[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
A.m ya shiga cikin tsananin tashin hankali ya juya ya kalli Juwairiyada take jin duk abin da yake faruwa,ga jikinta sai kyarma take yi harta fara haɗa haƙori kar-kar!
Sai tashin hankalin sa ya nunku ya kuma rasa tunanin da zaiyi.Hannunsa ya sa ya tallafe kan sa can kuma ya shiga shafa sumarkan sa ya na tunanin mafita,don shi babban tashin hankalin shi daZainab ba ita kaɗan za ta dawo ba ya san ce wa ta ce su zo ne surarrashe shi.
Wayarsa ya zaro ya yi kiranta ringing ɗaya ta ɗauka ta na kashemurya ta ce.” Hello Habibina ai mun kusa ƙarasowa gidan…”
Wata uwar tsawa ya daka mata da ya firgita ta ya ce.” Ni ko Zainabwallahi in kika shigo gidana na da waɗannan dabbobin sai na yimiki mugun rashin mutunci,don haka ki ce musu ko wace banziya takama gabanta tunna su mahaukata ne.Kuma zaki dawo zaki ga abinda zai faru! Allah ya sa su yi gangancin shigowa gidan.”
Da fushi yake magana tamkar ta na gaban shi don iya abin da zai yikenan ya hana su shigowa cikin gidan.
Zainab ta yi shiru da waya sororo a hannunta, ta rasa ya za ta yi gashi ta gama koɗa kanta ta isa da shi,don sun nuna ƙin zuwa sabodasun san halinsa ba kamar mazajen su yake ba.
“ Kai direba tsaya wallahi Zauji yau rashin mutunci yake ji kun jiabin da ya ce.”
Ta faɗa a kunya ce ta na kallon su.
“Mai ya ce ɗan rashin mutuncin?”
Anty Fati ta tamabaya don ta san za‘a rina sanin hali.”Gaskiya kowace mace ta tafi gidan ta ku sauke ni anan kawai ina ga ƴan iskanƴan uwansa sun zuga shi ne,amma da amincewar sa na tafi Dubaiyanzu ya na faɗa min kar ku zo mishi gida .”
Ta faɗa a kunyace don ya ba ta kunya ga shi ta gama zuga musuƙarya.” Kar ki yadda Zey ya haɗa ki fita kin ga dai irin ribar damuka samu,ki nuna mishi turjewar ki.“
Anty Fati ta faɗi cikin maganar zuga ta na son ta ƙara zuga ta don tashirya duk abin da yake ji.
“ Ke ma kin san halina kawai ba na son ya wulaƙanta ku ne ku jekawai ni wallahi akan sana’ta zan iya haƙura da aikin gwannati barekuma ya ce zai kawo min cikas.”
Anty Maryam da ba ta ce komai ba ita ma ta na tunanin abin da za tatarar,in ta koma sai yanzu ta yi magana ta ce.” To ki rabu da shimana yadda kike da kyan nan ai kin san ki na fita za’a wawushe.”
Wani mugun kallo ta yi mata tamkar za ta kai mata duka ta ce.” Kaji Anty Maryam da maganar banza ni da Hubbi ai mutu ka rabatakalmin kaza! So kike na kashe aurena na je na auri mai mata kowanda zai yi min kishiya nan gaba,hakan ma ba zai yiwu ba don nida kishiya ko a lahira ba na fata kuma zan iya yin komai a kanta nida ita yaƙi ne tsakaninmu.“
“To ki tafi mana ga shi har yanzu ana yayyafi kuma kin buɗe motakin tsaya ki na zuba,don kawai an miki maganar kishiya duk dafamily ɗin mu ba’a mana kishiya, amma Zey ki rage kishin ki to keda mijinki ba ya haihuwa wace mace za ta zauna da shi ai sai ke ƴarwahala.”
Dariya ta yi ta na ɗaga musu hannu ta ce da ƙarfi ta yadda za su ji tadon motar su ta fara tafiya.” A huta gajiya a haka nake son abinakuma sai mutuwa za ta raba mu.Kayana zan shigo na karɓa.”
Sannan ta juya da nufin ta shiga gida yayin da gabanta yake dukantara!Tara!! Don ta san ba za su kwase da sauƙi ba.
A.m ya juya da nufin ya yi ma Juwairiya magana amma sai ya ga bata a cikin ɗakin har ya fara taku zai bita sai kuma ya dawo,jikinsa narawa da shi kan sa ya kasa gane kansa ya na jin wani canji a jikinsa.
Sai kawai ya nufi cikin bayi don ya tsarkake kan shi ya yi sallaamma sa ya fasa jin ana buɗe gida da alamun Zainab ce ta shigo,dasauri ya ƴarasa gurin windo ya buɗe ilai kuwa ita ce ta shigo dagudu saboda ruwa da yake dukanta.
Girgiza kan shi ya wuce cikin bayi da sauri don ya san in Zainab tasame shi a haka za ta fahimci wani abu,kuma rashin mutunci yakeson ya yi mata sai dai yanayin da yake ciki na rashin ƙarfi ba zai bashi damar yin hakan ba.
Ya jima a cikin bayi duk da kiran da Zainab take kwaɗa masa bayanta shigo ganin ba ta gan shi ba,amma hakan bai sa ya ko ɗaga kan saba ya na ta tunanin da shi kansa in aka tsare shi ba zai ce ga dalilintunanin ba.
Ikon Allah dama Baba Sani ƙarya yake yi wa Juwairiya mace ce mainagarta da kamun kai?Haka kawai sai ya ji tsanar mutumim ya kamashi har ya na jin zai iya komai don ya taimaki rayuwarta.
Ko da ya fito faga ɗakin bai ga Zainab ba wacce ya tabbata ta ga jida zaman jiran shi ƙila ita ma ta na bayi ta yi wanka.
Sallah ya yi da sauri don yau ne karon farko da ya rasa jam’i shilokacin ne ya wuce gani yake yau gari ya yi saurin wayewa.
“ Hubbyna oyoyo zuciya ta yi kewar ka da gangar jiki.”
Ta faɗa lokacin da ta buɗe ƙofa duk da cikin tsoro take amma sai tadaure ta kauda tsoronta ta furta hakan,don ita a shirye take komamai zai faru ya faru in dai akan fita ne saboda ta ji daɗin fitan sosai.
Wani irin mummunan kallo ya watsa mata wanda ya sa ta firgita tatsaya tare da fasa rungume shi da ta yi ninya.
A.m da yake a zucuye da ita ya miƙe tare da fasa shafa addu’ar yagaura mata mari ji kake kau!
“ Banza mara mutunci ni zaki maida ɗan tasha ki tafi wata ƙasa batare da sanina ba ki dawo ki na min ilinbo ko.To wallahi sai dai kizaɓa ko ni ko fita zuwa waje.”
Zainab ta saka kuka iya ƙarfinta kamar yadda ta san ya tsani kukatare da watsi da kayan shafar shi da suke jere a madubi ta ce.
“ Ai wallahi ka mari auren ka ba sai na zaɓa ba dama na sha gayamaka duk ranar da ka ƙara marina sai na bar maka gidan ka!Donkawai na fita zuwa waje saboda ba ka wayewa ba za ka mare ni,daka zo nai man aurena da ka yi bincike ba‘a gaya maka Momina ta nafita zuwa waje saro kaya ba,ai kai ma ka san dole na yi sana’ar takuma in baka manta ba har jari Daddy ya ba ni lokacin da za’a kawoni gidanka.”
Da takaici ya kalleta ganin ɓarnar da tayi mishi ya matsa kusa da itadaidai lokacin da ta ruga za ta fita don ganin yanayin sa ta san dukanta zai yi,amma sai ya yi nasarar kamota ya riƙeta kamar zai ɓallata.
“ Zainab ba cin son ki da nake yi da rabuwa zan yi dake saboda bakida tarbiya ni kaina na yi kuskure da ban yi bincike ba,saboda munga Daddyna na tare da mahaifin ki ashe ƴar mace na aura.To bari kijiwallahi ba zan zauna dake a haka ba maza ki fice min daga gidamara mutunci kawai.”Ya ce zuciyar sa na tafasa kamar za ta fito.
Ya saketa cikin rashin tsoro ta tsaya ta kuma kauda duk tsoron datake ji na sa tuna huɗubar da Yayyinta,suka yi mata cewar su maduk sai da suka sha artabu da mazajen su sannan suka haƙura sukabar su.
“ Na gode da cin mutuncin da kake yi ma uwata amma ka saniyadda ba ka daraja mahaifiyata ba ni ba babu wani da banza da zandaraja, kuma Daddyna zan kira na gaya mishi dukana kake yi muguazzalimi mai dukan mace.”Ta ce ta na kuka da ƙarfinta.
Wani marin ya kawo mata ya na faɗin .” Ok haka kika ce to bari naƙara miki sai kiji daɗin faɗin kashe ki na yi,kuma yanzu zaki barmin gidana ba sai an jima ba ki je can ki sami shashasha irin ki kiaura,amma ni ba zan bar mace mafi soyuwa a gare ni ta na cuɗanyada wasu mazan ba ke ko kishin kan ki ba ƙya yi ….”
Katse shi ta yi ta na faɗin.”Babu in da za ni wallahi ai nasan ɓaɓatunbanza kake yi,amma ba zaka iya rabuwa da ni ba.“
A.m ya zaro bell ɗin shi ya na kallonta ya ce “ Tunna haka kika cezan nuna miki halina baki san wane ne ni ba,amma sai kin tafi gidanku in ya so in iyayenki suna son ki yi zaman auren sa hana ki tunnani kin raina ni.”
Zainab ta yi mamaki sosai ganin duk abin da za ta yi mishi ta yiamma ya kafe kan dole ta tafi,hankalinta ya tashi sosai domin in harta tafi ƴan’uwanta za su din ga mata dariyar a she dama ba ta fiƙarfin mijinta ba.
Sai dabara ta faɗo mata lokacin da ya janyo mata akwatinta ya turamata ta ɗauki waya za ta kira Daddynta, sai ta canza shawara ta kiraDaddyn A.m ta fashe da kuka ta ce.
“ Daddy A.m zai kashe ni da duka mun samu saɓani na kuma bashihaƙuri,amma kuma yaƙi dukana yake sosai.Don Allah Daddy ka zoka taimake ni!Ga shi nan da bell ya nifo ni.“Ta ce tare da saka sabonkuka ta saki ƙara ganin A.m ya yo kanta don ko kaɗan bai yi tunaninDaddy za ta kira ba.”
“ Baki da hankali ko mahaifina zaki kira uban me ya sa baki kiranaki ba?”Ya ce tare da doka wayar a ƙasa.
Hakalin Daddy ya tashi matuƙar gaske jin wayar ta mutu wanda yazargi A.m ya karɓe wayar,sai ya shiga safa da marwa don ya sanhalin ɗan na sa ba shi da haƙuri sam!
Har ya danna numbar ainihin mahaifinsa da nufin ya kira sa saikuma ya fasa ya kira numbar A.m,wace ta yi ta ringing bai ɗaga baduk da ya na kallon wayar.
A karo na ba adadi A.m ya ɗauki wayar tare da kanga ta a kunninsacikin fushi ya ce.
“ Hello Daddy.”
“Abdurrahman ba da hankali ko! Ƴar mutane kake duka wa ya cemaka ana dukar mace in ka saba mata da haka,kafiya za ta din gamata ita mace ai ƴar lallashi ne.Ka taɓa ganin wani ya duka matarsaa cikinmu irin tarbiyar da na baja kenan?”
Daddy ya tambaye sa cikin zafi ba tare da ya tsaya jin mai zai ceba.” Wallahi Zainab ta rai na ni nina san halin da take min!Daddywata ƙasa ta sallake ta tafi saro kaya har zuwa Dubai bayan na hanata.Shin Daddy na gaza ɗaukar ɗawainiyar ta ne?”
Shi ma ya furta cikin ɓacin rai da kuma murya mai sauti don yamanta da Daddy yake magana.
Daddy ya ji maganar wani iri tabbas ya ji ba ta kyauta ba,amma shiA.m har yau ya kasa gane wace irin mace yake aure kuma ƴar waye.
Jin Daddy bai ce komai ba sai ya yi ƙuta ya ce.” Na rantse dole tabar min gidana tunna ba ta da tarbiya ni ba zan yadda ta mai da ninamijin tace ba.”
Ya ce ya na huci don Zainab ta ba shi haushi matuƙar gaske shi yasa dama ya ɗauki alƙwarin in ta dawo ba za su kwashe ta daɗi ba,saita gane shi baya ɗaukar raini shi ya sa ya ɓoye sonta a wani guri nazuciyarsa don kar ya han shi ɗaukar mataki.
“ Abdurrahman dama ka auri ƴar abokina ne saboda ka tozarta ni, kanuna ban isa dakai ba saboda ba ni na haife ka ba ko?Ka na son katada min da taɓon ba na haihuwa ko?”
Daddy ya faɗa a raunane wanda hankalin A.m ya tashi da jin abin daya faɗa don ji ya yi kamar kuka yake yi.
“ No Daddy don Allah kar ka ce haka wallahi kai ɗin kafi mahaifinadon zan iya bijire masa,amma ban da maganarka ka yafe min.”
Ya ce hankalinsa a tashe ya na ma mata mugun kallo saboda yau nerana ta farko da Daddy ya yi mishi irin wannan maganar.
“To ina baka haƙuri tabbas ba ta kyauta ba karka ƙara dukanmatarka ta sunna yanzu gani nan zuwa gidan,zan yi mata faɗa kumadole ta daina tunna baka so ai kai kake da iko da ita.”
Daddy ya ce masa cikin muryar taushi da lallashi ya na son yakwantar da hankalinsa,ya san zai iya yin ɓatatta.
“ To sai ka zo.”
Ya kashe wayar ya na huci kamar mesa daga ƙarshe ficewa ya yi aɗakin ya bar ta ya koma farfajiyar gidan ya na jiran Daddy,don haryanzu bai huce ba dole Zainab ta zaɓi ɗaya duk da ya san barazanakawai yake mata amma ba zai iya rabuwa da ita ba.
Zainab kuwa ba yan fitarsa ta yi tsaki tare da saka makulli a ɗakin tana shafa ƙuncinta da ya sha mari ta ɗauki wayarta da ya fasa tace.Wahalalle kawai ka gama jarabarka sai ka siyar min wata wayarkuma ba zan fasa sana’a ta ba ƙarshen da zarar na samu lokaci wataƙasar zan koma.Sai dai in hauka za ka yi ka yi.”
Ya na tsaye a farfajiyar gidan ya ji hon wanda ya tabbata Daddy neya zo,mai gadi ya buɗe masa get ya shigo.
Da sauri A.m ya ruga kamar wani ƙaramin yaro ya faɗa jikin Daddyya na magana kamar zai yi kuka.Dariya ya yi ya shafa bayan shisuka shiga ciki.
Faɗa sosai Daddy ya yi ma Zainab wacce ta ɗauke shi a matsayinson kai kuma ya tursasa mata ta ba A.m haƙuri,sannan ƙar ya ƙarajin ta fita ko unguwa ba wata ƙasa ba in dai ba da izinin sa ba.
Ya kuma ƙara da ce wa.” Tunna A.m ba ya so ta dai na zuwa in yaso ko shi zai iya yi mata oder.
A kasale ta miƙe ta na ganin kamar son kai Daddy ya yi mata,ammata rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe ba wanda ya isa ya hana ta fitawaje,don har ta fara saka kanta a cikin matan da za’a fara irgawasuna da kuɗi a cikin Nigeriya, so ba wani ƙwaro da zai hana ta fita.
Amma a fili sai ta ƙara sakin kuka ta ce “ Na yi nadaama kuma naba shi haƙuri Amma ya ƙi haƙura.”
“ Shikenan Daddy ya wuce amma kar ta ƙara.”
Ya faɗa cikin ɓacin rai sannan ya miƙe ganin Daddy ya miƙe.” OkAllah ya kyauta ku yi haƙuri dama aure ɗan haƙuri ne ni zan tafi.“
A.m ya shafa kan shi ya na murmushi ya ce.” Daddy ya zo gidan sonamma ko ruwa ba’a kawo mishi ba,ka yi haƙuri Daddy ni kainahaƙuri nake da ƴar taku komai ba ta iya ba sai shegen yawon tsiyada rai na miji,Allah Daddy ko ruwan zafi ban taɓa sha ba wandaZainab ta dafa,asalima ce wa ta yi ba ta iya ba.Shi ya sa naketunanin ta rako mata ne kawai.
Daddy ya saki dariya ya na faɗin daidai lokacin da ya nufi ƙofa.” Ahah wanan to magana ake yada min ba haƙuri ake ba ni ba,ammakuma a haka ka ga ƴar tamu ka kace in ba ita ba sai rijiya.”
Tsaki ya yi ya na hararar ta ya ce “ Shigo shigo ciki akai min bansan halin ta ba na ba ta amanar zuciyata.”
Zainab kuwa mai da mishi da harar da yake mata ta yi ta ce.” Bawani nan wahala ce na ce ba zan yi ba ai ko addini bai ce dole sai nayi ba,kuma yanzu ai baka da matsalar abinci tunna ga Juwairiya nanmai aiki.”
A.m ya watsa mata wani kallo wanda shi ya sa ma’anar sa jin taambaci Juwariya.
Ganin Daddy zai fice sai Zainab ta ce.” Daddy bari na yi kiranJuwairiya ta kawo maka abinci,na san yanzu haka ta na kicin kumazaka yaba don ta na da zaƙinn hannu.”
Wani irin tashin hankali A.m ya ji ganin ta nufi kicin ɗin har ya nadana sanin maganar da ya yi gashi ƙilu zai jawo mishi bau!
Ya buɗe baki da nufin ya yi maganar da bai san me bakinsa zai ce basai ya ji Daddy ya ce.
“ Karki damu ƴata kin san bana karyawa sai sha ɗaya bari na tafiAllah ya yi muku albarka,kuma don Allah ku din ga haƙuri da junanku.”Sai ta dawo ta fasa ta na murmushi.
Wani irin wawan ajiyar zuciya ya saki wanda ya sa har sai da Zainabta juyo ta kalle shi,ya watsa mata harara,ya shige sama da sauri yanufi ɗakinsa ya kwashi zanin gadon da ya saka a warshing mashineya kunna da sauri har ya na sheƙa ruwa a ƙasa garin ya zuba a ciki.
Zainab ce ta shigo ta zauna a kan gadon ta na ƙare ma ɗakin kalloganin ya na bayi sai kwanta ta na jiran sa,amma sai yaƙi fitowa yatsaya kamar me tunanin wa ni abu da ya manta.
A hankali Zainab ta taso ta tsaya ta bayansa ta huging ɗinsa da sauriya ture hannunta ya koma gado ya kwanta tare da rufe idanunsa yajanyo bargo ya lulluɓa da shi.
Ganin haka ita ma ta hau ta ɗaga bargon ta shige tare da rungumeshi,ya sa ka hannunsa ya ture ta ta faɗi ƙasa don har yanzu haushintayake ji,haka kawai ta ba ma wata mace damar shigowa rayuwarsa gashi ya na jin wani abu da ba zai iya ce wa ga shi ba,don har yanzujikinsa babu ƙarfi.
Da takaici ya isheta sai kawai ta fashe da kuka don ta bugu sosai tamiƙe ta na share hawaye ta ce.“ Bari na fita tunna baka buƙatar songanina! Haba ko Allah muna yi mishi laifi ya yafe mana.”
Ta saka takalmi ta kuma ce wa.” Dama yunwa nake ji bari naje na ciabinci.”
Haba da sauri ya diro a kan gadon da ya ƙudundune kansa da bargoya janyo ta da ƙarfi ta faɗa kan gadon ya na zare ido.
“ Ke ce kika ban haushi matuƙa amma na haƙura tunna kin ce bazaki ƙara ba.”
Ya ce da ita ya na murmushin dole ya saka hannun shi ya tallabetaganin ta na murmushi ya ci gaba da ce wa.” Baki san tashin hankalinda na shiga ba da baki nan kin san duk yawon ki ba ki taɓa bari munraba shinfiɗa ba.Tun lokacin da na ce miki mun iso kika kashe wayana tsargu.“
Ya ƙura mata ido ya na kallonta ya kai bakinsa kusa da kunninta yana mamakin abin da zai ce mata.” Ko dafa da na dawo na ga baƙyanan sai wancan wa take da suna ta bani abinci wurgi da shi na yi,ahotel na zauna saboda gidan ya yi min baƙi na kasa bacci ni kaɗaigabaki ɗaya kewanki ya dame ni,gaskiya ina son ki matuƙa.”
Ya numfasa ya na mata wani tsadadden kallo da murmushi ya cigaba da ce wa.” Ina masallaci na ga kiranki duk da fushi nake dakehar na fito cikin hotel ɗin da nufin na ɗauki mota na ɗauko ki,sai gashi kin kira ni in bar shi mijin Fati ya turo muku direba shi ya sa nakaryo mota na dawo gidan tunna matar gidan ta dawo.”
Ya faɗa ya na kaida kansa gefe shi kansa ya na mamakin kansa.
Zainab murmushinta ya ƙaru ta na jin wani irin girman kai daalfahari da mijinta da take yi,sai ta kama shi ta rungume ta nafaɗin.”Ina sonka Habibina ni na san ba za ka iya rabuwa da ni ba,koce wa da ka yi na bar maka gidan ka kana faɗi ne kawai amma ni dakai mutu ka raba.”
“ Tabbas Zainab maganarki dutse da sai dai ki taho asibiti jinya.”Yafaɗa
Dariya suka yi duka ya rufe su da bargo ya kasheta da soyaryar shisannan ya sa ta baccin dole,saboda ya sakin mata nauyin shi waidole sai ta kwanta sun yi bacci,duk da ba shi take ji ba.
Kallonsa take yi yadda yake saukar da numfashinsa a hankali,dagagani baccin na kai mishi karo ita kuwa ta kasa baccin saboda waniirin yunwa dake ƙwaƙwularta,saboda rabonta da abinci tun darenjiya ta kasa ci ta na fargabar yadda za su kwashe da shi.
Shafa fuskarsa ta yi da yake ta sheƙi da kyau ta na mamakin mai yahana shi bacci,sai kuma ta danganta hakan da ce mata da ya yi ba’agida yake kwana ba ƙila ya kasa bacci ne.
A.m da fari baccin ƙarya yake yi ya saka mata nauyin jikinsa donkar ta ce za ta buƙaci abinci, ta je gurin Juwairiya don ya san a halinda take ciki ba yadda za‘a yi ta iya wani aiki a gidan,amma kumadaga ba ya saboda rashin baccin da bai yi ma wannan mai kukantsiyar da ta hana shi bacci sai bacci ya kwashe shi.
Da Zaina b ta gaji da juyi a gado ta bubbuga shi ya ɗan buɗe ido yana kallonta.
“ Gaskiya ka tashi ni fa na gaji da baccin nan yunwa na son ta yimin lahani.“
Ta faɗa ta na jan shi ya sauko shahada ya yi ya sauka tare da miƙada salati,ya shige bayi ganin haka ita ma ta sai ta wuce ɗakinta tashiga bayi wanka ta yi ta zira duguwar riga,suka fito falo suna taku ajere sai kace ba su suke ta faɗa ba.
************
Juwairiya kuwa bayan ta gama jin wayar da A.m yake yi da Zainabta shiga tashin hankali matuƙa! A wannan lokaci ji take kamar tabuɗe ido ta ga ba ta a doron ƙasa kuka take yi sosai na rashin abumafi girma a rayuwarta,wanda Baba Sani ya so ya yi galabar raba tada shi dama mutane da dama amma ta yi yaƙi tukuru,ta ada na abinta sai ga shi yau ta siyar da shi saboda kuɗi ta na shan wulaƙanci batare da an daraja ta ba.
Ta rintse idanunta ta na jin wani irin ciwo mai raɗaɗi a zuciyartayayin da wasu tarin hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta.
Cije bakinta ta yi lokacin da ta miƙe ta na jin wani irin azabar raɗaɗiya na zagaye duk ilahirin jikinta.
A hankali ta fice daga ɗakin ba tare da ya sani ba jin matar so tadawo yayin da hankalinta ya tashi,amma ta wani gefen ta na jin inama ace Zainab ta riske su a wannan yanayi koma mai zai faru yafaru,don ta gaji da tarin raɗaɗin azabar da take kurɓar ruwan baƙincikinsa a cikin rayuwarta.
Ta na shiga ɗaki sai ta fashe da kuka sosai har ta yi mai isar tasannan ta rarrafa ta shiga bayi ta gana ma kanta,azaba da ruwan zafidon ta rage ma kanta ciwo da nauyin da jikinta ya yi.
Bayan ta yi wanka ta fito ta yi sallah a zaune sai bacci mai haɗe dazazzaɓi ya kama ta wanda faɗan su ya tashe ta,ba wai don ta gaji dabaccon ba tunna duka yaushe ta kwanta sai dai ta ji daɗin baccin donya ɗan rage mata wani ƙunci daga cikin damuwarta.
Ta din ga jin hayaniyar su da kukan Zainab har da saukar marin daya yi mata.
Ta saka hannunta ta toshe kunnin ta amma sai ta ji sun sauko ƙasasuna ta faɗa sosai,ya faɗa ta faɗa sam babu tsari a rayuwar auren sudon ba sa daraja juna.
Gabaki ɗaya sai ta ɗauki laifin ta ɗora akan A.m wanda yanzu takejin haushin sa fiye da komai a rayuwarta,ga wani irin kishinsa da yaƙara ninkuwa a ranta mai girma wanda take jin kamar ta illata dukwadda ta raɓe shi.
Ta na jin suna faɗa daga bisani ta ji shiru sai muryar namiji ta ji yana sasanci,wanda daga baya ta game mahaifin A.m ne.
Sasancin da aka yi a tsakanin su suka koma ciki shi ya ba ta damaryin baccin wahala,duk da ta san ya kamata ta shirya ma mutanengidan abinci,sai dai ba za ta iya ba saboda jikinta da ko ina yakemata ciwo.
A tare suka sauko ƙasar sun ci gayu sosai an sha kyau.
Zainab ta tsaya ta na kallon dinning cike da mamaki ganin ba komaiwayam.
Ta kalli A.m ta na faɗin.” Ina wannan wawiyar take ba ta shirya minabinci ba duk da na kira ta ba ɗauka ba na tura mata da text.”
A.m ya da gaban sa ya faɗi amma sai ya taɓe bakin sa ya ce.
“ Ina zan sani ko kin bani ajiyar ta ne?Ni da ba‘a gida nake kwanaba.”
Ya faɗa ya na wani cin magani har da ɗan harara yake sakin mata.
Ƙwala mata kira ta yi sau uku sai ga Juwairiya ta fito a wani yanayita na jan ƙafarta.
Da masifa Juwairiya ta kalle ta ta fara magana da ce wa.” Ina abincina kuma gidan uban wa kika shiga na kira wayar ki na gaya mikizan dawo amma baki ɗauka ba.”
Ta faɗa tare da tsare Juwairiya da ido kamar ta na son ta gano dalilinƙin ɗaga wayar da ta yi.
Juwairiya ta saci kallon A.m da yake zaune a ɗaya daga cikinkujerun dinning ya na danna waya,kamar bai san da mutane a gurinba amma kuma a zahirin gaskiya hankalin sa na gurin su ya na sonya ji mai za ta ce,yayin da gaban sa yake faɗi duk a tsorace yake saidai ya yi ta maza ya dake.
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Juwairiya ta mai da kanta ƙasa hawaye na bin fuskarta jikinta harkyarma yake yi,saboda har yanzu zazzaɓi take ji,ita kanta ba za ta cega in da wayarta take ba don rabon ta ita tun jiya da ya ce ta gyaramasa ɗakinsa.
“ Ki yi haƙuri wayata ba caji na gaya ma maigadi ya kunnajannareto don ba wuta,amma ya ƙi tashi sannan na so na kunna solasai dai ban iya ba ina gudun kar na ɓata na haƙura k…..”
“ Rufe min baki nɓbanza daƙiƙiya jahila solar ce kika kasa kunnawaabu a rubuce ba na tunanin kin yi firamari,ni tsoro nake karki din gaƙona min kayan wuta ko ki ta da gobara ai dai yi asarar kuɗin tarawallahi.To uban me ya hana ki yin abinci.”
Zainab ta ce ta na hararar ta don ranta ya ɓace ta so ta samuabincinta da ta yi rashin sa na kwana biyu mai daɗi da,shi ya sa taƙisakin jikinta ta ci abinci da za ta taho.
Wannan karon A.m ya yi tsubbul da bakinsa ya ce.” Wa za ta dafama abincin ni da na gaya miki a hotel na ke kwana ita da masu aikine kawai ƙila sun yi sun ci,tunna ba ta san za ki dawo ba.”
Ya ce cikin sauri ya na tsoron kar ta yi katoɓara don ganin ta farakuka.
Juwairiya kuwa gwalalo idanunta ta yi ta na kallon sa jin ƙaryar daya shirya mata.
Karab! Kuwa suka haɗa ido kowa ya yi saurin ɗauke kansa.
A.m sai da ya sakin mata harara sannan ya ɗauke kansa,Juwairiyakuwa wani irin kunyarsa ya kama ta ta rintse idanunta da sauri.
“ Ke.”
Ta daka mata tsawar da ya firgita ta.” To uban wa kike ma kukadaga tambayarki?Maza ki je ki ɗora min abinci yunwa nake ji kumaki kawo min abun da zan iya ci kafin ki ɗora girkin.”
Sai hawayen Juwairiya ya ƙara zarya a fuskarata ta kalli Zainab tace “ Don Allah ki yi haƙuri bani da lafiya zazzaɓi nake ji,ba zan iyagirki ba.”
Ta faɗa cikin muryar da ta bayyana irin kukan da ta sha tun darenjiya.
Zainab ta harare ta ta ce.” Allah ya sa mutuwa za ki yi amma sai kinyi min abinci kin san yunwar da nake ji maza wuce.Kuma ki kawomin abin da zamu taɓa ni da zauji.”
Ta zauna tare da ɗaukar remote ta kunna kallo ta na karkaɗa ƙafa tana jan A.m da hira wanda ya kasa ko da tari ne ya na ta kallonfuskar wayarsa,da ya kasa ɗauke idanunsa a kanta bayan babu abinda yake yi.
Juwairiya na shiga ta haɗa kanta da bangon kicin ɗin ta na kukasosai take jin jikinta ba daɗi.
Ta daɗe a haka sannan ta soya dankalin turawa da ƙwai ta kumahaɗa musu da tea mai kauri ta kai musu,ta na tafiya tamkar wacceƙwai ya fashe mawa a cikin ta.
“ Ok maza ki je ki haɗa mai nauyi don wannan ba zai ƙosar da niba.”
Ta ce mata ba yan ta ije mata ba tare da ta kalle ta ba.
“Anty Zainab ki yi haƙuri ba ni da lafiya don Allah sa…”
Mari ta wanka mata a fuskarta da take jiƙe da hawaye ta ce.
“ Ban san lokacin da kika raina ni ba har kike musayan yawu da nibanza dangin matsiyata!Maza wuce ki yi abin da na saki.”
A.m ya tashi da sauri ya na faɗin “ Haba Zainab ta ce miki ba ta dalafiya ba ki da tausayi ne..”
Katse shi ta yi ta ce.” Ba da kai nake yi ba ba ta da lafiya ta shamagani,uban wa take son ya yi mana girkin meye amfanin ta agidan?Ko ubanta yake neman ma na kuɗin da za mu biya ta?”
A.m har ya buɗe baki zai ƙara magana sai kuma ya fasa,ya ɗaukiwayar sa ya haye sama ba tare da ya ƙara kallon ɗaya daga cikin suba.
Juwairiya ta dafe ƙuncinta hawaye na zarya a fuskarta da ma ta sandole watarana Zainab za ta dake,ta tun da halinta ne sai dai yadda taji saukar marin ta ji sam ba za ta iya ɗauka ba,domin da ya zoneman aurenta bai gaya mata har da duka a ciki ba.
Hawaye ta share ta juya ta nufi kicin saboda rashin ƙarfin da takeji,tsayuwa ma wahala take mata don haka ba ta ƙara ce wa komai bata shige kicin ɗin.
Jingina ta yi da slinder na gas ɗin kicin ta saki kuka duk da ta na jincewar,lokaci ya yi da za ta dai na asarar hawayen a banza akan susaboda ta fahimci bayan damuwar da suke saka mata,har da naauren su da suke faɗa kamar kaji su hana ƙwaƙwalwarta sukuni.
Da ƙyar ta samu ta kammala girkin da taimakon Baba da ta dametada tambayar mai ke damunta,ganin ta ƙi tanka mata sai ta kalle ta tace bayan ta gama kwashe abinci ta saka a kula.
“Ƴar nan ya kama ta ki naimi maganin basir saboda shi yake damunki,ji yadda kike cije baki ki na tafiya da ƙyar.”
Da takaicin maganar da ta yi mata ɗaki ta wuce ba tare da ta tankamata ba.
Tun daga wannan ranar Juwairiya ta kame kanta ba ta barin kohaɗuwa da shi su yi,saboda wani irin kunyar sa da take ji kamar tanitse in ta gan shi,don ko gyaran muryar shi ta ji sai jikinta ya kamarawa kamar za ta ruga.
Kwana biyu Zainab ta takura kanta ta hana zuciyarta fita don tafaranta masa,saboda ta ga canji kwana biyu ya na wani shareta,da tayi masa magana zai hayayyaƙo mata kamar zai cinye ta.
Sai ta danne zuciyarta ta ƙi fita ko ina daga aiki sai gida ta na ba shikulawa,wanda da ƙyar ta samu ya sauko suka koma rayuwar sukamar da.
Juwairiya kullum za ta yi musu abinci mai rai da lafiya su ci sunayabawa a zuci,don girkinta ya na matuƙar ƙayatar da su duk da babuwanda ya taɓa yabawa,amma har ɗan ƙiba sai da suka ƙara kaɗan.
Sai dai fa mai hali ba ya fasa halin sa Zainab a daddafe ta yi ƴankwanaki a gidan, wadda take jin kamar ta na gidan yari duk da irinkayan alatun dake gidan amma saboda ta saba fita sam komai ba yaburgeta.
Zaune take a ɗaki ta kulle kamar yadda ta saba duk lokacin da za tayi rawa ta tura.
Tasha ado da wasu riga da wanda na ƴan kanti masu kyau kalarpink,wandon bai kai ƙasa ba.
Gyara gashinta ta yi ta fara rawa cike da ƙwarewa ta tura ta namurmushi don ta san yanzu za ta ga ruwan comment da like.
Ilai kuwa ta na turawa aka fara liking ta na kallo ta na murmushi,tana shirin sauka wata numba da kullum take mata sallama afacebook,ta ƙara yi duk da ba amsa wa take ba amma ba ta gajiba,ku san kullum sai ta yi mata sallama.
Tsaki ta yi ta sauka da ga online gabaki ɗaya ta na mamakinwannnan numba da take damunta,saboda ita in dai ba ta san mutumba ba ta magana online,sanin cewar ita tauraruwa ce a yanar gizo soba ta da lokacin da za ta tsaya ta na kula su,amma a ranta ta ji ta nason ta amsa sallamar don ta ji mai ke tafe da ita,saboda ta dubaprofile ɗinta ta ga ita ma ba ƙaramar mace ba ce,don da BarristerMardiyya take bearing.
Murmushi ta saki tare da ije wayar da sauri daidai lokacin da A.mya murɗa ƙofar ya shigo,sai ta kama hannunsa ta riƙe ta na dariyatare da kashe murya ta ce.
“Barka da dawowa yanzu na ji ƙarar shigowar ka, ina wanka ne shiya sa ban fito ba.”
Dafe kan sa ya yi ya janye jikin sa ya zauna akan gefen gadon ya nakallonta tare da ƙoƙarin rage kayan jikin shi.
“Babyna na gaji matuƙa kamar kai na ciwo yake son ya yi,yunwanake ji kawo min abinci in ci anan bacci nake son na yi.”
Ya faɗa tare da kwantawa ya miƙewa a kan gadon don jikin sa koina ciwo yake masa.
Zainab ta ɗan canza fuska ta ce “ Na ɗauka za ka ci abincin adinning ne fita nake son na yi,kuma Juwairiya ta riga ta shiryaabinci meye sai ka wahalar da mutum gurin ɗaukowa.“
Ta ƙarashe maganar cikin yauƙi da yanga tare da ɗaukar wayarta,datake kusa da shi don ta tuna kamar ba ta sauka a online ba,sai daikuma da ta tuna ba ta taɓa ganin ya ɗauki wayarta da sunan ya dubaba,ko kuma ya ce zai yi wani abu.
Gaban sa ya faɗi da ta ambaci sunan Juwairiya ba zai ce ya mantada ita ba,amma sam ba ya son ya ji sunan sai ya ji haka kawai gabansa ya faɗi.
“ Zainab ba na son rainin wayo ni da gidana da kuma matata ba nida ikon na ce ga in da zan ci abinci?Kuma da kika ce wancan za takawo min,to ba ita nake so ba matata wacce nake da iko da ita nakeson ta kawo min,kuma ki je ki dawo bacci nake son mu yi babu inda za ki.”
A ɗan kausashe ya faɗa ya na harararta wanda ya zamar masaƙa’ida,kamar wani mace in dai aka gaya mishi ba daidai ba, sai ya yiharara.
Yarfe hannunta ta yi ta ije wayarta tare da fara ƙorafi ta na ce wa.”Haba Hubbi kai ma ka san na yi ƙoƙari ban je ko ina ba,na bakalokacina na tsawon kwanaki.
Ta ɗan matsa kusa da shi ta ce.” Yau fa bikin ƙanwar ƙawar AntyFati ake yi,ka ga ai ya zama dole na je ko?“Ta tambaye shi tare datsare shi da ido.
Kallonta ya yi bai ce komai ba sai ya miƙe ya kunna tangamementibin da ke ɗakin ya riƙe remote ya ce.
“ Dole ki je mana gayyar soɗi ni dai na gama magana ba in dazaki,ke ko kishina ba kya yi ki ta sa ƴan aiki suna kawo minabinci,ko tunanin in canza miki ba kya yi.”
Kusa da shi ta zauna ta na faɗin.” Yarda da kai ne Hubbi Allah in zaa ban kur’ani zan iya rantse wa a kan ka,sam ba ni da haufi ko da baka yi min alƙawarin ba za ka yi min kishiya ba,hankalina ba zaitashi ba saboda ban taɓa jin ka yaba wata mace ba.“
Ta ɗan kalle shi da murmushin yadda a fuskarta ta ci gaba da cewa.” Kuma duk abin da nake yi ai ba na zuwa da ƙawayenawaɗanda ba su da aure gidana saboda tsaro.”
Dariya ya yi jin abin da ta ce ya miƙar da ita ya na faɗin.” OkBabyna ina godiya sosai da yardar da kika yi min,kuma ke ɗinzazzafa ce ta ko’ina ga kyau ga ilmi da da tarin baiwa kala-kala,inagaya miki ba wata sai ke a nan.”
Ya nuna mata ƙirjin shi da da babbar yatsar shi dariya suka yi ta yihuggin ɗin sa,sannan ta ba manna masa kis ta ruga da sauri don taɗauko masa abincin,duk da ranta bai so haka ba amma fitar ta tarantse sai ta fita.
Don haka ko da ta dawo haka ta ci gaba da lallaɓar sa har ya amincesaboda ta dame shi,kuma bacci yake son ya yi da sauri ta ɗauki ɗangyalen ta ta fice daga gidan.
Bayan ya ci abinci ya ɗan miƙe tare da ba da tazara kafin yakwanta,saboda abincin da ya ci sannan ya kwanta bacci.
Juwairiya ta warke sumul bayan ɗan ciwon kwana biyu da ta yi tazage ta na ta aikinta,cikin ƙosawa a ranta ta na addu’ar Allah ya sa tasamu cikin ya ɗauke ta daga gidan,ganin yadda Zainab ta mai da itabaiwa,shi kuwa daga ranar bai ƙara neman ta ba.
Ta na falo aiki take yi goge su tibi da abin da ya kama ta a goge afalon take yi.
Sosai ta mai da hankalinta a kan aikin da take yi ta na son ta gama taɗora girkin abinci.
Ya fito daga ɗakin sa ya na sanye cikin doguwar riga na jallabiyamai ruwan madara,wayar sa riƙe a hannun sa sam fuskar sa babufara’a.
Juwairiya ta saki ɗan ƙaramin tawul ɗin da take goge tibin da shi zata ruga ganin ya fito, amma sai ya yi maza ya riƙe mata hannu tareda kiran sunan ta.
Tsayawa kan dole ta yi tare da juya masa baya cikin tsananin kunyarsa.
Juyo da ita ya yi da murya mai sanyi ya fara magana.
“ Ban san tunanin ki in da ya tafi ba tun daga ranar kin ɗauke wutakin mai da ni kamar wani dodo,bayan kin san wannan kamar sharanfage ne akan tsarinmu har zuwa randa zamu cimma haƙar mu,kowaya huta da wahalar da kan sa mu samu maslaha a rayuwar mu.”
Ta na son ta yi mishi magana irin ya faɗa ta amsa mishi ko damaganar da ya yi mata babu daɗi,amma kuma ta na matuƙar jinnauyin sa wanda ko haɗa ido a bisa kuskure take yi.
Sai ta kauda fuskarta a ranta ta na faɗin.” Kai ne kake son ka cimmahaƙar ka,amma ni ina son na kasance da kai har abada A.m inasonka burina ka ɗauke ni daga gidan ka nima ka sama min ƴanci narayu da kai duniya ta san mijina ne kai.”
Amma a fili sai ta yi ƙasa da kanta ta na kallon ƙafafun sa suke dakyau da sha’awa.
“ Ke ni fa ba na ɗaukar rainin wayo na yi ta miki magana kinasharewa,ki buɗe baki ki yi min magana kuma ni ban ce ki yi minkuka ba.“
Ya faɗa ganin ta yi rau-rau idanunta sun kawo ruwa.
Kamar umurni ya ba ta sai ta yi ƙoƙarin mayarwa ta na son kallonsa.
A.m ya saka hannun sa ya shammace ta kawai ya cire mata hijabinjikinta ya na faɗin.
“Ni fa yanzu ban ga abin ɓoye-ɓoye a tsakaninmu ba bayan kin sanke ɗin matata ce,wanda aure ya ba ni damar mallakarki a gurinmakwaɗaicin ƙanin mahaifinki.”
Ta kauda kanta ba ta ce komai ba sai kuma ta saka kuka.
Dunƙule hijabin ya yi ya jefar ya ci gaba da faɗin.“Anyway yanzudai ni maigida na ba da umurnin in dai daga ni sai ke ne a gidan,toamaryar wucin gadi ƙar ta ƙara saka hijabi ki bari sai in wanda kikejin kunya ta dawo sai ki saka abinki,amma ni da ke ai ba kunyatsakaninmu ko.”
Ya gama maganar ya na tambayarta ya na wani irin murmushi maikama da na mugunta ko ya na son shirya wani ƙeta.
Juwairiya ta ji wani irin sanyi a ranta karan farko haɗuwara da A.myau ne rana ta farko da ya yi mata murmushi,duk da murmushin nasa da wata manufa ya yi amma hakan ya ba ta matuƙar citta a ranta.
Ta matsa daga kusa da shi ganin irin ƙare ma jikinta kallo da yake tafara tafiya a hankali.
“Juwairaah.“
Ta tsaya cak daga tafiyar da take yi amma ba ta jiyo ba,shi ya tahohar in da take ya matsa kuda da kunninta ya ce “ Ina zaki matarwucin gadi ai ban gama magana ba,kin san ya kamata a ɗora daga inda aka tsaya ko.”
Banza da shi ta yi tana mamakin wai haka yake mai ya sa yau yaƙara zuwa da salo ne?
“ To shikenan tun da kin ƙi magana da ma zan yi godiya ne na ranarnan gaskiya na ya ba sosai,wannan daren momerable andremarkable ne a gurina,Allah shi zai saka miki saboda ai ba ta ki daƙanin mahaifin ki ya yi.”
Ya faɗa ba tare da kunya ba kuma ya na kallon ƙwayar idanunta.
Juwairiya ta ɗago ta kalle shi ba tare da ta shirya ba ta ji ta sakarmishi wani lalausar murmushin,har dimple ɗinta suka losa ta ruga dagudu ta shige ɗaki tare da rufo ƙofar.
A.m ya saki dariya don kunyarta ta na matuƙar burge shi matuƙargaske,saboda ya na son mace mai kunya juyawa ya yi zuwa waje jinshigowar motar Zainab,ya saki duk wani wulaƙanci da yake son yimata da tsanar ta da yake ji zai more abin sa kafin zuwa ranarrabuwar su,saboda tsakani da Allah ya ji wani girmanta a ranshi tunranar da ya mallake ta,tsananin talaucin da take ciki bai saka tazubar da mutuncin kanta ba.
Ƴa ƴan’uwana mata don Allah mu kama darajarmu domin shinemutuncinki, don Allah ƴan mata ka da son abin duniya ko jinkirinaure ya sa ki zubar da mutunci,don ki na tunanin kin daɗe ba ki yiaure ba ba zaki yi ba,ki tuna lokacin ki ne bai yi ba,kuma duk darendaɗewa in da kina raye za ki yi,yayin da ki ka yi aure wulaƙanci shine abin da za ki girba har ƙarshen rayuwarki.
Kuma ƴar’uwa da ki yi saurin aure ki fito gara ki daɗe ba ki yi ba,kidaure har ki samu wanda zai kula da ke emotionally,phisicallyfinancially,and mentally.Shawara ce.
Juwairiya gado ta faɗa tare da ɗaukar filo ta rufe fuskarta da shi.
“ Mai ya sa yake min irin waɗannan kalamai ne wai dama ba shi dakunya haka?Kai na rasa gane wa wallahi gabaki ɗaya ya canzadariya fa ya yi min.”
Sai ta saki murmushi ta mirgina wani gefen ta na jin wani irinnishaɗi a cikin zuciyarta.
“ To ko ya fara sona ne?”
Da sauri ta kori wannan tunanin a cikin zuciyar ta amma kuma ta nafatan haka ta kasance,da sai ta ce tafi kowace mace sa’ar mijiduniya,don A.m wuta ne gurin kyau da tsari.
Washegari Juwairiya ta na kicin abinci take haɗawa hankalintakwance cikin jin daɗin abin da ya faru,jiya tsakaninta da shi jiyasaboda kwana ta yi muryar sa na maimaita godiyar da ya yi mata.
A hankali ya shigo ba tare da ta sani ba don ta zage ta na haɗa mishiabincin da zai ƙayatar da shi.
Ji ta yi an rungume ta ta baya ba tare da ta lura ya shigo ba.Wani irinihu ta saki tare da matsawa gefe,sai kuma da ta lura shi ne ta ɗansaki murmushi.
“ Kai ki na da matsala Juwairaah!Yanzu da matar gidan na nan maikike tunanin zai faru?Ke akan komai sai an ga gazawar ki?”
Ta yi shiru kawai ta na murmushi ba tare da ta ce komai ba,don itaba ta san Zainab ɗin ta fita ba.
“Kawo min abinci yunwa nake ji.”
Ya faɗa tare da saka hannun shi a daidai gurin dimple ɗinta ya fita.
Bin sa da kallo ta yi har ya ɓacewa ganinta ta yi ajiyar zuciyasannan ta shirya masa abinci.
Bayan ta ije masa abinci ya na zaune da remote a hannunsa ya ce batare da ya yi duba gareta ba.”Amaryar wucin gadi zo mu yi hiratunda matar so ba ta nan,na lura kamar kina da ciwon rashinmagana.”
Sai ta tsaya ta na kallon shi da ya yi fuska kamar ba shi ya yimaganar ba.
“ Ki zauna mana kika yi min tsaye haba sai kace wata soja.”
Namma zama ta yi ba ta ce masa ƙala ba don ta lura so yake tatanka.
A.m da ya kasa controling ɗin kan sa ya matsa kuda da ita ya namata wasu irin abubuwa.
“ Don Allah ina roƙon ka bu ɗaya.”.
Ta ce yayin da idanunta suka fara zubar hawaye tsayawa ya yi ya nakallonta zuwa can ya nisa ya ce da ita.”Ina jin ki Juwairaah.”
A hankali ta yi ƙoƙarin saita muryar ta ta fara magana cikin sanyi.
“Ka ce kar na saka soyayyar ka a zuciyata ni ma ina roƙon ka da kadai na ƙoƙarin kusanta kan ka da ni mu tsaya daga iyasharaɗinmu,saboda ina tsoron kar zuciyata ta kamu da sonka duk dana san kai ɗin ba sa’ar soyayya da ni ba ne,kaddara ta haɗa mu inajin tsoron ranar da zan tsinci kai na cikin soyayyar ka don na san kayi min nisa na har abada,amma soyayya ba ƙarya ba ne kuma zuciyaba ta da ƙashi,A.m babu wata mace da za ta yi tozali da kai ba tareda ta faɗa cikin kogin son ka ba.
Jikinsa ya yi sanyi matuƙa ganin maganar da take yi daga cikinzuciyarta ta fito.
“Juwairaah kin taɓa ganin an yi zaman aure ba tare da haka ba?Dukauren da kika ga ya ginu to hakan ya gina shi.Bani da nufin na cutardake ki yadda da ni ki yi ƙoƙarin yaƙar zuciyarki daga son jefa kicikin wahala da take son ta yi,kafin na aureki sai da muka yi sharaɗibabu so a cikin tsarinmu don ba zan taɓa zama dake na har abada ba,amatsayin matata.Kuma karki manta uban maƙudan kuɗi na sa naauro ki“.
Ya numfasa ya na kallonta ganin kukan da take yi hannunsa ya sakatare da tarar hawayen da yake zuba kamar an buɗe famfo.
“ Ki adana sauran hawayen ki a kwai ranar da zaki buƙace su kar fasu ƙare,na tabbata ranar da kika haifa min baby in na baki abin da nayi ninya Juwairiya zaki nemi hawayen ki ki rasa bayan kin ƙarar dasu akan banza,don ni banga abin kuka a nan ba.Ki tuna mahaifiyarkina cikin kwanciyar hankali da jin daɗi shin hakan bai saka ki saka nia cikin farin ciki ba?”
Ya tambaye ta idanunsa a kanta hawaye suka ci gaba da zuba ganintaƙi magana sai sai ya miƙe ya fice daga gidan.
“Humh ba na tunanin a kwai abin da za ka ba ni na yi farin ciki fiyeda ka sani a cikin zuciyarka.Am ka ƙi ka gane abu ne na zuciyaAllah ya jarabce ni da sonka tun kafin ka bijiro da manufar ka akaina,na yi burin kar mu haɗu tun ranar da na yi tozali da kai akundin rayuwata.”
Kuka take kamar wata zararriya ta na maganganu sosai daga bayamiƙewa ta yi,bayan ta fahimci ya fice daga gidan ta ci gaba daaikinta.
A haka rayuwa take wucewa A.m ya na more amaryar wucin gadiduk da ya ƙosa su rabu,amma ya na girmama lamarin Juwairiya azuciyar sa.
Tun ta na ɗari-ɗari da shi har ta saki sosai da shi domin ya bada dukwata ƙofa da zai saka ta saba da shi,har ta kai ga A.m ya na waya daJuwairiya a ɓoye su sha hira ya na tambayarta ko ya jefa ƙwallon araga.
Duk sadda ya yi mata wannan maganar hankalinta ya kan tashimatuƙa ita gani take irin abubuwan da yake mata son ta yake.
Juwairiya ta saba da A.m ta na jin sa a ran sa kullum sai sun haɗu dajuna ranar da Zainab take gida kuwa,dole sai ya kira ta a waya sunyi hira wannan ya ƙara saka ma Juwairiya son shi na mutuwa ta najin duk ranar da ya rabu da ita mutuwa za ta yi.
Amma idan Zainab ta na nan ko kallon Juwairiya ba ya yi,har yau inzai yi maganar ta ko Zainab ta yi mishi nuna yake bai riƙe sunan taba,sai dai ya ce wancan ko wa ta ke da suna.
Tun Zainab na mata ƙorafin ta rinƙa cire hijabinta har ta gaji,ta daina don ta fuskanci ko mai za ta yi mata ba za ta dai na ba,kuma inaruwanta tun da ta fahimci Juwairiya a kwai tsafta da kula da kai.
Juwairiya ta goge ta waye ta ƙara wani irin kyau jikinta ya ciko koina,ita kanta mamakin yadda ta goge take yi,sai dai ko hoda ba tasaka wa bayan kwalli duk da Zainab ba ta hana ta ba.
To ina ma take da lokacin kanta daga aiki sai chert,don in dai ba tagurin aiki ta na riƙe da wayarta,ko magana take hankalinta na kanwayarta.
Duk lokacin da Juwairiya ta samu tsarki sai ta samu lemun tsami daruwan gishiri ta sha,ita burinta ko a matsayin mai aiki za ta zauna indai ya na nuna mata irin wannan soyayyar za ta rayu da shi na harabada.
Kimanin tsawon wata bakwai A.m ya na jiran ya ji ta ce mishi ta nada ciki,amma shiru kake ji malam ya ci shirwa,har ya fara tunanin toko shi ma baya haihuwa.
Hankalin sa ya fara tashi sosai gashi A.m har ya kasa daurewa yatambayi Juwairiya shi fa ya ƙosa,lallaɓasa take yi ta na faɗa mishiAllah ne bai kawo ba,amma a ranta ta san abin da take yi.
Ya na zaune a falo zuciyar sa na tafarfasa da ya tabbatar Zainab taƙara tafiya ba tare da ta sanar mishi ba,ya ji a ran shi tunna ya na daJuwairiya zai ci gaba da haƙuri har zuwa sadda za su rabu,ammaduk da hakan dole ta ɗauki mataki saboda ya kamata ta sanar mishiko da bai amince ba,ba wai ta kashe wayarta tafi ba.
Wayar A.k ya katse masa tunanin da yake yi sai dai bai ɗauka bawayar ta katse ya bi,amma ba network sai a ka ce wayar a kashe.
Wani irin bugu ya ji ana yi mishi wanda ya tada hankalin sa da sauriya fita don shi a zaton shi ɓarayi ne suke so su shigo mishi,duk da cewa ƙarfe huɗu da rabi ne na yamma.
Ya na isa get ɗin maigadi ya sheƙo da gudu ya na faɗin.” Ka yihaƙuri ina bayi na zaga.Wannan wa ne mahaukaci ne yakeƙwanƙwasa ƙofa Allah ya sa lafiya.”
A.m bai kalle shi ba ya buɗe kofar sai kuma ya ƙame cikin tsananinmamaki ganin Baba Sani a tsaye ya na ta mazurai.
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]