[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 65 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ranar aka salla mota sbd ita da yarinyar ta suna cikin k’oshin lfy

suna komawa gida da daddare akai musu waya Rubayya ta haihu ta haifi d’anta namiji rana d’aya kenan suka haihu da sulthana amma ita Rubayyan da daddare

rana d’aya akai shagalin suna sunyi gagarumin taro anyi wadak’a da mony kayan rabo kam duk xalamar mutum sai ya gaji y’ar sulthana taci sunan hajja Hafsat d’an Rubayya kuma sunan baban prince A.K Garkuwa wato kabeer.

sati biyu da sunan su sulthana da Rubayya

jannat ta tashi da zazzab’i mai zafin gaske ga tashin xuciya duk abinda taci sai ta dawo dashi hnklin ya khaleel ya tashi sosai ya kaita asibiti aka bata magunguna suka dawo gida bayan kwana biyu xaxxab’in ya dawo su ka koma asibitin akai mata test tana da ciki wata uku.

abin ya bata mmk shi kam khaleel murna yake sosai tun akan hanya ta had’a rai tana kallon d’ansu Muhammad me wata takwas yaro me kuxari da lfy dan har yana mik’ewa tsaye b’ul b’ul da shi ko kad’an bata son abinda xai tab’a lfyr d’an ranta b’ace suka koma gida asalima haushin ya khaleel takeji daya ke murnar cikin wanda take tunani shi sam baya ganin abinda xai faru suna komawa gida kai tsaye d’akinta ta wuce

tahad’a kai da gwiwa tana tunani mai xurfi ranta ab’ace.

d’akin ya shigo hannunsa rik’e da Muhammad daya ke bacci kusa da ita ya kwantar da shi ya xauna inda take had’e da janyo ta jikinsa

“beautyna har yanxu zazzab’in ne ?

kiyi hkr xaki warke ….”

tureshi tayi daga jikinta ta matsa nesa dashi tana masa wani irin kallo still ma tsowa yayi yana k’ok’arin rarrasan ta

“kwantar da hnklinki jannah ! inshaa Allah…”

afusace cikin fushi ta katse shi

“ka kyaleni ! sam raina bai son cikin nan ! ka kalli Muhammad baka tunanin halin da xai kasance idan ya sha ciki? zubar da shi xa’ayi …….”

da k’arfi cikin fad’a yace

” firdausi !wa ya isa ya xubda cikin nan !? babu shi sai Allah wllh ! wllh ! kada ki fara  dukansu y’ay’a nane ina sonsu kada na k’arajin wannan maganar”

“dama dole kace haka tunda bakai kake d’auke da cikin ba ba ajinkin ka yake ba kuma sai na zubar ba zan haifeshi ba dolene kayi duk abinda xakayi …”

“xakiga abinda xanyi dan sai na d’au babban mataki duk shegen likitan daya xubar dashi wllh sai na d’aureshi ke kuma ! xakiga abinda xan miki muddin kika tab’a cikin nan…”

ya wurga mata wata uwar harara ya fice

durk’ushewa tayi awajan tana kuka sosai xuciyarta na ingixata tana jin haushin ya khaleel sam wannan rashin adalcine kaso d’an da baka samu ba karasa wanda kake dashi ?

ina ita bazata iya ba

daren nan kam babu wanda yai bacci kowanne xuciyar shi na masa k’una uwa uba kewar juna dan wannan shine karon farko da suka raba wajan kwana

wasa wasa sun shafe kwana 7 babu me kula juna asalima yanxu ya khaleel sai 12 na dare yake dawowa gida tun bata damuwa har hakan ya fara bata tsoro ga kewar shi da ta addabe ta

tana xaune a falo ya shigo fuskarshi a murtuke ta kalli agogo !2:07 ta kalleshi axuciye take masa tamvaya

“daga ina kake ? meyasa ka dawo yanxu da ka sani acen ka kwana”

jim yayi yana kallonta al’amarinta ya daina bashi mmk ya dawo tsoro yarasa yadda akayi ta iya futsara haka kamarshi babba wannan yarinyar k’arama ta dink’a gasa masa maganganu ? lallai tagama raina shi kaje ka rufe ta da duka tasan kai ba sa’anta bane da sauri ya girgixa kai yana a’uxiyya

bai tanka mata ba ya wuce dan muddin ya tsaya tankamata bai san mai xai faru ba dan xuciyar shi har wani hayak’i hayak’i take sbd b’acin rai

bin bayansa tayi da kallo xuciyar ta cike da xugar da take mata

“lallai ma yarai na miki hnkl ya maidake wata mahaukaciya kina mgn ya kyaleki ki bishi ki faffad’a masa bak’ak’en maganganu”

fuuu ! tabi bayansa kamar ta tashi sama a xaune a bakin gado ta sameshi yana k’ok’arin cire riga rik’e k’ugu tayi tana karkad’a jiki xuciyarta na ingixata

“sbd tsabar rainin hnkl ina mgn ka kyaleni ? wato ka maida ni mahaukaciya ko ? me kake nufi ne ? ciki ko ? nace xaina xubar dashi kayi abinda xakayi”

kamar baxaiyi magana ba ya daure ya rarrashi kansa cikin ko inkula dan ko kallo bata ishe shi ba

“meya shafeni da xubar da cikin da xakiyi ? tunda har kina da amsoshin daxaki bawa ubangijinki in ya tambayeki name kike jiran nawa hukuncin ? ke mai wayo ce wayon naki ya kai ki iya yiwa wanda ya halicce ki kije kiyi duk abinda xakiyi kin san kwanakin daya rage miki aduniya ko ? kina da tabbacin xaki wuce gobe ko jibi ko ? ke kika ba kanki d’an kuma bakya so kinga dole ki watsa shi a bola jibi in kinga dama xaki kuma bawa kanki tunda ke daban kike baxa aimiki tambayar kwanciyar kabarinki ba its good kiyi duk abinda kiga shine dai dai “

axahirin gsky maganar shi tasa mata tsoro amma ta basar ta rasa ma amsar da xata bashi wa’axi yai mata cikin sigar bak’ar magana ta yaya xata amsa masa ?

afusace ta fice tana surutai k’anana k’anana

tab’e baki yayi yana mmkin canxawar jannat d’insa lallai d’an Adam tara yake bai cika goma ba dolene wata rana ya b’ata maka xo mu xauna xo mu sab’a dalilin dayasa yai mata uxiri kenan

d’aki ta koma tayi tagumi tana juya maganganun sa “kina da tabbacin xaki kai gobe ko jibi kin tanadi amsoshin kwanciyar kabarinki…”

gabanta ya fad’i ita da bata da lfy kuma tana son xubda cikin nan

shin inta xubar mai xata cewa Allah ? my b ma baxata sake haihuwa ba …. araxane ta mik’e ta k’urawa Muhammad ido tana son d’anta tana tsoron kar yasha cikin da y’ay’a suke sha suyi ta cuta ak’arshe ma su mutu dafe kanta tayi ya salam ! ya xatayi ? any’a kuwa xat iya xubar da cikin ? tsoron data keji kartaje ma garin xubar da cikin ta mutu alwala ta d’auro ta tada sallah tadad’e tana nafilfili sannan ta kwanta

tana kwance da jarirai guda biyu suna mata kuka tayi tayi su karb’i nono sunk’i asalima jariran hararta suke harara bata wasa ba tarasa yadda xatayi dasu a firgice ta farka cikin tsoro ta janyo Muhammad ta rungumeshi tana fidda gumi baccin da bata koma ba kenan

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

washe gari bata ga fitar sa ba tayi jigum kewar shi ta isheta uwa uba har yanxu tsoron mafarkin datayi takeyi ita da Muhammad kad’ai afalom sai sambatun da tv takeyi sallama taji a tsorace ta amsa

y’anmatane matasa suka shigo gidan su hud’u masu kama d’aya tsoro yak’ara kamata suka gaisheta a d’ad’dari ta masa ganin kamar tana jin tsoro sosai yasa babbar cikin su yin murmushi muryarta asanyaye tace

“sunana khadeeja Garkuwa wannan k’anwata ce sunan ta Zainab Garkuwa da Halima Garkuwa wannan itace k’aramar mu Rumaisa Garkuwa mu k’an nan Aysha Garkuwa ne”

sai yanxu tasamu xuciyarta ta sanyaye cikin murmushin da bai kai xuci ba tasake suka fara hira sosai dan ta fuskanci suna da hankali duk da yara ne hira sosai suka ye suna cikin hiran ya khaleel ya shigo tayi mmkin ganinsa ganin ya shigo yasa suka mik’e xasu tafi jannat tadakatar ta shiga d’aki ta had’o musu kayan kwalliya dan taga yaran y’an son kwalliyane sukayi gdy suka tafi

jigum tayi tana kallon k’ofar d’akinsa wata xuciyar tana taje ta rarrashe shi wata kuma tana hanata na ita fa macece tajawa kanta aji kartaje ta bari har sai yaxo inba haka ba sai ya rainaki ya xaci ma ke kika damu ko ke kike sonshi xugum tayi tarasa abinyi da sauri ta shiga d’aki ta d’auko carfi tana xkirin da duk yaxo bakinta ta kwanta tana xikirin ta tashi jikinta asanyaye qur’ani ta d’auko ta fara karantawa

tana karatun tana jin xuciyarta kamar an wanke mata ita ajjiye qur’anin tayi tana jin muguwar hud’ubar xuciyar ta karkije tayi a’uxiyya tayi addu’ar korar shaid’an ta shiga d’akin yana xaune yana kallon News kallo d’aya yai mata ya kauda kai

haushi ya kamata irin kallon dayai mata ta daure dan mafarkin jiya ya bata tsoro kusa dashi ta xauna tarasa ta ina xata fara mgn korar shad’an tayi dan tasan shiyasa mata waswasi muryarta tasanyaye ta fara magana

” nasan ban kyauta ba .. amma nayi cikin rashin sani….nasan na b’ata mk kayi hkr na janye waccen maganar Allah ya sauke ni lfy “

shifa dama ya damu matuk’a dan shi kad’ai yasan axabar da yasha na rashinta kusa da shi

kwatsam xuciyar shi tafara kai kawo

“kar ka hkr ka gasata tukunna dan yarinyar tagama rainaka banda rai nin wayo tace xata xubar da ciki ? wannan taxama mashirkiya ka kyaleta inda hali ma ka wanka mata mari ka koreta daga kusa dakai tuban muxuru tayi my b ma ta xubda cikin tunda tace sai ta xubar”

dafe xuciyar sa yayi da hannunsa yana juya zancen daurewa yayi ya kori shaid’an yai addu’a sannan yaji xuciyar sa tasaki kafin ya kuma jin wata xigar ya janyota jikinsa muryarsa asanyaye

” kin kyauta da kika gane kuskuren ki har kika janye sab’awa mahaliccinki,

rayuwa ta gaji hk xo mu xauna xo sab’a shi shaid’an babban burinsa rusa xaman lfy musamman ga ma’aurata dole ma’aurata su tashi tsaye suyi yak’i da shaid’an idan har suna son zaman lfy idan har yai nasara akansu tofa sun shiga uku dan basu babu farin ciki,

ya xama dole mu tashi tsaye beautyna mu yak’eshi tunda har yai nasarar samana jin haushin juna”

lallai sai yanxu tai tunanin hk data biyewa xuciyar ta da yanxu tana nan ranta ab’ace tada saukar da kanta tunda itace k’asa dashi sannan ita ta b’ata masa gashi yanxu tana jin farin ciki sosai

“hakane ya khaleel Allah ya rabamu da sharrinsa Allah yai mana tsari dashi” ya amsa da “amin”

ranar cikin farin ciki suka yini suka kwana suna nuna missing d’in junansu

kwanaki satittika watanni biyu suka wuce wato yanxu cikinta wata biyar cur jidda ta haihu ta haifi d’anta namiji me kama da fulani sak dan kamarsa d’aya da babansa nan da nan dangi suka cika gidan zahra ma taxo da cikinta wata uku  ita da ammy da ya mukarram da ysuf xuka xo sai sati na xagayo wa aka sawa d’an sunan dady Bashir anyi shagali kam dan abokanan mugun gaye sun xo na cen kauyan su sunyi irin nasu shagalin da wasan da sukeyi idan ammu su haihuwa .

ranar sunan hjy Nabila taja jannat gefe tana bata lbrn Hindu mahboob ke sonta ta k’e k’ashe k’asa tace bata so sam wai abin sai yai yawa asalima ita bata son auren xumunci dan ita mahbobb wane awajan hjy Nabila ranta asoshe take mgnr

” ni har mmk take bani tunda aurenta ya mutu da hafiz take gidansu mahboob d’in kuma yace yana so ta k’i Dadyn naku yace ba mai mata dole shi kuma Abbanku yace ko tana so ko bata so sai ya d’aura auren y’ar’uwar ku ce kuyi mata fad’a”

“umma kwantar da hnklinki zan mata mgn komai xai wuce Allah ya xab’a mata abinda ya fi alkairi”

ta amsa da “amin”

wata d’aya da sunan jidda jannat ta kira hindu kan mgnr ta da mahboob

“Hindu meyasa bakyason mahboob ?”

“nba sonsa bane banayi bana son auren zumunci ne kawai wllh ina son sa sai dai hkr dannyi yanxu ma na turawa dady wanda nake so”

xaro ido jannat tayi

“waxaki aura to”

“wani ne sunansa Auwal”

“haba Hindu ya mahboob d’inta fa ?”

kallon jannat d’in tayi ta girgixa kai

“jannat abun yayi yawa ke kina auren khaleel sulthana na auren haisam sannan ace dole sai na auri mahboob? yes  dukanku ba dole akayi muku ba asalima ku kuka had’a kanku amma baxan iya ba iya taku ta isa ni mahboob wana ne yayana ne baxan iya auren shi ba idan kuma damuna xakiyi da mgnr xanyi tafiya ta dan ban son maganar”

“hmmm Hindu kenan Allah shi ya had’a ba wani ba idan Allah yai mijinki ne ya xakiyi?”

shiru hindun tayi jannat d’in na mata nasiha fur tak’i sauraron ta dole ta kyaleta

ba ajima ba akasa ranar hindu da Auwal mahboob da meenat budurwar sa duk wata biyu kwanci tashi har wata biyun ta cika suka fara hidimar biki zahra taxo da cikinta d’an wata 6

ana sauran 1 week a d’aura aure

Hindu na kwance wayarta tai k’ara tana dubawa taga Auwal d’inta tai murmushi ta d’aga suka gaisa had’e da d’an tab’a hira kamar yanda suka sa ba bayan sun gama wayan bata kashe ba tana tunanin ya kashe ta ajjiye wayan ta koma ta kwanta kanta na dai dai inda wayan take taji surutun su Auwal d’in tana k’ok’arin kashewa maganar data ji sunayi ne yasa ta d’auke wan numfashi

hankalinta yai masifar tashi mmk da haushi da takaici ya dirar mata lokaci d’ya taji tana mugun danasani

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]