Ta kira sunansa cikin tsawa ganin ta‘asar da yake son yi.
“ A she har hanzu ba ka da hankali wai sai yaushe za ka daina kaihannunka jikin matanka da sunan duka?Ba ka ganin abin da kecikinta wanda ka daɗe ba ka samu ba,so kake ka yi mana asara.”
Da muryar tsawa take mi shi magana cikin zafi domin ranta ya ɓacesosai da ta shigo ta ga ya kai mata shaƙa.
“ To wai tsaya kisa za ki da za ka shaƙe ta?”
Ta tambaye sa cikin ƙubula saboda ta fahimci ba shi da hankali.
“ Momi cikina fa ta ce za ta ƙara zubar wa,ba ki san ta ba ne ba ta damutunci za ta iya aikata abin da ta ce,shi ya sa zan fara gwada matasakamakon abin da za ta gani.”
Ya kalli Juwairiya da ta yi tsamo-tsamo cikin tashin hankali datsoro,domin ba ta manta shaƙar da ya yi mata na asibiti.
“ Yarinya kin san Allah kika yi wannan gigin tare za ku tafi lahira dashi.“
Fakaitar idanun Momi ta yi ta kalle shi ta yatsina baki ta balla mi shiharara,tare da murguɗa baki ta kuma ƙara yatsina fuska.Cikin zafi yaƙara nufar kanta.
Momi dafe kanta ta yi ta kalle su duka sai suka ƙara ba ta haushi,takalli agogon hannunta ta har lokacin da aka ba ta ya wuce.
“ Maza kwashe kayanta yau za ta koma ɗakinta wallahi ba za kusaka mini ciwon kai ba.”Ta faɗa tare da fara janyo kayanta.
“ Momi don Allah ki bar ni a nan ba na son na koma gidansa.”Tafaɗa sai kuma ta kama kuka saboda tana tunanin yadda zaman su zaiyi a gidan,sannan wa zai rinƙa tarairayarta kamar yadda su ke mata.
“Momi ba zan ƙara ba don Allah ki bar ta anan yanzu ta zamaƙazamiya ba ta komai zuwa za ta yi ta ɓata mini gida.”Ya ce da itasaboda yana tsoron kar Zainab ta ji tana gidan,shi da yake son tadawo in ta ji komai zai ɓace.
“ Oho ko mai za ku ce yau za ku tattara ku bar mini gidana.”
Taƙwala ma mai aikinta kira ta ce.” Kwaso mata kayan abinta sutafi,sai kun bar gidan nan zan fita.”
Da ya fahimci da gaske take yi sai ya ɗauki jakar da Momi ta tilastami shi ya ɗauka,yana hararar ta da take ta matsar ƙwalla.
A mota sun yi shiru babu wanda yake tari a cikin su,A.m ya so ya yimata magana amma da ya ga ta shigo,sai ta zauna a gidan baya taɗauki ɗankwalinta ɗaure hancinta da shi,wato alamun har yanzuwarin yake mata.
Kamar kurame babu wanda ya yi magana sai shi da yake ta jantsaƙi.
Ko da suka shiga falon zaune ta yi a falo ba tare da ta kalle shi ba,tajanyo wayarta ta kunna data ta haye whatsapp da Hamdiya ta buɗemata,don ita da chert kwata-kwata bai dame ta ba.
“ A ɗakin masu aiki za ki ci gaba da zama kamar da,don har yanzumatsayin ki na nan bai canza ba.”Ya ce mata yana mata wani mugunkallo.
Ba tare da ta kalle shi ba ta ƙara sautin ƙarar wayarta da tsaƙwannike ta shigowa rututu,sai da ta nisa ta ce.” Ni ma ba na buƙatar yacanza kuma ba zan zauna da mutum yana mini warin jaɓa ba,gara naƙarashe sauran watannin da zan yi ba tare da na kusanta kaina da kaiba,don haka kar ka damu na zaɓi in da na saba zama.“
“ Hakan ya yi ai sai ki ci gaba da zama kayan ɗakin kawai zan canzadon ɗana ba zai kwanta in da talawa suke rayuwa ba.”Ya ce tare daɗaukar wayarsa ya fara hawa sama.
“ Aiko sai ya kwana don ba shi da mara ba da talakawan a jikin ƴartalaka ya fito ka ga shima dangin matsiyata ne.”
Da sauri ya sauko ƙasa kamar zai isa gareta amma sai ya fasa ya yimata wani mugun kallo.
“ Ƙarya kike yi ko da ya a fito a jikinki sai da na saka kuɗina nasiye ki da maƙudan kuɗi,kuma kar ki manta wacce zan ba ma wagaba da bayanta arziki suka gada ba tsaya ba.”
“ To dangin ƙaruna ai dai ba a canza ma tuwo suna.”Ta ce tare daɗaukar goruba ta fara ci don ta san ya tsani ya ganta tana ci.
Tsaki ya yi ya haye sama ba tare da ya ƙara ko kallonta ba.
Juwairiya na zaune a cikin falon ta ga ana shigowa da kayan ɗakimasu kyau,har aka gama jerawa suka tafi sannan na shiga ya yi kyausosai.
Kwanciya ta yi ba ta tashi ba sai gabda magariba,wani irin ƙulululuta ji cikinta ya yi na yunwa,sai ta far hawaye da ta tuna irin gatan dasuke mata.
Kicin ta shiga ta don ta yi faten da ya zama kamar al’ada ku san shine abinta a kullum.
Sai dai ko da ta shiga kicin ɗin warin gas ya hana ta yin komai,dukda toshe hancinta da ta yi ta kasa zama a kicin ɗin.
Kayan ciye-ciyenta ta kwaso ta dawo falo tare da kunna kallo tazauna tana ci.Gidan ta ji ya yi mata faɗi saboda babu kowa a gidansai maigadi,A.m kuma tun da ya fita bai dawo ba.
Bayan ta yi sallar magariba da ƙyar ta jira isha’i tana gyangyaɗi,akandaddumar ta kwanta sai bacci.
Sai misalin tara ya shigo ganin bai ganta a falon ba sai ya yi mamakisaboda da sai ta kai ƙarfe sha ɗaya tana kallo.
Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka kafin ya zo ya yi sallama da ita,donhaka ko turare bai shafa duk da yana jin wani iri,amma gudunrigimarta ya haƙura.
Dariya ya yi ganin yadda ta dunƙule kanta tana bacci a dadduma saiya shafa mata addu’a ya ɗaga ta cak ya kwantar akan gado tare darufo mata ƙofa ya fita.
A.m dake ta juye-juye a ɗakinsa shi kaɗai yana jin kewa na damunsamusamman na Zeey ɗin sa shida yake hutawa da matansabiyu,amma ɗaya ta gagare shi,don haka ba tare da wani tunani ba yafice daga ɗakin,bayan ya fesa turaren da take so a ɗakin.
Cak ya ɗaga ta don ya san ba za ta amince ta biyo sa ba,sai dai kafinya isa da ita ta farka tana mi shi bore amma bai kula ta ba,har sai daya dangana ta da ɗakin ya kwantar dare da rufe ƙofar.
“ Ki kwanta har na fara bacci Momi ta kira ni ta ce kar na sake kikwana ke kaɗai a ɗaki,saboda gudun matsala.”
Bakin sa ya taɓe yake magana ba tare da ya dube ta ba,ganin yaddata ci magani tana mi shi bore.
“ Amma ka san ba na son ƙamshin jikinka ba zan iya kwana da kaiɗaki ɗaya ba,sannan na yi alƙawarin babu abin da zai ƙara kawo niɗakin nan,saboda na gama aikin da aka biya ni.”
“ Na sani ni ma ba wannan ya sa na kawo ki ba ko da haƙuri nake yinake kula ki don na samu baby,amma kin san ai na wuce ajin da zankula ki.Fatana matar so ta dawo mu ci gaba da zamanmu lafiya.” Yace tare da kwanciya can gefen ta.
“ Oho ko ma me za ka ce ba ni da matsala Allah ya sa matar ladangona nake a gareka bai shafe ni ba.”Ta ce sannan ta fara mi shi boretana yatsina fuska kan za ta bar ɗakin.
“ Kin san Allah ko aman me za ki yi ba zan raba kwana da ke ba,saimatar so ta dawo gara ki kwantar da hankalin ki ki kwanta ya fi miki.”
Juwairiya da ta gaji da ta kwanta bayan ta ɗaure bakinta don ta lurakomai zai ta yi mi shi ba zai mai da ta ɗakinta ba,sai ta kwanta donbabu yadda za ta yi.
A.m da ya kasa bacci yana ta mutsu-mutsu yana jin tana ƙorafi harta gaji ta yi bacci,amma shi ya kasa bacci.
Wani irin juyi ya yi sai ga shi ya rungumota ya matseta a jikin sa.
Da sauri ta ture jikinsa cikin ɓacin rai.” Don Allah matsa za katakura mini ina bacci,ka san ba na son na ji na raɓe ka.”
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ƙara matseta a jikinsa yana jinzafin jikinta ya yi masa daidai da sanyin jikinsa.
“ Ki kiyayeni har yanzu a matsayin matata kike don haka ina daikon da zan taɓa ko ina a jikinki.”Ya raɗa mata a kunninta.
“ Ai ba ka isa ba in ba haka ba amai kake son ka yi wanka da shido..”
“ Allah ya sa abin da ya fi mai za ki yi amma saina matso kusa dake,ko ranar da kika yi mini ba kashe ni ya yi ba,in ma da gayya kikayi,sannan ki korar mini matar so sannan ki barni maraya,ai ba ki isaba,yanzu ɗin maneji zan yi kin san ba kamar ta kike ba.”
Ba tare da ta ji baƙin cikin abin da ya ce ba sai ta saka mi shi kukasosai,jin abin da yake mata sannan tana jin duk in da ya taɓa najikinta kamar yana ɗora mata garwashin wuta.
“ Ai in har ka taɓa ni ba zan yi wanka ba don ba na son na saka ruwa a kaina.”
“ Wannan kuma ke ya shafa matsalar ki ne ke da Allah.“Ya ce mataba tare da ya fasa abin da ya yi ninya ba.
Ganin da gaske yake ta ture jikinsa da ƙarfi za ta miƙe,amma sai yasaka ƙarfin tuwonsa ya riƙe ta ƙam.
“ Ka rabu da ni sadda ka je neman aurena cewa ka yi in samu ciki inhaihu ai baka nuna bayan cikin a kwai abin da zai shiga tsaƙaninmuba.”
Dariya ya yi jin abin da ta ce sannan ta ƙanƙame jikinta sosai,sai yatsaya cak ya kalle ta ransa ya fara ɓaci.
“ Har yanzu matata kike so ki kiyaye ni karki kai ni bango in yi mikidole gara ki saki jikinki.”
“Mugu azzalimi wallahi gobe gidan Momi zan koma ko na ɗaukoHamdiya mu rin ƙa zama tare.”Ta ce da shi jin ya kai mata waniwawan kis.
“ Allah ya ba ki sa a dama ki na da hali mai kyau da za ta karɓeki,na san mugun halinki na ƙazanta ya saka Momi ta kore ki,itaHamdiyar ba mahaukaciya ba ce kamar ki.”
Ganin abin da take mi shi ya tashi zaune da ɓacin rai ya ce.”Juwairiya ki fita idona ina tausayinki ne don babyna na rantse dayanzu jikin ki ya gaya miki.”Ya ce mata ran shi a ɓace.
“ To meye sabo a gareni ka duki matar so balle ni ai halinka ne.”Daɓacin rai ya kalleta ganin ta ƙi yadda sai ya sausauta murya.
“ Kar kiji ina roƙon ki gaisawa da babyna zan yi kuma maneji zan yida zarar Zainab ta dawo ko kallonki ba zan ƙara yi ba.”
Ganin ba za ta kula sa bai saurara mata ba sai da ya samu natsuwaya matsa gefe.Juwairiya da sauri ta miƙe tana kwara amai da faribiriss ya yi da ita amma gani yadda ta ke ƙaƙari sai ta ba shi tausayiya isa gareta tare da kama jikinta.
“ Karka taɓa ni dama na san ka tsane ba ka sona duk abin da zaicutar da ni shi kake so.”
Tsaki ya yi ya koma ya kwanta kuma ya ƙi buɗe mata kofa da ta gajita kwanta ita ma.
A.m da ya jima bai yi bacci ba yana ta tunanin canjin da ya ji ajikinta domin ta canza kamar ba ita ba,komai na jikinta ya zamawani iri wanda shi kan sa ya kasa tantance komai.
Hunnunsa ya tura cikin gashin kanta yana murmushi mai ɗauke dama’anoni wanda shi kaɗai ya san me yake nufi.
Haska fuskarta ya yi da wayarsa sai yaga ta yi bacci tana saukar danumfashi a hankali,yayin da fuskarsa take wani irin haske maiwalwali.
Murmushi ya yi kamar ya rungumota su kwanta amma ya san maizai faru sai ya kwanta cikin annashuwa,tare da tofa mata addu’a yakwanta da tunani barkatai a zuciyarsa.
“ A.m ka tashi don Allah.“
Juwairiya ta ke bubbuga shi a hankalinda wata irin murya,amma saibai ji ta ba kasancewar bai ya daɗe bai yi bacci ba.
Ganin haka kawai sai ta saka mi shi kuka da ƙarfin ta.Da sauri yabuɗe ido tare da kunna fitila,ya kalli agogo ƙarfe biyu da kwata.
“Lafiya mai ya same ki?”
Ta riƙe cikinta tana hawaye ganin haka ya ruɗe ya kamo ta jikinsa.
Ture shi ta yi ta ce.” Cikina ke ciwo kuma na kasa bacci.”
“ Mai ya faru take ciwo ko baƙin ciye-ciyen ki za ki ja miniasara.”Ya ce da ita cikin ɓacin rai da ta tashe shi da tsakardare,saboda bacci ne a idanunsa.
“ Yunwa nake ji kuma ɗanwake zan ci.”Ta ce tana fargabar abin dazai ce mata.
“Abinci da tsakar daren nan an ya ki na da hankali kuwa?”
“ Yunwa nake ji sosai kuma ba zan iya bacci ba sai na ci abinci,koda na dawo banci abinci ba,sannan kai ba ka damu dani ba,balle katambayeni.”
Sai ta saka kuka tana.” Allah Sarki ni dai kawai ka mai da ni gidanMomi na fi son na zauna acan,saboda kai ba ka iya komai ba saizalinci da mugunta.”
A.m tun yana tunanin ko wasa take masa har ya gane da gaskeyunwar take ji,tashi ya yi da sauri ya na dana sanin ɗauko ma kansajangwam da ya yi,ya buɗe mata ƙofa ya ce cikin tsawa.” Malamadallah zo ki fita gabaki ɗaya daga dawowarki kin tada hankalina kibari gobe in na kira ki sai ki yi mini abin da kika ga dama.Ai kin sanin da kicin ɗin yake sai ki je ki girka tun da kin zama cin yau,in banda iskanci da tsakar dare za ki ta she ni,Allah ya sa ki yi girki daaljanu su tsorata ki.”Ya ce a fusace yana kallonta kamar ya shaƙureta.
Turo bakinta ta yi ta ce.” Babu in da zan ni anan zan kwana kuma niba zan iya girki da kaina ba,saboda warin gas ba ya barina na yikuma in dai na yi girki ba ya mini daɗi,don haka kai za ka girkamini kuma ɗan wake zan ci.”
Tsananin mamaki ya sa shi kasa magana a ransa yake mamakin yaushe ta raina shi haka da har za ta kalli tsabar idanun shi ta ce shi zaidafa mata abincin da za ta ci.
“ A she za ki mutu don ko da rana ba ki taɓa ganin na shiga kicin nayi ma matar so girki ba balle ke yar karan kaɗa miya,kuma in ban dakin raina,ni zan yi miki girki kici da tsakar dare ko ba ki kalli agogoba.”
Ya yi tsaki ya koma ya kwanta yana jin haushin tashin shi da ta yi.
Juwairiya ta takura ta saka ƙara domin har jiri take gani sabodayunwa,sai ta fara kuka ganin ya kwanta.
“ Ai kuwa mutuwan kasko za ayi ni da abin da ke cikina don har naji ya daina motsi,kuma tabbas in banci abinci ba mutuwa zan yi kaga kai ka rasa ko banza Mama tana da Ibrahim,kai kuwa matarkajuya ce ba ta haihuwa“
A.m da yake ji kamar ya shaƙure ta saboda takaici a she Momiwahala suke ji shi ya sa ta haɗosa da ita,amma jin abin da ta ce saiya miƙe yana murza idanunsa,ya kalli cikinta da sauri ya ce.
“ Amma kin san ban iya kunna gas ba kuma ban iya ɗanwake ba.”
Ta so ta yi dariya ganin yadda ya yi maganar da tausayin kan sa afuskarsa,sai ta ƙara gasganta maganar da Hamdiya ta yi mata cewarduk abin da ta saka shi zai yi,saboda cikin in ko hakane duk sai tawahalar da rayuwar su duka.
Mu je na nuna maka sannan Momi ta haɗa mini garin ɗan waken saina zuba maka iya yawan ruwan da ake so ka kwaɓa.”
Tsaki ya yi ya zura duguwar jallabiya suka fice yana tafe yanatangaɗi don bacci yake ji.Haka kuwa aka yi ta nuna masa sai da tafita ya kunna,bayan ya zuba ruwa ya ɗauko kayan garin kamaryadda ta ba shi umurni ya kawo mata tana zaune a falo da wayartatana daddannwa ya ije mata fuskar shi babu fara’a ko kaɗan.
Da ya kwaɓa ya koma kicin yana mamakin kan sa.” A she haka nakeson ɗana?”Sai ya yi dariya ya ƙara cewa.” Na rantse duk ranar da kafito zan rinƙa kissing ɗinka wunin ranar shi ne horan da zan yi makason.”
Bayan ya saka su ƙwama-ƙwama duk da ta gargaɗe sa amma yanason ya baƙanta mata.
Gyangaɗi ne ya kama shi sai ya ji muryarta da ƙarfi a bakin ƙofa tace.” A.m.”
Da sauri ya duba girkin har ruwan ya ƙone saura kaɗan ya yi sauriya kwashe sannan ya kai mata.
“ Ji don Allah wani irin ɗanwake ne kamar an jefi ƙato.”Ba tare daya kalle ta ba ya fara tafiya zai haye sama.
“ To ina za ka je nufin ka ni kaɗai za ka bari a falo tsoro nake ji.”
Dawowa ya yi yana harara ta.” To ki zo mu je ɗakina ki ci acanbacci nake ji.“
“ Allah ya kyauta ba zan koma ɗakin ka ba ai ka sa cin abincin zanyi.”Ta ba shi amsa a taƙaice.
Kan two seater ya zauna yana kallon yadda take cin ɗanwaken tanata kushewa.
Gabaki ɗaya sai ya ga ta canza kamar ba wacce ya sani ba,maisanyin hali da haƙuri da kuka akan ya sota.
“ Kai wai haka masu ciki su ke yi ko tashi ce ƴar rainin wayo?”Yatambayi kansa zuciyar sa na tafarfasa.
Tun yana jiran ta gama har bacci ya kwashe shi a taƙaice a ranaranan suka kwana,sai da asuba kiran sallah ya tashe shi.
“ Sai ki tashi ki yi sallah saboda iskanci kalli in da kika bar mumuka kwana kamar wasu marayu,kin takure guri ɗaya ji kumakwanciyar da kika yi salon ki cutar mini da baby.”Ya ce tare da faratafiya zuwa ɗakinsa don ya yi alwala jin amfara salla.
Haka suke zaman na su gabaki ɗaya ta mai da shi ɗan aiki da ya faraƙorafi sai ta saka kuka ta ce baby,shi kuma sai ya ruɗe ya yi dukabin da ta saka shi kullum gidan nan cike yake da kayan ciye-ciye,tun bai iya soya kalallaɓa ba har ya ƙware saboda ƙa’ida ne saita tashe ya yi mata ɗaya daga cikin su,tun yana ƙorafi har yasaba,gabaki ɗaya ba ya samun bacci wadatacce,kullum cikin ƙorafitake yi sannan duk wani turare ya saka Juwairiya za ta yi tsalle tadire ta ce ba ta so,ƙamshin wanda take so shi ya kama gidan koina,shi kan sa yana tsoron ranar da Zainab za ta shigo cikin gidannan.
Kafin ta daina amai sun sha jarfa tun daga ranar da ta dawo duk daresai ya ɗaukota da kan sa ,ta yi masa bore amma ya jure saboda shokaɗai ya san yanayin da yake tsintar kan sa,amai ne dai ƙa’idawanda kullum dare sai ta yi shi,amma hakan ba zai hana sa bin da yayi ninya ba.
A.m ya rame sai hanci kamar shi yake laulayin saboda ba ta barin saya huta duk da ta yi mi shi ƙorafin ya ɗauko Hamdiya,amma ya ƙisaboda ba zai iya ɗauke idanunsa a kanta ba,kuma takura musu za tayi duba ga yadda take nuna ƙyamar sa ko kusa da ita ya zauna sai tatoshe hanci,A.k ya ke lallaɓar sa cewar sa za ta daina da cikin yafara girma.
A lokacin da cikin ya yi wata uku ya fara fitowa ya yi girma kamarba ɗan wata uku ba,ganin fitowar cikin A.m kamar zai yi hauka donmurna,wani irin kula ya nuna mata a ranar kamar zai mai da tacikinsa,ya sa ta saka duguwar riga baƙa,wacce ta bayyana cikin a filisosai saɓanin atamfa riga da siket ta yi ninyar sakawa,don ita kunyatake ji matuƙar gaske.
Fita da ita ya yi ya siyo mata kayan ciye-ciye sannan ya lodo matakaya kamar hauka,saboda kayanta ba ta jin daɗin su tafi sondoguwar riga,gidan A.m suka je matar A.k kamar za ta yi hauka tanataya sakaryar ƙawarta kishi,yadda ta ga yana mata kamar zai cinyeta,sannan ganin irin kyawu na Juwairiya da hankali sai ta tsoratatana ganin ta yi sakaci sosai.
Sun daɗe a gidan A.m na ta yanga har yana faɗa musu cikin ya fitowanda take ta saka hannunta tana karewa.Suna ta zolayar shi yayinda daɗi yake ji kamar ya kashe shi wai zai ga ɗan shi ya riƙe kumahar a kira shi da Baba.
Daga gidan su A.k gidan Daddy ya kai ta bayan sun jima ya kai tagidan su,saboda na cin roƙon sa da take ta yi.
Hamdiya ta ji daɗin ganin yadda yake ta yi mata sai da ya gaya makowa cikin ya fara fitowa,wanda hakan ya ba ta kunya sosai kamarza ta nitse,shi kuwa ko a jikin sa bai damu ba.
Hamdiya ta ƙara zugeta sosai tare da ba ta shawarwarin yadda za tawahalar da su har da Zainab da ta ji mahaifin sa ya ce yajebiko,saboda kamar sun fara saukowa.