Zainab da ke kwance ta miƙe cikin tashin hankali jin ƙarar A.m taruga ɗakin da gudu.Abin ta gani ya yi matuƙar razana ta,ɗorahannunta ta yi aka tare da sakin ihu,saboda ta rasa me za ta yi.
Girgiza sa ta fara yi tana faɗin.” A.m ka tashi don Allah kar ka mutuka bar ni!Ka san ba zan iya rayuwa babu kai ba.”
Ta kalli Juwairiya da take cikin wani hali gani ta yi kamar babu rai ajikinta,sai jikinta ya kama rawa ta rasa baƙin ciki za ta yi?Ko akasinhakan.
Dabara ta faɗo mata ta ruga da sauri ta ibo ruwa ta watsa masa.
Buɗe idanunsa ya yi da sauri tare da miƙewa ya kamata kamar zaiɓallata ya ce.” Ina Juwairaaah ta mutu ko?”
Zainab da ta kasa magana idanunta ta kai gurin da take kwance raikwakwai mutu kwakai.
Da sauri ya bi in da ta kalla da idanunsa sai ya miƙe zubbur ya nufeta ya ɗauke ta zai fita da ita.
“ A.m dare ya yi fa yanzu ina zaka kai ta?”
Ta yi masa tambayar da ko kallonta bai yi ba ya fice,ba ta ankara basai jin tashin motarsa ta ji ya fice da ga gidan.
A.m da yake tuƙi cikin tashin hankali Allah ne kawai ya kai shiasibitin.
Ba tare da ɓata lokaci ba likitoci suka rufu a kanta,wacce ba ta sanhalin da take ciki ba.
Jikinsa har rawa yake yi wani irin tashin hankali ya ziyarce shi,jiyake kamar zai yi hauka,domin ya rasa asarar babyn ɗinsa ne bai soya yi,ko halin da take ciki ya saka shi cikin wannan halin.
Wayarsa ya zaro a cikin daren ya kira A.k ya fi sau goma sai dai baiɗaga ba,sannan ya kira iyayensa ya sanar musu.
Ya yi shiru yana tsaye a gurin ɗakin da aka kwantar da ita sai leƙe tawindo yake yi,amma duk iya ƙoƙarin da likitocin suke yi ba tafarfaɗo ba,sai ya duƙar da kan sa yana jin tsananin tausayinta,yayinda hawaye yake bin ƙuncinsa.
“ Na shiga uku! Yanzu in yarinyar nan ta mutu ya zan yi?”
Ya tambayi kan sa cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa.
Salati ya ji tana yi cikin murya ƙasa-ƙasa sai kawai ya danna cikinɗakin ya durƙusa a kusa da gadonta ya kama hannunta ya riƙe.
“ Juwairiya ina son ki!Ina son ki!! Ina son ki!Kamar yarda kika faɗamini na maimaita miki,na roƙe ki don Allah kar ki mutu ki bar niwallahi ina son ki,ban san cewa son ki nake ba sai yau da na ga za kimutu ki bar ni.Na haƙura da baby kar ki mutu don Allah ki tashi zanrayu da ke ko da ba za ki ba ni baby ba.”
Cikin wata irin murya yake maganar yana ji kamar ciwon ya dawojikinsa,ganin yadda take shan wahala matuƙa.
Juwairiya ta buɗe baki za ta yi magana amma sai wani irin nishi yahana ta,ta rufe bakin da sauri tana salati a ranta,don ta sadaƙarmutuwa za ta yi,wannan nishin na cire rai ne.
Kawai sai suka ji kukan jariri yana ta tsala kuka sosai duk ya cikaasibitin da ihu.
A.m ya saki hannunta da ta rufe idanunta jin wani irin ciwo ya ta sokamar ba ta haihu ba.
Ya kai hannun da sauri zai ɗauki babyn yana faɗin.” Alhamdulillahiadada ma khalaƙa.”
Da sauri wata nurse ta riga shi ɗaukar babyn,sai ya duƙa ƙasa yanajin kamar an yi masa bishara da gidan aljanna.
“ Doctor Marwan ina ga kamar ƴan biyu ne za ta haifa da wani jariria cikinta.”
Doctor Bilal ya faɗa cikin razana ganin ciwo ya koma sabo.
“ Anya kuwa ba na tunanin haka saboda scanning ɗinta ya nunamana yaro ɗaya.”Ya ba shi amsa da shakku a fuskarsa.
Tun suna tunanin cewar mahaifa ce za ta biyo har suka yadda ƴanbiyu a cikin.
Ganin irin wahalar da take sha A.m kuma kamar zai zare kamata yayi ya riƙe,sai murna ta koma ciki.
Likita ya bada umurnin a fitar da shi saboda yana ɓata musuaiki,duk lokacin da ya ga sun danna cikinta ta saki ƙara mairazanarwa,sai ya ware zai bugi likitan.
Duk yadda likitan ya so ya raba hannun su, amma ina ya ƙasasaboda sun riƙe junansu ƙaƙam,sun ƙi saki daga ƙarshe kan dole yaƙyale shi.
Duk iya ƙoƙarin su jaririn ya ƙi fitowa,amma kuma in suka sakahannun suna taɓa kan sa.
Hankalin su ya tashi matuƙa gashi a lokacin ƙarfinta ya ƙare,komotsi ba ta iya wa balle ta yi nishi,sai idanunta da take wulƙita sucikin raɗaɗin azaba.
“ Ina gani ya kamata a kira doctor Garkuwa don shi kawai zai iyamaganin wannan matsalar,ƙila ya ce a shirya mata aiki fa,domin bata da ƙarfin da za ta iya nishi yaron ya fito.”Doctor Bilal ya ce dadoctor Marwan.
“ Ba ya ƙasar ka san ya yi tafiya zuwa ƙasar America akan ƙwallongasar ƙafa da zai buga.”
“ Kai wai me ya saka doctor Garkuwa yake yin haka! Sai ka buɗeasibiti amma ba za ka rinƙa kulawa da patient ba,kullum ba shi daaiki sai zuwa ƙasashen waje akan ƙwallon banza,wanda iyayensa basa son yana yi Yanzu ya yake son mu yi da wannan baiwar Allah datake cikin wani hali?”Ya faɗa cikin tashin hankali.
“ Waye wannan Garkuwa mahaukaci ne shi zai fifita ƙwallon ƙafaakan mutane?Na rantse in ya kashe mini mata sai na kashe shi kokuma kotu za ta raba mu.”A.m ya ce cikin hargowa bayan ya shaƙelikitan.
Da ƙyar ya ƙwace kan sa ya ce.” To sakar mini riga shi ma ɗan zafinrai ne kamar kai sai ka bi shi can ku ƙarata.“Ya ce tare da ƙwacerigarsa.
“ A nemo amininsa doctor Isa abin takaici jiya ya gama duting dar.“
“ Ashe asibitin mahaukata na kawo matata ba ku dahankali,asibintin ya zama ƙyalƙyali banza,ba ku damu da halin datake ciki ba,to bari na gaya muku in har Juwairiya ta mutu kuma duksai na kashe ku.”
Likitan ya buɗe baki zai yi magana da fushi ganin ya raina ƙoƙarinsu,sai suka ji kukan jariri da ya kusan faɗowa ƙasa,wanda taimakonAllah kawai ya fito da shi daga cikin.
“ Wayyo Allah na! Ƴaƴa biyu! Wallahi ƴaƴa biyu kika haifa minigaskiya aurenmu mai albarka ne.“ A.m ya faɗa yana kallon jaririnda ya daina kuka saboda wahalar da ya sha.
“ Na yi mata allurar tsaida jini amma ya ƙi tsaya fa.”Nurse ɗin ta cecikin tausayin wahalar da take sha.
Shiru kawai ya yi ya tsaya yana tunanin wace alllura zai ƙara yimata,kafin wannan mahaukacin mijin na ta ya farga.
Hankalin su ya tashi ƙwarai duk yadda suke ɓoye-ɓoye sai da yafahimta,ya riƙe hannunta ƙam yana hawaye.” Juwairaaah na gatashin hankalin dama haka mata suke wahala in za su haihu? AllahSarki Momi zan kasance mai yi miki biyayya har ƙarshenrayuwa,zan miki duk abin da kike so duk da na san ko mai na yimiki ba zan taɓa biyan ki ba.Bazan raba ki da yaran ki ba Juwairaahdomin in na yi haka Allah sai ya hukunta ni,wallahi kin biya nikomai da kika haifa mini yara har biyu duka maza.”
Ba ƙaramin wahala su ka yi ba kafin su tsaida jinin,don har idanuntasun fara ƙaƙƙafewa.
Ya tsura mata idanu yana kallon fuskarta da idanunta ke rufe tanasaukar da numfashi a hankali.
Kiran sallar asuba na farko ya sa shi ya miƙe sai kuma ya kallijikinsa,ba tare da ya shirya ba dariya ta kama shi ganin duk wannandiramar da ake kayan bacci ne a jikin sa.
Wayarsa ya ɗauka yana kiran mutane yana gaya musu,don a ranarhar wanda bai kamata ya gaya wa Juwairiya ta haihu ba,sai da yagaya musu,saboda in dai zai ga numba a wayarsa sai ya kira ya faɗamusu.
A.k ya fara isowa cikin asibitin kafin ya shigo sai ga motar suDaddy kowa yana rige rigen shiga,don ko gaisawa ba su yi da junansu ba.
“ Wallahi ta haihu ka gan su ni ma na zama Baba Allah Daddy za surinƙa kirana suna gudu suna bina,kuma fa kama da ni suke yi har databon fuskata.”Ya ce da A.k da ya sawo kai cikin ɗakin yana nunamasa yaran da suke cikin shawul,duk da ba su taho da kayaba,amma tsarin asibitin ne komai na buƙata a kwai.
“ Ikon Allah ka ga sabon shiga yara biyu a lokaci ɗaya! GaskiyaJuwairiya ta iya haihuwa.Amma na kasa gane tsakanin kai da itawanda ya yi naƙudar duba ga yadda jikinka ya ɓace da jini.”Ya faɗayana dariya bayan ya karɓi yaran a ran sa yana ta ya amininsamurna.
A.m ya ji kunya sosai saboda iyayensa da suka shigo shafa kan sa yayi ya ce.” Bari kawai ƴar albarka ta ci baƙar wahala,amma duk dahaka bayan shekara za ta rinƙa kawo mini kyawawan yara irinwaɗannan.“
Momi kuwa rungume yaran ta yi ta saka kuka sosai.” Ikon Allahashe a kwai ranar da zan ga yaranka Abdul,sam ba ka kyauta miniba da ka ɓoye mini wannan lamari,don kawai ka birge wata macecan wacce ta cuci kanta da kanta,wai kai ɗan soyayya haka kawai kahana ni ganin sanyin idanuwana jikokina.”Momi ta ce tana gogehawaye.
“ Sha kuruminki Momi duk da cewa ana shan wahala amma dukshekara za ta rinƙa kawo miki irin waɗannan.”Sai ya haɗa hannunsaya kama mahaifiyarsa ya rungume yana hawaye.
“ Momi tabbas na ƙara girmama lamarin uwa a raina ashe haka matasuke shan wuya kafin su haihu!Mutuwa ce kawai ba ta yi ba.Momizan miki biyayya har ƙarshen rayuwa,ko da wuta kika tura ni zanshiga.”
Kama hannunsa ta yi ta haɗa.” Kana yi mini biyayya Allah ya yimaka albarka ya shirya maka zuriya.” Sai kawai ya saki ƴar ƙarayana dukan A.k ya ce.” Yes ni ma na kai lokacin da za a yi mayarana addu‘a.“
“ Ya A.m ina Anty Juwai ɗin?”Hamdiya ta tambaye sa don burintata gan ta.
“ Kull karki ƙara ce mata Anty ai daga yau ta girma Maman ƴanbiyu za ki ce,saboda kin rage mata matsayi.”Dariya suka kwashe dashi.
Bayyana irin farin cikin da suka shiga abu ne mai wuya musammanA.m, da yake ji a ran sa dole sai ya yi sadaka don bai taɓa tunaninhaihuwa ta farko,za ta haifa mi shi zuƙa-zuƙan yara har guda biyukuma duka maza.
Gida ya dawo don ya yi wanka sannan ya yi wa Zainabalbishiri,saboda ya bar ta cikin jimamin halin da ake ciki.
A lokacin gari ya waye ko da ya dawo tana ɗakinta ga mamakinsasai yaga tana bacci,don haka bai tashe ta ba ya wuce bayi ya yiwanka,sannan ya saka turaren da yake so don ya san daga yau ba zata ƙara yi masa ƙorafi ba.
Wani irin gayu ya yi cikin murna da annashuwa bai taɓa tunani yanasonta haka ba,da ya duba halinta da haƙuri ga kula da ibada sai ya gatabbas ta ya kamata a so ta,uwa uba kuma girkin da take mi shi.
Ya auna tsaƙanin son Zainab da ita wa ya fi so sai dai shi kan sa yarasa ganewa,domin har yanzu yana son Zainab saboda soyayyartadaga Allah ne,bayan nan ga tausayinta da ya cika mi shi rai,ya sancewa za su kai ruwa rana in ya gaya mata abin da kezuciyarsa,amma ya zai yi ita zuciya ba ta da ƙashi,shi kan sa ba yinkan sa ba ne Allah ne ya saka mi shi sonta a cikin zuciyarsa,dominzuciya an halicce da son mai kyaukyata mata.
Ya sauko zuwa falo har ya ɗauki makullin mota zai fita, sai kuma yatuna bai yi magana da Zainab ba,da sauri ya juya zai haye saman,aran sa yana ma kan sa faɗa dole ya yi adalci a tsakanin su.
Matuƙar kunya ta kama shi ganin ta a saman bene tsaye da kayanbacci tana kallon sa,sosai ya ji kunya don fa har ya murɗa kofa zaifita ba tare da ya yi mata magana ba.
“ Inna lillahi! Tabbas zuciyata ta gaya mini yau A.m ya yi sabonabu, wanda ya saka har ya manta da ni Zainab wacce yake iƙirarinba zai taɓa rayuwa babu ita ba.”Ta faɗa yayin da idanunta sukakawo ruwa don ko bai gaya mata ba,farin cikin da ke ɗauke afuskarsa ya bayyana hakan.
Dawowa ya yi da sauri ya hayo in da take.” Tabbas ta haihu Zainabna ci ƙwallon Juwairiya ta haifa mini yara kyawawa har guda biyu.”
“ Wayyo Allah na!.”
Ta faɗa tare da zubewa ƙasa ta dafe kanta tana jin wani irin tashinhankali.“
Kamata ya yi ya rungume ta kalle shi da hawaye a fuskarata.” Nashiga uku da gaske yau ka samu abin da za ka raba mana soyayya dasu?Kuma ba yarana ba?”Ta ce cikin kuka.
“ Haba Zainab ke da za ki yi murna Allah ya albarkance mu da yarahar biyu,bai kamata ki nuna tashin hankali a rana irin ta yau ba.Nagaya miki babu abin da zai saka na raba son da na ke miki har yanzuson ki na nan a cikin zuciyata sa...”
Tura shi ta yi ta miƙe ta ce “ Ka barni na yi kuka domin ya zamadole a rayuwata,haihuwa fa ka yi da wata mace yau ko mutuwa kayi Allah ya cika maka burinka ka samu magaji,ni fa A.m ba zan taɓahaihuwa ba duk da tarin dukiyar da na mallaka.Kaga ya zama dolein yi kuka ko abin da ya fi kuka.”Kawai sai ta rushe da kuka ta kamaƙarfen benen ta riƙe bayan ta miƙe tsaye.
“ Haba Zainab yarana ai naki ne na har abada bai kamata ki ce hakaba,kuma na yi miki alƙawarin ba zan taɓa nuna miki wani abu akanyaran ba,sannnan zan kasance dake har ƙarshen rayuwata in har inanumfashi a duniya.”
Tun Zainab na kuka yana rarrashinta har ya gaji ya miƙe ya ce.” Barina kai kaya ana ta jirana.” Ya fice daga gidan.
Ƙaramin hauka ta yi duk da ta san A.m zai cika mata alƙawarin daya ɗaukar mata,amma ta ji kishin ta matuƙar gaske kamar ta je takashe ta,amma babu yadda za ta yi saboda ta san cewa ta yi sakacisosai.
A ƙalla sai da ta yi sati ɗaya a asibitin sannan ta warware ta samulafiya sosai.
Yara sun ci sunan kakannin su wato Dadddy da Abbu,wayyo Allahzo ka ga murna gurin takwaran Hassan wani irin gata ya nuna musuna ban mamaki.
Momi ta ce a kai Juwairiya gidanta har ta gama wanka,daga nan saiayi taron suna da shagalin bikinta da ba su san da auren ba,ammaA.m ya nuna ina sam hakan ba zai yu ba domin ba zai iya kwana batare da yaransa ba,sai dai in za ta ba shi gurin kwana to yayarda,daga ƙarshe Momi aka ce ta je ta kula da ita,ƙila ya mantayana da wata matar da zai tare a gidan,saboda ta lura yarda takezumuɗin yaran babu abin da ba zai iya ba.
A.m da ya ɗaukar wa kan sa alƙawarin in har mai asibitin ya dawosai ya yi masa nasiha,akan ya kula da asibitinsa don ranar gobekiyama sai Allah ya tamabaye shi akan yadda yake sakaci darayuwar al.umma.
Sai dai ya kama bakinsa ya tsuƙe saboda ganin sa da ya yi,zai iyacewa tun da ya ke bai taɓa ganin mutum mai ɗagawa da girman kaiirin sa,duk da cewa shi ma ya san yana da na sa,amma doctorGarkuwa ya dame shi ya shanye,yana kallon mutum kamar kashiwanda sam A.m bai fahimci haka halintar idanunsa take ba,shi a binda ya ƙara ba shi haushi da shi zuwa da gajeren wando da yake yi aasibitin,wanda ya fahimci dabi’ar sa ne,saboda ya ji ƴan asibitin sunagulmar sa ko waje zai fita da gajeren wando yake fita,kamar zaitsallake wuta.Sai dai kuma matashi ne mai kyau da kuɗi da aji ɗankwallo wanda sunan sa ya zagaye nahiyar duniya.
Sau ɗaya Zainab ta danne zuciyarta ta je asibitin sai dai ta shakuka,ta yi alƙawarin ba zata ƙara zuwa ba,saboda abubuwan da tagani yadda suke ji da ita,don Hajiya Binta take mata wanka,Momikuwa kullum tana asibitin .
Ta sha kuka ta bari a sallamota su yi ta taƙare da A.m ya karɓi yaranita za ta shayar da su ya sallami Juwairiya don zuciyarta za tabuga,wataƙila kuma ta amshi ta yi da Momi take mata,saboda ba zata iya barin sa da ita ba na har abada,duk da ta san ko yau ta bargidan ta fita na har abada ganin yadda danginsa suke nan-nan da itakamar za su lashe ta don so.
Wani irin so yake nuna musu na fitar hankali don a yarda yake ji dasu ko kan sa ba ya ƙauna haka.
Hajiya Binta ta hana shi sakewa da Juwairiya, saboda tun da tahaihu ta canza mi shi babu tsiwa,sai shiru-shiru sai kuma hawaye datake yawan zubarwa in har ya yi mata magana,wanda hankalinsayana tashi matuƙar gaske,ya yi mata tambayar duniya ba za ta amsami shi ba,gabaki ɗaya ta canza mi shi kamar wata kurma,wandahakan yake ɗaga hankalinsa matuƙa.
Zainab ta raina kanta ta muzanta tun tana mamakin halin da yakemata, har ta daina tana kallonsa kawai don ta fahimci shi bai ɗaukeshi wani abu ba.
Ko kwance suke haka zai ɗauki hoton su ya yi ta kallo yana dariyakamar mahaukaci,in har tana son ya yi mata magana to ta ce aiHasan ya buɗe ido ka ya yi kaza,sai ya saki baki ya yi ta zuba yanahira,gabaki ɗaya bai da lokacin ta sai na yaransa.
Duk da cewar Hajiya Binta tana mi shi faɗa amma bai san lokacinda yake aikata hakan ba,shi dai ya san yana musu son mutuwa.
Kwance suke Zainab tana gefen sa da kofi a hannunta tana shantea,domin ya ɗumama mata jiki,kasancewar lokacin sanyi ne.
A.m da waya a hannunsa yana ta kallon video na yaransa da ya yimusu,yau kwanan su sha takwas.
Dariya yake sosai yana kallon Husain da yake buɗe ido sai ya rufeda sauri ya ƙuma ƙara buɗe wa.
Zainab ta miƙe cikin fushi ta fisge wayar da take hannunsa ta kwaɗata da ƙasa ta tarwatse.
Hannu ya ɗaga da sauri zai mare ta ko mai ya tuna ya fasa yadunƙule hannun sa ya saki.
“ A she ba ki da mutunci kishi kike da yarana Zainab?”
Kawai sai ta fashe da kuka ta ce.” Na gaji A.m zuciyata gab take data buga! Ka san yarda nake son ka kuwa?Ka dai na kula ni ba ka dalokacina kullum sai na yaranka ba dole na yi kishin su.Ka sani ko dayaran nan sun dawo gurina ka ce haka za ka rinƙa yi musu,wallahiba zan lamu ta b…”
“ Ya she ki kar ki kawo mini maganar banza! Idan yaran ki ne za kifurta hakan,in har kika ce za ki yi kishi da yaran da na haifa to kinsaka ma kan ki wahala,don ina son yarana fiye da komai Shekarunawa na ɗauka ba tare da na samu magaji ba.“Ya katseta da faɗinhaka.
“ Zan yi kishi da su har ƙarshen rayuwata in har haka za ka rinƙa yimusu,sannan Juwairiya ta haihu don haka ka cika mini alƙawarin daka ɗauka.“
Kallonta ya yi sheƙeƙe ya ce.”Sai ta gama wanka zan tara ku nayanke duk abin da na zartar.”Ya faɗa a ɗaure ya ɗauki wayarsa yakoma ya kwanta.
“ Ai ko wallahi ka ɗauko ma kan ka tashin hankali matuƙar ka ce bazaka rabu da ita ba,domin ba zan zauna ku kashe ni a gidan nanba,son da nake maka ba zai bar ni na iya barin mata kai ba.Bari nagaya maka ka ji ina sonka in har kace za ka haɗa ni da wata zanɗauki mataki sosai kuma na bi duk yadda zan yi na rabaku ban damuda girman zunubin da zan ɗauka ba,domin zuciyata ba za ta iya barma wata mace kai ba,don haka kashedi nake maka da kakkausarmurya!”Ta fice daga ɗakin da gudu tana kuka.