fita” ta ɓata rai “To na ce ki ƙara”
Na ce “Wai ke Umma ko sanin mutum ba ki yi ba amma duk kin tashi hankalinki da zuwan sa”.
Hararata tayi “Meye abin tashin hankalin duk wanda kika ga kafin ya zo neman aure ya fara da neman izini, kin san na kirki ne. Kuma malam Mas’ud ya yi yabon halayensa”. Shiru nayi sanin halinta in ta tsaya kan tana son abu, mafi a’ala ka barta kawai.
Girki ma na ga ta ɗora, hada kazarta ta sa aka yanka, gwoggo ta ce min Baƙona za ta yi wa miya.
Kan ba yanda zan yi na sake sabon wanka nayi kwalliya, ina sa kaya na ji muryar malam Mas’ud suna gaisawa da su ummarmu, da sauri na zura hijab.
Yaron yayata da ake riƙo cikin gidan mu ya shigo ya ce in zo ana kirana, gabana na ji yana faduwa.

Na isa ɗakin cikin sanyin jiki, kaina a kasa malam ne ya amsa sallamar da nayi, gaisuwar da nayi musu ma shi ɗin ne ya amsa, ya ƙara da “Alhamdulillahi yau ga Ummulkhairi ga Tahir ƙanƙara” gabana na ji ya tsananta bugu dama tun shigowata na shaƙi ƙamshin turaren nake zargin kar dai a ce shi ne?
Ina fata za ku fahimci juna?
Muryar malam ta dawo da ni nutsuwata, miƙewa ya yi suka yi musabaha ya fice. Shiru ne ya biyo baya kafin ya yi gyaran murya, “Da farko sunana Tahir Abdurrahman ƙanƙara, ana kirana Sodangi a gidan mu, ai kin san dalilin da ke sa ake sanya wa yaro suna Sodangi ko?
Kai na yi saurin daga mishi, ya cigaba “Abokaina na kirana kankara, ku kuma kuna kirana da bakon malami, ko ba haka kuke cewa ba?
Shiru nayi ya cigaba “Ni haifaffen ƙaramar hukumar kankara ne ta nan jihar Katsina, amma a Kaduna na tashi, na dai dawo gida nayi auren farko, maaikaci ne ni, ina kuma taba kasuwanci, matana biyu. Tunda ya fara magana nake satar kallonsa dan mamaki da ya lullube ni, kwata kwatan shi ba zai wuce shekaru talatin da biyar zuwa da bakwai, amma ya ajiye mata har biyu yana hankoron tarkato ta uku. Ba shi irin tsawon nan duk kuwa da cewa shi ɗin ba gajere bane,
irin masu ginannen jikin nan ne, dan haka ba shi da ƙiba kuma bai cikin ramammu, fatar jikinsa da alama baka ce, amma tsananin gogewa da hutun da ya bayyana a jikinsa ya mayar da shi chaculate color.
Ba wani matsanancin kyau yake da shi ba, sai dai yana da matuƙar kwarjini da wasu irin fararen idanuwa masu ɗaukar hankalin mata ga kyakykyawar sumar kai da ta kara sa shi ya haɗu ya zama irin namijin da kowace mace za ta yi ma kanta sha’awar a ce shi ɗin nata ne.
Sai so nake in ji ya yi magana game da maluntarsa sai dai naji shiru bai yi ba. Ban san na shagala ina dubansa ba sai da na ji yana kiran sunana, kunya kuma ta lullube ni na sunkuyar da kaina, sai na amsa a hankali, magiya ya yi ta min in dube shi, da kyar na tada kai na kuma kallonsa, fararan idanuwansa da ke cikin glass ya kafe ni da su, maida kaina ƙasa nayi dan wani abu da naji yana yawo a cikina.
Mun jima har Ummata ta aiko da shiryayyen girkin da tayi mishi, zama sosai ya yi kan yar chanese carpet din da aka shinfida dan shi ya ci abincin, da na nemi in ba shi wuri hanani ya yi sai tsiya yake min wai daga jin wannan abincin girkin manya ne ba ni nayi ba.
Ni dai zaune kawai nake mamakinsa ya kusa kashe ni, ko kadan bai nemi jin ta bakina ba, ina son sa koko? A’a sai kokarin da yake na kiran sunana, wanda muryarsa take matukar tasiri a jikina, kuma ya ce sai na dube shi.
Idanuwan nasa ma ba sauki bane kallon su, ni kaɗai na san me nake ji da ya kammala ya ce in mishi iso zai shiga ya gaida su Umma”
Na wuce yana biye da ni har ɗakinmu, na bar shi da ita suka gaisa, ya bata tarihinsa kamar yanda ya faɗa min, kuɗaɗe ya ajiye mata, wanda tayi ta fadin ya dauki kudinsa.
Miƙewa kawai ya yi na kai shi ɗakin gwoggo, ita ma kuɗaɗen ya ajiye mata ya fito.
Ganin na tsaya ya waiwayo ya yafito ni, sai da muka je zaure ya ce “Ba ki raka ni ba? ya rungume hannayensa a ƙirji, yana kallona “Ba ki ce in gaida iyalina ba? dan jim nayi ba tare da na ɗago ba na ce “Afuwan ka gaishe su”.
Ya ce “Ki bani nombar mama” na kira mishi ya sa, nayi mamakin bai nemi tawa ba, sai ta Ummata. Taɓe baki nayi shi dai ya sani, na dai samu ya tafi.

Da daddare mun yi shirin kwanciya Ummata ta dube ni da murmushi a fuskarta, “Da alama mijin aure ya zo Ummuna”.
Na ce “Kai Umma?
Ta ce “Allah kuwa na yaba ƙwarai da shi, ai ni tunda ya biyo ta hannun malam na ji ya yi min.
Za a je har kankarar a yi bincike, Alh ma me mutane a can. Riƙe haba nayi “Kai Ummata, daga ganin mutum, ni gaskiya ban ma ji zan iya auren sa ba”.
“Saboda me? ta ce min cikin gatse, “Ni da ganin shi zai yi son mata duk ya bi ya kafe ni da ido”.
Umma ta fara hasala, “Ya yi miki maganar banza ne?
Na girgiza kai “To wallahi kika kuskura kika kore shi yanda kika saba yi wa masu zuwa, kowa da matsalar da za ki karanto mishi, ni da ke ne a gidan nan. Banda kina shashasha, mutuwar auren ki shekaru biyu kenan, har ƴan zannuwan da kika fito da su sun soma sanyi, kina raɓe komai sai an ba ki? Ƴan’uwanki kowacce tana ɗakinta, ba za ki yi fatan kema ki tafi naki ɗakin ba”
Tura baki nayi “Amma fa Umma matansa biyu”
Tsaki ta ja “To sai me? ni uwarki mu nawa muka zauna banda mutuwa da ta maida mu mu biyu.
Halin mutum ai jarinsa, da halinki za ki zauna”.
ganin ko ta ina na ɓullo ma Umma ba nasara yasa nayi shiru cikin tunani.

Gari na wayewa sai ga kiran sa, ya gaishe da Umma, ita kuma ta bada wayar aka kawo min.
Haka ya yi tayi kullum safiya sai ya kira Umma har yasa da an kira wayarta sai ta ce a duba mata, in shi ne sai ta ce a kawo min,
a rana sai ya kira sau biyar, dabarar tashi kuwa sosai ta ci, dan sai faɗa Ummana take min na samu me sona zan wulaƙanta.

Ranar wata juma’a na kai wa ƙanwata Hauwa’u ziyara, ubanmu daya.
Sai fira muke yaro ya yi sallama, ya ce “Ana sallama da ummulkhairi”
duban juna muka yi da Hauwa’u kafin na dubi agogo, “Amma waye wannan da rana gatse gatse?
Ta ce “Ki je ne Aunty sai ki gani”.
Ban ƙi ba hijab na sa sai na fito, a raina ina ta saƙa Allah yasa in samu wanda nake so, kafin Umma ta sa ni auren me mata biyu.
Kalle kalle nake dan samun nasarar gano me kirana, jikin wata bishiya na hango shi, shi ɗin ne dai Tahir Sodangi cikin shigarsa ta jallabiya, da farin glass ɗinsa manne a idonsa.
Karasawa nayi inda yake cikin mutuwar jiki, sallama nayi masa kafin na gaishe shi, ya ce “Daga kankara nake, na ga ba zan iya komawa kaduna ban gan ki ba”.
Yake nayi Na ce “Za mu ƙarasa gida ne?
Kai ya girgiza “No daga nan zan gan ki in wuce, da me mashin suka haɗo ni, ya kawo ni nan”
Na ce Uhmm ya ce “Na gan ki zan wuce, me zan samu?
Nayi turus kafin na yi ƙarfin halin cewa “Me to kake so?
Murmushinsa me tsada ya yi “Da wasa nake, ba yanzu ba”
Ledar da ke hannunsa ya miƙo min, na ɗora hannuwana saman hancina “Haba dai ya za ka ɗora wa kanka ɗawainiya? Idanuwansa ya watso min, ba shiri na miƙa hannu na karɓa, sallama muka yi nayi mishi fatan sauka lafiya.
Da shiga ta Hauwa’u ta karbi ledar tana fadin, “Aunty tayo samu”.
Sai ta buɗe, set ne na mai da sabulu da turare masu tsada.
Hauwa’u sai yaba kyautar da aka yi min take cikin murna da zumudi, musamman da ta fidda dalleliyar waya samfurin Samsung S10, ni kam tunani na faɗa cikin nazari anya kuwa mutumin nan me mata har biyu, ina ya samu wa’annan uban kuɗaɗen da ya yi min wannan sayayyar dan ya burge ni? ni fa ba irin wadannan matan ba ne, duk da jikinsa na nuna akwai hutawa da kwanciyar hankali a tare da shi.
Muryar Hauwa’u ta dawo da ni daga tunanin, “Kai Aunty wannan babba ne, irin wannan babbar waya haka?
ta kunna ta sai ta kawo “An riga an yi charging ta hada layi Aunty” ban samu abun ce mata ba sako ya shigo miƙo min tayi,
“Ga waya a kira kowa, amma banda rival ɗina.
Abinda sakon ya ƙunsa kenan,
Hauwa’u ta matso “Duba account balance ɗin, na san ba zai rasa zuba miki kuɗaɗe ba”
Maimakon dubawar wayar na miƙa mata,
da murnarta ta ce “Wallahi five thousand Aunty”
Na fidda ido ita kuma ta kama dariya “Kawai daddaɗan text message za ki tura mishi yanda za ki ƙara sace zuciyarsa”
harararta nayi “Ba ki da hankali Hauwa’u, matansa biyu fa mutumin, ta hannun malam Mas’ud ya biyo malamin mu ne, duk da cewar da aka yi yana aiki kuma yana kasuwanci, ina tsoron ya tarkato rigima ya riƙa kawo min dan ya samu shiga wajena, in zo in aure shi yan bashi su taso mana mu shiga uku”.
Duk da jikinta ya yi sanyi sai cewa tayi “In sha Allahu ma ba haka ba ne Aunty, mutumin kirki za ki aura wannan karon wanda zai riƙe ki har mutuwa.”
Na ce “Allahu ya sha”
Ledar kayan na tura mata gabanta “Haɗa su ki adana, har wayar ba amfani zan yi da ita ba”.
Marairaicewa tayi “Saboda me Aunty?
nan dai tayi ta min magiya har ta samu na yarda zan riƙe wayar,
Su turare da mayukan da sabulun nan na barta da su, duk yadda ta kwaɗaita min kyan su za su gyara min skin, na ce ta ajiye min.
Yamma sosai na bar gidanta na nufi gida.

Bayan magrib mazan gidan mu duk sun shigo ana cin tuwo, kanena Nura ya ce “Wallahi Ummu tayi babban kamu, kun ga ƙatuwar wayar da me son ta ya kawo mata? wal…….
“Dalla ko ba wani ustaz da ta yayibo ba”
Yaya Mustapha ne ya katse shi, sai kuma ya juyo kaina “Wawuya ke kuma da ba ki san kanki ba, haka auren farko kika yayibo wanda ya kasa riƙe ki, yanzu ma daga wannan garan ya zo sai wancan saunan. Yanzu kuma kin kwaso ustaz zai yaudare ki da ƙatuwar waya t….
Tsawar da Umma ta daka mishi ta sa shi yin shiru, dan daga cikin mu ba wanda ya ga zuwanta. Ni dama tuni na fara hawaye,
faɗa ta shiga yi mishi
kan idan ba zai mini fatan alheri ba kar ta kuma jin bakinsa.
Kwanon tuwon da nake ci na ɗauke sai na kai kitchen, ɗaki na wuce na kwanta sai share hawaye nake, wayar ta shiga ƙara , na miƙa hannu sai na dauko ta, ina ɗagawa muryarsa ta daki dodon kunnena.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: Maryam: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter twelve

Ba dai har kin soma barci ba?
ban ba shi amsa ba illa gaishe shi da na shiga yi,
“Ki kunna datarki muyi fira” na amsa da to sai ya kashe wayar.
Daurewa kawai na riƙa yi wurin ba shi amsar maganganun da yake min, dan har dalilin mutuwar aurena ya tambaye ni, ni ma nayi ƙarfin halin yi mishi complain kan kyautar da ya yi min tayi yawa, shi me iyali da yawa kar ya shiga hakkinsu.
Amsar da ya bani ita ce “Kin sa ni dariya sosai Ummuna, a takaice dai kina min nasiha da kar in ciyo bashin jama’a in riƙa kawo miki, dan son samun haɗin kanki, ganin ƙarfina bai kai na yin kyautar ba”
Mamaki ne ya rufe ni ya aka yi ya gane nufina? duk da fahimtar da nayi shi ɗin mutum ne me wayau.
Yan kame kame na shiga yi mishi na ni ba haka nake nufi ba, ya ce “To ya ji ya gode da nasiha, yana kuma cike da alfaharin samun mace mai hankali, tare da jimamawa tsohon mijina asarar da ya tafka.
Mun fi awa kafin na samu ya bar ni, ina ta mitar yanzu haka matarsa wadda ke da girki na nan zaune gefensa, ya shanyata yana shan firarsa da wata.
na kwanta sai dai barci ya gaza ɗaukata, firar da muka yi take ta mini yawo a kai,
Anan nake tuna rayuwata ta baya.

Alh sule me kwano shi ne mahaifina, haifaffen ƙaramar hukumar Dutsinma ne ta jihar Katsina, matansa na aure uku ne kafin Allah ya yi wa matarsa ta uku gwoggo Jamila rasuwa.
Mahaifiyata Bilkisu ita ce uwargida, yaranta shida biyar maza sai ni mace tilo a cikin su,
ni ce ta biyar sai kanena Nura shi ne auta.
Kasancewa ta ya mace guda da Ummarmu ta mallaka yasa na tashi kamar tsoka ɗaya a miya wurin Ummana.
Sai mai bi mata gwoggo Rabi yaranta bakwai, su kuma duka mata ne, tayi maza uku duk sun rasu, gwoggo Jamila yaranta huɗu duka maza, ta rasa ranta a wurin haihuwar ɗanta na hudun, Ummarmu ke rikon yaran da ta bari.
Sana’ar mahaifina sai da kwano na rufin sama, yana da rufin asiri.
An sa ni makarantar boko da islamiya kamar yanda aka sa ƴan’uwana, gidan mu suna kallon juna da na su Hafsa wadda aka ce kwana talatin ta bani a haihuwa, ajin mu daya a boko da islamiya, barci kawai ke raba mu.
Muna kuma kare karatun sakandare aka yi mana aure, Hafsa ta auri malam Mas’ud ni kuma na auri telan mu da ke mana ɗinki Abubakar, matashi ne shi kuma kaɗai mahaifansa suka haifa, mahaifinsa ya rasu, da yawan ƴan’uwana ba su so aurena da shi ba, su na cewa ɗan mace ne, ni kuma na tsaya kai da fata sai shi.
An yi auren mu an miƙa ni gidansa, tare muke da mahaifiyarsa, sai dai an kebe mini wurina, muna ta zuba amarci, daɗin amarci ya debi Abakar sam baya fita yini da kwana muna tare yana ɗaka kwance, ko abinci mahaifiyarsa ke yi ta miƙo mana, da daɗin duniya ya ishe shi sai ya kwashe rabin abincin garar ya sayar ya saka kuɗaɗen aljihu muka yi ta cin daɗin mu.
Idan mutanen da suka ba shi ɗinki suka zo, sai mahaifiyarsa ta ce “Ba ya nan”
A kwana a tashi gara ta ƙare, kayan kitchen ɗina da ba a bude ba ya yi ta zara yana sayarwa muna cin abinci har suka ƙare, dole ya koma dinkinsa, wanda ba kasafai ya cika samu ba daga ya gama kore costomers ɗinsa.
Gidan mu nake tafiya in gaya wa Ummata matsalata, haka za ta yo min hade haden kayan abinci da ƴan kuɗi in koma, ƴan’uwana duk wanda ya bata abu ni za ta adana mawa idan na zo ta ba ni.
A haka na samu shekara lokacin kuma ciki ya bullo jikina me azabar laulayi, Abakar kuma ya tasa ni da bala’i idan ya kai ƙarata wurin mahaifiyarsa kiri kiri ta ke bani rashin gaskiya ta rika rarrashin ɗanta.
In ya sa kai ya fita tun safe sai dare zai shigo, bai fi ya ajiye min dari ba ko dari da hamsin, mahaifiyarsa ban ma ga fuska ba ballantana in saka rai za ta sam mini dan wani abu da zan saka a baki.
A haka wata rana yayyena Wasila da Habiba suka kawo min ziyara, sun same ni ba yadda nake, waya suka yi gida aka zo aka ɗauke ni sai asibiti, ɓari nayi wanda na sha matukar wahala, sai da aka yi min ƙarin jini.
Ƴan’uwana sun ɗauki zafi da al’amarin, suka ce ba zan koma ba, mahaifina dattijo yasa aka shirya ni
bayan na murmure aka mayar wa Abakar.
Watana biyu kacal da komawa na kwanta wani ciwon, nan ma ƴan’uwana suka kai ni asibiti, likita ya yi ta fadan ulser da ta kama ni saboda rashin kula.
Ƴan’uwana sun sha alwashin wannan karon ba zan koma ba, dan haka da abokan Babanmu suka yi ta kamun ƙafa, su roke shi ya yi hakuri a raba auren,
dan aure ba zai yuwu babu abinci ba.
Da aka nemi Abakar ya bani takarda tsayawa ya yi kai da fata shi fa yana son matarsa.
An sha fama da shi kafin babban yayana na ɗakinmu Yaya Sani da duk ya fi ɗaukar zafi da halin da nake ciki ya ce “To zai yanko mishi sammaci, daga baya so a rabu lafiya, mahaifiyarsa ta lallaɓa shi wai ya yi saki ɗaya idan an kwana biyu suka huce sai ya dawo da matarsa.
Da haka na samu muka rabu, Yayana Sani da ke zaune a Katsina ya tasa ni ya tafi da ni gidansa, farkon abin da na fara yi da na koma can faɗawa wata islamiyya na jona karatuna na addini, dan dama nayi mutawassiɗ, sai na fara sanawiyya.
Matsala ta farko da na fara fuskanta a gidan dan’uwan nawa me matuƙar so na, ita ce kishina da matarsa ke yi Aunty Rahma,
dan duk ƴan’uwana suna taya Ummarmu so na.
Da ya shigo ni ce mutum ta farko da zai fara nema, yana cin abinci ina gabansa sai na kula sun fara samun matsala a zamansu, har ta kai ga yin yaji ta bar mana ƴaƴanta, ni kuma ina samu aka yo bikonta, sai na tattara kayana sai gidan ubana.
Ko da ya zo yana faɗan me yasa na taho? Rahma bata isa hana ni zaman gidansa ba, sai dai ita ta bar min gidan, ban yarda na bi shi ba, karshe Ummanmu ta ce ya tafi kawai ya bar ni.
Haka ya tafi ba dan yaso ba, mafarin dawowata gidan mu kenan.

Ranar Asabar da na je makaranta malaminmu na ainihi me mana matanir risala shi ne ya shigo.
Ai kam yana fita ajin ya dauki hayaniya ana tambayar juna ina sabon malami?
dan ba karamin cinye ƴanmatan ajin mu yake bakowacce na fatan ya taya.

Wasa wasa sai ga shi Tahir ya dage zuwa wajena a duk Lahadin duniya, makaranta kuwa tun daga ranar da ya kira ni a office din malam Mas’ud bai ƙara zuwa ba.
Ya samu babanmu ya ce yana so ya turo magabatansa, Dattijai sun zo sun nema mishi ni kuma bayan tafiyar su ya zaunar da ni ya ce sai in yi shawarar lokacin da nake gani zan kammala shirina, sai ya sa musu rana, dan ya ce su kawo sadaki, kuma yasa an mishi binciken gidan su a ƙanƙara, gidan su babban gida ne shi ma an yabi halayensa.
Ya sallame ni na tashi na tafi, da zamana a ɗaki sai na samu kaina ina hawaye, Ummata da ke ninkin kaya ta harare ni “Shashasha wadda bata san inda ke mata ciwo ba”.
gwoggo ta shigo suka haɗu suka yi ta mini faɗa.
Nan na ji Gwoggon tana tambayar Umma yau matar da aka sa tayo binciken gidan su Tahir a ƙanƙara za ta zo?
Umma ta ce tana nan zuwa amma bata faɗa mata ranar ba.
Ranar da matar ta zo tare suka zo da wata da ta ce cikin matan yayyen Tahir akwai ƴar’uwarta amma ita matar nan Dutsinma take aure, ita tayi ta basu labarin gidan su Tahir, mahaifinsa ya rasu tun yana yaro sai mahaifiyarsa, ta dube ni inda nake tsaye ina shirin makaranta,
“Ƴar nan shiga gidan Tahir sai kin yi shiri, matan nan nasa gogaggu ne, haka za ki ga sun zo suna yauƙi duk da uwargidansa yar ƙanƙara ce, makota suke gidan su da na su Tahir ɗin.
An ce duk aikin gwamnati suke.
Matar da suka zo tare ta ce “Ai maganin sammu kawai za a samo ki yi ta sha kina wanka”.
Ban ce uffan ba sai barin dakin da nayi, dakin Gwoggo na shiga na kwance nikab din da na ɗaura, kwanciya kawai nayi bisa gadonta maganganun matar suna min yawo a kai, duk na shiga rudu in a da ina fargaban auren Tahir saboda shi kansa, to yanzu ga labarin matansa da na samu na san suna nan kamar ka taba su jini ya fito dan gogewar fata, na dubi hannuwana da duk sauron ɗakin Ummata ya gama cijewa, shawarar wa zan nema dan samun mayukan da za su gyara min fata?
ban kai ga samun mafita ba na tuna an ce matan nasa ma’aikata ne, ni kuma ko turancin ban gama gwanancewa ba, wa zan samu ya koya min turanci?
abin ya mini yawa.
Miƙewa nayi na shiga makotanmu gidan su Hafsa wurin matar yayanta Aunty Zahra ƴar gayu ce, ita na tambaya mayukan da zan saya da za su gyara min skin, za na min sunayen su ta shiga yi da kuɗaɗen su, sunan ɗaya na ɗauka na ce zan saya, na ɗan jima kafin na tashi na koma gida, inda na samu magabatan Tahir sun zo sun kawo sadaki dubu Tamanin babanmu kuma ya sanya rana kwana arba’in.
Ummanmu ta kira duka yayyena a waya za su yi shawara kan yadda za a yi min kayan ɗaki, dan wadancan kayan nawa saida su aka yi bayan fitowata, aka ba yaya Sani kudin.
Yamma sosai yaya Sani ya iso, da daddare ya kira ni yana dakin Gwoggo yana cin tuwo, dan nesa da shi na zauna na ce “Ga ni yaya Sani”
loma ya kai baki “Malama Ummu ashe aure ya zo?
dan murmushi nayi ban yi magana ba,
“Ai na ga mijin, wancan satin ya je har Katsina ya gaishe ni”
Gane ba zan yi magana ba yasa ya cigaba “In kina da zaɓin kayan da kike so sai ki gaya wa Gwoggo ko Umma”
Na ce “To” ya gama ja na da wasa ya sallame ni.

Da safe duka suka haɗu a ɗakinmu Yaya Sani, yaya Isuhu, sai yaya Jamilu, sai Mustapha wanda nake bi mawa, Umma na zaune ni kuma ina gyara kayana.
Yaya Sani ya ce “Kowa ya faɗi abinda zai bayar gwargwadon samun sa”.
Kowa ya faɗi, yaya Sani ya ce ” Zan haɗa da kuɗaɗen ta na kayan ɗakinta, da gudunmuwar ku da tawa, in saya mata komai na kayan ɗaki”.
Umma ta miƙo sadakin
“Ga sadakinta nan tun jiya Alh ya bayar da su, ya ce a bata”.
To bata Umma sai tayi yan nata saye sayen na kayan kitchen”.
Miƙo min tayi na karɓa na saka a jakata sai na fito dakin, wanka nayi sa’adda na koma duk sun tashi sai yaya Sani ke musu bankwana zai koma.
Uwardaka na shige na shirya na fito yana miƙewa “Sai ina Ummun Ummanta?
dan murmushi nayi “Gidan Yaya Wasila za ni in dubo ɗanta da aka yi wa shayi”.
To mu je in sauke ki”
Ya faɗi yana yin gaba.

Washegari Lahadi Tahir bai zo ba Gwoggo sai magana take ko lafiya yaron nan yau bai zo ba? bai kuwa taɓa fashi ba tun da ya soma zuwa”.
Ni dai ina jinta nayi mata shiru.
Ƙarfe takwas na dare ina kwance aka aiko kirana cike da mamaki nake duban yaron “Ko dai ba ni aka ce ba?
Dan akwai yammata biyu kannena a dakin Gwoggo, su ma an sanya ranar bikin su bayan an yi nawa za a yi nasu.
Gwoggo ta ce in dai leƙa in gani, daga yaron na makota ne ya san ni sarai, dogon hijabina na saka dan an soma sanyi sai na zura silifas, a zaurenmu na ga mutane biyu zaune ta hasken wayar da ke hannun ɗaya daga cikin su na gane mace ne da namiji, dan zauren akwai duhu bamu da wutar lantarki, gaba ɗaya aka haske ni da torch din wayar, wata faɗuwar gaba na ji
Tahir ne da wata tsaleliyar mace kyakykyawa ajin farko, cikin matukar kwalliya take, karfin hali nayi na yi masu sallama kan wani benci da Kodayaushe za ka same shi a zauren suke zaune,
ita ta amsa sallamar jin muryarta kadai ya kara kidimani dan muryar tata me matukar dadi ce,
gefensa ya nuna min “Zauna man”
na zauna amma daga nesa da shi sabanin ita da har jikinsu na gogar na juna, shi na fara gaidawa kafin ita
ya ce “Wannan ita ce Basma matata ta biyu, Basma ga Amaryata ummulkhairi”
“Nayi murnar haduwa da ke amaryarmu”
ta fadi tana mishi wani duba da kashe ido,
wani mugun yawu na hadiya gaba daya duk na muzanta.
Ya ce “Ta kawo min ziyara daga abuja shiyasa ba ki gan ni da wuri ba, kamar in fasa zuwa sai wani weak din to ina son ganinki kawai sai muka taho tare”
ni dai “Uhm kawai na ce, ya ce “Ku shiga ciki ta gaishe da su Mama, ku kuma kara gaisawa haka nan na mike na wuce gaba kamar kazar da ƙwai ya fashe mawa, ɗakin Gwoggo na fara kai ta sannan namu, babanmu ya kwanta.
Mun fito muka sake zama goma ta gota ya ce min za su tafi masauki da safe za su wuce.
Sai da ya ga ta fita ya dawo gabana ya tsaya, a kuma daidai lokacin nefa suka maido wuta fitinannen kallon sa yake jifana da shi,
“Kike wani kakkama jiki ko duk sanyin ne?
Kai na girgiza
wani kallon ya kuma watso min
“Ba ki da matsala bana ai yarinya,
ba ruwanki da jin sanyi kina da bargo.”
Ƙara sunkuyar da kaina nayi,
“Wai yau saura kwana nawa ne?
Saurin ɗago kai nayi muka haɗa ido sai nayi saurin mai da kan,
“Me tambayar ai ya fi wanda ya tambaya sani”.
Murmushi me sauti ya saki “Kuma fa haka ne, Allah dai ya nuna min ranar.
tare muka fito na ƙara yi musu sallama, ina kallo suka miƙe titin gidan mu.

Dana kwanta kasa barci nayi, ina tunanin al’amarin da ke daɗa kusanto ni, to yau fa na ga zahiri irin matan Tahir
ɗin, wani tunani da nayi yasa nayi saurin janyo wata jaka tawa da nake ajiye ajiyena, ledojin kayan kwalliyar da Tahir yake siyo min na shiga fiddawa, ban taba gwada amfani da su ba.
Da safe na shiga wajen Zahra na nuna mata, tayi ta mamakin dama ina da mayuka da sabulai masu matuƙar kyau da tsada amma nake neman saye?
ɗibar mata nayi na fito zuwa dakin Innarmu maman Hafsa kenan kamar yanda muke ce mata, yayanta Umar na zaune, sai tsiya yake min ban tanka shi ba. Gadonta na haye ina gaishe ta, kallon Umar tayi “Ba ka gama ba ne?
ya zaro ido “A Innarmu ya da kora kuma?
ta ce “E idan ka kammala yi tafiyar ka” ya ce “Da fira za muyi da yar ƙanwata amarya”
ta girgiza kai “Ka same ta can ku yi” ya mike ya fita yana mitar Innarmu ta kore shi.
Sai da ta gyara labulai sannan ta dauko wata leda, su zumar mata, hakin daka gumba su tabaje da tsimi ta fiffiddo
ta haɗa ta dama sai ta miƙo min, “Maza shanye ummulkhairi” dafe cikina nayi duka wannan Innarmu?
Ɓata fuska tayi “Kin ga duk abin da ke cikin ledar nan sai kin shanye su, shashanci kenan za ki shiga cikin kishiyoyi ba za ki gyara kanki ba?
Musamman na sa yar Sokoto tayi min hadin su masu matuƙar kyau ne”
Na karba ina sha ina ɓata rai. “Kullum ki zo ki rika sha ummulkhairi” kai na daga mata nasiha take ta min ina saurarenta na daɗe sosai kafin na fito na koma gida, Yayyena na samu yan dakin Gwoggo su dukan su sun zo wuni, wurin su na shiga muka yi ta shan fira, kafin babbar yayar mu a dakin nasu Aunty Habiba ta ciro kuɗaɗe sai ta miƙo mini, “Dubu 25 ne ummulkhairi mu dukan mu kowacce dubu biyar, sai kuma wasu kudin da muka haɗa za mu yi miki kazar amare da cicciɓi, wata leda ta miƙo min me ɗauke da garin magani. “Maganin sanyi ne, jikawa za ki rika yi kisa yar tsamiya kina sha sau uku a rana”.
Na karba tare da godiya sosai a gare su kafin na miƙe zuwa ɗakinmu.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: WA GARI YA WAYA
Rubutawa
MARYAM IBRAHIM LITEE
(labarin zaman kishin mata hudu wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje abun sai wanda ya karanta.)

Chapter thirteen

Washegari da hantsi ne na nufi gidan Hafsa, ina shiga gidan da malam na fara cin karo da alama fita zai yi, bai amsa gaisuwata ba ya ce “Wai Malama Ummu lafiya kwana biyu ba ki zuwa koyarwa dalibanki na ta complain”.
Kafin in yi magana Hafsa ta fito “Kila har ta ajiye aikin” ta faɗi tana murmushin shegantaka”
ɗan tsaki na ja “Ka bari kawai malam, abubuwa ne sun min yawa, ni ko zan shiga ajin ai ba gane abin da zan koya musu zan yi ba. Saukina daya da muka kammala namu
karatun, da yanzu nake yi ai da tawa ta same ni”
Dariya suka min shi da Hafsa.
Ɗakinta na shiga na baje kan kujera, ta shigo bayan na ji fitar malam.
Amarya yar shagali, meye labari?
rausayar da kai nayi
“Ba labari Hafsa”
Na shiga bata labarin matsalolin da suka taru suka damalmale min tunani.
Wata roba ta ciro ta miƙo min, na buɗe
“Meye wannan ɗin?
Na tambaye ta, ta ce “Labari aka bani hadin yana gyara skin, mankade ne, sai man zaitun, da man alayyadi da man kwakwa, aka haɗa wuri ɗaya.
Ki gwada kafin mu fara gyaran amaren”.
Na fadi “Na gode”
Miƙewa tayi ta buɗe fridge, robar Swan ta ciro “Tsimin sassaken baure nayi miki, wanda aka dafa ya dahu sosai da karanfani da yar citta.
sai a zuba zuma, da mazarkwaila bayan an sauke”.
ta kuma ciro wata gorar
“Nan kuma sassaken kuka na dafa miki da karumfani, shi ma yana saukar da ni’ima, ai sosai nake so mu rikita me mata biyun nan. Dan wallahi Ummu kin yi mijin nuna ma sa’a, muna me mata biyu, ashe haɗadde ne dan gaye abin sa”.
Tsaki nayi na karbi gorukan ina yamutsa fuska, “Ni wallahi sai in ga kamar zolaya ta sa mutumin nan cewa yana so na, ke kin ga haɗaɗɗiyar matarsa, ban da malam ya kawo shi Allah cewa zan yi wata manufa yake da ita a kaina, ba dai so ba”.
Hannu Hafsa ta kada
“Kar ma ki soma wannan tunanin, kyau daban kauna daban, da kyau ke sa a so mace da wasu matan har su mutu ba su samun mazan aure.
Kauna Allah ke dasa ta a rai, ballantana ke ɗin ma ba mummuna ba ce ko baki da shahararren kyawun fuska, Allah ya azurta ki da kirar jiki me kyau, kyan fuskar ma kina da daidai gwargwado. Kyan kirar jiki kuma ai shi ne mace.
Na ce “Uhmm ke dan ba ki ga matar ba, daga jikin har fuskar ta haɗa ”
Ta taɓe baki “To sai me? ba yana ganin ta ya kuma zo gare ki ba?
me zai dame ki ke kam?
na ce “Kin san wani abu Hafsa?
ta ce “Sai kin faɗa”
Na ce”Magungunan mata basa min, idan na sha maimakon ni’ima ni ɗauke min tawa suke, na rasa dalili shi yasa ban ko damu da su ba sanda ina gidan Abakar”
Ta ce “Ikon Allah lamarin naki akwai ban mamaki,
amma gobe in sha Allah zan zo mu je gidan Malama Jamila, ki yi mata bayanin matsalarki za ta ba ki magani”
Na hura iska “Allah ya kaimu”

Kamar yanda Hafsa ta ce ta biyo min mun je gidan Malama Jamila nayi mata bayanin matsalata,
Ta ce “Yanzu ba maganin mata ya kamata mu fara b”. wani sassake ta ɗauko ta hado da wata roba cikin ta ya’yan hulba ne, ta ce “Ki dafa ki riƙa sha na infection ne”
Duban juna muka yi ni da Hafsa na ce infection kuma?
ai ni bana ganin alamun da aka ce masu ɗauke da shi suna gani”
Hafsa ta ce “Daga ta ji matsalarki kuma ga abin da ta ba ki, ki karba kawai”
Na gyaɗa kai.
Sai garin habbatus sauda ta ce “Ki riƙa kwaba shi da zuma kina sha ko ki sha da nono me kyau, sai ganyen magarya ki rika tafasawa idan ya sha iska, sai ki rika shiga ciki.
Ki yawaita shan zuma musamman da daddare, kayan fruit ya zamana kamar abincinki a yanzu, ki yawaita shan su, musamman kankana, da aya da gyaɗa.
Cike da mamaki Hafsa ta ce “Gyaɗa kuma Malama?
Ta gyaɗa kai “Kwarai gyaɗa tana daga cikin abin da ke gyara mace kwarai da gaske sai dai rashin sanin amfanin ta”.
Hafsa ta ce “Faɗa mana yanda ake amfani da ita dan Allah Malama”
Ta yi mana bayani
Hafsa ta ce “Da mun fita kafin mu kai gida, zan saya mana kwano biyu ni da ummulkhairi”
Malamar tayi murmushi
Hafsa ta ƙara matsawa kusa da ita “Aure za ta yi Malama, mijin matansa biyu, shi ne take cike da fargabar shiga cikin kishiyoyi.
Ina so ki gyara min ita ciki da bai”.
Kallona tayi cikin wani yanayi sai ta matso ta dafa ni, “Kar ki ji komai kin ji ƙanwata.
Ki riƙe Allah ki nemi taimakon sa, indai kin shiga da zuciya ɗaya Allah zai taimake ki.
Mu ga hannunki na miƙa mata.
Ta ce “Ya kamata mu fara gyara tun saura sati biyu, duk wani abu da zai taimake ki zan miki shi in Sha Allah”.
Ta ce kuɗaɗen maganin da ta bani dubu biyar,
Sai na gyaran da za a yi mini hada lallen biki wannan Hafsa ce me biya ita ta faɗa ma adadin kuɗaɗen.
Ta biya nima na biya nawa, mun daɗe tana ta koya min dabarun zama da miji, da yanda za ki kama shi a hannu ba boka ba malam. Ke dai ki gyara kanki kar ki zama koma baya wurin miji.
Har za mu tafi na ce
“Akwai abu ɗaya Malama sai dai ina jin nauyin ki”
Ɗan murmushi tayi “Ki yi maganar ki ni ma mace ce yar’uwarki”
Rage murya nayi “Ni sam bana jin sha’awa, har aurena ya mutu ban taba jin daɗin da ake cewa ana ji ba.
Murmushinta me kyau ta kuma jifa na da shi,
Ba matsala, abin da na ba ki za su yi miki maganin duka in sha Allah”.
Godiya muka yi mata muka tashi muka fito.

Da zamu rabu Hafsa ta ciro kuɗaɗe a hand bag ɗinta, ta miƙo min
“Gudummuwarki ne in ji malam”
Sosai nayi godiya na ce ki taya ni mishi godiya kafin in zo Dubu talatin ne cif.
Ina zuwa gida na nuna ma su Ummata da Gwoggo kuɗaɗen suka yi ta godiya da sa albarka.

Hafsa fa ta buɗe min wuta kullum da abin da za ta aiko min, garin zogale in sha da madara peak, sai garin tafarnuwa ina shan sa da ruwan kal, sai garin ganyen idon zakara ina shan sa da madara shi ma, Ni kuma a bangarena kullum ina aikawa a sawo min kayan fruit in sarrafa abi na in Sha.
Saura sati biyu bikin tafiya ta kama Tahir zuwa warri, daga wurin aikin sa ne, kuma ko zai dawo sai ranar daurin auren ko washegari, tuni Malama Jamila ta shiga gyara ni, kuɗaɗe masu dama Tahir ya turo min ya ce “In yi ƴan gyare gyare na.
Saura sati guda biki yayana Sani ya aiko da kayan furniture’s masu matuƙar kyau,
bayan saitin sai kuma ya hado da wani gado ya ce a sanya min idan daki biyu ne, ba ƙaramin alfahari bane samun wadannan kaya domin sun hadu dan’uwana ya fitar da ni kunya.
Ni kuma na haɗa da kudin sadakin da gudunmuwar da na samu , hatta Ummata gudunmuwar da ƴan’uwanta suka haɗa mata bani su tayi ta ce in yi sayayya ta.
Labulaye na saya masu kyau da tsada sai carpet, zannuwan gado, yan kayan ƙyale ƙyale sai kayan kitchen wa’anda ban wani cika ba.
Ina son fridge da tv amma ba kudi sai na haƙura, Babana ya yi min Gara, kuɗaɗen da Tahir ya turo min sai na sayi kayan da zan yi kwalliyar biki, Atamfofi biyu na saya sai shadda sai less ɗai ɗai ɗinkuna na musamman aka yi min, dan na ji mutane sun fara magana kayan lefe fa in yi mishi magana.
Ni kuma bai yi min maganar su ba ba zan mishi ba, dan ko gwoggo ana saura kwana uku bikin Hafsa ta zo muna zaune sai ta leƙo Hafsa ta duba
“Wai ku angon naku yaushe zai kawo zannuwan auren?
ɗan shiru tayi kafin ta ce
“Zai kawo Gwoggo, ya ce tafiyar nan da ta kama shi ta hana shi karasa sayayyar. Ƙila sai ta je zai bata, daga ya aiko da na cin biki”
Gyada kai Gwoggo tayi cike da gamsuwa
“To Allah ya rufa asiri ya sanya albarka a auren”
Hafsa ta ce”Amin”
Gwoggon ta juya sai ta fita.
Miƙewa nayi ina rufe jikina dan gidan Malama Jamila za mu za ta min wankan lalle, idan fa ka gan ni nayi shar da ni na fito a amaryata illa dai fargaba da ta cika min zuciya.
hararar Hafsa nayi
“Matar malam guda ta zauna ta gunduma ƙarya”
Ƴar dariya tayi
“Ai ta kare kai ce, kar ki wani damu.

 

Ranar daurin aure jama’a masu dimbin yawa ne suka shaida daurin aurenmu da Tahir.
Duk da ba ango ƴan’uwansa masu dinbin yawa ne suka suka zo, matan sai tirirrishin zuwa gani na suke.
Ni kam Marka marokiya na rafka guda fargaba ta ta karu, kawayena sosai suka yi min kara, haka malamai mata na makarantarmu, da dalibai .
Ƴan’uwana da su Hafsa sun tsaya kan walimar da malaman makarantarmu suka shirya min.
Zuwa magrib jama’a duk sun koma gidajensu sai yan gidanmu kawai, ina yin isha’i na hau gado, a maimakon barci tunanin da ya zame min jiki ne ya taso ya dabaibaye ni,
Ya zan yi ranar da na zama mallakin Tahir Sodangi? Ta ya zan iya hada jikina da shi?
To yau dai ta faru ta ƙare,
na daɗe cikin tunani kafin gwanin iya sata ya sulalo ya sace ni.

Da asuba da kyar na tashi na gabatar da sallah dan tsananin gajiyar da nake ciki, na koma na kwanta.
Dukan da ake daɗa min yasa ni bude ido na tashi zaune ba shiri.
Hafsa ce cikin mamaki ina murza ido na ce
“Ke kuma daga ina da safiyar nan?
Agogo ta kalla “Tara da rabin ne safiya?
Kai na jinjina “Kwanan nan malam ya sake miki da yawa matar nan”
Murmushi tayi “To ya zai yi bikin ƴar’uwa rabin jiki”.
Tana maganar tana tube hijab din jikinta, jakar da ta zo da ita ta buɗe turaruka na jiki da na daki ta ciro “Ki riƙe su a hannunki wa’annan ummulkhairi, kafarki kafar su”.
Na amsa na ce “Na gode”
Harara ta bani “Kin san abin da ya fiddo ni yanzu?
Na girgiza kai “Sai kin faɗa”
Ta ce “Angon na ji suna waya da Malam ya ce lallai yau zai shigo Dutsinma, yana so a wuce da kayan ki gobe.
Sai complain yake wa Malam ya kasa samun ki a waya, in ya kira sai ya ji a rufe, shi kuma ya kasa kiran ta Umma, shi ne na roƙi malam in zo in miki kitso.
Baki na bude “Lallai babbar magana, yau Hafsa ce da kitso?
dan ita ɗin gwana ce ta kware a kitso sai dai makyuyaciya ce ta gaske wurin yinsa, daidai da yarta kwaya daya Ramla bata iya yi mawa.
Ta gyara zama “Matso dan Allah mu fara, so nake mu gama cikin lokaci ki shirya kafin zuwan Angon”.
Hular da ke kaina na cire, na zare ribbon din da na kama gashin ya watsu kan kafadata,
yana daga abin da ke ƙara fidda fuskata yalwataccen gashi da Allah ya bani.
Na miƙa mata kan wanda ke ta sheƙi saboda gyaran da ya sha, ta soma yarfa min kitso
Umma da Gwoggo suka shigo suna ta yi ma Hafsa godiya kan dawainiyarta a gare ni.
Sai sha ɗaya da rabi muka gama, banɗaki Hafsa ta wuce ta haɗa min ruwan wanka wanda ta zuba ma turaruka, wanka me kyau na shiga nayi da na fito na shafa mai humra ta bani na shafe jikina, atamfofin da na dinka na ɗauki daya na sa ta kuwa karɓe ni sosai, sai walkiya nake.
Gidan ya dauki hayaniya dan ƴan’uwana sun dawo za su wuce Kaduna shirya min daki, Hafsa ta fesa min turare tana motsa kunun da Umma ta miƙo min, gaba ɗaya turaren na ji ya haye min kai, dan cikina ba komai, tun jiya ban ci abincin kirki ba, yau kuma ko karyawa ban yi ba.
Na tashi in ɗauko ribbon din da zai dace da atamfata sai kawai wani jiri ya kwashe ni, kafin in san abin yi na yanke jiki, sai salatin jama’a nake ji,
kafin komai ya tsaya min na ji dif.
Ban farka ba sai a gadon asibiti na gan ni ana min ƙarin ruwa.
A hankali na buɗe idanuna Gwoggo na gani zaune a gefena, ta ce “Alhamdulillahi kin farka ummulkhairi?
Sai ta fita da sauri kafin ta dawo da mutumin da na hakkake likita ne, allura ya min ya kuma ba nurse din da ta biyo shi umarnin cire ruwan da ake ƙara min ta canza wani.
Wani barcin na koma, sa’adda na farka kaina ya min nauyi kwarai, na shiga juya idona cikin dakin an cire min ƙarin ruwan, Tahir Sodangi ne kaɗai a dakin yana ta Safa da marwa a filin dakin.
Sanye yake cikin wata farar shadda, glass ɗinsa na rai da rai na manne a idonsa, juyowar da ya yi sai muka haɗa ido,
da sauri ya karaso gaban gadon kin farka ina ke miki ciwo? Kai na girgiza
Ba ko ina, jikina ne kawai ba karfi”.
Ok to bari in kira Dr ”
Da wayarsa ya yi amfani wurin kiran Dr
Da shigowar likitan tambayoyi ya rika min ina ba shi amsa karshe shawara ya bani in daina zama da yunwa saboda gudun motsawar ulser ta.
Ya juya wurin Tahir “Ko yanzu zan iya sallamar ta yallabai ku je gida, amma kasantuwar dare ya soma yi za ku bari sai da safe, idan na kara ganin jikin sai ku je gida a yi kokari yanzu ta ci wani abu.
Suka yi musabaha, ya ce Allah ya ƙara sauki, zan wuce gida, dama saboda kai yallabai na kai har yanzu a Hospital”.
Godiya ya mishi likitan ya fita.
Ya juyo wurina “Taso mu je ki yi brush sai ki ci abinci”
ganin ban motsa ba ya ce ko sai na kama ki?
ganin ya yo kaina na ce “Zan iya”
Na lallaɓa nayo brush din na dawo,
tea ya haɗa min me kauri na sha kafin ya zuba min abinci, kan ba yadda zai yi ya ƙyale ni, na koma na kwanta.
Zufa ce ta shiga keto min, tsayawa ya yi kaina hannayensa saye cikin aljihunsa ya kafe ni da idanuwansa “Me yasa kike wasa da lafiyarki? har kika sa ulser ki ta motsa?
Shiru nayi ganin ba wasa sam a tattare da shi.
Sai da ya ƙara maimaitawa na ce “Ka yi hakuri zan kiyaye nan gaba”
zufar da nake ta yawaita ga tea me zafi da na sha,
ga tsare ni da Tahir ya yi da mayun idanunsa, a hankali na yaye hijab din jikina ina maida numfashi, bi na ya shiga yi da kallo wanda har ya sanya ni kallon jikina, ɗinkin matsatstse ne ya fitar da surata.
Jikina na ji ya dauki rawa
waiwaye na shiga yi inda na ajiye hijab din, gefen Sodangi na gan shi, wanda ban san sanda ya fakaice ni ya ɗauke shi ba, na kai hannu na shafa kaina, ba dankwali, juyawa kawai nayi na ba shi baya, “Dan matsa min ni ma in kwanta”.
Muryarsa ta ratsa dodon kunnena.

 

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: L*WA GARI YA WAYA*

*Na kudi ne 300
biya dan samun damar karanta wannan ƙayataccen labari na zaman kishin mata hudu da aka dagargaji zaman kishi aka gwangwaje
*2108124716 Maryam nasir UBA bank* *dan nuna shaidar biya 07033400612*

14

Ajiyar zuciya na fidda na faɗi na ga ta kaina yau, hannuna da ya sha ƙunshin amare na ɗora bisa goshina, sai hannunsa na ji ya dora saman nawa yana murzawa, gabana ya tsananta bugawa, “Wai duk ina ƴan gidan mu? a rasa me jinyata sai shi”
Cikin kunkuni nayi maganar, ban ƙaddara ya ji ba.
Sai da na ji yana bani amsa, “Saboda ni na fi kowa iko da ke a yanzu shiyasa”.
Shiru nayi can na ce”Zan yi sallah” ya ce “Bismillah” sauka nayi a hankali na shiga bathroom din cikin dakin,
Alwala nayi na zo na rama sallolin da ban yi ba.
Nayi zaune kan sallayar na ki tashi tun yana min magana har sai da ya ce zai zo ya ɗauke ni idan ban tashi na zo na kwanta ba.
Tashin nayi ina hayewa gadon na rufe idona da karfi a fatan da nake barci ya ɗauke ni, na kuwa samu nasarar hakan.

Ban farka ba sai ana sallar asuba, ban gan shi ba cikin dakin, miƙewa nayi nayo alwala na kabbara Sallah, ina azkar ya shigo na gaishe shi ya tambaye ni jiki, na ce”Na ji sauƙi”
ya tambaye ni zan yi wanka?
Na ce “A’a sai na je gida”
Tea ya kuma haɗa min na sha.
Sai tara likitan ya zo ya sallame ni, kannena yan mata da suka kawo abin karyawa su suka dauki yan kayayyakin mu da ke dakin, ina tafiya a hankali yana biye da ni a baya,
a raina ina cewa ko mashin zamu hau ko adaidaita sahu oho!
Mun iso harabar asibitin sai ya yi gaba na koma bin sa a baya, wata dalleliyar mota samfurin *Corolla Camry* baka da ke ta sheƙin ɗauke ido cikin hasken ranar da ya soma bullowa ya buɗe tun kan ya gama karasawa inda take, umarni ya ban in shiga gaba na shiga na zauna cikin tunanin ko motar wa ya aro tare da yi ma kaina addu’a Allah yasa ba dan karya na aura ba.
Ya zauna mazaunin direba kannena suka shiga baya.

Ko da muka isa gidan mu tare da shi muka shiga ina gaba yana biye da ni har dakin Ummata,
kwanciya kawai nayi suka leƙo ita da Gwoggo ya gaishe su, suka yi mishi godiyar ɗawainiya.
Suna fita ya dawo kujerar da ke kusa da wadda nake kwance, “Daga kin warware ki tashi mu wuce ƙanƙara, gobe mu dawo. Idan na dawo da ke sai in wuce Kaduna”.
Hannuna na sa na dafe goshina “Ina rokon ka dan Allah ka rufa min asiri, me kake tunani zuriar ku za su tuna a kaina idan suka gan ni na bi ka ba tare da na tare ba?
“Ya rage nasu kome za su tuna, tun da ba sabon Allah aka yi ba, kwanciyar ki nan fa ganin dama ta ne idan ban so ba zan ce ki tashi mu wuce Kaduna.
Dan haka sai ki zaba”.
Miƙewa ya yi sai ya bar ɗakin,
Na bi shi da kallo cikin saƙe saƙe.
Ba a jima ba aka soma shigo da akwatuna set ne guda shida, yaron yayata ya duƙo saitin kunnena “Ga kayan lefenki nan, ya ce ki zabi wadanda za ki yi tafiyar da su, yana waje yana jiran ki”.
Kuka na fasa wanda ya yi sanadin shigowar su
Ummata suna tambayar dalili, ina kukan nake faɗa musu, Yayana Jamilu da suka shigo tare mummunan tsaki ya ja ya ce “Wallahi duk Umma ta sangarta yarinyar nan”.
su kuwa tafa hannu suke ita da Gwoggo kafin suka rufe ni da faɗa, kan dole na share hawaye.
Ruwa me zafi na samu nayi wanka ina fitowa samu nayi sun yi ma kayan akwatin ɗaiɗai sai ma sha Allah Gwoggo ke fadi, ni kuma da ke kwalliya ina satar kallon kayan tsoro ne fal ya cika min ciki, anya ba wani boyayyen al’amari game da Tahir Sodangi?
Da ganin waɗannan kaya ta’adi me yawa aka yi wa Naira kafin a mallake su, kaya ne masu matuƙar kyau da tsada, wani akwati da suka buɗe abayoyi ne na isassun mata wadanda na fi ganin ana tallar su a social media.
In ta burin mallakar ko da ɗaya ce, duk da yake yaya Sani ya taɓa saya min sau ɗaya.
Gwoggo sai mita take
“Kin samu yaro mai kaunar ki ummulkhairi, iyayensa masu mutunci, sai godiya suke na basu ke da aka yi, zai kai ki cikin su su san ki ki san su, meye abin daga hankali?
Ni dai ina jin ta, ga ƙannena A’isha da Aimana da ke ta kara zuga ta ta hanyar faɗa mata uban tsadar zannuwan da suke fitarwa.
Harara na galla musu yayin da na miƙe dan saka kaya, less din da nayi kwalliya ranar daurin aure shi na mayar, ina fesa turare Gwoggo ta ce “Ki zo ki zabi kayan da za ki yi tafiyar da su”.
Baki na tura “Kwana fa ɗaya ya ce Gwoggo ni kala guda zan ɗauka”
ta ce “An ji zo ki ɗauki dayan” sai ta fice su Aimana suka bi bayanta da sauri dan sun san sauran aka bar su da ni, Abaya na dauka wata da na ga ta bani sha’awa.
Cikin wata madaidaiciyar jaka na saka duk wani abin da na san zan yi amfani da shi, na zura takalmi sai na fito tsakar gida Umma nake tambaya inda ta ajiye min hijab di na wanda na dinka mahadin less din,
kafin ta fito daga kitchen din sai ganin Tahir nayi ya fito daga dakin su Nura da yaya Mustapha yana share baki da hanki, da sauri na juya zan koma daki muryarsa na ji yana cewa “Zo ki kwashe kwanonin nan”
nan na gane girki Ummata ta yi mishi, kan ba yadda zan yi na dawo yana tsaye inda yake yana aikin kallona, magulmatan ƙannena Aimana da A’isha suna kallon mu suna murmushi ƙasa ƙasa, dan mu kadai ne a tsakar gidan.
Na kwaso na kai kitchen sai na koma daki sai ga shi ya shigo, sallama ta ban girma tare da kyautar da suke ta faɗin tayi yawa ya yi musu, jakar da na zuba kayana ya dauka sai ya bar dakin, Ummata ta sa aka fitar da cincin da dubulan da alkaki da aka yi min, ta ce “In kai wa Mahaifiyar Tahir idan na tashi tarewa sai ayi min wani.
Ni dai kunya ke ɗawainiya da ni, su Aimana suka raka ni har gaban motar, na ji yana jaddada musu zuwa azahar motar kai kaya za ta iso duk me zuwa sai ya shirya, suna amsa mishi da “To”
Yana yi ma motar key ribas ya yi sai muka bar layin.
Yana tuƙin yana duba na har dai ya ƙare ya ce “Wai jikin ne ko kuma gidan na mu ne ba ki san zuwa?
Sauke tagumin da na rafka nayi “Kin duba kayan sun yi?
Ya kuma tambayata
“Sun yi Allah ya kara budi na alheri”
Na fada a hankali
“Ban sa bra ba sai mun je Kaduna sai ki zabi size ɗinki”
Idonsa na kan titi ya yi maganar, ni kuma na ji kamar in nutse,
amma haka nan nayi dauriyar cewa “Ba na sa wa”.
Ta fakaice ya dube ni “Saboda me?
“Ciwon kirji take sa ni”
na ba shi amsa
Duk waɗannan abubuwan da nake gani ta hijabi suna tsokale min ido, ba a tare su da komai?
To an kusa zuwa wajen”
na faɗi a zuciyata ina kuma jin kamar kasa ta buɗe in shiga, duƙewa nayi na sanya kaina tsakiyar cinyoyina, duk maganganun da yake min ba su sa na ɗago ba, har sai da ya ce “Ai sai ki tashi mun iso”.
Sai kallon inda muka zo ɗin nake, daidai wani gida ginin bulo da bulo muka tsaya kafin ka ce me yara sun cika wurin suna ta mishi barka da isowa “Mu je ko” ya ce da ni ban yi alamar fitowa ba na juyar da kaina daga kallo na da yake na ce “Saboda Allah haka zan zo musu hannu bi biyu?
Ya ce “Idan za ki kuma zuwa kya yi musu tsarabar” daga haka ya fice na bi shi a baya.
Gida ne na yawa me sasa daban daban, mata ne suke ta bullowa daga sasansu suna mishi murna tare da fadin ango ka sha ƙamshi, har da masu mishi guɗa rafar dari biyu ya lika wa wacce ta fi su baki.
Wani babban falo muka shiga, kujeru ne masu tsada na zamani a ciki amma rashin goge su dattin su duk ya fito, akwai kayan kallo amma su ma duk sun yi kura, kasa carpet ne me tsada, amma da gani yau bai samu shara ba. Dattijuwa ce farar bafulatana kyakykyawa duk da shekarunta take mana lale lale, kasa na zauna ina gaishe ta, ta ce In tashi kar in bata kayana yau jikokinta da ke mata shara ba su yi mata ba.
Tana ta sa ma aurenmu albarka, ta tashi ta kawo min abinci sai ta fita Tahir da ke ta danna wayarsu na ce mawa “In zuba maka ne?
kai ya girgiza wadannan matan me suka iya zan fita in nemi abinci”.
Ba zan iya ci gaban sa ba, dan haka sai da ya fita sallar Azhar sai na zuba kadan, ina idar da sallah matan gidan suka yi ta shigowa muna gaisawa, sai da suka lafa na zare hijab dina na soma sharar falon da na gama na kwashe wata yarinya da ke ta leƙena ta madubi na yafito, ruwa na ce ta kawo min da tsumma da omo sai da nayi mopping din falon sai na goge kayan kallon da tsumma me kyau da na sa ta ta kawo min, na goge kujerun na kunna fanka, suka fito fes ina goge ta karshen suka shigo shi da mahaifiyar tasa, hannu ta shiga tafawa “Daga zuwa yar nan kin ta da kanki tsaye?
Shi kuma sai kallona yake ta cikin glass din idonsa, fuskarsa kuma a haɗe ya ce kuma haj daga asibiti aka sallamo ta”. Ido ta fidda “Asibiti kuma?
Ya ce “Wallahi jiya jiri ya kwashe ta tana da ulser sai ta zauna da yunwa, ina isa na samu za a kai ta Hospital”.
Ta ce “Allah sarki sannu kin ji wuce ciki ki kwanta”
Na wuce na bari yana cewa a kira mishi yaran gidan ya ji dalilin kin gyara wa mahaifiyar tasa wuri.
Cikin ma yana bukatar gyara dan haka gyaran na shiga yi, motsina ya shigo da ita ta koma tana faɗa mishi shigowa ya yi ya ce “Ba kya ji ko?
Na ce “To wai idan bamu yi mata ba wa zai mata?
ya ce “Haka ne”
Sai ya fita ganin ya fita na ce mata ba wasu labulayen ta ce Akwai ta nuna min inda suke na ciro na cire na jiki na canza da wa’annan, carpet ne ba zan iya cirewa ba jikokinta majiya karfi ta kira bayan ta fita suka cire sharar wurin ce ta hanani suka share aka malala wata. Kudade na bayar na ce a wanke labulayen da carpet har turaren wuta na kunna cikin irin wadanda Hafsa ta hado ni da su nan da nan wurin ya yi ras, sai shi min albarka take.
Sai magrib ya shigo ina cin tuwo ya ce “Tun da kin gyara dakin tsohuwa saura na mijinki, zo mu je ki gyara min tawa shimfidar”.
Shiru na mishi ko da ya maimaita ban motsa ba, a kunnena ya rada min bayan ya rankwafo “Wa ya ce miki amarya na cin tuwo?
Sai ga Haj ta shigo ya yi saurin matsawa
“Ki sa baki Haj mu je sashina ni ma ta yi min sharar” ta ce “Maza kammala ummulkhairi” na miƙe dan dama na gama na wanko hannuna da bakina sai na shige su gadonta na haye nayi kwanciyata, jin shiru sai ta leƙo “Mijinki na jiranki ta shi ki je kin ji?
Ta fada cikin sigar lallashi kunya na ji ta dabaibaye ni “Ni mama ke na zo wa baƙunta”
ta ce “Na sani, yi hakuri ƴata”
Na miƙe sai na fito yana zaune yana danna wayarsa, miƙewa ya yi sai na bi shi a baya
Sasan da muka nufa duk gidan ba me kyan sa, ƙanƙararren gini ne na zamani, ciki ma ya hadu har ba magana a gyare yake fes ba batun wani gyara, kitchen ne farko sai ka ƙara gaba ka taras da lafiyayyen falo wanda ya ji kayan alatu kofofi uku ne kowace da inda ta kalla, a farkon falon na ga bokitan su alkakin da na zo da su, a raina na ce nan aka kawo su kenan.

Kujera na samu na haye shi kuma ya buɗe daya daga cikin kofofin wadda take a kusurwa ya shiga, can an ɗan jima ya fito daga shi sai guntun farin wando lafiyayyen kirjinsa me cike da kwantaccen gashi a waje sunkuyar da kaina nayi ya ce”Ki cire lillibin nan ki shiga kitchen ki dafa min ruwan lifton” da hannu ya nuna min kitchen din, ba tare da na cire lillibin ba kamar yadda ya ce sai da na ƙare ma kitchen din kallo kitchen ne na zamani da na kare mishi nazari sai na kunna gas na tafasa ruwan na juyo na kawo mishi “Ya ce “In za ki kwanta ki shiga ciki na ce zan kewaya kofar da ya shiga ya nuna min, na buɗe na shiga daki ne me ɗauke da makadeden gado na zamani sai dressing mirror a gefe da wardrobe da sauran tarkacen da za su fahimtar da kai cewa me wurin namiji ne.
Wata kofa da na gani ita ta sa ni tunanin nan ne makewayin, da na shiga sai da na murza key wanka nayi da na fito na same shi a inda na bar shi, na ce “Zan koma wurin mama”
wani kallo ya jefa min “Mama na dauko wa ke ko kaina?
Jakarki tana ciki, in kina son canza kaya akwai wata jakar ma ki yi amfani da kayan ciki”.
Ba ni da zaɓi dan haka cikin na koma tawa jakar na ɗauko na ciro kayan kwalliya nayi kwalliya, na saka turare, wata nineties ɗina na saka na koma karshen gado na makure bayan na tattake da hijab ɗina ina sauraren bugawar da ƙirjina ke yi.
Tara da kwata na ji ya kashe komai sai ga shi ya shigo bathroom ya wuce ya fito yana duban inda nake lemar jikinsa ta bani tabbacin wanka ya yi.
“Yo Alwala ki zo mu yi sallah” ya ba ni umarni
Mun idar da sallar ya dafa goshina addu’ar da Manzon rahma ya ce ayi idan an yi sabon aure ita ya yi min, kafin ya yi ta kwararo addu’o’i yana nema mana albarkar aure.
Shi ya fara tashi ya tsaya gaban madubi yana saka turare, sai satar kallon sa nake, ba sanannen ciki ya waiwayo ya kama ni ina kallonsa saurin kauda fuskata nayi, ya ce “Gulma, wata gulmar kunyata da ake ji, wata rana ke da kanki ban kira ki ba za ki zo ki haye nan” yana fadi yana shafa kirjinsa, sauri nayi na tashi na haye gadon na kwanta a inda na tashi na rufe idona ruf.
Ban san ya iso inda nake ba sai hannunsa da na ji kan ƙirjina yana lalube, “Kullun na ga ababen nan cikin hijab ba ƙaramin daga min hankali suke ba, dan duk boye sun da ake cikin hijab bai hana su bayyana ba”.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *WA GARI YA WAYA*

*15*

Ƙara nutsuwa nayi jin kalamansa, a wannan daren na tantance maza daban daban ne, Tahir Sodangi cikakken namiji ne, na gane banbanci me yawa tsakaninsa da mijina na baya Abakar dan shi kam baya wuce minti biyar ya gama abin da zai yi ya kama gabansa.
Amma Tahir wuya sosai na sha a hannunsa, dan ban saba da hakan ba ga kuma daɗewar da nayi rabona da abin, tsawon daren bai bar ni na huta ba ga gyaran da na sha, na gamsar da shi iya gamsarwa, ni ma kuma na gane maganin malama Jamila ya yi min.

Na idar da sallar Asuba na ga shigowar sa, kaina na ƙasa na gaishe shi gado ya hau ya kwanta
ganin ba ni da niyyar tashi ya ce “Ke nake jira fa” jikina ba kwari na miƙe gefen gadon na zauna ya janyo ni jikinsa ya zare hijab din jikina da zanen da na daura da zan yi sallar sai ya rungume ni, “Zan kara ummulkhairi, ko kin gaji?
Jin nayi shiru sai ya ce “Ni ina so Ummu”
Ya fara yamutsa ni muka ji ana buga ƙofa tsaki ya yi ya sake ni sai ya sauka ya fice, ina ji yana tambayar waye ban ji amsar da aka ba shi ba sai takun dawowarsa na ji, jallabiyar da ya tube shigowar sa ya shiga zurawa, a hankali na ce mishi”Lafiya” juyowa ya yi ya dube ni “Babban yayanmu ne ya aiko kirana, akwai wani gidan gona da nake so zan maida gidan kaji, shi ne yanzu ya aiko a shaida min me gonar ya zo gari dan shi ma ba anan yake ba in kuma ya tafi ya kan dade bai zo ba, shi ne za mu je yanzu dan yau zai bar garin”.
Na ce “A dawo lafiya Allah ya yi jagora” ya ce Amin ki kwanta ki yi barci, zan dawo yanzu”.
Na ce “To”
Ya fita ya bar ni cikin ƙara kullewar kai game da shi.
Na cigaba da juya tarin tambayoyin da nake da su a kansa nake kuma son samun wanda zai warware min.
Daga bisani barci ne ya sace ni.

Ƙarfe takwas da rabi na farka, gane Tahir bai dawo ba sai na miƙe, wanka nayi ban ko tsaya wata doguwar kwalliya ba na zura hijab, da na fito sai na dauki bokitan alkaki da cincin wani yaro na yafito ya taya ni dauka, sai muka isa sasan Haj tana zaune, da fara’a take min sannu da zuwa “Kin fito ummulkhairi?
Sai da na kai zaune na soma gaishe ta, ta yi min ya gajiyar aiki, kafin ta shiga godiyar kayan da ta ga mun shigo da su.
Koko da kosai ta turo min da kayan shayi, ta ce
“Aike na biyu ana cewa ba ki buɗe kofa ba, shi kuma Sodangi shiru ba su dawo ba”.
Koko da kosan na sha sai nayi mata shara na gyara mata wuri.
Ta sa aka raka ni duka sasan yayyin tahir su huɗu, kowanne matansa biyu illa babban yayansu shi ne me mata uku.
Sai da na shiga dakin kowaccen su kafin na dawo wurin Haj, na samu matan babban yayan su biyu uwargidan da me bi mata, sai kuma uwargidan me bi ma babban yaya suna raba kayan bikin da na zo da su.
Sai da suka gama suka tafi na ce wa Haj ina neman yaron da zan aika ya yo min cefane.
Murmushi sosai tayi ta ce “Yawwa
ƴan nan Allah ya miki albarka, gara ki yi wa mijinki girki ko da matansa ya zo sai dai ya yi ta gararin sayen abinci.”
Miƙewa nayi na koma sasan Tahir, can wani ɗan matashi ya bi ni na lissafa mishi abin da zai sawo min ya karɓa ya tafi.
Na koma ciki ina gyara wurin duk da ba wani datti ya yi ba, na dai ƙara tsaftace komai, na saka turaren wuta. Ina yan goge goge a kitchen yaron ya dawo,
Farar shinkafa na dafa da miyar ƙoda, sai kuma na shirya Spanish poiled cheaken, kaji uku nayi amfani da su wurin yinsa, wanda na ba yaron ya siyo min.
Zuwa ƙarfe ɗaya na kammala komai, Hajiyar su Tahir na ware wa kaza daya sai na shirya mata abincin a wani katon tray na dauka na kai mata, ni da Tahir kaza daya na cire mana sai na shirya kaza daya da abincin a wani tray na aika wa uwargidan babban yaya ta raba ma jama’ar gida.
Wanka nayi na gyara jikina, nayi kwalliya da shaddar da na dinka ta cin biki, dinkin fitted gown ne da ya yi matukar karba ta ya fidda surata,mayafi na sa sai na isa sasan Haj, na samu tana buɗe kwanonin sai sa min albarka take, tana cin abincin ina gefenta Tahir ya shigo, “Kai Haj ina kika samu abincin nan?
dan na san ba na surukanki bane”.
Ɗagowa tayi tana duban sa”Ai kam na surukaina ne”
Cokali yasa ya ci sau ɗaya sai ya lumshe ido abincin ya yi Haj”
Ya koma kan naman ya yaga ya sa baki “Uhmm delicious” ta ce “Ka ga malam kar ka cinye min ga naka can a daki”
Wani duban mamaki ya yi min dan maganar da tayi ta sa ya zargi ni nayi.
Na sauke idona, Haj ta ce “Daga yanzu yanzu sai muka ji ka shiru sai yanzu” ya ce “Bayan mun je gidan gonar an yi ciniki wasu filaye suka ja ni wai yana da kyau in saya in gina wa iyalaina, ni kuma ban da wannan ra’ayin, indai kina raye na fi san na shigo garin nan in sauka wurinki”
Ta ce “Ba laifi sayen ma yana da amfani”
Duk a gajiye nake, taso mu je ” ya fadi yana juyawa dan barin dakin, na miƙe na bi bayansa.
Zama kawai ya yi na zuba mishi sosai ya ci, sai ya sha juice din kwakwa da abarba da na hada mishi.
Sai sannan ya nemi sanin inda na samu kayan cefanen, na mishi bayanin na aika ne sai aka sawo min. Kai kawai ya gyaɗa sai ya mike wanka ya yi da ya fito na ji yana kirana, kwance na same shi bisa gado daga shi sai wando gajere, “To zo mana in ga kwalliyar in kuma bada tukuicin girki me daɗi da aka yi min” a hankali na taka kusa da shi da ƙafafuwansa ya nade ni sai ya janyo ni jikinsa, bayan gama abin da za mu yi daga bisani barci muka yi,sai dai ni nawa barcin bai yi nisa ba dan hankalina na ga komawa ta gida.
Ana fara kiraye kirayen sallar la’asar na soma taɓa shi a hankali, har ya buɗe ido na ce “An soma kiran sallah kar dare ya yi ka maida ni har ka dawo”.
Ya tashi zaune “To bari in dawo sallah sai mu yi maganar”.
A gurguje ya yi wankan sai ya wuce masallaci, ni ma nayi wankan nayi salla, na idar kenan cikin yaran gidan wani ya zo ya ce Haj na kirana.
a baya na bi shi har wurin Hajiyar
Ta ce “Garin dawa ne na ce ko za ki yi wa mijinki tuwo dan yana so”
Kaina ya ɗaure da zancen girki ni ita Hajiyar bata san yau zan koma gida ba?
Amma ba zan iya musa mata ba, na amsa da “To” ta ce “Yawwa ga daddawa nan me kyau ce ta kalwa ga kaza can na sa a yanka, sai ki yi amfani da ita.
Na dubi inda take nuna min, jikanta ne ke gyaran kazar.
Ta cigaba”Mijinki na san abincinmu na gargajiya duk da dadewarsa a bariki, to mata ne duk maƙyuyata, sai abincin ƙarya”.
ganin nayi ɗan murmushi ta ce “E man girkin zamani ai girkin ƙarya ne, zuwa na na farko gidan Sodangi, matarsa tun la’asar take ta kai da kawo, sai dai ka ji kwas ƙwas ana ta yanke yanke a raina ina faɗin za mu ci daɗi, wai sai da magrib ta zubo min latas da abarba da lemo wai su ne abincin dare”.
Ina son yin dariya ina kuma jin nauyinta, jikanta me gyaran kaza ya kwashe da dariya.
“Kai Haj cream salad da fruit salad fa aka kawo miki”. Wata budurwa da ke zaune tana daddanna waya ta fadi.
Baki Hajiyar ta taɓe “Shiriritar banza dai, haka dambu Sodangi na sonsa sosai”.
Kirana aka aiko yi wai in zo an kawo sako,
na isa kayan abinci ne jibge wai in ji Tahir, na store na sa suka shigar can, na kitchen aka sa kitchen.
Ban koma wurin Haj ba girkin na shiga yi, daga ban ma gan shi ba ballantana in yi zancan komawata gida, kuka na kaɗa ita ma Hajiyar ce ta bani, na zuba wa Hajiyar na ci nawa sai na shirya mishi na shi.
Bayan har na yi wanka ya shigo, ya ce “Kin ji ni shiru ko?. Idan na shigo garin nan jama’a ba sa bari na zama”.
Ya zauna ya soma cin abincin, ya ce “Dazu Hafsa ta kira ni, ta ce In Haɗa ku ta kasa samunki”
na ce “Kashe wayar nayi saboda masu kirana su yi min tsiya, baran ma ita Hafsa, ina son kiran Ummata amma ina jin kunya”.
Karamar wayarsa ya janyo umman ya kira ina jin muryarta dan yasa hands free, sai da ya gama gaishe ta sai ya min alama da hannu zan yi magana da ita?
Kai na girgiza
Ya yi sallama da ita ya kashe wayar.
Na ce “Ina ta jiranka ka zo ka mayar da ni gida, ba ka shigo ba sai yanzu”.
Kallona ya yi “Gida kuma? wane gidan?
“Gidan mu mana”
Sumar kansa ya shafa
Ai nan ne gidan ku, kuma kin zo kenan, in ma za ki tafi wani gidan sai dai in za ki koma Kaduna”
Shiru nayi raina ya ɓaci sai na miƙe,
“Ina za ki kuma?
Ban waiwayo ba na ce “Sallar isha’i zan yi”
Ko da na idar da sallar ban fito ba kwanciya ta nayi can sai ga shi “Kwanciya kika yi ba za mu yi firar ba?
“Barci nake ji” na faɗa ba tare da na buɗe ido ba.
“Amma ba ki kwashe kwanonin abincin naki ba”
Na sauka na je na kwashe sai na dawo,
kwance na same shi ya rufe rabin jikinsa, hannayensa ya buɗe da niyyar in shiga ciki
sai na ɗauke kai, nesa da shi na kwanta na juya mishi baya.
Mirginowa ya yi ya haɗa jikinmu sai ya rungume ni a kunnena yake rada min “Fushin me kike Ummuna?
Ke ɗin ai Malama ce, ya halatta mace ta juya wa mijinta baya a shinfida?
shiru nayi
“To yi haƙuri ko bani bane?
Kaina na kara kwantarwa kan kirjinsa “Ba ka ce ba zan koma gida ba?
Ya ce To ki yi haƙuri, ki bari idan na je Kaduna na dawo sai in mayar da ke”.
A haka muka rufe maganar na haƙura kan ba yadda zan yi.

Washegari Bakori ya tafi shi da yayansa me bi ma yaya Babba.
Haj ta bani kayan da zan yi dambu ni kuma na zauna na yi shi me daɗi ya ji zogale da wadatacciyar gyada, sai hanta da na yanka gutsi gutsi.
Da nayi wanka sai na shiga tunanin kayan da zan sanya, tunawa da jakar da ya ce akwai kaya a ciki in yi amfani da su yasa na janyo ta dogayen riguna ne dakakku yan gaske wannan tana wane wannan wannan tana wane wannan har kala goma sha biyu, akwai takalma da mayafai sai rigunan barci daya na dauka na sanya nayi rolling da mayafinta.
Motsin da na ji yasa ni fitowa falo, Tahir ne kallon da nayi masa yasa na shafa’a da yi masa sannu da zuwa, sai kallon suturar da ke jikinsa nake wata rantsatstsar shadda ce da ke ta masƙi hular nan ta zauna mishi a shatara, yana kokarin kwance agogon hannunsa ya ce “Ke lafiya kallon fa? Yar kunya na ji na yi mishi sannu da zuwa.
Yana cin abinci yana santi, ni kuma ina kan sopa na haɗe kafafuna idona na kan TV amma hankalina ya yi nisa wurin tunanin da na fara tun shigowarsa.
Ban san kammalawarsa ba sai dai na ji ya ruko ni, na miƙe tsaye sai da ya kwanta ya kifa ni kan cikinsa ya ce tunanin me kike tun shigowata ?
Na ce “Ba komai”
ya ce “Yi hakuri ki gaya min, ko kina da wanda ya fi ni anan ɗin?
Na girgiza kai “To gaya min” yana fadi yana jan hancina sai da na kara tura kaina a kirjinsa sabuwar kaunarsa da na tsinci kaina cikinta na ƙara fizgata har ina jin ina ma ace shi ɗin nawa ne ni kaɗai.
Sannan na ce “Ina tunanin sanin da nayi maka a ustazu, yanzu kuma ka rikide min wani mutum daban, da yawan lokaci kuma na kan so sanin dalilin zuwanka makarantarmu da niyyar koyarwa”.
Jin nayi shiru yasa shi yin wani murmushi me sauti, yanda abin ya faru ya soma mishi yawo a ido.
Ranar wata asabar ce da ba zai yuwu ya manta ranar ba, ya kai wa Malam Mas’ud ziyara a garin su Dutsinma lokaci na farko da ya yi hakan tun haduwar su a aikin hajji, wanda suka yi abota, ko bayan dawowar su zumunci me ƙarfi ne ya kullu a tsakaninsu.
Daliban malam Mas’ud suka rika fitowa cikin nutsuwa suna wucewa gidajensu, wani tunani ne ya darsu a ransa yayin da
yake duban su cikin sha’awa, dan sun burge shi.
Ya maida duban sa ga malam, ina ma cikin daliban nan naka mata in samu daya me hankali da nutsuwa in aura”.
dan nutsuwarsu ta bani sha’awa, malam Mas’ud ya ce “Ai in kana son hakan sai a nema maka me hankali”.
Ya ca “A’a malam, ina so yanzu idan zan kuma aure in auri wadda nake so take sona a ni din take so ba wai abin hannuna ba”.
Malam Mas’ud ya ce “To yanzu ya za a yi ka gan su har ka samu wadda kake so?
Nan ya faɗa mishi tunanin da ya yi zai rika zuwa duk weekend zai zama malami, da haka zai gan su. Malam Mas’ud ya ce To za a ba shi darasi a ajin masu fita yammata, ya je ya zo mishi da jadawalin darussan da suke yi, sai ya zabi sharhur risala, dan ita ce darasin da ya fi kauna sa’adda yana ɗaukar karatu a gaban uban goyonsa wanda ya kasance babban malami ne, shi ɗin ma har ya zama saurayi ya kan taɓa koyarwa a makarantar uban goyon nasa.
Jin shirun shi ya yi yawa yasa nayi tunanin ko barci ya ɗauke shi, motsi nayi sai na ji ya daɗa makale ni, sama sama ya bani labarin. Shiru nayi cikin nazari tare da juya ɗayar tambayar da ke min yawo a rai.

Tahir me fadin kwana uku zai yi ya koma Kaduna, sai ga shi yana neman yin sati biyu, kullum sai dai in ji shi yana waya da matansa.
Ni kuma ban gajiya da shirya mishi abinci, wani abincin gargajiyar ma ban ko iya shi ba Haj ke koya min, wadda sai a sannan na fahimci lalurar da take fama da ita ta ciwon Athma da pnimonia dan haka ban gajiya da temakonta, dan yanzu ne lokaci me wahala ga masu lalurar wato lokacin sanyi.
Na lura Tahir yana jin daɗin mu’amala ta da mahaifiyarsa. Wayata kuwa tuni na kunna ta iyaka duk wanda ya kira ni ya gama sherin shi ina ji, ba kamar Hafsa sharrin duniya ba wanda ba tayi min ba,
Kullum nake kiran Ummata dan ba kaɗan nake kewarta ba.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *NA KUDI NE 300*
*biya 2108124716* *Maryam nasir UBA*

farkawata daga barci sai na ɗora idona bisa agogo, ƙarfe bakwai saura minti takwas na safe. Jikina na zare cikin na Tahir sai na fito, bathroom na fara shiga kafin na isa kitchen, ruwan Lipton wanda na zuba ma kayan ƙamshi na ɗora, yana fara zafi na fito, zane na ɗaura saman riga da wando na barci da ke jikina sai na saka hijab, bayan ɗakina na fita na dauko murhun gawayi na zuba gawayin kafin ya ruru na koma na kashe gas ɗin na juye ruwan zafin cikin flacks, da sauri na fasa ƙwai na soya wa Haj, na gasa mata bread.
Wurin gawayin na koma ya ruru, na dauka zan wuce na ji muryarsa a kunnena “Ina za ki da wannan?
Haj zan sanya ma wa a daki”.
Na ba shi amsa, sai na wuce, a uwar ɗakanta na same ta, na ajiye nesa da ita dan kar ya takura mata, na juya muka haɗa ido da Tahir na ratse shi na wuce, abin karyawarta na koma na kawo mata.
Samu nayi suna magana, ban zauna ba kitchen na koma na kama aikina.
Koda na kammala namu, dakin Haj ya nemi in kai mishi, dan haka can ɗin na kai, sai da ya shigo, yake tambayata me yasa ake kaiwa Haj wuta a daki.
Ban ƙasa a gwiwa ba na ce “Saboda lalurarta, kuma ina ganin da za a daure da room heater aka sanya mata a ɗakin, bathroom ɗinta kuma a saka water heater saboda masu lalurar ba sa mu’amala da sanyi.
Idan aka yi hakan ina ganin ba ƙaramar lada za a samu ba”
Daga haka bathroom na shiga dan na gama komai wanka zan yi.
Shi ma da ya yi wankan Kano ya tafi.

Ina sallar la’asar na ji yaran gidan suna ta sannu da zuwa, sai da Tahir ya shigo na gane shi suke mawa, sai kuma da na shiga wurin Haj kai mata abincin dare sai na ga aikin da ake yi.
Water heater da room heater ake sanya mata, dan murmushi nayi a raina na ce sayen su ya kai shi Kano kenan.
Sai da muka nutsu a makwancinmu yake shi min albarka wai na tunasar da shi abin da yake wajibinsa ne.

Ana gobe zai koma Kaduna, da safe duk da nauyin sa da nake ji sai da ya gane ɓacin raina, wunin ranar bai je ko ina ba muna daki sai dai ya fita sallah ya dawo.
Ya dawo sallar isha’i aka kira wayarsa, ji nayi yana cewa ka shigo kawai, da shigowar baƙon miƙewa ya yi sai suka tafa,
“Shegen bisa yaushe a gari?
Tahir ya ce wa baƙon nasa,
“Da magaribar nan mutumina, ai ina sauka nake jin kana garin nan har sati biyu, shiyasa ko abinci ban tsaya ci ba na ce bari in zo in ga wannan amarya da ta iya riƙe ka har sati biyu”.
“Sharri ka shi zai kashe ka, wa ya ce maka ban taɓa sati biyu a ƙanƙara ba?
“Haba abokina ai rabonka da ka zo ka dade ina ga tun kana sakandare idan ka zo hutu”.
Dariya suka yi
Na ce “Sannu da zuwa”.
Ya juyo yi hakuri amaryarmu, ya amarci?
Na gaishe shi ya ce “A yi min afuwa amarya, ban samu halartar ɗaurin aure ba, muna wurin kwadago”,
Na ce “An dawo lafiya?”Lafiya ƙalau Alhamdulillahi”.
Tahir ya buɗe abinci “Bismillah”
Kallon abincin ya yi “Anya kuwa na ci abincin nan, ni ma nawa na can gida.
Dan yau ni ma ɗin ango ne, kar in ci kasa a min bore”.
Ya ce “Ci kawai malam, na rakaka har gaban Saratun, dama ai na ce kai mijin ta ce ne kullum kana fama da mace ɗaya”.
Ya cika bakinsa da abinci ya ce “Dole ka yi ta zama abokina, ko da wannan daddaɗan abincin ai a riƙe ka”.
Ya ce “Kai dai dan iska ne wallahi”.
Duba na ya yi “Dan bani ruwa mara sanyi ummulkhairi”
Sai da na je na kawo mishi sai na koma kitchen din duba farfesun danyan kifin da na ɗaura, ji na shiru Tahir ya ce “Wai me kike yi ne? na ce “Ina duba girki ne”
Na shiryo musu na dauko maganar da na ji suna yi cikin rage murya ta sa ni tsayawa sai na sa kunne.
Wallahi kar ka ga magiyar da Latifa take min in kawo mata kai, har kudi ta bani na ce ta riƙe kudinta za ka same ta har inda take”.
Ai kam za ta daɗe bata gan ni ba abokina”.
Tahir ya ba shi amsa
Ya ce “A’a dai abokina,ƙarshe dai zaƙin amarci ke dibarka”
“Ba za ka gane ba kai kam”.
Tahir ya ce mishi.
Sallama nayi musu na ajiye musu farfesun, sai na ji sun sauya fira zuwa ta wurin aiki.
Miƙewa nayi Tahir ya ce “Ina za ki?
Na ce “Zan kwanta ne”.
Ya dubi agogo
“Kwanciya ko tara bata yi ba?
Shiru nayi
Ya dubi abokin nasa
“Yau tun tashin ta fushi take zan tafi gobe in bar ta”.
Ya ce “Kawai ka tafi da a bar ka”.
Kai ya girgiza “Idan na tafi da ita can su nawa ke jirana? ka san basma ma ta dawo kaduna, an maido ta aiki nan.
Nan kuwa ita kadai ce.
Dariyar shakiyanci abokin ya saki
“Kafin ka harbeta ko?
Jin furucinsa ban ko tsaya ce mishi sai da safe ba, na shige da sauri har ina tuntube”.
Tahir ya dube shi “Daga ka kore min amarya kai ma sai ka tashi, dan ka san ango baya doguwar fira”.
Dariya ya yi har yana buga kafa
“Allah sarki ni daɗin abun dai ni ma Allah yasa ina da matar nan, yau da na mutu da takaici.
In ka gama amarcin muna nan muna jiranka, duk da dai har na fara tunanin duk aurenka ban ga wadda ka ruɗe har kake min irin maganganun da kake yi yau, anya?
Tahir ya buɗe ido “Anya me? Sharrinka dai kai zai kashe.”
Tare suka fita abokin na dariya.

Na kwanta cikin jujjuya maganganun nasu, ban so zuciyata ta yarda da zargin da take na jin zantukansu, ina ta kokowa da zuciyar tawa ya shigo, gadon ya hayo sai da ya sanya ni jikinsa sannan yake bani labari
“Wannan ɗin da kike gani, abokina ne tun na kuruciya, sunansa Shehu, tanki yake tukawa a ma’aikatar mu”.

Da safe ma da muka tashi fuskata ba walwala, ina haɗa mishi abin karyawa sai rarrashina yake.
Ganin ina hawaye sai ya mike kayana ya soma haɗawa, da na ce mene ne ya ce tafiya za mu yi
Na yi saurin duban sa
“Tafiya kuma zuwa ina?
gira ya dage min “Kaduna”
Ido na zaro “Ba za ni ba”
Dole kuwa ki je, dan ba zan bar ki kina kuka ba”
Na share hawaye to kayi hakuri na daina”
Ya kamo ni muka zauna bakin gado maganganu masu daɗi yake gaya min har sai da ya ga na hakuran da gaske,
sai ya ce in raka shi wurin Hajiyarsa, na raka shi,suka yi sallama sai dai duk yadda ya so in mishi rakiya wurin motarsa kasawa nayi, dan duk mutanen gidan sun fito mishi bankwana.
Gadona kawai na haye da na koma daki,
wunin ranar ban fito ba, sai dai in tashi in yi sallah in koma in kwanta.
Ban tabbatar da shakuwar da nayi da shi me yawa ba ce dai da ya tafi ya bar ni.
Haka na koma kan al’amuran da nake yi, amma kewar Tahir na tare da ni duk da yawan wayar da muke yi.

Ranar da ya yi kwana uku da tafiya, ina dakin Haj ina yi mata goge goge, na daga received na ɗaga dan in goge kasanta, wasu hotuna suka bayyana, cikin mamaki na dauka ina dubawa, dan abin da na gani a cikin su, wata budurwa ce jikin hotunan me matukar kama da Tahir, dan dai kawai ita ɗin mace ce, duk a yan’uwansa ban ga wanda suka yi kama haka ba,
Su duk Haj suka biyo, shi kuma Tahir da mahaifinsa yake kama, dan akwai hoton mahaifinsa kafe a falon Haj.
Yarinyar yayansa da ke zaune a falon na nuna ma hoton “Salma wace ce a hotunan nan?
Ta taso daga inda take tana leka hotunan
“Anty Hadiza ce, ita ce autar su babanmu”.
A ina take? Na tambaye ta cikin mamaki dan ni dai ban taba jin wanda ya yi maganar ta ba.
“Tayi aure ba a daɗe ba, mijin dan Nijar ne ya tafi da ita can”.
Shiru nayi cikin kakkaɓi ina ƙara duban hotunan.

Da daddare na kai ma Haj fira, akwai jikokinta a dakin suna kallo, ni ba kallon nake ba wata yar wansa da ke fama da dan’uwanta ya koya mata sarfu an basu aiki bata iya ba, ganin har ta soma hawaye sai na yafito ta, ta iso gabana a hankali na shiga koya mata har ta gane, sai na nuna mata tayi aikin da aka basu a makarantar.
Tun daga ranar duk wanda bai gane aikin da aka yi musu ba sai ya zo wurina, iyayen ma samuna suka yi suna so in rika koya musu karatu na ce ba damuwa sai su zabi lokacin da suka ga ya dace mu riƙa yi daga su ne masu yawan aiki.

Da Tahir ya samu keɓewa zai kira ni, bai zo ba sai da ya samu kwanaki goma sha biyu da tafiya.
Ya ce min gashi nan zuwa, dan haka shiri sosai nayi na tarar sa,
ranar da zai zo tun da na tashi ban koma ba, sai da na gyara ko’ina kafin na shiga girki, Dambu nayi na shinkafa sanin shi ɗin me son cin nama ne kamar yanda Hajiyarsa take yasa na tanadi kazata, kai da kafa kawai aka cire mata dahuwar shinkafa cikin kaza nayi sai nayi mishi juice din abarba da kwakwa.
Da na kammala wanka nayi me kyau na gyara jikina sai da na ji na dauki ƙamshi ko ta ina cikin doguwar riga, ban je sasan Hajiya ba a ɗakina na yi zamana, isowar yara da ledoji ya bani tabbacin Ogan ya iso kenan, ya ɗan jima bai shigo ba na san yana wurin Haj.

Ƙamshin turarensa na fara shaƙa kafin na ga shigowarsa, jamfa da wando ne sanye a jikinsa na wata ɗanyar shadda, farin glass ɗinsa na rai da rai manne a idonsa mayatattun idanuwansa a kaina, sauke nawa idon nayi dan duk ya daburta ni, kawai sai na samu kaina da zubewa gabansa, ya ɗago ni sai ya manna ni a kirjinsa, bedroom muka wuce duk da tuna mishi da nake ya ci abinci tukuna.
Sai la’asar ya janye daga gare ni ya wuce masallaci.
Da ya dawo ne ya ci abinci sai kuma ya janyo ni wai in ba shi labarin kewar sa da nayi.

Kwanaki uku ya yi min wadanda suka yi matuƙar yi mana daɗi.
Ranar Monday da sassafe ya yi sammakon tafiya, ko da na tuna mishi mayar da ni Dutsinma daure fuska ya yi ya ce yana sane, tilas na haƙura.

 

Haka ya yi tayi ya zo Friday ya koma Monday, har na samu wata biyu, kafin cikar watanni biyun na samu ziyarar ƴan’uwana dukan su hada matan yayyena, Hafsa ma ta so biyo su lokacin kuma Ramlarta bata da lafiya, sai dai koyaushe tana ce min tana nan zuwa.
Wani zuwa da ya yi zai tafi na raka shi wurin Hajiya zai yi mata sallama yake ce mata “Sati me zuwa in Sha Allah zan tafi da ummulkhairi Kaduna”.
Hajiya tayi dan jim kafin ta ce “Ina sha ka bar min ita nan kenan?
Ya ce “Na dai bar ta ne ta ga dangina ta saba da su”.
Sai ga Haj tana matse ido yana bata hakuri.
“Saboda Allah ka san ba bar min ita za ka yi ba ka kawo min ita?
Sai da na shaku da ita, yarinya me hankali da kirki da ganin girman mutane, Allah kaɗai yasan ƙaruwar da mutanen gidan nan suka samu zuwanta.
Ka ga ga karatu tana koya musu su da yaransu, daidai da girki zuwanta matan nan sun gyara girkinsu, ga ta bata da rowa komai ka kawo mata sai ta cire ma kowa, ni nan abin da nake so shi za ta girka min, kullun sai ta dafa min nama, ta gyara min daki, ta kwance min kai tayi min kitso,zannuwana ta wanke min.
Sai ta shiga kuka sosai tana fyace hanci, ya ce “Ki yi haƙuri Haj, nayi wa Fati magana (ɗiyar wansa ce) duk safiya ta zo ta gyara miki ɗaki ta kuma rika yi miki kitso, wanki da gugar kayanki kuma Na matazu zai rika aikowa a karɓa, nama da kwai za a cigaba da kawowa umma ta rika dafa miki, tun da kin ce duk matan ta fi su tsafta da iya girki.
In kuma duk hakan bai yi miki ba to ki shirya mu tafi tare.
Nan kuma tayi tsalle ta ce “Allah ya tsare ta da komawa gidansa.
Ya ce “To cikin sauran matana ki zaɓi wadda kike so zan kawo miki ita”.
Nan ma ta ce ya rufa mata asiri bata son ko daya.
Ya ce ki fahimce ni Haj na ɗauko ummulkhairi da nufin kwana ɗaya za tayi, in mayar da ita, yan’uwanta sun je Kaduna sun yi mata jere.
Ita kanta kullun korafin da take min kenan,
sai iyayenta da ƴan’uwanta su ji ta shiru daga tafiyar kwana ɗaya,
ki yi haƙuri Haj ayi mata biki irin na al’ada in yaso bayan ta tare a Kaduna sai in dawo miki da ita.
Da alama dai Haj bata da niyyar fahimtar sa, lallashinta ya shiga yi ya ce ya bar ni.
Kudade ya ciro ya ajiye mata, sai muka fito sai da ya shiga motarsa ya leƙo da kansa “Kina ji na da Haj? auren nan kamar ita nayi mawa”.
Ni dai murmushi nayi.

Na cigaba da zama a ƙanƙara, a matan yayyensa mun fi shiri da matar yayansa wanda yake bi mawa yaya Abubakar, uwargidansa sunanmu daya da ita, amma ita Umma ake ce mata ni kuma ina kiranta maman ummi sunan yarta ta farko, ɗanta na biyu me suna Faisal ba shi da ƙyuya ko’ina zan aike shi dan haka ni kuma komai zan ci da rabonsa sanadin sa kauna ta wanzu tsakanina da ita.
Sai na lura a gidan matar babban yaya ta biyun wadda yaranta ke kira da Amma da sannu sunan ya bi bakin kowa, ita ke faɗa aji a gidan ko a wurin yaya babban ita ce mandiya.
Ɗakinta nan ne majalisa ta yan gidan, ni dai ban zuwa haka ma maman ummi, domin amaryar maman ummi usaina yar dakin Amma ce.
Amma mutumniyar maradun ce ta jihar Zamfara, tana sayar da magungunan mata wanda idan ta je garin su ta kan saro ta taho da shi.

Bayan tafiyar Tahir nayi wanki, shanya ita tafi kaini tsakar gidan, ina cikin shanya naji yarinyar Amma tana ce min “Aunty Innarmu tana kiranki”. na ce ina zuwa
sai na cigaba da shanyata, sai da na kammala sai na isa ƙofarta nayi mamakin rashin samun kowa a ɗakin, na shiga da sallama ta amsa tana min fara’a, na soma gaishe ta ta ce “Haba ummulkhairi sai ka ce wata baƙuwa zauna man”. na zauna ina kallon abubuwan da ta baza a gabanta.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: [2/18, 1:06 PM] Maryam: *NA KUDI NE 300 KA BIYA A 2108124716*
*Maryam nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya*
*07033400612*

“To ummulkhairi na kira ki ne don ki gyara kanki, kin ga duk wannan rawar ƙafan da Sodangi yake yi da ke, daga zarar kin ƙare amarci in ba dagewa kika yi da gyaran kanki ba juya miki baya zai yi.
Ga kishiyoyi kina da su, kowace kokari take ta ga ta zama ta gaban goshi”.
ta shiga lissafa min sunayen magungunan matan da ke gabanta, “To dame dame za a ba ki?
Kunyarta ta sa na ɗauki wata gorar tsimi, ta ce min dubu biyu, na ce zan bayar a kawo mata, tayi tayi in ƙara wasu abubuwan na ce A’a.
Da fitowata sasan su maman ummi na fada,
Amaryarta tana tsifa a ƙofar ɗakinta ganina sai ta gintse fuska na miƙa mata gaisuwa ta amsa a dage, kamar yanda ta saba min tun fara shirina da kishiyarta.
Na daga labulan maman ummi zaune take ta tasa katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe.
Na shiga na zauna murmushi take jifana da shi “Me kika samo mana? ta tambaya tana miƙo hannu sai na miƙa mata robar tsimin,
yamutsa fuska nayi sai na bata labarin yanda muka yi da Amma,
baki ta rike “To tun wuri ki kiyayi kanki, kin san tib da taya? to haka suke da Halima”.
Wani kallo nayi mata “Wace ce Halima kuma?
ta gyaɗa kai “Lallai ma uwargidan taki ce ba ki sani ba”.
ajiyar zuciya na fidda
“Ina jinki, dan sam ban kawo ta ba”
“Duk wani shige shige ita ce ke yi wa Halima, shi ne dan rashin tsoron Allah ke ma za ta ja ki jikinta, masallaci ɗaya limami biyu kenan, ko kuma ke tayi miki shigo shigo ba zurfi.
Yanzu nawa ta sayar miki da wannan?
Na ce 2000″
Kama baki tayi lallai za ta mayar da ke saniyar tatsa, 500 take saida shi, ki yi kokari ki iya da kanki gudun kada ta kaiki ta baro.
Kuma Allah na tuba Magungunan Amma ai sai dai rashin sani, gamje gamje ne ba ma ko yi yake ba, tsoro kawai ke sa matan gidan nan saye, dan in bata yi da kai ruwa sai ya nemi gagararka a gidan nan”.
Mun ɗauki wani lokaci muna maida maganar kafin na koma wurina.

Kwanaki uku kawai aka yi Amma ta kuma kirana ce min tayi yakamata a dafa min kaza, in ci yan shila, kai har ma cicciɓi a dafa min, duk in ci kafin zuwan Tahir.
Dogon bill tayi min
Na ce yanzu bani da kuɗi ta bari tukun, ta ce ai zan bada wani abu ne saura kuma a hankali ina badawa,na ce ta dai bari in samu. Mata fa ta matsa min
Ranar da Tahir ya zo muna daki sai ga yarta ta turo kirana, gaba ɗaya jikina ya dauki rawa ina ganin kamar Tahir zai gane abin da kenan, ban motsa ba har sai da ya ce “Ki tashi ki je mana kin zauna kina rawar jiki”.
sim sim na miƙe na fice.
Da isata wani zobe ta miƙo min, “Ungo ki saka a hannunki, kin san tsafi to wannan zoben aikinsa kamar tsafi yake”.
A zuciyata nayi Auzubillahi na neman tsari da tsafi “Ki saka shi da duk niyyar da kike so za ki sha mamaki, dubu biyar ne kudinsa kacal, amma aikinsa, tayi ƙwafa, miƙa mata nayi “Bani da kuɗi Amma”
ta ki karba ki je da shi ki gwada amfani da shi ki ga yanda zai rika juye miki bakin aljihu, mijinki fa ba ƙananan kuɗaɗe gare shi ba”.
Ƙara miƙa mata nayi
duk kuma yanda taso tilasta ni in karɓa zullewa nayi.
Aikowar da akayi Tahir na kirana ta cece ni, na ajiye mata a hannun kujera na fito na bar ta cikin takaici.
Jikina ya soma rawa hango Tahir daga nesa yana kallon ƙofar Amma, da alama fitowata yake tsayuwar jira, ransa a haɗe, hannuwansa rungume a kirjinsa, na wuce shi kaina a kasa, ina shiga yana shigowa “Meye tsakaninki da Amma?
ya jeho min tambayar a ba zata, “Ba komai”.nayi ƙarfin halin ba shi amsa “To ko ma dai meye bana son kowace hulɗa ta haɗa ku, bayan ta gaisuwa, jaje da taya murna”.
Kai na daga mishi “In kuma wani abu ya biyo baya, wallahi sai nayi mummunan saɓa miki”.a ranar dai ban gane kansa ba daure min fuska ya yi,sai washegari na same shi na ba shi haƙuri.

Kwanan shi hudu da komawa maman ummi ta haihu, ya mace ta samu.
A wurin zaman jegon ne na ji matan gidan suna firar zoben Amma, anan har na ji kuɗin da take saida shi Naira dubu daya, ni kuma ta ce min dubu biyar.
Sai na ƙara nesanta kaina da duk wata mu’amala da za ta haɗa mu ni da ita.

Kayan maman ummi na wanke mata a laundry. Ina shanya kayan a igiya, na ga Amma ta yo rakiyar baƙuwa, zuwana inda suke tsaye bai sa ta canza firar da suke ba. “Matansa na Kaduna, ta biyun a Abuja take, ta farkon kuma ai Halima ce ta nan gidan su mai waina”.
Matar ta gyaɗa kai “Ƙwarai na santa”. “Sai wadda ya auro kwanan nan, ya ajiye a gidan nan.
Amma matan da suka amsa mata suna birni, ita kuma tana nan,ai me aiki ya samo wa uwarsa”.
daidai nan muka haɗa ido da ita, wani kallon banza ta min, na wuce su zuwa ɗakina, rasa abin da ke min daɗi nayi, har ji na riƙa yi kamar zazzaɓi zai rufe ni.
Dare nayi zazzaɓin ya bakunce ni, sai asuba ya sauka.
Tun daga ranar kuma Amma da kishiyar maman Ummi usaina, suka ta sa ni da neman fitina, ina kauce musu.
Ko da Tahir ya zo ya yi complain din zafin jikina da daddare, na ce lafiyata ƙalau.

Wata ranar Laraba na wanke kayan Haj ina shanya mata, sai ga usaina kamar an jeho ta. “To yan neman gindin zama, ya za ayi ki haɗe min shanya ki sanya naki? duban inda kayan nata suke nayi, sam shanyata bata je wurin su ba. Cigaba nayi da shanyata ban mata magana ba, gabana ta zo tana girgiza jiki, “Ni za ki mayar ƴar iska? ina miki magana kin min banza. Nan ma ban gwada na ji ma me take cewa ba, kayan da na shanya ta zo ta kwashe ta zubar. Rabi matar Yayan Tahir da ke wanke wanke ta ce “Haba meye haka za ki zubar mata da kaya? sam hakan bai dace ba”.
Raina ya gama ɓaci na ce “Wannan wane irin wulaƙanci ne za ki zubar min da kaya?
“An zubar ki dau mataki.
Aikin banza kawai, waɗanda aka ɗauka mata suna birni, Kaduna jansin lahirar makwadaita, muna mata kuma, ta rangada guɗa “An bar su a ƙauye, suna bauta”.
Idona na ji ya kawo ruwa na ce “Wai me nayi muku kuke min wannan cin kashin? Sai ga Amma kamar an jeho ta “Yo ƙarya aka faɗi?
Suka taru ita da usaina suna min tijara. Matan gidan suka taru duk kuma haƙurin da suke ba su basu samu nasarar tsaida su ba. Na cigaba da kwashe kayan da suka zubar min idona na cigaba da zubar hawaye, har ana riƙe usaina za ta zo ta duke ni.
Shirun da na ji wurin ya dauka ne yasa ni daga idona ina share hawaye.
Tahir ne tsaye, hannuwansa harɗe a kirjinsa yana kallon kowa ɗaiɗai ta cikin farin glass ɗinsa, Amma ta fara ankara ta soma sulalewa kafin usainar ta bi bayanta.
Na ɗauki bokiti da kayan na wuce ɗaki, a falo na zauna ƙasa ina kuka,
Tahir ya shigo kaina ya tsaya yana tambayata me ya haɗa mu.
Sai dai juyin duniya na ki magana, juyawa ya yi ya fita, zuwa sasan Hajiya, hankali tashe ya same ta tana sa wa a kira mata ƴaƴanta, duk da gaya mata da ake sun kusa dawowa daga lokacin dawowar ta su ya kusa, bata yarda da hakan ba.
Wuri ya samu ya zauna, kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ransa a matuƙar ba ce yake, da ɗaiɗai suka riƙa shigowa hada kanenta Kawu Attahiru, wanda sunansa Tahir ya ci, kuma shi ne marikinsa, dan Allah bai ba shi haihuwa ba, tare suka zo da Tahir shi
Tahir ya yo ma rakiya.
Sai da kowa ya zauna
sannan Haj ta kora musu abin da ya faru kamar yadda aka zo aka bata labari, an ce a kira ni ni da usaina da Amma.
Ni ce na iso karshe, dogon hijab har kasa na sanyo, na rabe daga bakin kofa, Amma aka nemi ta faɗi abin da ya faru kame kame ta shiga yi ƙarshe magana ta gagara, sai usaina, ita ma ɗin kame kamen ne, da aka zo kaina na fadi duk yadda abin ya faru, har ma da abubuwan da suka yi mini kafin yau.
Mamaki ne ya barke a dakin ana tambayar su dalilin su na yin hakan. Yaya Magaji me bi ma yaya Babba, duk ya fi su zafi ya tambayi gaban wa abin ya faru, Haj ta ce an ce gaban matarsa Rabi ne, a waya ya kirata sai ga ta, ya tambaye ta tare da mata gargadin ta gaya mishi gaskiya, yanda na faɗi ta maimaita.
Ran kowa a wurin ya ƙara ɓaci, Tahir dai ko tari bai ba Haj ta ce “To kun ji abin da ya faru, wlh ku ja wa matanku kunne, idan hakan ta kuma faruwa ba zan lamunta ba. Babu wacce za ta farraka min kan iyali, wannan yarinya ta wanke kayana, kai lawal matarka ta zubar, kayana lawal, kuma dan tana min aiki shi ne ya zame mata abin gori wurin matanku”.
Sai ta kama kuka
Yaya lawal na miƙewa ya ce ya saki usaina ta je gida.
Dakin aka ɗauki sallallami ana mishi faɗan saurin furta kalmar saki, Yaya Babba ma ya mike Kawu Attahiru ya tsaida shi, amma duk da haka ya rantse sai Amma ta tafi gidan su, daga mahaifiyarsa ce abar rainawarta.
Usaina da Amma suka fita kowacce tana kuka, na yunkura suka shiga bani haƙuri, na fita dakin na koma wurin mu na kara ɗauraye kayan Hajiya na wuce na shanya, na ɗauko bokitin na ga Tahir tsaye yana kallona, wuce shi nayi kitchen na shiga na soma girki, sai da na kawo ma Tahir inda yake zaune shiru a falo, kafin na wuce na kaima Haj ita da kanenta, na samu suna magana shi da Hajiyar, nasiha sosai Kawun ya yi min game da rayuwar aure da duka rayuwar ita kanta.
Kafin ya rufe da shi min albarka, da kara faɗa min in cigaba da abin da nake abu ne me kyau, kar abin da wadancan suka yi min yasa in daina
Na yi mishi godiya na koma wurina, wanka na wuce nayi, ko da na gama shirina kwanciyata nayi, Tahir ya leƙo, ganina kwance sai ya koma.
Haka muka ƙarasa kai dare da shi, bai ce min ba ban ce mishi ba, har sai da muka kwanta kamar yanda barci ya kasa ɗaukata, shi ma juyi yake ta yi yana tsaki, mirginowa ya yi inda nake, ya sa ni jikinsa.
“Ki yi hakuri Ummulkhairi, na rasa abin ce miki bisa abin da aka yi miki, matan ƴan’uwana ne, kuma albarkacin ƴan’uwan nawa suka ci, amma yau da wasu ne can daban suka ci zarafinki haka, da kin gane ko ke wace ce a wurina. Amma ina rokonki ki yi hakuri”.
Hawayen da suka fara gudu suna min zuba suka sauka kan kirjinsa, yasa hannu ya share min, ki yi min magana, ko ba ki haƙura ba?
Na ce “Ya wuce”. ya ce “Allah ya shi miki albarka” daga haka wasanninsa ya shiga yi, kafin mu shiga wata duniyar.
Sai da komai ya lafa ya ce Jikinki da zafi, gobe zan kaiki ki ga likita, wancan zuwan na ce kin musa min”.
Na ce “Ni lafiyata ƙalau”. Sai na ƙara maƙale shi dan sanyi nake ji.

Da safe na tashi garas na kama harkokina.
Ɗagowar hantsi Amma ta bar gidan, wanda ban ji dadi ba, dan ba daɗi abu mara dadi ya faru irin haka ace sanadinka ne.
Ita kuwa Usaina tun daren ta wuce, da safen ma ni na shirya ma Kawu abin karyawa na kai mishi ɗakin Haj, haka na rana, dan haka ban samu yin wanka da wuri ba, sai da nayi sallar azahar, nayi kwalliya cikin wasu riga da siket English wear, zuwan Tahir wancan karon ya zo min da su. Rigar ta kama ni yankakken hannu gare ta, gashina ana gobe sunan Maman Ummi muka ziyarci Sallon ni da Maman Ummin aka gyara mana, ribbon na sa na kama gashin ta tsakiya, sai duban kaina nake ta madubi, nayi bulbul gaba ɗaya nayi wani narai narai, komai nawa ya ƙara cika.
Bedroom din na bari na isa kitchen, cornflakes na haɗo da Madara na taho ina sha, Tahir da ke kwance rub da ciki a tsakiyar gado yana aikinsa a laptop ya kura min ido tun tahowata “Zo nan yarinya, ki faɗa min shekarunki”. Murmushi nayi na zauna gefen gadon ina nuna mishi da ƴan yatsuna.
“Ashirin da biyu? Ya tambaye ni na girgiza kai na ƙara nuna mishi “Ashirin da ɗaya? Na ɗaga mishi kai, cigaba ya yi da kallona har na shanye yana ganin na ajiye mug din sai ya janyo ni jikinsa, “Duk da kishin mutumin nan da ke taso min, idan na tuna ya riga ni saninki, wani lokacin kuma na kan ji kamar in gan shi dan in ƙara hakikance girman sakarcinsa na samun mace kamarki kuma ya yi sullancin da kika subuce mishi.
Murmushi nayi jin maganarsa.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: [2/18, 1:06 PM] Maryam: *NA KUDI NE 300 KA BIYA A 2108124716*
*Maryam nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya*
*07033400612*

“To ummulkhairi na kira ki ne don ki gyara kanki, kin ga duk wannan rawar ƙafan da Sodangi yake yi da ke, daga zarar kin ƙare amarci in ba dagewa kika yi da gyaran kanki ba juya miki baya zai yi.
Ga kishiyoyi kina da su, kowace kokari take ta ga ta zama ta gaban goshi”.
ta shiga lissafa min sunayen magungunan matan da ke gabanta, “To dame dame za a ba ki?
Kunyarta ta sa na ɗauki wata gorar tsimi, ta ce min dubu biyu, na ce zan bayar a kawo mata, tayi tayi in ƙara wasu abubuwan na ce A’a.
Da fitowata sasan su maman ummi na fada,
Amaryarta tana tsifa a ƙofar ɗakinta ganina sai ta gintse fuska na miƙa mata gaisuwa ta amsa a dage, kamar yanda ta saba min tun fara shirina da kishiyarta.
Na daga labulan maman ummi zaune take ta tasa katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe.
Na shiga na zauna murmushi take jifana da shi “Me kika samo mana? ta tambaya tana miƙo hannu sai na miƙa mata robar tsimin,
yamutsa fuska nayi sai na bata labarin yanda muka yi da Amma,
baki ta rike “To tun wuri ki kiyayi kanki, kin san tib da taya? to haka suke da Halima”.
Wani kallo nayi mata “Wace ce Halima kuma?
ta gyaɗa kai “Lallai ma uwargidan taki ce ba ki sani ba”.
ajiyar zuciya na fidda
“Ina jinki, dan sam ban kawo ta ba”
“Duk wani shige shige ita ce ke yi wa Halima, shi ne dan rashin tsoron Allah ke ma za ta ja ki jikinta, masallaci ɗaya limami biyu kenan, ko kuma ke tayi miki shigo shigo ba zurfi.
Yanzu nawa ta sayar miki da wannan?
Na ce 2000″
Kama baki tayi lallai za ta mayar da ke saniyar tatsa, 500 take saida shi, ki yi kokari ki iya da kanki gudun kada ta kaiki ta baro.
Kuma Allah na tuba Magungunan Amma ai sai dai rashin sani, gamje gamje ne ba ma ko yi yake ba, tsoro kawai ke sa matan gidan nan saye, dan in bata yi da kai ruwa sai ya nemi gagararka a gidan nan”.
Mun ɗauki wani lokaci muna maida maganar kafin na koma wurina.

Kwanaki uku kawai aka yi Amma ta kuma kirana ce min tayi yakamata a dafa min kaza, in ci yan shila, kai har ma cicciɓi a dafa min, duk in ci kafin zuwan Tahir.
Dogon bill tayi min
Na ce yanzu bani da kuɗi ta bari tukun, ta ce ai zan bada wani abu ne saura kuma a hankali ina badawa,na ce ta dai bari in samu. Mata fa ta matsa min
Ranar da Tahir ya zo muna daki sai ga yarta ta turo kirana, gaba ɗaya jikina ya dauki rawa ina ganin kamar Tahir zai gane abin da kenan, ban motsa ba har sai da ya ce “Ki tashi ki je mana kin zauna kina rawar jiki”.
sim sim na miƙe na fice.
Da isata wani zobe ta miƙo min, “Ungo ki saka a hannunki, kin san tsafi to wannan zoben aikinsa kamar tsafi yake”.
A zuciyata nayi Auzubillahi na neman tsari da tsafi “Ki saka shi da duk niyyar da kike so za ki sha mamaki, dubu biyar ne kudinsa kacal, amma aikinsa, tayi ƙwafa, miƙa mata nayi “Bani da kuɗi Amma”
ta ki karba ki je da shi ki gwada amfani da shi ki ga yanda zai rika juye miki bakin aljihu, mijinki fa ba ƙananan kuɗaɗe gare shi ba”.
Ƙara miƙa mata nayi
duk kuma yanda taso tilasta ni in karɓa zullewa nayi.
Aikowar da akayi Tahir na kirana ta cece ni, na ajiye mata a hannun kujera na fito na bar ta cikin takaici.
Jikina ya soma rawa hango Tahir daga nesa yana kallon ƙofar Amma, da alama fitowata yake tsayuwar jira, ransa a haɗe, hannuwansa rungume a kirjinsa, na wuce shi kaina a kasa, ina shiga yana shigowa “Meye tsakaninki da Amma?
ya jeho min tambayar a ba zata, “Ba komai”.nayi ƙarfin halin ba shi amsa “To ko ma dai meye bana son kowace hulɗa ta haɗa ku, bayan ta gaisuwa, jaje da taya murna”.
Kai na daga mishi “In kuma wani abu ya biyo baya, wallahi sai nayi mummunan saɓa miki”.a ranar dai ban gane kansa ba daure min fuska ya yi,sai washegari na same shi na ba shi haƙuri.

Kwanan shi hudu da komawa maman ummi ta haihu, ya mace ta samu.
A wurin zaman jegon ne na ji matan gidan suna firar zoben Amma, anan har na ji kuɗin da take saida shi Naira dubu daya, ni kuma ta ce min dubu biyar.
Sai na ƙara nesanta kaina da duk wata mu’amala da za ta haɗa mu ni da ita.

Kayan maman ummi na wanke mata a laundry. Ina shanya kayan a igiya, na ga Amma ta yo rakiyar baƙuwa, zuwana inda suke tsaye bai sa ta canza firar da suke ba. “Matansa na Kaduna, ta biyun a Abuja take, ta farkon kuma ai Halima ce ta nan gidan su mai waina”.
Matar ta gyaɗa kai “Ƙwarai na santa”. “Sai wadda ya auro kwanan nan, ya ajiye a gidan nan.
Amma matan da suka amsa mata suna birni, ita kuma tana nan,ai me aiki ya samo wa uwarsa”.
daidai nan muka haɗa ido da ita, wani kallon banza ta min, na wuce su zuwa ɗakina, rasa abin da ke min daɗi nayi, har ji na riƙa yi kamar zazzaɓi zai rufe ni.
Dare nayi zazzaɓin ya bakunce ni, sai asuba ya sauka.
Tun daga ranar kuma Amma da kishiyar maman Ummi usaina, suka ta sa ni da neman fitina, ina kauce musu.
Ko da Tahir ya zo ya yi complain din zafin jikina da daddare, na ce lafiyata ƙalau.

Wata ranar Laraba na wanke kayan Haj ina shanya mata, sai ga usaina kamar an jeho ta. “To yan neman gindin zama, ya za ayi ki haɗe min shanya ki sanya naki? duban inda kayan nata suke nayi, sam shanyata bata je wurin su ba. Cigaba nayi da shanyata ban mata magana ba, gabana ta zo tana girgiza jiki, “Ni za ki mayar ƴar iska? ina miki magana kin min banza. Nan ma ban gwada na ji ma me take cewa ba, kayan da na shanya ta zo ta kwashe ta zubar. Rabi matar Yayan Tahir da ke wanke wanke ta ce “Haba meye haka za ki zubar mata da kaya? sam hakan bai dace ba”.
Raina ya gama ɓaci na ce “Wannan wane irin wulaƙanci ne za ki zubar min da kaya?
“An zubar ki dau mataki.
Aikin banza kawai, waɗanda aka ɗauka mata suna birni, Kaduna jansin lahirar makwadaita, muna mata kuma, ta rangada guɗa “An bar su a ƙauye, suna bauta”.
Idona na ji ya kawo ruwa na ce “Wai me nayi muku kuke min wannan cin kashin? Sai ga Amma kamar an jeho ta “Yo ƙarya aka faɗi?
Suka taru ita da usaina suna min tijara. Matan gidan suka taru duk kuma haƙurin da suke ba su basu samu nasarar tsaida su ba. Na cigaba da kwashe kayan da suka zubar min idona na cigaba da zubar hawaye, har ana riƙe usaina za ta zo ta duke ni.
Shirun da na ji wurin ya dauka ne yasa ni daga idona ina share hawaye.
Tahir ne tsaye, hannuwansa harɗe a kirjinsa yana kallon kowa ɗaiɗai ta cikin farin glass ɗinsa, Amma ta fara ankara ta soma sulalewa kafin usainar ta bi bayanta.
Na ɗauki bokiti da kayan na wuce ɗaki, a falo na zauna ƙasa ina kuka,
Tahir ya shigo kaina ya tsaya yana tambayata me ya haɗa mu.
Sai dai juyin duniya na ki magana, juyawa ya yi ya fita, zuwa sasan Hajiya, hankali tashe ya same ta tana sa wa a kira mata ƴaƴanta, duk da gaya mata da ake sun kusa dawowa daga lokacin dawowar ta su ya kusa, bata yarda da hakan ba.
Wuri ya samu ya zauna, kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ransa a matuƙar ba ce yake, da ɗaiɗai suka riƙa shigowa hada kanenta Kawu Attahiru, wanda sunansa Tahir ya ci, kuma shi ne marikinsa, dan Allah bai ba shi haihuwa ba, tare suka zo da Tahir shi
Tahir ya yo ma rakiya.
Sai da kowa ya zauna
sannan Haj ta kora musu abin da ya faru kamar yadda aka zo aka bata labari, an ce a kira ni ni da usaina da Amma.
Ni ce na iso karshe, dogon hijab har kasa na sanyo, na rabe daga bakin kofa, Amma aka nemi ta faɗi abin da ya faru kame kame ta shiga yi ƙarshe magana ta gagara, sai usaina, ita ma ɗin kame kamen ne, da aka zo kaina na fadi duk yadda abin ya faru, har ma da abubuwan da suka yi mini kafin yau.
Mamaki ne ya barke a dakin ana tambayar su dalilin su na yin hakan. Yaya Magaji me bi ma yaya Babba, duk ya fi su zafi ya tambayi gaban wa abin ya faru, Haj ta ce an ce gaban matarsa Rabi ne, a waya ya kirata sai ga ta, ya tambaye ta tare da mata gargadin ta gaya mishi gaskiya, yanda na faɗi ta maimaita.
Ran kowa a wurin ya ƙara ɓaci, Tahir dai ko tari bai ba Haj ta ce “To kun ji abin da ya faru, wlh ku ja wa matanku kunne, idan hakan ta kuma faruwa ba zan lamunta ba. Babu wacce za ta farraka min kan iyali, wannan yarinya ta wanke kayana, kai lawal matarka ta zubar, kayana lawal, kuma dan tana min aiki shi ne ya zame mata abin gori wurin matanku”.
Sai ta kama kuka
Yaya lawal na miƙewa ya ce ya saki usaina ta je gida.
Dakin aka ɗauki sallallami ana mishi faɗan saurin furta kalmar saki, Yaya Babba ma ya mike Kawu Attahiru ya tsaida shi, amma duk da haka ya rantse sai Amma ta tafi gidan su, daga mahaifiyarsa ce abar rainawarta.
Usaina da Amma suka fita kowacce tana kuka, na yunkura suka shiga bani haƙuri, na fita dakin na koma wurin mu na kara ɗauraye kayan Hajiya na wuce na shanya, na ɗauko bokitin na ga Tahir tsaye yana kallona, wuce shi nayi kitchen na shiga na soma girki, sai da na kawo ma Tahir inda yake zaune shiru a falo, kafin na wuce na kaima Haj ita da kanenta, na samu suna magana shi da Hajiyar, nasiha sosai Kawun ya yi min game da rayuwar aure da duka rayuwar ita kanta.
Kafin ya rufe da shi min albarka, da kara faɗa min in cigaba da abin da nake abu ne me kyau, kar abin da wadancan suka yi min yasa in daina
Na yi mishi godiya na koma wurina, wanka na wuce nayi, ko da na gama shirina kwanciyata nayi, Tahir ya leƙo, ganina kwance sai ya koma.
Haka muka ƙarasa kai dare da shi, bai ce min ba ban ce mishi ba, har sai da muka kwanta kamar yanda barci ya kasa ɗaukata, shi ma juyi yake ta yi yana tsaki, mirginowa ya yi inda nake, ya sa ni jikinsa.
“Ki yi hakuri Ummulkhairi, na rasa abin ce miki bisa abin da aka yi miki, matan ƴan’uwana ne, kuma albarkacin ƴan’uwan nawa suka ci, amma yau da wasu ne can daban suka ci zarafinki haka, da kin gane ko ke wace ce a wurina. Amma ina rokonki ki yi hakuri”.
Hawayen da suka fara gudu suna min zuba suka sauka kan kirjinsa, yasa hannu ya share min, ki yi min magana, ko ba ki haƙura ba?
Na ce “Ya wuce”. ya ce “Allah ya shi miki albarka” daga haka wasanninsa ya shiga yi, kafin mu shiga wata duniyar.
Sai da komai ya lafa ya ce Jikinki da zafi, gobe zan kaiki ki ga likita, wancan zuwan na ce kin musa min”.
Na ce “Ni lafiyata ƙalau”. Sai na ƙara maƙale shi dan sanyi nake ji.

Da safe na tashi garas na kama harkokina.
Ɗagowar hantsi Amma ta bar gidan, wanda ban ji dadi ba, dan ba daɗi abu mara dadi ya faru irin haka ace sanadinka ne.
Ita kuwa Usaina tun daren ta wuce, da safen ma ni na shirya ma Kawu abin karyawa na kai mishi ɗakin Haj, haka na rana, dan haka ban samu yin wanka da wuri ba, sai da nayi sallar azahar, nayi kwalliya cikin wasu riga da siket English wear, zuwan Tahir wancan karon ya zo min da su. Rigar ta kama ni yankakken hannu gare ta, gashina ana gobe sunan Maman Ummi muka ziyarci Sallon ni da Maman Ummin aka gyara mana, ribbon na sa na kama gashin ta tsakiya, sai duban kaina nake ta madubi, nayi bulbul gaba ɗaya nayi wani narai narai, komai nawa ya ƙara cika.
Bedroom din na bari na isa kitchen, cornflakes na haɗo da Madara na taho ina sha, Tahir da ke kwance rub da ciki a tsakiyar gado yana aikinsa a laptop ya kura min ido tun tahowata “Zo nan yarinya, ki faɗa min shekarunki”. Murmushi nayi na zauna gefen gadon ina nuna mishi da ƴan yatsuna.
“Ashirin da biyu? Ya tambaye ni na girgiza kai na ƙara nuna mishi “Ashirin da ɗaya? Na ɗaga mishi kai, cigaba ya yi da kallona har na shanye yana ganin na ajiye mug din sai ya janyo ni jikinsa, “Duk da kishin mutumin nan da ke taso min, idan na tuna ya riga ni saninki, wani lokacin kuma na kan ji kamar in gan shi dan in ƙara hakikance girman sakarcinsa na samun mace kamarki kuma ya yi sullancin da kika subuce mishi.
Murmushi nayi jin maganarsa.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *NA KUDI NE 300*
*biya 2108124716* *Maryam nasir UBA*

farkawata daga barci sai na ɗora idona bisa agogo, ƙarfe bakwai saura minti takwas na safe. Jikina na zare cikin na Tahir sai na fito, bathroom na fara shiga kafin na isa kitchen, ruwan Lipton wanda na zuba ma kayan ƙamshi na ɗora, yana fara zafi na fito, zane na ɗaura saman riga da wando na barci da ke jikina sai na saka hijab, bayan ɗakina na fita na dauko murhun gawayi na zuba gawayin kafin ya ruru na koma na kashe gas ɗin na juye ruwan zafin cikin flacks, da sauri na fasa ƙwai na soya wa Haj, na gasa mata bread.
Wurin gawayin na koma ya ruru, na dauka zan wuce na ji muryarsa a kunnena “Ina za ki da wannan?
Haj zan sanya ma wa a daki”.
Na ba shi amsa, sai na wuce, a uwar ɗakanta na same ta, na ajiye nesa da ita dan kar ya takura mata, na juya muka haɗa ido da Tahir na ratse shi na wuce, abin karyawarta na koma na kawo mata.
Samu nayi suna magana, ban zauna ba kitchen na koma na kama aikina.
Koda na kammala namu, dakin Haj ya nemi in kai mishi, dan haka can ɗin na kai, sai da ya shigo, yake tambayata me yasa ake kaiwa Haj wuta a daki.
Ban ƙasa a gwiwa ba na ce “Saboda lalurarta, kuma ina ganin da za a daure da room heater aka sanya mata a ɗakin, bathroom ɗinta kuma a saka water heater saboda masu lalurar ba sa mu’amala da sanyi.
Idan aka yi hakan ina ganin ba ƙaramar lada za a samu ba”
Daga haka bathroom na shiga dan na gama komai wanka zan yi.
Shi ma da ya yi wankan Kano ya tafi.

Ina sallar la’asar na ji yaran gidan suna ta sannu da zuwa, sai da Tahir ya shigo na gane shi suke mawa, sai kuma da na shiga wurin Haj kai mata abincin dare sai na ga aikin da ake yi.
Water heater da room heater ake sanya mata, dan murmushi nayi a raina na ce sayen su ya kai shi Kano kenan.
Sai da muka nutsu a makwancinmu yake shi min albarka wai na tunasar da shi abin da yake wajibinsa ne.

Ana gobe zai koma Kaduna, da safe duk da nauyin sa da nake ji sai da ya gane ɓacin raina, wunin ranar bai je ko ina ba muna daki sai dai ya fita sallah ya dawo.
Ya dawo sallar isha’i aka kira wayarsa, ji nayi yana cewa ka shigo kawai, da shigowar baƙon miƙewa ya yi sai suka tafa,
“Shegen bisa yaushe a gari?
Tahir ya ce wa baƙon nasa,
“Da magaribar nan mutumina, ai ina sauka nake jin kana garin nan har sati biyu, shiyasa ko abinci ban tsaya ci ba na ce bari in zo in ga wannan amarya da ta iya riƙe ka har sati biyu”.
“Sharri ka shi zai kashe ka, wa ya ce maka ban taɓa sati biyu a ƙanƙara ba?
“Haba abokina ai rabonka da ka zo ka dade ina ga tun kana sakandare idan ka zo hutu”.
Dariya suka yi
Na ce “Sannu da zuwa”.
Ya juyo yi hakuri amaryarmu, ya amarci?
Na gaishe shi ya ce “A yi min afuwa amarya, ban samu halartar ɗaurin aure ba, muna wurin kwadago”,
Na ce “An dawo lafiya?”Lafiya ƙalau Alhamdulillahi”.
Tahir ya buɗe abinci “Bismillah”
Kallon abincin ya yi “Anya kuwa na ci abincin nan, ni ma nawa na can gida.
Dan yau ni ma ɗin ango ne, kar in ci kasa a min bore”.
Ya ce “Ci kawai malam, na rakaka har gaban Saratun, dama ai na ce kai mijin ta ce ne kullum kana fama da mace ɗaya”.
Ya cika bakinsa da abinci ya ce “Dole ka yi ta zama abokina, ko da wannan daddaɗan abincin ai a riƙe ka”.
Ya ce “Kai dai dan iska ne wallahi”.
Duba na ya yi “Dan bani ruwa mara sanyi ummulkhairi”
Sai da na je na kawo mishi sai na koma kitchen din duba farfesun danyan kifin da na ɗaura, ji na shiru Tahir ya ce “Wai me kike yi ne? na ce “Ina duba girki ne”
Na shiryo musu na dauko maganar da na ji suna yi cikin rage murya ta sa ni tsayawa sai na sa kunne.
Wallahi kar ka ga magiyar da Latifa take min in kawo mata kai, har kudi ta bani na ce ta riƙe kudinta za ka same ta har inda take”.
Ai kam za ta daɗe bata gan ni ba abokina”.
Tahir ya ba shi amsa
Ya ce “A’a dai abokina,ƙarshe dai zaƙin amarci ke dibarka”
“Ba za ka gane ba kai kam”.
Tahir ya ce mishi.
Sallama nayi musu na ajiye musu farfesun, sai na ji sun sauya fira zuwa ta wurin aiki.
Miƙewa nayi Tahir ya ce “Ina za ki?
Na ce “Zan kwanta ne”.
Ya dubi agogo
“Kwanciya ko tara bata yi ba?
Shiru nayi
Ya dubi abokin nasa
“Yau tun tashin ta fushi take zan tafi gobe in bar ta”.
Ya ce “Kawai ka tafi da a bar ka”.
Kai ya girgiza “Idan na tafi da ita can su nawa ke jirana? ka san basma ma ta dawo kaduna, an maido ta aiki nan.
Nan kuwa ita kadai ce.
Dariyar shakiyanci abokin ya saki
“Kafin ka harbeta ko?
Jin furucinsa ban ko tsaya ce mishi sai da safe ba, na shige da sauri har ina tuntube”.
Tahir ya dube shi “Daga ka kore min amarya kai ma sai ka tashi, dan ka san ango baya doguwar fira”.
Dariya ya yi har yana buga kafa
“Allah sarki ni daɗin abun dai ni ma Allah yasa ina da matar nan, yau da na mutu da takaici.
In ka gama amarcin muna nan muna jiranka, duk da dai har na fara tunanin duk aurenka ban ga wadda ka ruɗe har kake min irin maganganun da kake yi yau, anya?
Tahir ya buɗe ido “Anya me? Sharrinka dai kai zai kashe.”
Tare suka fita abokin na dariya.

Na kwanta cikin jujjuya maganganun nasu, ban so zuciyata ta yarda da zargin da take na jin zantukansu, ina ta kokowa da zuciyar tawa ya shigo, gadon ya hayo sai da ya sanya ni jikinsa sannan yake bani labari
“Wannan ɗin da kike gani, abokina ne tun na kuruciya, sunansa Shehu, tanki yake tukawa a ma’aikatar mu”.

Da safe ma da muka tashi fuskata ba walwala, ina haɗa mishi abin karyawa sai rarrashina yake.
Ganin ina hawaye sai ya mike kayana ya soma haɗawa, da na ce mene ne ya ce tafiya za mu yi
Na yi saurin duban sa
“Tafiya kuma zuwa ina?
gira ya dage min “Kaduna”
Ido na zaro “Ba za ni ba”
Dole kuwa ki je, dan ba zan bar ki kina kuka ba”
Na share hawaye to kayi hakuri na daina”
Ya kamo ni muka zauna bakin gado maganganu masu daɗi yake gaya min har sai da ya ga na hakuran da gaske,
sai ya ce in raka shi wurin Hajiyarsa, na raka shi,suka yi sallama sai dai duk yadda ya so in mishi rakiya wurin motarsa kasawa nayi, dan duk mutanen gidan sun fito mishi bankwana.
Gadona kawai na haye da na koma daki,
wunin ranar ban fito ba, sai dai in tashi in yi sallah in koma in kwanta.
Ban tabbatar da shakuwar da nayi da shi me yawa ba ce dai da ya tafi ya bar ni.
Haka na koma kan al’amuran da nake yi, amma kewar Tahir na tare da ni duk da yawan wayar da muke yi.

Ranar da ya yi kwana uku da tafiya, ina dakin Haj ina yi mata goge goge, na daga received na ɗaga dan in goge kasanta, wasu hotuna suka bayyana, cikin mamaki na dauka ina dubawa, dan abin da na gani a cikin su, wata budurwa ce jikin hotunan me matukar kama da Tahir, dan dai kawai ita ɗin mace ce, duk a yan’uwansa ban ga wanda suka yi kama haka ba,
Su duk Haj suka biyo, shi kuma Tahir da mahaifinsa yake kama, dan akwai hoton mahaifinsa kafe a falon Haj.
Yarinyar yayansa da ke zaune a falon na nuna ma hoton “Salma wace ce a hotunan nan?
Ta taso daga inda take tana leka hotunan
“Anty Hadiza ce, ita ce autar su babanmu”.
A ina take? Na tambaye ta cikin mamaki dan ni dai ban taba jin wanda ya yi maganar ta ba.
“Tayi aure ba a daɗe ba, mijin dan Nijar ne ya tafi da ita can”.
Shiru nayi cikin kakkaɓi ina ƙara duban hotunan.

Da daddare na kai ma Haj fira, akwai jikokinta a dakin suna kallo, ni ba kallon nake ba wata yar wansa da ke fama da dan’uwanta ya koya mata sarfu an basu aiki bata iya ba, ganin har ta soma hawaye sai na yafito ta, ta iso gabana a hankali na shiga koya mata har ta gane, sai na nuna mata tayi aikin da aka basu a makarantar.
Tun daga ranar duk wanda bai gane aikin da aka yi musu ba sai ya zo wurina, iyayen ma samuna suka yi suna so in rika koya musu karatu na ce ba damuwa sai su zabi lokacin da suka ga ya dace mu riƙa yi daga su ne masu yawan aiki.

Da Tahir ya samu keɓewa zai kira ni, bai zo ba sai da ya samu kwanaki goma sha biyu da tafiya.
Ya ce min gashi nan zuwa, dan haka shiri sosai nayi na tarar sa,
ranar da zai zo tun da na tashi ban koma ba, sai da na gyara ko’ina kafin na shiga girki, Dambu nayi na shinkafa sanin shi ɗin me son cin nama ne kamar yanda Hajiyarsa take yasa na tanadi kazata, kai da kafa kawai aka cire mata dahuwar shinkafa cikin kaza nayi sai nayi mishi juice din abarba da kwakwa.
Da na kammala wanka nayi me kyau na gyara jikina sai da na ji na dauki ƙamshi ko ta ina cikin doguwar riga, ban je sasan Hajiya ba a ɗakina na yi zamana, isowar yara da ledoji ya bani tabbacin Ogan ya iso kenan, ya ɗan jima bai shigo ba na san yana wurin Haj.

Ƙamshin turarensa na fara shaƙa kafin na ga shigowarsa, jamfa da wando ne sanye a jikinsa na wata ɗanyar shadda, farin glass ɗinsa na rai da rai manne a idonsa mayatattun idanuwansa a kaina, sauke nawa idon nayi dan duk ya daburta ni, kawai sai na samu kaina da zubewa gabansa, ya ɗago ni sai ya manna ni a kirjinsa, bedroom muka wuce duk da tuna mishi da nake ya ci abinci tukuna.
Sai la’asar ya janye daga gare ni ya wuce masallaci.
Da ya dawo ne ya ci abinci sai kuma ya janyo ni wai in ba shi labarin kewar sa da nayi.

Kwanaki uku ya yi min wadanda suka yi matuƙar yi mana daɗi.
Ranar Monday da sassafe ya yi sammakon tafiya, ko da na tuna mishi mayar da ni Dutsinma daure fuska ya yi ya ce yana sane, tilas na haƙura.

 

Haka ya yi tayi ya zo Friday ya koma Monday, har na samu wata biyu, kafin cikar watanni biyun na samu ziyarar ƴan’uwana dukan su hada matan yayyena, Hafsa ma ta so biyo su lokacin kuma Ramlarta bata da lafiya, sai dai koyaushe tana ce min tana nan zuwa.
Wani zuwa da ya yi zai tafi na raka shi wurin Hajiya zai yi mata sallama yake ce mata “Sati me zuwa in Sha Allah zan tafi da ummulkhairi Kaduna”.
Hajiya tayi dan jim kafin ta ce “Ina sha ka bar min ita nan kenan?
Ya ce “Na dai bar ta ne ta ga dangina ta saba da su”.
Sai ga Haj tana matse ido yana bata hakuri.
“Saboda Allah ka san ba bar min ita za ka yi ba ka kawo min ita?
Sai da na shaku da ita, yarinya me hankali da kirki da ganin girman mutane, Allah kaɗai yasan ƙaruwar da mutanen gidan nan suka samu zuwanta.
Ka ga ga karatu tana koya musu su da yaransu, daidai da girki zuwanta matan nan sun gyara girkinsu, ga ta bata da rowa komai ka kawo mata sai ta cire ma kowa, ni nan abin da nake so shi za ta girka min, kullun sai ta dafa min nama, ta gyara min daki, ta kwance min kai tayi min kitso,zannuwana ta wanke min.
Sai ta shiga kuka sosai tana fyace hanci, ya ce “Ki yi haƙuri Haj, nayi wa Fati magana (ɗiyar wansa ce) duk safiya ta zo ta gyara miki ɗaki ta kuma rika yi miki kitso, wanki da gugar kayanki kuma Na matazu zai rika aikowa a karɓa, nama da kwai za a cigaba da kawowa umma ta rika dafa miki, tun da kin ce duk matan ta fi su tsafta da iya girki.
In kuma duk hakan bai yi miki ba to ki shirya mu tafi tare.
Nan kuma tayi tsalle ta ce “Allah ya tsare ta da komawa gidansa.
Ya ce “To cikin sauran matana ki zaɓi wadda kike so zan kawo miki ita”.
Nan ma ta ce ya rufa mata asiri bata son ko daya.
Ya ce ki fahimce ni Haj na ɗauko ummulkhairi da nufin kwana ɗaya za tayi, in mayar da ita, yan’uwanta sun je Kaduna sun yi mata jere.
Ita kanta kullun korafin da take min kenan,
sai iyayenta da ƴan’uwanta su ji ta shiru daga tafiyar kwana ɗaya,
ki yi haƙuri Haj ayi mata biki irin na al’ada in yaso bayan ta tare a Kaduna sai in dawo miki da ita.
Da alama dai Haj bata da niyyar fahimtar sa, lallashinta ya shiga yi ya ce ya bar ni.
Kudade ya ciro ya ajiye mata, sai muka fito sai da ya shiga motarsa ya leƙo da kansa “Kina ji na da Haj? auren nan kamar ita nayi mawa”.
Ni dai murmushi nayi.

Na cigaba da zama a ƙanƙara, a matan yayyensa mun fi shiri da matar yayansa wanda yake bi mawa yaya Abubakar, uwargidansa sunanmu daya da ita, amma ita Umma ake ce mata ni kuma ina kiranta maman ummi sunan yarta ta farko, ɗanta na biyu me suna Faisal ba shi da ƙyuya ko’ina zan aike shi dan haka ni kuma komai zan ci da rabonsa sanadin sa kauna ta wanzu tsakanina da ita.
Sai na lura a gidan matar babban yaya ta biyun wadda yaranta ke kira da Amma da sannu sunan ya bi bakin kowa, ita ke faɗa aji a gidan ko a wurin yaya babban ita ce mandiya.
Ɗakinta nan ne majalisa ta yan gidan, ni dai ban zuwa haka ma maman ummi, domin amaryar maman ummi usaina yar dakin Amma ce.
Amma mutumniyar maradun ce ta jihar Zamfara, tana sayar da magungunan mata wanda idan ta je garin su ta kan saro ta taho da shi.

Bayan tafiyar Tahir nayi wanki, shanya ita tafi kaini tsakar gidan, ina cikin shanya naji yarinyar Amma tana ce min “Aunty Innarmu tana kiranki”. na ce ina zuwa
sai na cigaba da shanyata, sai da na kammala sai na isa ƙofarta nayi mamakin rashin samun kowa a ɗakin, na shiga da sallama ta amsa tana min fara’a, na soma gaishe ta ta ce “Haba ummulkhairi sai ka ce wata baƙuwa zauna man”. na zauna ina kallon abubuwan da ta baza a gabanta.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *NA KUDI NE 300 KA BIYA A 2108124716*
*Maryam nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya*
*07033400612*

 

Wani yammaci ban yin komai sai na kai wa Mmn Ummi fira.
Cikin firar nake ce mata ban taɓa jin labarin Kawun nan me sunan Tahir ba, har sai da ya zo.
Ta ce “Kuma shi ya riki mijinki, an ce tun ƙare primary ɗinsa, ya ɗauke shi. Halima kuma matarsa ta farko, tun primary school suke tare, saboda yawan shakuwar su, ake ce musu mata da miji, tun nan yake sonta take sonsa.
Lokacin da suka gama secondary School, aka nemi ta fitar da miji ta ce ita fa bata son kowa sai Tahir.
Iyayenta suka kaɗa suka raya, amma ta dage, shi ne suka aiko gidan nan, nan ɗin kuma suka ce kwata kwata Tahir ɗin guda nawa yake? da har za a yi mishi aure, dan shekarun su ɗaya.
Makarantar aikin jinya ta samu, har ta kammala ta fara aiki, suka ƙara aikowa Halima fa na jiran Tahir, akwai makotaka da zaman tare dan haka yan’uwan Tahir suka zaunar da shi, da lallashinsa kan ya yi hakuri ayi auren nan.
Lokacin ko aiki bai samu ba yana dai zuwa kasuwa wurin harkokin marikinsa, wanda yake babban malami ne, har makarantu yake da su na islamiya a Kaduna da Lagos, ana yin auren Kawun ya buɗe mishi shago, na sayar da sarƙa da ƴan kunnaye.
Kasuwancin ya cigaba da yi, har ya samu aiki a mamatar man fetur da ke Kaduna.
Gidan Kawu Attahiru ya fara zama da ita, kafin ya saya mishi gida su koma”.
Jin tayi shiru na ce “Ta biyun fa? ya aka yi ya aureta?
Wani kallo ta min “Ni uwar surutu ko? to ki tambayi mijinki”.
Marairaicewa nayi “Dan Allah ki faɗa min, da zai gaya min da bai gaya min ba”
Ta ce “Ita ƙanwar abokinsa ce, a Abuja suke zaune, mahaifinta me arziki ne. Ya kai wa abokin nasa ziyara ta gan shi, shi kuma Tahir na yabawa da ita ya ce “Ƙanwarka kyakykyawa, ya ce “Na ba ka ita. Shi ya ɗauki maganar wasa sai ga shi yana dawowa yayan nata ya kira shi kan maganar, shi ne ya zo yana fadi wa yan’uwansa, ke har mahaifinta sai da ya kira shi kan batun daga ta tayar musu ita fa tana san sa gata yar gata wurin mahaifinta wanda su biyu kawai ya haifa ita da wanta, mahaifiyarta kuma Allah ya yi mata rasuwa.
Tahir dai ya amince aka sha biki, wanda aka sha daru da Halima, jin Basma na aiki ita ma ta ce sai ya nemo mata aikin, a asibitin kawo take aiki yanzu haka.
Basma a Abuja take zaune, sai dai ya je mata hutun karshen mako, to yanzu ma na ji an maida ta aiki kadunan, Basma tayi ta yin bari har waje mahaifinta ya fitar da ita, Halima ce dai ban tunanin ta taɓa ko batan wata ba”. shiru nayi ina nazarin labarin da ta babba ni, duk da na dan san wasu ban san wasu ba.
Aikowar da Haj tayi kirana ya katse mana firar, na tashi.

Washegari ina barci sai na ji saukar duka akan cinyata.
Na tashi a firgice tare da mamakin waye zai min wannan aikin, Hafsa na gani, take na wartsake cikin matukar mamakin ganin ta “Yar duniya daga tafiyar kwana ɗaya, sai muka ji ki shiru, kina nan har wasu mazaunai kika ajiye, ke miji daɗi”.
Harararta nayi “Shi ne hada dukana, ke da waye? Ina Ramla? ta ce “Ni da ƴan kai amarya”.
na ce “Amarya kuma? wace Amaryar? ƴar dariya tayi “Ke amaryar mana, mun biyo ki ne”. na fiddo ido “Haba? dan Allah da gaske? ta ce “”Kar ki raina min hankali Malama”. na kwantar da kai, “Ki yarda wallahi ba ni da masaniyar komai”.
nan ta bani labari Ai Tahir ne ya tura ya ce a dauko masu raka ni a kaini Kaduna
na jinjina lamarin dan bai faɗa min ba.
Na ce “Ina sauran?
ta ce “Su na sasan Haj, ni kaɗai na zaro jiki na tambayi inda kike”.
Hure mata ido nayi “Wai sai kallona kike meye? ta ce “Na ga amaryar ne har an cika mata aiki, ana a’a a’a ga shi nan soyayya tayi daɗi jikin ma ya nuna kina karɓar sakon yan….
toshe mata baki nayi na faɗi “Na shiga uku, kin bani kina matar malam kina maganganun banza”. ta ce “Ko ba maganganun banza ba”.
na ce “Sharrinki dai ke zai kashe”.
ta cigaba da min tsiya, ni kuma ina ta ware ido in ga ta inda waɗanda suka zo tare za su ɓullo.
Matar Yayansa Rabi ta yo musu jagora, Yayyena mata su biyu, sai ƙanwata Hauwa’u, sai ƙanwar Ummata, Inna magajiya, sai Gwoggo.
Rufe fuskata nayi, da kyar na samu na gaishe su. Da na nemi Hafsa da Hauwa’u su zo mu shiga kitchen in musu girki, Hafsa ce min tayi “Ai da alama ke ce kaɗai ba ki san da zuwan mu ba, amma am mana abinci da abin sha waɗanda suka gwada an san da zuwan mu.
Tare muka kwana da ƴan’uwana da Hafsa, su Gwoggo suka kwana wurin Haj.
Sai da aka karya kumallo da safe, aka yi wanka kowa ya kintsa.
Nayi sallama da mutanen gidan, da Haj wadda ke ta matse ido.
Amma da Usaina dai har yau ba wadda ta dawo duk yanda aka kai ga roƙon mazan nasu, ba a sha kansu ba, sun ce sai sun gane muhimmancin mahaifiyarsu ko da za su dawo.
Hada Uwargidan Yaya Babba muka tafi da ta yaya Magaji.
Ni da Hauwa’u da Hafsa wuri guda muka zauna, bayan motar da Tahir ya turo yaya Babba ma sai da ya dauko wata.
Ƙarfe biyu na rana muka shiga garin Kaduna.
A unguwar NDC nan gidan Tahir Sodangi yake, muna ta wuce tamfatsa tamfatsan gine ginen da suka mamaye unguwar.Mai motar farko ya yi horn gaban wani tangamemen get, ba ɓata lokaci aka hangame get din, motar ta sulala ciki, me bi mata ta mara mata baya.
Harabar gidan yana da matuƙar girma, ga shuke shuke da suka ƙara ƙayata shi. Kowa ya fito muka nufi ainihin inda ginin gidan yake, wani katafaren falo muka shiga, inda wasu mata su uku suka tare mu, sai da muka yi sallah suka gabatar mana da abinci sai sannan na gane gidan Kawu Attahiru ne.
Matan biyu matansa ne, ɗayar kuma da ta fi su kuruciya Uwargidansa ce ta riƙe ta.
Kafin dare an yi matukar sabo da amaryarsa me suna Aunty Kulu, a lurar da nayi ita ɗin shuwa ce, dan kamanninta, da kuma yanayin shigar ta. Ko su Uwargidan Yaya Babba Maman saddiƙa, ba su santa ba, wai auren kwata kwata shekararsa uku, kuma wannan shi ne karo na farko da ta fara zuwa Arewa, a Lagos ya ajiye ta, sai dai ba yarinya ba ce za ta yi shekaru talatin da bakwai. Uwargidan shiru shiru take, sam bata magana.
Su ukun suka je suka gyara min daki. Sai dare bayan Kawun ya dawo an gaggaisa, Aunty Kulu da Uwargidanta, su ka ce za su mika ni ɗakina.
Hauwa’u da Hafsa ma suka ce za su sai ƙanwar Innata Inna magajiya. Tsakanin su ba nisa, shi ma tafkeken Gate ne, ginin gidan upstairs ne hawa ɗaya, akwai wadataccen fili wanda ya sha adon furanni, sai rumfar adana motoci, akwai bukka ta shan iska irin ta turawa.
Inna magajiya ta ruko ni a kunnena take raɗa min, “Ki yi ta jan duk wata addu’a da kika sani har mu shiga ciki.”
Ban ki ta tata ba addu’o’in nayi tayi, wata kofa suka tura muka shiga ta sadamu da main falo na gidan, wawakeken falo ne wanda aka yi matuƙar kayatawa da kayan more rayuwa.
Ba kowa ciki sai sanyin AC da ke ratsa duk wanda ya shigo, mun ratsa tattausan kilishin da ke barazanar shanye ƙafafuwan wanda duk ya taka.
Kofofi huɗu muka gani, biyu suna kallon juna, biyun ma suna kallon juna, Aunty Kulu ta sa key ta buɗe wata da ke kallon yamma, muka shiga falon nawa, ya yi kyau ƙwarai, an shirya shi da kujeru da labulaye, sai kayan Electronics wanda ko ɗar ban yi ba, na san Tahir ne ya sanya min, muka wuce ciki inda tankamemen gadona yake, me haɗe da mirror da wardrobe an shirya akwatuna sai ƙaramin fridge wanda na san shi ma Tahir ne ya sanya min.
Gadon na haye na yaye rufar da nayi dan in sha iska, wayar Aunty Kulu ta shiga ƙara, ta fita falo dan amsawa sai da ta ƙare sai ga ta ta shigo,
suka mimmike dan komawa gidan Kawu Attahiru Aunty Kulu ta ce “Hauwa’u da Hafsa su zauna su taya ni kwana.
Sun tafi suka bar mu, Hauwa’u ta shiga toilet Hafsa ta miƙe tana leka window, ta juyo ta yafito ni, sai na isa kusa da ita, kallonta nayi sai na dubi inda take nuna min, Tahir na gani zaune a rumfar shan iska da ke a harabar gidan, dan harabar tar take da haske kamar rana.
Sanye yake cikin kananan kaya, wadanda suka yi matuƙar amsarsa, farin Glass ɗinsa manne a idonsa. Farin teburin da ke gabansa wani glass cup ne yana shan abin da ke ciki, suna fuskantar juna shi da wani.
Zura mishi ido nayi, dan ba kaɗan ya yi min kyau ba, wata kaunarsa na ji tana ƙara fizgata, shagala nayi na lula cikin tunanin lokutan da suka shuɗe abubuwan da suka gudana a tsakanin mu.
Girgiza min kafaɗa da Hafsa take yasa na waiwayo cikin wani yanayi na ce “Meye? Wani kallo ta min soyayya manya yarinya”.
na galla mata harara Me nayi? tayi ƴar dariya ba ki yi komai ba.
Cikin sanyin jiki na koma bakin gado, ina cigaba da tunanin da ya ƙara daure min kai tun shigowar mu gidan, wai wannan tamfatsetsen gidan na Tahir ne, dan ba kaɗan ya ruɗa ni ba. Hauwa’u ta fito, ta zauna muka ji ana magana daga falo Hauwa’un ta tashi ta leƙa, Tahir ne ya aiko mana da gasassun kaji da kayan tande tande, ci muka yi muna fira har muka kwanta.

Da safe da baƙin rai na tashi. Wanda suka danganta shi da tafiyar da za su yi su bar ni, ni kuma abin da ya ɓata min rai tun zuwana Tahir bai neme ni ba, sai txt kadai da ya yo mini yana min ya hanya.
Dan ko da ya shigo gidan Kawu Attahiru na dai ji muryarsa yana gaishe su, amma ban gan shi ba.
Sai hantsi ƴan rakiyata suka baro gidan Kawu suka iso wurina, ina jin su sai shawara suke a kai ni wurin kishiyoyina wasu su na cewa a ƙyale ni, dan daga cikin su ba wacce aka ga idonta.
Ni dai ina riƙe da kofin kunun gyaɗa wanda aka kawo mana daga gidan Kawu Attahiru ina kurɓa a hankali, sallama muka ji wadda bata ko sa na ɗaga kaina ba, cikin girmamawa ya gaishe su, ya kuma yi musu sallama ta ban girma.
Sai da na ga sun zauna a mota kafin na fara share ido. Ina tsaye har motocinsu suka fice harabar gidan, na koma ciki na zauna gefen gado nayi zuru.

Na idar da sallar azahar, ina tsaye gaban mirror ina dan ƙara gyara fuskata,
na soma shaƙar ƙamshin turaren Tahir, waiwayawa nayi shi ɗin ne, yau ma cikin shigar kananun kaya yake, hannuwansa zube cikin aljihunsa yana kallona kwarjininsa yasa na kasa cigaba da kallonsa sai na sunkuyar da kaina, ya tako zuwa inda nake “Ranki ya daɗe Amarya”.
ya fadi yana zama bakin gadon, hannunsa ya miƙo ya kamo ni ya zaunar da ni kan cinyarsa, ya zagaya hannuwansa kan cikina, sai ya rungume ni ya dora kansa bisa wuyana, wai kuma sai ya ke ce min “Ko tausayi ma abin, kin danne ni da wadannan manyan abubuwan naki” ya ƙarasa fadi yana duka bombom ɗina, mutsu mutsu na kama yi zan sauka ya matse ni maganganun da yake gaya min suka sa ni rufe ido.
Jin na ƙi magana yasa ya ce “To tashi mu je ki ci abinci, akwai baƙi kuma da na kawo miki”.
Saurin miƙewa nayi ” “Baƙi? kuma ka bar su zaune”. cikin hanzari na fita zuwa falon, yara ne mata su biyu, wanda kamanninsu suka gwada alamar su ɗin yan biyu ne, Shekarun su ba za su haura shida ba. Na kamo su na zauna tsakiyar su ina tambayar su sunayen su, kamar yanda na za ta suka ce Hassana da Hussaina. Muka haɗa ido da Tahir ya ɗora ƙafa daya kan daya, murmushi nayi “Ƴan biyun waye masu ban sha’awa?
Mahaifinsu babban yaron Babana ne ( Kawu Attahiru) Baban shi ya yi mishi aure, cikin gidansa suka zauna da matarsa bata samu haihuwa da wuri ba sai kan yaran nan, tana kuma haihuwar su, Allah ya karɓi ranta. Ni kuma mahaifiyar tasu farkon kawo ni garin nan ita ke min komai.
Marairaice fuska nayi cikin nuna jimami, kamar yanda na ga shi ma ya shiga jimamin, nayi mata addu’ar samun Rahma.
Ya ce Dawo nan ki ci abinci” Flate na tashi na dauko na dawo na zauna, na juye abincin na janyo yaran mu ci, suka ce sun koshi.
Sai na basu ice cream din da na gani a wata ledar daban suna ta tsotsa, ni kuma ina cin abincina, Tahir na caccanza channel da remote control din da ke hannunsa.
Sai da na kammala ya ce min zai fita.
Ganin kan yaran a tsefe, ga su kuma masu gashi ne yasa na ce “Wa ke so in mishi kitso”.
Kowacce ta ce ita, na zauna na yarfa musu kitso me kyau.
Sai yamma likis, wata da nake zaton me aiki ce ta shigo sai da ta gaishe ni kafin ta ce “Alh ya ce su Hassana su zo”
Ban so ba, ta fita da yaran dan samun su a tare da ni ya ɗebe min kewar kadaicin da nake ciki.
Wanka kawai na shige, da na fito na ɗaura alwala, zane na daura da dogon hijab na kabbara Sallar isha’i, sai da na idar, sannan nayi kwalliya, akwatunana na sauke ina shi ma Hafsa albarka a raina, dan kafin a taho da kayana ta je ta dauki wasu daga cikin kayan akwatina ta dinko min, Atamfa na ɗauko wadda ta sha dinkin da ya zauna min, na koma gaban mirror ina yaba kyan kitson da Hafsa ta yarfa min da safe.
Two step ne kanana ban daura dankwali ba, turare na fesa sai na dawo falo na kishingida rashin sanin abin yi, ban wani daɗe ba aka buga ƙofar sai aka shigo, Basma ce, mun kalli juna ni da ita, kafin na miƙa mata gaisuwa da fara’a kan fuskata, ga mamakina ita tata fuskar ba walwala. “Sweety na kiranki” abin da ta ce min kenan sai ta juya, na yunkura na shiga ciki hijab na ɗauko na sanya kafin na fito sai sake sake nake a raina, ita kuma wannan me ya canza ta? wani barayi na zuciyata ya bani amsa da kishi mana, ke kishi wasa ne.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *NA KUDI NE 300 KA BIYA A 2108124716*
*Maryam nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya*
*07033400612*

 

Wani yammaci ban yin komai sai na kai wa Mmn Ummi fira.
Cikin firar nake ce mata ban taɓa jin labarin Kawun nan me sunan Tahir ba, har sai da ya zo.
Ta ce “Kuma shi ya riki mijinki, an ce tun ƙare primary ɗinsa, ya ɗauke shi. Halima kuma matarsa ta farko, tun primary school suke tare, saboda yawan shakuwar su, ake ce musu mata da miji, tun nan yake sonta take sonsa.
Lokacin da suka gama secondary School, aka nemi ta fitar da miji ta ce ita fa bata son kowa sai Tahir.
Iyayenta suka kaɗa suka raya, amma ta dage, shi ne suka aiko gidan nan, nan ɗin kuma suka ce kwata kwata Tahir ɗin guda nawa yake? da har za a yi mishi aure, dan shekarun su ɗaya.
Makarantar aikin jinya ta samu, har ta kammala ta fara aiki, suka ƙara aikowa Halima fa na jiran Tahir, akwai makotaka da zaman tare dan haka yan’uwan Tahir suka zaunar da shi, da lallashinsa kan ya yi hakuri ayi auren nan.
Lokacin ko aiki bai samu ba yana dai zuwa kasuwa wurin harkokin marikinsa, wanda yake babban malami ne, har makarantu yake da su na islamiya a Kaduna da Lagos, ana yin auren Kawun ya buɗe mishi shago, na sayar da sarƙa da ƴan kunnaye.
Kasuwancin ya cigaba da yi, har ya samu aiki a mamatar man fetur da ke Kaduna.
Gidan Kawu Attahiru ya fara zama da ita, kafin ya saya mishi gida su koma”.
Jin tayi shiru na ce “Ta biyun fa? ya aka yi ya aureta?
Wani kallo ta min “Ni uwar surutu ko? to ki tambayi mijinki”.
Marairaicewa nayi “Dan Allah ki faɗa min, da zai gaya min da bai gaya min ba”
Ta ce “Ita ƙanwar abokinsa ce, a Abuja suke zaune, mahaifinta me arziki ne. Ya kai wa abokin nasa ziyara ta gan shi, shi kuma Tahir na yabawa da ita ya ce “Ƙanwarka kyakykyawa, ya ce “Na ba ka ita. Shi ya ɗauki maganar wasa sai ga shi yana dawowa yayan nata ya kira shi kan maganar, shi ne ya zo yana fadi wa yan’uwansa, ke har mahaifinta sai da ya kira shi kan batun daga ta tayar musu ita fa tana san sa gata yar gata wurin mahaifinta wanda su biyu kawai ya haifa ita da wanta, mahaifiyarta kuma Allah ya yi mata rasuwa.
Tahir dai ya amince aka sha biki, wanda aka sha daru da Halima, jin Basma na aiki ita ma ta ce sai ya nemo mata aikin, a asibitin kawo take aiki yanzu haka.
Basma a Abuja take zaune, sai dai ya je mata hutun karshen mako, to yanzu ma na ji an maida ta aiki kadunan, Basma tayi ta yin bari har waje mahaifinta ya fitar da ita, Halima ce dai ban tunanin ta taɓa ko batan wata ba”. shiru nayi ina nazarin labarin da ta babba ni, duk da na dan san wasu ban san wasu ba.
Aikowar da Haj tayi kirana ya katse mana firar, na tashi.

Washegari ina barci sai na ji saukar duka akan cinyata.
Na tashi a firgice tare da mamakin waye zai min wannan aikin, Hafsa na gani, take na wartsake cikin matukar mamakin ganin ta “Yar duniya daga tafiyar kwana ɗaya, sai muka ji ki shiru, kina nan har wasu mazaunai kika ajiye, ke miji daɗi”.
Harararta nayi “Shi ne hada dukana, ke da waye? Ina Ramla? ta ce “Ni da ƴan kai amarya”.
na ce “Amarya kuma? wace Amaryar? ƴar dariya tayi “Ke amaryar mana, mun biyo ki ne”. na fiddo ido “Haba? dan Allah da gaske? ta ce “”Kar ki raina min hankali Malama”. na kwantar da kai, “Ki yarda wallahi ba ni da masaniyar komai”.
nan ta bani labari Ai Tahir ne ya tura ya ce a dauko masu raka ni a kaini Kaduna
na jinjina lamarin dan bai faɗa min ba.
Na ce “Ina sauran?
ta ce “Su na sasan Haj, ni kaɗai na zaro jiki na tambayi inda kike”.
Hure mata ido nayi “Wai sai kallona kike meye? ta ce “Na ga amaryar ne har an cika mata aiki, ana a’a a’a ga shi nan soyayya tayi daɗi jikin ma ya nuna kina karɓar sakon yan….
toshe mata baki nayi na faɗi “Na shiga uku, kin bani kina matar malam kina maganganun banza”. ta ce “Ko ba maganganun banza ba”.
na ce “Sharrinki dai ke zai kashe”.
ta cigaba da min tsiya, ni kuma ina ta ware ido in ga ta inda waɗanda suka zo tare za su ɓullo.
Matar Yayansa Rabi ta yo musu jagora, Yayyena mata su biyu, sai ƙanwata Hauwa’u, sai ƙanwar Ummata, Inna magajiya, sai Gwoggo.
Rufe fuskata nayi, da kyar na samu na gaishe su. Da na nemi Hafsa da Hauwa’u su zo mu shiga kitchen in musu girki, Hafsa ce min tayi “Ai da alama ke ce kaɗai ba ki san da zuwan mu ba, amma am mana abinci da abin sha waɗanda suka gwada an san da zuwan mu.
Tare muka kwana da ƴan’uwana da Hafsa, su Gwoggo suka kwana wurin Haj.
Sai da aka karya kumallo da safe, aka yi wanka kowa ya kintsa.
Nayi sallama da mutanen gidan, da Haj wadda ke ta matse ido.
Amma da Usaina dai har yau ba wadda ta dawo duk yanda aka kai ga roƙon mazan nasu, ba a sha kansu ba, sun ce sai sun gane muhimmancin mahaifiyarsu ko da za su dawo.
Hada Uwargidan Yaya Babba muka tafi da ta yaya Magaji.
Ni da Hauwa’u da Hafsa wuri guda muka zauna, bayan motar da Tahir ya turo yaya Babba ma sai da ya dauko wata.
Ƙarfe biyu na rana muka shiga garin Kaduna.
A unguwar NDC nan gidan Tahir Sodangi yake, muna ta wuce tamfatsa tamfatsan gine ginen da suka mamaye unguwar.Mai motar farko ya yi horn gaban wani tangamemen get, ba ɓata lokaci aka hangame get din, motar ta sulala ciki, me bi mata ta mara mata baya.
Harabar gidan yana da matuƙar girma, ga shuke shuke da suka ƙara ƙayata shi. Kowa ya fito muka nufi ainihin inda ginin gidan yake, wani katafaren falo muka shiga, inda wasu mata su uku suka tare mu, sai da muka yi sallah suka gabatar mana da abinci sai sannan na gane gidan Kawu Attahiru ne.
Matan biyu matansa ne, ɗayar kuma da ta fi su kuruciya Uwargidansa ce ta riƙe ta.
Kafin dare an yi matukar sabo da amaryarsa me suna Aunty Kulu, a lurar da nayi ita ɗin shuwa ce, dan kamanninta, da kuma yanayin shigar ta. Ko su Uwargidan Yaya Babba Maman saddiƙa, ba su santa ba, wai auren kwata kwata shekararsa uku, kuma wannan shi ne karo na farko da ta fara zuwa Arewa, a Lagos ya ajiye ta, sai dai ba yarinya ba ce za ta yi shekaru talatin da bakwai. Uwargidan shiru shiru take, sam bata magana.
Su ukun suka je suka gyara min daki. Sai dare bayan Kawun ya dawo an gaggaisa, Aunty Kulu da Uwargidanta, su ka ce za su mika ni ɗakina.
Hauwa’u da Hafsa ma suka ce za su sai ƙanwar Innata Inna magajiya. Tsakanin su ba nisa, shi ma tafkeken Gate ne, ginin gidan upstairs ne hawa ɗaya, akwai wadataccen fili wanda ya sha adon furanni, sai rumfar adana motoci, akwai bukka ta shan iska irin ta turawa.
Inna magajiya ta ruko ni a kunnena take raɗa min, “Ki yi ta jan duk wata addu’a da kika sani har mu shiga ciki.”
Ban ki ta tata ba addu’o’in nayi tayi, wata kofa suka tura muka shiga ta sadamu da main falo na gidan, wawakeken falo ne wanda aka yi matuƙar kayatawa da kayan more rayuwa.
Ba kowa ciki sai sanyin AC da ke ratsa duk wanda ya shigo, mun ratsa tattausan kilishin da ke barazanar shanye ƙafafuwan wanda duk ya taka.
Kofofi huɗu muka gani, biyu suna kallon juna, biyun ma suna kallon juna, Aunty Kulu ta sa key ta buɗe wata da ke kallon yamma, muka shiga falon nawa, ya yi kyau ƙwarai, an shirya shi da kujeru da labulaye, sai kayan Electronics wanda ko ɗar ban yi ba, na san Tahir ne ya sanya min, muka wuce ciki inda tankamemen gadona yake, me haɗe da mirror da wardrobe an shirya akwatuna sai ƙaramin fridge wanda na san shi ma Tahir ne ya sanya min.
Gadon na haye na yaye rufar da nayi dan in sha iska, wayar Aunty Kulu ta shiga ƙara, ta fita falo dan amsawa sai da ta ƙare sai ga ta ta shigo,
suka mimmike dan komawa gidan Kawu Attahiru Aunty Kulu ta ce “Hauwa’u da Hafsa su zauna su taya ni kwana.
Sun tafi suka bar mu, Hauwa’u ta shiga toilet Hafsa ta miƙe tana leka window, ta juyo ta yafito ni, sai na isa kusa da ita, kallonta nayi sai na dubi inda take nuna min, Tahir na gani zaune a rumfar shan iska da ke a harabar gidan, dan harabar tar take da haske kamar rana.
Sanye yake cikin kananan kaya, wadanda suka yi matuƙar amsarsa, farin Glass ɗinsa manne a idonsa. Farin teburin da ke gabansa wani glass cup ne yana shan abin da ke ciki, suna fuskantar juna shi da wani.
Zura mishi ido nayi, dan ba kaɗan ya yi min kyau ba, wata kaunarsa na ji tana ƙara fizgata, shagala nayi na lula cikin tunanin lokutan da suka shuɗe abubuwan da suka gudana a tsakanin mu.
Girgiza min kafaɗa da Hafsa take yasa na waiwayo cikin wani yanayi na ce “Meye? Wani kallo ta min soyayya manya yarinya”.
na galla mata harara Me nayi? tayi ƴar dariya ba ki yi komai ba.
Cikin sanyin jiki na koma bakin gado, ina cigaba da tunanin da ya ƙara daure min kai tun shigowar mu gidan, wai wannan tamfatsetsen gidan na Tahir ne, dan ba kaɗan ya ruɗa ni ba. Hauwa’u ta fito, ta zauna muka ji ana magana daga falo Hauwa’un ta tashi ta leƙa, Tahir ne ya aiko mana da gasassun kaji da kayan tande tande, ci muka yi muna fira har muka kwanta.

Da safe da baƙin rai na tashi. Wanda suka danganta shi da tafiyar da za su yi su bar ni, ni kuma abin da ya ɓata min rai tun zuwana Tahir bai neme ni ba, sai txt kadai da ya yo mini yana min ya hanya.
Dan ko da ya shigo gidan Kawu Attahiru na dai ji muryarsa yana gaishe su, amma ban gan shi ba.
Sai hantsi ƴan rakiyata suka baro gidan Kawu suka iso wurina, ina jin su sai shawara suke a kai ni wurin kishiyoyina wasu su na cewa a ƙyale ni, dan daga cikin su ba wacce aka ga idonta.
Ni dai ina riƙe da kofin kunun gyaɗa wanda aka kawo mana daga gidan Kawu Attahiru ina kurɓa a hankali, sallama muka ji wadda bata ko sa na ɗaga kaina ba, cikin girmamawa ya gaishe su, ya kuma yi musu sallama ta ban girma.
Sai da na ga sun zauna a mota kafin na fara share ido. Ina tsaye har motocinsu suka fice harabar gidan, na koma ciki na zauna gefen gado nayi zuru.

Na idar da sallar azahar, ina tsaye gaban mirror ina dan ƙara gyara fuskata,
na soma shaƙar ƙamshin turaren Tahir, waiwayawa nayi shi ɗin ne, yau ma cikin shigar kananun kaya yake, hannuwansa zube cikin aljihunsa yana kallona kwarjininsa yasa na kasa cigaba da kallonsa sai na sunkuyar da kaina, ya tako zuwa inda nake “Ranki ya daɗe Amarya”.
ya fadi yana zama bakin gadon, hannunsa ya miƙo ya kamo ni ya zaunar da ni kan cinyarsa, ya zagaya hannuwansa kan cikina, sai ya rungume ni ya dora kansa bisa wuyana, wai kuma sai ya ke ce min “Ko tausayi ma abin, kin danne ni da wadannan manyan abubuwan naki” ya ƙarasa fadi yana duka bombom ɗina, mutsu mutsu na kama yi zan sauka ya matse ni maganganun da yake gaya min suka sa ni rufe ido.
Jin na ƙi magana yasa ya ce “To tashi mu je ki ci abinci, akwai baƙi kuma da na kawo miki”.
Saurin miƙewa nayi ” “Baƙi? kuma ka bar su zaune”. cikin hanzari na fita zuwa falon, yara ne mata su biyu, wanda kamanninsu suka gwada alamar su ɗin yan biyu ne, Shekarun su ba za su haura shida ba. Na kamo su na zauna tsakiyar su ina tambayar su sunayen su, kamar yanda na za ta suka ce Hassana da Hussaina. Muka haɗa ido da Tahir ya ɗora ƙafa daya kan daya, murmushi nayi “Ƴan biyun waye masu ban sha’awa?
Mahaifinsu babban yaron Babana ne ( Kawu Attahiru) Baban shi ya yi mishi aure, cikin gidansa suka zauna da matarsa bata samu haihuwa da wuri ba sai kan yaran nan, tana kuma haihuwar su, Allah ya karɓi ranta. Ni kuma mahaifiyar tasu farkon kawo ni garin nan ita ke min komai.
Marairaice fuska nayi cikin nuna jimami, kamar yanda na ga shi ma ya shiga jimamin, nayi mata addu’ar samun Rahma.
Ya ce Dawo nan ki ci abinci” Flate na tashi na dauko na dawo na zauna, na juye abincin na janyo yaran mu ci, suka ce sun koshi.
Sai na basu ice cream din da na gani a wata ledar daban suna ta tsotsa, ni kuma ina cin abincina, Tahir na caccanza channel da remote control din da ke hannunsa.
Sai da na kammala ya ce min zai fita.
Ganin kan yaran a tsefe, ga su kuma masu gashi ne yasa na ce “Wa ke so in mishi kitso”.
Kowacce ta ce ita, na zauna na yarfa musu kitso me kyau.
Sai yamma likis, wata da nake zaton me aiki ce ta shigo sai da ta gaishe ni kafin ta ce “Alh ya ce su Hassana su zo”
Ban so ba, ta fita da yaran dan samun su a tare da ni ya ɗebe min kewar kadaicin da nake ciki.
Wanka kawai na shige, da na fito na ɗaura alwala, zane na daura da dogon hijab na kabbara Sallar isha’i, sai da na idar, sannan nayi kwalliya, akwatunana na sauke ina shi ma Hafsa albarka a raina, dan kafin a taho da kayana ta je ta dauki wasu daga cikin kayan akwatina ta dinko min, Atamfa na ɗauko wadda ta sha dinkin da ya zauna min, na koma gaban mirror ina yaba kyan kitson da Hafsa ta yarfa min da safe.
Two step ne kanana ban daura dankwali ba, turare na fesa sai na dawo falo na kishingida rashin sanin abin yi, ban wani daɗe ba aka buga ƙofar sai aka shigo, Basma ce, mun kalli juna ni da ita, kafin na miƙa mata gaisuwa da fara’a kan fuskata, ga mamakina ita tata fuskar ba walwala. “Sweety na kiranki” abin da ta ce min kenan sai ta juya, na yunkura na shiga ciki hijab na ɗauko na sanya kafin na fito sai sake sake nake a raina, ita kuma wannan me ya canza ta? wani barayi na zuciyata ya bani amsa da kishi mana, ke kishi wasa ne.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *NA KUDI NE 300 KA BIYA A 2108124716*
*Maryam nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya*
*07033400612*

Su uku na samu a cikin falon zaune kan ledar cin abinci.
Na zauna na gaida Uwargidan, wadda yanayin ta ke gwada a sama take, ban wani saki jiki ba, sama sama na dan taba abincin kadan dan ban saba da su ba.
Da aka kammala tsakiyar falon aka koma, me aikin ta zo ta kwashe komai. Sai mamakin shigar da Basma tayi nake a raina, riga da wando ne jikinta rigar me bayyana surar jiki ce, kuma bata sa komai a ƙasa ba, ga na shanunta nan zahiri waɗanda suke a tsaitsaye kuma manya.
A kasan raina kuma wani kishi ke cin raina, na ganin yanda take ta gilmawa gaban Tahir.
A fakaice na dubi Uwargida Halima gogaggiyar mace ce, ga hutu da ya ratsa ta, fara ce sosai gajera, ƙatuwar gaske. Yan biyu suna barci akan kujera. Gyaran murya megidan ya yi kafin ya yi godiya ga Allah, sai ya gabatar da ni a wurin matan nasa tare da nasihar mu zauna lafiya ni ma ya gabatar min da su.
Da ya gama bayanan sa ya ce in akwai me magana tayi, kowacce ta girgiza kai, ya ce “To ya batun rabon kwana daga ga amarya ta zo”.
Uwargida Halima ta kara ɓata rai, Ai Amarya ba yau ne za ta tare da kai ba, dan haka za ta jira har sai girki ya zagayo kanta”.
Basma ta ce “Haka ne”
A ranar Uwargidan ce da girki. Basma ya umurta ta nuna min General kitchen na gidan, ta nuna min wanda yake me girma ne kwarai, akwai Electrics kala daban daban da tukwane, kayan girki nau’i iri iri, ta kuma nuna min store.
Da muka fito ya ce in kwashe ƴan biyu su taya ni kwana, Husainar na fara dauka na kusa shigewa na tsinkayi muryar daya daga cikin su tana cewa “Ba ka ce gida za ka mayar da su ba? ban ji me ya ce ba na shige, na dawo ɗaukar Hassana na gan shi tsaye da alama fita zai dan har da key a hannunsa, na dauke ta na wuce, a gado na kwantar da su na cire hijab din jikina na matsa gaban dressing mirror ina ƙare wa kaina kallo, ina kuma tuna matan nasa da na gani, ina da kyauna daidai gwargwado dan ban da muni musamman idan nayi kwalliya ina matukar yin kyau, ba abin da na rasa na surar ya’ya mata, diri me kyau Ubangiji ya yi min, fatata tana da haske ba dai sosai ba.
Ban san iya lokacin da na ɗauka cikin tunani ba sai shigowar Tahir na ji, na ta da kai muka haɗa ido,
“Har yanzu ba ki kwanta ba? ya tambaye ni, na daga mishi kai, ledoji biyu ya miƙo min na karba tare da godiya.
Ki yi kokari ki kwanta, dare ya soma yi”
Ya faɗa yana juyawa na bi bayansa da kallo har ya kai ƙofa sai ya rufo min.
Ajiyar zuciya na fidda sai na buɗe ledojin, ta farko gasassar kaza ce, ta biyun kuma da ta fi girma tarkacen kayan shayi ne, da abubuwan amfanin yau da kullum. na ajiye komai inda ya dace sai na dan ci kazar sama sama na adana sauran, sai nayi shirin barci, wasu riga da wando na ɗauko na saka, rigar kamar best take, ta kama ni tsam ko cibi bata kawo ba, wandon ma me kama jiki ne, tsawonsa iya gwiwa, rigar fara ce wandon blue.
Na hau gado tsakiyar ƴan biyu na kwanta, na yi addu’o’ina na shafa musu ni ma na shafa. Na dade cikin tunani kafin gwanin iya sata ya yi nasarar sace ni.

Asubar farko na farka. Bathroom na wuce na dauro alwala, na fito na tada sallah, na idar ina Azkar wayata ta shiga ƙara, na miƙa hannu na ɗauko ta, sunan Haj ke yawo saman screen ɗin, nayi sallama murmushi kwance saman fuskata, tare da gaishe ta, ta amsa tana tambayata ba dai matsala ko, na ce lafiya lau, bayan tambayarta mutanen gidan sai muka yi sallama.
Ummata na kira sai dai ita faɗa ta rufe ni da shi wane irin kira ne da sassafe? na faɗar mata da gaba. Na ce “Kai Umma amma ita Hajiyar su Tahir yanzu ta kira ni”
Muka taɓa yar fira sai muka yi sallama.
Ganin yaran sun tashi zaune kan gado, yasa ni miƙa musu hannu suka sauko na wuce bathroom da su na wanko musu baki nayi musu wanka, sai da na gama yi musu kwalliya sai na rasa kayan da zan canza musu. Kettle na ciro na jona ruwa ya yi zafi na haɗa musu tea, suka sha suka haɗa da kazata ta daren jiya, ba su kammala ba aka kwankwasa kofa, daga ni sai kayan barcin daren jiya, zane na daura sai na buɗe, me aikin jiya ce, cikin mutuntawa ta gaishe ni ta ce “Me kai yan biyu makaranta ne, ya kawo kayansu, na karba na koma ciki na sanya musu uniform din, ta kama hannunsu sai suka fice.
Kamar in yi wanka sai na ga bari dai in gyara kumbata, zanen da na ɗora saman kayan na cire na zauna ina gyaran kumban, murɗa ƙofar da aka yi yasa ni daga kai Tahir ne cikin shiri yake na wani lallausan yadi, kamshinsa tuni ya karaɗe wurin, kallo yake ƙare min, ya ce “Kin karya? na ce “A’a” ya ce “Why? na ce “Wanka nake so in fara yi” “Ki tabbatar kin fita kin nemi abin da za ki ci, saboda fita wurin aiki, ba sa samun damar tsayawa yin abin karyawa, sai dai wadda ke da aiki tana bani abincin rana ni da ita. Da daddare ne ake yi gaba ɗaya. Kai na daga mishi, “Ni zan fita wurin aiki” nayi masa addu’a.
Ta window na koma ina lekensa, har sai da motarsa ta fice gidan.

Wanka nayi, nayi kwalliya da wata doguwar riga fara, sai gaban da aka yi ma ado da yarfin baƙi da brown, gyale me laushi kalar brown na ɗaura a kaina.
Tea na haɗa na sha ban fita ba kamar yanda ya ce, na gyara gadona zuwa yan goge goge da shara, da na gama barci nayi har zuwa azahar, yunwa ce ta tashe ni har jikina na ji yana rawa.
A daddafe nayi sallar azahar. Ban da zabi dole na fita zuwa kitchen, ban hadu da kowa ba sai da na shiga kitchen din, Halima ce tsaye da alama bata daɗe da shigowa daga wurin aiki ba, gabana na ji ya fadi da ganin ta sai na rasa me zan yi, sannu nayi mata ban ji ta amsa ba sai fuskarta da ta ƙara daurewa, juyawa nayi na koma ɗaki yunwa na ci gaba da nukurkusa ta, awa daya na bata kila ta kammala da na koma sai na samu kitchen din a datse an sa key. Cikin sanyin jiki na koma tea na ƙara haɗawa na sha.
Sai kusan la’asar Tahir ya shigo, ya ce na ci abinci na ce “E” ranar dai ban samu na ci abinci ba sai da daddare da aka haɗu gaba ɗaya, shi ma rashin sabo yasa na tsakura kadan na koma ɗakina.
Hakan yasa washegari suna fita wurin aiki ni ma na fita shinkafa jallof na dafa ban yi amfani da nama ba kifi nasa na zuba kayan lambu, har kunun aya na hada. Na koma daki na adana abi na sai azahar in ci lokacin da na zuba sai ga Tahir ya shigo ya ce “Na shigo a sa’a, dama fita zan yi neman abin da zan ci dan Halima yanzu za ta ɗora mana”. ban tanka maganar shi ba sai sannu da zuwa da na shiga yi masa, kunun ayar da na tsiyaya ya ɗauka ya sha ya lumshe ido “Da daɗi Ummuna”.
Murmushi nayi muka ci abincin tare sannan ya fita”.
Gadona na hau nayi ɗaiɗai ina jin dadin iskar da ke kada ni, tare da murnar ban yi amai ba, dan a yan kwanakin nan sai in yi ta fama da tashin zuciya, wani lokaci har sai na yi amai. Hafsa na kira muka sha fira, muna kammalawa kiran maman Ummi ya shigo muka gaisa da tambayar bayan rabuwa ta ce “Kina da labarin dawowar su Amma?
Na ce “Ko kaɗan”.
Ta ce “Sun dawo, iyayen Usaina ma sai da suka neme ki dan su ba ki haƙuri, aka ce kin koma Kaduna, amma sun kira Sodangi”.
na ce Kin ga kuma bai gaya min ba”. Mun ta fira har na soma hamma, sai da aka fara mata warning sai muka yi sallama.
Abin da ya yi ta gudana kenan sai sun fita wurin aikin su sannan in lallabo in yi abin da zan ci. Kuma matukar zan ci Tahir zai shigo tare za mu ci da shi, har a na gobe aiki zai zo kaina, duk sun fita wurin aiki cake nayi cikin sauri da niyyar zan adana abina ina ci a hankali, na kai shi ɗaki me aiki Ade ta iske ni ta ce min an yi baƙuwa.
Na fito falon, wata mata na samu ƴar gaye, na zauna ina gaishe ta ta amsa cikin fara’a “Ni matar abokin mijinki ce, Engineer Rabi’u Bello.
Sunana Haj Shema’u na kara mata sannu da zuwa, dan na ji sunan mijin nata a bakin Tahir, na miƙe “Zo mu shiga ciki Haj”. bata musa ba ta bi bayana, Ade dai tana ta goge gogenta a falon.
Muka shiga ta zauna tana ta kallon ko’ina a falon, na debo mata Cake din da nayi da lemo, tana ci tana kurbar lemon a hankali, ta dube ni “Ɗaki ya yi kyau Amarya, ya ma sunanki?
na ce “Ummulkhairi” murmushi tayi “Suna me daɗi, ina sauran matan gidan? ko da yake suna wurin aiki ko?
na ce mata “E” “Sai ke kaɗai suka bari” ta buɗe jakar da ta ratayo, wasu kwalabe da robobi ta ciro tana nuna min, “Kin ga kina amfani da wadannan, mijinki babu wacce zai kuma kallo da gashi sai ke, dan za ki zama tauraruwa, idan ma bai hankada su ba”.
Bayaninsu ta shiga yi min ɗaya bayan ɗaya ina kallon ta da saurare, sai da ta gama ta ce “To wanne, da wanne za a ba ki? dan kasaƙe nayi kafin na fadi “Bani da kuɗi” wani kallo ta min “Kina Amarya kike faɗin ba ki da kudi? to gara ki san wacce kike ciki, kishiyoyinki duk aiki suke suna diban albashi ga abin da suke samu wurin megidan, ke kadai ce yarinya a cikin su, kuma an ce iyakar karatunki Sakandire, to wallahi ina mai ba ki shawara ki hura wa maigidan wuta ya maida ki makaranta. Ta haka ne kaɗai za ki iya gogayya da wadannan matan. “Ungo”. ta miƙo min wata yar roba “Tsarki ake da shi, mijinki sai ya kusa suma in ya kusance ki, kina ganin ya susuce sai ki bijiro mishi da zancen ya samo miki makaranta”. ban amsa na ce “Ni fa ba ni da kudi” ta ce E na ba ki ne, taimakon ki zan yi Ummulkhairi, ina kallon ki kamar ƙanwata, idan ma maganin matan bai yi ba akwai inda zan amso miki taimako. Bani lambar wayarki. Na faɗa mata ta sa ta kira sai ta shigo. Na karbi maganin da ta bani ina godiya, da sauri na ga ta dubi agogo “Bari in tafi Ummulkhairi” na ce “Tun yanzu? ba ki tsayawa in yi girki” kai ta girgiza “Ke ke da girki kenan?
na ce A’a” ta ce “Ba dai ke ke musu girkin ba? na ce “A’a nawa ne ni kaɗai, megidan dai kan ci idan nayi”. Ta ce “A kul kika kuma ba shi, su suna wurin neman kudin su, ke kina nan, bayan gadin gidan da kike musu ki yi ya ci, nan gaba ma cewa zai ki yi har su, kar ki yarda ki zama ƴar tsaron gida”.
Ta soma tafiya na bi ta a baya har wurin motar da ta zo cikinta. Sai da ta shiga sai ta leƙo “Ko fa mijinki kar ki ba labarin zuwana”.
Kai na daga mata sai na koma ciki jikina a sanyaye ina tunanin al’amarin wannan mata, dan abubuwan ta da yawa sun ɗaure mini kai.
Dirowar na bude na saka abin da ta bani, na dubi agogo, lokaci ya tafi zai yi wahala har in gama girki wata cikin su bata shigo ba, tunanin kuma halin da zan kasance idan ban ci ba na tuna, dan yanzu ban jimirin yunwa. Haka nan na shiga na soma aikin ina jin faɗuwar gaba ina kuma auna wannan mata da inda ya dace in sa maganganun da ta zo min da su. Ina juye abincin Basma ta shigo, kamar yanda da na ga daya daga cikin su zan ji faɗuwar gaba yanzun ma hakan ce ta faru da ni, gane ba za ta kula ni ba yasa na gaishe ta, ta amsa ta cigaba da abin da take, na jera komai kan wani babban tire ban ko tsaya ɗauraye kayan da nayi amfani da su ba na fito kitchen din.
Har muna zaune muna cin abinci da Tahir tunanin matar bai bar ni ba, musamman da ta ce kar in kuskura in ƙara ba shi abinci na.
Da muna waya da Hafsa da yammacin ranar kamar in bata labari, sai dai na fasa.
Na dai yi kokarin yakice tunanin ta da ya hana ni sakat ya min tsaye a rai tsawon wunin yau.
Washegari da zai fita ya miƙo min key na wurinsa, na ce me zan dafa? sai da ya lumshe ido ya ce “Indai girkinki ne komai kika dafa zan ci”.
Da rana bai dawo ba, daga office taaziyya suka wuce shi da wani abokinsa zuwa Zaria.

Sau biyu ina fita da niyyar gyara sashen megidan sai in dawo.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *WA GARI YA WAYA*

*Daga marubuciyar*

*CANJIN BA ZATA*

*Maryam Ibrahim litee*

Sai a na ukun nayi ta maza.
Ban haɗu da kowaccen su ba har na taka step zuwa saman, da keyn nayi amfani wurin buɗe kofa wani wani kasaitaccen niimtaccen falo na soma taraswa sai dakin barci da bathroom ke manne cikin sa.
Nayi yan kakkabe kakkabe da goge goge, sai na canza zanen gado na fesa room freshener, kafin na shiga bathroom, shi ma na daɗa tsaftace shi, na fito na rufo ƙofar. Na kusa saukowa Halima ta shigo da alama daga wurin aiki take dan sanye take da kayan malaman jinya riga da wando sai dan guntun hijab iya kirjinta, tana rataye da jaka.
Gabana ya buga dam! dan duk cikinsu na fi ganin jin zafina a ƙwayar idonta, sannu da zuwa nayi mata, wucewa kawai tayi tana juya jiki, kitchen na shiga amma sai na shiga tunanin me zan dafa, anya idan nayi tuwo wadannan ƴan iyayin za su ci? wata zuciyar ta ce “Ba dai mijinki na so ba sai ki ƙi yi mishi dan wasu.
Da wannan ƙarfin gwiwar na yi tuwon Semo miyar kubewa danya, dan na ga kubewa fresh a kitchen din, na yi pepper soup, sai kunun aya na haɗa ƙarshe.Sai da na kammala komai nayi wanka sai nayi salkah. yau kwalliyar ta musamman nayi na sa ƙamshi sosai a jikina, riga da skirt na sa na English wear, rigar fara skirt din pink rigar ta kama ni, hijab na sa iya gwiwa na fito falo
dan yanda na ga suna yi me girki kan zauna ta jira shigowar megidan.
Zama nayi idona na kan TV da ke ta aiki, amma gaba ɗaya na gundura da zaman, dan bana so wata cikin su ta fito ta same ni, ina nan zaune kamar wadda ta yi ƙarya jin fargaba ta yi min yawa na tashi na gudu daki.
Na zare hijab din na zauna zan soma latsa wayata, ya turo kofar bakinsa dauke da wata makalallar sallama, na amsa nayi masa sannu da zuwa “Ya ba ki zauna na shigo ba?
Ya jeho min tambaya, shiru nayi sai ya miƙo min hannunsa “Mu je ɗakina”.
Bayansa na bi har saman, sai da ya yi wanka muka sauko, sun hallara idonsu kafe kanmu ni nayi saving din megidan na ɗaga manshanu “Kana so in zuba maka?
“So kai, ko kin manta Hajiyata bafulatana ce?
na zuba mishi su kam sai kallon tuwon su ke suna taba baki, tunanina ba za su ci ba, sai ga shi kowacce ta cinye wanda ta zuba, aka zuzzuba pepper soup shi wannan kam tasa aka gama da shi.
Har Ogan na tambaya akwai saura zai ci da safe. Na ce sai dai idan Allah ya kaimu safiyar in yi mishi wani. Na zuba mishi kunun ayan ban jira me aiki ba na soma tattara kayan,
Da mug din ya miƙe zuwa kan sopa labaru yake kallo a CNN. Sai da na gama kwashe komai sai na dawo na zauna ina latsa wayata, dan yau ban ga ta gudu daki ba, daga ni ke da Ogan.
Goma daidai na tashi na wuce ɗakina, kayan jikina na cire da ƴan kunnaye na rage daga ni sai bra da wani wando baƙi skin tight da ya lafe da fatar jikina.
Gaban fridge na wuce Kankanata wadda na zuba ma madarar ruwa peak na ɗauko abin da na wuni ina sha kenan gyaɗata da na sarrafa ita kyakykyawan sha nayi mata tun safe.
Na fara shan Kankanar kenan Tahir ya shigo “Lafiya kika dawo nan”
langabe kai nayi “Barci nake ji” “To barci anan za a yi shi?
ya miƙo min wayarsa Haj za ta yi magana da ke na miƙa hannu na karɓa daidai lokacin da kiran ya shiga Hajiyar ta daga bata tsaya amsa sallamar da nake mata ba, ta shiga korafi
“Lafiya Ummulkhairi duk yau an kasa samunki duk wanda na ce ya kira min ke, sai ya ce wayar ba ta zuwa”.
“Wayar ce yau take bani matsala am…..
“Shi ne ba ki ba shi an gyaro ba? ko a sawo wata, ina Sodangin?
“Bai sani ba Haj, ai yau ne”.
“To ba shi, in gaya mishi, a nemo wata ko a gyaro”
murmushi nayi “To Haj”
sai na miƙa mishi,
Sun ƙare wayar ya juyo inda nake “Me ya samu wayar?
na ce “Daukewa take”
“Shi ne ba ki gaya min ba?
na ce “Yau ai ta fara”
“Kawo in gani” ya amsa ya gama daddanna ta ya miƙo min.
“Ki wuce ɗakina” daga haka ya juya.
Na karasa yan kintse kintsena sai na saka hijab na fito,na rufe ƙofata, suna nan zaune inda na bar su, ban waiwayo ba har na shige.
Na fara barci na ji motsin shi, sai da ya gama komai ya rage hasken fitilar zuwa dream light ya hawo gadon, ba ka jin karar komai sai ta Easy da take ta aiki, jawo ni ya yi jikinsa, rada min ya yi “Wa ya ce yau za ki yi barci? za ki rama tsawon kwanakin da na ɗauka ba ki”
Wani kishi na ji ya taso min,,jin maganarsa mutumin da ke da mata har biyu amma yake wannan maganar.
Ajiyar zuciyar da yake ta fiddawa yasa nayi tunanin ko da gaske yake kewar tawa da ya ke faɗi ya yi? tsawon lokaci muka dauka yana nuna min kaunarsa a gare ni, daga bisani mun yi barci.
Asubar fari na ji ya zare jikinsa, sai da ya gama shirin fita Sallah sai na sauko, wanka na yi haɗe da alwala, anan dakin nayi Sallah, sai da nayi karatun Alkur’ani ina Azkar ya shigo, gaishe shi kawai nayi na sauko ƙasa, break fast na shiga haɗa mishi. Ina ciki kowacce ta shigo neman abin da za ta ci ta wuce wurin aiki. Farfesun kayan ciki nayi masa iyaka dan wanda zai ci, sai ruwan tea na soya chips da ƙwai, kan dinning na shirya mishi komai na haura upstairs na samu yana shiryawa, tare muka sauko na bar shi yana karyawa na wuce dan in shirya.
Ina kwalliya ya shigo ya ce min “Shi ya shirya zai wuce”
Addu’a nayi mishi ya ce “Ba za ki raka ni ba?
nayi narai narai da fuska
“Ban sa kaya ba” agogonsa ya kalla “Ina jiranki”
Doguwar riga baka me adon duwatsu a wuya da hannu nasa, na ɗauko hijabi, ɗago idonsa ya yi daga kan wayarsa, “Wannan hijab din, kullun kamar kin zo baƙunta na meye?maida shi nayi jin maganarsa ya ajiye min kudi sai ya juya.
Ina biye da shi har gaban motarsa, “Me zan taho miki da shi?
murmushi nayi “Komai ka kawo min na gode”
ya ja motar, motarsa na bayan ta Halima suka bar gidan.
Na kama hanya dan komawa ciki “Kar ki yarda ki zama ƴar tsaron gida” maganar Baƙuwa Haj Shema’u ta faɗo min, wasu maganganun fa da ta gaya min akwai ƙamshin gaskiya a cikin su, sai dai wasu sun fi kama da zuga, idan na biye mata za ta kai ni ta baro.
Jin na kusa karo da mutum yasa ni dawowa nutsuwata, Basma ce cikin sauri take tana rike da takardu da makullin mota.

Nayi aikina na kwana biyu. Ina shirya mishi abinci me rai da lafiya da safe da rana haka nan da daddare.
Ranar da na fita ya kai ni gidan Kawu Attahiru, can na wuni har sai yamma sosai ya je muka dawo tare.

Wata rana ya dawo aiki muna cin abinci, kamar yanda muka saba. Wayata tayi ƙara sabuwa ce fil ya kawo min, tun bayan da muka yi waya da Haj.
Ganin sunan me kiran yasa gabana bugawa, har rawa hannuna yake na daga kiran, gaishe ta na yi tayi dariya “Ban ji ki ba Ummulkhairi, magani ya yi kuwa? ya amsa zai nemo miki makarantar? ta jero min tambayoyin da suka sa na ji kamar zan saki fitsari, na saci kallon inda yake, cin abincinsa yake kamar ma bai san ina waya ba, na ce “Ban tambaya ba tukun” ta ce “To me ya hana? kar fa ki sake ki zama sakarai cikin kishiyoyi, ki yi kokari.
Yanzu ma kiranki nayi in ce miki tafiya ta kama ni, mahaifiyata ce bata da lafiya, zan je in dubo ta zan ɗan kwana biyu, idan na dawo zan shirya ki tsaf sai kin tsere ma wadannan matsiyatan”.
Wani irin kaduwa cikina ya yi, ji nake kamar Tahir na jin abin da take cewa. Nayi wa mahaifiyarta fatan samun lafiya, tare da mata Allah ya tsare. Sai na ajiye wayar na dawo inda na tashi sai dai na kasa cigaba da cin abincin, sai Ginger da na hada nake ta faman banka wa cikina, turo ƙofar da aka yi yasa muka kai duban mu wurin Halima ce cikin uniform take “Ina son ganin ka daga ka san ni ke da girki ba ita ba”
“To ki je ina zuwa” ya fadi ba tare da ya bar cin abincin da yake ba, ta juya ta banko ƙofar.
Sai da ya gama ya fita ashe tana kofar dakin, muryarta na ji na fara bambamin masifa tun bai tayata ba , har ya soma maida martani tsiyar bata ƙare ba har sai da ya fita ya bar gidan.
Ɗakina ta dawo kashedi ta min da in kiyayi Tahir ballantana har in ba shi abinci matuƙar ba ranar girkina ba ce.
Har dare bai shigo ba ita ma bata yi abincin dare ba.
Ni dai nayi zuru a daki, komai ban ci ba kuma tsoro ya hanani fitowa in dafa, sai sha dayan dare na ji shigowar motarsa, Komawa nayi na kwanta ina so barci ya ɗauke ni.

Washegari sai da suka fita na fito nayi girki, na boye abu na na ci ni kaɗai. Ko da ya shigo tambayata ya yi ban yi girki ba ne na ce “E” ya ce “To me zan ci? na ce zan fita in yi, ya ce ko ban da lafiya na ce Aa.

Ƙarfe uku ya kira wayata ya ce In same shi falo, hijab na sa sai na fito, su duka ne, fuskantar mu ya yi “Wace magana ce kuka zo da ita? shiru duka suka yi har sai da ya maimaita
sannan Basma ta ce “Mun ce bamu yarda tana ba ka abinci a ranakun girkinmu ba”
wani kallo ya watsa musu wanda na tabbata kowacce ta shiga hankalinta “Meye dalilin da zai hana ni cin abinci idan tayi?
“Saboda ba hakkinta ba ne” nan ma Basman ce ta ba kuma ba da amsa
“Good, ku masu hakkin me ya hana ku zama ku bani abincin?
cikin gunguni ta ce “Mu ba aiki muke zuwa ba”.
Halima dai da alama ba su shirya da ogan ba, dan ko zamanta a rabe tayi shi ba da ba da take zama tana hura hanci.
Ba zai yiwu ina da mata har uku ba, amma ina yawon sayen abinci kullum, kamar wani gwauro. Wadda kuma ke yi ina ci kuna ganin ba a yi muku adalci ba, to kowacce ta bar zuwa wurin aikin ta zauna ta kula da aurenta”.
Kowaccensu ta zaro ido suka bi shi da kallo, dan yana gama fadi miƙewa ya yi ya haura sama.

Ranar ni zan karbi girki. Kitchen na shiga, megidan dai bai kuma bi ta kan kowa ba yana sama Sallah kawai ke sauko da shi, har na gama girki na yi wanka ba motsin kowa zaman da suke yi wanda dama na fi danganta kishi ke sa su yin sa yau kowacce ta nabba’a ɗakinta.
Na ɗauki abincin zuwa sama, ban same shi falon ba sai na wuce ciki yana kwance daga shi sai gajeren wando ya tallafe keyarsa da hannayensa fuskarsa na kallon sama, ganin bai ko motsa ba tun shigowata yasa na zare jallabiyar da ke jikina sai na isa zuwa inda yake pillow da yake kai na sa hannu na zare ya yi firgigit ni kuma na yi maza na maye gurbin pillow da hannuwana sai na sa kansa a ƙirjina na rungume shi da hannayena, hakuri na shiga ba shi da wata murya da ban ma san ina da ita ba.
“Tun da na taso Ummulkhairi ban taba sha’awar tara mata ba, amma ya zan yi abin da aka rubuta kenan a allon kaddarata, yau an wayi gari matana uku, bana son kowace ta zarge ni da yi mata rashin adalci”.
Jijjiga kansa nake ina kuma taba duk inda na san zan motsa shi, har na samu nasara ya fara maida martani sai da ya kamu sosai muka yi soyayyarmu.
Ganin da ya yo wanka ya dawo zai kuma kwanciya na shiga mishi magiya har da yar kwallata ya zo ya ci abinci, mun fito falon na zuba mishi ya ci abinda ya sa ni jin daɗi daga bisani mun kwanta.

Da safe da na gama haɗa abin kari na hau sama samu na yi ya shirya muka sauko ƙasa tare, abin da yaso bani dariya kowacce zaune muka same ta cikin shirin tafiya aiki, ganin su yasa shi shan mur, ya wuce dinning ni ma ganin sun ya sa na mike zan gudu dakina, wani kallo ya min na koma na zauna muka karya tare, da daidai suka sulale kowacce ta nufi ɗakinta.

Wasa wasa fushi sosai yake da matan nasa, aiki kuma ba wadda ta kara zuwa kamar yadda yasa doka, wurin Kawu Attahiru suka kai karar sa, aka kira shi ya je ya same su.
Dole Kawun ya sa shi ya janye dokar hana su fita aikin su, kamar yanda suka rokai, shi ma kuma ya ce lallai duk wadda ke da girki sai ta ba shi abin karyawa kafin ta fita, ta dawo kuma ta ba shi na rana.

Ranar wata Asabar na tashi da amai da jiri.
Sai da ya shigo ya same ni a hakan, take ya ce in shirya mu je Hospital.
A hankali na shirya ya gaya wa matan nasa abin da kenan,sai muka fita. Wata asibiti me zaman kanta ya kaini, yanda ma’aikatan ke ba shi girma, suka karɓe ni a mutunce yasa na gane wurin zuwan sa ne. Family card ɗinsu aka fiddo aka kai ma Dr tare muka shiga likitan wanda ba Bahaushe ba ne hada miƙewa tsaye ya yi dan nuna girmamawa, suka gaisa da Tahir ya juyo gare ni muka gaisa. “Meke damun Madam?
ya tambaya da bagwariyar Hausarsa na fadi jiri da amai, ya cigaba da min tambayoyi ina ba shi amsa, Nurse ya kira ya ce mu je ta debi jinina a gwada yanzu a kawo mishi result, har aka diba na dawo suna zaune suna taba fira, bayan wani dan lokaci Nurse ta dawo ɗauke da sakamakon gwajin likitan ya karba ya duba kafin ya ɗago yana ma Tahir murna da albishir.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

*Ina masu buƙatar karin haske game da Aunty Gyaɗa? to ku matso kusa*
*ku jaraba wannan da yardar Allah zai yi muku. Auni gyadarki Hajiyata kwano ɗaya, ki kai ki ajiye, debi kofi daya na* *gyadarki, sai ki wanke ta* *ki gyara ta, sai ki zuba a cikin tukunya,*, *daga nan sai ki zuba ruwa kofi uku, e kofi uku za ki sa, cikin gyadar nan da kika zuba a tukunya,* *sai ki ɗora a wuta, ki tafasa ta, tafasa daya. Sai ki sauke ya huce idan ya huce, sai ki ta ce, Ruwan gyadar nan za ki kasa uku, ki sha kofi daya da safe, da ga nan* *ki sha daya da rana, ki sha daya da daddare, ban da fa gyadar ruwan za ki shanye, dan Allah* *Hajiyata ki jaraba wannan abu ki yi sati kina yi, koma kwana goma da yake yanayin jiki jiki ne, wata ta na shan abu za ta soma* *jikewa, wata kuma za ta daɗe kafin ya soma aiki a jikinta, dan haka ƴan’uwana mata a jaraba matsi da ni’ima, wasu ma sun ce yana wanke mahaifa*
*Allah ya sa mu dace*

 

Zama nayi a ɗaya daga cikin kujerun da ke falon, na soma gaishe ta, cikin nuna girmamawa tana amsawa cikin fara’a.
Ina tsohon mijinki? Tahir ya tambaye ta “Malam, ya fita ta’aziyya nan bayan mu”. “Kin yi girki ko in fita in samo muku abin da za ku ci, daga Asibiti muke, bata da lafiya”.
“Ash sha, sannu kin ji, Allah ya kawo sauki, mutane suna ta fama da zazzaɓi”. saurin cewa ya yi “To ita ba zazzaɓi ba ne, ciki ne da ita”. Wayyo! ji na yi kamar ƙasa ta buɗe in antaya, dan kunyar da na ji, ita kam murna ta hau yi da addu’o’i na Allah ya inganta, yasa wannan karon su ga kwansa. Ruwa ta kawo mana ya sha sai ya yi mata sallama ya ce in mata wuni, zai dawo ya ɗauke ni. Dawowar yan biyu daga makaranta, yasa na gane inda ya kawo ni, ba su manta ni ba suka hau murnar ganina, tsohon mijinta ya dawo.
Zuwa la’asar nayi sabo da dattawan masu matuƙar karamci da dattako.
Ni nayi musu abincin dare duk da hana ni da take wai bani da lafiya, na ce yanzu ban jin komai, a cikin firar mu take bani labarin ƴar ta Maman su ƴan biyu, “Mijinta dan dakinta ne, tun da aka kai ta gidan su, indai za ta yo aike shi ne dan aikenta Allah kaɗai ya san shakuwar da ke tsakaninsu, shekaru bakwai kenan Allah ya bata rabo aka yi ta murna, ashe hanyar tafiyar kenan, aiki aka yi mata aka ciro su sai dai ko farfadowa bata yi ba”.
Wani hali dattijuwar ta shiga, da alama mutuwar ta dawo mata sabuwa, hakuri nayi ta bata da yi wa mamaciyar addu’ar samun rahma. Sai da ta natsa sai ta cigaba, mijinki shi ke tsaye akan mu ni da malam, komai da ɗa nagari zai yi wa mahaifansa shi yake mana. Mun yi ta firar mu har magrib ta gabato,.wanka ta umarce ni in je in yi, “Ki gyara jikinki kafin dawowar mijinki, ba abin da ke kara ba mace muhimmanci a zuciyar mijinta irin tsafta da gyara”. na ce “To Haj”
wankan nayi na fito, kayan kwalliyar da ta ajiye min suka bani mamaki kamar ta san tunanina, “Mijinki ke famar kawo wa su ƴan biyu, kamar wasu yammatan kirki”. ƴar dariya nayi na soma shafa, na fesa turare, zan mayar da kayan jikina ta nuna min wata leda “Ga kaya nan, tsarabar Makka aka kawo min, ina ni ina saka kayan yara”.
na ɗauka na buɗe, doguwar riga ce, kalarta pink, ta sha kwalliyar duwatsu, sosai ta bani sha’awa, da na saka ta ajikina ba ƙaramin karbata tayi ba.
Na zauna ta miƙo min fura, “Maza ki sha, mijinki baya gajiya da kawo mana da nono me kyau”.
na ce “Cikina ya cika Haj, kar ya fashe”. ta ce “Wa ya ce miki ɗanyar fata na fashewa? na kafa kai kenan, gardin furar ya ratsa ni, na tsinkayi sallamarsa, tare da su ƴan biyu ya shigo, suna riƙe da shi, ledojin da ke hannunsa ya mika wa Haj, ta karɓa tana fadin “Kai dai ba ka gajiya”, gasassun kaji ne, guda biyu, kusa da ni ya zauna ya karɓe furar hannuna, ya kai bakinsa, sai da ya shanye sai ya dire mug din, “Tashi mu tafi”. Haj da ta shigo daga kai wa Malam ta shi kazar ta ce “Wane irin ta tashi ko naman bata ci ba, ga furar ka shanye mata”.
“Ci namanki tsohuwa, ita ma na saya mata nata”.
“oho, to zubo mishi abinci”. na tashi na kawo mishi, lomar farko ya gane ita tayi, Allah ya yi wa yarinyar baiwar girki ta sarrafa shi ya yi daɗi, duk yanda yaso ya ci kaɗan dan abincinsa na gida, bai ci ba ya fito ɗaukar Ummulkhairi, kasa hakuri ya yi sai da ya ji ya yi dam,.har zumudin ace abincinta zai ci yake duk da Halima ma ta kware, ita ganin kyashinta ne matsalarta. na kwashe kwanonin “Tashi mu je gida” ya bani umarni, na miƙe yan biyu ma suka miƙe, dan su da gaske suke bi na za su yi. Na ce “A dauko min kayan su, kakar ta ƙi ta ce Bani da lafiya idan na warke a kawo su. Mun shiga dakin Malam, tsohon na kishingide kan lallausan carpet din da ke malale a falon, yana sauraren Radio, muka yi mishi sallama sai shi mana albarka yake ya ce min “Zo nan yarinya” na matsa kusa da shi hannunsa ya sa ƙarƙashin tuntun da ya ɗora hannunsa, kuɗi ya ciro “Amshi yarinya, Allah ya baku zuri’a da za ta ji kanku”.
Turus! nayi na waiwaya na dubi Tahir, daga min kai ya yi in karɓa, na sa hannu biyu na karba ina mishi godiya, Tahir ya matso bandir ya ciro na yan Naira ɗari “To ga shi malam, kudin sayen goronka” a gefensa ya ajiye masa, yan biyu dai da ƙyar muka rabu.

Jingina kaina nayi da kujerar motar, na lumshe ido, kewar dattawan da na wuni da su yau kaɗai, tana ƙara rufe ni, sai kuma na tuna nawa iyayen, sai dai muyi waya, ina ji kamar kar in koma wannan gida, da za ka yi ta zama kai kaɗai kamar maye, babu me hulɗa da wani. Gudu sosai ya yi dan dare da ya soma. Bamu samu kowa a falon ba, na wuce ɗakina, ya wuce dakin Basma da ke da girki.

Satin da ya zagayo Tahir ya shirya tafiya Ƙanƙara. Ba magiyar da ban mishi ba, ya tafi da ni amma ya yi funfurus, tare suka tafi da Halima, danbun nama nayi na ba shi na ce ya kai wa Haj. Ban san za shi Dutsinma ba, sai ranar Lahadi da daddare, ina kwance Ummata ta kira ni, ce min tayi “Godiya sosai za ki yi wa mijinki idan ya dawo, ya cika mu da hidima”. na ce “Bayan ya ki zuwa da ni” ta ce “Tun da dai ana zaune lafiya, ai shi kenan, yawon ba shi da wani amfani” na ce “Kai Ummata, amma ai zan zo bikin su A’isha” ta ce “Idan ya bar ki babu laifi”,
“Ina son ganinki Ummata” dan murmushi tayi wanda na ji sautinsa a kunnena, “Ai auren kenan,Ummuna”. sallama muka yi dan wayar Tahir da ke ta shigowa tana yankewa. cikin siririyar murya na mishi sallama “Da wa kike waya tun dazu? abin da ya fara ce min kenan, jin muryarsa kamar ya hasala yasa na dan yi murmushi “Da Ummata ne ranka ya daɗe” sai na soma gaishe shi “Me kike har yanzu ba ki kwanta ba? ya kuma tambayata “Ai barcin zan yi yanzu, ina Haj? “Tana ɗakinta” ya amsa min “Kai kuma kana tare da matarka” maganar me kama da subutar baki, ta fito bakina ta isa kunnensa. Dan murmushi me sauti na ji ya yi “Matar tawa ai bata nan, tana gidan su, amma na san tana hanya”.
“Sai da safe” na fadi ina shirin kashe wayar, “Har kin gaji da ni? ya tambaye ni “Uhm uhm, na faɗi cikin jin kunya “Mu kwana lafiya” ya faɗi yana kashe wayar.
Na maida kaina na kwantar, ina mai jin dadin kular da nake samu daga mijina.

Washegari Litinin sammako suka yi suka taho. Shi maigidan ma bai dawo gida ba, Office ya wuce sai rana muka gan shi.

Wata safiyar Alhamis, tsaye nake gaban mirror sai kallon kaina nake cikin shigar da nayi, ta riga da wando ne Pink, sai gaban rigar aka ratsa fari tana da stones. Takalma flat shoe na ciro shi ma fari, sai gyale me yala yala shi ma fari.
Na kasa fita dan ba zan iya tsayuwa gaban Tahir a haka ba, dan sun lafe a fatar jikina, hatta dan cikina ya fito ya zauna das, shigowar sa tasa na fada gado na dukunkune, ya tako zuwa inda nake yasa hannu ya ɗago ni, ya haɗa ni da jikinsa, “Tashi in ga kwalliyar da kyau, ko bani aka yi wa ba? ƙara sunnewa nayi, “To tun da ba za ki tashi in gani ba, mu je ki raka ni kar in makara”. na ce. “To bari in ɗauko hijab” “Ki wuce mu je, waye a wajen? mai wanki bai zo ba”. ban so ba, haka nan na bi shi, da na buɗe mishi kofa ya shiga bai rufe ba, tsayawa ya yi yana kallona, Halima wadda ta fito cikin sauri dan tafiya wurin aiki tsayawa tayi turus! hango Tahir tare da munafukar yarinyar nan me fama da hijabi kullum. Mamaki ya kashe ta ganin dressing din da tayi, wani zafi kirjinta ya dauka, idonta ya canza kala, in ma ba idonta ke mata gizo ba ciki ne jikin yarinyar. “Impossible, ban haihu ba ba shegiyar da za ta haihu! ta fada a fili, kamar me magana da wani. Cikin sassarfa ta ƙarasa inda motarta take, cin taya tayi sai ta dibe ta a guje a tare muka bi motar da kallo, ina mamakin diban karan mahaukaciyar da tayi da wata kujerar canopy da ke kan hanya, murmushi Tahir ya yi, dan shi sam abin da tayin bai ba shi mamaki ba saboda sanin da ya yi yanda take masifar sonsa haka take kishinsa, yasan ganin sa da Ummulkhairi ne yasa ta wannan fushin.
Dan ya hakikance duk a matansa ba me mugun kishi kamar ta, rufe motar ya yi sai ya bar gidan.

Tana tafiya tana share zufar da ke keto mata.
Bata iya haƙurin ta bari ta isa Office ba kamar yanda zuciyarta ke ruwaita mata, wayarta ta ciro babbar aminiyar ta ta kira “Kina gida kuwa? abin da ta fara cewa ƙawar kenan, “Yanzu na fito gida, akwai inda za ni lafiya? wa ya taɓa min ke? “Ina son ganin ki yanzu, kuma ina kan hanya za ni wurin aiki”.
“Kar ki damu, zan same ki wurin aikin”.
Halima ta katse wayar.

A motar Halima suka kulle kansu. Ta zayyana wa kawar ta ta matsalar da ta taso mata.
Kafadarta ta dafa, “Ki kwantar da hankalinki Aminiyata, kamar yadda waccan ta yi yunkurin haihuwa ya’yan suna bin makwarara, wannan ma hakan ce za ta kasance.
Ki kwantar da hankalinki auren ma ai dan rufe shi ya yi ba mu ji da wuri ba, nan da sati daya cikin nan ya zama labari ni nayi miki wannan alƙawarin. Kina tashi wurin aiki ki kira ni mu wuce, ki dai kira mijinki ki san me za ki fada mishi”.
Halima tayi ƙwafa “Ai Basma, mahaifar gaba ɗaya aka lalata min, yaushe rabon da ki ji na ce miki tana da ciki”.
ƴar munafukar dariya ƙawar tayi “Ai na kan tudu yasan aikinsa.
Da haka suka rufe hirar, kowacce tayi nata wajen amma zuciyar Halima bakikkirin kamar ta janyo lokacin tashi.

A ranar dai Tahir ya tara mu ya bamu labarin takardar da ya samu a teburinsa yau, ta canjin wurin aiki da aka yi mishi zuwa Lagos.

Ranakun da suka biyo baya, shirin tafiya Tahir yake tayi. Halima ta samu nasarar zuba maganin da ta karbo wurin malaminta ko bokanta za a ce, dan zubar da cikin Ummulkhairi wata safiya tana haɗa abin da za ta karya da shi.

Ana gobe zai tafi ni ke da shi dan haka shiri nayi sosai yanda zai ji ni zam zam, yanda ko ya tafi zan tsaya a ransa.
Duk wasu dabaru da na sani na yi har Hafsa na kira na nemi taimakon ta, har maganin Haj Shema’u da na kasa yarda in yi amfani da shi yau na yi karambanin amfani da shi, kuma babu karya a yanda ta kambama maganin nata.

Ƙarfe goma na safiya ya sallame mu. Suka kama hanya da wani mutumi da ya dauka dan ya tuka shi.
Wuni nayi ina barci a ranar. Sai washegari na koma kan al’amurana, marata na ji tana min ciwo kadan kadan, ban damu ba bathroom na shiga dan in dan watsa ruwa, ɗan jini jinin da na gani yasa gabana bugawa, na dai yi wankan na fito, har zuwa dare ban kuma ganin komai ba.
Na kwanta ƙarfe sha biyu kamar an tashe ni.
dan wani mafarki da nayi wai ina tafiya jini na zuba. Ai kam cikin jinin na ji ni kwance male male, hankalina ya tashi na shiga bathroom na tsarkake jikina na dawo na kwanta. Wasa wasa jini ya ƙi tsayuwa kwana nayi ina zurga zurga a bayi, ana fitowa sallar Asuba na kira wayar Tahir wayar a rufe take, sai kawai na hau shiri.
Sanda na fito kowacce tana ɗakinta, da ɗaiɗai na buga kofar su, kuma na fada musu bani da lafiya zan wuce Hospital, lokacin da na fito gari ya soma haske, mai yin wanki ba gidan yake kwana ba, da safe yake zuwa, shi ke buɗe get bai kai ga zuwa ba, dan haka ban ga kowa a harabar gidan ba.
Kofar me tafiya a kafa na buɗe sai na fice. Hajiya Hajara ta tafi ta’aziyya ƙanƙara. Da kafa na taka har titi inda na samu motoci sun soma zirga zirga, me keke napep na tare, sai dai duk yadda na so tuna sunan Hospital din da muka je da Tahir kasa hakan nayi, sunan Barau dikko ya fado min da na ji su Haj da malam sun ambata lokacin da na je tudun wada.
Dan haka can din na ce ya kai ni, ɗari biyar ya ce zai kai ni.

Da isar mu sauka kawai nayi, na shiga raba ido, har sai da na samu wata baiwar Allah na tambaye ta. Rakani tayi har inda na sayi kati, na ƙara gaba wurin bin layi, har lokacin kuma ina jin zubar jinin, sa’adda layi ya zo kaina ƙafata ta fara rikewa, ina ganin likita nayi mishi bayani takardar scanning ya rubuta min.
Da tambaya na gano inda ake yi, bayan na biya aka yi min na kawo wa Dr, yana dubawa rubutu ya yi sai ya miƙo min takardar, “Maza ki sawo wadannan kayayyakin ki zo in raba ki da wannan masifar”. ya kuma gaya min kuɗaɗen wankin cikin da zai min, na ba shi sai na fito.
Da tambaya nan ma na sawo duk abin da ya rubuta, duk abin nan da ake ina tafiya idona na tara ƙwalla na auren nesa, da a garin mu nake da yanzu ƴan’uwana na kewaye da ni. Na sawo na kawo, ya tsallake patient din da ke son ganin sa ya wuce cikin sauri ina biye da shi.
Maternity muka nufa, masu haihuwa biyu muka samu suna fama, drip aka fara sa min wanda aka zuzzuba ma allurai kafin aka sa min wani magani kasan harshe, sannan likitan ya soma aikinsa, barci ke fizgata amma masifar wankin cikin ya hana.
Bayan wasu mintoci aka kammala, na dan kwanta jim bisa gadon kafin na buɗe idona wanda na kasa hana hawaye zuba a cikinsu, wadda ke kusa da ni da ta riga ta haihu ta ce “Baiwar Allah, ina ƴan’uwanki? na share hawaye da bayan hannuna “Ba anan garin suke ba”. ta ce “Ina mijinki?. na ce “Yana Lagos” bata gaji ba ta kara cewa “To ba wanda za ki kira, ya zo ku tafi?
sai sannan na tuna wayata da na baro gida, miƙewa nayi na shuri takalmina “Zan iya tafiya na gode” ina fitowa dakin wa’anda suka haihu ba lafiya jiri ya ɗebe ni na tafi luu! wasu mata suka tare ni. Nan ma miƙewar na ƙara yi na fita mutanen da ke harabar asibitin suna bi na da kallo dan yadda nake tafiya ina haɗa hanya dan wani uban barci da ke fizgata.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

 

Keke napep na kuma hawa, muna tafe barcin na dibata. Har ƙofar gida ya sauke ni, na wuce me wanki yana min sannu, ina shiga ɗakina gado kawai na faɗa, duk kuma yanda nake ji bai hanani janyo wayata ba, missed call din Tahir na samu rututu. Ummarmu na soma kira na faɗa mata abin da ya same ni, sosai ta shiga damuwa jin na kuma bari a karo na biyu, da muka gama sai na kira Tahir, “Me ya same ki? da ɗaukar sa abin da ya fara ce min kenan kafin kuma in yi yunkurin amsawa ya kuma cewa “Ina kika bar wayarki, nake kira tun safe? Sai na rasa wace tambayar zan soma amsawa na dai yi ƙarfin halin cewa Miscarriage na samu, shi ne a ka yi min wankin ciki”.
Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun ya yi ta maimaitawa da wata irin murya da duk tausayin kaina da nake sai da na ji shi ma ya bani tausayi. “Ke da wa kuka je Hospital din?
“Ni kadai na je”. “Haba Ummulkhairi, ke ma da nake zaton zan samu nutsuwa ta bangarenki kema din haka za ki yi min? hankalina na ji ya tashi da jin zancansa a kaina, da sauri na ce “Me nayi maka? “Saboda Allah ga ƴan’uwanki a gida sai ki fita ke kaɗai, cikin halin rashin lafiya?
a garin da ba ki san kowa ba, yanzu idan iyayenki suka ji ya za su kalle ni?
Da sauri na soma rantsuwa jin zargin da yake min “Wallahi duk kan su na buga kofar su da zan wuce” kashe wayar na ji ya yi ni ma na ajiye tawa, na maida kaina kan pillow na kwantar cikin tunani.

Awa biyu aka ƙara da yin wayar mu sai ga Hajiyar tudun wada da Malam.
Wani dan matashi da ba zai wuce tsarar kanena Nura ba ya kawo su, su Malam sun dan jima sai suka wuce, Haj suka bari wajena. Basma da Halima sun shigo sun gaishe ni a tsaitsaye.
Washegari malam ya dawo da su ƴan biyu, kwanaki uku Haj tayi da ni, har ƴan’uwana da suka zo daga gida Aunty Maimuna da Aunty Habiba nan suka zo suka same ni tare da ita.
Har ƴan kankara sun zo cikin su hada Hajiyar Tahir, su kwana suka yi da kansu kuma suka shiga kitchen abin da yasa takaici ya ishi Halima, ganin yanda suka sake sabanin da da in sun zo suke a raɓe.

Ranar Asabar maigidan ya iso, shigowar asuba ya yi, dan haka bai nemi kowa ba, saman shi ya haye,
Da safe na fito zan shiga kitchen neman abin da zan karya da shi, muka yi ido huɗu, a cikin tafiyar da nake yi kamar me sanɗa dan tun zubar jinin da nayi jikina ba karfi lallabawa kawai nake, na karaso na gaishe shi sai kallona yake ganin yanda na lalace cikin yan kwanaki kaɗan. Kitchen din na wuce Ade na ciki tana aikinta, gaishe ni tayi tare da tambaya ta jiki, na amsa na kama nawa aikin, na kammala ina shiryawa a tray Basma ta shigo, “Ki zo yana kiranki”. abin da ta ce min kenan sai ta juya, na sunkuci tray na bi bayanta.
Zaune na same su, Tahir shi da matansa, ina zama ya fara magana wadda ta shafi irin zaman da ake yi mishi a gida ba wadda ke shiga sabgar wata, tare da daura laifin kacokan kan Halima dan ya ce ita ce babba, dole ta ja kowa a jikinta. Kan dole ta ba shi haƙuri, ni ma hakurin na ba shi, na miƙe ɗauke da tray na zuwa ɗaki.
Ina zama karyawa na soma a hankali, sai ga shi ya shigo hannayensa kawai ya harɗe a kan kirjinsa yana kallona, kallo ɗaya na mishi na maida kaina ƙasa, takunsa na ji zuwa in da nake ya ɗago ni yasa ni jikinsa, kyakykyawar runguma ya min “Ki yafe min, Ummulkhairi”.
Me ka min? Na tambaye shi “Na tafi na bar ki kina ta shan wahala, rabon da Allah ya bamu ya zube bana kusa, ballantana in rarrashe ki”. Wasu hawaye na ji sun ziraro min, ɗago ni ya yi ya zura min ido “To ba gani ba, meye na kukan? ba zan kara barin ki ba, zan tafi da ke in kula da ke” jin tsayuwa na neman gagarar mu ya koma kan kujera zama ya yi ina jikinsa, hankacif ɗinsa yasa yana share min fuska ” Ki fara shirya kayanki, sammako za mu yi idan Allah ya kaimu” kai na gyaɗa mishi sai ya zame jikinsa ya mike “Zauna ki ƙarasa cin abincinki”.
a hankali na ce “To kai fa? Kai ya girgiza “Akwai abubuwan da zan aiwatar yinin yau, kar ki damu. Fita ma zan yi”.
yasa kai ya fice.
Maimakon cin abincin, bedroom ɗina na wuce ina kwanciya hawaye na cigaba da yi ina godiya ga Allah bisa canjin da ya yi min dan abin da ke ta sa ni kuka tuna sanda nayi bari a gidan tsohon mijina, ranar da aka dawo da ni ba wani nuna jin tausayi ko wata kauna, burinsa kawai ya biya buƙatar sha’awarsa, abin da ya takura shi kenan da ba ni. Dama kukan mu matan hausawa kenan, a kullum, rashin nuna kulawa daga mazajenmu. Mace na so a rarrashe ta a nuna an damu da ita, ko da ba a bata komai ba, ki yi abin kirki a yabe ki, a’a ba mazan yanzu ba, sai ki daɗe kina wa miji abin kirki, ba zai taɓa nuna ya ma san kina yi ba, sai randa kika saɓa mishi za ki ji kwandon Ala tsine.
Mata masu fama da irin wadannan matsalolin. ban san iyakar su ba.

Yana gama musu ganin dakin da ya shiga yasa duk kan su suka bi shi da kallo, kowacce da abin da take sakawa a ranta.
Halima ta ja dogon tsaki ta miƙe tayi ɗakinta, Basma ta bari zaune tana share zufar da ta ji tana tsatstsafo mata. Ba irin ta ta dace da zama da kishiyoyi ba, kishiyoyin ma har biyu ringis, ban da jarabtar da aka yi wa zuciyarta na masifar son Tahir Sodangi da ta haƙura da shi.
Ta dubi Halima da ke tafiya kamar kububuwa dan fushi “Gara ke da ni”
ta faɗi cikin siririyar murya. Ita ma miƙewar tayi ta nufi na ta dakin cikin sanyin jiki.

Halima na shiga na ta dakin gado ta fada ta shiga zabga kuka wiwi na bakin kishin wadannan mata da Tahir ya dauko mata, duk yadda ta so ta kori Basma ta bar mata gidan ta zauna ita kadai, abin ya faskara, sai ma wata da ya ƙara dankaro mata. Har sai yaushe Tahir zai bar zuciyarta ta huta? tuna rayuwarta a farko tayi tana ita kadai sai yanda tayi komai na shi ita yake miƙa mawa, yanzu kam dan karshen wulaƙanci sai ya tara su kamar awaki sannan zai ba su duk abin da zai basu, kuma iri ɗaya.
Girgiza kai ta shiga yi hawayen na daɗa ambaliya kan kuncinta. Amma da gani wannan yarinyar ta samu amsuwa a zuciyarsa yanda yake kaffa kaffa da ita, sam baya wasa da lamarinta. Ko Basma ɗiyar masu da shi, kyakykyawa ajin farko kyankyasar inji, da ta sha fargaban idan ta shigo Tahir zai juya mata baya sai ya bata mamaki, sai shafe wata bai tafi wurinta ba tana Abuja, lokuta da dama ma sai Basman ta dame shi da waya ko kuma ta dauki excuse wurin aikinta ta zo Kaduna. Kwafa tayi tuna amarcin wannan yarinyar sai ya shafe sati biyu a kankara, abin haushin ma wai bazawara, sanda tana kankaran kuma duk weekend baya daga kafa sai ya je. Ko a muamalarsu ta auratayya suna su biyu duk girkinta ya dinga takura mata kenan da bukatarsa, amma tun zuwan yarinyar nan idan ta gama aiki ita kuma ta amsa baya damunta, kishin hakan hana ta barci yake, tunanin abin da ya yi a wancan dakin ya taru ya kulle mata zuciya.
Aiki ne ja a gabanta, yarinyar nan ga ta da kuruciya daga zuwa har ta fara ciki.
Ƙwafa ta kuma yi “Mu zuba yarinya da ni kike wasan.

Tun fitar Ogan bai shigo ba sai dare. Ko da ya shigo kuma bai sauka kasa ba sama ya yi zamansa.
Halima me girki ita ta bi shi kafin daga bisani ta sauko kiran mu, bisa umurnin Ogan. Ni ce karshen zuwa dan sa’ar da ta shigo na fito wanka
ina kwalliya, simple make up nayi sai na zura wata jallabiya maroon colour na rufe kaina da gyalen rigar, takalmi flat na saka. A kujerar kusa da ƙofar na zauna Ogan na gaida kafin nayi musu Sannu, da alama wanka ya yi cikin jallabiya yake me guntun hannu sai annuri ke fita a fuskar shi, musamman idanuwansa masu haske, ga ƙamshin turarensa da ya cika wurin.
Glass cup ne a hannunsa yana shan abin da ke ciki. Ajiye cup din ya yi sai ya yi gyaran murya “Dalilin da ya sa na tara ku, gobe idan Allah ya kaimu zan yi sammako in koma wurin aikina, sun bani wurin zama ina da mata har uku, ba zan tafi in zauna ni daya ba, dan haka na tara ku in ji da wa zan tafi? ni dai na yanke zan tafi da guda, bayan wata kuma sai in dawo in tafi da wata”
Basma ta lumshe idonta ta kwantar da kanta jikin kujera, ban da matsalar ta da a shirye take ta ajiye aikinta dan ta kasance da mijinta. Kuɗi ne mahaifinta ya tara musu, mijinta na da su, account ɗinta cike yake da kudi duk wata za ta ji alert. Halima ce tayi magana “Amma Tahir aikin mu”.
Wani kallo ya jefa mata “Aiki da auren wanne ne a gaba? shiru tayi “Dan haka gobe da ke za mu tafi”.
Wata zabura tayi “Ni kuma Tahir? idan na tafi zan samu matsala” kallon dazu ya kuma jefa mata “To meye nufinki, ba za ki ba?
shiru tayi alamar hakan ne, duk da kishin da ke cin ranta na wadda za ta tafi ta kasance tare da ogan koma bayanta. Duk da shi ma aikin kishi ne ke sa ta yinsa.
Ya juya wurin Basma wadda har sai da na tabo ta dan yadda yake ta magana bata ko motsa ba. Ta sauke kyawawan idanuwanta a kansa ya gane karin bayani take nema ya maimaita mata ta ce ita ma za ta tsaya saboda aikinta.
“To tafiya kan amarya ta faɗa”.
Halima wadda ke jin kamar ta kai wa bakinsa duka idan ya ambaci kalmar amarya ta aika mishi da harara a fakaice, cikin kunkuni ta ce “Dama haka ka shirya” dubanta ya yi “Magana kike? saurin girgiza kanta hada hannayenta tayi kafin ta taɓe baki “Kuma a haka da jikin nan za ka kwashe ta? ta fakaice ya dube ta bai yi magana ba “Kamar yanda na ce muku, ba zan iya shigowa duk sati ba ko sati biyu, sai dai karshen wata, dan wani sati biyun zan je ƙanƙara ne in gano Hajiyata. Ya sallame mu na koma ɗakina.

Ban kwanta ba sai da na sauke akwatunana dan zaben wadanda zan yi tafiyar da su.
Ƙarshe na yanke in tafi da abu na duka dan in na bar su har sai yaushe zan dinka su? dan anan dogayen riguna.nake amfani da su sai tsirarun kayana, na kwanta cikin tunani, shi kenan yanzu ba rabon in halarci bikin kannena su Aimana, na dubi agogo lokaci ya yi nisa sai da safe zan kira Ummata da Babana da sauran ƴan’uwana in yi musu sallama.

Bayan dawowarsa daga sallar asuba zaune yake gefen gado, damuwa kwance saman fuskarsa. Uwargida sarautar mata na gefensa. “To yanzu me kike nufi? idanu ta dan kada “Ka san dai ba wadda ta yi maka sanin da nayi maka, in duk su sun yarda ni kasan na san ka sarai dama ka shirya tafiyarka da Amarya, ka ɓullo mana ta haka”.
Ƙara daure fuska ya yi “Amma na ba kowacce hakkinta, in ma hakan shi ne nufina”.
ita ma ɗaure tata fuskar tayi “Saboda ta fi mu ko? wani ɓacin rai ya ji ya taso mishi kamar ya biye mata sai kuma dalilin da ke sa yake kasa biye mata ya bijiro mishi, kome za ta mishi da ya tuna ta fara son sa tun a shi din take so, ta aure shi bai da komai sai ya kasa ci mata fuska. “Tsaye ya miƙe “Babu macen da ta fi ki a wurina halima, kina da daraja ta musamman, sai dai idan kin zubar da ita da kanki, shi yasa kullum nake nuna miki abubuwa kin kasa fahimtata”
Kanta ta ji ya fasu “To amma me yasa ka zaɓe ta cikin mu?
Ba zaben ta nayi ba ki shirya mu tafi.

 

,Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Cikin salon yaudara ta ɗa namiji ya ce “Ba zabenta nayi ba ke ce babba ki shirya mu tafi”.
Girgiza kai ta shiga yi, ya matsa kusa da ita janyota ya yi jikinsa suka faɗa tsakiyar gadon.
Sai dai tun kafin abu ya yi nisa ta soma bijiro mishi da zancen kudaden da take so ya bata, zuciyarsa ce tayi bakikkirin ya tsani wannan bakar dabi’a tata, in har zai yi kwanciyar aure da ita sai ta roke shi.
Ji ya yi shaukin abin ya sake shi, miƙewa kawai ya yi ya faɗa bathroom.
Cikin shigar kananun kaya ya sauko, dakin Basma ya fara shiga suka yi sallama kafin ya shigo wurina ya samu na gama shiryawa ina saka dan-kunne. Akwatunana ya soma fitarwa kafin ya dawo “Kin kintsa? na ce mishi “E” Kin karya? nan ma “E” ɗin na kuma cewa “Fito mu je” ya bani umurni na rataya jakata mahadin takalmin da ke ƙafata. Tare da sauran matan muka rankaya har inda motar da za mu yi tafiyar a cikin ta take, wata dankareriyar Jeep ce sabuwa dal tana sheƙi, a tafiyar sa ta farko ya fara hawanta, baka ce wuluk.
Mutumin da ya tuka shi a tafiyar sa ta farkon yau ma shi ne riƙe da sitiyarin.
Tafiya me karfi muka yi, saboda nisan inda muka nufa. Tun ina zaune kan mazaunaina, har na sulale na kishingida, Tahir ya janyo ni ya nade ni da jikinsa, dan haka barci sosai nayi. ƙarfe shida na yamma muka shiga garin na Lagos. Amma yawan cinkoso da go slow na ababan hawa yasa, bamu isa unguwar da za mu ba sai da muka shafe sama da awa guda.
Da ganin yanayin unguwar da muka shiga gidajen cikin ta na ma’aikata ne, gaban wani flat house ya Parker motar sai muka firfito hasken wutar lantarki ya haskaka wurin, flat hudu ne a rukunin,.waya waya ce kowacce waya flat huɗu ne. Wanda ya yi driving ya sallama bayan ya fito mana da kayan mu, Tahir ya buɗe kofa falo ne babba sai ɗakunan barci guda biyu, sai kitchen. Kan daya daga cikin kujerun da suka yi wa falon ƙawanya na nitse, Tahir na gama shigo da kayan datse ƙofar ya yi ya dawo gabana ya tsaya “Ya ya dai Madam, gajiya ko? Murmushi nayi “Taso muje ki yi wanka” bin bayansa nayi, a cikin bed room din akwai bathroom manne da shi.
Ni na fara yin wankan, ruwa me zafi nayi amfani da shi, wai ko zan samu sauƙin gajiyar da nake tare da ita.
Dama ga jikin ba karfi, da kyar nayi sallah, ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi Tahir wanda idar da sallar sa kenan ya miƙe sai ya tafi ya buɗe, hannu ya ba me kwankwasawsar sannan ya mishi tayin shigowa, muryar mutumin na ji ya ce “Dawowata yanzu kenan, Madam ke ce min ta ji dawowarka, shi ne na ce bari to in kawo maka abinci”.
Godiya Tahir ya shiga yi mishi ya ce “Yanzu dama zan fita in samo mana abin da zamu ci, ka san ni ma na ɗauko Madam” Ƴar dariya mutumin ya yi “A lallai ka temaki kanka”
“Ummulkhairi” Tahir ya shiga kiran sunana.
Na fito da hijab din da na idar da sallah a jikina na gaishe da mutumin me fara’a Tahir ya ce “Neighbour dinmu ne” na ce “Allah sarki” mutumin ya juya “Sai safe laila za ta shigo ku gaisa” na faɗi “Allah ya kaimu”
Ciki na koma na yi shirin kwanciya, na zura rigar barci, Tahir ya shigo “Fito mu ci abinci”.
Sai ya juya na fito da hannu ya nuna min wata kofa ya ce “Ɗauko mana spoon da flate”. Sai da na gama ma kitchen din kallon nazari ba abin da ba’a sa ba na nau’in kayan girki, haka nau’in kayan abinci.
Tare muka ci sai muka kwanta, wai Tahir ya dage tausa yake min, dan in huce gajiyar da ya ja min ga shi bani da lafiya. Sai dai daga tausar bai yi min komai ba muka shiga barci.
Da Asuba sallah kawai na tashi na gabatar na koma na kwanta, dan gajiyar da nake ji.
Sai dai na ji ana taɓa ni, na bude idona a hankali suka sauka kan Tahir, da ke tsaye kaina ya sha wanka yana fitar da sansanyar ƙamshi.
“Zan fita wurin aiki, Ummulkhairi”. Sauri na yi na tashi zaune “Za ka tafi ban baka abin break ba” “Kar ki damu, idan na fita zan karya, ki yi kokari ki dafa ko indomie ne, kar ki ce za ki yi abinci, zan taho mana da abinci.
Ki huta, har ki samu ki warware” kai na gyaɗa mishi, nayi addu’a ya fita ya ja min ƙofar .
Sai da na sha barcina na, karfe sha daya na tashi wanka na soma yi, nayi kwalliya da riga da zane na Atamfa, sannan na shiga kitchen ba kamar yanda ya ce ko indomie in dafa in ci ba, tea na haɗa na komo falo ina kurɓa a hankali.
Knocking na ji ana yi, abin da ya bani mamaki, amma dai na tashi na buɗe, wata matashiyar mace na gani, wadda za ta tasamma shekara 28 amma idan an gaya maka, in kuwa ba ka sani ba, za ka ce bata wuce Ashirin da hudu ko da biyar, dan hutun da ya ratsa ta.
Fara ce, doguwa mara jiki, sanye take cikin bakin material ɗinkin doguwar riga, ta yane kanta da siririn mayafi.
Kwando ne riƙe a hannunta, tana min murmushi, ni ma sannu da zuwa na shiga yi mata cikin murmushin muka shiga ciki, mun gaisa ta turo kwandon gabana, “Ga abinci nan na kawo miki” na yi mata godiya “Sunana Laila, ni ce Neighbour ɗinki, ta wancan flat din, da yake kallon naku”.
Na yi murmushi sai ni ma na gabatar mata da kaina, sunanta da ta fadi na gane matar mutumin jiya ce. Kasa na sauka ina cin abin da ta kawo min, muna ɗan taɓa hira “Na ji dadin dawowarki, kasancewarki musulma kuma Bahaushiya, sauran flat ɗin guda biyu mazaunan su, basu da mata”. Na ce “Allah sarki, ni ma na ji dadin haɗuwa da ke, me kirki da ke”.
Muka yi dariya tare, da ta tashi za ta tafi, na ce zan bi ta in ga wurin nasu. Tare muka fito, sai yanzu na ga wurin da kyau, akwai shukoki masu ban sha’awa da suka zagaye wurin.
Mun shiga wurin nata ina zaune tana girkinta, dan ta ki yarda in taya ta wai in bari in huta gajiya. Ƙarfe ɗaya nayi mata sallama, na ce zan je in yi sallah. Ina idar da sallah,. sai ga ta ta kawo min abinci, dan haka da Tahir ya kira ni sai na ce ba sai ya sawo abinci ba.

Ya dawo muna cin abinci , yake ce min sunan mijin Laila, Ahmad, mutumin kirki ne, na san shi tun Kaduna State University ( KASU) sai kuma yanzu Allah ya kuma hada su anan.
Tun daga ranar Laila bata taɓa fashin kawo min abinci ba, wai mijinta ya gaya mata na samu Miscarriage, ban gama warwarewa ba muka taho.
Aikina shi ne wanka sai in yi Sallah, in gyara wurina, sai ko shiga wurin Laila, kamar yanda ita ma take shigo min.
Mace ce me tsananin kirki, iyayenta mutanen Kano ne, a Kano aka haife ta, kasantuwar mahaifinta maaikacin gwamnati ne garuruwa daban daban suka zauna , sai a ƙarshe aka turo shi Lagos.
Bai jima da yin ritaya ba, yanzu haka suna America tun yin ritayar tasa, yaransu uku, Laila ce babba, sai mai bi mata namiji sai autar su, wannan kenan zamana da laila tun da ta fahimci ina da ilimin addini sai muke zama ina koya mata, ni ma sai nayi amfani da wannan damar na fada mata ina son ilimin zamani, iyakar karatuna sakandare kuma ina so in gwanance a Turanci, sosai take koya min abubuwan da suka shige min duhu, ƙarshe ta bani shawarar shiga wata makaranta Adult Aducation, da ke kusa da mu.
Da na tambayi Tahir bai hanani ba, shi ya karbo min foam, ina jin dadin makarantar, a gida kuma ina da Aunty laila.

Ya kai ni gidan Kawu Attahiru da ke agege, gida ne babba har ya fi gidansa na Kaduna, akwai jama’a sosai, duk wani bahaushe da ke ta wurin gidan Kawun ya mayar gidansu.
Sannan Aunty Kulu tana gyaran Amare wanda ta amsu sosai a garin, wuni mata suke shigowa, har da masu taya ta aiki ta ɗauka.
Wuni zungur nayi a gidan, sai yamma ya zo muka koma gida, na samu an yi min kitso, hada turaren jiki da na daki ta bani, Kawu Attahiru ya bani kudi.
Dana dawo na raba mana turaren ni da Aunty Laila. Dawowata da kwana biyu na soma ciwo, wanda zuwan mu asibiti binciken farko likita ya ce ciki ne, ba abin da nake iya yi ma kaina, Tahir na kula da ni yanda ya kamata, wata biyu shi ma kamar wancan nayi mafarki jini na bi na, shi ma haka ya bare, sai dai wannan da sauƙi ƙwarai, dan da gani sai Laila muka yi bidirin mu. Wasa wasa sai mafarkin jini ya aure ni, da nayi kuma zan tashi cikin jini, gaba ɗaya rayuwata ta canza, da dare ya yi jikina zai gashe kamar wuta, gari na wayewa sai in warware, abin da na lura da shi indai Tahir zai zo da bukatar shi to jikina zai ɗauki mugun zafi, mun je Asibiti, duk magungunan da suke faman rubuto min ba abin da ya canza, tun Tahir na kula da ni har na lura ya canza, yanzu da ya dawo wurin aiki zai yi barci, zuwa la’asar zai fesa wanka ya fita ba zan kuma ganin shi ba sai dare sosai, yana da yawan buƙata, amma an wayi gari baya nema na kwata kwata, sai dai randa rabo ya zo, yana yi kuma yana complain din zafin jikina, sai dai ya yi ta kalallame ni, da tausaya min yake bani da lafiya, shiyasa yake nesa da ni, kuma idan ya zauna kusa da ni ba zai iya riƙe kansa ba.
Kamar na yarda da maganarsa, sai ranar da muna zaune aka kira wayarsa, gaba ɗaya sai na ga ya canza, ya kashe wayar aka kuma kira ya kara kashewa, ana karshen sai ya kashe ta gaba daya, take sai na tsargu, zargi kala kala ya shiga zuciyata.
Bari nayi sai da ya yi barci na sato wayar, kitchen na shiga dama na rike time ɗin da aka kira shi, sunan da na duba Latifa na gani a rubuce, WhatsApp na shiga sunanta na bi na duba chart ɗinsu, ai ina karanta sakonnin da suka gudana a tsakanin su, wanda ko ni matarsa ba zan taba iya zagewa in rubuta mishi wadannan kalaman fitsarar ba.
Ba kunya kwata kwata ba ɗa’a, hotunan sassan jikinta da ta turo mishi ba dadin kallo, sai dai ba fuskarta iya gangar jiki ne.
Zuwa lokacin zuciyata ta gama tsinkewa, na gaza cigaba da ganin abin da nake ganin, hawaye ne ke shatata kan fuskata kamar sakarai ya kunna famfo
Take wani post da na gani yana yawo a kafafen sa da zumunta ya fado min, wai wata tsohuwa ce ke cewa “Kashedin ku da wayar miji, domin ita ɗin kamar albasa take kina bare ta kina hawaye.
Na goge wayar dan na jike ta da hawaye, na lallaɓa jiki ba kwari, na mayar da ita inda na ɗauko ta.

Sai ya zamto tun daga ranar da ya yi barci zan saci wayarsa, abin da kuma zan gani ya hanani kwanciyar hankali, da da ban binciki komai ba, idan lokacin barcina ya yi Tahir bai dawo ba kwanciyata nake in kuma yi barci na, amma yanzu ban iyawa, zuciyata ta din ga sakawa da warwarewa inda yake da kuma abin da yake yi, sa’a ta ɗaya cikin da na samu a wannan karon ya tsaya har ya soma girma.
Wani dare da na gaza barci iya daɗewar sa ya kai sha daya, amma ranar sai sha biyu ya shigo, pretending din da na saba yi idan ya shigo yau zaune ya same ni ina kuka, abin da ya sa shi ya rude yana tambayata jikin ne?
ganin ya ma raina min hankali yasa na ƙi magana, sai cewa ya yi wai meeting ne ya rike shi. A zafafe na ɗago halan da aljanu kake meeting din, cikin mamaki yake duba na dan bai taba ganin nayi mishi tsiwa irin haka ba.
“Me kike nufi da kalamanki?
Wayarsa da ya ajiye nayi maza na suro na buɗe na shiga WhatsApp na lalubo acc din Latifa sai na miƙa masa.
Tun kan ya karba ya fahimci komai.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Dan haka jikinsa ya yi masifar sanyi, ni kuma na soma magana cikin kuka. “Ka rabo ni da iyayena, ka kawo ni uwa duniya ka banzatar da ni.
Kana saɓa ma Ubangijinka, duk da cewa ka sani, amma ka take, Ubangiji ya yi maka ni’ima, ya baka wadata ka mallaki mata har uku na sunna, amma godiyar niimominsa a gare ka, shi ne ka saɓa masa.
Kuma kar ka ce ko ina daga cikin mata masu binciken wayar mazajen su, canjin da na gani a tattare da kai shi ya ingiza ni ga yin binciken. Gobe in sha Allah, zan nemi hanyar garin mu zan bar ka ka ji dadin cin karenka ba babbaka.
Ina zuwa nan na miƙe na soma sauke kayana, cikin karfin hali dan ba wani karfi ne da ni ba, jikina ba kuzari sam.
Takowa ya yi daga inda ya ƙame tun daga fara sauraron kalamaina, kunya ce ke ɗawainiya da shi, ji nayi kawai ya riƙe hannayena na waiwayo na balla mishi harara da jajayen idanuwana da kuka ya rinar da su, hankalinsa ya ji ya ƙara tashi da yanda fararen idanuwanta suka koma, dan da ganin idanuwan ba yau ta fara kokawa da su ba, rashin kulawarsa ga al’amarinta yasa bai fahimci halin da take ciki ba. Sakin hannayena ya yi ya ja baya kan gado ya zauna, dafe da goshinsa kafin cikin wata murya wadda ta fi kama da ruwa dan taushi ya shiga bani haƙuri, da alkawarin ya daina, karo na farko a rayuwarsa wanda ya tabbatar rudin sheɗan ne ya ingiza shi, amma ba halinsa bane.
Ban ce mishi kanzil ba, ina gama haɗa kayana wuce shi nayi na kwanta, jin surutansa na kare kai sun kara min ciwon kai da nake ji kamar kan zai sauka. Saukowa nayi daga gadon na fice dakin, dakin da ba komai sai carpet da labulayya na shiga na murza key.
Na kwanta nayi matashin kai da hannuwana ƙirjina na min suya, ina jin muryarsa yana kiran sunana.
Nayi nayi in tuna addu’ar da zan yi dan samun sauki, amma na kasa tuna komai daga cikin dimbin addu’o’in da na sani.
Sai gefin Asuba barci ya yi awon gaba da ni, muryarsa ta farkar da ni yana kiran sunana, ganin haske ta jikin labulai yasa ni fahimtar ba karamar makara nayi ba, cikin rashin kuzari na miƙe, bathroom din da ke cikin dakin na shiga na daura alwala, da na fito rashin hijab din da zan sa in yi sallah ya tilasta min bude kofar, yana tsaye hanya ya bani na wuce, na je nayi Sallah, idarwata jakar da na hada kayana na janyo, ja nayi na tsaya jin kofar gam! an rufe ta ta baya
kan kujera na zauna na shiga wani sabon kukan yana saurarena, shi ya shiga kitchen ya daho min tea dan shi kadai ya iya dafawa, ko kallonsa ban yi ba, har sha daya na safe muna zaune, na gane ba ko Office ba za shi ba.
Knocking din da ake yasa shi tashi ya buɗe, Laila ce, ganinsa gaisawa suka yi, ya ce ta shigo ta ce A’a tana son magana da ni ne, ina jin su dan haka tasowa nayi, ya dawo ciki, tana tsaye riƙe da kwando, kallona tayi da murmushi a fuskarta “Haba Mmn twince, wannan fuska, ina ga babyn nan shi da kuka ya zo mana”
Murmushin yake na saki ita kuma ta sha mur tana hararata, cikin rage murya ta ce “Oga na gida bai fita Office ba kike zaune haka jemai jemai ba ƴar kwalliya da kamshin da daga ka doso wurin zai tafi da kai, sai tsofaffin matansa sun karbe miki shi.
Dan guntun tsaki na ja “Ke ta miji kike, ni duniyar ce gaba ɗaya bata min daɗi”.
Ta rausayar da kai “Sai hakuri, shi ciki kowanne da yanda yake zuwa. Faten acca nayo miki da naji kina cewa bakinki ba daɗi”.
Na amsa ta godiya ta wuce tana cewa “A daure a dau wanka da kwalliya Hajiyata”.
Da na koma ciki wankan nayi, wanda a yanzu wahala yake min, mai kawai na murza na zura doguwar riga.sai na dawo falon.
Sa’a kawai nake nema in cika wa rigata iska, na sha faten na koma na kwanta kan kujera.

A takaice ranar a nan muka wuni yana gadina,
Bai fita ko nan da can ba.
Washegari ya kulle ni ta baya ya nufi wurin aiki.
Da Laila ta zo tana knocking ƙofar na zo na ce ta zagayo ta window, ta zagayo ta ce “Lafiya?
Na cije lebe “Kulle ni ya yi” murmushi tayi har tana daga gira “Mutanen nan salon soyayyar ku na burge ni” ta fada cikin salon basarwa na wayayyu, dan na san ta fahimci akwai matsala “Abinci na kawo miki”. Na buɗe window ta miko min, na koma na ci.
Da la’asar ya shigo, ya maida kofa ya rufe. Ban mishi magana ba, shi ma bai min ba, na lura ma kamar nauyi na yake ji.
Da daddare yana falo ina ɗaki, na ji wayarsa na ƙara, ba a dauki lokaci ba ya shigo “Ga Haj tana son magana da ke”.
tsayawa ya yi kaina kila yana tunanin zan faɗa mata kamar yanda na saba gaishe ta cikin nutsuwa da girmamawa haka na gaishe ta, ta ce “Tun jiya nake sa wa a kira wayarki, sai a ce min kafiran nan sun ce a kashe take” nayi murmushin jin maganar ta, (wayar tun jiya Tahir ya dauke ta)
amma sai na ce mata “Ruwa ta fada”. Ta ce “Ash sha shi ne ba a nemi wata ba? Na ce “Za a gyara Haj” ta ce “Kuna lfy ko? Na ce “Lafiya lau muke Haj” ta ce “Idan Sodangi ya zo zan ba shi magani ya kawo miki na sammu ne, dan yanzu mutane ba tsoron Allah suke ba, sai ka tashi tsaye da neman tsarin jikinka, da kuma na zaƙi”.
Na ce “To Haj, Allah ya kara girma”.
Na tambaye ta mutanen gidan, sannan nayi mata barka, dan maman Ummi ta faɗa min Usaina ta haihu.
Mun gama wayar na miƙa masa a bar sa, ya juya ya fice dakin. Na kai hannuna na shafi cikina, ni ma dai bana in Allah ya so zan riƙe nawa ɗan, zan samu me ɗebe min kewa, duk da ba wani uban girma ya yi ba na ciko, ramar da ta addabe ni ta sake ni na murje. Sai kuma na koma jin dadi na dacen da nayi da suruka me sona, mu’amalar da take yi da ni bata Suruka da Surukarta ba ce, mu’amala ce irin ta uwa da ɗanta. Kwanciya na gyara na lumshe idona.
A falo ya kwana, ni kuma na kwana a daki, yana gudun ya shigo in tafi ɗayan dakin in kwana a ƙasa.
Washegari ma lokacin tashin sa Office nayi sai ga shi ya dawo, nan ma bai ƙara fita ba, kamar hadin baki irin lokacin da Haj ta kira waya sai ga kiran Ummata, duk kararta ta kasa jure rashin ji na har na kwana biyu, ga halin da nake ciki, dan Hafsa na ba labarin ina da ciki ita kuma ta taka har gida ta fada musu.
Ita ma dai gaisawar muka yi, na ce mata muna lafiya, dan tausayinta da nake ji, bata da juriya kan matsala idan ta same ni, ko bata yi magana ba ramar da za ta shiga yi za ta fallasa abin da ke cikin ranta. Ballantana wannan matsala da nake ciki ba zan iya fallasa ta ga kowa ba, dan idan na fadi na asirin mijina na tona, na san dai tun da na shekara garin nake ma Tahir nacin ya kai ni gida, shi kuma sai ya ce ba yanzu ba sai na warke wannan ramar ta sake ni, dan ba zai kai ni yana laluben amsar da zai bayar na zargin da za a yi masa.

Mun ɗauki tsawon sati guda a haka. Office kadai ke fitar da shi sai Sallah, har na fara murna kila Allah ya shirye shi, sai dai ranar da muka cika kwana tara a haka, ya shiga wanka sai na saci wayar tasa in ga da gaske ya daina din, sakonninta ne kala kala tana mishi magiyar ya zo gare ta, amsar da na ga ya bata Madam ɗinsa ce ba lafiya ko zai zo sai ta warware. Ta ce to ta zo Office ta same shi? Ya ce A’a” kalaman fitsarar da take mishi ya nemi ta turo mishi ba kalaman kaɗai ba hada nude picture ɗinta ta turo , ai ban tsaya tantance abin da nake ganin ba na rufe wayar, na kwanta a falo ina sharar hawaye.
Har ya fito ya shirya, damunsa ake tayi da kiran waya daga wurin aikinsa, sai tsaki yake zabgawa dan ya makara, garin sauri ya manta bai rufe ni ba, na tashi, sai na ga keys a jiki, wani farin ciki ya lullube ni, na koma ciki na suro jakata, wadda dama har yau ban kwance kayan ba.
Hijab na sa sai na fito, na daɗe tsaye ina kallon flat din Laila, kallo irin na karshe, anya idan na bar garin nan ban ma Aunty laila sallama ba nayi wa kaina adalci? Nayi abin da ya kamata dan halak ya yi? Cigaba da tsayuwa nayi ina tunano alheran Laila a gare ni.
Can wata zuciyar ta rada min “In dai kina son barin garin nan, to ki hanzarta bacewa a wurin nan kafin ta gan ki, dan kin san tana ganin ki gudun nan da kike yunkurin yi zai zama tarihi.
Takawa nayi da sauri a kokarina na bacewa daga wurin, tafiya sosai nayi kafin in samu dan acaba, ko a Dutsinma ban faye hawan sa ba, haka na haye na faɗa mishi ya kaini inda zan shiga motar Kaduna, muna tafe ina sakawa ko ya zan yi idan aka shiga Kaduna cikin dare.
Inda wata taxi ke lodi wani dan Union ya kaini, akwai mutum uku a ciki, wanda na nakalci yan kasuwa ne, mutum ɗaya suke jira ya fito daga cikin kasuwa. Sai zuci zuci nake mutumin ya fito dan yanda gabana ke faduwa, hamdala nayi ganin isowar mutumin, an karbi kuɗaɗen mu, cuku cukun direbobi da yan Union shi suka tsaya yi, na jingina kaina jikin kujerar na lumshe idona, ina me jin farin cikin zan ga Babana da Ummata, da ƴan’uwana hada Hafsata.
“Ga ta nan Yallabai” Muryar namiji ce ta ambaci hakan gabana ya yanke ya fadi, nayi saurin bude idona, ban sauke su kan kowa ba sai kan Tahir da ke tsaye ya harɗe hannayensa a kirji.
Shi ma ni yake kallo, cikin farin glass ɗinsa, a kallon da nayi masa na fahimci ransa ya yi mummunan ɓaci. Dan kamashon da ya karbi kayana ya kuma rako ni shi ke yi wa Tahir wannan maganaar. “Lafiya? direban ya zo yana tambaya, “Wannan baiwar Allar, Yallabai ya zo nema”
An yi cirko cirko dan Tahir ya ki magana ni kuma ban fito ba, Direba ya shiga mazauninsa, Tahir ya zagaya dan ni daga karshe nake sai dai ji nayi kawai ya ɓalle murfin motar, hannu yasa sai ya janyo ni waje take na soma hawaye Direba ya fito “Yallabai ya za ka ciro ta, za mu tafi? Dan kamashon ne ya matso ya ce “Matarsa ce, tafiya za tayi bai sani ba” “Subhanallahi”. In ji Direba, take sauran mazan da ke wajen suka dauki salati wani cikin su ya ce “Sai hakuri zaman aure, baiwar Allah”.
Ni dai sai share hawaye nake na ki bin Tahir, dan kamashon ya ciro jakata, “Yallabai ya za a yi da kudin motar da ta bayar?
Ya ce “Ta bar maka” Direba ma ya zaburo “Alh yanzu sai na ƙara zaman jiran wani fasinjan? Wadannan bayin Allah daga Kaduna na dauko su, mutum ɗaya zan cika mu dau hanya.
Hannu Tahir ya zura aljihunsa kudade ya ciro da bai tsaya dubawa ba ya mika wa dan Union, ya kama godiya kamar zai ari baki, “Mu je Malama, Tahir ya ce min yana kara daure fuskarsa, hannuna na ji ya fincika ganin bani da niyyar bin sa ta lalama bai tsaya ko’ina ba sai inda ya adana motarsa, buɗe ta ya yi ya tura ni ciki, ya maida ya rufe ya zagaya zai shiga, dan Union ya iso “Ga jakarta Alh” Boot ya buɗe mishi ya jefata ciki.
Da mugun gudu ya finciki motar masifa ya fara min, “Ke yanzu da an bar ki haka za ki isa har Kaduna zaune jikin kato?
Sai kuma ya sassauta murya “Me ya ja miki wannan aikin? Kin san tun fitowarki mala’iku ke tsine miki, kin fito bada sanin mijinki ba? Meye ribar ki idan kika isa gaban iyayenmu da wannan bakin labarin, ke fa Malama ce Ummulkhairi memakon guduwa ki bar ni addu’a ya kamata ki taya ni, abu daya zan faɗa miki ki ji tsoron Allah, daga yau zan daina rufe ki, amma ki sani igiyar aurena na kanki, ban Kuma yarda ki taka ko’ina da ita ba.
Yanzu da kin samu nasarar gudu ba ki tunanin wani abu ya same ki a kan hanya? me za ki fada wa Ubangijinki.
Sosai maganganun suka ratsa ni tsoron Allah kuma ya cika zuciyata, sai na ƙara sautin kukana.
Da muka isa ma shi ya ciro ni dan kin fitowa nayi, har daki ya kaini ya kuma ki fita, na takura kwarai da zaman namu wuri ɗaya sai na tashi na shige bathroom, da na rasa abin yi sai na ji sha’awar yin wanka ta kama ni, Ruwa me zafi na haɗa na sa turarukan wanka masu dadin ƙamshi wanda har na manta rabon da in yi hakan na kwanta cikin ruwan nayi wanka me kyau, na wanke sumata, na sha mamakin yanda gashin ya kara haukan cika da tsawo, dama an ce gashi bai faye zuwa inda ake lailayarsa ba, ya fi hauka inda ba a damu da shi ba.
Tawul na daura, na kuma daura karami a kaina ina goge sumata, ban damu da ganin Tahir a zaune bakin gado ba kan mirror na wuce, mayukana da na manta rabon da in shafa su na shiga shafawa, na fesa turare kadan, hand dryer na kunna ina busar da gashin kaina kafin na shafe shi da mayuka.
Tahir wanda ke zaune ya yi mugun dauke wuta, yaushe yarinyar nan ta koma haka? Wai ma watanni nawa kenan rabonsa da ita me ya dauke mishi hankali da bai lura da canzawarta ba, kirjinta ya dada bunkasa, ta kara ajiye mazaunai.
Taku ya yi zuwa inda nake zaune ina ta je sumar tawa wadda ta sauka kan kafadata. Haɓar mutum kawai na ji kan wuyana ta mudubin muka haɗa ido na bata rai, hannuwansa yasa ya rungume ni, na shiga kici kicin kwace jikina, ya gwada min kashi ya jefa ni gadon, duk da rashin karfin jikina dambe na shiga yi da shi sosai dan kwatar kaina, shi kuma ya yi amfani da karfinsa ya gamsar da kansa da kyau. Kafin ya tsallake ni ya shiga bathroom, hawaye ne ke ta gudu bisa kuncina, har ya fito, tawul ya wurgo min “Ɗaura ki mike”.
Na bi tawul din da harara ina cigaba da kukana, cikin kukan barci ya yi awon gaba da ni, mafarkin da nayi jini na bin jikina yasa ni farkawa a firgice, sai zufa ke wanke min fuska, jikina ko’ina rawa yake.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Ban ƙara shiga tashin hankali ba sai da na ji abu ta kasa na yana bi na, dubawar da zan yi jini na gani, kuka na fasa na sauka kasa, ciwon mara ya sauko min ina ta mukurkusu na ji muryar Laila ta window da ta saba leƙo ni, nishin da ta ji yasa ta tambayar me ya faru na ce “Ki zagayo kofar a bude take” ai kuwa sai ga ta da gudunta ta shigo ta rungume ni, tana fadin “Me ya same ki? Cikin zafin ciwo na ce “Ina jin bari zan yi”
Wayarta ta janyo jikinta na rawa, kawarta Dr Fati ta kira, wadda na san ta saboda yawan zuwan da take wurin Aunty Laila, halin da nake ciki ta fada mata ta kuma nemi taimakonta.
Muna nan ina fama “Dr Fatin ta iso ta shiga taimaka min, cikin hukuncin Allah na haihu da Namiji, kuma sannan ne Tahir ya iso daga kiran da Aunty Laila tayi mishi a waya. Ya shigo ya iske Dr Fati tana taimaka min zan shiga bathroom, Laila ta nade babyn a zanena, hawaye hawaye shabe shabe take yi dan bai zo da rai ba, ta mika wa Tahir, duk da bai iya daukar jarirai ba haka ya fito falon, ko da yake bakwaini ba dan karami bane, sambalele ne. Bai iya cewa Aunty laila komai ba wadda ke kuka da gaske, shi ma ban da yana namijin duniya da kukan zai yi da alhakin yarinyar nan? Me yasa ya biye wa zuciyarsa ya yi ta cuta mata, bayan ya rabota da iyayenta? Ya ƙara duban yaron tausayin kansa na ƙara kama shi, yau ya samu abin da ya dade yana fatan samu amma kuma ba rai. Wayarsa ya zaro Hajiyarsa ya kira, jin yanayin muryarsa yasa ta ce “Lafiya? Ina Ummu” wata iska ya furzar me zafi, idonsa na kan babyn, ta haihu Haj, sai dai yaron bai zo da rai ba, dan bai kai watannin haihuwa ba”. Kukan da Haj ta fasa, ya kara jagula zuciyarsa, cikin kukan ta ce “Ka faɗa ma iyalan Attahiru, su kula da ɗiyar mutane, ka da ta mutu, a garin kabilu, da ta yi kwari ka kawo min ita, ko har sai yaushe zan ga kwanka? Ina take ka bani ita.
Ya lumshe idanuwansa “Wanka ake mata”. Sai yanzu ya tuna ya kamata ya sanar ma uban goyon nasa.
Tare da mutane Kawun ya iso, da Aunty Kulu, wadda ta same ni kwance bayan yin wanka na, zama tayi daf da ni ta cire kaina ta dora saman cinyarta, “Sannu kin ji yarinyata, jarabawa ce, kowane bawa da irin jarabawar da ake mishi, mu kin ga ma ko barin ba bamu taba yi ba, ke kuwa har ga dan ma kin gani, Allah yasa masu ceto ne, Allah ya kawo rayayyu”.
Su Aunty Laila suka ce “Amin”. Ita da Dr Fati wadda za ta wuce, sai na ji tausayin Aunty Kulu ya kama ni. Aunty Kulu na ma Dr Fati godiya, ni ma na ɗago nayi mata.

Suna tsaka da rarrashina in tashi in sha tea da Aunty laila ta haɗa min, Tahir ya shigo duk ya yi wani iri, kallona ya yi kafin ya maida duban ga Aunty Kulu, “Aunty, Baba, ya ce da ita za ku tafi, za ta fi samun kulawa a wurinki”
Ta ce “Kwarai kuwa ni ma nayi tunanin haka”.
Suka shiga haɗa min kaya, Anty Laila na share ido wai za ta yi kewa idan na tafi, Aunty Kulu na bata haƙuri.
Mijin Aunty Laila shi ya dauke mu a motarsa, Tahir ya tafi sawo magungunan da Dr Fati ta rubuta min.

A bedroom dinta Aunty Kulu ta yi min masauki, bata yarda an gyara min daki ba kamar yadda Kawu ya ce. Kwanciya nayi kan tattausan gadonta wanda yake makeke ne, sai kujera guda daya a cikin dakin, gefe ɗaya babbar ma’ajiyar zuba kayan sawa ce, bed side, sai kofar toilet, ɗaki ne yalwatacce yana fidda kamshi me sanyi.
Sai bayan sallar isha’i, lokacin har na kare cin abincin da Aunty Kulu ta kawo min, Tahir ya shigo har bedroom din, ganin sa sai na tashi na zauna har ya yo wanka ya canza cikin kananun kaya, daddaɗan ƙamshinsa na tare da shi. Hannunsa ɗaya na soke a aljihun wandonsa, dayan na rike da leda, ledar ya ajiye saman bed side drower “Sannu ya jikin? Ga maganin nan, ya dan yi wuyar samu ne, sai yanzu da na fito na samu”. Shiru na mishi dan wani kishi da ya taso min ganin yanda ya yi kyau, na san shi a daɗin shi da aka ɗauko ni, dama ce ya samu ta sheke ayarsa, kila ma gidan zai rika kawo ta, suna kwana abin su.
Ai da yin wannan tunanin sai na ji hawaye, kwanciya kawai nayi sai na juya mishi baya “Ki tashi ki sha maganin” ya fadi yana bude ledar, yi nayi kamar ban ji shi ba, gajiya ya yi ya fita, suka dawo tare da Aunty Kulu, ita ya mika wa ledar tana cewa in tashi na tashi na karɓa na sha sai na gyara kwanciyata, fita tayi shi kuma ya zauna. Bata jima ba ta dawo ɗauke da wani flate “Tashi Ummulkhairi” tun ban tashi ba ƙamshin abin da ke cikin farantin ya sa ni hadiyar yawu ba shiri, Flate ɗin ta miƙo min Nama ne, wanda da na ci sai da na rasa gane gasa shi aka yi, koko farfesu ne, ya yi matukar dadi kamar zan tsinke kunnena.
Ni fa Aunty, ina nawa?
Tahir ya fadi yar dariya tayi “A’a wannan ba gyaran masu jego ne”. Sai ta fita, ya dan duƙo gabana ba za ki san mini ba? Flate ɗin gaba ɗaya na tura mishi “Dauki abinki ki ci, da wasa nake miki”. Sai da ya maimaita sai na ɗauka, na ci sosai na ajiye Flate ɗin, mun ɗauki akalla mintuna talatin sai ya mike a hankali ya fita ya ja min ƙofar.
Da ganin fitar sa sai na tashi zaune na jingina jikin gado, ƙirjina har harbawa yake dan takaicin da ke cin raina.
Aunty Kulu ta shigo “Baki kwanta ba? Ta tambaye ni kai na daga mata “Maida hankali ki yi barci” na ce mata To” ta shiga cire shiryayyar kwalliyar da tayi, ta fada toilet, ta fito ta shiga shafe shafe, shafa wannan goga wancan, ni dai baki na sake ina kallon gayun tafiya wurin maigida. Wata kyakykyawar rigar barci na zura, nayi saurin rufe idona, ina saƙa abubuwa da dama cikin raina, ta fita ta ja min ƙofar, ban daɗe ba barci ya yi awon gaba da ni.

Asubar fari sai ga Auntyn ta shigo tana tambayata yanda na kwana ina cewa lafiya lau” ta ce “To koma ki yi kwanciyarki” na ce “To”
Ƙarfe shida na safiya ta ce in tashi in yi shirin wanka. Ita tayi min wankan, ta kuma gasa min jiki sosai, sannan ta sa wani ruwan da ta zuba wani farin ruwa ta ce in shiga sai da ya soma sanyi ta ce in fito, wani ruwan ta kuma haɗa min ta zuba turarukan wanka ta ce in yi wankan sabulu. Da na fito Room heater ta kunna dakin ya dauki dumi, na shirya ta dawo wata humra ta miƙo min “Shafa wannan, ki fito ki karya.
Zama tayi ta tasa ni sai da na ci na koshi, Tahir ya iso wanda Aunty tayi ta fadin mamakin da ta ji na isowar sa yanzu a cinkoso irin na Lagos.
Tana kuma ta korafin me yasa bai bari sai ya tashi gudun makara a wurin aikinsa.
Murmushi kawai ya yi yana tambayarta yanda na kwana, ganin idonta na gaishe shi, sai da ta fita ya ciro wayata a aljihunsa, ya miƙo min “Ga wayarki nan, na san mutanen gida za su so magana da ke”.

Mutanen Aunty Kulu suna ta shigowa daga makota, har zuwa abokan mu’amalar ta, haka mutanen Kawu Attahiru, da abokan Tahir na wurin aiki.

Ranar da nayi kwana uku da daddare ya shigo ya same mu ni da Aunty ina mata kuka, ya karasa shigowa cikin dakin hannayensa zube cikin wandon kayan sanyin da yake sanye da su, fararen riga da wando ne sakar ƙasar Jordan, kasantuwar an fara sanyi. Tambayar me ya faru ya yi Aunty Kulu ta ce “Ka san saboda ba yaron, nonon sun cika, shi ne suka dame ta”.
Juyawa kawai ya yi “Bari a samo magani Aunty”.
Shudewar wasu mintoci ya dawo, ni kaɗai ya samu, har lokacin ina goge hawaye, ɓare maganin ya yi ya miƙo min hada ruwa, na karba na sha, Mu gani, in ga yanda suka yi”.
Ya faɗa yana wani murza hannayensa, tura baki nayi sai na miƙe, a hankali nake takawa, dan gudun motsi me karfi, zafi suke min, na hau gado ba za ki nuna min ba” ya fadi yana duƙowa inda nake kwance, ban yi magana ba sai na cigaba da goge idona.
Ya ce “Zan tafi in kwanta” “Maimakon in yi magana wani kukan na saka “To ina ganin ba nonon kadai ke damunki ba”.
Hannuna na daga “Ni ka tafi kar ka bata mata lokaci” “To! Ya fadi yana wani dan malalacin murmushi, sai ya zauna a kujerar da ke cikin dakin, har Aunty ta kuma shigowa “Allah Sodangi, har yanzu ba ka tafi ka kwanta ba? to mu za mu kwanta. Daga kansa ya yi daga kan wayarsa “Ai zan tafi ta sa kuka, wai bata son tafiyata, dan kar in tafi in je tadi”. Wani zaro ido nayi jin zancensa kunyar Aunty Kulu ta dabaibaye ni, kudundune jikina nayi “Wane irin zance kuma? Mutun me mata har uku, ko kin manta da abokan zamanki su biyu? Jin zancen Aunty yasa shi saurin cewa “Ni ma dai shi na gani” “Tashi maza ka je ka kwanta” ta ba shi umarni ta kuma dauki abin da ya kawo ta sai ta fice.
“Na tafi Ummulkhairi”. Ban magana ba, sai dai yana ficewa na soma hawaye.
Aunty ta dawo, kusa da ni ta zauna, “,Me kike yi haka? Ko so kike a mayar mishi ke? Saurin girgiza kai nayi ina share hawayen, Tahir wanda bai wuce ba yana tsaye jikin ƙofa, ya girgiza kai sannan ya bar wurin.
Na kwanta lamo bayan fitar Aunty Kulu, kafin gwanin iya sata ya sace ni.

Ranar da nayi kwana bakwai da haihuwa sai ga Yayana Sani, ya taso matarsa Aunty Rahma wai sun zo duba ni. Maimakon murna kuka na tasa shi ina mishi, ido kawai yasa min yana kallo, Aunty Rahma tana ciki, wurin Aunty Kulu. Shi kuma yana zaune a shiryayyen falon Kawu Attahiru, inda mutanen gidan ke ta shigowa suna gaishe shi. A haka Tahir ya shigo ya iske mu, da alama dawowar sa kenan daga wurin aiki, dan tun ranar da nayi ta mishi kuka, washegari ya dawo gidan da zama, dan dama akwai dakin shi wanda aka shirya komai, duk da ba ma Lagos ɗin ya cika zuwa ba.
Sannu da zuwa ya shiga yi mishi cikin matukar nuna surukuta, sai dai da ganin yanda yake yawan kallona na gane a tsarge yake da ganin kukan nawa yana tunanin ko kararsa na kai.
Yaya Sani ya dube ni “Indai idan na zo wurinki haka za ki tasa ni kina min kuka, ba zan kuma zuwa ba”.
Saurin soma share hawayen nayi da bayan hannu “Yawwa, ko ke fa, Ummun Ummanta”.
Kwana ɗaya, Yaya Sani da matarsa suka yi, da za su tafi ma muna Sallama da Yayan a falon Kawu daga ni sai shi, kudade na ciro a cikin jikina “Ga shi Yaya Sani, ka kai ma Ummata” Duban su ya yi “Na mene ne? Na ce “Masu zuwa ne, suka bani” “To ki bar su za su yi miki amfani” wani kukan na soma mishi ya ce “To ko dai akwai wata mas’ala ne a zaman naku? Saurin girgiza kai nayi To ki daina kuka, ko so kike in je in ce wa Umma, tun da na zo kuka kike”. Kan na kuma girgizawa, “To zan kai musu dubu sha biyar, su raba su uku, hada Baba, da Gwoggo. Ki riƙe sauran a hannunki, ga ma wasu in kara miki. Ya ciro kudi a aljihu ya miƙo min, na ce “Na gode Yaya”

Washegarin tafiyar su, muna zaune da Aunty Kulu a falonta, fruits din da ta yanka min nake sha, dan koda yaushe cikin bani su take.
Bata daɗe da shigowa gidan ba, kuɗaɗen da akayi ciniki da bata nan aka kawo mata take kirgawa, Tahir ya shigo da sallama, kujerar da ke nesa da wadda muke zaune ya zauna, Aunty na mishi sannu da dawowa ta shiga kiran sunan ɗaya daga cikin masu aikinta, ta iso cikin sauri umarni ta bata ta kawo abincin Tahir, ta kai mishi dakinsa.
Ya ce A’a ta kawo mishi nan. Ya harari inda nake zaune “Ke ke shagwaba yarinyar nan Aunty, ga ta zaune, sai mai aiki ta kawo min abinci”. Daina lissafin da take tayi ta dubi gefenta inda nake, “Allah sarki bata gama warwarewa ba”
Ya ce. “Haka ne, bar mata ma garin zan yi gobe”, da mamaki Aunty ta dube shi. “Ina za ka?
Ni ma fakare nayi dan jin inda za shi, “Hutu na samu na wata daya, shi ne nake son in wuce Kaduna, zuwana na karshe nayi cinikin wani fili, ina son in gina ma kowaccen su Part ɗinta”
Ji nayi hawaye na min zuba tuna tsawon lokacin da na ɗauka ba tare da na je gida ba, Aunty Kulu tana ta mishi addu’a sai kuma ta juyo ta dube ni “Ah kukan me kike? Ban magana ba cigaba nayi da share hawayen “Ikon Allah, tafiyar da zai yi kike ma kuka, in ya zauna to me zai miki? Kunyar maganarta na ji na mike na shige bedroom dinta kwanta, sai ga ta ta shigo ta zauna tana rarrashina, “Kyale shi, ya yi tafiyar sa Ummu, tafiyar ma za ta yi mana daɗi, mu yi gyaran mu a tsanake”. Irin maganganun da tayi ta gaya min kenan.
Kuma ko a safiyar da zai wuce, da nayo wanka dan yanzu na iya, Atamfa ta kawo min, wadda ta sha dinki me kyau, ta ce in sanya, sosai ta karɓe ni, ita ma da ta dube ni sai da ta murmusa Jegon nan ya karbe ki Ummulkhairi” sunkuyar da kai nayi mayafi ta miƙo min “Je ki kuyi sallama da mijinki na ga har sun yi sallama da malam
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Na ce “Zai shigo, idan zai wuce”. Ta ce “Kul yi yanda na ce” jikina ba karfi na miƙa hannu na karɓi mayafin sai na fita. Tunda ya dawo ban taba bi ko hanyar dakin ba.
Ina ƙwanƙwasa ƙofar ya ce a shigo, na murɗa na shiga da Sallama, zaune yake yana kurbar tea, wando ne kawai a jikinsa sai farar singlet. Ganin kayan da ya ciro ya barbaza a ko’ina, yasa na shiga kintsa su, na haɗa mishi wadanda zai yi tafiyar da su dan ya ajiye su wuri guda, na gama na shiga kintsa dakin, ji nayi an janyo ni sai na fada kansa, ba ki iya gaisuwa ba ko? Ban magana ba sai tura baki da nayi “Kukan me kike jiya? Maimakon amsa kuka na kama mishi “Lallai yarinyar nan, wai yaushe kika zama shagwababbiya komai kuka? gane ba zan yi magana ba yasa ya shiga yamutsa ni ina mishi kuka “Tafiyar da zan yi take sa ki kuka? Ba ki ji me Aunty ta ce ba ko na zauna ba abin da zan miki. Ko abin kike so? Da sauri na shiga girgiza kaina sai ya ci serious “Ki yi hakuri to, kamar yau za ki ga na dawo, ki yi ta min addu’a kin ji? Ni ma zan ta miki Allah ya ba ki lafiya”.
Maganganu masu daɗi ya yi ta gaya min, sai na ji zuciyata tayi sanyi daga haushin sa da nake ji tun gano sherin da ke tsakanin su da Latifa. Mun dade tare har lokacin tafiyarsa ya kusa, dan jirgi zai bi, muka fito ya rufe dakin ya miƙo min key, har inda motarsa take nayi mishi rakiya bayan sun yi Sallama da Aunty Kulu. Wucewarsa komawa daki nayi na hau gado, lamo nayi, ina tunanin rayuwa.
Muryar da na ji suna gaisawa da Aunty Kulu ta sa ni bude ido ina duban ƙofar, “Wuce ciki ki same ta, ina jin ko tayi barci bai yi nisa ba” na tsinkayi muryar Auntyn, ta shigo da Sallama, wajen kafafuwana ta zauna yayin da nake tashi zaune, “Ka ga yar gatan, Aunty kina lunkume ta adana ki”.
Murmushi nayi “Kina dai yi min tsiya Aunty Laila” “Ba tsiya ba ce Allah, na ga ma kin sha kwalliya, an sa Atamfa ko yau za a maida mahaifa? “Kai Aunty Laila, kwanana goma fa kike min wannan maganar”. Ta ce “To ai ke ɗin ce, kullum kamar matar limamin Madina, ba ki da aiki sai saka dogayen riguna, kamar wacce aka yi wa gori”. Rausayar da kaina nayi “To dan Allah ya zan yi, tun aure na, kayan auren suna nan, a Kaduna ban san ko’ina ba ballantana in ce zan kai ɗinki, shi kuma bai ce min in kawo akai ɗinkin ba. Amma yanzu da na dawo za ki raka ni in bayar da dinkunan, dan tun zuwa na garin nan, kin san komai, ciwo ne ya dabaibaye ni”
Wani kallo take min baki sake “Kina so ki ce tun aurenki kayan auren suna nan ajiye? Na gyaɗa mata kai tayi shiru cikin tunani, wayarta da ke cikin jaka ta ɗauki ƙara ta ciro ta tana kokarin amsawa, Ahmad ne mijinta, ya ce yana waje. Miƙewa tayi tana shaida min abin da kenan, har falon Aunty aka shigo da shi, ya ɗan jima kafin suka tafi tare, txt ta turo min bayan wucewar su, ta ce akwai zancen da take so muyi sai ta dawo.

Muna waya da Tahir sosai bayan tafiyarsa.
Ranar da ya yi sati guda da barin Lagos, tun wayar safe da muka yi ban ƙara jin sa ba, sai dare har na kwanta ya kira na ce “Yau shiru?
Ya ce “Ƙanƙara ya tafi”. Muna yar hira ina zabga hamma, da yanayin yanda nake magana yasa ya ce “Mu kwana lafiya, yarinyar nan barci kike ji”.

Da safe nayi wanka ina saka kaya, kiran Haj mahaifiyar su, Tahir ta shigo wayata. Na ɗauka da murmushi a fuskata, bakin gado na zauna ina gaishe ta, yanayin yanda na ji tana amsawa yasa ni tunanin Lafiya, ta ce “Ina fata Ummulkhairi ba za ki daga hankalinki ba, ki yi hakuri ki danne, dan kishiya bata da dad’i, amma ki duba wasu kika tarar, ki yi hakuri dan girman Allah.
In banda taruwar da aka yi kaina, da tun jiya da ya iso ya warware auren da ya je aka dauro mishi ba tare da sanin kowa na shi ba”
Mamaki da faɗuwar gaba suka sa na kasa tambayarta makamar zantukan da take yi, wadanda nake ji suna min kama da almara. Har saida ta ce “Kina ji na Ummulkhairi? Da ƙyar na bude bakina da nake jin ya min nauyi na tambayeta “Ban gane maganganun ba Haj, Tahir din ne ya yi aure? ” Yanzu dama bai sanar miki ba? Mu ma jiya da ya zo yake faɗi, wai shekaranjiya”.
Wani haƙurin ta shiga bani, wanda na gwammaci da ta ƙyale ni in ji da halin da na tsinci kaina. Ina ajiye wayar Haj, gado na fada, wani irin yanayi nake ji wanda na san sai wadda aka yi ma kishiya ta san shi.
A haka Aunty Kulu ta shigo ta same ni, zama tayi kusa da ni “Ki yi hakuri, Ummulkhairi”.
Kallon mamaki na bi ta da shi watau su sun sani, kamar ta san tunanina “Jiya da daddare Sodangi ya kira ni ya gaya min, ya kuma roke ni, in rarrashe ki, Kawun ku ma ya turo ni in ba ki haƙuri.
Wani irin aure ya yi irin na bariki, ba wani na shi da ya sani, sai da aka ɗaura ya isa ƙanƙara yake faɗi.
Ajiyar zuciya na fidda ban yi magana ba, ganin duk iya kokarinta ban ce kanzil ba yasa ta kira Aunty Laila a waya ta shaida mata ta ce ta kira ni ta bani baki, maimakon kiran sai ga ta ta zo da kanta suka haɗu ita da Auntyn, duk maganganun da suke gaya min sauraren su kawai nake ban ce uffan ba. Aunty Laila ta ce “Dagewa kawai za ki yi ki gyara kanki, ki san ke wace ce, ba wata kishiyar da za ta tada miki hankali”.
Aunty Kulu ta ce “Shiyasa nake so ta kwantar da hankalinta ta bani hadin kai.” Ta tashi ta fita Aunty Laila ta bi ta da kallo, sai da ta ja kofar, sai ta fuskanto ni “Maganar da na ce za mu yi, Ummulkhairi tun haduwata da ke Allah ya haɗa jinin mu, nayi imani tsakani da Allah kike tare da ni, kamar yanda nake tare da ke dan Allah.
Na ce “Haka ne” ta cigaba “Ina so mu yi magana ta gaskiya, ki ɗauka kamar za ki gaya wa Yaya Sani, dan kin san in zai cuce ki, to kenan zai cuci kansa.”
Na ce “Ina fa jin ki, Aunty Laila, tsakanin mu ai amana ce da kauna ta gaskiya” ta ce “Yawwa so nake ki gaya min yawan Miscarriage din da kike ba ki ganin komai, ko jin komai? Dan kin ga duk a sakamakon gwaje gwajen da ake miki koyaushe ana tabbatar da lafiya kike ba wata matsala da ke haddasa miki hakan”.
Ajiyar zuciya na fidda “Humm, Aunty Laila yanzu saboda wannan tambayar kike ta wannan zagayen zagayen da kwane kwanen? Na gaya mata duk sa’adda nayi mafarki jini na bi na, daga bayan nan na hakakke indai Tahir zai kwanciyar aure da ni to zan yi mafarki ina yin mafarkin kuma zan tashi cikin jini”. Kai ta girgiza Sai kuma tambaya ta biyu, dan Allah ɗan zaman da kuka yi da kishiyoyin ki ya mu’amalar ku ta kasance? Maimakon in fara da mu’amalata da kishiyoyin nawa kamar yanda ta nema sai na faro mata tun fara neman aurena da Tahir ya yi, har zuwa auren mu, zamana a kankara, na gangaro komawata Kaduna, da irin zaman da nayi, har yanda ta kasance min a Lagos, yanda nake fama da matsanancin zafin jiki hakan yasa dole Tahir ya hakura da ni, idan kuma ya dage sai ya yi a hakan za ki ga rabo ya shiga ranar da ya ƙara kuma sai ki ga nayi bari.
Ga kuma matsalar kasala da ta sanya ni gaba, ban iya mora wa kaina komai”.
Ta ce “Ban katse ki ba, Ummu to kin ga wadannan suna daga cikin abubuwan da na nakalta a zaman ku, na ce ba karamin so mijinki yake miki ba. Yanda ba ki iya hassala ma kanki komai daidai da sharar ɗakinki sai na shigo na taimaka miki, za ki iya wuni ba ki yi wanka ba, amma duk ya hakura da ke a haka, alhali ga matansa can har biyu a gida” na ce “Haka ne” amma a raina na ce. Da ya kyale ni ai ba ki san tashin hankalin da ya haddasa min ba, yanzu kuma dan dan karan wulaƙanci kishiya ya min bai ko gaya min ba”.
Ta ce “Ina jinki”. Na cigaba “Kuma matsalar zafin jiki ko da rana Tahir ya zo da bukatarsa jikina zai dau zafi, rashin gyara kuma wallahi da ba haka nake ba ina iya kokarina wurin tsafta, amma sai na wayi gari daidai da wanka kan dole nake yinsa” na cire dankwalina “Sumata na manta rabon da in taɓa ta sai ranar da zan yi barin nan, ko cikin nan da ya kai yanzu, tun samun sa, Tahir bai ƙara zuwa da buƙatar sa ba, sai ranar da ya zube, na rufe fuskata da hannuwana “Kar fa ki ce ina ta miki rashin kunya Aunty Laila, abubuwan ne suna damuna gami da daure min kai, na rasa hanyar warware su”.
Wani kallo ta min sai ta tashi ta fice, ta jima suka dawo tare da Aunty Kulu, wadda na san yanzu cikin aiki take duk da tana da yara masu yi, ta kan yi wa mutane na musamman waɗanda suka ji suka gani za su biya ko nawa ta caje su.
Zama tayi Laila ta warware mata matsalata kamar yanda na shaida mata. Ni kam boye fuskata nayi dan kunyar Auntyn, da gamawar Laila ta dora da cewa “Na saka ki cikin maganar nan, Aunty dan ki taimaka ki isar ma Kawu, a cikin sanin da Allah ya ba shi ya taimaki rayuwar Ummulkhairi domin duk me hankali zai gane inda matsalar take”.
“Kwarai kuwa Laila”. Auntyn ta faɗa tana jijjiga kai “Duk hada laifin, Ummulkhairi tun zuwanta ya kamata ta maida gidan nan gidan su, da tuni cikin hukuncin Allah an gano matsalarta, to bata zuwa in ba Sodangi ya dauko ta ya kawo ta ba, su kuma tafi tare”. Laila ta langabe kai “Ki yi mata uzuri Aunty wadda bata da kuzarin yi ma kanta wanka ko share tsakar ɗakinta ina ta ga tunanin zuwa wani wuri? makarantar da take zuwa ita kadai take lallabawa ta je kuma Allah yasa har take fahimta.
Aunty ta ce “Shi kenan, bari in je in samu, Malam da izinin Allah matsalarki ta zo ƙarshe, Allah dai ya raba mu da sharrin makiya da mahassada”.
Laila ta ce “Amin” Auntyn ta fita.
Ta ɗan jima sai ga ta ta dawo, Taso mu je wurin Malam”. Na miƙe ina neman hijab, ta dubi Laila “Har ke ma taso mu je”. Dan haka mu ukun muka rankaya bisa jagorancin Aunty.
Kishingide yake akan darduma ya ɗora hannunsa kan tintin, cikin nutsuwa muka shiga bayan ya amsa Sallamar mu, muka zube daga nesa muka gaishe shi ya tashi zaune ya fuskance mu,
“Na ji matsalarki, Ummulkhairi wurin Maijidda, na ce kina yin azkar din safiya da maraice kuwa, da addu’o’in da muka samu daga fiyayyen halitta, da karatun Alkur’ani? dan da muka je neman aurenki ana ta fadin Tahir ya yi dace da mace ta kwarai, me tarin ilmin Addini, ko da dai ko kana yi ba za su hana idan Allah yaso ya jarabceka ba”. Da ƙyar na bude baki dan nauyin sa da nake ji na ce “Duk yadda na so yi tun zuwa na garin nan ban iyawa, sai ma in manta” kai ya gyaɗa “Allah ya shige mana gaba, Maijidda samo min ruwa a dan kofi” ta mike ta fita cikin sauri, da ta dawo addu’a ya dauki tsawon lokaci yana yi, kafin ya ce in taso in karɓa na miƙe har ina harɗewa na karbo ya ce in sha da Bismillah na koma wurin zamana na shanye ya ce “Za mu yi ta yin addu’ar nan, har tsawon sati guda, Maijidda dubo mun ganyen magaryar nan ki kuma sa a nemo min Dan Bello (babban yaronsa ne) ta fita cikin sauri ya ce Mu ta shi mu tafi, mu ka yi mishi godiya, ni da Aunty Laila, Albarka ya yi ta sanya mana ya ce Mu riƙe abotar mu, wadda muka ƙullata domin Allah.
Mun fita Aunty ta dawo ya dube ta “Tahir ya gagara shi ne za a sabauta baiwar Allah, addu’o’in da nake ba Tahir su zan bata In sha Allah, Allah zai warware al’amarin.
Aunty Kulu ta ce Amin, Malam, Allah ya kara girma” Isowar ɗan Bellon Aunty Kulu ta bar falon umarni ya ba shi ya tattaro mahaddata da ke karatu a makarantar Malam ɗin, za su fara saukar karatun Alkur’ani har tsawon sati guda.

“,
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

*Ina wacce rama tayi wa katutu take so ta murje* *akwai mafita in sha Allah *Abincin mu na yau da kullum su za ki haɗa da kanki*
*ki ciko ki yi ƙiba ki zo mu sa labulai*

 

Muna komawa ni da Aunty Laila, falon Aunty muka zauna ta ce “Kayan naki fa yaushe za mu kai ɗinki? Kaina na kwantar a bayan kujera, sai na girgiza kai “Idan dai an kara kwana biyu zan tambayi Kawu fita, sai in zo mu kwasa mu kai” ta ce ” Hakan ma ya yi, amma dan Allah ina so ki cire damuwa a ranki ki yi hakuri, Aunty za ta gyara ki dan h……..
Shigowar Auntyn yasa ta yin shiru Flate ɗin da ke hannunta ta ajiye gabana, ƙamshin ya daki hancina fish wit vegetables spaghetti ne, “Ga shi nan ku ci ke da kawarki”. Ta dubi Laila “Ki yi kokari ta ci”. Ta ce “In sha Allah Aunty” ta juya ta fita, me aikinta ta kawo abincin rana, sa’adda Aunty Laila ta kai kifin nan bakinta sai ta runtse ido “Kai gaba ɗaya matar nan tayi, anya wannan kishiyarta ba ƴar rakiya za ta zama ba? Murmushi nayi ko dai in sa miki waigi Aunty Laila? Hararata tayi “Meye nufinki santi nake?
Na ce. “Da fa? Me aikin ta kuma shigowa
da yankakkiyar kankana, ta ce “Aunty ta ce kina gamawa ki sha” na daga mata kai, Aunty Laila ta ce “Matar nan ta san ta kan gyara, kullum daga fruits sai vegetables take ba ki”. Na ce “Kuma kullum sai ta yi min kunun Aya na musamman wanda ya ji kwakwa da dabino da madara”. Ta ce wadannan ai su ne gyaran, ba kinshe kinshen magungunan da ba ka san ingancin su ba”. Na ce “Akwai masu kyau, har kin tuna min da wata matar abokinsa da ta taba kawo min ziyara lokacin da ina Kaduna, ta bani magani. Nan na kwashe komai, labarin yanda muka yi da Haj Shema’u na gaya mata.
Na kara da cewa a lokacin sai nayi zargin wannan maganin da ta bani ne yasa ya yi ta yin abin har yasa cikina barewa” Aunty Laila ta dafe haba “Kuma yanzu ina matar? Na tabe baki “Oho wallahi, tun dai da ta kira ni ta ce tayi tafiya, ban kara jin ta ba” hannu ta kada “Gara haka, daga jin al’amarin ta akwai abin gudu a ciki” na ce “Ni ma hankalina bai kwanta da ita ba”.
“Amma, Ummu ya kamata ki rika shiga kitchen, tare da Aunty Kulu kina kwashe salon girkinta”. Kallonta nayi “Auntn ta ce sai na kara warwarewa, amma ko ni ma ai ina son koyon wasu girke girken nata, har wurin da ake gyaran jikin nan nata nake son zuwa kallo, ta ce a’a sai na kara kwari”. Ta ce “Allah ya saka mata da alheri” tana surar jakarta “Dan Allah ki kwantar da hankalinki, Ummu kar ki sa tunani ki lalace, shi yana can yana holewarsa” na daga mata kai “Na hakura Aunty Laila, in ma ban yi hakurin ba ya zan yi? da ya damu da halin da zan shiga ai da ya gaya min, ba sai an daura ba in tsinci labarin” ta ce “Ba haka ba ne, kowane Namiji da irin tsarinsa idan zai kara aure” ta mike zan wuce Ummu, kasuwa zan leka, sai na kuma dawowa”. Na mike na dan taka mata sai ta wuce. Wunin ranar na dai yi shi ne amma zuciyata ba dadi. Abin mamaki a wurina da daddare zan kwanta sai na ji bakina yana furta addu’oin kwanciya barci, kamar yanda na saba a baya har suratu mulk da nake karantawa na karanta. Ina karatun ina hararar wayata da take haske dan na sanya ta a silent, kiran Tahir ne ke shigowa yana yankewa na kammala karatun zan ja abun rufa ta Aunty Kulu ta turo kofar ta shigo, mun hada ido ta zauna bakin gado sannu nayi mata, bata amsa ba ta jeho min tambaya “Me yasa kika ki amsa wayar Tahir? Baki na kumbura “Babu komai” “To akul kika yi haka, ya kira ni yana fada min, yana ta kiranki, ba ki picking, ki zama cikin wayayyun mata, Ummulkhairi nuna mishi abin da ya yin bai dame ki ba” Kai na gyada mata sai ta turo min wayarta ” “Ya ce zai kira” kamar jira wayar ta shiga kara na dauka sai ta mike ta ja min kofar muryarsa ce ta ratsa kunnena “Ranki ya dade, duk fushin ne? Baki na tabe ina jin wani takaici na kulle ni, “A’a fushin me kuma? Ango ka sha kamshi”. Murmushi na ji ya yi me sauti “A’a to ko dai ana fushi da ni na ji ba me tsanani ba ne, amma me yasa aka ki daga wayata? wayar na harara “A silent take, kuma na sa ta karkashin pillow, ban ji ba, Allah ya sanya alheri ya kade fitina” cikin wata murya me bayyana tsananin jin dadi yake fadin “Amin na gode Ummulkhairi” mun ajiye waya na kuma janyo abin rufata na ji shigowar sako cikin wayata, na dauko ta na duba Alert ne, yawan kudaden da na gani yasa ni tashi zaune, ban yi wata wata ba na kira Tahir a waya, kamar yana jira, tana shiga ya daga ” “Ya aka yi? Ya soma tambayata “Dama kudade na ga sun shigo na ce ko kayi mantuwa ne? Murmushin sa na ji cikin kunnena, “Ba mantuwa nayi ba, naki ne na faɗar kishiya, ki sayi duk abin da kike buƙata, sauran yan’uwanki ma na ba su” kai na kada, kafin na shiga yi mishi godiya.

Da safe Malam ya umarce ni in yi sadaka da hannuna domin sadaka maganin masifa ce, sai da na karya sai na kira Ummata, na bata labarin auren da Tahir ya yi, kamar yanda na zata cewa tayi “To mene ne? Ya canza miki ne daga yanda yake miki? Na ce “A’a” ta ce “To ki yi hakuri ki yi ta ma mijinki biyayya” na ce “To” labarin kuɗaɗen da ya turo min na bata, na ce zan turo su a raba duka gidan mu.
Ta ce “A’a ki raba kudin uku, ki aiko da kashi daya, sauran ki adana abin ki, so samu ki samu sana’a kina yi ba wai duk abin da kika samu ki ce za ki turo mana ba. Na ce “To Ummana”.

Da daddare kamar jiya sai ga kiran Tahir, hira muke a hankali, a cikin hirar yake gaya min maganganu na lallashi “Ki yi haƙuri, ban yi aure dan cin zarafin kowaccen ku ba, ko dan ban samu wani abu da nake da burin samu wurin ya mace
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

*Ina wacce rama tayi wa katutu take so ta murje* *akwai mafita in sha Allah *Abincin mu na yau da kullum su za ki haɗa da kanki*
*ki ciko ki yi ƙiba ki zo mu sa labulai*

 

Muna komawa ni da Aunty Laila, falon Aunty muka zauna ta ce “Kayan naki fa yaushe za mu kai ɗinki? Kaina na kwantar a bayan kujera, sai na girgiza kai “Idan dai an kara kwana biyu zan tambayi Kawu fita, sai in zo mu kwasa mu kai” ta ce ” Hakan ma ya yi, amma dan Allah ina so ki cire damuwa a ranki ki yi hakuri, Aunty za ta gyara ki dan h……..
Shigowar Auntyn yasa ta yin shiru Flate ɗin da ke hannunta ta ajiye gabana, ƙamshin ya daki hancina fish wit vegetables spaghetti ne, “Ga shi nan ku ci ke da kawarki”. Ta dubi Laila “Ki yi kokari ta ci”. Ta ce “In sha Allah Aunty” ta juya ta fita, me aikinta ta kawo abincin rana, sa’adda Aunty Laila ta kai kifin nan bakinta sai ta runtse ido “Kai gaba ɗaya matar nan tayi, anya wannan kishiyarta ba ƴar rakiya za ta zama ba? Murmushi nayi ko dai in sa miki waigi Aunty Laila? Hararata tayi “Meye nufinki santi nake?
Na ce. “Da fa? Me aikin ta kuma shigowa
da yankakkiyar kankana, ta ce “Aunty ta ce kina gamawa ki sha” na daga mata kai, Aunty Laila ta ce “Matar nan ta san ta kan gyara, kullum daga fruits sai vegetables take ba ki”. Na ce “Kuma kullum sai ta yi min kunun Aya na musamman wanda ya ji kwakwa da dabino da madara”. Ta ce wadannan ai su ne gyaran, ba kinshe kinshen magungunan da ba ka san ingancin su ba”. Na ce “Akwai masu kyau, har kin tuna min da wata matar abokinsa da ta taba kawo min ziyara lokacin da ina Kaduna, ta bani magani. Nan na kwashe komai, labarin yanda muka yi da Haj Shema’u na gaya mata.
Na kara da cewa a lokacin sai nayi zargin wannan maganin da ta bani ne yasa ya yi ta yin abin har yasa cikina barewa” Aunty Laila ta dafe haba “Kuma yanzu ina matar? Na tabe baki “Oho wallahi, tun dai da ta kira ni ta ce tayi tafiya, ban kara jin ta ba” hannu ta kada “Gara haka, daga jin al’amarin ta akwai abin gudu a ciki” na ce “Ni ma hankalina bai kwanta da ita ba”.
“Amma, Ummu ya kamata ki rika shiga kitchen, tare da Aunty Kulu kina kwashe salon girkinta”. Kallonta nayi “Auntn ta ce sai na kara warwarewa, amma ko ni ma ai ina son koyon wasu girke girken nata, har wurin da ake gyaran jikin nan nata nake son zuwa kallo, ta ce a’a sai na kara kwari”. Ta ce “Allah ya saka mata da alheri” tana surar jakarta “Dan Allah ki kwantar da hankalinki, Ummu kar ki sa tunani ki lalace, shi yana can yana holewarsa” na daga mata kai “Na hakura Aunty Laila, in ma ban yi hakurin ba ya zan yi? da ya damu da halin da zan shiga ai da ya gaya min, ba sai an daura ba in tsinci labarin” ta ce “Ba haka ba ne, kowane Namiji da irin tsarinsa idan zai kara aure” ta mike zan wuce Ummu, kasuwa zan leka, sai na kuma dawowa”. Na mike na dan taka mata sai ta wuce. Wunin ranar na dai yi shi ne amma zuciyata ba dadi. Abin mamaki a wurina da daddare zan kwanta sai na ji bakina yana furta addu’oin kwanciya barci, kamar yanda na saba a baya har suratu mulk da nake karantawa na karanta. Ina karatun ina hararar wayata da take haske dan na sanya ta a silent, kiran Tahir ne ke shigowa yana yankewa na kammala karatun zan ja abun rufa ta Aunty Kulu ta turo kofar ta shigo, mun hada ido ta zauna bakin gado sannu nayi mata, bata amsa ba ta jeho min tambaya “Me yasa kika ki amsa wayar Tahir? Baki na kumbura “Babu komai” “To akul kika yi haka, ya kira ni yana fada min, yana ta kiranki, ba ki picking, ki zama cikin wayayyun mata, Ummulkhairi nuna mishi abin da ya yin bai dame ki ba” Kai na gyada mata sai ta turo min wayarta ” “Ya ce zai kira” kamar jira wayar ta shiga kara na dauka sai ta mike ta ja min kofar muryarsa ce ta ratsa kunnena “Ranki ya dade, duk fushin ne? Baki na tabe ina jin wani takaici na kulle ni, “A’a fushin me kuma? Ango ka sha kamshi”. Murmushi na ji ya yi me sauti “A’a to ko dai ana fushi da ni na ji ba me tsanani ba ne, amma me yasa aka ki daga wayata? wayar na harara “A silent take, kuma na sa ta karkashin pillow, ban ji ba, Allah ya sanya alheri ya kade fitina” cikin wata murya me bayyana tsananin jin dadi yake fadin “Amin na gode Ummulkhairi” mun ajiye waya na kuma janyo abin rufata na ji shigowar sako cikin wayata, na dauko ta na duba Alert ne, yawan kudaden da na gani yasa ni tashi zaune, ban yi wata wata ba na kira Tahir a waya, kamar yana jira, tana shiga ya daga ” “Ya aka yi? Ya soma tambayata “Dama kudade na ga sun shigo na ce ko kayi mantuwa ne? Murmushin sa na ji cikin kunnena, “Ba mantuwa nayi ba, naki ne na faɗar kishiya, ki sayi duk abin da kike buƙata, sauran yan’uwanki ma na ba su” kai na kada, kafin na shiga yi mishi godiya.

Da safe Malam ya umarce ni in yi sadaka da hannuna domin sadaka maganin masifa ce, sai da na karya sai na kira Ummata, na bata labarin auren da Tahir ya yi, kamar yanda na zata cewa tayi “To mene ne? Ya canza miki ne daga yanda yake miki? Na ce “A’a” ta ce “To ki yi hakuri ki yi ta ma mijinki biyayya” na ce “To” labarin kuɗaɗen da ya turo min na bata, na ce zan turo su a raba duka gidan mu.
Ta ce “A’a ki raba kudin uku, ki aiko da kashi daya, sauran ki adana abin ki, so samu ki samu sana’a kina yi ba wai duk abin da kika samu ki ce za ki turo mana ba. Na ce “To Ummana”.

Da daddare kamar jiya sai ga kiran Tahir, hira muke a hankali, a cikin hirar yake gaya min maganganu na lallashi “Ki yi haƙuri, ban yi aure dan cin zarafin kowaccen ku ba, ko dan ban samu wani abu da nake da burin samu wurin ya mace kaddara ce kawai, kuma idan na ɗauki shawarar ki gara mu yi auren”. Wata irin faɗuwar gaba na ji gane wace ce ya aura, cikin rawar baki na ce “Wai ya sunan Amaryar taka? Dan jim ya yi kafin ya ce “Latifa” Ai ji nayi tamkar zan yi fitsari a wando, zufa na ji tana tsatstsafo min. “Wani abu ne? Muryarsa ta maido ni cikin hayyacina “Ba komai” na fadi kamar zan fasa kuka. Daga nan duk zantukan da yake min ban fahimtar komai, har ya gaji ya ƙyale ni, wanda ni ma ba fi so. Tagumi na rafsa hannu bi- biyu na tashi zaune tsakiyar gado, “Ni ba ta garin nan ba, yaƙi ya ci kwartuwa, ni Ummulkhairi ina zan tsoma gulmata? Wannan kwarkwararrar yar duniyar Tahir ya aura, shi kenan ni kam na sare, dan ban ga ta inda zan fara in iya karawa da wannan yar barikin ba.
Tahir ya dauko mana fitina. A wannan dare in na ce na rintsa nayi karya, haka na tashi da safe ido ya yi zuru zuru, saboda rashin barci. Gatan da Aunty Kulu ke min ban yarda da shi ba a wannan rana, kitchen na bi ta duk kuma yanda ta kai ga cewa in koma in kwanta ƙi nayi, tare muka yi komai da ita, ina nakaltar yanda take sarrafa komai. Na bi ta wurin gyaran jiki muka haɗa humra tare, wani abu da na tuna yasa ni komawa daki da sauri na ɗauki wayata, WhatsApp na shiga wani link na wani grp da Aunty Laila ta turo min ta ce in yi joining, ban ko bi ta kan shi ba, group ɗin na sayar da Supplement ne na gyaran jiki, nan take nayi joining.
Saƙo na tura mata “Ina son ganin ki Aunty Laila, ina cikin matsala”.
Ba a yi kwakwkwaran awa daya ba ta ga sakona sai ga kiranta ta ce “Mene ne? Na ce “Kan wadda Tahir ya aura ne” na bata labarin wadda ya aura, amma sai na sauya zancen na ce mata sanda ina Ƙanƙara na samu labarin yana tare da ita, wurin matar yayansa, wata kwantagwalalliyar, yar duniya ce. Kwantar min da hankali tayi, tare da gaya min maganganu na karfafa gwiwa, da shawarwari wadanda zan taimaki kaina. Na bata labarin kuɗaɗen da ya turo min, ta ce na gayawa Aunty Kulu? Na ce A’a dan ni dai gaskiya ina tsoron dangin miji, duk dadinka da su.
Ta ce “Haka ne, dama za ta ce in yi shiru kawai. Na ce “Sana’a nake so in fara Aunty Laila” ta ce mu bari Mamanta ta dawo wadda shahararriyar yar kasuwa ce, sai mu nemi shawarar ta” na ce “Ina so idan kin shigo in bi ki, in kwaso kayana mu kai ɗinki” ta ce. “Ba kin ce sai an kwana biyu ba? Kai na girgiza. “Ba a bori da sanyin jiki Aunty Laila, in dai kin shigo sai ki taya ni rokon Aunty Kulu ta bar ni mu je mu kwashi kayan.
Yar dariya Aunty Laila tayi “Matar nan dai ta kidima ki Ummu”
Na ce “Ba kaɗan ba”. Tana min dariya muka aje wayar. Sai washegari ta shigo, muka roki Aunty Kulu ta ce Mijina bai sani ba. Na ce “Zan mishi text” ta ce “Ba laifi”
Ina yi mishi text ɗin ce min ya yi Allah ya tsare.
A motar Aunty Laila muka tafi.

A ɗakina ina ciro kayan Aunty Laila tana tsaye riƙe da haɓa, Allah Ummulkhairi kina da wadannan kaya masu tsada kika bar su kina ta ajiyar su? Murmushi nayi, na janyo wata drower, “Sai mun fara biyawa shagon Momina mu canza wasu kayan”. Na ce “To” “Kai! yanzu dan Allah tunda nake baki magungunan (Supplement) ajiyar su kike ba ki sha? na ce “Ai yanzu ga shi zan sha” ta murmusa “Ai na ga kin ma yi joining da grp ɗinmu (beauty wit supplement) dan tsaki na ja ina taɓe baki “To ya zan yi? daga ina zaman lafiya an haɗa ni da rakai”. “Ai ba abin da ban ba ki ba, sai dai da yake ana turo sabbin kaya, kika fara amfani da su da kanki za ki bani labari”.
A jaka na sanya su muka fito sai na rufe wurin.
Na sha mamakin katafaren wurin da Laila ta ce min na Mamanta ne. Duk wani abu na kwalliyar ya mace ba abin da babu. Shugabar wurin, wadda ta zam mace ce, ita Lailar tayi wa bayani, za ta musanya kaya, ta juyo wurina ta ce in zaba, ta kuma taya ni zaben. Da muka gama Aunty Laila ta zabo min wasu saitin mai ta ce in gwada amfani da su. Daga nan sai wurin telan da ke mata ɗinki, muka bayar, sai la’asar na koma gida.

Na sa wa raina dangana sai dai na dage da addu’a a sujjadata, na kan ce “Ya Allah wannan al’amari da ya same ni, ban gaya wa kowa ba kai na gaya wa, ina rokonka Ubangiji ka zame min bango abin jingina ya hannanu ya mannanu ya badi’us samawati wal’ard, ya zuljalali wal ikram.
Na dage kuma da shiga kitchen tare da Aunty Kulu da taya ta ayyukan sana’arta. Ni ma ta soma min gyaran jiki, Kawu Attahiru yana ta bani addu’o’i na dage ina tayi, gaba ɗaya nake jin canji a tare da ni. Muna waya da Tahir, ya kira ni sau uku a rana. Iyayen Laila sun dawo dan haka roƙi Aunty Kulu zan je, ta ce “To in sanar da mijina” Na kira shi da safe, lokacin yana zaune a Hospital an kwantar da sarautar mata, wadda tun daura auren Tahir ta shiga tashin hankalin da bata samu sa’ida ba har sai da ta dangana da gadon likita.
Kwance take sharkaf wanda gaba ɗaya jikinta da zuciyarta ciwo suke mata. Tahir na zaune kujerar gaban gadon nata, Amarya Latifa na tsaye ita da kawarta Fadila wadanda basu jima da zuwa ba, ba kuma kowa ya gayyato su ba tun dai da ta kwana biyu bata ga Tahir ba, ya ce ba zai samu zuwa ba, Uwargidansa na kwance Asibiti. Kasa haƙuri tayi sai da ta nemi abokinsa Shehu, wurin sa ta ji inda aka kwantar da ran gidan, sai suka yo mishi tsinke, yanda take ji a jikinta ya hana ta tashi tayi musu korar kare. Har suka gama gaishe gaishen su, bata ta da kai ba, tana dai kallon su, zuciyarta na tururi, wayar Tahir ta shiga ƙara yasa hannu ya ciro ta a aljihu, ganin me kiran ya ba shi mamaki dan ba kiran sa take ba “Ya aka yi? abin da ya fara ce min kenan, ban amsa ba na shiga gaishe shi, kafin ɗora da cewa “Dama iyayen Aunty Laila ne suka dawo shi ne nake so mu je in gaishe su”. “Yawo ko? Kai na girgiza kamar ganina “Allah ba yawo bane” “Sai kun dawo, ki kula da kanki” na ce “In sha Allah, na gode” Latifa suka kalli juna ita da kawarta Halima kuma na kallon su, dan duk sun fahimci da wa ya yi wayar, cikin magana me kama da subutar baki Amarya Latifa ta dube shi “Ba bata da lafiya ba? har tana iya fita? Shiru ya mata kamar ba zai tanka ba, kafin ya jefe ta da idanuwansa “Wa ya ce miki bata da lafiya? Take ta gane kuskuren da ta tafka, kame kamen da ta shiga yi yasa Halima zura mata ido tana nazarin ta, ita Sarkin karantar mutane tuni ta gano Latifa, a ranta ta ce “Wato ban da asirin zubewar ciki da na yi wa yarinyar nan, ita kuma na rashin lafiya tayi mata kenan? Kamar yanda malaminta ya ce mata ita ma Latifa tun kan ta shigo gidan neman kowa take, lallai yarinyar nan ta kawo kanta.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

*Ina wacce rama tayi wa katutu take so ta murje* *akwai mafita in sha Allah ki zo mu sa labulai*

 

A tsanake na kammala ina jiran Aunty Laila. Tana zuwa wucewa muka yi, ita ke jan motar ina gefenta a Victoria Island iyayenta suke, tun daga shiga unguwar na tsinke, kafin mu shiga tafkeken gidan nasu wanda abin da za ka misalta shi da shi aljannar duniya. Wuraren da muka riƙa wucewa dan isa falon babanta kusan rikicewa nayi, wato shi wanda ya gaji arziki daban yake ban taba tunanin arzikin iyayenta ya kai haka ba, dan yanda take simple wato dai shi wanda ya gaji arziki daban yake . Kishingide muka same shi, na gaishe shi ya amsa min da fara’a, sai shi min albarka yake yi, kafin ta ja ni bangaren mamanta, bamu same ta a inda Lailar tayi zaton za mu same ta ba, wata cikin masu aikinta ta ce mana tana kitchen, can muka same ta ita da autar su su Laila Amira, Amirar tayo kan mu, ni ta rungume tana duban ƴar’uwarta “Wallahi Aunty, na gane ta, ita ce Aunty Ummunki” nayi murmushin jin ta kira ni da Aunty duk da yake ba za mu wuce sa’anni da ita ba. Da ta sake ni sai na matsa kusa da mahaifiyar su, ita ma kamo ni tayi ta sa ni gefen jikinta, Oyoyo Ummun Laila” ta ce min yayinda nake kokarin gaishe ta, Aunty Laila ta ce “Momi me kuke yi a kitchen? Murmushi tayi “Girki nake koya wa Amira” Dariya Aunty Laila tayi “Lallai ma autar Momi, har ma da kanta take koya miki? Momin ce ta ce “Ni ku bani wuri, kin zo da baƙuwa kin bar ta kitchen” Falo muka wuce, suka yi ta tarairayata. Har ɗakinta kafin tayi aure ta kaini, ina ta kara kakkaɓin halinta, dan ko inda take zaune take aure kai kasan arzikin gidan su ya fi ƙarfin nan. Kamar ta san tunanina, ta ce “Auren zumunci muka yi da Ahmad, Ummulkhairi” na kada kai. “Shi ɗin ya rasa iyayensa tun yana karami, a can garin su babanmu, Sumaila dake jihar Kano. Daddyna da Momi sun je garin, Momi ta gan shi ya yi matukar bata tausayi a matsayin shekarun sa ba shi da uwa ba shi da uba, mahaifinsa shi ne yayan Daddy, Momi ta roƙi Daddy su dauke shi su tafi da shi, lokacin Daddy yana aiki a Akure, suka tafi da shi Momi ta mayar da shi ɗanta dan sun jima basu samu haihuwa ba, an mayar da Daddy Sokoto aka haife ni, samuna bai sa sun rage komai daga kaunar da suke wa Ahmad ba, daga ni sai kanena Al’amin wanda na taɓa fada miki yana America yana karatu, daga nan sai auta Amira.
Mun tashi tare da Ahmad a gida ɗaya, kuma soyayya ta kullu a tsakanin mu, Momi ta so Ahmad ya karanci Business Administration saboda ya kula da harkokin kasuwancinta, dan ban da wurin da muka je da ke tana da wasu wuraren ma, har ma a Kano, amma Ahmad ya nuna ba shi da ra’ayi. Sai da na kammala Masters ɗina aka yi bikin mu.
Shigowar Amira yasa Aunty Laila yin shiru tana duban ta, “Amma kin ga da yake ita auta ce digiri na farko kawai ta kammala ta ce aure take so kuma su Daddy sun yarda za su yi mata.
Cikin shagwaba ta narke fuska “Ai dai zan cigaba da karatuna”.
Tare muka fito Aunty Laila ta jani bedroom din Momi, mun samu tana waya, ta ɗago ta dube mu kafin ta cigaba da wayarta, da hannu ta yafito ni na matsa kusa da ita, ta kamo hannuna ta zaunar da ni kusa da ita. Sai da ta kammala wayar ta kara matso da ni kusa da ita. “Laila ta ce min an yi miki abokiyar zama? Na daga mata kai “To ki yi hakuri kin ji Daughter? Na kuma daga mata kai “Ki yi kokari ki kama mijinki, ba ruwanki da wasu kishiyoyi, ki gyara kanki”. Ta mike ta fita kafin ta dawo da wasu kaya a hannunta “Ga kaya nan nayi miki tsaraba ki yi ma in low ɗina kwalliya”. Ta miko min wasu turaruka “Wadannan na sirri ne dan maigidanki kawai za ki yi amfani da su, ki kasance kodayaushe cikin tsafta, ka da ki sake ya rika ganin ki a yamutse, sai girki ki iya girki me dadi, ko ta nan za ki sace zuciyar miji, kin ga Amirana aure za tayi, da kaina nake shiga kitchen Ina koya mata da na gane bata so”
Haka tayi ta yi min nasiha wadda na ji dadinta kwarai sai godiya nake. A karshe Aunty Laila ta ce “Sana’a take son farawa Mommy, shi ne na ce ta bari ki zo mu nemi shawarar ki, dan ke ce business woman” daƙuwa tayi wa Lailar ita kuma Lailar ta kama dariya, “Ina ganin ku haɗa hannu ku buɗe wurin sana’a guda, akwai ginin wata plaza da ake yi ina ganin zan ba ku shago Daya sai ku zuba kaya, sai ku je ku yi nazari ku ga me za ku sa ka” Godiya muka yi mata. Sai da ta fita Laila ta buɗe jakar da ta bani dogayen riguna ne guda huɗu, sai riga da wando su ma hudu, sai riga da siket su ɗin ma huɗu, duk kan su kuma haɗaɗɗu ne masu asalin tsada.
Da muka yi shirin tafiya kudade irin kyautar su ta manya babanta ya bata ya ce ta riƙe min.

Sai yamma likis na koma. Inda Aunty Kulu ta ce “Hala kin manta da wankan? Na ce “A’a Aunty” ta nuna min toilet “To yi maza ki shiga”
Sanda na fito missed call din Tahir uku na samu na kira ya daga yana tambayata ina na shiga. Na ce “Wanka” ina jin ajiyar zuciyar da ya fidda “Har yau ba a gama sa miki tafasasshen ruwan nan ba? Kai na daga kamar yana kallona “Dama kira nayi in ji kin dawo” na ce “Na dawo” ya ce “Ya yi kyau, kina lissafin kwana nawa ya rage in dawo” idona na runtse na dafe goshina “E” wata tambayar ya kuma wurgo min “Kin warke ko yanzu, ba ki jin wata matsala a jikinki? Na ce “Na warke Alhamdulillahi” “To ma sha Allah sai ki yi shirin tara ta”.
Ya katse wayar ya bar ni sake da baki, dan sosai na gano inda zancen sa ya dosa. Namiji kenan, kana da mata uku reras a gabanka amma kana harin wata, cikin ukun ma hada Amarya.
Aunty Laila ta kawo min dinkunana wadanda suka yi matukar yin kyau har ba magana dan wuri ne na gwanaye, kuma kwararru.

Aunty Kulu ma a nata fannin ta ƙara ƙaimi wurin gyara ni da kanta, gashina ma ya sha gyara, jikina kuwa har sulbi yake ban da kamshin da ya kama jikina, nayi wani irin kyau ga cikar jego.
Saura kwana biyu ya dawo na tafi gidana da masu aikin Aunty Kulu mata biyu, muka gyara wurina, an wanke abin da ke buƙatar wanki na gogewa an goge, komai an gyara shi tsaf har labulayya da zanen gado an sake.

Ana gobe Tahir zai dawo, wata cikin masu aikin Aunty Kulu tayi min kunshi ina zaune zaman jiran ya bushe, wasu ƴanmata suka zo yin ƙunshi, wadda tayi min tayi wa daya a cikin su dan su biyu ne kuma ɗayar kawai za a yi wa. Sai da ta gama saka mata lallen ta fita, wadda aka yi ma wa ta dubi wadda suke tare, “Kin san nan wane gida ne ƙawata? Girgiza kai tayi dan hankalinta na kan wayarta. “Gidan su gayen nan ne da ya auri Latifa”.
Faduwar gaba na ji jin zancenta sai na ƙara kasa kunnena, idanuna na kan wayata dan kar su gane ina sauraren su, ita kuma saurin barin kallon wayar tayi ta fuskance ta, “Dan Allah? ya aka yi kika sani” “Ai na dade da sani” Ƙwafa waccan tayi “Allah ban yarda yarinyar nan ba abin da tayi wa gayen nan ya aure ta, da ganin su ma ajin rayuwar su ba iri daya bane, meye ban yi ba dan in samu ya dube ni kawai, ke bama ni ba gaba dayan mu duk wacce ke zuwa wurin na su wace ce bata yi fatan ya kula ta ba amma ba wacce ya taba kallo, sai ita daga zuwan ta, wai ya Aure ta”. Ta ƙarashe maganar da takaici me yawa a muryarta. Ɗayar ta karɓe “Ke ita fa ba a garin nan ta san shi ba, nan ɗin ma da kika gan ta shi ta biyo “. Waccan ta buɗe ido “To! ita kuma daga ina take? “Yar Kaduna ce, a yanda na samu labari, tun bai yi auren fari ba take bibiyar sa tayi tayi su buga duniya ko da ba zai aure ta ba amma bata samu nasarar hakan ba kin dai ga gidan su, Babansa shahararren malami ne, maido shi aiki garin nan ta biyo shi tana da yan’uwa na jone jone ta zauna gidan su, tana barikinta shi kuma ta da ɗa manne mishi.
Anan ne ma ta samu hankalinsa, kin ga har ta dace ya aure ta. Cikin matukar jin zafi waccan ta ce “Ta dai taki sa’a asirinta ya ci”. Shigowar wadda ta sa mana lallen yasa su yin shiru, nawa ta duba ta ce mu je in wanke, na tafi na bar yammatan, zuciyata cike da tunani kan maganganun su.

Da daddare muna zaune da Aunty Kulu. Nasiha take min game da zaman aure, har ma da yanda zan mu’amalanci kishiyoyina. Kuɗaɗe ta miƙo min, na dube ta dan neman karin bayani ta ce “Malam, ne ya bayar ya ce in saya miki abubuwan da suka dace,. shi ne na ce bari in ba ki ko da abin da kike sha’awa sai ki saya in kuma babu sa abin ki a banki”. Na ce “Yanzu dai ban da bukatar komai, ki ajiye kuɗaɗen a hannunki” ta ce “Sam ki karbi abin ki ke ya ba” wasu kwalaben humra ta dauko guda biyu “Ni kuma ga gudunmuwa ta nan, Ummu na musamman ne, ki tabbatar duk sadda za ki yi amfani da su, za ki wurin megida ne, dan Namiji duk taurin kansa ya shaƙa sai ya biyo, ki adana su da kyau su ne makamanki”. Na ce “To” kiran Kawu da ya shigo wayarta yasa ta tashi da sauri ta ce min tana zuwa.
Kwanciya kawai nayi, zuciyata na jinjina tsantsan karamci na wadannan bayin Allah. Dan haka da safe da muka yi waya da Ummata, ta ce in hada ta da Aunty Kulu, godiya sosai tayi mata bisa karamcin su a gare ni. Na je nayi wa Kawu Attahiru bankwana gami da godiya, Aunty Kulu ce ta raka ni gidana, bata jima ba ta ce min za ta koma dan tana da ayyuka, har ƴar ƙwalla nayi ta sabo da muka yi.
Ƙayataccen girki nayi wa megidan da abin sha, jirgin yamma ya biyo.
Wanka nayi na sha kwalliya da riga da siket na wani haɗadden less me ƴan ƙananan hudoji, da duwatsu, kayan sun zauna jikina sun fidda halittata, na murza humrar da Aunty Kulu ta bani ana sallar magrib ya shigo dan haka alwala kawai ya yi ya nufi masallaci, ni ma sallar nayi na daɗa gyara kwalliyata. Har ya dawo na zuba mishi abinci, a lurar da nayi zuciyarsa a ɓace take, dan ya tsare gida, ƙara nutsuwa nayi tun da na tambaye shi yanda ya baro su, dan Ummata ta ce min har gidan mu ya je, kammalawar sa wanka ya yi da ruwan da na hada mishi, ina zaune falo amma gabana sai faduwa yake sai addu’o’i nake dan ban san dalilin da ya sa ya ɗaure min ɗin ba, jin yana kiran Sunana yasa ni miƙewa kwance na same shi ya yi ɗaiɗai daga shi sai guntun wando, “Yi shirin kwanciya ki zo mu kwanta” Umarnin da ya bani kenan. Falon na koma na kashe komai sai na rufe kofar na cire kayan jikina na mayar da na barci humrar na ƙara sawa kadan sai na hau gado addu’o’in kwanciya na shiga karantowa na gama sai na shafe jikina na lumshe idona na ji ya mirgino inda nake sai ya rungume ni, ajiyar zuciya muka fidda a tare. Abubuwan da suka faru a tsakanin mu a wannan dare masu tsayawa a rai ne, daren yana cikin dararen da ba zan taba mancewa da su ba a tarihin aurena da Tahir.

Da safe mun tashi yana ta ji da ni sai zuciyata tayi min sanyi, sai gobe zai koma wurin aiki dan haka tare muka wuni, da na leƙa wurin Aunty Laila dan mu gaisa sai tsiya take min na baro ta ina cewa ki dai ji da sharrinki Aunty Laila.

Da daddare yana zaune ina kwance jikinsa, hotunan ginin gidan da yake yake nuna min ina ta yabawa tare da addu’a.
Haka rayuwa ta juya min, na samu lafiya da walwala ina kokari wurin kula da ibadata da mijina, na goge na waye zama da Laila, na koyi gyara jikina da nakaltar yanda ake kwalliyar, kashe min kudi kawai Tahir ke yi daga suturu zuwa kayan gyaran jiki da na kwalliya. Inda duk Laila za ta za ta gayyace ni, shi kuma bai taba hanani ba har gidan su Laila mun je tare da shi dan ni tuni na zama ƴar gida. Duk sati biyu yake tafiya Kaduna saboda gininsa, idan ya tafi ni kuma zan kai wa gidan Kawu Attahiru ziyara inda Aunty Kulu za ta gyara ni ciki da bai.
Wata ranar Laraba da yammaci na shiga wurin Aunty Laila. Girki take haɗawa ni kuma ina zaune kan wata drower jikin window ina latsa wayata, ɗagowa nayi na dube ta “Aunty Laila na samo mana sana’ar da za muyi ta waiwayo da ludayi a hannunta “Wace sana’a ce? Na ce “Mu sa kekunan dinki, sai mu samo kwararrun teloli mu zuba suna ɗinki muna biyan su” ta ce “Good idea dama shagon da Momi ta bamu jikin wanda take saida material ne” wayarta ta jawo momin nata ta kira ta shaida mata shawarar da na kawo ita ma tayi na’am ta ce mu hada kuɗaɗen mu za ta neme mu.
Muna cigaba da maganar na hango shigowar motar Tahir ta window da nake zaune, kasa na duro “Na tafi Aunty Laila” ta ce “Habibi ya dawo kenan? Na fito yana kokarin parking kallon da yake jifana da shi bayan fitowar sa, yasa na sha jinin jikina wuce ni da ya yi ba tare da ya yi min magana ba yasa na bi shi cikin sanyin jiki, dan gano laifina ya hanani shiga wurin Laila ba mayafi, jikina na duba wando da riga ne na material rigar karama ce sai wandon falazo sai baby hijab da na sanys
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Haƙuri nake ba shi bai ce komai ba, har ya sauya kayan jikinsa, ya zauna falo bai min magana ba. Haƙuri na ƙara ba shi sai na shiga ba shi labarin shawarar da muka yanke ta buɗe shagon ɗinki. Amsa min da ya yi yasa na gane ya haƙura, wayarsa ya miƙo min “Ga Hajiyar tudun wada, ta kira ni wai in haɗa ta da ke, dan kin kirata bata ji, na amsa sai da muka gama gaisawa da ita da Malam sai na ce ta bai wa su ƴan biyu, suka yi ta min shirmen su ina dariya.

Kwanakin da aka dauka ba masu yawa bane aka bude shagon ɗinki na zamani aka kuma nemi kwararrun teloli aka zuba, mallakin mu ni da Laila.

Wani hantsi ina aiki a bed room ɗina, na shirya kayan guga, na hango tsayuwar motar gidan su Aunty Laila, ganin Mominta ta fito yasa mamaki kana kama ni dan bata taɓa zuwa ba. Saurin kammalawa nayi dan in je in gaishe ta, hijab na sanya doguwa har ƙasa dan Ahmad yana gida, kasantuwar weekend ne, Tahir ma ya je kankara. Sai da na shirya mata dan abin taɓawa a faranti sai na isa wurin Laila, daga ita sai Ahmad na samu zaune suna magana, da Sallama na shiga na ajiye tiren a gabanta, sai na zauna kusa da kafafunta na soma gaishe ta, dafa ni tayi tana amsawa, kafin na gaishe da Ahmad. Ban ga Laila ba ina tunanin tana kitchen, na fito na koma wurina.
An shafe sama da awa biyu Momi ta fito za ta tafi, tare da Aunty Laila suka shigo wurina, ƙara gaishe ta nayi muka taɓa yar hira, da ta tashi za ta tafi wata leda ta ajiye min. Kayan yar Sokoto ne, “Jiya ta zo” na ce ,”Na gode Momi, Allah ya kara girma”. Sai da muka raka ta har inda motar da aka kawo ta take, ta shiga muka rufe kofar, motar Ahmad na bayan ta ta har suka ɓace wa idonmu.
Wurina Aunty Laila ta bi ni, muna shiga ta miƙo min ledar yar Sokoto da Momi ta bata, iri daya da tawa. “Ga shi ki haɗa” Haɓa na riƙe “Wai sai yaushe za ki gane alfanun magungunan nan ki riƙa sha? Gatsine tayi “Ke ni fa ba zan iya shan abubuwan nan ba” na wuce kitchen ina dauko kofi, “Da za ki san amfanin su Aunty Laila, da ba sai nayi ta rokon ki ba, za ki sha”. Kai ta girgiza tana kallona, na haɗa tsimi, da gumba da zuma na sha. ” Kin san labarin da na zo ba ki? Na ce “A’a” ta gyara zama “Daddy ne ya biya mana Saudiyya mu duka gidan mu, shi ne Momi ta zo rarrashin ɗan ta, ya ajiye aikinsa, dan ita dai aikin nan na Ahmad yana takura ta, duk inda za su sai dai su tafi babu Ahmad, saboda yanayin aikin sa, ta ce ya fadi duk irin sana’ar da yake so za su ba shi jari ita da Daddy, ya bar aikin. To ya dai roke ta, ya ce ta dan ƙara mishi lokaci zai ajiye aikin kamar yanda take so. Ta ba shi keys na gidan da Daddy ya gina mishi, ta ce wannan umarni ne ba shawara ba, dole ya tashi anan”.
Take hankalina ya tashi na ce “Yanzu tashi za ki yi ki bar ni anan, Aunty Laila? Murmushi tayi “Kin kuwa san kafiyar Ahmad? ba lallai mu tashi ba, zai san yanda ya yi ya lallaɓa ta. nayi murmushi “Mu’amalar Momi, da ya Ahmad tana burge ni, wani lokacin na kan yi tunanin kamar shi ta haifa ba ke ba” ita ma ta murmushin tayi “Kafin ke mutane da yawa sun faɗi haka, wata irin kauna ce tsakanin su”. Mun jima muna hira kafin ta koma sashenta.

Da Tahir ya dawo nake ba shi labarin tafiyar da su Laila za su yi zuwa aikin hajji. Na haɗa da rokonsa ya kai ni gida, ya ce ba yanzu ba.
Har na manta mun yi maganar zuwa aikin hajjin su Laila sai ga shi da takardu wai za mu je in yi passport ya biya min za mu tafi tare da su Aunty Laila, har ya je ya yi ma mahaifinta magana za su tafi tare da ni. Murna sosai nayi jin ni ce za ni kasa me tsarki sauke farali. Amma har kamar Laila ta fi ni jin dadin za mu tare, dan ita wannan ba shi ne zuwan ta na farko ba. Na ƙara roƙon Tahir ya kai ni gida in yi Sallama da su, ya ce A’a sai na dawo” jin da nayi yana waya na fahimci idan na tafi wata daga cikin matansa zai kawo, dan Mmn Ummi ta bani labarin matan nasa sun bar aiki, wai tun zuwan da ya yi ya yi wata guda, ya tada musu balli, ya ce dole duk wadda ke son zama da shi ta ajiye aikinta ta kula da aurenta. Sun girgiza duk kan su amma tilas suka haƙura. Sai na dauke duk wani abu nawa, har Suturu na na kai wa Aunty Kulu, ina dai ta fargaban idan ya tambaye ni abin da zan ce mishi, sai bai ma tambaya ba.

Bamu tashi da wuri ba, dan mu ne jirgin karshe. Ranar da zamu tafi muna Sallama da Tahir duk da idon mutane sai da ya kama hannayena ya riƙe cikin nashi, “Ki kula da kanki Ummulkhairi, Allah ya tsare min ke”. Na kasa cewa Amin dan zuciyata da ta tsinke har sai ga hawaye. Handkerchief ya fiddo ya goge min, sai ya ciro wasu kudade Dalar Amurka ya damka min a hannuna, “Kar ki ce za ki yi wata tsaraba, Ummulkhairi ki ci abinci me kyau, kar ki dawo a rame, ki yi ibada. Na daga kai muka haɗa ido, “Kuɗaɗen nan fa sun yi yawa, za a bani na guzuri” murmushi ya min kafin ya kai ga magana sai ga Laila ta karaso akwai ƴar kunya tsakanin su, dan haka sallama ya mata muka wuce ina jin ba dadi a zuciyata.

Aikin hajinmu me daɗi muka yi, dan kasancewar iyayen Laila a tare da ni. Hotel din da muka yi masauki na musamman ne kuma yana kusa da harami dakin mu daya da Laila, Momi da Amira, sai Daddy shi kadai, Ahmad dai ya zille bai zo ba, ya ce sai za su dawo Umara.

Mahaifiyar Laila, Haj Asma’u, mace me kwazo da sanin ciwon kanta, wayayya me dimbin ilimin addini da na zamani. Bata barin mu haka nan, kullum muna wurin ibada, har muka kammala aikin Hajji. Daga Saudiya Dubai za su wuce, daga can su shiga China za a yi ma Amira sayayyar kayan aure. Daga ni sai Aunty Laila ne masu komawa Nigeria, samun mahaifinta tayi ta ce ya roki Ahmad da Tahir su bar mu mu tafi tare da su. “Anya Lailata aka yi haka ba a shiga hakkin mazajenku ba? Kafa ta buga kamar wata yarinya karama, “Haba daddyna ba wani shiga hakki duka sati nawa ne? Ya ce “Shi kenan”. Tsalle tayi ta mika mishi wayarsa da ke kusa da shi da ɗai ɗari ya kira kowannen su ya nemi alfarmar barin matan nasu su tafi tare da su, wanda duk kan su dauriya me yawa suka sa wurin amsa wa dattijon.

Aunty Laila ta same mu tare da Momi da Amira da murnarta ta bamu labari. Kai Momi ta girgiza “Ai da ina wurin ba za a yi wayar ba, Alh ya yi ta biye miki da shirmen ki, da wane ido za mu kalli yaron nan Tahir in shi Ahmad ba yadda zai yi da Daddy.
Wani kallo Aunty Laila ta fakaici idon Momi tayi min “Oya taso mu je” miƙewa nayi dan dama a shirye nake, ta dubi Mominta, “Saura ke Momi ki tashi mu je” “Ku je abin ku, zan huta ne” marairaicewa Laila tayi har ta samu Momin na ta ta yarda za ta. Kama hannuna tayi “Mu je mu yi wa Daddy Sallama, kafin Momi ta shirya”. Inda Aunty Laila ta bar shi nan muka same shi, muka shaida mishi za mu fita sayayya, kuɗaɗe ya ciro ya damka ma Lailar ni ma ya bani kamar yanda ya bata, muka yi godiya muka fito. Mahaifiyar Laila na gaba muna bayanta, wani katafaren wurin saida turaruka muka shiga, mu wurin na sawa a daki muka nufa, Momi kuma magunguna irin na su na can ta saya mana ta haɗa kuma har sayayyar da muka yi ta biya kudaden. Daga nan sai wurin sayar da kaya, laffaya muka saya kala kala ko in ce Momi ta saya ta saya mana, har Aunty Kulu na zabar ma masu kyau.
Mun taho bisa hanya ina ta wa Aunty Laila mita, “Kullum za mu sayayya sai kin uzzura wa Momi, ko bata da sha’awar fita, dan wayon ta biya kudaden duk abin da muka dauka.
Shi kuma Daddy dole sai kin kaimu yi mishi sallama shi kuma duk zuwa zai dumbuzo kudi ya bamu, ni kam tun zuwa na ban kashe ko kwabo ba, komai su Daddy ne da Momi”.
Maimakon ta bani amsa sai ta shashantar da maganar, ta hanyar nuna min wani shagon dogayen riguna, haka muka shiga kuma Momi ta biya duk abin da muka dauka.
Ban gane me Aunty Laila take nufi da abin da take yi ba sai ana saura kwana uku mu bar garin ina zaune a masallacin Annabi, karatun Alkur’ani me tsarki nake. Wayata ta shiga vibration dan na sa ta a silent, dubana na kai inda take sunan Aunty Laila na gani na ɗauka ina magana can kasan makoshina “Ki yi sauri Ummulkhairi ki dawo za mu fita” kashe wayar nayi na soma tattara nawa ya nawa, na rataya jakata, cikin nutsuwa na riƙa takawa har na koma masaukin mu, na samu dama Laila jirana take. Yau dai bata ce wa Momi sai ta bi mu ba, ko Amira ƙanwarta da ta ce za ta raka mu, cewa tayi “Kwanta abin ki ki huta ƴanmata”.
Amma sai da ta kaimu wurin Daddy muka yi mishi sallama, shi kuma ba fashi ya ciro kudade ya bamu ya ce mu kara sayayya.
Bata kai mu ko’ina ba sai wani katafaren wurin saida kayan ƙarau na adon mata, dukiya ce iya ganin idon ka. Duba na tayi “To Hajjaju me son kashe kuɗin ta, ga lokacin kashe su ya yi, Allah ma yasa su ishe ki. Murmushi nayi ina naɗe da hannuna a kirji, “Me kenan za a saya malamata? Ita ma murmushin tayi “Ina son ki sayi sarƙa da ƴan kunnaye kamar set uku ko hudu iya dai inda kudinki suka tsaya, sai bangul ina son ki saya, sannan akwai wasu awarwaraye na gwal sirara ne guda goma sha biyu, Momi ta taɓa saya min, sai zobuna na gwal guda takwas.
Girgiza kai nayi “Tirkashi! babbar magana, duk ina na ga kuɗaɗen sayen waɗannan ababen da kika lissafo ? Hannuna ta kama “Za ki gani” sai dai wani jiri da na soma ji yasa ni kasa cire kafa. Duba na tayi “Yaya dai? Na ce “Jiri nake gani sai zuciyata da na ji tana tashi, kamar zan yi amai” A taƙaice dai ka sa tafiya nayi sai da taimakon Laila, taxi ta tare mana zuwa gida. Hankalin Momi da Daddy ya tashi ganin halin da nake ciki, sai da suka kai ni asibiti, binciken larabawa kuma ya bada sakamakon karamin ciki da nake dauke da shi wanda bai cika watanni biyu ba. Bayin Allan nan suka shiga murna, da tarairayata, Asibitin suka riƙe ni suka ce sai na kwana. Muna zaune a dakin daga ni sai Aunty Laila, Ayaba nake ci tana zaune gefena “Ina ganin dai wannan ɗan namu ɗan bankwana ne, aka maƙalo aka taho da shi”.
Rufe ido nayi na ce. “Na shiga uku Aunty Laila” ta kwashe da dariya. Tsokana ta tayi tayi, har na gaji na kwanta na juya mata baya.

Washegari na tashi garau, suka sallame mu. Ba mu koma wurin sayayya ba, Aunty ta ce mu bari sai mun isa Dubai. Mun bar Saudiyya muka shiga Dubai, sati guda muka yi anan ɗin na sayi duk abin da Aunty Laila ta lissafa sai dai set na sarƙa biyu aka samu, kuɗi suka kare kaf, har na account ɗina da na canzo na taho da su wa’anda na ce mata ban so in karar da su ina so in yi alheri da su idan na koma na je gida.
Ta ce Allah zai kawo na yin alherin.
Daga Dubai sai China nan kam yawo muka yi sosai dan na gane Laila sani ba na wasa ba tayi wa garin, ana gobe za mu bar kasar dan sati biyu muka yi, a Guangzhou muka sauka sai muka wuce yiwu muka yi kwana hudu daga nan muka wuce shon-hai muka yi kwana hudu, nan ma sai muka dawo Guangzhou idan muka kwana washegari sai mu wuce.
Mun je kasuwa mun dawo daga kasuwa zuwa hotel din da muka yi masauki babu nisa, takowa muka yi a ƙafa, muna tafe muna hira Laila ta ce “Kika ce oganki ya ce Kaduna za ki sauka? Na daga kai “Haka ya ce dan an tura shi wani course na wata tara a Kadunan, amma ni kam ban san haduwa da matan nan na shi”.
Wani kallo ta min
“To ina fata dai ba tsoron su kike ji ba?
“Haba dai tsoro? fitina ce kawai bana so”
“Yawwa, yanzu ba tsoro tsakaninki da su, ai kin gane? na daga mata kai. “Duk wata haɗuwa da mace za ta yi takama da ita ke ma kin haɗe, in bokon su ke ba ki tsoro, to kema yanzu da kowa za ki yi turanci, in kika haɗu da su kwalliya sosai za ki rika dauka dan su san yanzu ba da ba ce, da ba ki iya fita sai da hijabi, uwa uba mijinki na sonki”. Ajiyar zuciya na fidda “Haka ne” sai kuma na shiga tunanin halin da muke ciki da Ogan tun rokon da Daddyn Laila ya yi mishi sai ya dauki fushi da ni, ya daina kirana in kuma ni na kira shi a dakile yake amsawa.
Abin yana damuna amma sai na sa hakuri na bar wa raina, ina ta addu’a.

Ranar da zamu taho jirgin Ethiopia muka hawo, zaman awa goma sha bakwai muka yi hada yada zangon da muka yi a Ethiopia, Abuja muka sauka karfe daya agogon Nigeria, daga cikin jerin motocin da suka zo taran Daddy muka shiga daya, nan ma Daddy waya ya yi wa Tahir ya roke shi zan kwana da su anan idan Allah ya tashe mu lafiya zai sa a kawo ni Kaduna.
Shiryayyen gidan Daddy na Abuja muka yada zango, ni dai cikin fargaba nake yanda za ta kaya mana ni da Ogan dan an kara mishi laifi.

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

*Ina wacce rama tayi wa katutu take so ta murje* *akwai mafita in sha Allah ki zo mu sa labulai*

 

A tsanake na kammala ina jiran Aunty Laila. Tana zuwa wucewa muka yi, ita ke jan motar ina gefenta a Victoria Island iyayenta suke, tun daga shiga unguwar na tsinke, kafin mu shiga tafkeken gidan nasu wanda abin da za ka misalta shi da shi aljannar duniya. Wuraren da muka riƙa wucewa dan isa falon babanta kusan rikicewa nayi, wato shi wanda ya gaji arziki daban yake ban taba tunanin arzikin iyayenta ya kai haka ba, dan yanda take simple wato dai shi wanda ya gaji arziki daban yake . Kishingide muka same shi, na gaishe shi ya amsa min da fara’a, sai shi min albarka yake yi, kafin ta ja ni bangaren mamanta, bamu same ta a inda Lailar tayi zaton za mu same ta ba, wata cikin masu aikinta ta ce mana tana kitchen, can muka same ta ita da autar su su Laila Amira, Amirar tayo kan mu, ni ta rungume tana duban ƴar’uwarta “Wallahi Aunty, na gane ta, ita ce Aunty Ummunki” nayi murmushin jin ta kira ni da Aunty duk da yake ba za mu wuce sa’anni da ita ba. Da ta sake ni sai na matsa kusa da mahaifiyar su, ita ma kamo ni tayi ta sa ni gefen jikinta, Oyoyo Ummun Laila” ta ce min yayinda nake kokarin gaishe ta, Aunty Laila ta ce “Momi me kuke yi a kitchen? Murmushi tayi “Girki nake koya wa Amira” Dariya Aunty Laila tayi “Lallai ma autar Momi, har ma da kanta take koya miki? Momin ce ta ce “Ni ku bani wuri, kin zo da baƙuwa kin bar ta kitchen” Falo muka wuce, suka yi ta tarairayata. Har ɗakinta kafin tayi aure ta kaini, ina ta kara kakkaɓin halinta, dan ko inda take zaune take aure kai kasan arzikin gidan su ya fi ƙarfin nan. Kamar ta san tunanina, ta ce “Auren zumunci muka yi da Ahmad, Ummulkhairi” na kada kai. “Shi ɗin ya rasa iyayensa tun yana karami, a can garin su babanmu, Sumaila dake jihar Kano. Daddyna da Momi sun je garin, Momi ta gan shi ya yi matukar bata tausayi a matsayin shekarun sa ba shi da uwa ba shi da uba, mahaifinsa shi ne yayan Daddy, Momi ta roƙi Daddy su dauke shi su tafi da shi, lokacin Daddy yana aiki a Akure, suka tafi da shi Momi ta mayar da shi ɗanta dan sun jima basu samu haihuwa ba, an mayar da Daddy Sokoto aka haife ni, samuna bai sa sun rage komai daga kaunar da suke wa Ahmad ba, daga ni sai kanena Al’amin wanda na taɓa fada miki yana America yana karatu, daga nan sai auta Amira.
Mun tashi tare da Ahmad a gida ɗaya, kuma soyayya ta kullu a tsakanin mu, Momi ta so Ahmad ya karanci Business Administration saboda ya kula da harkokin kasuwancinta, dan ban da wurin da muka je da ke tana da wasu wuraren ma, har ma a Kano, amma Ahmad ya nuna ba shi da ra’ayi. Sai da na kammala Masters ɗina aka yi bikin mu.
Shigowar Amira yasa Aunty Laila yin shiru tana duban ta, “Amma kin ga da yake ita auta ce digiri na farko kawai ta kammala ta ce aure take so kuma su Daddy sun yarda za su yi mata.
Cikin shagwaba ta narke fuska “Ai dai zan cigaba da karatuna”.
Tare muka fito Aunty Laila ta jani bedroom din Momi, mun samu tana waya, ta ɗago ta dube mu kafin ta cigaba da wayarta, da hannu ta yafito ni na matsa kusa da ita, ta kamo hannuna ta zaunar da ni kusa da ita. Sai da ta kammala wayar ta kara matso da ni kusa da ita. “Laila ta ce min an yi miki abokiyar zama? Na daga mata kai “To ki yi hakuri kin ji Daughter? Na kuma daga mata kai “Ki yi kokari ki kama mijinki, ba ruwanki da wasu kishiyoyi, ki gyara kanki”. Ta mike ta fita kafin ta dawo da wasu kaya a hannunta “Ga kaya nan nayi miki tsaraba ki yi ma in low ɗina kwalliya”. Ta miko min wasu turaruka “Wadannan na sirri ne dan maigidanki kawai za ki yi amfani da su, ki kasance kodayaushe cikin tsafta, ka da ki sake ya rika ganin ki a yamutse, sai girki ki iya girki me dadi, ko ta nan za ki sace zuciyar miji, kin ga Amirana aure za tayi, da kaina nake shiga kitchen Ina koya mata da na gane bata so”
Haka tayi ta yi min nasiha wadda na ji dadinta kwarai sai godiya nake. A karshe Aunty Laila ta ce “Sana’a take son farawa Mommy, shi ne na ce ta bari ki zo mu nemi shawarar ki, dan ke ce business woman” daƙuwa tayi wa Lailar ita kuma Lailar ta kama dariya, “Ina ganin ku haɗa hannu ku buɗe wurin sana’a guda, akwai ginin wata plaza da ake yi ina ganin zan ba ku shago Daya sai ku zuba kaya, sai ku je ku yi nazari ku ga me za ku sa ka” Godiya muka yi mata. Sai da ta fita Laila ta buɗe jakar da ta bani dogayen riguna ne guda huɗu, sai riga da wando su ma hudu, sai riga da siket su ɗin ma huɗu, duk kan su kuma haɗaɗɗu ne masu asalin tsada.
Da muka yi shirin tafiya kudade irin kyautar su ta manya babanta ya bata ya ce ta riƙe min.

Sai yamma likis na koma. Inda Aunty Kulu ta ce “Hala kin manta da wankan? Na ce “A’a Aunty” ta nuna min toilet “To yi maza ki shiga”
Sanda na fito missed call din Tahir uku na samu na kira ya daga yana tambayata ina na shiga. Na ce “Wanka” ina jin ajiyar zuciyar da ya fidda “Har yau ba a gama sa miki tafasasshen ruwan nan ba? Kai na daga kamar yana kallona “Dama kira nayi in ji kin dawo” na ce “Na dawo” ya ce “Ya yi kyau, kina lissafin kwana nawa ya rage in dawo” idona na runtse na dafe goshina “E” wata tambayar ya kuma wurgo min “Kin warke ko yanzu, ba ki jin wata matsala a jikinki? Na ce “Na warke Alhamdulillahi” “To ma sha Allah sai ki yi shirin tara ta”.
Ya katse wayar ya bar ni sake da baki, dan sosai na gano inda zancen sa ya dosa. Namiji kenan, kana da mata uku reras a gabanka amma kana harin wata, cikin ukun ma hada Amarya.
Aunty Laila ta kawo min dinkunana wadanda suka yi matukar yin kyau har ba magana dan wuri ne na gwanaye, kuma kwararru.

Aunty Kulu ma a nata fannin ta ƙara ƙaimi wurin gyara ni da kanta, gashina ma ya sha gyara, jikina kuwa har sulbi yake ban da kamshin da ya kama jikina, nayi wani irin kyau ga cikar jego.
Saura kwana biyu ya dawo na tafi gidana da masu aikin Aunty Kulu mata biyu, muka gyara wurina, an wanke abin da ke buƙatar wanki na gogewa an goge, komai an gyara shi tsaf har labulayya da zanen gado an sake.

Ana gobe Tahir zai dawo, wata cikin masu aikin Aunty Kulu tayi min kunshi ina zaune zaman jiran ya bushe, wasu ƴanmata suka zo yin ƙunshi, wadda tayi min tayi wa daya a cikin su dan su biyu ne kuma ɗayar kawai za a yi wa. Sai da ta gama saka mata lallen ta fita, wadda aka yi ma wa ta dubi wadda suke tare, “Kin san nan wane gida ne ƙawata? Girgiza kai tayi dan hankalinta na kan wayarta. “Gidan su gayen nan ne da ya auri Latifa”.
Faduwar gaba na ji jin zancenta sai na ƙara kasa kunnena, idanuna na kan wayata dan kar su gane ina sauraren su, ita kuma saurin barin kallon wayar tayi ta fuskance ta, “Dan Allah? ya aka yi kika sani” “Ai na dade da sani” Ƙwafa waccan tayi “Allah ban yarda yarinyar nan ba abin da tayi wa gayen nan ya aure ta, da ganin su ma ajin rayuwar su ba iri daya bane, meye ban yi ba dan in samu ya dube ni kawai, ke bama ni ba gaba dayan mu duk wacce ke zuwa wurin na su wace ce bata yi fatan ya kula ta ba amma ba wacce ya taba kallo, sai ita daga zuwan ta, wai ya Aure ta”. Ta ƙarashe maganar da takaici me yawa a muryarta. Ɗayar ta karɓe “Ke ita fa ba a garin nan ta san shi ba, nan ɗin ma da kika gan ta shi ta biyo “. Waccan ta buɗe ido “To! ita kuma daga ina take? “Yar Kaduna ce, a yanda na samu labari, tun bai yi auren fari ba take bibiyar sa tayi tayi su buga duniya ko da ba zai aure ta ba amma bata samu nasarar hakan ba kin dai ga gidan su, Babansa shahararren malami ne, maido shi aiki garin nan ta biyo shi tana da yan’uwa na jone jone ta zauna gidan su, tana barikinta shi kuma ta da ɗa manne mishi.
Anan ne ma ta samu hankalinsa, kin ga har ta dace ya aure ta. Cikin matukar jin zafi waccan ta ce “Ta dai taki sa’a asirinta ya ci”. Shigowar wadda ta sa mana lallen yasa su yin shiru, nawa ta duba ta ce mu je in wanke, na tafi na bar yammatan, zuciyata cike da tunani kan maganganun su.

Da daddare muna zaune da Aunty Kulu. Nasiha take min game da zaman aure, har ma da yanda zan mu’amalanci kishiyoyina. Kuɗaɗe ta miƙo min, na dube ta dan neman karin bayani ta ce “Malam, ne ya bayar ya ce in saya miki abubuwan da suka dace,. shi ne na ce bari in ba ki ko da abin da kike sha’awa sai ki saya in kuma babu sa abin ki a banki”. Na ce “Yanzu dai ban da bukatar komai, ki ajiye kuɗaɗen a hannunki” ta ce “Sam ki karbi abin ki ke ya ba” wasu kwalaben humra ta dauko guda biyu “Ni kuma ga gudunmuwa ta nan, Ummu na musamman ne, ki tabbatar duk sadda za ki yi amfani da su, za ki wurin megida ne, dan Namiji duk taurin kansa ya shaƙa sai ya biyo, ki adana su da kyau su ne makamanki”. Na ce “To” kiran Kawu da ya shigo wayarta yasa ta tashi da sauri ta ce min tana zuwa.
Kwanciya kawai nayi, zuciyata na jinjina tsantsan karamci na wadannan bayin Allah. Dan haka da safe da muka yi waya da Ummata, ta ce in hada ta da Aunty Kulu, godiya sosai tayi mata bisa karamcin su a gare ni. Na je nayi wa Kawu Attahiru bankwana gami da godiya, Aunty Kulu ce ta raka ni gidana, bata jima ba ta ce min za ta koma dan tana da ayyuka, har ƴar ƙwalla nayi ta sabo da muka yi.
Ƙayataccen girki nayi wa megidan da abin sha, jirgin yamma ya biyo.
Wanka nayi na sha kwalliya da riga da siket na wani haɗadden less me ƴan ƙananan hudoji, da duwatsu, kayan sun zauna jikina sun fidda halittata, na murza humrar da Aunty Kulu ta bani ana sallar magrib ya shigo dan haka alwala kawai ya yi ya nufi masallaci, ni ma sallar nayi na daɗa gyara kwalliyata. Har ya dawo na zuba mishi abinci, a lurar da nayi zuciyarsa a ɓace take, dan ya tsare gida, ƙara nutsuwa nayi tun da na tambaye shi yanda ya baro su, dan Ummata ta ce min har gidan mu ya je, kammalawar sa wanka ya yi da ruwan da na hada mishi, ina zaune falo amma gabana sai faduwa yake sai addu’o’i nake dan ban san dalilin da ya sa ya ɗaure min ɗin ba, jin yana kiran Sunana yasa ni miƙewa kwance na same shi ya yi ɗaiɗai daga shi sai guntun wando, “Yi shirin kwanciya ki zo mu kwanta” Umarnin da ya bani kenan. Falon na koma na kashe komai sai na rufe kofar na cire kayan jikina na mayar da na barci humrar na ƙara sawa kadan sai na hau gado addu’o’in kwanciya na shiga karantowa na gama sai na shafe jikina na lumshe idona na ji ya mirgino inda nake sai ya rungume ni, ajiyar zuciya muka fidda a tare. Abubuwan da suka faru a tsakanin mu a wannan dare masu tsayawa a rai ne, daren yana cikin dararen da ba zan taba mancewa da su ba a tarihin aurena da Tahir.

Da safe mun tashi yana ta ji da ni sai zuciyata tayi min sanyi, sai gobe zai koma wurin aiki dan haka tare muka wuni, da na leƙa wurin Aunty Laila dan mu gaisa sai tsiya take min na baro ta ina cewa ki dai ji da sharrinki Aunty Laila.

Da daddare yana zaune ina kwance jikinsa, hotunan ginin gidan da yake yake nuna min ina ta yabawa tare da addu’a.
Haka rayuwa ta juya min, na samu lafiya da walwala ina kokari wurin kula da ibadata da mijina, na goge na waye zama da Laila, na koyi gyara jikina da nakaltar yanda ake kwalliyar, kashe min kudi kawai Tahir ke yi daga suturu zuwa kayan gyaran jiki da na kwalliya. Inda duk Laila za ta za ta gayyace ni, shi kuma bai taba hanani ba har gidan su Laila mun je tare da shi dan ni tuni na zama ƴar gida. Duk sati biyu yake tafiya Kaduna saboda gininsa, idan ya tafi ni kuma zan kai wa gidan Kawu Attahiru ziyara inda Aunty Kulu za ta gyara ni ciki da bai.
Wata ranar Laraba da yammaci na shiga wurin Aunty Laila. Girki take haɗawa ni kuma ina zaune kan wata drower jikin window ina latsa wayata, ɗagowa nayi na dube ta “Aunty Laila na samo mana sana’ar da za muyi ta waiwayo da ludayi a hannunta “Wace sana’a ce? Na ce “Mu sa kekunan dinki, sai mu samo kwararrun teloli mu zuba suna ɗinki muna biyan su” ta ce “Good idea dama shagon da Momi ta bamu jikin wanda take saida material ne” wayarta ta jawo momin nata ta kira ta shaida mata shawarar da na kawo ita ma tayi na’am ta ce mu hada kuɗaɗen mu za ta neme mu.
Muna cigaba da maganar na hango shigowar motar Tahir ta window da nake zaune, kasa na duro “Na tafi Aunty Laila” ta ce “Habibi ya dawo kenan? Na fito yana kokarin parking kallon da yake jifana da shi bayan fitowar sa, yasa na sha jinin jikina wuce ni da ya yi ba tare da ya yi min magana ba yasa na bi shi cikin sanyin jiki, dan gano laifina ya hanani shiga wurin Laila ba mayafi, jikina na duba wando da riga ne na material rigar karama ce sai wandon falazo sai baby hijab da na sanys
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Haƙuri nake ba shi bai ce komai ba, har ya sauya kayan jikinsa, ya zauna falo bai min magana ba. Haƙuri na ƙara ba shi sai na shiga ba shi labarin shawarar da muka yanke ta buɗe shagon ɗinki. Amsa min da ya yi yasa na gane ya haƙura, wayarsa ya miƙo min “Ga Hajiyar tudun wada, ta kira ni wai in haɗa ta da ke, dan kin kirata bata ji, na amsa sai da muka gama gaisawa da ita da Malam sai na ce ta bai wa su ƴan biyu, suka yi ta min shirmen su ina dariya.

Kwanakin da aka dauka ba masu yawa bane aka bude shagon ɗinki na zamani aka kuma nemi kwararrun teloli aka zuba, mallakin mu ni da Laila.

Wani hantsi ina aiki a bed room ɗina, na shirya kayan guga, na hango tsayuwar motar gidan su Aunty Laila, ganin Mominta ta fito yasa mamaki kana kama ni dan bata taɓa zuwa ba. Saurin kammalawa nayi dan in je in gaishe ta, hijab na sanya doguwa har ƙasa dan Ahmad yana gida, kasantuwar weekend ne, Tahir ma ya je kankara. Sai da na shirya mata dan abin taɓawa a faranti sai na isa wurin Laila, daga ita sai Ahmad na samu zaune suna magana, da Sallama na shiga na ajiye tiren a gabanta, sai na zauna kusa da kafafunta na soma gaishe ta, dafa ni tayi tana amsawa, kafin na gaishe da Ahmad. Ban ga Laila ba ina tunanin tana kitchen, na fito na koma wurina.
An shafe sama da awa biyu Momi ta fito za ta tafi, tare da Aunty Laila suka shigo wurina, ƙara gaishe ta nayi muka taɓa yar hira, da ta tashi za ta tafi wata leda ta ajiye min. Kayan yar Sokoto ne, “Jiya ta zo” na ce ,”Na gode Momi, Allah ya kara girma”. Sai da muka raka ta har inda motar da aka kawo ta take, ta shiga muka rufe kofar, motar Ahmad na bayan ta ta har suka ɓace wa idonmu.
Wurina Aunty Laila ta bi ni, muna shiga ta miƙo min ledar yar Sokoto da Momi ta bata, iri daya da tawa. “Ga shi ki haɗa” Haɓa na riƙe “Wai sai yaushe za ki gane alfanun magungunan nan ki riƙa sha? Gatsine tayi “Ke ni fa ba zan iya shan abubuwan nan ba” na wuce kitchen ina dauko kofi, “Da za ki san amfanin su Aunty Laila, da ba sai nayi ta rokon ki ba, za ki sha”. Kai ta girgiza tana kallona, na haɗa tsimi, da gumba da zuma na sha. ” Kin san labarin da na zo ba ki? Na ce “A’a” ta gyara zama “Daddy ne ya biya mana Saudiyya mu duka gidan mu, shi ne Momi ta zo rarrashin ɗan ta, ya ajiye aikinsa, dan ita dai aikin nan na Ahmad yana takura ta, duk inda za su sai dai su tafi babu Ahmad, saboda yanayin aikin sa, ta ce ya fadi duk irin sana’ar da yake so za su ba shi jari ita da Daddy, ya bar aikin. To ya dai roke ta, ya ce ta dan ƙara mishi lokaci zai ajiye aikin kamar yanda take so. Ta ba shi keys na gidan da Daddy ya gina mishi, ta ce wannan umarni ne ba shawara ba, dole ya tashi anan”.
Take hankalina ya tashi na ce “Yanzu tashi za ki yi ki bar ni anan, Aunty Laila? Murmushi tayi “Kin kuwa san kafiyar Ahmad? ba lallai mu tashi ba, zai san yanda ya yi ya lallaɓa ta. nayi murmushi “Mu’amalar Momi, da ya Ahmad tana burge ni, wani lokacin na kan yi tunanin kamar shi ta haifa ba ke ba” ita ma ta murmushin tayi “Kafin ke mutane da yawa sun faɗi haka, wata irin kauna ce tsakanin su”. Mun jima muna hira kafin ta koma sashenta.

Da Tahir ya dawo nake ba shi labarin tafiyar da su Laila za su yi zuwa aikin hajji. Na haɗa da rokonsa ya kai ni gida, ya ce ba yanzu ba.
Har na manta mun yi maganar zuwa aikin hajjin su Laila sai ga shi da takardu wai za mu je in yi passport ya biya min za mu tafi tare da su Aunty Laila, har ya je ya yi ma mahaifinta magana za su tafi tare da ni. Murna sosai nayi jin ni ce za ni kasa me tsarki sauke farali. Amma har kamar Laila ta fi ni jin dadin za mu tare, dan ita wannan ba shi ne zuwan ta na farko ba. Na ƙara roƙon Tahir ya kai ni gida in yi Sallama da su, ya ce A’a sai na dawo” jin da nayi yana waya na fahimci idan na tafi wata daga cikin matansa zai kawo, dan Mmn Ummi ta bani labarin matan nasa sun bar aiki, wai tun zuwan da ya yi ya yi wata guda, ya tada musu balli, ya ce dole duk wadda ke son zama da shi ta ajiye aikinta ta kula da aurenta. Sun girgiza duk kan su amma tilas suka haƙura. Sai na dauke duk wani abu nawa, har Suturu na na kai wa Aunty Kulu, ina dai ta fargaban idan ya tambaye ni abin da zan ce mishi, sai bai ma tambaya ba.

Bamu tashi da wuri ba, dan mu ne jirgin karshe. Ranar da zamu tafi muna Sallama da Tahir duk da idon mutane sai da ya kama hannayena ya riƙe cikin nashi, “Ki kula da kanki Ummulkhairi, Allah ya tsare min ke”. Na kasa cewa Amin dan zuciyata da ta tsinke har sai ga hawaye. Handkerchief ya fiddo ya goge min, sai ya ciro wasu kudade Dalar Amurka ya damka min a hannuna, “Kar ki ce za ki yi wata tsaraba, Ummulkhairi ki ci abinci me kyau, kar ki dawo a rame, ki yi ibada. Na daga kai muka haɗa ido, “Kuɗaɗen nan fa sun yi yawa, za a bani na guzuri” murmushi ya min kafin ya kai ga magana sai ga Laila ta karaso akwai ƴar kunya tsakanin su, dan haka sallama ya mata muka wuce ina jin ba dadi a zuciyata.

Aikin hajinmu me daɗi muka yi, dan kasancewar iyayen Laila a tare da ni. Hotel din da muka yi masauki na musamman ne kuma yana kusa da harami dakin mu daya da Laila, Momi da Amira, sai Daddy shi kadai, Ahmad dai ya zille bai zo ba, ya ce sai za su dawo Umara.

Mahaifiyar Laila, Haj Asma’u, mace me kwazo da sanin ciwon kanta, wayayya me dimbin ilimin addini da na zamani. Bata barin mu haka nan, kullum muna wurin ibada, har muka kammala aikin Hajji. Daga Saudiya Dubai za su wuce, daga can su shiga China za a yi ma Amira sayayyar kayan aure. Daga ni sai Aunty Laila ne masu komawa Nigeria, samun mahaifinta tayi ta ce ya roki Ahmad da Tahir su bar mu mu tafi tare da su. “Anya Lailata aka yi haka ba a shiga hakkin mazajenku ba? Kafa ta buga kamar wata yarinya karama, “Haba daddyna ba wani shiga hakki duka sati nawa ne? Ya ce “Shi kenan”. Tsalle tayi ta mika mishi wayarsa da ke kusa da shi da ɗai ɗari ya kira kowannen su ya nemi alfarmar barin matan nasu su tafi tare da su, wanda duk kan su dauriya me yawa suka sa wurin amsa wa dattijon.

Aunty Laila ta same mu tare da Momi da Amira da murnarta ta bamu labari. Kai Momi ta girgiza “Ai da ina wurin ba za a yi wayar ba, Alh ya yi ta biye miki da shirmen ki, da wane ido za mu kalli yaron nan Tahir in shi Ahmad ba yadda zai yi da Daddy.
Wani kallo Aunty Laila ta fakaici idon Momi tayi min “Oya taso mu je” miƙewa nayi dan dama a shirye nake, ta dubi Mominta, “Saura ke Momi ki tashi mu je” “Ku je abin ku, zan huta ne” marairaicewa Laila tayi har ta samu Momin na ta ta yarda za ta. Kama hannuna tayi “Mu je mu yi wa Daddy Sallama, kafin Momi ta shirya”. Inda Aunty Laila ta bar shi nan muka same shi, muka shaida mishi za mu fita sayayya, kuɗaɗe ya ciro ya damka ma Lailar ni ma ya bani kamar yanda ya bata, muka yi godiya muka fito. Mahaifiyar Laila na gaba muna bayanta, wani katafaren wurin saida turaruka muka shiga, mu wurin na sawa a daki muka nufa, Momi kuma magunguna irin na su na can ta saya mana ta haɗa kuma har sayayyar da muka yi ta biya kudaden. Daga nan sai wurin sayar da kaya, laffaya muka saya kala kala ko in ce Momi ta saya ta saya mana, har Aunty Kulu na zabar ma masu kyau.
Mun taho bisa hanya ina ta wa Aunty Laila mita, “Kullum za mu sayayya sai kin uzzura wa Momi, ko bata da sha’awar fita, dan wayon ta biya kudaden duk abin da muka dauka.
Shi kuma Daddy dole sai kin kaimu yi mishi sallama shi kuma duk zuwa zai dumbuzo kudi ya bamu, ni kam tun zuwa na ban kashe ko kwabo ba, komai su Daddy ne da Momi”.
Maimakon ta bani amsa sai ta shashantar da maganar, ta hanyar nuna min wani shagon dogayen riguna, haka muka shiga kuma Momi ta biya duk abin da muka dauka.
Ban gane me Aunty Laila take nufi da abin da take yi ba sai ana saura kwana uku mu bar garin ina zaune a masallacin Annabi, karatun Alkur’ani me tsarki nake. Wayata ta shiga vibration dan na sa ta a silent, dubana na kai inda take sunan Aunty Laila na gani na ɗauka ina magana can kasan makoshina “Ki yi sauri Ummulkhairi ki dawo za mu fita” kashe wayar nayi na soma tattara nawa ya nawa, na rataya jakata, cikin nutsuwa na riƙa takawa har na koma masaukin mu, na samu dama Laila jirana take. Yau dai bata ce wa Momi sai ta bi mu ba, ko Amira ƙanwarta da ta ce za ta raka mu, cewa tayi “Kwanta abin ki ki huta ƴanmata”.
Amma sai da ta kaimu wurin Daddy muka yi mishi sallama, shi kuma ba fashi ya ciro kudade ya bamu ya ce mu kara sayayya.
Bata kai mu ko’ina ba sai wani katafaren wurin saida kayan ƙarau na adon mata, dukiya ce iya ganin idon ka. Duba na tayi “To Hajjaju me son kashe kuɗin ta, ga lokacin kashe su ya yi, Allah ma yasa su ishe ki. Murmushi nayi ina naɗe da hannuna a kirji, “Me kenan za a saya malamata? Ita ma murmushin tayi “Ina son ki sayi sarƙa da ƴan kunnaye kamar set uku ko hudu iya dai inda kudinki suka tsaya, sai bangul ina son ki saya, sannan akwai wasu awarwaraye na gwal sirara ne guda goma sha biyu, Momi ta taɓa saya min, sai zobuna na gwal guda takwas.
Girgiza kai nayi “Tirkashi! babbar magana, duk ina na ga kuɗaɗen sayen waɗannan ababen da kika lissafo ? Hannuna ta kama “Za ki gani” sai dai wani jiri da na soma ji yasa ni kasa cire kafa. Duba na tayi “Yaya dai? Na ce “Jiri nake gani sai zuciyata da na ji tana tashi, kamar zan yi amai” A taƙaice dai ka sa tafiya nayi sai da taimakon Laila, taxi ta tare mana zuwa gida. Hankalin Momi da Daddy ya tashi ganin halin da nake ciki, sai da suka kai ni asibiti, binciken larabawa kuma ya bada sakamakon karamin ciki da nake dauke da shi wanda bai cika watanni biyu ba. Bayin Allan nan suka shiga murna, da tarairayata, Asibitin suka riƙe ni suka ce sai na kwana. Muna zaune a dakin daga ni sai Aunty Laila, Ayaba nake ci tana zaune gefena “Ina ganin dai wannan ɗan namu ɗan bankwana ne, aka maƙalo aka taho da shi”.
Rufe ido nayi na ce. “Na shiga uku Aunty Laila” ta kwashe da dariya. Tsokana ta tayi tayi, har na gaji na kwanta na juya mata baya.

Washegari na tashi garau, suka sallame mu. Ba mu koma wurin sayayya ba, Aunty ta ce mu bari sai mun isa Dubai. Mun bar Saudiyya muka shiga Dubai, sati guda muka yi anan ɗin na sayi duk abin da Aunty Laila ta lissafa sai dai set na sarƙa biyu aka samu, kuɗi suka kare kaf, har na account ɗina da na canzo na taho da su wa’anda na ce mata ban so in karar da su ina so in yi alheri da su idan na koma na je gida.
Ta ce Allah zai kawo na yin alherin.
Daga Dubai sai China nan kam yawo muka yi sosai dan na gane Laila sani ba na wasa ba tayi wa garin, ana gobe za mu bar kasar dan sati biyu muka yi, a Guangzhou muka sauka sai muka wuce yiwu muka yi kwana hudu daga nan muka wuce shon-hai muka yi kwana hudu, nan ma sai muka dawo Guangzhou idan muka kwana washegari sai mu wuce.
Mun je kasuwa mun dawo daga kasuwa zuwa hotel din da muka yi masauki babu nisa, takowa muka yi a ƙafa, muna tafe muna hira Laila ta ce “Kika ce oganki ya ce Kaduna za ki sauka? Na daga kai “Haka ya ce dan an tura shi wani course na wata tara a Kadunan, amma ni kam ban san haduwa da matan nan na shi”.
Wani kallo ta min
“To ina fata dai ba tsoron su kike ji ba?
“Haba dai tsoro? fitina ce kawai bana so”
“Yawwa, yanzu ba tsoro tsakaninki da su, ai kin gane? na daga mata kai. “Duk wata haɗuwa da mace za ta yi takama da ita ke ma kin haɗe, in bokon su ke ba ki tsoro, to kema yanzu da kowa za ki yi turanci, in kika haɗu da su kwalliya sosai za ki rika dauka dan su san yanzu ba da ba ce, da ba ki iya fita sai da hijabi, uwa uba mijinki na sonki”. Ajiyar zuciya na fidda “Haka ne” sai kuma na shiga tunanin halin da muke ciki da Ogan tun rokon da Daddyn Laila ya yi mishi sai ya dauki fushi da ni, ya daina kirana in kuma ni na kira shi a dakile yake amsawa.
Abin yana damuna amma sai na sa hakuri na bar wa raina, ina ta addu’a.

Ranar da zamu taho jirgin Ethiopia muka hawo, zaman awa goma sha bakwai muka yi hada yada zangon da muka yi a Ethiopia, Abuja muka sauka karfe daya agogon Nigeria, daga cikin jerin motocin da suka zo taran Daddy muka shiga daya, nan ma Daddy waya ya yi wa Tahir ya roke shi zan kwana da su anan idan Allah ya tashe mu lafiya zai sa a kawo ni Kaduna.
Shiryayyen gidan Daddy na Abuja muka yada zango, ni dai cikin fargaba nake yanda za ta kaya mana ni da Ogan dan an kara mishi laifi.

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300*
*a 2108124716 Maryam* *nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Mun dan tattauna maganar kafin ta ce tana so toye toyen da za a yi na Amarya ta kawo in ajiye. Na ce “Sai ta kawo”
Da suka fita ni ma fita nayi zuwa dakin Haj. Nan na samu Amarya Saddiƙa sai razgar kuka take Haj na rarrashinta. Na tambayi abin da ya same ta, Haj ta ce “Ki bari, saitin da ubanta ya ƙuƙuta ya yi mata audugar sa ya sayar duka, amma ƴar nan, bata gode ba, tana ta famar kuka wai auren ma bata yi” Na kamo ta zuwa jikina ina lallashi “Yi shirun ki ki kwantar da hankalinki, kayan ɗaki sai kin zaba in sha Allah”. Haj ta ce “A’a daina faɗa mata haka, ta dai yi haƙurin”. Sai ta kara fashewa da kuka na ja ta bed room din Haj ina ta gaya mata maganganu masu daɗi har ta haƙura.
Sai da Tahir ya shigo muka nufi wurin mu tare, a falo muka samu Halima, na shiga kitchen na fito mishi da abinci bayan na ɗumama ya ce min bai jin cin komai indai kawo mishi Black tea, ina fitowa kitchen na ji yana tambayar Halima da yaushe ta dawo ta ce sai da aka yi Isha’i.
Muna nan zaune, su hali dubu ana jira miji ya gama su shige daki sai ya ce “Nan dai ba kamar Kaduna bane, baƙunta muka zo, dan haka kowacce kwana ɗaya za ta rika yi har mu koma”. Sai Halima ta ɗauke wuta miƙewa tayi ta bar abincin da take ci, dan abincin da ya ce ba zai ci ba ita ta zuba tana ci.
Na kwashe kwanonin na kai kitchen.
Sai da muka yi shirin kwanciya nake ba Tahir labarin Sadiƙa, shiru ya yi kafin ya ce “Ai idan za a aurar da yara gidan nan, ni ya kamata ace nayi musu kayan ɗaki ko? Na gyaɗa kai “Kwarai kuwa, abin da ya kamata kenan”. “Da safe ki kira min Sadikar”. Na ce “Allah ya kaimu”
Da safe kafin ya fita Yaya Lawal ya aiko kiransa, godiya ya yi ta yi mishi kan Sabulu da omo da na kawo musu ya ce ka ga yanzu an samu sauki sai a ji da abinci.
Da ya dawo wurin da muke zaune za mu karya ka sa karyawar ya yi, har sai da Sadikar da na kira ta zo ta gaishe mu, kafin ta tsuguna “Ya ce Waɗanne irin kaya kike so? Shiru tayi ya ce “Ki buɗe baki ki yi min magana, Malama” dan zakudawa tayi. “Akwai a wayata” “To yanzu in haɗa ku da Direba ku tafi Katsina ke da Ummulkhairi ta taya ki zabe, ko in sa a turo min hotuna ki zaba? Shiru tayi ya kara maimaitawa nan ma shiru gane ba za tayi magana ba yasa ya ce “Shi kenan ki je zan sa a tura min sai in tura wa Ummulkhairi ta nuna miki”. Ta ce “Na gode Baba” ta tashi ta tafi, Halima dai bata ce komai ba kamar ma bata wurin. Sai da muka shiga daki ya ce “Kin ga ma na shafa’a da maganar saya musu abinci da muka yi, amma nayi magana za a kawo”.
Godiya na mishi sai na tambaye shi yaushe zan wuce Dutsinma shiru ya yi min har sai da nayi ta yi mishi magiya kamar zan yi kuka, sannan ya ce sai an gama bikin gidan nan. Shiru nayi sai ga hawaye yi ya yi kamar be ga me nake ba, ya shirya ya yi ficewar sa. Tun zuwana kankara yan gidan mu ke ta kira na su na tambayata yaushe zan taho, Sallamar Maman Sadiƙa da na ji yasa ni goge hawayen sai na fito, godiya ta min kan abin da nayi wa diyarta.

An shiga hidimar biki. Duk kuma wata ɗawainiya ni ake gaya wa ni kuma in gaya wa Tahir, baya ƙi sai ya yi anan na gane ba wai bai son taimakon ƴan’uwansa bane, me ɗora shi bisa hanya ne bai samu ba.
Mota biyu aka kawo na abinci, mota daya yan’uwansa suka raba a tsakaninsu, ɗaya kuma aka raba tsakanin dangi da makota da mabukata, hakan ba ƙaramin dasa farin ciki ya yi ba a zuciyoyin jama’ar gidan. Sai ana saura kwana biyu biki su Aunty Kulu suka iso, zo ka ga murna wurina, gidan Kawu Attahiru da ke garin suka yi masauki, ni na shirya musu abinci, barci kawai ya raba mu.

Zagewa nayi duk wata hidima da ni ake yi, duk ma abin da za a yi sai an neme ni, Halima dai tuni ta gudu ta bar min wurin ta koma gidan su.
Kwalliya sosai na sha da bikin, ga gwala gwalai na da na fiddo nayi ta caɓa ado, duk inda na bi sai an kalle ni, balle da Aunty Kulu ta fiddo kayan gyaran ta ta kuma gyara ni.
Ranar buɗan kai ya ce zai kai ni gida daga can ya wuce Kaduna. Nayi Sallama duka da matan gidan da Haj, har na shiga mota zai ja wani matashi ya zo gaishe da Tahir ya yi kafin ya faɗa mishi Malam Lawal na kiransa, ya ce yana ina. Ya ce yana gidan su mai waina, mamaki ne ya rufe shi sai dai ya bi bayan yaron. Dan gidan su Halima ne gidan su mai waina me wainar kakarta ce.
A dakin Mahaifiyar Halima ya kuma shan wani mamakin, Yayun shi ne Maza duk kan su ke zaune a dakin, ga mahaifiyar Halima da mahaifinta, sai ita Halimar da ke zaune tana rusa sharbar kuka tana rattafo rashin adalcin Tahir, ya kwashe dukiyar sa ya ba wannan yarinyar da ya auro a Dutsinma, sai yanda ta ga dama take yi. Tahir da ke duban ta cikin mamaki ya ce “Kuma duk ni ke yin wadannan abubuwan da kika lissafa? Cikin daga murya ta ce “E mana, E mana, nan da ta je aikin Hajji, dukiya ka na ɗa mata ta sawo gwala gwalai na miliyoyi, duk wanda ya zo bikin nan ai ya gani, ban da suturu na alfarma da take sawa. Sai ta fashe da wani irin kuka. Yayansa Babba ya shiga mishi nasihar girman adalci, a tsakanin iyali. Sai da ya gama bai katse shi ba sannan ya rantse da girman Allah kan bai ba Ummulkhairi kwabo kan gwala gwalai ko suturu da take fadi ba, da dai za ta tafi na ƙara mata kudi kan guzurinta, kuma ke ma da muka je tare na ba ki, abin da dai na sani akwai wata makociyar mu a Lagos tare suka yi tafiyar da iyayenta, Ummulkhairi ta shaida min basu bari ta kashe ko kwabonta ba, sayayya su suke mata har kudi suke bata nan ta sayi gwala gwalan da kike magana”.
Nan dakin aka ɗauki salati ana wa halima fadan zargi. Tahir ya shiga kwance abin da Halima take mishi, da yanda bai jin daɗin zama da ita yana haƙuri ne albarkacin iyaye ana tare.
Amma yanzu daga ta kawo kararsa to su bar ta ta huta. Ca! aka yi mishi ana ba shi haƙuri, Halima sai ido ya raina fata, ya bar ta a gidan nan na su ai da ta shiga uku, tunda bakin cikin Ummulkhairi yasa ta baro mata can ta dawo gidan su, komai a aljihunta take ma kanta hada gidan nasu ma, ƴan kuɗaɗen nata ma sun kusa karewa. Tana cikin tunani ta ga Tahir ya juya ya fice. Nan aka yo kanta ana ta mata faɗa ita kam ta gwammaci ko dukan ta za su yi su sa Tahir ya tafi da ita kar ya bar ta a kankara.

Mota kawai ya buɗe ya shiga yanda na ga yanayinsa yasa ni kama kaina. Ajiyar zuciya me ƙarfi na fidda ganin motar ta tsaya a kofar gidan mu, sai ware ido nake, da Nura kanena na fara haɗa ido wanda na ga ya wuce cikin gida da sauri.
Matasan da ke zama kofar gidan suka taso ganin na fito, suna mana barka da zuwa. Ina gaba Tahir na baya na muka shiga gidan. Gwoggo ce ta kama ni ta rungume, yayyena mata duka suna gidan suna ta ma Tahir Barka da zuwa, ni dai bakina kamar gonar auduwa bai wani jima ba ya sallame ni bayan ya ci abincin da Ummata ta shirya mishi, da yaro aka haɗa shi ya raka shi kasuwa ya gaishe da Babana, ya tafi bayan ya cika su Ummata da yaran yayyena da kuɗaɗe.
Sai dare Babana ya dawo shi ma sosai ya ji daɗin gani na. Hafsa ma a daren Malam Mas’ud ya kawo ta, ai kam da ƙyar muka rabu, nayi mata alkawarin gobe ina nan zuwa mata wuni. A gado daya muka kwana da Ummata, muka raba dare muna hira tana bani labarin bayan ba ni, ni ma na bata labarin nawa bangaren yanda ta kasance min, iya abin da na ji zan iya faɗa mata.
Da safe na fidda tsarabar kowa na ɗauki ta Hafsa da diyarta na nufi gidanta. Muna cikin hira ta kewaye ni da kayan daɗi ta ce “Amma dai Ummu ciki ne da ke? Hararar ta nayi “In ji wa ya faɗa miki? Ta ce “Idona, a yanda na gan shi ma ya fara nisa” gyara kafafuwana nayi “Ba ke kadai ba, Ummata ma ta gane” Kin fara zuwa Hospital ne? Na girgiza kai “Ban ma san ta inda zan fara shaida wa Ogan ballantana har in ziyarci Asibitin” gaba ɗaya ta zaro ido “Wace irin magana kike gaya min Ummu sai ka ce wata yar fari? Kina nufin bai sani ba? “Hafsa, saboda yanayin wadanda nake tare da su. Nan na shiga labarta mata zamana da kishiyoyi, da yanda nayi ta fama da barin ciki a Lagos”. Sosai ta nuna razanarta “Yanzu cikin wadannan iblisan Allah ya kai ki zama? Na ce “To ya zan yi? Ta jinjina kai “Allah ya daɗa kare mana ke, yasa ki sauka lafiya, amma dai ki yi kokari ki je Asibiti”. Na ce “Ina ta tunanin haka, kuma in sha Allah zan je”.
Kiran Tahir da ya shigo wayata ya katse mana hirar mu, mun ɗan jima kafin muka yi sallama.
Amma dai na fahimci yana son ki Ummulkhairi, kina da matsayi a zuciyarsa, dan haka za mu dage taya ki da addu’a, daga ba ki nufin kowaccen su da sharri Allah zai ɗora ki kansu”. Na ce “In sha Allah”
Da Azahar Malama ya shigo da kaji ya ce Hafsa ta gyara min, dan haka sai yamma sosai na koma gida dan fitowa nayi na taya ta aikin.
Kwanakin da suka biyo baya ziyara nayi tayi, har yaya Sani ma ya zo, na ce bi shi ya ce In nemi izinin mijina na tambaye shi ya ce A’a tilas na haƙura.
Ranar da nayi kwana tara na samu wayar Tahir da daddare ina kwance a dakin Ummata, su kuma suna tsakar gida suna hira. Ya ce “Kina kuwa kirga kwanakin da kika yi? Na ce “E” ya ce “Ba ki ga ya dace ace kin dawo dakinki ba? Ido na zaro kamar yana kallona “Haba duka kwana fa tara nayi? To shi kenan ki shirya gobe Direba zai iso, sai ku wuce ƙanƙara ku kwana jibi ki dawo gida, ganin gidan ya isa ni ma ina bukatar matata a kusa” kunya na ji kamar yana gabana na shiga ba shi haƙuri babu wanda ya san zan tafi gobe ban ma kowa sallama ba.
Da kyar dai ya kara min in ƙara kwanaki huɗu anan sai mu isa ƙanƙara in kwana daya. Godiya na mishi na ajiye wayar, ina tunanin gidan da na baro, na shafa cikina wanda ya fara motsi ina jin sonsa da kaunarsa tare da fatan Allah ya bani rayayye me albarka kifawa nayi nayi rub da ciki ina tuna ya zan ji a ranar da na gan ni da yaro ko yarinya? “Anya Ummu, maza ki tashi daga rub da cikin nan, ko bayan babu kyau a musulunci kin sani, masu ciki basa yinsa yin sa ke sa a haifi yaro da cibiya ta nade mishi wuya, da kwanciya ki kalli sama, in kuma za ki juya kwanciya sai kin tashi zaune”. Zaunen na tashi ina duban Ummata da ban san sa’adda ta shigo ba. Kwanon hura ta miƙo min da ake damawa Babanmu, “Ko za ki sha? Kai na girgiza “Na koshi Ummata cikina ya cika, wai kin ji shi Umma, nan da kwana hudu zan tafi” ajiye kwanon hurar tayi “To ai babu laifi, an gode mishi, Allah ya kaimu”.
Daga ranar kuma shirin komawata Umma ta shiga yi ta kuma aika wa ƴan’uwana ranar da zan tafi, mazan kuma duk wanda ya shigo za ta shaida mishi.
Kamar yanda suka zo ranar da na zo, haka ranar da zan tafi ma suka dawo kowacce kuma da tsarabarta. Sai Azahar direban ya iso muka dau hanya wanda da rarrashi na fito gidan har kuma ya fara gudu a titi hawaye bai daina gudu akan fuskata ba, na sa kwallen da Yaya Mustapha ya miƙo min na share fuskata.
Da isar mu Haj kawai na shiga na gaida na koma wurin mu nayi kwanciyata ban ga Halima ba, sai nayi tunanin ko ita ma ta koma Kaduna, sai da na shiga wurin maman Ummi mata uku na samu a ciki ana ta hira anan nake ji suna labarin abin da ya faru da Halima har ma na ji ba ƙaramin artabu aka sha da Tahir ba ya kafe sai ta zauna a gidan su. Sai da aka haɗa shi da Kawu Attahiru shi ya yi mishi magana jiya tayi shatar mota ta koma. Ni dai iyaka ta sauraro ban yarda na tofa tawa ba, gudun me zai je ya zo, na dai yi musu sallama Haj har da su matse ido.

Mun shiga Kaduna ana sallar la’asar raina na ji ya yi duhu tuna gidan da zan koma kiran Tahir na samu wanda tun tasowar mu yake kirana na ɗauka na shaida mishi mun iso yanzu.
Na samu falon shiru kamar yanda nayi tunani, na wuce ɗakina nayi sallah, duk kuma da halin da nake ciki na gajiya bai sa na zauna ba gyaran ɗakina na shiga yi, sai da naga ya yi min yanda nake so sai na yi wanka, riga doguwa ta wani yadi me taushi nasa, jin ƙwanƙwasa ƙofar yasa ni miƙewa na karasa dan budewa cike da mamakin ko waye, wata baƙuwar fuska ce a gare ni, riƙe da tray a ladabce ta gaishe ni tare da min bayanin sunan ta Laraba sabuwar me girkin da aka dauka. Na karba nayi mata godiya sai da na amsa wayoyin da ake ta kirana sannan na ci abincin, ina tunanin ni kam zan yi wa mijina girkin da zai ci duk da girkin nata da dad’i, ba zan zauna yar aiki ta bawa mijina abinci ba. Da na gama na kwashe kayan zuwa kitchen ruwa na dauko na zo fitowa muka yi kacibis da Tahir har kirjin mu na haɗuwa na matsa, muka kalli juna tare da tattausan murmushi tsakanin mu hannuna ya kama “Kin dawo? Ya fadi cikin wata murya da sai da na ji ni cikin wani yanayi na daga mishi kai sai karaf idanuwanmu suka shiga cikin na Halima da ke maƙale tana kallonmu.
Tunda ta dawo tana ɗakinta tana aiwatar da surkullen da sabon malamin da ta ziyarta a Ƙanƙara ya bata ya ce kuma wuyarta su haɗa ido da Tahir dole zai shiga taitayinsa sai yanda ta ce, duk da cewa tun dawowarta jiya aka bata miji kamar yadda ake yi a gidan to ita dai kam ka bata samu kwarin gwiwar fitowa ba, duk da tabbacin da malamin ya bata, ko kudin aikinsa rabi ya karba rabi ya ce sai ta ga biyan buƙata, wani mugun kallo ta bi mu da shi, ganin kamar ya manta inda muke yasa na bi ta gefensa na wuce hannayensa ya rungume a kirji ya bi ni da kallo har na shige, hakan kuma duk a idon Halima ta maza tayi ta karfafi zuciyarta ta tako zuwa ainahin cikin falon ta zauna, sai a sannan ya lura da ita, ƙara tamke fuskarsa ya yi, ya bi ta gefenta zuwa dakin Basma.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*KU SANI KU KARA SANI MACE ME AJI MALLAKAR KOMAI NATA TAKE BATA JIRAN ABIN SATA*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

“Tahir” ta kira sunansa, bai amsa ba, bai nuna alamar ya ji ba ballantana ta sa ran zai waiwayo, tsaye ta miƙe “Tahir” ta kuma kiran sunansa tsaki ya ja ya shige dakin Basma. Ya ɗan jima ya fito, cikin rashin tsammani suka yi kacibis dan tana tsaye tana sauraren fitowar ta sa, ba zato idanunsu suka shiga na juna, wani sarawa ya ji kansa ya yi ya dafe kan, sai ya fasa shiga dakin Ummulkhairi da ya yi niyya dan Latifa bata gidan, juyawa ya yi ya nufi sama da shigar sa zama ya yi kawai hannunsa na dafe da kan har lokacin.

Halima kuma ganin halin da ya shiga da haɗa idonsu, ya firgitata, saurin juyawa tayi zuwa nata ɗakin tana shiga wayarta ta lalubo ta kira lambar malaminta cikin tashin hankali, ko gaisawa bata bari sun yi ba ta kora mishi halin da Tahir ya shiga da hada idonsu. Wata irin dariya ya kece da ita, “Shaidar aiki ya ci kenan, Hajiya, yanzu abu daya ya rage ya ci hadin maganin da na hada miki yana ci an gama, zai dawo mai jin maganar ki, kimar ki da darajar ki da kika rasa za su dawo, babu kuma wadda za ta sha gabanki”
Murmusawa tayi tana zuba mishi godiya jin ana knocking yasa tayi mishi sallama ta bada izinin shigowa me girki ce, sai da ta gaishe ta cikin girmamawa kafin ta fada mata ta shirya tebur ok kawai ta ce tana fita ta bi bayanta, tana buɗe abincin tana tunanin yanda za ta zuba abin da aka bata Tahir ya ci shi kadai. Ta ɗan jima cikin tunani kafin ta samo dabarar da take ganin za ta fish she ta, falon ta koma ta zauna har aka kira sallar magrib sai da Tahir ya fito dan tafiya sallah sai ta koma ɗakinta, wanka tayi ta gyara jikinta, sai ta kuma fitowa falon ta samu Latifa wadda tun dawowarta sau daya su ka ga juna, sun gaisa sama sama.

Ni ma da nake zaune ɗakina ina ta sa ran Tahir zai shigo duba ni, har dai na ma cire, kamar in share fita cin abinci sai dai na fasa, ƴar kwalliya nayi sama sama sai na fito.
Duk kan su na same su zaune, mun gaisa da Basma da Latifa, Halima ce ko arzikin kallo ban samu ba, tana ta hura hanci tana shan ƙamshi.
Saukowar Ogan yasa duk aka miƙe zuwa cin abincin, kaɗan na ci dan cikina da na ji ya cushe, shi ma Ogan zama ya yi yana aikinsa a laptop ɗinsa
Kowacce ta nemi wuri ta zauna, da kansa ya nemi Halima ta kawo mishi coffee abin da ya yi bala’in mata daɗi har mu ma sai da muka gane canjawarta, na miƙe tsam sai nayi musu sai da safe, ta kasan idanu ya bi ta da kallo sai da ta ɓace wa ganinsa.
Ina shiga ɗaki gado na faɗa na daɗe ina zubar da hawaye, dan da gaske raina ya ɓaci da rashin samun marabar kirki daga gare shi, kiran Asiyar Dr da ya shigo wayata yasa ni share hawaye na daga kiran muka shiga hira kamar komai bai faru ba.

A wannan daren Halima ta samu mijinta yanda take mafarkin samu. Ya kuma mallaka mata makudan kudade kamar yadda ta buƙata, ta ce ya saya mata sarƙa nan ma bai musa ba ya amsa.
Da safe da ya shigo dan mu gaisa babu wani sakin fuska a tare da shi, ni ma sai na daɗa kama kaina, dama zaune ya same ni inda nayi karatun Alkur’ani, ina Azkar, da ya fita ban wani bi shi da kallo ba.
Miƙewa kawai nayi na kunna Tv na koma na zauna na ɗauki wayata, WhatsApp na shiga, sakonni suka yi ta antayowa daga kunna Data ta, duk yawancin su daga ƴan’uwana ne bin su nayi ina ta mayar musu da amsa, kafin muka shiga hira da Aunty Laila, magana muka yi tayi kan shagon mu na ɗinki, tana min bayanin yanda abubuwa suke tafiya, da shawarar da Mominta ta kawo mu bude Branch a Kaduna. Na ce zan yi wa Tahir Magana ya samo mana wuri.
Ta ce Manager na wancan wurin namu na Lagos shi zai nemi ma’aikata duk wanda aka yi wa interview ya haye shi kenan sai a ɗauke shi idan Allah yasa wurin ya daukaka kamar yanda na Lagos ke samun cigaba, sai mu raba kawai kowa ta ja ɗaya. Na ce “Hakan ya yi Allah ya shige mana gaba. Ta ce tana nan zuwa min kwana biyu. Na ce “Na dai ji ki Aunty Laila, Allah yasa da gaske kike” mun ɗauki dogon lokaci kafin na kashe datar.
Ɗakina na gyara zuwa bathroom, nayi wankana na gyara jikina. Bani da niyyar fita dan yin break fast, kwanciyata kawai nayi bisa sopa.

Tahir na barin gidan, Halima da ta dawo rakiyar sa ɗakinta ta faɗa ta lume a kujera tana kaɗa ƙafa cikin nishaɗi sai sakin murmushi take.
Knocking din da aka soma yasa ta tsuke fuska, tana bada umurnin shigowa, Latifa ce ta shigo ganin ta bai sa ta saki ranta ba, hakan bai damu Latifar ba sai ma murmushi da ta saki “Hutawa kike kenan? Ta faɗi tana kokarin zama, kallo Halimar ta bi ta da shi bata yi magana ba, bata damu ba ta cigaba “Yarinyar nan da ta dawo jiya, ita za tayi girki koko waccan shashashar, sauna me daɗin kishi? Kyaɓe baki tayi “Ke ma kin san dole ita da ta dawo tafiya ita za ta karɓa”. Siririn tsaki ta ja kafin ta farga da wayar da Halima ke miƙo mata.
“Meye a ciki? Ta tambaya tana mika hannu “Ki duba” Halima ta faɗi tana wani shu’umin murmushi. Zumbur Latifa ta mike kafin ta koma ta zauna tana share zufa kamar ba sanyin Ac a ɗakin. Ashariya ta lailayo ta antaya “Lallai ma a gaida Namiji munafiki, duk cikin mu wake da irin wadannan mahaukatan gwala gwalan? Koko zai ce ba shi ya saya mata ba”.
“Kema kya fadi, haka tayi ta ke ce raini da bikin nan, ta saka wannan ta fidda wannan”
“Lallai ma in ni ce, idan na yarda Allah ya tsine min, kuma girkin da za ta yi yau sai na bata mata daren”.
“Me za ki yi mata? Halima ta tambaya “Girkin zan lalata, yanda ko uwar su ɗaya da mijin ƙarshen soyayya ba zai iya ci ba, dama ina da takaicin yanda yake buɗe ciki a duk ranar girkinta, ita ga gwana”, ƙwafa tayi sai ta miƙe ta bar dakin. Wani malalacin kallo Halima ta bi ta da shi ta fara magana ƙasa ƙasa “Gaba ɗayanku, zan gyara wa kowa zama, duk kan ku sai kun fice kun ban wuri, dama wuyarta in kama Tahir a hannu”.
Sai ta janyo wayarta, malaminta ta kira ta fada mishi aiki ya ci fiye da tunaninta dan haka ya turo acc no ta ingiza mishi sauran kuɗaɗen aikinsa. Ta ajiye wayar da sauran murmushi kan fuskarta tana kara yaba iya aiki na sabon malamin nata, jininta na al’ada kawai ya nemi ta kawo da shi ya haɗa mata maganin da za ta rika zubawa Tahir a abinci, sai wani ruwa da ya bata ya ce ta shafa a fuskarta, suna haɗa ido da Tahir an gama. Tuna wani tayi da ya sa ta ta rika tsarki, ruwan ta rika dafa wa Tahir abinci duk da tabbacin da ya bata mallaka ce ta gaske bai hana Tahir ya subuce mata ba, dan haka dagewa za tayi wurin wannan mutumin bakin rai bakin fama.

Sai wuraren Azahar na fito na nemi abin da zan saka ma cikina, ina kuma gamawa na koma ɗakina, ban ga kowa ba sai sabuwar me aikin nan tana ta kokarin haɗa abincin gida, duk da dai Indo ta bi ni har daki mun gaisa.
Da cin abincina barci na shiga yi, cikin barcin na ji ana knocking ba da so na ba na tashi na buɗe, Latifa ce cikin murmushin ta da za ka rasa in da ta dosa tayi min godiyar tsarabar da na aika musu, ta ce “Na ji ki shiru shi ne na ce matar nan ba za ta shiga kitchen ba? Dan murmushi nayi Zan shiga, barci ne ya kwashe ni, na gode. Ta juya, na shiga ɗaki ruwa na sha sai na ɗaura dankwali fitowa nayi zuwa sama kamar yanda nayi zato dakin Tahir ba shi cikin kintsi, kwashe komai nayi boxes ɗinsa nasa a laundry na wanke na canza bedsheet din na share ko’ina na goge na fesa air freshener kafin na kunna turaren wutar da na ruko.
Sa’adda na sauko uku tayi dakina na wuce saboda haushin da Tahir ya bani na kudurta ba zan yi girkin ba yau me aikin tayi.
Da daddare ma kamar in ki fita cin abinci, sai na yi gudun ja ma kaina laifi, ina kuma gama ci na koma dakina, wanka nayi dan tun na safe ban ƙara ba, nayi yan shafe shafe sai na hau gado, shigowar saƙo cikin wayata yasa ni duba wayar, daga Tahir sakon yake “Ina jiranki” shi ne abin da sakon ya kunsa. Na harari wayar kamar Tahir din ne gabana ya iya min wulaƙanci amma kuma ya san ina da amfani a wurinsa ai da sai ya riƙe ginshirar tasa, cikin sauri na ƙara gyagygyarawa sai na fita zuwa saman.
Ban same shi a falo ba sai na wuce bedroom kwance na same shi ɗaiɗai bisa gado daga shi sai gajeren wando kirjinsa da ke kara dulmiyar da ni a kaunarsa waje, waya ce aje kusa da kunnensa a hands free take yana amsawa, kirjinsa yake shafawa da hannunsa, dakin ya ɗauki sanyi da ƙamshi me daɗi. Hannun ya miƙo min alamar in zo gare shi kawai sai na ji tunani ya zo min wai duk sauran ma haka yake musu ko? jin raina ya soma jagulewa yasa na fara addu’ar neman tsari da shaidan, na yaye hijab din da na ɗora saman wata sakaryar rigar barcin da na sa da dan rashin kirkinta ko hannu bata da shi.
A hankali na ƙarasa yasa hannun ya janyo ni, ya kwantar da ni gefen kirjinsa sumar kaina yake shafawa, yayinda ni kuma nake shaƙar daddaɗan ƙamshin da ke fitowa jikinsa, wata irin kaunarsa tana fizgata, ina kuma sauraron hirarsa da abokin wayar tasa. “To yanzu dai ya ka ji girkin na ta? Muryar na cikin wayar ta ratsa dodon kunnuwanmu, dan tsaki Tahir ya ja “Ta iya abokina, amma ni mutum ne da na fi son in ci abincin da matata ce ta girka ba wata macen ta daban ba”.
“Daga dai an samu nasara girkin Laraba ya yi maka, shekarar ta kusan shida tana yi wa Habiba girki, na haƙura na bar maka ita ne dan ka samu maslahar rigimar girki a gidanka, ka haƙura da dole sai ka ci abincin da matanka suka girka maka, ba dole komai kake so kake samu ba, daga dai Allah ya yi maka gata ya baka matan nan har huɗu kawai yi ta cin duniyar ka da tsinke mutumina ka bar mu da ɗaiɗai, ko fa goyo ka ce kana so rige rige za ka ga a……. “Dalla wuce mutumin banza kai dai dan iska ne Usama”. Dariya Usama ya kwashe da ita Tahir ya katse kiran. Yasa hannuwansa ya rungume ni “To ya aka yi” ya ce min cikin rage murya kai na girgiza gane hira yake so muyi dan sai cewa yake in ba shi labarin tafiyar, sai na ga bari in yi amfani da wannan damar in roke shi shawarar da na yanke sa’adda na je Dutsinma, ina so ya bar ni in rika zuwa makarantar Isamiya ta Kawu Attahiru, kusa da gidan Kawun take babbar makaranta ce da matan masu hannu da shuni da yaran su ke karatu. “To ai iyakarta Sanawiyya, kuma ke kin gama Ummuna” Na ce “E zan riƙa shiga Alhamis ne da juma’a duk littafin da kake so za a yi maka. Ya ce “Har yanzu karatun duk da kika yi bai ishe ki ba? Na daga kai “Karatu ai baya isa kuma ba a gamawa” ya ce “Haka ne” mafari kenan da na soma zuwa karatun zaure a makarantar Kawu Attahiru.
Zuwa safiya na nemi haushin da nake ji na Tahir na rasa dan tarairayar da na sha a wurinsa. Dan haka washegari zagewa nayi nayi mishi abinci wanda na san zai kayatar da shi zuwa magrib na kammala komai, ɗakina na shiga dan in shirya wanka nayi na fesa kwalliyar daukar magana dan wani dakakken less na sanya da aka yi wa dinkin da ya ƙara fitar da shi, na fiddo sarƙa da yankunnayena da zabba da awarwaro na ƙara ƙayata kwalliyar, nayi ɗauri me kyau ga sassanyan ƙamshi ina yi na zura takalmi na fito bakina ɗauke da addu’a. Fitowata tayi daidai da shigowar megidan kallo ɗaya ya yi min ya nemi haurawa saman sa, na dan ƙara sauri na karbi ledar hannunsa na bi shi a baya muka haura tare, ban bi ta kan Halima da Latifa da ke zaune muna shiga kayansa ya shiga cirewa yana gamawa ya juyo inda na zauna shiru ina duban sa, kamo ni ya yi sai ya sa ni jikinsa, al’amuran da ya shiga gudanarwa ban tsammaci zuwan su a lokacin ba kan ba yanda zan yi na biye mishi har ya samu nutsuwa, da gamawarsa tsallake ni ya yi zuwa bathroom dinsa, ni ma miƙewa nayi ina diban kayana da ya ciccillar na maida a jikina sai na sauka kasa dan komawa ɗakina, ban kalli inda su Halima suke ba dan zargin da na san za su yi da daɗewa ta a dakin nasa, ina shiga bathroom ni ma na shiga nayi tsarki da ruwa me dumi ban da lokacin wanka kayan ma ina tsoron canza su sai na fito kawai fitowata ta kara yin daidai da ta megidan dan haka sai na isa dinning nayi saving ɗinsa, su Latifa ma kowacce ta zuba wa kanta, watso da lomar farko da Latifa tayi kowa ya yi saurin duban ta kafin Halima da Basma su ma su bi bayanta megidan ne na karshe dubana ya yi “Me kika sa wa girkin ne Ummulkhairi? “Me nasa kuwa? Na fadi cikin mamaki “To ai sai ki ci ki ji” ya fadi cikin hasala cin nayi kuma a take na maido shi, dan kasa ce hade da kalanzir,. “Kasa kalanzir a girkina? Na fadi kamar zan fashe da kuka “Sai a kula a san irin kwamacalar da za a rika baiwa mutane da sunan girki”. Cewar Halima tana barin wurin. “Ina ruwan gwanaye”. Latifa ta fadi da wata yar dariya da za ta fahimtar da kai nishadin da take ciki . Tahir ma miƙewa ya yi ya haye saman sa kafin ya sauko riƙe da keys ɗinsa a hannu Basma dai umarni ta baiwa Laraba ta daho mata indomie ta kawo mata ɗakinta. Halima da Latifa na zaune cikin falon na wuce su zuwa ɗakina zuciyata na tafasa na tausayin kai irin zaman kaddarar da Allah ya doro min, na jima kafin na shiga bathroom na tsarkake jikina na fito na sanya kayan barci Addu’o’i nayi tayi iya sani na har na samu gwanin iya sata ya sace ni.
Latifa da Halima kasa barin falon suka yi har maigidan ya dawo sai sha biyu saura da suka tabbatar ba za ni turaka ba kowacce ta nufi ɗakinta cikin farin ciki.

*Maryam litee*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

Shi kuma megidan ganin har sha biyu ba ni ba labarina yasa mishi ɓacin rai dan bai san dalilina na yin hakan ba. Ga ɓacin girkina a yau wanda ya rasa shi ma abin da ya ja hakan.

Ko da gari ya waye ban yi yunkurin fitowa dan samar da abin karyawa ba. Knocking din da na ji ana yi muna tsaka da chart da Asiya ya daure min kai, na dai mike na buɗe, Laraba ce mun gaisa cikin mutunta juna kafin ta nemi izinin a akan me za a yi yanzu da safe?
Na ce tayi yanda ta saba yi na maida ƙofata na rufe.

Tahir na tashi da safe haushin rashin shigowata yasa ya fita da wuri zuwa makaranta, bai tsaya sauraron kowa ba ko wani abin karyawa.
Sai da na gama duk abin da na saba yi a ɗakina, kafin na tura mishi txt zan shiga gidan Kawu Attahiru, tsarabar da na dawo da ita na debi me yawa dan kai wa Hajiyar, da zuwa na ban wani jima ba na juyo kitchen na shiga dan dama kunun gyada da na ji ina sha’awa, Sallamar da na ji ana yi ta sa ni leƙowa, wata dattijuwa ce, gajera me jiki, kayan jikinta sun dan sha jiki hijabin ta ma a juye ta sanya shi. Suna riƙe da hannun juna ita da wata yarinya da ba za ta haura shekaru sha uku ba. Sannu da zuwa nayi mata fuskarta ta washe da fara’a, tana amsawa fitowa sosai nayi ina gaishe ta, muna cikin gaisawar Latifa ta fito, kallo ɗaya tayi wa inda muke tsaye na ga tayi kicin kicin dattijuwar ta kara fadada fara’arta tana duban latifa, magana tayi cikin yaren su wanda ban taba jin tayi ba, sai dattijuwar ta bi ta a baya zuwa dakin Latifar.
Dogon tsaki Halima da ke zaune a dinning tayi “An dai tafka asara, kana cikin wannan daular uwarka tana yawo haka a tsiyace. Wani iri na ji jin zancen Halima, dan ko bata yi gwari gwari ba na gane wannan dattijuwar mahaifiyar Latifa ce.
Komawa nayi cikin kitchen din, cike da madaukakin mamaki magana ta gaskiya bai dace a ce an ga mahaifiyar Latifa a yanda na gan ta ba, to ita ko me take ci da abin da mijinta ke bata da ba za ta taimaki mahaifiyarta ba. Na ga dai duk girkin da za ki yi na kwana biyu zai dauki kudade masu kauri ya baki, duk da cewar ba abin da za ki saya, haka zalika duk karshen wata zai dauki wasu kuɗaɗen ya ce kowacce ta sayi abin bukatunta, ko nan ina ganin za ka taimaki har yan’uwanka ba ma uwar da ta kawo ka duniya ba.
Na gama dama kunun na dauko na fito daki na shiga na sha, gama sha na sai duk kasala ta sauko min carpet kawai na bi na kwanta barci ya ɗauke ni. Na farka nayi saurin duba agogo lokaci ya yi nisa dan an kusa Sallar Azahar na fita dan kai cup din da na sha kunu kitchen in kuma ɗora abincin rana , Latifa ta tare ni ta ce ogan na neman mu a sama. Saman na wuce Inda na samu Halima da Basma sai Latifa da muka shiga tare. Zaune yake a wata kujera da na ga yana zama ya yi karatu. Sannu nayi musu shi kuma na gaishe shi, wasu fararen ledoji da ke saman wani dan stool ya nemi Halima ta dauki daya ta miƙe ta ɗauka sai Basma sai ni Latifa ce karshe wadda na fahimci duk sadda za a yi rabo irin wannan sai ka gane bakin cikin ta a fuskarta na zamantowar ta ta karshe.
Ni dai godiya nayi mishi da fatan kara samun budi na alheri a wurin Allah.
Na taso na tafi sai da na shiga daki na bude ledar, dankareriyar sarƙa ce, Dubai da ke ta sheƙin ɗauke idanu da yan kunnayenta ha da zobe. Murna nayi sosai tare da ƙara mishi addu’a sai na adana abi ta wurin da na adana sauran. Sai na fita dan yin girkin na fara aikin Halima ta shigo tsaki na ji ta fara ja ban waiwayo ba ballantana in san abin da take wa tsakin “Ke Malama wa ya ce miki yana da bukatar wannan jagwalgwalon naki? da kika shigo ki yi wa mutane. Na waiwayo na dube ta ban magana ba na maida kai na ci gaba da aikina. “Dama kin daina ba kanki wahala ki fita ki bani wuri, dan Ogan ya turo ni in sama mishi abin da zai ci”.
Ko da ban juyo ba hakika na ji abin, dan tsaki na ja “Dan Allah ki yi abin da ya kawo ki kawai, ba ruwanki da abin da nake yi”.
“Iyee lallai samun wuri, to nan in gaya miki gidana ne, ku ɗin nan duk raɓowa kuka yi ku ci arziki, kowacce sai da ta ga an tara ta zo a ci da ita, saura na aka samu ehee!
Murmushi me ciwo nayi jin zancenta, “Ai sai ki zagi ƙaddara, Halima dan ita tayi aikinta har kika gan ni anan kike min gorin na zo kwadayi ko na tarar da sauran ki, dan ban da kaddara irin wannan matsayin da kike alfahari da shi ni ma shi na baro kuma…….
Wani irin mari da ya shiga cikin idona yasa ni ganin wuta tare da daukewar ji na na wucin gadi yasa ni yin dif! Bayan ƴan sakwanni na buɗe idona dan ganin wanda ya yi min wannan aikin. Tahir ne tsaye yana huci “Ke har kin isa kiran aurena da ke ƙaddara ce ta kawo ki? Shi wancan sakaran me ya fi ni ? Ganin yanda har jikinsa ke tsima yasa na raɓa ta gefensa na fice kitchen din. Latifa na gani cikin sauri tana niyyar barin kofar kitchen din, kai hatta Basma da bata shiga shirgin kowa na gan ta kusa da kitchen din, kenan duk murna suke da abin da aka yi min?
Ɗakina na wuce idanuwana na zubar da hawaye, na hau gado na zauna tokare da kafafuwana, hannuna daya dafe da bangaren da Tahir ya mara wanda nake jin azaba na ratsa ni. Nayi kuka tamkar uwata ce ta mutu, har na ba uku lada.

Tahir shi ma fitowa ya yi daga kitchen din, ya nufi waje dan ficewa daga gidan, dan dama fitar zai yi ya leƙo kitchen dan ce ma Halima ta bar girka komai shi fita zai yi, dan bayan tashin kowaccen su Halima ta koma tana mishi kisisina wai da ganin shi bai ci komai ba, ita ba za ta iya barin sa da yunwa ba, bari ta shiga kitchen tayi mishi girki. Duk da mamakin da ya rufe shi wai shi yau Halima ta damu da rashin cin abincin sa, sai ya ce kawai ta bari fita zai yi, ta dai dage shi ne ta fito, shi kuma ya isko ta kitchen din ne ya ce ta bari fita zai yi. Ya tsinkayi muryar Ummulkhairi tana fadin kaddara ce ta raba ta da tsohon mijinta, wanda yake jin bala’i bala’in kishin sa, ta haɗa shi da ita, shi shi Ummulkhairi za ta buɗe baki ta ce ƙaddara ta haɗa su.
Yasa key dan tashin motar ya bar gidan, amma ya kasa tashin ta, kwantar da kansa ya yi kan sitiyari wai shi yau da hannunsa ya mari Ummulkhairi, take nadamar kasa saita kansa ta shige shi. Fitowa ya yi sai ya rufe motar, ciki ya koma sama ya hau, zama kawai ya dafe kai, ya ɗauki tsawon minti talatin kafin ya yi amfani da abin da zuciyarsa ke gaya mishi ka duba yarinyar nan. Ya mike cikin sa’a yana tura ƙofar ta ta buɗe bata sa key ba, bata falon sai ya wuce bedroom kuka take tana sheshsheka yanda bangaren fuskarta ya kumbura ya ba shi tsoro, ya taka har gaban gadon hannunsa ya kai jikinta ta ture hannun ta matsa, gadon ya hau sosai ya kamo ta buge buge na fara ina ture shi, jin yanda jikina ya dauki zafi ya kara ruda shi. “Dan Allah ka ga Tahir ka ƙyale ni” saurin kallona ya yi jin na ambaci sunansa, abin da yasan ba nayi sam sai dai ganin yadda kwayar idona wadda ya mara ta koma ya kara daga hankalinsa. “Yi haƙuri Ummulkhairi raina ne ya ɓaci ina jin kishinki me tsanani, ba zan juri kina ambaton wancan sakaran ba” ta karfin tsiya ya samu nasarar matse ni jikinsa, sai rokona yake in yi shiru. Ni kuma kamar yana ƙara zuga ni, ga wani uban ciwon kai da nake ji wanda na san yawan kukan da nayi ne ya janyo shi.
“Ki tashi mu je Hospital”. “Ka bar ni ba za ni ba idan ma mutuwa zan yi in mutu, dan na san bani da gata, ni ɗin kuma ba komai ba ce a wurinka”. “Ke ɗin ce ba komai ba a wurina? “E mana akwai wadda za ka yi wa tozarcin da ka min? Ka mare ni gaban kishiyoyi, duk cikin su wace ce za kayi wa haka. Sai na ƙara fashe mishi da kuka. Saki na ya yi ya mike wardrobe dita ya bude ya soma ciro kaya, har ya dauko wata bak’ar abaya haɗe da gyalen ta, ya dawo gare ni ta karfin tsiya ya zura min, duk da zazzaɓin da ya rufe ni rokona ya shiga yi in shige mu je. Na wuce yana biye da ni, shi ya rufe min kofa ya zura keyn aljihu har inda motarsa take ajiye, sai da na shiga na zauna ya zagaya ya shiga.

Latifa wadda ke kallon komai ta window ta, tayi wurgi da dankwalin ta, “Kan bal balin bala’i” ta furta tana barin dakin. Dakin Halima tayi wa tsinke, wacce ke kwance rub da ciki, farin ciki na ɗawainiya da ita. Karon farko daga yi wa Tahir maganar sarƙa ya saya ya kawo, duk da dai ba ita kadai ya saya mawa ba ta san zai yi wahala ya saya ita kadai, koma dai meye ta fada kuma anyi, ga kuma babban farin cikin ta marin Ummulkhairi da ya yi, duk da da ta tuna kishi ne me tsanani yasa shi yin marin, farin cikin ta kan ragu, kai ba za ta manta wannan rana ba.
Shigowar Latifa yasa ta daga kai, yanayin da ta gan ta yasa ta ce “Lafiya? “Ina fa lafiya” ta fadi tana wani uban numfashi “Kin san shegiyar yarinyar nan, tun shigowarki daki Sweety ya fada ɗakinta, yanzu kuma ya fito tare da ita sun shiga mota”. “Haba dai? In ji Halima da ta mike zumbur! Baki ta taɓe, “Za ki iya lekawa window ki dan ban yi tunanin sun fita gidan ba” ilai kuwa, Halima wadda har hannunta ke rawa wurin buɗe window ta hangi ficewar Tahir gidan hada Ummulkhairi zaune ɗare ɗare gaban motar.
Faduwa kawai tayi kan sopa tana da buƙatar kadaicewa a halin da take ciki, sai dai Latifa uwar san ganin kwakwab ba za ta bar ta ba. Jin shirun ta ya yi yawa yasa ta miƙe ta bar dakin tana wani killer smile.

Tahir na hawa titi ya dubi inda nake zaune na takure, hawaye na min zuba Wai ba za ki yi haƙuri ba Ummulkhairi? Banza nayi da shi wayarsa ya ciro bayan sun gaisa da wanda ya kira na ji yana tambayar ina zai same shi.
Wata haɗaɗɗiyar Asibiti me zaman kanta ya kai ni, ko da tsaida motar sai da ya yi ta rokona in dai na hawayen ko dan jama’ar da ke kai kawo a wurin. Na share hawaye da gyalen rigar sannan na fito na bi bayan sa. Mun ratsa reception kafin muka wuce Office din likita, likitan na zaune a ƙayataccen Office din nasa ya zura wa system ido. Dr Muhammad ya juyo gaba ɗaya yana duban mu, glass din idansa ya zare “Kai ba dai Madam ce ba lafiya ba? Tahir ya shafa kansa “Ita ce wallahi” “Zauna Madam Sannu da zuwa” sai kuma ya dubi fuskata “Subhanallah! Zama nayi kujerar da ya nuna min “Meke damun ki? Ya tambaye ni bayan ya karbi wata folder da wata Nurse ta shigo tana mika mishi “Ina jin zazzaɓi, sai kuma kaina da ke ciwo” “Fuskar kuma fa me ya same ta ta kumbura? Shiru nayi ban amsa ba ya Tahir “Me ya samu Madam a fuska kansa ya kara shafa “Tsautsayi aka samu marinta nayi” da sauri ya kai duban sa gare shi “Mari kuma? Marin lafiya ada fa na san kana shan maganin karfe, shi ne za ka hau yar mutane da mari so kake ta makance? “Daina min wannan fatar da na shiga uku” Tahir ya furta a hankali kamar ba shi ya yi maganar ba. “Ba ka shiga uku ba sai ka ƙara, kana duban yanayin da take ciki ai komai tayi a yafe mata, mata masu juna biyu ai haƙuri ake da su ko? Gaba ɗaya Tahir ya zare Glass din idonsa “Zancen juna biyu na ji kana yi wa kake magana me ciki? “Za ka ce min ba ka san tana da ciki ba? “Ciki kuma,? Tahir ya tambaya cikin matukar mamaki. “In kana tantama ai sai a gwada” “E a gwada, amma ina zaune da matar ka ce min wai ciki ne da ita”. “Kwarai ciki ma har ya miƙa” Nurse din da ta fita ya kira ya ce mu je ta debi jinina a gwada a kuma yi min scanning, yana son result yanzu.
ta amsa ta wuce na bi ta da ƙyar.
Yana ganin mun fice ya ɗaure fuskarsa tamau “Amma saboda Allah me ya ja maka aikata abin da kayin? Dan tsaki ya ja “Na fada maka Tsautsayi ne” ya ba shi labarin abin da ya faru. Kai Dr ya girgiza “Dama mata na cewa mu maza wadda muka ga tana bin mu mun fi sauke sharar mu akan ta, in ba haka ba me tayi na duka? “Ni fa idan Ummulkhairi tana son zaman lafiya ta daina maganar sakaran nan, dan da na tuna kafin ni Ummulkhairi ta san wani na kan ji kamar in hadiyi zuciya. Amma wallahi ina nadamar abin da nayi mata.
Sai da ta debi jinina ganin halin da nake ciki yasa ta ce In kwanta. Anan aka yi min scanning, Sai ta je ta samu Dr ta gaya mishi halin da nake ciki sai ga su shi da Tahir, magungunan da ya rubuta ya aike ta ta karbo mishi, da taimakon ta na sha magungunan barci ya fara fizgata na ji ta kawo mishi result “To kai me musu kana kallon me matarka na ɗauke da ciki har ya kai watanni shida ba ka sani ba? Anya Tahir kana kula da Madam ɗin nan taka yanda ya dace? Iska ya furzar “Wallahi ba ta gaya min ba, ni kuma da ba sanin kan abin nayi ba. Indai ba ganin ciki nayi ya yi katoto ba” wayarsa ya zaro ya yi mata albishir bai bari ta gama murnar ba ya kira Kawu Attahiru da suka yi sallama ji ya yi kamar ya kira mahaifiyarta dan ya kamata ta sani sai dai yana jin nauyi ba zai iya gaya mata zance irin wannan ba. Sai kuma ya tuna abin da ya yi wa Ummulkhairi idan ta fada wa iyayenta fa? Wata fargaba ya ji ta rufe shi sai kuma ya rika karfafa zuciyarsa Ummulkhairi matar rufin asiri ce, tun da suke bata taɓa kai kararsa ba, wannan ma in sha Allah ba za ta fadi ba.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

Shigowar Asiya wadda mijinta ne ya kira ta a waya ya katse mishi tunaninsa. Tana gaishe shi tana wucewa gaban gadon, ta kama hannuna ta riƙe cikin nata sama sama nake ganin ta dan barcin da ya soma cin ƙarfina “Me ya same ki fuska duk ta kumbura Ummulkhairi? Wani tube mijinta ya miƙo mata “Karɓi ki shafa mata” ta karɓa ya dubi Tahir “Ina ganin fa za ka bar ta anan sai zuwa gobe” kai ya girgiza “Dan Allah Malam kayi mata abin da za kayi mata in ta sa abata mu je gida, sai ta gaya min abin da nayi mata ta ɓoye min wannan alherin da ya same ni. Murmushi ya yi mishi “Amma dai ka haƙura ta warke ko? Kuma lallai ne sai ka bar ta nan ga Asiya sai ta kwana wurinta” “Ni aikin me nake zan kwana da ita, bari in je gida in dawo”.
Cikin nishaɗi yake tuƙin tare da jera addu’a a cikin ransa Allah ya sauki Ummulkhairi lafiya ya kuma jikansa ya ba shi rayayye.

Latifa gwanar zaman falo ita ya samu zaune. Shi ma zaman ya yi ganin fara’ar da ke kan fuskarsa yasa ta taya shi, tare da tambayar abin da ya same shi “Kin kusa yin ɗa ko ƴa” duk da faduwar gaban da ta ji sai da ta tambaye shi “A ina kuma? “Anan gidan daga wurin Ummulkhairi” ba ita ba hatta Halima da ke fitowa daga ɗaki sai da tayi matukar kaduwa. Ganin kallon da yake mata yasa ta kirkiro fara’a, da saurin saita kanta daga daburcewar da tayi. Ashe kwanan nan za mu fara jin motsin yara, kai gaskiya na ji daɗi”. Halima dai dan ta riga ta zo tsakiya ba halin ta koma ta iso ta zauna ita ma Allah ya raba lafiya ta ce wanda a ranta ji take ina ma duk su mutu wurin haihuwar daga ita har abin da ke cikin miƙewa ya yi zuwa dakin Basma, su biyun suka raka shi da kallo ransu fal baƙin ciki tamkar su binne kansu.
Yana tura ƙofar ya hango ta kwance riƙe da waya daga tsayen ya ce “Wai Basma ba ki gajiya da kwanciya? Birkitowa tayi tana kallonsa “To me zan yi? Dakin nata ya bi da kallo, duk da ba wani datti ya yi can ba, amma ya kamata a same shi a tsaftar da ta fi haka. Ko da dakinki kika tashi kika gyara bai fi ace kina kwance ba? Taɓe baki tayi “Yar aikina ce, ka kore ta, ni kuma ka san ba zan iya ba” duban ta yake cikin mamakin ta “To kin kusa yin ɗa daga Ummulkhairi” “Uhm” kawai ta ce ta maida kanta ta kwantar.
Juyawa shi ma ya yi dan barin dakin, yana mamakin halayyar matan nasa wai duk mata haka suke irin wannan zaman? koko shi ne bai yi dace ba. Sam ba haɗin kai, ba me shan inuwa ɗaya da ƴar’uwarta, gara Halima da Latifa suma kuma hadin kan nasu bana Allah bane, kuma ba masu yawan tayar mishi da fitina a gida a sama da su.

Ba wadda ya samu a falon ya wuce sama. Dr Muhammad ya kira ya tambaye shi ta farka? Ya ce “A’a amma Asiya na tare da ita” ya ce “Ok zai sa a dafa mata abinci sai ya zo da shi” Dr ya ce ya bar shi Hajiyarsa na hanya, za ta taho da shi. Ya ce “To sai nayi sallah zan shigo” A dakin ya zauna har sai da aka kira magrib da ya dawo sallah ne ya ce masu zai koma Hospital dan an ba Ummulkhairi gado zai kwana wurinta. To kawai suka ce yasa kai ya fita, a hanya ya tsaya ya sayi lemo da Ayaba hada Kankana da Apple, kafin ya karasa Asibitin. Sosai ya ji dadin samun familyn Dr Muhammad bayan mahaifiyarsa hada kannansa sun zagaye Ummulkhairi, mahaifiyar Dr ke riƙe da Ummulkhairi ta matsa mata ta ci tuwon Semon da ta yo mata. An gaisa sun tambaye shi me jiki shi kuma sai godiya yake sun yi shirin tafiya suka bar su daga Asiya sai shi sai Dr da ya shigo daga baya. Kusa da ni ya dawo “Ya jikin? Kallon sa nayi da kumburarren idona, ban yi magana ba. Ya dubi Dr Muhammad “Wai ba abin da za a sa ma idon nan jan ya yi yawa? Wani kallo ya jefa ma shi dan har lokacin yana jin zafin sa kan abin da ya yin. Hannunsa ya kai kan wuyana “Babu zafi” sai sannan Asiya tayi magana “E zazzaɓin ya sauka”. Sai goma Dr ya tafi kai Asiya gida, tare muka kwana da Tahir, duk kuma kokarin Dr sai da na kwana da zazzaɓi, ciwon kan ne dai na ji sauki, Tilas washegari ya fasa sallamata. Asiya ta dawo da safe da abin karyawa, haka ma na rana da daddare kuma ta kwana wurina dan ina ganin Latifa me girki ba ta amince da kwanan Tahir wurina ba. Sai da na kwana biyu sai ga su su duk kan su, daga irin kallon kurullan da suke bi na da shi, na gane labarin cikina ya je kunnuwansu, basu jima ba suka tafi.
Ranar da na cika kwanaki uku na ji sauƙi kwarai. Wanka nayo da ruwan da Asiya ta haɗa min dan duk kwanakin nan ma Tahir da sassafe yake zuwa idan ya duba ni sai ya wuce makaranta, sai kuma ya tashi sai ya dawo anan kuma yake hirar dare. Asiyar na duƙe jikin gado idonta na kan wayarta tana latsawa na wuce ta na hau gado ina goge jikina da karamin tawul din da na rufe jikina, ƙasa nayi da zanen jikina na soma murza mai ina wa Asiya mita “Ni fa wallahi mijinki ya sallame ni, na warke” “Ai idonki bai gama washewa ba” ta fadi ba tare da ta ɗago ba “E wannan kuma ai sai a hankali” na bata amsa ina tuna duk a yan kwanakin nan take so ta ji me ya same ni a ido sai in bugar da ita. Murɗa handle din ƙofar da aka yi tare da shigowa gaba ɗaya yasa duban ƙofar a razane dan halin da nake ciki, sai dai haɗa ido da Tahir da nayi yasa na saki wata munafukar ajiyar zuciya kusa da ni ya zauna yana jifana da wani irin kallo ni kuma na daure fuskata, ci gaba nayi da abin da nake yi kamar ma baya dakin suna gaisawa da Asiya na mike na sanya kaya shi ma fita ya yi suka dawo tare da Dr Muhammad, Sallama ta ya yi bayan an bude min file na awo. Muka dunguma zuwa gida sosai nayi mamakin rashin ganin Haj Hajara amma na bar shi a bata sani ba.
Ba mu samu kowa gidan ba abin mamaki har Haj Basma, ni da Asiya muka wuni har kusan magrib sai ta koma gida na bi ta da dinbin godiya me yawa a bakina.
Ban san dawowar mutanen gidan ba sai bayan magrib suka rika shigowa da daidai suna gaishe ni. Wanka na lallaɓa nayi da ruwa me dumi sai nayi sallar Isha’i, mai na goga da turare na dan mutsutstsuka hoda wata doguwar riga mara nauyi Pink color an mata ado a kirji guntun hannu take da shi, da dan gyalen ta na yane kaina. Falo na dawo na kwanta ina duba wayata, shigowar Tahir yasa ni daga kai kamar yanda na koma mishi tun da ya mare ni bana mishi magana dan haka daga kallon ban ce mishi komai ba, ya ce “Ya jikin? Na ce “Da sauki”. “Ya ba ki fito cin abinci ba? Kaina na langabar “Zan fito” “To taso” ban musa ba na mike ina bayan sa muka isa falon matan da ke zaune suka bi mu da kallo kadan na ci na mike “Ya ba ki ci da yawa ba? In ji Tahir kai na girgiza “Ya ishe ni” ban tsaya biye kallon da matan ke antaya min ba na koma ɗakina. Kafin in kwanta ya kuma shigowa, sai da ya ga nayi shirin kwanciya sannan ya ja min ƙofa ya fita.
Da safe ma yana dawowa Sallar Asuba ya shiga ya duba yanda na kwana ya ce min zai shirya ya fita zuwa makaranta, in ci abinci” na daga mishi kai, na fito na ci abincin da su Laraba suka girka, ina ɗakina har rana mun yi waya da Asiya sai Aunty Kulu da ta kira dan jin lafiyata. Har daki Laraba ta shigo sai da ta ƙara gaishe ni da jiki sai ta shaida min an kare abinci, na dan bata lokaci sannan na fito Latifa da Halima na kan dinning kaɗan na zuba na ci Halima ta turo mun jug din kunun Aya, raina na ji yana so, dan haka na tsiyaya na sha, na mike zuwa ɗaki gado na hau dan in yi barci kafin La’asar, na soma lumshe idona na ji marata ta tsira kan kace me mara ta hau ciwo mirgina mirgina na shiga yi ina kiran sunayen Allah can na ji bul! In duba sai jini na gani kuka na fashe da shi na rarumo wayata Tahir na kira yana dagawa na fashe da kuka “Me ya faru? Ban yi magana ba na cillar da wayar, ina ci gaba murƙususu banko ƙofar da aka yi da ƙarfi bai sa na ɗago ba sai muryarsa da na ji yana tambayata abin da ya same ni ganin jini a kafafuna ya kara daga hankalinsa, ciccibata ya yi ya fita dakin, sai da ya zaunar da ni kafin ya ja motar a sittin ya bar gidan. Asibitin Dr Muhammad ya mayar da ni cikin gaggawa suka amshe ni suka shiga min taimakon da ya dace, sun samu nasarar tsaida jinin aka gunguro ni zuwa dakin da na kwanta. Office ɗinsa suka nufa da Tahir wanda ke cikin yanayin da indai kana da imani sai ka tausaya mishi, da lallami ya samu ya zauna, “Me ya samu matata? Shi ma wannan cikin na rasa shi ko”.
Ya kare fadi da damuwa me yawa a fuskarsa, “Ba ka rasa shi ba, mun yi iya bakin ƙoƙarin mu jinin ya tsaya kuma abin da ke cikin yana lafiya, sai dai akwai abin da matarka ta ci ko ta sha wanda yaso fidda cikin” take ya dau zafi “Me nawa yarinyar nan za ta yi min haka? In dan marin da na mata sau nawa zan gaya mata kuskure ne kuma na bata haƙuri. Cikin mamaki Dr Muhammad ke duban sa “Wa takan kai dai matan kawai ka tara amma ba ka san hallayar su ba. Akan me za ta zubar da cikinta? tun da take da abin ta tsawon watanni ka kama ta da wata alama ta son zubar da shi sai yanzu kwanaki uku da sanin ka, ba ma kai ba kowa ma, yarinyar nan ko Asiya bata gaya wa abin da ya same ta a fuska ba, duk kuwa yanda taso ta sani”. Jin zancen Dr yasa Tahir rage zargin ɗora min laifin zubar da cikina tunani me zurfi ya faɗa har bai san sa’adda Dr ya fita ba, kiransa a waya da ya yi yasa shi dawowa hankalinsa ya dauka Dr ya shaida mishi ya same shi dakin da aka kwantar da Ummulkhairi.
Ya samu har Asiya ta iso dan gidan nata babu nisa da Asibitin, tana zaune kamar ta fasa kuka. Wasa gaske dai sai da na shafe tsawon sati guda a Asibitin. Kuma a zaman da nayi ne Dr Muhammad ya kuma min scanning ya gaya min abin da ya gani a cikina. Na roke shi da ya yi shiru kar ya gaya wa Tahir, ya ce shi ma akwai abin da yake hasashe wanda ya san tahir bai fahimta ba dan haka ba zai faɗa mishi ba. A ranar da na koma gida Tahir da ya rako ni ɗakina sai da na hau gado na kwanta ya ajiye min wata yar jarka me ɗauke da ruwan zam zam daga Kawu Attahiru addu’a ce ya tofa ya ce a kawo min, sai kuma wata jarkar zuma ce me kyau mara gauraye ya ce “Baba ya ce ki rika sha safe da dare, sai zumar ita ma ki rika sha shan ta na sa a haifi yaro me hazaka. Ki taimake ni, Ummulkhairi ki bar cikin nan shi ne cikon farin cikina”, ya juya ya bar dakin na raka shi da ido cikin matukar mamakin kalamansa da suka daure min kai. Me yake nufi da in taimake shi in bar cikin ni kenan nayi yunkurin zubar da shi, take wani takaici ya mamaye ni, dama ina lura da take taken shi a Asibiti sai ya yi ta wani cin magani baki na taɓe na isa gaban mirror ina kallon cikina wanda kamar jira yake a fallasa shi gaba ɗaya ya fito ko dan na rame ne? nayi fayau a yan kwanakin nan. Na dade wurin kafin na koma na kwanta. Ban fita cin abinci ba duk da cewa ina jin yunwa, da wuri nayi shirin kwanciya cikin wata yaloluwar riga iyakacin tsawon ta gwiwa, kaina Calabar ce da Asiya ta min a Asibiti. Jin knocking yasa na nufi kofar tare da mamakin ko waye Tahir ne baki na tura na kauce daga kofar ya shigo “Me ya hana ki fitowa ki ci abinci? Ya tambaye ni yana kallona tura bakin na ƙara yi “Ba komai” “Ah ya ba komai? “In ci wani abu ya same ni, ace ni na zubar da cikina”. Na fadi cikin kunkuni. Sai dai na gane ya ji dan kallon da yake min ledar hannunsa ya bude gasashshen naman rago ne yana fitar da tururi da ƙamshi “Oya zo ki ci, in kin ƙare rashin kunyar”. “Rashin kunya kuma? Na fadi ina kara tura bakin, ban ƙi ba zaman nayi dan gaba ɗaya yawuna ya tsinke ya fidda juice din Exotic ya ajiye kusa da ni “Ki karbi girki gobe” ya fadi yana miƙewa tsaye sai ya bar dakin na bi shi da kallo ina taɓe baki, sosai na ci naman ina korawa da juice din wanda ko tsayawa neman cup ban yi ba, sai da na ji nayi kat sai rufe sauran na kulle kofata. Ko da safe ban fito yin break past ba sai da ya shigo da kansa ya ce ba fa zan karya mishi dokar gida ba kan wani tunani nawa na shirme. Ko da na fito yi nayi kamar ina ci nan kuwa ban ci komai ba, yana miƙewa ni ma na shiga kitchen dan dafa abin da raina ke so, hayaniyar da na ji falon ya dauka ne ya sani leƙowa, wasu mata ne su huɗu daya ce ke ta bala’i sauran na taya ta da ƙyar na gane kan me suke yi bashi take bin Halima wanda take ta bin ta ta ƙi biya, Latifa na zaune tana kallon su, Basma ma na tsaye ta wurin kofarta. Mai gidan ne ya rika takowa steps cikin wani yadi yake da akayi ma dinki guntu half jamfa sai farin glass ɗinsa na rai da rai manne a idonsa bai sa hula ba sai takalmi cover shoes. Ya yi min kyau kwarai kallo yake bin matan da shi har ya karasa saukowa, ankara da sauran matan suka yi da shi yasa su yin shiru sai wadda ke bala’in, har sai da ya isa gaban su ta ankara shiru tayi ita ma tana girgiza jiki “Me ya faru? Ya tambaya cikin dakewa “Haj Halima nake bi bashi sai wahalar da ni take ta ki biyana”.

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

Takawa ya yi zuwa ƙofarta, ya ranƙwashi kofar shiru ba a buɗe ba, ya ƙara nan ma ba labari ya yi magana ba a buɗe ba. Wajen matan yi juya “Nawa ne kudin? “Dubu dari uku ne”. Kansa ya jinjina “Bani acc no da lambar waya” ya ciro wayarsa ta fada mishi ya sa “Ku je zan yi magana da ita in kuɗin haka suke zan tura maku” kwarjinin sa yasa ta kasa mishi musu suka juya, layin wayar Halima ya kira bata ɗaga ba ya tura mata text message Idan bata buɗe ba, za ta sha mamakin hukuncin da zai dauka a kanta. Nan take kuwa sai ga kofar an bude ya danna kai ciki, ta zauna kawai tayi tagumi da hannuwanta biyu, dubanta ya yi surkullen da tayi mishi yasa shi kasa buɗe baki ya yi mata bala’in da ya kudurta, zama shi ma ya yi sai ya fara mata magana cikin lalama “Wai dan Allah, Halima me kike da kudi? da har wadanda nake ba ki basu isarki sai kin ciyo bashin mutane kin wulaƙanta ni. A iya zamana dake ban san iya bashin da na biya miki ba me yasa Halima? dan kin san in ba ke din ba, ba macen da zan ɗauki wannan tozarcin daga gare ta. Ya numfasa “Nawa take bin ki? Kamar ba za ta tanka ba ta furta “Dari uku ne” transfer ya yi wanda ya yi sa’a bai samu matsalar network ba, ya kira layin da matar ta ba shi ya ce ya saka kudin. Ta ce “E yanzu ta ga Alert za ta fara godiya ya kashe wayarsa. Duban sa ya kai kan Halima “Na biya ta” sai ya mike ya bar dakin Latifa kawai ya samu a falo ni dama tun da ya soma saukowa na koma kitchen, ina fitowa kitchen din yana isowa mun kalli juna ni da shi na wuce ta gefensa shi ma ya bar falon. Yana zama cikin motar addu’ar da Kawu Attahiru ya turo mishi ya shiga karantawa yana dafe da kansa cikin matukar takaici na tozarcin da Halima ta ja mishi sunayen Allah ya shiga kira kafin ya ji zuciyarsa tayi sanyi sai ya yi wa motar key ya bar gidan.

Halima na ganin fitar sa ta janyo wayarta, malaminta ta kira ta kora mishi bayanin abin da ya faru da tsoron da take kan hukuncin da Tahir zai yanke mata, dan rashin yin fadan sa ba shi zai bata damar sakankancewa ba zai ci mutuncinta ba. Sai da ya gama sauraren ta sai ya yi dariya “Yanzu ya yi miki fadan ko cin mutuncin? Ta ce “Ba ko daya, sai ma maganar da ya yi min kamar yana rarrashina Ya ce “To ki saki jikinki, ko uwarsa kika zaga haka za ta kasance, ki yi abin da kike so ba ki da matsala”, dariyar jin dadi ta yi suka yi sallama tana kara jinjina kyan aikin malamin nan a iya kwanakin nan yanda take so take yi a gidan, dan ma wannan matsiyaciyar ta zo ta tozarta ta a gaban kishiyoyi, amma daga miji na hannunta duk wadda ta nemi yi mata maganar banza rufe ido za tayi ta ci mutuncinta, tana nan zaune cikin dakin
har lokacin da Laraba ta iske ta ta ce mata abinci ya kammala, mirsisi ta fito ta ci abincin ta duk da wani kallo da Latifa ke mata.
Ni dai ban fito cin abincin ba, wanda nayi na adana abi na na ƙara ci, na shiga kitchen din dan yin girki kamar yanda Ogan ya ce na fara kenan Halima ta shigo “Me kike min a kitchen ranar girkina? Kallonta nayi da kyau “Megidan ne ya ce in yi” “Lallai ma da kyau, to ki faɗa mishi sai na karasa girkina a yau ɗin nan dan jiya na fara” ban ce mata uffan ba sai wuƙar hannuna da na ajiye na bi ta gefenta sai na fita kitchen din. Ina komawa daki text nayi mishi na ce zan dan fita ayi min kitso” shi ma sakon ya turo min Girkin fa idan na fita? Na tura mishi matarka ta iske ni kitchen ta ce sai ta karasa kwana ɗayanta. Jin shirun sa na gane ya bar ni, na ajiye wayar ina jan tsaki, sai da na ƙara kintsawa sai na fito dan samun Direba in shaida mishi za mu fita, jawo motar ya yi har inda nake tsaye ina shiga kiran Asiya ya shigo wayata na shaida mata na fito ga inda na nufa ta ce mu haɗu a can. Dan haka ina zama sai ga ta, gyaran jiki aka yi min sai aka yarfa min kitso, sai daf da magrib na baro wurin.

Washegari da wuri na soma shirin karbar girki da dakinsa na soma sai da na gyara komai ya min yanda nake so kafin na shiga kitchen girki na musamman nayi kuma ban yarda na matsa daga inda nayi ba sai da na gama, gaba ɗaya ƙamshin ya bi ko’ina ya isa hancin kishiyoyina, cikin wata drower da ke kitchen din na adana abincin na zare key da ba a cire shi a jiki sannan na bar kitchen din, ko Laraba da Indo ban bari sun ga inda na adana ba.
Sai da na gama shiri na na fito na shirya tebur kuma nayi zama na a falon.
Ina ƙare girkina na kwana biyu Latifa ta karba.

………………………………

Na dawo daga islamiya riƙe da littafin bulugul maram zan shigo na haɗu da wata mace da na ji maigadi na ma tambayoyi haɗa idon mu sai wata me kama da Tahir na gani Ina ta tunanin inda na san ta har muka gaisa sannan na tuna Hadiza ce autar su Tahir da aka ce tayi aure Niger fara’a ta ta karu na ce “Baba ƙanwar megidan ce” tayi min duban mamaki shi kuma baba maigadin ya shiga gaishe ta na ce ta zo mu shiga ina ce mata “Autar Hajiya yaushe a gari? Murmushi tayi “Sati na guda kenan” ta fadi mamaki kwance kan fuskarta na san bai wuce na yanda ta ga na gwada na santa, na ce “Wa ya rako ki ko kin san nan ɗin ? Ta ce “Na manta nan ɗin, tare da yaya lawal muka zo yana gidan Kawu Attahiru”, a main falo muka zauna na kawo mata ruwa dan ta ce ba za ta ci abinci ba ta ci gidan Kawu. Mun dade kafin muka fito tare zuwa gidan Kawun na gaishe da Yaya lawal can muka samu Tahir nan na bar ta na ce sai ta zo, suna hira Tahir da Yaya lawal ita kuma ta samu wuri can kasa ta raɓe.
Jin shiru ba Hadiza yasa nayi tunanin ko can za ta kwana har sai da na fito cin abinci sai na gan ta zaune a falo, kusa da ita na zauna ina takalarta da hira na dan jima sannan sauran matan gidan suka fito, Ogan ne ƙarshe an zauna wurin cin abinci na ce ma Hadiza taso mu je” girgiza kai tayi na ce “Haba dan Allah ki tashi mu tafi” kiyawa tayi har na ga Tahir ya dubi inda muke gane dai ba za ta yarda ba sai na isa inda ake cin abincin na debo mata dan dama ni kam ba ci zan yi ba na kawo gaban ta na ce “To bismillah” ta fara ci tana duba na “To ke kuma fa? Kai na girgiza. “Ke dai ki ci” ta ci har ta koshi Ogan ya fara miƙewa wai kansa na mishi ciwo ya haye sama, Latifa ta take mishi baya, wayata da ake kira na duba Yaya Sani ne, na ɗauka ina murmushi na ce wa Hadiza ina zuwa bedroom ɗina na shiga mun gaisa tare da yar hira sai ya ba matarsa Aunty Rahma muka gaisa hada yaransa. Kamar hadin baki muna aje waya kiran Yayata Aunty Wasila ya shigo ita kam hira sosai muka sha har tana faɗa min haihuwar ƙanwata Aimana, nayi murna na ce zan turo sako dan na san ba zai bar ni zuwa ba, ta ce dama duka yaushe na tafi muna ta hira har kuɗaɗen wayata suka kare sai na kira ta wani barci da ya shiga idona sai jera hamma nake ita da kanta ta gane hakan ta ce “Bari in barki yar ƙanwata na ji alamar barci kike ji. Muna ajiye wayar anan na bingire na gyara kwanciya, wani irin barci na shiga yi wanda ban tashi samun kaina sai uku da rabi na dare shi ma wani irin fitsari da tun samun cikina ya zame min jiki bana riƙe shi sam ga yinsa akai akai ya kulle min mara a gigice na mike zuwa toilet ina fitowa ƙofata na zo na duba Allah ya taimake ni ban sakaci da rufe kofar, sallah nayi raka’a biyu sai na koma na kwanta ina karanto addu’o’i bayan na cire kayan jikina, ban jima ba wani barcin ya kwashe ni. Ta da Sallar Asuba ya farkar da ni na kuwa duro gadon da hanzari duk da jikina ya soma nauyi, ga cikin kullum kara wani irin girma yake. Alwala nayo na zo na kabbara Sallah sai da na idar da Sallah sannan karatun Alkur’ani ya biyo baya, azkar nayi karshe akan sallayar barci ya yi awon gaba da ni, ja min ƴan yatsun kafa da ake yi yasa ni farkawa ina buɗe idona Tahir ne tsugunne gabana, mun kalli juna kafin na yunkura na tashi zaune ina gaishe shi. “Me yasa in anyi abinci ba ki ci? Ya jeho min tambayar yana tsare ni da mayatattun idanuwansa kumatu na kumbura “Ina dafawa ina ci” “Kina son jawo min wata maganar a gida ko? Ƙara turo baki nayi na ƙi magana “To ki riƙa dai cin abinci kin ga ba ke kadai ba ce” na daga mishi kai “Zan fita yanzu ki fito ki nemi abin da za ki ci” kan na kuma ɗagawa miƙewa ya yi yana saka hannunsa aljihu kuɗaɗe ya ciro ya miƙo min ina amsa ina neman karin bayani da idona “Kin je Sallon ban samu na ba ki komai ba” godiya na shiga yi mishi ya juya sai na bi shi da addu’a. Fitarsa ke da wuya sai na tuna ina son tambayarsa za ni Tudun Wada in gaishe da yan tsofaffin nan in kuma ga ƴan biyu, sai na biyo shi ko hijab din jikina ban cire ba, na ratso falon Hadiza da na gani kwance a kujera ga falon ya dauki sanyin raɓa ga sanyin safiya ta kudundune da hijabin jikinta, “Hadiza, a falo kika kwana? Na fada cikin mamaki ina kashe A C jin maganata yasa Tahir rage saurin da yake zai fice “Tashi mu je dakina wallahi barci ne ya kwashe ni sam na shafa’a” ta mike “Ina kayanki? Na tambayeta wata leda me layi layi ya nuna min a bayan kujera dauko mu je na ce mata ina yin gaba ta dauko ta biyo ni, Tahir da ke tsaye cak tun soma maganar mu ya ja ajiyar zuciya sai ya bar wurin cikin sauri.

Muna shiga bathroom na ce ta shiga tayi wanka dan ta ce min ta roki masu aiki ta zagaya bayin su tayi Alwala, wani abu na ji ya daki ƙirjina jin zancenta ta shiga wankan ta bar ni cikin tunani ta fito na dube ta. “Anya Hadiza? Ko da yake ina zuwa” bathroom din na shiga na hada mata turarukan wanka sannan na fito na ce ta shiga ta kara wankan “To Aunty” ta ce min duk da za ta dan girme ni ko kadan ne. Wankan ta kuma shiga ta fito sai shinshina jikinta take wai ƙamshin da ta ji tana yi na kai ta gaban mirror na nuna mata mayukan da za ta shafa da wanda za ta shafa ma sumarta da ta wanke gashi me yawa take da shi amma rashin gyara yasa duk ya dankare, sai da ta gama ta buɗe jakar ledarta za ta canza kaya, kayan duk tsummokara ne dan haka na ce ta ajiye su doguwar riga na samo mata cikin kayana na ce ta saka sai na fita zuwa kitchen na ce mata ina zuwa me aiki tana aikinta ni ma ina nawa farfesun kaza nayi sai kwai da na soya, na dafa ruwan zafi na shirya su a katon tray na wuce ɗakina, tare muka karya ta fita da kayan zuwa kitchen ni kuma na shiga gyaran wurin, da ta dawo tare muka ƙarasa. Ni ma nayi wanka sai muka fita zuwa islamiyya tare, sai da muka dawo muka shiga kitchen ina yi mana girki tana taya ni, Latifa da ke da girki ta shigo dan duba yanda Laraba ke gudanar da girkin dan Ogan ya kusa shigowa ganin mu ta wani sha mur Hadiza ta dauki tray da na jera mana kayan abinci ni kuma na ɗauki jug din dana haɗa mana juice sai muka fito “Dakata Malama” Latifa ta fadi da kaushin murya cak! na tsaya sanin da ni take “Ba fa zai yiwu ki rika shigo mana da kowacce tarkace kitchen ba tana daƙuna mana kayan abinci” wani kallo nayi mata “Lallai an samu wuri, amma in ba haka ba ke da ba ki buɗe baki kin kira ƙanwar wanda ya ajiye ki da tarkace, ba ki kuma nuna kyamar ta alhali kayan da kike gadarar za a dakuna muku, dan’uwanta ne ya saya”. Wannan shi ne baki in ka san abin da za ka fadi ba ka san abin da za a mayar maka ba. gaba daya ta taso min tana naɗe tabarmar kunyarta da hauka dan na lura su ɗin yan rainin hankali ne kana kyale su sai su mayar da kai takalmin kafar su. Muka wuce ta ina cewa “Wannan da kike gani ta zo kika wulakanta ta maigidan nan zai iya sake ki, ita kuwa ba zai iya sake ta ba, sai ki bar gidan ita kuwa babu me korarta. Tsawar da aka daka min har kamar zan zubar da abinda ke hannuna na daga kai Tahir ne “Wuce zuwa ɗakinki” na wuce Hadiza ta biyo ni. Wannan kenan abin daure kai bayan abin da ya faru tsakanina da Latifa kan Hadiza, da yamma Halima ta karbi girki Hadiza ta fita mayar da wani mug da muka yi amfani da shi Halima tayi knocking budewa ta sai kashedi tayi min kan taɓa musu kayan amfani da nake sa Hadiza tana yi. Fitowa nayi sosai ita ma na wanke ta kamar yanda nayi wa Latifa ita ma rasa abin fadi tayi, Tahir na zaune a falon da laptop ɗinsa, namma tsawa ya min na koma daki. Da komawata kuka na ji ina yi kasa daukar bakin cikin nayi, na rasa wa zan kira in fallasa bakin cikin da yake cin raina Aunty Kulu ta faɗo min wayata na janyo ina kuka na shiga rattafa mata Tahir ba wadda zai rika tozartawa a gaban kowa cikin matansa sai ni. Haƙuri tayi ta bani da kalaman kwantar da hankali da falalar hakuri da sakamakon sa ga duk wanda ya yi shi, ina mata kuka. Muryar Kawu Attahiru na ji yana fadin “Yi shiru ki yi haƙuri ki saurare ni, Uwar alkhairi” shirun nayi ina shashsheka “Ki yi hakuri ki rika wa mijinki uzuri kin ji? A duk yan kwanakin nan mafarkinsa nake addu’a kawai nake tayi dan kar ya zamto abin da nake ganin ya zam gaskiya da kuma za ki san a halin da aka saka shi da kin gane ba ƙaramin kokari yake ba wurin kula ki, dan kowacce tsaye take tana son ta karbe shi ita kadai albarkacin addu’a kike zaune har yau an kasa ganin bayanki, ina addu’o’in da na aiko miki ina fata kina amfani da su na ce “E Kawu” “To ki ci gaba da izinin Allah za mu ga waraka, ko kin taba jin an ce gaskiyar wane ta ƙare? Na girgiza kai kamar yana ganina “Sai dai ace karyar sa ta kare ko? To in sha Allah nasara na tafe, cikin jikinki sai ta Allah in sha Allah za ki sauka lafiya”.
Haka dai ya yi ta min kalaman kwantar da hankali har na ji na nutsu na share hawaye na. Sai dai ina fitowa falo nayi kicibis da Hadiza ta cire rigar da na bata, ta mayar da kayanta ga lilliɓinta a kanta. Tana ganina ta sunkuyar da kanta “Ni zan wuce, Allah ya saka miki alheri bisa karamcinki a gare ni, ba zan taba mancewa da ke ba, kin karɓe ni a lokacin da kowa nawa ya juya min baya, domin na cancanci hakan a laifin da na aikata musu.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

Na taho wurin Yaya Sodangi ne dan ina tunanin so da kaunar da ya gwada min a rayuwa, shi zai iya yafe min, ya dube ni. Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, na ce “Ya isa Hadiza, abin da nake so da ke ki yi hakuri, bari in je in samu Yayan naki in….. Katse ni tayi “Dan Allah kada in sa ayi ta cin mutuncin ki, na gode bisa alherinki a gare ni, na gode na gode, za ta fice na ruko ta ina hawaye “Dan girman Allah, ko za ki tafi, ki jira ni in dawo” komawa tayi ta fadi kan kujera tana kuka. Ban damu da hawayen da ya damalmale min fuska ba ballantana in tsaya sharewa na fito dakin.
Latifa da Halima na gani zaune a falon, sun dube ni a tare step na fara takawa zuwa sama, ina tura ƙofar ba shi a falon na wuce bedroom din yana kwance rigingine ya dubi sama, ya yi pillow da hannayensa. Motsin shigowata bai sa ya ɗago ba, kukan da na fasa yasa shi tashi firgigit! shedar ya fada zurfin tunani. “Me kenan kake yi haka Tahir ? Yar’uwarka da kuka kwanta ciki daya ta zo gidanka har ka gwada matanka sun fi ta, ka bari a ci zarafinta kana kallo, ko kana tunanin su akwai wadda ta ta ƴar’uwar za ta zo ta bari ka wulaƙanta ta? Gara ni, na san ni ba komai ba ce a wurinka amma yar’uwarka fa? Koko abin da suke baka, dadin da suke jiyar da kai yasa kake ganin sun fiye ma ita? Ban san tashin sa ba, sai dai isowar sa gabana na gani ya daga hannu zai mare ni, ko gezau ban yi ba, ya sauke hannun. Cikin zubar da hawaye na ce “Ka mare ni mana ai na saba” janyo ni ya yi sai gamu bisa gado ta bayana ya rungume ni duk da cikin jikina na shiga damben kwacewa ya ce “Ki bari fa, ina irin wannan halin ki bar yi min musu, kin san dalilin da ya sa na share Hadiza? Shiru nayi Ita ce sanadiyyar samun hawan jinin Hajiyarmu. Lokacin da ta ƙare karatun makarantar unguwar zoma da ke Malumfashi, ta fitar da miji an sa rana bai fi saura wata daya biki ba ta tayar da kayar baya bata san wanda za ta aura kuma kin san waye? Bai jira amsawa ta ba ya ci gaba “Ƙanen Halima ne” saurin juyowa nayi na dube shi ya daga kai. “Kwarai Halima da kika sani ta gidan nan, bayan makotaka da ke tsakanin gidan mu da nasu, akwai zumunci ga kuma surukuta Halima na gidan mu, wanda kuma ta kawo ba a ko san asalin sa ba an ce dai mutumin Niger ne, an kada an raya amma yarinyar nan ta ki sai ma ƙara da ta kai gidan Hakimi wai za a yi mata auren dole. Mun zauna an kafa mata sharadi cewar indai ta aure shi mun bar masa ita, ta ma manta tana da wasu yan’uwa da iyaye, ta ce ta amince, ranar Auren ta Haj ta yanke jiki ta fadi dan duk ta fi tsanar al’amarin muka nufi Hospital da ita inda aka tabbatar jininta ya hau, Haj na Asibiti aka daura Aure, yarinyar nan ko gezau ta bi mijinta suka tattara a ranar ya dauke ta suka bar garin. Bayan fitowar Haj da ganewar da tayi yar’autarta ta tafi ta shiga wani hali jinin da aka samu ya sauka ya kara hayewa, dole muka mayar da ita Asibiti. Da kyar muka samu Haj ta hakura ta rungumi ƙaddara. To me za mu yi da Hadiza? Ni me zan ce mata? Nisawa nayi lallai bata kyauta ba, amma hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar, haka nan za ka yi hakuri”. “In na ce miki ban ji dadin ganin ta ba nayi karya amma dole in yi mata abin da nayi mata dan ta gane abin da tayin, duk da dai da ganin ta duniya ma ta biya mata karatun”.
Ji nayi ya zura hannunsa cikin rigata, ga kansa ya sanya saman wuyana yana sunsuna ta, jin ya sanya jikina shiga wani hali yasa na fara kiciniyar kwacewa sai dai da alama ya soma nisa riga ya cire min yana gaya min maganganu cikin fitar hayyaci, “Kina cikin abin da nake matukar so Ummulkhairi, ke wata aba ce me daraja a wurina, bana so kina shiga cikin fadan da ake min a gida, a duk lokacin da na ga ana yi da ke, na fi jin zafin naki, saboda matsayin da kike da shi a zuciyata. Ki taimake ni in samu kwanciyar hankali ta bangaren ki” bai bani damar magana ba yasa bakina cikin nashi. Nayi mugun kaduwa ganin abin da yake shirin aikatawa sai dai bai yin ba, gama jagulani ya yi ina mishi kuka daga bisani ya tsallake ni ya shiga bathroom, na tashi zaune ina lalubar rigata tuna Halima za ta iya shigowa dan na shigo mata a ranar aiki yasa ni ciccibawa sai ga shi ya fito, ba tare da na dube shi ba na ce “Ga ta can fa za ta tafi”. “Kina nufin Hadiza? Na daga mishi kai na sa kai dan barin wurin, na soma taka step na ji shi bayana tun fitowar mu Halima da Latifa wadanda dama zaman da suke hankalinsu na gare mu da Halima ta ce ita fa za ta je ka ta gani ka da aci amanarta, sai Latifa ta hana ta ta ce “Ke ba ki ga da yanda ta tafi ba, daru za su kwasa mu kuma mu sha kallo, yanzu ko kina zuwa ƙarshenta fadan ya koma kanki”. Ganin yanda muka fito sai ya kulle musu kai Halima ta mike tsaye ta zura mana ido mu kuma muka wuce su zuwa ɗakina. Mun tarar da Halima zaune tana ta razgar kuka wani kallo da Tahir ya yi mata yasa ta zama sosai ta hadiye kukanta “Ke yanzu kina da bakin kuka ko? Mu kin manta sanda kika tafi kika bar mu muna namu kukan? Ina sane na bar ki a gidan ana nuna miki iyakarki, ban da wannan, ya nuna inda nake tsaye “Da ta je tana min koke koke, barin ki na so yi sai gama gane kuranki, ban da kina Shashasha Namiji za ki zaba ki bar uwar da ta kawo ki duniya? Kika tafi kika bar Hajiyarmu, kin san halin da ta shiga bayan barin ta da kika yi? Ita dai kuka kawai take ni ce nake bada haƙuri “To yanzu da kika tashi kankarar za ki koma ki karasa mana uwa, koko inda kika fito za ki koma? Ya ja dogon tsaki sai ya juya ya bar dakin. Ina ta bata haƙuri ta share hawayen ta, “Na cancanci duk abin da za su yi min, bayan na tsallake na bi Rabe, bamu zame ko’ina ba sai magarya da ke karkashin yankin Damagaram a ƙasar Niger. Zaman wata uku muka yi ya tsallake ya bar ni wai ya tafi neman kuɗi ya bar ni tare da iyayensa da yan’uwansa wadanda suke nuna min banbanci ƙarara bayan wahalhalun ayyuka da nake na mutanen ƙauye wanda ban saba ba, kafin ka ce me na canza na fita hayyacina, sai da ya shekara biyu ya juyo, da ya dawon wata guda ya yi ya kuma komawa, yana kara dawowa ya dawo da shirin auren yar’uwarsa nan fa gaba ɗaya suka juya min baya ba a riga an yi auren ba mahaifiyarsa ta ce ya sallame ni, ba bata lokaci ya yi min saki uku da kyar na sai da wata akuya da diyarta da na mallaka na kamo hanya zuwa gida. Jinjina kai nayi cikin tausaya wa wannan kaddara ta ta. na ce “Ki yi hakuri kaddara ce, ke taki kaddarar haka ta zo ki yi ta addu’a har yan’uwanki su sauko su yafe miki”. Ta share hawaye “Tun dawowata ƴan’uwana suka sani gaba, Haj kuma hawan jininta ya tashi ganin yanda na koma, yaya Lawal ne kawai bai zafafa min ba yake tausayina ganin halin da na ke fuskanta yasa ya ce in shirya ya kai ni gidan Sodangi, kila can zan ɗan fi samun sakewa har komai ya daidaita. Shi ne ya rako ni. Na ce “Ki saki ranki ki yi hakuri, in sha Allah za su haƙura suna nuna miki kuskurenki ne, dan Allah ki cire kayan nan”. Ta tashi ta cire ta mayar da wadda na bata.

Halima suna shigewa ta tashi ta haye upstairs cikin sassarfa ta faɗa bedroom ganin yanda aka yamutsa shimfida ya kara daga hankalinta. Nazarin gadon ta shiga yi har zargin ta ya tabbatar mata da an yi abin da take gudun, kuka ta fasa ta fadi dabar tsakiyar ɗaki wani kishi ya tokare mata kirji. Kamar an zabure ta sai ta miƙe wurgi ta shiga yi da duk abin da hannunta ya hau kai kafin ta yayo zanin gadon ta yo ƙasa tana kuka. “Wallahi ba zan yarda da wannan cin amanar ba a ranar girkina a kwanta da wata, to wallahi ta fito ko ni ko ita a gidan nan. Kalmomin da suka shige kunnen Tahir kenan da fitowarsa daga dakin Ummulkhairi. Zanen gadon ta wurga mishi a fuska “Ni za a yi ma cin fuska a wulakanta? To wallahi ba a haifi ƴar ba”. Duban sashin da Indo me aiki ke goge goge, Laraba na shirya abinci, ban da Latifa da ke zaune cike da jin dadin wannan Film me daɗin kallo. Takowa ya yi inda take mu je dakina” fizgewa tayi tana ci gaba da maganganun da basu dace ba, Please ki yi hakuri mu je dakina” ya kara rokonta akaro na biyu dan ba abin da yake gudu irin kanwarsa ta ji dan dai masu aiki ta gama wulaƙanta shi gaban su. Sai dai fatan shi bai ci ba dan Hadizar ya gani tana kokarin komawa ciki ta karfin tsiya yake jan ta amma ta kwace saman ya haye ganin yanda ta maida mai daki ya kara tunzura shi sai ya sauko “Kin kure hakurina Halima, dan haka na datse igiyar aurena biyu dake na sake ki Halima pen din da ta ga yana kokarin cirowa yasa tsayawa cak daga iface ifacen da take “Ko zuciyata bata da kashi ya kamata in ji zafin abin da kike min, kuma ko ke ɗin ta gwal ce ya kamata in hakura da ke. Dan haka na datse igiyar Aurena da ke. Wani ihu ta yanka tana faɗin bani ta shiga uku.

Ko da page din bai yi yawa ba saboda rashin chaji na san zai saku farin ciki.

Maryam litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne 300 ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

A ranar dai gidan shiru ya yi kowacce ta nabba’a ɗakinta. Maigidan kuwa ba wadda za ta ce ta san lokacin da ya shigo, Halima ma ɗakinta ta shiga ta datse ta kira malaminta da daukar shi kuka ta fasa yana tambayar lafiya? Ta ce “Tahir ya sake ni” jimami ya shiga kafin ya ce “Aikin Mijinki yana da wuya, domin yana da tsayuwar dare, ba kowane lokaci ake samun sa’a akansa ba, idan ma an dace ba a wani daɗewa abin zai warware” ta gasgata abin da ya ce domin ko’ina ta je hakan ke faruwa “To yanzu ya zan yi” ta tambaya cikin marairaicewa. Wani aikin za mu ɗora, amma fa ki sani haka za a yi ta yi, muna yi ana warwarewa, dan na ga ma akwai wani tsaye kansa. Da sauri ta ce ƙanen mahaifiyarsa ne, shi ya rike shi, sai kishiyar tawa cikin sai girma yake, so nake ya zube, kuma ayi mata saki uku. “Ba ki da matsala, duk da dai ita ma yarinyar ba a zaune take ba” Halima ta ce “Haba ko da na ji amma shan gabana a wurin Tahir ai da mamaki indai ba asirin ba.” “Za mu yi iyaka kokarin mu, za ki turo kudin aiki kamar na wancan karon. Suka yi sallama.

Da safe Tahir ya nemi ganin mu a falonsa, mun hallara ya shaida mana shi ya kammala course ɗinsa, dan haka gobe idan Allah ya kaimu zai koma Lagos tare da Ummulkhairi, da ƙanwarsa Hadiza. Daga Latifa har Basma shiru suka yi dan ba fuskar da za su a mayar da abin da ke ransu. Yana gama fadi yasa kai ya fice kowacce ita ma ta mike zuwa ɗakinta, sai dai suna shigewa Latifa ta fito daga nata dakin ta faɗa na Basma bayan tayi knocking Basman ta taso ta bude mata, a hannun kujera ta zauna “Yanzu Basma haka za mu zura ido ayi mana wannan rashin adalcin, sai a ce da waccan yarinyar zai fara tafiya? Baki Basma ta taɓe. “To ke yanzu ba fa tafiyarki aka dauka ba, idan ma ya ce girma zai bi daga na har ke ba wadda za a ɗauka”. “In ji wa? Latifa ta tambayeta da sauri ba tayi magana ba sai zura mata ido da tayi. “To tun jiya kika koma uwargida, dan an yanka wa Halima red card, lallai Basma ke duk wannan buduri da aka sha ke kam me kike? Mamaki Basma ta ji a cikin ranta amma bàta bari fuskarta ta nuna ba.
“Shi kenan ya kike so mu yi yanzu? Ta tambayi Latifa “Yawwa” Latifa ta muskuta Kawu Attahiru ,za mu kira kin san ba wanda Sweety ke jin maganar sa irin sa, sai mu fada mishi”.
Kafada Basma ta kaɗa
“Shi kenan” “Yawwa to mu kira shi yanzu” cewar Latifa “Ba ni da lambar shi ni dai” in ji Basma, “Ni ina da ita” Latifa ta fadi tana danna wayarta. Ta soma kira ya dauka, sai da ta gaishe shi sai ta mika wa Basma ita ma ta gaida shi, sai ta amsa tayi mishi bayanin abin da Tahir ke shirin yi na daukar Ummulkhairi zuwa Lagos”. Haƙuri ya bayar ya ce zai ma Tahir magana. Godiya Latifa tayi sai suka yi sallama. Ta mike ta bar dakin tana kitsawa a ranta, ko da ba yanda za a yi tafiyar ta faɗa kanta kasantuwar ta ta karshe, amma da dai ta bari Ummulkhairi ta tafi ta gwammace wannan huhun ma’ahun ta tafi.

Tahi gr na kwance rigingine cikin tunani ya ji kukan wayarsa. Sai da tayi har ta tsinke bai tada kai ba, jin ta kuma ɗaukar ɓurari yasa ya tashi a fusace ya kashe ta gaba ɗaya sai sunan Babana ya gani yana yawo kan screen ɗin, ajiyar zuciya ya fidda kafin ya daga bakin sa dauke da wata makalalliyar sallama jin yanayinsa yasa baban yi mishi nasiha kam muhimmancin hakuri kafin ya dora da tambayar sa dalilin sa na daukar matarsa ta uku a farkon tafiya. Bai ɓoye mishi ba ya ba shi labarin rabuwar sa da Halima. Jimamin sa ya nuna kafin ya fadi mishi “Su mata haƙuri ake da su ba a biye masu, amma yanzu ya yi adalci a tsakanin iyalan nasa, ya fara tafiya da babba, daga nan sai ya soma canji. Bayan doguwar nasiha sun rabu.

Sauka kasa Tahir ya yi ya kuma tara iyalin nasa, ya ce Tafiya yanzu ta koma kan Basma, dan haka sai ta shirya zuwa gobe. Kuɗaɗe ya miƙo min, ki samu lokaci ku shiga kasuwa da Hadiza ta sayi kayan amfanin ta. Ya kuma miƙo min wasu “Wadannan kuma anjima za a kawo mata suturu, idan kun fita sai ku bayar da ɗinki. Godiya sosai nayi masa kamar ni ya yi wa. Ya ciro wasu kudin ya bamu ni da Latifa, Halima da ke leƙe ta kafar mukulli ta janye tana jan tsaki.
Da ya mike dakin Halima ya shiga ya ce zaman me take mishi bayan ya sake ta? Ta yi shiru ya ce “Ai dama gadarar mace da duk wani rashin arziki da za ta yi maka idan ka ce kana yi ne da ka ce ba ka yi ka datse igiyar shi kenan dan haka ban san ki ƙara kwanar min a gida. Ya sa kai ya fice.
Tilas a ranar ta fakaici idon kowa ta bar gidan.

Na koma daki na nuna ma Hadiza kuɗaɗen da dan’uwanta ya bayar a kai mata ɗinki da sayayyar da ya ce a yi mata. Can da rana kuwa sai ga Jakunkuna biyu cike da kaya na zamani, muka yi ta dubawa ni da ita cikin jin daɗi, ita kam har tana ƙwalla, ta ce min mu dan saurara da kai ɗinkin a ɗan kwana biyu ko za ta dan yi kumari. Na ce “E hakan ma ya yi, amma za mu je Sallon a gyara miki kanki.

Washegari Tahir suka wuce shi da Basma. Na mayar da hankalina wurin gyara Hadiza, sati daya muka dauka sai da ta sauya, muna waya da Tahir sosai kullum abin da yake gaya min in kula da kaina in kula mishi da cikin jikina. Sai yanzu na gane ba ƙaramin so yake wa ƙanwar tasa ba, baya nan amma kuɗi kawai yake kashe mata, bayan rantsatstsiyar wayar da ya saya mata kullum kuma cikin tambayarta me take so yake kwanaki goma da tafiyarsa aka maido Halima wadda wasu dattawa maza suka maido ina barci lokacin sai bayan na tashi Hadiza ke bani labari. Da muke waya da Maman Ummi kuma take labarta min ai jama’a kala kala aka yi ta tura wa Tahir da Hajiyarsa da yan’uwansa, dan ya mayar da Halima, Tahir kuma ya ja ya kafe ya ce sam, har yan’uwanta aka tada zuwa Lagos suka ba shi haƙuri amma basu ciyo kansa ba, karshe dai Kawu Attahiru ya rarrashe shi, wanda sai da ya yi wa Halimar faɗa sosai kan ta gyara zamantakewar ta da mijinta, wannan shi ne na karshe da zai tursasa Tahir a kanta. To ta dai samu ta dawo amma bata da hus a gidan ko habaice habaicen Latifa ya ishe ta, dan ma bata cika zama ba.

Saura kwana biyu zuwan Tahir sai ga Aunty Laila gidana. Tun da muka yi waya ta ce sun shigo garin na fita harabar gidan ina dakon isowar su, direban da ya kawo ni ne ya tuko ta.
Motar na tsayawa na nufe su, zan rungume ta ta rike ni tana kallona “Haka kika zama? Na ce “Kai Aunty laila, za ki fara daga zuwan ki? Muka wuce ciki riƙe da hannun juna mun shiga falon ta coge tana kare mishi kallo ina “Aunty Laila zo mu je” ta kama ƙugu “An gaida Namijin duniya, wato memakon ya yi wa kowacce part ɗinta, sai ya tara ku a falo daya yanda za a gwabza kishin da kyau a kansa yana kallo, da kyau jarimin maza. Na kamo hannunta “Zo mu je Aunty Laila” Latifa da ta fito daga kitchen ta dube mu, Halima ma da ke daukar ruwa a fridge ta saci kallon mu, su kansu daga duban Aunty Laila sun san ita ɗin bata wasan yara ba ce, ta girmi duk wata wayewa tasu.
Washegari na tambayi Tahir muka fita zuwa gidan Asiya, wuni me daɗi muka yi a gidan ta, dan tuni su ukun sun saba, Hadiza Laila, da kuma Asiyar. Har Sallon muka biya aka wanke min kai ni da Hadiza, na so yin kitso yamma tayi daga na lura Tahir na so.
Ranar da Tahir zai zo bayan Hadiza har Aunty Laila sai da ta taya mu yi mishi ƙayataccen girkin tarba, na kuma zage na gyara mishi wuri nasa ƙamshi. Duk da nayi wanka me kyau na tsala kwalliya sai dariya Aunty Laila take min, “Wai wannan tulelen cikin shi zai bata amarcin da za a sha yau. Baki na tura “Ba abin da zai hana”. Na fadi a hankali ban tunanin ta ji ba sai dariyarta na ji “A dai bi a hankali Hajiyata. Jin bude get yasa ni leka window, motar da na ga ta shigo na ji dadi ya lullube ni, ban motsa ba har sai da na ga fitowarsa ya yi kyau ya hadu karshe cikin shigar kananun kaya, glass ɗinsa na manne idonsa. Basma ma ta fito mai wanki da me gadi na ta fito da kaya, “Wai me kike kallo ne? Aunty Laila da ta ji na dauke wuta ta taso dan ganin me ya dauke min hankali ganin Tahir dariya tayi “Amarya ango ya iso kenan? Harara na bata ina ɓata fuska Na ce “Allah Aunty Laila kin sa ni a gaba” na daga kafa zan bar dakin ta ce “Sai ina? Na ce “Ta ran Oga” ruko ni tayi “Dan saurara Hajiyata, sai sun gama zuwa sai ki je karshe kai gyaɗa mata sai na koma bakin gado.
Tsadaddun turaruka masu sanyin ƙamshi Aunty Laila ta shiga sa min tana kara gyara min zaman rigata, Atamfa ce ɗinkin riga da zane da suka zauna ga cikina ya bi jikina ya zauna das. Nayi kyau a yan satikan nan, dan na samu lafiya ga kwanciyar hankali da gidan ya samu kwana biyu ba fitina, daidai da Hadiza ta murje har mamakin yanda ta koma nake cikin kankanen lokaci. Tana can kitchen tana tsaron abincin mu dan yanda Latifa ke ta shiga tana fita.
Da shigowar sa falo ya zauna iyalai na kawo gaisuwa, Basma ta wuce ɗakinta. Takalmi na saka na fito Tahir na zaune a kujerar da ke kallon ƙofata, idona na lumshe kafin na buɗe su fes akansa wata kaunar sa da son kasancewa tare da shi na sauko min. Shi ma kallona yake har na karaso, na zauna ina gaishe shi kafin na miƙe zuwa kitchen ganin ba wadda ta kawo mishi ruwa ruwan na hado inda na tarar da Hadiza kallona take “Kin yi kyau Aunty” murmushi nayi “Kyau Hadiza da wannan katon cikin? yar dariya tayi “Da gaske Allah kin san ai ba ma wasa” na ce. ” To shi kenan, gara ki fito ki yi wa yayanki barka da zuwa, sai mu fitar da abincin. Ta amsa sai ta miƙe tana bayana muka fito ya fara shan ruwan suka yi ido huɗu da Hadiza murmushin sa me tsada da ba koyaushe yake yi ba ya saki “Dan Allah Hadizata ce ta koma haka? Lallai dole in yi miki babbar kyauta, Ummulkhairi” hannunsa ya mika mata ta kama ya zaunar da ita gefensa na dama dan Latifa na zaune a gefen hagunsa. Halima dai a one sitter aka dake an zuba tagumi, da murmushi a fuskata na koma kitchen Abincin na soma fiddowa Hadiza ta isko ni tana taya ni. Na ce “Ban fa faɗa maka ba Aunty Laila ta zo tana gidan nan” fuskarsa ce ta washe “Dan Allah? amma ba ki kyauta min ba, da ban yi wa Ahmad godiyar zuwa mana baƙunta ba. Ya mike “Bari in je mu gaisa” matansa gaba ɗaya suka buɗe baki suna mamakin ita wannan baƙuwa wane irin muhimmanci take da shi. Sai ga ta ta fito fara’arsa ta karu suna ma juna Barka da zuwa sun gama gaisawa ta faɗa mishi Ahmad na Kano sai ya dawo zai biyo su tafi tare. Wayarsa ya zaro Ahmad ɗin ya kira sun gama wayar na ce “Wanka za ka fara yi ko abinci za ka fara ci? Idanuwansa ya lumshe “Zan fara wankan” ya mike ya fara takawa zuwa sama zan bi bayansa Aunty Laila da ta mike ta fara tafiya zuwa ɗaki ta kira ni mun shiga a tare wata yar kwalba ta ciro “Yi maza ki dan shafa kadan” dan matsawa nayi “Me kuma za a yi yanzu da rana? “Ba mu da lokaci ki yi yanda na ce idan kika dawo sai mu yi magana” fuska na narke “To bari sai dare ” juyawa tayi na ce “To bani” ta miƙo min bathroom na shiga na shafa sai na fito. Ban same shi falo ba sai na wuce bedroom
Ya cire kayan jikinsa, daga shi sai boxers hannayensa dafe da kansa yana zaune bakin gado. Na ce “Yi hakuri na bar ka zaune kana jirana” jin shuru yasa na ce “Lafiya? / idanuwansa ya bude wadanda duk sun kada ya ce “Kaina ke ciwo” saurin zama nayi gefensa jikina har rawa yake ina jera mishi sannu, na yunkura dan samo mishi magani na ji ya ruko ni, jikinsa ya sanya ni, ajiyar zuciya ya shiga fiddawa mun dan jima a haka kafin ya mike ya shiga wanka sai na sauko kasa latifa kawai ke zaune sai Hadiza da na san gadin abincin mu take. Ba jimawa ya sauko sai a ka ci abinci basma ma ta fito aka ci tare da ita anan na yi mata sannu da hanya Latifa dai fuskarta kamar hadari ta daure ta tamau idanuwanta sun kada cikin tabaranta. Halima kallon da ogan ke mata yasa ta barin falon ta gudu dakinta. Ko da aka kammala kowa ya bar falon sai Tahir da ya kira kanwarsa suna hira. Dakina na koma na hau gado muna hira da Aunty Laila kiran salla da aka fara yasa mu mikewa sai ga Hadiza ta shigo duban ta nayi Yayanki fa? Ta ce ya fita zuwa masallaci ” gyada kai nayi munyi sallah na gyara fuskata, muka fito na shiga kitchen tuwo nayi niyyar yi wa Tahir sanin yana so, dan Basma ban ma yi tsammanin ta iya ba.

*Maryam litee*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612*

 

Tahir daga masallaci wanda tare suka fito da Kawu Attahiru, shi ma Kawun jiya ya zo. Gidan Baban suka wuce, falonsa na musamman suka shiga. Duban dan nasa yake cikin tsantsan son da yake mishi, “Ya ka samu gidan naka? Murmushi Tahir ya yi yana shafa sumarsa “Lafiya Baba Alhamdulillahi” murmushi Baban ya taya shi yana jin daɗin farin cikin da ya ga dan na shi ciki. Haj Hajara ta shigo da kwanonin abinci, Tahir ya shiga gaishe ta tana tambayar sa saukar yaushe? Da fitar ta baban ya ce “Sauko mu ci abinci” girgiza kai ya yi da murmushin da ya ki barin fuskarsa “Na ci abinci Baba” Baban ya shiga cin abincinsa, “Yaushe za ka koma? “Kwana biyu kaɗai zan yi Baba”. “To yanzu da wa za ka koma? Kai tsaye ya ce “Da Ummulkhairi” murmushin su na manya baban ya yi “Ba ka mayar da uwargidan ka ba? Bai yi magana ba sai kallon baban da ya yi “Da ita za ka tafi” ɓata fuska ya yi sosai bai yi magana ba. “Ba na so ka bari iyalinka su fahimci wa ka fi karkata a kanta, ka bar komai a ranka, duk kan su kai ka ajiye su, ka yi kokarin kwatanta adalci a tsakanin su”. Sai da ya ji baban ya yi shiru ya fara magana “Ina iyaka kokarina Baba, ba wai rashin adalci yasa zan tafi da ita ba a wannan karon, na ajiye Halima a gefe na bar ta sai ta gane kurenta, rai fa tana son me kyautata mata Baba, yanzu zuwan Hadiza ba wacce ta saurare ta hasalima a falo suka watsar da ita. Ita ta ɗauke ta zuwa ɗakinta, ba wacce bata ci mata mutunci ba saboda Hadiza, ni ma sai da ta same ni da kukanta kan na wulaƙanta yar’uwata har ga shi na bada dama matana na wulaƙanta ta. Kai dai baba ka san yanda ta rike Hajiyarmu a zamanta ƙanƙara, yanzu haka ita ta tunasar da ni har hankalina ya kai kan yanda ƴan’uwana na gida ke rayuwa, taimakon da nake yi musu kullum cikin yi min addu’a suke”. Baba da ke ta murmushi ya ce “Ni ma na ce Allah ya shi mata albarka, ka samu mata Tahir, irin wadda ko wane Namiji ke fatan samu ta so ka kai da kowa naka ta so ka a kai din take so, ba kaɗan na ji daɗin samun wannan alheri da kayi ba, dan mace ta gari ita ce rabin addini, ka samu sai kayi ta kokari yanda za kayi adalci a tsakanin su, amma yanzu ka ɗauki babbar ba sati uku bane? Ya gyaɗa kai “Jiya na zo da addu’ar nan ta ruwan zamzam sai ka je mata da ita, zumar ce dai ba a kawo min ba har na taho, daga me kyau a ke so” Tahir ya yi godiya ya ce zai sanya a cincika mishi zumar a nan. Sun jima suna tattaunawa har sai da suka je sallar magrib suka dawo sannan ya yo gida.

Ina karakainar shirya abinci, Latifa ta kunna mp 3 a falo tana ta cashe rawarta, sai shilla dan kwankwasonta take, tana juya yan ƙananun mazaunanta masu kama da mara tana wakar “Mu dai igiyar mu uku uku zama dam zama dam. Ba zato sai shigowar Tahir muka gani ji nayi kamar in saki dariya dan yanda masu igiya uku aka yi wuri wuri, ai kau faɗa ya rufe ta da shi yana fadin ba ya son wannan shashancin za ta kunnawa mutane kida tana rawa, ya wuce sama.
Sai da ya dawo sallar Isha’i aka zauna cin abinci, Halima bata fito ba sai da aka kammala yasa Latifa ta kira ta, sai da ya daure fuskarsa tamau bai taba dariya ba, kafin ya ce “Kwana biyu zan yi, jibi zan koma dan haka Ummulkhairi za ta yi girki yau, Latifa tayi gobe, jibi za mu wuce tare da Halima.” Cikin ladabi Halima ta amsa ta mike ta koma ɗaki. Tana shiga kujera ta faɗa wani irin farin ciki ke ɗawainiya da ita, wanda ta rasa da wa za ta raba shi sai ta kira malaminta, tayi mishi albishir ɗin za a tafi da ita Lagos. Ya ce aiki ya yi mata sosai wanda yanzu ma akwai kuɗaɗen da za ta bayar dan a ƙara kama shi da kyau. Suka ajiye waya tana tunanin inda za ta samu kuɗaɗe dan ajiye tan nan da Tahir ya yi ba ƙaramin jin jiki take yi ba duk dan abin da take da shi ta miƙa wa malamai, sarkarta da Tahir ya saya musu ta fado mata ita kawai za ta kai kasuwa a bata kudinta, ta san yanzu da sun shirya kudi ba za su zama matsalarta ba.

Ni ma Halima na tashi na mike zuwa ɗakina, wanka na faɗa Aunty Laila na zaune kan gado Hadiza tana falo ta ki shigowa ciki wai kar ta takurawa baƙuwa. Na fito na zauna gaban mirror ina yan shafe shafe na, sai da na ji na dauki ƙamshi kafin na zura rigar barci doguwa har ƙasa, duk da take mara nauyi ba me bayyana surar jiki ba ce, hijab na sa iyakacin sa ƙirjina, na jawo kujerar mirror na zauna ina fuskantar Aunty Laila “In dan ni da kin yi tafiyar ki Mrs Tahir”. Girgiza kai nayi “Kina sa ni jin kunya Aunty Laila ni barci nake ji, sosai nake cikin gajiya” “Ai kina ma kokari cikin ya yi girma” kwalbar dazu ta ciro “To dan ƙara gogawa” fuska na bata “Abin ma ko tausayi Aunty Laila, so kike a kashe ni” “Da dai kin karba, dan wallahi za ki zo da kudinki kina roƙo na in nemo miki shi, abin nan ina me tabbatar miki ko matar gwamna aka siyar mawa ba za a ji kunya ba, kin samu a arha kina wani basarwa. Na ce ” Ba haka bane Halin da nake ciki za ki duba Aunty Laila” ƴar dariya tayi “Ni dai yanda na ji masu ciki ma sun fi son abun” kare fuskata nayi da hannuna na mike ta kara miƙo min kwalbar na amsa na shige cikin bathroom na shafa kadan dan fari ne kamar mai. Ina fitowa ban ko dubi inda Aunty Laila take ba na fice dakin, sai da safe nayi wa Hadiza har lokacin Basma da Latifa na zaune tare Tahir, kallo ɗaya nayi wa inda suke sai na wuce su na haye sama. Shigata kwanciya kawai nayi dan ba abin da nake so irin kwanciyar, ban sa ran shigowar Tahir a lokacin ba sai dai ina fara lumshe idanuwana na ji shigowarsa shirin barci ya yi kafin ya hawo gadon bayana ya kwanta ya rungumo ni ta baya yana shafa cikina “Cikin nan ya yi girma da yawa, ko dai yara biyu za ki haifo min? Da sauri har ina kaɗa hannu na ce “A’a daya ne” Duk yadda na so yin barci Tahir bai bani damar haka ba, wahala sosai ya bani har na ga kamar ya manta da cikin jikina. Dan haka ina idar da Sallah nayi niyyar guduwa ɗakina dan rama barci ko da yau zan koma Asibiti shigowarsa daga masallaci ya hanani umarnin in hau gadon in kwanta ya bani, sai da ya kare azkar ɗinsa ya hawo ya kwanta ya rungume ni ta baya muka shiga barci.
Karfe Tara na safe na farka gabana ya fadi lokacin da na dubi agogon, tuna ina da baƙuwa ban je na ga halin da ta tashi ba, kokarin tashi na fara yi ya ƙara kwantar da ni a hankali na ce “Lokaci fa ya tafi” idanuwansa ya buɗe “Ina za ki? “Ban duba Aunty Laila ba, kuma yau zan koma Asibiti” Bathroom ɗinsa ya nuna min “Shiga nan ki yi” ban cika son in ta yin musu da shi ba, dan miƙewar kawai nayi na shiga wankan na fito daure da tawul dinsa, na shafa man sa duk yana kwance ya yi matashin kai da hannuwansa yana kallona, narai narai nayi da fuska, shi kuma ya mike inda jakar da ya zo da ita take wata doguwar riga me matukar kyau kalarta danyen kore gaban kirjin caccabe da kwalliya ya miƙo min na sanya ba kaɗan ta karbe ni ba, damma katon cikina nayi rolling da gyalen rigar. Sai da ya gama kallona ya mike zuwa Bathroom “Ki shirya mu je Hospital din, idan muka kammala breakfast” kai na gyaɗa mishi. Ban yi mamakin ganin matan gidan su duka uku a falon ba, daki na wuce bayan na hada su nayi musu jam’un gaisuwa, zaune na samu Aunty Laila na zauna kusa da ita “Har kin tashi Aunty Laila? “Ba dole ba daga kin gudu ba dole mu nemawa oganki abin breakpast ba”. Ido na buɗe “Kai Aunty Laila dan Allah ha da ke a shiga kitchen? “Allah kuwa ki je ki samu Hadiza tana kitchen din” na juya sai na isa kitchen din, cikin mutunta juna muka gaisa da Hadiza muka kuma gaisa da Laraba da Indo. Mun jera abincin Ogan ya fito bayan an gama karyawa ya ce in je in shirya na samu Hadiza da Aunty Laila a ɗakina suna karyawa, fuskata na shiga gyarawa na canza doguwar rigar zuwa less, Aunty Laila za ta je unguwar Rimi wurin wata cousin dinta tare za su da Hadiza ni ma dan saboda Asibitin da zan koma da tare za mu, kiran Tahir da ya shigo wayata yasa ni miƙewa dama na kammala na sallame su na fito har ya zauna cikin motar, na zauna a front sit Ina satar kallonsa dan sosai ya min kyau. Yana tare da ni har aka yi min awon ya dauko ni maimakon mu koma gida, gidan da yake ginawa ya wuce ya shiga da ni ko’ina sosai na sha mamakin irin ginin da ake tamfatsawa Naira kawai ake ba kashi.

Daga nan sai wani wurin shakatawa muka dan huta sai yamma ya dawo da ni dan ko shiga bai ba sauka kawai nayi ya juya kan motar.
Na samu su Aunty Laila sun dawo. Washegari Tahir ya koma tare da Hali dubu kafin wucewarsa kuɗaɗe masu yawa ya bani ya ce in saya ma Aunty Laila tsaraba a ranar Asiya ta zo muka wuni. Sati guda Aunty Laila ta yi mijinta ya zo suka wuce mun rabu kan sai na zo bikin ƙanwarta Amira wanda Tahir ya ce zuwan da tayi ne kawai zai sa ya bar ni na kira Aunty Kulu na shaida mata batun zuwana birnin Ikkon. Na ci gaba da renon cikina da ke ta kara girma. Wata safiya Hadiza na zaune riƙe da wayarta na fito Bathroom wayar ta miƙo min “Ga Hajiyarmu” na amsa ina murmushi sai da na zauna na soma gaishe ta godiya take ta min da sa albarka kan rikon da nake wa Autarta.

Kwanan Laila goma da wucewa tafiyata biki Lagos ya zo ta jirgi za mu yi tafiyar ni da Hadiza saboda halin da nake ciki.

*Maryam litee*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

Cikin yan mintuna muka sauka birnin na ikko. Da motar gidan Kawu Attahiru aka zo ɗaukar mu. Mun samu kyakkyawar tarba wurin Aunty Kulu, sai da Tahir ya taso daga aiki sai ga shi shi ɗin kuma ya kwashe mu zuwa gidan su Laila, inda muka samu biki ya kankama kasaitaccen biki ake yi wanda aka ce tun saura sati guda aka fara, mun samu Aunty Laila tayi mana duk ankon da aka yi na bikin, ni dai dadin bikin rabi da rabi nake jinsa saboda cikin jikina. Sai da aka wuce da Amarya muka yi wa Momin Laila sallama, muka koma gidan Kawu Attahiru, da niyyar washegari za mu koma Kaduna. Dan Laila sun tafi Katsina raka Amarya ɗakinta. Sai dai me washegari muna cikin kintsawa sai ga text din Tahir ba fa yau za mu koma ba na ajiye wayar ina fadawa Hadiza abin da kenan, ita kuma ta fita gayawa Aunty Kulu. Lokacin tashin Tahir daga aiki sai ga shi bai shigo ba ta waya ya kira ni ina fita ya nuna min gefensa na shiga umarnin rufe motar ya bani sai ya yi mata key ribas ya yi ya bar layin, sai da muka dan yi nisa ya ce “Ke yanzu saboda Allah idan aka bar ki sai ki koma ba ki gana da mijinki ba? Shiru nayi ban yi magana ba daidai yana shiga wani wurin shakatawa da zaman mu tambaya ta ya yi me za ki ci na ce ban jin yunwa. Mun jima sosai a wurin sai dare ya mayar da ni wanda sanɗa nayi tayi kar Aunty Kulu ta gan ni har na samu shigewa dakin da aka yi mana masauki.

Latifa ke kai kawo a dakinta, rashin dawowar Ummu ya tsaya mata, bata kuma san wanda za ta tuntuba dan jin yanda ake ciki, haɗa su ya yi su biyu da Halima ko ya abin yake? da tayi yunkurin kiran Halima sai ta rasa kwarin gwiwa, dan rashin mutuncin da ta ragargaza mata da aka sake ta, har kuma ta tafi ba wani shiri tsakanin su. Wani tunanin tayi yasa ta suro wayarta ta kira ya yi biyar bata daga ba, kamar ta hakura sai dai ta kuma kira cikin sa’a ta daga, “Ya aka yi? Halima ta ce daga dagawarta, gaba ɗaya sai ta so daburcewa ta rasa ta ina za ta fara. Cikin karfin hali ta ce “Ina ta kira ba ki daga ba? Wata yatsina Halima tayi kafin ta ce “Ina tare da mijina time ɗin yaushe zan ji wani kiran waya? Wani malolon kishi Latifa ta haɗiya kafin ta sa dauriya me yawa wurin cewa “Ashe kuna tare ita wannan bakar dagar ta bar ki da shi? Ni na sha zuwan ta za ta dauke mishi hankali”. Wa kenan? Halima tayi saurin tambaya. Mutuniyarki Ummulkhairi, sai anjima fita zan yi” Latifa tayi saurin kare maganar kuma ta kashe wayarta.
Wata zufa Halima ta ji tana tsatstsafo mata Ummulkhairi na garin nan? To har yaushe ko da Tahir bai shiga sabgarta akalla da ya tashi aiki zai yo gida amma yan kwanakin nan baya shigowa har sai tayi barci dole ta dauki wayarta ta kira Latifa dan san jin karin bayani sai da ta ja mata aji sannan ta gaya mata. Halima ta ce “Bai kawo ta nan ba” sun dade suna magana kafin suka ajiye waya Halima ta nemi yar nutsuwar da take ciki ta rasa, da da ne tarar sa za tayi a yi ta ta kare dan ba za ta yarda yana barin ta yana fita wurin waccan shegiyar yarinyar da ta tsana.

Haka ta ci gaba da kasancewa kullun Tahir ya tashi wurin aiki zai zo ya fita da ni, mu zaga gari, har shagon mu na ɗinki mun je na ga ci gaban da wurin ya samu duk da cewa na Kadunan ma da Tahir ya nema mana tuni an fara aiki. Har sai ana gobe zai koma Kaduna ya samu a jirgi muka koma. Washegari kuma suka zo shi da Halima. Kowa ya san tafiyar nan tawa ce duk da a raina ba san tafiyar nake ba, dalilin cikin jikina da ya yi matukar yi min nauyi, amma sai ya ce Latifa ta shirya, ban nuna komai a fuskata ba na hadiye na bar ma raina. Sai shiri su Latifa ake yi cikin wani farin ciki na ta gaza boyewa. kwanan sa daya aka shigo da wasu galla gallan motoci na zamani guda biyu, ya damka makullansu ga Halima da Basma, nan ma kallo nayi da idona nayi musu murna. Latifa sai murna ta koma ciki yi tayi kamar za ta kama da wuta kan masu aiki ta sauke ɓacin ran ta, daga ba hali ta ce wa Ogan dan me? Ranar da ya zo Basma ce ta karbi bakuncinsa sai ni da zan karba yau, sai la’asar na shiga dakinsa na gyara, sai na fada kitchen muna tare da Hadiza ba ƙaramin taimako take min ba. Cake nayi a lokacin, sai na dama kunun gyada na shirya su a madaidaicin tray na ɗauka Tahir zan kai wa dan bai wani ci abincin kirki ba da rana, kamar ma dai yana da damuwa dan walwala tayi karanci a fuskarsa, shiyasa nayi tunanin sa ma mishi dan abin taɓawa kafin dare. Wata doguwar rigar material na sa, daga kirji ta kama ni sai daga kasa a ka buɗe ta, wani karamin bakin gyale na yane kaina da shi, na fito ina taku irin namu na masu ciki. Na shige Latifa da Basma da na samu zaune ta kofar baya, na bi wurin motsa jikin Tahir na nufa wani karfe yake ɗagawa ya yi gumi kashirban, na dan tsaya ina ƙare mishi kallo har ya fuskanci da mutum a wurin. Waiwaye na ga ya shiga yi har ya gan ni daga inda nake tsaye, sai da ya kare min kallo ya yafito ni, karasawa nayi inda yake wasu fararen kujeru da ke wurin ya isa ya zauna kan wata ta zaman mutum biyu kusa da shi ya buga da hannunsa, sai na zauna gefensa. Ruwa ya fara dauka ya sha ya ajiye gorar, sai na miƙa masa Cake, ci ya yi sosai sai na ba shi kunun gaba ɗaya ya shanye murmushi nayi sai na tattara kayan sai na miƙe, na soma tafiya na ji shi bayana, har ya zo ya wuce ni wurin motar da ya zo cikin ta ya isa ya bude Boot kayan da ke ciki ya shiga cirowa maigadi ya ƙwala wa kira, ya iso cikin sauri, zan shige su in shiga ciki ya kira ni, na karasa wurin su. “Kayan haihuwa na saya Ummulkhairi” ya fadi yana kallona murmushi nayi sai nayi mishi godiya “Maigadi zai kwashe sai ki kira Hadiza ta kwashe” Na daga mishi kai. Cikin na wuce na shaida wa Hadiza ta fita cikin sauri, da na shiga daki ta sa kayan nayi ina ta kallo suna da matukar yawa, kyau, da tsada, a dayan ɗakina muka adana su.

Sai da Tahir suka wuce da Latifa Kawu Attahiru wanda shi ma ya shigo garin ya aiko aka kira ni. Ina tsugunne gaban sa magana yake min, “Ni na hana Tahir tafiya da ke a wannan karon, Ummulkhairi. Duk da mamakin kalamansa da na ji ban ko motsa ba,. “Duk da shi ma bai so hukuncin nawa ba, ki zauna anan, ki ci gaba da rainon abin da Allah ya ba ki har Allah ya sauke ki lafiya. Kina amfani da sakon da ake kawo miki ko? Na ce “E”. “To ki ci gaba, Allah ya raba ku lafiya, ya bamu masu albarka” a zuciyata na fadi Amin a baki kuma na ce “Na gode”. Cikin matsananciyar kunyarsa da nake ji. Na cicciɓa na miƙe sai shi min Albarka yake, sai da nayi wa haj Hajara sallama sai na baro gidan.

Wannan karon Tahir bai samu shigowa ba Latifa ita kadai ta dawo, tana dawowa kuma Basma ta tafi. Tafiye tafiye yake tayi, ya dai je kankara duba Haj da ta yi fama da zazzabi, ko Hadiza ta so tafiya duba mahaifiyar tasu, amma Tahir din ya hana ya ce sai ya zo su tafi gaba ɗaya, dan akwai biki a gidan su na yaran yayyensa su uku mata biyu Namiji ɗaya, da Latifa wadda bata taɓa zuwa garin ba ya ce za a yi tafiyar, sai Basma, wadda ta gwada mishi bata son zuwa ya yi fushi duk da dawowar da tayi ta ce za ta je ganin yana fushi da ita, ya ce A’a. Ni dai har yanzu haihuwa shiru tuni watan haihuwar ya wuce Dr Muhammad ke karfafa ni da ba wata damuwa lafiya ƙalau ba wata matsala. To ya zan yi na zuba ma sarautar Allah ido ina dai ta addu’a in samu mu rabu lafiya.
Saura sati guda ya rage tafiyar su, da rana na ji duk na rasa me ke min daɗi, sai kawai na hau gado ba dan in yi barci ba, shiru kawai nayi idona rufe. Kukan wayata yasa ni miƙa hannu na dauko ta, sunan Yayata Habiba na gani na ɗauka ina gaishe ta, sai na ji tana fadin
“Ummulkhairi idan kin samu hali ki taho gida Babanmu ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ne ya buge shi yana Asibiti bai san wanda ke kansa ba.
Kuka kawai na saka na kashe wayar, na lalubo lambar Tahir, ina kuka nake gaya mishi halin da Babana yake ciki. Kwantar min da hankali ya shiga yi ya ce zai shigo gobe mu tafi. Na ajiye wayar na ci gaba da kuka na, Hadiza ta shigo tana tambayar abin da ya same ni, sama sama na fada mata, zama tayi tana ta bani baki. Haka muka ƙarasa wunin ranar, Hadiza dai tana ta aikin rarrashina, Tahir ma motsi kaɗan zai kira ni, ni dai na kasa kwantar da hankalin da suke so in yi, dan gani nake kamar mutuwa ya yi aka boye min musamman da na kira Ummata bata daga ba, tsoron kiran wani na ji sai kawai nayi ta addu’a.

Gari na wayewa ya fara min waya mu kasance cikin shiri dan da ya zo ba zai tsaya ba za mu wuce. Har kayan haihuwa na diba dan bamu san abin da Allah zai yi ba. Falo na dawo na zauna Abaya ce sanye jikina sai gyalenta na rufe kaina, “Ina masu tafiyar ku fito” Muryarsa da na ji a kaina ta sa ni daga kai na soma gaishe shi, sauran matan ma da ɗaiɗai suka riƙa fitowa suka yi mishi barka da zuwa “Ku zo mu je ina Hadiza? Ya fadi yana duba na, Hadiza ta fito tana janye da trolly ta soma gaishe shi ya juya ni dai mikewa kawai nayi na fito ina yamutsa fuska dan marata da na ji tana tsungula min. Direban da zai ja motar ya taimaka wa Hadiza saka kayan mu cikin Boot, ganin yanda nake yi Tahir ya ce yaya dai na ce ba komai. Ni da Hadiza ne a baya, sai shi da direba a gaba, wata irin tafiya nayi me matuƙar wahala muna isa kuma Asibitin muka zarce inda na samu duk yan gidan mu a can Ummata dai faɗa ta rufe ni da shi da ban yi hakuri ba na taho da wannan tsohon cikin. Kuka na kama mata mutanen cikin dakin suna cewa tayi hakuri ta daina min faɗa ta bar ni in ji da halin da nake ciki, Tahir dai na tsaye bai ko yi tari ba ya ɗan jima kafin ya yi musu sallama kuɗaɗe masu kauri ya ajiye ya juya ya bar dakin, sai da aka yi min magana na tashi na bi bayan sa dan har Hadiza ma ta fita, ina fita na gan shi tsaye hararata ya yi “Wai wa ya shagwaba ki ne yarinyar nan komai ki buɗe baki ki kama wa mutane kuka? Baki na tura ban yi magana ba, “Ki zauna mu ga abin da Allah zai yi, idan na shigo daurin aure sai mu koma tare, zan tafi da Hadiza in kai ta wurin Haj yau zan koma Kaduna”. Ajiyar zuciya nayi na ce “Allah ya tsare” “Zo ki raka ni, ko ba za ki iya ba? Na girgiza kai sai na fara tafiya, biyewa tafiyata ya yi muka jera har inda motar take nayi ma Hadiza sallama na ce ta gaida min Haj. Sai da motar tasu ta bar wurin na kama hanyar komawa ina takawa a hankali.
Kwana na hudu aka sallamo Babanmu wanda Alhamdulillahi ya samu sauƙi, har yana ce min me yasa na zo sai ga yan kankara mota guda sun zo duba Babana, hada Hajiyar su Tahir Hadiza dai da muka yi waya ta ce rashin wuri ya hana ta biyo su, na ji dadi sosai da karar da suka yi min, nayi ta godiya.

Washegari da hantsi na lallaɓa nayi wanka da ruwan da Ummana ta kai min, nayi kwalliya sama sama na sa doguwar riga ta Atamfa ɗinkin Babba ne, ban daura dankwali ba, kaina calaba ce tun da na zo daurewa kawai nake dan fama nake da ciwon baya musamman cikin dare, sai gari ya waye in tashi garau. Bakin gado na koma na zauna gwoggo ta leƙo “Ummu har an yi wankan? Ina murmushi na ce “E Gwoggo” ita ma murmushin tayi “Daki ya dauki ƙamshin turaren wuta kamar har an soma Jegon, Allah dai ya raba lafiya” a zuciyata na ce Amin” Sannunku da zuwa da ake ta fadi a tsakar gida yasa Gwoggo lekawa. “Ke Ummu ga mijinki nan hada wata kila cikin kishiyoyin ki ne”. Na ce “To” ina gwalo ido gwoggo ta kauce ita ma ta shiga fadin Maraban ku. Tahir ne gaba sai Latifa na biye da shi, ni ma sannu da zuwan na shiga yi musu da shigowar su, na ce wa Latifa “Zauna” ta zauna sai Tahir da ya tako inda nake kamar zai zauna, ko tuna gadon Ummana ne ya yi sai na ga ya fasa, kaina ya tsaya “Ya jikin? Na ce “Alhamdulillahi. Magana muka yi tayi yana gaya min lokacin komawata asibiti ya yi Dr Muhammad ya kira shi ga shi bana nan. jin motsin za a shigo yasa shi kaucewa ya zauna kujera yana kallona “Cikin nan ya miki girma da yawa muna komawa ba zan koma Lagos ba zan kai ki wurin Dr ya duba min ko akwai abin da zai miki. Murmushi nayi “Lokaci ne, yana yi zan haihu” Ummata ta ƙwala min kira na tashi na fita yana bi na da kallo abincin da ta shirya dan shi, ta bani in kawo mishi da kaina na zuba mishi zan zuba wa Latifa da ke ta wani yamutsa ta ce ta koshi na ce to ta zo mu je ta gaida Babanmu, muka dawo muka samu Tahir ya yi nisa da cin abincin “Ba na iya wuce tayin abincin Umma, Ummulkhairi, dan ita ɗin gwana ce wurin yinsa yasa mutum har ya ji kunnensa na motsi” murmushin zancen sa nayi Latifa kuma ta ƙara tamke fuska sai da ya gama ya ce “Tare da ke za mu wuce ƙanƙara Ummulkhairi” na dan jinjina abin sai na ce mishi “To” dan wallahi zuwa na gida ba ƙaramin daɗi nake ji ba kowa kaunarsa yake gwada min da tausayi. Mun yi sallama da yan gidan mu muka dauko hanya sai tunani nake a raina ita kuma ko ya zaman mu zai kasance da ita? Daga ita ba ɗaki ni ba ɗaki a Ƙanƙara.

*Maryam litee*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

Mun isa Kankara lafiya. Na sha mamaki da na ga ginin da Tahir ya yi a jikin gidan su, dan kwata kwata zuwan mu na ji yana maganar sayen gidan da ke jikin gidan nasu an gama shi tsaf sai maganar shiga. Mun bar Tahir tare da jama’a muka shiga ciki, cikin ba masaka tsinke, har Haj Hajara ta Iso, Kawu Attahiru ne dai da Aunty Kulu ba za su zo ba. Dakin Haj na kai mu daga Latifa zuwan ta na farko kenan, gyara sosai aka yi wa wurin nata, an maida shi two bed room flat an buda flat dinta ya zama katon gaske an kuma kayata shi da kayan more rayuwa. Nan muka ci abinci muka yi sallah Latifa da na hanga tana rada wa wata yarinya ta sasan yaya lawal ina ne part din Tahir? Ya sa ni dan guntun murmushi, mikewa tayi tayi wa Haj sallama. Ina nan har sai da nayi sallar Isha’i Haj ta ce “Ki tashi ki je ki huta ga gajiya, ga halin da kike ciki” Ban musa ba mikewa nayi Hadiza ta ce “Allah ya huta gajiya, sai da safe” na ce “Za ki sani ne, ina nan dawowa ki ma matsa min, wanka kawai zan yo”. Dariya tayi “Ina za ki tsafa da wannan uban cikin? gara ma kin yi kwanciyarki wurin ku”.

Na samu falon ba kowa sai candle da aka kunna, kofar dakin Tahir na tura dan ba abin da nake so irin in gasa jikina da ruwa me dumi, jakata da na zubo kayan amfanina na dauko, ina bude su ina tunanin komai nawa ya kusa karewa duk da nayi waya da Aunty Kulu bayan isowar mu da na samu labarin ba za ta zo ba, na ce komai na amfanina sun kusa karewa ta ce sai na haihu za ta taho min da su ta ware min wadanda nake saye. Latifa na gani baje bisa gadon, wani murmushi ne ya subuce min su Latifa manya, ashe saurin da take dan ta zo ta shige dakin ogan ne, dan dama Hadiza ta saurari hirar su da Halima tana gaya mata muddin Basma bata je ba, idan tayi wasa aka zo da ni kankane komai zan yi ta rasa wurin zama. Wayarta take latsawa ga kida ta kunna a wayar, kallo daya nayi mata na wuce bathroom sai da na hada ruwan wanka da turarukana na wurin Aunty Kulu masu dadin kamshi da kwantar da hankali kafin na gasa jikina dadi na ji sosai na dauro katon tawul dinsa na rufa da karami, sai na fito, na wuce ta zuwa falo wata kwafa ta saki “Ko da wannan fitinannen kamshin ta karbe miji, ballantana a zo batun girki sai dai hassada ta sa ka kasa yaba mata, ga dirin jiki na masifa da ko ke mace sai ta burge ki, bare namiji. Tayi duk iya yinta ta samu hanyar shiga dakinta dan ta ga sirrinta, amma hakan ya faskara. Gyara kwanciyar tayi cikin matukar takaici.
Sai da na fiddo mayukana na shafa sai na bi da turare, wata doguwar riga me bin jiki na zura na rufe kaina da gyale komai na maida shi inda yake na rufe jakar da dan karamin kwadon da nayi guzuri, na jefa dan keyn a hand bag dita. Sallamar da na ji cikin wata makalalliyar murya ta sa ni daga kai ina amsawa Tahir ne, “Yaya madam ke kadai ga duhu? Murmushi nayi na ce “Ba komai, mu da za mu shiga barci” Ya ce “Gen din ya samu matsala ya ki tashi, amma me gyara ya zo ana duba shi” Da yake ya saya musu katon Gen a gidan. Na ce “Dama solar ka sanya musu” ya ce “Shawara me kyau, sai dai yanzu sasan su nake so a maida musu na zamani, ayi wannan din daga baya” na fadada fara’ata “Allah ya kara budi na alheri ya kara daukaka, dan sashin Hajiya ba karamin kyau ya yi ba” Bai ce komai ba sai ya ce ” Ina Latifa? Da hannu na nuna mishi kofar dakin ya mike ya isa kofar ya tura ya shiga da sallama zaune ta tashi tana fara’a, “Ba ki yi barci ba? “Ban yi ba ka san bana barci da wuri” ya ce “Haka ne, to sauko ki ci nama, kina ta fama da duhun kauyenmu” fara’ar ta kara tana saukowa “Ai wallahi garin ya min” “Ashe ki ce idan zan maido ki nan din ba zan samu matsala ba? Shiru tayi tana tauna naman da ta sa ka bakinta, tana ta ci tana korawa da lemo duk yana kallonta, dadi ya gama kume ta sanin ya baro Ummulkhairi falo, rigar jikinta ta yaye tana mishi wani irin salo na jan ra’ayi murmushi kawai ya yi sai ya mike tsaye “Daga kin gama zo mu je falo mana” ba ta so hakan ba, amma ba yanda ta iya ta mike ganin har ya kai kofa.
Ina zaune a inda ya bar ni sai dai kishi da ya turnike ni kamar ya kashe ni, sai nayi kamar in tashi in yi tafiyata sasan Haj sai kuma in ba kaina magana in daure, zama ya yi ita ma ta zauna kusa da shi tana ta salo kamar za ta hada jikinta da na shi. Dakin ne ya gauraye da haske mikewa ya yi ya kunna TV sai ya canza wurin zama “Ummulkhairi ina ganin ki je sasan su Umma (Mmn Ummi) za ki fi sakewa” da to na amsa mishi duk da wani takaici da ya kulle ni, dan yana so ya kasance da matarsa shi ne zai kore ni. “Ki dauki abin da za ki bukata saboda safiya” nan ma to din na kuma ce mishi tashi nayi na suri jakar da na zubo kananan abubuwan amfanina ina mai da na sanin zuwana indai wannan nuna iyakar za a yi min. “Ke kuma Latifa ki shiga ki kwanta zan turo Hadiza ta taya ki kwana” “Kai kuma fa? Latifar tayi saurin tambayarsa “Mutane sun yi yawa gidan” “To ina za ka kwana” “Kar ki damu da inda zan kwana ni da garinmu”. Wata boyayyiyar ajiyar zuciya na fidda “Idan kin tashi akwai komai da za ki bukata a kitchen” ya ce wa Latifa ina ficewa na ji yana ce mata sai da safe, bata amsa ba sai wani kallo da ta bi shi da shi na zallar takaici ranar da ya koma kaduna daga kawo Ummulkhairi bai kwana ba jirgi ya bi ya koma Lagos yau kuma yana zuwa suka dauko hanya tana murna yau ita ke da miji dan sharri ya tafi ya bar ta.
“Ummulkhairi” na ji muryarsa a bayana ya yin da na dauki hanyar sasan maman Ummi jama’ar gidan da yan biki kowa ya nabba’a dan hadarin da ya hadu wanda a kowane lokaci ruwa zai iya sauka. A inda nake na tsaya cak ban waiwayo ba sanin kowaye. Har ya karaso inda nake hannuna ya kama ya kuma karbi jakar hannuna hanyar waje ya kama bi ni dai bin sa nake kamar raƙumi da akala har waje inda ya adana motarsa, buɗe ta ya yi ya kuma ba ni umarni in shiga sai da na shiga na zauna ya juya ya koma cikin gidan ya bar ni da tunanin ko me hakan ke nufi? Kofar Hajiyar su ya tsaya sai ya kira Hadiza a waya ta fito ta same shi umarni ya bata ta je part ɗinsa ta kwana a falo da to ta amsa tana tunanin dalilin yin hakan. “Idan kuma Latifa ta tambaye ki Ummulkhairi ki ce tana wurin su yaya lawal” kai ta daga mishi sai ya juya ta bi shi da sai da safe. Na muskuta gami da gyara zamana “Na bar ki zaune ko? Ya fadi yana wa motar key murmushi nayi ban yi magana ba. Muna tafiya ina tunanin inda za mu na ga mun isa gidan kajin sa gidan maabocin dogayen bishiyoyi ya yi horn aka buɗe mishi wani madaidaicin gini ya shigar da ni duk kuwa da cewa cikin haduwa ya yi ta karshe wani niimtaccen dakin barci ya kai ni, bakin gado na zauna bayan shigarsa toilet fitowarsa gani na zaune ya ce “Ba ki kwanta ba” kai na daga mishi “To zo mu je falo” na mike na bi bayansa leda ya bude gasassar kaza ce ya turo gaba na ya tashi kunna Tv tare muka ci ina gamawa na ce barci da hannu ya nuna min ƙofar bedroom na miƙe da kyar na wuce ina shiga kwanciya nayi ina jin wani sanyi dan hadari da ya taso gaba ɗaya har ruwa ya fara zuba sai ga shi ya shigo blanket ya ciro me matuƙar laushi ya lullube ni,har wata ajiyar zuciya na fidda, sai ya tuna min Ummata zuwan nan da nayi idan na kwanta ita ke lullube ni, ya kashe fitilar me haske, ya kunna bed side lamp, sai ya hawo gadon bayana ya kwanta ya rungume ni ta baya fuskarsa yasa a kan wuyana “Nayi kewarki Ummuna” abin da ya rada min kenan wani lokaci ya dauka yana abu daya sa’adda na samu ya sarara min sai marata ta dauka da ciwo
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

Haka na daure har sai da na ji ta lafa min sai na shiga barci. Gabanin Asuba na farka marar ce ta ci gaba da tsungula min Tahir na kan sallaya ya yi sujjada ga mahallicinmu. Har ya fita sallah ban samu na tashi ba, da kyar ta sakan nayi wanka hade da alwala, sai da na gabatar da Sallah na zauna nayi kwalliya Atamfa nasa ɗinkin doguwar riga. Sa’ilin ya shigo “Lallai ma me cikin nan akwai kokari har kin yi wanka kin sha ado? Murmushi nayi ina gyara daurin dankwalina na gaishe shi ya jani zuwa bakin gado, hira muka yi ta wani lokaci kafin muka kwanta. Wayarsa da ake kira ta tayar da mu ya sa ta a kunne sai na ga ya mike ya fita kafin ya dawo ya ce in zo mu ci abinci na ji dadin abincin dan haka sosai na ci sai sha biyu ya yi wanka ya shirya sai muka bar gidan, shi ma damunsa aka yi tayi da kiran waya, ana tambayarsa yana ina? Sashen mu ya shiga ni kuma na wuce na Haj Wanda na samu ya cika da jama’a. Hadiza da na hango ta sha kwalliya cikin wani rantsatstsen less na nufa muka yi wa juna murmushi “A kwana a hantse” ta fadi tana kama hannuna zuwa dayan dakin Haj da ba kowa dan rufe shi Hadizar tayi ta nuna min kayana da ta kwaso min ta kuma gabatar min da duk abincin da aka yi na bikin, da ta diba ta ajiye min. Na ce “Yanzu dai na koshi sai dai ko anjima” da ganin fuskar Hadiza akwai magana sai dai akwai yar nauyi tsakanin mu, ta dai ce min “Yaya Sodangi ya ninke matarsa” sanin inda zancen ya dosa sai nayi murmushi kawai canza kayan jikina nayi zuwa shadda ɗinkin doguwar riga, tun daga wuya kunnuwa da hannayena sun sha adon gwal walkiya kawai nake dan shaddar ba me ƙananan kudi ba ce takalmi da jaka na sa sai mayafi da na rataya a kafaɗata
Muka fito Haj na ta nuna ni ga yan’uwanta da suka zo da jama’ar ta “Wannan ita ce matar Sodangi wadda ta ke riƙe min Autata” sai ka ji ana fadin Allah sarki.
Karfe uku duk jama’a sun koma tsakar gida inda ake ta cashewa. Daga ni sai Haj da Hadiza Tahir ya shigo ya cire babbar rigar da ya sa sai ƴar ciki da wando yana zama Haj ta miƙe hurar da na ga tana ta damu ɗazu ta dauko mishi yana sha yana lumshe ido “Kamar ko kinsan ban ci komai ba Haj tun karin safe” ido ta fiddo “Duk abincin da aka fitar waje? Bari in dubo maka ba za a rasa abinci ba” “Huta Haj, ku ci abincin ku zan fita in nema, Hadiza kira Latifa” Ta tashi ta tafi text na mata na ce ta hado abinda za mu yi wa yayanta girki. Sai da ta tsaya tayi blending din kayan miya kafin ta dawo, dan haka latifa ta riga ta shigowa an sha kwalliya cikin less kusa da Tahir tana gaishe da Haj. Na mike zuwa kitchen din hajiyar Hadiza ta mara min baya, jallop muka yi cikin sauri wadda ta sha kayan lambu da wadataccen naman rago, Hadiza ta markada min Aya muka hada kunun Aya wanda na jefa ma kankara na juye madara peak. A tire na jera na fito Hadiza ta biyo ni da wani dan stool na dora mishi abincin, Haj ta rike baki “Yanzu dan Allah zaman nan namu har kin yi girki? Ni ko da nake ta jin kamshi ban kawo nan bane” Na ce “Dan dai girkin flate daya Haj ai ba wani bata lokaci” kitchen din na koma ina sauraron farfesun kazar da na dora ma Haj ya karasa. A Flack’s na juye na dauko zuwa falo na dire shi gaban Haj, lokacin Tahir ya kusa tashin abincin gabansa, Haj ta bude tiriri da kamshin naman suka buge ta ta dago ” Ma sha Allah, sannu Ummulkhairi Allah ya shi albarka, kina fama da kanki kika dora wa kanki aiki” murmushi nayi na zauna ina sauraron zancen da Tahir yake wa Haj kan tafiyar da zai yi gobe zai biya Kaduna su wuce tare da Halima, a Lagos din ma ba zama zai ba za shi wani aiki Port Harcourt. Latifa dai tana zaune kamar bata wurin jin anan Tahir zai bar ta sai na ga fuskarta ta canza. Ya juyo gare mu “Gobe idan Allah ya kaimu za a kawo furniture’s na dakunanku, kowacce sai ta je ta zabi daki a sabon gidan can, Sati guda za ku yi inna kammala aikin da ya kaini zan dawo mu tafi tare”. Dan murmushin su na manya Haj tayi “Wannan cikin har zai kai satin? Tahir da kamar bai fahimci zancen nata ba ya ci gaba da maganarsa, kiran da aka aiko ana mishi yasa shi mikewa, latifa kamar tana bisa wuta yana fita ta bi bayansa. Tana shiga bedroom, dankwalinta da ta bata lokaci wurin daurawa ta fincike ta wurgar gadon kawai ta fada zuciyarta kamar ta fashe hoton Ummulkhairi kawai ke mata gizo shigar da tayi ta matukar sa ta kaduwa bata yi la’akari da tsadar nata less din ba. Ga zaman kauyen nan da Tahir zai ja mata, wai ta zauna har sati. Wayarta ta jawo kawarta Fadila ta kira tana kora mata damuwarta hakuri ta bata, sai dai cikin zafi ta soma fadin “Wancan karan ma da ya sayi mota bai saya min ba cewa kika yi in yi hakuri kika hanani in yi magana, to wallahi yau zan yi maganar motar duk abin da zai faru ya dade bai faru ba” Duk yadda kawar tata taso nuna mata su bi komai ta siyasa latifa birkicewa tayi. Ana sallar Isha’i Tahir ya shigo sama ya same ta yana tambayar ta ci abinci tana maganar mota cikin mamaki ya ce “Wane irin zancen mota kuma za a yi anan, tun can ba a yi ba? Tana wani daga hanci ta ce “Na ga ba ka da niyya ne” ya ce “Ina da niyya zan saya idan lokaci ya yi, dan yanzu dai kina ganin hidindimun da ke gabana gini biyu nake, ko da na gama na nan, akwai na Kaduna. Daga murya ta fara ban yarda da sai wani lokaci ba a bani hakkina kawai yanda aka saya musu a saya min” Kallo sosai ya yi mata “Latifa, girma da arziki na dauko ki zuwa gidan mu, ka da ki neme ni da magana” juya ido tayi ta ci gaba da fadin maganganunta san rai mikewa ya yi yana neman rigar da ya cire “Ba zan iya kwana kina nema na da fitina ba, kuma ba zan biye miki ba dan gidanmu na kawo ki” ya maida rigar “Sai da safe” sai ya fice Wayata ya kira bata shiga ba, sai ya kira ta Hadiza lokacin muna dakin Haj da ba kowa daga ni sai ita, ni dai daga yin sallar Ishai da kyar na rube kayan jikina sai na sa wata riga iyakarta gwiwa, na kwanta ina kallonta tana amsa waya sai ta miko min jin muryar ogan yasa ni fasa tambayar ta waye. “_Ki fito ina waje” abin da ya ce min kenan ya kashe wayarsa bin wayar nayi da kallo cikin takaici ko tausayi ban ba shi ya ta do ni da daren nan siririn tsaki na ja sai na cicciba Hadiza da ke kallona ta ce Lafiiya? “Wai yayanki ne ya ce in same shi waje” cikin tausayawa ta miko min hijabi dogo har kasa na zura zan fito ta ce da kin dauki kayan da za ki sauya” kai na girgiza bar su kawai ” na sa kai na fita yana cikin motar, na bude na shiga ganin ya fara ribas na ce “Ina ce wurin Latifa za ka kwana yau? Wani kallo ya yi min nayi sauri na kauda idona, “Idan ba za ki ba in tsaya ki sauka malama, kema kar ki kara bata min rai ” Shiru nayi gane ransa a bace yake. Hadiza ta iso jaka ta miko min tana mana sai da safe.
Har muka je ba wanda ya kara magana. Ni dai gado kawai na nema ina zare hijab din sai na kwanta. Ina tunanin yau ba zai saurare ni ba, ganin yanda yake cika yana batsewa na soma barci sai jin mutum nayi a bayana, yau ma kamar jiya ciwon mara ya tado min, na kuma ta fama da shi har safiya, ko da ya ga yanda nake yi ya ce ya ya dai na ce ba komai. Karfe takwas muka bar nan din, kudade masu yawa ya sallame ni da su, ya nufi wurin Latifa. Kamar yanda ya ce za a kawo kayan dakunan mu an kawo na tashi daga barcin da tun dawowata ya dauke ni dan na samu marar ta lafa Hadiza ta ce in zo mu je in zabi dakin ga Latifa can ta tafi, na ce ta zabar min dan wani ciwon marar da ya dawo sabo. Tun ina yi ba wanda ya fahimta har Hadiza ta gane Haj ta kira nan take Haj ta kidime matar babban Yaya maman Sadika aka kira sai uwar gidan Yaya magaji suka tsaya kaina. An kawo mota ana cewa a fito da ni na ji wani ruwa ya keto gabana “Alhamdulillahi faya ta fashe in ji Maman Sadika in sha Allah an kusa bata rufe baki ba na fara wani uban nishi sai ga kai gaba daya sai dan ya fado, an dauke shi ana jiran uwa ta biya sai ga wani kan ya fara tahowa nishin na duka sai ga wani dan kasa sai mahaifa ta biyo shi. Take gida ya rude da murna yau Sodangi ya yi Yaya har guda biyu suma kuma Sodangin ne, kamar yanda Haj ta je biki gidan su ta haife shi mace ce da namiji. Ruwa aka dora matar babban yaya ta ce in hau gado in dan huta na girgiza kai na fi so in yi wankan da taimakon su na shiga bayin dan jin da nayi kamar iska za ta wancakalar da ni sa’ilin da na tashi. Na gasa marata da jikina da kyau kafin na fito na samu nurse din da yaya magaji ya turo ta iso duba ni tayi ta bani magunguna, na shirya cikin riga da zane na kwanta bisa gadon, yaran aka kawo min wadanda har an gama shirya su, yawan jama’ar gidan da baki yan biki yasa ban iya kallon su ba. Kiran waya ya rika shigowa yan gidan mu ne, da wata ta tsinke wata za ta shigo Hafsa ma ta kira, can sai ga kiran Laila da na Asiya, su na san Hadiza za ta kira su. Gasashshen Nama aka kawo min wai in ci maganin kan baki Hadiza ta hado min tea na sha sai na gyara kwanciya kiran Aunty Kulu ne karshe sai na shiga barci.
Bayan La’asar na farka Abinci Hadiza ta kawo min na ce ba zan ci ba sai ta kira Haj, lallashina Hajiyar ta kama “Abinci shi ne jego tashi ki ci” na tashi na ci, na gama na wanke hannu Hadiza ta miko min waya “Ogan bisa layi” na kai hannu na karba ina murmushi.

 

*Maryam litee*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *GARGADI*
*Hakkin mallaka na* *wannan littafin nawa ne ni kaɗai, ban yarda a sarrafa min shi ba ta* *kowace siga ko da kuwa ta hanyar mayar da shi document ne. Dan haka a kiyaye*

*Na kuɗi ne ka biya 300 a 2108124716 Maryam nasir UBA bank*
*dan nuna shaidar biya 07033400612**

“Me jego kin sha ruwan dimi” murmushi nayi me sauti “Ko ba haka ake cewa ba? Ban amsa ba na soma tambayarsa hanya ya ce “Alhamdulillahi, sai yanzu ake gaya min haihuwa, an ta kira na ba ta shiga wai wasu Sodangin sun iso. Na ce ni ban yarda sunan su Sodangi ba korau sunan su dan sai da suka kore ni suka iso, ya ya lafiyar ku ƙalau? Kai na gyaɗa kamar yana kallona. “An ce min a gida kika haihu, akwai wata likita abokina zai kawo ta anjima ta duba ki sosai har yaran. Na ce mishi To” “Abin da duk kuke bukata ki rubuta mishi zai kawo, Aunty Kulu za su taso gobe zan aika akai mata key na ɗakinki ta kwaso sauran kayan dan Hadiza ta ce min kin dauko wasu, ni ma idan Allah ya tashe mu lafiya zan wuce port Harcourt, an tutturo min hotunan yaran” murmushi na ƙara yi. Mun jima kafin na ajiye ina wa Latifa sannu wadda tun soma wayata ta shigo, gaishe ni tayi Hadiza ta kwaso mata yaran ta ce a bar su ta gan su, ta juya ta fita.

Da daddare bayan kowa ya wuce sai bakin Haj na nesa suka rage, su ma suna falonta, daga ni sai Hadiza taba ni ta rika yi daga kwanciyar da nayi na juya baya. “Ki tashi ki ga yaran nan, daga ba kowa dan ina kula da ke ba ki kalle su ba” zaune na tashi ina duban inda take miko minn namijin, na karbe shi ina kare mishi kallo idan ka ji kalmar bahaushe da yake fadin kwabo da kwabo to yaron shi ne kwabo da kwabo da mahaifinsa ko da yake jariri. Addu’a na tofa mishi sai na kwantar da shi na karbi yar’uwarsa, ba a mamaki da ikon Allah ban da haka da nayi mamaki ita kam kamar an tsaga kara da mahaifiyar Tahir yanda Haj take farar bafulatana kyakykyawa haka yarinyar take. Tahir shi mahaifinsa ya biyo shi da Hadiza, sauran yanuwansu ne ke kama da Haj. Ita ma na kwantar da ita ina ta kallon su ina jin dadi wai yau ni ce rike da dan kaina abin Allah har ma guda biyu.

Washegari yan gidan mu suka zo. Yayyena ne gaba daya sai gwaggo wai matan yayyena su sai gobe dan kar su yi yawa, Hafsa ta riga su zuwa ita da malam har falon Haj ya shigo aka kwaso mishi yaran na fito muka gaisa ya dauki jariran ya yi musu Addu’a. Yayyena sun wuni har yamma kafin suka tafi sai babbar yayata Aunty Maimuna aka bari za ta zauna da ni zuwa suna.
A wannan haihuwa na ga jama’a dan yadda family su Tahir su ke da yawa mu ma namu haka, zuwa kawai ake daga Dutsinma.
Ko da Tahir baya nan hidima sosai yake kan haihuwar. Haj Hajara ta tafi Aunty Kulu ta iso ita da Kawu Attahiru wanda da ya dauki jariran hada kwalla ya share wai yau yayan Tahir ne a hannunsu, kamar yanda Haj ma tayi. Duk wani shirin suna Laila da Asiya ke gudanar da shi dan haka sai ana gobe suna suka iso, Su Halima da Basma ma sun iso tun da rana amma ni dai ban gan su ba sai da me gayya me aikin ya iso da yamma suka biyo shi suka shigo tare, Basma dai ta ce tana son su amma ita bata iya daukar yara ba, Halima dai ganin idonsa ta dauka, ba su wani jima ba suka mike suka fita. Kallona ya yi bayan fitar su ” Kin yi kyau Maman biyu jegon ya karbe ki” murmushi nayi “Ya ya ba wata matsala ko? Kai na girgiza “Ba ka bar mu da ita ba” macen da ke hannunsa ta bude ido ya ce “Mamana ta tashi ” ya mike tsaye da ita tana kallon kwan lantarki “Me yasa ba ki koma dakinki ba? Ya jeho min tambaya dan shiru nayi kafin na ce “Na riga na haihu anan shiyasa ban koma ba” “Daga bakin da yawa a kai yan’uwanki dakinki” kai na daga mishi Namijin ya fara kuka saurin kwantar da macen ya yi ya dauko shi “Gyara to ki ba shi nono” nuku nuku na fara kafin na ciro ya sanya min shi a cinya na soma ba shi, shi kuma sai kallon mu yake macen da ya dauka ita ma ta sa ka kuka na ciro na hada su na shayar da su kamar yanda na koya. Ya dauki tsawon lokaci tare da mu har sai da aka kira shi. Cikin lokaci kadan Hafsa sun saba da su Laila. Sai da muka yi barci Aunty Laila ta ciro sarkokina da ta tafi da su tun zuwanta ta canzo min wasu, da kuma kayan da zan yi kwalliyar suna, dan ita na ba kudade ta sawo min kayan ta kuma bayar da dinki. Su uku muka kwana Hafsa, Laila sai Asiya.
Safiyar suna yaran sun amsa sunan Zainab sunan mahaifiyar sa da Tahir sunan Kawu Attahiru Attahiru bugu da kari kuma da ya cinye sunan ubansa. Ya yanka wa yaran ragunan su biyu, sai Sa da ya ce ayi abincin suna da shi an kira ni dan tambayata yanda za a yi da naman san na ce a kira masu gashin nama su yi ta gashi a tsakar gidan duk wanda ya zo akwai masu rabo su kai mishi
Laila da Asiya sun yi hayar wani shahararren gidan Abinci daga Kaduna su suka zo tun daga can an shirya runfuna da kujerun Canopy su suka yi ta raba abinci ga mahalarta sunan, an raba abubuwa da dama masu dauke da hotunan yaran, ya yin da nake ta shiga ina fita cikin shiga ta alfarma, kishiyoyina dai tun fitowa daya da suka yi ba su kara fitowa ba sai dai masu kai musu gulma su kai musu labari a wannan rana nayi kyau har na gaji na kuma samu alheri ko maman Laila Abin hannu na gwal da yankunne ta aiko wa Zainab sai kayan jarirai da zannuwa. Kanwar Aunty Laila ma ta zo daga Katsina, matan abokan Tahir sun zo sosai.
Washegarin suna yan’uwana soya nama suka yi aka raba suka shirya tafiya zuwa gida, da gwaggo za ta ci gaba da zama da ni, sai ta bi su suka tafi ta ce zaman me za tayi uwar mijina da yan’uwan sa na tsaye a kaina. Na roki Hafsa ta kara kwana ta ce “Cab! dan ma ke ce Malam ya bar ni kwana biyu” sun tafi sun bar ni da kewar su da tarin alherin da na yi musu ni da Tahir, Laila da Asiya ne suka rage sai gobe.

Ranar da su Laila za su wuce nayi wankan safe kwalliya na yi cikin wata farar super riga da zane rigar ta zauna a jikina ga cikar jego nayi kaina kitso ne two step aka yarfa min sun zubo har kafadata takalmi na zura na yafa wani yala yalan mayafi sarkar da nayi ado da ita daga karshe ran suna English gold na sa a wuya da kunne sai bangul da zobuna suna ta sheki. Na fito zuwa falo, yaran tun da aka yi musu wanka Haj ta goya Takwararta Mimi Hadiza ta goya Areef, ihu Aunty Laila da Asiya da ke zaman karyawa suka saka Wallahi me jegon nan kin hade, ko dai yau za a maida mahaifa” Kai na dafe duk da sanin da nayi Haj bata sasan, Hadiza kuma ta kauda kai, wuri na samu na zauna Asiya na daukata hotuna da wayarta “Dole ne angon karnin ya ga wannan kwalliyar” ta tura mishi hotunan. Sai dai a daidai lokacin da hotunan ke shiga wayarsa yana zaune a falonsa na sabon gidan sa su Halima sun sanya shi tsakiya wadanda tun tashin sa suka ce suna son magana da shi abin da bai sani ba tun ranar suna matan uku suka hade kansu, dan shigar da me jegon tayi tayi musamman gwalagwalan da tayi ta sakawa da kayataccen shagalin sunan da aka yi ya daga hankalin Halima da Latifa, suka karanta ma Basma suka nemi hadin kanta, sun shawarta su ritsa shi kan ba za su yarda da wannan rashin adalci, Ummulkhairi ita kadai ce matarsa da zai rika kashe mata dukiyarsa su ko oho. Hakan ko aka yi da wannan ta sauka sai wannan ta dauka yana sauraren su, wayarsa kawai ya jawo ya shiga kira.
Su Aunty Laila suna ta min tsiya kiran sa ya shigo na dauka zan soma gaishe shi na ji ya ce “Ki zo yanzu ki same ni”. “Lafiya? Na tambaye shi kit na ji ya katse kiran. Cikin jimami na sauke wayar ina fada musu abin da kenan. Sannu a hankali na fito mun gaisa da wadanda na gani a tsakar gidan har na isa kofar da aka yi wadda ita za ka shiga ta kaika sabon gidan na Tahir sai a sannan na ga sabon gidan, babu laifi tsakar gidan na da girma dakuna ne guda hudu kowacce ciki da falo da bayi sai na ogan shi ma haka, ban san wanne ne na shin ba sai na kira Hadiza a waya na tambaye ta, ta fada min sai na isa, da sallama a bakina na shiga falon, sai dai shi kadai nake tunanin ya amsa su ukun kowacce zaune take tana kada kafa. Zama nayi kujerar da ke fuskantar wadda yake kai, shi na soma gaidawa, kafin na hade su duka na ce ina kwananku? “Ku maimaita abin da kuka ce” ya fadi yana duban su, shiru duk kan su suka yi, ya maimaita sai dai ba alamar akwai wacce za ta tanka ya maido dubansa gare ni “Ke Ummulkhairi ki ji tsoron Allah, ki sani akwai ranar da za ki tsaya gaban Ubangijinki na taba saya miki sarka ta gwal? ban da wadda na ba ku gaba daya ” kai na girgiza “Tsakanina da Allah ba ka taba saya min wani abu, ba ma sarka ba, sai ka hada mu ka bamu tare”. “Good to wadannan bayin Allan sun sa ni gaba kan na saya miki gwala gwalai kin yi fitar suna su ban saya musu ba, nayi miki zannuwa masu asalin tsada su ban musu ba, ko wancan zuwan sai da muka samu matsala da Halima kan na saya miki gwalagwalai” Na fidda ajiyar zuciya “Ni ba ka sai mini zannuwa ba, kudade ka bani ka ce in sayi kayan da zan yi fitar suna, su kuma gwala gwalai ba lallai in tsaya fadin yanda na same su ba dan sirrina ne, amma ni bai bani kudin sayen su ba, sa’adda na saya ma bai sani ba. Su ya duba “Lokacin da na saya muku mota wace ce ban ba kudade ba? Suka yi shiru ya tambayi adadin kudaden da ya ba ni ban ko numfasa ba na fadi ya ce wacce ce ban ba haka ba? Suka kara tsit dogon tsaki ya ja ya tashi ya fice, ni ma mikewar nayi na baro gidan na koma sasan Haj, na samu su Aunty Laila sun tafi gidan Aunty Kulu sayen turaruka, sai Azahar suka wuce tare da dinbin kayan suna da hada musu sai kalmomin godiya da nayi ta jera musu.
Bayan tafiyar su sai na ji duk ba dadi, daga ni sai Haj sai Hadiza.
Da yamma nayi wanka jariran ma an musu suna ta barci zaune muke ni da Haj da Hadiza kamshin turaren wuta falon ke ta yi, Tahir ya shigo da sallama, gaida Haj ya yi muka gaida shi ni da Hadiza ya karasa inda suke kwance ya dauki Areef ya ce Hadiza ta dauko mishi Mimi bayani yake wa Haj gobe zai koma ta ce hada iyalin naka? Ya ce “Hada ma Ummulkhairi daga an yi suna ” salati ta rafka “Kai yanzu sai ka dauki wadanda yan bayin Allan, ka kwasar musu cuta, to ko za su koma sai yaran nan sun yi kwari, an nema musu magunguna su da uwarsu” bai kara magana ba amma a halin sa da na nakalta na san ransa ya so su da hukncin Haj, zama ya ci gaba da yi har sai da aka kira sallar magrib, ya fita zuwa masallaci.
Washegari kuma ya tattara matansa suka koma.

*Maryam litee*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: Wanka na ci gaba da yi cikin tsantsar kulawar da nake samu. Dauri dai yaran nan sun sha shi, ni kuma na sha maganin sanyi har na gaji, wurin Aunty Kulu turaruka na saya, na jiki da na tsugunno masu asalin tsada, dan ita kayanta yammatan gaya ne ga kyau ga kudi. Tahir bai samu dawowa duba mu ba saboda yanzu aikin nasa ya koma tafiye tafiye, har sai da muka yi wata guda Allah ya yi wa Malam na tudun wada rasuwa daga gidan gaisuwar ya iso Kankara, cikin jimami yake kwarai na rashin tsohon kwana daya ya yi ya koma. Ya ce wa Hajiya da nayi arbain din da ta ce zai turo a tafi da mu, Hajiyar ta ce ba zai yuwu ba dan ban je gida ba kuma akwai biki a gidan mu na yayana Mustafa da diyar Babbar yayar mu za ta aurar da diyarta ta farko.
Ana gobe zan yi arbain kuma ranar da zan yi arbain din zan wuce Dutainma, mun yi wankan safe Haj ta goya Areef ta ce in goya Mimi, in sa lullubina in biyo ta, fita muka yi daga gidan wata mota da ban san sa’adda ta kira me ita ba muka shiga, tafiya sosai muka yi zuwa wani kauyen fulani, ya sauke mu muka shiga rigar Haj ta ce ya jira mu. Sai lale ake mana aka yi mana shimfida, sai fillanci suke da Haj, aka kawo mana nono kindirmo, ni dai da ban iya shan shi haka ba, sai ban sha ba. Wani dogon bafulatani aka kira, a fuska yana kama da Haj, faraa sosai yake ganin Hajiyar suka gaisa cikin fulatanci ni kuma na gaishe shi da Hausa.
Daga yanda suke kallona na gane maganar ta shafe ni. Ta kwance goyon da ke bayanta ta mika mishi ni ma ta ce in yi yanda tayi. Sai duban yaran yake yana murmushi magana ya fara min ganin ina nonnokewa ya ce “Ki saki jikinki ki saba da ni, ni kane ne wurin Haj, kakanninmu daya” murmushi nayi sai na sunkuyar da kaina, wata da nake kyautata zaton matarsa ce ya kira ta iso cikin sauri magana ya yi mata ta amsa sai ta juya sai ga ta ta dawo dauke da wata kwarya ta ajiye gaban sa wasu sake saki ya ciro ya miko min, “Ki wanke wannan sai ki jika ku rika sha da yaranki, kar ki wasa” na karba ina ta mishi godiya wasu ya ciro “Wannan kuma dafawa za ki yi kuna sha shi ma ke da yaranki” Haj ta mike za ta kewaya sai da ya bi ta da kallo ya ga shigewar ta kafin ya ciro wata kwalba ita ma sake sakin ne a cikinta “Ki zuba turare kalar wanda kike so ki shafa ya yin tafiyar ki wurin me gida, in sha Allah za ki yi godiya ba kowa nake ba shi ba, amma ke saboda yanda Haj ta fada min halayyarki da muamalarki shi yasa na ga ya kamata in taimaka miki” Zagewa nayi sosai na shiga mishi godiya. Haj ta dawo na ce “Me zan bayar sadaka? Ta ce “Abin da Allah ya hore, dan bayar da sadakar yana da kyau” yan dari biyar na ciro na ajiye gaban sa, amma sai ya yi murmushi ya dauki daya. Wata mata me tsananin kamanni da shi ta shigo, fara’a sosai ta shiga yi ganin Haj ta zauna aka gaggaisa ita kam hausa ce a bakinta radam. Haj ta ce “Yaushe kika dawo? Dan’uwanta da na lakanci Baffa ake kiransa ya ce “Ga ta nan ta dawo bata iya cimar mu” Haj ta ce “Allah sarki” ta dauki yan biyu Haj ta ce mata yaran Sodangi ne ta ce “Shi bana Sodangi ya ga kwansa mu ne dai ni da Yaya Atta ba mu samu ba” ta ce “Kuma Allah bai manta da ku ba ta” Ta goya Mimi ta saba Areef ta fita Haj ta bi ta da kallo kafin ta juyo wurin dan’uwanta “Ko Wodile za ta gidan Sodangi ta taya Ummulkhairi kula da yaran nan? Daga ita din me son yara ce, kuma za ta samu cimar birni da ta saba da ita, Ummulkhairi bata da matsala, haka ita ma wodilen” Kira ya kwala wa yar’uwar tasa sai ga ta ya yi mata bayani ta ce “Ita bata da damuwa za ta je. Ya ce a kira Sodangin a gaya mishi, murmushi Haj tayi “Kar ka damu daga dai Wodilen ta amince zan gaya mishi. Sai da muka mike za mu tafi Haj ta sa a ka bude boot buhun shinkafa ne da kwalin taliya da na makaroni sai sabulai na wanka da na wanki da omo. Yaran gidan suka kwashe zuwa ciki sai muka kamo hanya. Mun yi nisa Haj take ban labari “Wannan kanwar Baffa ce, a Abuja tayi aure tana auren me gadin wani kusan gwamnati, Allah bai bata haihuwa ba, ga shi mijin Allah ya yi mishi rasuwa, na zaba miki ita, Ummulkhairi mace ce me kirki da zumunci, za ki ji dadin zama da ita, tana da son yara ga tsafta.
Sai da na kara sati guda na tafi Dutsinma dan Haj ta ce sai mun sha maganin nan kar in je can in watsar. Murna sosai gidan mu suka yi da gani na. Mun sha biki har guda biyu rawa sosai na taka a wurin bikin dan ni ma yanzu ko Tahir bai bani ba ina da abin da zan yi hidima, Akwati na hada wa yayana mustafa, Yaya Maimuna kuma na saya ma yarinyar ta kayan kitchen, nayi ma iyayena alheri da sauran yan’uwana, hada Hafsa da tilon yarta. Na koma Kankara Tahir ya yi wa Haj maganar komawa ta ta ce ya bata nan da sati guda, sai tayi mishi maganar Wodile wadda na ji su Hadiza na ce wa Daada, sai ya ce zai yi magana da Hajiyar tudunwada ta ba shi Hassana ko Hussaina daga yasan ba za ta yarda ta rabu da yaran duka ba sai su taya ni kula da yaran dan Hadiza muna dawowa makaranta zai mayar da ita. Shiri sosai Ummata tayi na komawata mutum biyu aka tado da za su yi min rakiya Matar yayana sai Yayata Aunty Wasila, anan gidan su Tahir Maman Ummi ce sai Uwargidan Babban Yaya, motar da Tahir ya turo ba za ta ishe mu ba sai da aka hada da motar babban yaron Yaya babba, motar Tahir ne ya yi mishi kyautarta. Karfe goma na safe muka kamo hanya
Mun shiga ba mu samu kowa a falon gidan ba Hadiza ta bude dakina bata kuma zauna ba ta soma gyaran wuri, duk wata kura suka goge ta ita da Mmn Ummi suna shirin shiga kitchen sai ga sakon abinci daga Asiya dan su laraba dama sun ce basu san da dawowar mu yau ba, Tahir ma baya nan sai gobe zai shigo. Nan kowa ya ci ya koshi, sai dare matan suka dawo kuma a tsaitsaye suka leko a ka gaisa Basma ma da ke gidan sai washegari muka sa ta ido. Gari na wayewa suka soma shirin tafiya duk da jin da nake kamar kar su tafi, Ko da basu ga Tahir ba sakonsa ya iske su. Na samu Daada mace me kwazo da tsafta ga juriyar dawainiyar yara dan haka na samu saukin goyon. Ni zan yi girki dan haka zagewa muka yi muka gyara gidan hada su laraba, na gyaro wurinsa abinci da na san yana so nayi mishi nayi kwalliya sosai cikar da nayi tun ta haihuwa tana nan har yanzu nayi dam dam, nayi mamakin ganin matan su uku suna maganar da tayi kama da ta sirri, a sanin da nayi su biyu ke irin wannan zaman Halima DA Latifa to yau har da Basma, na ji ba dadi dan ba yarda za a yi ka ji dadi idan aka ware ka, amma sai na kama addua nayi tayi har na samu na manta da lamarin su,na ci gaba da sabgata.
Yamma sosai Tahir ya shigo, ya zauna a falo yana makale da yaran idan ya dauki wannan sai ya ajiye ya dau wannan ya kasa daina fadin girman su, da wayon da ya ga sun yi masa. Har daki ya shiga suka gaisa sosai da Daada. Da daddare cikin tsoro na shirya zuwa turaka dan ina ganin yara har biyu gare ni ya kamata a daga min kafa, har su kara wayo damma sauki na daya ba su kukan dare, gaba daya ma basu da rigima. Daada nake jin kunya da wuri ta shige dakina dayan da na bar mata, ni kuma mu zauna da Hadiza. Mimi na saba a kafada na wuce, yana zaune daga shi sai guntun farin wando black tea da na kawo mishi yake kurba a hankali idonsa na kan TV yana kallon labarai a tashar CNN a gefe na ajiye ta na koma dauko Areef ina dawowa na samu Mimi tana kuka abin da bata cika yi ba. Na ajiye Areef na zare dogon hijab din da na dora saman rigar da na sa yar yala yala ce me hannun shimi iyakarta gwiwa na zauna ina bata nono Areef ma ya tashi ya fara kuka duk sai na rikice ya dora min shi ya zauna daf da ni ya hade jikinsa da nawa yana rada min maganganun da suka sa na rufe ido, ba su jima ba suka koma na kwantar da su gefe daya. Ina waiwayowa ya jani zuwa gado, al’amuran da suka faru a wannan dare masu tsayawa a rai ne, dan sambatun da Tahir ya rika yi na san idan haka nan ne ba zai taba yarda ya furta min su ba. Yana tafiya sallar Asuba na gudu dakina wanka nayi da ruwa me dumi na gasa jikina, na idar da sallah ina azkar ya shigo sai da ya leka Daada suka gaisa sai ya shigo jikin gado na boye fuskata dan samun kaina nayi ina jin kunyarsa. Ya leka yaran da ke ta barci sai ya fita ya koma saman sa.
Karfe tara ya tasa ni wurin rumfar ajiye motoci bayan na shigarsa guda biyu, akwai na Basma su ma biyu sai ta Hali dubu, wasu kuma sababbi na gani dal guda biyu fara da baka ya ce “Zabi daya” kallonsa nayi sai ya dage min gira na ce “Wai hidima bata yi maka yawa? Kafadarsa ya noke “Daga Allah ya hore meye amfanin su? anan inda ka same su nan za ka bar su” Na gyada kai sai na shiga godiya katse ni ya yi “Kin fi karfin komai da nake da shi Ummulkhairi, dama na yi deposit na motocin na ku, haukan da Latifa tayi min yasa na fasa saye sai wata shekarar, amma giyar dare da aka shayar da ni tilas in bada tukuici” sunkuyar da kaina nayi duk kuma maganar da yake ban dago ba. “Ki zaba ” ya maimaita, farar na nuna ya kwantar da kansa jikin motar yana min wani irin kallo “Mu maza wadda zuciyar mu ta kwallafa ita take son kasancewa da ita idan ba ita din muka samu ba ko me za mu samu ba ma gamsuwa nayi kewarki Ummuna” ban ce komai ba sai hanya da na kama ina tafiya a raina ina saka ni fa tsorona Allah tsorona munafuncin maza, su yi ta zura ka kai kuma kana hauka kana ce gaske ne, duk da dai Tahir ba mai fade fade bane amma daga daren jiya na rasa abin da ya hau kansa. “To jira ni mana” na ji muryarsa a bayana kin tsayawa nayi ido muka hada da Halima wadda ke fitowa a lokacin ina zuwa inda take na ce mata ina kwana sai na wuce ciki.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *Na kudi ne biya 300 a 2108124716* *Maryam Nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya 07033400612*

Ya same mu ni da Tahir da Halima ya mika wa Tahir foam din, sai da ya karba ya ce “Nawa ne? ban samu shigowa ba” kansa ya shiga sosawa “Ba sai an bayar ba ranka ya dade, a dai taimaka min in yi komai na shigar ta makarantar” murmushi Tahir ya yi ya ce in kira mishi Hadiza. Mun dawo tare da ita Areef na kafadarta Tahir ya ce ta miko shi “To ke Hadiza Kamal ya sawo miki foam yana roko ya yi hidimar makarantar taki, ki yi mishi godiya”. Kamar tana ciwon hakori ta ce “Na gode” ta tashi ta koma ciki Halima ta mike tana cika tana batsewa “Kai yanzu Kamal dan karshen rashin zuciya har ka kara duban yarinyar nan? Ta wuce fuu! ta shige dakinta ta banko kofa, cikin sauri ya tashi ya bi ta yana shiga ya same ta tana huci, ai kuwa tana ganin sa tayi kansa da masifa “In ban da ba ka san ciwon kanka ba me za ka yi da wannan yarinyar? Sai yanzu na gane dalilin dawowarka garin nan, saboda ita ne ko? tun da ta dawo gidan nan ban taba kallonta ba saboda abin da tayi maka amma saboda kare ya cinye zuciyarkahar ka dawo mata” Jin ta numfasa ya ce “Hakuri kawai za ki yi Aunty, ban san inda zan kai son da nake mata ba nayi nayi in yakice ta cikin raina amma hakan ya faskara, ki yi min addu’a kawai” Tsaki ta ja “Kana saurayi ka rasa wa za ka aura sai bazawara dan ci baya sai ka ce ita kadai ce mace, ni ban ga wata tsiya da take da shi ba da ka ki aure tun gudunka da tayi ka zauna karatu” murmushin takaici ya yi ” Haba dai Aunty kya ce ba ki ga tsiyar da na gani ba, kamar ta daya fa da mijinki, kuma ke ma haka kika kafa zaman jiransa, kila dai mu jininmu ne haka. Sake ya bar ta da baki jin maganar da ya yaba mata. Ya samu Tahir a inda ya bar shi, sun kara tattaunawa game da makarantar ta Hadiza sai ya mishi sallama ya bar gidan.
Tun daga ranar ya maida gidan gidan zuwan sa, zai dauki yan biyu ya yi ta wasa da su amma ko sau daya wadda yake zuwa dan ita bata taba gwada ta san da zaman sa ba. Har dai na gaji wata rana ya zo ya tafi duk dadewar da ya yi bata sa ya ga ko gilminta ba tana bed room tana barci, har kuma falona a ranar sai da ya shiga duka na dada mata a kafa ta tashi tana sosa wurin “Lafiya Aunty? Me yasa kike abin da kike yi din? Kallon rashin fahimta tayi min “Ni kuma me nayi? Harara na bata “Saboda Allah abin da kike wa bawan Allan nan haka ya dace kayi wa wanda ke kaunarka? Murmushin yake tayi “Ni kam me zan ce mishi? Ni ban ma so dawowar sa gare ni ba, domin ban cancanci hakan ba, ban ma da idon da zan daga in dube shi” “Kuma ba shi zai sa ki ki ba shi fuska ba, ni ina ce ma godiya za ki yi wa Ubangiji da ya ba ki me tsananin son ki haka” shiru tayi kafin ta mike ta shiga wanka, sanda ta fito muna zaune da Daada a falona ina ba Mimi nono, Areef na bayan Daada, zama tayi tana sauraren mu dan labari nake ba Daada muka hadu da Daada muna ta bata shawara karshe ta ce ta amince. Yana zuwa kuma a washegari ya aiko Hussaina wai yana son magana da ni wadda Tahir ya dauko da muka je tudun wada na ce ya shigo sai ga shi da sallamar sa mun gaisa yana rike da Areef ya ce “Wani taimako nake nema a wurin ki Maman yan biyu ” dan jim nayi kafin na ce “To Allah ya bani ikon taimakawa” ya ce “Khadija nake so ki yi wa magana tayi hakuri ta bani dama” Jin ya yi shiru na ce “Ba damuwa zan yi mata” ya mike yana min godiya. Yana kara zuwa kuma na shaida mishi ya mata magana a falona suka yi zancen ni da Daada muka fita can harabar gidan wurin rumfar shan iska. Halima dai bata nan dan wannan karon tafiyar ta ne, Basma kuma ta je Abuja ganin iyayenta, dama na ji Latifa na yi da ita Mata kamar mara hankali idan ta zauna bata taba sanin ya kamata ta je ta ga iyayenta ba, idan ta tafi kuma bata san ta dawo ba, shi kuma mijin da ba damuwa ya yi da ita ba, bai taba cewa ta dawo sai ta gaji. Dan haka wannan zuwan ma nike da shi tafiyar ma ni zan yi ta wadda nake ta tunanin yanda za ta kasance min ina fama da yan biyu, to na dai yi shiru in ga me ogan zai ce. Daren da ya zo muna kwance cikin dare bayan mun gama soyayyarmu, hannunsa na cikin gashina yana yamutsawa, “Na fa ajiye aikina Ummulkhairi. Saurin raba jikina nayi da na shi na tashi zaune kamo ni ya yi ya maida “Saboda me za ka yi haka dan Allah? Akwai alheri a cikin aikin nan, me zai sa ka ajiye” Aikin nan ya nesanta ni da iyalina, na gaji da shi kasuwancina kara bunkasa yake a kullun, gidajen mai guda biyu zan bude ina ganin za su ishe ni rayuwa. Addu’o’i na shiga jera mishi kafin muka shiga barci.
Washegari Hadiza ta soma zuwa makaranta. Ban yi wanka da wuri ba sai da aka gama karyawa, ina gaban mirror ina kwalliya na ji muryarsa suna gaisawa da Daada labulai ya daga na dago na dube shi “In kin gama shiryawa ki same ni mota, ba sai kin dauko yara ba. Kai na daga mishi na gama zura kaya na fito na ce ma Daada za mu dan fita ta ce “A dawo lafiya” Kan bonet din motata na gan shi ina karasawa ya ce “Koma ki dauko keyn” na juya sai na dawo dauke da shi ya shiga ya yi mata key, na bude na zauna a gefensa. Filin koya mota muka je ya gama min bayani sai dai ina rike sitiyarin ya ce “Anya na yarda ba ki iya tuki ba? Murmushi nayi masa “Aunty Laila ta soma koya min a Lagos, sai dai a tunanina na manta. Mun dade a wurin kafin ya ce mu je gida, hancin motar na shiga cikin gidan Hadiza na fitowa daga motar kamal, kallo daya ya yi masu ya fita ya nufi masallaci shi ma Kamal din jirana ya yi na karaso muka gaisa ya fada motarsa dan barin wurin. Tare muka shiga da Hadiza, Halima da muka gani tsaye tana huci Latifa kuma na zaune kan kujera, kan Hadiza tayo
“Ke yarinya ki kiyayi kanki ki kuma kama kan naki ki fita rayuwar kanena, dan ba abin da zai yi da bazawara yana saurayi” wani kallon banza Hadiza tayi mata “Ai sai ki fara fada ma kanen naki ya rabu da ni, ba ni za ki zo kina ma gayyar hakori a ka ba” “Ai wallahi ya ci baya ya aure ki, dan ba zan taba bari hakan ta faru ba” Wata shewa Hadiza tayi “Ai wallahi kuskure kato kika tafka da kika nuna min ba ki so, da kin yi wayo da ba ki bari na gane ba ki so ba, dan wallahi na saurari Kamal ne dan wadanda nake gani da daraja sun roke ni kan hakan, amma wallahi tun da kika nuna min bakin cikin ki a fili sai na auri Kamal kika ga hakan bai kasance ba to ki kaddara Allah ne bai yi ba, amma ba wani kulunbotonki ba”. Shigowar Tahir sai Halima ta saka kuka ta nufi wurinsa tana fadin an sanya Hadiza tana mata rashin kunya tana zaginta, har tana ce mata mara wayau” “Ki dai ji tsoron Allah a ina na zage ki? Hadiza ta fadi “Ki yi min shiru! Tahir ya fadi ma Hadiza cikin daka tsawa ya haye saman shi Halima ta take mishi bay. Muna zaune har mun manta sa’insar Hadiza da Halima sai ga Tahir ranshi a hade, fada sosai ya yi wa Hadiza kan abin da tayi wa halima ni kuma ya ce min bai kamata ina goya wa Hadiza baya tana ma wani rashin kunya a gidan nan ba. Na bude ido “Ni kuma? Magana dai ai ta Kamal ce da bata son sa da Hadiza, mun shigo dazu sai ta tare ta, ni me na ce? Gyada kansa ya yi sai ya fice.
Latifa ta iske Halima dakinta. Wani irin shiri suke a yanzu wanda ta kai har hada sirri suke, Halimar ta dube ta “Wai kuwa anya na yarda da ke ba abin da ke faruwa tsakanin sa da Ummulkhairi kina ganin yanda yake wani nan nan da ita, tsaki Latifa ta ja “Ni ma na fara shakkar abin, ina ganin sai mun hada hannu ko za mu yaki yarinyar nan, ki bari Basma ta dawo” wani mummunan tsaki Halima ta ja “Dan Allah kina maganar mutane ki bar sa wannan, in za mu yi abin mu mu yi kawai” kiran da ya shigo wayar Latifa yasa ta mikewa tana amsawa sai ta bar dakin.
A daren ranar Har Tahir ya fito cin abinci Latifa me girki bata fito ba, tsaki ya ja bayan ya zauna dan fita yake son yi, a waya ya kira ta shiru bata fito ba bayan ta ce ga ta nan zuwa, kara kiranta ya yi Latifa da ke dakinta tana laluben glashinta da ya subuce dan yanzu an kai da magrib tayi in har ba glass din bata gani, tsoron fushin Tahir yasa ta laluba hanya tana fitowa dan tana so ta ce mishi bata ga glass dinta ba, ya kashe wayar. Kowa ya hallara ana jiran me girki fitowar da tayi tana laluben hanya ya sa hankalin kowa ya koma kanta, Tahir ya ja tsaki “, Meye haka? Ta ce “Glass dina ne ban gani ba” wai sai ga mutumniyarta Halima na dariya kasa kasa, wani kallo Tahir ya mata ta gintse dariyar tana kauda kai. Halimar yasa ta je dakinta ta nemo mata glass din ta dawo dauke da shi a hannu tana dariya “Ke malama makauniya ai glass din da ka shiga yake” latifa ta zaburo jin Halima ta kira ta makauniya, nan suka kama bala’i Tahir bai ce musu uffan ba tsaki ya ja ya bar gida.
Zuwa safiya sun shirya radam dan Latifa bata da ruko da kanta ta nemo Halima Tahir kuma ya tattara su ya yi Asibiti da su Latifa kan matsalar idonta, Halima kuma wai tana jin motsi a cikinta. Latifa aka fara dubawa, sai ya koma inda Halima take ganin nata likitan scanning ya yi mata nan take kuma ya tabbatar musu da zatgin da yake na ciki a jikin Halima har ma ya soma kwari daga ita har Tahir kamar su ki yarda ya ce su je Asibitin Dr Muhammad ta ce “A’a su dai je wani wurin shi ma ba tare da latifa ba, ta roke shi kar ya fadi ma kowa. Sun taho bisa hanya ta fadi tana son Maltina latifa kuma ta ce tana son pad wani super market da ke bisa hanyar tasu ya yi shawarar tsayawa cewa ya yi su zauna ya shiga ya fito yana shigewa Halima ta hango wata mata tsaye rike da jaka Latifa take nuna ma ita “Kin ga waccan matar? Matar abokin Tahir ce kawata ce sosai, sai mijin ya nuna yana son wata kanwata mafarin watsewar kawancen namu, kuma abin haushi da auren yar’uwar tawa ko shekara ba a yi ba ya watse, dan Haj Shema’u Shu’uma ce shiyasa wata ran da na tuna ta sai in ga da muna tare da tuni ta yi mana maganin shegiyar yarinyar nan”. Latifa ta ce “Dan Allah? To mu kirata mana” Halima ta kara duban inda take tsaye kamar tana jiran wani “Anya za ta yarda? Sosai fa ta ji zafin abin nan” “Ke dai dan Allah mu je mu same ta” suka balle murfin motar suka fita zuwa inda take, ga mamakin su da fara’arta ta tare su suka gaggaisa ta tambayi Tahir Halima ta tambayi Engineer ta ce sun rabu shekaru biyu da suka wuce. Su Halima suka jajanta tare da tambayarta inda take a yanzu ta ce tudunwada sun yi musayar lambar waya suka rabu da alkawarin ziyartar juna. Sun koma inda motar take Halima tana kallon wani kayataccen shagon dinki da aka rubuta Ummulkhairi fashion design ta taba Latifa “Ke kin ga wani hadadden wurin dinki latifa ta kalla suka ci gaba da yaba kyawun wurin da irin dinkunan da suka gani har Tahir ya fito yaran shagon na rike mishi da kayan da ya saya motar ya shiga yaron ya sa mishi kayan a boot. Har ya ja motar yana jin matan suna santin wurin dinkin da zancen za su kawo dinki. Sai da ya juya ya dubi wurin kafin ya ce “Ai ta kwana gidan sauki dan yaruwarku ce me wurin” har suna hada baki wurin fadin wace yar’uwar tamu kafin kwakwalensu su tuna musu sunan wurin
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *Na kudi ne biya 300 a 2108124716* *Maryam Nasir UBA bank*
*Dan nuna shaidar biya 07033400612*

Ya same mu ni da Tahir da Halima ya mika wa Tahir foam din, sai da ya karba ya ce “Nawa ne? ban samu shigowa ba” kansa ya shiga sosawa “Ba sai an bayar ba ranka ya dade, a dai taimaka min in yi komai na shigar ta makarantar” murmushi Tahir ya yi ya ce in kira mishi Hadiza. Mun dawo tare da ita Areef na kafadarta Tahir ya ce ta miko shi “To ke Hadiza Kamal ya sawo miki foam yana roko ya yi hidimar makarantar taki, ki yi mishi godiya”. Kamar tana ciwon hakori ta ce “Na gode” ta tashi ta koma ciki Halima ta mike tana cika tana batsewa “Kai yanzu Kamal dan karshen rashin zuciya har ka kara duban yarinyar nan? Ta wuce fuu! ta shige dakinta ta banko kofa, cikin sauri ya tashi ya bi ta yana shiga ya same ta tana huci, ai kuwa tana ganin sa tayi kansa da masifa “In ban da ba ka san ciwon kanka ba me za ka yi da wannan yarinyar? Sai yanzu na gane dalilin dawowarka garin nan, saboda ita ne ko? tun da ta dawo gidan nan ban taba kallonta ba saboda abin da tayi maka amma saboda kare ya cinye zuciyarkahar ka dawo mata” Jin ta numfasa ya ce “Hakuri kawai za ki yi Aunty, ban san inda zan kai son da nake mata ba nayi nayi in yakice ta cikin raina amma hakan ya faskara, ki yi min addu’a kawai” Tsaki ta ja “Kana saurayi ka rasa wa za ka aura sai bazawara dan ci baya sai ka ce ita kadai ce mace, ni ban ga wata tsiya da take da shi ba da ka ki aure tun gudunka da tayi ka zauna karatu” murmushin takaici ya yi ” Haba dai Aunty kya ce ba ki ga tsiyar da na gani ba, kamar ta daya fa da mijinki, kuma ke ma haka kika kafa zaman jiransa, kila dai mu jininmu ne haka. Yana gama fadi ya juya sai ya bar dakin. Sake ya bar ta da baki jin maganar da ya gasa mata. Ya samu Tahir a inda ya bar shi, sun kara tattaunawa game da makarantar ta Hadiza sai ya mishi sallama ya bar gidan.
Tun daga ranar ya maida gidan gidan zuwan sa, zai dauki yan biyu ya yi ta wasa da su amma ko sau daya wadda yake zuwa dan ita bata taba gwada ta san da zaman sa ba. Har dai na gaji wata rana ya zo ya tafi duk dadewar da ya yi bata sa ya ga ko gilminta ba tana bed room tana barci, har kuma falona a ranar sai da ya shiga duka na dada mata a kafa ta tashi tana sosa wurin “Lafiya Aunty? Me yasa kike abin da kike yi din? Kallon rashin fahimta tayi min “Ni kuma me nayi? Harara na bata “Saboda Allah abin da kike wa bawan Allan nan haka ya dace kayi wa wanda ke kaunarka? Murmushin yake tayi “Ni kam me zan ce mishi? Ni ban ma so dawowar sa gare ni ba, domin ban cancanci hakan ba, ban ma da idon da zan daga in dube shi” “Kuma ba shi zai sa ki ki ba shi fuska ba, ni ina ce ma godiya za ki yi wa Ubangiji da ya ba ki me tsananin son ki haka” shiru tayi kafin ta mike ta shiga wanka, sanda ta fito muna zaune da Daada a falona ina ba Mimi nono, Areef na bayan Daada, zama tayi tana sauraren mu dan labari nake ba Daada muka hadu da Daada muna ta bata shawara karshe ta ce ta amince. Yana zuwa kuma a washegari ya aiko Hussaina wai yana son magana da ni wadda Tahir ya dauko da muka je tudun wada na ce ya shigo sai ga shi da sallamar sa mun gaisa yana rike da Areef ya ce “Wani taimako nake nema a wurin ki Maman yan biyu ” dan jim nayi kafin na ce “To Allah ya bani ikon taimakawa” ya ce “Khadija nake so ki yi wa magana tayi hakuri ta bani dama” Jin ya yi shiru na ce “Ba damuwa zan yi mata” ya mike yana min godiya. Yana kara zuwa kuma na shaida mishi ya mata magana a falona suka yi zancen ni da Daada muka fita can harabar gidan wurin rumfar shan iska. Halima dai bata nan dan wannan karon tafiyar ta ne, Basma kuma ta je Abuja ganin iyayenta, dama na ji Latifa na yi da ita Mata kamar mara hankali idan ta zauna bata taba sanin ya kamata ta je ta ga iyayenta ba, idan ta tafi kuma bata san ta dawo ba, shi kuma mijin da ba damuwa ya yi da ita ba, bai taba cewa ta dawo sai ta gaji. Dan haka wannan zuwan ma nike da shi tafiyar ma ni zan yi ta wadda nake ta tunanin yanda za ta kasance min ina fama da yan biyu, to na dai yi shiru in ga me ogan zai ce. Daren da ya zo muna kwance cikin dare bayan mun gama soyayyarmu, hannunsa na cikin gashina yana yamutsawa, “Na fa ajiye aikina Ummulkhairi. Saurin raba jikina nayi da na shi na tashi zaune kamo ni ya yi ya maida “Saboda me za ka yi haka dan Allah? Akwai alheri a cikin aikin nan, me zai sa ka ajiye” Aikin nan ya nesanta ni da iyalina, na gaji da shi kasuwancina kara bunkasa yake a kullun, gidajen mai guda biyu zan bude ina ganin za su ishe ni rayuwa. Addu’o’i na shiga jera mishi kafin muka shiga barci.
Washegari Hadiza ta soma zuwa makaranta. Ban yi wanka da wuri ba sai da aka gama karyawa, ina gaban mirror ina kwalliya na ji muryarsa suna gaisawa da Daada labulai ya daga na dago na dube shi “In kin gama shiryawa ki same ni mota, ba sai kin dauko yara ba. Kai na daga mishi na gama zura kaya na fito na ce ma Daada za mu dan fita ta ce “A dawo lafiya” Kan bonet din motata na gan shi ina karasawa ya ce “Koma ki dauko keyn” na juya sai na dawo dauke da shi ya shiga ya yi mata key, na bude na zauna a gefensa. Filin koya mota muka je ya gama min bayani sai dai ina rike sitiyarin ya ce “Anya na yarda ba ki iya tuki ba? Murmushi nayi masa “Aunty Laila ta soma koya min a Lagos, sai dai a tunanina na manta. Mun dade a wurin kafin ya ce mu je gida, hancin motar na shiga cikin gidan Hadiza na fitowa daga motar kamal, kallo daya ya yi masu ya fita ya nufi masallaci shi ma Kamal din jirana ya yi na karaso muka gaisa ya fada motarsa dan barin wurin. Tare muka shiga da Hadiza, Halima da muka gani tsaye tana huci Latifa kuma na zaune kan kujera, kan Hadiza tayo
“Ke yarinya ki kiyayi kanki ki kuma kama kan naki ki fita rayuwar kanena, dan ba abin da zai yi da bazawara yana saurayi” wani kallon banza Hadiza tayi mata “Ai sai ki fara fada ma kanen naki ya rabu da ni, ba ni za ki zo kina ma gayyar hakori a ka ba” “Ai wallahi ya ci baya ya aure ki, dan ba zan taba bari hakan ta faru ba” Wata shewa Hadiza tayi “Ai wallahi kuskure kato kika tafka da kika nuna min ba ki so, da kin yi wayo da ba ki bari na gane ba ki so ba, dan wallahi na saurari Kamal ne dan wadanda nake gani da daraja sun roke ni kan hakan, amma wallahi tun da kika nuna min bakin cikin ki a fili sai na auri Kamal kika ga hakan bai kasance ba to ki kaddara Allah ne bai yi ba, amma ba wani kulunbotonki ba”. Shigowar Tahir sai Halima ta saka kuka ta nufi wurinsa tana fadin an sanya Hadiza tana mata rashin kunya tana zaginta, har tana ce mata mara wayau” “Ki dai ji tsoron Allah a ina na zage ki? Hadiza ta fadi “Ki yi min shiru! Tahir ya fadi ma Hadiza cikin daka tsawa ya haye saman shi Halima ta take mishi bay. Muna zaune har mun manta sa’insar Hadiza da Halima sai ga Tahir ranshi a hade, fada sosai ya yi wa Hadiza kan abin da tayi wa halima ni kuma ya ce min bai kamata ina goya wa Hadiza baya tana ma wani rashin kunya a gidan nan ba. Na bude ido “Ni kuma? Magana dai ai ta Kamal ce da bata son sa da Hadiza, mun shigo dazu sai ta tare ta, ni me na ce? Gyada kansa ya yi sai ya fice.
Latifa ta iske Halima dakinta. Wani irin shiri suke a yanzu wanda ta kai har hada sirri suke, Halimar ta dube ta “Wai kuwa anya na yarda da ke ba abin da ke faruwa tsakanin sa da Ummulkhairi kina ganin yanda yake wani nan nan da ita, tsaki Latifa ta ja “Ni ma na fara shakkar abin, ina ganin sai mun hada hannu ko za mu yaki yarinyar nan, ki bari Basma ta dawo” wani mummunan tsaki Halima ta ja “Dan Allah kina maganar mutane ki bar sa wannan, in za mu yi abin mu mu yi kawai” kiran da ya shigo wayar Latifa yasa ta mikewa tana amsawa sai ta bar dakin.
A daren ranar Har Tahir ya fito cin abinci Latifa me girki bata fito ba, tsaki ya ja bayan ya zauna dan fita yake son yi, a waya ya kira ta shiru bata fito ba bayan ta ce ga ta nan zuwa, kara kiranta ya yi Latifa da ke dakinta tana laluben glashinta da ya subuce dan yanzu an kai da magrib tayi in har ba glass din bata gani, tsoron fushin Tahir yasa ta laluba hanya tana fitowa dan tana so ta ce mishi bata ga glass dinta ba, ya kashe wayar. Kowa ya hallara ana jiran me girki fitowar da tayi tana laluben hanya ya sa hankalin kowa ya koma kanta, Tahir ya ja tsaki “, Meye haka? Ta ce “Glass dina ne ban gani ba” wai sai ga mutumniyarta Halima na dariya kasa kasa, wani kallo Tahir ya mata ta gintse dariyar tana kauda kai. Halimar yasa ta je dakinta ta nemo mata glass din ta dawo dauke da shi a hannu tana dariya “Ke malama makauniya ai glass din da ka shiga yake” latifa ta zaburo jin Halima ta kira ta makauniya, nan suka kama bala’i Tahir bai ce musu uffan ba tsaki ya ja ya bar gida.
Zuwa safiya sun shirya radam dan Latifa bata da ruko da kanta ta nemo Halima Tahir kuma ya tattara su ya yi Asibiti da su Latifa kan matsalar idonta, Halima kuma wai tana jin motsi a cikinta. Latifa aka fara dubawa, sai ya koma inda Halima take ganin nata likitan scanning ya yi mata nan take kuma ya tabbatar musu da zatgin da yake na ciki a jikin Halima har ma ya soma kwari daga ita har Tahir kamar su ki yarda ya ce su je Asibitin Dr Muhammad ta ce “A’a su dai je wani wurin shi ma ba tare da latifa ba, ta roke shi kar ya fadi ma kowa. Sun taho bisa hanya ta fadi tana son Maltina latifa kuma ta ce tana son pad wani super market da ke bisa hanyar tasu ya yi shawarar tsayawa cewa ya yi su zauna ya shiga ya fito yana shigewa Halima ta hango wata mata tsaye rike da jaka Latifa take nuna ma ita “Kin ga waccan matar? Matar abokin Tahir ce kawata ce sosai, sai mijin ya nuna yana son wata kanwata mafarin watsewar kawancen namu, kuma abin haushi da auren yar’uwar tawa ko shekara ba a yi ba ya watse, dan Haj Shema’u Shu’uma ce shiyasa wata ran da na tuna ta sai in ga da muna tare da tuni ta yi mana maganin shegiyar yarinyar nan”. Latifa ta ce “Dan Allah? To mu kirata mana” Halima ta kara duban inda take tsaye kamar tana jiran wani “Anya za ta yarda? Sosai fa ta ji zafin abin nan” “Ke dai dan Allah mu je mu same ta” suka balle murfin motar suka fita zuwa inda take, ga mamakin su da fara’arta ta tare su suka gaggaisa ta tambayi Tahir Halima ta tambayi Engineer ta ce sun rabu shekaru biyu da suka wuce. Su Halima suka jajanta tare da tambayarta inda take a yanzu ta ce tudunwada sun yi musayar lambar waya suka rabu da alkawarin ziyartar juna. Sun koma inda motar take Halima tana kallon wani kayataccen shagon dinki da aka rubuta Ummulkhairi fashion design ta taba Latifa “Ke kin ga wani hadadden wurin dinki latifa ta kalla suka ci gaba da yaba kyawun wurin da irin dinkunan da suka gani har Tahir ya fito yaran shagon na rike mishi da kayan da ya saya motar ya shiga yaron ya sa mishi kayan a boot. Har ya ja motar yana jin matan suna santin wurin dinkin da zancen za su kawo dinki. Sai da ya juya ya dubi wurin kafin ya ce “Ai ta kwana gidan sauki dan yaruwarku ce me wurin” har suna hada baki wurin fadin wace yar’uwar tamu kafin kwakwalensu su tuna musu sunan wurin
5/12/22, 13:33 – Buhainat: *Yan’uwa barkan mu da sallah Allah ya karba mana yasa mun yi ibada karbabba*
*Na kudi ne biya a 2108124716 Maryam nasir UBA bank* *dan nuna shaidar biya 07033400612*

“Wace yar’uwar tamu? Halima ta tambaye shi. Shiru ya mata sai ma wayarsa da ya zaro ya soma amsa kira har kuma suka isa gida bai ajiye wayar ba ballantana su samu damar tambayarsa yana kuma ajiye su juya kan motar ya yi bai ko shiga ba.

An yi haka da kwana biyu da rana na fito kitchen, na ji ana knocking komawa nayi na bude, kallo daya na gane matar duk kuwa da cewa sau daya na taba ganin ta ga dadewa da aka yi tunda na gan tan ko da yake abin da ya taimaka min wurin gane ta bai wuce hoton ta da na dade ina gani a Dp dinta na WhatsApp dan na dade ina da lambarta kafin rashin ji daga gare ta yasa na gogeta.
Ba wata ba ce illa Haj Shema’u da ta taba zuwa har ta bani maganin mata farko farkon zuwa na Kaduna. Murmushi nayi mata “Sannu da zuwa Haj”. Ita ma murmushin tayi min “Yawwa kamar Amaryar Kankara ko? Kai na daga mata “Ikon Allah kin canza kamar ba ke ba, ya kwana biyu? Na ce “Sai alheri, ki shigo mana” na fadi ina bata hanya sai da ta zauna na kawo mata lemon da cincin din da nayi ta tambaye ni Halima fa? Sai da na duba motarta na ga tana nan sannan na ce “Kin yi sa’a tana nan ta dawo” mikewa tayi na nuna mata kwanar da kofarta take dan na ga kamar ta manta.

Da kallon mamaki tayi ta bin Halima ganin katon cikin da ke gabanta. “Ikon Allah, Halima ke ce da ciki? Murmushi tayi “Ai kuwa dai kin gani” labari suka shiga tana bata labarin kishiyoyin da aka yi mata da yanda take neman hanyar da za ta wargaza su duk kan su, amma dai muna tare da wadda kika gan mu tare duk da itam ma ba barin ta zan yi ba, yanzu dai wadda tafi rike min wuya matarsa ta uku, Ummulkhairi dan ya fi san ta”. Kama baki Haj Shema’u tayi tana sauraren ta. Wayarta ta janyo ta kira Latifa ba bata lokaci sai ga ta ta zo sun gaisa da Haj Shema’u sannan suka roki ta taimaka musu kan yadda za su yaki Ummulkhairi ta ce “Akwai mafita wani kasaitaccen me bada magani ta ba su labari, suka shirya ranar zuwa har sun yi sallama ta fito sai ta koma ta ce musu “Kuna da labarin tana da kasaitaccem wurin dinki na zamani? Zura mata ido suka yi cikin kaduwa ita kuma ta juya ta fice cikin jin dadi dan dama takaicin su take so ya karu.
Ina harabar gidan ina neman Indo in ce mata ta je makarantar su Hussaina ta dauko min ita na hango fitowar Haj Shema’u da fara’a na tare ta “Har kin fito Haj? “E wallahi ” na ce “Ina zuwa ciki na wuce na dawo rike da kudi dan yanayin da na gan ta na gane za ta bukaci kudin na mika mata ina fadin “Ki shiga mota Haj ” godiya sosai tayi min ta fita gidan tana zagin Halima a zuciyarta. “Marowaciyar banza bata iya gane rayuwa ta canza min ba ta temaka min, na zo ko na mota sai neman ta hada kai da ni a cuci baiwar Allah. Ai ba zan taba mancewa da cin amanar da kika yi min ba, Halima kin kuma kawo kanki yanzu, sai na rama.

Halima na zaune inda Latifa ta barta bayan sun gama juyayin bakin labarin da Haj Shema’u ta basu, bata ma da niyyar tashi a haka Tahir ya shigo ya same ta ganin ta a birkice yasa ya ce “Ya ya dai lafiya? Ta dube shi da fuskarta me kamar za ta fasa kuka “Yanzu Tahir adalci kenan? ashe har akwai macen da za ka daga ka fifita sama da ni? cikin rashin fahimta yake duban ta “Me nayi kuma? Wace macen na daga sama da ke? “Ummulkhairi Tahir, ka bude mata wurin dinki na zamani ni ko oho” wani duba yake mata ta cikin farin glass dinsa “Gaskiya ne Halima Ummulkhairi tana da wurin dinki na zamani yanzu haka ma aiki ya yi nisa za ta bude wani dan wannan din ya bunkasa, sai dai za ki dauko kur’ani zan yi rantsuwa ba kudina a bude shagunanta ma’ana ba ni na bata ba, na yarda dai ta tattala abin da nake bata sai ta bude. Wanda tun kina ke kadai nake so ki tattala abin da nake ba ki dan ki tsaya da kafarki amma hakan ya faskara sai ma masifar cin bashi da kika dora ma kanki wanda na rasa ta inda na kuskuro ki. Ki tashi malama ki yi alwala ki rantse. kan ni na bude mata ni kuma zan rantse kan bani bane na gaji da rainin hankalinki, ki tashi! Ya kare cikin daka mata tsawa har sai da ta zabura bed room dinta ta shige ta datso kofar ya ja mummunan tsaki sai ya bar dakin.

Kwana biyu da zuwan Haj Shema’u an zauna cin abincin dare. Tun da na shaki kamshin girkin Basma wanda aka saka ma kifi na ji hankalina ya tashi, cikina ya shiga yamutsawa amma son ganin yanda za ta kaya da Halima wadda ke ta salo bata son abincin sai maigidan ya fita ya nemo mata abinda za ta ci dan bata son wanda aka girka a cikin gidan ya hanani tashi sai da na ji amai zai zubo min na mike cikin sauri, a falona na wuce Hadiza da ke karatu dan gaskiya bata wasa da karatunta bathroom na shige na yi ta kwara amai gaba daya sai da na amayar da abinda na ci. Wanke fuskata nayi sai da na gama maida numfashi sai na fito Hadiza ta dago ta dube ni “Aunty na ji kamar kakarin amai? kai na girgiza “Amai dai? Kai a’a”. Daada ta fito rungume da Mimi muka dube ta a tare, ta miko min yarinyar “A bamu nono mu je mu kwanta” murmushi nayi na karbe ta sai na soma shayar da ita muna dan taba hira har ta saki dan kanta barci ya dauke ta, ta dauke ta suka shiga daki, dama yanzu haka take musu yau idan wannan ya kwana wurinta gobe kuma sai ta dauki dan’uwansa, ta koya musu cin abinci bayan madara dan haka basu damu na da tsotso.
Ni ma ban jima ba wurin Hadiza dan ita kam sai ta raba dare tana karatu. Wani sanyi sanyi na soma ji da ya sanya ni kashe fanka sai nayi shirin barci na kwanta Areef na gefena. Nayi barci sosai farkawar da zan yi wani amai na ji na shirin zubo min na tashi da sauri nayi aman kamar zan amaye yan cikina kafin na dawo daki, Hadiza na gani zaune “Aunty dama ke ke amai dazu? Ban samu amsar bata ba dan jin wani sabon aman na koma ba komai a cikina da zan amayar kakarin kawai na yi tayi na wanke fuska zan koma daki na ga Hadiza tsaye a bayana “Sannu Aunty” ta fadi tana dubana da tausayawa kai na daga muka koma daki, ina kwanciya na kuma jin wani. A wannan daren dai haka nayi shi a wuya ce tun muna yi daga ni sai Hadiza har ta tado Daada, ba yanda Hadiza bata yi da ni ta kira Tahir ta waya na hana ta. Zuwa Asuba nayi laushi matuka, ina yin sallar na kwanta ina jin shigowar Tahir ya dauki Areef ina ganin Hadiza ta ji rokon da nayi mata kar ta sanar mishi,
juyawa ya yi da yaron a kafadarsa yana fadin “Madam yau me barcin safe ce kenan? Na dade ina jin shi da yaron kafin barci ya dauke ni. Tabawar da na ji Hadiza na min ta sa ni bude ido, “Kin ji yadda jikinki ya dauki zafi Aunty? Ki tashi ko tea ki sha mu je Hospital” maida kaina nayi “Zan ji sauki Hadiza” bata bi ta kaina ba ta fice Tahir ta samu suna breakfast Basma na tare da shi da Latifa, Halima na zaune a daya daga cikin kujerun falon wai ba za ta iya zama ba kafafuwanta kunbura suke asibiti za ta. Ya ce ta bari zuwa anjima sai su je tare. Ta ce “A’a” dan Allah kadai yasan abin da ta karba a wurinsa tunda ta gane tana da ciki, bata kawai yake kamar bai san me take ba, dan a halin yanzu ba shi da bukatar hayaniya da ita tana dauke da cikinsa, fata kawai yake ya ga ta haihu lafiya.
A rikice Hadiza ta isa gabansa “Yaya Sodangi, Aunty fa bata da lafiya” “Me ya same ta? Ya tambaya cikin sauri “Amai ta kwana tana yi, yanzu kuma zazzabi ne jikinta me zafi”. “Shi ne da na shiga kika kasa fada min? Ya fadi yana ture kujerar da yake zaune cikin zafin nama ya nufi dakina Hadiza ta bi shi a baya.
Jin labarin Amai ba karamar kaduwa yasa matan ba, Halima da Latifa suka dubi juna Latifa ta kyafta ma Halima ido sai ta mike ta fara takawa zuwa dakin sai da Halima ta harari kofar Ummulkhairi kafin ta mike ta bi bayanta, Basma ta noke kafada kamar tayi tafiyarta dakinta sai dai ta yanke ta bi su.
Suna shiga idanunsu na kyakykyawan gani, Tahir na tallafe da Ummulkhairi wadda jikinta ya yi matukar gashewa ya karbi mug ya danna min a baki dan ya yi ya yi in sha na ki na ce idan na sha amai zan yi, ba shiri na shiga sha sai dai yana shiga cikina na maido shi gaba daya na bata ma Tahir jiki, na kwace jikina daga hannunsa na kwantar da kaina kan fillow rigar ya cire ya kamo hannuna “Zo mu je ki yi wanka” ya dauko wayarsa ya mika wa Hadiza da ta shigo lokacin “Kira min Dr Muhammad, ki ce ina son ganin sa yanzu, Ummulkhairi zai duba min. Ta karbi wayar “Tashi mu je” ya kuma bani umurni kamar sun hada baki suka dan basu san me zasu gani ba idan suka fito kila ma a kirji zai dauko ta, Hadiza ta fito falon tana dariyar mugunta kasa kasa dan ta san sun ji abin.
Sai da na fara wankan ya fita dan zuwa ya canza kayansa da fitowa ta Hadiza na samu ta gyara inda na bata falo na wuce na kwanta bayan da na sa jallabiyar da Hadiza ta ajiye min. Tahir ya dawo, Daada ta fito dauke da Mimi tayi mata wanka ta shirya ta cikin wasu riga da wando farare masu taushi, ta raba mata sumar ta biyu kafin ta dora mata hula. Ganin uban sai ta fara zallo za ta wurinsa ya mika hannu ya dauke ta, ta karbi Areef a hannun Hadiza dan ta je shi ma ta yi mishi Sannu ta min ta juya Tahir ya kuma kiran Dr ya ce yana hanya, a kafada ya sa Mimi ya fita daidai step din da ake takawa a shiga main fallow na gidan ya tsaya yana sauraren ta inda zai ga Dr Muhammad ya bullo, hancin motarsa da ya kunno kai ya zura wa ido, su biyu shi da wani abokinsu da suka dade basu hadu da Tahir ba suka fito suka nufo inda yake tsaye hannu suka ba shi suka gaisa “Kwana biyu Lawal? Tahir ya fadi ma wanda suka zo tare da Dr “Muna gefe Kankara, wannan yarinyar fa? Ya fadi yana miko hannu dan daukar Mimi wuyan uban ta makale duk da cewar ba kyuyar take ba gara ma Areef ya kan dan taba. “Yan biyun da aka haifar mishi ne” Dr ya ba Lawal amsa “Wow! ka ce wata beautiful babyn na ciki? /gaskiya ka more mutumina, duk yadda aka yi in ba balarabiya ka auro ta haifa maka wadannan zuka zukan yaran ba to Shuwa ce” duk da Tahir ba shi cikin yanayin son magana sai da ya ce “Kai dai ba ka da mutunci, to in fada maka yarinyar nan mahaifiyata ta dauko sak, dan an ce a duk fadin zuriarta ba a samu wanda ya biyo ta har kuma yaran da ta haifa duk kuwa da tana cikin shekarun girma sama da wannan yar tawa. Dan’uwan haihuwarta namiji ne shi kuma kamar mu daya da shi, ku mu shiga daga ciki” Cikin suka shiga a falo ya bar su ya shiga ciki wurina sai da ya ce Hadiza ta dauko gyalen rigar ta rufe min kaina sannan ya koma tare suka shigo da Dr, Hadiza ta ce min kwana tayi amai ga zazzabi? Kai Tahir ya daga mishi “Sannu Madam” ya ce yana nazarina, karin ruwa ya sa min wanda ya zuba wa allurai sai kuma ya debi jinina ya tafi dan gwajin, abokinsa da suka zo tare dai tun da ya ga yan biyu ya ce Dr ya je ya dawo, ya zauna ya tasa su yana musu wasa dan ya samu Mimi ta yarda da shi, sai fadin yanda suka burge shi yake ni dai barci nayi sosai .
Dr Muhammad na dawowa da result Tahir ya tare shi da son jin abin da ke damuna kai tsaye ya ce “Congrats Kankara ka Kara jefa kwallo a raga, madam dai juna biyu ne sai dai karami ne kwarai” Suna ta maganar su Lawal da ke wa yan biyu tafi ya dago “Amma watan su nawa har ake maganar wani cikin? 8 month” Tahir ya ba shi amsa maganar da suke tayi da dariya yasa su Halima san sanin sakamakon duk da ba sa son tabvatuwar zargin su, Latifa ta tari Tahir bayan tafiyar su Dr duk abin da ya kamata ayi ya bar shi a hannun Hadiza ya ce sai zuwa yamma za su dawo tare da Asiya, wadda ita ma tayi nauyi sosai “Amma wallahi Maman twince tana jin jiki, hala typhoid ne? Murmushin sa me tsada ya yi mata “Yan biyu ne za su samu kanne” juriya me yawa ta sa wurin yin murmushin yake “Amma ba ku yi wa yan biyu zalama ba? Wuce ta ya yi ba tare da ya ce komai ba, bata saurari Halima ba dakinta ta wuce ta datse kuka tayi hada birgima kafin ta ci alwashin ko za ta tafi tsitara sai ta ga bayan kishiyoyinta Ummulkhairi da halima dan sune suka rike mata wuya suka sha gabanta musamman Ummulkhairi.
5/12/22, 13:33 – Buhainat: Ban tashi ba sai Azahar. A daddafe nayi sallah tea na ce Hadiza ta hada min dan sai na ji ina sha’awar shan shi. Ikon Allah kuma da na sha ban yi aman ba.
Zuwan Asiya da yamma take tsokalata me juna biyu, nan na fahimci ciwona ciki ne, hawaye na kama yi har na ruda Asiyar, tana fadin “To meye abin kuka? kyauta ta Allah, yaranki lafiyayyu, dabo fa suke yi. A haka Tahir ya zo ya same mu, gane dalilin kukana sai ya sha mur, bai ce komai ba. Ko da Asiya ta tafi kwanciya kawai nayi kan fillow ina ci gaba da zubar da hawaye. “Tashi zaune ” na ji muryarsa ba tare da na san sanda ya shigo ba, kallon sa nayi ganin ba wasa sai na tashin ina goge hawayen da dankwalina. Ya tokare hannuwansa a kirji kamar yanda na fahimci ya fi yi idan ransa na bace “Cikin ne ba ki so? Na ji ya tambaye ni ban tanka ba sai ya kara maimaitawa nan ma ko motsi ban ba “Good” ya fadi sai ya juya ya bar min dakin.
Tun daga ranar fushi yake da ni, baya min magana zai dai shigo ya tabbatar na ci abinci na sha magani dan tun waccan ranar ban kara amai ba, Dr Muhammad ya fadi yanda za a kula da lafiyar twince da abinda za a rika ba su, zan kuma ci gaba da shayar da su. Ni ma din bana mishi magana, dan haushin shi ma nake ji ina ganin shi ya ja min. Ko da girkina ya zo ban leko ko kofa ba ballantana in yi wani girki ko gyara mishi wuri. Da daddare nayi wanka na bule jikina da kamshi, wasu riga da skirt na sa yan uban su, cikin kayan da muka sawo a Saudiyya ni da Laila, na kama gashina da ribbon na dubi kaina a madubi ni kaina na gane nayi kyau kayan sun yi min cif a jiki komai ya fito. Flacks na dauka zuwa kitchen ruwan zafi zan dafa, dan yanzu ba abin da nake so irin tea, in hada da cake. Tun da na hango su a dinning Tahir da matansa, sai na tabe baki wuce su nayi kamar ban gan su ba, ruwan na dora na sa kayan kamshi sai da ya tafasa sai na tace na juye a flacks dina sai na fito yanzu ma ban ko gwada na san suna wurin ba.
Su Hadiza na samu su na kallo da Daada da Hussaina. sai nima na zauna, kiran Kamal da ya shigo wayar Hadiza yasa ta mikewa zuwa ciki, mun jima kafin Daada ta suri Areef, ta tada Hussaina da ta soma barci suka shige, ni ma mikewar nayi na kashe kayan kallon na wuce daki Mimi na ta barcinta, bathroom na soma shiga kafin na fito na sauya kayan jikina na haye gadon ina karanto addu’o’in kwanciya. Hadiza da ke waya har lokacin ta dube ni kamar tayi magana sai kuma na ga ta ci gaba da wayarta, sama sama na ji ta kare wayar, sai ta rage hasken firilar dakin, tawa wayar aka soma kira ina dubawa ogan ne zan sanya ta a silent sakon sa ya shigo “Ki zo dakina za mu yi magana” ajiye ta kawai nayi a fatan da nake barci ya dauke ni na ji shigowar wani sakon, saurin bude idona nayi na dubi sashin da Hadiza take kwance duk da hasken da ke dakin ba me yawa bane ba zan iya gane halin da take ciki ba, ba ni da zabi sai na mike ina kara jinjina rashin kunyar namiji yana sane tare muke da Hadiza baya jin kunyar ta gane abin da kenan. Ban tsaya daukar Mimi ba na bar dakin da shiga ta zaune na same shi gefen gado rike da wayarsa can kuryar gadon na haye na juya baya.

Washegari ina zaune a daki ni kadai ce, Hadiza ta je makaranta Daada sun shiga gidan Kawu Attahiru ita da yan biyu. Wayata na ji tana ruri na kai hannu na dauka Aunty Kulu ce kan layi murmushi na soma yi mun gaisa cikin raha tana tambayar me gidanta da kishiyarta, na ce suna gidan Kawu sai na ji ta soma ce min “Me kenan ko meye sunan abin da kike yi wa mijinki? Hauka kike Allah ya yi miki kyauta irin wannan ki butulce? /mu ba ki ga neman ta muke ido rufe Allah bai bamu ba, sai ke Allah ya ba ki ya zabe ki cikin abokan zaman ki, yanzu kina ga murna za su yi da wannan rabon da Allah ya kuma ba ki, sai kuma ki ki wa mijinki dadin kai har ya kai ga kai kararki kina fushi da shi, to wallahi yana dawowa ki ba shi hakuri, kuma ku koma muamalarku kamar da. Ki gode wa Allah wannan cikin wata baiwa ce Ubangiji ya yi miki da bai yi wa bayinsa da yawa ba. Jin tayi shiru na ce “Zan ba shi hakuri Aunty, kuma na bari ki yi hakuri ke ma Aunty dan Allah ” Ta ce. “Na gode, Ummulkhairi ki gaida yaran”
Da Tahir ya dawo na ba shi hakuri na sa ma raina dangana da cikin.

Halima da ke dakinta zaune, waya suke da Haj Shema’u kan inda za su hadu. Ta wayar ta kira Latifa, a motar Halima suka tafi wani dan kauye ne can idan an fita cikin Kaduna. Sun karanta wa mutumin wanda ba musulmi ba ne bukatar su, ya ce bukatar su ta biya sun kawo kukan su inda za a share musu hawaye. Ya basu abinda zai basu kan cewa su zuba inda kishiyoyin nasu za su taka tare da bukatar su ga abin da suke so ya faru da su, sai kuma ka tabbatar wadda ka karba da sunanta ita ta taka idan aka samu akasin haka to kaikayi fa zai koma kan mashekiya. Kowacce guda daya ya bata tare da cajin su makudan kudade.
Sun taho cike da murna Halima ta amshi na Ummulkhairi Latifa da bata so Halima ta riga ta ba cikin rashin jin dadi ta amshi na Basma. Sun taho bisa hanya suka ba Haj Shema’u abin da suka yi za ta ba su idan ta raka su, a hanya ta sauka ta ce musu da inda za ta suna bace ma ganinta ta ciro wayarta mutumin ta kira ta ce acc no za ta turo ko ko dawowa za tayi ta karbi kash kamar yanda suka shirya? Wata dariya ya kece da ita ya ce shi magani na gaske ya basu bai basu feck ba kamar yanda suka shirya. Hannu ta dora a ka ta ce “Me zai sa ka min haka? Cikin kishiyoyin nasu akwai wadda ban so a zalunta, yanzu ya kake so in yi? Ya ce “Wannan kuma ruwanki, abin da dai na sani ba zan kashe wa kaina kasuwa ba, ina so gobe su dawo har ma su kawo min wasu. Wayar ta sauke cikin matukar da na sani drop ta dauka zuwa gidan nasu za ta je ta fada wa Ummulkhairi, dan ba za ta bari a cutar da wannan yarinya da Allah yasa mata kaunarta take jin ta kamar yar’uwar ta ta jini.
Sai dai tana isa daga bakin gate take tambayar gate man ya ce “Maman yan biyu? dan turus tayi “Da ma ta haihu? Ya ce “Kwarai kuwa, yan biyu ta haifa mace da namiji, amma yau din nan suka tashi ita da jama’ar wurinta zuwa Katsina” Dafe kai tayi tashin hankalinta ya karu “Ba zan samu lambar wayarta ba dan Allah ? Girgiza kai ya yi “A’a fa ni dai babu, sai dai in tambaya miki masu gidan ” ta ce “A’a” ya ce “To bari in bambaya miki su Indo da laraba masu aiki” Laraba da ya gani tana shanya ya fara tambaya ta ce “Ni kam ina da ita amma wayata na wurin gyara, Laraba ma kuwa bata da wayar” ya juyo wurin Haj Shema’u ya kora mata yanda suka yi, ta kara tambayar sa ko ya san sanda za ta dawo? Ya ce “A’a ” juyawa tayi cikin wani da na sani da ya kara rufe ta.

Mun sauka Katsina lafiya. Daada kuma muka kai ta har gida. Yayana Sani na je ma bakunta, zuwana kuma na farko kenan gidan sa tun da nayi aure. Matsa ma Tahir lamba nayi rokon safe daban magiyar dare daban, har Allah ya taimake ni ya bar ni. Kwanaki biyar nayi na isa Dutsinma nayi biyu, muka sha sunan kanwata Hauwau da ta haihu, sannan muka biya muka dauki Daada muka koma.

Latifa da ke tsaye gindin windon ta ganin motar da ta tsaya da mutanen da ke fitowa ciki dadi ya kamata, yau za ta cika aikinta, dan ita ko da ta amsa da sunan Basma a niyyarta kamar yadda ya ce da niyyar Halima ta amsa kuma ita take nufin sanya mawa, ta ce wa Halima ba za ta sanya wa Basman ba sai Ummulkhairi ta dawo. Dan guntun tsaki ta ja “In sa wa waccan shashashar a dauri kashi ko a bata igiya, ita da ma da ita da babu ai kusan daya ne. Za ta fara ta kan Halima kafin idan maganin ya yi ta koma ta amso wanda za ta sa wa Ummulkhairi, Fitowa tayi ta tare mu da fara’arta tayi mana Sannu, abin da ya yi matukar bani mamaki, ba ma ni ba har su Hadiza na san sun ji mamaki. Muna shigewa ta fada dakin Halima albishir tayi mata da dawowar su Ummulkhairi tare da fada mata ita fa yau za ta sanya na ta dan haka ita ma sai tayi kokarin sanya nata. Dan shiru Halima tayi ni wallahi sai da na dauki sanya wa yarinyar nan na gane na ta ya fi wuya, sashen ta da mutane da yawa” yar dariya Latifa tayi “Ba wata wuya in kin sa kanki, tana karbar girki da ta shiga yi mishi gyara yi kokari ki sa, dan kin ga sannan ma baya nan sai ki ga ta fito ta taka. Halima ta gyada kai cike da gamsuwa Latifa ta mike ta koma dakinta kafin ta wuce kuma sai da ta tsaya ta barbada abin a kofar Halima wanda yake fari tas kamar madara sai ka sa ido za ka fahimci da wani abu. Tana zama ta kira Halima “To ki yi kokari ki fito dan na aiki su Indo kasuwa Mutanen wurinta kuma na ga sun fita, ita kuma ta shiga kitchen in kin samu sa’a sai ki zuba mata kawai a wuce wurin ” Ciccibawa tayi ta dauko abin inda ta ajiye sai ta fito sai dai tana taka kafarta a kofar dakinta kanta ta ji ya sara ta maza tayi sai dai ta kasa daurewa ta tafi dakinta ta koma ta hau gado ta rasa abin da ke mata dadi.
Bata kara samun damar fitowa ba Tahir ma da bai ga ta fito ba dakin ya bi ta sai dai ce mishi tayi bata jin fitowar ne kawai. Abinci ma har daki su Laraba suka kawo mata, duk yadda ta so ta ci kasawa tayi, barci ranar tayi shi ne amma ba mai dadi ba, farkawar da za tayi da Asuba gabanta ya yanke ya fadi dan sabon al’amari a gaban ta, zanenta ta kai hannu ta yaye abin da ta gani ya sa ta kurma ihu! gaba daya gabanta ya zazzago birgima ta shiga yi tana kuka har falo, nan take gidan ya hadu kanta dan duk wanda ke ciki ya ji ihunta, temako Tahir ya nema wurin sa ta a mota zuwa Asibiti shi da mutumin da gidansa ke jikin na mu, sai ni da Daada muka zauna a baya tare da ita, an karbe ta a Asibitin an bata gado ko awa bata yi ba ta soma jijjiga likitoci suka rufu kanta, sun nemi sa hannun Tahir dan shiga da ita dakin tiyata an ciro yaro namiji wanda aka sa a kwalba dan bai isa haihuwa ba. Yan’uwan ta da na Tahir suna ta sintirin zuwa duba ta, mutum uku ke jinyarta mahaifiyarta sai kanwar ta da ke zaune gidan su saboda rasuwar mijinta, sai kuma karamar kanwar ta budurwa. Ranar da ta fara tashi zaune kai ta hada da gwiwa tana ta kuka,yan dubiya kowa sai bata hakuri ake amma yin shirun ta ya gagara.
Latifa dai ganin magani ya ci Halima yasa ta shiri ta koma dan karbo wanda za ta sa wa Ummulkhairi, sai dai bata yarda ta karbo wanda wani ciwo zai samu Ummulkhairin ba dan yanda ta ga ta kasance da Halima duk da abinda ya same ta Tahir bai tura ta gida ba, sai ma dawainiya da yake tayi da ita. Dan haka wanda za ayi wa Ummulkhairi saki uku ta karbo yanda za ta kara gaba kowa ma ya huta. Ya kuma ba ta tare da kara jaddada mata sharadin maganin sa, ta amsa ta koma gida tana ta farin ciki ta boye abin ta sai ta koma shige wa Ummulkhairi ni dai ban saki jiki da ita ba, duk yadda tayi ta fakon ta sanya mugun abin dan Ummulkhairi ta taka abin ya zame mata jan aiki, amma dai bata hakura ba tana ta bi ta hanyar kisisinarta da duniyancin ta,
5/12/22, 13:33 – Buhainat: Halima ta ci gaba da jinya a Asibiti cikin mawuyacin hali, gaba daya ta lalace. Wata biyu ta share aka sallame ta ba dan ta warke ba sai dai likitocin sun ce sun yi iyakar kokarin su sai dai ko zai fitar da ita waje, dan haka cuku cukun fitar da itan ya fara.
Ranar da aka dawo da ita mahaifiyar ta da kannenta suna kokarin taimaka mata ta fito, Latifa ta fito daga ciki an sha gayu za ta shiga motarta ga glass din nan ya yi das ya zauna a fuska, sun kalli juna ita da Halima wadda ke kara jinjina rashin amana irin na kishiya tun kwanciyar ta Asibiti sau biyu kacal Latifa ta taba zuwa duba ta. Latifar kuma ta hade su duka tayi musu kallon hadarin kaji kafin ta ce “Sannun ku ” sai ta wuce abin ta.
Cikin wheel chair suke tura ta da Tahir ya saya mata dan saukaka mata wahalar tafiya, mahaifiyar ta na rungume da jaririn me suna Abubakar Sadiq sunan babban yaya an cire shi daga kwalba sai dai baya shan nono dan nonon ba ruwa duk yadda aka yi kokarin nemo mata abinda za ta sha dan ruwan nonon ya zo hakan ya faskara kawai sai aka ci gaba da ba shi madara aka bar ta ta ji da kanta.

Latifa ta hau titi zuciyarta bakikkirin da ganin dawowar Halima kullun addu’arta Allah yasa idan gaban nata ya karasa rubewa ta mace a can kowa ya huta dan yanzu gidan ba karamin dadi yake mata ba ba Halima ga Basma ma bata nan ba ruwan ta da wannan dogon jiran kafin girki ya zagayo kanta, Basma ta kusa wata da mahaifinta ya zo ya tafi da ita wai waje zai fita da ita a duba ta kan matsalar rashin haihuwar ta da kuma lalurar ciwon kanta. Ita ma fata take da shige shige Tahir ya aika mata da takardarta, sai ta ji da wannan shegiyar yarinyar da har yau ta kasa samun yanda za ta sanya mata amma dai a juri zuwa rafi ta bugi sitiyari “In Allah ya yarda sai kun bar min Tahir ni kadai, sabon gidan da ya kankara babu me shigar sa.

A bakin Indo muka ji dawowar Halima na cicciba dan cikina ya fara nauyi ga gajiya da nake ciki ta sintirin zuwa gidan Asiya da ta haihu aka yi suna jiya, ta samu ya mace Hanifa. Sai da nayi wa Hadiza magana sau uku kafin ta yarda za ta wai kunyar mahaifiyar Halima take ji.
Da sallama muka shiga falon duk kan su suna zaune cikin mutunci suka amsa gaisuwar mu dan su kam suna taya Kamal son Hadiza dan yanzu shi ne komai a gidan su, shi ke musu abin da mahaifin su zai musu shi ya zame musu uba duk da uban na su yana nan. Sai wani sussunnewa Hadiza take yi, ba mu jima ba muka mike da muka fito na sa Laraba ta kai musu abinci.

Da daddare Kamal ya zo, wurin yayarsa ya fara isa kafin ya dire falona wurin Hadiza, mun gaisa za mu bar musu wurin ni da Daada ya ce yana son magana da ni sai na tsaya rokona ya yi in shawo mishi kan Hadiza ta bari ayi bikin su ba kamar yanda take cewa ba sai ta kammala karatu. Na ce kar ya damu zan mata magana. Sai da muka yi shirin kwanciya nake mata maganar ta ce Ita wallahi tsoron auren sa take sai ta ga kamar dan ya rama abin da tayi masa yasa ya matsa lamba sai ya aure ta. Na ce kuma in haka ne sai ya ki aure tun tafiyarki sai ma karatu da ya koma? tayi shiru sai na bata shawarwari ta kuma amince dan haka washegari nayi mishi waya na sanar da shi amincewarta, bai yi kasa a gwiwa ba ya tura yan neman aure a gidan su na Kankara, sai dai yayyen Tahir sun ce sun bar komai a hannunsa daga shi ke rukonta. Shi kuma ya ce Kamal ya je ya shirya duk ranar da Allah ya sauke ni lafiya ranar suna sai a daura aure, Halima dai duk da halin da take ciki an ce bata so.
Kwana uku da tsaida maganar na fara nakuda daga ni sai Hadiza muka nufi hospital na ce wa Daada tayi hakuri ta zauna da yaran dan Tahir baya gidan. Cikin gajeruwar nakuda Allah ya yi ikonsa na sauka lafiya na samu da namiji shi ma din kamar sa daya da Areef duk sun dauko Tahir har dan wurin Halima duk kamar su daya. An sallame mu mun dawo gida, washegarin da na haihu Hajiyar Tahir ta zo sai da muka kwana hudu ta koma ba yanda bamu yi da ita ba ta bari ayi suna ta ki fafur ta ce suna na yara ne suna nan zuwa ita barka ta zo.
Yan Kankara sun zo da yawa dan ban da suna ga daurin auren Hadiza yan uwan sa maza duka suka zo dan daurin auren suka koma da yammacin ranar yarona ya ci sunan mahaifin Tahir Abdurrahman wanda Tahir din da kansa ya fara kiran sa da Sudes, Hadiza dai ta ce bata tarewa sai nayi arba’in Tahir kuma ya biye mata.
Washegari yan suna suka koma har da yan’uwana, Laila bata samu zuwa ba dan kwance take sharkaf cikin laulayi, sai bana Allah ya kawo rabo, yan Kankara kawai suka rage.

Halima da ta gaji da zaman daki kannenta suka gunguro ta dan ta sha iska, Latifa da ke zaune ta dora kafa daya kan daya tayi musu yatsinannen kallon da ta saba, ran Halima ya baci ta ce da dai ba mu san asalin Ungulu ba sai ta ce daga masar take karyar banza karyar wofi ” wata irin shewa latifa ta yi ta daga wayarta da ta fara kukan neman agaji “Kawata ina kika shiga ina ta neman ki? Ki ji abin arziki, in ba ki labari sweetie ya biya min aikin hajji ga gidan mu da na turo miki hotonsa an gama za mu koma daga na dawo aikin hajji kuma sweetie zai canza min rantsatstsar mota” ta dan saurara kafin ta sa shewa “Ai mu duniya sabuwa mu wanke goma mu tsoma biyar” ta gama dararrakunta Halima da ta hana a gungura ta sai lokacin ta ce su wuce Latifa ta buga cinya “Sai dai mutum ya gan mu da miji, kwaalelen kare da hantar kura. Ko da su ka fita ba su wani dade ba ta nemi su mayar da ita ciki dan wani bakin ciki da ke cin ranta, suna dawowa falon anan kannen suka tsaya dan hoton wasu masu garkuwa da mutane da aka kama ake nunawa a tv falon, daidai nan “Ummulkhairi ta fito daga dakinta sakale da babyn ta cikin wani madaukakin mamaki da ya kama Halima ta ga latifa tayi saurin tashi ta nufe ta cikin wata fara’a da girmamawa irin wadda ta rika yi mata ta karbi yaron tana tambayar ta kwanan su Mimi, sai da suka gama gaisawa Ummulkhairi ta karbi danta, ta haura sama Latifa ta isa step din benen ta fakaici idon kowa da ke falon ban da Halima da ke ankare da ita ta fito da mugun abin ta barbada
Indo da take goge goge Halima ta duba “Indo yi sauri ki duba min dankunne na a kafar bene” cikin azama Indo ta nufi kafar benen dan tana kusa da wurin Latifa da ta bar wurin tayi azamar komawa dan tare Indo sai dai ta makara har Indon ta kai wani tashin hankali ta ji ya ziyarce ta Halima kuma ta shiga fadin “Muguwa, Azzaluma, yanda kika cutar da ni ki saurari naki, ba dai kin sa min na taka ba? yan’uwan Tahir da suka fito dan kallon abinda ake nunawa na masu garkuwa suka tsaya sauraren Halima cikin su hada mahaifiyar Halimar wadda ta tako inda yar tata take ta ce tayi shiru amma sai ta juyo ta dubi uwar “Ya za a yi in yi shuru Innai? Alhali na san abin nan ba shi da makari kuma wallahi Latifa ce ta sa min na taka ” cikin fushi uwar ta tare ta “Ke dai sam ba Allah a tare da ke Halima Allah ya jarabce ki ki dora abin kan wani? “Wallahi da gaske nake Innai, tare da ita muka karbo ni zan sanya wa Ummulkhairi ita kuma za ta sanya wa Basma, shi ne ta sanya min dan tana barin dakina ta kira ni wai in fito in sanyawa Ummulkhairi ta fito, ina kuma fitowa kaina ya sara” Uwar ta kama haba ta na tafa hannu mutanen wajen suka barke da salati “Ai shi kenan Halima kin kai ga yanda kike so, to yau WA GARI YA WAYA? kullun ina gaya miki illar biye wa rudin duniya da kike yi, amma ba ki ji yau kowaccen su na zaune lafiya ke ce cikin masifa” Halima ta fashe da kuka kamar yanda uwar ta ta ma ke kukan ta nuna Latifa “Wannan Azzalumar ta ja min” kukan kura Latifa tayi ta hankade Halima da ke kan wheel chair tana fadin ita za ta yi wa sharri Halima ta fasa kara ai kuwa kannen ta suka yi kan Latifa suka rufe ta da duka, duka kuwa ba na wasa ba duk tarin yan Kankara an rasa me matsawa ya kwace ta sai mahaifiyar su ke ta karajin su sake ta amma kamar ma tana kara zuga su, wata aka samu cikin yan Kankara ta kira Tahir a waya wanda ya yi sammakon barin gidan ta ce ya gaggauta dawowa gidansa za a yi kisan kai. An yi sa’a ya shawo kwanan layin zai dawo gidan shigowar sa yasa suka daga ta gaba daya sun gama yakushe ta sun yayyaga mata sutura ganin yanda Tahir ya tsaya cikin matukar bacin rai yasa Halima ci gaba da fadin Latifa Muguwa ce Azzaluma ita ta sa mata abu ta taka da sauran makirce makircen da suka yi tare ita ma Latifa jin za ta kwana ciki yasa ta soma ramawa tana fadin asirce asircen da Halima ta yi tayi kan zubewar cikunan Ummulkhairi har ma da Basma. Nan fa suka yi ta toma ma juna asiri. Harde hannaye kawai Tahir ya yi yana jin sa kamar a sama wai shi Allah ya jarabta da wadannan iblisan matan? Wani gigitaccen mari da uwar Halima ta yarfa mata yasa ta yin shiru ita ma Latifa kuka ta shiga yi na tozarcin da yan’uwan Halima suka yi mata tsawa Tahir ya daka mata ya ce ta tashi ta fice mishi a gida ya sake ta ihu ta kwarma tana tuma tana faduwa yan’uwan Halima suka kamata zuwa dakinta, ita ma Latifa da lalube ta koma nata dakin dan an tattake mata glass dinta, wanda ta ce bata ga me fitar da ita ba.

Yan Kankara sun shigo wurina suna maida yanda aka yi ina sauraron su, a bakin su na ji wai ita ma Basma da bata dawo ba ubanta ya kira Tahir a waya ya ce sabon gidansa kar yasa wa Basma irin kayan da zai sanya wa sauran matansa da ya ce saboda me ai shi duk daya suke a wurinsa sai ya ce ba daya suke ba Basma ta fi su domin ita din yar gata ce ya ce shi dai iri daya zai yi ya ce to ya bar na Basma zai yi mata order daga waje dan haka idan Tahir ya koma sabon gidansa ya kira shi sannan za ta dawo. Shi ne matar Yaya Magaji ta ke ce min Ita waccan doguwar da ta ce an biya mata hajji da gaske take? Na ce Ban sani ba abinda dai na sani na ji wayar Tahir da wani abokinsa ya ce banda cuku cukun da yake na fitar da Halima waje ya so biyawa Latifa aikin hajji, amma yana ganin sai dai wata shekarar. Sun ci gaba da maida zancen
Sai dare Tahir ya shigo maigadi ya tambaya Latifa ta fita ya ce mishi A’a dakinta ya wuce kai tsaye ya same ta ya ce zaman me take yi mishi a gida? Ta ce ita dai ya yi mata hakuri ya maida ita ya ma za a yi ya sake ta ita kadai ya bar Halima? ya ce “, Ok dan na miki saki daya shi ne kike ganin kina da wurin zama to na cikashe miki saki biyun, kuma idan kika bari gari ya waye har na fito na same ki zan sa a fitar min da ke da kayanki ” hannu ta dora a ka shi kuma ya sa kai sai ya bar dakin. Ta dade cikin tunani sanin waye Tahir kaifi daya ne yasa ta kiran Fadila kawarta a waya ta ce ta zo da sassafe ta fitar da ita da ta nemi jin yanda aka yi sai ta bata labarin komai.
Da Tahir ya fito da safe ya ga ta tafi sai ya kira masu mota suka kwashe kayanta ya aika mata da su gidan su.

Maryam Litee
5/12/22, 13:33 – Buhainat: Tun daga ranar ya fita harkar Halima. Dakinta da yake shiga ya duba ta ya daina, sai da aka kwana biyu a haka a na gobe yan Kankara za su koma Halima da ke daki ta rasa abin da ke mata dadi, dan mahaifiyarta tun wannan tonon silili da suka yi wa juna Halima da Latifa ta tattara nata ya nata ta sulale, ta bar gidan ko Tahir bata yi wa sallama ba sai dai ya ji bakin Hadiza. Ga Tahir idan za ta kwana tana kiran sa bata shiga wanda take jin faduwar gaba idan tunanin ya saka ta a black list ya darsu a ranta. Kanwarta bazawara ta kalla “Kai ni wajen Tahir Zabba’u” “Ki ce da shi me Aunty? Ke dai da kika samu bai kore ki ba ki rufa wa kanki asiri ki rabu da shi” da masifa ta taso mata “In za ki kaini ki kaini” kanwarta budurwa wadda suke cewa Baby ta dago kai daga kwancen da take kan tree sitter tana danna wayarta, tare da Allah Allah kar auntyn tasu ta ce ita dan bata dade da fita ba ta je kai kayan da aka zubo musu abinci, ta ga yan Kankara duk suna nan zube a falon. Kan ba yadda Zabba’un za ta yi ta gungura ta suka fito sun ratso falon kowa da ke ciki ya bi su da ido ba wanda ya ce su ci kansu, Tahir ma da ke zaune yana cin abinci dauke kansa ya yi, ran Halima ya yi mummunan baci ta ce kanwar ta ta ta mayar da ita. Sun koma daki ta dubi Baby “Kira min Tahir Baby” Ita ma gwada bata son zuwa tayi ta kwakwkwara mata zagi dole ta mike ta fita tana tura baki, tana gaya mishi dama ya kammala abarkacin idon mutanen wurin ya ce yana zuwa sai ya bi bayanta yana shiga suka dubi juna shi da ita, su kuma kannen nata suka shige bed room har yanzu zaune take kan wheel chair an dora mata danta kan cinyarta hannayensa ya nade a kirji ya tsare gida “Ga ni lafiya? Ta cije lebe sai hawaye “Jarabtar da aka yi min Ita za ta sa ka wulakanta ni Tahir? Abinda dai kika dauko wa kanki Halima, ke yanzu ba ki ji kunyar daura wa jarabawa da kika yi ba? Sakamako ne dai na abinda kika shuka ban kuma wulakanta ki ba dan da na wulakanta ki da tun a ranar da na san ko ke wace ce ba za ki kwana min a gida ba kuma d…….. ta katse shi cikin kuka “Kuma wallahi ban zama anan ina kallonka da wasu matan yayin da ni na zama mara amfani, ni ka sake ni in koma Kankara ” wani shegen murmushi ya sakar mata “Halima kenan, ai tun ranar da na saki latifa ke ma na karasa miki saki dayanki domin ganin ki ma bana so Halima, girman iyayenki yasa kika kawo war haka a gidana, ki kara hakuri za ki tafi ina so in sallami yan Kankara sai in kira iyayenki su ji halinki in yaso sai su tafi da ke” yana kai karshe ta mike tsaye hannunta akai tana famar kuka Tahir ya rufa mata asiri dan ta da ke bisa cinya ya fado ya tsala ihu cikin zafin nama Tahir ya cafko shi ya sa shi a kafada sai ya bar dakin da shi, ya wuce yan Kankara a falo bedroom dina ya yi wa tsinke ya shigo na fito daga bathroom daure da tawul wanda yake daga kirji zuwa cinyoyi, dan kullun zan kwanta ina shiga ruwan dumi mun zuba wa juna ido ni da shi, dan rabon da muyi wa juna wani dogon gani tun kafin wannan bahallatsar ta Halima da Latifa yaron hannunsa ya miko min na kai hannu na karbe sa ina jijjiga shi “Gwada ba shi nono mu gani” saurin duban sa nayi jin abin da ya ce sai ya kara maimaita min na dan yi jim, gane ba zan samu wani karin bayani ba a wurinsa sai na zauna bakin gado na balle tawul din na dunguna mishi nonon ya kama har yana sarkewa dan yadda yake ja da karfi kamar za a kwace mishi.
Tahir na tsaye yana kallon mu, “Na ba ki yaron nan Ummulkhairi, ki hada su shi da Sudes ki shayar da su ” wani razanannen kallo nayi masa sai kuma nayi kwal kwal “Ya za a yi ka raba uwa da danta? alhali ba mutuwa tayi ba, wane irin zagi kake so ayi min ka karbe mata da ka bani? Sai na fara hawaye “Ba zan so ayi min haka ba ballantana har ni in yi wa wata” “Na saki Halima! na cikashe mata igiyarta daya” barin kukan nayi nayi saurin duban sa “Ina so ki rike yaron nan ki shayar da shi nononki, ina jin tsoron ya dauko halayen uwarsa” “Addu’a dai kawai za a yi, amma daga jininta ne ta haife shi ba ka da makankara da ita”. “Ko dai meye ne ki taimake ni ki rike min shi bana so ya tashi karkashin tarbiyar Halima”. “Wannan fa duk ba shi bane ita Halimar ta ta mahaifiyar haka take? Takowa ya yi zuwa gadon ya zauna sai ya rungume ni kalamai masu dadi da yabon halayena yake yi yayin da yaron ya saki nonon ya zura min ido, kamar su daya da Sudes har rashin hasken fatar sai dai Sudes ya gwada mishi girma kadan dan shi an haife shi watanninsa ba su kai ba. Ba mu ji motsi ba sai dai bude kofa muka ji, Hadiza da bata san da shigowar Tahir ba ta fado dauke da Sudes saurin juyawa tayi ni kuma nayi saurin janye jikina daga Tahir ina tura baki “Ka ja min in ta jin kunyar Hadiza” na kwantar da yaron sai na mike sai na isa gaban wardrobe ina neman kayan da zan sa in kwanta, har na sa yana zaune “Ki zo mu je falo yarinya kin koyi zaman daki tun da kika haihu ” na dan langabe “Da barci zan yi “. “Ke wa ya ce miki kana bako ka riga shi kwanciya? Sai na ga gaskiyar sa dan haka a baya na bi shi muka fita dakin shi bai zauna ba wurin Kawu Attahiru ya ce min za shi. Na zauna cikin bakin ana hira, Hadiza ta kawo min Sudes ta karbi Sadiq. Kwanan da yaron ya yi wurina yasa suka gane Tahir ya bani shi Hadiza ta tambaye ni na bata labari sama sama ai kuwa suka shiga magana daga me fadin babu me bata dan kishiya ta rike ya girma ya ce da wa Allah ya hada shi ba da ke ba, sai me cewa ni yanzu duk cutar da Halima tayi min da mugunta a rayuwa har in amshi danta in rike? Ni dai amsa daya nake basu “Da na Tahir ne, kome zan yi dan shi zan yi kuma da zuciya daya zan yi. Sai dai dagowar hantsi suna ta shiri Tahir din ya shigo yana fadin Halima ta bar gidan nan me gadi ya fada mishi dan haka shi zai wuce Kankara idan motocin da za su mayar da su sun zo su taho. Yana fita suka balle ka ce na ce “Ko har yanzu surkullen da wannan me kama da tukunyar bai sake shi ba? In ba haka ba me zai kuma yi da wannan me bakin halin, abu ma ta riga ta tashi aiki, in ma ya rike ta sai dai ya taimake ta. Ko ni ma sai da na ji zafi wai shi har wane irin so yake mata jiya fa ya ce min ya sake ta amma yau ta bar gidan ya bi ta a kidime. Har suka gama shiri suka tafi ina jin zafin abin da Tahir ya yi wanda na san shi ne kishin.

Tahir na isa gidan su Halima ya zarce sai da iyayenta da yayyenta suka zauna sannan ya fadi abinda ta aikata har ta tsinci kanta a halin da take ciki a yau, da gore goren da suka yi wa juna ita da latifa wanda yasa ya sahale mata aurensa, gaba daya suka yi kan Halima ban da mahaifiyarta da ke ta faman kuka, yayanta wanda take bi ya yi tsalle ya karyo iccen bishiyar dalbejiya da ke tsakar gidan ya kwada mata ya daga zai kara mata wata gwoggon su da ke zaune cikin gidan ta tare amma duk da haka sai da ya kara hambare ta ta fada cikin wata kwata da ke tsakar gidan, ta kuwa fashe da kuka dan azabar da ta ratsa ta ga ta duka ga ta ciwonta da ta fama. Tahir ya mike ya bar gidan dan yadda gidan ya hargitse a tsaitsaye ya shiga gidan su sai ya dauko hanya duk da haka sai dare ya iso. A bedroom ya same ni yaran sun ruda ni, Daada tana dakin su ita da su Mimi, Hadiza bata gidan sun fita da Kamal. Barka da zuwa nayi masa sai ya karbi Sadiq na zauna ina ba Sudes nono, sai da ya koshi na karbi Sadiq ina gama ba shi goya shi nayi muka fito na ba shi abinci ya tambaye ni Hadiza na ce tana wurin mijinta ya ce “Ke ma ki bi naki mijin mu je mu yi kwanciyar mu” na ce “A’a sai da ya raka ni har daki, muka kwanta tare da yaran sai shi ma ya tafi ya kwanta, Hadiza bata shigo ba sai da na soma barci.

Da safe na fito gaishe shi yana zaune a falo da kofin tea a hannu yana kurba ganin yana waya sai na samu wuri na zauna abinda na fuskanta da mahaifin Basma yake wayar ya ce ta dawo dan zamu tare sabon gidan mu, amma sai mahaifin nata ya ce A’a ba za ta dawo ba dan kayan dakinta da aka yi order ba su zo ba zai yi tafiya sai ya dawo sai ta dawo. Da ya gama wayar murmushin da ya yi min da gani na karfin hali ne gaishe shi nayi ya tambaye ni ya muka kwana na dan jima wurin sa kafin na tashi na koma dakina.
Kwanakin da suka biyo baya shiri muke tayi na gyaran jiki ni da Amarya Hadiza wadda na lura yanzu wani irin so take wa Angon nata, ni dai ce Tahir yaki barin gyaran nawa ya dire kulllun kawo min hari yake. Tashin mu kuma ya ki fadin rana ya ce mu zama cikin shiri kawai dan haka na shishshiga makota da ake gaisawa na kuma yi wa yan ajin mu na islamiyya.

Wata na guda muka sha bikin tarewar Hadiza wanda Kamal ya matsa ya kasa hakurin in yi arba’in kamar yanda ta ce ni kuma nayi taro sosai har yan gidan mu sai da suka zo ba a maganar yan Kankara wadanda suka zo kwai da kwarkwata, mun mika amarya dakinta kokari sosai Tahir ya yi wurin shirya mata daki, Basma bata dawo ba har lokacin ranar da aka kai ta washegari duka bakin suka koma gidajen su, ina bedroom dina Tahir ya shigo ya same ni “Shirya ki raka ni wani wuri” da mamaki na dube shi “Ina zamu? Bai tanka ba ni ma sai na ci gaba da shirina ganin na gama ya ce “Mu je” na bi bayan sa har inda motarsa take muka shiga ya ja muka bar gidan.
Mamaki na ji ganin sabon gidan mu ya kawo ni, tamfatsetsen gida ne me part hudu sai wurin masu aiki, daga cikin sashen kowaccen mu aka yi mishi nashi wurin, wanda ya ce shi ne nawa ya bude muka shiga na shi ne farko daga ka shiga shi muka fara shiga, kafin muka fito muka wuce nawa three bedroom flat ne daga an wuce falo sai bedroom na farko a wata kwana yake sai biyun sune a tare suna kallon juna na farkon muka fara shiga wanda yake babba ne sosai bayan gado ha da kujeru aka shirya a ciki ya ce in bar wa Daada da yara na ce “To” sai muka wuce sauran guda biyun sai mamaki nake a raina wai wannan uwar dukiyar da aka shirya har ana hangen wadda ta fita, ina nufin mahaifin Basma wanda ya ce ayi mata wanda ya fi namu duk da su bai riga ya sa furnitures din ba suka kara mai. Ya dube ni “Wadannan kuma sune namu” dan kallon sa nayi “Naku kai da wa? ba ga naka can ba ” kai ya girgiza “Na daina raba daki, daga raba dakin ne yanzu ya cuce ni yau kwananki nawa da haihuwa amma guduna kike kin ki dawowa dakina da kwana? Wancan a suna yake nawa amma nayi shi dan Hajiyata ne zan dauko ta ko da ba za su bar min ita duka ba akalla ta rika zuwa tana hutawa” ganin yana nuho ni yasa na soma ja da baya jikina na rawa dan tsanar da nayi wa ciki da goyo, sai dai shi ma din abin a tausaya mishi ne mata hudu ka dawo ba ko daya dole ya shiga wani hali. Ban ankara ba na kai bango ya iske ni ya matse ni rokona yake in tausaya mishi in ba shi hakkinsa kan ba yadda zan yi na sallama ya yi gado da ni biji biji ya min ya kuma tsallake ni ya je ya tsarkake jikinsa da ya fito ne yake ce min zuwa anjima iyalan gidana za su dawo saurin bude idanuwana nayi daga lullumshesun da na fara “Kamar ya za su dawo? Ya ce. “Ke kin dawo kenan” saurin tashi nayi sai ga ni zaune “Wane irin tashi ne haka ba a yi sallama da kowa ba ko Haj Hajara sai dai ta ji na tafi? Ya dubi agogon hannunsa “Idan an kwana biyu kya je ki yi musu, ni fita zan yi ” ya fice na bi kofar da fita da kallo cikin tunani. Na tashi nayi wanka na tsaftace jikina, su Daada suka iso a wurin ta nake ji da ta shiga yi wa Haj Hajara sallama bata same ta ba ta fita. Har wata boyayyiyar ajiyar zuciya na fidda, Indo da laraba suka yi girki wadanda sune suka goyo min yaran.

*MARYAM LITEE*
5/12/22, 13:33 – Buhainat: Sai washegari Hadiza da Asiya suka zo min wuni. Ni kuma da aka kwana biyu na koma can tsohon gidan na kwaso suturuna, da yan abubuwan da nake so. Kayana na yanke rabawa yan’uwana, kamar yanda Tahir ma yan’uwan na shi ya ce su kwashe na shi.

Basma ta dawo kafin dawowarta sai da aka zo aka shirya mata wuri ta dawo da masu yi mata aiki su biyu, ba laifi an samu canjin zama tsakani na da ita, na kan shiga wurinta mu gaisa duk bayan kwana biyu, to ita ma ta kan shigo jefi jefi. Kawu Attahiru ya shawarci Tahir bayan na Asibiti da ake wa Basma kan rashin haihuwarta su gwada addu’a ko Allah zai sa a dace daga likitocin da suka duba ta sun ce za ta iya yuwuwa ta haihu. Kawun ke yo addu’ar a ruwan zamzam, Tahir kuma ya kawo mata. Ni dai sai addu’a nake Allah ya tsare ni da yin gwarne duk da dai iyakata wahalar ciki sai nakuda raino ina da masu taimaka mini, ga yaran na samu ba masu rigima bane musamman Sadiq yana da matukar hakuri ko yaushe hannunsa na cikin baki. Ban kuma ga fuskar tunkarar Tahir in ce zan yi tsarin iyali ba alhali ya dade bai samu haihuwar nan ba.

Wata rana na fito kwashe shanyan kayan yaran da Indo tayi musu ta fita zuwa kasuwa bata kwashe ba, igiyar bayan dakin Basma take, daidai saitin windon bedroom dinta, ina kwashe kayan ina ninkewa muryar Basman na rika jiyowa da wata da ban san kowace ce ce ba “Matsala gare ni Fauziyya, wadda ban taba sanar ma wani ba, ita ta ja min na zama koma baya wurin miji. Ina tunanin kin taba jin ana fadin wasu kyawawan matan kyan zahiri ake basu ba a basu na badini? Kamar yanda wasu munanan matan ake basu kyan badini” sai na ji muryar abokiyar hirar ta ta ta ce “Me kike son gaya min Basma? “Abinda nake son gaya miki ba ni da ni’ima ta yaya mata Fauziyya, Tahir ya taba bani misali da kaza a dafa ta ba gishiri ba Maggie”. “Cabdijam! shi ne kuma kike zaune haka ba ki amfani da magunguna? “Tahir ya nema min na Islamic amma haka nan dai nake ba canji “. “Lallai Basma ke wace iri ce shi ne kika zauna a haka cikin kishiyoyi? Saurin barin wurin nayi cikin wani madaukakin mamaki da ya rufe ni dakina kawai na wuce na hau gado Dama shi yasa Tahir bai damu da Basma ba cikin matansa, duk da kasancewarta macen sakawa a gaban mota? dan duk cikin mu babu wadda tayi kyanta. Wani tausayinta na ji ya kama ni gaskiya Basma tana cikin jarabawa me girma. Sai kuma na ji Tahir ya kara burge ni a karo na barkatai dan ba kowane namiji za ki kasance da wannan matsalar ya yarda ya zauna da ke ba wulakanci, ko wani banbanci. Motsin da na ji yasa ni daga kai “Tahir ne rike da hannun Areef da Mimi yanda na dubi fuskarsa ba walwala ni ma sai na tsuke tawa, yaran suka hawo gadon suka haye ni suna tumurmusa ta, shi dai yana tsaye yana kallon mu “Ki shirya gobe mu je Dutsinma ki wuni sai mu wuce Kankara mu kwana jibi mu dawo”. Ban amsa shi ba dan wani takaici da ya kulle ni shi ma daga haka juyawa ya yi yaran suka sauka da gudu suka bi shi.
Tun haihuwata ban je gida ba. Kullun fama nike da Tahir yana cewa in saurare shi, har Sudes ya yi wata hudu da ban da yanda zan yi da shi sai na fara mishi fushi a satin nan, shi ma sai ya share ni dan haka a yan kwanakin nan ni da shi ba me shiga harkar wani, wai kuma yanzu ya zo yana gaya min wuni daya zan yi, hawaye na ji na taho min na share har kanwata Aisha ta haihu sun yi sabon gida sun tare, dadi daya na ji gobe sunan matar yayana Isuhu zan ga yan’uwa gaba daya a gidan sunan. Wayata na janyo na kira Ummata labarin zuwana a gobe na bata, sai na kira Hafsa da muka ajiye waya shiri na soma.

Washegari sammako muka yi muka kama hanya bamu tafi da Daada ba dan mun bar mata Areef da Mimi daga Sadiq sai Sudes muka tafi da su sai Hussaina dan ta taimaka min da hidimar yaran. Mun shiga Dutsinma tara na safe kai tsaye gidan mu muka sauka, mun shiga tare da Tahir daga bisani ya fita ya bar ni nan Hafsa ta zo ta same ni sai muka tafi gidan sunan tare, bayan na shiga gidan su na gaida mahaifiyarta. Na shiga cikin yan’uwana ana ta hira sai Aisha ce bata zo ba an ce ciwon nono take fama da shi, na ce idan zamu wuce zamu biya in gaishe ta in mata barka. Na idar da sallar La’asar ina gyara fuskata kiran sa ya shigo in fito nayi sallama da kowa Nura kanena da Aunty Wasila ta kira a waya ya kawo mata sako na nemi mu je tare ya nuna min sabon gidan nasu, sai da na shiga motar na zauna sai na fada wa Tahir mu dan biya gidan kanwata da ta haihu in yi mata barka in kuma gaishe ta dan tana fama da ciwon nono, agogonsa ya kalla “Ban san magrib tayi min a hanya” na ce “Ba dadewa zan yi ba” na leka na ce Nura ya shigo shi ya nuna mana hanya har muka kai gidan kofar gidan akwai shaguna gaban shago daya a ciki Maza ne zaune su uku. Mun fito ni da Nura ina sakale da da Sadiq a kafadata Nuran ya dauki Sudes, daya daga cikin mazan da ke zaune ya taso a take na gane shi, duk da jiki da ya yi akan yanda na san shi shekarun baya Abakar irin dogayen mazan nan ne masu alamar karfi farin bafulatani, nufo ni ya yi ni kuma nayi saurin shigewa cikin gidan gabana na faduwa, sai ya karbi Sudes hannun Nura ya kuma hana shi tafiya yana mishi tambayoyi game da ni.
A cikin gidan na samu Aisha ta samu sauki hira kadan muka taba na mike sai godiya take min kan sakon da na aiko mata lokacin da ta haihu, ta sa hijab ta biyo ni dan ta gaida Tahir har lokacin Abakar na dauke da Sudes, Nura ya karbe shi muka karasa gaban motar, Tahir ya sauke glass suka gaisa da Aisha ta koma ciki Nura ma yaron ya miko ma Hussaina ya ce ba sai ya bi mu ba mashin zai hau zai shiga kasuwa. Na zauna gabana ya kuma faduwa ganin yanda fuskar Tahir ta koma, ya ja motar muka bar wurin text na tura ma Nura na tambaye shi sun yi wata magana da Tahir ne raply ya maido min duk kan su sun tambaye shi. Gabana na ji ya tsananta bugu, na lumshe ido ina jero addu’ar ALLAHUMMA LAA SAHLA ILLAH MA JA’ALTUHU SAHLAN WA’ANTA TAJ’ALUL HUZNA IZAA SHI’ITA SAHLAN Kukan Sadiq yasa ni bude idona jin kuma Tahir bai ce mu ci kan mu ba ya kara tabbatar min cikin fushin yake har na samu yaron ya yi shiru. Wurin Haj muka fara sauka har aka yi sallar Isha’i ina wurinta sai ga Hadiza ta shigo dan suna garin sun zo duba uban mijinta da ya karye sai da muka gama hira ta wuce gida ni ma muka tafi namu gidan ni da Hussaina shirin kwanciya muka yi muka kwanta na dade barci bai dauke ni ba jin shiru Tahir bai shigo ba, sai da na farka cikin dare na gan shi kwance a falo kan kujera.
Ko da muka karya da safe shirin tafiya muka fara, karfe tara na safe muka fita zuwa sasan Haj, yaran ta ce a dora mata kan cinyarta tana mana maraba ina cikin gaishe ta Tahir ya shigo shi ma cikin shirin tafiyar yake ya zauna ya fara gaishe ta ya ce Ku shirya Haj yanzu zamu wuce” ta dube shi “Amma ka daure ku shiga ku gaida malam Hashimu, na gaya maka mashin ta kade shi ya karye a kafa” dan bata rai ya yi ” Kin dai matsa Haj, na bada sako a ba shi, amma ko abinda zai tuna min da Halima ban so ballantana in shiga gidan su in gan ta”. Ta ce “Ka dai daure, ai ba dan ita za ka shiga ba ” ya dauki Sudes ya mike Haj ta min “Ke ma tashi ku je tare ” na mike dan dama ina son zuwa dakin Hadiza na gidan amma ban san yanda zan yi in shiga gidan su Halima ba. Yana tafe ina biye da shi Hussaina na rike da Sadiq, a tsakar gida karkashin bishiya aka yi ma tsohon shimfida, mutan gidan suna ta sannun ku da zuwa, muka zauna a tabarmar da aka shimfida mana muka gaida tsohon yana ta shi ma Tahir albarka da sakon da ya aiko mishi suka karbi Sadiq sai murnar ganin sa suke, mahaifiyar Halima ta karbi Sudes sai sannan na lura da Halima kan wata shimfida nesa da uban gaba daya ta dada fita hayyacinta kanta a kasa yake kanwarta baby ta je ta dora mata Sadiq a cinya, ni dai mikewa nayi na shiga wurin Hadiza mun gaisa nake tambayarta yaushe za su dawo? Ta ce da dai ta roke shi ya bar ta sai wani weekend din idan ya shigo sai su koma tare, amma daga zamu tafi da Haj gobe da safe idan zai yi sammako za su koma tare. Tare da ita muka fito ban ga Tahir ba na san ya fice na ajiye wa baban Halima kudi gefen shinfidar sa nayi musu sallama muka tafi tare da Hadiza, mun samu Haj ta kintsa sai muka yi sallama da mutanen gidan muka kama hanya.
Kamar yanda Tahir ya ce da isar mu dakin shi na bude nayi wa Haj iso, su Laraba suka tarbe mu da abinci, har lokacin Tahir fushin sa yake sai da muka zo kwanciya ya yi min tas! Dama ina son ganin tsohon mijina dan in wulakanta shi na ja shi ya je ya gan shi. Duk rantse rantsen da nake mishi bai sa ya saurare ni ba, nayi kuka me isa ta har sai da na ji kaina ya fara ciwo na kwanta lamo zuciyata na min zafi.
Kwana biyu ya dauka yana fushin ana ukun na kwanta sai mutum na ji bayana na san ya huce kenan, kwace jikina nayi na sauka na bar mishi gadon dayan dakin na shiga sai dai abin mamaki babu key din kofar jiki dole na fito da na rasa ina zan nufa sai na shige dakin Haj zaune take kan kujera rike da carbi, gadonta na haye na kwanta ta ce “Ina yaran? Na ce “Sun yi barci” sai ga Tahir zama ya yi suna hira sama sama kafin ya ce Ki zo mu je mu bar Haj ta samu ta kwanta” in bangon da ke dakin ya tanka ni ma na tanka Haj ta ce “Tashi Ummulkhairi kin baro yaranki na ce “Ki yi hakuri nan zan kwana ” haba ta rike “Wane irin nan? To akwai abinda kayi wa yarinyar nan me hakuri Sodangi, har ka kure hakurinta. Yi hakuri, Ummulkhairi ki je wurin yaranki” kuka na kama yi dan bakin cikin azabtar da ni da ya yi na rashin magana da baya min. Haj ta rufe shi da fada ta inda take shiga ba nan take fita ba karshe ta rarrashe ni na sauka gadon ina goge fuskata da dankwalin kaina na fita dakin na yi sa’a yaran ba wanda ya motsa, na kwanta can karshen gado Tahir ya hawo gadon ya kamo ni yasa a jikinsa albarkacin hakurin da Haj ta bani na hakura rarrashina ya shiga yi har ya ciyo kaina na hakura zuwa safiya mun shirya radam

Sati guda da dawowar mu sai ga yayyin Tahir su biyu, yaya babba da yaya magaji, a dakin mahaifiyar su suka yi masauki ni kuma na tsaya tare da su Laraba muka shirya musu abincin tara me kyau. Sun zauna tare da Tahir da mahaifiyar su wai daga gidan su Halima ne suke ta aike suna rokon a basu Sadiq, dama na ji wurin Hadiza ta ce tun zuwan mu Halima ta ga danta ta tashi hankalin kowa wai a karbo mata danta idan yana hannunta Tahir zai rika daukar dawainiyarta. To duk yadda suka kai ga bugawa basu ciyo kan Tahir ba a ranar suka juya. Sati daya tsakani aka kara tado wasu dattawa hada tsohuwa dan yadda ta birkice musu nan Haj ta zaunar da Tahir ta ce ya basu ba’a jayayya kan da Allah ya raya shi,cikin matukar bacin rai ya zo ya karbe shi a hannuna ya kai musu. Duk da sabo da nayi da yaron kowa san barka yake min da aka karbe shi. Wata guda kuma da karbarsa ya kamu da bakon dauro wanda ya yi mishi mummunan kamu suna ta aike a bada kaza a bada kaza na magani Allah ya karbi ransa wanda aka ce Halima dan karamin hauka tayi.

Allah ya taimake ni har sai da Sudes ya shekara uku sannan na samu wani cikin, cikin hukuncin Allah kuma tare muka samu da Basma yammata muka haifa duk kan mu, inda na hada yarana hudu, Tahir ya sauya mana gida sai ya bada wannan haya ya gina wani can kusa da gidan su Asiya ya ce wancan saboda part biyu da ba mutane ka da su lalace zaman mu lafiya da Tahir har Basma dan ita din ba me matsala ba ce. Tsakani na da Ubangiji sai godiya bisa ni’imominsa a gare ni

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Godiya ga Allahu subhanahu wataala da ya bani ikon kammala wannan labari kuskuren da ke ciki ina neman Allah ya yafe min ina fata za a dauki abu me amfani a watsar da mara amfani
Bissalam
Taku
Maryam Ibrahim litee malumfashi
Mu hadu a RANAR NAKA

*INA ROKON KU GWIWA TA A KASA DAN ARZIKN MANZON RAHMA KAR WANDA YA MAIDA MIN LABARIN NAN DOCUMENT A BAR SHI A HAKA IDAN KANA FATAR SAMUN RAHMAR ALLAH NA HADA KA DA ALLAH DA GIRMAN MANZON ALLAH KAR KA MAYAR MIN DA SHI

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *