[Advertisements⬇️]

SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 18 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tun daga wannan ranar Juwairiya ba ta ƙara saka shi a idonta bawanda hakan ya tabbatar mata da tafiya ya yi tafiya, ita ma kan tamai gidan ba zama take ba tun safe in ta fita sai dare za ta dawo,takwashi abincin da Juwairiya ta dafa,wanda tun daga ranar farko ta yiamanna da abincinta mai shigen daɗin tsiya,don ko A.m da ya ci yayaba sosai ji ya yi abincinta ya yi kama da wanda yake ci a gidaniyayen sa.

Rashin zaman mutanen gidan haka ya ba Juwairiya damar sakewa agidan kamar na ta ba ta da wani matsalar takura.

Juwairiya a ɗan zaman da suka yi da Zainab ta gane ko ita wace cemace mai son hutu da gata,ga shi ta tsani zaman gida ko da acemijinta na nan ga ta da shegen son ƙwalama kullum ta na yawonsiyo kayan daɗi da ciye-ciye.

Juwairiya ta ɗauki tsawon wata ɗaya a gidan a cikin wata ɗaya taƙara kyau da kuma irin mai da cimar da take yi,ita kanta in ta kallikanta a madubi sai ta ƙara juyawa ta kalli kanta cikin jin daɗinyadda ta sauya,wanda har take zolayar kanta da in ta je gida Mamaba za ta gane ta ba.

Juwairiya ba ta da son jiki ku san duk wani aikin gidan ta ɗauke shishi ya sa kullum gidan ya ke cikin tsananin tsafta da ƙamshi, ita kanta Zainab kullum yabawa take sai dai tsabar girman kanta ba ta taɓanunawa ba.

Aiki ɗaya da yake ɓata ranta shi ne gyaran ɗakin A.m wanda kullumta shiga sai ta yi kuka sosai,musamman da Zainab komai ba taɗaukewa sai ita take gyarawa cikin kuka da zafin kishi.

Ganin yadda Juwairiya take da hankali da natsuwa ga shi mijinta yayaba kuma har ya yi tafiya bai ce komai ba,sai Zainab ta ɗan sakijiki da Juwairiya kaɗan duk da ta san rabuwa za  su yi saboda ta isaaure,don haka ta yanke shawarar za ta ɗauko yarinya ta haɗa ta daJuwairiya ta din ga koya mata girki da yadda take gyarangidan,saboda ko baƙi ta yi sai sun ya ba gidanta.

Ta na tsaye a kicin ta na tunanin abin da za ta dafa sai ta ji Zainab taƙwala mata kira,da sauri ta ruga kamar yadda ta buƙata duk lokacinda ta yi kiran ta.

Ba tare da ta kalle ta ba ta na riƙe da jaka ta ci uwar gayu ta ce Fita zan yi yau zauji ya na hanya don haka ina son ki shirya abincimasu daɗi.”Fita ta yi ba tare da ta ji mai ta ce ba.

Kwan biyu da dawowar shi da rana ta na shirya abinci a falon cikinsauri take son ta yi ta kammala kafin ya fito,wanda ta yankeshawarar haka ya dace ta din ga kauce mishi ƙila zuciyarta ta hutada raɗaɗin son da take mishi.

Ta na cikin shirya abinci kan dinning ta ji ƙarar kiran waya ya shigosai ta shiga dube-dube a tunanin ta wayar Zainab ce ta manta faita,don sam ba ta kula da A.m da yake bacci ta bayan ta akandoguwar kujera.

Sai dai jin ƙarar wayar ya sa ta gane ba ta Zainab ba ce, wandakuma haka ya ba ta damar fahimtar a kwai mutum a cikin falon.

Kiran wayar ya sa shi juyawa da nufin ya kashe wayar saboda agajiye yake matuƙa! Kwanan nan sam bai samu ya huta ba,ya lalubawayar sa da nufin ya janyo wayar ya kashe bai jita in da yaketsammani ba,tunawa ya yi da jifa da ita da ya yi lokacin da ya shigocikin falon.

Sai ya buɗe idanun sa a wahalce ya na waigen in da yake jin ƙarar taamma tsabar gajiya ya saka shi kasa motsa jikin sa ya ɗauko wayar.

Ganin haka sai ta nufi in da wayar take ta na neman agaji ta ɗaukomasa tare da miƙa masa,yayin da idanunta suke cikin na sa kuma takasa ɗauke ƙwayar idanunta ga barin kallon sa.

Idanu suka zuba ma junan su na tsawon lokaci wanda hakan ya saJuwairiya ta rasa natsuwarta,shi ya fara ɗauke idanun sa ya lumshesu.

A hankali Juwairiya ta tako ta miƙa masa wayar da ta ƙara rurinneman agaji.

Idanun shi ya ƙara maida wa kanta ya na mata kallo ƙasa-ƙasa ya nason ya gano halittarta,don shi zai iya rantsewa bai taɓa yi matakallon cikakke ya san ya take ba,shi dai ya san ya yaba da ita har yaji zai iya aurenta matsayin matar da zai iya aure na kwangila ta haifamishi yaro.

Wayar da ta miƙo masa ya kai hannun sa zai ƙarɓa ya haɗa har dahannunta ya na ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa,da sauriJuwairiya ta janye hannun tare da fara tafiya a hankali da nufin tabargurin don jin wani irin tsau  da ta ji jikinta ya yi,yayin da take jinwani ƙarin saƙo daga zuciyarsa ya na aika mata cikin zuciyarta.

                            Juwairaah.”

Ya kira sunanta ba tare da ya miƙe ba cak tsayawa ta yi ba tare da tajiyo  ba,haka shi ma ya na kwance ya na kallonta kusan tsawonminti biyu,sai ta jiyo gabanta ne ya buga ras!

Da sauri ta ruga zuwa ɗakinta tare da faɗawa kan gado ta sakigwauron numfashi idanunta ta rufe cikin wata irin murya tace.”Allah na roƙe ka kasa na zama jaruma na gama kwangilata nabar gidan nan kamar yadda na saka ma raina.”

Ta nisa tare da ƙara juyawa ta kuma ce wa.” Haka kawai ka shigocikin rayuwata ka hana zuciyata sukuni.”

Idanunta ta buɗe suka tsarƙe a na A.m da yake tsaye a gefenta ya najin abin da take faɗi,ya kai hannu ya fi sau uku da nufin ya riƙe taamma sai ya kai ma iska nushi don ya na ganin in ya taɓa wata ƴamace bai yi wa Zainab halacci ba.

Ganin ta buɗe ido sai ya ja baya ya haɗe rai hakan sai ya ɗan tsoratahar sai da ta ja da baya ta na kallon shi don ba ta san ya shigo cikinɗakin ba.

Ji nan Juwairaah! Ko kaɗan kar ki saka a ranki zan iya rayuwadake kin ga matata kuma iya ɗan zaman ki a cikin gidan nan,kin gairin tsananin son da nake mata don bai kamata sai na gaya miki zakifahimta ba,don na faranta mata na aure ki don haka ki kiyaye dukwani abin da zai sa ki yaudari kan ki,don kin san haka ba mai yuwuwa ba ne sanin kan ki ne ruwa ba tsaran kwando ba ne?”

A hankali ta ɗaga mishi kai  ganin ya tsare ta da ido ya na son ya jiamsar tambayar sa.

Sannan kar ki ɗauka ko na manta dalilin da ya saka na aure ki ne.”.

Ya juyo ya na kallonta ya ce da ita.” Wallahi na rasa yadda za’ yi nafara ɗaukar ki a matsayin matata don ba mu dace ba,ni sai yanzunake dana sanin da idona da ya rufe na yadda na aure ki,amma dukda hakan zan daure na aiwatar da shirina da zarar kin sami ciki nakai ki wani gurin ki haihu na karɓi yarona mu shafe babinrayuwarmu.”

Ya na kai nan ya fice ba tare da ya lura da kukan da take yi ba nabaƙin cikin tsanar ta da ya yi,sai dai kuma daga ba ya ta dai na jinhaushin kalaman da ya faɗi saboda duk abin da ya faɗa gaskiyane,ita ma ta karɓi auren sa ne saboda ta ta ceci ran mahaifiyarta daɗan’uwanta.

Washegari da safe Juwairiya na kwance hayaniyar masu gidan yatashe su wanda ta kasa gane ko menene,amma ta tabbata ba lafiya bajin yadda suke magana sama-sama musamman muryar Zainabwacce har kukanta ta ji.

Matuƙar tsoro ya kamata ji ta yi ta ƙara mugun tsoron A.m don ba tasan haka yake da tsiya ba.

Ta na zaune a ɗakinta ta yi tsumu so take ta haɗa abin karyawaamma ba zata iya fita ba jin yadda suke ta ɗaga murya kamar za sudambace.

Mamaki ya kama ta sosai wai masoya ne suke irin wannanfaɗar,ganin sun ƙi yin shiru da sauri ta shige kicin ba tare da sun ganta ba,ta fara ɗora abinci jikinta na rawa gani take kamar a kantafaɗan zai ƙare.

Ta na shirya a binci a dinning ta ga A.m da ƙatuwar troley ɗin sa yana ja, ransa kamar an aiko masa da mala’kan mutuwa, ba tare da yakalle ta ba ya fice daga gidan.

Ba’a jima ba sai ga Zainab da na ta jakar ta na waya bayan ta gamawayar ta kalli Juwairiya ta ce Ke wai me sunan ki baki gaya minba?Ko ki na jiran na tambayeki ƙila uwar ki zan ci da sunan.”

A hankali Juwairiya ta furta.” Juwairiya sunana.”Yayin da hawayesuka fara turereniya a fuskarta.

Tsaki ta saki.” ko ma mene ne ni tafiya zan yi kuma ƙasar zan bari,ban ce kije ko ina ba kar a kwashi kayana akai gidan matsiyata,kikula min da gidana duk abin da kike so ga waya ki kira ni in damatsala.”

Jefa mata wayar ta yi a jikinta ta fice ba tare da ta yi tunanin za taiya fashewa ba.

Tsananin mamaki ya kama Juwairiya yanzu ne ta gane musabbabinfaɗar su.Da sauri ta leƙa ta windo don idanunta su fita da shakkunkayan da ta saka za ta ƙetare wata ƙasa a matsayin ta na matar aure.

Haka ta wuni sukuku daga kallo sai kwanciya tunna ba masu gidanda za ta yi musu girki.Da daddare sai ta kasa bacci saboda ita kaɗaine sai masu gadi,Baba in ta gama ayyukanta gida take tafiya sabodaba ta da nisa sosai da gidan.

Kasa bacci ta yi ta na ta juye-juye girman gidan yake matuƙartsorata ta, sai take ganin kamar wani zai shigo ga ihun karnikangidan da suka hana kunninta saƙat!

Da ga ƙarshe ma tashi ta yi ta ɗauro alwala ta yi sallah sannan taɗauki alkur’ani ta na karatun suratul Ali imran don ta samu ta yibacci.

A ƙalla mutane gidan sai da suka yi sati biyu ba su dawo ba.A.m yafara dawowa ranar talata da rana dama tun da safe Zainab ta kiraJuwairiya ta gaya mata zai dawo ,don haka ta shirya abinci wandaZainab ta saka direba ya siyo duk kayan buƙata na girki.

Misalin biyu da rabi ya shigo da jakar shi rataye  a kafaɗar sa,sai daikamar mahaukaci ya shigo saboda zargin sa da yake na Zainab ta yitafiya zuwa Dubai saro kaya duk da ya hana ta.

Duk da cewa ta ji shigowar shi sai ba ta fita ba ta yi zaman ta a ɗakita na jan carbi,domin ta sama ma kanta natsuwa.

                  Ina Zainab?”

Muryar sa ta ji lokacin da ya banko ƙofa ya shigo da sauri ta matsaganin kamar zai kai mata duka lokacin da yake tambayarta.

Ba ta ba shi amsa ba amma yanayin da take kallon sa ya tabbatarmasa da Zainab ta tafi duk da gargaɗin ta da ya yi,cikin ɓacin rai yalailayo ashar zai yi ko me ya tuna sai ya fasa ya fita cikin ɗakin dasauri.

Juwairiya da sauri ta bi bayan sa saboda tashin hankalin da ta ga yashiga,abincin da ta girka masa ya yi jifa da kwanonin da suke jere  adinning ɗin,ya zaro wayar sa ya kira ta sai dai har ta gama ringingba ta ɗauka ba.

Jifa ya yi da wayar ta faɗi a kan tayas ta fashe ya dunƙule hannun saguri ɗaya ya furta.” Zainab ki na son sa min hawan jini sai daiwannan karan ba zan ɗauki wannan iskancin ba,ina mijin ki kitsallake ki tafi wata ƙasa hakan ba zai yiwu ba.

Idanun Juwairiya suka kawo ruwa sai hawaye ganin ita kuma hakaAllah ya ƙaddara rayuwar ta su dun ga sauke fushin su akan ta.

                              Ke!”

Ya daka mata tsawar da ya firgita ta sannan ya ci gaba da magana dace wa.” Wallahi yanzu jikin ki zai gaya miki dukan ki na yi zakisaka min kuka bayan na gaya miki na tsani kuka a rayuwata,mazafice ki ba ni guri sannan ki ƙara min wani abincin.

Hakan ya ƙara saka ta sakin wani kukan tuna yadda ta sha wahalargirkin ya zubar kuma yake buƙatar ta ƙara yi masa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Da sauri ta wuce kicin ta bar shi  a falon ya kai gwauro ya kai marida ga ƙarshe wayar sa ya ɗauka da nufin ya kira A.k,sai dai kuma yaga aika-aikar da ya yi tsaki ya yi da nufi ɗaki don ya ɗauko wata.

Bai jima ba ya fito bayan ya yi wanka ya canza kaya ko kallonabincin da ta girka  bai yi ba ya fice daga gidan.

A haka suke ta zama na rashin daɗi duk da A.m na buƙatar ya kawoƙarshen zamanta a gidan amma ya kasa,haka dai yau ya daure danufin zai yaƙi zuciyar sa don ta bar mishi gidan sa saboda ba ya songanin ta a ciki.

Da misalin biyar da rabi ya dawo gida Juwairiya na falo ta na kalloda ƙaton hijabin ta,ya na hango ta ya tsaki wawan tsaƙi saboda shihaushin hijaban da take sawa yake yi bayan ta san ko shi wanene agurin ta.

Wawiya ƙazamiya a haka yadda kike ɓoye jikin ki ko uban metake ɓoyewa shi bai ga abin sha’awa a jikin ta ba.”

Ganin sa ya sa ta miƙe da sauri za ta shige cikin ɗakin ta.

                           “Ke.”

Tsayawa ta yi ba tare da ta kalle shi ba don ta san wani wulaƙancinzai yi mata.

Hararar ta ya yi ya zauna akan kujera tare da ɗaukar remote yacanza tasha,sannan ya kalle ta ya ce Gidan uban wa za ki sabodadodo ya dawo ko?Wai haka kika ga matan aure suna rayuwa a gidanmazajen su kullum cikin hijabi ke sam baki da wayewa ne?”

Juwairiya ta yi sororo ta na kallon shi jin wani sabon salon da ya fitoda shi,amma ba ta ce masa komai ba sai kallon shi da take tamkarbaƙo a gare ta.

Maza ki je ki kawo min abinci.”

Ya ce ganin ta kafe shi da ido ba ta san shi ma ransa a ɓace yakemaganar ba saboda tsanar ta da yake ji kuma wai ta na matsayinmatar sa.

Juwairiya ta so ta bi umurni n shi ta cire hijabin sai dai ina sam baza ta iya ba,don tsananin kunyar shi take da ke,don haka ta ƙi cirehijabin ta ɗauko abincin ta na ije mishi ta ruga zuwa ɗaki.

Bayan ya ci abinci ya na zaune a falon har aka kira magariba ya yisallah bai dawo ba sai da aka kira isha’i,sannan ya dawo gida ya rufegidan duk da ran sa a ɓace yake akan Zainab kuma ya rantse in tadawo sai ta ga abin da zai yi mata,amma sai ya daure ya ɗaukiwayar sa ya shiga ɗakin.

Ki biyo ni ɗakina kin san ba zan iya kwana a ɗakin ƙasƙantu ƴanaiki ba.”

Ya fice kallon sa kawai ta yi amma ba ta ce mishi komai ba har yafita ta gyara kwanciyar ta tare da karanto addu’ar bacci ta janyobargo ta kwanta.

Wataƙila maganar Baba Sani ta yi tasiri a  zuciyar sa ya yadda bani da kamun kai ne har yake tunanin na bi shi ɗakin sa a she zaibushe da jira na.

Washegari da safe bai ci ko abincin karyawar da ta yi masa ba yafice daga gidan, don ko da ta gaishe shi harara ya banka mata.

Sai abin ya ba ta dariya kawai ta ruga da sauri ta laɓe a ƙofar falonta na kallon sa har ya fice saboda wankan da ya yi ya tafi da imaninta.

Sakin labulen ta yi ta zauna a falo tare da ɗaukar filo ta rungume aƙirjinta ta na jin wani irin nishaɗi, don ko kaɗan ba ta yi tunaninrayuwa tare da shi ba ko da kuwa a matsayin matar sa kuma ƴaraikin matar sa.

Bai shigo gidan ba sai da daddare tare da A.k suka shigo  suna tahira abin su.

A.k na ta baza ido ya gan ta bai gan ta ba musamman da ya gaZainab ba ta nan,kallon A.m ya yi da yake ta aika ma cikin sa abincisaboda tun zuwan Juwairiya gidan hankalin sa ya kwanta na rashinsamun abinci.

Kai wai ina maryar ka ne ?Tun na yanzu madam ba ta nan na sanƙila an samu baby?”

Ya faɗa ya na kallon shi ya na dariya tare da kai mishi duka akafaɗan sa.Taɓe baki ya yi ya ce.Ina zan sani kai kyale ni da waniamarci Juwairiya muguwar bagidajiya ce kullum cikin hijabi ka sankuma ba haka Zainab take min ba.”

Ya ɗan kalli A.k da ya daina cin abincin ya na sauraron sa yace.”Jiya da na kira ta ɗakina ƙin zuwa ta yi ban san tunanin ta a kaina ba.”

To kai in ban da abin ka A.m ai kai za ka bi ta kuma kuma macetake Hausa dole ta ji kunya.”

A k ya ce da shi ya na kallon sa.A.m ya ƙara taɓe bakin sa ya ce.”Ok ka manta abin da ƙanin mahaifinta ya ce a kan ta ni ban ga abinkunya ba.”

“A haba A.m ka san halin sa kar ka yadda da maganar sa kumakoma mene ne kai ka amince za ka aure ta sai ka ba da azama musami baby.”.

Dariya suka yi duka daga bisani A.k ya matsa mishi ya kira ta sugaisa ya na zaune ya ƙwala mata kira ba ta jima ba sai ga shi tafito,kamar dama laɓe take musu ta na jin maganar da suke yi.

A.m tashi ya yi ya nufi ɗakin sa zai ɗauko tsaƙon da A.k ya biyo shiya karɓa ba tare da ya kalle ta ba.

Da ladabi ta  gaishe shi ya amsa ya na ta tsokanar ta dai murmushitake masa.

Na so mu haɗu kafin ayi auren ki da shi sai dai kuma Allah bainufa ba ko Juwairiya?”

Ya faɗa tare da mai da maganar ta tsigar tambaya.Ɗaga masa kan tata yi ta na kallon shi Ok ba komai da ma na so na ɗan miki watamagana ne Juwairiya don Allah duk yadda zuciyar ki za tai ki karkiyadda ki saka son A.m a ran ki kawai ki sama ran ki zaki ci arziki kitafi ne.Ki ɗauke ni a matsayin Yayan ki duk lokacin da wata matsalata haɗa ku ki sanar da ni.”

Ya yi maza ya ƙarashe maganar jin takun A.m daga matakalarbene.Kallon sa ta yi sai kuma ta ji ya burge ta sosai yadda bai ɗaukirayuwar sa da zafi ba.

Ɗaga masa kanta ta yi alamun ta ji amma kuma a cikin zuciyarta saita ce.

Ka makaro A.k da ce wa ka yi na yaƙi zuciyata da take son sa ƙilada na karɓi shawarar ,amma na riga na daɗe da shiga cikin koginson sa.”

Sai da A.m ya yi masa rakiya sannan ya dawo ya tsaya ya na kallonJuwairiya da ta kasa tashi ta na ta tunani a ranta.” Me hawayenbanza maza ki tashi ki gyara min  ɗakina saboda yau haushina dakike ji sai kika huce akan ɗakin,sam gyaran bai yi  kuma ki ƙarawanke bayi.”

Ya faɗa tare da zama a falon kamar ya na son ta gama sai ya shigo.

Wucewa cikin ɗakin ta yi ba tare da ta ce masa komai ba amma yafaɗi son ransa ne kawai duba ga yadda take ba da dukkan lokacin tain ta je ɗakin sa gyara.

A.m ya na ganin ta shige ya bi ta tare da tura ƙofar a hankali ganinya shigo ta tsaya dama tun da ta shigo ta rasa mai za ta gyara sabodaɗakin ya na tsaftace da kyan sa.

Ki zo mu kwanta a gadon da baki taɓa hawa ba amma albarkacinaurena zai saka ki din ga moresa in matar so ba ta nan.”

Hawaye suka wanke mata fuska ba ta ce mishi komai ba kuma ba tamotsa ba bare ya saka ran za ta hawo,asalima gaban ta ne ya faɗiras!

Hannunta ya jawo ya na faɗin.” Na lura kuka shi ne farin cikin ki toki sani ba zan taɓa buɗe bakina rarrashe ki ba,ko na ɗauki hannunana share miki hawaye da su.

Yanayin da suka shiga a ranar yanayi ne mara fasaltuwa dabayyanuwa a gare su musamman Juwairiya da ta sha kuka har tagode ma Allah,domin kwana ta yi ta na kuka ko kaɗan ba ta bar shiya rintsa ba,wanda in ta tuna dalilin kukan na ta biyu ne sai ta ƙarasakin wani kuka.

A.m da bacci ya fara ɗaukar sa a hankali bayan wata sabuwarduniya da ya shiga kuma ya kasa fahimtar wace duniya yakeciki,kukan da take yi ya na ɗaga masa hankali ya yi maganar duniyataƙi yin shiru,har ya gaji ya ƙyaleta ya rintse idanun sa da ƙarfi ya nason bacci ya ɗauke sa.

Ganin taƙi dai na kukan ya janye bargon da ya ƙudundune kan sa dashi ya kunna fitilar ɗakin.”    

                    Ke wai ke.”

Sai kuma ya yi shiru daga ninyar faɗar da yake ya yi mata ya ɗansausauta murya ganin dare ne ya ce.” Ko fa wace mace da kika ganta  a gidan mijinta da haka ta fara.Kuma idan bakya son haka ba saiki gaya min ki gode ma Allah auren kwangila muka yi so ba daɗewa za ki yi da ni ba.”

Hakan sai ya saka Juwairiya ta ƙara fashewa da kuka ganin ta ba mamutumim da ya tsane ta rayuwarta,ga shi bai san mahimmancin taba bayan wahalar da ta sha yake gaya mata waɗannan kalamai.

Bakinta ta murguɗa a ranta ta ce.” Mugu kawai azzalimi.”sai kumata ci gaba da kukanta wanda A.m ya lura harda shagwaɓa don shi yagama fahimtar ta shegen shagwaɓa ne da ita shi ya sa da an yimagana sai kuka.

Wani irin walƙiya a ka saki lokaci guda aka fara tsawa nan ne A.mya fahimci garin hadari ne ya taso,da sauri ya sauka don ya duba kowindina a kulle ne kawai sai ya tsinci kan shi da jin daɗin ya na yingarin har ya buɗe labule ya na shaƙar iskar gurin.

Iskar ya ƙara ma Juwairiya zazzaɓin da ta ji ya saukar mata ganinhaka sai ya rufe windon ya na addu’ar Allah ya sa ta yi shirukenan,jin ta sassauta sautin kukan da take yi sai ya koma ya zauna.

Wayar sa ta fara ruri da sauri ya ɗauka don gabansa ya faɗi ya natunanin waye da daddare zai kira shi,ganin numbar masoyiyar sa yasa shi miƙewa da sauri take ɓacin rai ya bayyana a fuskar sa.

A wannan lokacin da yake duba wayar sa aka tsuge da ruwa sosaikamar da bakin ƙwarya.

Zubbur ya miƙe ganin numbar Zainab ce ya yi kamar ba zai ɗaukaba,saboda tun da ya gaya mata zai dawo ta de na ɗaukar wayar saashe mara mutuncin tafiya ta yi tabar ƙasar.Sai kuma ya kangawayara  a kunnin cikin tsanani ɓacin rai a ransa ya na tunanin Allahkawai zai raba ta da shi.

Hello zauji don Allah gani a airport ka zo ka ɗauke ni kuma nasamu ƴar matsala da kayana har mutumim ya na min barazana.Gakuma ruwa da ake yi kazo ka ji zauji.”

Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ya kalli Juwairiya da takecikin wani hali don shi kan sa ya san ya wuce gona da iri,kuma batare da sanin haka ba ya kuma kalli kansa da har yanzu ya kasatantance duniyar da yake ci.

Tunani ya fara yi ko Zainab ta hauka ce ne da za ta dawo da tsakardare sai ya ɗauki wayarsa da nufin ya duba lokaci, ai wallahi ba zaifita yanzu ba sai dai koma mene ne ya faru musamman da ta ɓatamasa rai ta yi tafiya ba tare da izinin sa ba.

Tsananin mamaki ya kama sa da agogon wayar sa ya nuna mishiƙarfe biyar da mintuna,ya na cikin kokwanton ko wayar sa ce saitinta ya goce sai ya ji ladani ya kwaɗa kiran sallah.

Da sauri ya yaye labulen ɗakin don ya ƙara tabbatar ma kansa takekuwa ya ga har hasken alfijir ya keto gari ya fara wayewa..

Sai hankalin shi ya ƙara tashi musamamn da Zainab ta turo masatsaƙon ba sai ya zo ba,don sun daidaita da mutumim yanzu haka masuna hanyar gida,saboda mijin Anti Fati ya turo direba ya ɗauke sukuma duka za suzo gidan.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]