[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 66 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

wata murya ta bata sani ba taji ana mgn

“Auwal kai fa shege ne wai da gaske kake y’ar gidan Adam ched’e ce ? nasan ka mak’aryaci ne idan kuwa yarinyar y’ar shi ce gsky kayi babban kamu ka kamo mana k’aton kifin daxamu dink’a cin kitse”

“zauna nan d’an iska wallahi nayi mmkin yarinyar nan data soni bata son ni d’in shege bane aureta xanyi kaga nima nan gaba afara kirana Auwal ched’e hahahh”

“tasan kuwa kana da mata?”

“mahaukaci ne ni xan fad’a mata ina da mata ? naiwa kaina  asara bata son komai akaina ba kuma baxata sani ba ni dai nasan har ga Allah banda arxik’in gidansu wllh baxan sota ba naji fa lbrn ta tab’a yin aure kwana 3 auren ya mutu sannan ance ma yarinyar karuwa ce ta dad’e tana karuwanci da larabawa a dubai kai k’ar she ma kasan baxan b’oye maka komai ba wllh y’ar damfara ce kasan waye ya fad’a min ? k’anin matar da ta auri mijinta shiya bani labarinta ful,

da na aure ta tasan komai akaina tace xatai min hayaniya nima intada nawa b’allin kin fad’a min ke karuwa ce ? kaga dole tayi shiru,

hhhhh abokina sama taka Allah yai min arxik’i kuma dole kusamu naku”

“kai yanxu da hnklinka xaka auri y’ar damfara Auwalu?”

“ai nima babban d’an damfaran ne tunda nima damfare ta zanyi ita da ubanta ni banda mu wllh koka d’an bana sonta kud’in su kawai nakeso dana samu sakin ta xanyi,

d’an xaman danayi da ita na fuskanci bata da son hayaniya so wannan yana sa inajin tausayin ta shiyasa baxan wani d’au dogon lokaci tare da ita ba”

takaicine yahanata jin k’arshen maganar ta kashe wayan had’e ta fa shewa da kuka ta dad’e tana kukan sannan ta shi da sauri ta tafi gidan su a falo ta tarar da Abbanta yana duba jarida ta xauna had’e da sama sa kuka

da sauri ya ajjiye jaridan yana tambayan ta lfy dan bai son abinda xai tab’a masa y’arsa cikin kuka take mgn

“Dady kabani 10 millions dan Allah”

jim yayi yana kallonta hannunsa yasa akanta

“Hindu me xakiyi dasu?”

“akwai muhimman abinda xanyi dasu Abba”

ta kwashe lbr ta fad’a masa tagumi yayi maganganun yaron su  sosa masa rai amma ya xaiyi ? k’addara ce ba son ranta ba gashi yanxu ammata gori

check ya d’auko ya rubuta kud’in ya mik’a mata ta amsa had’e da ajiyar xuciya

“Abba xuwa xanyi na bashi tunda dan su yake sona amayar masa da komai nasa nafasa aurensa xan bashi wannan ne dan yarage masa rad’ad’in abinda xaiji ko kad’an bana son akan abin duniya wani yaji haushi na”

Abba kamar yai kwalla ya ce

“shikenan Hindu Allah yai miki albarka Allah ya baki wanda ba xai goranta miki ba”

ta amsa da amin ta fice yabi bayanta da kallo yana girgixa kai.

ta kirashi awaya yaxo suka gaisa cikin walwala da sakin fuska tana duba check d’in ta bashi ya amsa yana mmk ta fad’a masa taji komai ga wannan ta bashi kyauta ta wuce tai tafiyar ta kasa xaman gidan tayi tayo gidan jannat

tana xuwa tasawa jannat kuka ta dad’e tana rarrashin ta sannan ta bata lbrn komai jannat ta girgixa taji kuma dad’i da Allah yasa sukaji hakan

“ina son mahboob lokaci ya k’ure min Allah yabani miji nagari abin ma ni yafara ban tsoro ko wanne ba sa’a ?”

“kiyi hkr Hindu komai daga Allah ne Allah yayi ba maxajen ki bane Allah ya baki nagari”

tadad’e agidan hindu sannan ta tafi tana tafiya jannat takira Abba tafad’a masa hindu da bakinta tace tana son mahboob yaji dad’i yasa musu alvarka

ranara d’aurin auren duka mahboob aka bashi matan sai da aka fara d’aura auren shi hindu sannan aka d’aura dana meenat yaji dad’i sosai sbd yasami abinda yakeso ita kanta hindun tayi mmk dan bata sani ba sai da aka d’aura

anyi shagali anyi bikin al’adu kala kala an kuma kashe nera anyi watsi da ita fatanmu Allah ya basu xaman lafiya haka akayi shagalin bikin jannat na jan tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe.

sati d’aya da bikin bak’i na shirin komawa zahra taxo gidanta suyi ban kwana sbd gobe xasu wuce  suna hira Muhammad yaro mai wayau ya girma sosai dan ba inda baya xuwa da k’afarsa yanxu ma rigima yake shi sai an kaisa gidan abokinsa Abba jannat na rarrashinsa kamar k’ara tura sa take ta kira ya khaleel tafad’a masa yace gashi nan xuwa ya kaisa gidan Abban yana dawowa khaleel d’in ya wuce da zahran gidan Abba tai musu sallama bayan ya dawo ya tadda jannat d’in a dalo tana ta murk’usu su bayanta da marar ta na ciwo bai jira komai ba ya sunkuce ta sukaje asibiti ana dubawa aka ga haihuwa ce

cikin daren Allah ya sauketa lafiya ta haifi y’an biyu maxa kyawawa lafiyayyu cikin daren asibitin ya cika da dangi doctors d’in sun so sallamar ta dan dai dare yayi safiya nayi suka sallamesu komawar da zahra batayi ba kenan sai da akaci suna da su itama dai da cikinta 7 months

y’an biyun sunci sunan Dady da Abba Bashir (fawazz) da Adam (sa’ud) anyi shagali kamar na Muhammad fatanmu Allah ya raya y’an biyu.

watan su fawaz da sa’ud uku zahra ta haihu ta haifi d’anta namiji dangi daya suka shirya suka je  saudiyya har da su Abba da Dady

ranar suna tana cikin y’an’uwa suna hira taga kiran wayan ya khaleel ta bar wajan hiran ta fito harabar gidan ta xauna suna waya dashi a lallai sai taxo masaukinsu ya ganta dan tun asuba rabon ta dashi rarrashin sa takeyi sbd tasan muddin taje baxai bar tadawo da wuri ba da kyar ta rarrashesa akan ya jirata xata xo ammafa sai da yamma tana gama wayan tayi ajiyar xuciya tana murmushi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

wata zazzak’an murya taji tai mata sallama a hankali ta waiwaya kyakkyawar matashiyar mace tagani me kyau sanye cikin abaya tayi rolling d’in kanta da gyalen abayan hannunta rik’e da jaka madaidaiciya kalan stone d’in abayar ta tunda taxo wajan ya d’umi da k’amshin jikinta.

amsa mata sallamar jannat tayi tana mmk ganin tana mmk yasa tayi murmushi ta mik’o mata hannu alamun su gaisa

“sunana JASRA BELLO MOD’IBBO munxo sunan Zahra ne mijinta abokin mijina ne, naga kema y’ar 9ja ce”

murmushi jannat tayi tana tuna sunan tabbas tasan sunan a kano

“sunana JANNAT ADAMU CHED’E”

ware ido jasra tayi cike da mmk tace

“mashaa Allah tabbas nasan sunan nan a Kano na kuma san sunan ahhh….”

tayi dariya bata k’arasa ba dariya itama janna tayi

“…a ina kika san sunan?”

“…. awajan Ummee Garkuwa”

tak’ara sa tana kallon jannat

far tayi da ido

“tabbas hakane a novel d’inta Jennifer ko ?”

d’aga kai jasra tayi had’e da xama kusa da ita

“naji dad’in ganinki jannat dan nima ina son ganin Ummee Garkuwa ina son bata labarin kaina ta rubuta kamar yanda tayi naki”

“karki damu zan had’aki da ita “

“naji dad’i kuwa ki bani numb d’inta yanxu in ban ta kura miki ba”

“ba komai babu takwara ga numb d’in 080*********** “

“ngd sosai jannat bari na kirata mu gaisa tun yanxu dan gsky na matsu mu had’u da ita”

murmushi sukaiwa juna jasran ta sunkuyar da kanta tayi dialing number ta shiga ta d’an jima tana ringing sannan aka d’aga

Ummee Garkuwa:”assalamu alaykum”

Jasrah : “waalaikumus salam, dan Allah ina magana da Ummee Garkuwa?”

Ummee Garkuwa:”en itace ya kike?”

Jasrah:”lafiya lau ya jama’a?”

Ummee Garkuwa:”Alhamdulillah”

Jasrah:”na amshi numb d’inki a hannun jannat Adamu ched’e’

Ummee Garkuwa:”masha Allah kina tare da mutanen kirki”

  Jasrah: ” gaskiya kam hakane na amsa ne dan nabaki labarin kaina da kaina rikitaccen lbr mai ban tausayi ban haushi harma da takaici mai abin mmk da kuma soyayya mai karya xukata”

tak’arasa kamar xatayi kuka

Ummee Garkuwa:”tofah bari na gyara xama kin san mu da kibamu naman d’awisu k’ara ki bamu lbr”

dariya tayi jasrah

Jasrah:”kiyi hkr Ummee lbrn baxaiyiyu awaya ba sai na dawo 16 ga watan MAY in shaa Allah”

b’ata rai Ummin tayi kamar tana ganin ta

Ummee Garkuwa:”tohm shikenan Allah ya kaimu lokacin ngd sosai”

Jasrah:”ni ce da gdy zan kira latter ngd sosai byeee”

ta kashe wayan dai dai lokacin da jannat ta mik’e suka jeru tare suna hira suka shiga cikin gidan sunan.

kwanansu tara suka dawo daga sunan zahra da y’arta taci sunan umma Nabila watansu fawazz da sa’ud goma sha d’aya suna tafiya harda gudu ma dan sunyi wayo Muhammad miskilin yaro komai nashi na babansa sak ranar hindu ta haihu ta haifi namiji tunda ta haihu suke cikin hidima sosai hindu suna xaune lfy da abokiyar xamanta meenat suna mutunta juna sati nayi aka sawa d’an suna Abubakar sadik sun sha shagali sosai abin sai wanda ya gani dady da Abba kam cikin murna da godiyar Allah suke ta ko ina Allah na axurtasu da jikoki haka Umma da Momy dangi ya had’u ya cure sun maida kansu tamkar ciki d’aya sun had’a kansu suna kuma k’aunar junansu d’aya baxaiyi abuba batare da shawarar d’aya ba Alhamdulillah komai yayi yanda akeso sukam sai godiyar Allah hindu na kwance tana bawa d’an sadik nono mai gadin su yai sallama wai wani mutum yana sallama da ita da mmk ta fita wanda tagani ne yasa tak’ara sa da sauri kuka tasa

“Baba”

“naam hindu, Alhamdulillah Allah ngd maka dana ganki ahaka najin dad’in had’uwa da iyayenki da kikayi na kuma ji lbrn komai y’ata haka nakeso talatu Allah ya toni asirinta”

“hakane baba amma ya akayi haka ka fito daga prison ?”

jinjina kai yayi

“shareef alhussain ne ya satoni daga cen akan naxo na taimaka masa mu sato wani diamonds a gidan kayan tarihi na dubai d’in nima nagudo nan nasan bai isa yaxo nan yai min wani abun ba,

na tuba yanxu y’ata ba xan koma ko ina ba ina nan k’asata”

hindu na kuka ta cigaba da bashi lbr

nan da nan ta bashi lbrn komai ta kuma kira Abba tasanar dashi da kansa Abban yaxo suka tafi tare sbd ya mutunta shi kamar yanda yaiwa sauran da suka reni sauran y’ay’ansa.

agajiye ta dawo daga  kasuwa  falo tasa meshi shida Muhammad daya ke baccin agefan sa y’ar rainonta ta ajjiye fawazz ita ma ta ajjiye sa’ud da duk sukayi bacci tana k’ok’arin shiga ciki ya khaleel ya janyota jikinsa hannunsa kan cikinta yana shafawa yana kallonta zaro ido tayi tana kallon sa d’aga mata gira yayi

“yau zanyi wata ajiyar ta musamman dan 3ple zan ajjiye”

ware ido tayi sosai tana kallonsa dariya tayi ta xame kanta a hnkl

“ba ruwana Ummee Garkuwa tana jinka”

tab’e bakinsa yayi

“ina ruwana da Ummee Garkuwa bata son ke matata bace ? ki shirya beautyna yau fa sai na miki kyakkyawar ajiya ta musamman!”

TAMMAT BI HAMDULLAH

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]