TANA RAINA CHAPTER 66

Tun kafin suhail ya k’ara yaga call d’in mum, ya d’auka hello mum gani a hanyan zuwa, mum tace tose ka iso.
Bayan suhail ya isone mum take tambayanshi waime ke faruwane tsakaninka da hafsat? Suhail yace meta gaya miki mum? Mum tace ta dawo tanata kuka wai ita idan bazaka zab’a ko ita ko sabreenba tota hakura. Mum tace meya faru ina jinka? Suhail yace mum matsala muka samu amma na bata hakuri kuma nace karta tafi amma dana shiga wanka kafin in fito senaga bata nan?. Mum tace to suhail nidai abinda zan gaya maka shine kaji tsoran Allah duk amana suke agunka kuma duk wacce ka zalunta a tsakaninsu Allah yana gani, dan haka ka kiyaye ka zama mai adalci a tsakaninsu dan Allah? Suhail yace kiyi hakuri mum insha Allah hakan bazai sake faruwa kuma nagode?. Mum tace to Allah ya maka albarka Allah ya baku zaman lfy, yace ameen sega hafsat ta fito daga d’aki mum tace hafsat kiyi hakuri ki bishi ku koma kinji? Hafsat tace ni wlh bazan bishiba mum sedai ya zab’i d’aya a tsakaninmu?. Mum tayita rarrashin hafsat ita da suhail d’in amma sam hafsat taqi tace sam sedai ya zab’a?.

Mum taga dai da gaske hafsat takeyi se tacewa suhail to kawai inaga ka raba musu gida zaifi, ke kuma hafsat kiyi hakuri bazaiyu ya zab’i d’aya daga cikinkiba za’a raba muku gida ko wacce da nata. Hafsat tace eh na yarda amma kuma ni bazan bar wannan gidanba sedai ita ta fita?. Suhail zaiyi magana kenan se mum tace hakan za’ayi suhail ka nemawa sabreen wani gurin daban☺.
Suhail yace to shikenan mum zan nemi gidan haya se in sata kafin inyi mata nata?. Dad’i hafsat taji? se mum tace toku tashi ku koma yaushe zaka samawa sabreen d’in gidan? Suhail yace zan tambayi wani abokina☺duk yadda ake
ciki zan gaya miki. Mum tace to shikenan sannan hafsat ta fito da kayanta suka tafi.

Duk tunanin suhail shine yadda zai fiskanci sabreen da zance?. Tunda suke tfy babu wanda yace komai har suka isa. Lokacin sabreen tayi musu breakfast suka shigo tare bayan hafsat ta mayar da kit natane seta fito suka zauna a palo dukkansu. Suhail yace hafsat ina sake baki hakuri akan abinda muka miki ina fata zaki yafe mana? Hafsat tace bakomai ya wuce?, suhail yace mungode kuma ranan da sabreen zata fita girki zan rama miki kwananki kinji? Dad’i taji memakon ta e ta yafe shima se tace toh harda murmushinta?.suhail ya juya ya kalli sabreen yace inaso kibawa hafsat hakuri akan abunda muka mata. Sabreen tace hafsat kiyi hakuri?, hafsat tace aiya wuce sedai a kiyaye gaba?.
Suhail yace to Alhamdulilah magana na gaba shine zan raba muku gida?. Dad’i sabreen taji har cikin zuciyanta amma bata nunaba sam. Ita kuwa hafsat se kallon yanayin sanreen takeyi?. Suhail yaci gaba da cewa sabreen kiyi hakuri hafsat zata zauna anan ke kuma zan nema miki wani gidan?. Atake hawaye ya fara zuba daga idon sabreen? kome dalili oho? Daga suhail har hafsat sunga kwallan idontan, itadai hafsat dad’i taji sosai?. Suhail kuwa tausayin sabreen ne ya kamashi?ya rasa mezaice mata seta mik’e tare da ce musu ga abincinku akan dainning sannan ta wuce d’akinta tasa key.

Bayan sun gama cin abincine suhail yaje yanata bugawa amma sam tak’i bud’ewa kuma bayajin muryanta. Suhail ya pls wifey let me in okey?, amma sam tak’i harya gaji ya koma d’akinshi ya kira phone nata shima tak’i d’auka seya rabu da ita .
Sabreen bata fitoba se 4:30pm ta wuce kichine ta d’aura abincin cikin k’ank’anin lokaci ta gama ta shirya komai sannan koma d’aki tayi sallan magrib da isha sannan tayi wanka tasa english wears riga da siket ta fito su hafsat zuna zaune a dainig babu wanda yace komai har suka gama ta wuce da’akinta. Suhail yayiwa hafsat seda safe sannan ya wuce d’akin sabreen lokacin ta kwanta da kayan jikinta dayake basu da nauyi.

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *