[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 54 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

cike da murna suke kallonsa dan basu tab’a tunanin wannan maganganun nasa ba shiru yayi yana kallonsu.

dady yace,

“Alhamdulillah Allah mungode maka,

mr Solomon naji dad’in maganar ka duk da wannan ba abin mmk bane idan aka duba Allah subhanahu wata’ala dan shine mai shiryarwa mun godewa Allah daka kasance shiryayye, sannan shi musulinci tushensa shine imani da Allah

da kayi imani da Allah to magana ta k’are sai kuma kayi shahada ba’a cike form bare asiya don shi addinin mu addinine na aminci da salama da kuma zaman lafiya ubangiji Allah ya dad’a shiryar damu.”

nan dady ya bashi kalman shahada ya amsa cike da murna itama maman david aka bata tayi d’aya bayan d’aya aka basu kalmar shahada suka amsa.

jannat tayi mmkin hakan dan tasan su d’in mutane masu ak’ida da son addininsu lallai Allah shine mai shiryarwa ta fahimci dan basu san ya musulman suke bane tuntuni tunda gashi d’an xaman da sukayi tare yasa sun musulunta ubangiji Allah ya shiryar da bayinsa.

dady ya cigaba da mgn,

“menene sunanka?”

“solomon “

“akwai sunan da kk so?”

shiru yayi yana nazari.

Abba ne yace,

“tunda sunan shi Solomon ya xauna da sunan nashi Sulaiman ko ya ka gani ?”

da sauri yace

“eh haka yayi”

maman david tace

“ni sunana sera amma ina son na kuma fateema”

dady yace

“masha Allah fateema suna mai daraja”

ta nuna Emanuel

Abba yace,

“emah kaifa?

kansa a k’asa yace,

“ina son sunan kabeer”

Abba yace

“mashaa Allah kabeer daga yau ka kuma kabeer”

david daya ke kusa da maman shi yace,

“ni dai ina son yusuf”

dady yace,

“masha Allah yusuf sunan annabin Allah suna mai daraja,

ubangijin Allah ya tada kafad’inmu a aljannah”

dukansu suka amsa da

“amin”

Abbu yace,

“mahboob ya dai ? wacece surukar tawa ne ?

murmushi mahboob d’in yayi

“Abba ba yanxu ba tana karatune sai ta gama”

“toh mahboob ubangiji Allah ya kaimu lokacin”

suka amsa da amin

suka cigaba da tattaunawa inda xasu d’auko malamin da xai koya wa su papa yadda xasu kula da addini.

2 days ago

Sun gama shirinsu tsab xasu fara tafiya Italy jannat kam jikinta asanyaye yake tana tuna halin da ya khaleel xai shiga.

d’akinsa taje yana xaune fuskarsa kamar pepper tayi sallama ya amsa batare da ya d’ago kansa ba kanshi akan waya yana dannawa.

aranta tace “yau kam dannan waya akata shi dashi”

kusa dashi taje ta xaune had’e dasa kanta ak’irjinsa

bai kalleta ba still kanshi na sunkuya yana dannan waya

“ya khaleel” ta fad’a muryar ta assnyaye.

bai amsa ba bai nuna wata alama na taxo kusa dashi ba tasan abinda yake yiwa sbd xasu tafi ba xasu dawo ba sai sun gama xuwa ko ina wanda suna dawowa xa’a fara hidiman biki.

muryar ta kamar xatayi kuka tace,

“ya khaleel kana son jefani cikin wani hali?

kasan yanda nakeji idan ranka ya b’aci, idan har baka son tafiyar nan baxan tab’a yinta ba dan baxanso naje wajan da hnklin ka bai kwanta ba”

d’ago kansa yayi ya kalleta.

kamar baxaiyi mgn ba da kyar ya jure yanayinsa yace,

“me kikeso nace? kin san irin yanayin dana ke kasancewa idan bana tare dake?

   ba ina jin haushin ki bane ina tausayawa kaina halin da zan kasance idan banji lallausan jikinki ajikina ba”

lumshe ido tayi tana jin ba dad’i ita kanta bata son tafiyar kawai bata da yadda xatayine.

“nasani ya khaleel yanxu ya kk ganin zanyi ko kawai nace ba xani ba?”

fuskarsa yasaki kad’an ya sa hannu ya kwanto ta jikinsa.

“ina sonki jannah!”

kwanciya tayi ajikinsa had’e da sakin numfashi.

“ina sonka sosai ya khaleel”

shafa kanta yayi,

“kada ki damu kuje tunda hidima ce”

ashagwabe tace,

“nifa bazan tafi na barka ba”

cike da jin dad’i ya xaro ido

yasa hannunshi dai dai sai tun xuciyarta.

“ina nan cikin xuciyarki baxaki tafi ki barni ba kullum xuciyoyinmu suna tare da juna”

ranta ajagule ta tab’e baki.

“bana son nayi nesa da kai fa”

ajjiye wayar hannunsa yayi ya kishingid’a.

tabishi had’e da bajewa ajikinsa.

“waya ce miki xa muyi nesa da juna ?”

ya kalli agogon hannunsa

“tashi kije kada suyi ta jiranki”

wani kallo tai masa na mmk.

“korata kakeyi?”

yayi dariya

“bance ba”

ya fad’a yana kallon fuskarta datake a d’aure,

kwanciya ta kumayi ajikinsa.

“toh na fasa xuwa”

mik’ar da ita yayi,

ya shafa lip d’inta

“ina son d’ank’ara min bakin nan naki”

ya janyota yasa bakin shi cikin nata ya tsotse su tass sannan ya saketa yana numfashi.

ta mik’e jikinta a mace.

“muntafi ya khaleel ka kulamin da kanka”

kai ya d’aga mata yana shafa sumar kansa.

tayi mmkin rashin nuna damuwarsa akan tafiyar tasu sosai

ta fito ta samesu sun shirya kafin su k’arasa airport sai da sukaje kasuwa sbd jirgin nasu sai yamma xai tashi.

ba su isa Italy ba sai sha biyu na dare direct in da Abba yace su sauka nan suka sauka wanka sukayi da sallah su kwanta sbd gajiya

washegari da safe suna kitcean dukansu sallamar shi sukaji da mmki suka kallo k’ofa yana sanye cikin k’ana nan kaya hannun shi rungume da jakar kayansa hjy murja tayi dariya

“khaleel barka da xuwa ka biyo jannat d’inka ko ? ai nasan xa ayi haka”

murmushi yayi kad’an baiyi mgn ba sai jifan jannat yake da wani rikitaccen kallo.

taji dad’in ganin sa sosai dan baccin jiya duk shine amafarkinta.

bata son lokacin data k’araso ta amshi jakar kayan had’e da sakarwa juna

k’ayataccen murmushi.

dukansu su ka kallesu hjy murja ta girgixa kai tana murmushi aranta tace “yara kamar su cinye kansu dan soyayya”

kai tsaye wani b’angare tayi dashi na gidan d’aki na musamman ta kaishi suna shiga ya janyota jikinsa suna dariya cikin murna tace,

“nida man nasani jikina ya bani kana kusa dani”

shafa cikinta yayi ya ware ido

“nifa ajiyata naxo na kula da ita bazan iya xama bana shafa lafiyar ajiya ta ba”

wata iriyar dariya tayi.

“ni kuma fa wato ma ajiyar ka kabiyo naga alamar kafi son ajiyar nan taka dani”

ta fad’a tana k’ok’arin ture shi jikinta,

“ah beautyna kada kiyi kishi da ajiyata”

ta tabe fuska had’e da turo baki,

“ba dole ba tunda kafi sonta dani”

dariya ta bashi dan yana son shagwabar ta.

“kin san ke ta musamman ce awajena ajiya ta ma ta dabance,

fad’amin banbanci tsakanin ta musamman da kuma na daban “

far tayi da ido.

dariya yayi

“ina sonku duka beautyna”

ya sunkuya dai dai saitin cikinta ya d’age rigarta da sauri ya d’ago kai yana kallonta

“beautyna kinga ajiyata ta fara girma ko?”

shafa cikin nata tayi.

“ni ban gani ba”

d’agowa yayi ya shafa wuyanta daya ke kyalli da hasken fatarta

“zaki min bayani anjima”

ta xame jikinta

“bari na kawo maka breakfast”

dawo da ita  yayi jikinsa,

“noh ! ni da wani abu daban nakeso nafara breakfast dashi”

tsura masa ido tayi ta shafa sajensa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

yana shirin mgn ya ji bakin shi cikin nata ta sha cikin yanayi najan hnkl tuni ta rud’ashi ya k’ank’ameta yana maida mata martani cikin rikicewa dan baiyi tunanin xata iya hakanba

kafin wani lokaci sun rikita kansu tuni lbr yasha banban da sauri ta yakice kanta ya kuma dawo da ita ta kwace da kyar tayi nesa dashi.

“kayi hkr ya khaleel kayi breakfast ka huta tukunna”

idonshi a rine yake kallonta

da kyar ya iya d’aga kansa.

“ina sonki beautyna”

itama yanayinta asauye tace.

“ina sonka sosai ya khaleel”

ta fice daga d’akin idonsu akan juna.

tun aranar suka tafi wajan siyayyarsu tare suka tafi da ya khaleel yana lik’e da ita motsi kad’an sai yace”ki kula fa kin san akwai ajiyata a jikinki”

murmushi kawai takeyi sai dare suka dawo a d’akin shi ta kwana hannunshi rungume da cikinta wai baxai iya kwanciya shi kad’ai batare da hannunshi na tab’a lafiyar ajiyarshi ba

kwanansu biyu yau suna shirin gobe xasu wuce india dan dubai ne last inda xasuje.

tana tashi taga  9 miss cal d’in ya khaleel ta d’an xaro ido sam tamanta da wayar na silent ta kira wayar tajita akashe ta ajjiye ta nufi b’angarensa a kulle ta tarar da k’ofar gabanta ya fad’i tabbas tafi kowa sanin ya khaleel bai son ya kira waya ak’i d’agawa jikinta asanyaye ta dawo falo tana tunanin ko ina yaje?

wasa wasa har yamma ya khaleel shiru tun tana iya daurewa har ta kasa abinci ma kasa cinsa tayi suna shirye shirye tana gefe tayi ta gumi tana kallon wayar ta lokaci xuwa lokaci tana kiran numb d’insa

duk ta jita akashe ji takeyi kamar ta fasa ihu dan tuk’ik’in ba k’inciki.

duk sun kula da yanayinta tun safe kasa daurewa hjy murja tayi sai da tambayeta

“jannat me ya farune ?”

kamar zatayi kuka tace,

“ya khaleel tun safe bai shigo ba kuma baya b’angarensa na kira wayarshi a kashe”

xuba mata ido sukayi sulthana tace,

“toh ina ya tafi”?

girgixa kai jannat tayi

rubayya tace

“ko ya ce miki xaije wani wajan?”

girgixa kai ta kuma yi

zahra tace,

“ku kwantar da hnklinku baxai b’ata ba fa ina ga wani wajen ya tafi”

jidda tace,

“ikon Allah gsky da wuya ya khaleel ya kashe waya”

hajiya murja data ke binsu da ido ta dawo kan jannat da idonta yake kan waya,

“jannat kinsa fa namijine dole xaiyi sha’awar xuwa wani wajan ki kwantar da hnklinki xai dawo kinji”

kai ta d’aga mata

har dare kusan k’arfe goma shiru bai dawo ba jannat kasa daurewa tayi tasa kuka sosai breakfast kawai tayi bata ci lunch da dinner ba

ba yadda hjy murja batayi da ita akan taci abinci tak’i ci sai kuka.

sunyi kiran duniyan nan wayarshi akashe. xugum sukayi a falo suna rarrashinta.

muryarshi asanyaye yai sallama suka xuba masa ido.

jikinsa sanye cikin jessy kayan ball farare hannunshi rik’e da jaka k’arama ta kayan da ya fita dasu cikin k’asaita yake tafiya cike da jin k’arfi tamkar matashin sadauki.

dariya sulthana tayi tace,

“oyoyo majunun lailah”

kallonta yayi ya kauda kai.

dariya sukayi dukansu hajiya murja tace,

“wannan ai sunfi majnunun laila k’araso nan ya khaleel kayi laifi”

fuskarshi asake ya k’araso ya xauna kusa da jannat da kanta yake a b’oye jikin cinyoyinta.

sulthana tai karaf tace,

“haba majnun meyasa kabar lailanka cikin rashin sanin inda kake?”

wani kallo yai mata.

kama bakinta tayi,

“aw ashe fa tsoronka nakeji kai d’inne wllh idan ka b’ata rai tamkar sadauki awajen ya’ki umma ni dai na gudu dan wllh tsoron idon ya khaleel nake” tana tafiya gudu gudu tana maganar.

dariya sukayi suna kallonta sum sum

suma suka bi bayanta dan sunga fuskar tashi ba wasa.

hjy murja ta kalleshi tana dariya

“majnun yau kayi laifi ka tafi ka bar laila cikin wani yanayi,

ka ganta nan breakfast kawai tayi yanxu ta gama rusa mana kukan ita ya khaleel,

tun safe sai yanxu?

gata nan ka rarrashi kayar ka dan kai kad’ai ne xaka iya sauke wannan fushin ni dai na bi bayan y’ay’ana”

ta mik’e tayi b’angaren su.

shiru ba wanda yace wa kowa komai shi kam tunaninsa ta ina xai fara lallashinta?

ita kuma tunaninta ko har yanxu fishi yakeyi sbd bata d’aga wayanshi ba?

yana k’ok’arin yi mata mgn

cikin sanyin murya tace,

“kayi hkr nasan kaimin wannan horon ne sbd ban d’aga wayanka ba.”

katseta yayi ta matsowa kusa da ita kamar xai shiga cikinta.

yasa hannu ya d’ago fuskarta baiyi tunanin xatayi saurin bashi hkr ba jannat ta wuce tunanin shi wajan hkr da saukar da kai akansa

“wannan salon naki yana sani jinki tamkar kece ni,

ngd wa Allah daya bani matar da baxan wahala akanta ba duk abinda nakeso kin karance shi kin kuma iya shi,

na fahimci biyayyarki pure ce original kina yin komai ne sbd biyayya ga umarnin Allah da biyayya ga mijinki wacce hakan ne xai kaiki samin rahama daga Allah,

ngd wa Allah da yai min baiwar samun mace irinki mai hikima mai tsoron Allah,

ni yakamata na baki hkr kafin nayi mgn kin rigani,

wannan ya isa yasa naji bana son kasancewa da kowacce mace aduniya irinki,

“kiyi hkr beautyna ban kyauta ba, nasani amma ba zan kuma ba”

ya k’arasa had’e da rungomata jikinshi,

ya fi 30 mints yana rarrashinta had’e da wasu maganganu masu dad’i haka yai k’asa da kanshi wajan lallashinta bai barta ba sai daya ga tana dariya.

abinda yakeso kenan yaga dariyarta tuni ya saki shima

“meyasa kika wahalar min da kanki da kuma ajiyata?”

murgud’a baki tayi,

“bayan kai ka wahalar damu”

kiss yaiwa kumatun ta.

“ai min afuwa tashi muje na baku abinci kuci na kuma k’ara baku hkr”

ya mik’ar da ita tayi luu xata fad’i ya rik’eta cak ya d’auketa yai b’angarensa da ita.

abinci ya bata taci yana bata yana k’ara rarrashinta har taci ta k’oshi sai da tagaji da rarrashin ta turo baki,

“nifa ya khaleel nace maka na hkr”

“toh bari naji ajiyata ma ta hkr dan na san fushin har da ita,

itama fushin take dani”

kallonshi kawai tayi dan ya daina bata mmk

rigar ta ya kama yana k’ok’arin cirewa.

xaro ido tayi

“menene haka?”

kallonta yayi

“ina son bawa ajiyata hkr na kuma k’are mata kallo tunda ga sama har k’asa”

kafin tayi mgn har ya k’arasa cire ta duka

washegari suka bar Italy

india suka wuce nan ma kwanan su uku suka dawo Dubai anan sukai kwana biyu jannat kam tasha tarairaya da kulawa ko agaban waye baya shayin kula da ita ba kuma ya barin tayi nesa dashi ko tafiya xasuyi motar su daban idan suka sauka hannunshi cikin nata wai yana taimaka mata tunda yanxu ba ita kad’ai bace akwai ajiyarsa.

itakam mmkin ta sam tarasa gane inda ajiyar  ta shi take.

bayan sun dawo  aka kawo lefensu duka kowacce jakar akwati 36 kaya masu kyauta nagani na fad’a.

k’ayyade k’ayatuwar kayan wani sabon babine na daban ka fasaltasu da kanka. Alhaji Adam ched’e ne ya had’a lefen sbd yace shine tukwicinsa amatsayin shi na uban angwaye.

kwana uku da dawowarsu akafara shirye shiryen biki an tsara komai da irin hidomin da xa ayi day one ranar farko ta hidimar itace wacce anty safiyya ta shirya k’anwar momy ranar barebari sbd su  barebari ne  suna kiran ranar da:

*Wushe-Wushe* shine traditional day nasu wanda amare da k’wayensu xasuyi shiga irinta kanuri da mazajensu xa’a k’awata wajan da makad’an gargajiya irin nasu achashe da yiwa wajan ado da k’amshin turare mai dad’in gsk aci abinci na gargaji biski da burabusko da *banderu* waje yayi kyau sosai dan anan cikin gidan sukayi.

kowa ka gani yana cikin nishad’i da annushuwa gida yacika dam da dangin ched’e kyawawan yanmata dan gin hjy Nabila ma ba abarsu abaya ba ga dangin dady suma datasu gudunmawar wannan yana wane wannan sunyi rawa da lik’a manyan daloli.

motsi kad’an jannat tayi yana mata mitar tabi a hnkl bai son ta matsawa awajiyar shi.

yana lik’e da ita kamar cingam su sulthana an sami abinda ake so da sun faki idonsa su tsokane ta wai mai cingam ko suce majnu nun laila su kansu iyayen sun jinjina shak’uwa da soyayyar jannat da khaleel momy har mamakin sauyawar shi take duk irin miskilancin sa lallai ta yadda mace na sauyawa mijinta rayuwa.

103/104

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]