[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Juwairiya ta yi tsuru da jakarta ta na kallon Mama da ke tsaye agefen ta riƙe da hijabin ta a hannu ta na ƙoƙarin saka wa a kanta saita ji hawaye sun ƙara wanke mata fuska,ta share da sauri dominMama tun ɗazu take mata ƙorafin kuka yanzu ma da taga ta nahawaye sai ta yi tsaki ta ce.” Gaskiya kukan nan na ki ya fara siƙe niJuwairiya na ga ke da Baba Sani kuka shirya hakan,amma kin bi kindame ni da kuka in da kin san ba za ki iya ba uban wa ya ce kiamince.”
Sai ta rungume Mama ta ƙara fashewa da kuka ta na jin wani irinbaƙin ciki da fargaba ga gabanta da yake faɗuwa a kai akai don jitake kamar ta ce a ta fasa.
“Mama akan ki sami lafiya na amince amma ki yafe min in na ɓatamiki na ga kamar ran ki ba ya son na tafi.“Ta ce da ita cikin hawayefuskarta ta tura shi a jikinta.
“ Ki na ganin in da bai yi wa rayuwarmu halacci ba wallahi BabaSani bai isa ya saka ki ƙara wani aikatau ba,don kullum na yi sallahsai na roƙi Allah ya raba ki da shi saboda irin cin mutuncin da kikafuskan ta.”
Share hawayenta ta yi ba ta ce komai ba ta shafa kan Ibrahim tare dariƙe hannun sa suka fito tare.
“ Mama ji nake kamar kar na tafi sai kun tare a sabon gida.”Ta faɗatare da fuska.
Mama ta kalle ta ta ce “ Gara ki tafi Juwairiya saboda yau aka yizaki tafi kuma kin ga mutumim nan ya yi ma rayuwarmu hallaciwanda dalilin haka ina matuƙar girmama shi.”
“ Humh.” Ta ce a cikin zuciyarta sannan ta ɗora da ce aranta jin abinda Mama ta ce.” Da kin san abin da ya ƙulla da ba ki girmama shiba,shi ɗin macuci ne sosai ya fiye son kan sa da rayuwar matar sa dakin san dalilin da ya sa ya yi mana wannan abubuwan da kin tsaneshi har iya ƙarshen rayuwar ki.“
A lokacin da suka yi nisa mama ta kama hannunta ta riƙe sai hawayeta ce.” Juwairiya ki riƙe mutuncin kan ki a duk in da kike kuma, dukabin da ki kai kin san Allah ya na kallon ki mutunci na ƴa mace shine zai zama ado a rayuwarki,ba wai ina zargin ki ba ne a’ a ina mikinasiha a matsayina na uwa wacce ƴarta za ta yi nesa da ita,sannan yazama dole na saki a hanyar daidai don kar ki ga mutum zai aikataabu a ɓoye,ya na tunanin ya kauce idon mutane bayan ya mantamahaliccin sa ya na ganin duk abin da ke“
Jikin Juwairiya ya ƙara sanyi kamar ƙanƙara haka kawai sai ta ji tafara tsarguwa yadda Mama take ta mata wasu irin maganganu,wanda take shan jinin jikinta don in ta yi mata irin waɗannanmaganganun ko kallonta ba ta iya wa.
Yanzu haka ta kasance ta yi ƙasa da idanunta ta ce.”Mama an ya bazan.”
Katse mata hanzari ta yi tare da taran ɗan mashin ta karɓi jakarta data riƙe da ta yi tsumu ta ɗora a kan mashin ɗin sannan ta kalle ta tace.” Ma za ki tafi Allah ya tsare da kin sami lokaci ki leƙo.”
Juwairiya ta haye mashin jikinta babu karsashi hawayen fuskartasun ci gaba da kwaranya yayin da ɗan mashin ɗin ya fara tafiya akan titi.
Wani ƙarin abin da ya ƙara zubar hawayenta cikin ƙunar rai da tatuna yau gidan mijinta za ta akan mashin da ƙullin kaya a jaka, batare da an kawo mota kamar yadda ko wace mace mai gata waccemijinta yake son ta ake mata,duk lokacin da ta tuna wannan sai taƙara sakin kuka har ɗan mashin ɗin ya juyo ya kalle ta ya na faɗin.”
Lafiya Hajiya?”
Amma ba ta kula shi ba kuka sosai take har suka isa gidan Atine,alokacin da ta isa ba ta nan sai da ta jira ta sannan ta dawo sallah ta yisuka kama hanya.
Wani irin faɗuwar gaba take yi har sai da ta dafeƙirjinta.Kasancewar a kwai tazara sosai da gidan Atine sai da sukahau nafe.
A lokacin da suka iso ƙofar gidan da Juwairiya ta saka a ranta naA.m ne hankalinta ya yi matuƙar tashi matuƙa gaya.Kawai sai ta jiƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba ta sani A.m suna da kuɗi amma kokaɗan ba ta taɓa tunanin haka gidan sa yake ba.
“ Dole ka ce baka sona kuma ba zaka taɓa sona ba saboda ba mudace ba ni kai na sheda ne.”
Ta furta cikin karayar zuci don ta san ya fi ƙarfinta na harabada.Gaskiya fasalta gidan sa abu ne da zai ɗau lokaci saboda gidane mai matuƙar girma, da tsari ga shukoki masu kyau waɗanda sukaƙara ƙawata gidan,don haka mai karatu na bar maka aikin tsarafasalta iya tsaruwan gidan,A.m a hannun ka don in na ce zan yi zanɗauki lokaci ni dai na yi wa gidan suna da aljarnar duniya.
Lokacin da suka shiga cikin falon Juwairiya ku san nemannumfashinta ta yi ta rasa, don barazanar shiɗewa yake yi sabodatsaruwar falon da ke ɗauke da ku san set huɗu na kujerumabambanta.
Duk lokacin da ta ƙara taku a cikin falon zuciyarta karaya take dason A.m da ya shige zuciyarta saboda ta haƙiƙance ma kanta dayaudarar kanta take yi A.m babu abin da zai yi da ita.
A ƙasar kafet ɗin dake zagaye a tayas ɗin da ya sha guga ya na taƙyalli da ɗaukar ido ta zauna tare da rintse idanunta,hakan ta ji ba tason idanuwarta su yi tozali da matar A.m don ta san zuciyarta za tabuga.
Atine ta zaro wayar ta ta yi kiranta sai dai cikin takaici ta ije wayarta kalli Juwairiya ta ce.” Ba ta dawo aiki ba amma ta ce mi jira ta zata duba patient ta dawo.”
Sai Juwairiya ta sauke idanunta daga kallon Atine saboda kiransunan ta da ta yi,ta ci gaba da kallon ƙasa yayin da zuciyarta yakebugawa tamkar za ta fito.
Kusan waya biyu suka shafe suna zaune a falon sai kowa shiru jefi-jefi Atine take sakin tsaki,amma Juwairiya iya tsawon lokacin kotari ba ta yi ba sai sautin bugun zuciyarta da yake ta ƙaratsanantuwa.
Ƙwas!Ƙwas!!Ƙwas!!! Suka ji sautin takalmi wanda Juwairiya tasadaƙar da matar gidan ce ta dawo,bayan iya tsawon lokacin da taɗauka ta shanya su zaman jiran ta kamar wasu dussa.
Bugun takalmin Zainab ya na tafiya tare da bugun zuciyar Juwairiyada take jin tamkar za ta fito,ta rintse idanunta ta na burin a ce baZainab ɗin ba ne take ƙoƙarin shigowa,domin tsoro ya bayyana afuskarta sai take ganin kamar za ta gane dalilin shigowar ta gidan.
Koda ta shigo waya take yi zama ta yi ba tare da ta ce musu komaiba ta ci gaba da wayar ta.
Juwairiya ta kasa ɗago idanunta ta ga matar mijinta na wucin gadiwanda take cikin zuciyar sa yake fifita ta fiye da komai har ya zaɓiya cutar da rayuwarta duk akan ya farnta mata.
Amma idanuwanta sun kasa haɗa ido da ita hasalima ko ɗagowa bata yi ba, duk da ta fahimci ta gama wayar da take yi bayan ta ɗaukirabin awa.
“ Am Atine na ɓata miki lokaci ko?”
Tambayar da ta yi mata kenan ta na kallon matar da ta kusa jika daita a yatsine.
“ Ba komai Hajiya dama me aikin ne da muka yi magana damegidan ki na kawo miki.”Ta ce mata ta na kallonta.
“ Ok.”
Abin da tace kenan ta janyo wayarta ta kunna data yayin datsaƙwanni suke ta shigowa ta na duba wayar har na tsawonlokaci,daga bisani ta kashe ta kalle su duka daidai lokacin daJuwairiya ta yi sa’ar yaƙar idanunta, na tsoron haɗa ido da ita dasuke ta kalle ta, don ta ga wannan mace mai ji da kanta da wulaƙanta mutane.
Karab idanun su duka suka haɗu da juna Juwairiya da ƙyar ta yinasarar daƙile gangar jikinta da yake shirin tashi da zura da guduganin kalar matar da A.m yake aure.
“ An ya ƴar Nigeriya ce?”
Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki domin yanayin ta da kyantasurar ta gabaki ɗaya ya tsorata ta,saboda hasken ta har wani kasheido yake yi sosai da ta yi duba ga kalar fatar jikinta sai ta ga ta yibaƙa wuluk kamar gawayi,duk da ya ba kyan fatarta da ƙawayentasuke yi.
Zainab kuwa wani irin tsanar ta ya shiga ranta haka kawai sai ta jiba ta kwanta mata ba,ba wai kuma kyan da ta gani ba ne ya tsoratata a‘a ita sheda ne akan A.m ko ƴan mata larabawa za ta kawo mishiba zai yi dubi garesu ba, duba ga yadda ta sha wahala kafin yaamince da ita sannan tun da su kai aure ba ta taɓa jin ya yi maganarwata ko wata ta kira shi ba.
Amma sam Juwairiya ba ta yi mata ba saboda daga ganin ta za ta yimunafunci ganin yadda take duƙar da kanta ƙasa-ƙasa.
“ Atine an ya wannan ƴarinyar kina ganin ta yi?Kin san A.m a kwaishi da ƙyanƙyani ji yanayin shigar ta da wani zumbulelen hijabi kinsan ya na da tsafta, kar ta zo ta na ma na girki ya na shiga sannanwallahi zubin ta bai yi min ba don ni na daina ɗaukar ƴan aikigidahumai ƙauyawa,bai gaya miki ɗakin sa da komai na shi ita za tadin ga gyarawa ba?A can zo wata kawai.”
Juwairiya ta yi ƙasa da kanta jin abin da ta faɗa duk da ranta yaɓace,amma ta yi tunanin fiye da hakan a gurin ta saboda ta karanceta tsaf mace ce mai ɗagawa da nuna ta isa,musamman ga talakawaƙasƙantu irin ta.
Sai kuma ta ji daɗin abin da ta ce ranta ya yi fari ko banza ba za tazauna agidan wannan mai kama da canis ba sai ya zo ya san yaddazai yi da ita,ai dama abin da ya shirya a yi mata kenan shi ya sa yaaure ta ya kawo ta kuma ita ta sai ma kanta don in da ƙwaɗayi akwai wulaƙanci!
Atine ta ji jikinta ya yi sanyi sosai har ta fara tunanin in da za tasamu kuɗin A.m ta mayar masa don ya na ba ta ta kai ma mai kujeruakan bikin ƴarta marainiya wanda mijinta ya mutu ya bar mata.
Sai ta ji kamar ta ce ai mijin ta ne ma ya buƙaci ta kawo ta,amma data yi tunanin ba ta san dalilin da ya sa ka shi ya buƙaci hakan ba saita kama bakinta ta guntse ta ce.” Ai Hajiya Juwairiya a kwai aiki datsafta sosai ta yi aiki da dama shi ya sa na kawo ta,kuma za ki ya basosai sai kin gode min,amma ki gwada ta in ba ta yi miki ba sai akawo wata.Kin sai an gwada akan san na ƙwarai.
“ In ko haka ne ta na buƙatar gyara don sai na canza mata tufafi baza din ga mana girki da shi ba,ni ban san daƙiƙanci da rashinwayewa.”
Ta ce ta na kallon Atine da ta yi hamdala a ranta jin ta amince daita,sai kuma ta kalli Juwairiya ta na mata kallon tsaf irin na ciki dawaje har mutum ya gano munin ka.
“ Ina yini”
Juwairiya ta ce mata ganin ta na mata kallon ke ba kya gaisuwa ne.
Ɗauke idanunta ta yi ba tare da ta amsa gaisuwar ba duk da tatabbata ta ji gaisuwar da ta yi mata.
Sai ta miƙe ta kalli Atine ta ce.“Wash na gaji ba ri na shiga ciki.”Harta fara tafiya sai ta tsaya.
“ Ina fatan Atine ta yi miki bayanin aikin da za ki din ga yi a gidannan? Ina da da tsohuwa da take share-share da ƴan abin da ba’a rasaba.So ke aikin ki kula da ɗakina da na mijina da wankin underwearsɗin mu da girki.Kasancewar ba zama nake ba don yanzu waje zanfara fita na baki amanar gidana, da mijina duk sanda ba na nan kirinƙa kula da abincin sa ruwan wankan shi kayan sawan shi dawanda ko ina nan ke zaki kula da wannan.“
Ta ɗan numfasa ta ɗora da ce wa “ Game da kayan sawar shi irinwanda yake so ina fatan ke ba daƙiƙiya ba ce kuma ba‘ a yi asarantara ba na yi mishi time table a ɗakin sa na kayan da yake saka wasai ki din ga dubawa ki na cire masa.”
Wani iri Juwairiya ta kanta ya yi mata take wani irin zafin kishinmijinta A.m ya taso ya mamaye zuciyarta,har ya hana ta jin abin daZainab take ce wa sai kuma tausayin sa ya kamata matuƙa jin irinballagar mace da yake aure.
Ta ƙara rintse idanunta ta na jin kishin iya adadin masu aikin daZainab ta yi waɗan da suka gama kallon mata miji,kuma a hakayake iƙirarin ya na sonta lallai ta yadda so halitta ce kuma makahone.
“ Ki na ji na ina magana kin yi banza da ni!”
Zainab ta daka mata tsawa ganin ta tafi duniyar tunani.
“ Yi haƙuri ina sauraren ki ne.“
To ba na son shashanci in ina magana duƙar da kunnin ki saitina zaki yi kuma duk na yi magana ki ɗaga kanki.“
Ta ce sannna ta ci gaba da tafiya ta na faɗin.” Atine ba ri na ɗaukomiki abu.”
“ Kut! Na shiga uku A.m ya san halin matar sa ya kawo ni cikingidan nan.”
Ta faɗi ta na jinjina kanta tare da tunanin irin zaman da za su yi daita .A jiyar zuciya ta saki mai ƙarfi jin sakacin da Zainab ta yi damijinta.
Kuɗi masu yawa ta miƙa ma Atine wacce ta sandare dajiranta,saboda har wanka ta yi ta saka kaya shara-shara wanda al‘darta ce zama da irin wannan kayan a gida.
A lokacin Juwairiya ta gaji har ta fara gyangyaɗi ga yunwa dake taƙwaƙwular cikinta.
“ Kin ga na jima ban dawo ba ruwa na watsa ga shi ki yi haƙuri.”
Ta ce da Atine sannan ta kalli Juwairiya .” Ke ki tashi ki fara aikikuma na manta ban gaya miki ba! Ba na son raini da ƙazanta.”
Sai kuma ta ƙwala ma Baba mai aikinta kira da gudu sai ga shi taƙaraso mari ta zabga mata.Banza daƙiƙiya ba na ce miki za‘a yisabuwar mai aiki ba? Da kika gan su sai ki fara nuna mata aikingidan ko sun yi miki kama da irin baƙin da zan yi ne?”Ta tambayetata cikin zafin rai.
“Ki yi haƙuri Hajiya ai ba ki bani umurnin haka ba kuma…”
“ Rufe min baki banza maza ki je ki nuna mata.”
“ Allah ya huci zuciyar ki.”
Ta ce tare da kallon Juwairiya sannan ta ce .” Mu je na nuna mikiaikin.”
Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye ta dafe ƙuncinta don gani takekamar ita ta mara.Zainab ciki ta koma tare da ɗaukar wayarta ta yikiran rabin ranta.
Tsananin tashin hankali Juwairiya ta shige shi ji ta yi tamkar ba za taiya rayuwa a cikin gidan ba,a tare suka share hawaye da Baba sukakuma kalli juna.
“ Ki yi haƙuri Baba haka matar gidan take miki?Gaskiya ba ta damutunci a matsayin ki na wanda kika haife ta.Wai mai masu da shisuka ɗauki talaka shi ba mutum ba ne don kawai ya na nema aƙarƙashin wani sai wulaƙanci.”
Baba ta share hawayenta ta kama hannun Juwairiya ta ce “ Humh bazaki gane ba ne!Hajiya Zainab ta wuce tunanin ki ina tausaya mikiwallahi Allah ya sa kin iya girki.”
Ta ɗan ƙara matsowa kamar ta na tunanin Zainab za ta yi musu laɓeta ce.” Ina gaya miki wacce ta kora ta kawo ki da ta yi abinci juyemata ta yi a jikinta,ta rufe ta da duka wai mijinta ya ce ba ta iyagirki ba.Ni fa ban taɓa ganin mutum irin maigidan nan ba,ya tsanemu sai dai shi baya duka.”
Duk da Juwairiya ta san matsayinta a gidan amma sai da gaban ta yafaɗi ras!Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Da Juwairiya suka shiga kicin kusan ruɗewa ta yi kamar za taihauka,irin dukiyar da aka narka da kayan na‘ura,duk da ta yi aikataugidan masu kuɗi ta san yadda ake sarrafa na’ura amma a ranar yarƙauye ta dawo.
Abinci mai rai da lafiya Juwairiya ta shirya sannan ta shiga ɗakin daaka ba ta wanda Zainab ta yi mata umurnin duk ta yi girki ta yiwanka.
Juwairiya ta da fari kasa amfani da kayan bayin ta yi sai daga baya ahankali ta fara gane yadda ake amfani da shi bayam ta ɓata lokaci tana ƙauyanci.
Juwairiya ta yi mamakin irin kayan da ta jibga mata da sunan ta dunga amfani da shi,haka dai ta shirya ta na ta tunani barkatai a rantayayin da kewar su Mama ya kamata, matuƙa har ta ji hawaye nazuba a ƙuncinta.
Juwairiya na zaune a ɗakin da ya zama mallakinta bayan ta idar dasalla sai kuma ta miƙe da sauri jin kamar Zainab na kiran ta.
Ta na baƙin ƙofar fita daga ɗakin suka yi kicibis da ita za ta shigo.”Ke kurma ne ina kira kin yi banza dani.”
Ta faɗa cikin ɗaga murya.“ Ki yi haƙuri ban ji ki ba ne.”
Ta ce ta na kallonta amma kuma a tsorace take saboda kar ta kaimata mari.Tsaki ta yi.” Maza ki je ki shirya dinning za mu ci abincimijina yanzu zai shigo.Kuma ki cire wannan ƙazamin hijabin na kidon na san ina ya gani ba zai iya cin abincin ba.”
Juwairiya ta ji jikinta ya yi sanyi jin umurnin da ta ba ta domin ba zata iya fita a haka ba,amma sai ba ta ce komai ba ta saɓule hijabin takoma ciki.
Hankalinta ya kwanta da ta tuna a kayanta a kwai hijabi wanda baikai wancan tsawo ba,da sauri ta ɗauko ta saka a jikinta bayan ta sakaturare kamar yadda ta murceta.
Juwairiya na gyara dinning ta ji dirin mota alamun an shigo damota,gaban ta ne ya faɗi ras! Don jikinta ya ba ta masoyin ta ne yadawo haka kawai sai ta ji gaban ta na faɗi.
Da sauri take shirya dinnnig ɗin saboda ta gama ta kauce ma ganinsa,amma sai kafin ta gama ya riga ya shigo ya na takun sa dasarsarfa irin na ingarmar namiji mai jini a jika.
Shigowar sa ya yi daidai da fitowar Zainab daga cikin ɗakinta cikinwata irin shiga ta alfarma,amma fa a gurin sa wanda kuma Juwairiyata ga bai kamata ta fito da irin wannan shigar ba,sanin a kwai ta acikin gidan don har tafi shigar ɗazu rashin kyan tsari.
Da gudu ta faɗa jikin sa ta na dariya cikin farin ciki.
Shigowar sa ya sa Juwairiya ta gane ashe tafiya ya yi saboda direbansa da yake janye da troley ɗin sa guda biyu kuma masu girma.
Duka suke dariya sannan suka faɗa kan kujera suna bayyana iyakewar da sukai ma junan su.
A hankali A.m ya zura ma Juwairiya ido shi har ya manta sun yi daAtine yau za ta kawo ta.Ya ɗauke idanun sa da sauri ganin Zainab tabi in da yake kallo.
“ Hubbina sabuwar mai aikin da Atine ta kawo mana ne,Allah ya sata yi maka sai dai na ganta kamar gidahuma ce ko ina yawo dahijabi,amma haka zamu yi haƙuri da ita don gaskiya na gaji daɗaukar masu aiki.“
A hankali Juwairiya ta ɗago idanunta ta ɗara su akan A.m duk da bata son hakan,amma ta na son ta ji mai zai ce mata.
Ga mamakinta sai ta ga ya taɓe bakin sa ya kalle ta kamar ya gakashi ya ce.” Uhm na gan ta sai dai ki yi mata magana ta kiyayesosai in kuma taƙi dole ki canza wata don kin san halina.”Ya ce ataƙaice sai kuma ya canza maganar ya na kallon Zainab ya ce.“ Nayi missing ɗin ki babyna sati ɗaya da na yi kamar na yishekara,yanzu haka ma ban gama abin da na ke yi ba na baro A.k acan na dawo na ga kyakykyawar fuskar ki.”
Ya faɗa kamar zai yi mata kuka yayin da idanunsa suka bayyanahakan ga Zainab da take kallon sa da wani irin murmushi ta nakashe masa ido.
“ Allah ko zauji ka san ni da kai kamar hanta da jini ne ɗazu ina mawani operation, ka san Allah saura kaɗan na yanka sa ba in da yakamata ba kuma fa kai na ke tunani.”
Dariya suka yi duka ya riƙe hannunta ya ce.” Na san za ki yi fiye dahakan akai na amma ki kula rai ya wuce wasa.”
“ Ke banza wawiya!Ba ki da tarbiya ko?Ko baki ko ya a gida bain ma‘aurata suna magana ki ba su wuri maza wuce daga nan stupidkawai!“
Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye tun lokacin da A.m ya shige tanemi hankalinta ta rasa ji take kamar ta ruga da gudu ta faɗa jikinsa.
Gabaki ɗaya ta manta a wace duniyar take wasu irin zafafan hawayeta ji ya wanke mata fuska, saboda tsananin son da take masa waniirin kishin sa ya tokare mata maƙogaronta, har ta ji ta na son ta yiaman sa don ta na jin ɗacin sa ya na hawowa bakinta.
Muryar Zainab da ta daka mata tsawa ya fargar da ita halin da takecikin da sauri ta ruga da gudu,ta shige ɗakinta har ta na bugewa dabango ƙum!Amma ba ta kula ba don tsoron Zainab take yi sosai aranta.
Ta na shiga cikin ɗakinta ta fasa kuka sai kuma ta toshe bakinta tunako a ina take daga ƙarshe toleit ta shige, ta kulle ta ƙara sakin kukata na buga kanta a bango amma ba ta kula ba ko kaɗan.
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
“ Na shiga uku a haka zan rayu a gidan nan? Na tabbata zuciyata takusan kamuwa da hawan jini!Allah na roƙe ka ka yafe min laifin dana yi maka ka haɗa ni da A.m wanda da ma burin sa ya kawo nigidan sa kishin sa ya yi ajalina!”
Tun daga wannan ranar Juwairiya ba ta ƙara saka shi a idonta bawanda hakan ya tabbatar mata da tafiya ya yi tafiya, ita ma kan tamai gidan ba zama take ba tun safe in ta fita sai dare za ta dawo,takwashi abincin da Juwairiya ta dafa,wanda tun daga ranar farko ta yiamanna da abincinta mai shigen daɗin tsiya,don ko A.m da ya ci yayaba sosai ji ya yi abincinta ya yi kama da wanda yake ci a gidaniyayen sa.
Rashin zaman mutanen gidan haka ya ba Juwairiya damar sakewa agidan kamar na ta ba ta da wani matsalar takura.
Juwairiya a ɗan zaman da suka yi da Zainab ta gane ko ita wace cemace mai son hutu da gata,ga shi ta tsani zaman gida ko da acemijinta na nan ga ta da shegen son ƙwalama kullum ta na yawonsiyo kayan daɗi da ciye-ciye.
Juwairiya ta ɗauki tsawon wata ɗaya a gidan a cikin wata ɗaya taƙara kyau da kuma irin mai da cimar da take yi,ita kanta in ta kallikanta a madubi sai ta ƙara juyawa ta kalli kanta cikin jin daɗinyadda ta sauya,wanda har take zolayar kanta da in ta je gida Mamaba za ta gane ta ba.
Juwairiya ba ta da son jiki ku san duk wani aikin gidan ta ɗauke shishi ya sa kullum gidan ya ke cikin tsananin tsafta da ƙamshi, ita kanta Zainab kullum yabawa take sai dai tsabar girman kanta ba ta taɓanunawa ba.
Aiki ɗaya da yake ɓata ranta shi ne gyaran ɗakin A.m wanda kullumta shiga sai ta yi kuka sosai,musamman da Zainab komai ba taɗaukewa sai ita take gyarawa cikin kuka da zafin kishi.
Ganin yadda Juwairiya take da hankali da natsuwa ga shi mijinta yayaba kuma har ya yi tafiya bai ce komai ba,sai Zainab ta ɗan sakijiki da Juwairiya kaɗan duk da ta san rabuwa za su yi saboda ta isaaure,don haka ta yanke shawarar za ta ɗauko yarinya ta haɗa ta daJuwairiya ta din ga koya mata girki da yadda take gyarangidan,saboda ko baƙi ta yi sai sun ya ba gidanta.
Ta na tsaye a kicin ta na tunanin abin da za ta dafa sai ta ji Zainab taƙwala mata kira,da sauri ta ruga kamar yadda ta buƙata duk lokacinda ta yi kiran ta.
Ba tare da ta kalle ta ba ta na riƙe da jaka ta ci uwar gayu ta ce “ Fita zan yi yau zauji ya na hanya don haka ina son ki shirya abincimasu daɗi.”Fita ta yi ba tare da ta ji mai ta ce ba.
Kwan biyu da dawowar shi da rana ta na shirya abinci a falon cikinsauri take son ta yi ta kammala kafin ya fito,wanda ta yankeshawarar haka ya dace ta din ga kauce mishi ƙila zuciyarta ta hutada raɗaɗin son da take mishi.
Ta na cikin shirya abinci kan dinning ta ji ƙarar kiran waya ya shigosai ta shiga dube-dube a tunanin ta wayar Zainab ce ta manta faita,don sam ba ta kula da A.m da yake bacci ta bayan ta akandoguwar kujera.
Sai dai jin ƙarar wayar ya sa ta gane ba ta Zainab ba ce, wandakuma haka ya ba ta damar fahimtar a kwai mutum a cikin falon.
Kiran wayar ya sa shi juyawa da nufin ya kashe wayar saboda agajiye yake matuƙa! Kwanan nan sam bai samu ya huta ba,ya lalubawayar sa da nufin ya janyo wayar ya kashe bai jita in da yaketsammani ba,tunawa ya yi da jifa da ita da ya yi lokacin da ya shigocikin falon.
Sai ya buɗe idanun sa a wahalce ya na waigen in da yake jin ƙarar taamma tsabar gajiya ya saka shi kasa motsa jikin sa ya ɗauko wayar.
Ganin haka sai ta nufi in da wayar take ta na neman agaji ta ɗaukomasa tare da miƙa masa,yayin da idanunta suke cikin na sa kuma takasa ɗauke ƙwayar idanunta ga barin kallon sa.
Idanu suka zuba ma junan su na tsawon lokaci wanda hakan ya saJuwairiya ta rasa natsuwarta,shi ya fara ɗauke idanun sa ya lumshesu.
A hankali Juwairiya ta tako ta miƙa masa wayar da ta ƙara rurinneman agaji.
Idanun shi ya ƙara maida wa kanta ya na mata kallo ƙasa-ƙasa ya nason ya gano halittarta,don shi zai iya rantsewa bai taɓa yi matakallon cikakke ya san ya take ba,shi dai ya san ya yaba da ita har yaji zai iya aurenta matsayin matar da zai iya aure na kwangila ta haifamishi yaro.
Wayar da ta miƙo masa ya kai hannun sa zai ƙarɓa ya haɗa har dahannunta ya na ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa,da sauriJuwairiya ta janye hannun tare da fara tafiya a hankali da nufin tabargurin don jin wani irin tsau da ta ji jikinta ya yi,yayin da take jinwani ƙarin saƙo daga zuciyarsa ya na aika mata cikin zuciyarta.
“ Juwairaah.”
Ya kira sunanta ba tare da ya miƙe ba cak tsayawa ta yi ba tare da tajiyo ba,haka shi ma ya na kwance ya na kallonta kusan tsawonminti biyu,sai ta jiyo gabanta ne ya buga ras!
Da sauri ta ruga zuwa ɗakinta tare da faɗawa kan gado ta sakigwauron numfashi idanunta ta rufe cikin wata irin murya tace.”Allah na roƙe ka kasa na zama jaruma na gama kwangilata nabar gidan nan kamar yadda na saka ma raina.”
Ta nisa tare da ƙara juyawa ta kuma ce wa.” Haka kawai ka shigocikin rayuwata ka hana zuciyata sukuni.”
Idanunta ta buɗe suka tsarƙe a na A.m da yake tsaye a gefenta ya najin abin da take faɗi,ya kai hannu ya fi sau uku da nufin ya riƙe taamma sai ya kai ma iska nushi don ya na ganin in ya taɓa wata ƴamace bai yi wa Zainab halacci ba.
Ganin ta buɗe ido sai ya ja baya ya haɗe rai hakan sai ya ɗan tsoratahar sai da ta ja da baya ta na kallon shi don ba ta san ya shigo cikinɗakin ba.
“ Ji nan Juwairaah! Ko kaɗan kar ki saka a ranki zan iya rayuwadake kin ga matata kuma iya ɗan zaman ki a cikin gidan nan,kin gairin tsananin son da nake mata don bai kamata sai na gaya miki zakifahimta ba,don na faranta mata na aure ki don haka ki kiyaye dukwani abin da zai sa ki yaudari kan ki,don kin san haka ba mai yuwuwa ba ne sanin kan ki ne ruwa ba tsaran kwando ba ne?”
A hankali ta ɗaga mishi kai ganin ya tsare ta da ido ya na son ya jiamsar tambayar sa.
“ Sannan kar ki ɗauka ko na manta dalilin da ya saka na aure ki ne.”.
Ya juyo ya na kallonta ya ce da ita.” Wallahi na rasa yadda za’ yi nafara ɗaukar ki a matsayin matata don ba mu dace ba,ni sai yanzunake dana sanin da idona da ya rufe na yadda na aure ki,amma dukda hakan zan daure na aiwatar da shirina da zarar kin sami ciki nakai ki wani gurin ki haihu na karɓi yarona mu shafe babinrayuwarmu.”
Ya na kai nan ya fice ba tare da ya lura da kukan da take yi ba nabaƙin cikin tsanar ta da ya yi,sai dai kuma daga ba ya ta dai na jinhaushin kalaman da ya faɗi saboda duk abin da ya faɗa gaskiyane,ita ma ta karɓi auren sa ne saboda ta ta ceci ran mahaifiyarta daɗan’uwanta.
Washegari da safe Juwairiya na kwance hayaniyar masu gidan yatashe su wanda ta kasa gane ko menene,amma ta tabbata ba lafiya bajin yadda suke magana sama-sama musamman muryar Zainabwacce har kukanta ta ji.
Matuƙar tsoro ya kamata ji ta yi ta ƙara mugun tsoron A.m don ba tasan haka yake da tsiya ba.
Ta na zaune a ɗakinta ta yi tsumu so take ta haɗa abin karyawaamma ba zata iya fita ba jin yadda suke ta ɗaga murya kamar za sudambace.
Mamaki ya kama ta sosai wai masoya ne suke irin wannanfaɗar,ganin sun ƙi yin shiru da sauri ta shige kicin ba tare da sun ganta ba,ta fara ɗora abinci jikinta na rawa gani take kamar a kantafaɗan zai ƙare.
Ta na shirya a binci a dinning ta ga A.m da ƙatuwar troley ɗin sa yana ja, ransa kamar an aiko masa da mala’kan mutuwa, ba tare da yakalle ta ba ya fice daga gidan.
Ba’a jima ba sai ga Zainab da na ta jakar ta na waya bayan ta gamawayar ta kalli Juwairiya ta ce “ Ke wai me sunan ki baki gaya minba?Ko ki na jiran na tambayeki ƙila uwar ki zan ci da sunan.”
A hankali Juwairiya ta furta.” Juwairiya sunana.”Yayin da hawayesuka fara turereniya a fuskarta.
Tsaki ta saki.” ko ma mene ne ni tafiya zan yi kuma ƙasar zan bari,ban ce kije ko ina ba kar a kwashi kayana akai gidan matsiyata,kikula min da gidana duk abin da kike so ga waya ki kira ni in damatsala.”
Jefa mata wayar ta yi a jikinta ta fice ba tare da ta yi tunanin za taiya fashewa ba.
Tsananin mamaki ya kama Juwairiya yanzu ne ta gane musabbabinfaɗar su.Da sauri ta leƙa ta windo don idanunta su fita da shakkunkayan da ta saka za ta ƙetare wata ƙasa a matsayin ta na matar aure.
Haka ta wuni sukuku daga kallo sai kwanciya tunna ba masu gidanda za ta yi musu girki.Da daddare sai ta kasa bacci saboda ita kaɗaine sai masu gadi,Baba in ta gama ayyukanta gida take tafiya sabodaba ta da nisa sosai da gidan.
Kasa bacci ta yi ta na ta juye-juye girman gidan yake matuƙartsorata ta, sai take ganin kamar wani zai shigo ga ihun karnikangidan da suka hana kunninta saƙat!
Da ga ƙarshe ma tashi ta yi ta ɗauro alwala ta yi sallah sannan taɗauki alkur’ani ta na karatun suratul Ali imran don ta samu ta yibacci.
A ƙalla mutane gidan sai da suka yi sati biyu ba su dawo ba.A.m yafara dawowa ranar talata da rana dama tun da safe Zainab ta kiraJuwairiya ta gaya mata zai dawo ,don haka ta shirya abinci wandaZainab ta saka direba ya siyo duk kayan buƙata na girki.
Misalin biyu da rabi ya shigo da jakar shi rataye a kafaɗar sa,sai daikamar mahaukaci ya shigo saboda zargin sa da yake na Zainab ta yitafiya zuwa Dubai saro kaya duk da ya hana ta.
Duk da cewa ta ji shigowar shi sai ba ta fita ba ta yi zaman ta a ɗakita na jan carbi,domin ta sama ma kanta natsuwa.
“ Ina Zainab?”
Muryar sa ta ji lokacin da ya banko ƙofa ya shigo da sauri ta matsaganin kamar zai kai mata duka lokacin da yake tambayarta.
Ba ta ba shi amsa ba amma yanayin da take kallon sa ya tabbatarmasa da Zainab ta tafi duk da gargaɗin ta da ya yi,cikin ɓacin rai yalailayo ashar zai yi ko me ya tuna sai ya fasa ya fita cikin ɗakin dasauri.
Juwairiya da sauri ta bi bayan sa saboda tashin hankalin da ta ga yashiga,abincin da ta girka masa ya yi jifa da kwanonin da suke jere adinning ɗin,ya zaro wayar sa ya kira ta sai dai har ta gama ringingba ta ɗauka ba.
Jifa ya yi da wayar ta faɗi a kan tayas ta fashe ya dunƙule hannun saguri ɗaya ya furta.” Zainab ki na son sa min hawan jini sai daiwannan karan ba zan ɗauki wannan iskancin ba,ina mijin ki kitsallake ki tafi wata ƙasa hakan ba zai yiwu ba.
Idanun Juwairiya suka kawo ruwa sai hawaye ganin ita kuma hakaAllah ya ƙaddara rayuwar ta su dun ga sauke fushin su akan ta.
“ Ke!”
Ya daka mata tsawar da ya firgita ta sannan ya ci gaba da magana dace wa.” Wallahi yanzu jikin ki zai gaya miki dukan ki na yi zakisaka min kuka bayan na gaya miki na tsani kuka a rayuwata,mazafice ki ba ni guri sannan ki ƙara min wani abincin.
Hakan ya ƙara saka ta sakin wani kukan tuna yadda ta sha wahalargirkin ya zubar kuma yake buƙatar ta ƙara yi masa.
Da sauri ta wuce kicin ta bar shi a falon ya kai gwauro ya kai marida ga ƙarshe wayar sa ya ɗauka da nufin ya kira A.k,sai dai kuma yaga aika-aikar da ya yi tsaki ya yi da nufi ɗaki don ya ɗauko wata.
Bai jima ba ya fito bayan ya yi wanka ya canza kaya ko kallonabincin da ta girka bai yi ba ya fice daga gidan.
A haka suke ta zama na rashin daɗi duk da A.m na buƙatar ya kawoƙarshen zamanta a gidan amma ya kasa,haka dai yau ya daure danufin zai yaƙi zuciyar sa don ta bar mishi gidan sa saboda ba ya songanin ta a ciki.
Da misalin biyar da rabi ya dawo gida Juwairiya na falo ta na kalloda ƙaton hijabin ta,ya na hango ta ya tsaki wawan tsaƙi saboda shihaushin hijaban da take sawa yake yi bayan ta san ko shi wanene agurin ta.
“ Wawiya ƙazamiya a haka yadda kike ɓoye jikin ki ko uban metake ɓoyewa shi bai ga abin sha’awa a jikin ta ba.”
Ganin sa ya sa ta miƙe da sauri za ta shige cikin ɗakin ta.
“Ke.”
Tsayawa ta yi ba tare da ta kalle shi ba don ta san wani wulaƙancinzai yi mata.
Hararar ta ya yi ya zauna akan kujera tare da ɗaukar remote yacanza tasha,sannan ya kalle ta ya ce “ Gidan uban wa za ki sabodadodo ya dawo ko?Wai haka kika ga matan aure suna rayuwa a gidanmazajen su kullum cikin hijabi ke sam baki da wayewa ne?”
Juwairiya ta yi sororo ta na kallon shi jin wani sabon salon da ya fitoda shi,amma ba ta ce masa komai ba sai kallon shi da take tamkarbaƙo a gare ta.
“ Maza ki je ki kawo min abinci.”
Ya ce ganin ta kafe shi da ido ba ta san shi ma ransa a ɓace yakemaganar ba saboda tsanar ta da yake ji kuma wai ta na matsayinmatar sa.
Juwairiya ta so ta bi umurni n shi ta cire hijabin sai dai ina sam baza ta iya ba,don tsananin kunyar shi take da ke,don haka ta ƙi cirehijabin ta ɗauko abincin ta na ije mishi ta ruga zuwa ɗaki.
Bayan ya ci abinci ya na zaune a falon har aka kira magariba ya yisallah bai dawo ba sai da aka kira isha’i,sannan ya dawo gida ya rufegidan duk da ran sa a ɓace yake akan Zainab kuma ya rantse in tadawo sai ta ga abin da zai yi mata,amma sai ya daure ya ɗaukiwayar sa ya shiga ɗakin.
“ Ki biyo ni ɗakina kin san ba zan iya kwana a ɗakin ƙasƙantu ƴanaiki ba.”
Ya fice kallon sa kawai ta yi amma ba ta ce mishi komai ba har yafita ta gyara kwanciyar ta tare da karanto addu’ar bacci ta janyobargo ta kwanta.
“ Wataƙila maganar Baba Sani ta yi tasiri a zuciyar sa ya yadda bani da kamun kai ne har yake tunanin na bi shi ɗakin sa a she zaibushe da jira na.
Washegari da safe bai ci ko abincin karyawar da ta yi masa ba yafice daga gidan, don ko da ta gaishe shi harara ya banka mata.
Sai abin ya ba ta dariya kawai ta ruga da sauri ta laɓe a ƙofar falonta na kallon sa har ya fice saboda wankan da ya yi ya tafi da imaninta.
Sakin labulen ta yi ta zauna a falo tare da ɗaukar filo ta rungume aƙirjinta ta na jin wani irin nishaɗi, don ko kaɗan ba ta yi tunaninrayuwa tare da shi ba ko da kuwa a matsayin matar sa kuma ƴaraikin matar sa.
Bai shigo gidan ba sai da daddare tare da A.k suka shigo suna tahira abin su.
A.k na ta baza ido ya gan ta bai gan ta ba musamman da ya gaZainab ba ta nan,kallon A.m ya yi da yake ta aika ma cikin sa abincisaboda tun zuwan Juwairiya gidan hankalin sa ya kwanta na rashinsamun abinci.
“ Kai wai ina maryar ka ne ?Tun na yanzu madam ba ta nan na sanƙila an samu baby?”
Ya faɗa ya na kallon shi ya na dariya tare da kai mishi duka akafaɗan sa.Taɓe baki ya yi ya ce.Ina zan sani kai kyale ni da waniamarci Juwairiya muguwar bagidajiya ce kullum cikin hijabi ka sankuma ba haka Zainab take min ba.”
Ya ɗan kalli A.k da ya daina cin abincin ya na sauraron sa yace.”Jiya da na kira ta ɗakina ƙin zuwa ta yi ban san tunanin ta a kaina ba.”
“ To kai in ban da abin ka A.m ai kai za ka bi ta kuma kuma macetake Hausa dole ta ji kunya.”
A k ya ce da shi ya na kallon sa.A.m ya ƙara taɓe bakin sa ya ce.”Ok ka manta abin da ƙanin mahaifinta ya ce a kan ta ni ban ga abinkunya ba.”
“A haba A.m ka san halin sa kar ka yadda da maganar sa kumakoma mene ne kai ka amince za ka aure ta sai ka ba da azama musami baby.”.
Dariya suka yi duka daga bisani A.k ya matsa mishi ya kira ta sugaisa ya na zaune ya ƙwala mata kira ba ta jima ba sai ga shi tafito,kamar dama laɓe take musu ta na jin maganar da suke yi.
A.m tashi ya yi ya nufi ɗakin sa zai ɗauko tsaƙon da A.k ya biyo shiya karɓa ba tare da ya kalle ta ba.
Da ladabi ta gaishe shi ya amsa ya na ta tsokanar ta dai murmushitake masa.
“ Na so mu haɗu kafin ayi auren ki da shi sai dai kuma Allah bainufa ba ko Juwairiya?”
Ya faɗa tare da mai da maganar ta tsigar tambaya.Ɗaga masa kan tata yi ta na kallon shi “ Ok ba komai da ma na so na ɗan miki watamagana ne Juwairiya don Allah duk yadda zuciyar ki za tai ki karkiyadda ki saka son A.m a ran ki kawai ki sama ran ki zaki ci arziki kitafi ne.Ki ɗauke ni a matsayin Yayan ki duk lokacin da wata matsalata haɗa ku ki sanar da ni.”
Ya yi maza ya ƙarashe maganar jin takun A.m daga matakalarbene.Kallon sa ta yi sai kuma ta ji ya burge ta sosai yadda bai ɗaukirayuwar sa da zafi ba.
Ɗaga masa kanta ta yi alamun ta ji amma kuma a cikin zuciyarta saita ce.
“ Ka makaro A.k da ce wa ka yi na yaƙi zuciyata da take son sa ƙilada na karɓi shawarar ,amma na riga na daɗe da shiga cikin koginson sa.”
Sai da A.m ya yi masa rakiya sannan ya dawo ya tsaya ya na kallonJuwairiya da ta kasa tashi ta na ta tunani a ranta.” Me hawayenbanza maza ki tashi ki gyara min ɗakina saboda yau haushina dakike ji sai kika huce akan ɗakin,sam gyaran bai yi kuma ki ƙarawanke bayi.”
Ya faɗa tare da zama a falon kamar ya na son ta gama sai ya shigo.
Wucewa cikin ɗakin ta yi ba tare da ta ce masa komai ba amma yafaɗi son ransa ne kawai duba ga yadda take ba da dukkan lokacin tain ta je ɗakin sa gyara.
A.m ya na ganin ta shige ya bi ta tare da tura ƙofar a hankali ganinya shigo ta tsaya dama tun da ta shigo ta rasa mai za ta gyara sabodaɗakin ya na tsaftace da kyan sa.
“ Ki zo mu kwanta a gadon da baki taɓa hawa ba amma albarkacinaurena zai saka ki din ga moresa in matar so ba ta nan.”
Hawaye suka wanke mata fuska ba ta ce mishi komai ba kuma ba tamotsa ba bare ya saka ran za ta hawo,asalima gaban ta ne ya faɗiras!
Hannunta ya jawo ya na faɗin.” Na lura kuka shi ne farin cikin ki toki sani ba zan taɓa buɗe bakina rarrashe ki ba,ko na ɗauki hannunana share miki hawaye da su.
Yanayin da suka shiga a ranar yanayi ne mara fasaltuwa dabayyanuwa a gare su musamman Juwairiya da ta sha kuka har tagode ma Allah,domin kwana ta yi ta na kuka ko kaɗan ba ta bar shiya rintsa ba,wanda in ta tuna dalilin kukan na ta biyu ne sai ta ƙarasakin wani kuka.
A.m da bacci ya fara ɗaukar sa a hankali bayan wata sabuwarduniya da ya shiga kuma ya kasa fahimtar wace duniya yakeciki,kukan da take yi ya na ɗaga masa hankali ya yi maganar duniyataƙi yin shiru,har ya gaji ya ƙyaleta ya rintse idanun sa da ƙarfi ya nason bacci ya ɗauke sa.
Ganin taƙi dai na kukan ya janye bargon da ya ƙudundune kan sa dashi ya kunna fitilar ɗakin.”
Ke wai ke.”
Sai kuma ya yi shiru daga ninyar faɗar da yake ya yi mata ya ɗansausauta murya ganin dare ne ya ce.” Ko fa wace mace da kika ganta a gidan mijinta da haka ta fara.Kuma idan bakya son haka ba saiki gaya min ki gode ma Allah auren kwangila muka yi so ba daɗewa za ki yi da ni ba.”
Hakan sai ya saka Juwairiya ta ƙara fashewa da kuka ganin ta ba mamutumim da ya tsane ta rayuwarta,ga shi bai san mahimmancin taba bayan wahalar da ta sha yake gaya mata waɗannan kalamai.
Bakinta ta murguɗa a ranta ta ce.” Mugu kawai azzalimi.”sai kumata ci gaba da kukanta wanda A.m ya lura harda shagwaɓa don shi yagama fahimtar ta shegen shagwaɓa ne da ita shi ya sa da an yimagana sai kuka.
Wani irin walƙiya a ka saki lokaci guda aka fara tsawa nan ne A.mya fahimci garin hadari ne ya taso,da sauri ya sauka don ya duba kowindina a kulle ne kawai sai ya tsinci kan shi da jin daɗin ya na yingarin har ya buɗe labule ya na shaƙar iskar gurin.
Iskar ya ƙara ma Juwairiya zazzaɓin da ta ji ya saukar mata ganinhaka sai ya rufe windon ya na addu’ar Allah ya sa ta yi shirukenan,jin ta sassauta sautin kukan da take yi sai ya koma ya zauna.
Wayar sa ta fara ruri da sauri ya ɗauka don gabansa ya faɗi ya natunanin waye da daddare zai kira shi,ganin numbar masoyiyar sa yasa shi miƙewa da sauri take ɓacin rai ya bayyana a fuskar sa.
A wannan lokacin da yake duba wayar sa aka tsuge da ruwa sosaikamar da bakin ƙwarya.
Zubbur ya miƙe ganin numbar Zainab ce ya yi kamar ba zai ɗaukaba,saboda tun da ya gaya mata zai dawo ta de na ɗaukar wayar saashe mara mutuncin tafiya ta yi tabar ƙasar.Sai kuma ya kangawayara a kunnin cikin tsanani ɓacin rai a ransa ya na tunanin Allahkawai zai raba ta da shi.
“ Hello zauji don Allah gani a airport ka zo ka ɗauke ni kuma nasamu ƴar matsala da kayana har mutumim ya na min barazana.Gakuma ruwa da ake yi kazo ka ji zauji.”
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ya kalli Juwairiya da takecikin wani hali don shi kan sa ya san ya wuce gona da iri,kuma batare da sanin haka ba ya kuma kalli kansa da har yanzu ya kasatantance duniyar da yake ci.
Tunani ya fara yi ko Zainab ta hauka ce ne da za ta dawo da tsakardare sai ya ɗauki wayarsa da nufin ya duba lokaci, ai wallahi ba zaifita yanzu ba sai dai koma mene ne ya faru musamman da ta ɓatamasa rai ta yi tafiya ba tare da izinin sa ba.
Tsananin mamaki ya kama sa da agogon wayar sa ya nuna mishiƙarfe biyar da mintuna,ya na cikin kokwanton ko wayar sa ce saitinta ya goce sai ya ji ladani ya kwaɗa kiran sallah.
Da sauri ya yaye labulen ɗakin don ya ƙara tabbatar ma kansa takekuwa ya ga har hasken alfijir ya keto gari ya fara wayewa..
Sai hankalin shi ya ƙara tashi musamamn da Zainab ta turo masatsaƙon ba sai ya zo ba,don sun daidaita da mutumim yanzu haka masuna hanyar gida,saboda mijin Anti Fati ya turo direba ya ɗauke sukuma duka za suzo gidan.
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]