[Advertisements⬇️]

SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 30 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Zainab ji ta yi ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba,ta yi kukan kura sai tafaɗa kan Juwairiya ta ƙara shaƙe mata maƙogaro.

Uban wa ya yi miki ciki da ma ke ƴar iska ce.”

A.m da sauri ya yi kanta tare da ƙoƙarin ɗaga ta kanta ganin ta nason ta yi mishi illa.”Ba ki da hankali ƴar mutane za ki kashe?”Ya celokacin da ya ɗaga ta daga jikinta.

Barni da ita wallahi in  a kwai abin da yafi kisa zan yi mata! Ta yaya za ayi tayo ciki ta shigo mini da shi gida.”

Sai kuma ta ce. A.m don Allah karka sa na haukace ahalin yanzu jinake kamar numfashi na zai ɗauke!Ka da zargina ya zama gaskiyaka barni na koreta a gidan ta je can ta nemi uban cikinta.”

Zainab ki tsaya ki fahimce ni na yi miki bayan…”

Wai mai za ka gaya mini?In dai ba ka na son ka faɗa mini yau neranar da fitan numfashina zai yi bankwana da gangar jikina“!To naroƙe ka don Allah ka ƙyale ni.Juwairiya ta fita daga gidan nan shinekawai zai saka na fitar da zargi a cikin zuciyata.Ta ce tana kukasosai.

Sam ba za ta bar gidan nan ba samun sauƙin ki shine ki fahimciabin da zan gaya miki,domin ba ni da nufin na cutar da ke duk abinda yake faruwa na yi ne don ke.”

Ja da baya ta fara yi tana mishi wani irin kallo,sai ta kalli ta ta kumaƙara kallon sa  kawai sai ta shaƙe shi.

Na shiga ukuna ni Zainab zuciyata ,za ta buga A.m zai kashe ni,kada son yara da kake yi don kawai ba na haihuwa ya sa ka naimiJuwairiya ka haihu ta zina! Tur mai za ka yi da ɗan zina kuma yafito ta jinin matsiyata.”

Sai kuma ta sake shi ta nufi kanta tana faɗin.”Wallahi saina kashe kuiyaye sun danƙaramin dukiya,shine za ku din ga zina akan gadonahar ku samu ciki h.”

Ya ishe ki Zainab! Kar ki ƙara ai banta min yaro,kin san halina bazan taɓa aikata zina.”

Ya buɗe baki zai gaya mata matsayinta sai ya kasa ya sunkuyar dakan shi ƙasa,yayin da tsananin tausayi ya kamasa ganin yadda takoma kalar tausayi tana kallonsa.

Ki fahimce ni Zey ke san ba zan taɓa haɗa ki da…”

Ba na son ji! Ba na son ji!! Mayaudari munafiki mai alƙawarinbanza.Tur da na aureka na yi nadamar ranar da na ce ina sonka,karka matso kusa da ni in ba haka ba kashe ka zan yi!”

Ta faɗa tana girgiza kanta tare da toshe kunninta ganin ya nufi ta zairiƙe ta.

Wannan dalilin ya sa na yi duk iyakan ƙoƙarina na fahimtar dake.”

Ya ce da ƙarfi ya na kallonta sannan ya ci gaba da cewa.” To tun daba ki bani dama ba,bari na gaya miki gaskiya…”

Katse shi ta yi da ƙarfi tare da ƙara cakume shi ta ce.” Mai za kugaya mini mai kake son kace?Abu ɗaya na sani cewar mijina A.mya na kwana tare da ƴar aikina,wallahi kaf duniya sai sun ji don ajarida zan buga,A.m ya yi ma ƴar aikina ciki za su haifi ɗan shegeɗan zin.”

Wani irin shaƙa ya kaima wa da ya sa ta ji numfashinta zai ɗauke.

Kar ki ƙara aibata min ciki ɗan dake cikinta halastacce ne kuma taaure muka same shi,don ban san ta ba a matsayin ƴa mace ba,sai daaka karɓar min aurenta.

Ya zaro idanun sa ganin ba ta fahimci abin da ya faɗa ba.” A taƙaiceJuwairiya matata ce ta sunna wanda Daddy ya karɓar min aurenta!Don haka karki ƙara aibanta min yaro don wallahi sai kin gane bakida wayo.”

Kawai gani ya yi ta sulale a ƙasa ta faɗi sumammiya.Da sauri ya yikanta ya na kiran sunan ta.

Gabaki ɗaya ya ruɗe ya rasa ta in da zai fara rungumeta ya yi cikintashin hankali sunanta kawai yake kira.

Da gudu Juwairiya ta shiga kicin ta ibo ruwa ta watsa mata,ammasam ba ta farfaɗo ba jikinta ya yi ɗip kamar babu rai a jikin.

Zainab don Allah kar ki mutu ki barni ba zan iya rayuwa ba,in harbabu ke a cikin duniyar nan,ki tashi na yi miki bayanin na aure ta nedon ke,don Allah ki buɗe ido.

A.m yake faɗi ya na jijjigata cikin tashin hankali. Ya kamata a kaitaasibiti fa kar ta mutu.”

In ji Lantana da take kallon tashin hankali wanda ba’ a saka mishirana.

A.m ya miƙe daidai lokacin da Lantana ta ruga kiran direba,don yakasa komai sai zare idanu da yake yi.

Zubbur ya ga ta miƙe tare da sakin wani irin ƙara wanda sai dagidan ta girgiza,kawai sai ta saki dariya kamar sabon kamu.

Wani ihun ta saki da ƙarfi ta yi kansa ta na faɗin.” Ƙarya kake yiwallahi ni kaɗai na tashi a gidanmu na rayu ni kaɗai ban taɓasharing ɗin wani abu ba,sai kai abin da nafi so fiye da komai arayuwa.Ina hakan ba zai taɓa faruwa ba!”

Ta ƙara riƙe shi ƙam ta ci gaba da cewa.Ƙila mafarkinmu duniyarmahaukata ya kawo mu,don na lura kai kanka ba ka san mai kakefaɗa ba,don wataƙila baka cikin hayyacin ka.”

Mari ta kawo mishi cikin zafin nama ya kauce tare da riƙehannunta,ya zare idanun sa ya ce.”Tabbas bari na ƙara gaya miki itaɗin matata ce,gaskiya kunninki yake gaya miki,kamar yadda igiyaraurena uku yake a kanki,haka ita ma amma ki tsaya ki sauraareni,kin san ina sonki ba zan yi abin da zai cutar dake ba. na aureta nedon na…”

 

                             Kai.”

Ta daka mishi tsawa da idanunta da suka rine sukai jajur!Sabodatashin hankali.

Karka gaya min maganar banza ka rabu da ni macuci haƙiƙa kacuce ni,ka kuma yaudareni.Ka manta ka yi min alƙawarin ba za kataɓa min kishiya ba,balle ka sanar da ni ce ba na haihuwa shi ne yauka auri wata mace ban sani ba,kuma saboda cin mutunci ka kawo tagidana ka na kwana da ita a gadon da iyayena suka siyarmini,wallahi mafi girmar kuskuren da ka yi ka kawo ta gidana,kamaida ni banza shashasha sauna! Ashe in bana nan sakewarka kakeda ita?Har kana mini munafucin baka riƙe sunann ta ba.

      Wayyo Allah na! A.m ya maida ni banza ya kawo matarsagidana a matsayin mai aiki!Wace irin banza ne ni har na kasa ganetsakanin su?

Wallahi sai kun yi nadamar abin da kuka yi mini,zan nuna makacewar da gaske ba a yi ma family ɗinmu kishiya,take yanzu zankasheka in kashe kaina haka kuma in kasheta!Mutuwar kasko za muyi daku,ban taɓa sharing ko da wani abu ba balle na haɗa jiki dakaiƙazami kawai.”

Da gudu ta ruga kicin kafin ya farga har ta ɗauko wuƙa ta yi kansuta na faɗin.” A yanzu za ayi ta taƙare yanzu zamu yi mutuwarkasko,hisabi akan abin da kuka yi mini zan yi muku tun kafin ajelahira ku haɗu da ubangiji,munafuki mai karya alƙawari.”

Zainab ki ki natsu karki aikata dana sani! Look Zainab kar kiaikata abin da kike son yi,sheɗan ne yake so ya kaiki ya baro,donAllah ki natsu zan yi miki bayani,ina da dalilin da ya sa na ɓoyemiki auran.”

Kallon mahaukaci take mishi ta tsaita wuƙar daidai gurin Juwairiyatana matsawa kusa da ita.

Saina nuna miki kuskuren da kika yi mijina za ki aura,kin yibabban kuskure ni kaɗai nake rayuwa a gidan mahaifina,hakadangimmu kaf babu wata mace da aka yi wa kishiya sai ni?Wallahiba ku isa ba,sai na nuna muku kuskurenku.”

Gadan-gadan ta yi kanta data tsorata ganin ta nufo ta dawuƙar,ɓoyewa ta yi a bayan A.m da hankalin sa ya tashimatuƙa,saboda yadda Zainab ta koma za ta iya yin komai.

Zainab kar ki kashe musu ƴa za ki yi dana sani fa shari’a ba za taƙyale ki ba kema kashe ki za‘a y.”

“Don na kashe ƴar matsiyata uban wa zai taɓa ni na san ko an kulleni Daddy zai fito dani.”Ta bashi amsa idanunta a bushe.

To ni in kika kashe min ɗa wallahi saina kulle duk yan gidanku bake ba,saboda ko ba komai zan ga ɗana a duniya na rungume shiiyayena su yi alfahari  da hakan.”Ya ce mata cikin zafi da ɗagamurya.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kukan kura ta yi taho kan kanta da gudu jin abin da ya faɗa,yayin daidanunta suka rufe ba ta ji ba ta gani.

Yadda ba na haihuwa kai ma ba za ka taɓa ganin ɗanka ba,sabodakai na lalata mahaifata,don na faranta maka shine za ka auriwata,wallahi baka isa ba.”

Da sauri ya cakume ta ya riƙe ƙam iya ƙarfinsa ganin abin da takeshirin yi.

Juwairiya ta sadaƙar mutuwa za ta yi lokacin da ta yi kanta dawuƙar.Ta rintse idanunta tana salati.

Fuɗuwa suka yi a ƙasa ita da shi ya fara kiciniyar karɓe wuƙar.

Sai kawai ta kai mishi wukar jikin shi Allah ya ba shi sa’a yakauce,wuƙar ta yanki hannun sa sosai.

Ba Juwairiya kawai ba hatta wanda ta yi yankan sai da ta ɗan firgitaganin irin jini da ya fara tsartuwa a hannun sa.

A.m ya kira sunan Allah da ƙarfi ya ji wani irin raɗaɗin azaba yanaziyartar sa,jikin shi ne ya kama rawa ganin duk da yankar da ta yimasa,jini na zuba amma ba ta razana ba,sai ta nufi Juwairiya da ta yikan sa ta kama hannun sa tana kuka,mai haɗe da salati matuƙar tsoroya shige ta ganin abin da ta yi.

Ai na gaya muku wallahi sai kun gane kuskuren ku na cuta ta dakuka yi!Ta faɗa lokacin da ta yi kanta.

Da sauri A.m ya miƙe ya saka ƙafafun sa ya taɗiyeta ta faɗiyarab!Amma da ƙarfin hali duk da buguwar da ta yi,sai da ta ƙaranufo ta da wuƙar.

Ƙara hankaɗe ta ya yi za ta faɗi ya tare ta bayan wuƙar ya faɗi gefe.

Ta saki ihu tana zage-zage kamar wata mahaukaci.

Da ƙarfin tuwo ya riƙe ta tare da yin dubara ya sakata a cikinɗaki,sannan ya jawo ƙofar ya kulle.

Wayar sa ya ɗauka ya kira Mominta don ita kaɗai yake tunanin za tashawo kanta.

Zuciyar sa a fusace ya ja hannunta suka fita,a cikin mota ya saka tasannan ya shiga ya ja.

A.m dake tuƙi gabaki ɗaya hankalin sa ya tashi ƙwarai,ko a mafarkibai taɓa tunanin abin da Zainab za ta yi mishi ba,duk da daman yasan zai sha fama da ita.

Ya juyo yana tuƙi da bai san in da za shi ba ya kalle ta,sai ya ga tadunƙule jikinta hawaye yake turereniya a fuskarta,kamar rawarsanyi take yi ganin yadda ta takure lokaci guda.

Ya sani cewa ya tono ma kan musamman in iyayen sa suka ji abinda ke faruwa,don ya san Zainab sai ta fallasa komai.

Guri ya samu ya samu ya yi parking ba tare da sanin abin da zai yiba,ya kwantar da kan sa a jikin sitiyarin ɗin.

Karo na farko yau ta ga karaya a fuskar shi tun iya rayuwar da sukayi ba ta taɓa ganin abu ya saka jikin shi ya yi sanyi ba,ko da kuwaBaba ne Sani da ta lura ya na matuƙar tsoron shi,amma yanaɓoyewa,sai ya ba ta tausayi sosai.

Ta kalli hannunsa da yake tuƙi jini duk ya ɓata in da ya riƙe kuma yana ta zuba,kawai sai ta saka kuka tare da cire ɗaukwalin da taɗaura,ta kama hannun za ta ɗaure.

Asirina ya tonu ko kaɗan ban taɓa tsammanin lamarin zai tafi tahaka ba,ina tsoron mahaifina in ya ji abin da na aikata,Daddy zai yifushi sosai.Dama haka Zainab take da kishi kai mata basu da tunaniwallahi!Duk abin da na yi don na faranta mata ne.

Ina tsoron Daddy in ya jin wanan lamarin ban san abin da zai yimin ba,wataƙila ya tsame ni daga cikin yaran shi.”

Kamota ya yi ya riƙe da hawaye a fuskar shi ya ce.” Ki ba nishawara na rasa yadda zan yi zuciyata za ta fashe.”

Kawai sai ta fashe da kuka sosai tana tausayin kanta da shi,don itakanta tana tsoron ranar da za ta koma gurin Mama.

Rungumeta ya yi ƙam yana jin kamar rungumar za ta yi masamaganin damuwar sa.

Wani irin hucin zafi ya ji a jikinta da sauri ya matsa gefe yana kallonta,daidai lokacin da ƙamshin turaren sa ya ƙara taso mata da amai,tabuɗe motar a guje ta fara sheƙa shi.

A.m hankalin sa ya tashi sosai ya tsaya yana kallonta ya rasa wanitunani zai yi,gashi ko ruwa babu wanda za ta kuskure bakinta da shi.

Sannu yake ta jera mata ya riƙe ta sosai kamar zai mayar da ita jikinshi,sam bai damu da aman da take yi ba.

Da ta gama aman ta miƙe sai ta ji jiri ya kamata za ta zube a ƙasa,dasauri ya tare ta ta faɗa jikin shi,bai damu da jinin da ke zuba ba yariƙe ta sosai da hannun.

Mota ya mai da ita sannan ya ja suka wuce asibiti.

Doctor ka fara duba ta da gaske wani cikin ta ƙara samu?”

Ya ce da likitan bayan ya zaunar da ita akan kujera.

Likitan ya kalle shi ya ga irin jinin dake zuba a hannun sa,sannan yajuya ya kalle ta da ta yi sanyi sosai,ciki mai ilinbo gabaki ɗaya jinwani iri take a jikinta.

Ya kamata na fara duba ka kalli bleading hannun ka yake yi.”.

Kar ka damu da ni doctor kawai ka duba ta ina son na sani da gaskena kusa zama ubaA ɗokan ce yake magana.Ya faɗa jin abin dalikitan ya ce.

Ok to shikenan bari na kira doctor Garkuwa ya duba ka kar ka faraganin jiri.”

Congratulation ina farin cikin sanar dakai matarka na da ciki satiuku.”

Sujjada kawai ya ga ya yi sai ya rungume shi yana murna.” Ashenima zan zama Baba! Allah na gode maka.”

Gurin da take kwance ya nufa ba tare da ya ji kunyar doctor daketsaye yana kallon sa yana dariya ba,ya bata hot kis bayan yarungume ta.

Da gaske za ki haifa min Baby?”

Dariya doctor ya sannan ya kalle shi ya ce.”Aman da ta yi ya ɗangalabaitar da ita so yanzu za mu ba ta rest bed zuwa an jima sai kutafi,na rubuta muku maganin da zai dakatar da aman.”

No doctor a ƙara mata ruwa kawai saboda jikinta ya yi weak inason yarona ya samu kuzari,kasa ka mata drip kawai ba na son abinda zai cutar da shi,kaga in ba ta da ƙarfi ba zai samu damar ya juyayadda yake so ba.”

Dariya ya yi sosai ya bugi bayan sa.” To fa yau Allah ya haɗani dapatient sabon shiga to Allah ya sa madam ta haifi ƴan biyu,ammajikinta ba sai an saka mata ruwa ba,ka ba ta maganin nan da zararkun je gida.

Duk yadda doctor ya yi da shi amma ya kafe sai an yi mata ƙarinruwa,don kar yaron sa ya wahala,dariya sosai yake masa ganinyaushe akai daren da har gari ya waye yaron da ko gudan jini baizama.

A.m ya ruɗe duk da tashin hankalin da yake ciki amma in ya tunazai sami baby,sai ya ji ya ɗan rage damuwar shi.

Wayar sa ya zaro ya kira A.m akan ya zo asibiti ya same shi.

*********

Zainab ta sa saki wani gigintaccen kuka lokacin da Momi ta shigogidan tana sallama.

Ƙofa ta shiga bugawa tana faɗin.” Momi ki buɗe ni ina ɗaki ya kulleni.”

Jikin Momi ya kama rawa sosai ganin jinin da ya zuba a hannunA.m face-face a falon.

Mai ya saka ya kulle ki lafiya wai mai ke faruwa ne jinin waye aƙasa?”

Ta jero mata tarin tambayoyi cikin tashin hankali.

Faɗawa jikinta ta yi ta saka gigitaccen kuka.

Momi tun da na taso na taɓa neman wani a bu na rasa?Kuma kintaɓa ganin na yi sharing ɗin wani a bu a gidammu,ko da mota ce?”

Da sauri ta girgiza mata kai alaman

a’a.”

To wai Momi A.m yake tare da Juwairiya mai aikina da Lantana taba ni labarin suna tare, kuma wai auren ta ya yi har tana da ciki,yaije ta a gidana suna rayuwar aure.”

Sai ta saki razanannen kuka tana girgiza kanta.

Ni wallahi gani nake kamar mafarki nake yi! Komai ya canza cikinƙanƙanin lokaci.Wayyo Allah na!Na shiga uku.”

Da sauri ta miƙe a zabure. What impossible! Amma wasa kike miniko?Haba ina ta ya ya za’ai A m ya aikata wannan ɗanyan aikin,bayan ya san ba’a yi wa family ɗinmu kishiya,sannan kika ce tasamu ciki wa ya yi mata,bayan shi baya haihuwa ku…”

Momi ki tsaya ki fahimce ni na san na yi miki laifi ban taɓa gayama kowa ba,amma ki yi mini uziri don Allah!”

Ƙara miƙewa ta yi a zabure bayan ta gama gaya mata abin da taɓoye mata tsawon shekaru.

Zaro idanunta ta yi da ƙarfi ta furta.” Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Zainab.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]