SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 33

Hamdiya na roƙe ki kibar maganar nan don Allah,domin babu abinda zai saka ni sai tarin baƙin ciki.A halin yanzu wannan ba shi ne agabana ba,ina son na koma gurin Mama ina jin ban kyauta ma taba,duba ga irin wahalar da na ke sha,wallahi ji na ke komai naduniyar ya yi mini zafi.

Sai ta saki kuka sosai tare da miƙewa tsaye, da nufin ta fice da dafalon,amma wani irin jiri ne ya ibe ta,wanda ya saka ta koma dasauri ta zauna,tare da rintse idanunta.

Haka ne ba ki yi mata adalci ba,amma ki gode ma Allah da iyayenA.m su ka karɓe ki,in da ace kin haihu ne ya karɓi ɗan sa,da waneirin ido za ki kalli Mama?”

“Duk da haka ban yi mata adalci ba alhalin yanzu,iya tsananinwahalar da na ke ciki,ya kamata na gane kuskuren da na aikata.”

Sai ta ƙara sakin kuka.” Ki yafe mini Mama ina nan dawowa garekina nemi yafiyar ki.”

“Ya kamata ko da za ki koma gurin Mama,ki nemi mutuncin kan kia gurin Ya A.m,saboda abin da ya yi a gaban iyayenmu ya ƙonamini rai sasai,yana tare da ke amma ya dubi tsabar idanun ki ya cebaya sonki a gaban kowa.”

Juwairiya ta kalle ta da kamar ba za ta ce ko komai ba,amma kumaganin yadda ta mai da hankalinta da damuwarta gareta, amatsayin tana yar’uwar sa,sai ta ce.

Haka ne amma ni ban ga abin damuwa ba,tun kafin mu yi aureyake gaya mini ba ya sona,yana da matar so ni kuwa auren wucingadi muka yi da shi,duk da ada ina masifar son sa, amma haka yadin ga wulaƙanta ni yana kirana da matar shige,a yanzu na yadda nimatar shige ce,kuma na ƙosa mu rabu na huta da warin da nake ji ajikin sa.”

Hamdiya ta kwashe da dariya tana kallon ta.” Yanzu babban Yayaɗan gayu mai ji da ƙwalisa kike cewa yana wari?”

Wallahi wari yake yi mini mai haɗe da ƙarni sam ba na so na jimuryar shi,sai na ji warin ya fara tunkaro ni.”

Ta faɗa tana zuciyarta na tashi saboda maganarsa da ta yi.

To Anty Juwai ba kya tunanin wannan wata dama ce da za kiyi,amfani da shi ki ƙwato ƴancinki a gurin sa?Kamar yadda yakenuna miki baya son ki ki nuna kin tsane shi fiye da wanda yakemiki,ko da kuwa ba gaskiya ba ne a zuciyarki,sabada wani lokacinin ka nuna tsanar mutum ƙarara ko da shi ba ya ƙaunar ka,hakan yakan sa ka ya ji abin ya dame shi matuƙa,sai ki ga da ga baya ƙaunata zarge a tsakani”

Ta ce tana kallon ta amma ganin ba ta ce komai ba,sai ta ci gaba damagana tana cewa.

Allah ki nuna mi shi sam ba kya son ganin sa,saboda cikin da kejikinki a yanzu zai so ya din ga zama kusa dake yana ririta cikin,kekuma sai ki yi amfani da damarki ki wahalar da shi,domin duk faɗinda yake ba ya son ki ni ina ganin yana yaudarar kan sa ne,saboda inda ba ya sonki,ba zai aure ki ba koda kuwa na kwana ɗaya ne,dubaga matsayin sa da na iyayen sa.”

To a yanzu mai kike so na yi?Bayan kin san ni ko kallon sa ba nason yi.”Ta ce da ƙosawa saboda ita ambatar sunan sa da take yi,yaishe ta sai tana jin kamar za ta yi amai.

Ki wahalar da rayuwar shi sam kar ki nuna tausayi,kuma kar kibari ya matso kusa dake.”Ta faɗa ba tare da shakku ba.

In dai wannan ne kar ki damu fiye da haka zan yi mi shi.”Ta ba taamsa tare da mai da kanta ta kwanta,saboda wani irin bacci da takeji.

Tun Momi na ɗari-ɗari da ita da mutanen,gidan har suka saki sunanuna mata wani irin ƙauna,da abin da ke cikinta.A.m gabaki ɗayasai ya ji hankalin sa ya tashi,don ya so ace masoyiyarsa ake nuna waƙauna ba ita.

A.m ya ba ma Zainab lokaci zuciyarta ta huce sannan ya jegareta,saboda ya san cewa a halin yanzu babu abin da zai ce mata takula shi,Daddy ya gaya masa kutu mahaifinta yake so ya kai a ba tatakaddarta,in har A.m ya ƙi sakar mi shi ƴa,yayin da shi kuma yadage don bai ga abin da zai saka ya rabu da ita ba.

Juwairiya na zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon HajiyaBinta,abokiyar zaman Umma,ita da Hamdiya da ba ta daɗe dadawowa daga makaranta ba.

Hajiya Binta ta fi kowa tarerayarta a cikin gidan,saboda ta ya ba dahankalinta sosai kuma mace ce mara damuwa da ɗora ma kai jiji dakai,ku san duk ta fi kowa sauƙin kai a gidan.

Fate ne ta yi mata da ga ɗan manja sai magi da gishiri,in ban dakwatira ta ciki babu abin da zai saka ta sha.

Hira suke yi sosai da Hamdiya sai Hajiya Binta da take saka musubaki jefi-jefi,yayin da hankalinta yake kan tibi tana kallon shirindaɗin kowa.

A.m ya yi sallama ya shigo cikin shadda kalar bula mai kyau.

Daga ɗakin mahaifiyarsa yake aka ce mi shi tana nan,ya taho dazumuɗinsa ya ganta saboda tafiya da ya yi,zuwa cairo har tsawonsati ɗaya.

Idanunsa akan cikin shi burinsa ya ga ya fara girma don har yanzushakkun tana da ciki yake yi ya ƙosa ya ga cikin ya fito.

A a lale barka da mutanen turai.”Hajiya Binta ta faɗa tana kallonsada ya yinsallama ya shigo.Gefenta ya zauna yana shafa kansa.

Bayan ya gaishe ta ya kalli Juwairiya da ta haɗe girar sama daƙasa,ba tare da ta kalle shi ba ta kauda kanta gefe,tana shan fatenduk da ta ji ya fitar mata a rai,saboda ƙamshinsa da ta shaƙa.

Hamdiya ta gaishe shi ta fita Hajiya Binta ta miƙe tana faɗin.” Barina kawo maka abinci Momi ba ta dawo daga gurin aiki ba.”

Bai amsa ba ta shige kicin don haka ya ɗago kan sa ya watsa matawani kallo da ƙyamar a faten da take ci.

Matar shige ya babyna da fatan ki na kula min da shi?Ba ki bar shiya yi kukan rashina ba.”

Wata uwar harara ta sakin mata kullum a zaman su tana ƙara saninA..m, baya ƙaunarata kamar yadda yake nuna mata,sam bai gayamata ya yi tafiya ba.

Ganin taƙi tanka mishi sai ya tashi ya koma gefenta tare darungumota gabaki ɗaya yan faɗin.” Allah Sarki baby na yi missingɗin ka bari na ji lafiyarka.”

Juwairiya da ƙarfinta ture shi gefe tana toshe hancinta,yayin da tafara kakarin amai.

Don Allah ka rabu da ni kar ka ƙara matsowa kuda da ni! Ba nasonka kuma ba na son na ji ƙamshin turaren ka.Wallahi wani irinwari kake yi,wanda i don’t want to say ga irin sa.”

A.m ya zaburo cikin ɓacin rai ya kalle ta da ƙarfi ya ce.” Ke kar kiraina mini wayo kin ce ba ƙya son ƙamshin turaren na canza kandole, yanzu wannan daga Cairo na siyo shi,za ki raina mini wayo kice ina wari,bayan duk zuriyar ku babu ba wanda zai iya siyanturaren.”Cikin ɗaga murya yake maganar,amma sai ta kalle shi tasaki ɗan ƙaramin tsaki,wanda ya ji ran sa ya ƙara ɓaci sosai.

Ya akai yi Abdurrahman tana fama da kanta kake ɗaga matamurya?”Hajiya Binta ta faɗa lokacin da ta kawo masa abinci ta ije agaban sa.

Hararar Juwairiya ya yi ganin tana mi shi

wani kallo sama-sama yana mamakin rashin kunyar da take so tafara yi masa.

Ya zan yi da ita gabaki ɗaya tun da ta samu ciki take yi mini gani-gani,duk turaren da na sa sai ta ce bai yi mata ba,tana son ta nisantani da babyna.”Da shagwaɓa ya yi maganar da kuma murya maialamun ɓacin rai.

Sai ka yi haƙuri ka san sha’anin mata in suna da ciki,wataƙila ba yayi mata daɗi ne saboda ana fuskantar haka.”

Kasa cewa komai ya yi saboda takaici sai hararata yake yi,yayin daita hankalinta ba shi garesa goruba take ta gwawiya.

Cinyau kawai daga samun ciki komai kika samu kici,kuma nitakaicina cimar talakawa da kike yi.”Ya yi tsaki ya ƙaracewa.”Dama duk abin da ka haɗa da talaka sai ya ba kahaushi,yanzu fisabilillahi mai za ki ci da waɗannan cimar wahalarda  kike yi,to wallahi ba za ta saɓu ba dole ki canza ni zan tsara mikikalar abincin da za ki ci,kar yarona ya fito yana cin cimar talakawa.”

Juwairiya da takaici ya ishe ta tun da yake gaya mata magana baitaɓa damunta kamar na yau ba,ta buɗe baki za ta mayar masamagana,amma idanun Hajiya Binta ya saka ta kasa,sai kawai tashige ɗakin ta yi kwanciyarta.

Dole fa sai ka jure dama haka mata suke yi in suna da ciki,in ka yihaƙuri laulayi ne yana fara girma za ta daina.” Ta ce masa tanakallon sa da murmushin abin da ya ce.” Haba ji fa don Allah wannanabin mai kama da icce take ciki,salon ya karce yarona.”Ya faɗabayan ya ɗauki goribar yana juyata a hannunsa.

Miƙewa ya yi lokacin da take dariyar abin da ya ce.” Bari na gaisada baby na dawo ko hutawa ban yi ba.”Ya wuce ɗakin da ta shiga.

Juwairiya na kwance sai ji ta yi mutum ya kwanta gefenta tare daɗora hannunsa a cikinta.

Kafin ya yi magana wani irin amai ya turnuƙo ta shiga kyara shi ajikin sa.Am hankalinsa ya tashi sosai ran sa kuma ya ɓace,ganinyadda ta ɓata mi shi jiki da amai.

Wannan wane irin rainin wayo ne?Amai za ki yi mini a jiki.”Yafaɗa yana wani yatsina fuska tamkar shi ma zai yi amai

Ɗaga idanunta ta kalle shi a wahalce ta tabbata A.m ba shi datausayi a zuciyar sa.

Miƙewa ta yi za ta shige bayi ta ce.” Na ce ba na son ganin ka ballena ji warin jikinka,ba ciki kake da buƙata ba?Meye na ka da sai kaaddabi rayuwata,in na haihu sai ka yi yadda kake so da babyn,amma kar ka ƙara kusa toni,saboda babu wanda na tsana fiye dakai aduniya sa…”

To tun da ba kya sona sai ki zo ki kashe ni!An gaya miki ni ɗin sonki nake yi,kawai saboda na ji ɗumin yarona nake matsowagaraki.Aikin banza kawai.”Ya ce da ƙarfi saboda ya ji zafin tsanarshi da take faɗin tana yi,a tunanin sa ba wannan lokacin ya kamatata nuna masa ba ta son ya matso gareta ba,saboda yanzu yanabuƙatar ya din ga jin girman babynsa.

Ƙoƙarin cire rigar da ta ɓata ya yi ya ije mata a gefenta.” Kin sanAllah sai kin wanke rigar nan,kuma in mutuwa za ki din ga yi baamai ba sai na din ga jin motsin babyna saboda babu uban da ya isaya hanani kuɗi na biya.”Ya fice cikin ɓacin rai.Tsaki ta yi ta gyarajikinta ta koma ta kwanta

Bacci ya soma ɗaukarta ta ji ƙarar waya da sauri ta miƙe ganinnumbarsa ne ya sa ta datse kiran ta koma ta kwanta,sai dai yawankiran da yake yi ya sa ta ɗauka ba tare da ta ce komai ba.

Hello ki na ji na?”Ya tambayeta cikin ƙosawa.

                              Umh.”

Kawai ta ce mi shi ba tare da ta ƙara cewa komai ba.” Na kasa tafiyagida ina falon momi don Allah ki zo ki gaya mini kalar turaren dakike so na din ga sawa,amma ki bar ni na din ga jin lafiyar babynadon Allah.”

Ta yi shiru tana tunanin mai za ta ce mi shi sai ta ji ya ƙara cewa.” Indai a kwai kalar ƙamshin da ya yi miki,ki faɗa mini zan siye shi konawa ne.”

Ni babu ƙamshin da nake so sai humrar da Hamdiya takeshafawa.”Ta ce da shi.

Kamar tana ganin sa ya ware idanun sa da ƙarfi ya ce.” Amma ba kida hankali ni ne zan shafa turaren humra mata fa suke sawa.”Aƙufule kuma cikin muryar tsawa ya gaya mata duk da ya san A.k yagaya mi shi,ba a yi ma mai ciki tsawa,amma abin da ta ɗauko narainin da ta ɗauko ba zai ɗauka ba.

In ba za ka shafa ba dole ne dama ban ce dole sai ka shafa ba,nasan ta mata ce, ita take birgeni kuma nake son ƙamshinta,don hakaka sha zaman ka,ba dole sai ka zo in da nake ba ko ka taɓajikina,don yanzu kamar yadda ka tsane ni baka son wallahi na fi katsanar ka.”

Ɗif ta kashe wayar har wani huci take ita kanta ta san ta koyitsiwa,wanda ta rasa gane dalilin haka kowa ma haushin sa take ji.

A.m da ya yi sagalo da waya a hannunsa tsananin mamakinsa yakamata,tunaninsa yaushe ta canza.

Hamdiya ya ƙwala ma kira sai ga ta ta fito da sauri.” Don Allah sisturaren da na shafa ba shi da daɗi?”Dariya tambayar ta ba ta don tasan kanun,amma sai ta ƙunshe dariyar ta kalle sa yadda ya ci maganiran sa a ɓace ta ce.”A a yana da daɗi Ya A.m duk turaren a kwaidaɗi da fatan ka yi mana tsarabar sa?”

Tsaki ya saki.” A a wancan ƴar rainin wayon ta ce wari nake turarenbai da ƙamshi,tun da ba ta son turaren zan kawo miki sai na canzawani,yauwa ta ce turaren da kike shafawa take so humra ina son kiba ni.”Ya faɗa ba don yana so ba ran sa na suya saboda ta ce yanawari,kamar shi duk wanka da gayu da yake yi.

Duk yadda ta so ta ɓoye dariyar sai da ta dara ganin yadda ya yi.”Mai za ka yi da humra ta mata ne f..”

Ya kike so na yi kwata-kwata ta hanani in ji ɗumin babyna nikuma ba zan iya zama ba tare da jin ɗumin shi ba.”Ya faɗa ba tareda ya ji kunyar ta ba.

Ganin yadda ya yi maganar ba wasa sai ta shige ɗaki tana dariya takawo masa.

Bari na shafa sai na je.”

Ya faɗa yana sinsinar kwalbar turaren amma bai ji wani daɗin datake da shi ba.

Da ka yi haƙuri sai ka canza kaya ka shafa ka dawo kar ta ƙarawani amai,tun da a kwai ƙamshin wancan turaren da ba ta so ajikinka.”Ta ce da shi.

Ficewa ya yi ya nufi motarsa ba tare da ya tanka mata ba,shi a ganinsa Juwairiya raina mi shi wayo ta yi,shi ya sa take faɗin yana wari.

Bai zo gidan ba sai washegari gabaki ɗaya kunya ta kama shinda yafara shafa humrar sai ya ji sam ƙamshinta ba ta yi masa ba,ammakan dole ya shafa ya ɗauki wayarsa da ya gama tura ma Zainabtsaƙon text na ban haƙuri da gaya mata dalilin da ya saka ya aureta,ya sauko ƙasa.

A.k ya gani zaune a falon wanda tun ranar da bin ya faru bai ƙaraganin shi ba,har ya yi tafiya ya dawo sai yau.

Kamar yaro ya duƙa lamun yana ba shi haƙuri tare da ƙamakunninsa duka.

A.m da ke saukowa yana ganin sa ya ɗaure ya kauda kan sa don yaba shi matuƙar haushi,wato da kashe shi za a yi sai dai a kashe shikenan,shi ya gudu don haka ko kallon in da yake bai yi ba ya kamahanyar fita

Da gudu A.k ya ruga ya kama hannunsa yana roƙonsa tare da yimasa dariyar ƙeta.

Da  takaici ya ishe shi bin shi ya yi da gudu suka kama tsere-tserekamar wasu yara,har A.m ya riƙe hannunsa tare da ɗaukar filonkujera,ya din ga maka masa a jiki shi kuma yana dariya.

Da ya gaji sai ya faɗa jikinsa suna haki can kuma suka saki dariyasuka tafa.

Wato ka gudu ka barni duk abin da zai faru ya faru ko?Wallahi bansan ba ka da mutunci ba sai a lokacin sam ba ka cika aboki ba.”

Dariya ya yi.” Ah to ya kake son na yi kaga laifina haka kawaiyadda Abba ya harzuƙa so kake na ja ma kaina?Ai tsunttsun da ya jaruwa….”

Aiko na sha mari sosai kumatuna har sai da suka yi.”Ya faɗa masajin abin da ya ce.

Dariya suka ƙara yi sannan A.m ya miƙe.” Well zan je na ga babynaka san mun shiga da ga ciki,yanzu ina da wanda zan kula da shi soyanzu lokacin sa ne.”

To sabon shiga ofis nake son na je saboda tsoron kar mu haɗe nafara zuwa gidan ka sabon shiga.”

Ni fa ƙamjin turaren humra nake ji na mata ko Zainab ta dawone?”A.k ya ce yana wani shinshine-shinshine.

Bugu ya kai masa a baya.” Gulma babu kyau ban sani ba.”Dariya yayi .” Allah da gaske nake yi kamar irin na Maman Najwa da takeshafawa,na sani ko lallaɓo abin ka ta dawo.”Ya ce da shi lokacin daya buɗe mota zai shiga.

Ba ita ba ne wancan ƴar rainin wayon ce,wai ba ta son ko waneirin turare sai wannan turaren,har yanzu cewa take ina wari ka sanAllah bacin cikina da ke jikinta da sai ta gane ba ta da wayo da takefaɗin ina wari.”

Dariya sosai ya yi.” Ikon Allah sai haƙuri haka yawancin masu cikisuke yi,amma mafi yawancin mazaje ba sa ganewa sai suna ganinkamar ƙarya suke yi,bayan da gaske iya gaskiyar su suke faɗa.”.

Rufe motar ya yi.” Ok bari na je mu gaisa sai na shigo.”Ya ta damotar sannan A.k ya wuce gurin motarsa.

A.m ya yi sallama a cikin falon mahaifiyarsa wacce ya tabbata tanagurin aiki a wannan lokacin,kamar yadda ya yi tunani haka ne kuwadon babu kowa sai yan aiki da suke ta hidimar su.

Kai tsaye ɗakin da ya san take ya nufa a ƙofa suka kusan karo, daHamdiya ta ta fito da gudu da kofin tea a hannunta tana kurɓa.

Matsawa ya yi gefe ganin yadda take sauri kamar za ta tashi sama.”Barka da zuwa Ya A.m na yi latti sosai so by.”

Ta fice ba tare da ta bari ya amsa gaisuwan ba.”Shirmanmun yarakawai mutum ya san yana da lecture amma ya tsaya yana ɓatalokacin sa.”Ya ce tare da tura ƙofar ɗakin.

A.m da ya yi turus a tsaye gani  tana bacci ya yi kamar yajuya,saboda abin da Hamdiya ta rubuto masa har da ba a tashin maiciki da ga bacci.

Sai kuma ya fasa ya yanke shawarar ya gaisa da shi kawai  a hakan.

Hannunsa ya saka ya ɗaga rigarta ya ɗora hannunsa a lafaffencikinta da bai nuna alamun tana da ciki ba.Tsaki ya yi don shi yamatsu ya ga cikin ya fito.

Juwairiya da take bacci ta ji kamar an taɓa ta kafin ta buɗe ido sai taji ƙamshin A.m da ta tsana.

Da sauri ta buɗe ido ta yi ido biyu da shi da yake tsaye yana taɓacikinta.

Ture shi ta yi tare da miƙewa da gudu ta ruga bayi.Tsabar takaici yasa A.m tsayuwa kamar an dasa shi har ta gana amai, ta fito ta tsayacan nesa da shi yayin da miyau ya taru a bakinta.

Na lura iskanci da rashin mutunci yake saka ki kike miniwulaƙanci,kin mai da ƙamshin jikina sai kace warin kashi da namatso kusa dake ki fara amai,to ki sani wallahi ko kayan cikinki zaki mayar sai na din ga gaisawa da babyna,don na lura so kike kawaiya shaƙu dake ke kaɗai saboda in na raba ku,ya ne me ki,don ki saniba zan zauna dake ba kamar yadda iyayena suka faɗa mini.”

Tsaki ta yi ta tofar da miyau sannan ta yi mishi kallon banza ta ce.”Na lura ba turaren da ka shafa ba ne na tsana,kaine na tsana kakemini warin da ya fi na kashi ɗoyi,don haka kai ya dama in ka rabuda ni,saboda in zan din ga jin irin wannan warin  da nake ji ajikinka,to zan yi fatan Allah ya nisanta ni da kai har ƙarshenrayuwata.”

Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta a ran sa tunani yake to kodama yaudarar sa take da take cewa tana son sa,jin irin kalaman datake mi shi,wai yaushe ta zama haka duba ga da ko kallon sa cikinido ba ta yi,sai hawayen banza da take mi shi,lallai ya yi sake taraina shi.

Tun da mun tsani junanmu na ji daɗi sosai kin ga rabuwarmu za tazo cikin sauƙi,amma wallahi ba ki isa ki hana ni jin ɗumin babynaba.”

Da sauri ya matso tare da ƙanƙame ta kamar zai mai da ta cikinsa.

Juwairiya ta saka kuka da ƙarfi ji take da ya rungume ta kamar anasoka mata allurai,yayin da wani amai ya ƙara ta so mata.

Momi da ta dawo sakamakom mantuwar da ta yi ta ji kukanJuwairiya da ƙarfi,duk da ta ga motar A.m a gidan,amma kukan data saka da ƙarfi ba na lafiya ba ne.

Turus! Ta yi tana kallon sa yayin da kunya ya kama dukannin su.

Shafa kan sa ya yi.” Momi rashin mutunci take mini wai wari nakeyi duk iya gayuna,shi ya sa na murɗe mata baki don ni ba na ɗaukarraini.”

A kunya ce ya faɗa ganin ta gan shi rungume da ita.” Ba na soniskanci maza ka tattara ku tafi gidan ku,don ta ce kana wari shi ne zaka mata irin wannan matsar ina falo fa na ke jin ƙarar ta,kaman taabin da yake cikinta.”

Na sani raina ni ta yi da yawa don kawai ta samu ciki,to ta sani bazan ɗauki raini da ga gareta ba.Kuma Momi ta zauna a nan kawaihar ta haihu “Ya ce da ita saboda sam baya son ta ƙara komawagidansa,shi burinsa ya san yadda zai yi ya dawo da Zainab.

Ka san Allah gobe zan tura masu aiki su gayara muku gidanku kuje can ku ƙarata in kun so ku kashe kan ku.”Ta juya ta shige ɗakintadon ta ɗauko abin da ta manta.

A.m ya juya ya kalle ta tare da banka mata uwar harara.” Kin sanAllah ki gaya musu anan za ki zauna in kika bari aka tilasta miniyaga-yaga zan yi da naman jikinki,don kullum ina jikinki ina jinɗumin babyna ina ya so duk abin da zai faru dake ya faru.Bayan nanmatar so za ta dawo in ba so kike ta yi miki dukan mutuwa ba.”

Kwatankwacin hararar da ya ke masa ta mayar masa ko in ce fiye dahaka ta ce.” Allah ya ba ka sa a in ka so ka shige cikin jikina kazauna ba ka raɓe ni ba,amma ina gaya maka wallahi in ka takuranizubar da cikin nan zan yi sai na ga ƙaryar raɓar jikina tun da na gayamaka ba na son ka na tsane ka tsana mai tsanani,sannan matarka tadake ni ta daɗe kai za ta yi ma illah,kuma wallahi in har ka yadda nakoma gidanka sai na hana ka ko shan ruwa a gidan kai damatarka?…”

Da sauri ya kawo mata shaƙa yayin da idanunsa suka yi jajir jin taceza ta zubar da ciki.

Juwiriya ta takura ta tsandara ƙarar saboda hankalinta ya tashiƙwarai ganin yadda ya canza kammanni,ƙarar ya saka Umma tayarda abin da ta ɗauka ta rugo ɗakin da gudu,har da ma aikatanagida.

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *