[Advertisements⬇️]

SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 28 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Zainab dake shatatan hawaye ta karɓi acid ɗin da ta miƙa mata,tana jin wani irin tsanar Juwairiya  a ranta kamar ta je ta watsa mata da kanta.
Ganin Momy suka yi ta shigo tana murmushi a fuskarata ta zauna a gefen su.
” Humh ta yaro kyau take yi ba ta ƙarko.”
Ta ce tare da dafa kafaɗar Zainab da har yanzu take ɗigar hawaye,saboda gani take kamar a mafarki yake faruwa,ba ta taɓa tunanin fuskantar haka da ga gare shi ba.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saka tare da rungume Momy sai ta ƙara fashewa da kuka.
” Momy har yau na kasa yadda cewa A.m zai iya kula wata mace bayan ni,mace mara aji wanda ba ta da daraja a duniya duk cewar  zargi nake yi amma in na tuna,sai na ji kamar na shaƙe kaina na mutu.”
Cikin kuka ta faɗa da shagwaba gaba ki ɗaya ta haye jikin Momy tana shagwaba,sannan ta ɗora da cewa.
” Ke sheda ce irin wahalar da na sha kafin ya amince da soyayyata! Yanzu sai wata aba wacce ban ɗauke ta da ƙima ba ta shiga tsakanimu.Abin da ya yi min na ji na haƙura da shi amma fa babu macen da za ta raɓe shi,face na zama ajalin ta.”
“Na sani ba sai kin ɓata bakinki ba amm ni bana goyon baya akan acid ɗin da zaku watsa mata,saboda in har da gaske yake son ta zai iya yin komai don ta samu lafiya daga ƙarshe kin ga ke kika rasa,amma da za ki bar komai a hannuna da sannu za ta gane kuskuren shigowa rayuwarki da ta yi sa…”
” Momy yanzu kina nufin na fasa watsa mata acid ɗin?”
Ta katse ta da tambaya tana magana da muryar kuka.
” Abin da nake so kenan in har zai yiwu kar ki manta ke ce ƴata ɗaya tilo da na mallaka, ta ya ya za ai na bar rayuwarki ta ƙuntata ki bar min komai a hannuna,mijinki kuwa sai ya gane bashi da hankali don wahalar da shi za muyi ki ƙyale shi,zai gane ba irin ki ake wulaƙanta wa ba.”
” Ai ni da  nace ba zan kona gidan sa ba kawai ya sakeni na haƙura da shi.”Ta ce cikin shagwaba tare da riƙe hannunta.
” Ba ki da hankali mijinki za ki bar ma wata banza ƴar aiki? Ashe kishinki na banza ne tun da har za ki hau dokin zuciya ki kyale ma wata mijinki.”
” Wannan karon Nabila ce ta karɓe maganar da cewa.” Momy ya kamata ta fahimci waye mijinta sannan kin san Zainab da baƙin kishi,ni har yanzu na kasa gane gaskiyar lamarin dake faruwa,amma ya kamata ta gwara A.m ta nisan ta kanta da shi har sai ya gane kuransa.
Zainab cikin zumɓura baki ta ce.” Ki bar shi da ni yake yi ba Anty Safna za ta tafi ingila ita da mijinta ba,bin ta zan yi na huta acan  ba zan dawo ba sai na huta.”
Nabila da mamaki ta kalle ta ta ce.” Ki bar shi da ƴar aikin na ki Zey?”
” A”a na san cewa tun ranar da abin ya faru zai kore ta, so nake na gwara shi kin san yana masifar sona dole hankalin sa ya tashi.”
Dariya ta yi ta ce.” Haka ne ai bai kyauta ba amma yanzu Momy zuwana bai da amfani an fasa watsa mata acid ɗin?”
” Ƙwarai kuwa Nabila ku bar min komai a hannuna ita Zainab ta fita waje ta huta kafin muga abin da zai faru.”
Haka kuwa aka yi washegari Nabila ta koma Abuja.
A ranar da su A.m suka yi nasara Zainab ta fito musu sun ga rashin mutunci,don tun A k na saka baki yana ba ta haƙuri ta dawo,har ya gaji ya koma gefe yana kallon A.m da ya yi kalar tausayi,kamar zai yi kuka yana roƙonta.
Cikin muryar sanyi ya ce.” Ki fahimce ni tun lokacin da muka je ƙasar waje aka yi miki aiki,na tambayi likita ya ba ni wannan maganin tunanina ko za ki iya haihuwa.”
Kallon mayaudari ta yi masa ba tare da ta tanka masa ba,domin gani take ya ci uwar rainin wayo.
” Allah ki yadda da ni don Allah ki dawo ɗakina zuciya da gangar jiki sun yi kewarki.”
Ya faɗa a raunane kamar zai yi kuka tare da kama hannunta.
Fisge hannunta ta yi ta harare shi tare da yatsina fuska.” Ai ka gama tsarani wallahi gara ma ka fita harkata,domin zuwa gobe in sha Allahu na bar ƙasar nan ba zan dawo ba saina huta iya son raina.”Ta ce da shi tana kallon sa a yatsine
Wannan karon murya a ɗage ya fara magana.” Kar ki sake ki fita wata ƙasa don ba da izinina ba,kuma in kika sake kika je Allah saina ɓata miki rai”
” Ai kin banza kawai a suwa ai ni yanzu duk abin da ka zaɓa a aurenmu daidai ne in ba rabuwa za mu yi na fi son haka,da na zauna da fasiƙi wanda ba shi da aji ya rasa macen da zai kula sai ƴar aiki..”
” Ya ishe ki Zainab sau nawa zan gaya miki babu wani abu da ya shiga tsaƙaninmu da ita kin ƙi bani dama na yi miki bayani,ban taɓa kallonta da nufin wani abu ba don ni ban ga abin da zan nema ajikinta ba,kar ki manta yawo take a cikin hijabi kamar wata ƙonanniya.Yarinyar da ba ta da waye wa mai zan yi da ita….”
Zainab tsaki ta yi ta wuce kawai gani zai tsarata ya bita kamar zai shige cikin ɗakin ya na faɗin.” Na gaya miki kar ki bar ƙasar nan ba tare da izinina ba.”
Garam ta kulle ƙofar saura kaɗan ta haɗa da hannun shi da ya kai da nufin ya kamo ta ganin za ta shige.
Bango ya kaima duka tare da kama kan sa ya riƙe.
A.k da ke zaune  hankalin sa na kan waya amma a zahirin gaskiya yana jin badaƙalar da suke yi ne,mamakin aminin na sa yake yi saboda ya saki da yawa Zainab ta raina shi sama ba ta ganin darajar shi balle ta girmama auren su.
Ganin ya nufi hanyar fita ya miƙe cikin ƙosawa shi kansa ya gaji da zuwa biko,yana ji a ran sa ba zai ƙara rako shi ba don ya gaji da ruwan rashin mutuncin da yake kwankwaɗa daga gurin Zainab da iyayenta.
A mota suna tafiya shiru A.m ya yi ƙuta ya kalli A.k da hankalin sa ya na kan tuƙi ya ce.” Ka na jin wannan yar rainin wayon ko,wai wata ƙasa za ta!Zainab ta raina ni matuƙa ban san yadda zan yi da ita ba,amma in dai ta yi gigin fita waje Allah sai na hukuntata.”
Shiru A.k ya yi ba tare da ya tanka mishi ba yana tuƙin sa a ran sa cewa ya yi.” Kamar da gaske zai iya.”
Ƙaramin tsaki ya yi ganin haka sai A.m ya kama bakin sa ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba,don maganar da yake masa kame-kame ne lamarin Zainab yana ba shi haushi sosai.
” Har yanzu ban ji kayi maganar Juwairiya ba.”A.k ya faɗa ba tare da ya kalle shi ba.
” Shiru ya yi ba tare da ya tanka ba duk da ya ɗan daina jin zafin ta amma har yanzu yana jin haushin asarar da ta yi mishi.
” Ka rabu da ni da wannan  shiriritacciyar ina maganar matar so wake ta matar shige,sai ka bari na gama da wanda zuciyata take muradi ba wata can ba.”
Tuki A.k ya ci gaba da yi ba tare da ya tanka a bin da ya ce  ba a ran sa shika ɗai ya san me yake tunani.
Juwairiya riƙe da waya a hannunta suna kokuwa da Hauwa da ta rantse ba za ta kira shi ba.
” Hauwa ki taimake ni don Allah kada ki sa zuciyata ta fashe! Na san har yanzu A.m yana fushi da ni ne haƙurin zan ba shi.”
Wani mugun kallo ta sakin mata ta ce.” Wai ke ba ki da aji ne? Shi ya sa ya raina ki ya ke wulaƙantaki,Allah ya halicci mace da daraja mai girma a gurin ɗa namiji in kika ba shi lokaci da kan sa zai kira ki,don haka ba zan ba da wayata ba.”
” Wayata tana gidan sa babu ta in da zai kira shi kuma na san cewa ba zai taɓa kirana ba,ko sau ɗaya ki bani na kira shi don Allah.”
Ta faɗa tare da marairaice fuska hawaye a kan ƙuncinta.
” Bari na tura masa da tsaƙon haƙuri daga gareki in har yana buƙatar ya kira ki zai neme ki,amma ba zan bari ki kira shi ba nuna son da kike masa ya yi yawa shi yasa yake gasa miki gyaɗa a hannu.
Sai ta koma ta zauna ta zabga tagumi da kalar tausayi har hanzu hawaye na turereniya a fuskarata.
Yanayin da ta yi sai ya ba Hauwa dariya da takaici.
Wayar ta ɗauka ganin taƙi cin abincin da ta ije musu ta faɗa kogon tunani.
Tsaƙon haƙuri ta tura masa da basu wuce kalmomi biyar ba ta ije wayar.
A.m dake kwance  a kan makeken gadon sa da yake jin faɗin sa ya kai faɗin duniya.Filo ya jawo ya rungume da tare da jan tsaki.
Tsananin ɓacin rai yake ɗauke da shi saboda ya ya je gidan su Zainab ta bar ƙasar.
Da ƙyar ya iya dawowa gida ya kwanta yana jin wani irin zafi a ran sa.Tun ranar da tsaƙon ban haƙuri ya shigo daga Juwairiya wanda yau kwana biyar da shigowa, bai ko karanta da kyau ba balle ya tura reply  wani irin haushinta yake ji da yanzu ya fara irga ranakun da zai zama Daddy.
Wayar sa ta yi ringing har sau uku sai a na huɗun ya ɗauka a kasalance ba tare da ya tanka ba.
”  Ban yi tunanin za ka amsa kirana ba balle ka ɗauka.”Muryar Baba Sani ta daki kunnin sa.
Da hargowa ya ja tsaki da takaicin ƙin duba wayar da bai yi ba  ya ɗauka,wanda hakan ya kasance ne saboda baya son ya kalli wayar lokacin da kiran ya shigo.
” Ban san kai ba ne da babu abin da zai saka na amsa wayar,mara mutunci mai ya sa ka kira wayata?”
” Na kan yi mamaki in ka yi min wannan tambayar Juwairiya da take gidan ka irin mangwaro ce ka samo ka shuka ta fito,da kake tambaya ta dalilin kiran ka.”
Shiru A m ya yi masa a yanayin da yake baya buƙatar tashin hankalin Baba Sani don yana shakkun shi sosai.
” Na so na zo da kaina amma dana tuna baka da mutunci,kuma ka yi min gargaɗi sai na dana tsufana,gudun kar na mutu da ƙafa ɗaya sanin baka da mutunci,kuma sam baka girmama na gaba da kai.
“Fine gara da ka yi ma kanka ƙiyamullaini ƙaƙi zuwa  in da nake da sai ka raina kan ka wallahi.”A.m ya ce ran shi a ɓace.
” Ƴar ɗan’uwana na biyo naji ba’asi A k ya zo nemanta jiya.”Gabansa ne ya faɗi ya yi shiru bai tanka ba,amma tsoro fal a zuciyar sa ya manta Mama ba ta gari,kwata-kwata bai yi tunanin in da za ta je ba,saboda haushin da ta ba shi ko tunanin halin da take ciki bai yi ba.
” Na ji ka yi shiru ne ko ka ɓatar mini da ita ka san fa ita ɗin dukiya ta ce,so ka kiyaye don wallahi zan iya shuka rashin mutuncin da baka taɓa tunanin in da shi ba.”
” Har  a kwai wani rashin mutuncin da za ka yi min da zai firgita ni bayan san baka da mutunci gabaki ɗaya rayuwarka,a tsiya za ka ƙare don baka gaji arzikiba garyar matsiyata.”
Dariya Baba Sani ya saki jin abin da ya faɗa sai ya ba shi amsa da.
” Ashe masu arziki zasu zama matsiyata don in ka yi gigin ɓatar da ita saina zaman maka ƙadangaren baƙin tulu,don haka ka kula ba ni da mutunci kai ma sheda ne.”
A.m da ran shi ya ƙara ɓaci matuka kaɗa kan sa ya yi  sannan ya ba shi amsa” Kama ta ya yi na zo na kamaka in ji dalilin da ya sa take zubar min da ciki,don na san wataƙila kai kake saka ta kuma wallahi in har na gane da saka hannun ka sai na saka kaf zuriyarku an ɗaure ku.”Ya ce da shi ciin ɗaga murya .
” To shikenan ɗan Ƙaruna ina jiran ka amma ƙila ni zan fara ɗaure ka,matuƙar ka salwantar min da ƴar ɗan’uwa kuma jarina,wai yaushe kuɗin da ka ba ni zai gama aiki?”Ya canza maganar da sigar tambaya.
Da takaici ya kama shi jifa fa wayar ya yi ba tare da ya kashe ba,yana jin dariyar Baba Sani can kuma ya kashe wayar.
” Ina ga Juwairiya da tsinannen Babanta Sani su za su yi ajalina.”
Ko me ya tuna da sauri ya ɗauko wayar da ya yi jifa da ita.
Numbar da ta turo masa da tsaƙon haƙuri ya fara bincika duk da bai wani karanta tsaƙon sosai ba.
Wayar na ringing tana ƙara tayar masa da zafin dake cikin zuciyar sa.
Sau uku ya kira amma ba’a ɗaga ba har ya yanke shawarar ba zai ƙara kira ba,sai kuma ya ji muryar wata mace ta yi sallama.
” Ina Juwairiya take.”
Ya faɗa a gundure da takaicin kiran  da ya yi.” Ban sani ba kuma in ga wrong number ka yi saboda ban san mai wannan sunnan ba “
Ta faɗa da ɗan daga murya dama abin da ta yi ninyar ta yi masa kenan,saboda yanzu matuƙar haushi yake ba ta yana can yana wahalar da kan shi,ga in da ake masa son mutuwa.
” Ko da ban san ke wace ce ba kar ki raina min wayo kin san dai abin da ke tsakaninmu ,ba kiran ta na yi don ina so ba,a’a saboda ta ɓata mini kuma sai na nuna mata kuren ta.”Ya ce da Hauwa ran sa a ɓace.
” Ok kai da ka santa kake wannan maganar amma na yi maka bayanin ban san ta ba balle na sa abin da ya haɗa ku.”
Hauwa haushi yake ba ta ji take kamar ta kama shi ta yi masa shegen duka saboda irin mutanen nan masu gatsali.
Ta buɗe baki za ta yi magana ji ta yi an fisge wayar Juwairiya ce daga bayan ta wacce ta shiga bayi a she ba ta san ta fito ba.
Jikinta har rawa yake lokacin da ta kanga wayar a kunninta tare da fashewa da kuka.
” Hello don Allah ka yi haƙuri ka yafe min wallahi ba zan ƙara ba zuciyata za ta fashe na rashin ka a kusa da ita k…”Wata uwar tsawa ya daka mata.
” Ban kira ki don ki gaya min tsoki buruku ba kin ji na rantse kar ki bari mu haɗe dake don sai kin raina kanki.Gidan uban wa kike Baba Sani ya kira ni ya ce min ba ki a gidan sa?Da auren kike gantali ni dama na san ƴan iskan ƙawaye kika yi da su suke zuga ki,to makarantar ma na daƙile tun da baki san mutunci ba kuma na rantse miki za ki fuskanci fushina mai tsanani.”
” Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min na yi kuskure ba zan ƙara ba.”
Hauwa ce ta fara kiciniyar fisge wayar da ta yi mata kyakykyawar riƙo.
“Dole A.m ya din ga wulaƙanta ki haba kamar ba mace ba duk kin zubar da ajin ki ya raina ki an faɗa  miki so hauka ne haka ake nuna ma masoyi ?”
Duk yadda ta so ta karɓe wayar ta ƙi bata,har duƙawa ta yi tana ba shi haƙuri yayin da idanunta ke zubar da hawaye.
” Gidan ƙawata Hauwa Tukur.”
Ta bashi amsa har tana in ina garin saurin ta faɗa masa.” Minti goma na baki ki dawo gida in ba haka ba za ki fuskanci hushina.”
A wannan lokacin Hauwa ta ƙarɓe wayar.”A.m duk abin da kake yi Allah yana kallon ka,don Allah ya jarabce ka da ƙaunarka sai ka din ga wahalar da ita?Ina jiye maka ranar da Allah zai kama ka a kanta….”
” Ke karki kawo min maganar banza matata ce fa kin san irin maƙudan kuɗin da na saka na aure ta?In har na gane ke kike zugata saina ɗaure ki igiya tai rara.Maza ta dawo cikin mitinan da na bata.”
” Juwairiya ba za ta dawo ba saboda ba ta da lafiya sosai in har ka matsu da ta dawo to ka zo ka ɗauke ta.”
Ɗif ta kashe wayar cikin ɓacin rai saboda tunanin da take mishi ya wuce wannan.
” Haba Hauwa kina gani har sallar dare nake yi don ya kira ni shine za ki ce ba zan koma ba,kin san wannan batsa kika yi don tafiya zan yi.”Ta ce cikin murna.
“Ki ce dabbe za’a yi a gidan nan na ga wanda zai kada wani ko da ganina kin san ba za ki ibi komai a jikina.Wallahi mugun haushin sa nake ji ya faye son kan da da yawa na, yi baƙin cikin ɗauke Mama da ya yi ita ce kawai za ta iya ƙwatar miki ƴancin ki,don ke baki maida kanki mace ba shi yasa yake gara ki ya na amfani da son da kike masa.
A.m da yake jin haushin kiran da ya yi mata yana ta zagaye kamar mai ɗawafi.
Ya fi kusan minti talatin yana jiran ta dawo ko ba komai ya rage damuwar abinci da kullum yake fama da yunwa,don ko gidan su ya je babu wanda yake masa tayin abinci,ya san ana yin hakan ne don a hora shi.
Wayarsa ya ɗauka yana tsaki ya tura tsaƙo kamar haka.
” Turo min da adireshin gidan.”
A lokacin da tsaƙon ya shigo Hauwa na tsaye ta riƙe Juwairiya ƙam da take son ta fice daga gidan.
” Ina tausaya miki Juwairiya  ko wani namijin kika aura ba A.m ba za ki sha wahala sosai,na lura baki iya ɓoye so ba in dai kina son mutum su maza ba’a musu haka yayin da suka fahimci mace ma son su  wulaƙanci yake biyo wa baya.”
Hawaye ta share ta kalle ta ta ce.” Wataƙila ba ki taɓa soyayya ba ne shi ya sa kike daɗin haka amma son da nake ma A.m irin na in ban same shi ba sai rijiya.”
” Ina na taɓa so ai kin san auren ƙiyayya na yi da mijina.Ta yi mata gatse sannan ta ɗora da cewa “Ai ko kina ruwa wallahi don ina tausaya miki.”
Kama hannun Hauwa ta yi ta riƙe sai hawaye shar!”Ki bar ni don Allah na tafi.”
Kallon ta ta yi tana dariya ta ƙara cewa.” To mara aji matar mahaukaci, ya ce na tura masa da adireshin gidan, sai ki kwantar da hankali don na fiki murnar tafiyar ki ko banza yau zan yi bacci lafiya, ba tare da na yi rarrashin kukan da ake min duk dare ba.In kun so sai ku kashe kanku munafukai kawai.”Wani irin daɗi ya lulluɓe jin zai zo duk da tana tsoron haɗuwar su amma idanuwanta suna ƙaiƙayin son ganin sa.Yana isowa hon ya shiga yi ba ƙaƙƙautawa.
Da gudu ta ruga har tana bige ƙafa da ƙofa amma bata kula ba,ko sallama ba ta yi mata ba sai hannun da ta ɗaga mata.
Duk da bugun da zuciyarta take mata amma gaka nan ta yi shahada ta shiga suka zuba ma junan su ido.
A.m da yazo da fushi duk sai ya nemi fushin ya rasa musamman da ya ga ta rame kamar wacce ta yi ciwon shekara.
Kau da kan sa ya yi ga barin kallon ta ya ɗauki biro ya saka a tsakanin yan yatsun ta ya matse da ƙarfi har sai da ta yi ƴar ƙara saboda zaba.
” Kin san irin girman laifin da kima yi mini?Kin ɓata mini rai ƙwarai kuma saina miki horo mai tsanani,na rantse kika ƙara gigin ƙara zubar min da ciki saina illata ki sannan jikina ba zai yi wahala ba sai kin mayar da abinnda kika zubar.
Ƙaryar iskanci kike ba ki san waye ni ba muje gidan za ki ga abin da zai faru dake.”
Tsananin tsoro ya cika mata zuciya ganin irin muguntar da ya yi masa,sai ta ji tsoron kar yazo ba kowa a gidan ya kashe ta a banza,saboda har yau tana tuna irin shaƙar da ya yi mata.
Ganin fuskar sa babu fara’a hankalinta ya ƙara tashi.
” Ka yi haƙuri na gane kuskure na insha Allahu ba zan ƙara ba kuma na yi hakan ne…”
” Ban tambaye ki dogon surutu ba in har kina son na yi haƙuri to ki ƙoƙarta ki mayar da abin da kika yi mini asarar shi a yau.”
Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tuƙin da yake yi.
Yanayin yadda ya ya nuna mata hankalinta ya ɗan kwanta,domin ta yi tunanin fuskantar haka daga gare sa,ta ɗauka dukan mutuwa zai yi mata kuma ya kore ta.
Tun da ya faɗi wannan maganar bai ƙara cewa uffan fa har suka iso gida lokacin a na kiran sallar isha’i,don haka parking kawai ya yi ya fice masallaci.
Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi tana ƙare ma gidan kallo wanda rabon ta da wata biyu kenan
Da ta tuna Zainab sai da gabanta ya faɗi ras! Duk da ta san ba ta gidan shi ya sa ya je ya ɗauko ta,a ranta take tunanin ko ta yi tafiya zuwa waje.
Bayan ya shigo tana zaune a falon gidan sai ƙare wa falon kallo take saboda ganin ya canza,kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kan sa zai haye sama.
Da sauri ta riƙe hannun shi.” Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min wallahi na tuba kuma na yi nadama.”
Hararar ta ya yi tare da galla mata tsaki ya janye hannun sa sai kawai ta faɗa jikinsa tana kuka sosai.
” Ke fa matsala ce ta ko ina bayan asarar da kika yi min kukan banza za ki rarrashe ni da shi ko?Kawai zan haƙura ne in har kin yi alƙawarin yau za ki mayar min da asarar da kika yi min.”Ya faɗa cikin wata irin murya.
Ɗago kanta ta yi tana share hawaye ta kalle shi sai kuma kunyar abin da ya faɗi ya sa ta sunne kanta tana murmushi.
” Yunwa nake ji ƙwarai kin korar min matar so,sai ki maye makwafin ta kafin ta gama hutun ta dawo,sai ki yi ƙoƙarin mai da asarar da kika yi mini don ba zan wahalar da kaina ba.
Da sauri ta tashi ta ƙwalalo masa ido tana dariya sai kuma ta nufi kicin,wanda dama kafin ta yi alwala sai da ta ɗora masa abu mai sauƙi wanda zai ci,don ita yau murna ba zai barta ta ci komai ba.
Mamaki ta yi da ta ga ya biyota kicin ɗin duk da ƙorafin abin da ta yi masa yake yi,da kuma yi mata gargaɗin kar ta ƙara sai ta ji sanyi sosai a ranta ,saboda yana da saurin fushi zai kuma iya yanke komai ba tare da tunani ba,amma kuma yana da saurin sauka.
Ba ƙaramin mamaki ta yi ba da ya nuna mata shifa da gaske ita za ta mai da asarar da ta yi masa
Hakan ya sa ta dage sosai don ta faranta masa saboda ya manta komai.Daga ƙarshe da kan sa ya karɓi jagoranci komai,saboda bai san ya yi missing ɗinta alot haka,a haka bacci ya yi ya kasheta da ƙaunar sa da take sakata hauka  a kan sa,sai ya fake da duk a cikin horo yake mata wanda so yake ya maida asarar da ta yi masa.
Sai da suka makara sallar asuba ita ce ta farka ta zare jikinta sannan ta tashe ki,kan dole a gida ya yi sallah,ya kuma sawa suka koma bacci.
Ba su tashi ba sai misalin sha biyu na rana kiran wayar da A.k yake yi ya tashe shi.
Tsaki ya saki zai kashe wayar sai dai da sauri ya miƙe ganin kira rututu a wayarsa,da ya kalli agogo salati ya fara yana ɗan buga bayanta ganin sha biyu har ta gota.
Miƙe wa ta yi ita dama tuni ta farka ba ta so ta farkar da shi ne,ya sa ta ci gaba da kwanciya amma yunwa take ji matuƙa.
” Hello hala yau mutuwa ka yi ne ana ta kiran waya ka san muna da baƙi sai ka zo ka buɗe mini falon ka ina waje baƙi na ta jira.
Da sauri A.m ya sauka ƙasa shaf ya manta da client din sa da za su zo yau yana faɗin.” Ki sauko ki bani abinci mai sauƙi fita zan yi.”
A.k ya dogare a bakin ƙofa yana kallon sa ganin sa da kayan bacci.” Wai hala rashin matan na ka ya sa ka fara shaye-shaye ne? Haba bacci har sha biyu da ƴan mintina sai ka ce wanda ya yi sabon aure.
Shafa kansa ya yi ya ce.” Kai fa banza ne bari na watsa ruwa mu tafi.”
Yana ƙoƙarin hawa Juwairiya ta fito da nufin ta shiga kicin ta ɗora girki kanta a sunkuye ta gaishe da A.k da ya yi tsaye yana kallon Am da yake shafa kansa.
” Kai amma ka ci uwar ɗan rainin wayo ka bar ni ina can ina ta neman ta,Baba Sani ya tasa ni a gaba ashe kana nan ka na cin amarci har da makara.”
Tsaki ya yi ya harare shi daidai lokacin da ta shige kicin ya sausauta murya ya ce.”Nima ganinta na yi ta dawo.”
Ya na taɓe baki ya yi maganar ya ɗauki remote ya kunna tv bari na yi sauri na watsa ruwa ka rage zama.
” Allah ya yi munafuki anan ka yi sauri ka fito kai ka sani da gulmarka.”
Dariya ya yi ya bugi bayansa.” Da babu ai gara ba daɗi.”Ya ce tare da haye wa sama.
Kusan sati biyu tun da Zainab ta tafi Lantana ba ta zoba,sakamakon yarta da take aure ta haihu an yi mata aiki ta tafi jinya.Hakan ya ba su damar sakewa suna jutawar su.
Kullum ranar duniya sai A.m ya kira Zainab amma ba za ta ɗaga ba, kuma yana ta biko gurin iyayenta,sai wulaƙanci suke masa daga ƙarshe mahaifinta da kan sa ya kira Daddy A.m a kan ya daina zuwa gidan shi Zainab sai ta huta za ta dawo.Da zarar ta dawo za ta dawo ɗakinta don haka ya daina damunsa.
A.m ya yi fushi sosai sai ya yi zuciya ya ƙyaleta musamman da ga matar wucin gadi,ta dage tana faranta masa ko ba komai zai yi maleji kafin ta dawo.
Juwairiya ta yi amfani da wannan damar ta saka rayuwarta a cikin ta A.m duk da irin gwasaleta da yake yi, yana yabon Zainab amma da ya fita zai kira ta yana gaya mata ya yi missing hawayenta na banza don Allah ta yi mishi kukan zai siya.
In ya faɗi haka dariya take mishi ta ce ashe kukan banza ya ƙara matsayi tun da har siye ake son ayi.Haka dai suke zaman su cikin girmama juna da kulawa.
Washegari Zainab ta kira lantana aka ta je ta gyara mata gidan ta,saboda tun da ta tafi kewar sa ya dame ta ko bacci kasa yi take yi,duk kiran da yake mata rungume wayar take yi tana kuka,amma shegen girman kai ya hana ta ɗaukar wayar in ta tuna kuma da abin da ya yi mata sai ta ji duniyar ya yi mata zafi.Ita tunanin ta A.m zai biyo ta ƙasar ne.
Sai dai tana tunanin yadda za ta iya danne zuciyarta,ta zauna da Juwairiya bayan ta gane amanarta suke ci,duk da A.m ya yi mata rantsuwar yana shan magani ne saboda ita, amma kuma bai ƙaryata numbarsa a wayar Juwairiya ba,sai dai ya nuna sam bai san zancen ba wataƙila son sa take don kwanaki ana kiran sa da baƙuwar numba,bai dai taɓa ɗagawa ba ne shi yasa bai fahimci komai ba.
Zainab ta gane sam ba za ta iya rayuwa babu shi ba,amma dole ta canza zaman su domin sai ya gane kuran sa,ita kuwa Juwairiya Momi ta ce ta bar lamarinta a hannunta don sai ta yaba wa aya zaƙinta.
Lantana ta shigo gidan da mamakin ƙofar a buɗe duk da ta ga motar A.m a gidan,amma ta san ba’ abarin ƙofar falon a buɗe.
Tura ƙofar ta yi ta shigo tana ƙarema gidan kallo yadda yake tashi da ƙamshi da gyara komai tsaf,jikinta ya bata a kwai mace a gidan.
Tsaye ta yi tana ɗan tunani sai kawai taga Juwairiya ta rugo da gudu daga sama tana dariya,jikinta daga ita sai yar bes fara da wando fari tirikwata wa da A.m ya siyo mata da suka fita,saboda shi yana koyi da hadisin ma’aiki wanda yake mana  koyi da saka fararen kaya.
Da gudu take saukowa tana dariya shi kuma ya biyo ta cakulkuli yake mata wai kan dole sai ta yi mishi kuka yaga hawayen banza.
Kamar yadda Lantana ta yi tsuman tsaye tana kallon su haka suma suka zuba mata ido cikin firgici.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]