[Advertisements⬇️]

SO BAISAN JINI BA BY UMMU NASMA - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

[3/25, 10:55 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Ana tare fan’s naji daɗin yanda kuke ƙaunar wannan book ɗin, yanzu ma dai ina son ku bani haɗin kai kamar yanda kuka bani a part One ta hanyar SHARHIN KU hakan shi zai bani ƙwarin gwiwwa wajen dagewa da typing*

*Dan Allah ku dinga bibiya kar sai nayi nisa wasu su dinga cewa na turo musu daga farko, hakan yana bani wahala gaskiya.*🙏🏻

*Muje karatu domin ana jone*🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••1️⃣↗️2️⃣

Gabaki ɗayan su komawa sukayi suka zauna, sai Sharifa wacce tabi bayan Indo ganin yanda ta fita a guje cikin kuka, gyaran murya Daddy Yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa Momy ya fara jefowa tambaya.

” A’isha me kike faɗa babu jininki babu waye? Maimaita min naji ko kunne nane yake min ƙarya”

MOMY tana huci kuma cikin fushi ba tare da ta dubi Daddy ba tace.

” Cewa nayi babu JININA babu Indo domin kuwa bazai ɗebo mana irin tsiya ba, sanin kanka ne wannan yarinyar iyayenta ma bata raga musu ba, akan me ɗana zai aureta nima azo a yaɓa min baƙin iri gaskiya bazai yiwu ba.”

Murmushi sosai Daddy Yayi yana duban Momy kafin yace.

” Ni kuma nace akwai *JININ ALHAJI HARUNA DA JININ MALAM MUSA* domin kuwa kusan jini ɗaya nake ɗaukar su, A’isha ki sani cewa muddun cikin waɗannan ƴaƴan nawa, ɗaya cikin su ya daidaita da Indo, muddun kuma suna son juna, to ki sani cewa sai sunyi Aure, idan kuma basuyi ba, to ki ɗauka cewa Allah ne ya ƙaddara babu rabon Aure a tsakanin su, waima na tambayeki, shin wai Indo kam tana bin maza ne koko ta taɓa zaginki ko ɓarauniya ce? Bani amsa.?”

Shuru Momy tayi Zuciyarta na tuƙar baƙin ciki domin ita bata ƙaunar Indo cikin rayuwarta idan tace Indo tana da ɗaya daga cikin wadannan abubuwan da Daddy ya lissafa tayi ƙarya sai dai tasan yarinyar bata jin magana ga yawan faɗa duk da taga yanzu ta daina amma ita bata sonta har cikin ranta duban Daddy tayi tace

” Babu ko ɗaya amma ai kasan……..”

Haɗa ransa Daddy Yayi tare da dakatar da Momy ta hanyar ɗaga mata hanu yace.

” Enough enough A’isha baki da wani abun faɗi, ki sani cewa Ƴata ta ciki na na ɗauki Indo sannan duk sanda na kalleta ina hango fuskar mahaifiyata a tattare da ita duk sanda na mata abu kuma ji nake kamar Inna na yiwa idan tana farin ciki tabbas nasan farin cikin Inna ne ki faɗa min taya zan kasa riƙe farin cikin mahaifiyata?” shuru Daddy Yayi kafin ya ɗago ya kalli Momy da Aunty Hindu cikin kausasshiyar Murya ya cigaba da magana ” wannan dalilin yasa bazan iya bawa Hindu Indo ta koma da ita Egypt ba, ko yanzu nasan na cika umarnin Inna na bawa Hindu riƙon Indo na tsawon wannan lokaci, dan haka Hindu kiyi hkr bazan iya baki Indo ba, ki haɗa mata kayan ta gobe ta dawo gida, idan yarinya kike buƙata a gabanki ki ɗauki *Sharifa* na baki ita duniya da lahira, amma Indo ni zan riƙeta da kaina, ke kuma A’isha idan zaki cire mungun niyyar ki kan wannan YARINYAR ki cire bamu taɓa samun matsala dake ba tsawon zaman Auren mu, yau shekara 30 amma ki sani cewa muddun kika cigaba da wannan abun da kikeyi wa Indo kika cigaba da takura mata to tabbas zamu samu mummunar matsala kuma komai zai iya faruwa tsakanina dake.”

A matukar razane Momy ta ɗago tana duban Daddy, domin kuwa bai taɓa mata wannan furucin ba, cikin Zuciyarta ta furta cewa ( lallai wannan YARINYAR tana shirin tarwatsa min gida tunda harta ɗauko ɗamarar haɗani faɗa da miji na to kuwa kafin ki tarwatsa ni saina fara tarwatsa ki tabbas kin kusa barin cikin garin nan gabaki ɗaya, zan ɓatar dake daga wannan garin ki tafi can inda babu mai jin labarin ki har abada baki san waye A’ISHAH ba, ko nace baku san waye niba, zaki san dani kike) juya kawai tayi ta haura sama ba tare da ta kalli kowa ba, runtse idonsa Mustafa Yayi cikin jin Zafin maganganun Momy ya tashi shima ya fice daga cikin gidan gabaki ɗaya, babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar dashi, Habeeb kuwa kansa na sunkuye shi kaɗai yasan Abunda yake ji a cikin ransa ko magana ya kasa gashi nanne dai yana zaune kamar gunki, Aunty Hindu ko kaɗan bataji Zafin maganganun Daddy ba tafi jin na Momy, tasan tana son Indo har cikin ranta, sai dai soyayyar da take mata bazai sa tayi faɗa na faɗa da ɗan uwanta ba, tasan tabbas Indo zatasha wahala hanun Momy amma ba komai akwai Allah shi zai kareta duban Daddy tayi tace.

” Babu komai Yaya Sharifa ma da ka bani na gode sosai Allah yasa hakan shi yafi Alkairi, nasan kai mutum ne na gari tabbas zaka kula da rayuwar ta, na barka lafiya.” Tana gama faɗin haka ta miƙe tsaye.

Murmushi kawai Daddy Yayi sannan yace

“na gode Hindu Allah ya miki Albarka ki gaida mai gidan naki.”

” Zaiji kawai ta furta sannan ta fice da haushin Momy na munguwar ƙiyayyar da take gwadawa Indo.

Daddy duban Habeeb yayi wanda yayi shuru ya sunkuyar da kansa kasa duk maganganun da ake babu wanda yasa bakinsa ciki sai dai daga kallon yanayin sa zaka fahimci akwai Abunda ke damunsa, Daddy ne yace.

” Yaya dai Habeeb lafiya kuwa naga ka sauya lokaci ɗaya meke damunka.?

Habeeb bai ɗago kansa ba domin kuwa ya tabbata yana haɗa ido da Daddy zai fahimci Halin da yake ciki, kansa sunkuye yace.

” Babu komai Daddy kaina yake ɗan ciwo.”

Murmushin manya Daddy Yayi domin kuwa ya fahimci halin da ƴaƴan nasa duka suke ciki.

” Allah ya sauwaƙa ka tashi kaje kasha magani ka huta koh.”

Tashi Habeeb yayi tare da furta amin ya fice cikin sauri Hasina tashi tayi tabi bayan sa da sauri itama RAUDA kuwa tashi tayi ta haura wajen Momy suka bar Daddy shi kaɗai da su Sharif a wajen.

💢💢💢💢💢💢💢💢

” Ki tsaya Indo ina zakije? Magana fa nake kina jina bazaki tsaya ba? Sharifa ke wannan maganar.

INDO tana huci tace.

” Ki koma kawai Aunty Sharifa babu inda zan dawo.”

” Kifa dawo Indo magana fa ake kika fito aiko ba komai zaki tsaya a ƙarasa wannan meeting ɗin dake.”

Ko inda Sharifa take Indo bata kalla ba ta cigaba da tafiyar ta mai adaidaita ta tsayar yana tsayuwa kuwa ta shige tana ce masa Gidan gomnati zai kaita, ja yayi suka tafi, dakatawa da tahowa Sharifa tayi tana cizon yatsa kafin ta koma, kwantar da kanta Indo Tayi jikin sit din napep ɗin tana tuno Abunda ya faru yanzu ( wai yana sona ko Kunyar faɗa baiji ba, dake ance masa ni kuma shegiya ce saina soshi aiko sai dai sonka ya kasheni wawa mungun banza, kuma muddun baka fita harka ta ba, saina saka cikin bala’in da baka taɓa tunanin zaka shiga ba, bana sonka na tsaneka mungun azzalumi, me zakayi dani *ƘAZAMAR ƘAUYE KUMA ALJANA* ) ta furta cikin Zuciyarta tana cije yatsa a ƙofar gidan su zarah aka sauƙe ta, ta biya mai napep kuɗin sa, bata wani sha wahala wajen shiga gidan ba, kasancewar ta saba da securities d’in.

Suna zaune dukansu a babban falon har momma, gaishe da momma Indo tayi sannan ta shige bedroom ɗin Zarah tashi zarah tayi tabi bayan ta tana tubanin meya sami Indo ta shigo kamar a fusace, kusa da ita Zarah ta zauna tace.

” Malama lafiya na ganki a wani harzuƙe?.

Fashewa da kuka Indo tayi ta dafa kafaɗar Zarah tace.

” Sai yanzu sai yanzu Zarah sai yanzu.” Ta ƙarasa maganar cikin kuka.

” Sai yanzu sai yanzu me? Please kimin magana yanda zan gane me akayi yanzun.?

Dubanta Indo tayi hawaye shar kuncinta tace.

” Sai yanzu da lokaci ya ƙure ya furta min kalmar so, na soshi abaya amma a yanzu na tsanesa sakamakon ƙyamar daya nuna min, bai taɓa sona ba sai ƙyama ta, sai yanzu dana dawo mutum cikakkiya shine yace yana sona, sai yanzu ya Mustafa zaka furta min kalmar so meyasa baka soni tun ina ƴar ƙauye ba meyasa? Ta ƙarasa maganar da ƙarfi.

Tsuka mai ƙarfi Zarah taja tare da cewa.

” Mtsssssss! Aikin banza, to sai meye danya furta miki kalmar so, har zaki ɗaga hankalin ki a banza nasan kina sonshi har yanzu, to bari kiji na sanar dake gaskiya, *Mustafa ƙarya yake ba sonki yake ba tsabar iya yaudara ne, so yake ya kaiki ya baro ki duk da bansan nufinsa a kanki ba, amma dai nasan tabbas mutumin da bai soka tun kana cikin ƙazantar kaba, sai da ka dawo mutum tukunna wannan mutumin ba MASOYIN GASKIYA BANE* A’isha ina mai baki shawara da karki kuskura soyayya ta kaiki ta baroki koda wasa karki yadda da Soyayyar sa domin mayaudari ne Mustafa ba mutumin kirki bane ƙawata kuma kema kinsan haka.”

A wannan lokacin kukan Indo ya fara tsananta cikin kukan ne tace.

” Gaskiya ne Maganar ki ƙawata tabbas bazan taɓa yadda na faɗa tarkon sa ba, duk da nasan ina sonshi, amma bazan taɓa aurensa zan jira me sona da gaskiya yazo zan kuma rufe ido na na kawar da Soyayyar da nake masa, na Auri na ƙwarai ba irin Mustafa na banza ba.”

Dafata Zarah tayi tace.

” Ƙawata ba sai kin jira na ƙwarai ba, domin kina tare dana ƙwarai kuma mai sonki da gaskiya, wanda ina da tabbacin cewa zaki samu farin ciki a gidan sa, wanda zaisa ki manta da wani Mustafa cikin wannan duniyar, ki basa dama na tabbata shi kuma zai baki farin ciki.”

Kallon Zarah Indo take cikin alamar tambaya da kuma mamakin waye kuma mai sonta da gaskiya, duban ta Zarah tayi cikin murmurshi tace.

” Kin shiga cikin tunanin cewa waye mai sonki da gaskiya ko? To ba wani bane sai *YAYA HABEEB* yana sonki da gaskiya mutumin kirki ne, ya soki tun kina cikin ƙauye ya ƙaunace ki tun kina cikin ƙazantar ki bai taɓa nuna miki ƙyama ba, haka kuma yana daga cikin waɗanda suka kawo miki haske cikin rayuwarki, kuma na tabbata yana sonki, mai zai hana bazaki bawa wannan Adalin mutumin Soyayyar kiba, Indo ta wannan hanyar ne kawai zaki saka masa da alkairin daya miki cikin rayuwarsa, duk da bazaki iya biyansa ba, amma idan kin soshi zaiyi farin ciki kuma kema zakiyi farin ciki a gaba.”

Zaro ido waje Indo tayi tace.

” What kin san me kike cewa kuwa Zarah yaya Habeeb fa kike cewa yana sona, kinyi kuskuren fahimta ƙawata babu Soyayya tsakanina da ya Habeeb illah ƙauna Irin ta ƴan uwan da suka fito ciki ɗaya, TAUSAYINA kawai yake ba soyayya ba.”

” Hmmm A’isha kenan kece kike ɗaukar hakan a matsayin ƴan uwantaka shi ba haka ya ɗauka ba, shi matsayin masoyiya yake ɗaukar ki, kince tausayin ki yake, to ki sani duk inda tausayi da shaƙuwa yayi yawa to tabbas akwai Soyayya koki yadda ko karki yadda HABEEB yana sonki tamkar yanda yake son ransa, ki koma kiyi tunani kan magana ta, ki kuma fara lura da *TAKUN SAƘAR SA* na tabbata zaki gaskata magana ta.”

” Ki daina faɗin wannan maganar Zarah kin manta waye ya Habeeb yake Aure, *AUNTY HASINA* ce fa wacce take ɗaukata tamkar ƴar uwarta, da ita kike nufin nayi kishi naso mijinta, ina hakan bazai taɓa kasancewa ba, ya Habeeb da Aunty Hasina kawai ya dace su biyun su za suyi rayuwar su bana mata fatan kishiya cikin rayuwarta, kinga Zarah kunne na bazai iya ɗaukar Maganar nan ba dan Allah mubarta haka.”

” Okey shikenan tunda haka kika ce, na barta amma zakice na faɗa miki.”

Jingina kanta tayi ba tare data ce komai ba tana tunanin Maganar Zarah.

Allah ne kawai ya kawo Habeeb cikin gidan lafiya tun kafin ya gama gyara parking ya fice daga cikin motar ko key ɗin bai cire ba, yana ƙarewa motar Mustafa kallo da alamu dai yana cikin gidan, Hasina da take bin Habeeb da kallo tun fitowar su ne tasa hanu ta zare key ɗin motar, sannan ta fito tabi bayan sa, kafin ta isa ma tuni ya shige bedroom ɗinsa ya danna key, jin ginuwa Hasina tayi jikin ƙofar tana riƙe ƙirjinta da taji ya fara mata nauyi, sosai take jin kishin Indo cikin ranta domin kuwa taga abun Habeeb ya fara yawa TABBAS yau zarginta ya kasance gaskiya, ƙarar zubar da abu cikin bedroom ɗin da tayi ne yasa nutsuwa tana sauraron maganganun Habeeb wanda baima san tana tsaye a wajen ba.

” Meyasa meyasa Mustafa meyasa? Zakayi gaggawan furta mata why! Ba LAIFIN ka bane laifin Zuciyata ne data kamu da Soyayyar ta, baki min adalci ba zuciyata, kinsa ina mata Soyayyar da bazan iya rayuwa ba muddun babu ita cikin rayuwata, ina sonta fiye da yanda nake son Raina na shiga Uku ni Habeeb ya zanyi da dakon Soyayyar ta, anya kuwa Soyayyar ta bazata kasheni ba.”

Wani irin kuka Hasina tasa tare da silalewa ƙasa ta zauna tana toshe bakinta karya jiyo sautin kukanta.

 

Karku manta da COMMENT idan kun manta nima zan manta da typing duk da nasan bakwa wasa wajen COMMENT.😄

*Vote*
*share*
*and*
*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻

*(Ummu Nasmah ce)*
[3/27, 10:11 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••3️⃣ ↗️ 4️⃣

” Ina sonki! Indo ina sonki ya zanyi da dakon Soyayyar ki, meyasa kika kasa fahimtar ina sonki, meyasa!?”

Ya ƙarasa maganar da ƙarfi tare da sakin kuka ya dafe saitin zuciyarsa, yana cigaba da sambatu cikin kuka kamar ƙaramin Yaro, HASINA dake zaune ta rufe bakinta tana rusar kuka marar sauti ta tashi da gudu ta faɗa bedroom ɗin ta domin kunnen ta bazai iya cigaba da sauraron Habeeb ba idan kuma ta saurara to tabbas Zuciyarta zata iya tarwatsewa, saman bed ta faɗa ta saki marayan kuka tana cewa.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un! Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un! Ya Allah ka sassauta min nauyin da nake ji cikin ƙirji na, tabbas ina kishinka miji na sai dai Soyayyar da nake maka bazai rufe min Idona ba har na kasa tayaka yaƙin neman Abunda kake muradi tabbas kafi sonta da buƙatar ta fiye dani cikin rayuwarka, duk da nasan kana sona amma Soyayyar da kake mata tafi wacce kake min yau na shaida hakan sai dai kash wacce kake yi domin ita bata san kanayi ba, ya Allah ka sassauta min wannan kishin cikin raina ya Allah ka bani ƙarfin gwiwwar da zan iya taya miji na yaƙin neman Auren ƴar uwata Indo, domin ganin cikar burinsa da farin cikin sa, tabbas Indo mutumiyar kirki ce, sai dai sam zuciyata bata son haɗa kishi da wacce take kallo a matsayin ƴar uwar ta ta jin, *TABBAS WANNAN ITACE ƘADDARA TA* mijina zaka Aure ta da yardar Allah tabbas zaka aureta na tabbata Mustafa bazaiyi Nasara akanka ba, domin kaine wanda ya dace ka Auri Indo ka mata Hallaci kuma na tabbata Indo bazata maka butulci ba, tabbas zata rama maka Alkairi da Alkairi za kuma kayi nasara da yardar Allah.”

Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka mai ban tausayi, Hasina ta daɗe tana kuka kafin ta tashi ta shiga tollet tayi wanka ta fito bayan tayi sallar la’asar ne ta shiga kitchen ta ɗaura abincin dare sannan ta nufi bedroom ɗin Habeeb, shi kuwa Habeeb yana kwance cikin ɗaki ko sallar la’asar ma yau a ɗaki yayita shi kaɗai, wani irin ciwo kansa yake masa, magani ya ɗauko yasha sannan ya koma ya kwanta hawaye na zuba cikin idanunsa sallamar ta da yaji shine ya sashi saurin goge hawayen sa tare da amsa mata da raunanniyar Murya, tahowa Hasina tayi tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta zauna gefen sa tare da cewa.

” Lafiya kuwa sweetie na na jika shuru tun ɗazu baka fito kaje masallaci ba?”

Cikin ɓoye damuwar sa shine saboda kar Hasina ta fahimci Halin da yake ciki yace mata.

” Kaine yake ciwo shiyasa kawai nayi sallah a ɗaki nasha magani, kinyi kyau fa sosai SweetHeart ɗina kin ganki kuwa kamar na sace ki na gudu” ya ƙarasa maganar cikin zolaya duk dan kar Hasina ta fahimci yana cikin damuwa.

Murmushi Hasina tayi cikin jinjinawa ƙarfin hali irin na mijinta da wasa baya basa wahala a ko wani hali yake ciki tace.

” Ayya sweetie sorry gashi har idon ka yayi ja Allah ya baka lafiya, ai ba sai ka sace niba domin kuwa ni taka ce ta har abada kaga kuwa ai babu sata tsakanin mu”

Murmushin jin daɗi Habeeb yayi tare da tashi ya ɗaura kansa a cinyar ta ya kamo tafin hanunta ya haɗa da nasa ya fara magana kamar haka.

” Kimin alƙawari HASINA zaki zauna dani a ko wani irin hali na tsinci kaina a ciki bazaki taɓa rabuwa dani ba komai tsanani komai wahala, tabbas ke ɗin matar rufin asiri ce, ina ƙaunar ki Hasina dan Allah karki rabu dani komai tsanani komai wahala kimin wannan alƙawarin.”

Ya ƙarasa maganar yana danƙe hanunta cikin nasa, Hasina idanunta cikowa sukayi da hawaye domin itama tana son mijinta sosai fiye da yadda yake sonta kuma a shirye take data zauna dashi a ko wani irin hali, sunkuyowa Hasina tayi da kanta ta ɗaura a nasa kayin tace.

” *Babu ƙaddarar da ta isa ta shiga tsakani na dakai miji na komai muninta kuwa, ZAN RAYU DAKAI HAR ƘARSHEN NUMFASHI NA, DA KUMA SOYAYYAR KA ZAN KOMA GA MAHALICCINA karka damu mijina na maka alƙawarin cewa zan zauna dakai a ko wani irin hali, daɗi ko wahala ina tare dakai*.”

Murmushin jin daɗi Habeeb yayi cikin ransa yake furta (tabbas nayi dacen mata ta gari mai haƙuri da juriya) dubanta yayi yana murmurshi yace.

” Ina sonki HASINA Allah ya barmin ke har ƙarshen rayuwata bazan taɓa gajiya da furta miki wannan kalmar ba *I LOVE YOU*.”

MURMUSHI Hasina tayi sun juma suna tattaunawa Hasina koda wasa bata nunawa Habeeb alamar taji Abunda yayi ba, haka kuma bata sauya masa ba, tuno da girkin data ɗaura ne ya sata ɗaga kan Habeeb daga cinyar ta ta ɗaura a filo ta fita da sauri, murmurshi Habeeb yayi tare da kanƙame fulo yana tuno Indo cikin Zuciyarsa.

Mustafa kuwa ko a jikin sa harkokin sa yake domin kuwa ji yake cikin zuciyarsa ya samu Indo ya gama tunda daman can da Soyayyar sa ta taso, yasan dole zata soshi, dan haka shi baida wata damuwa, RAUDA sanda tayi sallar la’asar sannan ta shigo cikin gidan yana zaune a falo yana danna laptop ɗinsa yaji sallamar ta, amsa sallamar yayi kansa yana ga laptop ɗin ba tare daya ɗago ya kalleta ba, jikinta a matukar sanyaye ta ƙaraso gefen sa ta zauna, cikin sanyin murya tare da ƙunar Zuciya ta furta masa cewa.

” Ya Mustafa ashe daman Indo kake so, ka dinga wulaƙanta rayuwata, ya Mustafa meye laifi na danna soka? Meye laifin mutumin daya soka tsakani da Allah ya yarda ya zauna da kai cikin tsananin wahala domin ban taɓa jin daɗi koda na sakan ɗaya bane a cikin gidan nan, *SABODA ITA DAMAN KAKE WULAƘANTA NI* ni bazan hanaka Auren Indo ba, haka kuma bazan ɗaga hankali na ba, tunda nasan baka sona kaga babu wani amfani nayi kishi a kanka kuma bana tunanin zaka soni ko nan gaba bazanyi yaji dan zaka ƙara Aure ba, bare har na tona asirin aurena a gidan muba, sai dai ina son ka sani cewa zalintata da kake akwai Allah yana ji kuma yana gani shine kuma mai sakayya, ina maka fatan Alkairi game da neman aurenka Allah ya baka Sa’a.”

Cikin kuka ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tabar wajen domin a yanzu taji ta fara tsanar Mustafa cikin rayuwarta muryar sa taji cikin tsawa yana cewa.

” To munafuka me kike nufi Allah ya isa kika jamin ko meye, munafuka da kike cewa akwai Allah yana ji yana gani Kuma shine mai sakayya, to daman ai shine mai sakayya, kuma nine zai sakawa da kika cuceni aka aura min ke dole ba tare da ina sonki ba, nine ya kamata na ja miki Allah ya isa domin aurenki cuta ce a gare ni, kuma bari kiji daman ni da Sa’a ta nake yawo da ita nazo duniya so bana buƙatar Addu’ar ki tunda ba uwata bace ke, idan kinga dama ki tayar da hankalin naki wannan damuwar kice ba nawa ba, ni wlh da zaki tafi gidan naku ma da kin taimake ni, dan zanfi sakewa nayi walwala idan babu ke cikin gidan nan *NA MAIMAITA MIKI INDO ITACE NAKE SO KUMA ITACE ZUCIYATA ITACE RAYUWATA GABA ƊAYA* Tashi ki ɓace min da gani mtsss.” Ya karasa maganar tare da tsaki.

Shuru RAUDA tayi hawaye na gudu a kuncinta ta shige cikin ɗaki, zama tayi gefen gado tayi tagumi sai yanzu taji ta fara danasanin Auren Mustafa domin ƙiyayyar da yake mata ya fara yawa, wayarta ta ɗaga ta dannawa Zaliha kira ƴar baffan ta wanda suke ciki ɗaya, tana ɗagawa RAUDA tace ” kizo gida na ki sameni ina cikin matsala Zaliha” tana gama faɗin haka ta katse kiran ta kwanta, can taji shigar text message cikin wayarta dubawa tayi taga Zaliha ce ta turo mata cewa.

” Bazan samu zuwa yau ba, amma gobe zanzo da yamma.”

Allah ya kaimu RAUDA ta furta tare da kwanciya cikin tashin hankalin ƙalubalen da yake gabanta hawaye na cigaba da zuba cikin idanunta.

💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

Ta juma sosai a gidan su zarah kafin drivern gidan ya dawo da ita gidan Aunty Hindu da Sallama ta shigo cikin falon muryar sa taji ya amsa mata da cewa.

” Ameeen Wa’alaikimussalam farin ciki na barka da dawowa.”

Turus ta tsaya tana duban sa jin ya ambace ta da wani sabon suna wai *Farin ciki na* taɓe bakin ta tayi tuno da zancen Aunty Hindu na ɗazu da take cewa Barrister yana sonta, duban sa tayi ba tare da ta sanja masa fuska ba tace.

” Barrister Umar kaine tafe da la’asar haka, sannu da zuwa” ta furta masa tare da zama tana fuskantar sa.

Shima cikin happy yake kallon ta kamar zai haɗiyeta yace.

” Wlh kuwa nine tafe na jiraki harna fara ƙosawa ina kikaje haka tun ɗazu nake zaman jiran ki?”

Murmushi Indo Tayi ba tare da ta nuna masa wani sauyawa cikin fuskar ta ba tace.

” Naje gidan su Bestie nane kace kasha jirana, to sorry.”

Murmushi Barrister Umar yayi cikin zolaya yace.

” Sorry for what Hajiya?”

Murmushi itama tayi kafin tace.

” Sorry for waiting me, naga kamar ka gaji da yawa na jirana dama gashi rago ne kai ɗin Allah dai yasa Ummi ta baka ruwan sanyi kasha nasanka da son ruwan sanyi.”

Cikin dariya ta ƙarasa maganar tana duban sa.

Murmushi Barrister Umar yayi yace.

” Ke kuwa ina kika taɓa ganin inda uwa ta hana ɗanta ruwan sanyi ai ina zama ummi na tana kawo min ruwa, kinga aiki zan tafi nasan yanzu haka Oga Mustafa yana can yana jira na, daman na biyo na ganki ne kawai na wuce.”

Jin sunan Mustafa da Indo tayi Habeeb ya ambata sai da gabanta ya faɗi, murmurshi kawai tayi tace.

” Na gode Barrister Allah ya bada Sa’a a dawo lafiya.”

” Ameen bye.”

Murmushi INDO tayi itama ta tashi tayi ɗaki wajen Aunty Hindu.

” Ina kika shiga A’isha? nayi zaton gida kika dawo nazo na tarar bakya nan.”

” Ummi gidan su Zarah naje.”

Girgiza kanta Aunty Hindu tayi ba tare da tayiwa Indo maganar Mustafa ba da Barrister Umar tace

” Daddyn ku yace bazai yiwu ki bimu Egypt saboda baya son kiyi nesa dasu yace ma gobe ki koma gida, dan haka ki haɗa kayan ki duka gobe da yamma zaki koma can.”

Shuru Indo Tayi idonta ya ciko da hawaye tace.

” Yanzu Ummi tafiya zakuyi ku barni, Ummi bana son zaman gidan Momy PLS Ummi ki tafi dani dan Allah nafi son na zauna tare dake.”

” Kiyi hkr Indo bai kamata muyi musu da Daddyn kuba, ki koma gabansa ki zauna ki ɗauko hakuri da juriya ki sa a cikin rayuwarki na tabbata wata rana zaki ci ribar haƙuri ki musu biyayya tamkar yanda za kiyiwa iyayenki hakan shi zaisa ki shiga ran kowa.”

Sosai Indo taci kukan rabata da Aunty Hindu da Daddy Yayi amma babu yanda ta iya haka taci kukanta tayi shiru ta ɗauƙi dan gana.

Da sallama ya shiga office ɗin nasa, yana jin sallamar tasa yayi banza dashi kamar bai jiba, sanda yayi sau wajen uku kafin ya amsa da ƙyar, ƙarasowa Barrister Umar yayi ya zauna yana miƙawa Mustafa hanu, amsa yayi sukayi musabaha sannan Barrister Umar yace.

” Sorry Oga nayi let na biya wani waje ne amin afuwa, na haɗa duka infomations ɗin da kake buƙata sai dai …….”

Dakatar dashi Mustafa Yayi ta hanyar ɗaga masa hanu yace.

” Ba wannan bane a gaba na, so nake ka fara sanar dani *MENENE YAKE TSAKANIN KA DA SHATUU IDAN BAKA GANE BA INA NUFIN INDO*.?”

Shuru Barrister Umar yayi yana kallon sa Kafin ya buɗe bakin sa yace……………

 

 

*Muje zuwa yanzu aka fara wasan*🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[3/31, 10:00 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••5️⃣ ↗️ 6️⃣

” Meyasa kamin wannan tambayar Barrister?

Barrister Umar ya jefowa Mustafa Wannan tambayar cikin mamaki.

Murmushin gefen baki Mustafa Yayi cikin isgili ya cewa Barrister Umar.

” Wai kai a haka lauyer kake ɗaukar kanka ko? Hmmm su malam lauyer manya, a matsayinka na lauyer akwai dokar da ta ce ka maida tambaya cikin tambaya kafin amsar tambayar farko, na tambayeka baka bani amsa ba shine kake kuma jefo min wata tambaya robbish lauyer kenan kake ƙoƙarin maida kanka, da a gaban Shari’a kake tabbas da ka faɗi, ya kamata kake aiki da doka a matsayinka na Barrister, answer Question meye tsakaninka da *INDO*?”

SHURU Barrister Umar yayi na wasu lokuta dan ya ɗan ji zafin maganganun Mustafa kafin ya dubesa cikin ɓacin rai yace.

” Oga banda amsar tambayar ka ta biyu, a yanzu, sai dai ga amsar ka ta farko, ina zaton cewa zuciyata ta kamo da matsanancin ƙaunar ta, wacce take tafiya tare da ko wanni bugun numfashina Rayuwata ce ita ɗin.?”

Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin maganganun Barrister Umar cikin ƙwaƙwalwar sa da kunnen sa tamkar ana masa feshin wuta, buɗe idanunsa yayi waɗanda suka kaɗa suka koma jajaye lokaci ɗaya, ya fara maidawa Barrister Umar Magana son ransa.

” Ya kamata zuciyarka tayi gaggawar cire INDO cikin ta, domin kuwa Indo bazata taɓa sonka ba, kayiwa Zuciyar ka faɗa tun kafin lokaci ya ƙure maka ta kasa amfanan ka, ka tausashi numfashinka tun kafin ya fara neman ɗauke maka kana jawosa yana ƙoƙarin barin jikin ka, domin kuwa Indo ba matar Auren ka bane ina sanar dakai wannan shawarar ce a matsayina na abokinka domin ina tausayawa zuciyarka kamuwa da mungun ciwon Soyayyar wacce bazata sameta ba domin ta maka zarra.”

Wani irin kallo Barrister Umar yake bin Mustafa dashi mai cike da alamomin tambaya, cikin tashin hankali Barrister Umar yake tambayar Mustafa.

” Me kake nufi da wannan maganar taka, shin Indo tana da wanda take so tuntuni ko me kake nufi.?”

Murmushi Mustafa Yayi yana duban Barrister Umar Kafin yace.

” Yes ka amsawa kanka tambayar ka, tana da wanda take tsantsar so wanda bazata taɓa iya rayuwa babu shiba, ba zata iya ciresa cikin Zuciyarta ba, wannan mutumin shine rayuwar ta, shine duniyar ta, shine farin cikin ta, dan haka ka cire kanka cikin niyyar shiga tsakanin masoya dan zakayi danasani ne a gaba marar Amfani amma shawara ce idan ka ɗauka.”

Murmushi sosai Barrister Umar yayi kafin yace.

” Na fahimce ka, na kuma fahimci shi wanda kake kira tana so, sai dai kuma banga Soyayyar wani cikin Zuciyarta ba, tunda gashi na fara hango soyayyata cikin idanunta, karka damu da wahalar da zan shan indai akan Indo ne na shiryawa hakan zan iya shiga ko wani irin hali ne saboda farin cikin zuciyata, zan kuma iya karawa dashi wanda kake kira duniyar ta, *ITA MACE AI ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO SHIKE ƊAUKA* dan haka ina yiwa mai rabo fatan Alkairi, mu zuba muga wanda zai ɗauka nasan ina tafe da nasara ta a ko yaushe.”

Barrister Umar yana gama faɗin haka ya sarawa Mustafa tare da juyawa ya fice daga cikin office ɗin ba tare daya ƙara sauraron Mustafa ba.

Murmushi mustafa Yayi yana yiwa Barrister Umar kallon tausayi dan yana da tabbacin cewa muddun yana raye Indo bazata taɓa son wani Namiji ba, tashi yayi ya kwashi Key’s ɗinsa ganin an kusa fara kiran sallar magaruba, bai shiga cikin gidan sa ba, sai da yayi sallar magaruba sannan ya fara shiga part ɗin Momy domin kai mata hira.

Habeeb kuwa suna zaune da HASINA yaji ringine ɗin wayar sa, dubawa yayi yaga kiran Aunty Hindu ne, kallon HASINA yayi yace.

” Aunty ce take kira bari muji Allah dai yasa lafiya”

Da “ameeen” Hasina ta amsa shi kuma Habeeb ya ɗaga wayar basu wani juma ba ya katse kiran yana duban Hasina yace.

” Kira na Aunty take, tace nazo yanzu bari naje na dawo.”

Duban Habeeb tayi tace.

” Allah yasa dai lfy Ummi take neman ka yanzu kaje Allah ya dawo da kai lafiya.”

” Ameen” Habeeb yace tare da ɗaukar key ɗinsa ya fice, tunda Habeeb ya fita ƙirjin Hasina yake bugawa domin kuwa tasan dole zai haɗu da Indo a can, dafe ƙirjin ta tayi tana lumshe idanunta tare da jin wani kishin Indo yana taso mata.

Cikin mintuna kaɗan Habeeb ya shiga cikin gidan Aunty Hindu, a falo ya tarar da ita tasa Indo a gaba ga akwati a gaban su Indo sai famar sharɓar kuka take, cikin sauri Habeeb ya ƙaraso wajen nasu yana cewa.

” Subhanallah! AUNTY meya faru take faman kuka haka?”

Duban sa Aunty Hindu tayi tace.

” Ko kaima ka tambaya, kiran dana maka kenan, gata nan dan kawai nace ta haɗa kayan ta, Anjuma driver ya maidata gidan ku shine take rusar wannan kukan ita dole bazata koma ba, kuma kasan Daddyn ku cewa yayi gobe tayi sammako ta dawo, shine ta koma kawai yanzu yafi tayi sammakon, tace ita dole saita jira Abban Hasina ya dawo daga Abuja kuma shi dawowarsa babu lokaci, dan wata ƙilma nice zanje canna samesa mu wuce Egypt.”

Murmushi Habeeb yayi tare da zama yana duban Indo yace.

” Barni da ita Aunty jekiyi Aikin ki kawai.”

Tashi Aunty Hindu tayi ta wuce bedroom ɗin ta tana yiwa Indo sababi.

Haɗa ransa Habeeb yayi yana duban Indo da itama ta maida dubanta garesa yace.

” Da a ina kike kafin Aunty Hindu tazo kasarnan okey na gane wato bakya son gidan mu saboda ba’a biya miki bukatunki ko? Ba’a miki Abunda kike so babu mai kula da lamarin ki ko okey ba damuwa wata ƙila mu bamu da Abunda zamu baki shiyasa zaki gujemu yanzu.”

Zaro ido Indo tayi tana kallon Habeeb cikin yanayin tashin hankali tace.

” Me kake faɗa haka ya Habeeb babu ko daɗin ji, ya Habeeb ni kuwa ina inke da gatan daya fi wanda kamin kaida Daddy, koni butulu ce bazan ce wani gida yafi na Daddy ba, kawai na shaƙu da Ummi ne shiyasa nake ji kamar bazan iya rabuwa da ita ba, amma dan Allah ka daina faɗin wannan maganar.”

” Bakya san rabuwa da Aunty Hindu amma kina son ɓacin ran daddy ko?”

Muryar Indo kamar zata sake fashewa da kuka tace.

” Ya Habeeb ya za’ayi naso ɓacin ran Daddy haba ya Habeeb ka daina faɗa min wannan maganar haka, na yadda ka tashi kawai mu tafi ka daina faɗamin.”

Murmushi Habeeb yayi cikin ransa ganin harya samo kanta cikin sauƙi kafin yace.

” Jeki kuyi sallama da Aunty Hindu sai kizo mu tafi.”

Tafiya Indo tayi bedroom ɗin Aunty Hindu ta sameta Zaune bakin bed ɗinta tana ninke kayan ta zama tayi gefen ta tace.

” Ummi zamu tafi da ya Habeeb zai sauƙe ni a gida.”

Kallon tausayi Aunty Hindu take yiwa Indo har Zuciyarta taso a bata Indo sai dai babu yanda ta iya fadan daya fi ƙarfin ta dole ta maida shi wasa, ko zuwa ƙauyen DASINA ma ta fasa daman saboda Indo zata tunda kuma bazata ba ta fasa duban Indo tayi tace.

” Kiyi hkr Indo Babu yanda na iya ne naso na riƙeki har na aurar dake da hanuna, sai dai Allah bai ƙaddara hakan ba, Indo kullum nasiha ta ɗaya ce gareki shine ki kasance mutum mai haƙuri a duk inda kika tsinci kanki, domin shi haƙuri yana kai mutum zuwa ga matakin babban nasara, tabbas kuma haƙuri haske ne, karki damu da duk abunda mahaifiyar su Mustafa zata miki, zai zama tarihi wata rana ki mata biyayya karki gaza dan tana hantarar ki kice bazaki bita ba, kiyi hkr ki mata duk wata biyayya da ƴa zata yiwa mahaifiyar ta, nima kuma kafin na tafi zanzo” kuɗi Aunty Hindu ta ɗauko ta danƙawa Indo a hanunta tace.

” Gashi 10k ne ki riƙesa ko data zaki dinga saya dashi ki gaishe da su Daddyn naku.”

” Karɓa Indo tayi cikin sanyin jiki ta yiwa Aunty Hindu godiya har bakin mota Aunty Hindu ta rako Indo ta shiga mota shima Habeeb sallama yayiwa Aunty Hindu sannan yaja motar suka bar gidan Aunty Hindu tana ɗaga mata hanu, sunyi nisa da tafiya babu wanda ya cewa wani komai Habeeb lura da yayi da ran Indo a ɓace yake yasashi samun gefen titi yayi parking ya dubi Indo yace.

” *HABIBTY NA* cire tagumin haka ko na juya na maida ke wajen Aunty Hindu.”

Zaro Ido Indo tayi tana kallon Habeeb tace.

” Ya Habeeb *HABIBTY* kuma meyasa ka kiran da wannan sunan yau kuma?”

Murmushi Habeeb yayi yana duban ta yace.

” Bakya sone na kiraki da hakan ko kuma ban dace na kiraki da sunan ba ne?”

” A’a bawai baka dace bane gani nayi saurayi ne yake kiran *BUDURWAR SA* da wannan sunan Kuma baka taɓa kirana da sunan ba shiyasa na tambaya.”

Murmushi sosai Habeeb yayi tare da cewa.

” Okey to ki ɗauke ni a matsayin *saurayin* idan har kina ganin na dace da hakan, ni kuwa ina maraba da hakan *HABIBTY NA*”

Dam! Gaban Indo ya buga maganganun Zarah ne suka fara yawo cikin ƙwaƙwalwar ta *ƙawata yaya Habeeb yana sonki da gaskiya mutumin kirki ne ya soki tun kina cikin ƙazantar ki bai taɓa nuna miki ƙyama ba*.” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un take furtawa cikin ranta ashe daman maganar Zarah gaskiya ne ya Habeeb sona yake kai anya kuwa ina ga dai yanzun ma zolayata yake, tabata da Habeeb yayi yana dariya tare da cewa.

” Tunanin me kike haka *HABIBTY NA* Kodai na saki cikin searching ne?”

Murmushin dole Indo tayi tare da haɗiye yawu dakyar tace.

” A’a babu wani tunanin da nake yaya Habeeb ai nasan hakinka da zolaya” kawar da maganar tayi ta hanyar cewa.

” Ya Habeeb yaushe zamuje Dasina, ina son zuwa naga Mama.”

Murmushi Habeeb yayi tare da tayar da motar ya harba titin yana ce mata.

” Wannan ba maganar yanzu bane ki bari sai mun sami zama, keda zaki fara zuwa makaranta ina ke ina zuwa ƙauye, amma zamuyi maganar daga baya.”

Indo bata sake magana ba haka shima Habeeb har suka isa cikin gidan parking Yayi kusan tare suka fito suka nufi cikin falon Momy suna zaune gabaki ɗaya suna hira Momy Mustafa Sharifa Ishaq Sharif, da Sallama suka shiga Sharifa ce ta amsa, Mustafa kuwa wani Shu’umin kallo yake bin Indo dashi yana lumshe idanunsa Momy kuwa wani ƙazamin kallo take bin Indo dashi tare da tsantsar tsana cikin idanunta, Ishaq da Sharif kuwa da gudu suka tashi suka nufi Indo suna mata Oyoyo, akwatin nata Sharif ya karɓa yana ƙoƙarin kai mata cikin ɗakin su suka ji muryar Momy ta daka masa tsawa tana cewa.

” Dan ubanka bata akwatin ta, jakinta ne kai shegen shishshigin tsiya nifa bana son kuna shigewa jikin wannan abar ƙyamar zan ci muku mutunci wlh idan baku fita harkarta ba daga ku har yayun naku.”

Ajiye akwatin Sharif yayi ya koma gefe yana fushi Habeeb kasa magana yayi ya tsaya yana duban Momy domin kuwa yasan koya mata magana bazata fahimce sa ba, sai dai ma ta zagesa, Mustafa kuwa Sarkin rashin haƙuri tuni ya fara yiwa Momy Magana.

” Haba haba! Momy wai meye Indo ta ci miki haka kika tsaneta, ya kamata ki sassauta wannan ƙiyayyar da kike mata karki manta da cewa itama mutum ce kamar kowa kuma tana da Iyaye suna sonta kuma kamar yadda kema kike son naki ƴaƴan Abunda bazaki ji daɗi ba idan an miki bai kamata kiyiwa ɗan wani ba, itama fa Momy tana gata da Asali kamar yadda ƴaƴan naki suke dashi, ko mummunan laifi ta miki ya kamata ace kin yafe mata ki kuma mata fatan shiriya barema babu abunda ta miki pls Momy ki sassauta ƙiyayyarki gareta karki manta da cewa zata zama surukar ki nan gaba kaɗan.”

Shuru Momy tayi tana sauraron Mustafa bata katsesa ba harya gama sannan ta fara magana.

” To ubana ka gama min faɗanne, to banji ba dan ubanka, na RANTSE DA ALLAH Mustafa zan iya rabuwa da kai na yafewa duniya kai muddun baka janye Maganar Soyayya da wannan abar ba, bare harta kaiku ga Aure idan kana neman zaman lafiya dani kana kuma neman albarkata to ka rabu da wannan YARINYAR domin na tsaneta bana ƙaunar ta cikin Rayuwata.”

Gabaki ɗayan su cikin tashin hankali suke kallon Momy mussaman Mustafa da yake jin bazai iya rayuwa babu Indo ba Habeeb kuwa suman tsaye yayi yana jin maganar mahaifiyar tasu kamar sauƙar aradu, juya kawai Habeeb yayi ya fice daga falon ganin hawaye na neman zubo masa, Indo kuwa tuni hawaye ya wanke mata tata fuskar kuka take harda sheshsheƙa Abunda take gudu kenan shiyasa taƙi dawowa Aunty Hindu ta tilasta mata dole sai ta dawo yanzu ga irinta nan, jan akwatin ta kawai tayi ta shige bedroom ɗinsu, Mustafa kuwa ranshi idan yayi dubu to ya ɓaci idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ya dubi Momy ya fara faɗin mata maganganu.

“Da farko kin min Auren dole kinsani na amshi matar da ban taɓa sonta ba a matsayin matar aurena na kuma miki biyayya na amshe ta a matsayin ki na mahaifiyata, duk da raina baya son ta, sai gashi yanzu nayi tozali da matar da nake so na Aura a matsayin zaɓina a karo na biyu kince baki yarda da hakan ba, anya kuwa Momy wannan karon zan iya miki biyayya anya Momy ina sonta fiye da yanda nake son komai na rayuwata ciki harda Numfashina, na daɗe da Soyayyar ta cikin Raina, meyasa Momy zaki tarwatsa Soyayyar Shekara da shekaru karkiyi wannan ɗaukar alhakin Momy domin……………”

Sauƙar marin da yaji ne yashi kasa ƙarasa maganar da yayi niyya yana duban Momy da jajen idanunsa wacce ta sauƙe masa mari magana Momy ta fara cikin tsawa wanda yasa Sharifa fashewa da kuka tana duban Momy.

” Na isa da kai! Shiyasa nayi maka katanga tsakaninka da ita, kuma dole kamin biyayya idan kuma kace bazaka min biyayya ba to kajeka babu ni babu kai karka sake takowa inda nake har abada ɓace min da gani.”

Bai cewa Momy komai ba ya taka ya haura sama bedroom ɗin su Indo ya shiga ya sameta tana zaune ƙasan tayels sai riskar kuka take harda majina sunkuyawa yayi ya kamo kafaɗarta ya ɗaga ta tsaye, sannan ya kama hanunta yana ƙoƙarin janta su fita, ƙwace hanunta Indo take ƙoƙarin yi amma ina Mustafa ba riƙon wasa ya mata ba, janta kawai yake tana cijewa har suka isa gaban Momy hanunsa riƙe dana Indo ya tsaya a gaban Momy yana kallon sa, Indo kuwa tsabar tsoron Momy rufe idanunta tayi tana jiran taji sauƙar duka………

 

 

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/2, 11:01 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••7️⃣ ↗️ 8️⃣

Magana ya fara cikin tsantsar ɓacin rai.

” Gani ga Indo a gaban ki Momy zan ƙara maimaita miki a karo na biyu *INA SONTA INA SONTA INA SONTA!* Ina kuma fatan mu kasance ƙarƙashin inuwar Aure ɗaya, karki rusa mana farin cikin mu Momy na roƙeki da Allah kiyi hkr ki barmu muna tsantsar son junan mu Soyayyar mu daɗaɗɗiya ce dan Allah Momy ki ƙyale mu da farin cikin mu.”

Cikin sauri Indo ta buɗe idonta jin maganar Mustafa kamar sauƙar aradu cikin kunnuwan ta, da ƙarfi ta fisge hanunta daga nashi tana mishi kallon marar Hankali, cikin fusata da ɓacin rai Indo ta fara maidawa Mustafa martani.

” Me kake cewa? Muna son junan mu, kai da waye? badai da Indo ba, domin kuwa ni bana sonka na tsaneka bazan kuma taɓa sonka ba har abada, daga yau karka ƙara kirana da sunan masoyiyarka domin sunan san bai dace da mungu irinka ba duk duniyar nan babu mutumin dana tsana sama dakai a rayuwata” tsagaitawa Indo tayi da maganar tana duban Momy Ido cikin ido kafin ta cigaba da cewa, ” ba sai kin yiwa ɗanki baki ba Momy babu alaƙar Aure da zata shiga tsakani na dashi, Momy koda ace kina son na Aure ɗanki bazan yarda na Aure shiba domin kuwa na tsanesa ba tsanar wasa ba, kiyi hkr ki gafarce ni idan har maganata ta ɓata miki rai, na sanar dake haka ne domin ki daina zagin ɗanki, nasan kuma shima kanshi ya Mustafa ƙarya yake ba sona yake ba ”

Mustafa tsayawa yayi yana kallon Indo tamkar wani gunki domin kuwa jin maganar ta yake tamkar tatsuniya cikin kunnen sa, Momy kuwa Hamdala tayi a fili daya kasance Indo bata son ɗanta, a fili ta furta cewa.

” Kin taimaki kanki da kika yankewa kanki hukunci domin kuwa ɗana yafi ƙarfin jakar ƙauye Irin ki wacce ta gagari iyayenta har saida suka dangana ta da iyayen wasu.”

Dariya sosai Mustafa yake tamkar wani sabon mahaukaci Abunda bai cika yiba cikin tarihin rayuwar sa wato yawan dariya yana duban Indo yace.

” Ƙarya take Momy tana sona cikin ranta duk duniyar nan babu wanda take so sama dani cikin rayuwarta, ki duba cikin ƙwayar idonta zaki ga zallar soyayyata cikin su, karki cuci kanki Indo ta hanyar haramtawa kanki Abunda kike so, idan kuma kikayi wannan kuskuren to tabbas zaki dasawa zuciyarki babbar cuta na tabbata nine *DUNIYAR KI NINE FARIN CIKIN KI NINE KUMA MAFARKIN KI*.”

Girgiza kanta Indo takeyi tamkar ƙadangare tana dubansa kafin tace.

” Ƙarya kake babu wata Soyayyar ka a tattare dani sai tsantsar ƙiyayyarka Na kuma ƙara furta maka *I HATE TO YOU*” tana gama faɗin haka ta haura step ɗin da gudu tana sakin wani kuka mai cin Zuciya.

Daddy daya daɗe tsaye bakin falon yana sauraron su basu san da zuwan sa ba, ya juya ya koma waje domin baya buƙatar susan yaji wannan abunda ya faru tsakanin su yana lura da take-taken kowa Kuma insha Allah ya kusa maganin matsalar.

Shima Mustafa juyawa yayi cikin mungun ɓacin rai yana haɗa hanya cikin layi tamkar mashayi ya fice daga falon cikin ikon Allah kuma bai lura da Daddy dake zaune compaunt ɗin gidan ba harya fice Daddy yana masa kallon tausayi, Momy kuwa ko a jikinta ta samu waje ta zauna tana Hamdala Indo bata son ɗanta yanzu hankalin ta ya kwanta saura kuma tasan yanda zatayi ta koreta daga cikin gidan kota ƙarfin tsiya ne, Sharifa tashi tayi ta haura step ɗin tana hawaye tayi bedroom ɗin su ruf da ciki ta samu Indo sai Rusar kuka take tare da sauƙe a jiyar ZUCIYA magana Sharifa ta soma mata.

” Meyasa zaki ƙaryata Soyayyar ki? Bayan ganan Soyayyar sa a cikin idanunki ana ganinsu, duk wanda ya sanki a cikin garin Dasina yasan kina son ya Mustafa, soyayya kuma ta gaskiya kuma har yanzu kina sonsa karki cuci kanki Indo ki amshi Soyayyar sa, na tabbata zaki samu kulawa domin shi mutum ne mai daraja Abunda yake yaso bai iya son abuba idan yana son abu yana iya komai dan ganin ya adana Sa, na tabbata ya Mustafa yana miki mahaukacin SO na hango Soyayyar gaskiya cikin idanunsa pls ki basa dama dan Allah ko sau ɗaya ne.”

Tashi Indo tayi tana goge hawayen idonta tana duban Sharifa cikin muryar kuka tace.

” ki daina wannan zargin cikin Ranki ni babu Soyayyar Mustafa cikin zuciyata na daɗe da mantashi cikin babin rayuwata da kike maganar cewa yana min Soyayyar gaskiya, wannan zancen naki ba gaskiya bane, Mustafa baya sona da gaskiya domin kuwa da Soyayyar gaskiya yake min daya soni tun ina ƴar ƙauye ta daya kawo min gyara cikin rayuwata amma duk baiyi hakan ba sai ƙyama da tsangwama daya dinga nuna min mugunta kala-kala ya nuna min haka zagi iri-iri yamin hakan shi kike ƙira Soyayyar gaskiya eh tabbas naso Mustafa a baya amma a yanzu na tsanesa, na tabbata yanzu ma akwai Abunda yake buƙata a jiki na ne shiyasa ya shiryo min wannan yaudarar da zarar kuma ya samu Abunda yake buƙata zaiyi watsi da rayuwata, dan Allah ina riƙon ki Aunty Sharifa ki daina shiga cikin lamarina da Mustafa domin ni nasan abinda ke baki sani ba game dashi, *ƊAN UWAN KI MACIJIN SARI KA NOƘE NE LUMBU LUMBU NE SHI WUTAR ƘAIƘAYI* dan haka ki ƙyale maganar haka ta wuce.”

Shuru Sharifa tayi sai can tace.

” Shikenan na ƙyale, sai dai ina son na baki Hkr game da abubuwan da Momy take miki…….”

Dakatar da sharifa Indo tayi ta hanyar cewa.

” Ba sai kin bani Hkr ba, duk abunda Momy tamin takai tamin ne, tana da iko dani dan haka ban damu ba dan ta zage ni.”

Shuru Sharifa tayi tana jingina kanta da jikin bed ɗin tana jinjinawa hkrn Indo wanda lokaci ɗaya Allah ya bata shi ta tabbata da sanda Indo take Indon ta ne sai ta rama zagin da Momy ta mata sai kuma gashi yanzu cikin ikon Allah har a zagi Indo ta ƙyale Lallai UBANGIJI shine mai gyara bawansa a duk sanda yaso, komawa Indo tayi ta kwanta tana cigaba da zubar da hawaye cikin ƙunar Zuciya.

Habeeb kuwa cikin fushi ya shiga part ɗin nasa a falo ya sami Hasina ta shirya abinci a daining tasha wanka cikin ƙananan kaya tana jiransa, da sauri ta tashi tana cewa.

” Sannu da dawowa sweetie na, gaskiya ka juma da yawa harna fara gajiya da jiranka ina shirin kiranka sai gashi ka shigo.”

A taƙaice Habeeb ya cewa Hasina.

” Eh na shiga part ɗin Momy ne shiyasa na ɗan juma.” Yana maganar yana shigewa bedroom ɗinsa, tsayawa Hasina tayi tana dubansa cikin mamaki domin ba haka ya saba shigo mata cikin gida ba, da fara’a yake shigowa harma ya rungume ta yanzu kuma taga saɓanin haka ya shigo mata rai ɓace binsa tayi cikin bedroom ɗin nasa yana zaune saman kujerar ɗakin mai biyu ya jingina kansa yayi shuru yana kallon silim, zama tayi kusa dashi tace.

” Lafiya kuwa sweetie na naga ka shigo cikin ɓacin rai?”

A taƙaice yace mata.

” Lafiya lau babu komai.”

” Amma ba haka ka saba shigowa ba sai nake ga kamar akwai Abunda yake damunka pls ka sanar dani dan Allah ko na maka wani laifi ne mijina bana son ganinka cikin ɓacin rai.”

Cikin fara gajiya da tambayoyin Hasina gashi shi ya tsani idan yana cikin damuwa ake masa magana ce mata yayi.

” Nace miki babu komai ko zan miki ƙarya ne ni babu abunda kika min kawai banji HAPPY ne yanzu.”

” Shikenan to ga nan abinci na gama daman kai nake jira, idan kuma wanka zaka fara sai na kai maka ruwa.?”

” Na ƙoshi bazan ci Abincin ba wankan ma bazan yiba ” ya faɗa mata cikin ƙaguwa da maganganun ta.

” Ka ƙoshi kuma me kaci da zaka ce ka……..”

Cikin tsawa ya dakatar da ita ta hanyar cewa.

” Kin fara isata da magana malama! Nace miki bazan ciba ana dole ne, pls And pls live me a long, bana son damuwa ki fice min daga ɗaki nace bana buƙatar ki kusa dani.”

Tashi Hasina tayi baki buɗe tana ja da baya cikin tsoro domin kuwa tunda take da Habeeb bai taɓa mata tsawa ba sai yau Tambayar kanta take laifin me ta masa haka yake mata tsawa, harta fice daga ɗakin nasa ta faɗa nata zama tayi ta fashe da kuka tana tuhumar kanta laifin me tayiwa mijinta sosai take kuka, domin ta fahimci tunda Habeeb ya fara son Indo komai yake neman sauyawa cikin gidan ta mussaman farin cikin mijinta, tasan wannan fushin nasa yana da alaƙa da Indo tunda daga gidan su yake Kuma tasan Indo tana cikin gidan.

” Ya Allah ka dawo min da farin cikin gida na, dole na sanar da Indo Soyayyar da mijina yake mata, ko zai samu SASSAUCIN CIWON DAKE CIKIN ZUCIYAR SA wannan itace kaɗai mafitar da nake dashi.

Mustafa kuwa bedroom ɗinsa ya shige ya hau fashe fashe komai na glass dake cikin ɗakin Mustafa sai da ya fasa tamkar mahaukaci ya dawo yana maganganu.

” Akan me zaki ƙaryata Soyayyata akan me zaki ce bakya sona why! *SHATUU* so kike ki tarwatsa Zuciyata meyasa zaki hukuntani da hukunci mafi muni pls *SHATUU* karki zalunci Rayuwata nasan kina sona to meyasa yanzu zaki ce soyayya ta ƙarya ce”

Tamkar mahaukacin zaki haka Mustafa ya dawo RAUDA jin ƙarar fashe-fashe da tayi shi yasa ta nufo bedroom ɗin nasa da gudu hanunsa duk ya yanke sai zubar da jini yake da sauri ta riƙe hanun nasa tana cewa.

” Subhanallah ya Mustafa lafiya meya sameka kaida waye kaga hanunka yanda yake jini?”

Mustafa fuskar Indo yake kallon RAUDA gani yake kamar itace a gaban sa hatta muryar RAUDA ta Indo ta koma masa, Rungume ta yayi da sauri yana sauƙe ajiyar Zuciya, a hankali ya soma Magana.

” Please karki ƙara cewa bakya sona, karki barni dan Allah mutuwa zanyi idan kika ƙyale ni, ina sonki kece Rayuwata.” Ya ƙarasa maganar suna zubewa saman bed, wani mungun daɗi ne ya tsargawa RAUDA yau Mustafa ne ya furta mata cewa itace rayuwar sa, ƙara ƙanƙamesa tayi tana jin wani farin ciki.

” Bakin sa Mustafa ya haɗa dana RAUDA, shi duk a haukar sa Indo ce gabansa, wani hot kiss yake mata tare da nasarar capko harcen ta, sosai yake wasa da sassan jikinta daman ya lafiyar kura bare kuma ta samu nama ita kuwa RAUDA sai wani irin miƙar daɗi take yi cikin hikima da Nasara ya samu damar rabata da suturar jikinta shima yayi fillo da nasa ƙasa RAUDA bata fara dawowa hankalin ta ba saida ta fara jin zafi ta ƙasanta, sannan ne ta fara neman zamewa amma ina Mustafa yayi nisa baya jin ƙira duk kukan RAUDA da yakushin ta Mustafa bai ƙyaleta ba sai ma cewa da yake.

” Ina sonki SHATUU dan Allah karki rabu dani wallahi mutuwa zanyi idan babu ke cikin rayuwata ina SONKI SHATUU na, tun sanda kike Dasina har zuwa yanzu da nake tare dake.”

Wani irin baƙin ciki ne ya doki zuciyar RAUDA mijinta ne yake saduwa da ita yake kiran sunan wata yunƙura tayi da ƙarfi tana kuka zata ƙwaci jikinta daga nasa amma ina Mustafa yafi ƙarfin ta, duk ihun RAUDA saida Mustafa yasha romonta bai ƙyaleta ba sai da ya gaji dan kansa sannan ya mirgina gefe yana lumshe idanunsa, RAUDA kuwa kuka kawai take na baƙin ciki ga wani irin mungun zogi da ƙasanta yake mata…..

 

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/4, 10:09 PM] Ummu Nasmah: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CaoZrO2pfJ99s0CxBTC5RW

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Ga mai buƙatar wannan group ɗin sai yayi joining amma group ɗina yana da dokoki zan faɗo muku dokokin a ƙarshen page ɗin nan.*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••9️⃣ ↗️ 1️⃣0️⃣

Lumshe idonsa yayi tare da jawota jikinsa ya ƙanƙameta yana rufe su da blanket, har yanzu RAUDA bata daina shashsheƙar kuka ba, ta kuma kwanta lamo a ƙirjinsa a haka bacci mai nauyi yayi gaba da Mustafa RAUDA kuwa idanunta da suka kaɗa sukayi jajur ta ɗago tana ƙarewa Mustafa kallo tabbas tana son mijinta sai dai sam shi bata cikin rayuwarsa, hanunta ta kai ta shafo fuskarsa tana furta cewa.

” Bani da wani aibin da zaka ƙini, kullum tunani nake menene aibina da zaka tsaneni haka, laifi na shine kawai danna soka na aureka meyasa kake ambaton sunan Indo bayan dani kake tarayya a wannan lokacin wannan shine daren farko na dakai sai dai gashi yazo min da ƙalubale a cikin sa kaicona ni RAUDA da na biyewa son zuciyata Gashi yanzu ina cikin tsaka mai wuya.”

Ta ƙarasa maganar tana ƙara sakin kuka mai ban tausayi duk abunda take Mustafa bai san tana yiba baccin sa yake hankali kwance a haka itama bacci ɓarawo ya saceta, ƙiran sallar asubar farko a kunnen Mustafa a hankali ya buɗe idanunsa ya akan RAUDA ya sauƙe su ƙara ware idanunsa yayi yana mamakin meya kawo RAUDA bedroom ɗinsa har kuma saman ƙirjinsa, dafa kansa yayi zuciyarsa na tariyo masa Abunda ya faru tsakanin su tiryan-tiryan.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!” Ya furta tuno Abunda ya shiga tsakanin su, shikenan Abunda baya so ya kasance tsakanin sa da RAUDA ya faru yaso adana maitar sa har zuwa Ranar da Allah zai mallaka masa Indo a matsayin matar sa ta Sunnah yaso ace da ita ya fara sanin wata mace a duniya sai gashi lokaci ɗaya RAUDA ta wargaza masa tanadin daya daɗe yana yiwa *SHATUUN SA* duban sa ya ƙara kaiwa gareta Baccin ta take ganan bushashshan hawaye kuma kwance a fuskar ta, haka kawai kuma sai yaji ta basa tausayi domin shi kansa yasan tasha wahala daren jiya, a hankali ya zameta daga ƙirjinsa ya mayar mata da kanta bisa filo, tashi yayi ya shige tollet hanunsa daya yanke ya ɗauki hankicin ɗinsa ya ɗaure hanun, wankan tsarki ya fara kafin yayi wanka, ruwa mai zafi ya haɗawa RAUDA kafin ya fito ɗaure da towel ya fice daga bedroom ɗin kitchen ya nufa ya ɗebo gishiri kaɗan ya dawo bedroom ɗin tollet ɗin ya ƙara shiga ya zuba gishirin a ruwan zafin kafin ya dawo ya zauna bakin bed ɗin a hankali yake tashinta ta hanyar dukan kafarta buɗe idonta RAUDA tayi takai dubanta ga Mustafa kafin tayi saurin sauƙe kanta ƙasa tana mai jin kunyarsa, taɓe bakin sa Mustafa Yayi kafin yace.

” Ki tashi ki shiga tollet ki samu ki gasa jikinki na haɗa miki ruwan zafi” yana faɗa ne tare da kawar da kansa gefe.

Ƙoƙarin tashi RAUDA tayi tana rufe jikinta da blanket ɗin, taji wani mungun zafi a ƙasanta Wash ta furta da ƙarfi ta koma ta zauna cikin sauri tana cije leɓenta sai kuma hawaye shar, duk abunda take Mustafa yana kallon ta ta ƙasan ido tashi yayi yazo har gabanta bata ankara ba taji mutum ya ɗagata caɗak tare da wurgi da blanket ɗin gefe, rufe idonta RAUDA tayi cikin jin kunyar babu komai a jikinta, tollet yayi da ita, a cikin ruwan ya ajiye ta, ai kuwa RAUDA wani azabar zafi taji ƙara tasa tare da ƙoƙarin miƙewa daga cikin ruwan, hanunsa Mustafa yasa ya danneta a cikin ruwan cije leɓenta tayi tare da runtse idonta tana jin azaba sunfi 20 minute a haka kafin Mustafa ya saketa ƙanƙame jikinta RAUDA tayi cikin takura domin tana mungun jin kunyar ganinta da Mustafa yake a haka babu komai jikinta, taɓe bakin sa yayi yace

” Wani dare ne jemage bai gani ba kuma ai saidai daren mutuwar sa, idan kin so kiyi wankan tsarki idan kinso kuma karkiyi wannan ruwanki ne ganan towel a sama” yana gama faɗin haka ya fice daga tollet ɗin.

Binshi kawai da kallo RAUDA tayi tana ƙara sakin jikinta cikin ruwan domin yanzu ruwan ya daina mata zafi sai daɗin sa da take ji, ta juma cikin ruwan kafin tayi wankan tsarki tare da wanka ta fito ɗaure da towel ta ɗaura ɗaya kuma a kanta tana bin bango da ƙyar ta iso tsakiyar ɗakin, bata ganshi ba cikin ɗakin sai towel ɗin da ya cire ya rataye jikin drower agogon bangon ɗakin ta ɗaga kai ta kalla 5:15 hakanne ya tabbatar mata da sallah ya fita kayanta ta ɗauka ta fice tana bin bango harta samu tayi nata bedroom ɗin gadon ta ta faɗa ta kwanta tare da runtse idonta tana jin wani mungun bacci, a haka kuma baccin ya sace ta.

Mustafa kuwa bayan sun idar da sallah ne ya hango Habeeb Zaune can gefen masallaci yayi shuru yana tunani, kusa dashi Mustafa yazo ya zauna har ya zauna Habeeb baisan yazo ba dafa kafaɗar sa Mustafa Yayi, firgit Habeeb ya ɗago kansa ya kalli Mustafa yana sauƙe ajiyar Zuciya duban sa Mustafa Yayi yace.

” Bros meyake damunka haka tunanin me kake har nazo na zauna kusa da kai baka sani ba, ga kuma idonka yayi Red sosai meke damunka?”

Mustafa ya masa tambayar cikin tashin hankali domin kuwa ya tsani ganin ɗan uwansa cikin mungun yanayi ya gwammace ace shine yake ciki ba ɗan uwansa ba, Habeeb ɗago kansa yayi yana duban ɗan uwansa ji yake cikin zuciyarsa kamar ya sanar da ɗan uwansa Soyayyar Indo ce take neman zauta shi sai kuma ya tuno maganganun ɗan uwan nasa game da Indo inda yake cewa *( Nine Wanda ya dace da Indo ba Umar ba, nine Wanda na juma da ajiyar Soyayyar ta cikin zuciyata tun kafin takai ga wannan matakin Aunty Hindu SHATUU BUGUN NUMFASHI NANE INA SONTA FIYE YANDA NAKE SON KAINA HAKA KUMA INA DA TABBACIN CEWA ITAMA TANA SONA TUN TANA ƘARAMAR TA)* Runtse idonsa yayi yana jin wani mungun nauyi cikin ƙirjinsa bazai iya furtawa ɗan uwansa cewa ciwo ɗaya ke damunsu ba baisan wani hali ɗan uwansa zai shiga ba idan yaji damuwar sa, Mustafa dafa kafaɗar Habeeb yayi yace.

” Tunanin me kake haka Bros please tell me Hankali na ya tashi ka sanar dani dan Allah meke damunka na tabbata ba ƙaramin abu bane zaisa ka shiga wannan halin, nasan ka fiye da yadda nasan yunwar ciki na babu abunda yake ɓata maka rai yasa ka cikin damuwa
Duk duniyar nan domin kuwa kana dannesa gashi kuma har Rama kayi na tabbata akwai gagarumin Abunda yake damunka pls ka sanar dani ko zan iya maganin matsalar ka.”

Hawaye ne yake ƙoƙarin fitowa daga Idon Habeeb saurin mai dashi yayi ya dubi ɗan uwansa yace.

” Babu wani Abunda yake damuna fa kawai kwana nayi da ciwon kai ban samu nayi bacci ba shiyasa kaga idona yayi Red bani da wata damuwa ɗan uwa na ka kwantar da hankalin ka.”

Kaɗa kansa Mustafa Yayi yana cewa.

” Ban yarda ba Bros tabbas akwai Abunda yake damunka na tabbata ba ciwon kai bane idan ba haka ba meyasa ka rame lokaci guda me Kuma ya haɗa ciwon kai da tunani akwai Abunda yake damunka sai dai idan sanar dani ne baka son yi, kamin adalci ɗan uwana ka sanar dani matsalar ka, ko ka manta da cewa bama iya ɓoyewa junanmu damuwar mu ka manta da cewa matsalar ɗaya daga cikin mu matsalar muce duka karka barni cikin tunanin Abunda yake damunka pls ka sanar dani.”

Sosai jikin Habeeb yayi sanyi amma yasan komai zai faru bazai taɓa furtawa Mustafa damuwar sa ba, yasan idan ya furta masa sai ya shiga halin da yafi wanda shi yake ciki kallon Mustafa Yayi yace.

” Brother na gaya maka damuwata fa babu wani Abunda yake damuna kasan dai rashin bacci yana kawo rama ko, sannan shi ciwo yana saka mutum cikin tunani, karka ɗan uwana babu abunda yake damuna bayan ciwon kai, idan na faɗa maka wani abu bayan wannan to ƙarya kawai zan maka Please ka dakatar da Tambayar haka.”

Kaɗa kansa Mustafa Yayi ba tare daya yarda da maganar Habeeb ba, duban sa yayi yace.

” Okay ka tashi ka shiga cikin gida kaje kasha magani sai ka kwanta ko zaka samu kayi bacci Allah ya sauwaƙa.”

“Ameeen” Habeeb ya furta sannan ya miƙe tare suka shiga da Mustafa ya tsaya bakin part ɗin Habeeb har sai da yaga shigewar sa cikin gidan sannan yayi nasa part ɗin yana tunanin damuwar ɗan uwansa.

Habeeb yana shiga yaji wasu hawaye masu zafi sun zubo masa RAUDA da ta gama gyaran part ɗin nata ta zauna tana ɗan hutawa kafin ta ɗaura breakfast taga shigowar Habeeb cikin tashin hankali a kujerar da take ya zauna ta ɗaura kansa a kafaɗarta sai kuma ya saki kuka kamar ƙaramin Yaro shuru HASINA tayi domin yanzu ta fara sabawa da halin da mijinta yake ciki amma duk da haka duk sanda ta gansa cikin damuwa hankalinta yana mungun tashi shafa kansa tayi tace.

” Sweetie na menene kuma ya saka kuka da sassafe haka haba karka bada maza mana kaifa namiji ne wanda aka sanshi da jarumta da juriya dan Allah ka daina ɗaga hankalin ka akan ƙaramin abu.”

Saurin tashi daga kafaɗar ta yayi ya ɗago ido yana dubeta yana goge hawayen sa yace.

” Baki san damuwata bace shiyasa kike ambatar sa da ƙaramin abu amma a waje na babban abune wanda idan nayi wasa zai kawo min babbar illah cikin lafiyata ki daina kiran Abunda baki sani ba da ƙaramin abu.”

HASINA dafa kafaɗar sa tayi cikin hikima da dabara tace.

” Hakane bansan damuwar ka ba, shiyasa na faɗi haka tabbas nayi kuskure cikin maganata, sai ina ga ba laifi na bane laifin kane a matsayinka na mijina sirri na ka kasa sanar dani damuwar ka, sai dai kullum ka shigo min cikin gida rai ɓace a tunani na rashin yadda da kuma rashin bani mahimmanci cikin rayuwarka shine yasa ka kasa sanar dani matsalar ka, Abunda ya kaini ga fara tunanin fara ɓoye maka nawa sirrin tunda naga kamar babu yadda tsakanin mu.”

” Subhanallah! HASINA da bakinki kike furta min wannan maganar marar daɗin sauraro, ni kuwa idan ban baki yarda ta ba waye zan bawa, ba komai yasa na ɓoye miki damuwata ba, sai dan jinta baida wani amfani gareki saima cikin ƙunci da zaki shiga wanda ni bazan iya jurar ganinki cikin wannan halin ba, ki cigaba da taya ni da addu’a Allah ya yaye min wannan halin da nake ciki, karki matsa sai kinji matsalata domin bana son ki sani, ki cire duk wani zargi cikin zuciyarki ki kasance cikin kwanciyar hankali hakan yana sani farin ciki *INA ƘAUNAR KI HASINA I LOVE YOU*.”

Murmushi Hasina tayi ta faɗa jikin mijinta tana cewa.

” I love You too sweetie na, insha Allah Ubangiji zai yaye maka damuwarka.”

Sun ɗan juma a haka suna tattaunawa kafin HASINA ta tashi domin ɗaura musu breakfast shi kuma Habeeb kwanciya yayi bisa kujerar yana cigaba da tunanin sa kafin ya tashi yayi bedroom ɗinsa Shirin fita aiki.

💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

Misalin ƙarfe biyu na rana tana kwance bedroom ɗinsu gefenta kuma Sharifa ne kwance tana wasa da wayarta chart Indo take shigowar saƙon Barrister Umar ta gani bata buɗe saƙon nasa ba saida ta gama duba sauran saƙonnin kafin ta duba nasa.

” Hajiya ta na kira ki ɗazu baki ɗaga kira na lafiya kuwa, kinsan dai bana jin daɗi idan harna wuni ba tare da naji muryar ki ba ko.”

Tsuka mai ƙarfi Indo taja tare da tura masa cewa.

” Bana kusa da wayar ne da na zo na ga miss Call ɗin kuma na kira network ya hanasa shiga.”

Tana tura masa ta kashe datar ta, tana duban Sharifa tace.

” Ke Kuma Aunty Sharifa shirin me kike naga ɗazu da safe sai wani saka kaya cikin akwati kike, ina zuwa haka.”

” Wai baki da labarin cewa gobe zamu wuce Egypt da Aunty Hindu?”

Shuru Indo tayi take taji ranta babu daɗi hankalin ta ya tashi jin Sharifa zata tafi ta barta………

Kuyi hkr da wannan yau ina busy ne mu haɗu a next page, gashi ban samu nayi editing ba sorry for typing error.

DOKOKIN group ɗina sune👇🏻

Amsa sallama dole.

Dole ki fito ayi hira dake muddun kina online.

Yin sharhi dole domin shine ƙwarin gwiwwar WRITER’S.

Banda turo min Link ko TALLAH banda turo Abunda ya danganci batsa idan kuma kika turo zanyi remove ɗinki take.

Banda faɗa ko cece kuce banda zagin WRITER’S idan kin taka min doka ni kuma zanyi waje dake.

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

 

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/8, 7:23 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Duk wanda yace wannan BOOK ƊIN na kuɗi ne ƙarya yake Damfarar ku zaiyi book ɗina FREE ne bana kuɗi bane, book ɗina na kuɗi shine RUƊANIN ZUCIYA BIYU kuma ban fara sakin sa bama tukunna, dan haka SO BAI SAN JINI BA free ne bana kuɗi ba*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••1️⃣1️⃣ ↗️ 1️⃣2️⃣

” AUNTY Sharifa da gaske dake Ummi zata tafi Egypt, yanzu ni kaɗai zan zauna a bedroom ɗin nan bazanji daɗi ba Aunty Sharifa idan kika tafi zanyi kewarki sosai.”

” Kiyi hkr Indo ni kaina ba son tafiyar nake ba dole ne tasa zan tafi tunda umarnin Daddy ne, itama Aunty Hindun tana zuwa Anjuma naso ace kece kika tafi Egypt domin na tabbata zakiji daɗin zama da Aunty Hindu fiye da zama da Momy da kike cikin takura kina hkr da Momy Indo ni shaidace akan haka ki kuma ƙara hkr insha Allah komai zai wuce tamkar bai taɓa faruwa ba.”

Murmushi Indo tayi tana duban Sharifa tace.

” Aunty Sharifa waya ce miki bana jin daɗin zama da Momy, nikam ina jin daɗin zama da ita sosai ki daina cewa bana jin daɗin zama da Momy karki ƙara dan Allah, tafiyan ki Egypt kuma Allah yasa hakan shi yafi Alkairi.”

Ameeen Sharifa ta amsa tana cigaba da danna wayarta Ishaq ne ya shigo cikin bedroom ɗin yace.

” AUNTY Indo wai kije inji Daddy yana falon ƙasa kema Aunty Sharifa harda ke.”

Da to Indo ta amsa sannan ta tashi tare da ɗaukar ɗan kwalinta ta yafa tabi bayan Ishaq, Indo bata juma da fita ba itama Sharifa ta bi bayan ta, kusa da Daddy Indo ta Zauna tana cewa.

” Barka da HUTAWA Daddy.”

Murmushi Daddy Yayi amsa mata da cewa.

” Barka ƴata, Ishaq yace ina kiran ki ko.?

” Eh Daddy shiyasa ma na zoni.”

MOMY haɗa ranta tayi tana hararar Indo tare da jin haushin ta, gyaran murya Daddy Yayi yace.

” Masha Allah ya dai zaman gidan kina jin daɗin sa kuwa.?

Kanta sunkuye Indo tace.

” Ina jin daɗi sosai daddy.”

Dubanta Daddy Yayi kafin yace.

” Ki faɗa min gaskiya kina jin daɗin zaman gidan nan babu wata matsalar da kike fuskanta idan akwai karki ɓoye min ki sanar dani a matsayina na mahaifin ki kema nan gidan kune baki da banbanci da ƴaƴan dana haifi .”

Murmushi Indo Tayi tace.

” Babu wata matsala fa Daddy ina jin daɗin zaman gidan SOSAI.”

Kara jefa mata tambaya Daddy Yayi cikin rashin yarda da maganar ta yace.

” Kin tabbata babu wata matsalar dai ko.?

” Da gaske Daddy babu komai, normal komai yake tafiya Banda wata matsala.”

” Okey daman kiran da na miki akan maganar cigaban karatun kine so na samu abokina prof Usman Abba Gaɗan munyi magana sosai so ya bani admission ya kuma cemin na bada kuɗin registration ɗinki kawai ana farawa zai miki nace Cose ɗinki kuma ya cike miki ɓangaren Maths Education Allah ya baki Sa’a, yace zai kira ya sanar damu ranar da zaki fara lectures yau sati Uku kenan da maganar da mukayi dashi to sai ɗazu ya kira ni yake shaida min cewa ya miki registration a University of Dutse ranar monday zaki fara lectures, Allah yasa Cose ɗin da na zaɓa miki ya miki.”

Sosai Indo tayi farin ciki da jin zata fara zuwa jami’a tayi farin ciki sosai duk da dai Cose ɗin da take so bashi Daddy ya zaɓa mata ba ita Science taso tayi shi kuma Daddy ya cike mata Maths Education duk da haka taji daɗi sosai duban Daddy tayi tace.

” Daddy yayi sosai bani da wani zabi zaɓinka shine dai-dai a wajena, na gode sosai da kulawar ka gareni Daddy na gode Allah ya ƙara buɗi.”

” To alhamdulillah tunda ya miki babu damuwa Allah ya miki jagora yasa ki fara a Sa’a A’isha karki sa wasa cikin ranki kiyi Abunda ya kaiki kiyi karatu sosai banda shiga shirgin ƙawaye Allah ya miki albarka ya Albarkaci karatun da zaki fara ki gama cikin nasara.”

Da “Ameen” Indo ta amsa tana murmurshi, kafin Daddy ya kai dubansa ga Sharifa yana mata nasiha game da tafiya da zasuyi Egypt da Aunty Hindu sosai ya mata faɗa, har Aunty Hindu tazo.

Wuni kas Aunty Hindu tayi duk Inda tayi Indo tana kusa da ita har wajen Hasina sukaje tare sanda suka je Habeeb baya nan ya fita aiki, Hasina kaɗai suka samu Kuma ko a fuska Hasina bata nunawa Indo wani sauyi ba yanda suka saba mu’amala yauma haka sukayi cikin wasa da dariya, har suka tafi haka suka shiga wajen RAUDA ma sun sami Mustafa yana Zaune falon ita kuma RAUDA tana zaune a gefe cikin sakin fuska RAUDA ta tarbesu hatta Indo RAUDA bata sanja mata fuska ba sai dai harga Allah tana jin zafin Indo cikin ranta amma bata yadda hakan ya fito a fuskar taba, Mustafa kuwa tun shigowar su hankalinsa yana kan Indo, gaishe da Aunty Hindu yayi yana cewa.

” AUNTY kardai ace sallamar kenan Egypt tayi kira.”

Dariya Aunty Hindu tayi tace.

” Eh mana Egypt tayi kira aima naga wannan karon mun juma cikin Nigeria.”

” Gaskiya kunsha Nigeria sosai ma kuwa, wannan kam Aunty kin sadakar mana ita muna nan tare babu ita babu komawa Egypt” ya ƙarasa maganar yana nuna HASINA.

Dukkan su dariya sukayi Hasina tana dariya tace.

” Bashi kaci zan rama, naga alamar so kake nayi azarɓaɓi a gaban Ummi to bazan yiba amma dai zamu haɗu zan rama.”

Murmushi yayi yace.

” Ai kuwa sai dai ki rame malama badai ki rama ba” nuna Indo Yayi yana cewa ” Aunty wai ita wannan kurma ta zama ne, naga ta kasa Magana oh sorry ashe dai tana kunyar yiwa masoyinta magana a gaban surkarta, Aunty Hindu kin min kofsi kin hana naji muryar masoyiyata.” Ya ƙarasa maganar yana kannewa Indo Ido.

Harara Indo ta doka masa tana kawar da kanta gefe HASINA kallon tausayi take yiwa Mustafa kai harma da Habeeb da baya wajen ita tsoron ta ma kar Soyayyar Indo tayi sanadiyar rabuwa tsakanin waɗannan ƴan uwa biyu da suke tsantsar son junan su, cikin zuciyarta take addu’ar Allah ya hana hakan faruwa, Aunty Hindu kuwa murmurshi tayi tace.

” Kai da yaron nan baka da kunya a gaban nawa kake furta waɗannan kalmomi, aidai ka saya ko dan albarkacin idon ƴata RAUDA ko, kunga ku tashi mu wuce kafin ya ƙara ɗauko wata maganar.”

Ita dai RAUDA bata ce komai ba sauraransu kawai take amma cikin zuciyarta tana jin zafi ita kanta ta matsu subar cikin gidan, shi kuwa gogan dariya yayi yace.

” Au dan kawai na faɗi iya gaskiya ta Aunty shine rashin kunyar, to ai Aunty indai ina kusa da *ABINCIN ZUCIYATA* bazan taɓa iya control ɗin kaina ba.”

Tsuka mai ƙarfi Indo taja tare da tashi ta fice daga falon, ai kuwa shima Mustafa rufa mata baya yayi Aunty Hindu da RAUDA har Hasina binsu da kallon mamaki suke, ita Hasina tausayin su take ji domin kuwa tana hango zallar soyayyar Indo cikin idanun Mustafa kamar dai yadda ta saba gani a idanun mijin ta.

Da ƙarfi ya fisgo ta tare da janta yayi garden da ita, ƙoƙarin fisgewa Indo take daga hanunsa amma ta kasa har suka isa Garden ɗin sannan ya sake ta yana Binta da kallo, cikin haki da masifa Indo tace masa.

” Meye haka Malam zaka wani jawoni tamkar wata ƴarka, wai me kake nema a waje nane ka takurawa rayuwata haka.?”

Murmushi sosai Mustafa yake cikin confidence ya amsa mata da cewa.

” *SOYAYYAR KI* Soyayyar ki ita nake nema itace kawai dalilina na takurar da kike ƙira ina miki duk da dai ni nasan babu wani takurawar da nake miki.”

Duban sa Indo take Ido cikin Ido kafin ta bushe da dariya sosai take dariya tana nunasa da hanu, shiko binta kawai yake da kallo yana ƙara hango tsantsar kyawun ta, mussaman dumple ɗinta da suke lotsawa ji yake kamar ya jawota jikinsa ya rungume, wani irin Soyayyar tace yake fisgar sa, muryar ta daya ji ne yasa shi dawowa daga duniyar daya faɗa cewa take.

” Ni kuma nace bana sonka, bana ƙaunarka dabadan alkairin da ya Habeeb ya min ba cikin rayuwata da sai nace ko mai kama da kai bana ƙauna amma bazance haka ba, saboda ya Habeeb Ya Mustafa na roƙeka da ka ƙyale ni ka daina damuna akan Soyayyar ka ta ƙarya domin kai maha’inci ne mayaudari bazan kuma taɓa yadda na faɗa tarkon yaudarar ka ba.”

Shima dariyar yayi kafin yace.

” Ina mamakin yadda kike iya ƙaryata Abunda ya bayyana a gareki tare da alamomin su, ko kin manta a gaban wa kike furta wannan kalaman ne, Mustafan kine fa Wanda kike so tun ƙuruciyarki wanda duk ƙauyen ku anshaida wannan Soyayyar da kike min ko kin manta da *kifiyar Soyayyata da kike furta cewa suna sukan ki aduk sanda naje garin ku* ashe itama duk ƙarya ce?”

Murmushi Indo tayi tare da kaɗa kanta sannan tace.

” Alhamdulillah tunda a cikin kalamanka ka furta *ADA* kaima kace da kuma ai kaga da da yanzu ba ɗaya bane wancan haukar yarinta ce tare da tsantsar ƙuruciya, *Mlm Mustafa ya kamata fa yanzu kasan cewa Yanzu ba Indon dasina bace a gaban ka wannan A’ISHA CE wacce ta waye ta kuma goge Ras a cikin birni kaga kuwa kamata yayi kasan cewa yanzu na kai matakin da zan iya BANBANCE TSAKANIN FARI DA BAƘI dan haka yanzu na wuce tunanin ka Mlm, idan ma kana tunanin cewa Indon da kasani dace wacce zaka taka ta ta bika to yanzu ka dawo daga shirmen tunanin ka domin kuwa BANA SONKA sai kabi wani sarkin kuma badai wannan ba*.”

Kuyi hkr da wannan Wlh yau ina busy ne naso nayi typing ɗin yafi haka yawa afuwan fan’s🙏🏻

Na tsayar da posting ɗin so bai san jini ba sai zuwa bayan Sallah idan Allah ya kaimu dan gaskiya bazai yiwu na gama book ɗin ba kafin azumi gashi kuma azumi ya kawo kai, ga kuma uzirori da suka sani gaba suke hanani typing insha Allah sai Bayan Sallah idan Allah ya kaimu zan cigaba da posting.

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

 

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/10, 1:47 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

*Da nace na tsayar da wannan book ɗin sai bayan Sallah, sai gashi kuma Fan’s sun sakoni a gaba cewa lallai nayi hkr na cigaba da musu posting kafin azumi*.

*Zan cigaba da posting amma a duk sanda na samu Lokaci it means ba kullum ba*.

*A ƘAFTA FAN’S MUJE KARATU📖*
__________________________________

*P*••••••1️⃣3️⃣ ↗️ 1️⃣4️⃣

” Hmmm *ƘARYA KIKE SHATUU!* Ba ki isa ki rusa min farin ciki na ba, bazaki wargaza min mafarki na ba domin duk duniya babu macen da nake so sama dake ki sani cewa rasaki tamkar rasa numfashina nane, eh rasa numfashina domin kuwa babu ta yadda za’ayi numfashi ya daidaita ba tare da taimakon hanci da baki ba, idan hanci ya toshe baki kan taimakawa wajen shaƙar isa haka zalika idan baki na rufe hanci shike bada numfashi, kinga idan babu su babu Rayuwa kenan domin sune masu taimakawa ruhi wajen tafiyar da daidaiton Rayuwa, misalin yadda Soyayyar ki take a gareni kenan, rasaki tamkar rasa Rayuwata ne karki kasance daga cikin masu neman rayuwar ɗan adam mussaman ni da na kasance masoyi gareki idan har na mutu sanadin Soyayyar ki to TABBAS kece ajalina zan kuma yi farin cikin cewa na mutu da Soyayyar ki cikin zuciyata, ta wani ɓangaren kuma zanyi baƙin cikin har na mutu ba tare da kin furta min kalmar *I LOVE YOU* karki kasance cikin mata masu son kansu *SHATUU karki zama ajalina SHATUU*.”

Tsagaitawa Yayi da maganar yana duban ta da idanunsa da suka kaɗa suka koma jajaye ya na mungun jin zafin maganganun ta a cikin ransa, murmurshi Indo tayi kafin ta maida masa amsa da cewa.

” idan har ka cigaba da ƙaryata kalamai ma to tabbas ƙwaƙwalwar ka ta toshe, idan har kana ɗauka cewa nice farin cikin ka to daga yau ka fara ɗaukata a Matsayin Baƙin cikin ka, idan har nice mafarkin ka, to ka daina bacci domin kuwa mafarkin ka ƙarya ne bazai taɓa zama gaskiya ba bare kuma ya tabbata, idan har nice macen da kake so ina mai baka shawarar cewa ka ɗauki wannan ƙaryar Soyayyar taka ka bawa matar ka ta sunan domin kuwa itace ta dace da kai sam ni bana ɗaukar ka a matsayin masoyi sai Maƙiyi, idan kuma har na kasance nice Numfashin ka kamar yanda ka ambata to daga yau ka fara lissafin ranar mutuwar ka, domin kuwa saina toshe duk ta inda wannan Numfashin zai isa gareka, karka yaudari kanka Mlm ka yi tunanin zaka yaudareni da waɗannan kalaman naka ina mai baka shawara daka taushi zuciyarka ka bata shawarar cewa ta fice daga cikin rayuwata domin wahalar banza take sha, idan kuma har ta cigaba da sani cikin ta to tabbas *ZUCIYAR KA TANA GAF DA BUGAWA DOMIN BAZAN TAƁA SONKA BA* Ina kuma tabbatar maka da cewa idan baka gaji da furta min *I LOVE YOU* ba to ni kuwa bazan gaji da furta maka *I HATE TO YOU* ba ka taimaki kanka ka fita daga cikin rayuwata ka barni na huta kaima ka hutar da zuciyarka.”

Juyawa tayi da niyar barin wajen kawai sai tayi kicibus da Habeeb a gabanta domin kuwa yadda fuskar sa ta sauya tabbas hakan ya nuna mata cewa yaji komai dake faruwa tsakanin su Tambayar kanta Indo take yaushe Ya Habeeb ya zo nan kallon sa tayi tace.

” Ya Habeeb yaushe…….”

Dakatar da ita Habeeb yayi ya ɗaga mata hanu cikin tsantsar ɓacin rai tare da cewa.

” Ba sai kince komai ba jeki kawai ki jeki.”

” Amma ya Habeeb……….”

Cikin tsawa Habeeb yace.

” Nace ya isa ko! Ki shige daga gabana malama.”

Zaro ido Indo tayi tana duban Habeeb cikin mamaki to mai ta masa ko dan tace bata son ɗan uwansa shine shima zai tsaneta, da gudu ta fice tare da sakin kuka, runtse idonsa Habeeb yayi yana ƙoƙarin juyawa yaji muryar Mustafa yana cewa.

” *Me nake hangowa cikin idanunka kamar kishi Allah yasa kar zargina ya kasance gaskiya muna son abu ɗaya nida ɗan uwana wanda wannan abun dole mutum ɗaya ne zai mallakesa, menene yasa idanunka juyawa lokaci ɗaya menene dalilin daya sa zuciyarka fusata har ka kasa jure hakan sanda fuskar ka ta nuna, a tunanina TSANTSAR KISHI NE KAWAI YAKE JAWO HAKAN* Kasanar dani menene amsar tambayoyina shin hasashe na gaskiya ne.?”

Shuru Habeeb yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi gashi har yanzu tsantsar kishin ɗan uwansa yake ji cikin ransa tunda ya shigo cikin gidan yaji labarin cewa Indo tana tare da Mustafa a garden hankalinsa ya kasa kwanciya shine dalilin daya sa harya zo nan wajen duk da baisan Abunda suke tattaunawa ba zuwan sa wajen kenan Indo ta juyo, amma zuciyarsa na sanar dashi cewa SOYAYYA suke mussaman daya kasance cikin Garden suke, ba tare daya amsawa Mustafa tambayar sa ba ya nufi hanyar fita, kiransa Mustafa yake amma Habeeb bai sauraresa ba, taɓe bakin sa Mustafa Yayi tare da juyawa yana jin cikin ransa yanzu ma ya fara son *SHATUUN SA* domin a tunaninsa gani yake kamar Abunda ya mata a ƙauye take ramawa yana tunanin zata sosa idan harta huce.

INDO kuwa fitowar ta bata ga kowa ba babu su Aunty Hindu, ba tare da wata tambaya ba, kawai itama ta fice daga cikin gidan, Habeeb kuwa a fusace ya wuce part ɗinsa zuciyarsa na wani irin tafasa Wato Indo amanarsa zata ci ta kasa gano cewa yana sonta har yanzu duk abunda Mustafa ya mata na wulaƙanci harta mantasu tazo ta basa haɗin kai har suna Soyayya TABBAS ɗan Adam butulu ne, fashewa yayi da kuka ya durƙusa da gwiwowinsa yana kuka yana ambaton cewa.

” Ban taɓa tunanin akwai Ranar da zan miki son Aure ba bayan na ƴan uwantaka, ban taɓa tunanin tausayin ki zai rikiɗe ya juya min SOYAYYA ba, Sai daman SONKI zai min kamun Huhun goro, gashi Yanzu ya dabaibaye ni yamin ƙullin da bazan iya suncewa ba, tabbas Rayuwata tana cikin haɗari na Soyayyar ki lallai na faɗa tarkon Soyayyar da ba mai iya fitar dani sai Allah Tabbas igiyar sonki ta zargeni fisgeta KUMA tamkar fisge rayuwata ne, meyasa zuciyata zaki min zaki kamu da Soyayyar wacce kinsan tana da wanda take so tun ƙuruciyar ta?”

Sosai Habeeb yake sambatu shi kaɗai tamkar wanda ya zare, Hasina dake tsaye tana sauraronsa tare da danna recording a wayarta tana naɗar dukkan maganganun Habeeb, juyawa tayi tare da komawa bedroom ɗin ta zama tayi tare da yin tagumi, ita wannan lamarin yanzu ya fara isarta ta gaji da ganin rashin kwanciyar hankali tattare da mijinta gashi har yana neman ya shafi rayuwar auren su, tashi tayi tamkar wanda aka tsikare ta ta ɗauki mayafin ta ta fice cikin sauri.

INDO kuwa tana shiga part ɗinsu ta hango Barrister Umar tsaye jikin motarsa tsuka mai ƙarfi taja ita fa gaskiya ta fara gajiya da takurar sa, kawai gara ta faɗa masa gaskiya ita bata sonsa Zuciyarta ce kuma tace mata, to ai bai furta miki cewa yana sonki ba, tsuka ta ƙara ja tana ƙarasowa tsayawa tayi a gabansa tana cewa.

” Sannu da zuwa Barrister ya aiki.”

” Alhamdulillah na gaji da rashin ɗaukar wayata da bakya yi ko text na turo miki babu reply shiyasa nazo naji dalili?”

Murmushi Indo kanta na sunkuye a ƙasa ga kuma ɓacin rai da zullumin Habeeb, dubansa tayi tace.

” Ba kin ɗaukar wayar ka nake ba, kawai kana kira sanda bana kusa da wayar ne, laifina Kuma shine na rashin bin kiran da banayi kayi hkr.”

Murmushi Barrister Yayi ganin ta ɗauresa da jijiyoyin jikinsa, tunda gashi ta basa hkr dubanta yayi yace.

” Magana mai mahimmanci ne take tafe dani Allah yasa zaki fahimce ni.”

Amsa ta basa da cewa.

” Ina sauraron ka”

Kafin Barrister Umar yayi magana HASINA ta rigasa t Hanyar yin Sallama, amsa sallamar sukayi, Barrister Umar ya gaisheta sannan Hasina ta dubi Indo tace.

” Idan kun gama ina jiran ki a ciki.”

Da to Indo ta amsa kafin HASINA ta wuce ciki magana Barrister Umar ya fara.

” *A’isha* ina sonki.”

A firgice Indo ta ɗago kanta tana duban Barrister UMAR, shi kuwa murmurshi yayi yace.

” Eh ina sonki tun randa na fara haɗa Ido dake Ranar Denern su Oga Mustafa tun ranar Soyayyar ki ta ɗarsu a cikin zuciyata Allah yanda nake ji cikin zuciyata kema hakan kike ji.”

Ɗago kanta Indo tayi ba tare da shaƙƙun komai ba tace wa Barrister Umar.

” Kayi Barrister Babu soyayya cikin zuciyata bawai nace bana sonka bane, a’a kawai ban tashiwa Soyayya bane ka fahimce ni, mu ajiye batun soyayya a gefe mu cigaba da mutunci.”

Murmushi sosai Barrister UMAR JIJJI yayi kafin yace.

” Karki yanke hukunci cikin gaggawa, kije kiyi tunani kafin ki yanke hukunci, zanzo daga baya naji menene ra’ayin ki, ita Soyayya ba’a dole idan ban miki ba, zan ɗauki ƙaddara domin ita Soyayya haka ta gada kije kiyi nazari, ki koma ciki Hasina na jiranki nima zan shige.”

“Na gode” Indo ta furta sannan ta juya ta shige cikin gida, a falo ta tarar da Momy da Hasina da Aunty Hindu sai Sharifa Zaune, kusa da Hasina Indo ta zauna Momy kuwa harara ta zabgawa Indo sunkuyar da kai Indo tayi ba tare data ƙara haɗa ido da Momy ba, kama hanun indo Hasina tayi suka haura sama har bedroom ɗinsu, kallon Indo Hasina tayi kafin tace.

” Alfarma nazo nema a gareki Indo Wannan shine karo na farko dana fara neman alfarmarki ina fatan zaki min wannan alfarmar.”

Kallon Hasina INDO tayi sannan tace.

” AUNTY HASINA niko me zaki tambaya a gareni wanda bazan iya miki shiba ki tambaye ni koma menene zan miki shi muddun ina da halin haka.”

Murmushi Hasina tayi tace.

” Sanin kina da alfarmar da zan tambaya a gareki yasa nazo nementa gareki.”

” Ina sauraron ki Aunty Aunty Hasina ki faɗa min abunda kike buƙata a gareni na samu na miki shi cikin gaggawa.”

” *So nake ki Auri MIJINA* ki Auri Habeeb ceto rayuwar MIJINA daga halin da Soyayyar ki take neman jefa shi na gaji da ganin shi damuwa ina son gani farin ciki a idanun MIJINA wala Allah ko nima zan samu farin ciki daga garesa.”

Tunda Hasina ta fara maganar Indo take binta da kallo tana girgiza kanta cikin Ruɗani tare da tsantsar mamaki take duban Hasina kafin tace.

” Kinsan me kike faɗa kuwa Aunty Hasina, Ya Habeeb kike kira na Aura keda kanki kike wannan maganar, Aunty idanma kinzo ki gwada nine to ki sani cewa nikam ba maciya amana bace bazan taɓa Auren mijinki ba, ki daina wannan tunanin cikin ranki.”

Murmushin ƙarfin Hali Hasina tayi tace.

” Nasan Abunda nake faɗa Indo, ba kuma gwadaki nake ba da gaske nake miki wannan maganar Tabbas MIJINA nake so ki Aura ba kuma haramun bane dan kin Auri mijina bamusha nono ɗaya ba bare kice akwai haramci a ciki MIJINA yana tsantsar sonki soyayyarki har nema take ta masa illa Soyayyar ki tana neman ta wargaza min farin cikin gidana dan Allah ki taimakeni ki Auri MIJINA ko zamu samu cikakken farin ciki a cikin gidanmu domin kece kaɗai wacce zata dawo min da farin cikin MIJINA nikam na kasa amma ina da tabbacin ke zaki iya.”

Hawaye ne ya gangaro a Idon Indo tace.

” Bazan iya ba! Bazan iya ba Aunty Hasina bazan iya auran mijinki ke Tamkar ƴar uwata ce wacce muka fito ciki ɗaya keda ya Habeeb kun jawoni jikinku a lokacin da nake buƙatar ƴan uwan da zasu rarrasheni kun ɗauki damuwata damuwarku kun min komai cikin Rayuwata Aunty Hasina ki faɗa min taya zan iya Auren mijinki dan Allah ki daina wannan maganar.”

” Murmushi Hasina tayi itama idanunta na ƙoƙarin zubar da hawaye, tayi saurin mayar dasu saboda kar Indo taga rauni a tattare da ita tace.

” Hakanne yasa nake son ki sakawa Habeeb da alkairin da ya miki ta hanyar Auren sa, karki damu dani har abada kina matsayin ƙanwata dan kin Auri MIJINA matsayin da kike dashi a zuciyata bazai taɓa goguwa ba, sai dai ma ya ƙara ninkuwa MIJINA yana sonki fiye da yadda yake sona kullum da tunaninki yake kwana yake tashi yana mungun jin dadi idan yaji ana hirarki ya kan ji farin ciki a duk sanda yake kallon Soyayyarki har kuka ta sashi” tsayawa da maganar Hasina tare da ɗauko wayarta ta dannawa Indo recording d’in da tayi ɗazu sanda suka gama ji sannan ta cigaba da cewa ” Zaɓi ya rage gareki ki ceto rayuwar sa ko ki barsa cikin damuwar da komai zai iya faruwa dashi, sai dai ki sani muddun wani abu ya samu MIJINA a dalilin ki bazan taɓa yafe miki ba.”

Tashi Indo tayi cikin tashin hankali cikin kuma tsawa da tsantsar tashin hankali take cewa.

” Wai me ake nema da rayuwata ne, ya kuke so nayi da rayuwata ne wai, kowa *SO SO!* Duk kanku kuka sani ke kince mijinki ya Mustafa yace kansa shima Barrister yace kansa ki faɗa min ta ina kuke so nasa kaina gabaki ɗaya kun sani a tsakiya.”

Murmushi Hasina tayi ta tashi tace.

” Kije kiyi tunani ki yankewa kanki Hukunci *WAYA KAMATA KI AURA A CIKIN SU* tana gama faɗa ta juya ta fice daga cikin bedroom ɗin………..

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻

 

 

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/11, 10:54 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

_____________________________________

*P*•••••••1️⃣5️⃣ ↗️ 1️⃣6️⃣

Sosai hankalin Indo ya tashi wunin Ranar haka ta yishi sukuku bata jin daɗin Zuciyarta ko kaɗan Ko bacci ba tayi wani ishashshe ba washe gari kuwa da safe ta sake shiga cikin wani sabon tashin hankali na tafiyar Sharifa Egypt sun rabu cikin kewar juna domin ita kanta Indo tasan tayi babban rashi na Sharifa cikin gidan mussaman idan ta tuno cewa daga ita sai Momy zasu zauna a cikin gidan Zuciyarta na mungun tsinkewa idan ta tuno da hakan, a ranar da sharifa ta tafi itama Indo bata wuni cikin gidan ba Daddy ta tambaya taje gidan su zarah sun tattauna sosai da Zarah game da Habeeb inda Zarah tayi murmurshin tana tuna mata maganar data gaya mata cewa Habeeb yana sonta haka zalika ta bata shawara cewa Habeeb shiya dace ta Aura ita dai bata nunawa Zarah cewa ta amince da maganar ta ba har suka rabu Indo ta koma gida.

Lokaci na tafiya yayin da satittika suke shuɗewa, Indo dai ta fara zuwa makaranta cikin Nasara yayin da Itama Zarah tayi joining ɗin school ɗin sosai alaƙa mai ƙarfi ta daɗa ƙarfi tsakanin Indo da Zarah ƙullu haka kuma Habeeb tana sauraronsa kamar yadda suke a da amma ko a fuska bata nuna masa cewar tasan yana sonta ba, haka har yau bata bawa Hasina Amsa ba asali ma bata yarda sun haɗu ba kusan zance wasan ɓuya suke haka kuma Barrister UMAR ta sallamesa ta hanyar sanar dashi gaskiyar zuciyarta a cewar ta bata da ra’ayin Soyayya yanzu cikin aminci kuwa Barrister UMAR ya haƙura Mustafa ne dai kullum suke cikin dabi haɗuwa goma faɗa ashirin Momy kuwa kullum cikin ƙara tsanar Indo take gashi yanzu tsabar tsana harta dawo tana mata mugunta duk wani aikin daya shafi gidan itace take yinsa karatunta kuwa sosai take yi kuma tana ganewa sosai sai dai duk muguntar da Momy take yiwa Indo bata hana ta zuwa makaranta ko aiki take mata tana ganin time ɗin makarantar ta yayi zata karɓi aikin ta, a haka rayuwar take tafiya Daddy kuwa a wannan satin yaje shi DASINA ya sanar da Momy cewa akwai abu mai mahimmanci da zai kasa ta masa addu’a Allah yasa ya samu Abunda yaje nema Daddy da yaje da niyar ya dawo a ranar haka bai samu ba saida yayi kwana ɗaya washe gari ya juyo ya dawo cikin dutse.

💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

Yau tun safe ta tashi da tashin zuciya ga wani jiri da yake damunta ga kuma kasala daya sata a gaba, tashi tayi ta ruga da gudu banɗaki sai amai take ta famar kwararawa, Mustafa dake Zaune ne ya tashi yabi bayanta domin kuwa tun jiya yake lura da yanayin ta, a bakin tollet ɗin ya tsaya yana kare mata kallo ta juyo da niyar fitowa ne tayi taga-taga zata faɗi saurin tare ta yayi ta faɗo jikinsa har bakin bed ɗinta ya ajiyeta tare da cewa.

” Wai me yake damunki ne kam tun jiya ina lura da yanayin ki.?”

” Nima bansan me yake damuna ba, sai dai ina yawan jin murɗa ga jiri da yake damuna sai kuma yanzu da nayi amai.”

Taɓe bakin sa yayi yace.

” Okay Allah ya baki lafiya”

sannan ya juya ya fice, yana fita RAUDA ta fashe da kukan baƙin ciki, ganin mijinta bai damu da lafiyar ta ba sosai da tasha kukanta tayi shuru dan kanta.

Yana zaune yaji ƙiran Daddy ɗagawa yayi bayan sun gaisa Daddy yace yazo ya samesa yanzu a gida, amsawa yayi da to sannan ya ƙatse wayar yana rufe system ɗinsa ya fice daga part ɗin nasa ya nufi kiran Daddy.

Zaune Indo take a bedroom ɗinsu ta gama aiki ta gaji ta ɗauko assignment ɗinta tana dubawa Ishaq ya shigo bedroom ɗin kusa da ita ya zauna yace.

” Aunty Indo kina assignment ne.?”

Kallon sa tayi tana murmurshi tace.

” Eh assignment nake Ishaq har kayi wankan ne, ina Sharif.?”

” Eh nayi Aunty, Sharif kuma yana falon ƙasa, Daddy ne yace wai kije yana ƙasa.”

Ajiye LITTAFIN Indo tayi tace.

” Okay tashi muje to, idan na dawo na ƙarasa assignment ɗin.”

Tashi Ishaq yayi suka sauƙa tare a gefe Indo ta zauna tare da cewa gani Daddy, tana hararar Mustafa dake zaune gefe murmurshi kawai yayi tare da kanne mata Ido Habeeb Kuma yana kusa da Momy suma Daddy ne yayi kiran su.

Duban Habeeb tayi tace.

” Ya Habeeb wai ina ka shige ne tun safe ban ganka ba.”

Hararar ta Habeeb yayi tare da cewa.

” Da baki ganni ba kuma ai baki nemeni ba.”

Dariya tayi sosai tace.

” Kai ya Habeeb meye abun jin haushi kawai fa cewa nayi bari na gani zuwa dare idan baka zo ba saina kira ka, sai kuma gashi yanzu kazo.”

Murmushi Habeeb yayi yace.

” Kaji Sarkin wayo uwar iya kare kai kekam da low kika karanta jama’a sun banu.”

” Dariya Dukan su sukayi sannan Daddy Yayi gyaran murya ya fara magana yana maida hankalin sa ga Indo yace.

” *A’ISHA INDO* Tambayar ki nake son nayi shin kina da wanda kika ajiye a matsayin miji ma’ana wanda zaki Aura, lokaci yayi daya kamata ace kin fitar da mijin Aure mahaifin ki yamin magana akan hakan kuma kinsan al’adar garin namu na Dasina 12 to 13 years ake yiwa yara Aure kinga ke kuma yanzu kina da 18 years ya kamata ki sanar dani idan da wanda kika fitar.?”

Shuru Indo tayi kanta na ƙasa ta rasa me zata cewa Daddy domin dai ita yanzu babu wanda zata ce ta tsayar a matsayin mijin da zata Aura, Habeeb kuwa Shida Mustafa gabaki ɗayan su zuba mata Ido sukayi suji me zata ce, dukansu zuciyoyin su dukun uku-uku suke yi kowa yana tsoron yaji wa Indo zata fitar a matsayin miji, Daddy Kara maimaita mata Tambayar yayi a karo na biyu ganin tayi shiru ta kasa cewa komai, a sannan Indo ta kaɗawa Daddy kai alamun babu wanda ta tsayar, hamdala Habeeb yayi cikin ransa yana kuma sawa a zuciyarsa a yau zai sanar da Indo Soyayyar da yake mata domin ya gaji da ajiyar Cuta cikin zuciyarsa dole ya sanar da ita ko zai samu sauƙin nauyin da ƙirjinsa yake masa, Mustafa kuwa Sarkin rashin haƙuri har zaiyi magana Daddy ya ɗaga masa hanu duban Momy yayi sannan ya kalli Indo yace.

” Alhamdulillah! Daman na tambaye kine domin na baki damar ki *A’isha* kiyi hkr da hukuncin dana yanke akanki koda bai miki Daddy, Aisha akwai wasiyyar da *INNA* ta bar mana daf da zata rasu wannan wasiyyar nake son cika mata shi yanzu, Inna ta bar wasiyya cewa kar wani daban yazo ya Aure ki idan ba tsakanin Mustafa ko Habeeb ba, hakanne ya sani nayi dogon nazari tare da fahimtar ku sai nake ganin kamar akwai alaƙar Soyayya tsakanin ki da Mustafa shiyasa na ɗauki ƙafata da kaina naje DASINA wajen magabatan ki da kuma nawa iyayen na sanar da mahaifinki cewar na haɗaki Aure da Mustafa mun tattauna sosai da mahaifinki dare da ƴan uwa kuma alhamdulillah! Kowa yayi na’am da wannan haɗin a taƙaice dai ban bar DASINA ba har saida aka saka shartin aurenki da Mustafa Wata biyu kacal aka saka, ban sanar da kowa wannan maganar ba har mahaifiyar ku gata nan sai yanzu, na kuma gama haɗa kayan Auren ku yana kasuwa jibi za’a kawosa, Allah yasa ban muku katsalandan cikin rayuwarku ba.”

Wo ho ho kuzo kuji daɗi wajen Mustafa ji yake tamkar Daddy ya masa bushara da gidan aljanna wani irin farin ciki yake ji cikin ransa ganin ya samu Abunda yake so cikin sauƙi, Habeeb kuwa wani irin bugawa Zuciyar sa tayi zogi take mata ta toshe cike da tarin baƙin ciki, jin maganganun Daddy yake tamkar sauƙar aradu a kansa wai har anyi baiko tsakanin Mustafa da Indo, dafe ƙirjinsa yayi yana jin wani mungun baƙin ciki duk abunda Habeeb yake Indo tana ganinsa ta ƙasan ido ta kuma tausaya masa ainun Tabbas idan akwai wanda ya dace ta Aura to Habeeb ne, a yanzu ta fahimci halin da yake Tabbas zata faranta masa kamar yadda ya faranta mata bata gama tunanin nata ba taji sauƙar muryar Momy cikin kunnuwan ta tana cewa.

” What! Alhaji kasan me kake faɗa kuwa aure tsakanin ɗana da wannan abar, Allah ya sawwaƙa, Abunda bazai taɓa yiwuwa ba kenan, tun wuri Alhaji kamar yadda kaje ka haɗa wannan maganar Auren to kaje ka sunce domin alaƙar da bazata taɓa ƙulluwa bane.”

Zabura Mustafa Yayi zaiyi Magana Daddy ya katsesa tare da ɗaga masa hanu duban su yayi yace duk su tashi su tafi saboda baya so yayi hayaniya da matarsa gaban ƴaƴan sa duk da basu gama maganar da suka fara ba, tashi Habeeb Yayi yana tangal-tangal ya fito bayan sa Mustafa ya biyo yana dariya tare da dafa kafaɗar sa yace.

” Alhamdulillah! Bros mafarkina zai cika zan mallaki shafukan Indo a matsayin matar da na daɗe ina mafarkin samu gaskiya yau DADDY ya faranta min raina ina cikin farin ciki yau.”

Murmushin mai ciwo Habeeb yayi cikin danne damuwarsa ya miƙawa Mustafa hanu yace.

” Congratulation Bros kayi dacen mata Allah ya sanya Alkairi.”

Murmushi mustafa yayi tsabar daɗin da yake ji yasa ya kasa gane halin damuwar da ɗan uwansa yake ciki amsa masa yayi da.

” Ameeen bros yau zan wuni cikin farin ciki.”

Murmushin ƙarfin hali kawai Habeeb yake har suka rabu da Mustafa kowa yayi part ɗinsa, Habeeb zama kawai yayi a falo ya dafe ƙirjin sa yau tsabar baƙin ciki yasashi kukan ma ya kasa, a jiyar ZUCIYA kawai yake shi kaɗai yasan Abunda yake damunsa.

Can kuwa Daddy duban Momy yayi yace.

” A’ishatu ki fita a idona na rufe, ina sanar dake cewa idan kika kuskura kika kawo min matsala cikin wannan lamarin to Tabbas kisa a ranki cewa zamu samu mummunan saɓani, ranki zaiyi mungun ɓaci kina ji ko.”

” Ina ji Alhaji sai dai ka sani bazan taɓa lamunta da wannan haɗin ba, bazan taɓa yadda ɗana ya auri wannan fitsararriyar YARINYAR ba wlh komai zai faru sai dai ya faru.”

Tana gama faɗin haka ta juya ta haura sama kaɗa kansa Daddy Yayi yana yiwa Momy kallon rashin Hankali sannan shima ya wuce nasa bedroom ɗin.

INDO kuwa tun shigar ta bedroom ɗin nasu ta kasa sukuni tausayin Habeeb kawai take ji cikin zuciyarta, Tabbas ya mata Alkairi, to meyasa ita bazata saka masa da Alkairi ba, idan har ta bar Habeeb a cikin wannan halin Tabbas ta cika cikakkiyar butulu, idan da akwai wanda ya dace ta Aura to Habeeb ne, Mustafa sam bai dace da rayuwar ta mutumin daya dinga wulaƙanta rayuwarta mutumin daya ƙyamace ta, mutumin da kullum yake ciki hantarar mutumin da baisan darajata ba to akan meyasa zata auresa duk abunda ya mata yaci banza kenan, shi kuma ya Habeeb ya yiwa rayuwar ta Hallaci kuma har gobe a cikin mata Hallaci yake dole ma ta Saka masa, Indo takai kusan 11pm tana tunani ta kasa bacci kamar yadda haka yake shima Habeeb a garesa ya kasa sukuni muƙurƙusu kawai yake yau da wuri ya rufe bedroom ɗinsa SABODA baya so Hasina ta shigo ta samesa a Halin da yake ciki, yasan hankalin ta zai tashi sosai ita Hasina daman ta fuskanci halin da yake ciki shiyasa ma bata tunkaro bedroom ɗinsa ba, Habeeb yana cikin wannan halin ne yaji wayar sa tana ringine dubansa yakai ga screen ɗin wayar sunan Indo ya Baiyana tashi yayi tare da ɗaga wayar ba tare da Sallama ba yace.

” Meya hanaki bacci a wannan lokacin.?”

Share hawayen ta Indo tayi tace.

” Abunda ya hanaka bacci nima shiya hanani bacci, ka fito ka sameni ina tsakar gidan ku.”

Cikin mamaki Habeeb yace.

” What! Tsakar gidan mu kuma taya kika fito har kika shigo nan.”

” Yanzu ba lokacin Tambaya bane ka fito kawai ina jiran ka.”

Katse wayar yayi ya sauƙo daga bed d’in sannan ya nufo waje

A tsaye ya ganta tana jingine jikin part ɗin nasa tsayuwa yayi yace.

” Meya fito dake cikin wannan daren?”

Kallon sa tayi Ido cikin ido sannan ta fara magana cikin raunin murya.

” Ya mutuwa zanyi zan mutu ya Habeeb.”

Cikin tashin hankali ya dubeta yace.

” Wacce Irin magana kike wannan waya ce miki zaki mutu.?”

” Ya Habeeb kasani cewa muddun ka bari jibi aka kawo kayan aurena da ya Mustafa to ka sani mutuwata ce aka kawo domin a ranar zan haɗiyi zuciya na mutu.”

Murmushin baƙin ciki Habeeb yayi yace.

” Babu Abunda zai kasheki karki manta da mustafan ki kika samu to me zai kasheki bayan kin samu burin ki na shekara da shekaru.”

” Bana son ya mustafa kai nake ya Habeeb kaine zaɓina kuma na tabbata kaima kana sona ya Habeeb kaje ka ware Aure tsakanina da ya Mustafa ni kaine zaɓina.”

Murmushin rainin hankali Habeeb yake yiwa Indo kafin yace.

” Baki taɓa ji daga bakina nace ina sonki ba, dan haka kije ki riƙe zabin iyayen ki.”

Yana gama faɗin haka ya juya zai bar wajen sai yaji muryar ta tana cewa.

” Ranar Litinin itace ranar da za’a sallaci gawata domin itace ranar mutuwata Ranar da za’a kawo min bakaƙen akwati a matsayin na aure na, ka tanadi likkafani da igiya domin kaine nake son ka kaine makwancina.”

A firgice ya juyo idanunsa sun sauya kala cikin firgici yake cewa.

” Bazaki taɓa mutuwa ki barni ba, ba gawa za’a sallata ba gawawwaki za’a sallata domin bazaki ke kaɗai ba sai dai mu mutu tare, ki sani duk abunda nima ya sameni idan Gurguwa kika zama to ki sani nima zan sa adda na sare ƙafafuna duka mu zauna idan kuwa tsautsayi ne afka idanunki kika makance to ki sani ba ɗan jagora zan zame miki ba, zan nemi kara ne na tsokane nawa idanun muyi dai-dai ki daina ambaton mutuwa domin kuwa kina ɗaga min hankali idan kina ambaton sa.”

Murmushi Indo tayi hawaye na gudu a idanunta tace.

” Idan har baka son ganin mutuwa ta to ina so a wayewar safiya kaje ka sanar da Daddy muna son juna idan ya kirani zan tabbatar masa da hakan.”

______________________________________

Tirƙashi yau ake yinta ko ya waɗannan ƴan uwa zasu kasance wai me yake shirin faruwa ne tsakanin wannan family?

Ku biyoni domin warware muku.😄

 

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/12, 11:57 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

________________________________________

*P*•••••1️⃣7️⃣ ↗️ 1️⃣8️⃣

” Da wani Ido kike so na kalli ɗan uwana, bana son ganinsa cikin damuwa, gara kawai ni ki barni cikin damuwata bana son abunda zaisa ya ji haushi na.”

” TABBAS ya Habeeb baka ƙaunar Rayuwata na tabbata da kana ƙaunar Rayuwata da zaka ceci rayuwata, na gode amma ka sani muddun baka sanar da Daddy Soyayyar mu ba ka sani babu makawa sai na mutu idan kuma na mutu sai kai ka rayu da ɗan uwanna ka kuma kaine sanadi na.”

Tana gama faɗin haka ta juya a guje tabar wajen a hankali ta bugawa mai gadi get buɗewa Yayi yana cewa.

” Hajiya ai ɗazun na gaji da jiran kine shiyasa na taho Saboda kar wani abu ya faru kiyi sauri ki shige a hankali kar wani ya ganki.”

Godiya Indo ta yiwa mai gadi sanna ta wuce a hankali harta shiga ɗakin sannan ta rufe a hankali tasa key still a hankali ta haura sama ta shige bedroom ɗinta, faɗawa tayi saman bed ta saki kuka mai cin rai tana cewa.

” Ina SONKA ya Mustafa Tabbas Soyayyar ka a jini na yake sai dai ka wulaƙanta rayuwata ka ƙyamaci ni ka tsangwame ni baka taɓa nuna min ƙauna ko kulawa ba a sanda nake gigin sonka duk da a lokacin ban gama sanin meye Rayuwa ba, sai dai nasan zafin Soyayyar ka duk da ƙanƙantar shekaru na, sai yanzu dana zama mutum zaka ce kai lallai kana sona, ya Mustafa ina sonka amma dole zan danne Soyayyar ka zanyi ƙoƙarin ganin na cireka a rayuwata, domin kuwa ya Habeeb shine wanda ya dace da rayuwata ina da tabbacin zan samu ingantacciyar rayuwa a wajen sa Tabbas zai kula dani zai riƙeni bisa Amana, Ya Habeeb kaine wanda zan aura insha Allah zan soka koda a gidan kane Tabbas kaine ka dace da na bawa soyayyata.”

Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka harda majina sam bata saka Abunda Momy tayi ba a cikin ranta domin kuwa idan da sabo ta saba da tsanar da Momy take mata dan haka ba tayi mamakin Abunda Momy tayi ba yau.

Habeeb kuwa komawa yayi ya zauna tare da zuba tagumi yana nazarin maganganun Indo hankalin sa yayi mungun tashi da maganganun ta domin kuwa yana jin tsoron furucin ta hanunsa ya ɗaga sama sannan yace.

” Ya Allah gani gareka ya Allah ka zaɓa min abunda yafi Alkairi a rayuwata, idan har akwai Alkairi tsakanina da Indo Allah ka bani ƙwarin gwiwwar tunkarar Daddy, idan kuma babu Alkairi tsakanin mu Allah ka cire min Soyayyar ta cikin Raina.”

Kwantawa yayi tare da yin shiru a haka bacci ɓarawo ya sacesa cike da tarin mafarkai ya kwana.

Mustafa kuwa yau cikin HAPPY yake ko masifar da yake yiwa RAUDA yau bai mata ba duk da itama fama take da kanta wani sa’in sai ta wuni a ɗaki bata fito ba gobe kam tayi niyar zuwa asibiti shiyasa tana jin shigowar sa ta fito falon sannu da dawowa ta masa bisa mamakinta sai taji ya amsa cikin sakin fuska, sanar dashi tayi cewa tana son zuwa asibiti gobe DAKATAR da ita yayi yace bari ya kira likita yazo dubata babu wani ɓata lokaci kuma ya kira doctor Sadiq cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya iso ya dubata sosai inda ya bata har gwajin fitsari, bayan ya gama dube-duben sane ya tabbatar musu da cewa tana da shigar ciki har na tsawon wata ɗaya da sati biyu, daga Mustafa har RAUDA babu wanda baiyi farin ciki ba, mussaman Mustafa har kyauta ya yiwa doctor.

MOMY kwana tayi ba tayi bacci ba tsabar tashin Hankalin maganganun Daddy wai Jinin ta ne zai Auri Wannan fitinanniyar YARINYAR INDO ina bazai taɓa yiwuwa ba, dole na wargaza Auren nan ko ta Halin yaya ne, da wannan mungun ƙudirin Momy ta kwana.

Washe gari da safe Indo ce ta haɗa breakfast cikin sauri domin kuwa tana da lectures 11:00am bayan ta jera komai a daining ne ta haura sama tayi wanka 10:30 dai-dai ta gama shirinta sannan ta sauƙo ƙasa Momy da Daddy sai su Ishaq ta samu a daining har sun fara breakfast zama tayi tare da cewa.

” Good morning Daddy”

Murmushi Daddy Yayi yace.

” Morning my daughter da fatan kin tashi lfy.”

” Lfy lau Daddy” duban Momy tayi tace.

” Good morning Momy”

Inda Indo take Momy bata kalla ba bare tasa rai zata amsa mata, girgiza kansa kawai Daddy Yayi sannan yace.

” Allah ya sauwaƙa, Ci Abincin ƴata karkiyi let ɗin school.”

Cikin sanyin jiki Indo ta ɗebi abinci muryar Sharif taji yace.

” Good morning Aunty Indo.”

Murmushi Indo tayi domin kuwa Momy bata sonta amma ƴaƴan ta suna sonta dalilin daya sa take haɗiye duk wani Abunda Momy take mata.

” Morning Sharif, ba zaku school bane yau.”

” Eh Aunty bazamu ba sai ranar monday yau Friday.”

” To Allah ya kaimu.”

Shima Ishaq gaishe da ita yayi, bayan sun gama breakfast ne Indo ta tashi ta haura sama ɗauko bag ɗinta, tana haurawa su kuma Mustafa da Habeeb suna shigowa, gaishe da Daddy sukayi ya amsa cikin sakin fuska, Momy suka juyo suka gaisar amma Momy bata amsa gaisuwar Mustafa ba, ta Habeeb kawai ta amsa nanma fuskar ta a haɗe zama sukayi Habeeb da zuciyarsa ke dukan Uku Uku yana son sanar da Daddy kuma ya rasa ta inda zai fara maganganun Indo ne suke faɗo masa cikin zuciyarsa tiryan-tiryan hakanne ya basa ƙarfin gwiwwar cewa.

” Daddy ina da Magana ne, bansan kuma yaya zaka kalli maganar tawa ba.”

Maida hankalinsa Daddy Yayi ga Habeeb yace.

” Umhumm ina sauraronka sanar dani menene.?”

Kauda kansa gefe Habeeb yayi sannan yace.

” *DADDY AKWAI ALAƘAR SOYAYYA TSAKANINA DA INDO MUN JUMA MUNA SON JUNAN MU, KUSKUREN FAHIMTA KAYI INDO DA MUSTAFA SAM BABU WATA SOYAYYA TSAKANIN SU DADDY NINE WANDA YA DACE NA AURI INDO BA MUSTAFA BA.*”

Wani iri Mustafa yake jin maganganun Habeeb ji yake tamkar kunnen sa ƙarya yake masa, domin kuwa yasan ɗan uwansa bazai taɓa son abunda yasan yana so ba sai Gashi yanzu yana jin kunnen sa yana masa ƙarya, Momy kuwa cikin sauri ta ɗago idanunta tana bin Habeeb da wani mungun kallo wani irin tsanar Indo ne ya ƙara ɗarsuwa a zuciyar Momy lallai YARINYAR nan ta cika mayya tunda gashi ta lashe mata Zuciyar ƴaƴan ta duban Habeeb Mustafa yake cikin ƙaraji yayi kukan kura ya tsakumi wuyan HABEEB yace.

” Me kake cewa ka faɗa min me kake cewa! Kuna soyayya da SHATUU oh kace kuna cin amanata, kai kai kai 👉🏻 kaine zaka ci amanata Habeeb, ɗan uwana ne fa kai wanda muka kwanta ciki ɗaya da kai aka haife mu rana ɗaya muka sha nono tare muka tashi tare har girman mu bamu taɓa samun saɓani ba, bama son abunda zai taɓa ɗaya daga cikin mu, shine yau zaka ci amanata na yadda da kai ban kuma taɓa tunanin cewa zaka taɓa yunƙurin rabani da farin ciki na ba sai gashi ka ɗauko hanya idan wasa kake Habeeb ka daina domin bamu saba Irin wannan wasan da kai ba kaji ɗan uwana.” Ya ƙarasa maganar yana sakin wuyan Habeeb tare da ja da baya yana huci.

Sunkuyar da kansa Habeeb yayi ya kasa haɗa Ido da Mustafa kafin ya fara cewa.

” Banci amanar kaba Ɗan uwana, ka sani babu wasa a cikin soyayya duk maganar da nake faɗa gaskiya ne kuma har zuciyata nake faɗa maka shi, nayi duk yanda zanyi dan ganin na cireta a cikin raina amma na kasa sonta har barazana yake min da rayuwata, karka ga laifi na ɗan uwana domin kuwa shi *SO BAI SAN JINI BA* idan ya tashi shiga zuciya kawai yake ba tare da tunani ko lissafi ba, da so yana da lissafi da bai shiga zuciyar ɗaya daga cikin mu ba kamata yayi kawai ya tsaya a zuciyar mutum ɗaya Ni ko Kai amma tsabar rashin adalci Irin na SO shine ya shiga zuciyoyin mu duka biyu, *SO BASHI DA HANKALI ƊAN UWANA* ka daina ganin laifi na kaida kanka ka nuna cewa baka ƙaunar Indo kasha faɗa min da bakin ka, hakanne yasa nayi sakacin barin Soyayyar ta ta shiga cikin zuciyata komai ya faru laifin kane da tun farko ka amshi Soyayyar ta kamar yadda ta nuna maka da bazan taɓa yadda sonta ya shiga zuciyata ba, bare har yamin mungun kamu, kace min kana sonta tun tana DASINA idan har da gaske ka sonta a wannan lokacin to meyasa ka ƙita kake ƙyamar ta meyasa ka kasa kula da lamuranta meyasa kake zaginta a duk sanda kuka haɗu hakan duk yana cikin SOYAYYA ne? Ka bani amsar tambayata .”

Ja da baya Mustafa yake yana nuna Habeeb da hanu yana cewa.

” Kana jinshi ko Daddy kana ji fa daddy wai SHATUU yake so numfashina yake so Daddy kasheni yake neman yi rayuwata zai karɓa Daddy, anya kuwa shi ɗan uwana ne Daddy, daddy anya ɗan uwana Habeeb ne dana sani Daddy ƙarya yake baya soyayya da SHATUU nasan ni kaɗai take so nine kawai a cikin ranta kana ji Daddy har wani banzar tambaya yake min .”

MOMY da ta gama ƙula ne ta tashi cikin fusata ta ɗauke Habeeb da tagwayen mari, sannan ta taka har gaban Mustafa shima ta ɗaukesa da mari cikin ƙaraji take cewa.

” Meye a jikinta har kuke neman raba alaƙar dake tsakanin ku, me zakuyi da ita wannan tantiriyar data gagari iyayenta sanda suka haɗota damu me zakuyi da wannan taburmar ƙayar, to bari kuji idan nine uwar ku dana sunkuya nayi naƙudar ku na rabaku da wannan YARINYAR babu ku babu ita har abada domin kuwa bazan taɓa yadda ɗaya daga……”

Tsawa Daddy ya daka mata yace.

” Ya isheki haka A’ISHA ki rufe min baki karna ƙara jin maganar ki anan wai meyasa ne kike haɗa hankalinki da tuwo kike cinyewa ne, ki kama girman ki tun kafin ƴaƴan ki su daina ganin girman ki, ki kuma sassauta wannan munguwar ƙiyayyar da kike gwadawa yarinyar nan domin kuwa baki san gaba ya zata kasance ba wata ƙila ta amfane ki fiye da ƴaƴan ki da kika haifa ki sani cewa *ƳAƳA DA DUKIYA BA’A MUSU MUGUNTA* Saboda baka san wa zai taimake ka ba gaba, ki riƙe wannan a ƙwaƙwalwar ki ƙi kuma shiga hankalin ki.”

A fusace Momy tace.

” Babu wata ranar da wannan YARINYAR zata min yarinyar da bata yiwa iyayen ta rana ba wa zata yiwa Rana, nifa Alhaji ina kan bakata Wlh babu ƴaƴa na babu wannan YARINYAR.”

Tana gama faɗin haka ta ɗauki jakarta da hijab ɗin ta dama unguwa zata ta fice tana jefa yarannata mungun kallo, Daddy maida hankalin sa yayi garesu yace.

” Kowa ya shige ya tafi wajen aikinsa kun kusa kuyi let zan neme ku daga baya, kuma ban yafe ba idan kuka yi koda cacar baki ne a hanya kuje Allah ya muku albarka.”

A fusace Mustafa ya juya ya fice daga falon Habeeb cikin sanyin jiki ya fita Indo dake tsaye a step ɗin falon ne ta sauƙe ajiyar Zuciya tare da ficewa tana kiran Zarah a waya, koda ta fito dukkan su sunja motar su sun bar gidan itama motar da driver yake jiranta ta hau suka kama hanyar makaranta.

MOMY DARECT gidan su RAUDA ta nufa wajen Mamy domin ta taya ta neman solution hon tayi mai gadi ya wangale mata get ɗin ta shige.

_______________________________________

Kuyi hkr da wannan yau ina cikin busy ne🙏🏻

 

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/13, 8:29 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

_______________________________________

*P*•••••••1️⃣9️⃣ ↗️ 2️⃣0️⃣

Parking tayi sannan ta shige falon Mamy darect tana ɗauke da Sallama a bakin ta, tana zaune ta harɗe kafafunta ɗaya kan ɗaya tana danna waya, taji sallamar Momy tana dariya ta tashi tace.

“Ameeen Wa’alaikimussalam Hajiya A’isha yau kene tafe gidan nawa lale marhaba.”

Murmushi Momy tayi tana zama bisa kujera tace.

” Nine tafe Hajiya Turai naga kin yafe gidana ne tunda muka Auri ƴarki ko gidan namu kin daina kallo bari muyi tunanin ganinki.”

Dariya Mamy tayi tace.

” Kema dai kinsan halina ba son yawo gareni ba, jiya muke magana da Hajiya Hindatu akan cewa zamu je muga ɗakin RAUDA, ta kiran ma ta sanar dani bata jin daɗin jikinta ɗazun nan wai mun samu ɗan jikalle.”

Dariya Momy tayi cikin farin ciki take cewa.

” Masha Allah! Kinga nida nake tare dasu ma bani da labari to Allah ya raba Lafiya shiyasa kwana biyu bata shigo min niko Hankali na baya kwance shiyasa ban leƙata ba.”

Murmushi Mamy tayi tana ƙoƙarin tashi tare da cewa Momy.

” Bari naje na kawo miki ko ruwa ne kisha sai mu zauna musha fira kinga gashi an juma ba’a haɗu ba.”

Dakatar da ita Momy tayi tare da cewa.

” Kibar ruwan nan yanzu muka gama breakfast so bana jin ƙishirwa, kinga nifa matsalace ta kawo ni gidan ki nazo wajen kine nasan ba’a rasa sulution a wajen ki.”

Komawa Mamy tayi ta zauna cikin mamaki take cewa.

” Matsala kuma Hajiya A’isha sanar dani mu samo mafita yanzun nan.?”

Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe ta dubi Mamy tace.

” Eh Matsala Hajiya Turai babbar matsala ma kuwa ina cikin tashin hankali sosai Wlh.”

” Kinga Hajiya A’isha kin kulleni a duhu fitar dani haske meke faruwa sanar dani.?”

” Hajiya Turai kin dai san akwai yarinyar da Alhaji ya ɗauko daga ƙauyen su ko? wannan fitinanniyar YARINYAR dana taɓa baki labarin ta, koda yake kin santa ma tunda kinsha zuwa ki sameta a cikin gida na.”

” Eh na ganeta wani abunne ya faru da ita.?”

” Ai Hajiya Turai da wani abu zai sameta sai na fi kowa farin ciki musamman ma ace min ta mutu da saina zuba ruwa a ƙasa nasha, bana ƙaunarta ko kaɗan” labarin Abunda yake faruwa Momy ta bawa Hajiya Turai bata ɓoye mata komai ba har zuwa yau da Habeeb shima ya furta yana son Indo.

Shuru Mamy tayi tana sauraron Momy harta dasa aya kafin tace.

” Cap BABBAR MAGANA, yanzu ke Hajiya A’isha me kika yanke kin yarda ne? idan har ke kin yarda to ni bazan yadda a yiwa ƴata kishiya ba, ban zauna da kishiya ba kinga kuma ƴata bazata zauna da kishiya ba, sanar dani me kika yanke.?”

” Hmm Yanzu ke Hajiya Turai idan aka ce miki na yadda da wannan Auren sai ki yadda, kema dai kinsan na tsani YARINYAR nan to kuma taya kike tunanin zan yadda da wannan haɗin, nifa Abunda ya kawo ni gidan ki neman mafita ne, kinga Alhaji yana son Auren nan sosai har takai yana min barazana da kalmar saki nema fa take ta koreni daga gidan uban ƴaƴana kuma wlh bata isa ba.”

Wani malalacin murmurshi Mamy tayi na mugunta tana duban Momy tace.

” Kwantar da hankalin ki ƙawata kamar kin kashe ɗan Mutum tunda kika kawo wannan matsalar wajena an gama da ita, kin gane, ki bari Ranar Lahadi, misalin ƙarfe 12:00am na rana kizo ina da inda zamuje a yi maganin wannan matsalar karki saka damuwa cikin ranki kar kuma ki sake yin faɗa na faɗa da mijinki kina shurun ki su da kansu zasu wargaza Maganar da kansu ta hanyar sa musu tsanar yarinyar a zuciyarsu badai Malam yana raye ba to kwantar da hankalin ki insha Allah komai yazo ƙarshe kamar anyi ruwa an ɗauke.”

Dariya dukansu suka saka Momy ne tace.

” Shiyasa nake sonki ƙawata akwai ki da neman mafita, badai a kawo matsala wajen kiba sai kinyi maganinta, kice na kusa yarda ƙwallon mangoro na huta da ƙuda kinsan Allah yarinyar nan ta shige min hanci da ƙudunduno neman yadda zanyi na fyace ta nake yi ko zan samu sa’ida.”

Dariya sosai Mamy take ta cewa Momy

” Ai kawai ki kwantar da hankalin ki ƙawata kin kusa fyaceta ki huta badai kinzo wajen Turai ba ai an gama kawai.”

Dariya sukayi duka sun juma suna hira kafin Momy tayiwa Mamy sallama da alƙawarin cewa zata zo ranar Lahadi har parking space ta rakata sanda taga fitarta sannan ta koma falon nata, tana shiga ta sheƙe da dariya cikin salon mugunta take cewa.

” Alhamdulillah! Lokaci yayi da zan tatsi kuɗin uban mijina daga gareki Hajiya A’isha na daɗe ina jin baƙin cikin kuɗin da mijinki yafi nawa mijin gashi dai a ƙarƙashin inuwar uban mijina kuka tashi, Hajiya A’isha lokaci yayi da kuɗin ki zaiyi kuka zan tatseki kamar yadda makiyayi yake tatsar nonon saniya” waya ta ɗaga ta kira Malamin ta zance ko bokan ta, ringine ɗaya ya ɗaga.

” Cau cau dai Malam, mai aiki da aljanu malamin daya gagari manya bare kuma yara, ranka ya daɗe malam mai aiki da baƙin aljani.”

Wani irin dariya tsinannen bokan yayi marar daɗin sauraro kafin yace.

” Faɗi menene damuwar ki, marar tsoron Allah, wacce kika kauce daga hanya maza yimin ƙarin bayani.”

Shiga taitayinta Mamy tayi sannan tace.

Bayanin Momy ta masa sannan ta ƙarasa maganar da cewa.

” Mlm so nake muyi raba dai-dai da kuɗin da zata kawo ma’ana ka ninka mata kuɗi domin kuwa mijinta mai kuɗin gaske ne, sannan mlm bana so ka bata maganin da zaiyi amfani da wuri Saboda mu samu mu tatsi rabon mu, karka damu da ƴata da take auren ɗanta wannan ba ƴata bace ƴar tsintuwa ce a gidan marayu muka karɓo ta sanda bamu sami haihuwa ba, shiyasa kaga batayi halina ba, nima kuma ban damu ba ita da wahalar ta, nidai bana son ka bata sahihin magani gara muta wala gigi da hankalin ta, ka samu na samu.”

Dariya ya sheƙe dashi yace.

” Baki da Matsala aike customer ce yanda kika ce haka za’ayi Lallai Turai kin cika baƙar munguwa.”

Dariya ta sheƙe dashi tare da yi masa Godiya sannan ta kashe wayar.

Mustafa kuwa ikon Allah ne kawai ya isar dashi court ɗin nasu yau bai saurari kowa ba kamar yacce ya saba, office ɗinsa ya shige darect ya dannawa office ɗin key zama yayi ya kifa kansa a table ɗin wasu hawaye ne suka zubo masa masu zafin gaske shi kaɗai yasan abinda yake ji a cikin zuciyarsa wai yau shine yake hawaye akan mace RAUDA ce ta faɗo masa cikin ransa a fili ya furta cewa.

” Allah sarki ashe daman haka kike jin zafi cikin zuciryaki RAUDA, ashe daman haka zafin Soyayya take ban taɓa jin zafin ta ba sai yau, Tabbas na zalince ki sai yau nasan da haka dana ɗanɗani makamancin ɗacin da kikaji a cikin zuciyarki zan gyara zamantakewa ta dake insha Allah, meyasa zaka min haka Habeeb kafi kowa sanin nine a zuciyar SHATUU to meyasa kake ƙoƙarin shiga tsakanin mu, laifin mena aikata maka haka kake son cutar da rayuwata karka manta da kaifa ɗan uwana ne mafi soyuwa a gareni, karka cutar da rayuwata dan Allah na roƙeka.”

Kusan Hauka Mustafa Yayi a wunin wannan Ranar domin kuwa ya kasa sukuni maganganun kawai yake shi ɗaya wunin Ranar baiyi aikin komai ba.

Shi kuwa Habeeb tun shigar sa asibitin aiki kawai yake amma baida nutsuwa ko kaɗan ji yake tamkar bai kyautawa ɗan uwansa ba Tabbas yayi sake da har ya bari Soyayyar Indo ta shiga cikin zuciyarsa, bai taɓa tunanin Mustafa yana son Indo ba domin kuwa shiya nuna cewa baya sonta abaya ” ashe wai shi hakan sone a wajen sa, ada naso nunawa Mustafa kuskuren sa ta hanyar yiwa Indo Soyayyar ƙarya sai gashi kuma akasin haka ya faru nazo ina mata haƙiƙanin Soyayya, *SOYAYYAR GASKIYA* meke shirin faruwa tsakanina da ɗan uwana.?”

Ajiyar Zuciya ya sauƙe tare da zuba tagumi, sai kuma maganganun Momy suka faɗo masa a rai Zuciyarsa ce ta cinke cikin sauri ya ambaci sunan UBANGIJIN sa tare da tashi yayi office ɗin doctor Sadiq waiko tunanin zai ragu masa.

💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢

” Lectures ɗin yau gaskiya ban ganesa ba sosai.”

” Ƙawata ina kuwa zaki gane lectures ɗin yau bayan kin shigo school da tunani, nifa yau tunda muka shiga Class nake lura da ke sam hankalin ki baya kan lectures ɗin nan, kinfi bada hankalin ki zuwa ga tunani.”

Murmushi Indo tayi ta ɗaga kai ta kalli Zarah sannan tace.

Kedai Zarah bari kawai ina cikin tention Ina son Ya mustafa Zarah sai dai bazan iya Auren sa ba, na yanke shawarar Auren Ya Habeeb domin shine wanda ya dace da Rayuwata ina da tabbacin kuma zai koya min Soyayyar sa kamar yadda ya koya min shiɗin malami nane bazan taɓa manta alkairin sa gareni ba, Zarah kina ganin Abunda nayi kuwa nayi dai-dai.?”

Murmushi Zarah tayi tare da dafa kafaɗar Indo tace.

” Shawara mai kyau ƙawata, wannan shawara da kika yanke yayi dai-dai Tabbas kin cika ƴar halak da kika zaɓi Habeeb a matsayin wanda zakiyi Rayuwa dashi, nasan kina son ya mustafa Soyayya kuma ta gaskiya, sai sam bai dace da rayuwar kiba, kina da faɗa shikuma ya Mustafa yana da zafin zuciya kinga koda ace kin ɗaukesa bana tunanin zaman ku zaiyi daɗi domin kuwa biyu bata haɗuwa waje ɗaya dole ko wanne da lissafin sa, shi kuwa ya Habeeb mutum ne mai sauƙin kai zakiji daɗin zama dashi kuma ko ba komai shine wanda ya nuna miki Soyayyar gaskiya domin kuwa mutumin da bai taɓa kyamarka ba sanda kake cikin ƙazanta wannan shine masoyin gaskiya, ƙawata kiyi ƙoƙari kiga kin samu kin cire shi cikin zuciyarki ki Rungumi Ya Habeeb domin kuwa shine dai-dai ke.”

Murmushi Indo tayi tare da kaɗa kanta tace.

” Anya kuwa zan iya ciresa a raina cikin sauƙi kin fa Soyayyar yarinta bana ji zai fita cikin raina nan kusa sai dai kawai zan danne zuciyata dan ganin na bawa ya Habeeb duk wani farin cikin daya dace.”

Dubanta Zarah tayi tace.

” But amma ƙawata kina ga babu kuskure kuwa ga wanda kikeso kuma kice ga wanda zaki aura daban, a gani na cire Soyayyar Mustafa a ranki shine kawai mafita.”

Murmushi kawai Indo tayi tare da ɗagawa Zarah hanu tana cewa.

” times is off ya kamata mu shige Class kafin doctor Ahmad ya rigamu shiga.”

Kaɗa kanta kawai Zarah tayi sannan ta tashi suka shige Class.

Da Sallama Hasina ta shiga falon RAUDA tana kwance jikinta duk a mace tun safe take amai duk abunda taci baya zama a cikin ta, ƙarasawa kusa da ita HASINA tayi ta Zauna tace.

” Baki da lafiya ne na ganki haka kwance, tun jiya banji motsinki ba, shiyasa na leƙo naga lafiya.”

 

____________________________________

Gaskiya kuyi manage da wannan bana jin daɗi yau sorry for typing error🙏🏻 banyi editing ba.

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

 

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/15, 3:42 PM] Ummu Nasmah: *_KU FITO MASOYA NA DOMIN NUNA MIN KALAR SOYAYYAR DA KUKE MIN TA HANYAR SAYAN NOVEL ƊIN MU, KUNDAI SAN KALAR RUBUTU NA KUN KUMA YANAYIN LABARI NA DAN HAKA KU GARZAYO DOMIN SIYAN WANNAN NOVELS ƊIN_*

 

*_INA KUKE MASOYAN KAINUWA WRITER MAZA KU GARZAYO KU KWASHI GARABASA DOMIN KUWA TAFE TAKE DA SABBIN LITTATTAFAN TA WANDA ZAKU AMFANA DASU KUMA KU NISHAƊANTU DOMIN KUWA MUNYI LALUBE MUN ZAƘULO MUKU FASAHAN MARUBUTAN ZAMANI WANƊA SUKA ƘWARE WAJEN KAWO MUKU TSAFTACACCEN LABARI MAI SANYA ZUCIYA SANYI_*

*_ZAKAƘURAN MARUBUTAN DAZA SU FADAKAR DAKU ACIKIN WAƊAN LITTAFAN NASU SUN HAƊA DA_*

*AISHA ABULLAHI FULANI*

Wacce ta nishaɗantar daku a cikin littafinta mai taken *MA’AURATA*.

Yanzu ma a shirye take tsaf domin ganin ta faranta muku rai tafe take da sabon salon labarin ta mai taken.

*RAYUWAR MU*

 

*RASHEEDAT USMAN*
*(UMMU NASMAH)*

Wacce ta nishaɗantar daku a cikin wannan shahararren Novel ɗin nata wanda yazo muku a cikin fittatu 15 daga ƙungiyar kainuwa Wato.
*INDO A BIRNI*

Yanzu ma dai tafe take da Sabon salon labari mai Ruɗa Zuciyar mai karatu kun dai santa bata wasa wajen zaƙulo muku daddaɗan labari mai cike da darasin Rayuwa tare da nishaɗi to yanzu ma dai gata tafe da sabon book ɗinta mai taken.

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU*

*Haleematu Hassan Leemat*

Wacce ta ni shadantar daku acikin littafinta na ADALI’LIN DA NAMIJI

yanzu ma ta sake kawo muku wani sabon littafinta mesuna *LAIFIN WA?*
*(MAZAN KO MATAN)*

*FAUZIYA AUWALU ALIN BABA JINGAU*

*(YAR MUTAN JINGAU)*

Itace dai wannan shahararriyar marubuciyar da take nishaɗantar daku wacce ta jajurce wajen zaƙulo muku labari kan lamuran dake addabar mu cikin al’umma wacce ta kawo muku labarin.

*ABINDA KE FARUWA*

Yanzu mai dai tafe take da labarin da zai taɓa zuciyar mai karatu zai nishaɗantar daku ya kuma faɗakar daku mai taken.

*DAMUWA MUNGUN CIWO*

*NA’EEMA SULAIMAN*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wani ga nawa, ina kuke tarin masoya ku matso kusa ga dama ta samu a yau ma dai tafe nake da sabon salon labari wanda zai saku nishaɗi ku kasance cikin annashuwa nice dai wacce na nishaɗantar daku cikin book ɗina mai taken.

*ASHE ƳAR BABATA CE*

Nayi nitso nayi ninƙaya na zauna na baje kolin bajinta ta, na zaƙulo muku labarin da zakuji daɗin sa wanda zai faɗakar daku mai taken.

*SAI NA AURE TA*

*MARYAM UMAR*
*(MAMAN YUSUP)*

Ina kuke tarin masoya to ku matso kusa ku nuna mana tarin ƙaunar da kuke mana nice dai taku maman yusup wacce na nishaɗantar daku cikin book ɗina mai taken.

*MUTUM CE KUWA*

Yanzu ma dai gani tafe cikin sabon salon labari na sabon zubi sabon ɗauka mai taken.

*KYAUTAR ZUCIYA*

________________________________

Ina matuƙar baku haƙuri masoyana na tsaida posting ɗin *SO BAI SAN JINI BA* da nayi sakamokon abubuwa da suka min yawa.

Sai dai ina muku Albishir da cewa zan sake muku complete ɗin book ɗin gabaki ɗaya Ranar bikin ƙaramar Sallah ta uku a matsayin *HAPPY SALLAH* kumin UZIRI pls.🙏🏻

Sannan kuma ina muku Albishir da cewa zan fara sakin sabon Novel ɗina mai taken *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Wanda ina da tabbacin cewa salon labarin sa na daban ne ina kuma da tabbacin cewa sai yafi *INDO A BIRNI* haɗuwa ku sani cewa ba wani dalili yasa na saki *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* a matsayin na kuɗi ba sai Saboda kunsan sha’anin ƙarfe wata rana dole wayar ka zata buƙaci gyara ga kuma matsalar Siyan data da kuma na Battery nasan dai nafi ƙarfin wannan kuɗin a wajen ku, ku fito ku nuna min ƙauna ta hanyar ciyen littattafan mu.

Sai ku tuntuɓe mu ta numbobin wayar mu da suke sama domin sanin yanda zaku biya kuɗin

_Zaku sami waɗannan littatafan namu a cikin farashi mai rahusa, domin kuwa ƙungiyar bata tsawalla ba farashi ne mai sauƙin biya, ku fito masoyan mu ku nuna mana ƙauna ta hanyar sayen littatafan mu kan farashi 👇🏻

Duka guda bakwai ɗin zaku samesa ne akan farashi Naira 500 kacal👌🏻

Mai son shida kuma zai biya Naira 450.

Mai son guda biyar zai biya Naira 400.

Mai son guda huɗu zai biya Naira 450.

Mai son guda uku zai biya Naira 350.

Mai son guda biyu zai biya Naira 300.

Mai son guda ɗaya zai biya Naira 200.

Farashi ne mai sauƙi muka baku domin ƴan uwana ku sami damar biya kuma cikin nishaɗi.

Ku tuntuɓe mu ta waɗannan numbers domin sayan book ɗin mu.

*08147537180*
*09035027743*
*08106795647*
*08176841985*

Gareku ƴan Niger kuma fa baza’a barku a baya ba ku kwantar da hankalin ku domin ku sami damar siyan littatafan mu zaku iya tuntubar wannan NUMBER👇🏻

*+2278456476*

Muna muku barka da zuwa daga Shahararriyar ƙungiyar ku Wato KAINUWA WRITER’S ASSOCIATION✍🏻[4/15, 3:45 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

_____________________________________

*_KU FITO MASOYA NA DOMIN NUNA MIN KALAR SOYAYYAR DA KUKE MIN TA HANYAR SAYAN NOVEL ƊIN MU, KUNDAI SAN KALAR RUBUTU NA KUN KUMA YANAYIN LABARI NA DAN HAKA KU GARZAYO DOMIN SIYAN WANNAN NOVELS ƊIN_*

 

*_INA KUKE MASOYAN KAINUWA WRITER MAZA KU GARZAYO KU KWASHI GARABASA DOMIN KUWA TAFE TAKE DA SABBIN LITTATTAFAN TA WANDA ZAKU AMFANA DASU KUMA KU NISHAƊANTU DOMIN KUWA MUNYI LALUBE MUN ZAƘULO MUKU FASAHAN MARUBUTAN ZAMANI WANƊA SUKA ƘWARE WAJEN KAWO MUKU TSAFTACACCEN LABARI MAI SANYA ZUCIYA SANYI_*

*_ZAKAƘURAN MARUBUTAN DAZA SU FADAKAR DAKU ACIKIN WAƊAN LITTAFAN NASU SUN HAƊA DA_*

*AISHA ABULLAHI FULANI*

Wacce ta nishaɗantar daku a cikin littafinta mai taken *MA’AURATA*.

Yanzu ma a shirye take tsaf domin ganin ta faranta muku rai tafe take da sabon salon labarin ta mai taken.

*RAYUWAR MU*

 

*RASHEEDAT USMAN*
*(UMMU NASMAH)*

Wacce ta nishaɗantar daku a cikin wannan shahararren Novel ɗin nata wanda yazo muku a cikin fittatu 15 daga ƙungiyar kainuwa Wato.
*INDO A BIRNI*

Yanzu ma dai tafe take da Sabon salon labari mai Ruɗa Zuciyar mai karatu kun dai santa bata wasa wajen zaƙulo muku daddaɗan labari mai cike da darasin Rayuwa tare da nishaɗi to yanzu ma dai gata tafe da sabon book ɗinta mai taken.

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU*

*Haleematu Hassan Leemat*

Wacce ta ni shadantar daku acikin littafinta na ADALI’LIN DA NAMIJI

yanzu ma ta sake kawo muku wani sabon littafinta mesuna *LAIFIN WA?*
*(MAZAN KO MATAN)*

*FAUZIYA AUWALU ALIN BABA JINGAU*

*(YAR MUTAN JINGAU)*

Itace dai wannan shahararriyar marubuciyar da take nishaɗantar daku wacce ta jajurce wajen zaƙulo muku labari kan lamuran dake addabar mu cikin al’umma wacce ta kawo muku labarin.

*ABINDA KE FARUWA*

Yanzu mai dai tafe take da labarin da zai taɓa zuciyar mai karatu zai nishaɗantar daku ya kuma faɗakar daku mai taken.

*DAMUWA MUNGUN CIWO*

*NA’EEMA SULAIMAN*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wani ga nawa, ina kuke tarin masoya ku matso kusa ga dama ta samu a yau ma dai tafe nake da sabon salon labari wanda zai saku nishaɗi ku kasance cikin annashuwa nice dai wacce na nishaɗantar daku cikin book ɗina mai taken.

*ASHE ƳAR BABATA CE*

Nayi nitso nayi ninƙaya na zauna na baje kolin bajinta ta, na zaƙulo muku labarin da zakuji daɗin sa wanda zai faɗakar daku mai taken.

*SAI NA AURE TA*

*MARYAM UMAR*
*(MAMAN YUSUP)*

Ina kuke tarin masoya to ku matso kusa ku nuna mana tarin ƙaunar da kuke mana nice dai taku maman yusup wacce na nishaɗantar daku cikin book ɗina mai taken.

*MUTUM CE KUWA*

Yanzu ma dai gani tafe cikin sabon salon labari na sabon zubi sabon ɗauka mai taken.

*KYAUTAR ZUCIYA*

________________________________

Ina matuƙar baku haƙuri masoyana na tsaida posting ɗin *SO BAI SAN JINI BA* da nayi sakamokon abubuwa da suka min yawa.

Sai dai ina muku Albishir da cewa zan sake muku complete ɗin book ɗin gabaki ɗaya Ranar bikin ƙaramar Sallah ta uku a matsayin *HAPPY SALLAH* kumin UZIRI pls.🙏🏻

Sannan kuma ina muku Albishir da cewa zan fara sakin sabon Novel ɗina mai taken *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Wanda ina da tabbacin cewa salon labarin sa na daban ne ina kuma da tabbacin cewa sai yafi *INDO A BIRNI* haɗuwa ku sani cewa ba wani dalili yasa na saki *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* a matsayin na kuɗi ba sai Saboda kunsan sha’anin ƙarfe wata rana dole wayar ka zata buƙaci gyara ga kuma matsalar Siyan data da kuma na Battery nasan dai nafi ƙarfin wannan kuɗin a wajen ku, ku fito ku nuna min ƙauna ta hanyar ciyen littattafan mu.

Sai ku tuntuɓe mu ta numbobin wayar mu da suke da suke ƙasa domin sanin yanda zaku biya kuɗin

_Zaku sami waɗannan littatafan namu a cikin farashi mai rahusa, domin kuwa ƙungiyar bata tsawalla ba farashi ne mai sauƙin biya, ku fito masoyan mu ku nuna mana ƙauna ta hanyar sayen littatafan mu kan farashi 👇🏻

Duka guda bakwai ɗin zaku samesa ne akan farashi Naira 500 kacal👌🏻

Mai son shida kuma zai biya Naira 450.

Mai son guda biyar zai biya Naira 400.

Mai son guda huɗu zai biya Naira 450.

Mai son guda uku zai biya Naira 350.

Mai son guda biyu zai biya Naira 300.

Mai son guda ɗaya zai biya Naira 200.

Farashi ne mai sauƙi muka baku domin ƴan uwana ku sami damar biya kuma cikin nishaɗi.

Ku tuntuɓe mu ta waɗannan numbers domin sayan book ɗin mu.

*08147537180*
*09035027743*
*08106795647*
*08176841985*

Gareku ƴan Niger kuma fa baza’a barku a baya ba ku kwantar da hankalin ku domin ku sami damar siyan littatafan mu zaku iya tuntubar wannan NUMBER👇🏻

*+2278456476*

Muna muku barka da zuwa daga Shahararriyar ƙungiyar ku Wato KAINUWA WRITER’S ASSOCIATION✍🏻
[4/22, 8:17 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

______________________________________

*P*••••••2️⃣1️⃣ ↗️ 2️⃣2️⃣

Daƙyar ta ɗago kanta ta kalli HASINA tace.

” Bana jin daɗi wlh kwana na huɗu ina kwance ya Habeeb bai sanar dake ba ne wataƙil ina ga Ya Mustafa zai sanar dashi.”

” Subhanallah sannu wlh ban sani ba kuma Habeeb bai sanar dani ba, amma ina ga gaskiya bai sani ba dan daya sani zai sanar dani gaskiya daya sani kam zaima ce nazo na duba ki.”

” Nima nayi wannan tunanin gaskiya dan daya sani shi kanshi zai shigo ya dubani kinsan Halin ya Mustafa bana gabansa shiyasa duk wani lamurana baya damuwa bare ya sanar da wani, HASINA ina rayuwar Aure ne cikin baƙin ciki na tabbata Rabon cikin da yake jikina ne ya kawo ni cikin wannan wahalar domin ni ban taɓa jin daɗin Aure ba, Hasina ji nake kamar bazanyi wani dogon Rayuwa ba Zuciyata tana min nauyi ji nake kamar mutuwa ta tana kusantoni kullum cikin baƙin ciki nake Rayuwar Aure na sam babu daɗi.”

Ta ƙarasa maganar cikin kuka tana duban Hasina kafin taci gaba da cewa.

” HASINA tunda nayi Aure Mamy bata zo taga ɗaki na ba, babu wanda yazo daga cikin gidan mu haka dangi babu wanda ya leƙoni, sai Abba kawai da yake kira na a waya HASINA baƙin ciki ne ya min yawa a cikin zuciyata har nake tunanin kamar shi zai kashe ni, Ga Rayuwar Auren ma babu daɗi.”

Shuru HASINA tayi tana sauraron RAUDA cikin tausayin halin da take ciki domin kuwa wannan babbar damuwa ce ace bakayi dacen gidan Aure ba, ga dangi babu wanda ya kalle ka to da wanne zakaji, duban RAUDA tayi cikin muryar rarrashi tace.

” Damuwa ba ta nufin mutuwa kedai kisa hkr da juriya cikin zuciyarki ki dinga yawaita addu’a insha Allah komai zai wuce kamar bai taɓa faruwa ba, mijinki Kuma zai soki ki daina sa damuwa a cikin ranki mussaman yanzu da kike sanar dani kina ɗauke da ciki, mai ciki bata son damuwa domin kuwa yana haifar mata da matsala, kiyi hkr komai mai wuce wane babu abunda yazo zama duniya fatan dai Allah ya baki lafiya.”

” Shikenan Hasina na gode sosai insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na kiyaye na gode sosai.”

Hasina ta juma suna hira da RAUDA kafin ta tashi ta mata shara tare da girki sanda ta tabbatar ta gyara mata komai na part ɗin kafin ta koma nata part ɗin, sosai RAUDA taji daɗin Abunda Hasina ta mata.

**************************

Wasa wasa yau har anci wajen wata huɗu yayin da cikin RAUDA yake da wata 6 a yanzu tana ɗan samun kula daga wajen Mustafa duk da ba yanda take so ba amma dai abubuwan da sauƙi sosai tunda ya ɗauke mata aikin komai ya ɗauko mata mai aiki amma itace take masa girki Momy ma kullum sai ta shigo ta dubata haka Momy da Mamy sunje wajen bokan ya gama tsarawa Momy ƙarya tare da bata wasu surkullen ƙarya yace taje ta zubawa yarinyar a cikin abinci da kanta zata ce bata son yaran nata haka kuma akayi ta zuba mata kuma taci.

Haka Daddy har yau bai sake kiran su ba kan maganar Auren yayi shuru yaƙi cewa komai, ya kira can Dasina ya sanar dasu cewa ya ɗaga auren zuwa wani lokaci sosai suka fahimci juna da malam musa, daga Habeeb har Mustafa hankalin su baya kwance kullum cikin zullumi suke na wani irin hukunci Daddy zai yanke domin kuwa shurun nasa ya fara basu tsoro, Mustafa kuwa har wata ƴar rama yayi mussaman yanda Indo take masa walaƙanci sam bata sauraronsa sosai take nuna masa ƙiyayya a fili tsakanin sa da Habeeb yanzu Ido koda Habeeb ya hango Mustafa kafin ya iso wajen Mustafa zai tashi yabar wajen haka kuma ko a ɗakin Momy suka haɗu Mustafa tashi yake ya barwa Habeeb wajen idan kuwa shine yazo ya sami Habeeb a wajen to juyawa yake yabar gurin.

Wajen Indo kuma abun ba haka yake ba kawai tana daure zuciyarta ne amma har yau Soyayyar Mustafa tana cikin ranta sai dai wannan alƙawarin ta ɗauke sa koda Soyayyar sa zata kashe ta bazata taɓa Auren sa ba Habeeb shine wanda zata aura.

*********************************

Da sauri ta sauƙo daga step ɗin hanunta ɗauke da bag ɗin ta sauri ta ke domin kuwa sunyi alƙawari da Zarah zasu fita shopping by 4:00pm gashi har 5:00 har zata fice taji muryar Daddy yana cewa

” *A’ISHA* Ina zaki haka kike sauri dawo ki Zauna a nan”

juyowa tayi ta dawo ta zauna kusa da Daddy tare da cewa.

” Daddy dama kana nan ban hango ka ba ai.”

Murmushi Daddy Yayi yace.

” Ina kuwa zaki ganni hankalin ki yayi gaba ina zaki haka kike wannan saurin?”

” Daddy jiya ba nace maka zanje shopping ba, shine ai yanzu zan tafi.”

Murmushi Daddy Yayi yace.

” Sarkin shopping ba to yau dai ki haƙura da shopping ɗin nan sai gobe yanzu akwai abu mai mahimmanci da zamu tattauna da ƴan uwanki na kira su suna shigowa yanzu.”

Bata ce komai ba sai kiran Zarah da tayi a waya tace mata tayi hkr sai zuwa gobe su fita “Yanzu ba hali Daddy ya ce ta tsaya za suyi meeting.”

Da to Zarah ta amsa mata kafin suka katse wayar.

INDO suna zaune a wajen har suka zo su, Habeeb ne ya fara shigowa kafin Mustafa, sai Momy da ta sauƙo cikin isa domin kuwa tana da tabbacin cewa yau Indo da bakinta zata furta bata son ƴaƴan nata, zama tayi tana murmushin mugunta, yau cikin sakin fuska ta amsa gaisuwar ƴaƴan nata bayan kowa ya zauna ne Daddy ya buɗe taron da addu’a kafin yace.

” *A’isha* Indo na tara ku anan ne badan komai ba sai don naji ra’ayin ki da farko na yanke hukunci kai tsaye ba tare da bincike ba, sai daga baya nake jin wata magana, ina so ki sanar dani wa kike so tsakanin Mustafa da ɗan Uwansa Habeeb?”

Dukan su ukun dam!Dam! Dam gabansu yake faɗuwa sunkuyar da kanta Indo Tayi ƙasa ta kasa magana, su kuwa gabaki ɗaya ita suka mayarwa hankalinsu don jin me zai fito daga bakinta, Momy kuwa wani Shu’umin murmurshi tayi tana jiran Indo tace bata sansu.

Ganin Indo bata da niyar Magana yasa Daddy ce mata.

” Please *A’isha* karkiji tsoro tell me wa kike so karki ɓoye min komai.”

INDO ta rasa ya zatayi domin kuwa har ga Allah Mustafa shine muradin Zuciyarta, Habeeb kuma shine zaɓinta daure zuciyarta tayi kanta na ƙasa ba tare da ta ɗago ba ta amsawa Daddy da cewa.

” *YA HABEEB* shine zaɓi na Daddy shine Wanda nake so, babu soyayya tsakanina da *ya Mustafa*”

Ajiyar Zuciya mai nauyi Habeeb ya sauƙe yana godewa UBANGIJIN sa daya tseratar da Zuciyarsa, wani ɓangare daga cikin zuciyarsa ce tace masa ” to shi kuma ɗan uwan naka fa kana tunanin ka masa adalci kuwa shin wani hali zaka jefasa ciki?” Ɗaya Zuciyar kuwa ce masa tayi, ” ina ruwanka da halin da zai shiga komai ya samesa ai shine ya jawa kansa ba shine mai walaƙanta mata ba, ga nan matar sa ta cikin gida ma ya kasa riƙe ta kullum yana cikin walagigi da rayuwarta, karkayi sake ka bar masa Indo yazo yana wulaƙanta ta, Kamar yadda yake yiwa RAUDA, kaine ya kamata ka aureta domin zakafi kowa riƙeta bisa Amana da gaskiya, idan ka lura ma ai kaine kake mata son gaskiya.” Da wannan huɗubar na Zuciyarsa Habeeb ya yarda tare da sakin murmurshin farin cikin samun Indo.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Mustafa kuwa wani irin bugawa Zuciyar sa tayi, jiri ne yaji yana ɗebarsa domin kuwa ga baki ɗaya ɗakin juya masa yake IDANUNSA sun kaɗa sun koma kamar gauta wani irin tsanar Habeeb ne ya ɗarsu cikin zuciyarsa yayin da Zuciyar tasa ta masa nauyi tsabar baƙin ciki gagara Magana yayi, yayin da yake bin Indo wani irin mungun kallo ita kuwa kanta sunkuye yake taƙi ɗago sa domin kuwa ita kaɗai tasan Abunda take ji a cikin Zuciyarta gani take kamar bata yiwa kanta adalci ba sai dai babu yanda zatayi Auren Habeeb shine kawai mafita a gareta.

Wani irin zabura Momy tayi tana ƙarewa Indo kallon tsana domin kuwa tasha mamaki yarinyar da ta samata magani a cikin abinci kuma tana kallo tacii abincin sannan kuma yanzu ta furta da bakinta tana son Habeeb a madadin tace bata sonsa sai tana sonsa ne ya fito daga bakinta, to wani irin magani bokan nan ya bamu, *TABBAS WANNAN YARINYAR MAYYA CE* dole sai na tashi na tsaya domin kuwa bazan taɓa yadda na haɗa zuri’a da ke ba, shuru tayi bata ce musu komai ba domin kuwa ita tasan bazata taɓa yadda wannan auren ya ƙullu ba, ba kuma zata sake faɗa na faɗa da mijinta ba.

Daddy kuwa murmurshi yayi tare da furta cewa.

” Alhamdulillah! Hakan yayi kyau Mustafa da Habeeb ai duk ɗaya suke babu bare kuma daman burina kenan ki zaɓi mijin da kike so da kanki Allah yasa hakan shi yafi Alkairi, Habeeb kaine wanda *A’ISHA* ta zaɓa a matsayin mijin Auren ta, sai kayi ƙoƙari wajen ganin ka kyautatawa Rayuwar ta, insha Allah nan da wata biyar masu zuwa za’a tada Maganar Auren, Kafin nan kaga sun sami hutun makaranta sai taje ta duba iyayen ta.”

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

” Shi kenan Daddy Allah ya nuna mana lokacin na gode sosai Daddy da wannan damar da ka bamu domin ganin ka bawa kowa haƙƙinsa Allah ya saka da Alkairi.”

Da ameeen Daddy ya amsa kafin ya maida dubansa ga Mustafa da kansa ke sunkuye baice musu ƙala ba sai zogin da yake ji cikin zuciyarsa sa kafin Daddy yace.

” Muhammad Mustafa, da farko na yanke hukunci bisa rashin Sani sai kuma daga baya naji cewa *A’ISHA* ba kai take so ba ɗan uwanka take so hakanne yasa na yanke shawarar Tambayar ta da bakinta naji waye ne zaɓin ta, to kadai ji da bakinta ta furta cewa Habeeb take so ba kai ba ni kuma bazan mata Auren dole ba shiyasa na bata wanda take so a tunanina dakai da Habeeb duk ɗaya ne kuma zaka iya Hkr ka bar masa Ita duk Soyayyar da kake mata domin ganin farin cikin ɗan uwanka kayi hkr karka saka damuwa cikin zuciyarka domin na fahimci akwai Soyayyar ta cikin zuciyarka.”

Sai yanzu ya ɗago kansa ya dubi Habeeb sannan ya maida dubansa ga Indo Wanda Yayi dai-dai da ɗago nata idanun suka haɗa ido da sauri ta maida kanta ƙasa cikin tsoro da tsinkewar Zuciya domin kuwa idanunsa sun bata tsoro, cije leɓensa yayi sannan ya ɗaga IDANUNSA da suka koma Red colour ya fara magana cikin dakiyar zuciya.

” Yaudarar ɗan uwa cutarwar zalincin ɗan uwa yau duk na gansu akan ɗan uwan da ban taɓa tunanin zan samesu a garesa ba, kamar yadda kace nayi haƙuri bazan iya haƙora da ita ba, kuma bazanyi jayayya da hukuncin ka ba, ni mai biyayya ne a gareka Daddy ina musu fatan Alkairi, ina Kuma matuƙar godiya cutarwar ɗan uwana, ita kuma bani kaɗai ta zalinta ba harda Zuciyarta domin na tabbata har gobe nine a cikin Zuciyarta hmmm *SHATUU* ki sani zan kasance da Soyayyar ki har ƙarshen rayuwata, sannan kuma ki sani cewa duk abinda ya faru dani kece sanadiyyar shiga ta, idan kuma na mutu a halin da kika sani ki sani cewa kece Ajalina, duk yawan tarin zunuban laifina gareki bancancanci wannan hukuncin gareki ba, Tabbas kin yanke hukunci cikin gaggawa, danasani yana gabanki, Allah ki zaman lafiya da zaɓin ƙwaƙwalwar ki domin bata zuciyarki bace.”

Ya ƙarasa maganar cikin rawar Murya kuka yana neman kwace masa, miƙewa yayi tsaye ya nufi hanyar barin falon, da sauri Habeeb ya miƙe tare da dakatar da Mustafa da fitar da zaiyi ta hanyar cewa.

” Me kake nufi da maganganun ka, kana nufin Na cutar da kai koko kana nufin bana ƙaunar ka.”

Murmushin baƙin ciki Mustafa Yayi jin tambayoyin Habeeb kafin ya maida masa amsa ba tare daya juyo ya dubesa ba.

” Duk yadda Zuciyarka ta fassara maganganu na haka ne *Mister Lover SO BAI SAN JINI BA SO BASHI DA HANKALI* bazan manta da waɗannan maganganun naka ba, kullum suna min amsa kuwa cikin kunnuwa na, idan har shi so bai san jini ba, to lallai kuwa dole ya kasance alaƙa ta jini ta yanke a tsakanin waɗannan ƴan uwan, a yanzu na yake alaƙa tsakanina dakai bani da wani ɗan uwa mai suna *HABEEB* na ɗauka ni kaɗai aka haife ni ba mu biyu ba.”

Yana gama faɗin hakan ya fice cikin sauri domin kuwa baya son sake jin muryar kowa cikin falon Daddy dake ƙoƙarin masa magana ma bai samu damar masa ba sakamakon ficewa da yayi, duban Habeeb Daddy Yayi yace.

” Karka damu Habeeb ranshi ne ya ɓaci shiyasa yake waɗannan maganganun amma na Tabbata zai sauƙo ku barshi ya huce kafin ku ƙara tunkarar sa.”

Shuru Habeeb yayi zuciyarsa cike da jin zafin maganganun ɗan uwan nasa, taya Mustafa zaice baya sonsa bayan duk duniya babu wanda yake so sama dashi, what ɗan uwana zaka min kallon mayaudari, duban Daddy Yayi yace.

” Shi kenan Daddy Allah yasa ya sauƙa da wuri bana son ganin yana fushi dani bani da ɗan uwan daya fisa amma ya sanja alaƙar dake tsakanin mu da wata manufa wanda sam babu shi a cikin Zuciyata Allah yasa Mustafa ya fahimce ni daddy bani da niyyar cutar da rayuwarsa ɗan uwana ne fa Daddy taya zanso rashin kwanciyar hankalin sa mutumin da muka kwanta ciki ɗaya dashi taya zan Cutar dashi, Daddy meyasa zai guje ni akan Mace Daddy hakan yana nufin cewa daman can babu Soyayyar da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin mu, ka bani amsa Daddy na fara shiga cikin duhu.?”

Tsuka Momy taja tare da tashi ta haura tana taɓe baki harara ta sauƙewa Habeeb sannan ta wuce, kallo kawai Daddy ya bita dashi kafin ya dawo da kallonsa kansu Habeeb ya umurci Indo da ta koma bedroom ɗin ta tayi alwala domin kuwa amfara kiran sallah, ” kaima Habeeb jekayi alwala ka tafi kubar maganar zai sauƙo da kansa ransa ne ya ɓaci waɗannan tambayoyin duk ka ajiye sa a gefe.”

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe Sannan ya miƙe ya fita itama Indo ta haura sama shima Daddy tashi yayi yaje ɗauro alwalar ya fice masallaci.

MOMY tana shiga bedroom ɗinta layin Mamy ta kira, cikin tashin hankali take cewa.

” Wani irin magani bokan nan ya bamu ne kam, nafa bata maganin nan da Idona Kuma na ganta taci, sannan yanzu ta ƙara furta cewa Habeeb take so bayan kuma shi malam yace da bakinta zata furta cewa bata son ƴaƴana, nifa Turai Hankali na a tashe yake domin kuwa bazan taɓa lamunta ɗana ya auri wannan fitsararriyar YARINYAR ba.”

Daga can Mamy tayi murmurshin mugunta tana yiwa Momy kallon wawiya marar lissafi kafin tace mata.

” Haba Hajiya A’isha ya kike gaggawa ne kam shikenan daga baki magani sai akace miki zai yi amfani lokaci ɗaya, ina kika taɓa ganin anyi haka, kinga malama ki kwantar da hankalin ki komai sannu ake binsa, a hankali zamu kamo bakin zaren har mu cinka sa dan haka kwantar da hankalin ki yanzu ma zan kira Mlm na masa bayani naji maiya kamata ayi.”

Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe tare da cewa.

” Yauwa kira sa dai gaskiya hankalina zaifi kwanciya dan Wlh bana ƙaunar YARINYAR nan, ni ko nawa ne zan basa muddun zan samu biyan buƙata.”

Murmushi sosai Mamy tayi tace.

” Gaskiya kam ya kamata ki ƙara masa kuɗi fiye da wanda kika basa a baya, dan mu samu shima ya ƙara dagewa mu samu biyan buƙatar mu da wuri kinsan dai yanzu irin wannan harkar ta koma sai ana sakewa malaman nan kuɗi sannan suka zasu samu suyi aiki da kyau komai ya koma sai da kuɗi.”

” Karki damu ƙawata indai kuɗi ne kema ai kinsan bani da matsalar su, ko nawa ne zan iya kashewa muddun za’a raba ni da wannan raƙai ɗin shegiyar ƙaya mai suka, ni fa ta dameni da suka, bukata ta kawai na yageta na huta Banda damuwa da kuɗi ko nawa zan iya kashe wa domin kuwa akwai su.”

Wannan karon dariya sosai Mamy tayi kafin tace.

” Ai kuwa ki kwantar da hankalin ki, zaki yageta koda kuwa da naman jikin kine dole sai tabar gangarki koda kuwa bata bar gidan ki ba.”

Murmushi Momy tayi domin kuwa bata fahimci Mamy Hausa tayi mata ba, ita nufin Mamy na koda Naman jikinta ne, shine koda ɗanta zai aureta ya fitar mata da ita daga cikin gidan zuwa gidan sa, ce mata tayi.

” Da kuwa kin taimaka min wlh, yanzu kuyi Magana dashi duk abunda ake buƙata kimin magana zan turo miki ta account karki damu da yawan kuɗi ko nawa ne zan iya biya.”

” Shi kenan baki da matsala, sai kin jini zuwa gobe.”

“Allah ya kaimu” Momy tace kafin ta kashe wayar ta ajiye kan bed ɗin ta kafin ta shiga tollet alwala.

*******************************

RAUDA sosai cikin jikinta ya fito ga wani ƙiba da tayi, yanzu laulayin ma da sauƙi ya sassauta mata, Zaune take tasa ayaba a gaba tana ci, ya shigo cikin fushi ko Sallama baiyi ba, ya shige bedroom ɗinsa, kallo kawai RAUDA ta bishi dashi cikin mamaki domin kuwa rabon da ya shigo cikin wannan yanayin harta manta lokacin, bata gama dawowa daga tunanin ba, sai kuma ta gansa ya fito riƙe da key a hannun sa ya fice still ba tare daya kalleta ba, tashi tayi ta ɗaga labulen window tana leƙensa motar sa ya shiga ya ja da ƙarfi ya fice daga cikin gidan, sake labulen RAUDA tayi tana tunanin kome aka masa, zama tayi ta cigaba da cin ayabar ta domin kuwa tasan halin sa sarai zai iya wannan fushin ma ba tare da amsa wani laifi ba.

Shiko Mustafa gudu kawai yake a titi ba tare da yasan inda zashi ba, maganar zuci kawai yake shi ɗaya.

(Wai yau ni Habeeb zai wulaƙanta ni Habeeb yake shirin kwacewa numfashina daga jikina wani irin laifi na masa haka da zai min Hukunci mai muni irin wannan ko a mafarki ban taɓa tunanin haka daga garesa ba)

Jin ƙarar haɗuwar motar sune ya sashi saurin dawowa daga tunanin sa, yana ƙoƙarin riƙe sitiyarin motar, da ƙyar ya samu ya taka burki ya tsaya yana dafe kansa tare da ambaton ubangi, shi kuwa Barrister Kamal cikin masifa ya fito daga motar yana ƙoƙarin zagin Mustafa sai dai mai yana sako kansa su kayi Ido huɗu da Mustafa daya dafe kansa yana sauƙe ajiyar Zuciya, nunasa da hanu Kamal Yayi yace.

” Barrister mustafa kaine kake wannan gudu haka bisa titi ko kasan wannan wasa da Rayuwar ka kake yi.”

Ajiyar Zuciya Mustafa ya sauƙe tare da ɗago idanunsa da suka koma Red color da ƙyar cikin nauyin Murya yace.

” Sorry Barrister Kamal na maka asara a motar ka ko, Ni kaina bansan wani irin tuƙi nake ba, gabaki ɗaya bana cikin tunani na bamma san inda zani ba kawai tafiyar nake, sorry”

Cikin mamaki Barrister Kamal yace masa.

” Baka san inda zaka ba kuma lafiya kuwa kake Barrister mustafa? naga alamar kamar baka cikin nutsuwar ka, kaga bari naja mota ta mu wuce, *Amada club* ma ƙarasa maganar a can.”

Cike da mamaki Mustafa ya tambayi kamal.

” Club kuma Barrister Kamal me zai kaika Club kuma?”

Murmushi kamal yayi tare da cewa.

” Kaga Barrister mustafa babu Time ɗin tambaya yanzu muje kawai tunda kaga kaima ba wai wajen zuwa kake dashi ba.”

Kaɗa kansa kawai Mustafa Yayi sannan suka ja motar, suka nufi Club ɗin, koda sukayi parking shiga sukayi cikin club ɗin, babu abunda yake tashi sai sautin ƙiɗa, mata ne ƴan bariki birjik cikin Club ɗin ga baki ɗayan su babu wani mai suturar arziki a jikinsa, waje suka samu suka zauna bisa kujerun dake zagaye cikin Club ɗin yayin da maza da matan dake wajen suke sheƙe ayar su ta tsiya, shidai Mustafa zama yayi tare da jin gina kansa yana sauraron kiɗan dake tashi a wajen, zuciyarsa Kuma har yanzu bata daina suya ba, wasu ƴan mata biyu dake tsaye gefe daga su sai wando 3 cutter da wata ƴar ƙaramar Best, ɗayar ce ta zubawa Mustafa ido tana jin wani irin feeling a kansa, itafa gayen ya mata domin kuwa yayi bala’in haɗuwa, Magana suke ƙasa ƙasa ita da ɗayar, wanda baza kaji Abunda suke cewa ba, Still wata ce ta taho cikin sauri ta faɗa jikin Kamal, tare da kai masa kiss a kumatun ta, Wani irin kallon takaici Mustafa ya bita dashi tare da runtse idonsa yana tir da halin ta, kamal kuwa ƙara ƙanƙameta yayi a jikin sa kafin ya dubi Mustafa yace.

” Barrister Meke faruwa ne, bani meya fito da kai daga gida cikin fushi.”

Taɓe bakin sa yayi yana ƙare musu kallo daga shi har yarinyar kafin yayi Magana yana nuna yarinyar da yatsa.

” A gaban wannan abar kake cewa na faɗa maka damuwata ta, a gaban wannan renon barikin, ba dai ni ba.”

Murmushi Kamal Yayi sanin halin Mustafa sarai yasan idan yaja da yawa ma, zai iya kaiwa wannan yarinyar mari, ita kuwa Ranta idan yayi dubu ya ɓaci domin kuwa babu wanda ya taɓa shigowa cikin Club ɗin ya zageta sai shi, Kamal dubanta Yayi yace.

” Sorry Safiya jeki idan mun gama zan nemeki.?”

Cikin ɓacin rai tace masa

” But amma…………”

Dakatar da ita Mustafa Yayi cikin tsawa wanda har saida hankalin mutane ya dawo kansu.

” Keeeeeeee!!!!! Get out wuce ki bamu waje ballagaza cikon lissafi, ko kunya bakya ji kina mace mai daraja, ki zubar da rayuwarki kina rayuwar bariki, kinzo wani ginɗin-ginɗin dake ki ɗafe jikinsa kamar wanda kika samu jikin mijinki, ki gyara rayuwar ki domin ki samawa kanki ƙarshe mai kyau.”

Iya ɓacin rai wannan baiwar Allah ta jishi domin kuwa gani take ya mata mungun wulaƙanci, ya tozarta ta cikin mutane, ita kuma tayi alwashin cewa sai ta rama Abunda ya mata, juyawa tayi cikin ɓacin rai tabar wajen yayin da sauran matan wajen suka sheƙe mata da dariya shi kanshi Kamal baiji daɗin Abunda Mustafa ya mata ba cikin mutane.

( Wannan shi ake kira bariki gidan da babu kunya a cikin sa)

Juyowa kamal yayi tare da cewa.

” Baka kyauta ba Barrister ka tsinka ta cikin mutane.”

Murmushin takaici Mustafa Yayi kafin yace.

” Kabar wannan maganar muyi Abunda ya kawo ni.”

” Okey ina sauraron ka tell me?”

Ajiyar Zuciya Mustafa ya sauƙe tare da duban Kamal ya fara zayyano masa abubuwan da suke faruwa, kafin ya ƙarasa maganar da cewa.

” Ban taɓa tunanin cewa Habeeb zaimin haka zuciyata ɗaya na ɗauke sa, amma abun takaici ɗan uwana na jini wanda muka kwanta ciki ɗaya muka girma tare muka rayu tare wai shine yanzu yake ƙoƙarin rabani da farin ciki na, ƙarin abun takaicin ma wai Daddy ya biye musu, Kamal kana TUNANIN cewa sun min adalci kuwa.?”

Ajiyar Zuciya Kamal ya sauƙe yana duban Mustafa kafin yayi murmurshi yace.

” *Shege SO* mai haɗa faɗa a tsakanin Aminta, yanzu kai Barrister mustafa menene abun mamaki a nan, indai *SO* ne zaiyi fiye da haka, karka manta da shi so *BAI SAN JINI BA* yana haɗa ɗa da uba ma faɗa wannan kaɗan ne daga cikin aikin soyayya yakan raba aminta, ni a nawa tunanin karka wani zargi ɗan uwan ka, kawai ka rabu dasu, suje su karata badai Mace bace ƙwaya ɗaya tak, Barrister shiga gari zaka samu goman ta waɗanda suka fita ma kyau, mussaman kai da kake juya Naira ka kuma taka ta, na Tabbata Mata har wawanka sai sunyi saboda yanzu harka da mai Naira ake yinta, ka manta da ita ka cireta cikin rayuwar ka, idanma zuciyarka zata dameka da tunanin ta, ka nemeni ina da maganin wannan damuwar akwai barasa da kuma ƙwayoyi na Tabbata zasu rage maka matsala zama su yaye maka ita gabaki ɗaya.”

Wani irin kallon mahaukaci Mustafa yake bin Kamal dashi wai ya manta da *SHATUUN SA* Lallai Kamal ya cika cikakken mahaukaci, duban sa yayi kafin yace.

” Na gaji!! Na gaji!! Da jin wannan kalmar *SO BAI SAN JINI BA* bazan taɓa iya mantawa da ita ba domin kuwa numfashina ne ita, da zaka tara min matan duniya duka idona bazai taɓa kallon wacce tafi SHATUU ba sai kasa da ita babu wanda zai taɓa maye gurbin ta cikin sarautar zuciyata, ka daina kira min wannan banzar maganar, kamal ina da munguwar sha’awa da jarabar mata sai dai ko kaɗan bai ɗaura min son matan banza ba, basu kuma taɓa burgeni ba, ba kuma zasu taɓa burgeni ba, Kamal naga alamar baka da shawara mai mahimmanci da zaka bani kaga tafiyata.”

Murmushi Kamal Yayi yana duban agogon hanunsa yace.

” Ina zaka yanzu ƙarfe 2:00pm ka haƙura kawai sai gobe yanzu kam dare ya kusa rabawa.”

Dafa kansa Mustafa Yayi yana ƙarewa agogon hanunsa kallo, dole tasa Mustafa komawa ya zauna yasan bai isa yanzu ya koma gida cikin daren nan ba, tashi kamal yayi ya je ya kamawa Mustafa ɗaki shi kuma yayi ɗakin ABOKIYAR shashancin nasa, zama Mustafa Yayi bakin gadon ya dafe kansa wani irin Soyayyar INDO na ƙara bugar zuciyarsa ita kawai yake kallo cikin ƙwayar idanunsa, daya kwanta ma juyi kawai yake, yana jin wani irin ɓacin rai na Habeeb duk yanda yaso bacci ya ɗauke sa abun yaci tura domin kuwa duk satar bacci Ranar ya gagara satar Mustafa, gashi yana son Yayi baccin ko zai samu *SASSAUCIN CIWON DAKE CIKIN ZUCIYAR SA* ganin abun na ƙara damunsa Zuciyarsa na ƙara bugawa ya sashi fara tunanin ko dai ya kira Kamal ne ko zai samu maganin bacci a wajen sa.

 

____________________________________________

Tirƙashi wannan shi ake kira ƙayar baya wai garin nema ƙiba an tafi neman rama, to wai ya wannan daren zai kasance a wajen Mustafa ne cikin Club.?

Ku dai ku biyoni.

Sorry for typing error banyi editing ba.

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻

 

*(Ummu Nasmah ce)*
[4/27, 10:23 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

2️⃣3️⃣ ↗️ 2️⃣4️⃣

Har Ƙarfe Uku da rabi bacci ya gagari Mustafa babu abunda zuciyarsa take masa sai saƙa ga mungun faɗuwar gaba da yake damunsa wayar sa ya ɗaga ya kira kamal lokacin daya kira sa suna tsaka da tambaɗewar su, wajen miss Call uku kafin Kamal yasa hanu ya jawo wayar daƙyar ya buɗe idanunsa da jaraba ya rufe su, ya duba screen ɗin wayar Barrister mustafa ya gani saurin tashi yayi daga kan Safiya ya ɗaga wayar tare da cewa.

” Lafiya kuwa Barrister kira tsakiyar dare haka.”

Daga can Mustafa yace

” Na gagara bacci Kamal, zuciyata tana buga min ji nake kamar zata bar jiki na, GIZO take min cikin idanuwa na, ta hanani bacci, ƙirji na kuma yana min nauyi, PLS Kamal maganin bacci nake so, ko zanji relief Idan ba haka ba ƙwaƙwalwa ta zata zauce.”

Murmushi Kamal Yayi yana kannewa Safiya Ido da take sauraron duk abunda Mustafa ke faɗa kasancewar a handsfree ya saka wayar Kamal ce masa yayi.

” Okey jira ni yanzu akwai maganin bacci wanda zai saka bacci yanzu kuwa bari na bayar a kawo maka yanzu.”

Komawa gefe yayi yana kallon safiya kafin yace Mata.

” Lokacin ki zai fara daga yanzu, tashi kije ki karbi Coca-Cola ki karɓi kwaya wajen John ki wurga masa a ciki, daga can kya taya sa kwana ni na jawo Serah mu ƙarasa daren.”

Tashi Safiya tayi tana murmurshi domin kuwa ta samu damar rama Abunda ya mata ɗazu rigarta taja wata ƴar firit wacce da ita da babu duk ɗaya tasa, wajen John ta tsaya ta karɓi cock da ƙwayar maye, ƙara tambayar sa tayi ya bata na Feeling (sha’awa) ɗaukowa yayi ya bata, karɓa tayi tare da ɓalle murfin Cock ɗin ta watsa ƙwayar a ciki girgizawa tayi sannan ta mayar ta rufe, kwankwasa ɗakin da yake tayi, Mustafa dake zaune zaman jiran Kamal ya tashi cikin sauri ya buɗe ƙofar tsaye ya ganta gabansa tana sauke masa wani Shu’umin murmurshi, kauda kansa yayi gefe tare da Cewa.

” Meya kawo ki nan ɗakin na kira ki ne.?”

Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce masa komai ba, tasa kanta ta wuce cikin ɗakin tare da ajiye masa cock ɗin a saman tebur, hanunta tasa ta ɗauke key ɗin ɗakin da yake kan tebur ɗin ta danƙesa a hanunta yanda bazai taɓa lura dashi ba, ficewa tayi daga cikin ɗakin Still tana sakin murmurshi, tsuka yaja tare da rufe ƙofar ya sa mata kuba, sannan ya wuce ya ɗauki Cock ɗin bai kawo komai cikin ransa ba ya ɓalle murfin tare da kafasa a bakin sa, bai sauƙe ba sanda yaji babu komai ya ƙare sannan yayi wurgi da gorar, yana kwanciya rigingine ya kafawa slim ɗin ɗakin Ido, mintuna kaɗan maganin suka fara aiki a jikin sa, gabaki ɗaya ɗakin juya masa yake, komai bibbiyu yake kallon sa, ga wani bala’in Feeling da yake taso masa babu abunda yake buƙata Irin yaji mace a jikin sa, wani irin tashin hankali ya shiga, ita kuwa Safiya sanda ta daidaici time ɗin da maganin yayi nisa a jikinsa sannan tasa key ɗin ta buɗe shiga tayi tare da rufe ƙofar, faɗawa tayi jikin sa, shi kuwa kamar wanda yake jira ya kanƙameta domin kuwa babu Hankali a jikinsa, Haɗa bakinsu sukayi waje ɗaya, sun juma suna rommace ɗin junansu kafin daga baya salon nasu ya sanja.

(Wa’iyazubillah Allah ka raba mu da sharrin HATSABIBIYAR mace da mungun Aboki)

Sanda suka gama aikata masha’arsu kafin ya gangara gefe yana sauƙe ajiyar Zuciya a haka bacci mai nauyin gaske ya ɗauke sa, kallo Safiya take binsa dashi tana murmurshi tare da shafo gashin ƙirjinsa tana son gayen cikin zuciyarta sai miskili ne na ajin farko, sanda ta gama saƙe saƙen ta sannan ta dirƙo daga gadon tollet ta shiga tayi wanka sannan ta fito tare da maida kayan ta ta fice tana murmurshi.

Mustafa shine bai farka ba sai ƙarfe 12:00 na rana da salati a bakinsa ya buɗe idanunsa yana ƙarewa agogon ɗakin kallo da sauri ya tashi yana cewa.

” Subhanallah 12:00 wani irin bacci nayi haka oh my maganin da wannan ɗan Iskan ya bani, mema ya sani karɓa ne, oh shart duk *SHATUU* kece kika jawo min zuwa Wannan wajen harta kaini ga kwana” dafe goshin sa yayi yana tariyo Abunda ya faru dashi daren jiya tiryan-tiryan yake dawo Masa mussaman Abunda suka aikata da Safiyya wasu xafafan hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunsa tunda yake a rayuwarsa bai taɓa kusantar Zina ba, sai gashi rana tsaka ya afka cikin ta, lallai wannan YARINYAR sheɗaniya ce, sai dai ba kowa bane ya jawo min wannan masifar sai *SHATUU da HABEEB* duk sune suka jefa ni cikin wannan halakar, “innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un, Astagfurullah Allah na tuba ka yafen badan hali na ba, Allah ka yafe min ban aikata maka wannan zunubin da niyya ba, Allah kaga zuciyata nafi kowa kyamatar Zina sai gashi yau ƙaddara tasa na afka cikin ta, ya Ubangiji nasan ni mai laifi ne a wajen ka Allah ka yafe min.” Cikin hawaye yake Maganar tashi yayi ya wuce tollet yayi wankan tsarki tare da wanka ya maida kayan jikinsa ya fito a zuciye Allah kawai yake roƙo ya haɗasa da Kamal da Safiyya shi kaɗai yasan kalar walaƙancin da zai musu, sai kash kafin Mustafa ya fito tuni Kamal ya kama gabansa, dube-dube Mustafa yake ta ina zai hango su, ita kawai ya hango jikin wani mutumin daban ba Kamal ba, girgiza kansa Mustafa Yayi a fili ya furta. *ƳAR AKUYA KENAN MAI BIN DUK WANI BUNSURU* nufar wajen nata yayi a zuciye, yana zuwa ya sauƙe mata kyakkyawan mari mai lafiya, gabaki ɗaya jama’ar wajen dawo da hankalin su sukayi wajen su, cike da mamaki, riƙe kumatun ta tayi tana kallon sa, wanda take jikinsa ne shima ya tashi cikin zuciya yana nuna Mustafa da yatsa yace.

” Waye kai da zaka zo har nan ka mari Sofy kasan waye ni kuwa da zaka mareta a gabana, Lallai kayi kuskure.”

Murmushi mustafa yayi yana ƙare masa kallo tare da kamo yatsar da yake nuna masan ya murɗeta da ƙarfi har sai da ya danna ƙara sannan Mustafa yace.

” Bansan waye kai ba kuma bana buƙatar sanin hakan Bunsuru ɗan AKUYA kawai, kuskure kuwa kaine wanda ka tafka sa da kayi kuskuren nuna min yatsa domin kuwa ba’a min haka, ka bari tukunna banzo kanka ba da wannan Akuyar idan nazo idan yaso sai ka isar min da saƙon naka, yanzu dai kaje ka fara jinyar yatsar ka tukunna dan ina da tabbacin ta karye” ya sake masa yatsar yana ƙara ɗauke Safiyya da mari tare da jideta ta faɗi kasa belt ɗin jikinsa ya zare ya hau zabga mata, ihu Safiyya take sosai sai dai abun takaici an rasa mai kwatarta a hanunsa domin kuwa ga baki ɗaya wajen shakkar Mustafa suke sanda ya tabbatar tayi lilis yanda dakyar take motsi sannan ya ƙyaleta nuna ta yayi da yatsa yana cewa.

” Gobe ki ƙara kwatantawa wani makamancin Abunda kika min, banza daƙiƙiya ballagaza jaka cikon lissafi kekam wlh iyayenki sunyi asarar haihuwar ki, dubi yanda kika maida bariki sana’a kika watsar da rayuwarki, bisa titi, kika sayar da mutuncin ki, kika kasa jikinki a kasuwa, da wanda yakai da wanda bai kaiba ma yazo ya saya, kiji tsoron Allah ki yiwa Rayuwar ki karatun ta nutsu ki tuba zuwa ga UBANGIJIN ki kafin lokaci ya ƙure miki, kizo kina munguwar nadamar da bata da Amfani.” Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin club ɗin motar sa ya hau yana tunanin wani hali RAUDA ta shiga ganin bai kwana a gida ba, harya ɗauki hanyar gidan sai kuma yayi ribas ya karya hancin motar ya harba zuwa makarantar su *INDO* domin kuwa yasan yanzu tana can ta daɗe da tsufa a can.

” Allah Zarah yau pro Sani ya bani dariya, shi fa tsakanin sa da Allah yake son sai munje Delta practical ɗin nan.”

” Ke ya bawa dariya ko ni kuma wai iya mata mu goma zamu, idan akwai gaskiya mai zai hana a saka da maza cikin tafiyar, nikam ma gashi daman ya daɗe yana kaimin hari mayen Mata”

INDO ta ƙarasa maganar tana dariya har tana dafa Zarah, ya daɗe tsaye cikin motar yana kallon yanda take walwala abunta har da dariya ita ko a jikinta, shi ta bari cikin wahala da damuwa fitowa yayi daga cikin motar ya nufe ta, ko Sallama bai mata ba ya tsaya a kanta yace.

” Tashi mu tafi.”

Murmushi Indo tayi cikin jin daɗin ganinsa dama tun jiya take ƙaunar ganin halin da yake ciki, sam Hankalin ta baya kwance, ƙin dago kai tayi ta kallesa bare yasa ran zata tashi, cikin ƙula da halin ko inkula data nuna masa cikin tsawa yace.

” ba dake nake Magana bane kinyi banza dani!!”

Har yanzu Indo bata ce masa komai ba kuma bata da niyar tashi, iya ƙula Mustafa ya ƙula ransa idan yayi dubu to ya ɓaci, Zahra ce ta dubeta tace.

” Haba kawata ya mutum yana miki Magana kina ji kinyi shuru, ki tashi kije kiji mai zai faɗin miki.”

Duban Zahra tayi tace.

” Me zance masa sannan me zai sanar dani, duk abunda zai faɗa ya faɗesa a nan badai kunne na bane yake jin Magana sai ya faɗa ai idan ina da amsar Maganar sa na basa idan kuma babu sai yayi hkr, babu wata alaƙa yanzu tsakanina dakai daya wuce na ƴan uwantaka, meyasa bazai gane haka bane, ki sanar dashi Zahra dan Allah yayi hkr ya kyale ni, na riga da na fidda mijin da zan Aura.”

Sam Zarah bata ji daɗin Abunda Indo ta yiwa Mustafa ba, buɗe baki tayi tace.

” Amma dai ya kamata kije ki sauraresa koma menene yake tsakanin ku bai kamata ki wulaƙanta sa ba karki manta da ɗan uwanki ne koda babu alaƙar Soyayya tsakanin ku.”

Idonsa sun rufe tsabar ɓacin a yanzu ya fara tunanin da gaske zai iya rasa, ya kuma san rasata tamkar rasa Rayuwar sa ne, duba yake Binta dashi kafin ya durƙusa a gabanta yana dubanta da idanunsa da sukayi ja yace.

” Gani durƙushe gabanki ina mai neman afuwar ki, na tuba nasan tabbas na miki laifi a baya, na kuma amshi kuskurena, ki taimake ni karki gujeni, Wlh kece Rayuwata rasaki tamkar rasa numfashina ne, ki taimakeni karki Auri wani ba niba Wlh ina sonki fiye da yanda nake son Rayuwata, ki taimake ni karki Auri wani ba niba nasan mutuwa zanyi muddun na rasaki.”

Ga baki daya jikin su yayi sanyi mussaman Indo wani irin tausayin sa take ji, sam Zuciyarta bata mata daɗi ba ganinsa a cikin wani mawuyacin hali, amma duk da haka sai ta daure zuciyarta ta ɗago cikin ƙarfin gwiwwa tace masa.

” Ƙarya kake ya Mustafa baka sona da kana sona da baka wulaƙanta ni ba, da kana sona da baka kyamace niba da kana sona da baka dokeni ba. Shi Wannan ɗin duka a cikin Soyayya ce, baka taɓa nuna min hanya mai kyau ba duk kaucewar da nayi baka taɓa ajiyeni ka nuna min cewa ga inda zanbi rayuwata tayi kyau ba, baka taɓa ɗaukata a matsayin mutum sai ma dangana ni kake da suffar aljanu da dabbobi, idan ban manta ba akwai sanda ka ce min ( Allah ya sauwaƙa naso ƙazama Irin ki kazamar ƙauye, waima tukunna waye zai miki kiss da waɗannan yellow haƙwaran naki ɓace min da gani kafin na targaɗaki, mahaukaciya kawai marar lissafi, amma dai Wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zaki ce kina so sai ni, to Wlh Allah ya isa kin cuceni) ka kuma cemin.

( Nidai wannan YARINYAR ta zamo min masifa duk randa zanzo ƙauyen Nan, da tsinkewar Zuciya nake zuwa, tunda nasan zan haɗu da bala’i)

Kayi tunanin duk na manta da waɗannan maganganun naka ne, to yanzu kuma me zakayi da ƙaramar ƙauye mahaukaciya mai yellow haƙori marar lissafi wacce ka yiwa Allah ya isa, ka kirani da macuciya ka kirani da masifa da bala’i wanda har na zamo tsinkewar Zuciyar ka duk kawai dan nace ina sonka, meye laifina a nan ka faɗa min meye laifin Zuciyata dan ta ce kaine take so sai dai alhamdulillah ko yanzu na godewa Allah daya cire min Soyayyar ka cikin zuciyata, kaje ka riƙe matar ka ina ga hakan zaifi maka, nikam na riga da na yankewa kaina hukunci bana ƙaunar ka a yanzu.”

Ta ƙarasa maganar cikin zubar hawaye da rawar Murya, kallon tausayi Zarah take binsu dashi Tabbas tasan suna son junan su har gobe, sai dai ƙaddara ta gifta tsakanin su, wanda har ta kaisu ga rasa Aure tsakanin su, Tabbas wannan shi ake kira *SO BAI SAN JINI BA* domin kuwa da yasan jini bazai taɓa shiga zuciyoyin waɗannan ƴan uwa biyun ba, gashi har yana son shiga tsakanin *ZUMUNCIN SU* Shi kuwa Mustafa cikin mungun tashin hankali yake duban ta, jin maganganun da take tuna masa shi harga Allah ya manta ma da wannan maganar da take tuno masa sanda ta faɗa masa sannan ya tuna dashi ashe ita tana sane da shi cikin zuciyarta, Tabbas ya tafka babban kuskure, dubanta yayi tare da cewa.

” Tabbas na aikata miki kuskure wai yawa na amshi laifi na, ina mai baki haƙuri da ki yafe min dan Allah komai ya wuce ki ceci Rayuwata karni bari Rayuwata ta lalace ta sanadin Soyayyar ki.”

Murmushi Indo Tayi mai cin rai kafin tace.

” Lokaci ya riga daya ƙure maka domin kuwa nima bazan yarda nayi sanadin shigar wanda ya taimaki rayuwata ba ta lalace sanadin Soyayya ta, kayi hkr ka cire Soyayyata cikin ranka domin kuwa ba kai nake so ba ɗan uwanka nake so *YA HABEEB* shine zaɓin Rayuwata shine wanda ya cancanci nayi rayuwa dashi ba kai ba ka cire Soyayyata cikin ranka ko karka cire wannan damuwar kane ba tawa ba, domin kuwa son maso wani kake.”

Tana gama faɗin haka ta tashi tabar wajen cikin sauri jin kuka yana neman kwace mata Soyayyar sa yana son karya mata zuciya yasa har tausayin sa yasa ta kauce layi ta hanyar yiwa Habeeb butulci, kuma Abunda bazata taɓa yadda ya faru ba kenan.

Runtse idonsa yayi cikin jin Zafin maganganun ta, wani irin ƙuna Zuciyar sa take masa, baisan ya zaiyi SHATUU ta fahimce sa ba, ta kasa gane kalar Soyayyar da yake mata, tausayin sa sosai Zahra taji, dubansa tayi tace.

” Kayi hkr Mustafa na fahimce halin da kake ciki, ka daurewa Zuciyarka, ka cireta cikin ranka tunda kaga har iyaye sun yanke hukunci, nasan irin zafin da kake ji amma ya zakayi ƙaddara ta riga fata.”

Tashi yayi tsaye ba tare da cewa Zarah komai ba ya shige cikin motarsa yana layi, girgiza kanta Zahra tayi sannan itama ta tashi tabi bayan INDO, a Class ta sameta ta kifa kanta jikin kujera sai Rusar kuka take zama Zarah tayi tare da dafa kafaɗar ta tace.

” Meye amfanin kukan? karfa ki sawa zuciyarki wani ciwo.”

Ɗago kanta tayi idanunta sunyi jajur tace.

” Dole nayi kuka Zarah na rasa farin ciki na, gashi yana cikin wani mawuyacin hali, bana son ganinsa cikin damuwa Zahra ina son Ya mustafa bana son ganinsa cikin damuwa.”

” Idan ma kina sonsa ya kika iya tunda dai ƙaddara ta riga fata Daddy ya riga ya yanke hukunci, meye aibun Habeeb da kika kasa sonsa, meye banbancin Habeeb da Mustafa, basu da wani banbanci koda kuwa ta kama ce, kawai ki kalli Habeeb a matsayin shine Mustafa wala Allah zaki samu sassauci a cikin zuciyarki.”

” Ba zaki taɓa ganewa ba Zarah, ke bakya ganin banbancin su amma ni ina gani suna banbanci sosai, ki daina furta min kalmar na manta dashi bazan taɓa iya mantawa da ya Mustafa ba CIKIN RAYUWATA, ni kaɗai nasan Abunda nake ji akansa.”

Shuru Zahra tayi bata ƙara cewa Indo komai ba haka itama Indo har suka gama lectures suka tashi jikin Indo a mace yake murus tana tunanin wani Hali mustapha yake ciki.

Bayan yayi parking ne a harabar gidan sannan ya fito ya dumfari part ɗin Habeeb yana huci kamar mayunwacin zaki babu ko Sallama ya faɗa falon Habeeb yana kwance bisa cinyar HASINA sukaji tsayuwar mutum a kansu da sauri suka ɗago idanunsu Mustafa ne suka gani tsaye, tashi Habeeb yayi ya zauna yana kallon Mustafa domin kuwa yasan ba Alkairi bane ya kawo sa, cikin sakin fuska yace.

” Bros kaine bismillah ka Zauna mana kana tsaye.?”

Wani irin mungun kallo Mustafa yake bin Habeeb dashi kafin yace.

” Hmm!! Kana TUNANIN cewa akwai Abunda zai kawo ni ɗakin maci Amana irin ka har na samu wajen Zama Allah ya sauwaƙa ko yanzu ina jin takaici da baƙin cikin kasancewar ka ɗan uwa a gare ni, da ace ina da ikon sanja ƙaddara to Tabbas da saina cireka daga sahun alhalin mu.”

Sa ke baki Hasina tayi tana kallon sa domin kuwa Abunda bata taɓa gani ba kenan tashin hankali tsakanin su ikon Allah kawai ta tsaya kallo shi kuwa Habeeb runtse idonsa yayi yana jin Zafin maganganun ɗan uwan nasa, cigaba da cigaba da cewa Mustafa Yayi.

” Nazo ne na sanarda kai cewa kayi gaggawan fita a harkar SHATUU domin kuwa SHATUU mallaki nace, idan kuma kaƙi to Wlh ka guji Abunda zai biyo baya dan bana tunanin zai maka kyau, maha’inci maci Amana dubeka ko kunya baka ji kana son BUDURWAR ɗan uwan ka, na dai sanar da kai ka fice daga harkar ta *IDAN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA*.” Yana gama faɗin haka ya fice ba tare da ya saurari abinda Habeeb zai faɗa ba.

Harya fice Hasina na binsa da kallon mamaki, kafin ta maida dubanta ga mijinta tare da jefa masa tambaya.

” Meya haɗaka da ɗan uwanka, waye kuma SHATUU, naga ya Mustafa a fusace yana faɗin magana marassa daɗin sauraro pls meya shiga tsakanin ku.?”

Ta ƙarasa maganar tana kallon idonsa, ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe tare da cewa.

” Soyayya itace ta shiga tsakanina da ɗan uwana, ba wata dabam bace SHATUU INDO ce haka yake kiranta dashi, tabbas maganganun sa babu daɗin ji, amma nasan ɓacin raine ya jawo yamin haka karki damu komai zai wuce.”

” Idan har na fahimce ka dai-dai INDO kuke so dukanku, sannan kuna shirin wargaza zumuncin ku saboda Soyayya koh, yaushe ka fara son ƙanwarmu Indo, ban taɓa jin labarin ba, kuma baka taɓa nuna min ba ko a fuskar ka, wata ƙila zan kawo maka matsala ne cikin Soyayyar ku ko, meyasa ƙaddara ta haɗaku son abu ɗaya bayan tasan ƙarfin alaƙar jinin ku tabbas ƙaddara bata muku adalci ba, da ta zukatan *JINI ƊAYA* masu ƙaunar junan su meyasa so zai muku haka.?”

Ta ƙarasa maganar ba tare ta nuna masa tasan Maganar ba zuciyarta kuma tayi sanyi, shuru yayi yana matukar jin nauyin matar tasa kafin ya kamo hanunta ya fara mata magana cikin sanyin murya da sigar rarrashi.

” Ki gafarce ni matata, Tabbas na ɓoye miki damuwata ta Soyayyar Indo, badan komai nayi hakan ba sai dan nasan bazaki ji daɗi ba idan kika san ina sonta, ni kuma bana buƙatar na sanar dake Abunda zai ɓata miki rai, Tabbas Soyayyar Indo tayi nisa a cikin Zuciyata yanda bazan taɓa iya cireta ba, a dole zan miki kishiya badan kin gaza min ba ko kina da wani aibu, a’a ba haka bane duk abunda namiji yake nema wajen matarsa to nikam babu abunda baki min ba na samu jin daɗi da farin ciki marar misaltuwa a gareki, kawai zan ƙara Aure ne domin Soyayya ba don gazawar kiba, kimin uzuri ki fahimce ni, akan wannan Auren da zan ƙara, Mustafa ya shigo gidan nan ne cikin ɓacin rai badan komai ba, sai dan takaicin da yake ji Cewa nine wanda nayi nasarar samun Indo bashi ba, ma’ana ni aka yiwa baiko da Indo har Daddy ya bayar da kuɗin sadaki, kuma Aure bazai wuce nan da wata huɗu ba, kinji labarin.”

Ajiyar Zuciya HASINA ta sauƙe tana murmurshi ta furta cewa.

” Alhamdulillah gaskiya nayi farin ciki sosai daya kasance mijina shine yayi nasarar samun ƙanwarsa a matsayin matar Aure nasan mijina mai Sa’a ne bai cika neman abu ya rasa ba, Indo ai mutumiyar kirki ce, gaskiya kayi sa’ar samun mata ta biyu, na kuma ji daɗi sosai domin kuwa ko ba komai ina son abunda mijina yake so taya hakan zai ɓata min rai, bayan kai ya faranta maka, ka sani cewa duk abunda yake farin ciki a wajen ka, to Tabbas nima abun farin ciki nane mussaman Indo wacce na mata farin sani wanda kuma nake da tabbacin cewa bazata taɓa cutar dani ba, na kuma ji daɗi da yabon da ka min nayi farin ciki sosai da zaka ƙara Aure badan na gaza maka ba, dole na fahimce ka MIJINA domin kuwa UBANGIJI shine ya halarta muku ƙara Aure, yace kuyi ɗaya, kuyi biyu kuyi Uku kuyi huɗu, amma idan zaku iya adalci, to me zai dameni nasan MIJINA mai adalci ne, Allah ya sanya Alkairi yasa ayi damu shine kawai fata na.”

Ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya, zuciyarta cike da kishin Indo sai dai tayi farin ciki da mijinta yayi nasarar samun Abunda yake so.

Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Habeeb, tare da wani mungun Soyayyar matar tasa da ta ƙara ninkuwa a cikin zuciyarsa tabbas wannan itace ake kira da mata ta gari.

” Tabbas ke abun alfahari ne a gare ni, bansan taya zan misalta miki irin farin cikin da naji ba, da kika fahimce ni har kika karɓi Abunda nake so da hanu biyu, Allah ya miki albarka.”

Da ameeen HASINA ta amsa kafin suka cigaba da zancen su, amma duk rabin hankalin Habeeb yana ga ɗan uwansa.

Babu sallama ya faɗa falon nasa, RAUDA na zaune cikin tashin hankali, na rashin kwanan da mijinta baiyi ba a gida, gashi idan ta kira layinsa baya ɗauka da har ta fara tunanin zuwa ta sanar da su Momy sai kuma taga shigowar sa yanzu cikin sauri ta miƙe da kyar kasancewar cikin nata ya fara tsufa tace.

” Ya Mustafa tun jiya hankalina yake tashe, na kasa bacci ina ka kwana Allah yasa dai lafiya.”

Tsuka Mustafa yaja yana ƙare mata kallo, cikin gatsali ya mayar mata da amsa daman da haushin sa ya shigo, dake ita ce ƙaramar katangar sa daɗin ƙetara yace mata.

” Inda kika aikeni naje ni uwata, dake zaman ki nake ai dole na sanar dake duk inda zani Uwata.”

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

 

*(Ummu Nasmah ce)*
[5/1, 9:31 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

________________________________________

*P*•••••••2️⃣5️⃣ ↗️ 2️⃣6️⃣

” Allah ya huci Zuciyar ka hankali nane ya tashi naga baka saba kwana a waje bane shiyasa hankalina ya tashi, amma Allah ya huci Zuciyar ka.”

Tsuka yaja ba tare da ya kalle ta ba ya shige cikin bedroom ɗinsa, zama RAUDA tayi zuciyarta na cunkushe duk da ta samu sauƙin Abunda Mustafa yake mata sosai amma har yanzu yakan mata wasu abubuwan da bata jin daɗin sa, tagumi tayi tana jinmamin halin da Mustafa, shi kuwa bayan ya shiga bedroom ɗin nasa kwanciya yayi tare da yin shiru damuwa na cinsa ya rasa ya zaiyi da Zuciyarsa babu abunda take masa sai suya, haka ya wuni kas cikin ɗaki har dare.

Washegari da safe Indo ta sauƙo ta yiwa Momy duk aikin da ta saba bayan ta gama aikin ne ta ɗaura breakfast, shima da ta gama ta jera a daining tana shiga bedroom ɗin ta Momy ta bi bayanta, ta samu waje gefan bed ɗinta ta zauna tare da cewa Indo, ta zauna za suyi Magana, zama Indo tayi tana fuskantar Momy, dubanta sosai Momy tayi kafin ta fara magana.

” INDO wai meyasa ke mayyace kam dole sai kin Auri ɗana ne, nace bana sonki na tsaneki amma ki dage dole sai kin haɗa jini dani, dan Allah na roƙeki ki fita daga harkar ƴaƴana kije ki sanar da Alhaji cewa kin fasa wannan auren, ni kuma na miki alƙawarin duk abunda kike so zan baki ko meye ne idan ma kuɗi kike buƙata ki faɗi ko nawa ne zan baki.”

Shuru Indo tayi tana al’ajabin ƙiyayyar da Momy take mata ta rasa me ta tare mata a duniya take gwada mata wannan baƙar ƙiyayyar kanta sunkuye tace.

” Ki gafarce ni Momy gaskiya bazan iya tunkarar Daddy da wannan maganar, amma Momy idan babu me zai hana shi ya Habeeb ki sanar dashi ya faɗawa Daddy ni na amince zan haƙura da Auren ƴaƴan ki Idan har hakan zaisa ki sassauta ƙiyayyata cikin zuciyarki, bana buƙatar komai daga gareki domin kuwa babu wani abun duniya da nake buƙata a wajen ku, idan banyi addu’a Allah ya hore min na baku ba Ni ai bazan yi burin karɓar naku ba, kiyi hkr Momy idan maganganu na sun ɓata miki rai iya gaskiya ta na sanar dake.”

Wani mungun kallo Momy take bin Indo dashi na tsana kafin cikin ɓacin rai tace.

” Lallai kin iya magana kam, kamar mutumiyar kirki, sai dai ki sani wannan daɗin bakin naki bazai yi tasiri a kaina ba, ni shawara na baki akan ki fita harkar ƴaƴana, amma tunda kinƙi ji to ki sani bazaki ƙi gani ba, domin kuwa bazan taɓa barin ki kiji daɗin Aure ba, muddun kika Auri ɗana.”

Tana gama faɗin haka ta tashi ta fice tana ƙwafa, hawaye ne ya ziraro daga idanun Indo, kafin ta goge ta kwanta ruf da ciki, ranar haka Indo taƙi fitowa falo domin kuwa itama yanzu ta fara jin Zafin Momy, ko ganinta bata son yi saboda tsantsar jin takaicin tsanar da Momy take gwada mata.

A haka rayuwar ta dinga tafiya yayin da Mustafa ya daina koda kallon inda Habeeb yake shi kuwa Habeeb duk sanda suka haɗu sai ya yiwa Mustafa Magana amma ko kallon sa Mustafa baya yi, Mamy kuwa kullum cikin ruɗar Momy take da wajen bokan ƙarya, haka ta dinga ɓatar da ita amma Momy ta kasa ganewa.

*********************************

Yau watan cikin RAUDA tara yayin da take cikin watan ta na haihuwa, sassafe ta shirya domin zuwa gida gaida Abbanta baida lafiya, Mustafa yana bedroom ɗinsa, kwance shima ba lafiyar bace dashi, dan harma ya ɗan rame, ciwon ƙirji ne yake yawan damunsa ga nauyi da ƙirjin yake masa yana kuma yawan yin tari bedroom ɗin nasa RAUDA ta shigo ta gaishe sa kafin tace.

” Ya Mustafa baka da lafiya ne.?”

Ɗago kansa Mustafa Yayi ya dubi RAUDA cikin sanyin Murya yace.

” Lafiya ta ƙalau babu abunda yake damu na me kika gani kinga alamun rashin lafiya a tattare dani ne.?”

Zama RAUDA tayi a gefan sa tace.

” Eh mana naga alamunka duk sun nuna kamar baka da lafiya, PLS ya Mustafa ka sanar dani me yake damunka, hankali na yana tashi idan na ganka cikin wani yanayi na gwammace ni na kasance cikin wannan halin kai ka Zauna cikin farin ciki, dan Allah ka sanar dani me yake damunka.”

Wani irin tausayin RAUDA ya kama Mustafa, ta na yawan damuwa idan ta gansa a cikin wani hali tana lura da duk wani lamuran sa, amma sai dai shi ya kasa bata farin ciki, bazai iya sanar da kowa Abunda yake ji cikin zuciyarsa ba, ya gammaci ya mutu ko zaiji sauƙin Abunda yake damunsa baya ƙaunar Allah ya nuna masa ranar da zaiga auren Habeeb da SHATUUN sa, gara kawai yaga mutuwar sa da yaga wannan auren, duban RAUDA yayi yace.

” Karfa ki damu babu abunda yake damuna, kiyi tafiyar ki kawai, ki gaishe da Abban nima zanzo na gaishe daga baya.”

Kaɗa kanta kawai RAUDA tayi badan ta yadda da Maganar Mustafa ba ta wuce abunta, bata juma da fita ba shima Mustafa ya fito yayi part ɗin Momy tana zaune ya sameta ta haɗa fuska, zama yayi yana cewa.

” Momy lafiya naga kamar ranki a ɓace.”

Tsuka taja tana cewa.

” Lafiya lau waɗannan yaran nake jira su sauƙo ƴan iska mayu tun ɗazu suka haura amma sunƙi fitowa ni so nake ma ta fito ta wuce ƙauyen nasu ko zan huta.”

” Wasu yara kuma Momy.?”

” Waye kuwa bayan Habeeb da wannan baƙar mayyar Indo, kasan yau zata bar garin nan zai kaita ƙauyen su, gobe idan ta koma jibi kuma za’a kai kayan Auren nasu bazata dawo ba sai an ɗaura Auren naji Daddyn ku yana cewa Habeeb ɗin ne zai kaita.”

Dam ƙirjin Mustafa ya buga wani mungun kishin Indo ne ya daki zuciyarsa, hankalin sa ya kasa kwanciya mussaman da Momy tace suna ɗaki su biyu da Habeeb, tari ne ya sarƙe Mustafa sosai yake tarin sanda idanunsa sukayi jajur, hanunsa yasa yana tare bakin sa, ɗago hanun nasa da zaiyi sai jini ya gani, saurin danƙe hanun nasa yayi kar Momy ta gani Hankalin ta ya tashi goge bakin nasa yayi da ɗaya hanun yana ƙara ɓoye hanun nasa, Momy saurin duban sa tayi tana cewa.

” Lafiya meya sameka yanzu? Tana buga masa bayan sa, ganin bai daina tarin ba ya sata tashi da sauri ta tafi ɗauko masa ruwa , ai kuwa Mustafa kamar wanda yake jira Momy ta tashi, shima ya tashi cikin sauri ya bar part ɗin, part ɗin su ya nufa ya faɗa cikin motar sa ya figeta da ƙarfi ya bar unguwar gabaki ɗaya, koda Momy ta dawo tasha mamakin rashin ganin sa inda ta barsa ƙwafa kawai tayi ta ajiye ruwan tana cewa.

” Oh ni a’ishatu yanzu na barka zaune anan kana tari yanzu kuma na dawo ban sameka ba, sai kace wani aljani, ko ina kuma yayi sai Allah.”

Ta ƙarasa maganar tana taɓe bakin ta

Tare suka sauƙo suna dariya, harda Zarah ma ashe suke cikin bedroom ɗin, Habeeb shine yake jan akwatin Indo, har suka sauƙo ƙasa, kusan tare suka fito da Daddy domin kuwa suna sauƙowa shima yana fitowa daga bedroom ɗin sa, murmurshi yayi yana tsokanar Indo.

” Yau dai ƴata ana murna za’a gida, naga bakin yaƙi rufuwa yau za’a ga Mama da Baba.”

Dariya sosai Indo tayi sai kuma idanunta suka ciko da hawaye tana cewa Daddy.

” Daddy ai dole nayi dariya, yanda na daɗe rabona da gida, sai dai kuma Daddy zuciyata sam babu daɗi sanda zan taho birni da *INNA* na taho sai dai kuma gashi yau zan koma ƙauye babu *INNA* ba kuma zanje can na ganta ba, hankalina yana tashi idan na tuno da wannan abun Daddy da wani ido zan iya kallon gidan Inna babu ita a ciki, Daddy……..”

Ringine ɗin wayar ta ne ya katseta tana duban wayar taga *SHARIFA* ce murmurshi Indo tayi tana goge hawayen fuskar ta tare da ɗaga wayar tana cewa.

” AUNTY Sharifa kin wuni lafiya.”

Daga can Sharifa tayi murmurshi tare da cewa.

” LAFIYA lau Indo, kwana biyu shuru matar ya Habeeb, shine Wato ko ki bani labarin cewa tsuntsun Soyayyar ya tashi daga kan ya Mustafa ya koma kan ya Habeeb, anya kuwa kin yiwa kanki adalci Indo Wanda kike so daban wanda kika zaɓa a matsayin miji daban, meyasa kika yanke wannan hukuncin.?”

Runtse idonta tayi tana murmushin dole tare da duban ya Habeeb da Daddy sannan tacewa Sharifa.

” AUNTY Sharifa Yanxu ina hanya ne zanje DASINA idan na ƙarasa insha Allah zan kira ki sai muyi Maganar.”

Daga can Sharifa tace

” Shikenan Allah ya kaiku lafiya, ki gaishe da Mama idan kin isa.”

 

” Shike nan zataji insha Allah ki gaishe min da Ummi idan na ƙarasa zaki haɗamu.”

” Zataji ” Sharifa tace tare da kashe wayar tana ganin tsantsar wautar Indo.

Daddy ne yakai dubansa ga Indo yace.

” Karki saka damuwar rashin Inna a zuciyarki, duk sanda kika tuno ta ki mata Addu’a, dukkan mai rai mamaci ne fatan mu Allah ya mata Rahma, gacan siyayyar da na miki nasa an haɗa miki a mota tare da na Habeeb wanda ya saya miki, idan kin ƙarasa zan kira ki, ki gaishe da mahaifan naki.”

” Zasuji insha Allah Daddy na gode Allah ya saka da Alkairi.”

Wajen Momy ta ƙarasa tare da sunkuyawa a gabanta tace.

” MOMY zan tafi gida kimin addu’a idan kuma akwai Abunda na miki ba dai-dai ba ki yafe min Saboda bani da tabbacin cewa zan dawo ko bazan dawo ba, saboda halin tafiya.”

Taɓe bakin ta Momy tayi tana mata kallon tsana da ƙiyayya kafin tace.

” Ni uwarki ce da zan miki addu’a, to bazanyi ba, idan kinga dama karki dawo idan kin tafi, ai dole ki roƙe ni gafara tunda kinsan kin cuceni kin liƙe min kin liƙewa ƴaƴana to wlh babu yafiya tsakanina dake, kawai ki rabu da ɗana sai mu Zauna lafiya idan kuma ba haka ba, Allah ya isa yanzu na fara ja miki ita.”

Sosai maganganun Momy suka yiwa indo zafi, hawaye ne suka ɗigo daga idanunta tasa hanu ta goge su sannan ta miƙe tsaye tare daya cewa Daddy na tafi
[5/7, 11:13 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

________________________________________

*P*•••••••2️⃣5️⃣ ↗️ 2️⃣6️⃣

” Allah ya huci Zuciyar ka hankali nane ya tashi naga baka saba kwana a waje bane shiyasa hankalina ya tashi, amma Allah ya huci Zuciyar ka.”

Tsuka yaja ba tare da ya kalle ta ba ya shige cikin bedroom ɗinsa, zama RAUDA tayi zuciyarta na cunkushe duk da ta samu sauƙin Abunda Mustafa yake mata sosai amma har yanzu yakan mata wasu abubuwan da bata jin daɗin sa, tagumi tayi tana jinmamin halin da Mustafa, shi kuwa bayan ya shiga bedroom ɗin nasa kwanciya yayi tare da yin shiru damuwa na cinsa ya rasa ya zaiyi da Zuciyarsa babu abunda take masa sai suya, haka ya wuni kas cikin ɗaki har dare.

Washegari da safe Indo ta sauƙo ta yiwa Momy duk aikin da ta saba bayan ta gama aikin ne ta ɗaura breakfast, shima da ta gama ta jera a daining tana shiga bedroom ɗin ta Momy ta bi bayanta, ta samu waje gefan bed ɗinta ta zauna tare da cewa Indo, ta zauna za suyi Magana, zama Indo tayi tana fuskantar Momy, dubanta sosai Momy tayi kafin ta fara magana.

” INDO wai meyasa ke mayyace kam dole sai kin Auri ɗana ne, nace bana sonki na tsaneki amma ki dage dole sai kin haɗa jini dani, dan Allah na roƙeki ki fita daga harkar ƴaƴana kije ki sanar da Alhaji cewa kin fasa wannan auren, ni kuma na miki alƙawarin duk abunda kike so zan baki ko meye ne idan ma kuɗi kike buƙata ki faɗi ko nawa ne zan baki.”

Shuru Indo tayi tana al’ajabin ƙiyayyar da Momy take mata ta rasa me ta tare mata a duniya take gwada mata wannan baƙar ƙiyayyar kanta sunkuye tace.

” Ki gafarce ni Momy gaskiya bazan iya tunkarar Daddy da wannan maganar, amma Momy idan babu me zai hana shi ya Habeeb ki sanar dashi ya faɗawa Daddy ni na amince zan haƙura da Auren ƴaƴan ki Idan har hakan zaisa ki sassauta ƙiyayyata cikin zuciyarki, bana buƙatar komai daga gareki domin kuwa babu wani abun duniya da nake buƙata a wajen ku, idan banyi addu’a Allah ya hore min na baku ba Ni ai bazan yi burin karɓar naku ba, kiyi hkr Momy idan maganganu na sun ɓata miki rai iya gaskiya ta na sanar dake.”

Wani mungun kallo Momy take bin Indo dashi na tsana kafin cikin ɓacin rai tace.

” Lallai kin iya magana kam, kamar mutumiyar kirki, sai dai ki sani wannan daɗin bakin naki bazai yi tasiri a kaina ba, ni shawara na baki akan ki fita harkar ƴaƴana, amma tunda kinƙi ji to ki sani bazaki ƙi gani ba, domin kuwa bazan taɓa barin ki kiji daɗin Aure ba, muddun kika Auri ɗana.”

Tana gama faɗin haka ta tashi ta fice tana ƙwafa, hawaye ne ya ziraro daga idanun Indo, kafin ta goge ta kwanta ruf da ciki, ranar haka Indo taƙi fitowa falo domin kuwa itama yanzu ta fara jin Zafin Momy, ko ganinta bata son yi saboda tsantsar jin takaicin tsanar da Momy take gwada mata.

A haka rayuwar ta dinga tafiya yayin da Mustafa ya daina koda kallon inda Habeeb yake shi kuwa Habeeb duk sanda suka haɗu sai ya yiwa Mustafa Magana amma ko kallon sa Mustafa baya yi, Mamy kuwa kullum cikin ruɗar Momy take da wajen bokan ƙarya, haka ta dinga ɓatar da ita amma Momy ta kasa ganewa.

*********************************

Yau watan cikin RAUDA tara yayin da take cikin watan ta na haihuwa, sassafe ta shirya domin zuwa gida gaida Abbanta baida lafiya, Mustafa yana bedroom ɗinsa, kwance shima ba lafiyar bace dashi, dan harma ya ɗan rame, ciwon ƙirji ne yake yawan damunsa ga nauyi da ƙirjin yake masa yana kuma yawan yin tari bedroom ɗin nasa RAUDA ta shigo ta gaishe sa kafin tace.

” Ya Mustafa baka da lafiya ne.?”

Ɗago kansa Mustafa Yayi ya dubi RAUDA cikin sanyin Murya yace.

” Lafiya ta ƙalau babu abunda yake damu na me kika gani kinga alamun rashin lafiya a tattare dani ne.?”

Zama RAUDA tayi a gefan sa tace.

” Eh mana naga alamunka duk sun nuna kamar baka da lafiya, PLS ya Mustafa ka sanar dani me yake damunka, hankali na yana tashi idan na ganka cikin wani yanayi na gwammace ni na kasance cikin wannan halin kai ka Zauna cikin farin ciki, dan Allah ka sanar dani me yake damunka.”

Wani irin tausayin RAUDA ya kama Mustafa, ta na yawan damuwa idan ta gansa a cikin wani hali tana lura da duk wani lamuran sa, amma sai dai shi ya kasa bata farin ciki, bazai iya sanar da kowa Abunda yake ji cikin zuciyarsa ba, ya gammaci ya mutu ko zaiji sauƙin Abunda yake damunsa baya ƙaunar Allah ya nuna masa ranar da zaiga auren Habeeb da SHATUUN sa, gara kawai yaga mutuwar sa da yaga wannan auren, duban RAUDA yayi yace.

” Karfa ki damu babu abunda yake damuna, kiyi tafiyar ki kawai, ki gaishe da Abban nima zanzo na gaishe daga baya.”

Kaɗa kanta kawai RAUDA tayi badan ta yadda da Maganar Mustafa ba ta wuce abunta, bata juma da fita ba shima Mustafa ya fito yayi part ɗin Momy tana zaune ya sameta ta haɗa fuska, zama yayi yana cewa.

” Momy lafiya naga kamar ranki a ɓace.”

Tsuka taja tana cewa.

” Lafiya lau waɗannan yaran nake jira su sauƙo ƴan iska mayu tun ɗazu suka haura amma sunƙi fitowa ni so nake ma ta fito ta wuce ƙauyen nasu ko zan huta.”

” Wasu yara kuma Momy.?”

” Waye kuwa bayan Habeeb da wannan baƙar mayyar Indo, kasan yau zata bar garin nan zai kaita ƙauyen su, gobe idan ta koma jibi kuma za’a kai kayan Auren nasu bazata dawo ba sai an ɗaura Auren naji Daddyn ku yana cewa Habeeb ɗin ne zai kaita.”

Dam ƙirjin Mustafa ya buga wani mungun kishin Indo ne ya daki zuciyarsa, hankalin sa ya kasa kwanciya mussaman da Momy tace suna ɗaki su biyu da Habeeb, tari ne ya sarƙe Mustafa sosai yake tarin sanda idanunsa sukayi jajur, hanunsa yasa yana tare bakin sa, ɗago hanun nasa da zaiyi sai jini ya gani, saurin danƙe hanun nasa yayi kar Momy ta gani Hankalin ta ya tashi goge bakin nasa yayi da ɗaya hanun yana ƙara ɓoye hanun nasa, Momy saurin duban sa tayi tana cewa.

” Lafiya meya sameka yanzu? Tana buga masa bayan sa, ganin bai daina tarin ba ya sata tashi da sauri ta tafi ɗauko masa ruwa , ai kuwa Mustafa kamar wanda yake jira Momy ta tashi, shima ya tashi cikin sauri ya bar part ɗin, part ɗin su ya nufa ya faɗa cikin motar sa ya figeta da ƙarfi ya bar unguwar gabaki ɗaya, koda Momy ta dawo tasha mamakin rashin ganin sa inda ta barsa ƙwafa kawai tayi ta ajiye ruwan tana cewa.

” Oh ni a’ishatu yanzu na barka zaune anan kana tari yanzu kuma na dawo ban sameka ba, sai kace wani aljani, ko ina kuma yayi sai Allah.”

Ta ƙarasa maganar tana taɓe bakin ta

Tare suka sauƙo suna dariya, harda Zarah ma ashe suke cikin bedroom ɗin, Habeeb shine yake jan akwatin Indo, har suka sauƙo ƙasa, kusan tare suka fito da Daddy domin kuwa suna sauƙowa shima yana fitowa daga bedroom ɗin sa, murmurshi yayi yana tsokanar Indo.

” Yau dai ƴata ana murna za’a gida, naga bakin yaƙi rufuwa yau za’a ga Mama da Baba.”

Dariya sosai Indo tayi sai kuma idanunta suka ciko da hawaye tana cewa Daddy.

” Daddy ai dole nayi dariya, yanda na daɗe rabona da gida, sai dai kuma Daddy zuciyata sam babu daɗi sanda zan taho birni da *INNA* na taho sai dai kuma gashi yau zan koma ƙauye babu *INNA* ba kuma zanje can na ganta ba, hankalina yana tashi idan na tuno da wannan abun Daddy da wani ido zan iya kallon gidan Inna babu ita a ciki, Daddy……..”

Ringine ɗin wayar ta ne ya katseta tana duban wayar taga *SHARIFA* ce murmurshi Indo tayi tana goge hawayen fuskar ta tare da ɗaga wayar tana cewa.

” AUNTY Sharifa kin wuni lafiya.”

Daga can Sharifa tayi murmurshi tare da cewa.

” LAFIYA lau Indo, kwana biyu shuru matar ya Habeeb, shine Wato ko ki bani labarin cewa tsuntsun Soyayyar ya tashi daga kan ya Mustafa ya koma kan ya Habeeb, anya kuwa kin yiwa kanki adalci Indo Wanda kike so daban wanda kika zaɓa a matsayin miji daban, meyasa kika yanke wannan hukuncin.?”

Runtse idonta tayi tana murmushin dole tare da duban ya Habeeb da Daddy sannan tacewa Sharifa.

” AUNTY Sharifa Yanxu ina hanya ne zanje DASINA idan na ƙarasa insha Allah zan kira ki sai muyi Maganar.”

Daga can Sharifa tace

” Shikenan Allah ya kaiku lafiya, ki gaishe da Mama idan kin isa.”

 

” Shike nan zataji insha Allah ki gaishe min da Ummi idan na ƙarasa zaki haɗamu.”

” Zataji ” Sharifa tace tare da kashe wayar tana ganin tsantsar wautar Indo.

Daddy ne yakai dubansa ga Indo yace.

” Karki saka damuwar rashin Inna a zuciyarki, duk sanda kika tuno ta ki mata Addu’a, dukkan mai rai mamaci ne fatan mu Allah ya mata Rahma, gacan siyayyar da na miki nasa an haɗa miki a mota tare da na Habeeb wanda ya saya miki, idan kin ƙarasa zan kira ki, ki gaishe da mahaifan naki.”

” Zasuji insha Allah Daddy na gode Allah ya saka da Alkairi.”

Wajen Momy ta ƙarasa tare da sunkuyawa a gabanta tace.

” MOMY zan tafi gida kimin addu’a idan kuma akwai Abunda na miki ba dai-dai ba ki yafe min Saboda bani da tabbacin cewa zan dawo ko bazan dawo ba, saboda halin tafiya.”

Taɓe bakin ta Momy tayi tana mata kallon tsana da ƙiyayya kafin tace.

” Ni uwarki ce da zan miki addu’a, to bazanyi ba, idan kinga dama karki dawo idan kin tafi, ai dole ki roƙe ni gafara tunda kinsan kin cuceni kin liƙe min kin liƙewa ƴaƴana to wlh babu yafiya tsakanina dake, kawai ki rabu da ɗana sai mu Zauna lafiya idan kuma ba haka ba, Allah ya isa yanzu na fara ja miki ita.”

Sosai maganganun Momy suka yiwa indo zafi, hawaye ne suka ɗigo daga idanunta tasa hanu ta goge su sannan ta miƙe tsaye tare daya cewa Daddy “na tafi Daddy Allah ya sada mu da Alkairin sa”

Gabaki ɗayan su ransu baiyi daɗi ba game da maganganun da Momy ta sanarwa Indo SOSAI maganganun suka yi masa zafi, murmushin takaici Daddy Yayi yana duban Momy cikin ɓacin rai bai kuma cemata komai ba, ya nunawa su Indo hanya alamun su tafi, tafiyar kuwa sukayi a harabar gidan suka ci karo da Hasina itama sukayi Sallama, Indo harta shiga cikin motar sai kuma Mustafa ya faɗo mata cikin zuciryata, ji tayi bazata iya tafiya ba tare da ta gansa ba, duban Habeeb tayi tace.

” Ya Habeeb na manta ban samu nayi Sallama da Aunty RAUDA ba, please dan Allah kumin afuwa naje na mata Sallama yanzu zan fito mu tafi.”

Habeeb bai kawo komai a cikin ransa ba, ya amsa mata da to, ita kuwa Zahra sarai ta harbo jirgin Indo mustafa kawai take buƙatar gani ta fake da RAUDA kaɗa kanta kawai Zahra tayi tare da kwantar da kanta a sit ɗin motar, ficewa Indo tayi daga cikin motar ta doshi part ɗin Mustafa, sai dai kash a kulle ta samu part ɗin, sosai taji haushin hakan, zamewa tayi a ƙasa ta saki wani kuka mai cin rai sanda tayi ya isheta kafin ta tashi ta goge fuskar ta, ta dawo motar, zama tayi tare da cewa.

” Zamu iya tafiya.”

Habeeb ne yace.

” Lafiya kuwa HABIBTY na naga kamar mood ɗinki ya sauya lafiya kuwa.?”

Murmushin ƙarfin hali tayi tace.

” Babu komai fa, muje kawai.”

Kaɗa kansa yayi sannan yaja motar suka bar gidan, Zahra taɓe bakinta tayi ba tare da tace musu komai ba, har suka isa govt hause ɗin suka sauƙe Zahra, Sallama sukayi tare da alƙawarin cewa zata zo daf da bikin idan anyi biki ma dawo tare.”

Cikin awa biyu suka Isa cikin garin DASINA sosai Indo take ƙarewa garin nasu kallo tana ganin sauye-sauye sosai ba kamar yadda ta tafi tabar ƙauyen ba, har suka yi parking a ƙofar gidan nasu, fitowa Indo tayi karaf idanunta suka sauƙa a ƙofar gidan INNA, wani iri taji cikin zuciyarta, yau gata cikin ƙauyen DASINA babu INNA cikin ta, ƙofar gidan nasu ta ƙarasa su Baba dukansu suna Zaune a rumfar ƙofar gidan, ƙarasawa sukayi wajen nasu tare da sunkuyawa suka gaishe su Mlm Abubakar ne yace.

” *INDO* kece haka na kasa gane ki sai da kikayi Magana, um um kinga yanda kikayi jawur dake kuwa sai kace baturiya.”

Murmushi Indo tayi shima Habeeb murmushin yayi, Baba ne yace.

” Mlm Abubakar ai dole tayi jawur, gidan Mlm Haruna fa take, kasan kuma ƴar taka da son jin daɗi.”

Dukan su dariya sukayi kafin INDO tace.

” Kuji Baba da wani zance, waye baya son jin daɗi, ai Baba ko kaine ka samu jin daɗi, ina ga yaro ƙarami zaka dawo wannan furfurar duk sai an nemeta an rasata.”

Ta ƙarasa maganar tana dariya cikin salon zolaya, dariya Baba Yayi shida Mlm Abubakar, yana cewa.

” Kaji ja’irar yarinya ko, Muhammadu Habibu, maza ka ƙarasa ka samu kasha ruwa ka huta ka rabu da wannan ja’irar yarinyar.”

Dariya sukayi Indo ta tashi ta musu jagora har cikin gidan nasu da Sallama suka shiga Mama tana sunkuye tana shara taji sallamar Indo ɗago kanta Mama tayi cikin fara’a da gudu Indo ta ƙarasa ta rungume Mama tana cewa.

” Mamana sannu da aiki nayi missing ɗinki.”

Cikin farin cikin ganin ƴarta ta Mama tace.

” INDO yau kece tafe cikin ƙauyen nan, sannu da hanya, kunsha tafiya.”

Sake Mama Indo tayi tana dariya tace.

” Nine Mama, tun jiya na kasa bacci Allah Allah nake gari ya waye mu taho na ganku mama ina ya Tanimu yake?.”

” Tanimu yaje cin kasuwar Ɓaure sai dare zai dawo, ina ga zai kai bayan Sallar isha’i.”

” Allah ya dawo dashi lafiya Mama.”

Sai yanzu Mama ta lura da Habeeb dake tsaye a gefe yana kallon su cikin burgewa sosai suka basa sha’awa yanda yaga soyayya mai ƙarfi tsakanin su, murmurshi Mama tayi tace.

” Wai daman da Habibu kuke tafe ne baki sanar dani ba muka barsa a tsaye, bismillah Habibu ga taburma ka Zauna.”

Zama Habeeb yayi yana murmurshi tare da cewa.

” Ba komai Mama kinsan ƴartaki Sarkin zumuɗi, dole ta manta dani tunda yau anga Baba da Mama amma dai zan rama nima.”

Cikin dariya INDO tace.

“Ai kuwa sai dai ka rame badai ka rama ba, domin nasan ba iyawa zakayi ba, Kuma kasan dai ni bana biyan bashi kona ɗauka, sai dai mutum yayi haƙuri.”

” Au haka kikace, kinji ko Mama wai bazan iya ramawa ba, to bari mu zuba mu gani ko Mama.?”

Murmushi Mama tayi tana ƙoƙarin tashi tare da cewa.

” Kunga ni dai babu ruwana cikin lamarin ku domin kuwa kunfi kusa, kona shiga tsakanin ku Anjuma kaɗan zaku bani kunya, bari naje na kawo muku ruwa tukunna kusha, idan yaso sai ku ɗaura daga inda kuka tsaya.”

Sannan ta shige ta ɗebo musu ruwa a randar ƙasa, bayan sunsha ruwan sun huta ne Mama ta kawo musu abinci tuwan dawa ne miyar ɗanyar kuɓewa tasha manshanu tare da nama, SOSAI Habeeb yaci abincin kasancewar sa mutum mai son Abincin gargajiya da la’asar lis Habeeb yasa yara suka shigo da kayan tsarabar da sukazo dashi, lami kuwa jin labarin zuwan Indo yasata zuwa gidan da la’asar ɗin tare da goyon ta a bayanta sosai Indo taji daɗin ganin aminiyar tata ƙawar tsokana, duban Lami Indo tayi tana cewa.

” Oh Lami kece haka, an daɗe ba’a gamu ba, wai ya na ganki da goyo ne, YARINYAR waye kika goyo.?”

Sauƙe goyon Lami tayi ta dawo da ita saman cinyar ta, tana duban Indo kafin tace.

” Ke Indo kinga kuwa yanda kikayi jawur dake, kinyi kyau, har wani ɗauke Ido kike, dubi fa yanda kika dawo wata ƴar gaye dake, sai kace ba wannan INDOn dana sani ba mai jiki duk dauɗa gaskiya ƙawata birni ya karɓe ki.”

Tsuka Indo taja tana cewa.

” Bana son walaƙanci Lami ya kike tuno da Abunda ya riga ya wuce, kema fa kince birni kinga kuwa ai dole na sanja nidai tambayar ki nayi wannan ɗin ƴar waye ne.?”

” Ƴata ce wai baki san nayi Aure bane, to kinga bana shekara ta biyu da Aure, nayi zaton ai kinji labari.”

” A’a banji labari ba wlh, yanzu wannan ƴarki ce Lami, ikon Allah nima fa yanzu da ammin Aure ko, ina su Hansai da Zainabu.?”

” Hansai ma tayi Aure shekaran jiya ma ta HAIHU tana can tsallaken ɗan masari, ita ma Zainabu tayi Aure amma ta dawo gida bata da lafiya wai Mayu sun kamata, ɗazun nan ma naje na gaishe ta, tana jin jiki gaskiya.”

Ajiyar Zuciya Indo ta sauƙe tare da cewa.

” Ikon Allah dukkan ku da ƴaƴan ku, to Allah ya raya ita kuma Zainabu Allah ya bata Lafiya, yanzu dare yayi da munje mun gaishe ta, amma insha Allah gobe idan na fita zan biya na dubata.”

Allah ya kaimu Lami ta furta sun juma suna hira kafin Lami ta koma gidan ta da sakaliyar la’asar Habeeb kuwa da daddare ya shigo cikin gidan ya zauna hira da Indo da Mama kasancewar shi Baba yana waje bai shigo ba, suna tsaka da hirar Tanimu yayi sallama ɗaure da buhu a kafaɗar sa, a gefe ya ajiye buhun yana sake wata sallamar jin kamar basu jisa ba, Habeeb da Mama ne suka amsa, Indo kuwa tashi tayi ta nufi Ya Tanimu da gudu ta faɗa jikin sa tana cewa.

” Oyoyo ya Tanimu sannu da dawowa tun ɗazu nake tsumayar dawowarka.?”

Murmushi Tanimu yayi yana girgiza kai tare da cewa.

” Oh ni Tanimu wato dai shi mai hali baya fasa halinsa, har yanzu dai kina nan da shiriritar ki, baki daina ba.?”

Tura bakinta Indo tayi tana cewa, kai ya Tanimu ka jika da wata magana, duk wannan hankalin da nayi shine zaka wani cemin shiriritacciya, wlh nayi Hankali, ko ya Habeeb.?”

Ta ƙarasa maganar tana kallon ya Habeeb murmushi sosai Habeeb yayi kafin yace.

” Ai kuwa yanzu Indo tayi cikakkiyar Hankali dan kuwa ba waccar Indo da ka sani a baya bane ta ƙauye wannan *INDON BIRNI CE* wacce Hankali da tunani ya wadace ta, kuma Mama ma ta shaida da hakan.”

Dukan su dariya sukayi ya Tanimu ya shige ya ɗibi ruwa a bokiti ya shiga wanka, bayan ya fito ne ya zauna kusa dashi Mama ta kawo masa abincin sa, kafin suka shiga hiran yaushe gamo, Tanimu sosai yaji daɗin yanda yaga ƙanwar tasa fes da ita babu alamar wahala a tattare da ita sannan Abunda yafi masa daɗi ganin yanda Indo tayi sanyi hankali yazo jikin ta, sun juma suna hira kafin Habeeb ya musu sallama tare da cewa zaije gidan INNA ya kwana a ɗakin su, da farko Mama bata yadda yaje can ba a cewar ta kawai su kwana tare da Tanimu a ɗakin sa, amma sam Habeeb yaƙi, babu yanda Mama ta iya haka ta haƙura ta ƙyalesa ya tafi can ɗin, ya barsu zaune suna hira a wajen, Baba ma da ya shigo wani sabon babin hiran suka ɗaura.

Habeeb tunda ya shiga cikin gidan yake bin ɗakin Inna da kallo, yana tuno rayuwar da sukayi da ita, idanunsa ne suka ciko da hawaye yasa hanu ya goge tare da ƙara kai dubansa da ɗakinta dake kulle ɗakin su da suke sauƙa ya buɗe duk yayi ƙura, sanda ya gyara sosai ya share ko ina, wanda yasan da INNA tana nan bazai taɓa samun ɗakin da ƙura ba, fes zai samesa, fitowa yayi ya nufi randar ƙasar tata, da niyar ɗiban Ruwa yayi wanka, a bushe randar take babu ɗigon Ruwa a cikin ta, dole ta sashi ajiye bokitin ya koma ɗaki yana tunanin INNA, ya daɗe cikin takurar rashin wanka wanda ya zamo masa jiki baya iya kwanciya sai yayi sa, wayar sa ya jawo tare da kiran Daddy ya shaida masa sun isa lafiya insha Allah shima gobe zai juyo, kafin ya katse kiran ya kira Mustafa kusan six miss call mustafa baiyi picking call ɗin ba, shuru Habeeb yayi yana tunanin yanda ɗan uwan nasa yake son lalata musu ZUMUNCIN su da ƙarfin tsiya, ya rasa ya zaiyi Mustafa ya fahimce sa, ya tsani gabar da yake yi dashi yana cikin tunanin ne kiran HASINA ya shigo wayar sa ɗagawa yayi yana murmurshi sun kusa raba dare suna hira kafin ya kashe wayar ya kwanta.

 

**********************************

Mustafa kuwa titi ya harba ba tare daya san inda zashi ba zuciyarsa ce kawai take masa tafarfasa a yanzu kam ya yanke hukuncin cewa bazai sake komawa cikin gidan su ba, bazai iya kallon baƙin ciki ba, yana gani ɗan uwansa daya fi so a rayuwarsa ya ci amanar sa, wacce yake so Itama ta kasa fahimtar sa, ta juya masa baya, Daddy shima ya nuna masa banbanci tsakanin sa da Habeeb ya fifita Habeeb fiye dashi, ita kuma kwatakwata bata son farin cikin sa, taya zai cigaba da zama cikin mutanen da basa ƙaunar farin cikin sa, ya gwammace yaje yayi rayuwarsa shi kaɗai ba tare da kowa ba, kafin Allah yayi ikonsa a kansa dan yasan ba lallai bane ya ƙara Rayuwa mai tsayi a cikin wannan duniyar mai cike da ƙalubale a garesa, da wannan tunanin Mustafa ya isa Abnur hotel, ɗaki ya kama sannan ya dawo parking space ya bawa mai gadin hotel ɗin umarnin cewa a rufe masa motar sa da tenpol, haka kuma akayi, ɗakin Mustafa ya shiga tare da zama ya riƙe kansa dake barazanar barin jikin sa, ya rasa ya zaiyi da ransa kwanciyar hankali ya ƙaurace masa, bashi da wata nutsuwa kullum cikin tunaninta yake, ta kasa fita a zuciyarsa, baƙin ciki ya masa yawa da ƙarfi ya riƙe kansa yana runtse IDANUNSA, a daren ranar duk yacce yaso bacci ya ɗauke sa ya gagara, shawarin Kamal ne ya faɗo masa cikin rai waya ya ɗauka tare da dannawa Kamal kira bayan ya ɗauka ne yake tambayar sa, wani irin ƙwaya ranar yasa aka basa, murmurshi Kamal Yayi tare da sanar dashi sunan ƙwayar, kashe wayar gabaki ɗaya Mustafa Yayi sannan ya ɗauki wayar hotel ɗin dake cikin bedroom ɗin, ma’aikatan ya kira tare da bada umarnin cewa a nemo masa ƙwayar a kawo masa cikin mintuna kaɗan kuwa aka kawo masa tare da Pepsi karɓa Yayi ya jefa kwayar a cikin Pepsi girgizawa Yayi sannan ya ɓalle murfin ya kafa a bakin sa bai ɗaga daga bakin nasa ba sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da gorar gefe yana dafe kansa baifi 30 minute ba kuwa yaji ɗakin yana juya masa cikin wannan halin mayen bacci ya ɗebe sa, sosai yayi baccin shine bai farka ba sai 11am da salati a bakin sa ya furta yana duban agogon ɗakin, da sauri ya miƙe yana mamakin baccin da yayi, wani irin bacci yayi haka harya makara bai tashi yayi sallar asuba ba, tollet ya faɗa yana riƙe da kansa dake masa nauyi, alwala kawai ya ɗauro ya fito ba tare da ya tsaya wanka ba da Astagfurullah har ya ɗauki sallaya ya tada Sallah bayan ya idar ne yayi addu’oin sa, yana roƙar UBANGIJI daya mutu ya huta da baƙin cikin dake damunsa bayan ya gama addu’oin ne kuma ta faɗo masa cikin zuciyarsa, wayarsa ya jawo ya kunna tare da kulle layikansa ya sakasu a jirgi yanda kiran kowa bazai shigo masa ba, pic ɗin ta ya ƙurawa ido dake saman screen ɗin wayar tasa, hoton ta ne tun tana ƙauye, wanda Habeeb ya taɓa turo masa wani sonta ne yake ƙara fisgarsa, hawaye ne suka gangaro masa saman fuskarsa, goge hawayen yayi tare da jingina kansa jikin bango, wankan ma ji yake bazai iya ba, yana cikin wannan halin ne yaji ana masa Nocking ɗin ƙofa ko bai sani ba yasan ma’aikatan hotel ɗin ne, daga inda yake cikin nauyin Murya yace.

” Waye ne?”

Daga bakin ƙofar mahaukacin yace.

” Ma’aikacin hotel ɗinne.”

” Me kuke buƙata?” Ya jefa masa tambaya.

” Breakfast ne daman muke so muji me kake bukata, sannan kuma muna son zamu gyara bedroom ɗin.?”

Cikin gajiya da maganar Mustafa yace masa.

” Kaje kawai bana buƙatar ko ɗaya yanzu idan ina buƙata zan kira ku, amma yanzu kam bani da bukata.”

” Okey” ya furta tare da barin wajen.”

Cigaba da tunanin sa Mustafa yayi shi yanzu Abunda yafi damunsa ma shine jinin da yake gani idan yayi tari ga wani zafi da ƙirjin sa yake masa ƙwayoyin da aka kawo masa ya ɗauka tare da ɗaukar ɗaya ya je frich ya ɗauko ruwa ya wurga ƙwayar a bakin sa domin gani yake kamar ƙwayar tana rage masa damuwar haka Mustafa ya wuni cikin maye.

RAUDA hankalin ta a matukar tashe yake tun daren jiya ta kira numbobin wayar sa yafi a ƙirga switch Off ake ce mata, koda gari ya waye a cikin wannan damuwar suka shirya breakfast ita da Mustafa a tunaninta idan gari yayi haske zai dawo amma ina shuru kake ji wai Mlm yaci shirwa babu Mustafa babu labarin sa, ƙara kiran layinsa tayi har yanzu dai switch Off, iya tashin hankali RAUDA ta shigesa, sai tayi yunƙurin tashi taje ta sanarwar su momy sai ts fasa ta koma ta zauna tana tsoro karta sanar musu kuma idan ya dawo yaci mutuncin ta yace ta haɗa sa da iyayen sa, dole yasa RAUDA ta hakura ta zauna cikin damuwa da tashin hankali, ita Abunda yafi ɗaga mata hankali ma numbobin wayar sa da suke rufe, hankalin RAUDA bai ƙara tashi ba sai da taga 11pm babu Mustafa babu labarin sa, wannan daren haka RAUDA ta kwana cikin tashin hankali, bacci kuwa gagarar ta yayi.”

Habeeb kuwa tun 9pm ya shigo cikin gari Ganin kamar dare yayi shiya hanasa shiga wajen momy gara ya bari kawai sai da safe.

Habeeb daga masallaci bai koma part ɗinsa ba yayi na Momy tana lazimi ya sameta a bedroom ɗinta zama yayi ya jirata harta gama sannan ya gaisheta babu yabo babu fallasa Momy ta amsa bata Kuma tambaye sa ya dawo lafiya ba shima bai damu ba domin kuwa yasan Halin mahaifiyar sa mussaman ma idan akan abinda ya shafi Indo ne.

Suna zaune RAUDA ta shigo tana kuka, jikin Momy ta faɗa ta ƙara sakin kuka, dubanta Momy tayi tana cewa.

” Subhanallah RAUDA me yake faruwa ne haka na ganki cikin tashin hankali sai famar rera kuka kike, kuma kisan cewa mace mai ciki bata son damuwa.”?

Cikin kukan tace.

” Ya mustafa Momy ya Mustafa ne.”

Zabura Momy tayi tare da cewa.

” Mustafa kuma, me Mustafan ya miki faɗa kukayi ne dashi.?”

” A’a Momy ba faɗa mukayi ba, tun shekaran jiya, baya gida Momy idan na kira layinsa baya tafiya yau kwanan sa biyu kenan baya gidan Momy Hankali na yana tashe.”

A zabure Momy ta miƙe tsaye cikin tashin hankali tace

” What kwanan Mustafa biyu baya gida, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un to ina yake me yake faruwa dashi na shiga Uku ni A’isha ina dana ya shiga, Allah ka rufa min asiri na kasa yana halin lafiya.”

Habeeb shima cikin tashin hankali ya miƙe tsaye tare da cewa.

 

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻

Ummu Nasmah ce
[5/9, 2:41 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••2️⃣7️⃣ ↗️ 2️⃣8️⃣

” Yanzu ke RAUDA kwanan Mutum biyu baya gida amma shine kika zauna kikayi shuru baki sanar ba tuntuni, wannan kuskure ne.”

Cikin kuka RAUDA tace.

” Ya Habeeb tun jiya naso nazo na sanar sai dai kuma ina tsoro ne karya dawo yamin faɗa yace na haɗasa da iyayen sa, shiyasa ban faɗa ba amma ina cikin tashin hankali nima Momy.”

MOMY cikin faɗan itama tace.

” Faɗan banza faɗan wofi sai me idan ya miki faɗa dukanki zaiyi, gashi yanzu bamu san wani hali yake ciki ba.”

 

Habeeb wayar sa ya ciro ya kira layin Mustafa, amma Switch Off.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un Momy layin sa baya shiga.”

Hawaye ne ya zubo a fuskar Momy cikin sauri ta sauka kasa suma binta sukayi cikin sauri bedroom ɗin Daddy ta faɗa cikin tashin hankali Daddy dake zaune yana danna loptop dinsa ne ya dago kansa ya kallesu tare da cewa.

” Lafiya kuka shigo min a firgice.?”

Cikin tashin hankali Momy tace.

” Ina lafiya kuwa Alhaji Tun jiya babu Mustafa babu labarin sa kwanan sa biyu baya gida.”

Ɗaga kai yayi ya kalli Momy yace.

“Yaro ne Mustafan da za’ace ya ɓata, ina ga kawai fushi yayi yabar muku gidan saboda bamu masa biyayya ba, mun basa Abunda yake so, dan haka karku ɗagawa kanku Hankali yanda ya tafi haka zai dawo.”

Wani irin kallon mamaki Momy take bin Daddy dashi kafin tace.

” Kasan Abunda kake faɗa kuwa Alhaji Mustafa shi waye da baza’a saceshi ba, karka manta da cewa munafukai sunyi yawa a cikin wannan ƙasar tamu ta Nigeria, ga ƴan kidnapping da sukayi yawa a duniya, ka daina wannan tunanin Alhaji kawai ka tashi mu san yanda zamuyi ɗana ya dawo gida.”

Murmushin manya Daddy yayi cikin kwanciyar hankali yace wa Momy.

” Babu inda zanje ba kuma zan ɗaga Hankali na ba, Saboda nasan Mustafa bai ɓata ba, babu abunda ya samesa dan haka kuma ku kwantar da hankalin ku, ku basa wasu lokutan zai dawo da kansa.”

Allah sarki tsakanin ɗa da uwa sai Allah barema yanda Momy take ƙaunar Mustafa fiye da dukkan ƴaƴan da ta haifa, kwatakwata Momy taƙi yadda da maganar Daddy haka shima Habeeb hankalinsa ya tashi domin kuwa baisan wani hali ɗan uwansa yake ciki ba mussaman idan yayi la’akari da yanda ƙasar ta lalace a hallakar da mutum ba wani abu bane sun ɗauki ran ɗan Adam tamkar kiyashi Momy ce ta dubi Daddy cikin ɓacin rai tace.

” Meye hujjar ka na cewa bai ɓata ba yana halin lafiya, idan kuma har da gaske kasan bai ɓata ba, to ina ɗana yake ina farin ciki na yake.?”

Murmushi Daddy Yayi tare da cewa.

” Ko ɗaya ni bansan Inda ɗanki yake ba, kawai dai zuciyata tana bani yana halin lafiya ne, kinga A’isha, leave me a long ina lissafi ne karki ɓata min lokacin.”

Cikin tsawa Momy ta buɗe bakinta zatayi Magana Habeeb yayi saurin tare ta da cewa.

” Dan Allah karki ce komai Momy ni zanje na nemo ɗan uwana, na miki alƙawari zan dawo dashi gida muddun yana raye kai koma ya mutu zan dawo da gawarsa gida, muje dan Allah.”

Ficewa tayi tana ƙwafa tare da cewa.

” Barema ɗana bai mutu ba yana raye insha Allah.”

Bayan sun dawo falo ne Habeeb ya dubi Momy yace.

 

” Zan fita Momy naje na fara binciko shi ki mana addu’a Allah yasa mu dace kuma yana halin lafiya.”

Da addu’ar kuwa Momy ta bishi, hankalin ta yana mungun tashe, ta rasa inda zata saka ranta, alƙawarin da suka yi da Mamy ma na komawa gun boka ta manta dashi tsabar ɓacin rai RAUDA kuwa kusa da ita ta zauna tana cigaba da kuka.

 

Habeeb duk inda yasan zai samu Mustafa yaje amma babu wani labari kowa cewa yake rabonsa dashi yau kwana Uku, hankalin Habeeb bai tashi ba sai yanzu duk yanda ya ɗauki abun ashe Zafin sa ya wuce nan tambayar da yake yiwa kansa shine ina Mustafa yaje, shin yana halin lafiya, shin maganar Daddy gaskiya ne fushi yayi akan INDO yabar gidan Tabbas idan haka ta faru bazai taɓa yafewa kansa ba, domin kuwa zai kasance shine silar shigar ɗan uwansa cikin wani hali da wannan tunanin ya dawo gida, ya kuma shirya ƙaryar da zaiyiwa Momy dan ganin hankalinta ya kwanta, a falo ya tarar dasu Zaune sunyi shuru suna jiran dawowar sa, kusa da Momy ya zauna tare da ƙaƙalo dariyar dole yace.

” Momy Mustafa fa yana cikin halin lafiya, kinsan yanayin aikinsu, yanzu da naje office dinsu ogansu yake sanar dani cewa, sun tafi wani ƙauye bincike, tafiyar ta taso musu ne cikin gaggawa, yace kuma ƙauyen da suke babu network shiyasa ba’a samun wayan su, akan ma yanzu zaizo ya sanar daku sai kuma na rigasa zuwa.”

Ajiyar Zuciya mai nauyi Momy ta sauƙe tare da cewa.

 

” Alhamdulillah! Sai yanzu naji Hankali na ya kwanta, amma kuma ai shi ogan nasu bai kyauta mana ba, kamata yayi ya sanar mana tuntuni amma tunda ansan inda yake ai arziki yayi, yanzu yaushe suka ce maka zai dawo.”

Shuru Habeeb yayi sai can yace.

 

” Gaskiya Momy sunce babu rana dan sunce binciken da aka tura su yana da matuƙar hatsari dole sai sunbi a hankali, amma may be suyi one month.”

Da Allah ya kaimu Momy ta furta sannan ne hankalinta ya kwanta ita kuwa RAUDA sam bata yarda da maganar Habeeb ba, zuciyarta taƙi amincewa da Maganar tasa tashi Habeeb yayi ya nufi bedroom ɗin Daddy da Sallama ya shiga Daddy amsa gefen Daddy ya zauna yayi shuru, ganin haka da Daddy yayi ya sashi rufe system ɗinsa ya maida dubansa ga Habeeb kafin yace.

” Habeeb akwai Magana ne naga ka nutsu.”

” Eh Daddy akwai Magana.”

” Okey ina sauraron ka meyake faruwa.?”

” Daddy akan maganar Mustafa ne, Daddy Mustafa fa baya kusa dan duk inda ya nasan yana zuwa Daddy naje baya nan, a duba lamarin nan Daddy yanzu haka ƙarya na yiwa Momy sannan hankalinta ya kwanta na ce mata daga Office ɗin su aka tura su wani ƙauye bincike kuma ƙauyen babu network shiyasa ba’a samun wayar sa, PLS Daddy.”

Murmushi Daddy Yayi kafin yace.

” Shikenan Habeeb zan saka amin bincike, insha Allah komai zaizo da sauƙi jiya munyi waya da Mlm Musa mahaifin Indo akan Maganar kai kayan da za’ayi mu tattauna dashi mun tsayar da Magana cewa babu maganar kai kayan Auren saboda wannan cutar data addabi duniya coronavirus, SO taron Auren ma nace masa bazai yiwu ayi taron biki ba, idan an ɗaura Aure kawai washegari mutum Uku ko hudu su kawo ta ya isa in suka ga ɗakinta sai su koma, kasan sati Uku kawai auren ya rage so sai kaje kayi gyare-gyaren daya zakayi idan kuma akwai taimakon da kake nema a waje na sai ka sanar dani insha Allah zan taimaka maka.”

Shuru Habeeb yayi sai can yace.

” Daddy me zai hana a dakatar da Maganar Auren yanzu mun tunkari abinda yake gaban mu, na neman ɗan uwana, Daddy bazan ji daɗin wannan auren ba, muddun ba’aji labarin ɗan uwana ba, pls Daddy a ɗaga wannan Aure har sai munga dawowar Mustafa.”

Haɗa fuska Daddy yayi cikin seriours ya yiwa Habeeb Magana.

” Babu Abunda zai dakatar da wannan auren sai dai idan mutuwa akayi bari kaji na sanar dakai ɓacewar Mustafa bazai sa na ɗaga wannan auren ba, zamu cigaba da neman sa duk da ina ji a jikina Mustafa bai ɓata ba, kawai yayi fushi ne akan ban basa Auren Indo ba, kafin ya tafi kwana nawa baizo ya gaishe ni ba, ka tashi ka tafi kaima ka bani waje.”

Tashi Habeeb yayi ya fita yana cewa Allah ya huci Zuciyarka Daddy, sannan ya fice a falo ya samu Momy ya mata Sallama sannan ya fita da sauri RAUDA tabi bayan sa tana cewa.

” Ya Habeeb kawai ka faɗawa Momy haka ne domin ka kwantar mata da hankali amma ina ji a jikina baka samu labarin Ya Mustafa ba pls dan Allah ya Habeeb ka nemo min MIJINA.”

Kallon tausayi Habeeb yake yiwa RAUDA kafin yace.

 

” Tabbas banji labarin Mustafa ba, amma ina nan ina bincike kuma Office ɗin su ma zasu taya mu bincike, sannan zanje police station na sanar karki damu insha Allah zai dawo gida cikin halin lafiya, ke dai ki cigaba da addu’a karki daga Hankalin ki komai zaizo ƙarshe.”

Share hawayen ta tayi tace

 

” Shike nan ya Habeeb insha Allah zan cigaba da addu’a, Allah ya fito min da mijina.”

” Ameeen” Habeeb yace sannan yace ta koma ɗakinta ta Zauna haka kuwa ta koma part ɗin ta amma har yanzu hawaye bai tsaya daga idanunta ba.

 

*****************************************

” Ke Indo wato ba zaki tashi ki je ki gaishe da Goggo ba ko, tunda kika zoki kinƙi fita ko nan da waje, yau kwanan ki Uku, ai ko ziyara kya fita, tunda dai sati Uku kacal zakiyi ki koma kuma da Auren ki maza ki tashi ki fita kije kiyi ziyara.”

Tura bakinta INDO tayi tace.

 

” Mama wlh bana son fita ne naga gidan INNA hankali na yana tashi mussaman idan na tuno Rayuwata da ita a baya Mama ina son INNA sosai naso ace INNA taga Aure na ta kaini gidan mijina da kanta sai gashi mutuwa ta hanata ganin Aure na bare har ta kaini ɗaki na.”

Ita kanta Mama sai da taji wani iri, yanda Indo ta shaƙu da INNA ko ita da ta haife ta basuyi wannan shaƙuwar ba, sai dai ya zasuyi dole suyi hkr domin kuwa shine kawai Abunda zasu iya, su mata Addu’a duban Indo tayi tace.

 

” Haƙuri zakiyi Indo bake kaɗai ba har muma muna jin zafin rashin INNA sai dai babu yanda muka iya dole muyi mu bita da addu’a shine kawai gatan da take buƙata yanzu a wajen dukkan masoyanta.”

” shike nan Mama zan shirya yanzu na tafi bari ma naje nayi wanka sai na fita.”

Cikin murmurshi Mama tace.

 

” Yauwa maza shirya kije, tsaraba kam na raba na bawa kowa, sai dai na innar hansai ne zan baki ki tafi mata dashi, koda Ibrahim zan haɗaku ya ɗauki buhun shinkafar ku tafi tare.”

Wanka Indo ta shiga bayan ta fito ne ta shirya ta ɗauki bag ɗin ta ta yiwa Mama sallama tare da cewa mama ta bawa Ibrahim tsarabar innar hansai ya kai musu daga baya.

Tunda ta fito Indo take ziyara duk gidan da ta sani da suna zuwa sai da ta shiga kowa yaga Indo sai yayi mamakin sauyawar da tayi, wasu kamma basa ganeta sai an musu bayani, tana hanyar ta ta zuwa gidan su Zainabu ne, ta hango kamar Garba abokin faɗanta, ƙarasawa wajen tayi ta tsaya, kusa dashi ba tare da tayi masa Sallama ne, zungure masa kai tayi tace.

 

” Kai Garba ɗan rainin wayo wai daman kana duniyar nan baka mutu ba.?”

Sai yanzu Garba ya gane Indo da tayi Magana yana dariya ya miƙe tsaye tare da cewa.

” Hegiya Indon INNA wai daman kece kika dawo balarabiya haka, aradu ban gane ki ba, kin dawo ƴar binni, nayi zaton ai bazaki ƙara dawowa ƙauyan nan ba, aradu tunda kika bar ƙauyen nan muka daina faɗa ahe daman kece mai jawo rigimar.”

Dariya sosai Indo tayi mussaman tuno tsiyar data tsula a cikin ƙauyen, tace.

” Allah sarki yarinta kace su mai gari an huta da kai ƙara Garba an tsula tsiya fah.”

Shima Garba dariyar yayi tare da cewa.

 

” Yanzu kam ai mun koma ga Allah, amma dai zaki wajen mai garin ki gaishe sa, naji ma ana cewa wai auren ki ya kusa, zaki Auri jikan INNA wannan ɗan gayen mai zuwa da mota, Allah sarki INNA, kamar ba azo duniya ba, Indo kema kinyi rashi aradu.”

Ciccikowa idon INDO yayi da hawaye jin Garba ya ambaci INNA, kafin tace.

” Eh saura sati Uku ma Auren, ai Wlh bazanje na gaishe da mai gari ba mutumin da baya sona ya tsaneni tun da can Allah bazanje ba.”

. dariya Garba yayi yana ƙara tuno rashin mutuncin Indo sun juma suna taɗin yaushe gamo kafin Indo ta wuce gidan su Zainabu, da Sallama ta shiga Goggo Hali dake tsugunne tana shara ne ta dago kanta tana amsa sallamar tare da bata wajen zama duk bata gane Indo ba sanda Indo tace.

” Sannu da aiki Goggo ya jikin Zainabu.?”

” Da sauƙin Goggo Hali ta amsa tana cewa, sai dai ban ganeki ba baiwar Allah.”

Murmushi sosai Indo tayi tace.

 

” Haba Goggo Hali yanzu har kin mantani, Indon INNA ce fa ta wajen Baba Musa.”

Salati Goggo Hali ta ɗauka tana tafa hanu tare da cewa.

 

” INDO wacce na sani fitinanniyar nan ƴar wajen Mairo kece haka kika koma jawur dake kamar ƴar Larabawa lallai kuwa kin samu duniya masha Allah.”

Dariya Indo tayi tana cewa.

 

” Ehh nice Goggo yanzu Goggo Hali har nayi sauyawar da baza’a gane niba.”

Ko kafin Goggo Hali ta maida mata da amsa tuni Zainabu ta fito daga ɗaki tana dariya ta zauna kusa da Indo tare da cewa.

” Mutanen birnin sai yau kika tuno damu kenan, tun shekaran jiya Lami tace min kinzo harma taje gidan naku.”

” Eh tazo mun juma ma, yanzu ma haka daga gidan nata nake, na samu ma bata nan wai gaisuwar mutuwa.”

” Ai Lami ba’a cika samunta a gida ba, yawon tsiya gareta, Indo munga tsaraba mun gode sosai Allah ya saka da alheri, ya haƙurin rashin INNA ban samu na miki ta’aziya ba gashi naji Lami na cewa kin dawo ne ayi bikin ki nan da sati Uku ko ki koma binni da Auren ki, Allah dai yasa da Mustafa za’ayi Auren.”

Wani irin bugawa ƙirjin Indo yayi jin an soso mata inda yake mata ƙyaiƙyayi kafin tace.

” Alhamdulillah mun godewa Allah, INNA kwana ya ƙare, eh Wlh biki na ya kusa amma ba da Ya Mustafa bane, da ɗan uwansa ne ya Habeeb.”

” Subhanallah kaddai ace har yanzu ya Mustafa baya sonki kece kaɗai kike haukar sonsa, amma gaskiya banji daɗin wannan labarin ba naso ace Mustafa kika aura, koda yake shi *AURE ƘADDARA CE* sai ku gama Soyayya da saurayi amma a ƙarshe sai ya kasance ba shi bane Allah ya ƙaddara mijin ka, Allah yasa haka shi yafi Alkairi.”

Murmushin takaici Indo tayi kafin ta amsa da ameeen tashi tayi tace

Kinga bari na samu na gudu kar dare yayi ina son na shiga na gaishe da innar hansai kafin na wuce gida da Goggo Hali sukayi Sallama har zauren gidan Zainabu ta raka Indo, Kafin Indo ta wuce gida sanda ta shiga gidan su hansai, INNA Lami kishiyar mahaifiyar hansai ta samu zaune tana ɓarar gyaɗa kusa da ita Indo ta zauna tana ɗaukar gyaɗar ta kai bakinta kafin tace.

” SANNU da aiki INNA lami.”

” Yau sannu” tare da dago kai tana kallon Indo lokaci ɗaya ta gane Indo bata yi mamakin ganinta ba domin taji labarin zuwanta yanzu ma kuwa Ibrahim ya fita ya kawo masu tsaraba, ” Su Indo gidan fitina yanzu kuwa kina fitinar ko kin tuba.”

Tuntsirewa da dariya Indo tayi kafin tace.

” Kai INNA Lami wato har yanzu baki manta da haura katangar banɗaki ba kenan, da ɗinma fa INNA Lami yarinta ce, kuma kinga ai yanzu na girma bazanyi ba, amma fa INNA Lami Ranar na tsula miki tsiya, Allah sarki yarinta mai daɗi.”

Ta ƙarasa maganar tana dariya,

” Ta yaya zan manta da wannan Ranar da kika kusa sani fita waje tsirara, ja’ira yarinta ko tsiya, gashi kuwa ai yanzu birni ya gyara ki,.”

Suna cikin hirar ne innar hansai ta fito gaisawa sukayi da ita sun juma suna hira kafin Indo ta musu sallama ta tafi, Indo har zata shige gidan su ta hango gidan INNA fasa shiga cikin gidan nasu tayi ta shige na INNA tun daga zauren gidan idanunta suka fara zubar da hawayen kallo take bin gidan dashi ta ko ina idanunta ne ya sauƙa a bedroom ɗin INNA ƙarasawa tayi tasa hanu ta tura ɗakin ta shiga ganan komai nata a ajiye komai yana nan babu abunda aka taɓa, gadon nata ta hau ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka tana cewa.

” Allah sarki INNA kin tafi kin barni da kewarki, ganan komai naki a ajiye amma sai dai ke bakya nan, Allah ya jiƙanki INNA ashe barinki ƙauyen nan kin barsa kenan har abada bazaki dawo ba,”

Share hawayen ta tayi tana tuno Ranar data saka fararen kaya ta tsoratar da ita da mutuwa Allah sarki ashe kuma mutuwar taki tana kusa, Indo ta juma tana tuno rayuwarta da INNA, kamar wacce aka tsikara ta tashi da sauri ta ɗauki tsintsiya tahau shara, sanda ta gyara komai na gidan tana cewa.

” INNA gidan ki bazai wulaƙanta ba dan babu ranki zan cigaba da gyarawa har na bar ƙauyen nan.”

INDO dai bata bar gidan INNA ba har magaruba sannan ta shiga cikin gidan su, daddare ma Sharifa ta kirata sun juma suna taɗi harta haɗata da Aunty Hindu ma suka gaisa sosai Aunty Hindu ta bawa INDO haƙuri na rashin samun halartar aurenta da bazasu yiba sakamakon bullowar wannan cutar ta coronavirus da ta tsayar da komai na duniya sun juma suna tattaunawa kafin daga baya suka kashe wayar.

 

**************************************

Allah sarki Rayuwa yau kimanin satin Mustafa biyu a kulle cikin hotel yayi wani irin rama har duhu yayi ga wani ƙasumba daya cike masa fuska baida aikin daya wuce ya wuni yana Shaye-Shaye wasu ƙwayoyin ma Kamal da kansa yake zuwa ya kawo masa ya koma, amma fa sanda Mustafa ya hani Kamal daya sanar da kowa inda yake, kwata kwata yanzu rayuwar Mustafa ta sauya ga shi yanzu wani sa’in haka zaita aman jini ga tari dake damunsa amma tsabar taurin kai irin na Mustafa yaƙi fita yaga likita ko ya kira likitan yazo ya dubasa, kullum kuma cikin sambatu kiran *SHATUUN SA* Yake Rayuwar sa ta koma abin tausayi.

Haka Habeeb yana cikin munguwar damuwa na rashin ɗan uwansa duk bincike da zaiyi yayi amma babu Mustafa babu labarin sa hankalin sa a matuƙar tashe yake, ko Maganar Auren nasa yanzu baya yi ɗan uwansa ne kawai a cikin ransa, haka ko kiran Indo a waya bayayi haka itama Indo bata kiran Habeeb ɗin domin kuwa kwanakin nan da Mustafa take kwana take tashi a zuciyarta ga wani irin tsinkewa da zuciyarta take yi, haka zata shiga cikin ɗaki ta yi kukanta ta goge hawayenta ta fito, RAUDA kuwa tafi kowa shiga cikin damuwa domin kuwa yanzu kuka shine ya zame mata abincin ta ta daina cin abinci, ta rame sosai tayi baƙi, ga yawan ciwo da cikin ta da ƙirjinta yake mata, duk wanda yasan RAUDA ya ganta yanzu sai ys tausaya mata, haka Momy itama tana cikin damuwa kullum cikin hawaye take tana roƙon ubangiji daya bayyana mata ɗanta, domin kuwa Habeeb ya sanar da ita gaskiyar Abunda yake faruwa ganin har yanzu babu labarin Mustafa, shine ya yanke shawarar sanar da Momy domin ta tayasa da addu’a saboda bakin uwa bashi da hijabi da UBANGIJI, wato yanzu tsabar tashin hankali Momy har mantawa take da Habeeb zai Auri Indo domin kuwa yanzu hankalin ta yana kan ɗanta, ko sanda Mamy ta kirata take sanar da ita Maganar zuwa wajen boka Momy cewa tayi ta rabu da ita kawai yanzu ba shi bane a gabanta, sosai Mamy taji haushin Abunda Momy ta gaya mata, domin kuwa bata so su tsaya iya nan ba taso ace tafi haka yagar kuɗi a wajen Momy.

DADDY yana zaune a kasuwa gabaki ɗaya yau tunanin sa yana kan ɗannasa zuwa yanzu abun ya fara basa tsoro, ya juma yana tunani duk binciken daya kamata yayi yayi amma babu wani good imfomotion, jin kiran Sallah yasa Daddy tashi ya ɗauro alwala ya shige massalaci bayan sun idar ne Daddy yana zaune a massalaci Kamal ya masa Sallama, Amsa sallamar Daddy yayi kamal ya mikawa Daddy hanu sukayi musabaha sannan ne kamal yace.

” Sunana Kamal ni abokin aikin ɗanka Mustafa ne, na kawo maka infomations ne akansa.”

Maida hankalin sa Daddy Yayi kan Kamal tare da cewa.

 

” Bismillah ina sauraronka.”

” Alhaji Mustafa ba ɓata yayi ba yana nan cikin garin nan, a nan Abnur hotel ya kama ɗaki mai no 10 yana can ya mayar da Shaye-Shaye abincin sa, babu kalar ƙwayar da Mustafa baya sha na masa faɗa amma Mustafa yaƙi dainawa na ce masa ya dawo gida nan ma yaƙi, ban san dalilin sa na barin gida ba, amma dai nasan yana Abnur hotel.”

Ran Daddy yayi mungun ɓaci har wani duhu idanunsa yake masa Tabbas Mustafa yayi mungun raina sa ya ci masa mutunci, wato dan yaƙi aura masa Indo shine zai fita yabar gida, har ya koma Shaye-Shaye murmushin takaici Daddy yayi sannan ya cewa Kamal.

” Na gode sosai Yaro na gode da sanar dani halin da ɗana yake ciki, zan kuma ɗauki mataki.”

Murmushin mungunta Kamal yayi tare da cewa Daddy.

” Amma Alhaji dan Allah karka sanar dashi cewa nine na faɗa maka inda yake.”

 

” Karka damu yaro insha Allah bazan sanar dashi ba.”

Godiya Kamal yayi wa Daddy kafin ya tafi, Daddy ransa ya ɓaci sosai ya kuma yi alƙawarin cewa bazai sanar da kowa halin da Mustafa yake ciki ba, Abunda ya fitar dashi daga gida shine zai dawo dashi.

*****************************************

Rana bata ƙarya sai dai uwar gijiya taji kunya, yau Alhamis gobe juma’a itace ranar daurin auren Habeeb da Indo, Momy yanzu ko Maganar Auren bata yi, saboda ba shi bane damuwar ta yanzu, yau da misalin ƙarfe biyu na rana Daddy ya dawo da akwati nan Auren Indo akwati shida Daddy ya haɗa mata
Momy ko kallo kayan basu isheta ba, Habeeb kuwa babu nairar sa cikin kayan duka Daddy shiya haɗa da kuɗin sa, HASINA da RAUDA ce kawai suka ga kayan, itama RAUDA ƙarfin hali ne kawai ya sata ganin kayan turmi talatin Daddy ya sa mata masu tsadar gaskiya kaya fa masha Allah komai yayi.

Daddy kuwa bai sanar da kowa labarin da yaji game da Mustafa ba, yayi shuru ya ƙyale maganar, haka kuma ya kwantar da hankalin sa.

 

*****************************************

A can Dasina kuma sosai Mama suke hidimar su da ƴan uwanta, haka maƙota duk sun shigo musu, Lami kuwa tun safe take cikin gidan, Indo tana ɗaki sai sharɓar kuka take mussaman idan ta tuno gobe ne ɗaurin Auren ta kuma da wani daban ba ya Mustafa ba, zuciyarta na mungun bugawa idan ta tuno da wannan, jin kamar Muryar Zahra ne a tsakar gidan nasu ya sata saurin goge hawayen ta ta sauko daga saman gadon Mama ta fito da sauri, Zahra ce kuwa da gudu Indo taje ta rungume ta tana mata Oyoyo, gaggaisawa Zahra tayi da jama’ar wajen kafin Indo ta kama hanunta suka fice zuwa ɗakin Mama, sanda aka kawowa Zahra ruwa tasha bayan ta huta ne Indo tace.

” Sannu da hanya, da ai nayi zaton bazaki zo ba da naga shuru tun jiya baki zoba.”

Murmushi Zahra tayi tare da cewa.

” Ai kuwa da bazan zoba, saboda wannan cutar wai Abba babu ruwansa yana tsoron coronavirus gashi cikin jama’a zan shiga da ƙyar dai ummi ta lallashe sa Kafin ya barni na taho, Amarya amarya s gidan ya Habeeb sai ƙanshi fa kike hajiyata.”

Cikowa idanunta sukayi da hawaye kafin tace.

“Zahra har yau ban ƙara jin labarin ya Mustafa ba, ina son sanin halin da yake ciki nasan yana cikin damuwa.”

Ta ƙarasa maganar hawaye na sauƙa a idanunta, Zahra kuwa tsuka taja tare da cewa.

” Haba A’isha meyasa kika kasa ciresa a cikin ranki, karki manta fa wannan mutumin bashi zaki AURA ba gobe ɗaurin Auren ki, kuma yanzu nake jin cewa ya kamata ace kin ciresa a ranki ki yiwa kanki ƙiyamal laili karki je gidan wani da tunanin wani.”
.

” Zahra kinsan dai………….”

 

” Karki ƙarasa wannan maganar kawai ki cire shi a cikin ranki, ni yanzu ba wannan ba, ina son ki haɗani da Baba muyi Magana, saboda Ummi na ta miki komi na saitin ɗaki har kayan kitchen ta Kuma sanar da Daddy, yanzu haka nabar Ummi sun tafi miki jere.”

 

Sosai Indo tayi farin ciki, bata yi ƙasa a gwiwwa ba ta ɗauki Zahra sukayi wajen Mama da Baba, suma sosai sukayi murna, daman kuma Baba bai sayi saitin ba, yana sone sai gobe idan za’a tafi da ita ya bada kuɗin aje birni a saya mata irin nasu na birnin.

 

Rana bata ƙarya yau ne juma’a Ranar ɗaurin Auren INDO da Habeeb yayin da Indo take jin wani irin mungun nauyi a cikin zuciyarta sam bata murnar wannan Aure da za’a ɗaura ita Abunda yake ɗaga mata Hankali ma, yanda Habeeb ya daina kiranta a waya ko jiya da ta kirasa ma ƙin ɗagawa yayi kuma har yanzu bai biyo kiran ba, to me yake nufi da nine, tana maganar zucin ne tana kuka, Zahra da take gefe girgiza kanta kawai tayi, domin kuwa ko bata tambaya ba tasan damuwar ƙawar tata.

MOMY kuwa yau baƙin ciki biyu ne ya haɗu mata na wannan auren da ya zama mata dole tayi haƙuri tana gani a ɗaura sa da kuma na ɓacewar ɗanta wanda yafi soyuwa a zuciyarta, tana cikin tunanin ne taga Daddy ya fito cikin manyan kaya, shida Habeeb kallon ta Daddy yayi tare da cewa.

” To A’i mufa mun shige ɗauro auren ɗanki sai ki mana addu’a.”

A dole kuma cikin ƙarfin hali Momy tace.

” Allah ya dawo daku lafiya, amma yanzu dan Allah Alhaji muna cikin wannan jimamin na rashin ɗan mu shine kai kuma kake ta tafiya ɗaurin Aure, kamar wanda baka damu da rayuwar ɗanka ba.”

Murmushi Daddy Yayi yace.

” Karki damu ɗanki naji labarin sa, yana nan cikin halin lafiya, yama kusa dawowa kawai yaji ya muku saboda kun hanasa Auren Indo.”

Daga Habeeb har Momy kallon mamaki suke bin Daddy dashi kafin Habeeb yace.

 

” What Daddy da gaske kasan inda ɗan uwana yake, pls Daddy ka sanar dani yanzu naje na ɗauko sa dan Allah.”

Murmushi Daddy Yayi yace.

 

” Yanzu babu wannan lokacin muje muyi Abunda yake gaban mu idan yaso idan mun dawo sai mu ƙarasa Maganar, yauwa matar gwamma Hajiya Hari zata zo ita da ƴan uwanta za suyiwa Indo jere acan ɗaya part ɗina na baya.”

Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe kafin tace Allah ya dawo daku lafiya.

Daddy basu wani juma ba suka isa cikin ƙauyen DASINA a gidan INNA suka sauƙa harda amininsa Alhaji Ahmed mahaifin RAUDA, su Uku suka je tarba kuma ta mutunci aka musu Daddy da kansa ya miƙawa Baba da amininsa Baba Abubakar sadakin Indo Naira dubu hamsin.

misalin ƙarfe 2 na rana bayan an sauƙo daga Sallar juma’a aka shigo da goron ɗaurin Auren Indo cikin gidan nasu, Goggo Hali ce ta saka guɗa, tabbacin an ɗaura Aure, ai kuwa Indo tana jin wannan guɗar ta saka kuka sosai take kuka ganin da gaske ta rasa Mustafa a matsayin mijin Aure.

 

Kuyi hkr fan’s ban samu nayi editing ba zaku haɗu da typing error.

 

*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*

Ummu Nasmah ce
[5/11, 12:52 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*

Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.

_________________________________________

*P*••••••2️⃣9️⃣ ↗️ 3️⃣0️⃣

Sosai ta bawa Zahra tausayi Tabbas rashin masoyi akwai zafi sai dai ya zatayi ƙaddara ta riga fata, babu yanda zasuyi tunda Allah ya rubuta cewa Habeeb shine mijinta ba Mustafa ba, cikin tashin murya Zahra tace.

” A’isha idan har kinyi imani da Allah da kuma ƙaddarar sa, to ya kamata ace kin Rungumi ƙaddara kin daina saka damuwa a zuciyarki, nasan akwai damuwa amma haƙuri zakiyi duk sanda ya taso miki ki dinga ambaton UBANGIJI, karki manta ko babu rabuwar rayuwa tsakanin ki da Mustafa to ki sani fa akwai ƙaddarar mutuwa, ko kuma idan ya mutu zaki bishi ne, yau ina INNA ta mutu duk son da kike yiwa Mustafa dole zaku rabu koba juma ko ba daɗe tunda akwai mutuwa, to meyasa ba zakiyi hkr ba yanzu ki godewa UBANGIJIN ki ki kuma Rungumi mijin da ya baki ki godewa UBANGIJIN ki A’isha domin kuwa ya miki ni’ima maɗaukakiya, tunda harya cireki daga cikin duhun jahilci ya haska ki a cikin hasken ilimi ta sanadiyyar fitar dake daga cikin wannan ƙauyen zuwa birni, ki godewa UBANGIJIN ki.”

Jikin Indo yayi sanyi ƙalau sosai nasihar Zahra ya shiga jikin ta shuru tayi tare da goge hawayen ta, Abokanan wasa kuwa sai shigowa suke suna tsokanar ta, can wajen ƙarfe Uku Mama da Goggo Asabe suka saka Indo a cikin ɗaki sosai suke mata faɗa akan zaman Aure, Mama ce ta dubeta tace.

” Kiji tsoron Allah Indo ki yiwa mijinki biyyayah domin kuwa aljannar ki tana ƙarƙashin ƙafarsa, shi zaman Aure sai da haƙuri dole domin kuwa wahalar sa yafi daɗin sa yawa, duk abunda mijinki ya umarce ki dashi to kibi muddun bai sabawa UBANGIJI ba, ki sani cewa Rayuwar ki ta da babu Aure ba ɗaya bane da rayuwarki ta yanzu da igiyar Aure ya shiga ya zargeki, sannan kiso ƴan Uwansa tamkar yadda zaki so naki ƴan uwan, kiyiwa uwar mijinki biyyayah kamar yadda zaki min domin kuwa itace mahaifiya gareki yanzu.”

Sosai mama ta mata nasihar haka Goggo Asabe ma, kafin daga bisani suka turata wajen Baba shima sosai ya mata nasa faɗan Zainabu da Hansai sai Lami suma dasu akayi wunin juma’ar, shima ya Tanimu ya mata nasa faɗan, koda sukazo tafiya birni mutum huɗu ne zasu raka Indo, Goggo Asabe da Goggo Hali sai Lami da Innawuro Mama bata bar ƴartata ta tafi haka ba sai da ta kaɗata da ƴan kayayyakin su na ƙauye, haka ma ta haɗa mata da kayan gara mai yawan gaske, Indo tana kuka suka rabu da Mama.

INDO har suka shiga motar aka tayar suka tafi bata saka Habeeb a cikin idanunta ba, hakan kuma ya mata zafi cikin ranta sai dai bata nuna hakan a zuciyarta ba har suka shiga cikin birni, part ɗin Momy aka sauƙe su, Indo ganin sun sauƙa part ɗin Momy sai da zuciyarta ta tsinke amma haka ta daure suka ƙarasa har cikin falon, su taradda Momy da Mamy sai ƙanwar Momy Aunty Zulai da kuma mahaifiyar Zahra, a wannan karon sosai Momy ta bawa kowa mamaki yadda ta saki ranta take fara’a tamkar tana son Auren da kanta Momy ta haura dasu bedroom ɗin Indo, abinci kuwa kala-kala aka shiga musu dashi tare da musu ban gajiya, Hasina kuwa ta bawa marar ɗa kunya domin kuwa zaka rantse da Allah ba itace akayiwa kishiya ba, mussaman ta zo part ɗin Momy ta tare su RAUDA kuwa tun safe tana ɗaki sai muƙurƙuso take yi sosai cikin ta yake mata ciwo, ko tashi bata iya yi, Hasina ce data lura da babu RAUDA ya sata zuwa part ɗin nata taga ko lafiya, ai kuwa cikin jini ta sameta cikin mawuyacin hali, da gudu tazo ta sanar da Momy halin da RAUDA take ciki, Momy batayi wata-wata ba ta ƙira Habeeb, cikin sauri aka saka RAUDA a cikin mota sai Hospital.

Koda isarsu Hospital ɗin RAUDA ta galabaita sosai, babu sunan wanda take kira sai Mustafa, Emagency aka shige da ita DARECT, harda Habeeb cikin masu duba RAUDA, binciken da sukayi shiya tabbatar musu da haihuwa ce sai dai bata da ƙarfin da zata iya haihuwa da kanta dole sai dai a mata c’s Habeeb ne ya fito ya haɗa Uban gumi ya dubi Daddy tare da cewa.

” Daddy haihuwa ce sai dai bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai an mata C’s shine muke so ka saka mana hanu tunda shi Mustafa baya kusa.”

Cikin sauri Daddy yace

” Habeeb meyasa sai ka sanar dani kaima zaka iya yanke ko wani hukunci akan RAUDA matar ɗan uwanka ne fah kaje kasa hanun a madadin ɗan uwanka, mudai burin mu ta sauƙa lafiya.”

Ai kuwa da sauri Habeeb ya koma cikin, a cikin mintuna kaɗan aka gama komai na shirin Cs amma RAUDA taƙi fir a shiga da ita ɗakin tiyata,tace dole sai taga Mustafa kafin ta shiga, Habeeb ne ya fito ya sanar da Daddy yace Daddy ya shiga ya mata Magana ko zataji nasa, koda Daddy ya shiga da ƙyar RAUDA ta ɗago idanunta ta kalli Daddy tare da cewa.

” Ka taimake ni Daddy ka kira min ya Mustafa na gansa akwai Maganar da nake so muyi dashi kafin na shiga ɗakin nan, ka taimaka min Daddy naga mijina kafin na tafi.”

Sosai ta bawa Daddy tausayi bai ce mata komai ba ya juya ya fito cikin sauri tare da cewa Habeeb su jirasa yana zuwa yanzu, Daddy motar sa ya hau da kansa ya tuka bai tsaya ko ina ba sai Abnur hotel, yana zuwa ya samu ma’aikatan hotel ɗin yace su duba masa waye ya kama ɗaki mai number 10 suna dubawa suka tabbatar masa da cewa Mustafa Harun shine wanda ya kama ɗakin, har ƙofar ɗakin Daddy yasa aka kaisa da kansa Daddy yayi Nocking, Allah ya taimaka lokacin Mustafa ba’a shaye yake ba, daga cikin ɗakin yace.

” Waye ne.?”

Cikin ƙula Daddy yace.

” Ubanka ne, nace Uban ka ne?”

Jin muryar Daddy yasa zuciyar Mustafa tsinkewa, da sauri yasa hanu ya buɗe bedroom ɗin, tunda ya buɗe bedroom ɗin Daddy yake binsa da kallo yanda yaga ɗan nasa gabaki ɗaya ya sauya ya fice hankalin sa, ga wani uban ƙasumba daya tara kafin Daddy ya maida dubansa ga bedroom ɗin kwalaben Shaye-Shaye ne birjik zube a cikin bedroom ɗin girgiza kansa Daddy Yayi tare da saka hanu ya ɗauke Mustafa da mari har Uku kafin yasa hanu ya figesa da ƙarfi, har cikin mota, jan motar Daddy yayi da mungun gudu har cikin Hospital ɗin, kafin ya ƙara jawo hanun Mustafa shidai Mustafa bin Daddy kawai yake cikin Ransa kuma yana ayyana waye a cikin asibiti, Momy Mamy Hasina Indo Goggo Asabe gabaki ɗayan su tashi sukayi suna kallon Daddy da Mustafa, Indo gani tayi gabaki ɗaya Mustafa ya sanja mata shima kuwa Indo yake bi da kallo har Daddy yayi cikin ɗakin da aka ajiye RAUDA kafin ya sakesa, gabaki ɗayan su su Momy suma shigowa sukayi ɗakin ƙwarai sun tausayawa halin da RAUDA take ciki Mustafa kuwa da sauri ya ƙarasa gabanta ya tsugunna cikin tashin hankali yake cewa.

” Me yake damunki RAUDA, meya sameki, kike kwance gadon asibiti.?”

Ya mata Tambayar cikin tashin hankali, murmushin farin ciki RAUDA tayi na ganin mijin nata, tana cije leɓenta yayin da take jin munguwar azaba daƙyar ta buɗe bakinta tace.

” Ya Mustafa kaine nake gani a gabana, ina kaje haka ka barni cikin tashin hankali, na shiga damuwa sosai na rashin ganin ka, kana lafiya ko ina kan babu abunda ya sameka.?”

Wani irin sanyi jiki Mustafa yayi, har kunya yaji gashi dai shi ya tafi ya barta bai taɓa tunanin ta a cikin zuciyarsa ba ko sau ɗaya, Allah Sarki ashe ita dashi take kwana take tashi, kama hanunta Mustafa yayi tare da saka ɗayan hanun nasa ya goge mata gumin da take haɗawa kafin yace.

” Kiyi RAUDA bada son raina na tafi na barki ba, ya zama min dole ne nayi nesa da ahalina domin samawa zuciyata sauƙin Abunda ke damunta ina mai baki haƙuri a karo na biyu daki yafe min.?”

Murmurshi tayi tare da kamo hanun nasa ta ɗaura a cikin ta, kafin tace.

” Kullum cikin yafiya nake gareka ban taɓa kwana ba tare dana yafe maka duk wani laifin da kamin ba, a yanzu nine nake buƙatar neman yafiyar ka domin kuwa ina ji a jikina cewa bazan fito daga ɗakin tiyatan nan ba da raina mutuwa zanyi ya Mustafa bazan tashi ba.”

Kaɗawa idanun Mustafa yayi yayi jajur hankalin sa yayi mungun tashi, gabaki ɗaya mutanen dake tsaye a wajen babu wanda bai tausayawa RAUDA ba, Indo kam ma uwar ƴan saurin kuka, sai sharɓar kukan take, ta maƙale jikin Zahra, hankalin ta yayi mungun tashi, domin kuwa shigen Abunda INNA tayi kafin ta rasu shi rauda takeyi yanzu, Mustafa cikin tashin hankali yace.

” Bazaki mutu ba RAUDA bazaki mutu ba, ba tare da na nuna miki Soyayya ba da kulawa tare da tattali, A yanzu ina sonki ina sonki karki tafi ki barni ki tsaya mu raini ƴarmu tare karki tafi ki barta cikin maraicin rashin uwa.”

Murmurshi sosai RAUDA take mai haɗe da hawaye tana shafa cikin nata kafin tace.

” Ƴata baza tayi maraicin rashin uwa ba, muddun HASINA da INDO suna raye na Tabbata bazasu bari tayi kukan rashi na ba, alƙawari ɗaya zaka min shine ka karka bari ƴata tayi kuka ina son ka nuna mata kulawar dani na rasa a wajen ka ko yanzu nayi farin ciki da furta min kalmar so, sannan na yafe maka kaima ka yafe min ina sonka MIJINA.”

Ta ƙarasa maganar tana danƙe marar ta dake mata ciwo, duban Mamy tayi dake gefe tana rausar kuka tace.

” Ki daina kuka Mamy ki min addu’a sannan kice Daddy ya yafe min nima na yafe maku, ina sonki Mamy ki cewa kalit kar yayi kewata shima yamin addu’a, Momy kema ki yafe min kinji.”

Gabaki ɗayan su kuka suka saka Mamy gagara Magana tayi tsabar kuka yaci ƙarfin ta, RAUDA hanunta ta ɗaga tayiwa Indo alamar tazo, da sauri Indo ta ƙarasa gabanta tana hawaye, cikin ƙarfin hali RAUDA tace.

” Ki yafe min nasan na miki kuskure a baya ina roƙon ki yafiya, sannan ga Amanar ƴata nasan ba lallai na samu damar ganinta ba bayan na haife ta ki riƙemin ita nasan zaki kula da rayuwar ta hanu ta miƙawa Indo alamun ta mata alƙawari.”

INDO kuka ta fashe dashi kafin tasa hanunta cikin na RAUDA tace na miki alƙawari kuma na yafe miki, insha Allah ma zaki tashi zaki RAYU da ƴarki bazaki mutu ba.”

Habeeb ganin da yayi Maganar RAUDA ba mai ƙarewa bane ya sashi tura gadon yayi tiyata room da ita, Mustafa da sauri yabi bayan su yana ajiyar Zuciya, tana kallon sa har aka shige da ita ɗakin Cs ɗin, jin gina Mustafa yayi a gefe sai famar ajiyar Zuciya yake sauƙewa, kowa dake wajen tsaye yake cikin tashin hankali, wajen awan su Huɗu da shiga Cs ɗin sannan Habeeb ya fito riƙe da jaririya a hanunsa jikin sa a matuƙar sanyaye, Indo ce ta tashi da sauri ta amshe jaririyar daga hanun Habeeb tana ƙare mata kallo, Mustafa cikin sauri ya k’arasa wajen Habeeb ba tare daya kalli jaririyar ba yana cewa.

” Ina RAUDA ina fatan tana cikin halin lafiya ko?”

Girgiza kansa Habeeb yayi tare da cewa.

” Sai dai muyi haƙuri domin kuwa RAUDA ta amsa kiran mahaliccin ta, Allah ya mata rasuwa.”

Ja da baya Mustafa yake yana nuna Habeeb da hanu yana cewa.

” Ƙarya kake RAUDA bazata mutu ta barmu ba, nasan zata tsaya ta rayu damu bazata barni nayi biyu babu ba, nasan UBANGIJI na bazai rabani da masoyana duka biyu a lokaci ɗaya ba ya barni cikin kaɗaici ba, ka daina faɗa min wannan maganar.”

Gabaki ɗayan su kuka suka saka, hankulan su yayi mungun tashi Daddy ne kawai yayi ƙarfin hali a cikin su ya ke kiran sunan UBANGIJI, turo RAUDA da akayi rufe da yadin tiyata, yasa Mustafa ƙarasawa da sauri ya yaye zanin, tana kwance fuskar ta rufe, sunkuyawa kanta yayi yana cewa.

” Nasan bacci kike, ki tashi ki faɗa musu su daina miki kuka ke baki mutu ba da ranki ki tashi ki gaya musu, bazaki tashi ki gaya musu ba, nasan bazaki tafi ki barni ni kaɗai ba.?”

Ganin da Daddy yayi Mustafa yana ƙoƙarin zaucewa ya sashi ƙarasowa gabansa tare da dafa sa yace.

” Wanda ya mutu bazai taɓa dawowa ba, ka dawo cikin hankalin ka, ka yiwa matar ka addu’a domin kuwa ta rigaka gidan gaskiya, ita da ta rigaka tafiya ba sauri tayi ba, haka kaima da kake nan bakayi jinkiri ba, duka a hanya ɗaya muke kowa jiranta yake, dan haka kayi tawakkali ga UBANGIJIN ka.”

Tari Mustafa ya fara sosai yake tarin, yayin da jini kuwa sai bulbulowa yake daga bakinsa danƙe ƙirjin sa Mustafa yayi yana cigaba da tarin da sauri Momy ta karaso wajen ko kafin Momy ta iso ma tuni Mustafa ya yanki jiki ya faɗi ƙasa.

Kansa sukayo cikin kiɗima Indo kuwa ƙara fashewa tayi da kuka tana ƙanƙame da jaririyar a hanunta, ta ƙarasa wajen Mustafa tana cewa.

” INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJU’UN, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!! Dan Allah ya Mustafa ka tashi karka tafi ka barni ka tashi, Daddy kace masa ya tashi, Momy kina ganinsa ko ki tashesa Momy” ganin da tayi basa tanka ta ba yasata tashi ta riƙe hanun Habeeb tana cewa, ” ka tashe shi ya Habeeb ka tashe shi tunda kai likita ne, idan ya mutu nima mutuwa zanyi dan Allah kuce masa ya tashi.”

Wani irin mungun kallo Habeeb yake bin Indo dashi hanunsa yasa ya karɓi jaririyar ya miƙawa Momy ita, doctors ya kira suka kama Mustafa suka shiga dashi Emergency, duk ƙoƙarin likitotin na ganin Mustafa ya farfaɗo amma abun yaci tura, bincike suka duƙufa akansa na ganin sun gano meke damunsa, amma har aka kira sallar magaruba basu gano komai ba, sai dai sun saka masa oxgying tare wasu drug, yana kwance ne dai shi ba macacce ba shi ba rayayye ba.

Daddy ne yasa su dukan su su koma, gida, amma Indo fir taƙi yarda ta koma a cewar ta bazata iya tafiya tabar Mustafa a cikin wannan halin ba sanda Daddy ya mata jan ido sannan ta koma aka bar Momy da Habeeb tare da Mustafa, RAUDA kuwa mutuware aka shiga da ita Daddy yace sai gobe misalin ƙarfe goma za’a mata sallah a kaita makwancin ta (Allahu Akbar rai baƙon duniya yau dai ga RAUDA ta tafi gidan ta na gaskiya)

Mamy bata koma gidan ta ba gidan Momy ta wuce tana kuka mai cin rai sai yanzu take nadamar watsar da RAUDA da tayi tunda tayi Aure Abban ta ma an sanar dashi sosai shima yaji bakin cikin rashin ƴarta sa, sai dai shi yayi tawakkali, Indo kuwa kuka take tsakanin ta da Allah anyi rarrashin duniya taƙi shuru, idanunta har sun kunbura, cikin ƙanƙanin lokaci mutuwar RAUDA ta zagaye dangi kota ina zuwa ake.

Babu wanda baiji mutuwar RAUDA ba, Ranar Indo kwana tayi tana kuka kusan ma dai zance duka gidan babu wanda ya RUNTSA Habeeb madarar yara ya siyowa jaririyar shi aka kwana ana bata, yarinyar kuwa kyakkyawa sak uwar ta babu inda tabar RAUDA sai fari da tafi RAUDA kasancewar mahaifinta farin gaske ne, yarinya kuwa mai haƙuri sam bata da rikici, domin kuwa bata da yawan kuka.

Washe gari da safe Daddy yasa aka ɗauko gawar RAUDA aka dawo da ita gida, duk wanda yaje yaga RAUDA kwance babu Numfashi sai yayi kuka Abban ta ma ya shiga ya ganta tare da mata Addu’a, Iya ladi mahaifiyar Mamy da Goggo Asabe sune suka yiwa gawar tata wanka, Allah sarki Rayuwa Mustafa bai samu an kai Matarsa maƙabarta dashi ba, yana can kwance shima rai a hannun Ubangiji, da Habeeb aka kai RAUDA makwancin ta, sai lokacin hawaye ya zowa Habeeb na tausayin RAUDA, rayuwarta kawai yake tunawa na da a cikin gidan su.

Allah sarki rai baƙon duniya dukkan wani mai rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa yau dai ga RAUDA rayuwa ta ƙare an rufe ta cikin ƙasa kowa ya watse ya barta daga ita sai halinta, Habeeb ya dawo suka Zauna a wajen zaman makoki, ya ɗan juma yana zaune kafin ya tashi yayiwa Daddy Magana cewa zaije Hospital yaga result ɗin MUSTAFA.

Bisa mamakin Habeeb yana shiga Hospital ɗin yaga Indo zaune gefen Momy sai famar sharɓar kuka take tana kuma riƙe da jaririyar a hanunta, sosai yayi mamakin zuwan nata, to wama ta tambaya ta fito, yayiwa kansa tambayar itama Momy hawaye ne kawai yake gudu bisa fuskar ta, sunkuyawa yayi gaban Momy ya gaisheta, bata samu damar amsawa ba sai kai data ɗaga masa, dubanta yayi yace.

” Dan Allah Momy ki daina kukan nan, ki cire damuwa cikin ranki ki yiwa RAUDA addu’a shine kawai gatan da zamu mata, ta riga ta tafi bazata taɓa dawowa ba, dan Allah kiyi hkr, shi kuma Mustafa zai tashi da yardar Allah.”

Share hawayen ta Momy tayi sannan tace.

” Kuka ya kamani dole, dole nayi kuka mussaman idan na kalli wannan jaririyar da aka bari cikin maraici, ga shima Mustafa yana kwance sai yanda UBANGIJI yayi dashi, Habeeb ina tsoron na rasa Mustafa.”

” Karki damu Momy insha Allah bazaki rashi ba, zai tashi Momy, bari na ƙarasa wajen result ɗin sai musan Abunda yake damunsa, insha Allah ma nan da 24 hours zai farfaɗo.”

” To Allah yasa jeka karɓo result ɗin, Allah yasa muji Alkairi.”

Da ameeen Habeeb ya amsa kafin Indo cikin dashewar Murya alamun taci kuka ta ƙoshi ta gaishe sa, amsawa yayi tare da karɓar jaririyar daga hanunta ya fita da ita, Momy kuwa kallon Indo kawai tayi kafin ta jingina kanta.

 

Koda Habeeb ya karɓi result ɗin MUSTAFA sosai hankalin sa ya tashi, number wayar Daddy ya kira tare da cewa yazo asibiti yanzu, Daddy baiyi wata-wata ba, take ya tashi ya garzayo asibitin, tare ya samesu da Momy tsaye kafin ya karaso yana tambayar jikin Mustafa, duban s Habeeb yayi cikin raunin Murya yace.

 

” Kaga Abunda nake faɗa maka ko Daddy, gashi yaje ya dawo, Daddy damuwa ce ta yiwa Mustafa yawa harta haifar masa da ciwon zuciya, mummunan ciwon zuciya kuwa, shine yake saka sa yawan tare da aman jini, sannan ya kamu da hawan jini, Daddy koda Mustafa ya tashi dole sai ya samu farin ciki kafin lafiyar sa ta ɗaure, idan kuma bai samu Abunda yake so ba, to Tabbas zuciyarsa zata buga ma’ana heart Sttack, domin kuwa yanzu ma Allah ne ya rufa asiri bai samu Sttack ɗin ba, a yanda zuciyarsa ta kamu da ciwo, Daddy dole Mustafa yana buƙatar farin ciki, yanzu akwai drip ɗin da zamu ɗaura masa, insha zaiji sassauci nan da 24 hours zai farfaɗo.”

Shuru Daddy yayi yana jinjina girmar lamarin kafin ya dubi Habeeb yace.

” Allah ya basa Lafiya daga baya zamu san yanda zamu bullowar lamarin.”

Duban su Momy tayi tace

” Har sai ya tashi kafin mu sama masa Abunda yake buƙata, RAUDA ce kuma babu ita cikin wannan duniyar Tabbas ɗana zai mutu, na shiga Uku, taya zan samawa Mustafa farin ciki ina son sama masa farin ciki domin ganin na rayu da ɗana bana son rasashi.”

Kusa da ita Habeeb ya ƙaraso yana duban mahaifiyar tasu duban tausayi kafin ya kama hanunta yace.

 

” MOMY ba RAUDA bace kawai farin cikin Mustafa, Tabbas tana daga cikin farin cikin sa sai dai kuma ba ita bace jigon farin cikin sa, Tabbas Momy damuwar Mustafa yana da nasaba da INDO wacce baƙya so cikin rayuwarki wacce kika tsani ki buɗi ido ki ganta cikin gidan ki, itace farin cikin da ɗanki yake nema itace farin cikin daya kamata ki samo masa, zaki tabbatar da haka idan har ya farka da sunan ta a bakinsa, domin kuwa duk abunda yake buƙata dashi zai tashi a bakin sa.”

Wani irin duba Momy take masa kafin tace.

” Wacce irin magana kake faɗa min, ta ina zan samo masa Indo a matsayin farin cikin sa, bayan a halin yanzu ta kasance haramun a garesa, matar ɗan uwansa, cemin kawai zakayi Mustafa zai mutu domin kuwa baida sauran farin ciki.”

” MOMY ɗan uwana bazai mutu ba, zai tashi ya rayu cikin iyalin sa, zai rayu da matar sa da yarsa domin kuwa ba dani aka ɗaurawa Indo Aure ba, da Mustafa aka ɗaura mata Aure, Momy tun sanda naga ɗan uwana ya daina kulani ya daina zama a inda nake duk da ƙauna da shaƙuwa dake tsakanin mu, mutumin da baya son yaga damuwa ta, yakan jure ko wani irin hali zai shiga muddun ni zan samu farin ciki, amma ya kasa jure rashin Indo hakanne ya tabbatar min ba son wasa yake mata ba, tana da matuƙar mahimmanci a cikin rayuwarta, hakanne yasa na ƙudurce a raina cewa shine zai Auri Indo ba niba domin kuwa ya fini dacewa da ita na gane cewa ba son Indo nake ba tausayin ta nake haka itama Momy bani take so ba, Mustafa shine wanda take so ko yanzu Momy kika ƙarewa Indo kallo yanda ta shiga cikin damuwa na kwanciyar Mustafa rashin lafiya zai nuna miki tsantsar Soyayyar da take masa kawai halacci zata min shiyasa ta amince da Aure na, bawai dan tana sona ba, sam bani bace a cikin Zuciyarta, Mustafa shine maƙale cikin zuciyarta, hakanne yasa na roƙi Daddy alfarma bisa waɗannan hujjojin aka ɗaura Aure tsakanin Mustafa da Indo, dan Allah kiyi hkr ki amshi Indo a matsayin surkar ki, ki sassauta ƙiyayyarta cikin zuciyarki.”

INDO jin maganar Habeeb take kamar almara wani irin sanyi ne yake sauƙa cikin Zuciyarta, sosai take jin wani nutsuwa na zuwar mata.

 

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

Ummu Nasmah ce
[5/13, 3:28 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘

*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*

*Cigaban*

*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

 

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*

AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••3️⃣1️⃣ ↗️ 3️⃣2️⃣

Naunauyar ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe tare da furta

” ALHAMDULILLAH!! Idan har Indo itace farin cikin Mustafa, idan har samunta a matsayin matar Auren sa zaisa ya samu cikakkiyar lafiya da kwanciyar hankali, to na amince na karɓi Indo a matsayin ƴata bama suruka ba, Tabbas na gane kuskurena na ƙiyayyar da nake nunawa Indo, bansan dalilin daya sa na tsaneta ba, amma insha Allah komai ya wuce.”

Hanu Momy ta miƙawa Indo alamun tazo, tashi Indo tayi tana share hawayen fuskar ta na farin ciki taje kusa da Momy, Rungume ta Momy tayi tana cewa.

” Ki yafe ni Indo nasan ni mai kuskure ne a gareki, na miki abubuwa da dama na rashin kyautawa ina mai neman afuwar ki, naso RAUDA na nuna miki ƙiyayya sai gashi UBANGIJI daya tashi nuna min ikon sa, sai ya ɗauke wacce nake so ya barni da wanda bana so domin ya nuna min muhimmancin ki a rayuwata, ya kuma ɗaurawa ɗana Soyayyar da dole sai dake zai rayu, Tabbas UBANGIJI ya nuna min girman ikon sa .”

Murmurshi mai haɗe da kuka Indo tayi tare da cewa.

” Baki taɓa min laifi ba Momy duk abunda kika min ina ɗaukar sa a matsayin tarbiyya ne, ban taɓa kwana ba tare da na yafe miki duk wani abu da kika min ba Momy.”

Murmurshi Momy tayi tare da shafa kan Indo tace.

” Allah ya miki albarka ya Albarkaci Rayuwar Auren ku ita RAUDA Allah ya mata rahama ya raya Abunda ta bari bisa sunnar Manzon rahama, shi kuma Mustafa Ubangiji Allah ya tashi kafaɗunsa ya basa Lafiya.”

Daga Daddy har Habeeb murmushin farin ciki suke yi kware sunji daɗin yanda UBANGIJI yasa Momy ta sassauto lokaci ɗaya, Tabbas sai an rasa wani abu ake samun wani abun Allah ya jiƙan RAUDA da rahama.

Daddy shine ya koma wajen zaman makoki yabar Habeeb tare da su Momy a asibitin, Aunty Hindu ma ta kira Daddy ta masa ta’aziya haka Momy ma ta kirata har Momy ta haɗata da Indo, anan ne Momy take sanar da Aunty Hindu Maganar Auren Mustafa da Indo sosai Aunty Hindu da sharifa sukayi farin ciki.

 

*****************************************

Misalin ƙarfe goma na dare Mustafa ya buɗe idonsa, cikin bacci Indo dake zaune gefen gadon yayin da Momy take kwance a bisa taburma, Habeeb kuwa yana gefe sukaji kamar wanda ake kiran sunan Indo, da sauri suka buɗe idonsu sukayo kansa.

” Indo RAUDA dan Allah kuyi hkr karku tafi ku barni dukanku lokaci ɗaya, ku taimaki Rayuwata.”

Girgiza kanta Momy tayi na tausayin ɗannata, mussaman ma yafi kiran sunan Indo, INDO ce ta matso kusa dashi tana cewa.

” Ya Mustafa bazamu tafi duka mu barka, dole ne sai ɗaya ya kasance tare da kai a tsakanin mu, ka taimake mu ka tashi domin ina buƙatar ka cikin rayuwata, rasaka tamkar rasa numfashina ne, ka buɗe idon ka ka kalle ni Indon kane take magana.”

Ta ƙarasa maganar tana riƙe da hanunsa, Mustafa riƙe hanun nata yayi gan, yayin da a hankali yake buɗe idonsa harya buɗe su ras a fuskar ta lumshe idanunsa yayi ya ƙara buɗewa, cikin raunin Murya yace.

” Da gaske kece kusa dani SHATUU, da gaske ne Abunda kunnuwa na suke ji min, da gaske kin amince kina sona zaki Aure ni.”

Kaɗa masa kai Indo tayi tare da cewa.

” Tabbas nine nine a gabanka ya Mustafa, ina sonka fiye da yanda nake son kaina, na tabbata kasan da hakan Soyayyar ka a jini na take, da ita na girma taya kake tunanin zan iya mantawa da kai taya zan iya daina sonka, ka sani cewa yanzu ina tsaye a gabanka ne a matsayin matar ka ta Aure, wacce Daddy da kansa yasa aka ɗaura mana Aure.”

Murmurshi mai haɗe da dariya Mustafa yake yi yana ƙoƙarin tashi ya zauna, tare da maida hankalin sa kan Momy da Habeeb yana murmurshi yace.

” Da gaske ne Abunda take faɗa da gaske ne an ɗaura mana Aure.”

Murmurshi Momy tayi tare da cewa.

” Marassa kunya masoyan zamani, da gaske ne.”

Ta faɗa masa tare da bashi labarin sadaukarwa da Habeeb ya masa, murmurshi Mustafa yake yi tare da miƙawa Habeeb hanu alamun yazo, murmurshi Habeeb yayi ya ƙarasa wajen ɗan uwansa suka Rungume juma, sosai suka yafi junan su, sai yanzu Mustafa yace.

” Ina RAUDA, tana nan ko an Kaita makwancin ta.?”

Habeeb ne yace.

” RAUDA bata nan an Kaita gidan ta na gaskiya, dan Allah ɗan uwana karka daga Hankalin ka bata buƙatar wannan a gareka addu’a take nema a wajen ka yanzu a matsayin ka na mijinta,.”

Cije leɓensa yayi tare da cewa.

” Allah ya jiƙanki da rahama RAUDA Allah ya baki jin daɗi a cikin kabarin ki, nasan baki samu farin ciki a gida na ba, Allah ya baki na can, ina jaririyar ku bani ita.”

Momy ce ta ɗauki jaririyar ta miƙawa Mustafa, ya karɓe ta ya juma yana kallon yarinyar yayin da ƙaunar jaririyar ke daɗa shiga cikin ransa, huɗu ba ya mata tare da miƙawa Habeeb ita yace.

” Gashi ɗan uwana, wannan itace kyautar da zan baka, kwana ki ka taɓa sanar dani cewa bincike ya tabbatar maka da cewa bazaku taɓa haihuwa ba, kaida matar ka, duk da Ita haihuwa ta UBANGIJI ne kuma insha zai baku, sai dai ga ƴata na baka kyautar ta duniya da lahira, kaine ubanta ba niba, karku taɓa nuna mata cewa nine mahaifinta, ya kasance kaine zata ɗauka a matsayin uba gareta na mata huɗu ba da sunan mahaifiyar ta.”

Cikowa idanun Habeeb da Momy yayi da hawaye Tabbas Mustafa ya yiwa ɗan uwansa Hallaci, hanu Habeeb yasa ya karɓa tare da cewa.

” Bazan taɓa mantawa da wannan hallacin da ka min ba a cikin rayuwata, ada na fidda rai ga samun ɗa sai gashi lokaci ɗaya Ubangiji ya bani ƴa, Tabbas wannan yarinyar bazata taɓa kuka ba a rayuwarta, zan bata gatan da ba ko wani uba bane yake bawa ƴarsa, Allah ya raya min ƴata RAUDA ya Albarkaci Rayuwar ta.”

Da ameeen duka suka amsa suna murmushin farin ciki, Indo ce ta tashi tazo gaban Habeeb ta sunkuya tare da cewa.

” Tabbas kamin alkairai da yawa a cikin rayuwata samun mutum irinka a Duniyar nan yana da matukar wahala Tabbas kai mutum ne na musamman, na gode sosai ya Habeeb bazan taɓa mantawa da alkairin ka ba a rayuwata.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Komai mutum yayi a rayuwa kansa zai yiwa karki damu komai ya wuce tunda yanzu gaki ga masoyinki Mustafa.”

Dukkan su dariya sukayi, Habeeb ya dubi Momy yace.

” MOMY tashi muje gida ki huta, ki barsa da matarsa tayi jinyar sa zuwa gobe da safe sai mu dawo, nima bari naje na kai ƴata wajen mahaifiyar ta, itama taji ɗumin jikin mamanta.”

Murmurshi Momy tayi ta tashi suka fice, har sun fita Habeeb ya sake leƙowa tare da cewa.

” Asha soyayya lafiya.”

Murmurshi kawai Mustafa yayi shi kuma Habeeb ya fice, Mustafa hanu ya miƙowa Indo yace tazo garesa tashi Indo tayi tazo kusa dashi ta zauna murmurshi Mustafa yayi tare da kama hanunta yace.

” Ina farin cikin samunki a matsayin matar Aure na cikar farin ciki na SHATUU, ina sonki.”

” Murmurshi itama Indo tayi tare da cewa.

” Haka nima ina matuƙar farin ciki da kasancewa a matsayin ƙarƙashin Inuwar auren ka, kamin bazaka taɓa rabuwa dani ba har ƙarshen Rayuwar mu.”

Murmurshi Mustafa yayi tare da cije lips ɗinsa yana jin ƙirjinsa na masa ciwo yace.

” Bazan taɓa sakaci da rayuwarki ba, zan tattalaki kamar yadda ake tattalin ƙoyi karya fashe, zan ƙauna ce ki fiye da yanda zan ƙauna ci kaina.”

Murmushin jin daɗi sosai Indo tayi, kusan kwana sukayi daren ranar suna hira washe gari da safe ya kama kwanan RAUDA Uku ranar ne kuma akayi sadakar ukun kowa ya watse daga zaman makokin, yayin da ƴan uwa da abokan arziki suke garzayo wa asibitin suna gaishe da Mustafa tare da masa ta’aziya, ƴan Dasina ma har asibitin suka zo suka yiwa Mustafa Sallama a yana kwance ma check ya rubuta na dubu ɗari yace Habeeb yaje ya cire musu kuɗin ya basu, Indo ma binsu tayi taga tafiyar su tana musu Allah ya kiyaye tare da kewarsu.

a Hospital ɗin ma sun ɗaura Mustafa akan magani tare da saka masa dokoki sun kuma sanar dashi cewa ya guji sake shiga damuwa.

Kwanan sa bakwai a asibitin suka sallame sa ya dawo gida da farko part ɗinsa yaso zama, Daddy yace a’a ya ɗauki matarsa su kuma sabon part ɗin da aka yiwa INDO jere, haka kuma akayi Indo da Mustafa suka koma nasu part.

Rayuwa gudu take yayin da yau rasuwar RAUDA wata biyu, Habeeb da Hasina sosai suke kula da RAUDA ƙarama, suna son ƴarinyar sosai, mussaman Hasina ko kukan yarinyar bata son ji, tana jin ta fara kuka zata shiga damuwa harsai taga ta daina kukan.

Mustafa sosai yake samun sauƙi dan kwata-kwata yanzu baya jin ciwon ƙirjin, shaƙuwa kuwa sosai ta shiga tsakanin sa da Indo, kullum suna liƙe kamar cingum babu dare babu rana

Wata daren ranar Alhamis ne auratayya ya shiga tsakanin Indo da Mustafa a ranar abun ya zowa Indo a bazata ta kuma sha munguwar wahala wajen Mustafa, sai dai daman ai ta mace dole sai wannan daren ya risketa, Mustafa yaji daɗin yanda ya samu matarsa cikakkiyar budurwa, wannan kenan.

Rayuwa sai gudu take Yayin da Soyayya mai ƙarfi ke sake shiga tsakanin Mustafa da Indo, kwatsam rana tsaka Indo ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki, ga zazzaɓi da yawan tashin zuciya, sosai hankalin Mustafa ya tashi, koda sukaje asibiti aka tabbatar musu cewa Indo tana ɗauke da ciki harna tsawon wata ɗaya, kuzo kuga murna da farin ciki wajen Mustafa haka suka dawo cikin farin ciki ya cigaba da tattalin matar sa.

************************************

” A’a fa Abban RAUDA karka yar min da yarinya naga sai wani faman cilla min ita, kake sama, bani ƴata kayi na kuɗin ka.”

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Ikon Allah, wato dai so kike ki nuna min cewa ban iya raino ba, to na dai fiki iya raino, kuma nasan ma tafi sona fiye dake.”

Dariya Hasina tayi tace.

” Kaji wata tatsuniya, to bari muga” kallon ƴarinyar tayi tana mata wasa tare da cewa.

” Baby na waye kika fi so tsakanin ummi da Abba faɗa min.”

Ita dai RAUDA ƙarama babu abunda take sai dariya, domin kuwa ita bata sanma me suke yi ba, kallon Habeeb Hasina tayi tace.

” Kaga tamin ni tafi so kenan.”

Dariya Habeeb yayi yana kara cillata sama tare da cewa.

” Wannan kuma zance kike tafi son Abban ta ko Baby na.”

Dariya kawai Hasina tayi tare da tashi ta shige kitchen tana girgiza kanta.

 

A bedroom ɗin ta ya shigo ya sameta kwance sai famar tura baki take, murmurshi Mustafa yayi tare da zama ya ɗaura kansa bisa kagaɗar Indo tare da cewa.

” Hasken rayuwata ya dai me kuma ya faru kike famar tura baki, faɗa min wani marar adalci ne ya taɓa min Rayuwata.”

” Masoyi ba kai bane tun jiya nake binka cewa ka barni naje a amshi kayan Auren Zahra dani amma kaƙi kasan dai idan banje ba gaskiya ban yiwa Zahra adalci ba.”

Murmurshi Mustafa yayi tare da cewa.

” Daman wannan ne fushin naki to kwantar da hankalin ki, itama Zahra tace ta yafe miki zuwa tunda tasan baki da lafiya, kina fama da wannan laulayin ne zaki wani karɓar kayan Aure.”

” Shikenan tunda haka kace Allah ya sanya Alkairi daga baya naje naga kayan.”

Rungume ta yayi tare da kai mata kiss a kumatun ta, yana cewa.

“Ya Mustafa kamin kuss irin wanda ake yi a tibin Hajiya INNA”

Murmurshi Indo tayi ganin Mustafa ya tuno mata yarintar ta, dubanta yayi yace.

” Miƙo min bakin na miki kuss, ƴar ƙauyen DASINA, yanzu ba sai kin nemo agajin jama’a ba na suzo su taya ki rokata na kuss yanzu ba ke kaɗai kike sona ba, nima ina sonki matata.”

Dariya Indo tayi tare da haɗe bakinta dana Mustafa tana tsotsa kamar wacce ta samu sweet, sun juma a haka kafin salon nasu ya sauya.

Daddare Indo ta kira Zahra a waya sun juma suna taɗi da Zahra kafin Indo ta kashe kiran.
************************************

Rayuwa tana gudu yayin da kwanaki sai tafiya suke, cikin Indo ya cika wata Tare da kwana goma ranar wata juma’a Indo ta tashi da naƙuda sosai hankalin Mustafa ya tashi babu abunda yake tunowa sai RAUDA, ranar da take naƙuda a asibitin su Habeeb a kai Indo haihuwa, sosai hankalin Mustafa yake tashe da Momy aka kai Indo haihuwa ita dai Momy addu’a kawai take yiwa indo Allah ya sauƙeta lafiya, cikin ikon Allah kuwa Indo ta haihu bayan taci baƙar wahala yayin da ta haifi yaranta biyu wato ƴan biyu mace da namiji wayyo Allah kuzo kuga farin ciki wajen wannan family, sosai sukayi farin ciki da samun wannan ƙaruwa da sukayi, yaran aka fara fitowa dasu naɗe a cikin towel, farare dasu kyawawa, Momy ce ta amshi namijin tana dariya tare da cewa.

” Gaskiya bazan ɗauki kishiya ba, gara na ɗauƙi mijin yafi min.”

Dariya Habeeb yayi da ya fito daga Office ɗin sa kasancewar ba shi bane ya karɓi haihuwar doctor Zainab ce ta amsa karɓar yarinyar yayi daga hanun doctor Zainab yace.

” Kai Momy irin wannan tsoron kishiya haka, lallai ƴata da kwarin ta tazo tunda har ta fara sakawa wasu tsoro cikin zuciyarsu.”

Dariya Momy tayi tace.

” Haba ta isa ta samin tsoro, Baby RAUDA ma ya ta ƙare dani bare kuma ita ƙaramar ƙwaro data iso duniyar yanzu.”

Dariya sosai Habeeb yayi Mustafa yace.

” Babu wani nan ke dai kawai kin tsorata kinga manyan mata sunzo.”

Cikin farin ciki da ráha suke wasa da dariya, har aka fito da Indo zuwa ɗakin hutu, bayan sun mata allurar bacci Saboda ta samu hutu.

Ƙarfe biyar na yamma Indo ta farka Momy ta gani zaune yaranta kuma suna kwance gefen ta, bin yaran take da kallo yayin da take jin wani sonsu na shiga zuciyarta, ai kuwa kamar wacce suke jira ta tashi, macen ta fara callara kuka, Momy ne ta tashi tace.

” Maza tashi ki Zauna ki bata nono tasha.”

Sunkuyar da kanta Indo tayi alamun kunya, murmurshi Momy tayi tare da cewa.

” Wai kunya ta kike jine, kinga tashi ki bata tasha aima sunyi ƙoƙari tun safe fa basu nemi nonon ba, tashi Indo tayi ta zauna, Momy da kanta ta ɗauki yarinyar tasa mata a cinyar ta, aikuwa Indo na samata nonon a bakin ta, tana fara zuƙa Indo taji wani azabar zafi da sauri ta cire nonon daga bakin ƴarinyar tana cije leɓenta, murmurshi Momy dake kallon su tayi tace.

” Daurewa fa zakiyi ki basu nonon nan da zarar ruwan nonon ya fara kaiwa bakinta zaki daina jin zafin duk wata macen data haihu sai da taji wannan zafin shayarwar, bata maza ina kallon ki.”

INDO bata ce komai ba ta mayar mata da nonon bakinta, tana runtse idonta, haka ta daure ta bawa yarinyar nonon.

Da magaruba Mustafa ya shigo asibitin lokacin kuma Momy ta fito shan iska waje, a gefen gadon ya zauna, tare da duban Indo, ya sunkuyawa ya manna mata kiss a goshin ta yace.

” Sannu Uwar biyu, ya dai ina dai normal kike jin jikin ki babu Wata matsala, sun bamu sallama ne yanzu.”

Murmurshi Indo tayi tana kallon mijin nata tace.

” Babu Abunda nake ji komai normal.”

” ALHAMDULILLAH!!” Ya furta tare da saka hanu ya ɗago macen da take hanun Indo dabino ya ciro daga aljihun sa yasa a bakinsa ya tauna sannan ya dinga sawa ƴarinyar a bakinta, Bayan ya gama ne ya ɗauko zamzam shima ya bata, kafin ya kama kunnenta ya mata kiran sallah, har sau Uku, sannan ya ajiye ta ya ɗauko namijin shima yanda ya yiwa macen haka ya masa kafin ya dubi Indo yace.

” Alhamdulillah!! Na godewa UBANGIJIN na daya nuna min wannan ranar da kika kasance matsayin uwar ƴaƴa na, na daɗe ina mafarkin wannan ranar sai gashi Allah ya cika min buri na, tabbas Ubangiji ya min ni’ima, fatana Allah ya yiwa Rayuwar waɗannan yara uku da Ubangiji ya bani Albarka, ya jiƙan mahaifiyar Baby.”

Da ameeen Indo ta amsa tana murmurshi, shigowar Momy shine ya katse musu zancen nasu, cewa Momy tayi.

” Bari na haɗa kayan mu shige ko.”

Tashi Mustafa yayi tare da cewa.

” Bari naje na musu bill ɗin kuɗin su kafin ki haɗa kayan sai mu wuce.”

Fita Mustafa yayi ita kuma Momy ta hau haɗa kayan.

Ƙarfe tara suka shigo cikin gidan, Inda suka samu Hasina tana Zaune ta gama gyara musu gidan, Mustafa a falo ya samu RAUDA ƙarama wacce suke kira da Baby, ɗaga ta sama Mustafa yayi yana mata wasa, ita ko sai dariya take Rungume ta yayi a jikin sa yana jin ƙaunar ta, bedroom ɗin sa ya shige da ita a kafaɗar sa, murmurshi Hasina tayi, domin kuwa tana ganin darajar Mustafa a cikin idonta domin kuwa ya mata Hallaci a rayuwarta ada kullum tana cikin kukan rashin haihuwa, sai gashi lokaci ɗaya Mustafa ya share musu hawayen su ta hanyar basa kyautar ƴa, tun sanda ya musu wannan kyautar basu ƙara tunanin haihuwa ba.

MOMY tollet ta shige ta haɗa ruwan wanka mai ɗumi sannan tasa Indo a gaba har tollet ɗin Momy da kanta ta gasawa Indo jikin ta da towel, sannan ta fito ta barta a tollet ɗin zatayi wanka soso da sabulu, Momy bata yiwa yaran wanka ba kasancewar sunce dole sai gobe kafin a musu wanka, sosai Indo taji daɗin jikinta da tayi wankan, Hasina ce ta daga yaran tana yiwa indo SANNU, Momy kallon tausayi take yiwa Hasina domin kuwa rashin haihuwa akwai ciwo.

Ƴan Dasina ma an buga musu an sanar dasu haihuwar, Goggo Asabe da kanta ta ɗauko hanya washe gari domin itace zata zaunawa Indo har tayi arba’in.

Washe gari da safe Momy ta wanke yaran tas ta shirya su cikin pink ɗin riga da wando sosai yaran sukayi kyau Mustafa sanda ya shigo dubasu ne yayiwa yaran huɗu ba, sannan ya musu Sallama ya shige wajen aiki, Zahra ma ba’a barta a baya ba, duk da ranar ce bikin ta, amma sanda ta silalo tazo taga yaran aminiyar tata, duban Zahra Indo tayi tare da cewa.

” Ƙawata gaskiya naso ace wannan bikin naki dani za’a yisa, sai kuma gashi yaranki sun mini cikas sunzo da wuri.”

Murmurshi Zahra tayi tace.

” Karki damu ƙawata, kinsan fa komai sai Allah yayi Allah ya yiwa Rayuwar su albarka, kinga yanzu bari na samu na tafi daƙyar ummi ta barni na fito, tace ma tana gaidaki kafin tazo.”

” Shikenan ƙawata babu damuwa na gode sosai, ki cewa ummi ina gaisheta bari ma na baki saƙo ki kaiwa Ummi.”

Tashi Indo tayi ta buɗe durowar ta ta ciro wani shegen agogon bango mai tsadar gaske tare da rafar kuɗi tazo tacewa Zahra gashi ki kaiwa Ummi kice ina gaisheta, karɓa Zahra tayi kafin Indo ta rakata har parking space, Goggo Asabe ta iso lafiya yayin da Indo tayi murnar zuwan nata.

 

Ana gobe suna Aunty Hindu da sharifa suka diro ƙasar, sosai Indo tayi farin cikin ganin Sharifa, Ranar kusan kwana sukayi suna hirar yaushe gamo, washe gari suna yarinya macen taci sunan *HAJIYA INNAH* wato *NANA KHADIJAH* shi kuma namijin sunan Baban Indo yaci *MUSA* Inda Sharifa tace ake kiran macen da *Ijlal* shi kuma namijin ake kiran sa da *Mus’af* taro yayi taro sosai Indo ta samu kaya sosai Aunty Hindu ma akwati biyu ta mata cike da kayan baby, Mustafa kam ba’a maganan Abunda yayi domin kuwa faɗin Abunda yayi ma bata lokaci ne, Habeeb ma ya taka rawar gani.

Haka akayi taro lafiya aka tashi lafiya cikin farin ciki.

Kwanan su Indo talatin da haihuwa sosai Kuma take samun kulawa a wajen mijinta da uwar mijinta ranar da ta cika kwana arba’in washe garin ranar Goggo Asabe ta koma da tara ta arziki, a nan ne take sanar da Indo cewa Mustafa ya saka an rushe gidan su an musu ginin zamani, tace har ruwan bohol yasa aka ja musu a cikin garin sannan ya buɗewa Tanimu babban shagon tireda wanda babu Irin sa kaf cikin garin, sosai Indo tayi farin ciki, harda hawayen ta domin kuwa taji daɗin ruwan daya ja musu domin kuwa Dasina sun juma suna fama da rashin ruwa sai na rafi na rafin ma wahala yake musu a rani.

Yau Indo da shirin ta tsaf ta shiga bedroom ɗin mijin nata bayan ta kintsa yaranta, a gadon su dake gefen na mahaifin su ta kwantar dasu, sannan ta faɗa saman bed ɗin mijin nata, murmurshi tayi tare da cewa.

” Thank miji na, bazan taɓa mantawa da alkairin da ka min ba.”

Jawota Mustafa yayi jikin sa tare da cewa.

” sorry for what numfashina.”

Murmurshi Indo tayi tare da cewa.

Abun alkairin da kamin na gyara gidan mu, da kuma buɗewa ya Tanimu shago, da ruwa daka kawo mana gaskiya naji daɗi sosai Allah ya saka da Alkairi ya kara arziki.”

Murmurshi Mustafa yayi ba tare daya ce mata komai ba ya haɗe bakin su waje ɗaya yana mata wani hut kiss, yayin da itama ta biye masa suka lula duniyar ma’aurata.

 

***********************************************

*AGURGUJE*

 

Da ƙaton cikin ta na hango ta tana ƙwalawa yaran kira dake famar wasa a compaunt ɗin gidan.

” Ijlal wai ba kiran ku nake bane, kuzo maza ku ɗauki bag ɗin ku, ku tafi islamiyya lokaci yayi, ashe daman tun ɗazu dana sa muku uniform ɗin nan kuka fito kuka tsaya wasa.”

Da gudu Ijlal ta ƙaraso wajen ta tana cewa.

” Ummu brother Mus’af nake jira, fa yace zaije ya kira Aunty Baby a part ɗin su, kuma Ummu yanzu uncle Ishaq ma yace idan muka yarda har ya dawo daga masallaci bamu tafi school ba, sai ya zane mu.”

Kama hanunta Indo tayi tana cewa.

” Ai gara ya zana kun ko zaku daina let ɗin school muje maza ki shirya kafin shima Mus’af ɗin ya shigo ya sameni.”

Ai kuwa bata rufe bakinta ba Mus’af ya fito da gudu daga part ɗin Hasina yana cewa.

 

” Ummu Aunty Baby harta shirya mu kawai take jira.”

Tisa ƙeyarsu Indo tayi a gaba har bedroom ɗin su, ta ɗauki bag ɗin nasu ta basu tana cewa.

” Kuyi addu’ar fita daga gida fa karku manta.”

To suka ce mata sannan suka fice da gudu, Indo ajiyar zuciya ta sauƙe Sannan ta nufi kitchen ta cigaba da aikin abincin dare, ta bayan ta taji an Rungume ta, tasan ba kowa bane sai ogan nata, juyowa tayi tana kallon sa kafin tace.

” Hmmm, wato dai kai da yaran ka bazaku barni na huta ba, na samu na kora su school nazo kitchen zanyi aiki shine kaima ka shigo ka hanani aiki ko, wai ma tukunna mai ya dawo da kai daga wajen aiki yanzu.?”

 

Murmurshi Mustafa yayi tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yana shafa cikin ta da yayi ta haihuwa ko yau ko gobe yace.

” Na dawo da wuri ne domin naga *BUGUN NUMFASHI NA* naga INDON ƘAUYE DA YANZU TA DAWO INDON BIRNI uwar biyu, wai ma tukunna ya naji kitchen ɗin ya turniƙe da ƙamshi ne, me ake dafa mana *MASOYIYA*.”

MURMURSHI INDO tayi tare da turasa waje tana cewa.

” Na dai ga alama so kake ka hanani aiki, *MASOYI* maza samu waje ka jirani idan na kammala na fito na same ka” ta ƙarasa maganar tare da kanne masa Ido.

 

Murmurshi kawai Mustafa yayi, shima ya kanne mata ido tare da cewa.

 

” Ina sonki masoyiya.”

Murmushin itama ta mayar masa tace.

” Ina sonka Bugun numfashina.”

 

 

Tamat bil hamdulillah.

Anan na kawo ƙarshen wannan littafin.

Abunda na faɗa dai-dai ina roƙon ubangiji ya bani ladansa, kuskuren dana yi kuma ya yafe min.

 

Ina roƙon ubangiji daya sa makaranta su amfana da darasin dake cikin wannan littafin.

Masoyana bazan taɓa mantawa daku ba domin kuwa Tabbas kun nuna min ƙauna a cikin wannan littafin tun daga part one har zuwa part two, ina sonku masoyana a duk inda kuke.

 

To masoyana bari na baku wani albishir, kuce min goro.

Yanzu ma dai inan tafe da sabon labari na, wanda na daɗe ina muku nazarin sa labari ne wanda yasha banban da labaran da nake kawo muku labarin ya ƙunshi tsantsar SOYAYYA tausayi yaudara cin amana ƙiyayya, Rashin yarda Damuwa duk cikin labari na mai taken *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Wanda zan fara saki muku shi ranar ƙaramar sallah.

Shi dai *RUƊANIN ZUCIYA BIYU* na kuɗi ne zan sake muku shi akan farashi mai sauƙi *200* Kacal zaku biya ku karanta cikin sauƙi karku manta da cewa ta hanyar Siyan LITTAFI nane kawai zai sa ku nuna min ƙaunar da kuke min ga mai buƙatar Siyan LITTAFI na sai tuntuɓeni ta wannan number.

*08147537180*

*Alƙalamim Rasheedat Usman✍🏻*

 

*Ummu Nasmah ce*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]