SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 35

Zainab zaune a cikin ɗakinta riƙe da wayarta,hawaye ne ke sintiri afuskarta da ta jiƙe sharkab da hawaye.A ranta tana jin wani irintsananin baƙin ciki da tashin hankali mai tsanani,duk sadda ta tunaabin da ya faru tsakaninta da A m,wanda har yau ta kasa yarda wai azahirin gaskiya lamarin ke faruwa.

Wayyo Allahna! Da gaske A.m ka guje ni saboda wata ƴa macemarar gata a duniya,da gaske jikinka da na ke kishinsa ka mallakawa wata mace wulaƙantacciya.Me ya sa ka yi mini haka bayan ka yimini alƙawarin ba za ka taɓa haɗa jikinka da wata ƴa mace ba?

Sai ruwan hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta tana jintsantsar baƙin ciki da kishin Juwairiya a zuciyarta.

Ƙaran tsaƙo da ya shigo a cikin wayarta ya saka ta yi tsaki tare dajefar da wayar,wanda ta san A.m ne ya yi,don kusan a rana sai ya yimata sun fi goma,amma ba ta taɓa gigin buɗe wa ba.Da wayar akashe take barin ta sai yanzu da ta ji zuciyarta ta ɗan rage zafi takunna ta.

Ba zan ɗaga wayarka ba macuci azzalumi mayaudari! Ka mai dani shashasha ka sa ina ta iyayi a cikin ƙawayena mijina ba ruwan shida mata,ni ce mace kaɗai  birnin zuciyarsa a she banza ka mai da nirainin wayonka ya fi na kowa,yanzu da wace fuskar kake son nakalli ƙawayena suna faɗa musu?Haba ai gara a ce mutuwata nasanar musu.”

Sai kuma ta miƙe kamar wata zararriya ta ƙara cewa bayan ta fisgeɗan kwalin kanta ta ya mutsa gashinta da ke ɗaure tare da cilli daribon ɗin.

“Mai ya sa na rayu don na ga ranar da A.m ya yi wa wata ciki bayanni ba na haihuwa?”

Kamar wata zararriya sai kuma ta ɗauki wayarta da sauri tare daƙoƙarin ɓuɗe saƙon da ya yi mata.

Na rantse sai na koyar da ku hankali sai na shayar da ku ruwanbaƙin ciki saboda girman zunubin da kuka aikata mini.”

Ta ce sannan ta fara karanta tsaƙon cike da jimami da tashin hankalibayyane a fuskarta.

(Zainab don Allah ki tsaya ki fahimce ni tabbas na san ban yi mikiadalci ba,amma in kika fahimce ni za ki gane na yin wannan aurenne saboda ke.”Kalar saƙonnin da ya turo mata ranar farko kenan.)

Wata uwar ashar ta danna masa sannan ta buɗe na gaba.

(I dan son Juwairiya nake yi ta ya ya za yi na ije ta a gidanki amatsayin mai aikin gidanki,haba ya kamata ki gane na yi hakanneduk saboda ke.Kin san irin yadda nake son yara .Kin ji na rantsemiki da zarar ta haihu zan saketa kuma na ba ki yaron da ta haifa, tafita daga rayuwarmu domin an halicci rayuwata da ke kaɗai.)

Ire iren saƙonnin da yake yi mata kenan waɗanda ba ta dubi zuwagare su,sai yau ta fara dubawa domin ta gaji da zama ita kaɗaizuciya da gangar jiki sun yi rashin sa,da zarar ta yi shiru muryarsatake mata amsa kuwwa ma kunnenta.

Ka cuce ni!Da na yanke rabuwa zan yi dakai sai dai na lura ba zaniya yin haka ba,domin kai ne namiji na farko wanda na ji zan iyamutuwa akan sa,amma mai ya sa ka zaɓi ka cutar da ni bayana kasan ina son ka matuƙ.”

Mijin na ki za ki yi fushi ki bar ma wata! Lallai ba ki da hankali.”

Momi da take tsaye ta harɗe hannunta a ƙirji tana jin abin da takecewa,ta tambayeta da mamaki a fuskarta.

“Momi ya kike son na yi A.m ya cuce ni bazan iya yafe masa ba.”

Rungumeta ta yi tana rarrashi ta ce.” Na yi magana da Hajiya rabigobe za ku je in da na gaya miki s…”

No Momi na gaya miki ba zan ɓata aurena da wannan ba in har baza ki taimaka mini,ta wata hanyar ba to ni zan koma ɗakina narantse sai na ga bayanta,da kaina zan ɗauki mummunar mataki akanta.Ita da abin da ke cikin zan bankawa wuta duk su ƙon…”

Rufe mini baki banza kawai shashasha! Ana nuna miki hanya ki nakaucewa ki je ki yi duk abin da kika ga dama,ai dama da za ki aikataba ki nemi shawarata ba,wai  ke daɗi miji ai gayi nan in da yakaiki,duk abin da kika ga dama ki je ki yi,amma ina tuna mikimundin kika salwantar mi shi da ciki ba zai barki ba.Ita yarinyar kinsan ta yadda suka yi har ya aureta kasancewar ta ƴar matsiyata.”

Fuuuu! Ta fice daga ɗakin ranta na zafi sosai saboda gani take ba tada wayo,da ba zata bi hanyar da ta saka ta ba don ita ce kawaimafita a garesu.

Sai ta kife kan gado tana kuka domin duniyar ta yi mata zafi sosai.

Kusan sau uku yana kiran wayar ba ta ɗauka ba,sai a na huɗu kamaran saka ta dole ta janyo wayar tare da kanga ta a kunninta.

Munafiki mayaudari mai za ka ce mini na baro gidanka ba za kabar zuciyata ta samu sausauci ba.”Ta faɗa a zafafe da ɓacin rai.

Ya saki naunauyar ajiyan zuciya mai ƙarfi wace ta taɓa zuciyarta,yarintse idanunsa yana jin zafin abin da ta ce mi shi,amma sai ya daureya ce da murya sansanya.

Zainab please don Allah kar ki kashe waya ki bari ki saurari abinda zan gaya miki don Allah!”

Tsaki ta yi ta yi shiru ba tare da ta tanka masa ba.

Ya cire wayar a kunninsa ya kalli wayar don a tuninsa ta katsewayar,amma sai ya ga ba ta yanke ba,sai ya fara magana da muryarda ya san yana kashe mata zuciya,yake kuma narkar da bargonsoyayyarsa ya zagaye duk wata kafa da take jikinta har ta kasa ganegirmar laifin da ya yi mata.

Kin san Allah ya jarabce ni da son yara ko?Sannan ki duba irintarin dukiyar da nake da shi,amma ba ni da magaji Zey ba kyatausayin rayuwata,ke kan ki ina za ki kai ɗumbin dukiyar da kike dashi?Sannan in muka mutu ba mu da wanda zai rinƙa yi manaaddu’a,duniya za ta manta da mu.”

Ya numfasa ko za ta ce wani abu amma sai ya ji ta yi shiru don jitake kamar ta shaƙe shi ta wayar.

Wannan dalilin ya sa na ga da in ce miki mu yi adopting yaro agidam marayu, na ga dacewar kawai na auri mace na siyi ɗan da zata haifa.”

Shiru ta yi bayan ta ji duk abin da ya ce zuciyarta ta kasa yadda dalamarin da ya faɗa,ba rashin son ɗa da ba ta yi bane ya dameta donba za ta iya wahala da shi ba,amma kuma wannan ba matsala ba cesaboda za ta iya ɗaukar mai aiki ta kula da rayuwarsa,to amma itaJuwairiyar za ta iya ɗauke idanunta daga gareshi.”

Abin da take ta tunani kenan a cikin zuciyarta, sannan  kuma mai yasa bai gaya mata ba tun lokacin,sai kawai ta sauke ajiyar zuciya maiƙarfi.

Kamar ya san abin da ke zuciyarta ya ce.” Na ƙi gaya miki ne donba lallal ba ne ki amince,sannan kuma idanuna sun rufe sosai ina sonna ga yarona a haɗa sunana da na sa,idan kika san Juwairiyamatsayin matata ba za mu taɓa samun zaman lafiya,ga shi rashinfaɗa miki bai yi amfani ba saboda na so ace cikin ƙarya kika yilokacin da ta samu ciki,sai mu yi ƙaryar ciki har ta haihu.”

Jikinta ya ƙara yin sanyi matuƙa kamar wacce ta fito da ga firjin.

Haba dama na san A.m ba zai taɓa cin amanata ba sai yana dadalili ga shi yanzu baƙin kishina ya saka na je na tona asiri,da yaronni zan ce na haife shi.”Ta ce take wani irin mugun nadama yashigeta ganin yadda ta kwafsa gefe guda kuma sai ta ba shi laifin ƙingaya mata da ya yi.

Ki yi haƙuri ki dawo gareni ji nake kamar zan mutu na yi rashinwaɗannan hot kis na ki masu zafi da sanyaya zuciya,yanzu aikina yaƙare da ita ko kallonta ba zan ƙara ko kallonta ba ke kaɗai cematata.”Ya ce mata da salon muryar shi da yake rikita ta.

Na ji zan dawo duk da ka zubar da ƙimata a idanun duniya ammata zauna a gidanku har ta haihu in ya so sai a bani yaron ita ta tafi.”

Gaban sa ne ya faɗi ras!Amma kuma ba zai iya gaya mata gaskiyaba,gara in ta dawo sa fuskanci wannnan matsalar.

Ba ki da matsala na zo na ɗauke ki?”Ya ce zuciyar sa da fargaba.

                        Ba yau ba.”

Ɗif ta kashe wayar tana jin haushin sa matuƙar gaske domin yazubar mata da ƙima a gurin mutane.

A.m ya riƙe waya yana kallonta sororo har yanzu zuciyarsa bugawatake yi,ya san in ta dawo ta ga Juwairiya a kwai dirama,balle ta gayadda ta koma ta yi wani irin kyau komai na jikinta ya buɗe shi kansa baya iya ɗauke idanunsa a kanta.

Mai da wayar ya yi cikin aljihunsa ya fesa turaren da ya zamar masadole,tun ba ya son ƙamshin har ya fara so don babu yadda zai yi,saiya fara saukowa ƙasa zuciyarsa na ta ɗar ɗar

                    A.m!

Ta kira sunan shi da ƙarfi kuma cikin isa da gadara ba tare da ko ɗangirmamawa ba,ganin yana son ya fita bai kalle ta ba,duk da ya gantaa falon.

Wani irin kallo ya yi mata ganin yadda ta zauna a falon riga dabanzani daban sai hular sanyinsa wacce ya ba ta saboda jin sanyi datake yi,tana riƙe da remote a hannunta fuskarta cike da tsiwa,gakayan ciye-ciye nan a gabanta da ta gama da wannan ta janyowannan.

Kusa da ita ya zo ya tsaya yana ƙare mata kallo.” Ba na hana kikiran sunana gatsai babu girmama wa ba,ko banza yanzu kyakarrama sunana da Baban baby.”

Kallon shi ta yi a yatsine ta ce.” Ba wani Baban da zan kira ka, saika bari wadda za ka ba wa yaron in ta dawo ta rinƙa ce maka.Kumani ba wannan ba ciyo ya ƙare shi nake son ka siyo mini.”

Gefen ta ya zauna tare da lakuce mata hanci ya shafa cikin wa da dasauri ta ture hannunsa tana hararar sa.Hannunsa ya ware ya ce.

Allah ina roƙon ka ka fito da baby lafiya na huta da wannanyarinyar da ta addabi rayuwata.

Taɓe bakinta ta yi ta ce.” Oho koma me za ka ce ka ce amma nibuƙata ta ka siyo mini ciwo.”

Amma na gaya miki ba lokacin sa ba ne Juwairiya,Allah kowaɗanan da kika ga na samo miki wani ƙauye can aka yi manakwatance ki tausaya wa rayuwata ki kalli yadda na koma.”

Ya faɗa da muryar sanyi da yake bayyana tausayi don kawai tatausaya mi shi.

Ashe ma a kwai in da ake siyar wa ai na ɗauka babu shi ne Allahko bangon duniya sai ka samo mini.”Ta yi maganar cike dashagwaba tana game a wayarta.

To ba in da za ni don na lura abin naki rainin wayo ne.”Ya ce tareda miƙewa zai fita.

Juwairiya sai ta kama rigarsa ta riƙe za ta fara kuka.” Allah sai kasiyo ko da yake ba zan damu ba,ai na ji an ce in mai ciki ta ga abutana so ba a siya mata ba, yaron da tabon rowa yake fitowa kumajikinsa baƙi-baƙi yake yi,sannan ka ji abin da Hamdiya ta ce cikinkuma na iya zubewa,gara ni zan iya ƙara wasu da yawa kai kuwa faƙila ni in na yi aure ƴan biyu zan fara haihuwa masu kyau ba irin kaba babu kyau sai koɗaɗɗiyar fuska...”

Buge bakinta da sauri ya yi kuma ta ji zafi ta sa kuka.

Mara mutunci kawai da aurena kike faɗin za ki auri wani kihaihu.”

Ya ɗaga kafaɗarsa yana mata murmushin ƙeta ganin yadda takehawaye saboda ta ji zafin buge mata bakin da ya yi.

Ji be ta mai hawayen banza har sallar dare zan rinƙa yi kar yaronaya gado ki,saboda in zai rinƙa irin kukanki ƙila na rinƙa tunaki inmun rabu.

Taɓe bakinta ta yi tare da sakin rigar shi ta koma ta zauna ta ɗaukiyalon Bello ta ci sannan ta ce.” Kai har a kwai abin da zai saka katuna da ni in mun rabu,ni kam na ƙosa mu rabu na huta da addabarrayuwata da kake yi.

A.m da ya tuna Zainab za ta dawo sai ya matsa ya zauna kusa da itatare da ɗaure fuskar shi.

A kwai maganar da zan yi dake kuma mai mahimmanci ba nawasa ba,don na lura yanzu na sakin miki fuska gabaki ɗaya kin rainani.Matar gidan za ta dawo duk wannan iskancin ki ije shi agefe,saboda kin san ba za ta ɗauka ba yadda kike gara ni kamarwani ƙwallo,sannan maaganar turare ya tsaya iya ɗakinki dole zancanza wanda na ke shafawa domin na faranta ranta.”

To ni dama na yi maka dole ne in dai ka shafa wani ba wannan bakar ka sake kazo kusa da ni.”Ta ba shi amsa kai tsaye jin abin da yace.

Bai ba ta amsa ba ya ɗora da cewa.” Maganar tashina da daddare dakike yi na yi miki girki zan daina ke ko da safe ne,saboda kin sanZainab ba za ta ɗauka ba,don tun da na ke da ita ban taɓa shiga kicinba na yi girki,da tashina da kike yi na zauna zaman jiran ki a faloƙarshe sai dai na kwana anan.Kin san Allah kika yi wannan gigin saina ɓata miki rai.”Ya ƙarashe maganar da nufin gargaɗi.

Wannan kuma bai shafe ni ba abin da na sa ni in har baby ya ce zaici abinci Allah sai na zo na tashe k..”

Juwairiya ranki zai ɓace fa ki kiyaye ni.”

Da kaukausar murya ya katse ta jin abin da ta ce sai kuma ya duƙa agabanta duk da bai so yin haka ba.” Don Allah ki tausaya minikamar yadda na ke son yaron jikin ki haka na ke son Zainab.”

Wani iri ta ji babu daɗi a ranta abu mai kama da kishi wanda ba tagane hakan ba ya tsaya mata a maƙogaro sai ta miƙe da sauri tashige cikin ɗakinta.

Momi ki barni Allah yau a gidan Mijina zan kwana,saboda na luraba zan iya rayuwa in babu shi ba,kuma ya sanar da ni duk abin da yayi saboda ni ne yana tsoron kar watarana a tilasta mi shi, ya yi aureya sa ya auri yar talakako in ce ya siye ta don ta haifa mana baby.”

Zainab ce take gaya wa mahaifiyarta maganar saboda ƙwacewayarta da ta yi jin suna hira da shi.

A she ke banza ce ke anya nonona kika sha lallai na yadda ba ki dahankali.”

Ta numfasa saboda takaici da ya rufe mata ido ta ci gaba da cewa.”Don ya gaya miki wannan ƙanzon guregen kika yadda da shi,karkimanta namiji ne fa shi,yau na yadda ba ki da hankali karki bari aƙwato miki ƴanci ki koma gidan na sa da kanki za ki dawo kinakuka,don wallahi zaman gidan sai ya so ya fi ƙarfinki.”

Momi ta ce cike da takaicinta saboda ta yi-ta yi da ita su je gurinMalami,amma ta bijire mata.

Ko ma me za ki ce ki ce amma ni ba zan je na ɓata aurena ba,nasan A.m na sona kuma da zarar ta haihu za ta bani ɗan ta koma in data fito,kuma yanzu a gidansu ya ije ta.”

Momi da ta harzuƙa kamar ta kwasa mata mari take ji.” Au hakakika ce ni da na so a zubar da cikin ne,saboda barin a haife shikamar wani babban kuskure ne za ki yi.”Ta ce mata tana son tashawo kanta.

No Momi barin sa ya ga ƙwansa shi zai saka ya samu natsuwa, kinsan in son sa ba zan so na ga yana cikin damuwa ba,kawai ya haihunhakan zai fi mana samun kwanciyar hankli.

To ai ke kika sani duk abin da ya ƙara faruwa karki ƙara nema naki je ciwon so ya kaiki ya baro.”

Ranar da A.m ya je ɗaukota ya sha faɗa sosai a gurin Daddy.

Daddy ya yi masa faɗa sosai kamar zai kai mi shi duka har ya ɗorada cewa. Ka ji na rantse maka don kawai Zainab ta aikata kuskure arayuwarta,wanda mun yi mata faɗa sosai da kuama kunyarmahaifinka da na ke ji,da albarkacin son ka da take yi maka,ammawallahi kulle ka zan yi sai igiya ta yi rarara.

Sakaran banza kawai ka rinƙa dukan mace goto-goto da kai ba ka jinkunya,tun da nake da ita ban taɓa saka hannu na buge ta ba saikai,an ce maka jaka na haifar maka.

Ya numfasa tare da ɗorawa cikin zafi sa ƙunar zuciya na saboda ƙaradukan shalele da ya yi.

Na so ka sakin mini yarinya na tura ta in ingila ta yi rayuwarta acan,ai ka san kai kai ke da asara,saboda duk wanda ya yi rashinZainab ya tafka babbar asara wallahi,ga kyau ga kuɗi da ilmi.

A.m shiru ya yi don haka A.k ya ƙi rako shi don ya san dama zai garashin mutunci.

Haka suka shanya shi kusan rabin awa yana jiran ta har ya yi fushiya raya a zuciyarsa in har ba ta fito ba,minti biyu ya yi zai tafi,sai gata ta fito tana cika tana batsewa da tiren kayan lambu a hannunsa.

Ware hannunsa ya yi har ta taho za ta faɗa sai kuam ta duƙa tare dasakin  kuka sosai.

A hankali ya ƙaraso ya ɗaga ta ya rungume.” Is ok babyna na riga nagaya miki duk abin da ya fa..Katse sa ta yi cikin kuka.

Dole na yi kuka sosai kamar yadda kake rungume ni a faffaɗarƙirjinka haka kake mata gaski..”

Wa ya gaya miki? ai irin wannan yana faruwa ne don kana sonmace,ni kuwa kin ga sam ba na sonta,kawai na tsaya na zaɓo maikyau don kar a haifa mana baby mummuna.”Ya ce da tsigarrarrashi.”

Tsarata ya ci gaba da yi yana gaya mata kalamai masu kwantar dazuciya,har ta manta komai ta miƙe akan za ta ɗauko kayanta su tafi.

Momi kuwa ko kallonta ba ta yi saboda ta yi fushi da ita sosai,saihaɗa kayanta take yi cikin sauri kamar wacce za ta tashi sama,ko data yi mata sallama tsaki ta yi ta juya mata baya.

A.m dake tuƙi idan ya juyo ya kalle ta sai ta balla masa harara tasaki tsaki tare da kauda kanta.

Wani irin fargaba yake damun sa in ya tuna Juwairiya nagidan,kuma ya san Zainab ba za ta yadda ba,sannan a halin yanzu bazai yadda ta yi nisa da shi ba,saboda in ya ga ɗan cikin da ya farafitowa sai yaga kamar ɗansa yake gani,uwa uba ga ɗumin jikinta dayake masifar so ya ji sa a kusa da ita,duk da yaki ce sa da take yi.

Zainab ina son za mu yi magana don Allah ki natsu ki fahimce n .”

To mai kake so ka gaya mini yanzu kuma?Don Allah ka ƙyale nina gaji da yaudara ta da kake yi kana gaya mini kalaman bakinka nayaudara.”

Ta katse shi da murya mai ƙarfi saboda haushi ya ke ba ta sosai jitake kamar ta shaƙe shi,domin ya ha’ince ta ya ije mace a gidanta batare da ta sani ba.

Kawai sai hawaye suka fara turereniya a fuskarta daga ƙarshe fashemi shi da kuka ta yi sosai.

Allah ka na gani A.m ya cuce ni na yi dana sani son ka da nakeyi,ga shi na kasa iya cire shi a raina.In kana son ka samu baby maizai saka sai ka kawota cikin gidana,har yanzu in na tuna akangadona kake kwana da yarinyar nan,ina ji kamar na sha guba namutu.”

Shiru ya yi ya riƙe sitiyarin motarsa yana kallonta yayin da yake tatsaƙe-tsaƙe a zuciyarsa.

Duk ya riga ya wuce wannan meye amfanin dawo da hannu  agogobaya,sannan na gaya miki dalilin aure k..”

Don Allah kar ka taɓa ni baka san ƙyamar ka nake yi ba,mu tafikawai ka tada motar duk abin da za ka ce mini in mun je gida kagaya mini.”Ta ce mi shi yayin da ta ga ya yi nufin kamata.

Kifa kan sa ya yi akan sitiyarin yana jin kukan da take na damunsa,amma ya san za ta yi fiye da wannan in ta ganta a gidan,da yaddata sake abin ta don shi kan sa tsoron rigimarta yake yi,shi ya sa ya soya yi mata bayani amma ta ƙi sauraran sa,kawai sai ya tada motarkomai ta fanjama fanjamjam.

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *