[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 47 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kuka sosai sabreen takeyi dajin muryan kamal d’inta. Bayan sun d’an samu nutsuwa ne se Incle D yace yakamaya amaida sabreen d’akinta donyin takaba. Haka aka maida ita maman munirane tazo ta zaina da ita dasu kaka duk suna gurinta. Da akayi kwana bakwai da rasuwanne su Aliyu suka koma tare da uncle D amma mummyn kamal tana nan tare da sabreen agidan da kyar suke sata taji abinci. Desa mummy tayi 1month sannan suka tafi pakistan da suhail. Har kabarin kamal su sadiq suka kaishi nanma yayita kwalla suka mashi addu’oi sosai sannan suka tafi. Kowa seyayiwa suhail ta’aziya don kowa yasansu tare.

***
Sabreen tayi 4month 7day sesu mummy suka dawo nigeria ita da suhail da uncle D, saura 3days ta fita takaba.
Malamin,sunna suka samo lokacin data fita takaba aka raba gado domin saukewa mamacin nauyi, komai na kamal suhail ya tattaro ya mikawa umcle D, aka rabawa mummy da sabreen gadonsu. Inda aka barwa sabreen wannan gidan da take ciki da kuma kud’ade masu yawa😭😭. Tunda ake rabon taketa kuka tana tuna cewa yanzu shikenan bazaka dawoba yah kamal😭. Hakuri aketa bata har aka gama aka watse, kudin sanreen ta mikawa suhail tace aje a gina masallaci dashi ayitawa mijinta addu’a Allah ya gafarta mishi.
Yadda takeso haka akayi gidanne kawai suke zaune a ciki itadasu kaka.
Kafin mummy su tafine aka taru mummy tace suhail kaji abinda kamal yace bakace komaiba, shuru suhail yayi baice komaiba, uncle D yace sujail lokaci yayi da zakayi aure tinda dama akwai maganan aurenka da hafsat to kar’a tsaya b’ata wani lokaci seka auresu dukkansu biyun, mum tace tabbas haka ya kamata suhail kayi hakuri😰, sabreen tace mummy kuyi hakuri bazan iya auren yah suhail ba😭. Mummy tace sabreen nasan abinda kikeji dan kiwa nima ya faru dani amma ki daure kodan cikawa mijinki burinsa😰. Sabreen tace mummy kuyi hakuri hakan bazai yubane seta mike zuwa d’aki tanata kuka😭. Baban munira yace inaga da an kara mata lokaci tukunna, uncle D yace haka za’ayi suhail ka zauna mu zamu koma pakistan ke kuma hafsat kiyi hakuri kinga ba haka akasoba amma muna namu ALLAH na nashi, fatanmu shine Allah ya sanya alkhairi, mummy tace dan Allah suhail ka shawo kanta dan ayi da wuri, suhail yace to uncle naji kuma na amince zan aure su biyun. Sukace Allah ya baka albarka Allah ya sanya Alkhairi aka amsa da ameen sannan suka watse.
Wasje gari su mummy suka tafi bayan nasiha datayiwa sabreen ita da uncle d. Kaka dasu maman munirama sukace ta amince ta aureshi ai zata dinga ganinshi a matsayin kamal tunda aminaine, musammanma kaka dayan komai. Ita dai sabreen batace musu komaiba se hawaye da takeyi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tun daga wannan ranan hafsat bata sake zuwaba, kuma ko so d’aya bata kira sabreen a wayaba. Abin ya dami sabreen kuma tasan dalilin hakan, koba komai hafsat ta zama kawarta sannan kuma ace zasu had’a miji d’aya, kai wani se mutuwa😭😭 ko sabreen ta kira wayan hafsat bata d’auka harta gaji ta dena kira.
Rarrashi sosai mum tayiwa hafsat tate da nasiha amma duk bai shige hafsat ba, dan aduniya idan akwai abinda ta tsana shine KISHIYA sannan kuma ace kawarta sabreen, inah gaskya da sake😡😠.
Wata bakwai kenan da rasuwan kamal, yaune mum tacewa suhail yazo gurin sabreen ta batun aurensu, hafsat tana jin haka ta wuce d’aki rai ab’ace😡 suhail yana ta binta da kallo yace mum wannan abun zaiyu kuwa😨? Mum tana tausayawa d’an nata tace zaiyu insha Allah menene damuwarka? Suhail yace mum hafsat bazata tab’a amincewaba, mum tace zata amince tashi kaje gun sabreen ka barni da ita, ba musu ya wuce se gun sabreen. Bayan sun gaisa dasu kakane se maman munira taje ta kira sabreen himar nata har k’asa tazo palo ta zauna ko kallonshi batayiba bare tace mishi wani abu.
Suhail ya rasa me zaice har na tsawon mintina sannan yace sabreen ya karin hakuri? Tace Alhamdulillah, yace to Allah ya jikanshi ya mishi gafara, tace ameen tana hawaye😓. Suhail yace sabreen nasan kinsan abinda ya kawoni, ina fata zaki amince da bukatar kamal dukka cewa haka ya d’ade a zuciyata nikam, dan haka kiyi hakuri sabreen dan Allah ki amincemin, sabreen tace yah suhail kabar zancennan nizan zauna haka wlh😓, suhail yace bazan yadda da hakanba sabreen pls ki amincemin, sabreen tace yah suhail hafsat fa, kasan ko wayat ta dena d’auka yanzu, ina mutunta kawancemu bazan iyaba kayi hakuri kawai😒. Suhail kamar,zaiyi kuka yace sabreen pls kinsan na soki tun farko amma daga baya na hakura nasawa raina cewa zan auri hafsat amma ki sani bazan iya kaushewa abokina kudirinsaba inaso in cika mishi burinshi ne sabreen, duk kaunar da nake miki ban tab’a fatan kamal ya mutu in aurekiba wlh inason kamal kamar yadda nake son kaina sabreen pls😥
Sabreen zata bud’e baki da nufin cewa bata yardaba se SALMA ta toshe mata baki sannan tayi muryan sabreen d’in tace shikenan yah suhail na amince. Dad’i yaji sosai har cikin ranshi yace “thankyou sabreen😊 nizan tafi kijeki huta, salma tace toh sannan ya tafi…

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]