DOGUWAR HANYA CHAPTER 8

Yanayin suturar jikinta ya kalla ya d’auke kanshi gefe d’aya, yana bak’in cikin wannan rayuwar tasu, kalli mace tsirara ace wai wannan fatar sune sutura, kallonshi itama takeyi cikin wani yanayi dabazata iya fassar ko meye ba, abu d’aya ta sani bazata barshi ya tafi ya barta ba, koma yayane seta bishi har inda zashi koda zasu ci gaba da magana ne irinna kurame, batasan dalilin ta na bijirewa iyayenta ba ta cutar dasu akan wannan abun, abin takaicin ma shine takasa gane dalilinta nason tabishi to akan me?……

Kowa yae shiru tsit kakeji acikinsu, babu wani abu dake tashin sauti se bugawar zuciyoyin su dake tserereniya wurin fitar da sauti sauri da sauri.

  Wuta suka fahimci ana zagayen bukkar tasu dashi, kallon kallo suka shigayi, me hakan yake nufi kenan? Wannan kuma wace *Doguwar Hanya* ce suka k’ara b’ullowa aciki? Kodai wani sabon ajalin ne ke kiransu? Tunda Allah ya kub’utar dasu na wuccin gadi daga wancen gidan, suna nan har aka wuce su batare dasun koda motsa ba, hankalinsu duk atashe yanda sukaga rana haka sukaga daren ranar, suna ganin haske ya soma fitowa sukai taimama sukai Sallan Asubahi dukansu sannan suka fito daga wannan bukkar, yauma kamar jiya babu wanda ya kallesu ma bare yasan suna gun,sun dai kula ana gasa mutum lafiyayye bayan an cire masa kai, to me hakan yake nufi? Wannan ne ya sanya sukai hanzarin barin garin sukai  doshi wata *Doguwar Hanyar* dababu me tabbacin zata b’ulle acikinsu, tafiya sukai me nisa sbida har k’arfe biyu tayi lokacin yunwa ta soma galabaitar da Lawuri an saba dacin me kyau, kallon ta Abu Hurairah yae cikin tausayi yace da Dawood

“Yarinyar nan yunwa takeji Dawood, bansan mesa ka barta take ta binmu ba, mu kanmu bamuda tabbacin fitar mu a wannan k’uncin bare kuma mu iya kare su, mata kasani sunada rauni matuk’a abubuwan dazamu iya karo dasu mu daure ya kake tunanin su zasuyi, kumama wai shin mesa suke binmu? Akan me?” Ta kula fad’a yakeyi kuma ta tabatar akansu ne, kallon sa shima dawood keyi tunda ya soma magana, dafa kafad’arsa yae

“Ka kula yarinyar nan addinin Allah ne yake shirin janyo ta izuwa garemu, yaya zamu bari hasken musulunci ya gagara ratsa ruhinta alhalin munada damar yin hakan?” Sauke nannauyan ajiyan zuciya yae yace

“Ya akai kai ka gane cewan musuluncin ta biyo?” Murmushi yae ya shiga nodding kanshi a hankali

“Na tabbatar kaima kaga abinda na gani, sedai idan bakason gaskiyar ne kawai, kaga wannan dabanne, sena umarce ta akan ta koma kawai” cikin damuwa yace

“A yanzu dai gwara ta koma gaskia sabida bamida tabbacin bata wata kariya, ka duba fa ka gani yanda ake gasa mutum da kaman ana gasa kasa, kuma wancen garin baka kulaba bewa wani magana, dani dakai duk bazamu iya cewa ga dalilin shirun na kowa ba, mu kanmu kuramen k’arfi da yaji muka zama” Cikin fusata Dawood yace

“Mesa kakeda sankai ne wai? Yanzu itama tace damu ta b’ata, idan ta koma wancen gari suka yankasu fa? Kai wane irin mutum ne wai?” Kasa cewa da Dawwod komai yae ya k’urawa Lawuri ido cikeda tausayi besan dalilin sa najin matuk’ar tausayin taba, besan me gaba ta tara ba

“Shikenan dawood muje”

Haka suka d’unguma cikin wahala ga uban k’ishiruwa Abu sufyan dai baya Cewa da kowa uffan shi ta kanshi ma yake yi dan bayajin lafiya sam ajikinsa wannan dukan ya masa raunika sosai ajikinsa, tafiya suke shiru shiru kamar wasu kurame, Har sukazo wani k’aton fili wanda bashida maraba da sahara danko banda yashi babu komai aciki, gashi kuma ba bishiya ko d’aya se k’walleliyar rana, basason su tsaya a samu matsala, haka suka dinga cin wannan yashin me tattare da wata uwar Doguwar hanya mara b’ullewa, Lawuri da Barbo dai ankaisu k’arshe dan har gwara Barbo su dama sun saba abinci d’aya a wuni ruwa idan lokacin damunane so d’aya,  lokacin sanyi ma so d’aya amma lokacin zafi so uku a rana, to yanzu dai damina ta soma sauka amma akan kwanaki ma ba ai ruwan ba….

  Kasawa tae takai zaune ga yamma tayi sosai, shikansu Sufyan ya gaji sosai, Abu Hurairane ya rik’o d’an uwansa suka zauna suma ba laifi yashin ya soma d’aukar sanyin yammaci yace

“Sannu Twin, jikinne ko?” Hawayen dayaketa k’ok’arin adanawa ne suka zubo masa yace cikin wata murya me rauni

“Abu Huraira tsoro nakeji, gani nakeyi tamkar bazan k’ara ganin Momyna ba, kuma daddy shine bezo nemanmu ba, ga babban wayana ma yana waccem jakar naga ban ganku da shiba” Dafe kanshi yae

“Jakar kam bamuda damar dok’arta amma wayarka gata a aljihuna, na kashe maka ita dama cajin ba yawa sufyan, ka manta tun sanda muka saka karatun alk’urani me girma mukai bacci ta d’auke seda kai cajinta da wayan dawood cajin ba yawa gaba ntwrk me zakai da ita ne?” Wasu yawu ya had’iya masu d’acin gaske yace

“Bro kishi nakeji, da yunwa sosai, nakusa in mutu wlhy” Shi kanshi kukan yake yanzu kam

“Munshiga tashin hankali mara misaltuwa Twin, kayi hakuri ka dena ambatar mutuwar nan inshaa Allah dukkaninmu zamu kub’uta da yardar Allah zamu b’ullewa wannan doguwar hanyar, Allah daya kawomu nan shine ze kub’utar damu” shiru sukai dukkansu dagacen yakai dubanshi zuwaga Lawuri duk ta fita hayyacinta, tausayinta yakeji matuk’a, matsawa yae kusa da ita besan dawane yaren ze mata magana ba se kawai yace da ita

“Sannu” Murmushi ta sake masa amma batace masa komai ba dan ba gane me yake cewa take ba, ya jima dirk’ushe a inda take kafin ya mik’e taimama ya somayi, itama tazo ta somayin kaman yanda taga sunayi, kallonta yae ya sakar mata lallausan murmushi itama murmushin ta mayar masa batare datace komai ba, haka sukai sallah agun yanata mamakin yanda tabisu bayan ance ta tsaya baya ya sani ba sallan ta dan batamasan me suke ba, bayan sun idar ta kalli Dawood dakejin yaranta tace

“Wannan maganan dakuke idan dudduk’awa kuna burgeni ina sanshi sosai ka koyamun” murmushi yae

“Idan Allah ya fitar damu lapia aishi kenan, sena koyar dake ko Abu Sufyan dankuwa shine ogan mu gaba daya, amma yanzu kowa tsorace yake” murmushi tae batace komai ba”

***************

 “Alummomi daban daban a sassan na duniya kaf d’inta, gaba d’aya sunada wasu mutane na jeji  wanda basuda addini ma kwata kwata, dazakace musu akwai wata al’umma bayan suma bazasu yarda ba, basuda abinda suke bautawa se tsafi a wannan yankin dasuka bi akwai irin wannan al’ummar da dama, bana tunanin zasu tsallake kaidinsu dansu kansu kad’ai suka sani, karkuyi saurin tsallakar wannan ruwan ku bundiga ne daku, amma a ire iren wuraren nan dama ai tsafi yafi yawa, kuje da jirgi me saukar angulu sekun gama zagaye area kaf, anyi stodying na wurin nima zan shirya muje daku” Nisawa oga shamsu yae cikin takaici kan yace

“Ba damuwa General, zamuyi yanda kace amma inaga zamuyi hanzarin zuwa sabida me rakamu a jejin wanda ya san hanya laraba laraba kurun yake zuwa, gashi yau kaga sunday idan mukai wasa seyace se wata larabar gashi kace mahaifiyar suma batada lapia, gwara musan me ake ciki” Jinjina kanshi yae

“Zan shirya dani zakuje yaushe zaku tafi?”

“Yau nake shirin mu rage hanya” ya bashi amsa cikin girmamawa, nisawa yae yace

“Koda 12:pm zatayi ku zama a bakin mota zn fito nima” haka sukai sallama akan zasu shirya tafiyar.

**********

   Anan suka kwana a tsorace seda asuba sukai sallah sannan suka nemi yi gaba, Alhamduliillah basu jima da soma tafiya ba suka soma barin saharar, suka had’u da wuri me yalwar itatuwa da ‘ya’yan itatuwa masu yawan gaske, Bismillah sukai suka zauna sukaci tufa dasukagani burjin awurin had’e dayin uban guzuri dn kuwa Abu Huraira rigarshi ya cire ya cikata fam da Tufa da Mango sannan sukaja yana goye da rigar. Kuma ba jimawa suka had’u da ruwa, anan suka sha ruwan kowa da hannunshi sannan suka huta sukai azahar da la’asar sanan suka mik’i hanya dan yanzu ba laifi kowa cikinsa ya d’ago, rana ta k’wale  se dukansu take gashi yanzu kam sunkai wurin wasu ciyayi masu yawan Gaske anan Lawuri ta taka k’aya, k’ara ta k’walla me k’arfin gaske aikam da sauri Sufyan yayo kanta, baze manta taimakon datamai ba har abada matsawa yar ya rik’o k’afar tata ya zaunar da ita seda ya cirw mata k’ayar sannan ya tasheta tsaye, takalmin k’afarsa ya zare ya nuna mata su akan tasaka, kallonshi tae kowa yayi turus acikinsu bame cewa komai, ganin bata saka ba ya sanya da kanshi ya tsuguna ya saka mata, sannaj yaja hannunta sukai gaba….agaba suka wuce da k’yar take tafiya da takalmin sabida rashin sabo shi kuwa Abu Hurairah besan mesa beji dad’in yanda Abu sufyan yae ba, sukse yaji ma jikinsa yae sanyi, ranshi yana d’an sosuwa a hankali a hankali musamman daya kula lokaci zuwa lokaci sukan kalli juna su sakarwa juna lallausan murmushi meke nan hakan yake nufi?…

A b’angaren Lawuri kuwa burge ta yakeyi takula yafi d’an uwanshi sakin jiki yafishi kirki kuma, sannan suna burgeta sabida sunason taimakon wani, yanayin dayake rik’e da hannunta kuwa yana tayata tafiyar danya kula bata iya bane, se abin yake sakasu dariya dukkansu har suke manta damuwar su, dazaran tad’anyi wani taku ba daidai ba seya nurmusa itama kuma hakan.

********

 Sunyi tafiya me nisan zango, yayinda sukeda tabbacin ana biye dasu, koda yake sun b’ace hanya suma bare mabiyan su, K’arar da Lawuri ta k’walla ne ya mayarda dukkan hankulan mazajen uku akanta harma da Baiwarta Barbo, tahau surfafa yare tana sambatu tana nuna k’afarta had’e da yarfe hannayenta duka biya, Abu sufyan da har lokacin suna tafiyane agaba yae sauri mayarda dubanshi ga k’afar har lokacin duhu be sauka ba,  k’atotuwar kunama ya gani agefenta, da sauri ya janyeta a wurin yace

“Dawood kunama ce ku kalleta k’atotuwar gaske” shida Abu Huraira duk suka kalli gun ita kuwa kunamar da sauri ta shige acikin ciyayi tae tafiyarta, yayinda Lawuri se k’ara take, sunkuyawa yae yana duba inda harbin yake, seda suka janyeta daga wurin ciyayin dannan aka zare takalmin a saman babban d’an ya tsantane ta harbeta amma a yanda suka kula dukta soma haye mata sama tama rasa ina zata nuna, Abu sufyan rigarshi ya cire ya ya yageta da sauri dukda k’arfin datake dashi ya daure yatsan, sannan ya zari k’aya ya caki gun ya sanya bakinshi ya tsotse jinin tatas, yana zubar wa a k’asa, se gumi take had’awa suna mata sannu, Abu Huraira yayi sororo yasani abinda qaninsa yae taimakone amma mesa yakejin ba dad’i a ranshi? Menene yasa bayaso yaga ana taimakon wannan baiwar Allah alhali shi kuma ya tabbatar har k’asan zuciyarsa yana tsananin jin tausayin yarinyar. Abu sufyan kuwa dukya tashi hankalin sa, gashi macece bare ya goyeta gashi basason duhu yae batare dasun isa inda ya dace su isaba, san wannan wurin an sma da kunama  inata ga kuma dare yayi, dole sui sauri su bar gurin, ganin taimakone kuma babu wata hanya se wannan ya sanya yace ze goye ta, harara Abu Hurairah ya wurga masa cikin takaici yace dashi

“Kai kana haukane zaka ce zaka giyeta abayanka?” Kallon sa yae cikin mamaki

“To anan zamu tabbata Bro, kana gani fa bazata iya tafiya ba, idan dare ya mana anan an soma da kunama ya kake tunanin zata k’are? Kokuma Waze goyetan to? Wannan macece bazata iya d’aukar taba” cikin b’acin rai yace

“Nizan goyeta bakai ba kamaji na gaya maka matsamun agun!” Ko motsawa Abu sufyan beyiba zabida mamakin kalaman yayan nashi kuma tawayenshi meke damunshi haka?…

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *