Shiru ya biyo tsakanin su babu mai magana kowa yana tsaƙe-tsaƙe a zuciyarsa,sai kukan Zainab da sheshsheƙa da yake tashi a hankali.
Ko da suka isa gidan da gudu ta fice daga cikin motar ba tare da ta kalle shi ba,ta haye sama kai tsaye bayi ta wuce,tare da sakar ma kanta shower tana wankan dole,don kawai kar ya kula ta.
A.m da ya gaji da zama tashi ya yi ya leƙa bayin don ya tabbata ta kammala wankan,ƙin fitowa ta yi,yana leƙawa ya gan ta a tsuguna tana kuka sosai.
Jikinsa ya yi sanyi sosai shi kan sa bai yi tunanin tana kishin sa haka,don gani ya yi abin ya wuce misali,saboda duk ta bi ta rame kamar ba Zainab ƴar ƙwalisa ba.
” Zainab don Allah ki fito daga bayin nan ki zo mu fahimci juna,karki saka wata cuta ta kama ki.”Ya ce da ita cikin tsananin tausayin ta.
” Ka fita don Allah na dawo gidanka ne don ba zan iya rayuwa babu kai ba,amma hakan baya nufin na sake amincewa da kai.”Iya abin da ta ce mi shi kenan ta ƙara sakin kuka,mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Da ya gaji da tsayuwar jira sai ya fita falo don ya duba lafiyarta,amma sai bai gan ta a falon ba,cikin sanɗa ya leƙa ɗakinta sai ya gan ta kwance tana bacci da sauri ya ja ƙofar ya fita,tare da sakin ajiyar zuciya mai nauyin gaske.
A.m dake tuƙi ya fita don ya siyo musu abin da za su ci,duk da cewar mai aikin da Momi ta kawo musu ta yi abinci,amma ya rasa ta in da zai fara lallashinta,shi kan sa bai yi tunanin haka take ba,saboda ya gaya mata dalilinsa amma sam ta ƙi ta manta komai.
Ko da ya dawo siyo musu abinci ɗakin Juwairiya ya fara zuwa,amma har wannan lokacin tana bacci.
Jikinta ya taɓa sai ya ji ɗumi hankalinsa ya tashi jin zazzaɓi a tare da ita.Wayarsa ya ciro tare da kiran likita don ya duba ta,ya ije mata kayan ciye-ciyen ta ya fice daga ɗakin ba tare da ya tashe ta ba,saboda gudun rigimarta da yake tsoro.
Ɗakin Zainab ya nufa amma sai ya ji ta kulle har da makulli.
Bai yi ko tari ba ya juya zuwa ɗakin sa ya ɗauko spare makulli ya buɗe.
Har yanzu tana zaune bayan ta yi sallar magariba hawaye yana bin ƙuncinta.
” Ya kamata don Allah ki manta komai Zainab kukan ki yana cutar da zuciyata,na yi miki bayani amma kin ƙi saurarata.”Ya faɗa bayan ya tallabo ta jikinsa.
” Na fahimce ka kawai na kasa yadda da abin da ke faruwa a tsaƙaninmu n…”Ya katse ta da cewar.
” Wallahi ba ni da nufin na cutar da ke. Ita ma katsesa ta yi ta ce.” Ya wuce sam bana son ka ko ambaci sunanta don Allah ka kyaleni kawai.”
Ganin haka sai ya ja ta jikinsa yana shafa bayanta,kamar wata ƴar baby yayin da ita kuma ta lafe jikinsa,tana jin ƙaunarsa fiye da ta da.
Ya mantar da ita komai da kalar soyayyar da yake nuna mata, wanda take ji ba za ta iya rabuwa da shi ba,sannan za ta iya zama ajalin duk wata mace da ta yi gigin raɓarsa.
Da a kira salar isha i sai suka yi wanka sannan suka kwanta,a ran A.m na ta addu’a Allah ya sa kar wancan rigimammiyar ta tashe su,saboda sam Zainab ta ƙi yadda ya yi mata bayani.
Juwairiya bayan ta yi salla ta zauna tana cin kwaɗon zogala, wanda ta saka mai aiki ta yi mata tun yamma,saboda jikinta da babu daɗi ta kasa ci.Wanka ta shiga duk da ba ta son ta yi amma jin jikinta yake yi mata wani iri.
Likita da ya shigo ya kira wayarta da A.m ya tura mi shi da cewar in ya zo ya kira ta.
Duk yadda likitan ya so ya yi mata allura ta ƙi, don ita ba ta ga wani ciwon da zai saka A.m ya kira likita ba,ta lura mugu ne so yake kafin ta haihu duk ya tsire mata jiki da allura.
Cikin dare misalin biyu da kwanta kasa bacci duk da ba ta yi ninyar zuwa ɗakin su ba,kamar yadda Hamdiya ta yi ta zuga ta don har text ta yi mata,amma ita tsakani da Allah yunwa take ji matuƙar gaske,wanda take jin za ta iya shiga cikin wani hali kafin gobe.
” Inna lillahi A.m ɓarayi ne suka shigo cikin gidan nan!”Zainab ta faɗa da tashin hankali a fuskarta jin ana ƙwanƙwasa musu ƙofa.
A.m da bai samu ya rintsa ba har sai da lokacin da take tashin sa ya gota,sannan wani nauyaryar bacci ya ɗauke shi.
Ƙara juyawa ya yi tare da rungumo ta amma sai ta ture shi cikin tashin hankali tare da girgiza shi da ƙarfi.
” Na shiga uku! Allah ya sa ba ƴan garkuwa da mutane ba ne suka zo.”Ta faɗa a tsorace wanda ya saka A.m miƙewa da sauri cikin tashin hankali.
Ji ya yi kamar ya ɓoye saboda bai san ta in da zai fara ba.
Ƙofar ya nufa da tsoro a fuskarsa har zai murɗa ta riƙe shi ta ce. ” Don Allah karka buɗe su cutar da kai.”
” Mene ne”.
Ya ce cikin wata irin murya da ya saka ta kalle shi da shakku a fuskarata.
” Tambaya kake mene ne A.m?Ka san waye a tsaye a ƙofar ɗakin ne?”Da tashin hankali ta faɗi tana masa wani irin kallo.
A.m da ya yi tsuru-tsuru kamar ɓarawo a hannun mata sai kawai ya buɗe ƙofar ta bayyana, da take tsaye da kayan bacci duguwar riga a jikinta da hijabi da ta ɗora ga ɗan titsin cikin da ya fara fitowa a jikin hijabi.
Zainab ta girgiza idanunta ta ƙara ta kuma kallonta da ta yi tsaye fuskarta cike da tsiwa,tana musu kallon kamar ta ga kashi har da wani ɗan girgiza take.
Ta ƙara girgiza idanunta ta kuma goge fuskarta a ranta tana tunanin anya Juwairiya ce ta canza kala ta dawo haka.
” Ka san lokacin cin abincina ya yi shi ne baka girka mini batun ɗazu cikina ke ciwo.”
Ta ce da shi ba tare da ko fargaba tana kallon su duka da tsuka tsaya ƙiƙam kamar wasu gumaka.
A.m ya yi wani iri da shi ya kalli Juwairiya sannan ya kalli Zainab da ta yi suman tsaye,har yanzu ta kasa yarda ita ce a gabanta.
Sai haushin kan sa ya kama shi gani yake kamar bai cancanci ya zamo mijin mata biyu ba,duba ga dukannin su tsoron su yake yi.
” Innalillahi!Momi na shiga uku da gaske wannan yar iskar yarinyar da ka ce tana gidanku ashe tana gidan nan?”
Ta faɗa tare da cakume shi tana kuka kawai sai ta ɗaga hannunta za ta mare shi da sauri ya riƙe ya ce.” Zainab ki kula har yanzu da saurana don ban zama irin mazannan da mace za ta rinƙa duka ba.Na so na yi miki bayani amma ke kullum ba kya yi mini uzuri ki saurare ni.Abba ya tilasta mini na kawo ta gidana amma da zarar ta haihu zan sallame ta.”
Zainab ta kalle shi ta fashe da kuka ta ce.” In har kana son zamana a gidan,nan ya zama dole ta bar gidan nan don na tsaneta ba na son ƙara kallonta,kuma har wani abinci kake mata A.m tun da nake da kai ka taɓa dafa mini ko ruwan zafi.”
Hunnunta ya kama ya galla ma Juwairiya harara ya ce.” Saboda babynmu nake yin hakan kin san mai ciki duk abin da ta ce dole ayi mata,kin san Allah da ke kike da cikin nan in da ana yi ma mutum numfashi to zan sauwaƙe miki yin sa,don haka duk abin da nake yi mata saboda baby ne,kuma da zarar ya fita shikenan.”
Ya ce mata da murya sanyayya yana kallon Juwairiya a wulaƙance.
” Gaskiya dole ka yi magana da Abba ta koma gidanku na yarda,ko miliyan nawa zan ba da in har za a kula da ita amma ta bar mini gidana.”
Ta faɗa masa cikin karayar zuci saboda ganin yadda ta koma ya firgita ta.
Tsaki ta saki ta kalle su duka ta ce.” Kan ku ake ji ni kaina na ƙosa na bar wannan gidan da baku san haƙƙin kowa ba sai kanku.”Ta juya ta koma falo.
“Yanzu da gaske girkin za ka ka yi mata da wannan daren?”Kawai sai ta saka kuka ganin yana saka doguwar riga.
“Yarona zan yi wa girki karki damu cikinta ya shiga na wata huɗu, kin ga mun kusa yarda ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda.”Ya ce da muryar rarrashi.
A lokacin da ya fita kifa kanta ta yi ta din ga kuka sosai baƙin ciki cushe a zuciyarta,tana jin wani ɗaci na ganin ta a gidan,wasu irin abu da suka faru dama waɗanda ba su faru ba ta rinƙa hasasowa,sai ta ƙara sakin wani kukan tana buga kanta da gini.
Da ga ƙarshe kasa zama ta yi ganin uku har ta gota ta sauko ƙasan,sai ta ga a wannan lokacin A.m ya kammala ɗanwaken ya kawo mata,amma saboda muguntar da ta saba ta ce sai ya jira ta ta gama.
Da takaici ya ishe ta komawa ɗaki ta yi tana ta kuka sosai a yadda ta ga Juwairiya, daga yau ta ije aiki har sai ta haihu ta bar musu gidan,don ba za ta iya barin ta da shi ba a cikin gidan.
Kamar yadda suka saba kwana a falo haka ta kasance yau ita Juwairiya ba ta yi bacci ba,sai shi da yake ta gyangyaɗi daga ƙarshe bacci ya kwashe shi.
Ta gyara zamanta ta ci gaba da kallo tana karanta lintafin Hausa novel mai suna(Burin duniya na Jamila Lawal Zango Jamcy)Wanda Hamdiya ta tura mata saboda ya rage mata kaɗaici.Sai dai tsoro da tashin hankalin da yake cikin lintafin da tausayin Khairi da kuma takaicin doctor Garkuwa ya sa ta ije lintafin, da tsananin tsoro ta kashe wayar gabaki ɗaya.
A.m da ya ji kiran salla zubbur ya miƙe ya kalle ta wadda tsoro ya sa ta baccin dole.
Ji ya yi kamar ya shaƙeta da sauri ya haye sama ko tashin ta bai yi ba,saboda takaicin gani girkin da ya yi mata ko guda uku ba ta ci ba.
Ya tura ɗakin ya shiga har yanzu bacci take yi saboda bayan kukan da ta sha bacci ya ɗauke ta ba don ta so ba.
” Zainab ki tashi kiyi sallah.”
Sai ta yi tsuru tana kallon sa yayin da hawaye yake bin gefen fuskarta.
” Na rasa ta yadda zan fito na yi miki bayani ki yarda da ni Zainab.”Ya faɗa muryar kaukausa domin shi yana ganin bai kamata ta ɗaga hankali a kan yarinyar da baya jin sonta a cikin ransa ba.
” Na gaya miki ba so a cikin auren nan na yi shi ne don kawai mu samu ɗa,kuma na yi miki alƙawarin da zarar ta haihu zan cika miki alƙawarin da na ɗaukar ma ki ba ta saki uku.”
” Zuciya ce take ɗar-ɗar amma tun da haka ka ce shikenan ka yi ma Abba magana ta koma gidanku.”Ta ce mishi lokacin da ta yi hanyar bayi.
” Wannan ba zai yiwu ba domin Abba ya ce dole sai na zauna da ita,amma ni ba zan iya zama da wata mace ba bayan ke,ki yi haƙuri har ta haihu sai mu bar garin bayan na saketa mu koma London sai mun ɗauki tsawon shekaru kowa ya manta mu dawo.”
Rungume shi ta yi tare da manna mi shi kis ta ce.”Na yadda da kai mijina na san duk wannan matsalar ni na kawo shi,domin da ban biye wa son zuciya ta ba,da son gayu da ƙyalƙyali na haihu ko da ɗaya ne, da baka janyo Juwairiya cikin rayuwarmu ba,na yi takaici sosai ban san cewa kana son yara haka ba,sannan ba za ka iya rayuwa dole sai ka so ka ga ɗanka.”
Sai kuma ta sake shi ta sa kuka ta ci gaba da cewa.” Kaicona da na bi ruɗin duniya na ƙi bari na haihu ko sau ɗaya ne,ina ma matan da suke shan maganin hana haihuwa don wani buri na su,ko mazan suka umurce su za su daina duba ga irin yadda na tsinci kaina cikin nadama.Don Allah A.m karka karya alƙawarin da ka yi mini,saboda kishin ka zan ije aikina har Juwairiya ta haihu na ƙosa ta fita daga cikin rayuwarmu ba zan iya barin ka kai da ita ba,wallahi jiya da na gan ta hauka ne kawai ban yi ba,saboda duk kyan da na ke da shi na tsorata da ganinta.Ashe haka mata suke canzawa in suna da ciki.”
Riƙe ta gam ya yi har cikin ran sa yana jin tausayinta don in ya kalli cikin Juwairiya ji yake yi kamar zai sume,to ina ga ranar da ya fito duniya ya ga ɗan mutum ace na shi.
” Na yi miki wannan alƙawarin ba ki da matsala.”
Duk wani abun da A.m zai yi ya kwantar da hankalin Zainab yana yi,abu ɗaya ne ya ji sam ba zai iya ba yadda ta hana shi ko da kallon Juwairiya,domin ko motsi ya yi idanunta na kan sa.
Gabaki ɗaya ta ije duk wani yawonta da take nadamar yin sa da ta yi,tana zaman gida sai ta yi kwanaki ba ta fito ba.
Duk sadda ta ga cikin Juwairiya da yaƙe ƙara girma, sai ta shiga ɗaki ta yi kuka ta yi kuka har ta ji babu daɗi,watarana sai ta yi ta buga kanta a bango tana nadamar riƙon sakainar kashin da ta yi masa.
Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da Juwairiya ta fara kubburi duk da alokacin cikinta wata shidda da sati biyu,hankalinsa ya yi dubu ya tashi kamar zai yi hauka,wanda Zainab ta ka sa gane akan baby yake yi ko uwar baby.
Da suka je asibiti likita ya ƙara tura su scanning sannan jini za a ƙara mata,saboda jininta ya yi ƙasa,take A.m ya ce a iba na shi a saka mata.
Zainab ta tada hankalinta matuƙa tsiya sosai suka yi akan ya siya jini a saka.
Sai dai ba ta yi nasara a kan sa ba, don kwana biyu ya yi ana iban jinin sa wanda aka sakawa Juwairiya,da yanzu ta fara raina kanta ganin yadda take komawa har kammanninta sun fara canzawa,ga ƙafafuwanta da suke kubbura.
Bayan an saka mata jini suka dawo gida Allah ya ɗauki wani irin tausayin Juwairiya ya saka a zuciyar A.m,wanda ko juya idanunta ta yi sai ya ji wani madarar tausayinta a cikin ransa.
In yana gida sam ba ya iya zama a ko ina sai falon ƙasa,daga baya ƙarya ya yi wa Zainab cewa Momi ta ba shi umurnin ta koma sama,in ya so a ba ta ɗaki ɗaya ta zauna madadin zaman ta a ƙasa.
Zainab hankalinta ya ƙara tashi saboda tun da ta dawo ta ga duk sun canza mata suna wani nan-nan da ita.
Kullum suna sintiri gurin kawo mata abinci na ƙwaɗayi,haka Momi da Abba kullum sai sun kirata sun ji lafiyarta.
Ta raina kanta matuƙar gaske kullum cikin nadamar abin da ta aikata take.Ga tarin dukiyar da take buri ta samu ta samu don yanzu Ƙasar ingila take son ta haɗa hannu da asibinta,kuɗi kam ba ta da matsalar su amma babu kwanciyar hankali,saboda ta lura yanzu sam hankalin A.m ba shi a jikinsa,da ta yi masa magana ya ce zuwan baby ne.
A.m da Zainab suka shirya zuwa waje suka yo siyaryar kayan baby,wanda ita kanta Zainab ba ta san iya yawan kuɗin da ta kashe ba.
A.m sai haɗa tarin dukiya yake yi ma Juwairiya har da wasu share ɗin sa na waje yake son ya bar mata,saboda kar in suka rabuya rage mata jin zafin rabuwa da baby.
Ita kanta Zainab ta yi masa alƙawarin za ta ba ta dukiya masu yawa, ita dai burin ta ta bar mata A.m da babyn da yanzu take jin ta fara son sa a cikin ranta,don son da za ta nuna masa shi kawai zai ƙwato mata martabarta a gurinsa.
Bayan Juwairiya ta dawo sama wata ƙaryar ya shirga ma Zainab akan dole yanzu ya rinƙa kwana da ita saboda cikinta da ya shiga wata na bakwai.
Da fari ƙin amincewa ta yi amma daga baya sai ta yarda akan za su dun ga kwana dukansu tare.
Sai dai A.m yaƙi mata ya ɗan nuna mata hakan ba zai yiwu ba ta amince,don ta san yanzu in dai ba rashin tausayi ba bazai kalle ta ya buƙaci wani abu daga gareta ba,duba ga yadda ta koma.
Juwairiya na ɗanɗana kuɗarta duk wani wahala da take ba ma mutanen gidan,da tsiwa kan dole ta watsar domin yanzu ta kanta take yi,kusan kullum cikin wahala take domin cikin na matuƙar ba ta wahala sosai,kamar za ta mutu ko nishi ta yi sai ta ji wani azaba,ita kam ta sheda mutuwa za ta yi,shi ya sa kullum take kuka sosai akan ya kai ta gurin Mama,saboda ta san mutuwa za ta yi.
Ranar wata daren Alhamis A.m hankalin sa ya tashi matuƙa ganin yadda take sauke numfashi sama-sama.
A lokacin cikin wata takwas ya shiga amma duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata,saboda ta yi wata irin ƙatuwa a yadda kamanninta suka canza ina tunanin ko Mama ta ganta sai ta yi da gaske za ta gane ta.
A.m hankalin sa ya tashi ƙwarai tun da ya fara kwana da ita ya shiga tashin hankali,ganin irin wahalar da take ji sam ba ta samun bacci.
Hannunsa ya sa da nufin ya kamata cikin tausaya,amma sai ta ture shi ta riƙe kwankwasonta tare da rintse idanunta,tana jin wani irin azabar raɗaɗin mutuwa yana shigar ta.
” Wayyo Allah na!Mama ki yafe mini dama haka kika ji kika haife ni! Wayyo Mama ba laifina ba ne halin da kike ciki ya sa na amince da abin da mugu azzalimi ya zo mini da ita.Baba Sani Allah sai ya saka wa mahaifina sam baka riƙe maraicin da mahaifinmu ya baka amana ba.”
Sai ta cige baki ta miƙe da nufin ta tashi,amma ta kasa da sauri ta koma ta zauna, tare da jingina kanta a kan gadon don ji take kamar ɗan dake cikinta zai fito ta bakinta.
A.m da yake jin wani tashin hankali kusan haka suke kwana duk da sun je asibiti,amma sai a ce musu lokaci bai yi ba,sannan (E.D.D)ɗinta bai yi ba balle ayi mata aiki,don haka su jira lokaci.
Duk iya juriyar sa in ya ganta cikin wannan tashin hankalin sai ya ji hawaye da nadama na shigar sa.
Bai san cewa ya shaƙu da ita ba musamamman lokacin da ta fara masa tsiwa, tana nuna ba ta son sa da tsoron sa.
Hunnunsa ta kama ta riƙe ta kalle shi da fararan idanunta wanda yanzu suka koma suka rine saboda ruwan azabar da take kwankwaɗa.
” Bazan yafe maka ba kai da Baba Sani, kai harma da A.k duk da na san ka tilasta shi ne,amma wataƙila da ya jajirce bai amsa ba da ba ku zo gurina tun da kana jin maganar sa b….”
” Juwairiya ki yi shiru za ki haihu lafiya ki koma gurin Mama in sha Allahu Mama za ta ƙara tozal…”
Katse shi da ƙarfi ta yi.” Ka yi shiru don Allah mutuwa zan yi! Jikina ya ba ni bazan ƙara ganin Mama ba a rayuwata,ka raba ni da Mama don kawai burinka na ka samu ɗa.Ka tuna ni ma ƴa ce wacce uwa ta haifa take sonta, kamar yadda kake son ɗan da za ka haifa,saboda burinka na haihu ka ba wa matarka ka nisanta ni da Mama A.m ba ka yi mini adalci ba,na tsane ka bana sonka.Dubi irin wahalar da nake sha amma fatan ka na haihu ka rabani da ɗana,saboda ka faranta ma matarka.Wai shin ita ce mace kaɗai a duni…”
Wani irin hajijiya da take yi ya hana ta ƙarashe maganar sai da ta ɗauki tsawon lokaci ta ce a wahale.
” Wayyo Mama na ƙara girmama lamarin uwa a raina,na san haƙƙin ki yake bibiyata tur da irin ƴa kamata wacce za ta aikata wani abu ba tare da sanin mahaifiyarta ba!Tur da ni kaicona da na yi miki butulci na yi aure ba tare da sanin ki ba.
A m ka ɗauki kukana ka tura ma Mama ta yafe mini ko na samu salama a makwancina.”Ta ce yayin da idanunta ke rufewa muryarta na ƙasa-ƙasa.
” Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!”A.m ya faɗa cikin tsananin tashin hankali yana jijjigata.
” Da gaske mutuwa za ki yi Juwairiya! Don Allah kar ki mutu wallahi ban aure ki don na kashe ki ba,ki buɗe idanunki Juwairiya ki tashi don Allah mai kike so na ce ma Mama da take zaman jiran ki?”
A.m ya ruɗe sosai jijjigata yake amma tamkar babu rai a jikinta.
Hawaye yake yi cikin tashin hankali a ransa yana tunanin dama haka mata ke haihuwa.
Yana tsaye a kanta yana jijjigata ya rasa na yi zuwa can sai ta buɗe idanunta, tana wani irin jijjiga kamar wacce ta kamu da tsinƙa-tsinƙa,sai jini ya fara zuba sosai kamar an buɗe famfo.
A.m ya miƙe daga jikinta tare da sakin wani iri ƙara ya ce.
” Juwairaaaaah!”
Kawai ya zube ƙasa babu numfashi.