DOGUWAR HANYA CHAPTER 7

Sauke abinda ke kanshi yae yace

“Karka tsorata Hurairah Dawud ne, dama ina bayanka, na rufe fuskatane na sace kayan jikin d’aya daga cikin masu gadin mu, shiyasa kamun nisa ma, naga suma haka suke yawon dare da ganye akai shine na d’ora” Ajiyan zuciya me nauyi sosai Abu Huraira ya sauke yace

“Kayi hakuri Dawud, banda nutsuwar zama acen nabar d’an uwana a uk’uba koda hakan ce sun kasheshi gwara amai salla Dawud, basusan darajar mutane ba”  Rik’o hannunsa Dawud yae

“Kashe fitilan wayar nan muyi adu’a kar wani ya hango haske, mutafi inaga nanne hanyan bayan gari, sabida nan sukace sun kaishi sun wurgar kuma akwai naman jeji inaga fa” shiru yae baya ya kashe suka rik’e hannun juna sannan sukai gaba cikin sand’a, seda sukaji sun dena yawo ajikin bishiyoyin sannan suka kunna fitilar wayar su, lokacin har gari ya soma wayewa, sunyi nisa sosai harsun k’araso wurin ruwan suka hangoshi yashe ko motsi bayayi, da sauri sukai kanshi, d’an uwanshi ya tallafo kanshi sosai ya d’aura asaman cinyar sa yana zubar da k’walla, ganin yanda duk kanshi ya kukkunbura harma da jikin sa sabida azabar duka, kwantar da kanshi yae jikin k’irjinsa yaji yana zuciyar sa na bugawa amma cen maqale, hannunsa ya d’aga ya rik’e ta wutsiyar da kan yatsunsa yaji purse nashi ma ba laifi sedai a hankali sosai komai yayi law sosai

“Dawud yanada ranshi duba mana jirgi mubar nan gun dashi kawai” D’aga kai Dawud yae amma ba alamar jigin k’asa ko d’aya, wannan alamace ta cewar wancen jirgin ma da sani aka turashi gun hanyar ba wacce ake yawan bi bace ba, kai ba’a ma bi ruwan yayi yawan da bazasu iya tsallakawa ta hanyar aiki da jikin suba

“Abu Huraira babu jirgi anan, sedai da ace a farke yake zamu iya amfani da manyan icen cen kowa ya rik’e d’aya mubar nan jejin tun muna shaida juna” ruwa ya ebo a hannunsa ya wankewa Sufyan Fuska dashi, seda yae kusan so uku sannan ya farfad’o sedai ba k’arfi, suka tashesa a zaune yana buqatar ruwa ba abin shansu, haka suka dinga ebowa da hannu suna bashi harya k’oshi, Shiru sukayi dan sunga garin ya soma washewa sosai, tabbas kuwa se anbi bayansu, dan zuwa yanzu dole ansan basa nan

“Ka bari na sanya Al-hasan a bayana mu tafi, biyo sahu zasuyi kuma tabbas sesun tarar sun fimu sanin hanya” Tashi tsaye sukayi ya sanya Abu Sufyan a bayan shi suka kama hanya cikin sassafarwa, agefen ruwan dabasuda tabbacin zasuga k’arshen sa. Basufi 30mns suna tafiya ba aka zageyesu, cikin takaici Abu Huraira ya k’walla k’ara ya sauke Abu sufyan a k’asa yabi k’artin da kallo, matsowa Lawuri tae sosai suka had’a ido da Abu Huraira kallon dayake mata kawai ya isa ya nuna tsantsar tsanar dayake mata a k’wayar idansa, hannunta takai ta rik’e masa hannu, yanayin rik’on datamai bega alamar na fad’a bane wanan ya sanya yae sororo yana kallonta, jira yake kurun yaga me take nufi da wannan salon iskancin kuma, Abu sufyan ta nuna da yatsanta tace

“Ku bashi yasha” Da sauri gardawan sukai kanshi suka tashshi zaune suka d’ago kanshi suna shirin qyanqyama mai ruwan, kallon Dawud tae tace

“Dashine ya kashe lamme (zaki) da tuni ya mutu, nasan wannan ne me hanani nutsuwa ya kashe sa, shisa na kawo masa magani inba hakaba shima dafin ruwan a hankali a hankali ze zagaye jikinsa harya mutu” kallon Abu Huraira yae cikin sauri yace

“Barshi  yasha Abu Hurairah magani ne, ta gano bashi bane ya kashe wancen zakin kaine” bece komai ba se kallon cikin k’wayar idanta dayakeyi, Abu sufyan yana shaye ruwan ya singa aman jini ya jima sosai yanayi kafin ya tsagaita, ruwa tasa aka bashi yasha sekuma gashi ya mik’e asaman k’afafuwanshi, kallon muk’arabanta tae maza da mata, babu wanda yasan tafito tasan bayanta zasu biyu musamman dayake baqi ma sun gudu, koda yake seda ta sumar da masu gadin su, hannun Abu huraira taja

“Kujagirancemu mu rakasu  hanyar barin gari me sauki, wacce muke bi da sarki”  Zaro ido wani daga cikin su yae kanshi a k’asa ya soma bata hakuri akan ta dubawa Danginta da mahaifinta tabar biyu su tafi amma d’ayan na sacrifice a barshi ya koma” kallonsa tae tace

“Naji muje semu dawo da d’ayan, ainima bazanyi hakan ba” haka suka kama hanya cikin sauri harsu har ita, koda yake duka ya lankwashe Sufyan seda wani gardi ya goyeshi ma.

**************

     Sarki K’uru bebi takan suba yau, bekuma bi takan ‘yarsaba idan da sabo ma yarigada ya saba da yawan yawon ta na tsiya, zema iya cewa tafishi sanin wannan garin nashi da kewaye, shidai hankalin shi ya kwanta tunda ya samu wanda zeyi garkuwa dasu.

Maganin baccin data baiwa masu gadin shi kuwa ta dumar dasu juju ne na garinsu, ze iya sumar dakai kwana biyu ma, sabida haka babu wanda yasan meya faru seda mekai musu abinci yaje ya tarar suna bacci zuwa,kumama be tashesuba ajiyewa kurin yae ya juya abinshi wannan ne ya sanya babu wanda ya nemesu.

************

   Gardawan nan ilahirinsu tace su juya zatazo tare da Dawud bayan sunyi tafiya me nisa data tabbatar cewar bazasu iya qarisawa gidaba se cikin dare, yarinyar ta Barbo kurun tace zasu dawo tare, babban cikinsu ne ya mata gaddama akan bazata iya juyawa ita kad’ai ba, take ta sharara masa mari

“Dacen danake zuwa jeji nai kwana biyu tare muke zuwa? Ina ruwanka? Nace ka koma ban gayawa kowa na fitaba hankalinsu seya tashi” duk’ar da kanshi yae

“To kozamu koma tare da wannan d’inne?” Ya tambayeta yana nuna Dawood, harara ta wurga masa

“Ni zanzo dashi da kaina nace, kuma idan kaje kace wad’annan duka biyu sun mutu, dama ai ana tsammanin wannan ya mutu ko?, to kace bamu ganshi ba yabi ruwa wannan kuma kace dukanshi kukai bayan ya gudu akazo da tsautsayi ya mutu kanaji ba?” Cikin girmamawa yace “to” suka juya aka barta itada Baiwarta Barbo kurun.

Abu Huraira shine ya koya d’na uwansa tajagorancesu cikin sassarfa acikin wannan mugin jejin, banbancinsa da wancen shine akan had’u da ‘ya’yan itatuwa kala kala asha.

*******

*Littafina na kud’ine, idan har kika karanta baki biyaba keda Allah, idan kinason siya ki tuntub’i wannan lambar 07084161619*

***********

  Duk iyakar qoqarin da sojojin nan zasuyi sunyi suda Barda tabbas Barde ya sanar dasu sun tsallaka ruwa ne, kuma wannan ruwan shima mahaifinsa ya tsallaka be dawo ba, sabida haka shikam baze shigaba, sannan ba jirgi dan acewar kakansa lokaci zuwa lokaci suke aiko da jirgi k’walli d’aya jal tamkar abun tsafi, dan haka idanma bi zakayi sedai kai kazo da jirgin ka, wannan ruwan kogi ne babba, wanda yake had’a gari zuwa gari bakasan ina ya tsaya ba” Shiru Oga shamsu yae yarasa bakin magana dankuwa shida kanshi duk yawan dazukan dasuka shiga bega kamar wanan ba, ba naman jeji ko d’aya ba ‘ya’yan itatuwa kuma ba ruwa se wannan, abin akwai hatsari, Sir munir ne ya dafa kafad’arsa yace

“Dolene semunyi ta soja, yanzu kasan mezai faru? Komawa zamuyi gida amma akan hanyarmu ta komawa kowane itace muka gani mu shafa penti gudun b’acewar hanya, sannan adawo da jirgi me saukar Angulu k’waya hud’u da motar yak’i k’waya biyar, a samo motarmu k’waya biyar sannan azo da mayak’a, muzo da floating bridge mu tsallaka wannan ruwan inaga wannan shi kad’aine solution” Nisawa yae sannan ya sakar masa murmushi

“Munir kaime basirane sosai, dole hakan zamuyi dan general baze d’agamuna k’afaba” da wannan shawarar suka juya zuwa gida.

********

  Ansha fama kam wurin tafiya, koda wancen suka ankara har sunyi tafiya me nisan gaske, sarki yashiga tashin hankali dole yace abi bayansu da gudun fanfalaqi, acewarsa zasu cutar masa da ‘yarsa tunda dukansu mata ne.

A b’angaren su Abu sufyan kuwa mamaki sosai suke yanda take leading nasu tana musu bayanin so take ta fitar dasu daga garin gaba d’aya yanda baza’a kowa acikin su ba, har take baiwa Dawud labarin abinda ake da mutane idan an kamasu a k’arshen shekara, yasha jinin jikin sa har yakewa maimaitawa Abu Huraira labarin data bashi shida kanshibya tsorata, ta qara da cewar bata san dalilin dayasan takejin bazata iya kallo akashe suba musamman Abu Huraira sedai kome ze faru ya faru, tana kuma son wannan maganar dasuke had’a baki sunayi susu duka idan sunayi setaji sanyi, wannan ne karon farki da Dawood yae murmushi tun zuwansu wannan Doguwar hanyar yagano karatun alk’ur’ani me girma take nufi hakan abu ne dake nuni da yanda takeson addinin nasu alamace dacewar zasu zama wani Haske ga wannan al’ummar idan Allah yaso…..

        Tunda sukazo wannan d’an k’aramin garin suka sake tsorata, Babu wanda ya kulasu agarin bakuma suji kowa na magana ba har yarama kowa shiru yake, Lawuri ta kalli Dawud cikin tashin hankali tace dashi

“Ni bantab’a had’uwa da wannan garin ba, ga alama nima na b’ace hanya ne, dan gaskia yaci ace mun isa hanyar dazaku hau jirgin ruwa zuwa wani wurin ni bansan kowane yare bama se biyu, kuma wancen garin banan hanyar bane ba, gaba da namune sosai, wannan mutanen kuma waye su?. Turus suka tsaya suna kallon mutanen dasukayi tamkar ma basu san anyi ruwan tsiyar su bama.

  Suna nan har yamma  ta qarayi duhu na fara sauka suka soma ganin mutanen garin na sharara uban gudu suna shigewa k’ananun bukkokin su, kowa kuma tsita bame magana amma se ruwan gudu ake ana b’oyewa hakan ce ta sanya su Dawud suma rugawa su adana kawunansu cikin wata bukkar dasuka kula babu wanda ya shiga acikinta,

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *