DOGUWAR HANYA CHAPTER 9

Mik’ewa tsaye yae yana mamakin Brother shi kanyace

“Ur over reacting bro, calm down mana menene yasa zakace kaine zakayi, open all wahalan daka sha akaina, tun yaushe kake tafiya dani a bayanka? Gaskia tunda naji sauk’i nine zan d’auketa” Sauke ajiyar zuciya hurairah yae

“Kaida Bakada lafiya yaya kuma zaka k’arawa kanka ciwo, dubi kanka fa har yanxu da sauran k’umburi ga k’afarka ma haka” Dawood ta kalla cikin damuwa sosai tace

“Kamar fad’a suke ko?” Girgiza kanshi yae yace

“Abu sufyan ne ya kafe akan ze d’aukeki kinga kuma bashi da lapiya, shine, Abu Huraira yace dakanshi ze d’auke ki amma fad’a suke ba zancen kenan” murmushi tae tace dashi

“Dan wannan aibama sesun wahala ba, zan iya tafiya ai sekace maciji?” Jinjina kanshi yae

“Da gaske zaki iya?” Ya tambayeta

“Allah zan iya, Barbo tayani in kik’e kawai, haka suka shige gaba ita da Barbo, tafiyar shiru kakeji wannan karon har duhu ya sauka basui magana ba, seda taradda fili sannan suka samu zaunawa sukai sallah, sukaci tufa da mango sedai ba ruwa, Haska fitila Abu Huraira yae yana nazarin wurin, tabbas Filine amma bame zaunuwa ba har a wani kwanta, ramukan dake wurin filin sunyi yawa ko ina ramuka ne gasunan burjik, kamar na macizai dan  haka  ya jagoranci tafiyar dauke da Adu’a a bakunan su suka k’ara nausawa cikin hanyar sunkai 11:pm na dare suna tafiya kansu tadda ruwa, badan huraira yasoba sukai masauki agun, ga dare gashi  basusan me ruwan ya k’un sa ba.

**********

   Haka tafiyar su General ta yiyu acikin kwana d’aya suka isa k’auyen, inda jiragen masu saukar angulu suka rigasu zuwa jejin suna me zagayar gun sun tabbatar bayan an tsallake ruwan akwai garuruwa kusan bakwai dasu kaga mutane suna rayuwa aciki, amma basu san wanne ne ba, da wannan suka koma akan idan ma me sh8ga jejin bazeje ba zasuwa jejin saukar aradu zasu fara da garin dake manne da ruwan dazaran an tsallaka, wannan ya sanya suka shirya helicopter har 4 suka nausa da manya manya bindigoginsu a garin.

  Tunda suka sauka a garin suke shan mamakin yanda mutanen garin suke kallon su, wasu mamaki qarara a fuskar su wasu se rugawa suke sa gudu jin k’arar jirgin, haka sun kula yaren nasu yasha banban danasu, takawa sukai har cikin garin da k’yar wani ya tsaya yin magana dasu, sun fahimci yare yake kamar yarbanci sedai ba duka bame yarbancin da wannan ya jagorance su zuwa gun sarki bayan ya sanar dasu sarki yau kwana uku beda lapia sabida b’atan ‘yarsa, wanini me suna geoge da wani kanu suke magana dasu dan sune yarbawa. Sun sanar dasu akan tabbas sunzo amma sun sace ‘yar sarkin sun gudu

Kafin kace meye wannan sun nemi kawowa sojojin hari basusa  meye bundiga ba, seji sukai an soma mayar da martani jini yana zuba gasu su qananun wuqaqenw dasu dana katako wanda ake feqewa, aikam lokaci s’aya k’auyen ya rikice aka hau gudu ana ihun cewar dama ance garin ya kusa mutuwa.

Sojojin basu  b’ata lokacin suba suka juya gun general suna so su gaya mai cewar ga abinda sukaji daga garesu.

************

  Washe gari da asuba sega wani me tuk’in jirgi koma ince jiragen ruwa sunkai 10 wasu sun kawo passengers wasu kuma empty sukazo, abin mamaki fulatanci suke wannan abun ya burge su Hurairah dan kuwa yarem momy kenan sunaji sosai,mutanen suka sanar dasu akwai rugar fulani a gaban kad’an kuma sannan akwai ‘ya’yan itatuwa dasuke zuwa d’eba anan suna kaiwa cikin gari siyarwa, itatuwa  a zube suke a jejin na Allah, haka suka shiga jirgi d’aya dama sunada kud’i a aljihunsu sedai bame yawa ba amma ba laifi suka biya ya gangara dasu bakin ruwan bekoda wani tsayi sosai, shisa mutane sukai yawa ba jimawa suka taradda rugar fulani ga shanaye nan burjik babu iyaka ga gonaki nan malale k’auye me yalwar ni’ima, anan akai musu iso gun me garin bayan sunmai bayanin abinda ya samesu yace a baiwa matan suturu yana mamakin dama anan kusa dasu akwai garin maguzawa har haka, acikin Nigeria nan ya dace aje musu da addinin islama dai kam…dattijo me karamci d’aki aka basu bukka d’aya sedai far sunada nisa da cikin gari, matsalar ma jiya mota ta tashi yanzu se bayan sati biyu zata dawo dama haka takeyi, bama wannan ba akwai garuruwa uku dazasuje dole kfin Allah yasa sukaiga inda motar take, wannan labarin be musu dad’i ba sam idan akwai abinda suke buk’ata shine su isa gida kafin wayewar garin gobe, amma koda wannan rufin asirin Allah ya barsu sun gode masa.

Lokacin da dare ya tsala sun shiga takura sosai, sabida da farko dai da k’yar suka samu suka iya shan zallan Nonon da aka basu susha sabida k’arnin nonon, sannan kuma bukkar kyasone kurun aciki gata qarama gasu susu biyar ne, Cikin tausayi ganin su Lawuri a takure Abu sufyan yace da Abu Huraira

“Mu kwanta a waje mana,  inyaso da safe semu shiga ciki, yaya zasu samu nutsuwar bacci a tare damu?” Kallon shi Huraira yae

“Bakan tunani ne me kyau, mu basu wuri, haka suka fita ranar kuma aka sheqa ruwan sama, sunsha wuya, badan sun soba suka kwana a bukkar tare dasu, da Asuba bayan sunyi sallah Abu Hurairah ya kalli Dawood yace

“Naga kamar ana kamun kifi a bakin rafin cen, mezai hana muje mugani ni zaman tunanin duniyar nan ma ya ishen wlhy” kallon mamaki ya masa  yace

“Kaida nasan bakasan k’arnin kifi kuma?” Mezaisa kaje wurin?”

“Nidai zanje, idan bazaka ba se naje ni”  

“Bro Nima zanje zan bika” Atare suka mik’e Dawood na mitan kafiya irin na Hurairah, ya sani k’arnin kifi har amai yake sakashi amma ya kafe akan seyaje aise yayi tunda yaji yakuma gani…

**********

    Mommy kam jiki yayi nisa, sam batada lapia ko kad’an, duk yanda taso tacire abun aranta lamarin yafi k’arfin tunaninta, Cyama da Hanifer sune suke jinyarta dan har ankwantar da ita ma, ita Cyama babu abinda yake damunta irin rashin lafiyan mamanta, batasan meya samu ‘yan uwantaba gakuma momy a kwance, hanifer ma haka, Abu huraira take so kamar ranta ze fita, tunda ta nemeshibta rasa kuwa bata cikin nutsuwarta da kwanciyar hankalinta, haryau tana tuna yanda sukai sallama bayan daya bata aran motar sa, lumshe idanta tae kurun cikin tsananin damuwa.

***********

  General yayi shiru yana nazarin jejin, tabbas yaranshi suna shirin tashin hankali mara misaltuwa, da wannan ya yanke shawarar ashiga jejin gadan gadan dankuwa shi kad’aine solution agaresu, da wannan sukawa wani fili saukar angulu suka soma tafiya da k’afa agaban jejin domin nemansu.

Sunyi tafiya me nisa harta kwana biyu dayike su sojojine basu sha wahala ba kamar su, suna iya yin tent na wuccin gadi su zauna, a hankali harsuka isa garin nan da ake cin naman mutane, da wannan suka samu damar tambayar en garin kosun gansu, amma ga mamankisu kowa sukai qoqarin yiwa magana baya amsa musu, ko kallonsu ba’ayi, sunsha mamaki sosai na wannan rayuwar to kodai aljanaine wannan garin, General ne yae umarni akan tunkan dare yae musu sui gaba dn wannan garin tabbas ba lafiya acikin sa, haka suka yi nisa wa garin sosai sannan suka yada zango awani fili me yalwar yashi, hankalin general be kwanta da garin ba still dan haka sukace zasu koma cikin dare sui bincike yana ganin kamar ko yaranshi suna garin ne, da wannan sukai shiga irinta soja suka nausawa garin cikin sand’a.

Gani sukai wasu mutane suna yawo sa wuta suna zagayar d’akunan mutanen garin, sannan daga bisani suka cinnawa wata bukar wuta sega mutanen ciki sunfito da gudunsu suna qoqarin guduwa, suna kallo suka sassaresu su kusan hud’u, sannan suka d’aukesu suna rera wak’a abakunan su suka rawa, general jikinsa yae sanyi suna nan a b’oye har safiya ta soma yi suna kallo aka hasa wuta aka d’add’auresu ajikin ice aka soma gashin su, kansu ya masifar d’aurewa mekenan ake nufi, komawa sukai inda suka fito suke baiwa sauran labari, sabida akwai mamaki akasheku kuma makasanku suzo suna gashinku acikin gari sannan babu yako d’aga ido ya kallesu me za’ayi da naman? General dai duk dauriyar sabyau seda yae kuka yana tsoron indai ba ankashe masa yaran saba, tunda wancem garin sun sanar cewar sun gudu kuma anzo nemansu ba’a samesu ba. Shawarar kaiwa garin hari akayi amma koda suka bazama sesuka tarar kowa naman nan ake yanka masa yana ci, cikin tashin hankali sukai gaba, dan duk yanda sukaso babu wanda ya kulasu, kenan gudun da mutanen garin keyi gudu ne na gudun kar a yankasu a gasa? To amma shirun fa? Na meye? .

General yasha kuka sanda suka bashi akan sunada yaqinin yanda basu kulasuba suma bazasu kulasuba koda sunzo dan haka sunyi gaba, da wannan suka k’ara ci gaba da tafiyar dasuke.

*************

  Sunyi enjoying rayuwar su abakin ruwan, har kamun kifi sukayi, sannan suka hasa wuta suka dafa shi, suka yanke shawarar kurun suje su kaiwa wannan matan dasuka baro, sunga yanda duk suka rame akwanaki qalilan kenan.

Kwanansu hud’u agarin suka nemi hanyar yi gaba inda Me garin ya basu ‘yan  rakiya susu biyu suka jagorance su har suka isa bakin ruwa daganan ma seda suka tsallaka dasu sannan suka dawo, anan ma sunci karo da wata rugar fulani masu karamcci an karrama su ba kad’an ba agarin, seda suka kwana uku sannan suka bar garin, a haka a haka har suka isa inda motar zata tashi zuwa cikin gari nanda kwanaki uku masu zuwa, sedai ba kamar sautan garuruwa ba dole ce ta sanya su kwana a tasha.

*********

  General kuwa yasha wuya shida yaranshi kafin su taradda wannan ruwan, basu wani sha wahalar tsallaka ruwan ba suma suka isa garin,anyi sa’a general da kanshi yake jin fulatanci, bayan doguwar tambaya aka sanar masa tabbas sunzo anma sun wuce yafi da sati motar ma da ake saka ran su hau nanda kwanaki uku zata tashi, da wannan ya bada umarni akan manyan su koma inda jiragen shida wasu zasu bi sahun su twins, amma se wani ya bada shawarar su bari suje gaba d’aya inyaso se aje da wasu jiragen a d’auki wancen tunda garin dake kusa dasu naman mutane ne abincin su, hakan kuwa akayi jirgi uku suka hau a ranar suka naushi d’ayan garin.

**********

   Zazzab’i sosai Lawuri keyi amma bata sanarwa kowa ba, tarasa dalilinta najin yawan fad’uwar gaba me tsanani aduk sanda ta tuna mahaifanta, da ‘yan uwanta anya ta kyauta kuwa? Yanzu harse yaushe zasu samu wani sui sacrifice dashi? Idan akace basu smu bafa hakan yana nufin ta kashe iyayenta da ‘yan uwanta da hannunsu, ada tana tunanin tamkar yin hakan ba komau bane mma yanzu ta hango tsantsar rashin kyautawar dabatayi ba, amma yazatayi da rayuwar ta? Tsari d’aya kenan dayazo mata, batasan yazatayi da ranta na akan wannan al’amarin, taso ta yakicewa zuciyarta amma batasan meke hanata ba akan yaran nan, ita kanta bazata iya cewa ga takamaimai abinda yasanya take binsu ba, bata tsammani akwai ranar dazatazo rana d’aya ta guji danginta ba haka kawai, anya bazata koma ba kuwa? Amma idan kuma wani abun ya same tafa? Ta tabbatar wa kanta yanda suke murna sun baro wannan bala’in bazasu yarda su rakata ba bare kuma har sun tarardda wurin da ake gasa mutun, kai koma ba hakan ba ita bazata komaba ta rasa me mata wannan maganar dasuke susu uku, ga kayan da aka sanya mata ma a wancen k’auyen a bingili suke ga masifaffen sanyin dake ratsa ta sabida zazzab’in datakeji tako ina, tarasa nutsuwarta da farin cikin ta, gefen k’irjinta na hagu zafi sosai yake mata, Barbo cema ta fahimci batada lafiya harta gayawa Dawwod data kula shishi kad’ai yakejin yaren su, anan suka taimaka mata sun neki chemist amma babu haka suka kwana tanashan wahalar sanyi.

*******Bayan kwana uku*

Ba k’aramin sanyi sukaji ba a ransu dasuka samu hawa mota for the first time tun bayan dasuka bar motarsu a wannan jejin, abin takaicinsu d’aya sama suka samu asaman kayan amfanin gona suda wasu Fulani masu qarnin tsiya,  sunyi sa’a sosai  sedai fa hanyar batada kyau sam, sunyi tafiya ta kusan awa uku kafin su tarar da wani titin dasukeda tabbacin tun zamanin mulkin soja aka shinfid’ashi, duk ya gama mutuwa sedai sufa hakan wata rahama ce agaresu dankuwa yaushe suka saka ran zasu ga qara ganin titi ma a rayuwar su? Ai basu zataba sam.

   Su General koda suka zo ansanar dasu ai motar tafi sa’o’i uku da d’aga wa, kuma tabbas samari uku da ‘yan mata biyu sun samu shiga kotar, sedai shi general baze iya jiran zagowar makon nin biyu ba kafin  ya koma gida dn haka ya nemi wata hanyar musamman yasa azo masa jirgi me saukar angulu yawa hanyar k’aura, atake wani bafillatani yace dashi shi yana motar sama, kurun k’a’idane sati bibbiyu ake zuwa kuma hanyar ce ba kyau, take general ya tilas ta masa kaisu cikin garin zema k’ara masa kud’i akan wanda ake biyanshi.

Tafiyar tasoma gajiyar dasu sanda aka  taresu, wasu mutane masu furka a rufe da qyalle sa manya manyan bindigogi ne suka tare motar, take dulanin nam suka soma salati suma su Dawood  suka hau yin salatin, duk inda kake kanajin qarar bundigar sanda wanin su ya harbata a sama, hankula sun matuk’ar tashi musamman twins dake tsammanin wahalar su ta k’are ashe ashe tsugune bata gama k’are musu ba!!!! Sunfi 4 hours suna binciken su snin hanyar bame bi ba soja ba ‘yan sanda kafin daga bisani su soma shirin barinsu anan suna qoqarin tafiya da motar cikin jeji sabida dama kayan amfanin ginar suke so, da kudad’en dasuka zo dashi, Abu Hurairane ya shiga musu magiya akan su taimaka su barmusu motar, yaya zasu bar wannan *Doguwar hanyar* idan babu mota dan Allah su taimaka……aikam take agun wani daga cikinsu Ya dage bundigarsa ya danna masa harsshi take ya xube agun kowa yae tsit se Abu sufyan daketa faman kuka yana rik’e dashi, suna kallo suka bar wurin bayan har wayoyinsu sun karb’e suka kuma tafi da motar, cikin azaba Abu huraira ke mayar da numfar fashi sama sama, sauran se kuka suke Abu sufyan cikin kuka yace

“Daddy kana inane haka? Gashin mun shiga halaka ka turomun wannan *Doguwar Hanyar* mara b’ullewa, daga wannan bala’in se wancen Allah ka kawo mana d’auki, Allah ka ceci ran d’an uwana ya Allah, kowa kuka yakeyi cikin tashin hankali….

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *