[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 35 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Washegari da safe munira da sabreen suna karyawa se munira take cewa jiya kince Allah ya tabbatarwa hafsat da suhail alkhairi, sannan kuma naji kina cewa karyayi aure mekike nufu kenan? Sabreen tace ina ruwanki, dama ashe kunnenki nagunmu😙, munna tayi dariya tace mude namu eye👀.
Lokaci se tfy yakeyi kamal da mummynsa da kuma mijin mummynshi wanda suke kira da “UNCLE D” suna ta shirye shiryen zuwa biki, tare da abokansu na pakistan d’in. Gidan kamal da yake nigeri an sake gyarashi an canja komai na gidan d’akin sane kawai ba’a canjaba, dan bai dad’e da canjashiba, guri yayi kyau sosai abin se wanda ya gani😊. Mum kuwa tana ta shirye shiryen zuwan su mummyn kamal, hafsat kuwa tana can gurin su sabreen suna nasu shirin harda salma. Munira dad’i sosai taji wai yau gata ga aljana suna ta shirye shiryensu cikin kwanciyan hankali, itama sabreen ta sake jikinta anata mata gyara sosai😘. Su kakama dukda dai kamal tace baya bukatan suyi komai amma sunyi mata garan abinci sosai da kuma kayan sawa masu tsada. Gidansu Abbakar d’in munirama shiri sosai sukeyi abindai seni (SAD-NAS) danake d’auko muku rahoton😎
Shi kuwa suhail yana can yana gudanar da nashi shirye shiryen dan ganin bikin AMININSA da kuma SABSU d’inshi yayi kyau, dan shi kansa baisan adadin kud’in dayake kashewaba. Yau laraba ne su kamal suka shigo nigeria inda suhail da sauran friends nasu na nigeria sukaje d’aukosu. Hotel mai kyau suka sauk’esu da kuma UNCLE D, ita kuwa mummyn kamal tana gidansu suhail agun k’awarta mum. Bayan sunci abinci sun watsa ruwane se kamal yace to nidai zanje inga amaryata dan nayi missing d’inta😍, dukkansu suka kama hanya su 8 se k’auyen su sabreen🚘.
Kwaliya sukayi sosai amma ita sabreen light make-up hafsat tayi mata sunyi kyau sosai suka fito😘. Kamal dad’i yaji sosai kamar yaje ya rungumota😁, shi kuwa gogan naku SABSU murmushi kawai yakeyi a fili kome yakeji a zuciyarsa kuma oho😔😒. K’arasowa sukayi tare da sallama, angwaye suka amsa sallamar sannan su gaggaisa sabreen tana jin kunya😉. D’aya daga cikin angwaye se kallon salma yakeyi🙄, ita kuwa matsowa tayi kusada suhail tace nasan dai kaine suhail koh? Suhail yace eh nine😊, tace hafsat ta damemi da suhail tin d’azu😊 to Allah ya sanya alkhairi, suhail yayi murmushi yace ameen. Salma tacewa kamal to ango nidai zan tafi amma dai zan dawo, kamal yace to mingode bari a saukeki, salma tace a’a wlh ana jirana a bakin titi, suhail yace dukda haka dai zamu kaiki bakin hanyan to kodon addu’an da kika mana😉, hafsat tace to shikenan sannan tacewa su sabreen sena juyo🙋🏻, suma hannun suka d’aga mata sannan suhail tace SADIQ shiga muje, salma ta shiga baya suka tafi suna d’agawa junhannu🙋🏻. Tun kafin su k’arasa suka hango wata farin PRADO tana tsaye a gefen titi. Bayan sun k’arasone se wani kyakkyawan saurayi fari tas dashi wane balarabe ya fito ya k’araso gunsu tareda yimusu sallama ya mik’awa suhail hannunsa mai sanyi kuma mai laushi suka gaisa yana mishi murmushi😊, sannan suka gaisa da sadiq. Salma ta Matso kusa dashi ta gabatar mishi da suhail da kuma SADIQ sannan suka tafi, su suhail ma suka tafi suna yaba saurayin😎.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]