KAINE GATANA BY FIDDAUSI SO DANGI

[12/5, 3:54 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA ?

1⃣

NA
FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Yarinyace matashiyar budurwa wacce bazata wuce shekara sha hudu ba,s “sanye take da wata kod’add’iyar atamfa riga daban zani ma daban, kanta d’aure da d’ank’wali irin mai santsin nan d’uk’un d’uk’un take kayan sunyi Bala’in daud’a sai tsami ne ke tashi ajikin ta, bak’ace sosai, tanada tsawo amman ba sosai ba. Kanta d’auke da bokiti da alamar ruwa ta d’ibo, sai sauri takeyi ruwan cikin bokitin na zubowa yana jik’a mata jiki,

“Sannu da aiki goggo” Dan uwarki sai yanzu kikaga damar dawowo?” tunyaushe kika tafi d’ibo ruwan kinje kin tsaya yawon iskancin naki shine zaki wani shugo kina min sannu!” aikece da sannu bani ba dan kece agajiye, anya kuwa kausar kina tsoron yanda k’arshan ki zai zama kuwa?” ace yarinya k’arama dake amman kinsan ki ringa bin maza!?” kai ni talatu wannan jaraba dayawa take wannan wani irin bala’i ne haka, kai!!” Allah yasauwaka maki. Shegiya munafuka kallo na kika tsaya yi bazaki sauke ruwan ba saikin kwaro minshi ajiki dawannan sanyin iyyee!!”

“Dasauri tafara k’ok’arin sauke ruwan akanta aiko nan bokitin ya subuce yafad’o k’asa dama bokitin roba ne nan ruwan ya malale ak’asa. Ciki da masifa goggo ta mike ta shak’e kausar ta had’a ta da bango tashiga jibga saikace tana bugun k’ato, “dan Allah gaggo kiyi hakuri wallahi bada gangan nayiba fad’owa yayi kiyi hakuri” saida taga jini nafitar mata hanci da baki sannnan ta k’yaleta haka nan taci gaba da d’ura mata ashar, kuka kawai kausar keyi, fice min daga gidannan karki sake ki shigo batare da sabon bokiti naba yar’iska kawai, haka kawai yarinya kinzame min jaraba babu dangin iya babu na baba kullum ina ciyar dake ina shayar dake amman ke kullum burinki ki bakanta min rai kiringa jawo min asara!” to wallahi bazan k’ara yarda ba duk sanda kika min asara saikin biyani wallahi nagaji da adashin da babu k’wasa zaki fice kosai na shake ki kin mutu!” bakar banza da wofi kawai wacce tayi gadon mugun hali, “dagudu kausar ta fice tana kuka abin gwanin ban tausayi…………………

 

Fido sodangi❣

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN (kausar luv)
[12/5, 3:55 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ??KAINE GATANA??
2⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI❣

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Tana fita taci karo da malan mamman mak’ocinsu, yace subuhanalillahi kausar lafiya?” meke faruwa haka naganki a wannan yanayi?” cikin kuka sosai tayi masa baya nin abinda ke faruwa,yace assha!” wai meyasa talatu take irin haka ne?” anya kuwa talatu, anya! ” shige muje ciki inji, ta girgiza kai ta mak’ure jikin bango, Ya girgiza kai kawai ya shiga k’wad’a sallama, goggo naji amman tayi shuru ta k’yale, saida yayi sallama wajan sau hud’u sannan taga damar amsawa tafito tana sababin waye ne yake ta doka mata sallama haka baiji anata amsawa bane!” tafito taga malan mamman tsaye ga kausar rakube, nan danan ta d’aure fuska tace lafiya malan da sassafen nan!” yace lafiyar ce takawo haka, nandai yashiga bata hakuri akan ta k’yale kausar tashiga cikin gidan, amman sam ta runtse ido taita bala’i daga k’arshe harsai daya biyata kud’in bokitin sannan ta hakura tabari tashige ciki, malan maman nata Allah wadai da ita acikin zuciyar sa sannan ya kad’a kansa yai gaba.

“A hankali wasu zafafan hawaye suka cigaba da bin kumatunta, tana shieshikar kuka. A hankali2, har tagajie da kukan ta tashi ta share hawayen dake zuba mata a ido ta dubie cikin dakin, da duk yayi datti, ga wasu kaya gefe an ajiye sai wari sukeyi, zaune tai kan tabarman da ita dayace mallakinta a gidan, ta dubie fatan jikinta, a hnkli cikin zuciyanta ta fara magana “yaushe wannan azaba da nake ciki zata barni”? Wace irin rayuwa ce nake hka”? Shin ni dayace a duniya dake shan wahala? Wata zuciyar ke cewa a’a Kausara! Ai komai halin dake tsinci kanki a cikinta to ki tabbata akwai wanda yafiki wahala a cikinshi”.
Tana cikin wannan tunanin tajie ana sallama wanda wnnn ba kowa bace face kawanta mai suna Rahane, kai tsaye rahane ta dushie dakin da kausar take ciki, dasauri kausar ta mike tana fad’in inazaki haka rahane naga kinsha kwalliya kinyi kyau!” rahane ta washe baki cikin jin dadin kausar tace tayi kyau tace ai burni zamu wuce yanzu nida salame da uwani, uwani ce tasama mana gidan dazamuyi aiki ana biyan mu duk wata, takara washe baki kamar gonar auduga, kausar ta zare ido tace da gaske rahane?” Dan Allah kuje dani zan biku dan allah?” rahana ta dafe kirji tace ke kausar babu ruwana ai duk wanda yatafi dake yajawo wa kansa bala’i dan goggonki ba kirki gareta ba kinsani kausar ta d’uk’a ta rik’e k’afar rahane tashiga kuka sosai tana rok’onta dan girman allah sutafi da ita batare da goggon tasani ba………

Fido sodangi❣

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
( kausar luv)
[12/5, 3:55 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ??KAINE GATANA??
3⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI?

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Rahane taja ajiyar zuciya tace to shikenan kausar karki damu zamu tafi dake amma sai naje nagaya ma uwani tukun idan ta yarda kinji? Kai kawai kausar ta d’aga mata alamar taji, rahane tafice abinta kausar tabi bayanta da kallo kawai tana hawaye,

“Rahane nashiga gidansu babarta tafara yimata fadan danme zataje ta dade ana jiranta,nan ta shiga warware masu abinda ke faruwa aikuwa uwani tafara washe baki ta kalli babar rahane tace to ai mu adadin mu kinga kawai tafiya da ita zanyi idan anfara biyanta albashi sai mu rabe shi tunda dai ai batare da sanin goggon nata zataba kinga shikenan mu adadinmu gara da akai haka koya kikace? Jinjina kai kawai babar rahane tayi tace to uwani ai kinfini dabara nikam banida tacewa yanda kikace ai haka za ayi, uwani ta kalli rahane tace ke maza tashi jeki taho min da ita inganta danni bama sanin ta nayi ba, jiki asanyaye rahane ta dubi uwani tace to ai goggon nata nacan takasa ta tsare a tsakar gidan ina tsoron inkoma ta koroni kinsan bataso anazuwa wajan kausar, tokenan bakiso atafi da ita birnin kenan? Cewar uwani, dasauri rahane tace inaso mana uwani aikinsa kausar itace babbar kawata aduk fadin kauyan nan banda wacce tafita, babarta ta dubeta cikin fada fada tace to tashi mana ki taho da ita lokaci na tafiya , dasauri ta tashi tafice.

“kausar na zaune a d’akin kamar yanda rahane tabarta sai raba ido take taga ta inda rahanan zata bullo, aikuwa sai sallamar rahane taji daga tsakar gida, goggo na zaune a tsakar gidan tanata yan wak’okinta, a fusace ta kalli rahane tace wai yau uwar mekuke k’ullawa ne kiketa sintiri a gidan nan tunda safe!” ke nifa banason kicihi da iyayi! Idan ke bakida aikin yi to ita tana dashi fice kiban waje kafin inmike in fasa maki kai! Dagudu tayi hanyar waje, goggo taci gaba da fada cikin kumfar baki, candai datayi tagaji ta k’wallama kausar kira kee dan uwarki zonan in aike ki gidan lanto saura kuma daganan kitafi niman mazan dakikasaka agaba shegiya jarababbiyar yarinya mai fuskar munafukai kawai, da gudu kausar tafito dan abin nima ne yasamu dama, kicema lanto wai sai yaushe za a hada min k’udin adashi nane tun jiya fa yakamata in kwasa amman dan iskanci har yau shuru! Tokice mata nace hakuri na yagama k’arewa! Kuma wallahi kikaje kika zauna wallahi sainayi k’ulunk’ulun kubura dake acikin gidan nan dan wallahi jikin kine zai gaya maki, wuce kibani waje bak’ar banza mai kama da uwarta!

“Da gudu kausar ta fice tana murna kai tsaye gidansu rahane tashiga nan ta taddasu tsatsaye sunyi cirko cirko tamkar marasa gaskiya, kausar na shugowa rahane tahau washe baki yauwa uwani kingantanan tazo kausar ya akai goggonki tabarki kika fito? Uwani tace ke rahane yanzu dai ba lokacin tsayawa ayi surutu bane dan haka mukama hanya kawai mutafi dan munsoma mu makara, nandai sukayi ma babar rahane sallama suka tafi da d’an k’ullin kayan rahane a d’an k’wali,

“kausar wacce take d’uk’un d’uk’un sai tashin wari take tamkar wacce ta fad’a k’wata hak’oran nan nata sunyi jawur dasu tawani washesu tana jin dadin yau zata burni, ta dubi rahane tace kee kikace min harda salame zamu burnin toya bangan taba kefa hanne kincika k’arya alk’ur’an, ke dallacan gidansu zamu mu d’auko ta, uwani ta dubi kausar tace to ke kausara bayan gidan su salame zaki jira mu dan banaso asan dake zamu tafi kar aje agayawa goggonki ta d’agama babar rahane hankali tunda ance ita haka halinta yake, dasauri kausar tace Eh ai babu komi uwani hakan ma yayi ai Allah ya amfana……..

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(kausar luv)
[12/5, 3:55 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

4⃣&5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

Haka Kausar taita tsayuwa a wajan har zuwa lokacin dasu uwani suka dawo suda salamen, “izuwa lokacin duk ta kosa da tsayuwar jiransu awajan, gani take tamkar wani zai ganta yaje ya fada ma goggon ta tazo ta tasa k’eyarta zuwa gida, “sai lokacin data hango su sun karyo kwanar inda take sannan hankalin ta yadan k’wanta, cike da d’oki ta washe jajayan hak’oranta tana fad’in to uwani ai yakamata muyi gaba haka nan kar muyi rana ko? Kokuwa birnin babu nisa a mota ne? Amman kuma ai daga nan zuwa tasha akwai nisa sosai! “Duk wannan tambayoyin dataketa jerowa uwani basu riga sun iso inda take ba amman ka rantse da Allah kusa da ita take,

” Tafiya sukeyi sunata zabga sauri kowannansu da d’an k’ullin kayan sa bisa kai k’afafuwan nan nasu sunyi butu butu kasancewar tashan nada dan tazara da inda suke, “A lokacin dasuka isa zuwa tashar mota daya ce jal tarage bata cika ba saidai wajan mutum uku kacal yarage, nan uwani ta dubi kausar wacce idanuwanta harsun cika taf da hawaye taga samu zataga rashi, kanta tasoma girgizawa da karfi tana fadin dan Allah uwani karkice in koma dan girman Allah, “k’wandastan motar ne yayi saurin cewa A’a yanmata menene abin kuka ga bayan motar nan basai ki shiga ba idan zaki iya?amman fa zakisha zafi kuma ga uban lodin kaya, dasauri kausar tace wallahi zan iya mezai haka nidai inza atai birni dani ai babu matsala ko a saman motar zan iya zama ai, gaba dayan su suka kwashe da dariya uwani tace eh lallai y’arnan kina kaunar zuwa birni!

“Tafiyar awa biyu ce takaisu cikin garin katsina inda suka d’ira a sabuwar tasha, dak’yar kausar ta iya ajiye k’afarta a kasa saboda tsabagen tsamin dayayi, duk tayi wani zuru zuru sai zare ido takeyi saikace wacce tayi karya, kallo daya uwani taimata ta fashe da wani mugun dariya saikace wata gardi, ” fuska a yamutse kausar ta dubeta tace wallahi uwani fitsari nakeji kamar zanyi a wando nakeji, tafadi tana rike zaninta da hannu, k’ullin kayan dake bisa kanta uwani ta karba tare da nuna mata wani waje nisa dasu tace da kin karya waccan kwanar zakiga kewaye a wajan taciro wata yamu tsatsiyar naira goma ta mika mata tace inkinje saiki basu wannan zasu barki ki shiga mu bari mu jiraki daga nan gefe, dasauri kausar tayi gaba harda dan hadawa da gudunta dan kuwa fitsarin kiris yarage yafara zubowa,

“A lokacin data fito daga k’ewayan sai taga gaba daya hanyar ya canza mata kasancewar ya kasu kashi uku tarasa ta wacce ta biyo zuwa wajan dan lokacin datazo a rude take fitsari ya sha mata kai, nanfa ta shiga rud’u ” A rikice ta dubi dattijon dake can gefe a zaune tace dan Allah baba ta ina na biyo nazo nan? Wani irin duba yai mata yace yarinya tayaya zanyi insan ta inda kika biyo? Tace wallahi baba hanyar ce ta rikice min naganta har uku, yace to ai duk wacce kika bi aciki zata kaiki har cikin tashar duk daya ne, ya kauda kansa gefe tamkar bashi yai maganar ba, jiki a sanyaye kausar ta dubeshi tace to baba nagode, daga haka bata kuma cewa komi ba ta nufi daya daga cikin kwanar wacce tana tunanin itace hanyar data biyo…………..

 

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:56 PM] ‪+234 813 502 2313‬: [7/5, 11:53 AM] fiddausi sodangi?: ?KAINE GATANA?

5⃣to1⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

*********BARKA DA SALLAH******

Dafatan kunyi sallah lfy ubangiji Allah ya maimaita mana Ameen, Allah ya sa ibadarmu karb’abbiya ce Ameen,

“Nagode da sak’onnin gaisuwarku danaketa samu ubangiji Allah yabar kauna SODANGI tana kaunar masoyanta tana kuma baraba dasu akoda yaushe?

***************************

 

” Wai kai Aliyu sai yaushe zakaima kanka fada ne! Ace wai kayi aure amman kullum saikazo ka matsa min dazancan abinci? Kuma dan tsiya kace kai bazakaci na yan aiki ba sai wanda na girkawa abban ku shizakaxo ka saki jiki ka cinye! To ka bude kunnuwanka kaji ingaya maka daga yau sai yau kar ka kuma zuwa ka hau dinning table dinnan dasunan cin abinci ka ringa tsayawa can gidan ka kana cin na matar ka kaji nagaya maka! “Abincinsa kawai yake ci cikin natsuwa batare daya ce mata kala ba, inda sabo yasaba da gorin da mahaifiyar tasa ke masa akan abinci Amman shikam bai iya yin zuciya, ” Dariyar da Umar Faruq yake ta rikewa tuntuni ne ta subuce masa yaringa yi yana karawa, wani irin mugun kallo Aliyu ya watsa masa hade da kara tamke fuska ba shiri ya hade dariyar tasa dan yasan halin yayan nasa, ” murmushi kawai abban nasu yakeyi yana duban kowa d’ai d’ai,

“Adai dai lokacin da mai gadi Malan iliya ya danni kararrawar falon inda daya daga cikin yan aikin gidan taje kofar ta bude suka gaisa da Malan iliya yace hajiya na kusa kuwa? Tace eh bari ai mata magana, ta koma cikin falon cikin natsuwa ta isa gaban hajiyar tadan duka tace hajiya Malan iliya ne ke magana, cike da murmushi tace to kice masa ya shigo, dasauri ta koma ta gaya masa, shugowa yayi hade da doka sallama, ya dan d’uk’a ya gaida su kansa a d’uke yace hajiya wata yarinya ce a waje take niman taimako yarinya ce karama da alama bacewa tayi sai kuka take tayi gwanin ban tausayi shine nace bari in gaya maku ko za a iyayin wani abu akai, cike da tausayi hajiyar ta dubesa tace jeka ka shigo da ita, dasauri ya mike yafice, takai dubanta kan fuskar abban wanda shima dubanta yakeyi, cikin fuskar tausayi tayi masa magana da ido dasauri ya kawar da fuskar sa yana duban wani waje daban,

“Sallamar malan iliya ya katse masu abinda suke gaba dayan su suka kai dubansu wajan, wani irin bala’in wari ne ya dume falon kausar wacce hawaye da majina yayi dabe dabe bisa fuskar ta saboda tsabagen kukan datasha, a firgice Aliyu da umar suka mike lokaci daya suna toshe hancin su kakarin amai Umar Faruq yasoma da gudu yayi hanyar wata yar k’wana saikace wani dan yaro karami, ido suka bisa dashi dukkan su, jiki a sanyaye Aliyu ya koma ya zauna, haryanzu hannunsa d’aya na nan toshe da hancinsa fuskar nan tasa tamkar wanda aka aikowa da mutuwa,

” Abban ne yace shikenan Malan iliya jeka abinka, godiya yayi ya fice yana maiyimasu saida safe, tasowa hajiyar tayi ta kamo kausar dukda tsananin warin dake fita a jikinta hakan baihana ta rungumar taba tana dan bubbuga mata bayanta alamar lallashi, ajiyar zuciya kawai kausar keyi saboda kukan data sha koma ince take kansha, baki kawai Aliyu ya bude yana bin mahaifiyar tasa da kallo abin na bashi mamaki wannan wani irin tausayi keda mahaifiyar tasa? Ganin babu mai basa amsa yasashi mikewa toshe da hanci yana fadin saida safen ku abba nina tafi, abban ne kawai ya amsa masa banda mahaifiyar tasa wacce gaba daya hankalinta nakan kausar,

“A hankali ta dago kan kausar tace yasunan ki? Sunana kausar, “wow suna mai dadi kausar! Nikuma sunana hajiya nafisa amman yarana suna kirana da mummy inafata kema zaki ringa kirana da hakan? Kai kawai kausar ta daga tana kallon mummy, abba ne yace yau naga ikon Allah nafisa daga ganin sarkin fawa kawai sai miya yayi zak’i ikon Allah sai kallo hararar wasa mummy ta watsa masa hade da fadin kaidai kasa ido kai kallo Allah ne yakawo min y’a har cikin gida na nikam Allah yatayani rik’o “wai ke nafisa wace iri ce ke daganin yarinya ance ta bace kawai ke bakya tunanin a nimo inda iyayanta suke a hadasu da y’arsu kawai saikice wani wai kinyi y’a ina kika taba ganin anyi haka? Adan zafafe yake maganar, “haba abban su wai meyasa kake haka ne? Hmm! Yayi k’wafa kawai ya nufi hanyar zuwa d’akinsa abinsa, ido kawai mummy tabishi dashi har ya bacewa ganinta,”a hankali ta maido dubanta kan kausar wacce itama tabi abban da ido dukda bata fahimci abinda yake fada ba saboda gaba daya magan ganun dasukeyi da turanci sukeyi ita kuwa kausar baji takeba balle ta fahimta, mummy tajawo hannunta tanufi d’akin ta da ita……..

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)

HAPPY SALLAH?
[12/5, 3:56 PM] ‪+234 813 502 2313‬: [7/6, 8:17 AM] fiddausi sodangi?: ?KAINE GATANA?

1⃣0⃣to1⃣5⃣

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Alhaji Muhammad Sadiq K’urfi shahararran d’an siyasan nan wanda ahalin yanzu shine mataimakin governor katsina, mutumin kiirki ne wanda duk tarin dukiyar sa baisa yazama mai girman kai ba, yana da tsananin tausayin talaka kuma sam bai yarda da cutaba yana iyakar kokarinsa wajan ganin ba a tauyewa kowa hakkin saba, mutum ne mai imani da tsoron Allah kowa yabonsa yakeyi shiyasa akoda yaushe k’ofar gidansa ba a rabashi da jama’a yan niman taimako, “yanada matar auran sa guda d’aya tal wacce tazame mashi uwar y’ayansa maza guda biyu watau Umar Faruq dakuma Aliyu gadanga kusar yaki!

“Matar sa nafisa mutuniyar kirkice wacce saboda tsananin tausayin ta dakuma kyautatawa y’an uwan mijin nata yasa suke bala’in kaunar ta tamkar su lashe ta, shiyasa mijin nata yake alfahari da ita akoda yaushe, macece jaruma kwarai da gaske wacce ilimin boko dana addini yagama ratsata, hmm! Justice nafisa Umar Aliyu kenan mata a gidan alhaji Muhammad Sadiq kurfi!

” ALIYU HYDAR”

Aliyu Haydar yaro matashi dan kimanin shekara 31 d’an k’walisa mai cike da kyau da takama, Aliyu Haydar kyakkyawan matashi ne son kowa kin wanda yarasa, yakasance cikakken likita ne mai zaman kansa wanda al’ummar katsina ke dakama daji dashi, yanada natsuwa sosai gashi miskili wanda sam magana ma wuya take masa, shiyasa wanda bai fahimce shiba zaice girman Kaine dashi saidai sam bahaka abin yake ba, “Aliyu haydar sam baya son raini ko kadan yatsani araina sa gashi da zafin zuciya abu kadan ke kular dashi, idan ransa ya baci zakaga jikinsa har rawa yakeyi muryarsa na sarkewa, ” Aliyu haydar ya shaku da mahaifiyar sa matukar shakuwa tanaji dashi tamkar tsoka daya a miya, fadin kyawun Aliyu haydar tamkar batama kai lokaci ne, ya hadu haryama gaji da haduwa, watan shi hudu kenan dayin aure Amman koda yaushe a gidan su yake cin abinci sau uku a rana komeye yasa haka? Tonimadai jikanyan SODANGI bansani ba mudai je zuwa ************

“UMAR FARUQ”
*******************
Umar Faruq yaro ne matashi shima dan kimanin shekara 29 mai jini a jika, yanada hargowa kwarai da gaske, saidai mutum ne mai fara’a sosai koda yaushe ka kalli fuskar sa zaka sameshi a sake yana murmushi mai karama fuskar tasa kyau, kama yake da mahaifin sa sosai tamkar k’wabo da k’wabo, inda Aliyu kuma ke kama da mahaifiyar su tamkar an tsaga kara, “Umar Faruq nada kyau sosai shima daidai shi, shikuma yafi shakuwa da mahaifin nasu sosai, cikakken lawyer ne mai zaman kansa, hmm! Rigimamman abban sa kenan, Barister Umar Faruq Muhammad kurfi kenan, to yanzu kuma labarin zaici gaba insha Allah kudai kuci gaba da bibiyar y’ar mutan SODANGI………..

 

Fido sodangi?

Let me be the first to say Taqabbalallahu minna wa minku to my lovely family and friends.
. May Allah accept all our 30days fast and answer all our du’a , count us among the few on the day of reckoning, count us among those that will witness the forthcoming Ramadan and take hardships away and bring ease to Nigeria and all other nations that Muslims are being oppressed. Preserve all our scholars striving day and night to revive the sunnah and make it easy for the ummah in practicing the sunnah,Ameen . Eid Mubarak.
[12/5, 3:56 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣5⃣to2⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Hannun kausar mummy ta kama harzuwa d’akinta ta dubeta tace kausar ga toilet nan ki shiga kiyi wanka, kallonta kausar tayi k’wak’walwarta na nanata mata kalmar toilet da mummy ta ambata, ajiyar zuciya tayi takuma tuna kalmar wanka da mummy ta ambata kawai sai zuciyar ta fad’a mata aikila bandaki shine toilet ma’ana kewaye, hanyar da mummy ta nuna mata da hannu ta nufa kai tsaye, “jiki a sanyaye ta bude kofar toilet din tamkar wacce za acewa kee! Ta arta a guje, k’ofar ta turo a hankali ta jingina da k’ofar tana karema toilet din kallo,

” mummy dake zaune zaman jiran fitowar d’iyar tata daga wanka,taji shurun yayi yawa tsawon minti talatin kuma bataji karar ruwa ba alamar wanka, hakan yasata mikewa tsaye ta nufi hanyar toilet din ta k’wank’wasa a hankali tace Kausar banji alamar kin fara wankan ba har yanzu ko inshigo in taimaka maki ne?” Dadan karfin ta tace hajiya narasa yanda zanyi in kunna ruwan ne asalima bansan inda zan tsaya inyi wankan ba! “Dasauri mummy ta tura ta kutsa kai ciki, tsaye ta taddata sai raba ido takeyi, dariya ya kufcewa mummy tashiga yi ba kakkauta wa dan ganin yanda kausar keta raba ido tamkar wacce tayi karya, “cikin dabara dasanin yakamata mummy tashiga gwada mata yanda ake amfani da komi tare da wanke mata gashin kanta tas, nan danan tafito tayi tas da ita bakin nan nata mai kyau da sheki ya dad’a fitowa sai haskawa take tayi, mummy tayi murmushi ta kamota suka fito, “wani had’ad’an man shafawa mai bala’in k’amshi mummy ta mik’o mata tace shafa wannan bari indubo maki yar riga kisaka zuwa gobe tunda yanzu dare yariga yayi kuma kinga yarana duka maza ne manya banida kayan y’ar budurwa, wata rigar bacci taciro mata mai bala’in kyau da alama nata ne dumin kuwa sanda kausar tasaka har k’asa yakai mata gashi yai mata fad’i dayawa, murmushi mummy takuma yi a karo na biyu tace wow y’ata kinyi kyau sosai muje kici abinci ko? Ta kamo hannunta suka fice zuwa dinning room, abinci mai rai da lafiya ta zuba mata ta aje mata a gabanta, kausar duk da karancin shekarunta hakan bai hanata mamaki ba wannan wata irin mace ce mai kirki haka? Tambayar data ketayiwa kanta kenan har saida mummy takuma furta cimana kausar kinata kallon abincin ko bai yi maki bane in zuba maki wani? Dasauri kausar tafara kai loma ba k’akkautawa, sai da tayi kat sannan ta kora da lemo tace mummy na koshi,

“D’akin suka koma inda mummy ta umurceta data hau gado ta k’wanta ita zata side din abban su, to mummy saikin dawo,murmushi mummy takuma yi ta fice ta turo mata k’ofar,

” Bacci yafara d’aukar ta taji anturo k’ofar anshigo kuma bataji alamar tafiya ba,dasauri ta bude idonta,”ido hudu sukayi da Umar Faruq ya na tsaye yana k’are mata kallo, a hankali ta ce ina wuni yaya! Kallonta yakuma yi yace ina Mummy batare da ya amsa gaisuwar tata ba, tace tana wajan abban ku tace! Baki ya tabe sannan yace bansan kiba daga ina kika zo?” Daidai lokacin mummy ta iso k’ofar tace to malan matsamin in wuce ko?” Dasauri ya k’arasa cikin d’akin yana fadin mummy ina kika samo yarinya black beauty haka? Bantaba ganin bakin mutum mai kyau ba sai yau Allah mummy, duka takai masa ya fice da guda yana fadin saida safe to tunda yau kinyi bakuwa koratama kikeyi………….

 

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv).

 

 

[12/5, 3:56 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

2⃣0⃣to2⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“WASHEGARI”

“Gaba d’ayansu sun hallara bisa dinning table dan gudanar da kalacen safe, “kowannan su ka dubi fuskarsa wasai take d’auke da murmushi bai ban sha’awa sunata auna ma cikin su daddad’an girkin mummy wacce sam bata yarda yan aiki suyi mata girkin da mijinta zaici ba, acewar ta hakan ba burgewa bane mijin ta bazai iya cin kowani kwamacala ba, shi yasa a kullum take bata lokacin ta wajan shirya masa had’addun girki fiye da kala uku dan kawai ta faranta masa rai,

” Aliyu ne yai sallama yashigo fuskar nan tasa a hade kamar hadari, ya d’uka har k’asa ya gaida iyayan nasa kafin yaja d’aya daga cikin kujerun ya zauna yana wani yatsine fuska, Umar Faruq ne ya danne dariyar dake cinsa yace yaya haydar ina kwana?” Ya madam?” A subane ya dubesa a kaikaice tamkar bazai tanka ba sai kuma yace lafiya tamkar wani mai ciwon baki, kausar daketa kai loma abinta ba kakkautawa ta dubesa itama tace yaya Ali ina kwana?” Dasauri ya d’ago kansa ya kalleta sai kuma ya maida kansa wani gefe tamkar badashi tayiba, “dasauri takuma furta yaya Ali ina kwana ya madam?” Dallah malama wayace maki haka ake gaya min! Idan baki iya fadin sunan ba dole ne saikin gaishe ni!?” Asanyaye tace to Alin madam kayi hakuri ai ni bansan ya asalin sunan naka bane, wani mugun tsaki yasaki ya jawo plate ya shiga lodan abincin sa,

“Dariya Umar Faruq yasaki harda d’ukawa kasa rike da cikinsa hawaye sai zuba sukeyi amman bai fasa dariyar ba, “mummy ce ta daka mai tsawa ganin Haydar din ya mike tsaye tace kai Umar Faruq meye haka?” Me akai dakake irin wannan dariyar kamar wani zararre?” Nan danan ya hade dariyar sa amman dukda haka fuskar sa na d’auke da murmushi alamar dariyar bata isheshi ba, “kwafa Aliyu yayi kafin ya koma ya zauna,

“Mummy ta dubi Kausar fuskar ta d’auke da murmushi dan itama abin ya matukar bata dariya kawai dannewa tayi dan kar ran gadanga yafi haka baci, tace Kausar sunan shi yaya Aliyu daga yau kinji?” Baya so anace masa Ali kinji?” Kakar sa ce kawai ke gaya masa Ali itama rikici sosai sukeyi kinji ko?” Dasauri Kausar tace naji mummy insha Allah zan kiyaye, yaya Aliyu kayi hakuri bazan karaba kaji yaya Haydar?” Hararan ta kawai yayi yaci gaba dacin abincinsa,

“Abba dabai tofa ba tuntuni yace waikai Haydar ba jiyan nan naji mummyn ku nayi maka fadan cin abinci a gidan nan ba?” Yafada tare da duban sa, kafin yaci gaba dafadin kokuwa kana aza da wasa ake maka ne?” To wannan shine na k’arshe banso in k’ara ganin ka a gidan nan dasunan kazo cin abinci kanajina ko!?” Asanyaye yace naji abba amman…….amma me!?” Banaso inji komi daga gareka kawai umurni nake baka kuma dole kabi!

“Mikewa yayi batare daya ce komi ba yana k’okarin ficewa mummy tace au! Fishi kayi kenan zaka bar abincin ka fice?” Fuska a daure yace A’a na koshi ne sai anjiman ku, yafice abinsa dukkansu suka bishi da ido,

“Bayan sun gama karyawa ne abba ya tara su gaba dayansu a falonsa inda yanimi da kausar tabasu tarihinta ko Allah yasa su gane inda iyayan ta suke domin su mai data, dukda karancin shekarun kausar hakan baisa takasa basu labarin taba kamar yanda suka bukata babu abinda tarage saidai wanda bata sani ba amman dukkan abinda take iya tunowa saida ta fadi masu tas! “Nanfa hankalin su yai bala’in tashi musamman mummy wacce tuni ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, shikansa Umar Faruq tuni yanayin fuskar sa ta canza zuwa kalar tausayi, abban kuwa dayake mai dakakkiyar zuciya ne fuskar sa ba yabo ba fallasa,

“Abba ya dubi Kausar bacin takare maganar ta yace kausar ki kwantar da hankalin ki Allah ne yahada mu dake, kuma da izinin Allah zamu rike ki da gaskiya da amana tamkar mu muka haifeki, inaso ki zauna damu tsakaninki da Allah kema kuma ki dauke mu matsayin iyayanki insha Allah zakiyi alfahari damu ga yayunki nan ya nuna Umar Faruq ki rike su yan uwa ko bayan ranmu nasan zasu kula dake,

” mummy ta amshe maganar dafadin kausar ki godewa Allah daya hadamu dake domin kuwa zamu zauna dake ne tamkar yanda muke zaune da ya’yan mu kuma inaso ki kasance mai ladabi da biyayya,kinji ko Kausar?” Hawaye cike a fuskar kausar tace to mummy nagode kwarai Allah yasaka maku da alkairi yabiya maku bukatocinku na alkairi gaba dayansu suka amsa da Ameen ya rabbi………

 

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: [7/12, 9:01 PM] FIDDAUSI SODANGI?: ?KAINE GATANA?

2⃣5⃣to3⃣0⃣

 

 

NA FIDDAUSI SODANGI

©TASKAR MARUBUTA?

“BAYAN WANI LOKACI”

**************************
Kwanaki sunja rayuwa tacigaba ayanzu Kausar nada shekara 16 inda take jss3 saboda promoting daaka mata,kowa na sonta,
********
Yau takama Saturday kowa na gida babu school babu work, umar faruq da kausar suna garden a field suna buga basket ball,dan yana bala’in ji da kausar kaman kanwarsa ta jini itama haka take sonsa,
Kausar na sanye cikin mini short skirt na sport wears da riganshi mai short hannu,kirjinta acike suke tam tamkar zasu yage rigar kasancewar ta mai cikar gaba,” blue color, tasa blue facing cap yafito da jelar gashinta Wanda yanzu yakusa kaiwa gadon bayanta,da witsle a bakinta ta daura fararen compos sai tsalle takeyi.
Ball dinne yafita daga field, Umar Faruq yace kausar jeki dauko mana, aiko dagudu tabi kwallon, ta durkusa zata dau kwallon hartakai hannu saitaga wani kakkyawan kafa dake sanye cikin black cover ya daura akan ball din.
Atsiwace ta Mike batare data kalli fuskanba tace meye haka zaka takemana ball, tana turo wanan karamin bakin nata, tai rau rau da ido tace give me d ball,we are playing basketball, ya umar said I should bring d ball 4 him duk maganan bata kalli fuskanba,ganin anki daga ball din yasa iya karfinta ta daddage ta tura kafan amma ko gezau kafan baiyiba, sa bakinta tayi a gwuiwan kafan ta gansara cizo nan ma baiyiba, dukan kafan tafara sosai tana kuka tana cewa ya umar!” someone is trying to still our ball jin muryanta yasa Umar Faruq zuwa wurin dagudu amma ganin Wanda take duka yasa shi tsayawa cak batare daya motsaba, wata irin natsuwa tashige shi kaman ba shiba, ” tsawon lokaci sannan yai karfin halin karasawa dasauri yadagata tafashe da kuka ta fizge kanta ta koma kan mutumin ta turashi, wani gigitachen mari taji a fuskanta fau tasasssss,

“Ta sandara ihu, Aliyu
yakara falla mata wani kakkyawan mari, ta fadi akasa belt din jikinshi yaciro yafara lafta mata yace bakida tarbiya abi?kin raina nagaba dake,am back zan gyaraku duka, sai alokaci ta kalli fuskanshi tagane Yaya Aliyu ne wanda tsawon shekara biyu baya k’asar shida matarsa ummi Aisha,
“Cikin kuka tace Yaya am sorry bazan karaba,plz 4give me, baimabi takantaba saida ya zaneta sosai tass sai ihu take, ya kalleta fuska adaure yace hold ur lips, idan nakarajin koda tarinkine saina saba miki, da sauri tarike bakinta tana hadeye kukan,ya maida belt dinshi. da yatsa ya nuna Umar Faruq yace zonan kaima, meye dalilinka na wasa da mace da irin shiganan?” Yayi zuru zuru da ido, bakasan kaiya kamata Ka gyarataba? Bakaga tafara girmaba, 4 god sake wot is wrong wid u?” kaida nakema kallon mai hankali kaiya kamata kai couching dinta,” bakasan haryanzu yarinya bace?”batasan komiba y? Ita bakasan mace bane dakake koyamata abubuwan mazaba, 4rm today nabaka last warning ko ka gyara kona saba maka, ” yace Yaya Aliyu kayi hakuri bazamu karaba. Itama kausar tasake bashi hakuri
. dukda tana inda take jikinta narawa tarike bakin nata gam hawaye nazuba, ya daka mata tsawa Mike ki wuce cikin gida maraji kawai, tamike jikinta narawa, yace cire hannun 4rm ur lips da sauri tacire tawuce cikin gida.

“Tana zuwa da gudu tafada jikin mummy dake falo tafashe da kuka sosai, mummy arude tace my kausar menene maisa kike kuka?wayatabaki? Takara shigewa jikin mummy tareda daura kanta kan hannun mummy tace mummy Yaya… Sallamar dataji yasa takama bakinta da sauri jikinta narawa, Aliyu ya Balla mata harara,yace sauka ajikin mummy,da sauri ta sauka tana hawaye tana rike lips dinta, hararanta yakarayi wuce kibamu wuri da sauri tajuya hartana kokarin faduwa tabar wurin.

“Mummy tajuyo ranta adan bace tace Aliyu maisa zaka dake ta haka?” Bakasan yarinya bace?banason nama fada agabantane dankai yayane amma karka Kara dukanta haka banso, yace mummy kiyi hakuri batada kunya ne! mummy tace yanzu gashi ai kasa tana tsoranka zaka hanamin yaa walwala, yay murmushi yadawo kusa da ita ya kwanta akan cinyanta yace mummy ai gwara tadinga tsorona. Mummy zatai magana ya shagwabe yace I missed u mum, hakanan yanzu kinfison kausar kanmu haba mum, yaufa nadawo harkin faramin fada kan ita, mum tace banason kana yawan dukanta mace ne, idan tai Abu ba daidaiba ka gyarata amma karka samata tsoranka aranta yace shikenan mum naji daganan suka cigaba da hiran da da uwa….

 

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)

 

[12/5, 3:56 PM] ‪+234 813 502 2313‬: [7/13, 1:53 PM] FIDDAUSI SODANGI?: ?KAINE GATANA?

3⃣0⃣to3⃣5⃣ 3⃣5⃣to4⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Kausar bata Kara fitowa daga dakintaba,bayan sallan isha an hadu a dining zaayi dinner amma babu kausar,

“Abba yace ina kausar?”mummy tace tana daki haydar ya tsoratamin ita takasa fitowa, Abba yace kai Umar Faruq jeka kirata,

” tana zaune kan gadonta umar faruq ya shigo da tsallenta tahau kanshi dayake kausar akwai son mugun wasa, Umar Faruq yadan zaro ido yace kinason Yaya yadaken?baya hanaki wasa dani ba?” adan taorace tace ai kai katoto ne kanada tsawo bazai dakekaba, yace injiwa? Yaya Aliyu yana decipline din kowa komi girman sa, baya daukan nonsense, yace tashi muje dinner Abba nakira, tamake kafada hawaye yazuba a idonta tace Yaya zai daken ai ko? “Umar Faruq yay murmushi yace ai sai anyi laifi yake duka yanzu dai mutafi tashi tayi tarike hanunshi gam suna kaiwa dining jikinta yafara rawa takasa zama ta tsaya, mummy tace zoki zauna my kausar ta girgiza kai tareda rike lips dinta tana kallon kasa, Abba yayi dariya yace my kausar zo kinji Haydar bazai Kara dukanki ba, dawani irin gudu tawuce inda Aliyu ke zaune ko dago kanshi baiyibama yanadai jinsu. Ta zauna kusa da Abba aka faracin abinci sai wasa take da abincin, mummy tace zaki farako wai mesa bakison cin abinci? ta tabe baki tareda buga kafa tana juya kai tace nibanaso, “Aliyu ya daure fuska yace oya eat ur food nabaki 1min kigama da plate dinan, da sauri tahauci taci Rabin plate tarike cikinta tacigaba daci, mummy tagane takoshi tace Haydar amata hakuri batada yawanci duka plate din yamata yawa murya Chan kasa yace OK. tashi tayi tafara kwashe plate din tana kaiwa kitchen tazo gaban Aliyu amma takasa daukan plate din hanunta narawa mummy da Abba suka Mike suka bar dining din, Umar Faruq ma haka, jikinta yacigaba da rawa, ya dago fararen idonshi ya kalleta yanda take hawaye tarike lips dinta gashi takasa cemishi zatadau plate din saitabashi dan tausayi.

“Yace kewai komi saikinyi kuka? Ta girgiza kai, yace hadiye hawayen ta hadiya, yace nace kiyi hold ur lips ne? Ta girgiza kai, ya daka mata tsawa will u remove ur hand 4rm ur lips my friend da sauri tacire. Yanda yaga tana harhada kafa yagane fitasari takeji kar tsoranshi yasa tasaki anan,yace dau plate din kitafi da sauri ta dauka tajuya takai kitchen tatafi dakinta tai fitsari. Bayan tagama shirin bacci ta fito ta kulle kofanta tawuce side din Umar Faruq saboda duk nyt yana bata story labari mai dadi sai 10 yarakota dakinta shima yatafi dakinshi.

“Tana shiga taga mutum akan gado ya lullube da bargo, da gudu tafada kanshi ta kwanta akan jikinshi tace yaya umar bacci kake is tym 4 my story, “Tahau birgima ajikinshi tana wakeup, duk da rigar jikinta nada kauri sosai amma yanda take goga mashi jikinta ajikinshi yasa kasala ta saukar mai,

” tunkudata yayi tafadi akasa ya Mike, daidai lokacin Umar Faruq
Ya shigo dakin yana fadin ya Haydar naje har gidan nasu amman tace ita bazata tahoba a can zata kwana, nikuma nayi tahowata,

“Kausar jabaya tafarayi a zaune tana neman hanyar guduwa, amma yariko hannunta yace waike wace irin mace ne? Namiji ne abokin wasan ki?” Yauzakici gidanku

“Waya gaya maki mace na wasa da maza?” Bakisan babu kyau ba! Sorry yaya wlh baxan sake ba.pls. idanuwansa ya kura Mata aikuwa da saurinta ta runtsa ido dan kuwa bala’in tsoron idon sa takeyi.ya Kama kunninta yaja da karfi tasaki ihu wayyo ya Aliyu pls am sorry baxan sakeba pls. Wlh idan kika kuma sai na cire wannan dan iskan bakin naki! Yasaketa aikuwa ta zura da gudu sai da takai dakinta sannan ta tsaya tana haki. Aikuwa tana kwanciya bacci ya dauketa cike DA tsoron Aliyu Haydar gadanga kusar yaki!

“Da safe suna zaune a parlour suna kallo itada mummy kanta na bisa cinyar mummy tanata zuba Mata shagwaba tana bata lbrn cartoon dinda akeyi sunata dariya.saiga Umar Faruq nan ya shigo, da gudu ta mike ta rungume shi tana fadin i miss u bro yau bangan kaba tun dazu Ina kashige? Sorry kausar naje unguwa ne , na manta ne jiya ban fada maki ba. Ta zunburo baki tasake shi ta juya masa baya tace kasayo min ice cream din?” Yace no sai anjima sai muje musayo ko? Tace A’a tare da bata fuska zatayi kuka nidai gaskiya yanzu nakeso mum ba tun dazu nake jiran Saba? Mummy tace gaskiya kuje asayo Mata.

“Tsalle takama yi tanajin dadi ahaka suka fice sanye take da riga da wando kanta ko dan kwali babu, Umar Faruq na rike da hannunta,

“Sun shiga motar zai tada kenan sai ga ya Aliyu nan yace Kai! inazaku haka!?”

Umar Faruq ne yace ice cream zamu musayo Mata. Ice cream?” Bataci abinci bane?” kobabu abinci a gidan ne?” da tsawa yake maganar da allah kufito Ku wuce Jo!!! dubeki!! Kalleki! ko dan kwali babu akanki amman wai ahaka zaku fita! Sai na karya maki kafa idan baki kiyayeni ba wallahi! da gudu ta ruga cikin gidan tabarsu nan tsaye yana cigaba da masifar sa,

“Jikin mummy tafada tasaki kukan ta mai bala’in cin rai da tsuma zuciya.a gigice mummy ke tambayan ta lfy me yafaru ina faruq din yake?” Kuka kawai takeyi itakuwa mummy hankalin ta ba karamin tashi yayi ba suna ahaka yayi sallama yashigo tsit Tayi ta hade kukan nan tamkar ba itabace take ta rusa ihu ba.

” Yace au kuka kikeyi? dasauri ta mike ta rike baki tana girgiza Kai no! Ba kuka nakeyi ba! Abinma dariya yabashi yadake yace tome kikeyi?” Mum tace wai dama Kaine kasata kuka?” Aliyu wai meyasa kakeyin haka ne wlh banajin dadin abinda kakeyi Sam tunda kadawo yarinyar nan atakure take inadalili ni kam banison haka gaskiya! To mummy menayi Mata dan kawai nace baxa a siyo ice cream ba?” Au wai hanawa kayi dama?” to wlh maxa ka tafi kasayo Mata inajiran ka yanzu kuma!

“Harara ya watsa Mata yace Bari kallo na Ana min magana kin tsareni da ido! dasauri ta runtse ido harya fice sannan ta bude.mummy Nata lallashinta.

“Towai mummy meyasa bazai koma gidan saba yake kwana mana a gida?” Ina matar tasa ne?” Nidai gaskiya mummy ki koresa yakoma gidan sa, wallahi ni nafison yaya umar, meyasa kika haifi ya Aliyu mummy bayada kirki fa! Murmushi kawai mummy tayi taka ra rungume ta, kausar takara shigewa jikinta tace mummy kuma kice masa yadaina cemin yar bak’a banaso! Banaso! Wai bak’a! Aidai bak’ina mai kyau ne ko mummy?” Murmushi mummy takuma yi tace ai kinma fishi kyau y’ata,

“Ranan monday misalin 2:30 umar faruq ya daukota daga skul yana ajeta yajuya yace Mata wani waje zashi.

” Jakanta ta goya a bayanta da gudu tashigo cikin gidan mummy nazaune a parlour tana karanta newspaper ta fada jikinta tana fadin am back mum mummy ta rungume ta tana shafa bayanta mum yaufa anbamu assignment bari kigani tasauko kasa ta zazzage littafan duka akasa tana niman book din da assignment din keciki can tace la!!! la!!!! Wlh mum sainabi zainab Muktar gidan su yanzunnan wlh ta dauke min book Dina ta mike ta nufi kofa mummy ta rukota tana fadin sorry my baby Kibari gobe idan kuka hadu a skul sai ki karba kuka ta fashe dashi tana cewa no! Mum no! Niyanzu xani! Mummy Nata lallabata dakyar dai tai hakuri kancewa gobe ta karba din.

Amman wai ita saitaje ta gayata da yaya Umar dinta saiya Zane ta gobe.mum tace to kije kicire kaya idan kikai wanka kikai sallah sai kixo kici abinci kinga sai kije Kai karar ko?” Ina ai da gudu ta fice ta nufi side dinsa, tana tafiya duwai nannan na kadawa kamar wata babbar budurwa, koda yake 16yrs aiba nan kusa bane, Uniform din riga da skirt din Iya gwaiwa sai dan hijabi Karami Iya wuya.kayan sun bala’in yimata kyau kamar ba uniform ba.daidai kwanan daza a shiga side din akwai wani lungu dan karami harzata shige sai taji kamar Ana magana kasa kasa aikuwa lungun ta nufa tana fadin waye ne awajan nan?” Ido hudu sukai da ya Aliyu yana zaune bisa kujerar roba hannunsa daya rike da waya akunninsa alamar waya yakeyi daya hannun kuwa sigari ne yake zuka (Taba) yana wani fesar da hayaki cikin kware wa. Ai kuwa da sauri takama ja baya tana kare fuskar ta da hannu alamar wai ita bata ganshiba. Yace ke!!!! Mekikazo yi anan? Jikinta na kyarma take fadin Allah ban gankaba wlh ko ganinka banyi ba.nibanma ko kallekaba Allah ya Aliyu!!!!

” Dariya ce taso kufce masa yace tocewa nayi kin kalleni?” Ta girgiza Kai yace waya koma inda kika fito! da gudu kuwa ta ruga yace keee!!!! Zonan!! Ta dawo tana jujjuya hannunta alamar ban hakuri sai kuma ta rike kunni tana motsa baki alamar pls am sorry dinnan.yace idan naji kingaya ma wani kinganni inashan wannan ya daga Mata sigarin hannun shi yace sai na yanka maki wuya na huda cikin ki!! Ido ta zaro alamar tsorata tace wlh ni banma gankaba! Yace gud kina Iya tafiya.ta gudu ta ruga ya fashe da dariya abinda baitaba ba.first time in history…….

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

4⃣0⃣to4⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Tun daga bakin gate kausar ke jin hargowar Aliyu Haydar da alamar ransa a bace take, “dawowar ta daga islamiyya kenan, lefewa tayi a jikin k’ofar tana mai tsoron shiga, “kalaman dake fita a bakinsa yasakata natsuwa tana saurare, “A’a mummy! “Maganar Allah fa ba son zuciya ba, tayaya za ace k’atuwar budurwa kamar kausar ace tana irin wannan sangarta?” Yarinya sam bata san wani wai wannan namiji bane baligi bai kamata inayi masa kaza ba, baidace ni ina kaza ba! Haba mummy! Karfa ki manta yarinyar nan amana ce a hannunki! Na rantse da Allah wannan wasannin banzan dasuke aikatawa itada Umar Faruq haramun ne! Saboda ba muharraman sa bace! “Kai koda ma ace muharraman sace bai dace ba wallahi mace fa take! Gaskiya lamarin gidan nan akwai gyara wallahi sosai aciki dan wannan ba waye wa bace wallahi! Muji tsoron rannan da Allah zai tambaye mu, “mummy kiyi tunani ki duba maganata idan kuma ranki ya baci akan abinda na fadi to Allah ya huci zuciyar ki Amman wannan kam wallahi ba cinye wa bace!

“Waini abinda ma ke bani mamaki yarinyar nan fa tashin k’auye ce! To yaushe tayi irin wannan wayewar haka?” Acewai budurwa y’ar shekara goma sha shidda amman tana irin wannan sangarta saikace d’iyar goye?” Hmm! Allah ya kyauta, nabarki lafiya,

“Daidai k’ofar fita yaci karo da kausar wacce ke rakube gefe sai hawaye ne ke gudu bisa fuskar ta, tsayuwa yayi cak yana kare mata kallo,yaji dadin da Allah yasa tajiyewa kunnuwanta zancan sa, dan haka batare dayace mata uffan ba yai tafiyar sa,

“K’arasawa cikin falon tayi ta zube a jikin mummy tana wani irin kuka mai ban tausayi, mummy kanta shuru tayi takasa cewa komi illah bayanta datake d’an bubbugawa, sai da tayi Ku kanta iya son ranta sannan tafara magana cikin rawar murya, “hakika mummy abinda yaya ya fad’a gaskiya ne kuma nayi alkawarin cewa insha Allah zan canza halina daga yau zan gyara, ta tashi da gudu ta shige d’akinta tana mai cigaba da kukan nata,

****************************
” BAYAN SHEKARA UKU”
****************************

 

“Abubuwa sun faru sosai a wannan shekarun dasuka wuce ciki kuwa harda kammala karatun Kausar na secondary school,

“Kausar anzama babbar budurwa,Allah yayi mata k’ira mai daukar hankali komi na jikin kausar a cike yake,duk kayan data saka sai sun karbeta sunyi mata bala’in kyau gata dai bak’a kirin amman kuma bakin ta mai kyau ne,

“Soyayya suke itada Umar Faruq abin babu kama hannun yaro,wata irin soyayya ce mai wuyar fassarawa, suna bala’in son junansu sosai,

“Zaune suke a harabar gidan akan wasu kujerun roba suna fuskantar juna, “kausar meyasa kikeso ki ringa wahalar da zuciyata ne! Nace maki ki bari insamu abba da maganar mu amman kinki! Why?” Why?” Meyasa kike hanani mekike tsoro ne iyee! Yaya umar dan girman Allah ka rufa min asiri! Wallahi Allah ina tsoron faruwar wani abu, “A fusace ya mike tsaye yana fadin mekike tsoro meye shi abinda kikema tsoron faruwar?” Kausar kodai baso na kike ba! Idan baki sona kigaya min ki daina wahalar da zuciyata da gangan jiki na! Kifito fili ki gaya min cewar baki sona! Amman bawai kiyi tamin wasa da hankali ba ki dubenifa ni ba yaro bane yakamata ace na dade da aje iyali! Amman na tsaya inata jiranki nayi rainonki har kin girma na jure duk wani gori da ake min akancewa naki aure na toshe kunnuwa na amman sai ki zauna kina raina min hankali a banza a wofi! “Fashewa da kuka tayi tana fadin ba haka bane yaya Umar wallahi ba haka bane ina sonka ina kaunar ka bansan yanda zanyi maka bayanin irin sonda nake maka ba! Amman…..katseta yakarayi a fusace jikinsa har wani rawa yakeyi Amman me mekikeso ki gaya min kausar! Yaya Umar ina tsoron ya Aliyu……dasauri ya kuma katseta cikin rawar murya yace bangane kina tsoron Aliyu ba! Mekikeso ki gaya min iyyye!!………. Gaba dayansu hankalin su yakoma kan gate din gidan da mai gadi ya wangale yana wani rawan jiki, motar sabuwace dal wace tashigo gaba dayan ta tint ce bak’a wulik babu yanda za ayi na waje ya ga naciki, motar tazo ta parka har a gaban su dukda cewar ba wajan parking bane wajan, “kusan minti uku sannan nacikin motar ya fito bayan ya kare masu kallo tas cikin kuluwa ya nufosu, zuciyar kausar tamkar zata tarwatse dan tsananin tsoro da gudu ta nufi cikin gida tabarsu nan tsaye kowanne zuciyar sa na bugawa tamkar zata fito waje…………….

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

4⃣5⃣to5⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Wani irin mugun kallo Aliyu kewa umar wanda zuciyar sa ke tafasa yana kissima wani abu a zuciyar sa, “k’awafa Haydar din yayi sannan yai wani irin taku zuwa gaban sa ya nuna sa da d’an yatsan sa yana fadin nalura kamar kanka na rawa kwanannan ko?” To wallahi wallahi ka kiyayeni! Na rantse da Allah bakin rijiya bawajan wasan yaro bane! Kuma karka manta BABBAN GORO SAI MAGOGIN K’ARFE! “Yajuya a fusace zai bar wajan, Umar Faruq yayi saurin tsaidashi dafadin hyyy!!!! Dakata Malan!!! Ya isa har inda yake sannan yashigar da idanuwansa cikin nasa, cikin d’aure fuska yafara fadin nifa ban fahimce kaba bansan mekake nufi ba ban san manufar kaba wannan tada jijiyoyin wuyan nameye?” Yakama kafito ka fiddani cikin duhu……wani mugun tsaki Aliyu yayi yace lallai yaro wuyar ka ya giga! Tunda har kake iya kallon cikin ido na ka gaya min magana! Yayi k’wafa yabar wajan,

“Kausar jikinta na k’yarma ta shigo falon mummy na zaune tana kallo tazo ta wuce ta a guje zuwa d’akinta, mummy tabita da ido tanason kiranta amman bakinta yai mata nauyi, ajiyar zuciya kawai ta sauke taci gaba da kallonta abinta,

“A fusace Aliyu ya shugo ganin mummy zaune yasashi natsuwa ya d’uka yace mummy barka da maraice kun yini lahiya?” Lahiya kalau ya matar taka?” Wallahi batajin dad’i shinema nazo in dau kausar ta dan tayata dawasu aiyuka kafin Allah yasa ta warware, amman dai kasan kausar bason ta tafi wani waje tabar ni takeba ko?” To mummy ai lalura ne kuma dataji sauki ai saitayi dawowarta ko, to shikenan tana d’aki saikaje ka gaya mata ai amman fa idan bata yardaba baza a takura mata ba sai animi yanda za ayi! Baice komi ba shidai ya nufi hanyar d’akin mata,

“Zaune take rike da wayar ta a hannu ta kura masa ido tamkar meson gano wani abu acikin wayar, saidai da alama hankalinta ba nan yakeba, turo k’ofar da akayi ne yamaido da hankalin ta kan k’ofar, mikewa tayi jikinta na rawa tace ya Aliyu yakamata kayi min uziri haka nan! Karka manta a yanzu nagama makaranta idan kace…….rufemin baki stupid kawai! Mekikeso ki gaya min?” Haka mukayi nida ke?” Girgiza masa kai tayi hawaye na gudu bisa fuskar ta, kausar wallahi wallahi yazama dole ki aure ni koda kuwa baki so! Bawai nace ki soni bane A’a aure nane yazamar maki dole! Idan kuma kince taurin kai zaki min tokuwa zakisha mamaki wallahi Allah kinji na rantse maki! Ke in banda ma rashin hankali Umar Faruq fa kaninane kinsani to danme zaki ringa kulasa bancin tunba yau ba nagaya maki ki kiyayesa sau nawa zangaya maki ne?” To wallahi za ayi yaki a cikin gidan nan duk ranan danakuma ganin ku atare! Kuma ki shirya ki dauki wasu daga cikin kayanki gida na zamu sai inga idan akwai dan iskan daya isa yazo min gida! Wuce ki hada kayanki mutafi karki batan lokaci!

“A razane take kallonsa bakinta na rawa tace ya Aliyu ka rufa min asiri kabarni a gidan nan dan girman Allah……….tsaki yayi yawuce wajan ajiyar kayan nata, wani empty akwati ya jawo yashiga loda kayanta aciki duk wanda hannunsa yaje kai kawai yake jawowa, saida ya cika shi tam ya rufe sannan yajawo hannunta da k’arfi ya fisge ta zuwa falon ganin mummy bata falon yasashi cigaba dajanta har zuwa cikin motarsa, kuka kawai ta fashe dashi tana kallon irin wannan karfin hali da Aliyu Haydar yake gwada mata, k’atuwar budurwa kamarta amman yake yi mata duk yanda yaga dama itakam gaskiya ya takurama rayuwarta yakamata ace zuwa yanzu ya shafa mata lahiya…………..

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

5⃣0⃣to5⃣5⃣

 

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Gudu yake ta shararawa bisa titin tamkar wanda aka biyo, “A tsorace take dubansa ganin fuskar tasa babu annuri yasata saka fuskar ta acikin cinyoyinta, ” wai meyasa ya Aliyu yakeda bak’ar zuciya ne?” Ita kam sam baya burgeta…….wani irin burki yataka jikake kuuuuuu!!!!!!!!! “Cikin tsananin firgita kausar ta fad’a jikinsa ta kankamesa jikinta sai rawa yakeyi, “wani irin shock ya ziyarce shi tamkar wutar nepa ne yaja shi, dasauri ya hankad’a ta ke bakida hankali ne! Bakiga tuki nake ba?” Yi hakuri yaya tsoro ne yakama ni, bai kuma cewa uffan ba har suka isa tangamemen gidan nasa,

“Matar gidan ce a hakime cikin daya daga cikin kujerun dake falon, tana wani taunar cingum ta daura k’afa daya bisa daya tana kallon tashar zee aflam, da alama hankalin ta ya dauku bisa kallon, sanye take da riga da wando kanta ko d’ank’wali babu, tasha kwalliya kamar wacce zata gasar kwalliya,

” Aliyu ne a gaba yayinda kausar ke biye dashi a baya, da gudu ummi Aisha ta taso ta rungume mijin ta tana basa kiss a kuncinsa tare da fadin i miss u sweetheart wlh kawai sai tashi bacci nayi naga har ka fice! (Hmm abin kunya tana can tana baccin asara har mijin ta ya tashi ya shirya ya wuce office batama san anyi ba dan tsabagen lalaci! Injini fido)

“K’ara kankameta yayi yana fadin my ummi kin cika lalaci sosai! ” turo baki tayi tana cusa kanta acikin k’irjinsa alamar taji haushi, dago kanta yayi ya hade bakinsu waje daya yana tsotsa gaba dayansu sun wani lumshe ido suna jin dadin sak’onnin dasuke aikama juna k’afafuwansu ne suke niman su gagaresu tsayuwa hakan ne yasashi sunkutar matar shi zuwa dakin baccin su,

“Kausar dake tsaye tamkar wata gunki ta fashe da kuka wannan wani irin iskanci ne haka?!! Wallahi itakam bazata zauna ba tafiyar ta zatayi, Ak’watinta tafara ja tana kokarin ficewa a falon,

“Shi kuwa Aliyu Haydar yana d’ire ummi bisa gadon sa tamkar kuma wanda aka tsikara dasauri ya nufi k’ofar dakin ya fice, hangota yayi tana k’okarin ficewa daga gate din gidan, keee!!!!! Cak ta tsaya batare data juyo ba, ina kike kokarin zuwa ne?! Yayi tambayar a fusace, gida zankoma! Tafada batare data dubesa ba, kina wasa dani ko?” Na rantse da Allah saina tattakaki idan baki kiyaye niba Allah kuwa! Hannunta yajawo da k’arfi itada akwatin nata har zuwa cikin gidan.
*****************

“Mummy wai ina kausar ne ni bansan menayi mata ba taketa fushi dani ba inata kiran wayar ta taki ta dauka naje k’ofar d’akinta inata bugawa taki ta bude min……au! Bata sallmeka ba kaima?” Wallahi ni kaina bansan sanda suka fice ba nasan ba son zuwa take ba shiyasa tayi fishi ta tafi babu sallama, ina taje mummy?” Tana gidan Aliyu wai matarsa bata lahiya…….gidan Aliyu?! A fusace ya mike tare da nufar k’ofar fita, cikin rashin gamsuwa da yanayinsa mummy takirasa Umar!! Juyowa yayi ya dubeta, zonan! “A sanyaye yadawo ya zauna zuciyar sa na tafasa, meke faruwa ne kaida Aliyu a yan k’wanakin nan naga kamar akwai abinda kuke boye min a tsananin Ku?” No! Babu komi mummy kawai dai kinsan kausar bawani shiri sukeyi da shi yaya Aliyu ba so bazata wani sake a gidan saba, murmushi kawai mummy tayi tace to yanzu ina zaka?” Kansa ya sadda kasa yace zanje in tahoda ita ne dan banaso ana shiga hakkin ta! Kul!! Kar ka kuskura kaje gidan nan dasunan zuwa daukota ka kyaleta kawai ahaka zata saba! Hmm! To shikenan mummy bazani ba nabarta, “jikinsa a sanyaye yabar dakin zuciyar sa na k’una yana maimaita kalaman mummy.
*************************
” BAYAN K’WANA UKU”

“Dr Aliyu ne yashigo gidan nasa da sauri sakamakon mantuwan dayayi, a falo ya iske kausar kwance bisa kujera tana karanta wani nvl waishi (Y’ARGATA! NA FIDDAUSI SODANGI) ” Gaba daya hankalin ta ya dauku akan karatun datake tana tunanin yaza ayi itama ta ringa yima yaya Aliyu yanda yargata keyiwa Aliyu?” Dama ace zata iya aidata huta da bala’in ya Aliyu!

“Kallo daya yaimata ya dauke kai ya nufi d’akinsa bincike yasuma yi inda ya aje abinda yadawo nema amman sam bai gani ba babu inda bai duba ba, hakura yayi ya nufi d’akin ummi kila can ya aje, karar ruwa yaji daga toilet alamar wanka takeyi, bincike yahauyi tako ina yana dubawa ko Allah zaisa yagani, wasu file file dinsa dake dankare waje daya yasoma bubbudewa yana duddubawa,daga k’arshe ya hakura yana kokarin maida su inda suke, tsautsayi yasa hannun sa bige wani dan abu dake gefensa aikuwa gaba daya kayan ciki suka watse a gaban sa hannu yasa ya k’waso magungunan yana dubasu d’aya bayan d’aya hankalin sane yai bala’in tashi cikin tafasar zuciya ya kwashesu ya watsa su aljihunsa ya maida komi inda yake idanuwan nan nasa sun kada sunyi jawur dasu bai ankare ba hawaye suka fara bin fuskar sa………

Fido sodangi

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:22 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

5⃣5⃣to6⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Hawayen dake bin fuskar sa ya goge a fili yafurta wallahi tallahi Ummi Aisha sai kin dau ciki na da izinin Allah! Watau tsawon shekarun damuka dauka a tare magungunan hana haihuwa kike sha!”kenan baki bukatar hada jini dani?” Kenan ba kaunata kike ba basona kike ba k’arya kawai bakin ki ke furtawa! Hmm! Yazama dole ki dau cikin Aliyu Haydar cikin satin nan da izinin Allah insha Allahu sai kin haifi d’an Aliyu Haydar nanda wata tara! Ficewa yayi daga d’akin zuwa nasa,

“Wanka yaje ya sheka ya d’auro wani babban tawul yafito zuwa d’akin ummi Aisha, yana fitowa kamar ance da kausar d’ago kanki sukayi ido hudu da Aliyu daga shi sai tawul, a tsorace dakuma wani irin sauri kausar ta kauda idonta aikuwa littafin dabataci gaba da karantawa ba kenan ta tashi da gudu tabar falon jikinta na k’yarma kamar mazari,

“Dasauri Aliyu ya shige d’akin ummi wacce take zaune gaban madubi tana tsara kwalliya, ta cikin madubin take dubansa shima ita ya kura ma ido, cikin sanyin muryar ta take fadin sweetheart yaushe kadawo har kayi wanka?” Kuma lafiya kuwa ka dawo yanzu harda yin wanka alhalin nasan cewa baka tashi aiki ba?” Shuru yayi mata yana cigaba da karasowa inda take yiyi, juyowa tayi tana duban yanayin sa da alamar akwai wani bacin rai kwance a fuskar sa, tsoro ne yashigeta cigaba da matsowa yayi harya karaso inda take, jawota jikinsa yayi yafara shafata tako ina yana kissing dinta a tsorace take kallon sa ganin yanda yake mata abu wuta wuta kamar wani mayunwacin zaki, muryarta na rawa tace Aliyu ina zuwa bari inyi fitsari dan Allah ko sauraran ta bai yiba yaci gaba da abinda yake, lokaci d’aya ya rabata da tawul din yai cilli dashi gefe dasauri ta rike shi tana fadin wallahi fitsari nakeji dan Allah……… Bakinsu ya hade waje daya cikin sauri yasoma………
****************

“Kuka ummi Aisha keyi sosai har muryar ta bata fita sosai wayyo Allah Aliyu laifin menayi maka kakeso ka kashe ni! Dan girman Allah ka kyaleni haka bai kamata ka hukuntani ta wannan hanyar ba! ” hmm Aliyu saikace kara zugashi takeyi, wayyyyo Aliyu wallahi Allah zanmaka Allah ya isa! Wallahi zanma ihu! Wayyo nika kyaleni wallahi…… Cizo yakushi d’uka dukka babu wanda ummi Aisha batai masa ba amman yayi biris da ita kawai soyake ya kureta, “Awanshi uku yana wahalar da ita dama musamman yasha maganin….shima dan kawai ya wahalar da ita itama, ” mirginawa gefe yayi yana maida numfashi zuciyar sa fari kal tamkar farar takarta, wani irin farinciki yake ziyartar zuciyar sa, yana mai rokon Allah yasa ciki ya shiga jikinta ayau dinnan,

“Ita kuwa kuka takeyi tana hararar sa da kyar ta mike tsaye taje tayi wanka harta fito yana nan kwance bai motsaba daga inda yake, wani tunani ne ya darsu a zuciyar ta dasauri ta nufi ma’ajiyar ta empty taga yar robar babu komi ciki, ido ta zaro a rikice take kallon fuskar Aliyu murmushi yayi mata nan takuma rikicewa tasaki kuka mara dalili,

“Mikewa yayi yawuce yai wanka abinsa yazo ya fice daga dakin tana nan cikin rud’u tana kuka tasan shurun Aliyu yana nufin abubuwa dayawa agareta!

“Kausar kwance bisa gado tana takaicin zaman gidan Aliyu Haydar, gaba daya atakure take,wayar tane yahau ruri dasauri ta jawo shi dantasan Umar Faruq ne mai kiran nata, nan ta dauka tasakar masa kuka,cikin rud’u yake tambayar ta me akai mata meke damunta?” Yaya Umar nikam nagaji nagaji dazaman gidan ya Aliyu na gaji gaskiya dan Allah kazo ka maida ni gida dan Allah! Yi shuru kausar kwantar da hankalin ki gani nan zuwa yanzu insha Allah ki saurareni nanda minti talatin da izinin Allah…….

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:22 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

6⃣0⃣to6⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Umar Faruq ne keta doka sallama a k’ofar falon gidan Aliyu gaba dayansu suna d’aka babu wanda yajishi, shigowa kawai yayi abinsa ya zaune a daya daga cikin kujerun dake falon, tsawon minti biyar babu wanda ya fito,wayar shi ya ciro daga cikin aljihunsa yasoma latsa number din kausar wacce take kwance tana jiran zuwansa, dasauri tajawo wayar ta tana murmushi kawai cewa yayi gani nan a falo! “Dasauri ta d’iro bisa gadon ko tsayawa dibar kayanta batayi ba ta fice abinta, zaune ta iskeshi a falon tace yaya Umar wuce muje karsu fito, au! Suna ciki dama Eh mana, harda Aliyu?” Eh shima yana ciki! K’ofa suka nufa daniyyar ficewa Aliyu ne yafito cikin shigar sa mai kayatarwa sai kamshi yake zubawa…what!!!!!! Umar!!! Uban me kake min acikin gida! Uwar mekazo d’auka! Wani irin juyu Umar Faruq yayi kafin ya nuna kausar da hannu yace kaga wacce ta kawo ni ita nazo dauka! A fusace Aliyu yanuna masa k’ofa mallan fice kabar min gida stupid kawai!! Murmushi Umar Faruq yayi yajawo hannun kausar wacce jikinta ke rawa tsabagen tsoron Aliyu, dasauri Aliyu ma ya ruko hannnuta a fusace ya kifa ma Umar Faruq mari jikake tasssss!!!!!! A tsorace kausar ta dago tana dubin fuskar Aliyu kafin tamaida dubinta akan Umar Faruq wanda ya daga hannu zai rama marinda Aliyu yai masa, dasauri Kausar ta rike masa hannu tana girgiza masa kai A’a ya Umar kar kayi haka barshi da halinsa indai akainane zanyi hakuri in zauna kayi hakuri ka wuce kawai tafada kafin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,

“Harara Aliyu ya watsa mata tare da daka mata tsawa wuce ki bani waje kafin in tattakaki!! Stupid kawai! Dagudu ta wuce tana rusa kuka, k’ofa yakuma nunawa Umar Faruq akaro na biyu yana fadin fice kabar min gida! Wallahi duk ranan danakuma ganin kafar ka acikin gida na saina illataka! Fice nace! Yakuma fadi cikin tsananin hargowa, dasauri Umar Faruq ya fice tamkar zai hadiyi zuciya dan tsabagen takaici,

“Wani mugun tsaki Aliyu yayi kafin ya fice shima ya rufe su tawaje tare dasakama k’ofar key, “ummi Aisha wacce ke tsaye bakin kofar ta cikin rud’u tana kallon dukkan abinda ke faruwa cikin tsananin kaduwa zuciyar ta ke wassafa mata abubuwa da dama saidai tsananin mamaki yasa takasa gasgata abinda d’ayan zuciyar tata ke gaya mata, a fusace ta nufi dakin da kausar ke ciki,

” A fusace ta bude k’ofar ta tsaya tana kare ma kausar kallo wacce taketa rusar kuka maicin rai, a firgice kausar ta dago tana duban ummi Aisha wacce keyimata wani mugun kallo,

“Keeeee!!! Uban meke tsakaninki da miji na?” Nace uwar meye a tsakaninki dashi dahar yake bugun dan uwansa akan ki! “Tsaf kukan kausar ya dauke lokaci daya, wani irin kallo tayima Ummi Aisha tare dafadin mekike tunanin yana a tsakanin mu?” To duk abinda zuciyar ki yagaya maki to haka ne!!!

“A fusace ummi tayo kanta dasauri kausar ta mike tace wallahi idan kika tabani yau sainaga uban daya tsaya maki har ki tabani! Mijinki din banza dawofi?” Mezan da mijinki! Mezanci da mijinki ganida gwarzon maza Umar Faruq! Wanene Ali! “Ni mijin ki bai ishe ni kallo ba baikai matsayin in kulasa ba wallahi ko a kafa aka daura minshi saina k’wance shi na wurgar wallahi! ” aini wallahi idan ba Umar Faruq ba akai kasuwa! Ko kunya bakijiba kinzo kina haushi akan wani…….bata karasaba taja tsaki ta watsar,

“Cike da borin kunya ummi Aisha tajuya zata fice, ” cikin daga murya kausar tace Ashe kina son mijin naki kike barinsa da yunwa! Kullum kina bacci harya gama shirinsa ya fice baki tashi ba! Common abinci ma ki dafa masa baki iyawa lalaci da kasala ya kashe maki zuciya kullum bacci kamar kasa!

“Harara ummi ta watsa mata tafice abinta a zuciyar ta tana fadin Allah yasoki yarinya dayau kingane bakida wayau! Sa karya!………..

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:22 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

6⃣5⃣to7⃣0⃣

 

 

NA FIDDAUSI SODANGI

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Umar Faruq ne zaune agaban su mummy itada Abba kansa a k’asa bayan yagama koro masu jawabinsa akan kausar tare kuma dasanar dasu irin wainar dasuka soya a jiya shida Aliyu akan ita kausar din, inda yakara dacewa Abba nadade ina kaunar kausar amman sam tahanani ingaya maku ni bansan dalilin ta nayin hakan ba!

“Zancan banza zancan wofi! Fadin Abba kenan, shi Aliyu yana nufin son kausar din yake shima?” Matar safa?” Yaya zaiyi da mata biyu idan ba had’ama ba! Kira min wayar Ali din kace masa yazo yanzun nan ina niman sa maza maza! “Abba ai ko na kirasa bazai d’aga ba! Gara kawai kakirasa dakanka zaifi, ” Abba yaciro wayar sa yakira Aliyu ya shaida masa cewa maza yazo yana niman sa kafin ya kashe wayar sa,

“Sai a lokacin mummy tayi magana, Abban su gaskiya maganar Allah Aliyu yataba yimin maganar kausar kusan shekara uku kenan, nice nataka masa burki na k’wabesa nace kada yakuskura inkara jin wannan zance,badan komi ba kuwa sai dan abar kausar tayi karatun ta cikin kwanciyar hankali, ” banaso a bata k’wak’walwa dazancan soyayya, “Abba ne yakatse ta dafadin toni dai bazan ba Aliyu auran kausar ba……dai dai lokacin Aliyu ya karaso, furuccin Abba ne yai masa kuwwa acikin kunni dasauri ya toshe kunnuwan nasa d’uka da hannuwansa d’uka biyun, gaisar da iyayan nasu yayi kafin yanima waje yazauna, Abba ne yafara magana cikin fad’a kai Aliyu Ashe bakada hankali bansani ba! ” da dan uwanka zakayi rigima akan mace! Gaskiya kaji kunya wallahi yafada yana nunasa da yatsa, ” Ali ka mance sanda yarinyar nan tazo gidan nan ne?” Ka mance da irin abubuwan daka ringa yi mata?” Ka mance irin bugun dakake yimata ina hanaka! Kamance yanda kake k’yamarta?” Ka mance cewa a kullum ka ganta hannunka na bisa hancinka har lokacin dazaka bar gidan nan?” Kamance irin k’yarar daka ringa yimata ne?” K’azama, y’ar k’auye, bagidajiya, kai har jaka naji kataba gaya mata! “To shine yanzu dun bakada kunya zakaxo kace kana kaunar ta! To wallahi karya kakeyi! Mutumin banza kawai! Tashi ka bani waje kuma ka tabbatar yau dinnan kadawo min da y’ata gida! Kaji nagaya maka!

“Mummy ce ta kalli Abba da fuskar tausayi tare dafadin ” haba abban su gaskiya bai kamata ayi haka ba abinda yakamata shine abawa yarinya zabi duk wanda tazaba acikin su shikenan sai ayi dashi amman idan akayi haka tamkar an tauyesu dukkan su tunda ita kausar din bamusan watake so acikin suba dan haka kai Aliyu kaje ka d’auko ta yanzu muna jiran ka,

“Idanuwan Aliyu dasuka kada sukai jawur yadubi mummy dasu tare da fadin to mummy idan kuma tace shi takeso ni ya zanyi kenan, no! My son kada ka sare dan Allah ai wani baya auran matar wani dan haka jeka kazo da ita muji ta bakinta,

” jiki a sanyaye ya mike ya fice, Umar Faruq yai murmushi yace aini wallahi banda haufi dan nasan ni kausar keso! Ai kowa ma yasan yanda kausar ke sona kawai dai wannan guy din naso yaimin shigar shugula ne kawai……….

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:22 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

7⃣0⃣to7⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Kausar ce k’wance bisa gado gaba daya yau wani kasala takeji ko rigar baccin jikinta bata cire ba bare ayi maganar wanka kocin abinci, k’ofar d’akin aka bude da Karfi a tsorace ta dago kanta tana kallon shi fuskar nan tasa a hade kamar hadari, tsawa yadaka mata ke!! Taso dallah kin wani kuran ido kamar wata mayya! A tsorace ta mike tare da fadin ina kwana ya Aliyu?” Wani irin kallo yake mata tundaga tsakiyar kanta har zuwa yatsun kafarta, (kallon kurilla inji fido)

“Nace ki daina kallo na! Dasauri ta dauke kanta ta d’ukar, wuce muje Abba yace in dauko ki! ” kausar batasan lokacin da murmushi ya subuce a fuskar taba, yace wuce muje! Yaya bari inyi wanka insake Kaya na, “wani mugun kallo ya watsa mata ok ga d’an iska kin aje ko?! Injira ki gama iskancin ki sannan muje ko dallah wuce muje mallama,! A rude tayi gaba, dan uwar ki bazaki dau hijabi ba ahaka zaki fita! A rikice takuma juyowa ta sungumi hijjabin sallarta wanda idonta yakai kai, dasauri tasaka hannunta na rawa ta wuce shi yabiya da wani irin kallo kafin yabi bayanta,

“Gudu yaketa shararawa tamkar zasu tashi sama, kai tsaye hanyar barhim ya dauka, ido kausar ta zaro a zuciyar ta tace ina kuma zamu a barhim yanzu?” Mamaki ne yakuma kamata ganin yanata kukkutsawa cikin gidajan barhim din, haka nan ta tsinci kanta da faduwar gaba,

“A rikice ta dubesa tare da fadin ya Aliyu inakuma zamu?” A fusace yabata amsa dacewar gidan uban dakika aikeni nan zani! Bakinta taja tai shuru har zuwa lokacin dasuka isa d’aya daga cikin gidajan barhim din, dakansa ya sauka ya bude gate din da key sannan ya shigo ya shigar da motan ciki, hankalin kausar idan yayi dubu to yatashi, fitowa daga cikin motar yayi yaje ya bude gidan ya shiga, baiwani jima ba ya fito, bangaran da kausar take ya nufa ya bude k’ofar tare da fadin fito! Cikin daure fuska,a rikice Kausar ke dubansa, tsawa yakuma daka mata bazaki fito ba saina sabeki a wuya na! Dasauri ta sauko tana raba ido, hannunta ya jawo da karfi har zuwa cikin gidan, a falon gidan ya wurga ta sannan yakoma ya rufe kofar harda saka key, “kausar tashiga cikin tsananin rudani hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin falon dawani irin duhu sosai, ” hijjabin jikinta ya fisge yai wurgi dashi, wayyo Allah na nashiga uku na dan girman Allah kayi hakuri menayi maka?” Au! Bama kisan mekikayi min ba saboda kin dauke ni takkwali ko?! To bude kunnuwanki kiji ingaya maki!

“Ance wai inkawo ki domin kizaba wakikeso acikin nida Umar Faruq saikace wasu kayan gwanjo! To ni nafi k’arfin ayi min wannan domin kuwa ke kanki kinsan cewa dama rufa maki asiri kawai zanyi amman kedin ba ajina bace ai kinsani ko?!

” Dasauri kausar ta d’aga masa kai alamar eh! Gud! Saboda haka nasan cewa idanma anje din Umar Faruq zakice kin zaba dan haka yazama dole in yanke maku wani bangare nadaga jin dadin ku zan rabaki da abinda nasancewa Faruq zaiyi farinciki dasamunshi! Zan dasa maki wani miki a zuciyar ki wanda zaki ringa yawan tunawa dani idan kukayi aure! Kuma banason kuka ko kadan kukanki yana nufin inkara awannin danayi niyyar yi dake! Kukanki yana nufin kina jin dadin abinda nakeyi maki! Kukanki yana nufin abubuwa dayawa agare ni! Dan haka shurun ki dabani gudun mawa shi kadai ne GATANKI! “Nasha jinki kina furtawa Umar Faruq wai shine GATANKI! HMM! “KAINE GATANA!”

“Dan Allah kada kamin haka ya Aliyu kaji tausayi na karka yi haka dan Allah wallahi bazance inason Umar Faruq ba zance kai nakeso wallahi zan aure ka zansoka idan har ba ka aikata uzirin ka akai naba dan Allah ka rufa min asi please yaya Ali dan Allah…… Karya kikeyi kausar! Nizaki yaudara?” Karya kikeyi nasani karya kikeyi wallahi gara kawai in rusa maku farincikin ku dan nasan hakan ne kawai zaisaku BAK’INCIKI!

“Matsowa inda take yasoma yi, ganin hakan yasata sakin kuka a rude tana matsawa tana hadashi da girman Allah yayi hakuri gaba daya ta rikice kuka kawai takeyi tana fadin yarufa mata asiri! ” ci gaba da matsowa yayi harya k’ureta a jikin bangon falon, gaba daya yawani matseta yana matso da bakinsa saitin nata, wani irin ihu tayi wanda yabashi damar hade bakin su waje d’aya……………

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

7⃣5⃣to8⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Tsotsan bakinta yake tamkar yasamu alawa mai d’anbanxan zaki, ” hannayansa gaba daya suna saman k’irjinta yana wani matsasu yana lumshe ido saiwani nishi yake sama sama, kuka sosai kausar keyi duk iya kokarin ta ganin cewa ta turesa amman abin ya faskara, “kici kicin rabata da rigar jikinta yakeyi aikuwa data tabbatar da gaske yakeyi tuni ta gantsara masa wani mahaukacin cizo, a firgice yasaketa ya dauketa da mari tasss!!!!!

” A haukace ya fisge rigar jikinta gashi ko bra babu a tare da ita, wani ihu tayi hade da ajiyar zuciya lokaci d’aya ta tafi luuuuu! Tayi kasa a sume,

“A rikice yasaki rigar tata yabita ya dagota yana jijjigawa,kausar!kusar!kausar!!!!!!!!!! ” wani irin mugun tsoro ne yakamashi a rikice yakai kunnuwansa saitin kirjinta dan yaji koda rai a jikinta, dasauri ya dibo ruwa ya watsa mata a rikice yakeyin komi, amman ko motsi batayi ba hankalin sa ya tashi a rikice yake dubanta, yafi minti goma ahaka batare daya yankema Kansa shawara ba, “rigar ta yafara kokarin sakamata hade da hijjabinta, daukanta yayi cak zuwa cikin motarsa ya shimfideta a baya kafin yaje ya rufe gidan yana fadin wallahi kausar wasa nakeyi maki kawai nayi maki haka ne dan in tsorata ki amman bawai niyyata kenan ba na rantse da Allah dan Allah kada ki mutu ki tashi haka nan please natuba wallahi bazan karaba! ” da gudu yaja motar yajefata bisa titi bayan ya maida gate din yarufe, “gudu yakeyi naban mamaki Allah ne kawai yakai su asibitin dayake aiki lafiya, ” nanfa ya sunkuceta dagudu yayi ciki da ita,wata nurse data hango shi tabishi a baya da gudu itama,

“Duk wani kokarin sa naganin cewa kausar ta farka amman ina abin ya faskara nanfa hankalin sa ya tashi yanimi taimakon wani abokin aikinsa likita danyazo shima yanuna tasa k’warewar,

“Kuka Aliyu keyi sosai yana rokan kada Allah yasa yarinyar nan tamutu ta wannan hanyar shikam ya shiga uku mezaice da iyayan su, d’an likitan ne yadafa kafadar sa yana mai basa hakuri kayi hakuri Dr Aliyu insha Allahu zata farfado nanda awa uku ta tsoratane dayawa shiyasata shiga wannan halin, ka kwantar da hankalin ka komi zaixo dasauki insha Allah,

” Ajiyar zuciya mai k’arfi Aliyu yasaukar tare dayima likitan godiya, murmushi kawai yayi yafice abinsa yana mamakin irin rudewar da Ali yayi lallaikam yanaji dawannan kanwa tasa acewar likitan,

“Wayar sa dake aljihun wandonsa ya zaro yafara kiran number Abba,

” Gaba dayansu zaune suke a falon harzuwa wannan lokacin suna jiran zuwan su Aliyu din, Abba yagaji da korafi harya gaji yai shuru mummy ce ke tausar zuciyarsa, Umar Faruq kuwa jiyake tamkar yabisu danshikam sam baiyarda da Aliyu ba shiyasama baiji dadi da akace ya daukota ba yaso ace shine yaje ya daukota dakansa amman dai dole yahakura dan babu yanda zaiyi,

“Wayar Abba ce tashiga niman agaji dasauri ya daukota ganin number Aliyu yanaso yaji uwar dazai gaya masa ya shanya su tamkar kayan wanki, a fusace ya daga yana sauraransa, what!!!!! Garin yaya haka ta kasance?!………..mummy ce ta katse shi a rikice tana fadin meya faru abban su?” Wai hatsari sukayi a hanyar su tazowa yanzu kausar na asibiti……

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

8⃣0⃣to8⃣5⃣

 

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“A fusace Umar Faruq yamike yana fadin wallahi karya ne! Wallahi karya yakeyi! ” Abba karku yarda dazancan sa karya yakeyi…..tsawa mummy ta daka masa tana fadin bakada hankali ne?” To meye abin karyan aciki zancan Aliyun ne karya kokuwa zancan Abban kune karyar kokuwa hatsarin ne karya?” Dallah wuce kakaimu Mallan inga halin da yata ke ciki……..a fusace Umar Faruq yafice a zuciyar sa kuwa fadi yake na rantse da Allah saina d”aure Ali har igiya tai rara idan har abinda nake zato shi ya faru hmm!Barister Umar Faruq kenan me saurin karantar mutum, kodan yana Barister ne oho!

“Gudu yaketa shararawa kamar zai tashi sama mummy ta daka mai tsawa kai dan uwarka ni tsaya in sauka! wannan wani irin tuki kakeyi na hauka haka?” Wallahi Umar wannan bakar zuciya taka babu inda zata kaika gara kayiwa kanka fada tun wuri wallahi!

“Sassauta gudun yayi yanawani cika yana batsewa! ” A haka suka isa asibitin,nurse din dazu ce taimasu jagora zuwa dakin da kausar ke ciki kasancewar ta shaida iyayan Aliyu ne, suna shiga suka iskeshi zaune akan gadon datake kai yawani kafeta da ido, dasauri mummy taka rasa tana fadin Aliyu ya jikin nata?” Dasauki mummy bataji ciwoba tsoratane kawai tayi saboda yanda taga motar na juyawa amman dai Allah ya tsare nima babu abinda yasameni, yafada yana wani sosakai,

“Abba ma yakaraso kusa da gadon ya tattaba jikin kausar tare dayimata fatan samun lfy, ” Aliyu ne yacigaba dafadin ai dogon suma ne kawai tayi insha Allah nanda anjima kadan zata farka,

“Umar Faruq nadaga k’ofa yana kare masu kallo, shikam sam hankalinsa bai kwanta da zancan Aliyu ba bai kuma san meyasa ba, ” kujera suka ja suka zauna dukkan su ahaka har lokacin sallar azzahar tayi gaba daya mazan suka fice danyin sallah inda mummy ma tashiga toilet ta dauro alwala wata nurse ta bata dadduma ta shimfida ta gabatar da sallan ta,

“Ta idar kenan bada dadewaba Kausar ta farka a firgice daidai lokacin dasukuma mazan suka dawo suka shigo gaba dayansu, ” wayyo Allah na ya Aliyu kayi hakuri dan Allah wayyo!!!!!! Nashiga uku!!!!!!!!dasauri Aliyu ya karasa inda take yayi saurin yi mata allura ganin zata tada zaune tsaye!

“Wani irin shak’a Umar Faruq yayi masa yana fadin uban me kayimata! Mekayi mata Aliyu mekayi mata nace?!! “Sam Aliyu yakasa wani yunkuri dan yasan baida gaskiya gaba daya jikinsa yai bala’in yin sanyi, ” wani wawan mari mummy takwashe Umar Faruq dashi tana fadin bakada hankali ne?” Wai yaushe ka haukace ne ni bansani ba Faruq?! Kokuwa kanaso ka gaya min cewa kai bakasan kaddara bane?! Kokuwa kanaso ka gaya min cewa da gangan Ali yayi hatsarin da ita?” Idanuwan Umar sunkada sunyi jawur sai ajiyar zuciya yakeyi alamar ran maza ya baci! “Dakyar ya iya bude baki cikin sarkewar murya yace but mummy……. Shiiiii!!!!! Ta katse shi banaso inji komi daga gareka mezaka gaya min mezakace sake shi dallah! Asanyaye ya saki wuyar rigar tasa yanayi masa wani mugun kallo, Abba ne yace tunda haka abin yazama to dukkan Ku kuzo mu koma gida shi Alin yazauna da ita ya kula da ita har ta farka, yadubi Aliyu yace bana bukatar ayi mata wata allura idan har ta farka ataho min da y’ata gida kawai kanajina ko?” Eh naji Abba, oya kumuje yayi gaba yabarsu nan, wani irin kallo Umar yayi masa kafin ya fice, “mummy ce ta dafa kafadar sa tare dafadin kayi hakuri son bansan meke damun Faruq haka ba! Bakomi mummy kowa yayi nagari ai kansa! Hakane Allah yabata lafiya Ameen,

” Bayan tafiyar su da awa daya takuma farkawa tana ihu ido kawai Aliyu yasama har ta bude idonta ta diro daga kan gadon, ido suka hada da Aliyu hadiye kukan tayi tana fadin kayi hakuri ya Aliyu dan girman Allah kada ka tabani ka rufa min asiri please! “Wani irin malolo Aliyu ya hadiye ya dubeta yace kausar ki kwantar da hankalin ki wallahi dama wasa nake maki babu abinda zan maki kawai inaso in gwada ki ne dama kinji?” Kai kurum ta daga masa amman zuciyar ta sai bugun tara tara yake, “sai data huta tashiga natsuwar ta kafin yatasata gaba zuwa gida,………..

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)

 

 

[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

8⃣5⃣to9⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“BAYAN K’WANA BIYU”

 

“Babu irin nacin da Umar Faruq baiyiba akan Kausar tagaya masa abinda Aliyu yayi mata amman sa ta kiya,cewa take kawai wallahi babu komi towai kai ya umar mekake tunanin zaimin ne?” Hmm! Shikenan tunda bakiso ki gaya min yanzu munfara yan boye boye a tsakanin mu kenan, nima bazakidinga jin cikina ba daga yanzu! “Ahakadai aka shashantar da zancan,

“Da daddare bayan sungama cin abinci abba ya kira Aliyu yace maza yazo yana bukatar ganin sa yanzu, ” ba a dau wani tsawon lokaci ba saigashi ya baiyyana, zaune suke gaba dayansu a falon abba, yaran na zaune a k’asa su mummy kuma suna bisa kujera, “abba ne yafara da kallon kausar yace y’ata wannan taron fa domin ki akayi shi, yanyinki ne suke rigima akan ki to nikuma gaskiya banason abinda za a tauye maki hakki, dan haka yanzu zamu baki zabi acikin su ki fidda duk wanda yayi maki zuciyar ki keson shi kike ganin halinsa yayi maki kuma zaki iya zama dashi batare danaji wata rigima ta taso ba! Ina fata kin fahimce ni?” Zuciyar kausar in banda bugawa babu abinda yakeyi, itakam ansakata a tsaka mai wuya!

“Kanta tadan dago tasaci kallon Aliyu shima ita din yake kallo idonshi ko kiftawa bayayi, dasauri ta kauda kai, Umar Faruq ta kalla wanda shima nasa idon akan ta yake fuskar shi na dauke da murmushi,

” mummy tace uhum munajin ki baby na! “Cikin sarkewar murya tace abba ni yaya Faruq nake so……aikuwa kafin ta rufe baki Aliyu yai wani wawan tsalle ya kai mata wani naushi a baki nanda nan jini yafara zubowa, Umar Faruq ya mak’ure sa yana fadin uban me tayi maka dazakaji mata ciwo?! ” wani maka da Aliyu yai masa saigashi k’asa warwas, “Abba yace yauwa ku kashe kanku, idan d’aya ya kashe d’aya sai kuyi mana magana muna ciki, ” nafisa tashi muje! “Mikewa tayi itama adan fusace tayi gaba abinta, ” kuka sosai kausar keyi ganin kamar ran iyayan nata ya baci dangane da zabinta, “Umar Faruq ya mike ya nuna Aliyu da dan yatsar shi yace ” fice kabar mana gida tunda tace batayi dakai ai sai aje a rungumi hakuri aci gaba kuma da maneji da……..wani irin dariya Aliyu yayi yace k’arfin hali barawo da sallama! Yasake fashewa da dariya ya nuna Umar Faruq yace ni kake kora a cikin gidan nan?” Nida kai wayafi wani iko da gidan! Lalle to bari in tuna maka idan ka manta…….

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

9⃣0⃣to9⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Kul!!! Naji maganar nan tafito daga bakin ka,bakada hankali ne?” To yanzu idan ka tuna masa a haukar ka me hakan zai haifar?” Meye amfanin yin hakan?” Bashida wani amfani! Dan haka shurun shiyafi zama alheri! Fice kabani waje mutumin banza kawai! “Abba ne keta wannan fadan danjin Aliyu zaiyi masa katobara acikin gida!

” A fusace Aliyu ya fice kai tsaye gidan sa ya nufa yasa key ya bude kofar ya shiga, “gidan shuru tamkar babu kowa a ciki, kai tsaye wajan firij ya nufa gorar ruwan swan ya dauko irin babban nan, budewa yayi yakafa kansa yaringa kwankwada bashi ya ajeba saida yaga ya shanye shi tas! Sannan ya hakura ya fada bisa kujera yana maida numfashi tamkar wanda yayi tsere,

“Yafi minti goma ahaka kafin ya mike zuwa d’akin sa wanka yayi yaji sanyi kafin yasaka kayan baccin sa, wasu magunguna ya balle ya hadiya tare da korawa da ruwa sannan ya zauna kamar minti goma yana lallatsa wayar sa kafin ya kasheta ya fice daga d’akin tare da rufo k’ofar, ” kai tsaye d’akin ummi Aisha ya nufa ‘kwance take bisa makeken gadonta tana bacci, wata yar guntuwar rigar bacci ce a jikinta gaba daya ya tattare yayi sama, “kyakkyawan fuskar ta ya tsurama ido na tsawon lokaci kafin ya kashe wutar d’akin, gadon ya haye tare da jawota jikinsa yafara shasshafata cikin sauri sauri, ” a tsorace ta farka tana zare ido, “cikin rawar murya tace Aliyu dan Allah kayi hakuri ka yafe min bazan karaba please dan Allah! Shiiiii!!!! Ya dora dan yatsan sa bisa bakinsa,alamar taimasa shuru! ” cigaba da shafata yayi yanawani shinshinarta tamkar wani mage, jin yana kokarin rabata da rigar ta yasa tai saurin rike masa hannu tana kuka, Aliyu wallahi na gaji yaufa kwata kwata abinda karinga yi kenan ko fita yau bakayi ba in banda abba daya kiraka dan Allah kayi hakuri wallahi natuba bazan kara ba….bakin sa yakai cikin nata yanai mata wani irin salo, “da karfi ta fisge kanta tana kuka tana fadin nace kayi hakuri nace kayi hakuri kaki! Indai akan maganine ai ka kwashe bashi kenan ba to mezaisa ka ringa cutata!

” Hannu yasa ya kunna wutar d’akin yana kallon cikin idonta, a fusace yafara magana ohh!!! Ashe kinsan laifin naki! To tunda kinsani inaso inji meye dalilinki nayin hakan?! “Sonane bakiyi kokuwa kaunata ne bakiyi?! Kokuwa tsabagen iskanci ne dasamun waje! Ke nake sauraro! Kuka kawai takeyi sam takasa magana, daga k’arshe jawota yayi da k’arfin tsiya nan suka shiga kokawa da karfinsa ya kece rigar ya shiga aiki babu ji babu gani, tun tana daurewa harta fara zanbada ihu tana niman kufcewa, haka yaita wahalar da ita har asuba,

” Dasafe bayan yayi wanka yayi shirin zuwa aiki ya kalleta a fusace fuska babu annuri yace “kada indawo gidan nan in taddaki tunda baki kaunar hada jini dani banga amfanin zama dake ba! ” a tsorace take kallon sa har ya fice daga dakin ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya tana mai data sani, yanzu mezataje tace a gida?” Itakam tashiga uku idan mahaifin ta yasamu wannan labarin, wai ita anata haukan bataso tafara haihuwa yanzu ta tsofe Aliyu yai sabuwar Amarya ya fara yi mata wulakanci, ita kuwa a rayuwarta ta tsani kishiya ko sunanta batason ji! Yanzu meye lafiya?” Wayyo ni ummi Aisha “NAGA TA KAINA!” Aliyu meyasa zakace intafi gida bayan kasancewa “KAINE GATANA!”………..

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

9⃣5⃣to1⃣0⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“BAYAN SATI BIYU”

*******************

“Bayan dukkan wani sabani da a ka samu a k’arshe dai abba ya yanke hukun cin cewa nanda wata biyu za ayi bikin kausar da Umar Faruq kowa ya hutu, ” ran Aliyu ba karamin baci yayi ba dajin wannan furucci na abba, acewarsa ai dashi kausar ta dace bada Umar ba, kuma ai badole sai tanason saba za a Iya bashi ba, shikam gaskiya ba ai niyyar bashi bane kawai!

“Mummy ce keta kwantar masa da hankali, my son dan Allah kacire damuwa a ranka kasandai wani baya auran matar wani dan haka kaidai kaci gaba da addu’a kawai,

“Kausar kuwa sun dad’a kullewa da Umar Faruq soyayya akeyi baji ba gani akoda yaushe zaka samesu tare suna tattauna yanda bikinsu zai kasance, ” idan akai kaza za ayi kaza,kullum maganar kenan,Aliyu kuwa har zuwa gidan ya rage dan kuwa bayason ganin kayan takaici acewar sa, wani irin haushin su yakeji musamman ma kausar wacce yakeji tamkar ya mak’ureta dan tsananin haushinta dayakeji,
***********************

“Abba ne zaune a falo shida mummy suna dan tattaunawa akan bikin,
“Nafisa wani tunani ne nakeyi acikin zuciyata, a hankali mummy ta dubesa tare da gyara zama, tunanin mekakeyi haka abban su?”

“Inagani lokaci yayi dayakamata mu waiwayi k’auyen su yarinyar nan kausar saboda muji ko akwai wani lbr akan iyayan ta ko y’an uwanta, domin kuwa yakamata asakasu cikin lamarin auran nan koya kika gani?”

“Ajiyar zuciya tasauke mai Karfi tare da fadin tabbas kayi tunani mai kyau abban su, saidai wani hanzari ba gudu ba, mezai hana mu bari akare bikin lafiya sai mu tafi gaba dayan mu inaga su iyayan nata da yan uwanta zasufijin dadi ganin mun riketa da amana harmun aurar da ita,inaga hakan zaifi koya kagani?” Hakane nafisa, hakane, abinda yakamata kenan,Allah yayi mana jagora Ameen,
***********************

“BIKI WAN SHAGALI!”

“Biki fa ya kankama shagali kuwa babu kama hannun yaro, biki akeyi na kece raini abin sai wanda yagani, anyi party yakai kala goma sannan daga k’arshe aka gudanar da walima wanda yatara manyan malamai akayi wa Amarya da ango nasiha mai ratsa jiki wanda gaba dayansu babu wanda jikinsa bai yi sanyi ba,(Aliyu dai yace shiririta kenan saida aka gama zuk’e albarkar auran awajan party sannan za a wani fake da walima)

” Ranan d’aurin aure yakasance jama’a bayan ansauko masallaci, dubunnan jama’a suka shaida d’aurin auran Umar Faruq da kausar, “hakika wannan d’aurin aure yaga tarin mutane daga kasa kasa gari gari kasancewar abba d’an siyasa,

” Amarya tayi kyau harta gaji duk wani gyara daya kamata aimata babu wanda ba ai ba musamman mummy ta dauko masu gyaran amare tundaga Niger, sokoto, Maiduguri, dan kawai a gyara mata y’arta ciki da bai, aikuwa ba karamin gyara tasha ba dan har wani k’elli takeyi batun k’amshi kuwa ba a cewa komi domin kuwa itacema k’amshin! “Maganin mata kuwa masu inganci tasha su har tausayawa kanta takeyi domin kuwa tasan ma’anar su tunda ba k’ankanuwar yarinya takeba, hatta Umar Faruq mummy bata kyale ba shima ya shassha wayanda suka dace yasha, har mamakin mummy yakeyi sam batajin kunyar su kanta a waye yake tazama free da y’ayan nata shiyasa suma basa iya boye mata komi nasu, fruits kuwa sunshashi harsun gode Allah domin sunama kan sha dan kuwa yazame masu abincin cinsu, gaskiya mummy ta taka rawar gani!

“Da daddare anata shirye shiryan kai Amarya gidan ta,wata kanwar mummy ce ke shirya ta cikin wata lifaya tayi bala’in yin kyau tamkar a sace a ruga, wayar ta sai tsuwwa takeyi, gashi sai kira akeyi babu kakkautawa, kanwar mummy mai suna maijidda ta miko mata wayar amshi hala ma angon ne ya ishemu inma yayi hakuri ai yanzu ne za a kai masa ke! ” kausar dai ta amsa tana murmushi kafin ta duba screen din wayar aikuwa shine ke kiranta, asanyaye ta d’auka tana fadin “hello!” Ki fito wajan gate yanzu ina jiran ki kiyi sauri! “Daga haka bai kuma cewa komi ba ya kashe wayar tasa, dasauri ta mike tace anty maijidda inazuwa dan Allah! Ina zaki inazuwa dai tayi ficewar ta mata dankare a falon anajiran fitowar su, dasauri sauri ta fice kamar wata tsuntsuwa dan bama kowa ya lura da ficewar taba, ” hankalin tane bai kwanta ba dayanda taji muryar Faruq dinta jin muryar tayi tamkar ba tasa ba, kuma tamkar wanda yasha kuka ya koshi!

“Tana fitowa wajan gate din taga motarsa batare da tunanin komi ba ta fada kasancewar motar tint bataga kowaye ba harsai data shiga ta zauna, motar ya dannawa luck, a firgice take kallonsa ita rabonma data gansa tunkan asoma hidimar biki! Bakinta na rawa tace “yaya Aliyuu!!……….

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:25 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣0⃣0⃣to1⃣0⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

©TASKAR MARUBUTA?

Bakinta na rawa tace
yaya Aliyuu!” bai sauraretaba yaja motan dagudu wanda hatta mai gadin sai dayaji tsoro dagudu ya lek’o dan ganin meke faruwa, baici nasarar ganin komi ba illa iyaka kurar daya turnike wajan, a dan tsorace yadawo ciki yana kissima abubuwa a zuciyar sa, to koma dai meye Allah yasa lafiya acewar sa,

” Gudu Aliyu yake a titi kamar zai tashi sama,itako kausar sabo da tsabar tsoro ta kasa magana saidai jikinta dake rawa kamar ana kada mazari,idonta kuma nafidda hawaye kamar anbude famfo ta takure jikinta akujeran, tana mai rokon Allah ya rabata da sharrin Aliyu Haydar!

” Acan gida kuma anty maijidda tagaji da jiran kausar gashi mutane harsun fara kosawa, wata yayar su mummy ce tashigo tana fadin maijidda wai wani irin shiri kikema y’ar taki haka ne har yanzu kunki fitowa tamkar an shuka dusa?” Ganin maijiddar ita daya yasata fadin to ina amaryar kuma?” Murmushi anty maijidda ta kirkiro na karfin hali tace tashiga toilet yanzu zata fito, “to yakamata dai tafito haka nan ahadata da abban nasu yaimata nasiha atafi hakanan dan ga hadari nan ya hadu sosai mutane kowa naso akaita ya kama gabansa, tafice abinta tana ci gaba da sababinta,

“Hankalin Anty maijidda yakara tashi ganin ankuma k’wasar wasu mintinan batare da dawowar kausar ba, haushi da takaici yasata
fitowa daga dakin tanufi d’akin mummy kai tsaye, tasami dakin cike makil da kawayen mummyn, matsawa tayi har inda mummyn take ta sassauta murya tafada mata cewa faruq yakira kausar gashi haryanzu bata dawoba kuma tashafe sama da minti talatin,

” Aiko nan mummy tahau ta dafada meyasa zata barta tafita wannan ai rainin wayau ne! wani irin aikin banza ne zasu maidamu iyayen kawai,kai yaran yanzu suncika zumudi inyayi hkr saura minti nawa ne zaakai mishi ita?” Wata kawar mummy ce tafadi haka jin inda zancan na mummy ya nufa, maijidda dauko mun wayata gashi can akan drower inkirashi inji inda suke.

“Anty maijidda tanufi wajan da sauri zuciyar ta cike da takaicin yanda aka d’ora mata laifin fitar kausar din, mummy takira wayar faruk fiye dasau goma amman shuru babu amsa, tashiga kiran kausar din itama shuru daga k’arshe ma aka kashe wayar, hawaye ne yacika idon mummy wannan wani irin tijara ne haka!

“A bangaran Umar Faruq kuwa tun bayan d’aurin aure yake niman wayar sa bai ganta ba bai kuma san ina ya ajetaba har izuwa yanzu da abokansa suka cika farfajiyar gidan su da motoci na alfarma dan daukar amarya, gaba dayansu sun kosa daganin fitowar amaryar dankuwa har an fara yayyafi, sai a lokacin ya lura da babu motarsa ma a inda ya ajeta, bai wani damuba dan yayi tunanin kila daya daga cikin abokansa wani ya dauka tunda sha’ani akeyi kuma dama key na ajiki yabar ta dazu dan saurin yashiga ya fito,” wani abokinsa mai suna faisal yace kai Faruq ka shiga ka fito da ita da kanka tunda sunki fitowa, hararar sa Umar Faruq yayi yace ai sai kazo ka jawoni! Bai karasa fadin abinda yayi niyya ba yayi shuru dan hango mummy dayayi ta taho wajansa a fusace,

“Batai wata wata ba tanazuwa ta d’aukeshi da mari har guda hudu k’warara baki yasake yana kallonta hannunsa dafe da k’uncinsa, bama shi kadai ba gaba daya abokansa dake wajan bakin nasu a bude yake suna tambayar zuciyoyinsu dameyayi zafi haka za a tsittsinkawa ango mari a irin wannan lokacin?”

“Hannu ta nuna masa tana huci, cikin sarkewar murya tafara magana daganinta kasan ranta a matukar bace yake, aidama ance tsintaccan mage bashi mage! Nizaka wulakanta ka tozarta?” Menayi maka Faruq dakake nima ka kunyatani a idon duniya?” Cikin kidima yace ban fahimce kiba mummy menayi maki?” Wani marin takuma sakar masa tana fadin au! Tambayata kakeyi?” To ina kausar?!!!! A firgice ya dubeta yace kausar? Wallahi mummy tunda safe rabon da in ganta! “Murmushin takaici tayi tace ni zaka rainama hankali Faruq ta nuna kirjinta da dan yatsanta, na rantse da Allah mummy rabona da inga kausar tun dazu da safe! ” ido mummy ta zaro tana kallon sa……….

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:26 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣0⃣5⃣to1⃣1⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“ido mummy ta zaro tana kallonsa cikin rawar murya tace kausar din allura ce kenan dazata bace ko?! ” wani tunani ne yazowa Umar Faruq dasauri ya juya zai tafi mummy tace wallahi umar zanci mutuncin ka idan baka turo min y’ata ba! Mummy Kausar na wajan Aliyu duk inda yake a yanzu! A fusace tace mekake nufi da wannan kalma taka?! Cikin wata irin murya tayi maganar, bai kara cewa komi ba dasauri yabar wajan, ido ta bishi dashi kafin tayi k’wafa ta wuce,

“Da sauri faisal yabi bayan Umar da mota, mai gadi ya bude masa ya fice can ya hango umar nata sauri ko ina zashi oho! Hon yayi masa dasauri Umar Faruq ya waigo yana ganin shine ya fada motar yana fadin Faisal taimaka muje barhim yi sauri dan Allah! Cikin rashin fahimta Faisal ya dubesa mezakajeyi ne a barhim yanzu?” Cikin kuluwa yace baza ka kaini bane in sauka?! Dasauri yaja suka tafi,

“Kuka takeyi sosai tana fadin nace maka bazan shaba dole ne! Wallahi ka maida ni gida Aliyu idan baso kake inyi maka abin da baka zata ba! ” dubanta yakeyi da tsananin mamakin yanda sam yaga rashin tsoron sa a idonta, ni kikema tsawa kike kirada Aliyu gatse haka?! Ni tsaran kine?! Na fada na fada kazo ka maida ni gida! “A fusace ya jawota yana fadin wallahi saikin sha shi matse ta yayi da k’arfin tsiya duk iya kokarinta na ta kufce ta kasa sai mutsu mutsu take, hannuwanta ya batse a bayanta sannan yashiga dura mata yar maganin dake cikin kwalba na hannunsa, saidaya dure mata shi tas sannan ya saketa , dasauri ta mike, saikuma ta tsaya cak tana kallonsa nanda nan idanuwan ta suka canza kala, ” a hankali ya taso ya iso inda take dasauri ta fada jikinsa tana maida numfashi, dago kanta yayi yana kallon cikin idonta sannan yace kausar! “Dakyar ta iya amsawa yace kina sona?” Dasauri ta daga masa kai, ko tunanin meyayi oho kawai dasauri ya tureta daga jikinsa ta tafi luuu zata fadi dasauri ya tare ta daukarta yayi cak zuwa bisa kujera ya kwantar da ita yana kallonta hawaye ne ke bin fuskar ta ita kanta batasan na meye ba, cikin murya kasa kasa tace ya Aliyu dan Allah matso kaji! Kai kawai ya girgiza mata alamar a’a kawai saita fashe da kuka tana fadin pls ya Aliyu pls……tsayuwar mota yaji daga wajan gidan can, dasauri ya karasa wajan window yana lekawa, Umar Faruq ya hango ya bude gate din da Karfi tare da shigowa kamar wani zaki haka Aliyu ya hango sa, aikuwa dawani irin sauri ya isa inda kausar take yasoma rabata da kayan jikinta, ita kuwa dasauri ta goge hawayenta tana murmushin jin dadi rikeshi tayi tana fadin i love you Aliyu…. Kuramata ido yayi yana kallonta, fisgoshi tayi ya fado kanta tashiga shafashi ta ko ina daidai lokacin Umar Faruq ya bugo k’ofar da karfi yashigo, cak ya tsaya yana kallon ikon Allah Aliyu najinsa amman yayi kamar baijiba, yace kausar kibari kinsanfa ke matar aure ce ko?! Rikeshi takarayi tare da tura masa bakinta cikin nasa, wani irin mugun tsawa Umar Faruq ya daka masu yana fadin tir da halinku masu halin karnuka! “Adan firgice irin ta yan duniya Aliyu ya daga kausar yana wani kauda fuska, ” dasauri Umar ya karaso cikin falon kai tsaye kausar yafara fisgowa tare da kifa mata mari ya shaketa yana fadin nizaki cuta kausar ni zaki wulakanta?! “Hawayene yasoma gudu bisa fuskar sa sakinta yayi kafin shiga dukanta yana fadin nasake ki kausar! Na sakeki! Na sakeki bana kaunar ki kausar bana kaunar ganinki! Ganin dukan yayi yawa yasa Aliyu shiga tsakani yana fadin to dama kai sai yau kasan muna irin wannan haduwar da ita, dallah malan bar dukan masu y’a tamkar kasamu jaka kaji ko?! Kausar wacce ke kuka sosai sam ita bama tasan metake ciki meke damun taba,

” fada ne ya kaure a tsakanin Aliyu Haydar da Umar Faruq naushin juna sukeyi sosai suna zage zage, Faisal dayaji shurun yayi yawa ya shigo gidan saboda ai shidai a iya saninsa wannan gidan Aliyu ne kuma ba zama yakeba, dan haka kai tsaye ya shigo har falon dasauri ya karaso ya shiga tsakaninsu yana fadin meye haka meye haka?! Bakuda hankali ne?! Dakyar suka rabu sai a lokacin hankalin faisal yakai kan kausar wacce keta kuka itakam kukan katse masu hanzari da Umar Faruq yayi takeyi wani irin abu takeji tamkar zata mutu, “dasauri Faisal ya kauda kansa izuwa yanzu yagama fahimtar komi, hannun Umar Faruq ya kama suka bar gidan, dasauri shima Aliyu ya maida ma kausar kayanta yaja hannunta suka fice daga gidan tana kuka tana tirjewa……

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:41 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣1⃣0⃣to1⃣1⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

Note
Afuwan pls, naji k’orafinku dangane da last page dina! Kuyi hakuri banyi daniyyar cin zarafin aure ba ko makamancin haka ba sam! “Yakamata kuyi min uziri kuji k’arshan lbrn.
****************************

 

“A lokaci daya suka k’araso gida inda mai gadi ya wangale masu gate Aliyu ya faka motarsa inda shima faisal ya paka tasa, a lokaci daya suka fito d’ukansu, idanuwan Umar Faruq sam babu kyawun gani sun kada sunyi jawur, ahaka ya doshi falon abba, Aliyu na ganin haka ya juya yai tafiyar sa, kausar tabishi da kallo tanason tuno wani abu amman ina tunaninta ya tsaya cak! ” dasauri tabi Umar Faruq da gudu wanda harya kusa shiga falon abba,

“A lokaci daya suka shiga falon yana gaba tana bayansa, mummy da abba ne tsaye cirko cirko a falon dukkansu sun tsura ma kofar shigowa ido, ” wani irin tsawa abba ya daka masu yana fadin daga ina Kuke?! “Umar da zuciyar sa ke tafasa kai tsaye yace daga barhim muke! ” wani irin mugun kallo mummy ta watsa masa hade dacewa dan iskanci amman umar ka kyauta mana kenan mutara jama’a sai ka dauketa ku fice abinku?” Wannan wani irin rashin kunya ne ni tunda nake bantaba jin irin wannan tantirancin ba kawai dai dukkan ku kunnuna mana bamuda cikakken iko akan ku shiyasa kukayi mana ahaka amman babu komi kanku kukai mawa, kekuma Kausar ta nuna ta da dan yatsanta, rashin kunya ko?” Kinbishi kun fice dan rashin mutunci to bari kiji shi namiji komi yayi adone kekuwa mace fa?” Hmm! Komi daran dadewa saikin…..kul nafisa kul! “Karki sake kiyi mata baki a matsayin ki na uwa! “Kai Umar Faruq kanajina ko?” Maza dauki matar ka kutafi Allah yabada zaman lafiya! “Hawaye ne yafara bin fuskar Faruq bakin sa na rawa yace kuyi hakuri abba…..shut up!! ” ka dau matar ka ku fice nace!

“Cikin tsananin bacin rai Umar Faruq ya fice kausar tasamu kanta dabinshi a baya, baisan tana binsa ba saida ya isa jikin motar sa,karki karaso nan! Yafada cike da hargowa, cak tayi tsaye tana zaro ido lokaci daya abubuwan suka fara dawo mata, hannu biyu tasa ta dafe kanta tare da kurma razanannan ihu,

“Da gudu mummy da abba suka fito saura kiris mummy ta kifa da gudu Kausar ta fada jikinta tana wani irin kuka hade da ihu, a firgice mummy ke tambayar ta meya faru?” Ina kuka kawai take tana fadin nashiga uku mummy nashiga uku! “Cikin lallashi abba ke fidin kausar natsu kiyi mana bayani meke faruwa?” Dole idan ka kalli Kausar sai ta mugun baka tausayi gaba daya ta fice daga cikin haiyyacin ta,

“Hawaye mummy tafara itama dan kukan kausar bakaramin taba bata zuciya yake ba, ganin hakan abba ya tarkata su d’uka zuwa falon sa,

” Umar Faruq kuwa tunsanda kausar tasaki ihu ya fice da motar sa cike da kunar zuciya sam ya tsane su baya bukatar ganin su ko kadan! Gudu yakeyi bisa titin shi kansa baisan inda ya nufa ba lokaci daya kuma ya fashe da kuka harda shessheka, wata babbar mota ce ta nufosa gadan gadan, duk iya kokarin sa na ya kauce mata amman ina….kiiiiiiiiiii!!!!! Cikin hukuncin Allah motar ta tsaya cak sai dai wani abin mamaki sam Umar Faruq baya motsi kansa bisa sitiyarin motar, mai babbar motar ne yayi saurin fitowa dan ya duba lafiyar sa aikuwa yana karasowa yaga halin da Umar Faruq ke ciki, tsoro ne ya mamaye zuciyar sa yana tunanin kila tsoratan dayayi ne yajawo masa hakan,

 

“Nafisa kina kuka tana yi yaza ayi musan meke damunta for god sake! Dan girman Allah kiyi shuru mu rarrasheta muji meke faruwa! ” saboda shima umar na lura kamar baya cikin haiyyacinsa kawai dan yariga ya batan raine shiyasa nayi masa haka, y’ata kiyi shuru haka nan kiga yamin meke faruwa? ” cikin wani sabon kukan kausar ta kan kame mummy tana gaya masu abinda yafaru wanda ganinsa tayi tamkar a mafarki komi ya faru,

“Cikin tsananin tashin hankali suka shiga k’wad’a salati suna mai tsananin al’ajabin faruwar hakan, abba ne ya mike cikin tsananin fusata yana safa da marwa a tsakiyar falon fuskarsa sam babu annuri ko kadan, mummy kuwa kuka ta fashe dashi tana fadin meyasa Ali yayi haka why?” Lallai kuwa wannan karan zan nuna masa yayi babban kuskure a rayuwar sa dan bazai taba samun abinda yake ma k’wak’wa ba Sam!!

“Wayar abba ce tashiga kuwwa a cikin falon, jiki a sanyaye abban ya tafi ya d’auka da kyar ya iya bude baki cikin sarkewar murya yayi sallama, tsawon minti uku ya dauka yana wayar kafin ya iya furta Kalmar ya salam da k’arfin sa, “ganinan zuwa doctor dan Allah Ku kular min dashi kafin in k’araso……..

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:43 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣1⃣5⃣to1⃣2⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Mekuma yafaru?” Mummy ce ke tambayar abba, Umar Faruq ne ba lafiya yana asibiti! “Ya salam! Tafada da k’arfi” kai Aliyu! Aliyu! Aliyu bai kyauta mana ba sam wallahi! “Nafisa tashi muje yanzu ba lokacin takale takale bane, ” gaba daya suka fice harda kausar dake faman kuka ayanzu kukan nata ma karuwa yayi danjin cewar Umar Faruq ba lafiya tasani koma meye yasami umar dinta to Aliyu ne yajawo masa kuma bazata taba yafe masa ba sai Allah yayimata sakaiya! Tanajin tsanar Aliyu mai tsananin gaske a zuciyar ta,

“Suna isa asibitin adai dai lokacin da likitan ya fito daga d’akin da umar din yake ciki, “Dr Muhammad safana kenan,likitan daya kasance family doctor dinsu, kasancewar asibitin yafi kusa da inda abin yafaru shiyasa direban yakawosa nan, sai kuma Allah yasa sukayi dace da k’wararran likitan yana kusa, atake ya shaida Umar Faruq dan haka yai gaggawan sanar da abban sa, ” gumin fuskar sa ya share da dan hankicin hannunsa, dasauri su abba suka nufosa suna tambayar meke damunsa?” Nan yace masu su biyo shi office dinsa yai gaba abinsa, “jiki a sanyaye suka rufa masa baya bama kamar kausar wacce ke d’aga k’afa dakyar,

“Bayan sun zazzauna ne likitan ya dubi abba tare da cire farin madubin dake idon sa, yace ku kwantar da hankalin ku alhaji, abinda muka dade muna jira ne yake kokarin faruwa insha Allah! Watau abinda ya faru shine hatsari ne yaso ya afku dashi Umar Faruq din to sai Allah ya tsare hakan bai kasance ba, to saboda tsorata da razana dayayi shine k’wak’walwarsa ta juya atake abinda yafaru a shekarun baya suke so su dawo masa to a sanadiyyar hakan ne yasashi shiga wannan halin dayake ciki, to amman insha Allahu daya farka zai dawo cikin hankalin sa abinda yafaru a dacan duk zai tunosu, idan baku manta ba dama na gaya maku cewar duk dadewar daza ayi idan Allah yaso to zakuga yadawo tamkar yanda yake saboda dama yayi losing memory dinsa ne idan ban manta ba shekara goma sha biyar kenan da abi ya faru koba haka ba?” Hakane doctor inji abba, “mummy tace to yanzu doctor kana nufin idan ya tashi zai iya gane garin su dakuma yan’uwansa da komi nasa kenan?” Mummy tayi tambayar cikin rawar murya, “eh haka nake nufi hajiya! Insha Allahu nan da awa uku zai tashi! To doctor mun gode kwarai Allah yasaka da alheri, ” kausar dai sai dubansu takeyi sai kace wacce ta bace, “doctor zamu iya ganinsa kuwa?” K’warai kuwa saidai baya bukatar hayaniya!

“Zaune suke dukkan su sun zagayeshi, a lokacin agogo yana nuna mana k’arfe d’aya da rabi na dare, ” kausar na lafe a jikin mummy sam takasa run tsawa gashi anyi anyi da ita tabi su Anty maijidda su koma gida sanda sukazo amman sam ta kiya, dole suka rabu da ita suka tafi, ita kanta mummy abba yace ta tafi gida amman tace gara zaman ta anan din yafiye mata kwanciyar hankali dan kota je gidan ba iya bacci zatayi ba, “wasu irin na’urori ne aka jona masa akansa sai wani haske abin keyi yana canza kala, lokaci daya abin ya dau wani irin kara gaba daya hasken ya dauke dif gadon tare da shi Umar Faruq din sai jijjiga sukeyi, dasauri abba ya rikesa,

“Doctor Muhammad nacikin office dinsa ya k’ura ma wata yar computer ido dasauri ya mike ya fice daga office din tare da nufar d’akin da Umar Faruq ke ciki tamkar zai kifa, dasauri ya zare masa abin tare da dafe masa kai yana kallonsa, wani irin ihu Umar Faruq yayi da k’arfi sai kuma yafara fadin Kalmar…innalillahi…..tare kuma da kalmar shahada…a lokaci daya kuma yake fadin babaaaaa!!!!!!!! ” sai kuma ya fashe da kuka a lokaci daya ya bude idonsa, ido hudu sukayi shida kausar atake yai tsit yana kallonta irin kallon da ake kira na kurullah, saikuma ya kauda fuska yana kallon kowa na d’akin daya bayan daya, sannu Umar Faruq sannu kaji! Abba ne ke fadin hakan, kallo kawai Faruq ya bishi dashi a zuciyar sa yana maimaita sunan Umar Faruq din, to su kuma wayannan suwaye haka?” Atake ya maida dubansa a jikinsa dasauri yasaki salati yana kokarin mikewa tsaye, dasauri doctor ya dakatar dashi ta hanyar cemasa yi hakuri Umar Faruq nasan kana mamakin yanda akayi ka dawo haka ne to ka kwantar da hankalin ka zuwa gobe insha Allahu za kaji komi da yardar ubangiji,……….

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:43 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣2⃣0⃣to1⃣2⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Gaba dayansu sun hadu a falon abba wanda dakyar Umar Faruq ya yarda ya biyosu acewar sa shi kam bai sansu ba kuma shi basunansa Umar Faruq ba suna shi “Nasir!” Dakyar dai abba ya lallabasa, “Aliyu kuwa wanda abba yai masa waya cewar yazo maza yana niman sa cikin tashin hankali ya iso gidan yana addu’a Allah yasa kausar bata tona masa asiri ba ameen, saidai shigowar sa falon abban ne ya raina kansa inda abba yadin ga kifa masa mari tare dacin kwalarsa yana fadin nizaka tozarta Ali! Irin tarbiyyar danabaka kenan Aliyu?” Kai ranan Aliyu yasha mari da zagi na fitar hankali daga karshe mummy ta karbe tayi tayi itama tamkar zata ari baki, fuskar sa duk ta kumbura da mari, kausar kuwa dadi tamkar ya kashe ta ita aganintama wannan ai yayima Ali kadan, batasan me zatayi masa a duniya ta huce ba amman tasha alwashin cewa saita rama kota halin k’ak’a!

“Umar Faruq dai sai binsu da ido yakeyi shikam wannan abu na matukar d’aure masa kai ya matsu yaji meya sameshi haka ne?” A daya bangaran na zuciyar sa kuma yana tunanin k’anwar sa da baban sa!

“Bayan komi ya lafa ne abba ya dubi Umar Faruq yace ka gafarce ni d’ana yanzu zakaji abinda yafaru,

“Shakara goma sha biyar data wuce a wata safiyar jama’a a hanyata ta zuwa k’urfi nida d’ana Aliyu muka sami hatsarin mota a hanya idan baka manta ba kaida mahaifin kane a cikin motar yana tuki kai kuma kana gaba to inajin motar ce ta k’wace masa daidai lokacin nikuma na taho da gudu to idan Allah yakawo tsautsayi babu yanda za ayi, Allah yariga ya hukunta, nasami karaya a k’afata da hannuna inda d’ana Aliyu kuma hannunsa na dama ne ya k’arye, mahaifin ka kuma Allah yayi masa rasuwa kai kuma kasami juyewar k’wak’walwa inda likita yasanar mana cewa ka mance da duk wani abu daya faru dakai a baya illa sabuwar rayuwa dazaka fuskanta, saidai akwai yuwuwar dawowar hankalin ka zuwa wasu shekaru masu yawa wanda shi kansa bazai ce gasu ba,

“To bayan ka war ware ne na d’auko nadawo dakai gida na ina rike dakai har zuwa yanzu bayan mun saka maka suna da Umar Faruq! Munyi iya binciken mu dan gano dangin ka amman wallahi sam hakan bai samu ba bamu taba jin wanda yace yasan kaba, gaba daya dai abba yafada masa komi bai boye masa ba harda abinda Ali yai masa bai rage ba!

“Nanfa Umar Faruq yashiga kuka wiwi suna lallashinsa,dakyar suka samu yai shuru inda shima yasoma basu labarin sa kamar haka,

” Mahaifiyata Allah yayi mata rasuwa a wajan haihuwar k’anwata wacce tazamemin “SANYIN IDANIYATA! “muntaso nida kanwata a hannun matar baban mu wacce takasance mace ce mai son zuciya! Sam bama jin dadin zama da ita musamman ma k’anwata wacce takasance yar shekara hud’u a lokacin, ina tsananin kaunar yar’uwata dakuma tausayinta, haka matar baban nan tawa take azabtar damu gashi baban mu bashi da tacewa akanta sai abinda tace, ahaka dai har na kammala karatun secondary school dina anan cikin garin dutsanma din inda nasamu admission a umaru Musa yar’adua university, to a lokacin da hatsarin nan ya afku muna kan hanyar mu ne nazuwa can makarantar domin infara registration, munbar matar babana a gida tare da k’anwata gashi kuma Allah yayima baba rasuwa ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, hakuri d’uka suke ta bashi tare dayima iyayan nasa addu’a,

” kausar wacce taji tausayinsa ya bala’in kamata atake tasoma kuka tana tuna rayuwar ta itama dayanda ta bar goggon ta itama a garin dutsanma, nan tace yaya Umar Faruq ashema garinmu daya nan yayi mamakin ashe basu abba suka haifetaba, abba ne yabashi labarin ta itama ya tausaya mata matuka sai tunanin k’anwar sa yadawo masa d’anye yana tuna ko a wani hali take yanzu a hannun wannan azzalumar matar oho! Nanda nan hankalin sa yayi garin dutsanma yanaso yaje yaga a wani hali k’anwar sa take,

“Atake ya shaida ma abba k’udirinsa tare dayi masa godiya bisa d’awainiyar dasukayi dashi har yazama wani a yau! ” abba yace kayi hakuri umar ka kara warwarewa sai mutafi gaba dayanmu mudubasu ina gani hakan zaifi, nanfa umar yace shifa alanbaran bazai iya kara k’wana batare dayaga k’anwar saba gaskiya! “A dole suka shirya gaba dayansu cikin k’atuwar motar abba suka d’au hanyar dutsanma……..

 

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:44 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣2⃣5⃣to1⃣3⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Sunshiga cikin garin dutsanma da misalin k’arfe sha biyu da rabi na rana, nan danan hankalin kausar yai bala’in tashi zuciyar ta tahau bugawa tana tunanin haduwar ta da goggonta dan kuwa abba yace har can gidan zasu domin su sadu da dangin kausar din, ” har abada kamannin garin nasu bazai taba sauya mata ba, duk da ci gaban da aka samu na karin gine gine dawasu sauye sauye, zuciyata bugawa kawai yake tamkar zai fado k’asa,

“Shi kuwa Umar Faruq wani irin farinciki ne ya lullube masa zuciya, awani bangaran kuma yana danjin faduwar gaba dan bai san a halin dazai tarar da kanwar tasaba,

“Shike zaune a gaba da abba dan haka shike nuna masa hanya, “mamaki ne yakama kausar ganin sun tsaya cak a k’ofar gidan su, ido ta zaro itakam tsoron shiga gidan nan take, towaima ya akai ya Faruq yasan gidan su?” Tambayar datakeyiwa kanta kenan, mamaki bai gama kamata ba sai da dukkansu suka sauko daga motar taga ya Faruq ya nufi k’ofar gidan yana doka sallama, hannun mummy ta matse da k’arfe cikin nata tana sauke ajiyar zuciya,

“Muryar goggo sukaji cikin fada tana fadin waye haka yake doka min sallama kamar naci masa bashi ban biya ba!” Gaban kausar ne yayi bala’in faduwa jin muryar goggo, shi kuwa Umar Faruq zuciyar sace ta tsinke yana fadin haryanzu dai tananan da bakin halinta!

“Goggo ce ta karaso tana kallonsu d’aya bayan daya,kafin ta tsada idonta akan Umar Faruq, cikin wani irin kid’ima da rawar murya take furta kalamar nasuruuu!!!!!!!!!!!! ” A tsorace take ja baya tana nuna Umar Faruq, “dama kana raye baka mutuba?” To ina mallan yake?” Wayyo ni talatu naga ta kaina dama kuna raye tsawon wannan lokacin kuka yada ni?! Sai kuma tasaki kuka mai k’arfi tana ihu, “ganin zata tara masu jama’a ne Umar Faruq yace abba mu shiga daga ciki, gaba dayansu suka shiga banda kausar data saki hannun mummy ta kame a bakin k’ofa, mummy tace muje mana hawaye na bin idonta ta girgiza ma mummy kai alamar bazata ba, wata kod’add’iyar tabarma goggo ta shimfid’a masu tana fadin bisimillan ku, d’uka mazan suka zauna akai abba ne yakai dubansa kan mummy dake ta fama da kausar yace nafisa meke faruwa ne?” Abban su kausar ce taki shigowa wai ita tsoro takeyi ni narasa tsoron me takeyi haka ji yanda jikinta ke rawa fa, abba dakansa ya mike ya kamo hannun Kausar suka shigo ciki, ido goggo ta tsare kausar dashi sai dai sam bata ganeta ba kamace kawai acewar ta, kai nasiru ina Malan?” Ina kabaro shi ne?! “A hankali Umar Faruq yace Allah yayima Malan rasuwa nan dai yabata dukkan labarin da abba ya bashi, aikuwa atake goggo tasaka ihu tana fadin shikenan tashiga uku ta lalace sai kace wata arniya, aikuwa nanfa mata suka fara cika gidan ana tambayar ta ko lafiya?” Kuka take tana fadin Ashe Malan mutuwa yayi Allah yayiwa malan rasu hatsarin mota sukayi Ashe shida nasiru ga nasirun nan yanzu suka iso shida mutanannan yake fada mani, tasake sakin wani sabon kukan tana jan hanci,

“Nandai akaita jajanta mata saikace a lokacin abin ya faru, ” babar rahane kawar kausar wacce suka tafi birni atare idan baku manta ba tace ohhh! Allah mai iko to kuma ina shi nasirun ya gano kausar ko ba ita bace wannan ne dannaga wannan y’ar gayuce dukda dai shima nasirun yazama d’an gayu dakyar na shaida shi?” Goggo tasake kallon kausar wacce gaba daya jikinta k’yarma yakeyi tace A’a ba ita bace kamace kawai waccan y’ar iskar ai izuwa yanzu nasan ta mutu tunda yawon karuwanci tasaka agaba! Yanzu kuwa wannan ciwo na zamani ai baya k’yale tsinannu la’anannu fasikai! Ubansu yakece aini wallahi nagode wa Allah kullum godiya nake agaresa!

“Cikin muryar kuka kausar tace wallahi nice goggo wallahi ba yawon karuwanci najeba! Tafada tana mai fashewa da kuka mai ban tausayi, ido goggo ta zaro tare da mikewa ta k’arasa inda Kausar take kafin mummy ta ankare harta shake kausar tana jibga duk kuwa data tsufa duk wahala ya mokad’ar da ita, dasauri mummy ta shiga tsakaninsu tana mai mamakin meke samun tsohuwar nan ne?”

“Izuwa yanzu k’wak’walwar Umar Faruq na niman rikicewa wai meke shirin faruwa ne haka?! Yana fata dai ba k’anwar sa bace wannan?” Mikewa tsaye yayi domin ya k’ara tabbatarwa yace goggo talatu ina k’anwata kausar take?!

“Gatanan kuwa kana gani a gabanka tashiga yawan duniya gatanan tazama bak’ar baturiya ai duk wanda yaga wannan yasan babbar yar bariki ce! ” aishi Allah ba azzalumin bayinsa bane saidai Wanda ya zalinci kansa! Sakaiyace da hakkina ke bibiyarta! Ki fice kibar min gidana kada kisaka min d’aud’a a cikin gida!

“Basu ankara ba kawai ganin Umar Faruq sukayi ya yanke jiki ya fadi, gaba daya su abba suka Mike suma a rikice dan izuwa yanzu suma sun fahimci abinda ke faruwa, tofa! Ana wata gawata kenan, ……….

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)

Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Zanyi amfani dawannan damar domin in mik’a sakon ta’aziiyata ga iyalan marigayi Alhaji Ibrahim Kaduna! Da rashin d’ansu Nasir dasukayi, ubangiji Allah yajikansa yasa ya huta, Allah yayi masa rahama yasa mutuwa yazamo hutu agaresa, Ameen! Allah yakara mana hakuri da dangana Ameen!?
[12/5, 5:44 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣3⃣0⃣to1⃣3⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Basu ankara ba kawai ganin Umar Faruq sukayi ya yanke jiki ya fadi, gaba daya su abba suka mike a rikice dan uzuwa yanzu suma sun fahimci abinda ke faruwa. ” innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Kalmar da abba ke furtawa kenan, a rikice Aliyu yayu kansa wanda tun zuwansu yaketawani yatsine fuska yana cin magani dakyar ya zauna akan tabarmar dama shi ala dole d’an gayu bayaso ya bata jiki, shikam badan abba ya matsa ba aida baiga abinda zaikawoshi wannan k’auye ba acewar sa kenan.

“Ruwa aka dibo masa adan kofi ya dan diba ya yaiyafa masa a fuskar sa nandanan yai ajiyar zuciya sannan ya fashe da kuka yana fadin wannan wace irin rayuwa ce ace mutum ya auri k’anwar sa ta jini baisani ba! Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Allah nagode maka dakasa kausar bata tare a gida naba Allah kaine abin godiya,

” kausar wacce ke kuka tamkar ranta zai fita ta fada jikin umar Faruq tana fadin Ashe banyi karya ba danake cewa KAINE GATANA! ashe da gaske kai gatan nawa ne! Allah nagode maka daka kara hadani da d’an uwana a karo na biyu, a hankali yake bubbuga bayanta alamar rarrashi,

“Goggo ce taja wani mugun tsaki tana fadin aikin banza aikin wofi anje angama tambadewa za a wani fake da zancan dababu gaira ba dalili! “Alhaji da hajiya dan Allah Ku tashi kubar min gidana dan ina ganin d’an mutuncinku tun wuri gara ku fice kafin rashin mutunci na yatashi! ” kafin ma ta rufe baki mak’otanta dasuka cika gidan kowa ya fara ficewa d’aya bayan d’aya dan sun riga sunsan halinta tunda ta furta hakan,

“Umar Faruq zaiyi magana abba ya d’aga masa hannu alamar dakatarwa, nan sukayi ma goggo sallama suka tafi abinsu tace yadai fiye maku inga dan shegen dazai kuma dawo min gida! Kuje can ku karaci gantalinku mutanan banza da wofi kawai! ” taci gaba da masifar ta tamkar suna wajan,

“Haka su abba suka tafi da mamakin halin goggo, Umar Faruq yace ai abba wannan kad’an ne daga halin ta! Mummy tace to umar wai bakuda wasu yan uwa ne kuma?” Ina nufin dangin baban ku kona maman Ku?”

“Ajiyar zuciya kawai yayi idanuwansa cike da hawaye yace mummy bamuda sauran dangin mu wayanda suka rage, dama baban mu su biyu ne shida Yayan sa, kuma a shekarar dana gama makaranta Allah yayi masa rasuwa, ita kuma maman mu dama ita d’aya iyayanta suka haifa kuma Allah yayi masu rasuwa tun tana raye, ” cike da tausayawa mummy ta kara jawo Kausar a jikinta,

“Aliyu dai bazan iya cewa ga yanayinsa ba wayar sa kawai yaketa latsawa, tamkar babu shi a cikin motar, (miskili kafi kare ban haushi, Aliyu Haydar kenan,Ali Jan zaki, Ali Jan rina ba nama ba, Ali gadanga k’usar yaki!)

“BAYAN K’WANA BIYU”

**************************

“Aliyu nizaka maida mutumin banza! To wallahi tallahi baka isa ba! Kayi kadan ka wulakantani wajan mutanan dake ganin mutunci na da kimataba! Yarinya tsawon wata biyu ka korata gida batare dawani daliliba?” Sannan ubanta yanata kiranka kaki kaje balle yaji me kake ciki game da y’arsa! Waikai Ali sai yaushe zakayi hankali ne ace kullum kana girma amman iskancinka karuwa yake amaimakon ya ragu to wallahi nabaka nan dazuwa anjima kaje ka maida matar ka idan ba haka ba zaka gamu da bacin raina! Kaji na gaya maka kenan wuce kabani waje mutumin banza kawai!

“Dasauri ya kalli abba yana kokarin yimasa bayani amman ina abba ya daka masa tsawa fice kabar min gida nace!!! Jiki a sanyaye Aliyu ya fice wai shi dan Allah meyasa yanzu abba sam bayayi masa uzirine?” tunsanda ya kashema Kausar aure abba yake nuna masa halin ko inkula, shi anashin ganin aima shahada yayi tunda badan yayi haka ba kila da yanzu kausar din nacan da cikin yayanta ajikinta, shikam ai godiya ma yaci aimasa bawai aringa nuna masa tsana da tsangwama ba haka! Shikam dole ma ya auri kausar kodan yakawo shiri tsakaninsa da iyayan sa!……….

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:45 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣3⃣5⃣to1⃣4⃣0⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“BAYAN WATA UKU”

Kausar ce ke kuka tamkar ranta zai fita, tsugunne take a gaban Umar Faruq wanda ya hade rai tamkar baitaba dariya ba, “yaya dan Allah kayi hakuri bazan kara k’watanta hakan ba, amman wallahi yaya harga Allah banason ya Aliyu zuciyata kwata kwata babu kaunar sa aciki! Idan aure kake bukatar inyi yaya kabani nan da wani d’an lokaci wallahi zan fiddo dawanda nake so amman nikam bana son ya Aliyu!

“Cikin kakkausar murya ya kira sunanta kausar!!! Kalleni! ” a sanyaye ta d’ago kanta tana kallon cikin idonsa, ba shawarar ki nake nima ba! Bakuma ra’ayinki nakeson jiba! Haka kuma ba zabi nabaki ba! Bakuma so nake inji kina sonsa ko baki sonsa ba no! Niba haka nakeba! Niba butulu bane! Bankuma iya son zuciya ba!

“Ke yanzu ba abin kunya da takaici bane ki iya duban tsabagen idon mummy da Abba kice wai ke baki son d’ansu ba! Ai ko basu fada ba dole zasuji zuciyar su babu dadi ace duk halarcin dasuka yi maki ki guji jininsu, kokuwa dan kinga sunayi maki haka saikiyi tunanin son Aliyu ne ke basuyi?” Wallahi ko d’aya suna tsananin son d’ansu da kaunar shi kawai dai suna mana alkunya da kara ne! Dan haka idan mafarki kikeyi maza ki farka kuma yanzu bada bata lokaci ba inaso kije maza ki basu hakuri kuma ki gaya masu cewa kin amince da auran Aliyu idan bahaka ba Wallahi wallahi sainayi bala’in saba maki! Tashi kibani waje sakarya kawai!

“Jiki a sanyaye tamike zata fice, zonan! Ok zaki je masu kina kuka kenan saboda magana ta bata shiga kunnin kiba ko?” Dasauri ta goge idonta ta saisaita kanta kafin ta fice, yabita da kallon tausayi shikam bada son ransa yaimata fada ba kawai dai hakan yakeso tayi domin kuwa basuda abinda zasu sakawa wayannan bayin allan dashi.

“A cikin wata ukun nan sunyi bala’in shakuwa shida k’anwar tasa shakuwa irinta jini sam baya son bacin ranta yanzuma dan ya zamar masa dole shiyasa kawai yayi mata haka dan yanata lallashinta tana wani botsarewa, yasani sarai Aliyu bai kyauta ba to amman yaza ayi da ikon Allah hakan ai shine alkairi agaresu baki d’aya,

“Mummy da abba ne zaune a cikin falon abba din, yayinda Aliyu yake zaune akasa yawani sunkuyar dakai kamar wani munafuki, da alama fada ake masa, ” dai dai lokacin kausar tayi sallama ta shigo gaidasu tayi sannan taje kusa da Abba ta zauna kanta na a k’asa, Aliyu ne ya harareta tare da fadin ke ni bazaki gaidani ba?! Ga sa’an ki ko?” Saida ta fakaici idon su mummy sannan ta hararesa tare da murgud’a masa baki tace ina k’wana ya Haydar?” Shuru yayi mata tareda yin k’wafa, wannan ai rashin kyautatawa ne Aliyu yaya kace yarinya bata gaida kaba kuma ta juya ta gaidakan kaimata banza waikai wani irin tsiya ne akanka ne k’wanannan ne?” Fad’an fa damuke yi maka kenan fa yanzu! Hmm! Nafisa wannan d’an naki saike aidama ke ce kika sangartashi! Murmushi kawai mummy tayi,

“Abba yace y’ata ya akayine naga kamar akwai magana a bakin ki ko?” K’ara sunkuyar da kai k’asa tayi tace Abba dama nazo inbaku hakuri ne kuma in shaida maku cewa na amince da auran ya Aliyu kuma kumaku yafe masa dan girman Allah!

“Farinciki mara misaltuwa ne yakamasu har suka kasa boyewa, mummy tajawo kausar jikinta tana fadin Allah yayi maki albarka y’ata shima abba addu’a yaketa yi mata yana saka mata albarka, ” shi kuwa gogan sai wani murmushi yake yana wani kallonta k’asa k’asa,
***************************

 

“Tofa biki kam ya kankama shagali akeyi babu kama hannun yaro, duk wani abu dayakamata mummy tayi tayishi itace uwar Amarya itace ta ango, shima Abba hakan ne ya kasance, shi kuwa Umar Faruq daya zama babban abokin ango kuma wan Amarya ai abin ba a cewa komi hidima kawai yakeyi sai kaiwa da kawowa yake tayi bashi nan bashi can!

” Amarya kuwa fuskarta babu yabo babu fallasa, tashirya duk irin zaman da mai gidan da matar sa suka zaba suyi da ita, a shirye take data taka duk wanda ya toneta, bazata ragawa kowaba! Haka taketa fada a zuciyar ta,

“Tayi kyau harta gaji tasha gyara yanda yakamata, mummy ta gyara y’arta tsaf dan tace sam babu wasa tunda gidan kishiya za a kai mata y’a gara taje da shirinta, dan bazata yarda y’arta tazama bora ba!……..

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:45 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣4⃣0⃣to1⃣4⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

 

“Yau ya kasance ranan jama’a ranan d’aurin aure, bayan an sauko masallaci ne jama’a suka shaida d’aurin auran kausar da Aliyu Haydar, akan sadaki naira dubu ashirin, Umar Faruq ne yazamo waliyin amarya yayinda abba yazamo na ango, bayan an tashi d’aurin auran ne aka gudanar da walima ta maza zalla, anyi wa’azi sosai masu ratsa jiki, taro ya watse cikin k’wanciyar hankali, saidai mummy tace baza a kaita ba sai washe gari,abba ya tambaye ta dalili tace yayi hakuri kawai yabari har goben, dole yayi shuru dan baisan meye hujjar taba,

” Aliyu ne k’wance bisa gadon Umar Faruq idanuwan sa a lumshe, shikuwa Umar Faruq ya dau wanka cikin manyan kaya saiwani sharce kai yake tayi yana kara kallon madubi,turare kuwa yafesa fiye da kala biyar sai wani irin k’amshi yake yi mai bala’in dadi, “kai malan ni na tafi zance ka rufe min d’aki na idan zaka tafi, kawani kwanta kanata tunani saikace ba sabon ango ba! Kallonsa kawai Aliyu yayi a hankali ya ce dan Allah ka kira min kausar kafin ka tafi, ido Umar Faruq yadan zaro yana nuna kansa da yatsa, au nima zaka aika?! Kaii nifa sirikin kane koka manta ne?” Dakyar Aliyu ya iya furta kalmar please! “Ficewa kawai Umar Faruq yayi dan yariga ya gano matsalar Aliyu tunba yauba, ad’aya bangaran na zuciyar sa kuwa tausayi k’anwar tasa ke bashi sha’anin Aliyu sai shi, shi wani irin hali gareshi mai wuyar fahimta! Tabe baki yayi a fili yake furta to ni ina ruwana nema ai matar sace koma meye can ta matse masu!

” yana shiga falon kuwa yaci sa’ar ganin kausar din tafito daga d’akin mummy hannunta rike dawani d’an k’ofi, laaa!! Yaya wallahi dama niman ka nakeyi ta fada idanuwan ta cike da hawaye, meye kuma na kukan to?” Dasauri ta had’iye tace yaya ina abinda mukayi magana akai d’in?” Kallonta yayi sama da k’asa yayi murmushi yace kije side d’ina ki duba akan gado zakiga abin, yafice abinsa, har yakai k’ofa ta bishi da gudu tace yaya ina zaka haka ne kaci kwalliya?” Saida ya k’ara gyara zaman hularsa sannan ya kalleta yace zance zani! Ido tadan zaro tana murmushi wanda tunda aka fara bikin nan batayi irinsa ba sai yau, tace Allah yaya?” Wacece wannan mai sa’ar kuwa?” Murmushi yayi mata kawai yace kiyi sauri kije ki duba ki d’auko, murmushi tayi tanufi side dinsa,zuciyar ta cike da farincikin jin cewa zashi zance, kenan shima ya kusa aure?”

“Tana shiga falon taci karo da takalmi a k’ofa, bata kawowa ranta akwai kowa aciki ba, ta kutsa kai kawai zuwa cikin bedroom din, cak ta tsaya a tsakiyar d’akin cike da tsoro, dasauri ta juya zata fice kuma, dasauri yace kausar dawata irin murya wanda sam bata san shi dashi ba,juyowa tayi tana kallon sa meye! Tafada tana hararar sa, bai damu da kallon datake masa ba yace zo nan, ya fada a hankali, ido ta zaro tana fadin mezan ma?” To kizo mana sai ki gani, nifa kasan ba y’ar iska bace kuma……..nine d’an iskan kausar?” Yafada da sanyin murya saikace ba Aliyu Haydar ba, baki ta murguda masa tace aini ba haka nace ba! To kizo nace, yakuma fadi tamkar zaiyi kuka. K’afa ta buga a k’asa tana fadin nifa ka dameni gaskiya, haba mana Kausar please mana dan Allah kizo kiji, zuwa yanzu muryar sa har sarkewa takeyi, gaskiya ya Aliyu nasan halin ka ni dai kawai sai anjima ta fice da gudu daga d’akin, Aliyu yayi tamkar ya d’ora hannu aka ya kurma ihu shikam ya shiga uku ummi Aisha taki kulasa tana fushi dashi dan yayi aure gashi kuma mummy tace kausar bazata tare yauba shikan yaga ta kansa, hannu yasaka a aljihunsa ya d’auko k’walin tabarsa yahau zuk’a baji ba gani kamar wani tababbe,

“A guje kausar ta shigo falon tana haki, mummy dake bayanta tace kekuma daga ina haka?” Wallahi mummy ya Aliyu ne, ya Faruq ya aike ni d’akin sa Ashe ya Aliyu naciki shine shine…..saiwani haki takeyi takasa natsuwa ta karasa maganar nata, ido mummy ta zaro dan ta riga ta gane da gangan Umar ya tura ta d’akin watau ita za a nunawa zamani! Tace fada min kausar meya maki badai bugun ki yayi bako?” A’a mummy nandai Kausar ta gaya mata dan anata ganin ba komi bane, aikuwa mummy ta hau fada ok tanan zai bullo kuma to shikenan ni dashi ne ai naga mai bashi ke nan da sati daya ma ingani! Tabar Kausar nan tsaye ta shige side din abba abinta, kausar kuwa farinciki ne fal ranta jin furuccin mummy………

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:45 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ?KAINE GATANA?

1⃣5⃣0⃣to1⃣5⃣5⃣

 

NA FIDDAUSI SODANGI

 

©TASKAR MARUBUTA?

 

“Tunda aka gaya ma kausar cewar yau ne za a kaita gidan Aliyu taketa rusa kuka duk ta tashi hankalin ta,daga k’arshe dai mummy tace kausar kodai baki son Aliyu ne kika boye mana?” Dasauri ta goge idonta tana fadin ba haka bane mummy ina tsoron matarsa ne kawai kinsanfa batason kishiya ko kad’an mummy! Murmushi kawai mummy tayi tace ki kwantar da hankalin ki kausar babu abinda zai faru sai alkairi insha Allahu!

“Haka dai mummy taci gaba da Kwantar mata da hankali har lokacin daukar Amarya yayi,

” Abba da kansa ya sakata a mota ya nufi gidan Aliyu da ita wanda yake a GRA tsayawa fadin tsarin gidan bata lokaci ne gidan yahadu karshe, hannunta abba ya ruko harzuwa falon,Aliyu ya taso da sauri ya taresu, nan ummi Aisha ta gaida abba ciki ciki kamar wacce akaima dole, abba ya amsa cikin sakin fuska daga baya yacigaba dayi masu fada mai tsuma zuciya kausar kuwa kuka kawai takeyi tana karawa,

“Haka yaringa gaya masu yanda zaman aure yake a musulunci. da abinda ya halatta miji yayima matar sa da wanda ya halatta Mata tayiwa mijinta. Yacigaba dacewa Aliyu ga amanar kausar nan nabaka. Don Allah ka kular min da ita ka kula da hakkinta daya rataya a wuyanka kada kaci amanar ta kada ka zulunceta idan taimaka kuskure ka ganar da ita cikin ruwan sanyi yadda zata fahimta idan taimaka laifi Wanda yafi karfin hukuncin ka Dan Allah kanimeni koda a waya ne. Nikuma in allah nanyarda zanyi maka maganin abin koma menene. Yajuyo kanta yace kekuma kausar hakika nayi murna da farinciki da samun ya mai biyayya kamar ki Ina alfahari dake nagode Allah yasaka maki da alheri Dan girman Allah kausar ki zauna kiyi zaman aure Dan bakida abinda zakimin Wanda yawuce kiyi zaman aure kausar kiyi biyayya ga mijinki yinayi Bari na Bari shine zaman aure kada ki sake mijinki yakawo min karar ki kosau daya ne kinji nagaya maki kada insake inganki dasunan yaji! Kizamo mai boye sirrin mijinki danaki. Kada ki tozarta mijinki koda sau daya kidaure duk abinda zai shiga tsakanin ku kumagance ma kanku shi. Sai dai in abin yafi karfinku sai Ku gayama nagaba daku. Kausar kada kisake mijinki yakawo min kararki inakara shaida maki idan na bincika naji kece bakida gaskiya to wlh Zan mummunar Saba maki.kinsan halina sarai.aure ba abin wasa bane kiyi biyayya aljannarki na karkashin kafarsa saiya daga zaki shige kina jina ko? Cikin kuka tace eh!

“Yace ke kuma ummi kema ga amanar kausar nan nabaki kindai ga yarinya ce karama dole sai kunayi kuna kwabarta domin har yanxu bata mallaki hankalin kantaba.Dan girman Allah Ku zauna lfy kuyi kishi irin na matan sahabbai ba irin kishin haukan da akeyi yanxu a wannan zamanin ba Ina fata nasihata ta shige ku kuma zakuyi aiki da ita! Gaba daya suka amsa da insha Allah. Banda kausar daketa kuka tamkar Zata shide. Ahaka Abba yayi masu sallama yatafi,

” Aliyu ya raka sa har mota, yana fita ummi Aisha tamike tsaye tare dajan wani mugun tsaki tana fadin ubanwa za a bawa amanar kishiya! Wallahi ban dauka ba dankuwa niba sakara bace kajimin tsohon kawai!

“Kausar dake lullube cikin mayafi kuka yaci k’arfinta badamar magana saidai tabi ummi Aisha ta kallo harta shige d’akinta, mik’ewa tayi itama tanufi nata d’akin tanacigaba da kuka………

 

Fido sodangi?

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:59 PM] ‪+234 813 502 2313‬: ? KAINE GATANA?

1⃣5⃣5⃣to1⃣6⃣0⃣

Na FIDDAUSI SODANGI

©TASKAR MARBUTA?

 

“A bakin gado ta zauna jikin ta a sanyaye tanata kuka a hankali, sallamar Aliyu ya katse mata kuka, gabanta sai dukan uku uku yake, gefenta ya xauna yana kallonta kasa kasa wani tausayinta ya tsurga masa amma daya tuna Daren farin cikin su ne nan da nan ya kawar, wani murmushi yayi daya tuna halin mata idan an nuna masu tausayi sunfi raki da fitsara acewar sa kenan,

“A hankali ya furta sunanta “KAUSAR! Wani irin abu taji yana yawo a duka jikinta, takasa koda motsawa, ya matso gab da ita kanshin turarenta ya dakeshi, hannunsa ya saka ya zame mata mayafi suka kurawa juna ido, nan da nan ta janye nata ta sunkuyar da kai kasa ya furta a hankali ” tashi muyi nafila mugodewa Allah SWT munemi albarka a auran mu, wani sanyayyen kamshi taji yana fitowa daga bakinsa , a ranta tana jinjinar tsaftar Aliyu ” a hankali ta mike ta nufi toilet tayi wanka tare da brush ta fito ta Tarar baya wajan, bakin mirror ta nufa tayi shafe shafenta na mata , turaren da mummy ta bata ta dauko ta saka a bayan kunnenta da duk wata gaba ta jikinta, tayi alkawarin kyautatawa Aliyu tsawon ranta insha Allahu!……

************************
“Da sallamar sa, yashigo ya ce bismilla ya tayar tana bayansa, raka’aa 2 sukayi ya Dade zaune yana musu addu’a ya kama kanta ya tofa mata suka shafa, yamike ya fita ta rakashi da ido ta tabe baki tabi lafiyar gado, kwanciyarta keda wuya yadawo dauke da tray ya kalleta da hijabinta a jiki yyayi wani shu’umin murmushi, sauko sweetheart muci abinci, tace ‘ nakoshi ta juya yayi daria kawai yaci abinsa yayi nak tare da maida kayan kitchen.

“Hawa gadon yayi ya rage hasken fitilar dakin, yana facing dinta yaga ta rufe ido yasandai ba bacci takeba, matsowa gab da ita yayi ya xare mata hijabi ta bude ido ! Ba abinda xanyi miki kwantar da hankalinki , yaxare mata hijabi yaga halittar kirjinta duk a waje ya salam! Nan fa hankalin aliyu haydar yai bala’in tashi, wani kanshi na turare ya daki hancinsa ya janyota jikinsa, har wani tsuma jikinsa keyi, rawar jiki ta fara sosai itama, dan Allah ya Aliyu kayi,hakuri, shhiii!! A hankali yace bana son surutu pls! A rikice yake gaba daya, da sauri ya hadata da kirjinsa yanajin saukar boobs dinta a jikinsa ya lalubo bakinta yafara kissing dinta, wani Abu ya daki xuciyar ta kissing dinta sosai yakeyi, yana shafata gaba daya ya rude ya fice a haiyyacinsa, saida kausar tabari yayi nisa sam baijin kira aikuwa ta turesa da k’arfi ta sauko daga kan gadon, dasauri ya fisgota yana fadin wani irin iskanci kenan kausar?! Nifa ya Aliyu gaskiya…….. Bakin su ya hade waje daya yashiga sarrafata son ransa,

” Kausar ganin babu sarki sai Allah yasata daurewa kawai tashiga
maidawa kura aniyarta, Aliyu yaji mamakin yanda Kausar ke sarrafa bakinsa a natse, nan hankalinsa yafara fita daga jikinsa, ya lalubo boobs dinta yafara tsotsa kamar jariri hankalinta ya tashi, plx ya Aliyu kayi hakuri da kyar ya mike ya kashe wutar dakin gabadaya ya cigaba da sarrafata, hannu yakai kasanta yaji alamun danshi bashiri Yakuma rikicewa saida ya tabbatar ta jiku sannan ya Shiga……….. Ihu Kausar keyi amma ina Aliyu yayi nisa saiyaji shi a duniyar da betaba xato ba, sai da yayi awa 4 yana Abu daya sannan ya sararawa Kausar.

*********************
Kunna wuta yayi yaganta a kwance tamkar ba itaba duk ta fita haiyyanta, kallonta yake kamar Wanda ya warke daga cutar makanta, tuno daren yayi lallai mata kala kala ne, yayi gamsuwar da be tabayi ba.

“Ya killace jikinsa tare dayin nafila dan nuna godiya ga ubangiji daya mallaka masa kausar a matsayin matar shi ta sunnah, motsin ta yasa shi juyowa suka hada ido wani tausayinta ya mamayeshi , kara sowa yayi y rungumeta am sorry my kausar! tafashe da kuka tana fadin ya Aliyu kasheni kayi niyyar yi hala?” Kiyi hakuri wlh nakasa sarrafa kaina ne, rarrashinta yaitayi da kyar dai yasamu tayi shuru tasaki ranta,

“Oya muje kiyi wanka asuba takusa, ta lallaba ta mike dakyar aikuwa ba shiri ta xauna sai kuka, yace sorry kwanta na duba ki, da kyar ta yarda ya dubata hankalinsa ne yai bala’in tashi yanda yaga yaji mata ciwo sosai, first aid box ya dauko ya mata allura sannan ya bata magani suka Shiga toilet ya gyarata.

******************

 

Around 10 ta farka daga bacci Aliyu na xaune yana aiki da laptop , ta kalleshi fuskar nan a hade tasa kamar kumurci, daria ta xo mata ” dubeshi kamar bashi ba yakwana sunbatu, wani kalaman nasa ma daria yake bata wlh, karaf suka hada ido ta turo masa baki, ya tashi ya rungumeta morning my Angel! Ya cikata look at u mai kuka kawai , raguwa dake kina turo min baki, any way ya jikinki? Ba sauki har yanxu pains nikeji fa, ya kalleta sosai ina keciwo yanxu? Duka jikina ya xaro ido kai sweetie nifa waje daya nayiwa laifi yana nunawa da hannun, kunya taji hmmn kai wlh bakajin kunya ya Aliyu dinnan dariya yafara hmmn Kausar ina batun kunya a aure kedai Allah miki albarka ta rufe fuskarta suka xube a gado…….

Fido sodangi?

 

Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
( Kausar luv)

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *