DOGUWAR HANYA CHAPTER 10

Haka ya dinga zubar jini yana juyi agun, lawuri ta kalli Barbo tace da ita cikin yarensu

“Yana zubar da jini da yawa, naga kaman akwai ganye aja anan wurin da sauri ki tsinkamun” Batare da Barbo tayi magana ba ta juya da gudu cikin jejin, seda ta had’o ganyaye kusan uku sannan ta dawo, ba wani ruwan dazasu wanke ganyayen hakla ta murje ganyayen da hannunta ta ta kama k’afar da aka harba ta cura su tana nan manne da wurin sesa taga jinin ya dena zubowa, sannan abu sufyan ya qara yagar rigarsa aka d’aure k’afar

“Mubar nan wurin, nizan goyeshi, mu taimaki kanmu kar daren

yae mana anan, bamusan mezai faru ba” Driver kuwa kallon su yae yace da hausarsa ta fulani

“Sa’a suka samu daganan zuwa cikin gari ba wani nisa, ko’a mota befi mana saura mintuna 25 ba, sunsan kota bata zuwa k’auyen nan se bisa tsautsayi dan haka mutaka, bana tunanin nanda awanni biyu ma bazamu isa koma qasa ga hakan” jinjina kai dawood yae

“Bakajin dad’i abokina, barin goye shi idan na gaji ka tayani, ni asibiti nakeso mui rushing muje” shidai Abu Hurairah bayama cikin hayyacinsa azabar dafin billet daya ratsa shi kawai ya ishesa, haka suka rankaya Dawood yana goye dashi suka ci gaba da yankan doguwar hanyar, taimakon da Allah ya musu ma titine ba kwana ko shiga gona ko jeji bare ka b’ata.

***********

  Sunyi tafiyar kamar awanni biyu kafin suka taradda babban gari anata hada hada, kai tsaye asibiti suka wuce dukda bame waya acikinsu babu kuma wanda yakeda ko k’wandala,wahala sosai sukasha akan sesun kawo police report kafin a karb’eshi daga k’arshe kuma akace baza’a musu aiki ba kud’i ba, a binciken da Abu sufyan yae kuwa garin dasuka sauka ko kusa beda alaqa da garin dasuke yanzu, tafiyace ta tsawon kwanaki kafin ka isa wancen garin dasuka baro kayansu kuma ATM card d’inshi yana cikin kayan sa, dama Na huraira ne suka fito dashi kuma ya b’ata tuni, ajakar dasuka baro k’auyen su Lawuri yake, dafe kanshi yae ganin yanda jini ke zubar masa cikin ma an tsare dana hausa gashi harya suma ma sabida azaba

“Dawood yanzu ina zamu samu kud’i anan? Yaya zamuyi ni kaina ya d’aure wlhy” kallonshi yae shima cikesa damuwa

“Bansan yanda zamuyi ba? Bansan  wasu irin k’addarori bane marasa dad’i suke bibiyar mu, na rasa gano inda al’amarin ya dosa” shiru sukai dukkansu suna tunanin mafita

************

  Sun tsaya da motarsu ganin jini akan titin, inda d’aya daga cikin sojojin wanda likitan soja ne shi ya Duba jinin, kallon general yae yace

“Baze wuce 3 hours ba da faruwar abun, abun kuma jinin na mutum ne” Nisawa yae cikin tashin hankali ya kalli dirensu yace

“Dama ana fashine anan?” Asuwakin dake bakinsa ya goga hak’waranshi dashi

“Sosai kau, sabida ai sunsan a wannan ranar kad’ai mota ke wucewa se kuma bayan sati biyu irin ranar, kuma kayan abunci suke karb’ewa sedai kuma sukan tafi da motar ne, wani zubin ma sekaga sun ajiye motar abakin titin nanda en kwanaki, kuma idan akai gaddama sukanyi harbi gaskia” Shiru General yae kanshi ya k’ulle, duk abinda ya faru da yaran nan laifin sane, besan mesa ya kafe akan sesunyi tafiyar nan ba, mahaifiyar suma tace hankalinta be kwanta da tafiyar ba, shi har yanzu mamakin kanshi yake wlhy, yanda ya dage yanzu wa gari ya waya?

“Amm yanzu mintuna nawa zasu kaimu cikin garin?” Kallonsa yae

“Ai munzo, mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar sun wadatar, an kusa zuwa cikin garin ai” bece komai ba ya koma mota sukai d’auki hanyar cikin garin, bayan da duka isa yace da General

“Yanzu tashar mu zamuje semuji meya faru awurin direban” jinjina ka shi yae yana mamakin yanda gabaki d’aya kanshi ya dena aiki, har suka k’arisa bece komai ba.

Sunyi sa’ar ganin direban kuwa inda suke basu labarin meya faru, har abinda ya faru da en bunnin nan, hankalin General ya tashi matuk’a dajin wannan zancen

“Yanzu wane asibitin sukaje?” Rike baki Direban ya

“Sunce su bak’ine basu tab’a zuwa nan garin ba, nima kuma ban tab’a sanin wani asibiti ba anan, amma dai gabas sukayi danko kud’in dazasu hau adaidaita basuda shi” Godiya General ya musu sannan ya nemi gidan soji na nan garin ya karb’i mota da direban su, kana ya soma yawon asibito cin garin kaf neman yaranshi.

***********

  “Koyaya naso nai tunani sena gagarayi, zuciyata tana mun tserereniya akan abinda ze faru ga d’an uwana Dawood, ina cikin tashin hankali mara misaltuwa bansan waze taimakemu ba, asibitin nan basuda imani suna ganin mutum helpless su taikeshi bashi bane a ransu se zancen kud’i?” Kallonshi Dawood yae cikin damuwa yace

“Ga bamuda waya, gabansan number kowa aka ba” cikin zaquwa yace

“Nasan number mom aka, muje gun kiran waya na kud’i kokuma ma mu ari wayar likita anan ko wani staff”

“Hakan yayi muje” hakan sukaje suka samu wata mace a reception suka ari wayanta suka kira mom, haka sukayi ta kiranta a waya bata d’agawa har kusan so ba adadi, cikeda damuwa ya wurgawa dawood idanshi

“Bata d’auka ba wlhy” ya fad’a cikeda damuwa

“Ita kad’aice number dakake da itane?” Shiru yae nad’an lokaci kanyace

“Se Number Ayusher, barin gwada neman ta muji” kiranta yae ringin biyu ta d’aga kuwa, cikin muryanta me dad’i tace

“Hello” guntun tsaki yaja

“Badai zaki dena ba kenan ko?” Tashi zaune tayi cikin mamaki

“Father sword da gaske kaine, where have you been? Hav bn trying ur number all this while but its not going through” dafa goshin sa yae cikin qosawa da zancen nata yace

“Ayusher saurareni mana” shiru tae dan tasan seya datse kiran yanzu

“Ina cikin problem and bayaga number mommy banida number kowa aka bayan naki, so zanje wurin first mony agent zan qara kiranki a waya, u transfer 150k in to their acc inyaso sesu taimaka su bani cash” Nisawa tae

“Meya faru dakai hakane Farher sword?” Haushinta ya somaji

“Look Ayusher banida time na dogon bayani, just do as i say, u makesure that kin ajiye wayanki a kusa dake, zn kiraki da wani layin daba wannan ba yanzun nan ba jimawa, sena tura miki acc details d’in” murmushi tae

“Alright Pure hrt bye” ta kashe wayan, neman gun first money agent sukai, sunsh fama dasu kafin su yarda, sabida acewar su sedai ka bada kud’i a tura ma waninka, koka basu ATM su cira da kansu  su baka, da qyar gashi weekends ne suka yarda da wannan shawarar, suka taimaka yashirata ta turo mai kud’in aka bashi sannan suka koma asibiti.

************

  Alhamdulillah anyi masa aiki an cire bullet d’in lokaci bullet ne ma, na irin bundigar nan ta farauta, alamun dai qauyawa ne, aka saku damar gayar k’afar kuma anyi sa’a da aikin dan kuwa zuwa dare harya farfad’o, shi kuwa General beyi tsammanin zasuce asibiti ta garin babba ba, sedabya gama karad’e asbitocin garin kaf da clinics be samesu ba sannan ya nemi makwanci badan yaso ba, se washe gari ya soma neman Su a teaching hospital ta garin.

Besha wahala ba gun gano har d’akin dasuke, koda Abu sufyan ya ganshi a d’akin kasa koda k’wak’waran motsi yae ya k’ura masa na mujiya kawai yana kallon sa!, a hankali ya taka gun gadon na Abu huraira ya kalleshi yana bacci tausayin yaron ya sanyashi kuka, gashi kuma duk Abu sufyan yafita hayyacin sa, banda wahala babu abinda kake hangowa a fuskokin su, seda Abu Sufyan ya rungumeshi suka sha kukansu kafin su zauna baiwa juna labarin abinda ya faru, shirin tafiya gida yae musu ba b’ata lokaci sabida mahaifiyar su dake cikin halin ciwo ba qaqqautawa.

*Ban saniba ko iyakar tsawon hanyar kenan, ban saniba ko sun gama shan wahalar rayuwa kokuma da saura, bana tunanin nasan mezai faru agaba, abu d’aya na sani shine yanxu aka soma wasan, wasan na manya ne, wasan me wahala ne, dani daku semun daurewa bin Doguwar hanyar nan atare kozamu samu madafar b’ullewa*

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *