[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 53 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

kallonshi tayi tana mmkin canxawarsa lokaci d’aya janyota jikinsa yayi yana dariya.

“kina min kallon kamar yau kika sanni”

langwab’ar da kanta tayi a k’irjinsa.

“naga ka canza min”

shafa bayanta yayi

“ke kika canza ni tsakanin jiya xuwa yau kinsa ina jin kaina tamkar yau naxo duniya”

dariya ya bata tayi a nutse had’e a kai masa d’ank’aramin duka a k’irjinsa.

“kaji ka ko ? yanxu kuma xolaya ka fara?”

d’ago da fuskarta yayi ya kashe mata ido d’aya.

“kin san baxanyi xolaya  ayau d’innan ba duk abinda kikaji nafad’a haka yake kin sauyani tsakanin jiya xuwa yau,

shiyasa ako da yaushe nake ce miki ta dabance yes ke d’in daban kike”

lumshe ido tayi taji dad’in yaba mata da yayi.

“kaima na daban ne”

da xolaya yace.

“nasani tunda na tabbatar da hakan a jiya da daddare”

ya k’arashe da dariya.

kukan shagwab’a tasa masa had’e da dukan k’irjinsa kad’an.

“ni ba ruwana”

tana k’ok’arin tashi daga jikinsa.

fincikota yayi yana dariya,

“babu inda xaki fa yau ajikina xaki yini”

cikin shagwab’a tace,

“wanka fa zanyi”

kafin tak’arasa ya d’agata cak daga jikinsa ya sureta bai direta a ko ina ba sai cikin toilet yana k’ok’arin cire mata kaya tana kauce kauce had’e da dariya shima dariyar yake.

“karki manta da sharad’ina yau baxaki wahalar min da kanki ba nixan miki komai”

ya cire mata kayan jikinta yai mata wanka  sun b’ata lokuta kafin su fito daga toilet d’in gaba d’ayansu suna cikin nishad’i da farin ciki kowannansu xuciyoyin su cike da k’aunar juna

daren yauma bai kyaleta fur yak’i saurara mata dan jin kansa yake mara hak’uri baxai iya kallonta kwance kusa da shiba tasha wahala duk da bata kai ta jiya ba.

da kansa yai mata wanka da safe tana ta fushi sbd rashin hkrn daya nuna jiya cikin hikima ya lallasheta ta hkr suka fara shirin dawowa jikinsa a sanyaye ya kalleta ta gama shirya kayansu tana ta murna xasu koma.

“jannah ! murnar me kike haka?”

fuskarta d’auke da murmushi tace.

“ina murna xamuje gida mana”

wani irin kallo yai mata ranshi ab’ace,

“kina murna dai xaki daina sauke hak’k’ina akanki ko”

kallonshi tayi tasan a k’ufule yake ta kuma gane dalilin k’uluwar tasa gefenshi ta xauna tasa kanta a kan kafad’ar shi hannunta a k’irjinsa tana shafawa muryarta a tausashe cikin lallashi tace.

“bazanyi murna da hakan ba kada kayi tunanin kai kad’aine xakayi missing d’ina ni kaina zanyi fiye da yadda xakayi sbd kasa ba min da kwanciya a jikinka kasa ba min da abubuwa masu yawa yanda idan har ban jika ajikina ba ni kad’ai nasan yanayin dana ke shiga,

kasan kai na daban ne a wajena kada ka b’ata ranka bafa rabuwa xamuyi ba muna tare ko da yaushe”

cikin sanyin murya yace.

“saura kwana nawa ma ki tare?”

dariya tayi tace,

“wata shida”

zaro ido yayi ya d’anci mur

“lokacin kin kusa saukemin ajiyata”

ya fad’a yana shafa cikinta rufe idonta tayi takasa magana dan muddin ya fad’i haka yana sata jin kunya sosai.

ya kalli fuskarta da idonta yake a rufe ya ja dogon hancinta ya cije leb’ensa na k’asa.

“nayi ajiyata a cikin ki plx ki d’inka kular min da ita”

da sauri ta bud’e idonta

“ajiyar me kayi da xan kula da ita?”

shima kallonta yayi da mmk

“ajiyar babynmu nayi tun shekaranjiya jiya kuma na k’ara masa kuxari”

da sauri ta rufe masa baki tana kallon k’ofa.

“baka jin kunyar wani yaji”

ware ido yayi ya tab’e baki

“ko ma waye yaji rungume nake jikin matata mai d’auke da ajiyata acikin wannan shafaffen cikin”

mik’ewa take k’ok’arin yi daga jikinsa.

dawo da ita yayi

“ina zaki tafi kike gaggawa haka”

kwab’e fuska tayi kamar xata sa masa kuka.

“ya khaleel muta fi gida”

had’a ransa yayi

“nafasa tafiya yau sai nest week”

kama bakinta tayi ta rufe lip d’inta.

“nest week ya khaleel?”

bai amsa mata idonshi nakan rigar jikinta da d’inkin ya xauna mata sosai ya fito da halittar k’irjinta.

lumshe ido yayi,

ganin haka yasa ta mik’e da sauri ta juya xata bar wajan.

ya rik’o hannunta yana jifan ta da shu’umin murmushi tayi narai narai da ido kafin tayi wani motsi ya dawo da ita jikinsa yana dariya

“kinfiya tsoro beautyna”

ajiyar xuciya tayi

“ba dole ba kai d’inne ba wasa”

haka ya rikitata da salo ya ya mutsata tafi mints 20 yana mata abin da yaga dama da kyar ya kyaleta

yasa hannunsa ya tallabo fuskarta

“kwara da kika gane ni d’in bani da wasa wajan kula da ke”

yafad’a had’e da mik’ewa,

murgud’a masa baki tayi a

had’e da yi masa hararar wasa.

” duk maganar da nayi sai ka bani amsar ta da wannan salon naka ko ? zan rama ne”

janyota ya yi ya d’an xaro mata ido,

“me xaki rama?”

ta turo baki

“abinda kakemin”

ware baki yayi cike da xak’uwa

“plx beautyna rama yanxu kinji? wllh karki yarda rama ki nuna min kema fa gwana ce”

yafad’a yana dariya

kwace jikinta tayi itama tana dariya

“zan rama amma ba yau ba sai ranar da …”

matsowa kusa da ita yayi.

aguje tabar wajan.

ya marairaice murya

“plx ki bari na miki wani abu kafin mu fita yanda xakiji dad’in ramawa”

dire diren k’afa tafara yi kamar yarinya k’arama.

“nifa…. nifa….. mutafi “

tab’e baki yayi

“toh naji mu tafi idan na biye miki xamu kai ishsha’i “

dariya tayi

“oh ! ni ce ma kai”

yanda tayi yayi

“oh! ke ce ma ni”

ya fice yana dariya

“ki canza wannan kayan dan kin san na ya mutsa miki su”

kafin ya kai bakin k’ofa tace

“zan tafi gida dasu a haka ince kai ka ya mutsa minsu”

tsayawa yayi ya waiwayo

“da gaske ? da kin taimakeni kinga shikenan sai suce kutafi gidanku ba sai nan da wasu 2 weeks ba”

sakin numfashi tayi

“ni dai jeka plx kada kasa murasa jirgin nan”

ya fice falon gidan xuciyar shi tass cike da son matarshi wacce yake burin taxama uwar d’ansa na farko

bata dad’e ba ta fito shirye cikin brown d’in laffaya me ado da duwatsu kalan orange.

ya d’ago kansa ya kalleta fuskar shi d’auke da murmushin mugunta ya mik’e tsaye ta k’araso hannunta d’auke da jakar kayansu ya amshi jakar,

“muje maman y’an biyu”

xaro ido tayi ta girgixa kai ta shiga gaba yabi bayanta yana dariya k’asa k’asa dan yasan abinda ya shirya mata tana fita harabar gidan ta nemi motor d’in drivern su tarasa da mmk ta waiwayo ta kalli khaleel

“ya khaleel ina drivern yake”

shima da mmk ya kalleta

“shine abinda nake son tambayarki kin aikeshi ne?”

b’ata ranta tayi

“ni ban aikeshi ko ina ba”

shima b’ata ransa yayi cikin ko in kula yace.

“shikenan myb baya son mu tafi yau baxan iya xaman jiran sa anan ba komawa ciki xanyi”

kamar tasa kuka dan haushi,

“ka kira wayar shi mana”

a kaikaice ya kalleta.

“ki kirashi mana ga waya nan a hannunki”

zuba masa ido tayi.

“bani da numb d’insa”

d’age kafad’arsa yayi

“nima bani da numb d’insa”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

haushi sosai ya kamata dan ta fuskanci yana sane idan batayi da gaske ba fa baxasu koma gida a yau ba.

jikinta asanyaye ta wuce tagaban shi ta shiga cikin gidan a falo ta xauna tayi tagumi.

ya bita da kallo had’e da biyo bayanta.

kusa da ita yaje yasa hannu ya xame tagumin da tayi ta kalleshi ya girgixa mata kai

“gani kusa dake tagumin me za kiyi?”

muryar ta asanyaye tace,

“bana son muyi wa Abba k’aryane”

cike da gamsuwa yake kallonta bai ce komai ba ya juya ya shiga bed room.

ganin maganarta tayi masa tasiri yasa ta mik’e tabi bayansa.

atsaye ta sameshi ta rungumo bayansa hannuwanta xube a saman k’irjinsa yasa hannunshi ya shafo hannayenta.

a hnkl tace masa,

“kayi hkr my king nasan baka son mutafi sbd kana tunanin in muka tafi zan gujeka,bana tunanin akwai ranar da xata wuce batare da na jini kwance jikinka ba,

kayi hkr mu tafi kwana 2 Abba yace muyi idan muka k’ara baxaiji dad’i ba kasan hnklin shi atashe yake bayason mu dink’a nesa dashi sbd abinda ke faruwa”

juyo da ita yayi gabansa ya warware laffayan jikinta yasa hannu a kafad’arta

“xamu tafi yau amma jirgin yamma xamu bi”

dad’i taji dan tason kad’an da aikinsa yace baxa su koma ayau ba,

“ngd ya khaleel”

shafa lip d’inta yayi

“saura idan mun koma kullum sai nayi cigiyarki” ya k’arasa da jan hancinta.

far tayi da ido

“zanxo da kaina ba sai kayi cigiya ba”

ya shafo cikinta

“ina son ganin ranar da xa’a haifemin ajiyata”

tab’e baki tayi

“ina mmkin wannan ajiya ayi min ita batare da na saniba”

dariya ta bashi

“xata bayyana kanta duk da bana son bayyanar tata ta wahalar min da ke”

basu bar abuja ba sai yamma gab da magruba suka isa kano tunda suka shigo yake b’ab’bata rai wai yana jin haushin missing d’inta da xaiyi daren yau.

itakam b’oye dariyar kawai tayi koda suka isa gida duk jama’ar gidan kowa ya fito yana murnar dawowarsu shikam fuskarshi a d’aure take

kai tsaye d’akinta ta k’arasa aciki ta tarar da rubayya tana waya sulthana ma wayar take hindu tana kwance tana karanta novel jidda na chating ita da zahra cikin murna suke mata sannu da xuwa xama tayi suna tsokanarta musamman sulthana

“babbar anty antyn soyayya hop ansamo mana d’an abuja”

ta k’arasa da dariya dukansu dariyar sukai banda jannat data had’a rai ta mik’e ta shiga toilet tana jinsu suna cigaba da tsokanarta

bayan ta fito daga wanka tana shafa mai rubayya data ke waya ta waiwayo ta kalleta

“antynmu ance inmiki sannu da xuwa”

da mmk jannat ta kalleta kafin tayi mgn sulthana ta katseta

“anty rubayya ki fad’a mata gsky,

anty jannat bayan tafiyarki ansawa anty rubayya rana”

da murna jannat ta bud’e baki

“mashaa Allah naji dad’i”

sulthana tace “baki tambayeni waye angonba”

“waye angon namu”

far sulthana tayi da ido

“yaya prince A.K Garkuwa”

da murna jannat tace

“ikon Allah naji dad’i sosai”

sulthana ta cigaba da mgn

“ansa rana d’aya da bikinki da ya khaleel wato nan da 2 weeks sai ki shirya yanxu amaren biyar ne ” jannat ta ce “biyar kuma?”

zahra tai saurin cewa

“hindu ce cikon ta biyar ita da yaya hafiz k’anin hjy murja ni kad’ai ce nayi saura acikin ku”

wani iri jannat taji tausayin zahra ya kamata muryarta a d’an sanyaye tace.

“bakomai zahra komai lokaci ne idan yayi dole ayishi Allah ya baki nagari”

dukansu suka amsa da

“amin”

washegari da yamma suna gerdin d’in gidan kamar yanda suka saba suna hira jannat hankalinta nakan ya khaleel da suka fita yau tun safe shida Abba da dady wayar sulthana tayi k’ara tana duba screen d’in wayar sunan ya mukarram ta gani ta d’aga yace ta xo yanxun nan yana son ganinta yana kashewa ta mik’e tana mmkin wannan kiran na gaggawa da yai mata a bayan gidan ta sameshi yana waya kana gani kasan da mace yakeyi ganinta yasa ya kashe wayan

“xauna kiji wani abu k’anwata”

murgud’a baki tayi “kawai kafad’amin ba sai na xauna ba”

hararta yayi

“ina nan fa da halina ba canxawa nayi ba ko ki xauna kona nad’a miki duka”

zama tayi tana turo baki

“shikenan sai ace xa’a dakeni danna k’i xama”

dariya yayi

“yi hkr k’anwata kin san me ya faru ?”

k’ara turo baki tayi

“ina xan sani tunda ni ba allan musuru bace”

tak’arasa da murgud’a baki.

dariya ya kuma yi

“ina son wannan siririyar nan wata ke ma ?”

sakin fuskarta tayi tana dariya

“wacce acikinsu fad’i naji?”

“wata siririya zahrah “

wata iriyar dariya tayi.

“zahra ce naji dad’i ya mukarram”

“yanxu sulthana ya xa’ayi ? nifa in san samuna ne a had’a da bikinku har nawa”

mik’ewa tayi

“barmin aikin awajena nasan yadda xanyi”

“yawwa sulthana ina jiranki” ta tafi tana tsokanar shi ya bita da murmushi.

da daddare suna xaune dukansu xa’a fara tattauna abubuwan da xaayi da bikin anan hajiya murja tace “tana son xasu tafi italy ita amaren cen babban companyn daya ke kayan d’aki su xab’i wanda suke so daga nan tana son suje india subawa companyn rajah sarry su fidda irin designing na kayan  da xasuyi fitar biki dashi da kuma dubai nam ma suje companyn El’mukhtar suba su aikin kalan kayan daxasu saka na biki da kuma yanayin  irin adon sark’ar da xasu saka haka ta d’ink’a lissafe lissafe.

Abba yace

“bakomai xuwa jibi ma xasu fara tafiye tafiyen kuje duk inda kukeso”

kamar wata yarinya suna cikin tsare tsare sulthana tace,

“ya mukarram na fad’a ?”

ware ido yayi yakasa magana dan baiyi tunanin wannan wautar xatai masa ba.

hajiya Nabila ta kalleta dan kowa mmkin mganarta yayi

“fad’i mana”

ta yi dariya

“ya mukarram bari na fad’a”

kamar ya nutse dan kunya.

“cewa yayi wai yana son zahra wai asa ranar auren dashi”

dariya sukayi dukansu

Abbu yace

“ja’iri kalli yanda yake k’ifta ido”

Abba yace

“mai xai hana mukarram in dai tana sonka”

dady cike da murna yace

“nabashi ai mukarram mai xab’awa zahra mijine”

Abbuu yace

“ah’ah Dr sai fa munji ta bakin zahra baxa aiwa y’ata dole ba”

Abba yai dariya yana jin dad’i mara misaltuwa daa gidansa ya kasance ana rayuwar bak’in ciki ta dalilin rasa gudan jininsa yanxu ta dalilin gudan jinin nasa ana rayuwar farin ciki sannan gidan nashi cike da mutanen arxik’i way’anda baxai iya fad’in adadin alkairinsu akanshi ba dan sun reni tsokar jikinsa batare da sun axabtar dasu ba,

Abbuune ya katsewa Abba tunaninsa

“kana ji Alhaji Adam wai sai anyiwa y’ata dole abari muji ta bakin ta”

kansa Abba ya girgixa

“a’ah nima ina bayan Dr Bashir mun bawa mukarram zahra”

itakam kanta yana sunkuye dad’i ya cikata tunda ta ganshi taji yai mata sai gashi shima ya nuna yana sonta itakam tayaya xata k’i wannan santalelen balaraben.

hjy murja ce ta katsesu da cewa

“zahra kina son d’ana mukarram”

murmushi zahra tayi ta rufe fuskarta

jidda datake gefe tace

“tana sonshi gashi nan ta rufe ido tana dariya”

dariya sukayi dukansu

Abba yace

“mashaa Allah nayiwa Allah gdy daya nuna min wannan rana ina jin farin ciki mara misaltuwa Allah ngd maka”

papa dayake gefe tunda aka fara mgn baice komai ba shida maman david da yaransu sai dai in anyi abin dariya suyi.

ya kalli dady

“Dr bashir plx a ina ake siyan form a cike idan xa’a shiga musulunci ? ni dai ina son cike form d’in nan  dan xama na daku na d’an wannan lokacin yasa na fahimci addininku addinin gsky ne addinin taimako addinin da baya kyamatar wanda ba d’an addinin ba addini mai cike da tsabta da son junansu addini mai cike da dogara ga Allah addini mai taimakon marasa shi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]