[Advertisements⬇️]

SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 29 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Juwairiya kunya ta kama ta matuƙar gaske ji ta yi kamar ta nutse aƙasa,juwaya ta yi za ta koma ciki,amma sai A.m ya janyo ta tare dahaɗa ta da ƙirjin shi.

          Ke! Wace irin mahaukaciya ce da za ki shigo gidanma‘aurata kai tsaye sai ka ce ɗakin gidan ku.”

Lantana jikinta ya kama rawa kamar mazari saboda tsawar da yadaka mata,ta yi mugun firgita ba ta gane abin da ya ce ba.

Ka yi haƙuri yallaɓai wallahi ban san ka na ciki ba,kuma HajiyaZainab ta ce na zo na gyara gidan za ta dawo.”

Ta faɗa jikinta na rawa kanta na asa ta na mamakin abin da ta ganidon ta firgita.

A.m ya yi farin ciki sosai jin abin da ta ce sai ya ɗan ture ta dagajikinsa,ya kalli Lantana da har yanzu idanunta a ƙasa suke,ba ta sonta ƙara ganin abin da ta gani,domin ƙila ƙarya suke mata.

Ok sai ki je ki yi aikin ki munafuka na sha mamaki da Zainab tatunume ni akan ina tare da Juwairiya,a she ke ce munafukar da takeson raba aure.

Wallahi kin ji na rantse miki in har kika yi gigin faɗa mata abin daidanun ki suka gani,kaf ƴan gidan ku ni ne ajalin su don bom zansiya na tashi gidan.”

Ware idanunta ta yi tsananin tsoron sa ya kamata saboda idanun sasun tabbatar mata da zai yi fiye da haka.

Ba ke kin iya munafunci ba to bari na ƙara miki da abin da zaikashe ki,don ba za ki iya faɗa mata ba duk munafuncin ki saboda inban kashe ki ba,to ita za ta yi ajalin ki kin ga gulma ta yi ribakenan.”

Ya ce da ita ya na zare mata ido domin haushi take ba shi,tun da yaji ita ta faɗa mata komai,ga shi yanzu ta korar masa da matar so.

“Juwairiya matata ce wanda na aura a bisa wasu dalilai da ba zangaya miki ba,saboda bai shafe ki ba.”

Ya ƙara matse ta sosai a jikin sa kiss ya sakin mata a kumatunta,yana mata wani irin kallo da ya saka ta kauda idanunta saboda kunyarLantana.

Kin ga in ta dawo sai ki gaya ba mata yau ƙin ƙara gani ba kumaiyakan runguma ba,ki sanar mata duk abin da kika gani kar ki rage.”

Lantana da sauri ta shige kicin tare da rufe ƙofar.

        Innalillahi na shiga uku!”

Ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yayin da kanta ya kulle ta rasa in daza ta fara tunani.

Wallahi wannan mutumin ya rikita ni na rasa mai zan faratunanin,a halin yanzu zuciyata ba za ta iya fahimtar komai ba,dominya saka ni a cikin ruɗu.”Ta ce yayin da ta ɗora hannu akanta.

Da gaske ya ke faɗin matar sa ce ita?A ‘a lamarin nan a kwairikitarwa! Ji fa yadda ta koma tamkar wata gilas,saboda tsabar kyaukai Zainab shashashar mace ce,wai ta je hutu ai kuwa ki dawo za kiga sakamakon hutu.”

Wa ni ai komai na ga kuna yi ba zan iya gigin gaya mata ba,hakakawai ku da holewa ni da shan bugu.Kai amma fa A.m ƙarshe negurin rashin mutunci don ko kaɗan Zainab ba ta yi tunanin ta nagidan ba.”

Irin maganar da take yi a zuciyarta kenan ta buɗe ƙofar a hankali tana leƙen su,sai ta ga sun ƙara rugawa da gudu sun yi ciki.

Allah ya kai mu ki dawo gidan nan za mu

sha kallo!Allah ya sa kar ki yi shigowar dare in ba ma idanunaabinci,sai ki gane sakaci kika yi ko halin maza A.m yake nunamiki.”Ta faɗa sannan ta kama aikinta zuciyarta cinkushe da tunanikala-kala.

Bini-bini za ta leƙa ta na kallon sama amma sai ta ji shuru kamarbacci suka yi.

Ha ina tausayin ki yarinya ba ri Zainab ta dawo.”Ta ce ta na aikicikin mamakin lamari da al’ajabi.

Humh namiji bunun ƙaya.”

Abin da take ta nanatawa kenan a cikin zuciyarta.

A.m ya rungume hannun shi ya na kallonta da ta kwanta akan cinyarshi,ta ɗora filo a ƙirjinta idanunta lumshe kamar ta na bacci,sai dai azahirin gaskiya ba bacci take yi ba.

Zuciyarta cinkushe da kishi da tunani jin Zainab za ta dawo,domin ayadda take jin son sa da kishin ta ba za ta iya ɓoye kanta ba,kamaryadda ta yi a farko ta na jin ko sama da ƙasa za su haɗe za ta nunakanta a wannan karon.

Kamar yadda take tunani shi ma haka zuciyar sa take cinkushe datunani,ga shi ya gagara samo mafita.

Duk da cewa zuciya da gangar jiki sun yi kewar Zainab,amma in yatuna za ta dawo gaban sa yake wani irin yankewa ya faɗi.

Ya sani a yanzu babu wanda zai kalle ta yabce ita yar aiki ce,dubaga yadda ta koma tamkar wata tarwaɗa.

Ya na ta tunanin ko ya ɗauke ta daga gidan sai dai ya na jin ba zaiiya jure rashin abincinta ba,saboda har yanzu ya kasa iya cin abincinLantana.

Wayarsa ya zaro ya gwada wayar Zainab da ya daina kira,saboda ƙinɗauka da take yi.

Sai dai ringing ɗaya ya ji ta amsa tare da sakin kuka.

Ka daina sona A.m ban taɓa tunanin a kwai ranar da zan yi fushida kai ka ƙyale ni ba.”

Ta amsa daga ɓangarenta ta na wani irin kuka da yake tafarfasamasa zuciya.

Tsam Juwairiya tamiƙe daga jikin sa ta fice daga ɗakin ba tare da takalle shi ba,yayin da zuciyarta ke mata luguden bugu na kishin sa.

Binta da kallo ya yi ganin ta canza kalar fuskarta kamar ba wacce yasani ba.

Sai da ta fice daga ɗakin ya saukar da nauyayyar ajiyar zuciya.

Ya kike son na yi kin mai da ni kamar wani ƙwallo don kawai kinga Allah ya jarabce ni da son ki?Kawai na ba ki dama kije duk abinda kika yi ninya ki yi,ni dai har yanzu ba zan fasa gaya miki inasonki ba.”

Ya ce da ita ya na jin tsananin haushinta da kuma fargabar abin dazai faru,domin ya na ji a jikin sa kamar lokaci ya yi da zai gaya matazaman Juwairiya a gidan su,don su daina samun saɓani,duk da yasan zai sha wahala kafin ta amince.

In har ka na sona da gaske A.m ka daina kawo rigima a cikinaurenmu,sannan ka tuna da alƙawarin da ka yi min don Allah karkacanza.”

Shiru ya yi bai ce komai ba ya rufe bakin sa da hannun sa ya na jinsaukar kukan da take yi.

Ka yi shiru ba ka ce min komai.Ta faɗa cikin muryar kuka.

Mai kike son na ce miki Zainab wane irin halacci ne ban yi mikiba! Ki dawo a kwai wata magana mahimmanciya wace za mutautauna,kuma in kika fahimce ni in sha Allahu ba za mu ƙarasamun tarnaƙi a aurenmu b.”

A.m a kwai matsala ne don Allah ka faɗa min?”

Ta tambaye shi da zaƙuwa jin muryar sa ta canza.” Babu kuma karmaganar da na ce miki za mu yi ya ɗaga hankalinki domin alkhairice.”

Ok to shikenan baby ba matsala,amma fa ka canza gabakiɗaya,domin da ace babu wata matsala cewa za ka yi in jira ka mutaho tare.”Ta ce da shi da wata kalar murya.

Wataƙila da izinana kika tafi?

Ya ce da ita a ƙufule kawai sai ta ji ya datse wayar, a lokacin da takefaɗin.

Tun da ba za ka zo ba sai ƙarshen za mu dawo,saboda zamu tsayamu yi siyayya.”

Miƙewa akan gadon ya yi tare da shafa gemun sa da ya ƙawata masafuska.

Wani irin damuwa ya ji ya lulluɓe shi sosai.

Gaskiya na canza shawara ina ganin kawai zan ɓoye Juwairiya duksan da ta samu ciki,sai na saka Zainab ta yi cikin ƙarya a zuwan itatake da ciki in ta haihu ɗan ya zama Zainab a zuwan ita ce ta haihu.”

Take ya amince da shawarar sai ya miƙe da sauri ya saka takalminsa ya fice zuwa ɗakinta.

Ta na tsaye a gaban mirrow ta juya bayanta tare da ɗan jingina kantada gefen mirrow,a ranta ita kaɗai ta san mai take tunani,domin iyatsananin damuwar dake kan fuskarta na hango.Ba tare da ta san yashigo ba ya fara magana.

Kallon sa take yi da wani irin canji a fuskarta har ya gama matabayani,ba ta tanka ba illa kallon sa da take kamar baƙo a gare ta.

Ganin ba ta da ninyar magana sai ya saki tsaki ya juya ya na faɗin.”Ina fatan kin ji mai na ce.”

Ko kaɗan A.m bai canza mata ba wai don Zainab za tadawo,haushin da take ba shi duk ya yi mata maganar abin da yatsara sai ta yi shiru ta zamar masa kamar wata kurma.

Zaune suke a falo sun dawo daga siyayya A.m ya ce ta raka shi akwai turaren da yake son ya siya.

Sun zaune a falon ƙasa sun baje kayan ciye-ciye suna ci

Turaren da ya siyo ya na son ya yi haɗa da wanda yakeshafawa,saboda turaren ya tafi da imanin sa gashi ba zai iya canzawanda yake fesawa ba.

A hannunta ya kama ya fesa mata a hannun ya ce.” Matar shige ki jiƙamshin sa ya yi daɗi ko?”

Juwairiya har ga Allah ƙamshin bai yi mata ba,kallon sa ta yi ta ɓatafuska tare da toshe hanci.” Humh ni ban ji wani ƙamshin daɗi badon ni warin almiski ya yi mini,kuma ni ba na son almiski.”

Allah ko ka ji gulma wannan turaren ko shugwaban ƙasa ya shaƙiƙamshin sa ba zai kushe ba,balle ke ni na san gulma ce irin ta ki donko wanda na ke shafawa ba ki taɓa cewa ya na daɗi ba.”

Dariya ta yi lokacin da ta toshe baki ganin haka sai ya ji haushi sosaiya biyota ya na faɗin.” Allah sai na fesa shi a jikin ki duka.”

Zagaye falon suke yi har ya kamata zai fara fesa mata turaren,yayinda take roƙonsa don har ga Allah bai yi mara ba.

Wayar sa da take aljihun wandon sa ta fara ƙara da sauri ya ciro,jinkiɗan da ya saka ma Zainab ce.

Hello gani a airport ka zo ka ɗauke ni.”

Ya kalli Juwairiya da ta ji abin da Zainab ɗin ta ce saboda ta na jikinsa ya ɗaga wayar.

Da ido ya yi mata magana sannan ya ɗauki key ɗin motar sa ya fice.

Ta na ganin sa ta faɗa jikin sa tare da sakin kuka sosai.” I miss youhoney.”

Da so ya yi ya ture ta ganin irin shigar da ta yi duk da cewar a da inta yi shiga wani lokacin ya na ƙorafi,amma yau ganin ta da gyale tayi roling ɗin sa,sai ran sa ya ɓace sosai,domin shi da za ta farashigar Juwairiya ya na so,saboda ya gane hijabi wani sirri ne daAllah ya bawa mata duba ga jikin Juwairiya da yake mamakin ƙirarsa.

Ga mamakin ta sai ta ga ya yi shiru, bai cika magana ba sai kallonhanya da yake yi,hakan bai saka ta damu ba saboda ta yi tunanin kohar yanzu fushi yake yi da ita,duk da cewa ita ya kamata ta ƙi masamagana,amma sanin hali sai ta kama bakinta ta yi shiru.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Wayarta ta ɗauko ta yi kiran Momy ta gaya mata jirgin su ya saukalafiya.

Ko da suka isa gida wanka ta shige saboda ta gaji matuƙargaske,kanta har wani sarawa yake yi saboda ciwo,in da Allah yataimake ta ta ci abinci a jirgi,so babu abin da za ta nema illa ta yisallah ta bi lafiyar gado.

Ya shigo da dubuwar farar rigar bacci wanda ya ɗaure igiyar tabayansa,ganin ta kashe fitilar ɗakin ya kunna fitila mara haske.

“Zainab ki tashi magana za mu yi kuma mai mahimmanci.”

Ya ce da ita don yau yake son ya gaya mata komai,gudun kar taganta a gidan lamari ya jagule,saboda ya tabbata gobe in ta yi idobiyu da ita,zarginta zai zama gaskiya don ta wuce a kalle ta ace mataƴar aiki.

Wash Allah na!Haba A.m na gaji fa wallahi kaina ciwo yakeyi,komai za ka gaya min ba zan fahimta ba, ka bari zuwa gobe sai kagaya mini duka fa yanzu na dawo.”

Ta ce mishi cikin ƙorafi saboda ta san bai wuce ƙorafin abin da yafaru a tsaƙanin su zai yi mata magana ba.

Miƙewa ya yi ya koma ɗakinsa ya san tun da ta ambaci sunan sa baza ta saurare shi ba,dama in dai ta kira sunan shi yayin da suke sa’insa ba,ba za ta yi abin da yake so ba.

Washegari da safe A.m tun da ya yi sallah bai dawo ba,sakamakonƙanin sa da aka kira shi bashi da lafiya ya na asibiti.

Zainab ba ta tashi ba sai kusan ƙarfe da rabi saura minti biyu,wankata yi sannan ta yi salla,saboda duk tashin da A.m ya yi mata ba tatashi ba,gajiya ce sosai a jikinta har zuwa sadda ta tashi ba ta dainajin bacci ba.

Wani irin yunwa take ji a daddafe ta yi sallah,sannan ta ziradoguwar riga ko hoda ba ta shafa ba ta fito don ta karya,ta san cewazuwa wannan lokacin Lantana ta kammala abinci.

Da ga wanka ta fito bayan ta ɗauki tsawon lokaci ta na dirje jikinta,da yake wani irin haske tamkar zara cikin wata,ita kanta mamakinhasken da ta yi take yi ta san cewa ta na da haske,amma ita ba faraba ce sai dai yanzu wani irin haske ta ƙara har kusan kashe ido takeyi.

Duk da ta ɓata lokaci gurin yin kwalliya amma fa ba wata kwalliyata yi ba,kasancewar ta ba mai irin sha’awar kwalliya irin waɗan daƴan mata suke yi,su zama tamkar aljanu.

Wata doguwar riga ta saka kalar milk amma jikinta an yi mata adoda farin duwatsu,masu kyau don yanayin rigar ya fi kama da naindiyawa.

Turaren da ta ɗauka wanda A.m yake shafawa tun da shi ta feshejikinta da shi,ta na son ƙamshin sa sosai saboda in ta shaƙi ƙamshinsa ji take kamar A.m na kusa da ita,amma wanda ya siyo samƙamshin sa bai yi mata ba,har cikin zuciyar ta ta tsani turaren, ammashi gani yake kamar watsa take masa.

Juwairiya a yadda ta tsara ma kanta hak za ta fita Zainab taganta,don ta na ji a ranta kuma ta rantse ba za taci gaba da ɓoyekanta ga a gurin ba,za ta bayyana na komai kuma duk ta shirya daabin da zai faru.

Sai dai kuma yadda ta ga surarta ya fito ba za ta iya fita a hakaba,kasancewar ta mai alkunya da yakana.

Ƙaramin hijabi ta ɗauka ta rufe jikinta da shi sannan ta ɗaukisabuwar wayar da A.m ya canza mata mai kyau da tsada,bayan yagargaɗe ta da kar ta bari kowa ya ga wayar saboda tsadar ta.

A lokacin da ta kama murfin ƙofar fita ɗakin sai abin ya matamamaki,domin ita kanta mamakin kanta take na yadda ta shiryahakan,duk da ta san dala za ta ɗauko ma kanta babu gammo.

“Sannu da shigowa Hajiya Zainab barka da dawowa Allah ya jazamanin ki a gidan A.m.”

Lantana ta ce mata kamar ta na mata gatsali kamar kirari,amma azuciyarta dariyar ƙeta take yi don ta san za‘a kwashi ƴan kallo.

“Lantana ya kai ban ga abinci a dinnig ba ke wace irin shashashace,kin san na dawio ko dama haka kike barin mijina da yunwa?”

Allah ya huci zuciyarki Hajiya!Amma ba ni nake girki a gidan nanba tun da kika tafiTa ce cikin sauri saboda ita ta ƙosa ayi ta ta ƙare.

Ban gane ba shi yake yi ko fita yake ya siyo bayan son na ki.”Tatambaye ta da mamaki duk da ta san A.m ya tsani abincinta kamaryadda yake mata ƙorafi.

Ba a waje yake siyo ba Juwairiya ce take girkawa,amma yau bansan mai ya hana ta fitowa ta girka ba.”Tsabar gulma da yake cintahar saurin baki da take yi ta faɗa in ina ta fara.

                    Juwairiya?”

Ta faɗa cikin zare ido don ita ko kaɗan ba ta tunanin ta na gidan ba.

Wayyo Allah na! Uban me yar iskan yarinyar nan take min a gida?Da ma ta na gidan nan ba ta bar gidan ba.”

Lantana ta matsa daga gefe tare da kare wuyanta ganin ta nufe ta,aranta addu’a take yi.

Buɗe kofar kicin ɗin ta yi ba tare da ta nuna ko ɗar a ranta ba,duk data ji hargoguwar Zainab sai dai hakan bai razanata ba.

Lokaci guda Zainab ta yi shiru lokacin da ta yi ido biyu da ita.

Gabanta ne ya yanke ya faɗi dam!Ganin ta canza mata kamar ba itaba.

Wani irn tashin hankali ya ziyarce ta ba tare da wani tunani ba,shaƙeta ta yi tare da sakin wani irin kuka.

“Ke dan ubanki mai kike yi a gidana?”

Juwairiya ta fisge gabar rigarta da ta riƙe ba tare da ta ce matakomai ba, ta nufi gurin gas za ta ɗora abinci,da ba tare da ta ji tsoronta ba.

Lantana kuwa tsalle ta yi gefe jikinta har rawa yake ganin yaddahankalin Zainab ya tashi,duk ta ƙosa a fara ta ga yadda za‘a ƙare, azuciyarta ta so ace munafukin ya na nan,sai ta ga ƙarya da nuna isaya na faɗa mata matarsa ce.

Shaƙeta ta yi sosai kamar za ta kaita lahira ta na faɗin.” Wallahi yausai kin raina wayon ki saina nuna miki kuskuren shiga gonata dakika yi,duk cin mutuncin da kika yi mini ashe ki na nan a gidankuna cin amanata bari ya dawo haɗaku zan yi na ƙona.”

A.m dake tafe a mota da sauri har baya ganin gaban sa ya so ace yana gida uwar haka,sai dai ciwon ya tashi sosai don aiki a ka shiga dashi afendis ke damun sa.

Ya na tuƙi amma hannun shi rawa yake yi saboda ya san a wannanlokacin,Zainab ta farka kuma komai zai iya faruwa.

Ko da ya iso gida bai yi parking ba ya ije motar tare da rugawa zuwacikin gidan.

Zargin sa ya tabbata daidai saboda tun kafin ya shigo cikinfalon,yake jin ƙarar Zainab da hargowa.

Zainab ki bar abin da kike yi ki tsaya zan yi miki bayani.”Ya ce daita don yau ta faru ta ƙare.

Wani irin banzan kallo ta yi mishi tare da sakin ƙara.” Uban me takemini a gida kalle ta fa A.m sam ba ta yi kama da mai aiki ba,duktunani na tabar gidan na...”

“Wannan dalilin ya sa nake ta son ki ba ni dama na yi miki bayaniYa katseta ya na faɗin haka.

Bayanin me za ka yi mini buƙata ta kawai ta bar gidan nan.”

Janye rigarta ta yi da ƙarfi ta ture Zainab daga jikinta cikin tsawa.

Ya ishe ku gabaki ɗayan ku na gaji kuma kar ki ƙara riƙe ni ki natuhuma ta,saboda matsa…”

Wani irin saukar mari ta ji ƙuncinta mai zafi wanda ya saka ta ji jiriya kwashe ta,ta yi taga-taga za ta faɗi amma ta riƙe drower na kicinɗin.

Ki iya bakinki kuma ki tsaya  a matsayin ki.”A.m ya faɗa bayan yakwasa mata mari.

Ka ƙyale ta ta faɗi abin da za ta faɗa yau sai na wulaƙantarayuwarki.”

Juwairiya da ta ji saukar marin har ƙwaƙwalwarta ta rintse idanuntacikin kuka sosai,don yau ta tabbatar A.m ba ya sonta! Munafiki nemayaudari ne kawai ya na more jikinta ne da mugayan kalamansa dayake yaudarar ta.

Ta buɗe baki za ta yi magana sai ƙamshin turaren A.m da ya canzaya daki hancinta,wani irin amai ya taso mata duk yadda ta so ta maida shi ina ta makara!

Da sauri ta ruga zuwa bayi amma tun kafin ta kai ta fara amaitamkar za ta amayar da ƴan hanjinta.

Sai Zainab ta din ga kallon A.m da ya tsaya tamkar gunki ta buɗebaki za ta yi magana,ta kasa sai ta ji kamar babu harshen ta  a cikinbakinta,yayin da kanta ya ɗaure iya ɗaurewa kuma ya yi matanauyi,jin kanta take ya yi nauyi, tamkar an yi mata gammo an ɗauramata duniya da abin da ke cikinta.

Matsawa ta yi gurin A.m sai kuma kamar an tsikare ta,ta ruga dagudu cikin ɗakin Juwairiya da take ta sheƙa amai tamkar ba za ta yirai ba.

Allah sarki tsayawa ta yi ta kasa komai kamar jira take ta gama tafito ta yi mata sannun a yadda ta nuna,amma iya tashin hankali datake ciki ya sa ta yi mutuwar tsaye,har ta kasa banbance wacerayuwa take ciki tsaƙanin ta duniya da lahira.

A.m da ya ƙaraso da sauri don bai fahimci wainar da ake toya waba,ya yi tunanin ko Zainab ta biyo ta ne da dake ta.

Abin tausayi amai take yi tamkar ba za ta daina ba,kuma A.m ya yimamaki har ta gama amai ta fito bayan ta wanke bakinta,Zainab bata tanka ba,sakamakon suman tsaye da ta yi.

Wani irin ajiyar zuciya ta saki tare da firgita kamar wacce ta dawodaga doguwar suma.

Duk da cewa ita ba likitar mata ba ce,amma a iya zaman ta cikinasibiti ta san yadda ake gane mace mai ciki.

Hannu Juwairiya ta kama tare da duba tsakiyar hannun,sannan taɗaga ƙwayar idanunta.

Gabanta ya buga da sauri sabo da fahimci abin da Zainab takedubawa,lokacin da ta je asibiti ita da Hauwa abin da likitan ya dubakenan ya ce mata ta na da ciki.

Sam ba ta yi tunanin ciki ne da ita ba saboda wancan ba ta yi amaiba sai kwaɗayi.

Na shiga uku ya Allah karka saka mafarkin da nake yi ya zamagaskiya!Ka sa na buɗe idanuna tun kafin na aikata abin da duniya zata yi tur da ni a cikin mafarkin.

Juwairiya take da ciki wa ya yi mata?”

Ta faɗa cikin ƙaraji tamkar wata zararriya ta na ihu gabaki ɗayakamanninta ya canza

Juwairiya da A.m har ma da Lantana da ta yi laɓe a bakin ƙofa ta najin mai ke faruwa!Suka haɗa baki gurin faɗin

                    Cikiiii.”

Sai kawai na ga Lantana ta hantsila ta yi waje cikin tashin hankali,batare da na yi wani tunani ba na bita a guje,saboda ba zan iya ganinwannan badaƙalar ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]