[Advertisements⬇️]

KHADIJATUL SABREEN HAUSA NOVELS - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN*🧸

 

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

Arewa book👉@Miss Hajo✍️

*MARUBUCIYAR*
👇
< *Komai muk’addari ne* >
< *K’addarar soyayyya ta* >
< *Najmat Abiy* >
< *Ni da Yaya Arman* >
< *Auren wata Tara* >
~And now~
< *KHADIJATUL SABREEN* >

بسم الله الرحمن الرحيم

TEAM GAWURTATTU BIYAR✨🔥
________________________________

 

*GODIYA*

_Ina Godiya ga Allah ( s w a ) da ya k’ara bani ikon Fara rubuta wannan littafin Mai taken *KHADIJATUL SABREEN* tsira da aminci su k’ara tabbata ga Annabi Muhammad ( S A W) tare da ahalinsa da tsarkakkun sahabbansa,Ina rok’on Allah ( s w a )yanda na Fara rubutun Nan lafiya ya sa na Gama lafiya cikin amincewarsa da yardarsa Allah bani ikon rubuta abunda zai amfane Ni ya amfani al’umma ko bayan Raina,Allah ya tsari alkalamina da rubuta abunda yake ba Alkhairi ba,Allah yafe Mani Dukkan kura Kuran da zanyi a rashin sani zanyi amfani da wannan damar wajen nuna tsantsar Godiya ga d”aukakin masoya nagode kwarai da zallar soyayyarku gareni Ina matukar alfahari daku a duk inda kuke ALKHAIRIN Allah Yakai muku har Gadon baccinku farincikinku shine nawa masoyan asali miss hajjo takuce ta har abada Ina fatan Shima wannan littafin zaku so Shi ku kaunace Shi fiye da yanda kuke Cikin kaunar littafai na na baya nagode kwarai da nuna soyayya love you all my fans_ 💃💃💃

*GARGAD’I*

“`Ba yarda wata ko wani yayi amfani da wani Bangare ko ya juyamun labari ko sayarmun ko edit da dai sauran abubuwan rashin adalci littafin Nan mallakina ne Ni Hajara L Sadeeq (Miss Hajo) muddin haka ta faru Zan d’auki tsatsauran mataki“`

*GAISUWA*

_Dubun gaisuwa a jinjina ga d’aukakin members na novels group miss hajo Ina matukar alfahari daku Ina ji daku irin sosai d”innan Tatattun masoya Allah yabar kauna da soyayyya ina yimuku fatan Alkhairi Gabaki d’ayanku,dan ban Isa iya lissafo sunanku ba ,Tare da Daukakin members na kungiyar jarumai writers d’aya tamkar da dubu,Alkhairin Allah yakai Muku har gadon baccinku ina yinku Kuma ina kaunarku fiye da yanda Kuke Cikin nunamun_

“`BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM“`

🅿️………*1 & 2*

Matashiyar yarinya ce wacce a shekaru bazata wuce shekara Goma Sha d’aya ba sanye take cikin wata y’ar karamar y’ar kanti da ta tsaya Mata iya gwuiwa tsalle_tsalle kawai take Ta na wasanta hankali kwance A compound d’in tsararren Gidan da ya had’u Dukda bashi da wani girma na azo a gani Amma Gidan ya tsaru da shukoki ga tsarin gidan ya had’u Wanda kallo d’aya zakayiwa Gidan kasan mamallakin Gidan Yana Da Hali Sosai parking space din Gidan bazai wuce d’aukar mota biyu zuwa ukku ba,.

,part d’aya ne Gidan Wanda komai Yana ciki sai d’akin Mai gadi dake gefen jikin hadad’d’en get din Gidan dake zageye da wayar security,gefe guda Kuma motoci da kekuna tare da tarkacen abubuwa na wasan yaran tundaga kan Lilo,da sauransu Sosai nayi mamakin tilin kayan wasan dake wajen ba abunda babu na wasan Yara,tayi wasa da wancen tayi da wancen kafin tahau kekenta ta Fara jagaye Gidan dashi,.

Mai gadi dake Zaune Yana Jin radio Ganin Tayo wajenshi da Keke ne ya sanyashi saurin tashi ba shiri Yana komawa gefe Dan yasan k’aramun aikin ta ne ta bigeshi Saida yaga wucewarta kafin ya Girgiza Kai ya ce “Allah ya shiryeki yarinyar Nan”

Wata matashiyar Mata Ce ta fito daga cikin part din sanye take cikin tsadadden doguwar rigar Leshi da yasha d’inki ubansu ,Doguwace Mai madaidaicin jiki black beauty ce Masha Allah kyakyawa dukda shekaru basa boyuwa Amma a k’alla bazata wuce shekara talatin ba zuwa sama kad’an Amma hutu da gayu da Jin dad’i Dana Lura sun zauna a wajen bazaka kalleta kace takai shekarunba,.

Kai tsaye wajen Da taga Yarinyar tayi da keken ta nufa cikin sauri tayi sand’a ta kamota tare da rik’e keken ta ce “Tun d’azu nayi maki magana Kizo na Sanya maki Kaya ki tafi islamiya shine Kika gudo Nan to maza,wuce muje kishirya Dan gidanku Kullum saikin sani ciwon kai Akan islamiya”.

Juyowa tayi tare tsatsareta da Dara daran idanunta masu matukar d’aukar hankali tubure fuska tayi kamar zata Sanya kuka cikin shagwababbiyar fuskarta da na Lura fuskartama gaba d’aya ta shagwab’e ce ta ce “Ni Mom bazanje ba na gaji ki rabu da ni “ta k’arasa fad’a Tana Shirin fashewa da kuka “.

Sai Sannan na kare Mata kallo kyakyawa ce sosai ta bugawa a jarida Fara ce Sosai Haskenta har wani shuni_shuni yake,Tana da round face Tare da manyan idanunta Wanda sune babban abunda ya k’ara fito Mata da ainahin kyaunta,hancinta madaidaici da yayi das da kyakyawar fuskarta,sai d’an k’aramun bakinta Daya chuno gaba Masha Allah shine kawai abunda zaka kalla yarinyar ka ambata saboda wani fitinannen kyau da Allah yayi Mata (Gaskiya za ayi budurwa a Nan Na fad’a a cikin zuciya ta) Doguwace y’ar Charas da Ita Bata da k’iba sannan Bata da rama ,lalllausan bak’in gashin kanta da akayi Mata kitso shuku ukku an Sanya beat masu matuk’ar d’aukar Ido duka gashin kan Nata ya saukar Mata har kasan k’eyarta Ni kaina Saida nayi mamakin yawa da silb’in gashin saika d’auka attachment ne aka Sanya saboda yawanshi Duk inda kyau yake yakai kyau to dai yarinyar Nan takai a kirata da kyakyawar k’arshe shuwa Arab kenan(Na fad’a a cikin zuciya ta Dan Ni kaina kyaun yarinyar Saida yaso ya zautar Dani kyau kamar aljana lol).

“Cikin sama da murya Mom ta ce “Kinma Isa kik’i zuwa islamiya Sabreen yaushe rabon ki da islamiya kusan sati guda kenan ko Dan Kinga na kyaleki na zuba Miki Ido ubanme kike a gidan da bazaki je makaranta ba awa guda kuntashi,saikinje wlh ko Kuma na lillisaki a gidan Nan tunda Mai d’aure Miki d’in ganinshi Yana hanaki zuwa School d’in baya Nan”

Ta fad’a cikin y’ar Tsawa Tana kamata tare da sauketa daga kan keken “Jin abunda mom ke cewa NE na saitaje makaranta Wanda ba abunda ta tsana sama da zuwa islamiya ya sanyata tirjewa tare da zaunewa a wajen ta Fara kuka da burgima a wajen kamar wacce akawa bugun mutuwa Sosai take kuka Tana cewa Bata zuwa.

“Takaici Duk ya Isa mom inda sabo ta saba da sangartar y’ar Tata Wanda Duk mijin ta ne ya sangartata ita kanta tasan bilhak’k’i matsayinta na uwa Tana iya bakin k’ok’ari wajen Ganin ta bawa y’ar Tata ingantacciyar tarbiya Amma abun ya gagara Kota Fara Daddynta saiya ruguza Mata ta rasa yanda zatayi da wannan bahagon halin na y”artata Wani irin zafi takejin ranta Gashi dai Tana ji Tana Ganin ilimin addini Yana neman gagarar tilon y’artata Sa’anninta hada Wanda suka kusa sauka Amma sabren hizif biyar cikakke Bata kawo maka Shi sangarta da b’aci da wasa da Jan magana Shi kad’ai ta iya”.

“Numfasawa tayi daga wanna tunanin da ta lula tasan duka baya yiwa sabren da duka yanayi Mata da tuni ta shiryu dukda ita kanta ba ason ranta take dukan Nata ba durkusawa tayi tare da kamo hannunta ta fusge Tana kuka ta na cewa

“Daman nasan bakya Sona Dad kawai ke Sona Shiyasa kike yimun Tsawa Kuma saina fad”a Masa idan baya nan kina duka na “ta karasa fad”a cikin kuka kamar wacce aka daka”,.

Cikin lallami da lalashi mom tace “Sorry Mom D’in Dad Ba tsawa nake maki ba Ina sonki Nima kamar yanda dad dinki ke sonki,kiyi hakuri muje na saukeki a school nasan Kema kinason kiyi karatu ki hardace Qur’an kizama babbar malama ni da dad muyi alfahari dake ko daughter na to yi hakuri tashi muje na kaiki idan muka dawo Zan saya maki manyan chocolate”

Turo Baki tayi Tana murza.idonta ta ce “Mom malamin Ne mugu Ni banason zuwa “Had’e fuska Sosai mom tayi ta ce “Kinga Ina lallamaki shiyasa kike b’atamun lokaci ko?Turo Baki tayi Tana cigaba da murza idanunta”mom ji take kamar ta daketa hakanan take daurewa Tana wannan lallamata d”in Dan batason ace sai duka Ne kad’ai zatayi Abu saboda Shi saboda ba abunda take tsoro sama da tab’a.lafiyarta amma Dole ta tsoratata cikin fad’a ta ce,.

“wlh Zan zaneki Sabren ,Dan iskanci waike yarinya ce da za ace Kullum saikin bani wahala Akan komai,jibi Sa’anninki fa akan idonki haka suke da iyayensu Meyasa kikeson bani wahala Sabren komai sainayi fafatu akanki ,kinsamun ciwon Kai kafin kiyi to wlh Zan dake ki yanzunnan tunda bakisan lallami ba duka Kika sani”

Jin abunda mom ta fada ya Sanya sabren tsorata saboda tasan halin mom Sarai zata iya zaneta musamman taga dad bayanan kuma ta rantse bazataje islamiya ba hakan ya sata saurin Mikewa tsaye Tana kallon mom ta ce “Zanje to Amma saidai ki d’aukomun kayan makarantar Ni bazan shiga ciki ba”

“A wajen Zaki sauya kayan me cikin yayi Miki da bazaki koma ba uwar kinibibi”mak’e kafad’a tayi ta ce”Ni dai Indai kina son naje saidai ki d’aukomun kayan nasa a nan”Girgiza Kai mom tayi tare da cewa “Allah ya shiryeki ya kawomun lokacin da Zan huta da fitinarki Akan islamiya kin b’atamun sama da mintuna Talatin”kafin ta juya ta shiga ciki da niyyar ta d’auko Mata kayan,.

Ai SABREEN na Ganin mom ta shiga ta kwashi k’afa da gudu ta ruga tayi bakin get ta fara kokarin bud’e k’ofa Mai gadi daga dakinshi Jin Kara ya sanyashi cewa.

“waye”Ai Tana Jin haka tayi sauri ta bud’e k’ofar tare da kwasawa a guje Tana dariyar wayan da tayiwa mom gida Mai kallon gidansu ta nufa kwankwasa k’ofar tayi da karfi Wanda ba shiri Mai gadin ya taho da sauri ya bud’e Yana Kallonta yasan Daman wanna aikintane bubbuga get kamar zata b’alla cikin Gidan Kai tsaye ta nufa Tana Dariya a parlour ta tarar da maman su Anesa “wajenta ta nufa ba gaisuwa ba komai ta ce”Momy Ina Anesa” “Suna makarantar islamiya sabren ke meya hanaki zuwa “.

” ta fada Tana Kallonta “Ba tare da ta Bata amsar tambayar da tayi Mata ba ta juya ta yi waje Saida ta lek’a taga ba kowa k’ofar gidansu kafin ta fito gidansu Ummy ta nufa nanma Tana zuwa akace Mata suna makaranta tsaki taja Tana Jin haushin ta rasaa abokan wasa tunowa da Affan Shima irinta Ne bayason zuwa islamiya ya sanyata saurin rugawa gidansu dake kusa da gidansu shima irin bugawar get din datayiwa Gidan su anesa tayi mashi a compound ta tarar da Shi Yana Lilo ajiyar zuciya ta sauke tare da rugawa inda yake ta bayanshi ta zagaya tare da rufe Masa fuska “hhhh ai naganeki yarinya duk sanda zakizo saikin rufe mun fuska shiyasa na ganeki kima bud’e”.

Dariya tayi Tana budewa tare da cewa”Ai Zan chanza salon tsorataka Zan dingayi Sosai”Dariya yayi ya ce “Haba yarinya ai bazaki iya ba Kema bakije islamiya ba “gyada Masa Kai tayi Tana Turo baki ta ce “mom tace sainaje shiyasa na gudo Nan Muyi wasa”tab’awa sukayi ya ce “good girl besty Gwara da bakijeba Nima Aunty ce kadai a Gidan mama Bata Nan shiyasa nace Mata bazanje ba “.

Sosai suka shiga wasansu kamar ko yaushe Wanda har magriba hankalinsu kwance Bangaren momy Kam Sosai ta shak’u tare dayin alkawarin ta dawo saita zaneta Ta tsani wanna yawo gidajen unguwa Da take Mata ta rasa wani irin jarabar wasa ne a ran yarinyar Tata Gashi batasan magriba tayi ba ta dawo gida saidai ta dinga bi gida gida Tana neman ta yanzun ma Ganin magriba tayi ya sanyata mik’ewa tare da Sanya hijab dinta ta fito Tana nad’e da karamar bulalarta.

Gidan su Anesa ta Fara nufa kafinma ta Ida shiga ta tambayi Mai gadin Tana ciki”yace tashigo tun dazu ta fita cike da takaici ta juya Tana kallon unguwar ba kowa sai mazajen wasu dake haramar nufa masalacci gidansu Affan ta nufa kamar tasan Tana chan Tana ko shiga ta hangota ita Affan suna game a Tab Cikin sand’a ta nufa wajen.

SABREEN Bata lura da mom ba sai saukar bulala da taji a cinyarta data yace game yayi dad’i ba shiri ta kwalla uban k’ara Wanda duka sai da ya kauraye Gidan k’ara tsalla Mata wata mom tayi Sosai sabren ta k’ara rikicewa ta Kara kwalla k’ara tare da Fara birgima a wajen Tana ihu Tana kuka Maman Affan Da shigowarta kenan Gidan ta dawo daga unguwa cikin sauri taje tare da rik’e bulalar dake hannun Mom Tana Shirin lafta Mata wata ta ce “Haba Amina meye haka Zaki Samu yarinya kiyi ta duka me tayi Miki “Cikin b’acin Rai Mom ta kalleta ta ce,

“Rabu na zaneta maman Affan Yarinyar Nan sati biyu kenan rabonta da islamiya yau karkiga lallashinshi da nayi Mata akan tazo na kaita ta k’iya karshema sai wayau tayimun kafin na shiga cikin na dauko Mata Kaya wlh sai neman Yarinyar Nan nayi na rasa sama ko k’asa yanzu fa abunda takemun kenan yawo yau Bata chan Gidan gobe Bata chan na Hana Mai gadi barinta fita Amma wlh saitasan yanda tayi ta fita na dake ta d’in na dake ta d’in Amma abun bayama baya sai gaba yakeyi”.

Ta karasa fad”a cikin k’unar Rai”cikin kwantar da murya maman Affan tace “Sai hakuri Amina yaran Nan na yanzu saidai addua kinganshi Nan Shima aminin Nata in ba Ina Gidan Nan ba baya zuwa makaranta Ni da mahaifinshi kadai yake shakka Amma yayyunshi gaba d ‘aya ya rainasu Basu Isa su sanyashi yayi ba ai Daman duka biyu Kika zanemunsu yanzu dai kiyi hakuri Dan Allah karki sake dukanta bazata sake ba “.

,a ran Mom ta ce “Ni Ai da Tana shakkar tawa ma ai da dad’i da na gyarata “a fili kuwa Murmushi tayi ta ce “Shikenan maman Affan bari muje magriba nayi saina zagayo”

“To Shikenan Amina karfa ki sake dukanta”Insha Allah “mom ta fad’a fuskarta dauke da Murmushi dakyal maman Affan ta samu ta mikar da sabren Harta yarda mom ta Kama hannunta suka wuce gida Wanda har lokacin shashshekar kuka take,.

A gida ko sauya Mata fuska Sosai mom tayi hakan yasa batayi Mata gardama wajenyin sallah ba Tare sukayi Dan tasan Zata iya sake dakarta Dan taga dad baya Nan a ranta take ta ayyanawa Dad Yana dawowa duk saita fad’a Masa zalincin datayi Mata Saida sukayi isha’i kafin Suyi dinner Har lokacin sabren fushi take da mom itama Bata Kuma Mata magana ba,.

wayar mom ce tayi ringing bayan tayi picking kalmar Da Dad ya fara ambata Daga wayar shine “Ina Baby Bani naji muryarta please I miss her so much wlh ”

kallon sabren mom tayi Jin tanajin abunda dad yace taga har wani zumud’i take a Bata Shi, danne speaker tayi tare da Kauda wayar daga kunnenta ta ce.

“Saura kice Masa na dakeki kiga irin dukan da Zan sake maki “Dan tasan Sarai ta fad’a Masa ta daketa jarabar dazai Mata Bata wasa bace musamman tayi mashi kuka ma zai iya b’arin Course D’in daya tafi wanda Yana gamawa Za a k’ara Masa babban girma,a wajen aiki ya dawo.

Cikin sauri sabren ta gyadawa mom Kai kamar zatayi kuka ta ce bazance Masa ba mom Dan Allah ki bani shi”.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da Kara wayar a kunne inda taji Yana cewa “kinyi Shiru Ina magana Sweetheart kina jina Kuwa”Sorry dear network Ne ga ta”.

Ta fad’a Tana mikawa sabren wayar cikin sauri ta maza ta Kara a kunne fara’a cike da fuskarta ta ce.

“hello dad”Hey My Beautiful Angel Yakike nayi missing d’inki yau banji muryarki ba sai yanzu fatan kinyiwa Dad hakuri aikine yayi mashi yawa Yana inda ba network”.

cikin shagwaba ta ce “Dad Yaushe zaka dawo I miss you more please ka dawo”ta k’arasa fad,a kamar zata fashe da kuka,.”Daga bangaren dad ya ce “i”m sorry my angel Zan dawo soon kodan na ga babyn Dad kidaina damuwa please aiga mom d’inkinan Kuma zamu dinga waya ko”.

Tana Shirin fashewa da kuka Ta fara diddira k’afa ta ce “Ni dad gobe nakeson ganinka ka dawo ni banason Zama da mom”.

Hararar Da mom ta Galla Mata ce ya sanyata turo Mata Baki “hankali tashe dad ya ce subhnallah daughter me mom d’in tayi maki”.

chaza mom ta janyo tare da Mata nuni da zata tsaula Mata hakan ya sanyata zaro ido Tana Shirin rugawa”Daga Bangaren dad yace “Baby fad’amun me mom d’in tayi maki”bakomai dad jaraba dai takemun tunda ka tafi”Badai ta dukan mun ke ba ?.

gyada mashi Kai tayi kamar Yana gabanta ta ce “Eh Bata duka na”Nauyayyar Ajiyar zuciya Dad ya sauke wanda har Suna ji daga waya ya ce “Kiyi hakuri zanyi mata magana bazata sake maki jaraba ba,Turo Baki gaba tayi ta ce .

“Ni dad ban yarda ba inma Kayi Mata maganar ai Baji take ba nidai kawai kadawo sannan Kuma yau ma ko ice cream d’in da kace ta dinga sayamun kullum.bata sayamun ba “.

“ita aminar ce take Miki haka Daughter?ita Aminar fa dad Danma ban fad’a maka saura mugancin…..kwace wayar da mom tayi ne yasanya Bata k’arasa abunda take son fad’a ba da Ido ta nuna Mata da ta shiga daki da gudu ta ruga Tana kukan sangarta, Kara wayar a kunnanta mom tayi ”

“Meyasa Kika amshe wayar ki bani y’ata muna magana “dad ya fada “Dare yayi baccci zatayi kasan gobe akwai school sanadin ta bani wahala wajen tashi ne Gobe kwayi wayar”Daga Bangaren dad ya ce,

“Wai meyasa bazaki chanza ba Amina keda yarki d’aya tilo kenan Da Allah ya bamu Amma batajin dad’in Zama dake fisabillahi bazaki jawo yarki jikiba ki nuna Mata soyayyya taji dad’inki Amma Banda fad’a ba abunda kika iya Mata Amina wanna rayuwa ce kuwa fisabillahi,,”

“Kasan Sarai banason haka Abban Sabren duk kokarin da nake akan Yarinyar Nan nasan ba gani kake ba to ba ruwanka da tsakani na da ita kamar yanda bana shiga tsakaninku,Meye na tambayar yarinya Dan baka Nan saikace wacce take hannun matar uba ,gaba d’aya kaja yarinyar Dana haifa ta rainani Ina Gini kana ruguzamun saina tallabo y’ata na Fara Bata tarbiya da kazo ka ruguzamun duk ginin da nayi fisabillahi banason haka wlh kasan abunda ke had’ani rigima dakai kenan Sarai”

Cikin kwantar da murya dad ya ce “uwar Y’an fad’a abar maganar ya gida ya Kuma kewata “Ajiyar zuciya mom ta sauke tare da sakin lallausan Murmushi ta ce “kewarka ta na Nan ta addabemu dear…..sun dauki tsawon lokaci suna hirarsu cike da so da kaunar juna Saida dare ya tsala kafin Suyi bankwana.

 

Koda tashiga Dakin Sabren tarar da ita tayi tayi rubda ciki Tana bacci ga alamun ma tajima Tana bacci gyara Mata kwanciyarta tayi tare da tofa Mata adduo’i kafin ka kashe Mata glove din dakin ta rage Mata gudun fan ta kashe ac kafin ta wuce bedroom dinta itama Dan ta kwanta.

washegari tun Asuba Saida ta Gama shirya Mata break fast da abunda zata tafi dashi school kafin ta tasheta dakyal…

cikin 30 minutes Tagama shiryawa suka fito mom na rik’e da basket da bag dinta,sabren Tana Sanya da kayanta na makaranta da rigar ta da ta tsaya Mata iya gwuiwa safarta Mai hade da Wando Fara kal sai Yar karamar hijab dinda ko k’irji Bata rufe Mata ba momy ke.driving har suka Isa makarantar su Wanda a bakin get ta sauke ta bayan taja Mata kunne akan fad’a Saida taga shigarta kafin ta juya da kan motar ta.

Sabren ko kamar ko yaushe Tana shiga class Bangaren maza taje ta zauna Dan shine permanent seat dinta Kuma sune abokanta Dan kawayenta Mata Basu da yawa Amma maza Kam kowa abokintane tafijin dad’in mu’amularta da maza fiye da Mata ,Hindu ta hango ita da zeey kawarta da sukayi fad’a jiya suna nunota alamar gulmarta suke Sabren Daman Mai jira Kallon Affan bestynta dake kusa da ita ta yi ta ce.

“Besty yau sainaci uban Yarinyar chan kagansu chan gulmata suke taho muje ka tayani muci ubansu,Kallonsu Affan yayi yaga sunyi tsuru tsuru, Dariya yayi ya ce “Aikuwadai mu duka biyun suke kallo zasuci ubansu muje kafin uncle ya shigo”suna zuwa Sabren ta shak’o zeey cike da tsabar masifa ta ce “………..✍️

Somin tab’i💃

_Ya kukaji saloooon labarin a cikin zuciyarku masoyan Gaskiya da Gaskiya Ta hanya zazzafan comment Mai dauke da sanyayyen sharrhi Mai sanyaya zuciya shine zai tabbatar mun da yanda kukaji salon labarin a cikin zuciyarku gamai bukatar shiga grp d’ina na what’s app Sai a tuntub’eni Akan wannan number 07026166536_

 

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

 

_*Miss Hajo ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

Arewa book👉@Miss Hajo✍️

 

🅿️………….*3 & 4*

Ta ce “Dan ubanki Ni sa’arkice da Zaki dinga gulma ta Daman bakisan haushinki nakeji ba zako kici ubanki”

Ta k’arasa fada Tana shakota tare da Fara Kai Mata bugu shima Affan Hindu ya shak’a ya hau jibgarta kafin kace me dambe ya kad’ame tsakaninsu class sai hayaniya ake.

Dukda sabren tare suke jibguwa Dama d’aya ta samu ta kada ita nanko ta hau ruwan cikinta tahau jibga sosai zey ta Fara kuka ana haka Uncle ya shigo class d’insu hankali tashe yazo ya rabasu Wanda Saida ya tsoratasu da bulala kafin ya samu ya rabasu,.

“Ku biyoni Office zanyi maganinku Gabaki d’ayanku harke Mai tsukakken bakin Nan jarababbiya Baki da aiki sai fad’a da mutane a aji Duka saina zaneku” .

ya fad’a Yana nuna sabren Da ta ke hura hanci Jin abunda yace NE ya sanyata sakin tsaki tare da murguda Masa Baki ta ce”Ni ba jarababbiya bace ai Ja na su ka yi”.

nuna kanshi yayi Yana mamakin rashin kunyar Yarinyar ya ce “Dani kike”Ganin Yana Shirin lafta Mata bulala NE ya sanyata saurin buga ihu tare da zubewa a wajen ta Fara birgima da ihu kamar wacce ya buga,.

Tsaki Uncle yaja a ranshi ya ce “Allah wadararan irin wannan sangartar، iyaye karfi da yaji su maida y’ay’an su mahaukata da sunan so ” juyawa ya yi ya kalli sauran abokan fad’an Nata ya ce .

“Ku biyoni office ke Kuma minti biyar na Baki Baki sameni office ba kinsan sauran “Yana Gama fad’ar hakan ya fice suna biye dashi Saida sabren taga ficewarsu kafin ta Mike Tana goge hawayen da ta Fara ta kalli Yan class d’insu Daman dukansu su 15 ne ta ce,.

 

“idan uncle ya tambayeku shaida ku ce su suka Fara janmu su suka Fara Kai Mana duka suna zagar Mana iyaye shiyasa har muka Rama idan ba haka ba wlh Babu wacce Zan sake sayawa chocolate da biscuit har ice cream gobe Zan saya muku Indai kuka fad’i haka wlh”.

“cikin sauri Yan class din suka hau ihu suna angama baby SABREEN Big girl ai gwara da Kika dakesu Baki da case zamu Kara abunda baki ma ce ba Amma wlh Allah saikin cika Mana alk’awarinmu na ice cream idan ba haka ba gobe mu tona”

Hararar Jamcy dake maganar tayi ta ce “na tab’a muku alkawari ban cika ba”Sudais “ya amshe da cewa “rabu da ita big girl karta b’ata maki time “Juyawa Sabren tayi ranta gall ga wani dad’i da takeji yanda Yan class dinsu ke kod’ata,

A office din uncle nura Koda ya bincike su, su zey suka ce ita ta Fara jansu ta karyata ta ce” Kuma ko Yan class za a tambaya su suka Fara janmu Saida suka Fara dukanmu tukwana muka rama”,

Duk mamakinta su hibba suke kafin Zey dake kuka ta ce “Karya take uncle Kuma a tambayi y’an class d’in”gardamar da sukeyi ne ankasa gane Mai Gaskiya cikinsu ya Sanya uncle cewa muje na tambayi y’an class d’in naku sannan duk Wanda na Kama shike da laifi saina hukuntashi”

Duka suka amsa sun amince, ana zuwa ko Nan Yan class dukansu suka karyata su hibba ,sukace su suka Fara jansu sudais Ne Mai cewa “uncle Har zagin iyayenta suka dingayi ta kyalesu Saida suka Fara dukanta ne ta Rama “.

Sosai su Zey suka hau kuka Sabren ko wani dad’i takeji a ranta ganin yanda uncle ya hau musu fad’a har Saida yayi musu bulala biyu biyu inda ya had’a har Affan ita Kuma sabren Bai dake ta ba saboda ance janta akayi dukda yayi mamakin har sabren ce za a jata a daketa ta kyale yanda kullum suke fama da case d’in Yarinyar akan fad’a ,amma shaidar da duka y’an class suka Bashi ne yasan ba zaiyu suyi mashi k’arya su duka ba ranshi yace “ko ta Fara hankali ne”.

Saida suka koma seat dinsu Ta dinga bawa Affan hakuri k’asa_k’asa Akan dukan da akayi mashi da hannu yasa ya bugar Mata cinya da k’arfi Wanda ya sanyata sakin dariya ba shiri kallonta uncle yayi Ganin yanda take dariyar ya murtuke tare da yi Mata warning Akan ta sake zai daketa “Hakan ya sanyata yin shiru,.

,bayan barin uncle class d’in Nan sabren ta hau yiwa su Zey dariya tare da yi musu gwalo ta ce gobe ma ku tab’oni kuji Irin abunda zanyi muku,.

Koda akayi break abubuwan da sabren tazo dashi su biscuits chocolate da soyayyar doya da kwai tare suka cinye da y’an class d’insu d’aya kad’ai ta samu taci da haka take saye class mate dinta kome ta samu saita kawo musu ita sai tak’i ci ma ta Basu saboda su dinga tsoranta suna Mata fadanci data shigo ana kitunzurata.
big girl wanna abun sosai yake k’ara tunzurata .

,Koda a ka tashi motar Gidan su Affan tahau kamar ko yaushe a ita ake mayar da ita kaita Ne kawaii mom take shima wani Karin tare take kaisu su biyun,.

 

sai yunwa takeji a palour ta tarar da Mom Tana latsa waya da gudu ta ruga Wajenta tare da yin hug dinta rungumota mom.tayi Tana cewa”oyoyo momyn dad andawo sannu ko ya gajiya”

“Thanks God mom abinci yunwa nakeji “ta fad’a Tana shafa cikinta Daya lotsa tare da marairaicewa ,Mom na rage Mata school materials dinta ta ce,

“Wai ina kike Kai uban abincin da nake girka maki kina tafiya dashi sabren ,na tabbata abincin da nake zuba maki yafi karfin cikin ki dukda, nasanki ba wani abincin kirki kike ci ba Amma kullum Kika dawo da yunwa kike dawomun na kasa gane al’amarin Nan kodai Yaran gari nakewa wahala ta fad”a Tana Kama hannunta tare da nufar dinning Area da ita”

“Mom ba Wanda nake ba fa yunwar ce kawai take zuwa “ta fad’a Tana janyo dining chairs tare da Zama “ta Fara cin lafiyayyar jolloup d’in macaroni da Tasha kifi sukumbiya da vegetables.

Tana ci tana yiwa mom surutu Tana cewa “Mom dad Bai Kira ba yau ki kiramun Shi vedio call Ina son ganinsa nayi kewarsa”ki Gama cin abincin sai na.kira maki Shi “.

Da yamma batayiwa mom gardamar islamiya ba saboda taga Affan harya tafi a chan dinma ba wani karatun kirki sukayiba rabi wasa rabi an dauka har lokacin tashin su yayi mom ta mayar dasu a gidansu sabren suka hau wasansu Tare da su anesa da suka dawo tare bama su wuce gidajen su ba suka yada zango Gidan su sabren ba Wanda ya cire uniform cikinsu sai bayan magriba mom ta hada su da sweet kafin su wuce gidansu da niyyar sai gobe ,

Da daddare sabren ta rasa yanda zatayi ta samu kud’in da zata sayawa y’an class dinsu alkawarin da tayi musu na ice cream ga dad baya nan Daman shine da ta tambayeshi ko nawa yake Bata a palour tayi jugum Kamar wata marainiya tunani ta dingayi idan fa Bata saya musu ba zasu Raina ta su dainayi Mata Kallon big girl ma ta koma small girl kamar su Hindu sannan Nan gaba ko tayi tsokana bazasu goyi bayan ta ba ,oh my God ta fada a cikin ranta kamar wata babba ,fitowar mom daga kitchen kenan ta gama simple girkin da tayi musu taga sabren Tana ta tunani zaunawa tayi tare da Kiran real name d’inta ta ce.

“Khadija Lafiyanki qlau tunanin me kike?ba komai mom Tunanin dad nake yaushe zai dawo”

 

A sanyaye mom taje inda take tare da janyota jikinta Dan tasan shakuwar Sabren da dad baitaba dadewa basa tare ba tasan Dole ta damu cikin sigar lallashi ta ce,..

“Zai dawo soon Insha Allah ki dinga yi Masa addu’a ya tafi wani Course ne da za a k’ara Masa babban girmama a wajen aikinsa nasan ai kina son dad ya k’ara samun kudin da zai dinga saya maki ice cream da chochulate ko?

Cikin sauri Jin abunda mom tace ya sanyata gyada Kai ta ce “Ina so mom”yawwa momyn dad saiki dinga Masa addua idan kinyi salla kina cewa Allah ya bawa dad sa a “Cikin sauri tace

“tO mom yanzuma idan nayi sallah zance “Allah ya bawa dad sa a yasa yasamu nasara duka ya cinye yafi kowa ya samo Mana kudi masu mugun yawa ya bud’e mun babban shagon ice cream nayi ta Sha”

Dariya mom tayi Tana Girgiza Kai ta ce “Ameeeen Daughter”a palour suka ci indomie din da ta girka musu a tare Bayan sunyi salla tare mom ta Bata littafin qur’ani ta dinga karantawa sura D’aya ta karanta dukda mom na cinta g’yara ta Kama hamma bacci take Ji Saida mom ta kaita har bedroom d’inta Tana Shirin fita ta Mike tare da turo Baki ta ce “Mom Ni dai mu kwana tare banason kwana Ni Daya”Naji rigimammiya kwanta to idan kinyi bacci Nima saina kwanta”mak’e kafad’a tayi ta ce ”

“Nasan wayau kikeson kiyimun nidai saidai mu kwanta tare”Ba yanda mom ta iya Dole aka sanyata kwanciyar Dole ba shiri a ran Mom Tana Jin dad’in Ganin y”artata ta Fara daidaituwa a ranta ta ce “Daman nasan duk Kai kake rikitamun Yarinya wlh aka barni daga Ni sai ita na wata guda ma saita gyaru”.

Washegari sabren duk hankalinta ya tashi akan kudin da zata samu ta sayawa Yan class dinsu ice cream Tana zaune a palour tayi jugum mom ta fito tare da Aje Mata Basket din abincin break d’inta ta ce “D’an jirani minti biyu na fito Daga Wanka saina kaiki saboda Ina son biyawa kasuwa nayi sayayya.

Mom na shiga Wanka a bathroom d’inta na bedroom sabren tayi sauri ta Mike tare da nufar dakin gabanta sai fad’awa yake yau zatayi abunda Bata tab’ayi ba watau daukar kudin da ba a Bata ba,.

Tana shiga taji k’aran ruwa a toilet cikin sauri ta shiga duba lockers d’in Dakin taga ba komai jakar mom da ta hanga a kan bed ya sanyata saurin zuwa tare da zagewa taga kud’i masu uban yawa y’an dubu dubu Tana waige ta d’auki guda hud’u tare da zugewa tayi sauri ta fita palour Tana sauke Ajiyar zuciya a school bag d’inta ta boye kudin Tana murmushin Jin dad’i……….✍️

*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536 haka zalika masu buk’atar tallata musu hajarsu suma su tuntub’eni akan wannan number*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

 

_*Miss Hajo Ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

Arewa book👉@Miss H@jo✍️

 

🅿️…….……..*5 & 6*

 

Koda mom ta sauketa a School ta wuce kasuwa domin sayayyar kayan shafarta da suke shirin karewa tasan dubu Talatin ta saka a jaka da safe Amma Kuma Koda ta lissafa sai ta ga dubu ashirin da Shida mamaki duk ya Gama cikata ,itadai tasan ba y’ar aiki gareta ba bare tace anfara Mata sata,gashi ba Wanda yashigo Gidan daga ita sai sabren saurin barin tunanin an dauka tayi saboda idan ba aljani ba to wazai dauka saita lak’anta da cewa kilan tayi mantuwa ne wajen lissafin ba 30k din da daukoba da haka ta samu hankalinta ya kwanta Tana Gama sayayyarta ta wuce gidan wata kawarta.

Sabren ko anayin break Tana Daga zaune ta hakimce taba wata Sopy Yar class dinsu dubu hudu cikin gadara ta ce,.

“Amshi kije restaurant din makaranta ki sayomun ice cream na roba d’an 250 na duka kudin”.

zaro Ido Sopy tayi ta ce “Kai waida da gaske kike Zaki saya Mana baby waya Baki kud’i da yawa Haka”Harararta sabren tayi ta ce .

“Ina ruwanki da Wanda ya bani kud’i y’ar sa Ido zakija na’ki Baki fa”Cikin sauri Sopy ta ce “Sorry big girl”tare da wucewa.,

“nan fa y’an class d’insu aka hau tab’i ana “sai big girl” sabren ko sai kara fasa mata Kai suke,Hindu ko da sukayiba fad’a ganin tasan Bazata Basu ba ya sanyata komawa kujerar da sabren take tare da marairaicewa ta ce,.

“Kawata Dan Allah Kiyi Hakuri Nima ki bani wlh bazamu k’ara fad’a ba Daman Zey ce tayi gulmarki bani ba Kuma Daga yau ma ba ruwana da ita,

Dariya mazan kawayen sabren sukayi sudais ya ce “k’arya take karki Bata zalamammiya ce”to saina Bata d’in Ina ruwanki ai kawata ce “kafin ta kalli Hindu ta ce “Na hakura Zan Baki Amma Daga yau ke Zaki dinga rik’emun jaka Dakin ganni na shigo school d’in Nan “.

Cikin sauri tace “na yarda “Dariya sabren tayi Tana Jin dad’in yanzu zata k’ara samun girma a wajen students d’in school d’in.

,ranar dai sabren tayiwa Yan class dinsu liyafa kowa da ka kalleshi da robar ice cream Yana Sha Banda Zey datayi shiru Tana ta Kallonsu suna Mata k’walele ga haushin Hindu da takeji na yace Mata baya da tayi yanzu ta Zama ita d’aya a class ko magana ba maiyi Mata,”,

Daga gidan kawarta mom ta biyo ta wuce da su sabren gida kasancewar ta d’an yi biye biye yasa har ta jima

After one week Sabren ta na wasa a Kekenta Bayan magriba dukda mom ta hanata tak’iya a compound batama lura da shigowar mota Gidan ba Saida taji muryar dad ta bayanta Yana cewa,.

“Surprised”Aida sauri ta juya Ganin shidinne da gaske ai batasan sanda ta saki keken ba Tare da fadawa jikinshi sama yayi da ita kamar wata yarinya dariya ta kyalkyale da ita ta ce.

“I miss you so much dad ai bazaka koma ba ka barni ba ko?Murmushi dauke a fuskar dad ya ajeta tare da durkusawa ya lakuta kumatunta ya ce.,

“miss you too momyn dad Naga kinyi kyau ko wani Abu mom take Baki”Dariya ta kyalkyale da ita ta ce “dad kaima kayi kyau Amma ka rame”Dariya yayi ya ce Kema kin rame muje na tuhumu mom me yasa ta ramar mun da daughter “.

Saida na Kare Masa kallo Naga farin dattijone Ne sosai da Ka kalleshi kaga asalin bafullatani,bazaka tab’a cewa Ya haifi kamar sabren ba sbd kyan jiki da tsari da kuma gayun da yake dashi.sai sannan na fahimci inda sabren ta gaji hasken Nan suna Kama Amma ba sosaiba yanayin fuskarshi ne da hasken iri d’aya da nata Amma sak magananta da dogon hancinta irin na mom ne,.

Har suka Isa palour Tana dariya Tana yiwa dad surutu Yana biyeta sosai mom tayi mamakin Ganin Dad cikin farinciki ta ce .

“Dear irin wannan suprised haka me yasa baka sanar man zakazo ba na shirya maka special girki,”Murmushi dauke da fuskar dad Wanda na Lura Haka yake da yawan Fara a ya ce “ai nafison Hakan nazo muku a Bazata sweetheart”

mom Tana Zama gefensu ta ce “To ya Gajiya ya kuma hanya Muje ka watsa ruwa kafin na Gama maka girki nasan ka shawo gajiya”

“hakane bari dai mu Gama gaisawa da daughter kinsan nayi kewarta over ,”mom na marairaicewa ta ce”Watau ita kad’aima kayi kewa Banda Ni ko”Dariya yayi ya ce “Ah maida wuk’ar uwar gida sarautar gida Kewarki kinsan ta musamman ce”Kuma Amarya ba “mom ta fad’a Tana Dariya”A a a a Amarya Tana hanya fa mu’kami biyu yayi Miki yawa fa”.

“Mik’ewa mom tayi Tana nufar hanyar kitchen ta ce”Allah ya kawota lafiya Ina maraba da ita kaga ko ba komai na samu y’ar tayin aiki da Mai yimun wanke wanke”Dariya sosai dad yayi ya ce “kai Kai nufinki y’ar aikima Zan kawo maki kenan”

Juyowa mom tayi Tana jujjuya idanu tace “Fad’i da k,’ari y’ar aiki Kuma y’a ka ga sukayimun laifi saina had’a har sabren na Zane.,

“Tana Gama fadar haka ta wuce kitchen Tana Murmushi Dan tasan ta biyewa barkwancin mijin Nata ba tsiyar da zata shuka Masa.

,Ganin mom ta wuce ya Sanya dad maida hankalinshi ga sabren Ganin yanda ta Had’e Rai kamar zata fashe ya sanyashi wara idanunshi ya ce “what happened daughter”.

Kamar Mai jira take ta fashe Masa da kukan sangarta hada diddira k’afa “Cikin kid’imewa da rud’u dad ya Fara lallashinta Amma kamarma tunzurata ake dakyal dad ya samu ya Fara lallashinta Yana tambayarta me akayi Mata cikin sangarta ta ce.

“ba Kaine ka kyaleni ba ka biye mom ni kayi banza ka kyaleni”Sorry momyn dad waya Isa ya kyaleki Kiyi Hakuri ga chochulate Dana taho maki da ita”,Jin an ambaci chochulate ya sanyata saurin yin shiru wasa dad ya dinga mata hada chakulkulo kamar wata Yarinya yar goye Tana dariya Yana yi a Haka har mom ta fito Daga kitchen .

Kallon mamaki ta dinga bin dad dashi kafin ta ce “Daman baka shiga ka Watsa ruwan ba dear baka ko huta ba ka biyewa Yarinyar Nan”.,

Anjima na Watsa ruwan Amina karki damu muna gaisawane da daughter”Kallon Sabren da ta d’ane jikin dad mom tayi tace ,.

“Tasarshi baby na Wanka zaije yayi ya huta yaci abinci saiku cigaba da kaunar ko?Mak’e kafad’a sabren tayi ta ce “umm umm bazan sauka ba Ina ruwanki ba dad ‘ina bane aiba cinyar ki na hau ba”,

Jin Haka ya Sanya mom sakar Mata tsawa ta ce “Zan zaneki Kika bari na karaso wajen Nan”wani uban k’ara ta saki Wanda duk saida ya firgita iyayen tare da fashewa da kukan sakata tahau birgima da ihu”

Cikin b’acin Rai dad ya kalli Mom ya ce “Meye haka Amina me yasa zakiyi mata Tsawa ban hanaki yimata wannan tsawar da kike ba gashinan Daga dawowata kin firgita mun Yarinya Meye Haka dandai sainayi magana kice Ni nake lalata ta ke Hakan da kike Mata gyarane ko barna kike”

Bata tanka Masa ba mom ta juya ta wuce kitchen Tana Jin haushi a ranta ta ce “Ai Kuma shikenan duk ginin da nayi sati kusan biyu da baka Nan ka Rusa Shi gabaki d’aya”Tana sake sake a ranta Harta kammala girkinta.,

Dad ko lallashi ba irin Wanda baiyiwa sabren ba Akan Tayi shiru ta k’iya ta murje Ido sai kuka take Wanda Jin kukan Nata yake har cikin ransa tunowa da ice cream shine kawai za a Bata tayi shiru ya Sanya dad saurin fita ya bawa get man kud’i akan yayi sauri yahau machine ya sayo Mata Saida aka kawo ice cream din dad ya Fara Bata tukwana ya samu tayi shiru sai sauke Ajiyar zuciya take ta lafe jikinshi Yana Bata ta na sha,.

Har mom ta Gama shirya abincin dinner Bata bi ta kansu ba Saida zata wuce bedroom nema ta musu kallo Daya ta wuce Ganin gaba Daya hankalinshi na ga sabreen.,

Wanka sosai mom Tasha cikin tsadaddar shaddarta ta Tasha d’inki ubansu tayi daurin dankwalin zahra buhari gaba Daya jikinta ta fesheshi da turarruka kala kala palour ta fito Wanda kamshin turaren Nata shiya Sanya dad ya gane zuwanta Murmushi ya sakar Mata Yana Kara godewa Allah Daya mallaka Masa Amina matsayin Mata Gayu,tsafta,iya girki,kullum sake koma Masa Yarinya take komai ma.ta had’a ya fada a cikin ransa a fili kuwa cewa yayi .

“Wow tubarakalla Masha kinyi kyau sosai sweetheart ta karfi da yaji dai kin hanani Kara Aure”Lokaci guda mom ta Had’e fuska tare da Kauda Kai cikin shagwaba ta ce “Yanzunma ai saika k’ara tunda ba hana ka ba nayi”Dariya dad yayi ya ce “Maida wuk’ar wasa neke Amarya Kuma uwar gida ai Daga ke ba k,’ari kin rufe ko Ina kinyi Kaka gida Ina dake wazan kalla har ta burgeni ke kad’aice a cikin zuciyar daddyn Sabren kinsan da haka”,.

Murmushin Jin Dadi mom tayi Tana karajin kaunar mijin Nata ta musamman “Sabren ce da hankalinta duka na kansu ta shagwabe fuska tare da Kallon dad ta ce “Dad kace ita kad’aice nikuma fa”wara idanu a tare Mom da dad sukayi kafin Suyi dariya dad ya ce.

“a. A a Ina nufin ke kad’aice Baby Bakijiba”Cikin sauri ta Fara dariya tare mikawa dad hannu suka Taba ta ce “Nima Kai kadai Ne dad Mom na dariya ta ce”Ni Kuma fa?Make kafad’a tayi ta ce “Ke ai mun B’ata duka na kike Kuma kina yimun tsawa'”Dariya dad ya dinga yiwa mom yayinda itama Tana dariyar ta ce “zasu Had’e”.

A tare suka gabatar da dinner dinsu Bayan sun gabatar da sallar isha’i a tare dakyal mom taja hankalin sabren wajen kunna Mata game a wayarta da haka dad ya samu yaje ya yi Wanka ya shirya sunjima suna hira a palour cikin tsantsar kauna da burgewa sai wajen 11 bacci ya dauke sabren a palour a hankali Dad ya dauketa ya Mayar da ita dakinta kafin ya kashe Mata glove ya fito suka nufi nasu bedroom d’in Shida matarsa abun son sa,

Dad Baiyi minti Biyar da kwantar da ita ba cikin bacci taji ana Daddab’ata Cikin sauri ta zabura Ta tashi waige waige ta fara ga duhu da ya baibaye ilahirin d’akin kuka take so ta fashe dashi Amma ta kasa saboda tsabar rud’u fitilun Dakin taga sun kawo gabaki d’aya ilahirinsu yayinda taji Kuma sun dauke haka suka Fara Mata su kawo su dauke da gudu ta Mike tare da rugawa a guje ta wuce bedroom d’in su Mom a lokacin suna Shirin kwanciya sukaji fadowarta Bata zarce ko ina ba sai wajen Dad Tare da Mak’alk’ale sa ta Fara kakkafewa A matukar rude suka Fara Tambayarta lafiya Bata iya Basu Amsa ba sai da ta Gama rudewar kafin ta Fara sauke Ajiyar Zuciya a tattare Cikin rud’u mom Ta ce.

“meya faru fada Mana sabren”dad ma cewa yayi “Lafiya daughter meya faru”Sai sannan ta iya daidaita nutsuwarta cikin shagwaba ta ce.

“Dad a wajenku Zan kwana Ni bazan kwana Ni kad’ai ba”Ran Mom b’ace Ta ce ” da girmanki da komai Zaki kwanta tsakiyarmu da chan da baya Nan ba ke d’aya kike kwana ba saikin gansa ki kawo sabon iskancin Nan”.

‘daga Mata hannu dad yayi akan tayi shiru kafin ya dukursa ya kamo hannun ta ya ce”Kiyi Hakuri muje na rakaki ki kwanta baby na Har Kiyi bacci ko “kuka ta Fara tare da murza Ido ta ce “Dad bazan koma ba dodo yake tsoratani Ni wajenku Zan kwanta”,.

ta k’arasa fad”a Tana cigaba da kuka Jin haka ya Sanya mom Jan dogon tsaki tare da juyawa ta koma gado bata sake ce da su komai ba ,dad ko Numfashi yaja tare da cewa”Shikenan bar kukan zomu kwanta”.

“Sai sannan ta sauke Ajiyar zuciya tsakiyarsu Dad ya kwantar da ita zuciyarsa chunkushe da tunannika kala_kala,Mom ko juya musu baya tayi cike da takaici ba ayi 5 minutes ba sabren tayi bacci Saida daddy ya tabbatar da tayi bacci kafin ya Mike zauna.

“Amina “ya Kira sunanta a hankali,shiru tayi Bata Bashi amsa ba,nasan kina jina ki taso muyi magana ,sai sannan Mom ta juyo tare da Mik’ewa zaune kamar Mai Shirin yin kuka ta ce “Ina jinka”Saida yaja Numfashi kafin ya ce”

“Kin tab’a Jin alamun tsoratarwa a Gidan Nan,na kasa gane wani irin tsorone Yarinyar Nan take cewa ana Bata tun kafin na tafi me Hakan ke nufi”.

Tuni hawaye har sun wankewa mom fuska ta ce “Karya take dear wlh ba wani tsoro da ake Bata tunda ka tafi ita kad’ai take kwana a d’akin in Banda Rana Daya da muka kwana tare Shima ba dalilin tsoro ba iskancine kawai me yasa da bakanan Bata cewa ana Bata tsoron sai sanda kake Nan wata biyu fa kenan Yarinyar Nan ta na bijiro Mana da wannan sabon iskancin Kuma idan munje Dakin nata muga Lafiya qlau, kaikuma kana biyeta Ai Shikenan sai muyi ta kwana taren mu ukkun da gard’amemiyar budurwa shekara Sha biyu y’ar j s s one gado d’aya tunda burinta kenan har mahadi ya bayyana “.

ta k’arasa fad’a Tana goge hawayen da suke zubar Mata tare da sake juya musu baya wasu sabbin hawayen takaicin na sake zubar Mata…..cikin kwantar da murya Dad ya ce.

“Kiyi Hakuri Dan Allah Amina mu bi al’amarin Nan a sannu har mugano kan matsalar tsoratata d’in da take fad’ar anayi ya Fara bani tsoro.

“Takaici ya Hana mom batace dashi komai ba Dan harshi duka jinsu take Tana Jin haushinsa wata biyu kenan a haka…..dakyal wani wahalallen bacci yayi gaba da ita dad ko dukda gajiyar dake tattare dashi bai hanashi tashi ya jera nafiofilu ba kafin Shima Baccin ya daukesa.

Washegari around 9:Am zaune suke a dining Momy tayi serving dinsu Kasancewar week end sabreen Bata zuwa makaranta,

Sabren sai labarai take yiwa dad yayinda dad ke biyeta dukda Yana lura da yanda mom keyin Abu kamar marar lakka nanko baisaba ganinta haka ba.

,Bayan sun Gama ne Ganin hankalin sabren baya kansu Ta na palour Tana game a laptop d’inta ya Sanya dad Kama hannun mom tare murzasu ya ce”,

“Meke damunki My Menah Naga kinyi sanyi ko nayi wani laifin ne”Kirkirarren murmushi mom Ta saki Dan tasan ba abundanda ke tayarwa da dad hankalina sama da yaga ta sauya ta ce “Bakomai Dear”.

Murmushi yayi tare da Kama hannunta suka Mike a tare Ya ce “Muje ciki sainaji meye matsalar ko?murmushin Jin dad’in mom Tayi Tana sauke boyayyar Ajiyar zuciya “ta Mike,.

,Suna shirin shiga ciki suka jiyo katuwar sallama a palour sabreen na Ganin BaBa ce ya sanyata murtuke fuska Tare da yatsineta kamar taga Kashi ,.

Mom ko da dad saurin sakin hannun juna sukayi ba tare da komawa palour kowanne da fara’a dauke da fuskarsa ,Cikin ladabi suka dukursa suka gaishe da Baba Tana amsa musu Cikin washe Baki cikin muryarta ta tsaffi ta ce “kwana biyu Naga Mustapha bakaje ba hankalina duk ba kwance ba Hakan yasa nace bari na leko naji ko Lafiya?.

“Lafiya qalau Baba ai tun tafiyar Nan Dana fada maki nayi sai jiya na dawo”Allahsrk ka jima kenan d’an kirki andawo Lafiya”,

“Alhmdullh BaBa ya muka sameku ai da ma Baki wahala kinzo da kanki ba Daman yanzu nake shirin lek’a ku”A a a d’an Nan ai gwara da nazo da Naga lafiyarku da ta Jikata da Bata zuwa inda nake” .

murmushi dad yayi ya ce “Insha Allah zata dinga zuwa ganinki akai_Akai,sabreen najin haka ta Mike tare da Jan dogon tsaki ta yi hanyar waje,tsawa mom ta daka Mata ta ce “Dan gidanku Baki ga baba bane tun dazu kik’i gaishe ta ba!! “.

dad da sabreen na kasa banbance Wanda yafi wani rud’ewa,turo Baki gaba tayi tare da juyawa tayi hanyar waje zata fita Hankali kwance ta ce “Baza’a gaishe ta d’in ba ina ruwanki “,

dad ko cikin fushi ya ce “Wannan wace irin tsawace kikeyiwa yarinyar Nan Amina saiki rud’ar mata da kwalwa haba! Dan nayi Mata magana akan rashin gaishe da kakarta shine nayi laifi?cewar Mom Tana Masa k’uri da Ido”Baba tayi sauri ta ce “Kunga karku wani damu Yarinta ce Nan gaba da kanta ma Baku sani ba zataje har inda nake”….

Sabreen Kai tsaye gidansu Anesa ta nufa suka hau wasa kafin ta wuce gidansu Affan a chan ta ci ma abinci Rana Dan wasa ya kad’i hankalinta har yamma suna yawon wasa gida gida ita da abokin yawon nata…

.BaBa ita ce bata bar gida ba sai bayan magriba Wanda dad ya dauketa a mota Dan ya wuce da ita gidanta da ke jimeta local government Wanda minti Sha biyar ya kaika daga Yola zuwa chan kusan ma Had’e suke.,

Saida mom ta Gama lafiyayyen girkinta kafin hankalinta ya koma ga sabreen Kallon agogo tayi taga har seven eleven,Saida taja numfashi kafin ta Mike Tana Jin ciwon wannan yawon na sabren akuyar daure ta samu sake shiyasa yau tayini a waje Bata ganta ba…

.Mai gadi ta aika ya lalleka gidajen da take zuwa su taho tare…a gidansu Ummy ya samesu suna cikin fad’a da yayar Ummy dakyal Mai gadi ya rabasu Dan chan cikin gidanma basusan wainar da ake toyawaba dakyal ya shawo kanta ta bishi gida Tana ta hure huren hanci a Dole antab’ota…..

…kallo Daya mom Tayi Mata ta Kauda Kai taci gaba da lazumin ta zaunawa tayi kan sopa Tana ta hure hure Ganin mom ta kyaleta Ne ya sanyata Mik’ewa tare da zuwa kusa da mom kamar zata fashe da kuka ta ce “Ina dad mom”

“ajiyarshi Kika bani “Kuka ta fashe dashi har da birgima a haka dad yashigo Hankali tashe yayi kanta yahau Tambayarta lafiya daughter Sai sannan ta sauke Ajiyar zuciya tare da lafewa jikinshi kamar wata jaririya ta ce “dad wannan Matar ce”

“Me tayi miki”ya tambayeta mamakinshi mom Tayi a zatonta ko baiyi Mata fad’a ba zai nuna Mata abunda tayi ba daidai bane Amma sai tambayarta yake me tayi Mata a ranta tace wannan da matar uba ce ke ruk’onta tuni aurenta sunanshi matacce uwartama ana tuhumarta bare matar uba”

“Tsawa take yimun dad Bata Sona”Ta karasa fada Tana hawaye lallashinta dad ya dingayi Wanda Hakan har haushi yabawa Mom da kanshi ya Bata abinci Daren ranar ma su ukku suka kwana……

After two days sabren ta dawo daga islamiya Wanda dad da kanshi ya dauketa Bayan ya biya ya saya Mata ice cream da manyan choculate suka wuce gida da Daren around 10pm sun zauna a dining Area mom Tayi serving din kowannensu Kallon abincin sabren tayi tare da yatsine fuska ta kalli dad ta ce.

“Dad Ni na koshi ba zanci abun Nan ba”Kallon Ta dad yayi ya Ce”bazakici ba Baby to me kikeson kici”Sakwara da Miya “ta fada Kai tsaye Tana tubure fuska.

” Sakwara Kuma?Mom ta fada tare da cewa “Chab kina da aiki kinshirya kwana da yunwa kenan “Daddy na fuskantarta ya ce”,Sakwara Kuma baby da Daren nan Kiyi Hakuri Kici wannan din gobe sai a dafa maki sakwarar”.

Mak’e kafad’a tayi Tana Fara kuka Ganin Tana Shirin Fara diddire diddiren nata NE ya Sanya dad saurin cewa “To Shikenan yi shiru babyn dady meye abun kuka yanzu za a Girka maki yi shiru kinsan ba abunda na tsana sama da kukanki ko”,

shiru tayi Tana shasheka tare da murza Ido a rude dad ya kalli mom ya ce “Dan Allah Sweetheart jeki Samar Mata da sakwarar tunda ita take bukata please banason wannan kukan da take wlh”

“Chabdi lallaima Dear bansan me ka mayar Dani ba jaka ko Kuma baiwarku ,karfe goma Daren Dan ita kad’aice d”iya a Duniyar Zan tashi na kirb’a Mata Sakwara gata uwata to wlh bazan girka ba ai ba haihuwa ta tayi ba Nina haifeta “mom ta karasa fada cikin fushi”

Mik’ewa dad yayi Yana aje abincin Da ya fara ci yayi ya Ce “,Shikenan ai ba abun Doguwar magana bace ni bari Naje na Girka Mata “.

.da mamaki mom take binshi da kallonta Ganin da gaske yake Harma ya shige kitchen cike da takaici Kamar zata kurma ihu ta kalli sabreen dake chuno Baki ta ce “kin bani wahala sabren tunda na haifeki har yanzu cikin bani ita kike bakison kiga na huta a rayuwa bazanyi Miki Baki ba Ubangiji ya shiryeki”

A kitchen ta samu dad Yana Fara fere doya maza tayi ta amshe ba tare da ta kaleshi ba ta ce “Kaje zanyi”Ki bari muyi tare tunda Naga kin gaji sweetheart”ka barshi tunda nace kaje parlour zanyi “Dakyal ta lallami dad ya fita a ranta Tana ayyana wannan wani irin so ne dad keyiwa sabren kamar ita Daya ta rage y’a a Duniya.

Kasancewar akwai stew ya Sanya mom Bata wahala sosai ba Harta Gama ta zo ta dungura Mata gabanta Tana Jan tsaki “ita dai sabren ko a kanga tunda dai tayi Mata abunda take so ai shikenan,

Da daddare Saida suka lura Sabren tayi bacci sosai kafin dad ya mike tare da Kallon mom ya ce “daukarta mu maida ita d”akinta tunda tayi bacci”Haka ko akayi Sadaf suka mayar da ita dakinta suka kwantar da ita tare da juyawa a hankali suka koma dakinsu suna sauke Ajiyar zuciya.,

Sabren cikin bacci taji ana Daddab’ata kamar yanda ake Mata kasancewar bacci Mai nauyi ya dauketa ya sanyata kasa tashi cikin bacci ta dinga Jin wata murya da Bata tantance ta ba ta na Kiran sunanta Tana cewa”Baby Baby baby”.

A matukar rude ta Mike tare da fashewa da kuka ta Fara laluban su Mom taga Basu Nan Kuka ta fashe dashi sosai tare da Fara ihu kasancewar Karan gen dake Bayan bedroom d’inta ya Sanya su Mom Basu jiyota ba ga duhu a rude ta Mike Tare da Fara laluban kofa Harta samu ta gane tare da fitowa palour Allah yasa da hasken glove Basu kashe na palour ba Tana kuka ta ruga dakinsu tare afkawa da gudu dukda duhu ne d’akin.

sauri mom Tayi ta kimtsa dad Ne yayi saurin Zuwa ya kunna glove din dakin Sabren na Ganin haske ta kankame dad tare da fashewa da kuka ,”A rude dad ya rungumota Tare da zaunawa Tana jikinshi ya dinga tofa Mata adduo’i a haka har wani Baccin ya sake daukarta ya kwantar da ita .

kallon mom da tayi Tagumi ta Lula wata Duniyar tunanin yayi ya Ce,

“Na Fara tsorata da lamarin Nan Amina meyasa ake tsorata yarinyar Nan Wai kwanannan Meke faruwa”.

Ka tambayeni nima nifa ban yarda ba da ana tsoratata tsabar wulakancine irin nata kasan ba abunda ta tsana sama da ta ga na huta a rayuwa me yasa sai kana Nan take cewa ana tsoratata din “.

Shiru dad yayi yashiga dogon nazari”Mom na Ganin haka ta juya tayi kwanciyarta a tare da Jan bargo ta rufa kallonta dad ya dingayi yanata tunaninnika a ranshi ya ce.,

“idan karya take me yasa da chan tun da Tana Yarinya ma bama kwana gado d’aya da ita dakinta ita ‘Daya take kwana Bata taba cewa an tsoratata ba sai watannin Nan biyu …Kuma me yasa sai Ina Nan Hakan take faruwa”?…….✍️

 

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

 

 

*_Miss Hajo ce*_
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

 

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

 

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

 

🅿️………..*7 & 8*

 

Washegari Kasancewar dad da kanshi ya kaita school suna tsayawa bakin get ta marairaice fuska tare da kallonsa ta ce “Dad I want you to give me money please”Yana shafa kanta ya ce ” how much do you need My Angel?”10k dad anma karka fad’awa mom”ta karasa bada Tana turo Baki”.

Murmushi dauke da fuskar dad ya ce “shikenan daughter bazataji ba 10k ya ciro tare da Mika Mata”Cikin murna ta amsa tare da Rungume dad Cikin farinciki ta ce “I’m very proud of you my dad thanks so much,”

Shidai dad murmushi kawai yake Yana kallonta cike da so da kaunar tilon y’ar tasa da Allah ya mallaka Masa a duniya a rayuwar dad Babu wacce yake so a fadin duniyar Nan sama da sabren baya son bacin ranta Yana kaunar farincikinta fiye da nashi kodan hakan ya samo nasaba ne bisa ga wahalar da suka Sha kafin Allah ya mallaka musu ita”.

Ai sabren ganin kud’in wannan hannunta da mulki ta shiga school din tanajin kanta na k’ara Mata wani girma ta na cikin tafiya ta hango wata safiya y’ar s s two Daman basa jituwa Aiko taki Bata hanya itama Taki Bata hanya Suna kurewa juna Kadan ya Hana Suyi Karo da juna ja safiya tayi ta tsaya tare da fardo sabren ta ce “ke maras tarbiya Dan Ubanki Baki ganina a hanya ne watau ke isashshiya ban Isa ki bani hanya ba ko”Ta fada ta na huci”.

Fincike wuyanta sabren tayi tare da Galla mata harara ta ce “dallah sakarni nonsense Ni nafi karfin na hada jiki da stupid irinki Mai warin Kashi Amma ki sani yau zakisan kin tabo babbar Yarinya a school dinnan ki saurari result anjima kazama”Tana Gama fadar haka tayi gaba Tana Jan tsaki.

Ranar anayin break da 10k din da Dad ya Bata suka shiga shop ita da duka y’an class dinsu suna take Mata baya suna kirarata da big girl gaba daya 10k din ta kashe musu har zey da itama sun shirya yanzu ganin Yan class dinsu sun Goya Mata baya liyafa sosai tayi musu a class din ,anan NE take fada musu Tana son su hadu su ci Mata uban safiya yanda Nan gaba ko harararta Bata Isa tayi ba Nan suka hau hargagi Suna cewa

“Aiko yau safiya saita ci ubanta zatasan ta tabo Mana sarauniyar class din haka dai har aka tashi Suna kitsa yanda zasu jibgi safiya Wanda zey ta bada shawarar a bari sai an tashi ai a kasa take tafiya su bita da bulalu suci ubanta.

Haka ko akayi Ana tashi gaba daya Saida suka ga safiya ta rabu da class mate d’inta tayi hanyar gida suka bita suka tareta suka zagayeta sabren dake tsakiyarsu ta kwashe da dariyar ta ce “Daman ba Saida na fad’a maki ba saina ci Ubanki zakisan yau kin tabo *KHADIJATUL SABREEN* a makarantar Nan kafin ta kalli Yan class dinsu ta ce “Hey guys ku Fara aiki”kafin safiya tayi wani motsi yaran su harar Mata sosai suka dinga jibgarta Tana ihu Tana kuka Yara Sha hudu a kanta hada maza sabren ko Banda dariya ba abundai take ganin yanda safiya ke kuka Tana Bata Hakuri bazata sake ba,.

Uncle dinsu yazo wucewa gida kenan yaga wanna ta asar saukowa yayi Daga motarsa ya nufo wajensu hankali tashe sabren na ganinsa ta ce “Mu gudu ga Uncle Nan ku rabu da ita” kafin uncle ya ciro bulala a bishiyar dake gefensu sabren ta kwasa a guje sauranma suka bita da gudu kowa ya watse,.

Da dare sabren na jikin dad dinta da anjima anjima saita kwashe da dariyar tunowa da irin dukan da ta Sanya akayiwa safiya da yanda take Bata Hakuri duk wanna karyar da take a school,kallonta dad yayi ya ce “Yadai daughter dariyar me kike tun dazu”wata dariyar ta kumayi kamar mahaukaciya Shima dad dariya yayi ya ce “ga alamun dai yau Daughter na cikin farinciki take”Tana dariyar ta Mike zaune tare da Kama hannun Dad ta ce “Dad Bari na baka Labari “.

wayarsa ce tayi ringing ya sanyata yin shiru bata karasa abunda takeson fad’a ba Kallon Mom tayi dake yi Mata gugar uniform harma ta Gama ta Mike ta ce “Dan Allah mom Gobe karnaje school”Harararta mom tayi ta ce “ki zauna Kiyi me a gidan saikinje “,

Kwabe fuska tayi tare da turo Baki batace koma ba “ta bud’e robar ice cream din da dad ya sayo Mata ta Fara Sha “Gama wayar dad yayi tare da kallon sabren dake Shan ice cream d’inta hankali kwance saikuma ya kalli Mom dake kallonsa ya ce”Wai kinji malaman Makarantarsu baby ne suke son gani na Gobe da safe tare. Da daughter,”

“ikon Allah to Allah kiyaye ba wani laifin tayi ba har ina murna an kwana biyu ba a kirani case d’inta ba kafin ta kalli sabren ta ce “laifin me kika yi kuma”Wara hannu tayi irin I don’t care dinnan ta ce “Nima bansaniba”Tana Gama fadar haka ta Mike ta wuce bedroom d’in su Mom ta ce “Bacci zanyi mom Dad good night”.

Numfashi dad yaja bayan barinta Dakin da damuwa ya kalli Mom ya ce”Muje matsala ta gaba wacce tafi damuna Amina ta tsoratar da yarinyar Nan da ake Ina mamakin al’amarin Nan Wata ukku kenan muna haka nifa na Fara tsorata da Al’amarin meyasa saimun tashi…..kasa karasa maganar yayi sakamakon shigowar sabren Dakin Tana Hamma Kai tsaye wajen dad ta nufa Tare da kama hannunsa ta ce “Muje mu kwanta dad bacci nake ji banason a tsorata ni”okay Muje daughter Dad ya fad”a Yana mik’ewa,, da harara mom ta bisu har suka wuce,Dan ita har yanzu Bata yarda da Ana tsoratar da sabren ba.

Washegari a tare da mom suka je school din Dan tasan halin dad akan fad’a da malaman makaranta da yake Akan sabren a pri makarantun da ya sauya Mata Akan dalili marar tushe ita kanta bazata iya lissafasu ba.

Kamarko ta sani yanzun ma fada ne ya kusa kaurewa dashi da vice principal din makarantar tare da Iyayen safiya da suka kawo Kara sauran iyayen yaran da aka Kira duk sun bada Hakuri bayan anyiwa yaransu furnishment da bulala ukku ukku nanfa Dad ya ce wlh Bai yarda ba in duniya zata hadu kasa da sama ba Wanda ya Isa ya tabar Masa y’a saidai ya cireta daga makarantar gaba d’aya,.su kansu iyayen sauran yaran Saida suka tsaya kallon ikon Allah su da yarshi taja aka Dakar musu y’a y”a suce me,sabren ko duk ta tsure jin dad yana cewa zai cireta Bata ta’ba yin school din da taji dadinta irin wannan ba saboda yanda take juya Yan class dinsu son ranta sanna yanda ta Fara Suna a school din duka term dinsu Daya Taya zata yarda Dad ya cireta “Kuka ta fashe dashi tare da cewa “Dad na yarda a dakeni d’in Dan Allah karka cireni”.

Daga mom har dad kallon mamaki suke binta dashi yanda suka San Yar tasu da tsoron bulala “Kamota dad yayi ya ce “Bamai dakar mun ke daughter Muje na cireki daga school din ai ba ita kadai ce school a garin yola ba duk ga su Aliyu mustapha academy, Con codia, da yawansu gasunan birjik sai Wanda na zaba,cikin sauri mom ta karbe sbabren daga hannunsa tare da Had’e rai sosai tasan ba abunda ya Tsana sama da yaga ta Had’e rai ta ce .

“Ka rabu da ita tunda tace ta yarda a daketa din Kuma kaga laifi tayi su sauran daliban da aka dakesu finta sukayi,banason haka daddyn sabren ka fita waje gani Nan zuwa yanzu Dan Allah”zaiyi magana mom tayi sauri ta amshe da cewa “Please ka fita zamuyi solution matsalar”Yana fita mom ta bawa Vice din Hakuri murmushi yai ya ce “Bakomai Hajiya mun Saba da irin wadannan case din “Kama hannun sabren data tsure mom tayi sosai tare da kaita gaban vice ta ce “ga ta malam yi sauri dakarta karya dawo”.iyayen sauran yaran tuni sun bar office din Daman.

Kunsan ance ko mutuwa na tsoron idon mahaifi vice kasa dukan sabren yayi girgizawa Mom Kai yayi Dan ta burgesa yanda ta Bashi Hakuri Sannan da kanta ta ce a daketa ya ce”rabu da ita Hajiya Nan gaba ta sake tasan sauran zamu Had’e da ita”

” a a Kar ayi haka malam kaga sauran yaran an dakesu ita kadai Aki dakarta “Girgiza Mata Kai yayi Yana murmushi ya ce “ba yafe mata nayi ba zamu Had’e next time ta sake wani laifin zanyi Mata double purnishment sakarta ta tafi class”Mom na sakin sabren ta saki wata Ajiyar zuciya Dan da dukta tsure da gudu ta ruga hartaje bakin office ta juyo tare da cewa “Mom “Tana juyawa ta yi Mata gwalo tare da yin dariya ta ce “Ai dai ba a dakan ba lolololo”Tana Gama fadar haka ta kwasa a guje ,.

GirGiza Kai kawaii mom tayi tare da cewa Allah shiryeki Vice dai dariya yayi kafin yacewa mom” ba komai hajiya Dan Allah ki k’ara kula da yarinyar Nan lurar da nayi tundaga haka kina k’ok’ari ki k’ara Akan yanda kike kinsan icce tun Yana Karami ake tankwarashi idan ya girma baya tankwaruwa ku rage sangarta yarinyar Nan da yawa ko ba yanzu ba saboda gaba mace ce sannan Dan Allah a daina Bata kudi da yawa budewa yaro Ido da kudi babbar matsala ce “.,

Murmushin da yafi kuka ciwo mom Tayi ta ce”insha Allah na gode”a mota ta samu dad Tana shiga ya banka Mata harara Wanda Saida ta sanyata ta Dara ta ce “maida wukar na Amina ikon Allah ba a dake ta ba”.

“Cikin sauri ya juyo ya ce Da gaske ko wasa”Da gaske sun Mata Hakuri kafin ta bashi labarin yanda sukayi da malamin Nauyayyar Ajiyar zuciya dad ya sauke Yanajin wani sanyi a ranshi Jin ba a Dakar Masa yar lele ba murmushin yayi ya ce “sai Yanzu hankalina ya kwanta yanzu muyi sauri muje gida muna Da Free time kinsan nayi Kewarki sosai…murmushi kawaii mom tayi Tana kauda Kai.,

sosai ta Lula duniyar tunanin yanda zata tankwara sabren kamar yanda malaminsu ya Bata shawara tasan ba karamar sangartata dad yayi ba tun Tana ciki kafinma tazo duniya ya d’auki son duniya ya Dora mata ,itama zata iya cewa tanama yiwa sabren fiye da son da yake mata Amma Dole ta danne son wajen ganin ta samu tarbiya me kyau Amma yanzu Tana ji Tana gani ko yawo batayi da sabren saboda kunyatata din da take cikin mutane tunowa da wahalar da ta dingasha kafin a haifeta Saida tayi b’arin ciki har sau biyar Wanda ana shiddar ne dakyal da Addua Allah ya zaunar musu Wanda shine silar zuwan sabren duniya,.

dalilin operation din da akayi Mata da rashin hutu da mahaifarta Bata samu saboda akai akai ta dinga samun ciikin dan shekaransu ukku da aure tayi barirrikan Nan ya Sanya mahaifarta samun matsala Wanda akayi Mata aiki aka ma cire Mata ita gaba d’aya tasan ita da Kara haihuwa har Abada shiyasa take Kara godewa Allah da mallaka Mata sabren da Kuma Mijinta Mai matukar kaunarta tsakani da Allah ،dan tasan da wanine aure zaice zai Kara dukda tasan yanda yake fama da danginshi akan rashin Karin auren ya samu wasu y’ay’an Suna tunanin ita ta Gama dashi tayi mashi asiri Amma Yayi burus ya kyalesu ya ce Matarsa da y’arsa d’aya sun isheshi Albarka yake nema ako yaushe ba yawa ba .

,.tunowa tayi da duk lokacin da zatayi b’arin cikunnan Daren ranar mafarkin da take na wata Mata ta juya Mata baya Bata ganin fuskarta Ta Rufa da wani k’aton bargo ta baya take Chaka Mata wani Abu a cikinta Wanda da zarar ta farka take tashi da ciwon da zaiyi Sanadiyar misscarrige d’inta tunowa tayi da haihuwar sabren sau ukku Tana mafarkin ta Sai tazo zata Chaka Mata abun Daddy yazo ya dauketa yayi Sama da ita ana gobe zata haifi sabren ma Saida tayi mafarkin matar lokacin cikin fushi take harta iya juyowa gareta Amma Bata yarda taga fuskarta ba saboda gaba daya ta rufe fuskarta Cikin fushi Ta dauko abunda ta Saba Chaka Mata harta tillo abun kawaii saitaga Wani hasken Abu ya fito daga cikinta ya mayar mata da abun Wanda Saida matar fa fadi kasa cikin fushi ta Mike zata Kara dab’a mata wani Dad din sabren Yasa hannu ya fardota jikinshi harta farka “Daga lokacin ya dage da Bata adduo’i na azhkar da sauransu sannan ya Kara karfafa Mata gwuiwa akan ruk’o da addini da adduo I tundaga lokacin Bata sake mafarkin Mai Kama da wannan ba Saboda Kara riko da ibada da ta yi Dan tasan Mijinta mutum NE Mai tsananin ibada da ruko da Sunnar manzon Allah s a w “.

“Tab’in da Dad yayi Mata Ne ya sanyata dawowa daga duniyar tunanin da ta Lula “ya ce “Ranke Dadi wannan dogon tunanin fa”murmushi ta kirkira Tana fitowa daga mota ta ce “Har munzo kenan”hannunsu sakale Dana juna suka shiga palour mom sai farinciki take yau daga Ita sai dad a gida gabanta ne yaja ya fad’i cin Karo da Sadiya da tayi a palourn ta hakimce Tana Cin tuffa ,.

 

Cikin sauri ta Mike Tare da Fara gaishe da dad cikin Fara a ya amsa Mata tare da cewa “Ya su BaBa”Lafiyansu qlau “ta fada Tana Yar in Ina “tare da kallon mom da tayi tsaye ta ce “Ina kwana Aunty Amina Yau cewa nayi kwana biyu Bari nazo mu gaisa”

“Daidaita nutsuwarta mom tayi ta ce “Muntashi lfy Sadiya yasu baba ya yaran”Lafiyansu qalau”Ina Momynmu sabren ko ana makarantar “Eh ana school “Mom ta fada Tana maida gabanta ga television Takaici duk ya Gama isarta Dan harga Allah tanabukatar mijinta feel free daga Ita saishi a gida Amma kullum gidan su tunda yazo baya rabo da Baki daga kowani bangare wannan yazo wannan yazo…

Sabren dawowarta kenan daga School duk ta gaji tun a compound ta Fara cire takalmi da safa tare da wurgar da hijab din a palourn farko Tana ta turo Baki ita yunwa take Ji harta karaso babban palourn.

Aunty Sadiya dake tsaye a bakin dining table ta bud’e Zane Tana barbada wani magani a abinci Taji shigowar SABREEN ta na ganinta tayi sauri ta maida maganin bayan ta Gama barnadawa a miyar ta matsa daga wajen hankali Tashe dukta rude, kirkiran murmushi tayi tare da nufo sabren Tana cewa”oyoyo oyoyo Mamanmu ke nake ta jiran dawowarki Yar albarka”Ta fada Tana nufarta da niyyar rungumeta”.

Sauri sabren tayi ta matsa Tana wani yatsine fuska ta ce “Ni karki tab’ani Malama”me nake gani haka sabren rashin kunyar Taki har mamantaki zakiyiwa manya ma Baki Bari ba”cewar Mom ta na fitowa daga kitchen”

“Allah kiyaye Ni ba mom d’ita bace wannan shirgegiyar Allah kiyaye ta Zama mom Dita”ta fada Tana turo Baki

“Salati mom tayi ta ce “Kanwar Baban naki kike fad’awa hakan dan Baki da mutunci sabren”Mom ta Tana nufota Aunty sadiya duk ta tsure tsoro take Kar aje sabren taga abunda ya zuba dukda tasan Daman yarinyar ba kaunarsu take ba Bulala Daya mom ta tsala Mata ta charger waya Wanda ihun data kwalla Duka Saida ya kewaye Dakin wani irin ihu take kamar ana zarar ranta Aunty sadiya dukta rude ta ce.

“dan Allah Kiyi Hakuri Aunty Yarinta ce Ni wlh banjima komai ba”Haba Sadiya akanme komai tayi sai ace yarinta yarinyar Nan ba fa Yarinya bace da za ace a shekarunta Bata San darajar manya ba,sabren ihu kawaii take hange take wata barnan zatayiwa mom wacce zataji ciwo fiye da yanda Taji na bulalar.,

hango abinciccikan da ke jera a dining tayi tasan mom ba abunda ta tsana sama da barnan abinci Aiko ba Inda ta nufa Tana ihun kukan sangartata sai dining Tana zuwa ta hau watsi da komai Dake dining din miyar ta dauka Tare da watsawa a farin carpet din palour aunty Sadiya da suka nufo wajen hankali tashe mom da Dora hannu aka tace na shiga Ukku sabren abincin da tun safe nake wahalar girka sa Kika zubarmun miyar da Nayi ta kwana ukku Kika watsarmun ita Wasu hawayen bakin ciki NE suka zubowa mom saboda bakar wahalar da Tasha Ai Bata San lokacin da ta furta Cewar”Yanda Kika wulakanta abincin Nan wata rana saikin nemeshi da idonki kin rasa Dan ubanki”.

( da yawa wasu iyayen fushi na sanyasu ga fad’awa yayansu mugayan kalamai na Baki wanda saisun Manta ma bakin ya dinga bibiyar yayansu saboda ance bakin uwa dafi ne Allah yasa iyaye su gane su dinga Kai Zuciyarsu nesa yayinda yayayensu sukayi musu wani Abun da basuji dadinshi ba Allah sa mu gyara). wayar wuta Mai kauri ta wawuro tare da nufarta da ita sabren na ganin haka ta kwalla ihu tare da nufar hanyar kofa

mom ta Mara Mata baya Dan Yau Mai raba ta da ita sai Allah sabren hankalinta duk ya tashi bude k’ofar palour tayi ta kwasa a guje Maigadi ya Mike Yana tambayarta Lafiya saijinshi yayi kasa sakamakon bangajesa din da tayi mom Kira take,.

“,yusha’u karka barta ta fita ka rik’emun ita kafin ma yusha’u ya Mike ta bude k’ofar get d’in ta Kara kwasawa a saba’in Bata nufi ko Ina ba sai gidan su Affan……….✍️

*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*

 

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

 

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

🅿️………….*9 & 10*

Yanda ta shiga gidansu Affan Ne a guje ba ko hula ga ko uniform Bata cire ba ya Sanya Mamansu dubanta ta ce”Lafiyanki kuwa Baby ya haka Naga ko uniform Baki cire ba “Tana murza Ido ta ce “Mom nayiwa laifi shine zata dakeni na rugo ”

“Daman na sani uwar yar laifi jeki Dakin abokin naki Yana ciki”Turo Baki gaba Tayi ta ce “Ni yunwa nake ji mama”murmushi kawai mama tayi ta na kallon budurwar yarta ta ce “tashi ki zuba Mata abinci”Saida taci Abinci ta koshi ita da Affan kafin su Mike su shiga wasan da suka Saba mama nayi musu mitar sun Girma da wasa ba Wanda ya kulata cikinsu.

Aunty sadiya ihu ne kawai batayi ba saboda takaicin bakincikin asarar da sabren tayi Mata dama ce babba ya samu wacce Bata taba samun irinta ba Amma tsinanniyar yarinyar ta B’ata Mata shiri ta tsinewa Sabren yafi dari a ranta ba shiri ta jawo Jakarta tayiwa mom bankwana Tana cewama ta jira Dad ya dawo Amma Bata saurareta ba.,

________Tana Isa Ba sallama ta fad’a gida Kamar ta fasa ihu tayi dabas ta zauna baba dake taunar goro ta ce “Lafiya sadiya meya faru”Baba komai ya lalace yarinyar Nan Allah tsine Mata albarka ,baba kituna bakar wahalar da Nasha na tsallaka Nigeria na je har gari ya na marad’i ki duba Nissan tsakanin yola da marad’i Banda ciwon wahalar da Nasha naje wajen malamin Nan na amshi maganin Nan Wanda ya tabbatar mun matsawar suka cishi shikenan komai zai rikice zaiji ba wacce ya tsana sama da ita bazasu Kara Kwana Daya ba zai saketa ,ba, na samu babbar dama na saka Musu a abinci kawai yarinyar Nan ta zubar da miyar gabaki daya gashi Duka maganin ne na Sanya”ta karasa fad’a hada hawayen Takaici.,

Salati BaBa tayi ta salamce ta ce “Kai anyi lalatacciyar Yarinya kijimun shegiyar Yarinya tsinanniya yar asara shiyasa kikaga na tsani yarinyar Nan da uwarta Bana kaunar Yan iska yanxu kenan komai ya lalace”

“Komai Mana ya lalace BaBa na rasa wani irin shegen taurin Hali ne da tsinanniyar Aminar Nan Asirin munyi munyi ba nasara ,Yanzu fa tuna da Asirin Nan Na kwanaki da Boka yayimun kuma shima an tabbatarmun da aikinshi kamar yankan wuka Shima ba nasara ”

“Lallashinta Sosai BaBa tahau yi ta ce “Ki kwantar da hankalinki y’ata Dole ne Amina tabar gidan Nan idan Kuma tak’i ta Taki ajalinta zanga uban waye bokan ta a kasar Nan Dole ki Auri Mustapha Kuma kiyi yanda kike so dashi ba y’ar katsinawa ba ita Tana takama da ta Gama dashi bayabin umarnin kowa sai nata To ko Yar maguzawace sai na gwada Mata zaren ba kalar yadin bane barni da ita d’iyar kirki ”

“Sai sannan sadiya hankalinta ya Fara kwanciya Kallon Baba tayi ta ce “Ya banji girbin yaran ba”Tabe Baki BaBa tayi ta ce “Malalacin uban su yazo ya tafi da su”..

 

______”Lafiya palourn Naga ya firgice haka ga Miya kacha kacha meyake faruwa”?

Dad yake fad’a shigowarshi kenann Palourn”,Mom da kuka ne kawai batayi ba Dan Takaici ta ce.

“Daman na’ki gyarawa ne dam kaga abunda yarka tayi da idonka sabren ta lalata gaba Daya abincin danayi “ta karasa fad’a kamar ta saka kuka.,

“Subhnallahi daughter tayi Aikin wannan kenan to Amma nasan dai haka kawai bazatayi haka ba me kikayi Mata”.

Sakato mom tayi Tana kallonshi cike da Takaici Ta ce “Ohh tambaya ma kake me akayi Mata bama fad’a zakayi Mata ba to wlh yau bazan Kuma shiga kitchen nayi girki ba saidai Duka gidan muzauna a haka “.

Murmushi dad Yayi ya ce “Sorry my menah me Yayi zafi yanzu mu gyara wajen sai muje joint muci abinci muyi order na dare shikenan ko yanzu Ina daughter?.

Sai sannan mom ta danji sanyi kafin ta Mike ta ce “Ta tafi yawon da ta saba ta san dukanta zanyi ba zata dawo gidan Nan Dan wasa ba”Barema Bata dakuwa tunda ga dad dinta”Harara mom ta galla Masa yayinda Shi Kuma yasa dariya.,

 

Har magriba sabren Bata bar gidan su Affan ba Saida suka ci abincin dinner kafin Mamansu Affan ta kalleta ta ce “Baby tashi ki wuce yayarku ta rakaki dare nayi Kar mom ta nemeki ko?.

Make kafad’a tayi Tana turo Baki ta ce “Mom wlh Duka na zatayi Ni bazanje ba “to wayace kiyi Mata laifin tashi muje Ni na rakaki kar su nemeki dakyal ta Yarda maman Affan ta rakata Tana makale jikinta har suka Isa Palourn Tana ganin mom ta Kara tsorata ganin irin hararar da take aika Mata Lokacin Basu jima da dawowa daga unguwa ba ,dad na ganinsu ya fadada fara’arshi maman Affan Tana zauniya ta ce.

“Biko Nayo Amina ayi Hakuri Kar a daketa tunda ta tsorata murmushi Mom tayi ta ce “Saida ta tasoki kenan Aunty ai Daman nasan Tana chan in bandake Allah da saina daketa Amma taje taci arzikinki ygd “bayan sun Gama gaisawa har dad maman Affan ta wuce gida Sabren ko jikin dad taje ta daddareshi Dan karma mom ta daketa.,

After two weeks Dad ya koma wajen aikinsa Lokoja kasancewar babban immigration ne Yanzu Haka Yana gab da taka matsayi babba dalilin Zuwan Shi course din sati biyun nan dad ya kasance mutum ne mai sa’a tun yarinta hakan yasa kowani course yaje tofa saiya yi nasara(Zakuji tarihin waye dad a Nan gaba) gidan duk Yayi Musu ba Dadi musamman sabren hakan yasa mom ke Kara janta jiki yanzu ko laifi tayi Mata saidai ta tsawatar Mata ko tayi mata addu’ar Shiriya.

,.kasancewar Dad Bai Saba Tafiya Yana barinsu ba duk wajen aikin da za ayi post nasa tofa tare yake Tafiya da iyalan nasa Duka basufi wata biyar da dawowa yola ba da Zama dalilin mom na Cewa hada zaman kudu yake Kara rikirkita tarbiyar Y’ar tata yasa ta kafe Akan Dole yola zasu zauna a gidansu da idan sunzo hutu suke sauka ganin ta kafe ya Sanya dad hakura yake Tafiya Amma duk sati biyu saiya dawo koma k’asa da Haka Dan Daidai da Second daya bayason Nesa da iyalan nasa.

Tana kwance a saman lallausan carpet dinsu Tana note wayar mom dake gefenta tayi ringing dubawa tayi taga ansaka “Aunty Aisha “Cikin sauri ta dauka Tana dariya ta ce.

“Hello Auntyn katsina”Wanakeji kamar baby”Dariya tayi ta ce “Nice Aunty kedama Kika Manta Dani inajinki ko waya kuke da mom bakya nemana sannan kin daina zuwa gidanmu”Ina Ni ina mantawa da Y’ar diyata guda Yakike ya school din ya Kuma rashin ji Yana Nan ko andaina”.

Turo Baki gaba tayi ta ce “Nasan Mom ce take muku gulma ta take cewa Banaji inaji itace dai kawai ta Saba jaraba ai dad Bai taba cemun Mai rashin jiba sai ita ”

“Ke banason wannan maganganun naki mararsa kan gado da har yanzu Baki iya gaisuwa ba ina Maman Naki Take Kai Mata wayar”Mik’ewa tayi ta ce “Bari nakai Mata wayar Maman katsina Ina yaranki Yama sunansu na manta sunansu Mufidat kawai natuna kice Musu Ina Gaishe su”.

Yaza ayi Daman ki sansu keda bason shiga y’an uwanki kike ba To wannan Karin idan mamanki zatazo ki biyota kuzo tare sai kiga y’an uwan naki”,mak’e kaf’ad’a Sabren tayi Tana dariya ta ce “umm umm ni bazanzo ba saidai ku kuzo”.

“to karkizo din ja’ira sai kiyita Zama a garin naku da bakison barinshi Ni bani Y’ar uwata Kar ki cinyemun credit da shiriritar zancenki “Mom dake tsane kanta da hand Drayer bayan fitowarta daga Bathroom ta mikawa wayar ta ce “Mom ga sisterki Maman Katsina “Amsa wayar mom tayi sabren na ganin haka ta ruga Palour tunowa da 8:pm tayi an Fara series din da take so.,

“Ya naji muryarki haka kamar kina cikin damuwa Amina meke faruwa”Numfashi mom taja sai Taji kamar ta fad’awa Y’ar uwartata damuwar da take ciki ta fasa gwara ta cigaba da rike sirrinta tunda wannan din sirrinta ne”Numfashi taja ta ce.

“Ba komai Aunty yagida ya fama da jama’a “Alhmdulillah ya yolar komai dai Lafiya qlau ko?Lafiya qalau Aunty ya Hajja Ina ta Kiran numberta kwana ukku switch up “Ai itama ta sanya ni kiran kinsan Hajja ba Zama take da waya ba da ansaya mata an sace ita tace na Baki sako kin kwana Biyu bakijeba kikaga gida idan da Hali da kin samu kinje “Inshallah Allahu Aunty Zansamu na shiga ko zuwa Jibi Daman Makarantarsu Sabren kinsan basuyi hutu ba Kuma Makarantarsu basa son fashi Amma Zan ajeta gidan makota sainazo nayi kwana Biyu Nima gaba daya hankalina na gunku”.

“Eh Kuma hakane Amma naso ma kinzo da ita ataga Yan uwanta Dan yaushe rabonmu da yarinyar Nan kusan shekara biyar fa Yana dakyau ki dinga zuwa da ita Tana ganin Yan uwanta tunda dai Allah ya cilla Mana ke Auren nesa”Murmushi mom tayi ta ce “Inshallah Allahu Aunty idan suka samu dogon hutu ma taho taren”,

 

Ranar da mom zata tafi katsina Sabren bataji komai ba saboda Jin cewar gidan su Affan zata zauna saboda wasa kwanan mom hudu a katsina ta dawo saboda gaba Daya hankalinta Naga sabren tasan akuyar daure ce ta samu sake Aiko Tasha yawan gida gida Danma mamansu Affan ta na hanasu.,

Yau Sabren tayi niyyar daukarwa Mom kudi a Karo na biyu saboda ta kashewa Yan class dinsu Yanzu ta rage kashe musu kudi tunda dad Baya Nan mom na kitchen Tana shirya Mata break fast ta ruga d’akin tare da Daga drawer ta Inda taga ta na ajiyar kudi babban tashin Hankali ne da tsoro ya mamaye zuciyarta cin Karo da katoton maciji ya bude harshe alamun Yana gab da Sara a matukar rude ta kwalla Kara tare da rugawa da gudu Tana Shirin fita mom na kawo Kai a rude ta riketa ta ce.

“Lafiya Baby Karan me kike?”Cikin tsananin tsoro ta ce “Mom maciji na gani wlh katon maciji a Cikin drawer ki “maciji Kuma?mom ta tambaya cike da mamaki Dan tsawon rayuwa Basu taba ga abunda yayi Kama da ko maciji ba a gidan nasu “Kuka ta fashe dashi ta Ce .

 

“Wlh Mom maciji ne na Daga Zan daukar maki kudi na gansa”tsananin tashin Hankali ne ya bayyana a fuskar mamy Tana dafe kirjinta ta ce “sata kikajemun Sabren na shiga ukku Kenan ke kike daukarmun kudi kwanakima ke.kika daukarmun dubu hudu Cikin jaka me muka rageshi dashi da Zaki koyi halin banza”Kuka ta fashe dashi Tana Mak’alk’ale mom ta ce “Mom Ni na dauka Yan class dinmu nake kashewa Amma wallahi bazan sake ba idan na sake ki kasheni”.

ta karasa fada tana kuka “itama mom din ji take kamar tafasa kuka Dan bakin Ciki A tsorace ta karasa d’akin tare da duba drawer Abun mamaki bataga wani Abu da yayi Kama da ko maciji ba Duk duben da zatayi ta duba Amma bataga maciji ba Fitowarta tayi Inda ta tarar da Sabren a Palour sai kuka take itama zaunawar tayi batasan sanda Taji kukan bakinciki yazo Mata ba ‘ a matukar rude Sabren ta rungumeta Tana kuka ta ce.

 

” Dan Allah mom kiyi hakuri wallahi bazan sake ba Ki yafemun”ta fada tana jijjiga mom take kuka “tajima Tana bawa mom Hakuri Tana kuka dakyal mom ta iya daidaita nutsuwarta ganin fushi ba nata bane ya sanyata janyo hannunta ta ce .

“Me muka rageki dashi a duniyar Nan Sabren,ci Sha ,sutura,Jin Dadi wanne ne bama maki da har zakiji sha’awar daukar Kudin daba a Baki ba sata fa kikayi Kenan barauniya kika Zama Kenan?.

kuka ta fashe dashi ta ce “Wallahi mom Ni ba sata nayiba gani nayi kayan kine shiyasa harna dauka Amma bazan sake ba”Hade fuska sosai mom tayi ta ce “To ai ko kayan iyayenka ka dauka bada saninsuba sata kayi dan haka kimun alkawari ba kayana ba ko na wani Kika Kara Dauka Alkawarin da kikemun ya Ciki”.

Tana hawaye ta ce “bazan sake ba mom kiyi hakuri”Duk abunda kikeso Kika Tambayeni in har baifi karfina ba Zan Baki Sannan me kikeyi da kudi harhaka?Mom Yan class dinmu kadai nake kashewa wlh “Cike da Takaici mom ta ce “Ke Uwar neman gindin Zama to wallahi Kika Kara daukarmun ko wani ma wani Abu zangani saboda Yanzu Nasa Miki wata boyayyar CCTV camera a jikinki Komai kikayi Ina gani Sannan Kinsan Da Allah Yana ganinki kome kike Kiji tsoransa”Tana yarda da wayan da mom tayi Mata ta ce ta yarda”

 

,Dan son tabbatarwa har Mai cire maciji mom tasa Mai gadinta ya Kira mata yazo ba dube_duben da hayake hayaken da baiyiba Amma baiga alamar maciji bama ya taba Zama a gidan sosai mom tayi mamaki sai tabar mamakinta da Cewar shiriritar Yar tatace ma kilama kyankyaso ne tagani tacewa maciji tundaga ranar sabren Bata Kara sha’awar daukarwa mom kudi ba Komai takeso saidai ta tambayeta.

 

______A Koda yaushe lokaci gudu yake kamar yanda kwanakinmu suke ta tafiya suna Karewa mutuwa na Kara kusantomu kwana a tashi ba wuya a gurin Allah a halin Yanzu sabren hartayi jarabawar JSCE d’inta saidai Ba abunda Yayi baya game da sangartarta saima gaba da Abun yake babban Abunda Yafi tadawa mom hankali game da ita jarabar yawonta da ya karu saboda ada iya unguwane kawai Amma Yanzu har cikin gari saidai ta nemeta ta rasa sunyi magamami da friends d’inta na Makaranta sakamakon lafceciyar wayar da Dad ya saya Mata Wanda ba asan ran Mom ba hakan ta faru,.

tsakanin Mom da Dad kuwa har Yanzu babu wani Abu dake tsakaninsu duk Lokacin da suka so Bukatar junansu hakan baya samuwa Dole sai hakura sukayi suka sanyawa sarautar Allah ido Wanda dukkaninsu abun ba k’aramun damunsu yake ba musamman Mom da Har Y’ar Rama Tayi wata guda Dad yakeyi a Lokoja wajen aikinsa yadawo Yayi sati Biyu da iyalan nashi dukda ba yanda Baiyi ba Akan mom su koma tare chan d’in Amma Taki ta ce “Ita batasan zaman kudu wancenma da sukayi zaman kudun Dan sabren Tana Yarinya Ne Amma Yanzu bataga abunda zai mayar da ita kudu ba a Nan ma Arewa cikin hausawa Sabren na yanda taso inaga sun koma kudu ta hadu da yarabawa.

Sabren na zaune a Palour Tana latsa waya Sanye take cikin wasu English wears Riga da wandon jiens wandon ya matseta sosai Gwara ma rigar ta na da D’an fad’i kanta Ba kitso sai parking gashinan da tayi sosai Naga kyawunta ya karu fiye da da ta Kara girma Dukda shekarunta Basu wuce 15 ba Amma Naga yanda ta fara Albarkatun jiki Masha Allah musamman hips d’inta Kasancewar wandon ya matseta ya bawa hips d’inta damar bayyanuwa kamar tasa hips pant Nan ko Surar da Allah Yayi Mata ce kawai”dukda ba wata k’iba tayi ba har Yanzu ba Amma shape d’inta sun bayyanu

Chart take hankali kwance Tana taunar Apple dake hannunta “Kirane ya shigo wayar bayan ta Dauka Sudais ya ce “yadai big girl Kina gida na samu na fito da motar Dad Yanzu haka Ina hanyar gidanku Ki maza ki fito Kafin na d’auko Affan munyi waya Yana ma k’ofar gida yau akwai Outing a gari”Ihun murna Sabren ta buga ta ce “Allah na wajena i will come Now Now da ka iso ka dannamun munafukin flash yehooo kace yau akwai chilling akwaidai isassun kudi hannunka”

“Baki da case din wannan saina iso”yana katse wayar sabren tayi wani ihu ta Ce “Yessss “ta fad’a Tana gusha da Hannu”.

Ihun meye kike haka baby”Mom dake fitowa daga kitchen ta fada “Ba komai mom”.

ta fada Tana aje wayarta “okay tashi muje ki taimakamun da Aiki yamun yawa kinsan yau dad dinki zai shigo gari muje ko cocumber ki yankamun”.

“Diddira kafa ta Fara cikin shagwaba ta ce”Ni wlh mom na gaji ban iya yanka ba kiyi ta wahalar da kanki bayan Dad Yayi a daukar Miki Yar aiki kin kiya Toni gsky bazan iya wahalar Girki ba kalata ba kalar wahala bace kalar hutu ce “ta karasa fad’a Tana turo ‘Dan k’aramun bakinta gaba..

Kame Baki mom tayi ta ce “Dan ubanki kenan ni ce kalar wahalar ko? “Ni ai bakiji nace ba”ta fada Tana Turo Baki.

“Marar kunya kawai Ina gab da daina abinci dake a gidan Nan tunda Ni ba baiwarki bace wasu kamar ke su sukeyiwa iyayensu komai Amma ni har yanzu ban huta ba”.

“Sai Dad ya daukarmun maid house Mai kula Dani Dan Gaskiya na gaji ma da wankin uniform dukda a washing machine Ne Ni nagaji bari dad yazo kawai a daukarmun Mai aiki gidajen kawayena duk da masu aikinsu Amma ke kinkiya a daukar maki kullum kina kitchen
morning,Evening,Afternoon,night kamar Mai Aikin restaurant waidan karsu kwace Miki Miji dad me zaiyi da wata y’ar aiki Amma kishi ya rufe Miki…..kasa karasa maganar tayi sakamakon dukan da Mom takai Mata a baya ba shiri ta Mike Ta shige bedroom d’inta Tana turo Baki .

“Ai da kin tsaya Kinga yanda zanyi dake tabbatacciya irin kina magana da sa’ar Nan Taki”kafin ta koma kitchen taci gaba da ayyukan tarbar mijinta.,

Wayartace tayi ringing Tana dauka Sudais yace ki fito “K’aramun beil Baki kawai ta yafa kafin ta Sanya wani combust Mai shegen kyau jikin madubi taje ta Dan shafa hoda Kadan kallon kanta tayi a madubi yanda tayi wani masifar kyau murmushi tayi tare da fitowa cikin sand’a tabar gidan kar mom ta jita Tana fita ta iske Sudais ya faka mota a k’ofar gida wajensu ta nufa ta na dariya ta ce .

“Manyan Yara Ashe da gaske ka iya mota Aiko Nima saika koyamun”Big girl ake gaya muku wannan show haka zamu yaki people fa “Far da Ido tayi ta ce “ya son ranka “faruq Daya daga cikin class mate d’inta ya ce “Kai wankan Nan fa Yayi tawajena kodai hada ciko”Harara ta b’alla masa ta ce “Shafa kaji”.

Duka dariya suka kwashe Affan ya ce “Wlh ki daina wannan Saran ta shafa muji d’innan da Kika tarko wani shafawa zaiyi”Dako ya shafowa uwarsa da ubasa kwanan sell ta fada Tana bude murfin motar tare da shiga Tace “Kuyi sauri mu biya mu d’auki zey ta shirya.

“Saida suka biya suka d’auki zey kafin su wuce yawonsu guri guri wet learn park and garden suka Fara nufa sosai suka shakata a park d’in suka Sha hotuna kafin su wuce admiral Park Shima sun jima suna shirme da Shan ice cream da hotuna har bayan magriba Kafin su wuce gida ikon Allah ne kawai yamaida kowannensu gida saboda Kasadadden tuk’in D’an koyon da suka hau Dan kwananshi Biyu da Gama koyon motar.,

Saida ta shigo gida ne da danji wani iri tasan mom saitayi Mata fad’a sosai akan yawon da ta tafi tun azahar Ganin motar Dad a parking space ya Sanya hankalinta kwanciya tare da kutsa kanta cikin Palourn…

*KATSINA STATE*
_Ta Dikko ‘Dakin Kara_

Gaba D’aya masarautar ta kauraye da bushe bushe da kide kide na maroka,motoci ne na alfarma kwara Biyar suka kutso cikin masauratar Wanda shigowarsu ya k’ara sanyawa gurin ya hargitse da mabusa,.

busa ake sosai irin ta gidan sarauta tare da kirari ta ko wani bangare “D’an sarki ,jikan sarki magajin sarki D’aya tamkar da dubu sha kundun mahassada,an buga dakai an barka Jan Zaki mai bawa maza tsoro,.

,kaid’inne Mai firgita namun Daji taka Lafiya yariman da Babu kamarsa ,saukarka Lafiya asalin jinin sarauta ,mazan fama,takawarka Lafiya D’an Uwar gida Hajiya Aisha fulanin mai martaba Uwar sarki Kuma matar sarki barka da zuwa shalelen Mai Martaba ,Kuma shalelen masarautar katsina da kewayanta Ganinka sai Mai sa’a,kaid’inne dai Mai firgitasu,.

kirari ake sosai Ana bushe bushe da kid’e_kid’e Sojoji ne sunkai Goma suka fito tare da zagaye motar da yake kowannensu fuskarsu murtuke ba alamar imani a cikinsu suna rik’e da bindigu Nanfa waje ya Kara kaurayewa da sabon kirari D’aya daga cikin sojojinne ya bud’e murfin motar tare da kamewa ya sarawa Wanda yake ciki kafin suma sauran su kakkame tare da sarawa da jinjinar ban girma Saida akayi kusan 10 minutes kafin ya zuro kafarsa D’aya wacce ke dauke da Wani tsatsadan cover shoe Wanda ko mahaukaci ya kalli takalmin yasan mallakarshi sai manyan gaske Wanda suka Isa, saidai Yayi kusan two minutes kafin ya zuro dayar kafar A hankali Yake fitowa daga Motar cike da Tsantsar tak’ama da izzah “Ai sumar tsaye nayi cin Karo da……..✍️

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN*🧸

 

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

Arewabook👉@miss Hajo✍️

🅿️…………*11 & 12*

 

Cin Karo da kyakyawar fuskarsa mai dauke da tsantsar kwarjini da haiba Gaba Daya jikinsa a mummurde yake daka kallesa kaga kakkarfan gaske Kyakyawane ajin karshe Wanda tsayawa kwatanta Kyawunshi ma B’ata baki Ne Dan page D’aya Yayi Mana kad’an mu bayyana ainahin surar wannan bawan Allah wannan Shi ake kira da ainahin mijin novel(lol)Kyakyawane na bugawa a news Ba Fari bane irin chocolate colour dinnan ne da fatarsu har wani glowing take,gaba Daya kyakyawar fuskar tasa zagaye take da lallausan sajen da yasha g’yara kallo Daya zakayiwa sajen kasan ba k’aramun g’yara yake Sha ba duba da irin yanda ya kwamta luf bakin sajen har wani shining yake,dogon hancinshi kamar an zana idanunshi ko kallo Daya zaka yi mashi ka sadda saboda wani irin kwarjini da haiba(,Nayi sakato Ina jinjina Tsantsar kyau da Allah Yayi a wajen wannan bawan Nasa, Bansaniba Ashe har ya wuce saurin binsa Nayi hada had’awa da gudu Dan dauko muku rahoto yanda ya kamata).

 

Tafiya yake irin ta jinin sarauta Taku yake cike da izza har Lokacin masu kirari da bushe bushe Basu bari ba Wanda Jin hakan yake tamkar ana d’iga Masa digon darma a kansa dan a rayuwarsa inda Abunda ya tsana Bai wuce hayaniyar jama’a da irin wadannan abubuwan masu hawa ka ,

baiyi Wata Tafiya Mai tsayi ba ya Isa ga fadar Mahaifinsa Mai Martaba Alhaji Salim muhmod ko ban fad’a ba kunsan dai yanda kyau da tsaruwa yake na Gidan sarauta musamman Aje ga fadar Mai gayya Mai aiki ,gaba Daya hakimai,da Yan fadar sarki suna zazzaune.

sosai aka shiga yiwa Yarima barka da zuwa Fuskar Yarima da Annuri ya karasa ga kujerar Mai Martaba Wara Masa Hannu Yayi Inda ya shige ya lafe a jikin mahaifin nasa yanajin Wata nutsuwa Na saukar Masa sauran fadawa da Y’an zaman fada gaba Daya watsewa sukayi saboda dokar sarki ce Indai Yana magana da iyalansa Bamai Zama a wajen musamman Kuma *Yarima Anwar* da yake star a wajensa ,.

a hankali Mai Martaba Ya dago dashi daga jikinsa tare da shafa kyakyawar fuskarsa ya ce “Soja na barka da zuwa nayi farinciki matuka da Allah ya dawomun dakai lafiya da kuma nasarar da kukayi a yaki munga irin karramaka din da akayi sannan ina tayaka murnar karin girma da ka sake samu shiyasa a Koda yaushe nake matukar Alfahari dakai my son Allah dafa maka akan komai”Ameeeeen Abba na nima Ina matukar Alfahari da Kasancewarka uba a gareni fatan munsameku lafiya”gaisuwa sukayi irin ta soyayyar d’a da uba Kafin ya Tashi ya wuce Bangaren mahaifiyarsa.,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tungada shigarka Bangaren Uwar gidan sarki Hajiya Aisha Fulanin sarki mahaifiyar Yarima Anwar zakasan ka shigo daular masarautar,Palour ne D’aya bayan Daya zakayi ta wuce su kowannensu Kuma shake yake da Abun duniya kayan alatu,da Kuma kaya irin na Gidan sarauta ko wani daki lik’e yake da kyawawan hotunanta ita da Mai martaba gaba D’aya ,Hadiman dake aiki a Bangaren Saida suka k’ame ganin shigowar, Yarima Anwar kowannensu na kawo irin tashi gaisawar tare da dukursawa kowa Yayi k’asa da kansa ba Wanda ya Amsawa tafiyarsa kawaii yake Cikin izza da takama.,

Saida ya karasa Babban palour Wanda ya take wad’ancen komai da kyau Aljannar duniya kenan Mahaifiyarshi dake sanye cikin Lafceciyar Alkebba Mai matukar Kyau da daukar hankali sanye take cikin tsatsatsadan lace Mai masifar kyau Tana ganin shigowarsa ta Mike tare fadada fara’arta ta na ware Masa Hannu ta ce.

“Oyoyo my son ur welcome ,sannu da zuwa Mazan fama namijin duniya na oyoyo “Lokaci guda ya saki wani lallausan Murmushi Tare da rungume mahaifiyar tasa yanajin guminta wata irin nutsuwa Na k’ara sauko Masa ,.”cike da farinciki ya dago tare da dago da fuskar mahaifiyar tasa Yana Murmushi ya ce “miss You alot Mamy na”.

yanayin yanda Yayi maganar ma kadai ya Isa ya saukarwa da Mai sauraro kasala cikin wata zazzak’ar murya Mai cike da nutsuwa.

“Murmushi Mamy tayi ta ce “Miss You too Soja na muje ka ci special girkin da na Sanya akayi domin Kai kadai” I can’t eat anything now I want to rest mammy anjima idan na huta zanzo naci”.

ya fad’a Yana D’an langabewa “kardai har Yanzu kana Nan da rashin son cin abincin Nan naka son “murmushin gefen Baki Yayi Wanda ba kowa zai fahimta yayishi ba ya ce”Ina ci Sosai Mamy na ko Kinga na rame Ne”Girgiza Masa Kai tayi ta ce”.

“A a a a kyau ka k”ara ta fad’a Tana latsa wayarta tare da yin Kira ta ce “Ku shigo ku gaisa mun gama.gaisawar”Saboda girmamasa da ake Indai Yana magana da Mamynsa tofa ko kannansa Basa Zama wajen har sai sungama”.

Tana sauke wayar Y’an Mata su Biyu suka shigo Palourn kallo D’aya zakayi Musu kasan sud’in jininsa ne D’aya Bazata wuce 22 years ba sai d’ayar bazata wuce 17 years ba “Kowaccensu da fara’arta ta shigo Palourn cikin girmamawa da nuna Farincikin dawowarsa Sukayi welcoming nasa tare da dukursawa har k’asa suka gaishe sa ,ya Amsa Musu tare da tambayar lafiyarsu Suka Amsa Masa da Alhamdulillah”Tare da Kallon Mufeeda ya ce “Ya school d’in hope kina maida hankali ko ?”.

Tana fara’a ta ce “Ina mayarwa Sosai Yaya Ai munshiga s s two Yanzu”Yana latsa waya Ya ce “Karatun naku baya sauri”wara idanu tayi sai Kuma tayi Dariya ta ce “Yaya na zata haka za kace Yayi gudu fa?.

Shiru yayi mata Hakan bai dameta ba Dan tasan yayan nasu ba mutum bane Mai fiya doguwar Magana idan yaso “Maryam dake zaune gefensa ta ce “Yaya Ni baka Tambayeni ya school d’inba Ina maida hankalin?.

Ba tare da ya dago ya kalle Ta ba ya ce “a a a karki maida Tunda Position ake rubuta muku”Yar Dariya tayi ta ce”Uhm to Nima dai Ina maidawa Dan Second semester dinnan Bani da c o ko Daya” good girl”Ya Fada Yana jinjina Mata da Hannu.

“Yana mik’ewa ya kalli Mamy ya ce “Na wuce Part d’ina Zan huta'”Okay a biyoka da abincin kenan”Eh Nan da 2hours, Mufee ko Maryam su kaimun ”

Murmushi Mamy tayi bayan barinshi Palourn ta Girgiza Kai ta rasa dalilin da yasa ‘Dan nata bayason hada Hulda da Mata Ko gyara part dinsa za ayi Dole sai baya part din hakan yasa ko hadima bashi da ita ita gani take kamar ma tsoron matan yake gashi dai jinin sarauta tilon d’a namijin sarki Wanda ake sa ran shine magajin masautar Amma kwata_kwata Bai damu da sarautar ba kwata kwata ta lura sarautar ba itace gabansa ba yafi mahimmanta aikinsa fiye da ita.”,

Kwanciya Yayi a makeken royal bed dinsa d’akin ba abunda yake Dauka sai sanyayyen kamshi har wani lumshe Ido yake saboda Shi Daman can mutum ne ma’abucin son kamshi a Rayuwar Yarima Anwar Yana Kaunar kamshi shiyasa kullum Baya rabuwa da turare motarshi, office dinsa,duk inda zaije tofa zakaji yana kamshi Bai Jima da kwanciya ba baccin gajiya ya daukesa.,

Koda ya farka Yayi mamakin jimawar da Yayi a bacci Bathroom ya fad’a Yayi wanka bayan ya fito ya shirya cikin wasu tsatsadan kananan Kaya da suka Amsa sunansa Sai Baza kamshi yake Cikin takunsa kamar Wanda baison taka k’asa Ya fito Palourn sa Wanda ni kaina Saida nayi kauyanci cin Karo da tsadaddun Furnitures din dake shake a Palour Kai tsaye dining ya nufa ganin an jera abinciccika da drinks² kala_kala yasan aikin Mamynsa Ne,Baici wani Mai yawa ba fruit salad din Ne ma yasha Mai D’an yawa masallacin cikin masarautar ya nufa Dan gudanar da Sallar la’asr Da aka Kira cikin jam’i..

*HAJIYA TALATU*

Safa da marwa kawaii take ta kasa zaune ta kasa tsaye Ga waya a hannunta Kallon matashiyar budurwar da Ta haura 24years tayi ta ce,.

“Kina Gani surayya Wai har Anwar ya shigo masarautar Nan tun 1pm Amma har Yanzu Bai Tako ya gaishe Ni ba,kina gani Da idan ya shigo masarautar Nan kafin ya je Bangaren uwarsa ma saiya Fara zuwa ya gaisheni me hakan ke nufi,kodai tsinanniyar Uwar sannan ta shiga ta fita ta rabani da d’an da na raina da hannuna ,ita harta Isa ta rabani da Anwar D’an danasa buri a kansa,fiye da yaran Dana haifa,never wlh abunda bazaiyu bane wallahi,tallahi,kinji na rantse Bata Isa ta rabani Da Anwar ba haihuwarsa kawaii tayi Amma Ni ta haifawa Bata Isa taci gajiya biyu ba ta ci gajiyar sarki yanda ta mallakesa komai sai ita,Kuma taci gajiyar Uwar sarki,Ni Nan nice Zan Zamewa Anwar uwa Ni zanyi yanda nake so dashi ,Kartayi tunanin ita kad’ai keda d’a namijin Ni da nake da Mata Zan tashi a tutar banza saidai ita ta tashi a banza ,hmmm Mai laya ya kiyayi Mai zamani muje zuwa Yanzu zamu Fara buga wasan dake Hajiya Aisha “.ta karasa fada Tana wani shu’umin murmushi.,

 

Surayya Dake latsa waya Bata dago ta kalleta ba bare ta sa ran amsa hakan ko Sosai ya kular da Hajiya TALATU,cikin fushi ta ce “Watau Ina magana kin mayar Dani mahaukaciya bakima da Lokaci na”Mik’ewa tayi Tana had’e fuska ta ce.

“Ba abunda ya shafeni bane “Tana Gama fad’ar haka ta Mike tabar Palourn,”Sakaran banza wacce batasan ciwon uwarta ba “.

ta karasa fad’a Tana Jan dogon tsaki tare da Kara dannawa number da take ta trying Kira ta Kara a kunne Jin Tana ringing kamar yanda tayi ta Kira daukace ba ayi ya sanyata Jan dogon tsaki cike da fushi ta ce ,”Sakaran banza ita ma ko Ina ta Sanya wayar”,Bata rufe Baki ba aka Dauka “Cikin fad’a ta ce “Wai Gidan ubanwa Kika Aje wayarki tun dazu Ina kiranki Baki dagawa”.

Cikin gigin bacci tace “Ina bacci ne Aunty meya faru”to saiki tashi daga baccin asarar *Yarima Anwar* ya shigo gari kome kike ki barshi ki chanchada ado sannan ki shafo turaren Nan na wajen boka Lauje ki barbade jikinki dashi sannan ki Sanya kwallin Nan da duk kayan da ya Baki ki maza ki taho kiyi shigar daukar hankali na fad’a maki’ “Ina jiranki yanzu Yanzu”.

“Ihun murnar da ta buga ne ya Sanya hajiya TALATU kauda wayar daga kunnanta ta ce Sakaran banza Shekara da shekaru kin kasa sace zuciyarsa kina mace Amma ki kasa.sace zuciyar d’a namiji shima sai shegen taurin kai,.Bata rufe bakinta ba Taji sallamarsa cikin Palourn”Lokaci guda ta hargitse tare da Nemo nutsuwarta Cikin fara’a ta Fara da cewa.

“Lale Mar haban d’ana na kaina D’aya tamkar da dubu Yanzu nake Shirin zuwa Wajen naka samun labarin da nayi kazo Naji ko lafiya nasan dai Kayi watanni bakanan baka ga mamanka ba Ni zaka Fara mamarin gani hankali na duk ba kwance ba Yana wajenka saida naga cin nasararku a yak’in Nan hankali na ya kwanta “D’an murmushin gefen bakin da ya Saba Yayi Mata Tare da cewa.

 

“Ina Yini Mama na sameki lfy “Tana zauniya gefenshi cikin kulawa ta ce “Lafiya qalau My son ya hanya Kun shawo gajiya Sannu ko “.

Sosai mama TALATU da dinga janshi da hira Wanda baya biyemata Sosai hakan Bai dametaba saboda tasan halinshi mutum Ne marar son yin maggana da rashin son hayaniya.

“Jin karar bud’e k’ofa Ne ya Sanya Hajiya Talatu Daga Kai Ta kalleta sanye take cikin wasu matsatsun Kaya Atamfa Riga Da sicket sicket din bayanshi Mai katuwar tsaga.

,Kasancewarta Mai kiba Sosai ya Sanya kayan suka Dame jikinta Sosai Bata da Wani Kyau na azo a gani haka Bata da muni tana dai da kyanta Daidai misali bak’a ce Amma ba’kin nata Mai kyau taci daurin tuge kaga tsiya gyale a kaf’ad’a Tana taunar chumgum ta karaso tsakiyar Palourn ta gefen Ido Hajiya Talatu ka kashe Mata Ido D’aya itama kashe Mata tayi tare da Gyaran murya cikin muryar daukar hankali ta ce “Assalamualaikum”.

Anwar har Lokacin Kanshi sadde Yana latsa waya Bai dago ba haka bata sa ran zai dago ba saboda sanin halin izzarshi da gadara da tayi hajiya ce ta Amsa Mata da cewa “wslm Ummulkulthum yanzu Kika dawo kenan “Tana wani yauki ta ce.

 

“Wlhko Aunty Ina Yini”Kafin ta karasa kujerar da Anwar yake cike da pretending Ta ce “Lah Ya Anwar Yaushe ka zo Waida kaine zaune ina Yini”.

Sai Sannan Ya D’ago tare dayi Mata kallo Daya ya Tabe Baki ya ce “Lafiya”Kafin ya Mike Ya kalli Hajiya ya ce “Na wuce mama”.

ba zaka zauna muci gaba da hirar ba son kasan nayi kewarka fa da yawa” Zan dawo mama Yana Gama fad’ar haka Ya bar Palourn Cikin takun kasaitarshi Wanda kulthum garin kallonshi Har Faduwa Daga kan sopa taso tayi dankwashin da mama ta Kai Mata ne ya dawo da ita Daga duniyar Tunanim shaukin kaunar Yarima Anwar data Lula Firgit ta zabura ta ce.

 

“Me nayi Miki Aunty”Ubanki kikayimun Dan Ubanki haka Kika zauna Har yabar d’akin Sakaran banza da Kika rako Mata ko shagwabar Nan Baki iya ba ta Mata Mai makon ki bishi kina shagwaba kina rangwada Kina cewa”Haba darling ya zaka tafi Bamu ko gaisaba ,me kakeson na girka maka,ko Uhm muje to na bika nayi maka hira ,da sauran shagwabar Mata Amma banzar Kika barsa yatafi haka sakkarai Shaka tafi kawaii…..

*Adamawa Yola*

“Daga Gidan ubanwa kike Tun dazu da wannan tsinanniyar shigar Dan Ubanki ”

Mom ta fad’a Tana tasowa ranta a matukar Bace ta nufota”Baya Sabren tayi da niyyar rugawa Taku Daya mom Tayi ta chafeka Tare a wanketa da Marin da Bata taba Mata irinshi ba .

“K’aran da ta fasa ta durkushe a wajen ya Sanya Dad fitowa daga bedroom da zuwanshi garin ba jimawa Kenan.

“Duka Mom ta hauta dashi cikin fushi take cewa”Dan Ubanki ban hanaki yawo ba,ban hanaki fita ba,Gidan ubanwa kike zuwa bada izinina ba,Khadija daukar magana kike son kimun Shekara Sha Biyar Tsit dake Aiko yau zanji Gidan ubanda kike zuwa”.

“ta fad’a Tana niyyar Kai Mata wani dukan Dad ya riketa cikin fushi ya ce “me tayi maki Zaki hau mun Yarinya da duka meye haka Amina sau nawa Zan fada maki ki daina Dakar mun y’a matukar ba sabawa kikeson muyi ba meyasa Ina kiyaye abunda ke bata miki rai Amma Ni bakya kiyaye nau so nawa Zan fad”a maki idan kina son bacin Raina ki tab’amun y’a why Amina kike dukanmun y’a sau nawa zanyi maki kashe”Cikin fushi mom ta D’ago ta ce.

 

“Rabona da ita tun azahar fa bansaniba tayi sand’a tabar Gidan Nan dubamun awa nawa tayi a waje Ina taje da wannan shigar,da da Yanzu fa ba D’aya bane yanzu ba Yarinya bace kome zakace saidai kace Amma wlh bazan yarda ta lalacemun ba saboda kan a zageka sau Daya an zageni sau dubu Dan haka ba ruwanka da tsakanina da ita ka barni na Tarbiyantar da y’ata Abban Sabren Banason Abunnan Nima matukar ba so kake mu samu sabani ba wlh Ka Bari na binciki inda take zuwa Tunda tayi jsce dinnan yawonta ya Tashi daga unguwa ya koma Gari ,Gidan ubanwa take zuwa,wata sani a garin ?”

Ganin Mom tayi sama ne ya Sanya dad kwantarwa ya ce “Yi Hakuri To Naji mu bincike ta din Amma. Karki sake dakanta please”Kafin ya kalli Sabren dake kuka Tana diddira kafa ya ce ,Sorry daughter yi shiru Ina kikaje”.

Saida Yayi ta lallashinta Wanda hakan k’ara kular da mom Yayi Kafin cikin kuka tace Dad Ni ba inda nake zuwa Ina Gidan su Affan tun d’azu”Taso to my daughter sorry yiwa mom Hakuri rashin sani ne Kafin ya kalli mom ya ce.

 

“Kinji ko ba ason Yanke hukunci cikin fushi”Ban yarda ba wlh Bari na Kira Maman Affan d’in na Tambayeta Karya take”

 

“Tana Gama fadar haka ta janyo wayarta daga chaji gaba D’aya Sabren ta tsure kallon dad da tayi ya Sanya hankalinta kwanciya tare da lafewa jikinshi Tana turo Baki a ranta ta ce “Ai tunda Dad na nan Baki Isa ki sake Duka na ba”.

“Ringing Biyu Maman affan ta dauka ko gaisuwar kirki basuyiba Mom ta ce “Dan Allah Aunty Sabren tazo Gidan Nan yau kuwa?.

“A a a Gaskiya Tun yau ban sata a Ido na ba Yanzu ma nake yiwa Affan fad”a tun azahar rabona dashi”Okay nagode”Mom ta fad’a tare Da katse wayar Chazar wayarta ta dauka tare da nannadewa ta ce.

“Wallahi koki fad’amun inda kikaje ko Yau mu fitar da raini Ni dake a Gidan Nan ?ta fad’a Tana rib’a wayar charger Biyu”Wata irin zabura Sabren tayi tare da Mak’alk’ale dad ta fashe da kukan Tabara Ta ce “Dad Karka Bari ta dokeni wallahi Zan fad’a Mata inda bazata dokeni ba………..✍️

*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

@Arewabook👉 @Miss Hajo✍️
@whats app👉07026166536
@Facebook👉Hajara L Sadeq
@instagrams👉Miss Hajo
@Tiktok👉Hajara L Sadeq

🅿️…………*13 & 14*

“oya Ina jinki fadamun inda kike zuwa “mom ta fad’a Tana huci”Sabren Tana muzurai ta ce “Sudais ne ya dauko motar daddynshi ya kaimu park daga nan ba inda mukaje”.

“shine Dan Baki da d’a a kika shiga har cikin mutane da wannan kayan to wallahi Daga Rana irin ta yau Kika Kara ficewa daga gidannnan kukayi magamami da kawaye Kuka tafi yawo ki tabbatar ranar saina fasa maki jikinki sakarai da Bata da abokan yawo sai maza wuce kije kiyi sallah ”

B’arin jikin dad tayi tare turo k’aramun bakinta Tana gunguni tayi hanyar bedroom d’inta “Ni kike murgudawa Baki kikewa gunguni ?mom ta fad’a batare da ta juyo ba ta ce “Idonki ne baigani sosai Ni ba abunda nayi”Tana Gama fadar haka ta shige bedroom d’inta Tana Jan tsaki gado ta Haye tare da Jan dogon tsaki ta ce “Kuma ba ayin sallar”sallar da batayi ta ba kenan “,.

Saida tagama chat d’inta da kalle_kalle a waya sai wajen 11:pm ta Fara Jin bacci d’akin su Mom ta wuce tare da hayewa gado taja bargo Takaici duk ya Gama cika mom Mik’ewa tayi Tare da daukar pillow zata Fice dad ya ce.

“ina Zaki Kuma”Palour Zan Kwana ku dinga kwana Kai da ita tunda haka kuka zaba “Tana Gama fadar haka ta wuce Palourn tare da kwancewa Kan kujera zuciyarta duk ba Dadi ,Girgiza Kai dad Yayi ya Mike da niyyar yaje ya lallasheta Sabren ta rikeshi cikin shagwaba ta ce.

“Kaima dad ka rabu da ita dan taga kana ta Tarairayarta shiyasa take maka wulakanci ta Kwana a Palourn muma muyi kwamciyarmu ita zatayi kwanan kujera ta kasa motsawa ta tashi da ciwon jiki”.

ta karasa fad’a Tana saka dariyar shakiyanci,shima dad dariyar Yayi ya ce “Allahko daughter”Eh Mana Dad'”ka rabu da ita “washegari mom da fushi ta tashi Dakyal Dad ya samu Ya shawo kanta da kalamai masu Dadi “.

_____Yau Dad da mom sukayi wani shiri wajen Azahar suka shirya bayan sun Gama lunch gaba Daya suka wuce Gidan kawar mom Dake dou girie sosai Sabren ke murna Kasancewar akwai kawayenta a Gidan gasu Suma irintane akwai rashin ji sosai Maman Janna tayi welcoming nasu Sabren ko Kai tsaye wajen kawayenta ta nufa suka hau tsallen murnar ganin juna bayan mom sun gaisa Da kawarta ta Mike ta ce.

“Maman Janna Bari zanje na dawo ba jimawa tare muke da Daddyn Sabren”Har bakin get ta rakata bayan sun gaisa da dad Tana zolayarsa da yazama bita zaizai Dariya Yayi ya ce.

“to ai malaminku Daya da kawar Taki kema ai haka Kika mayarmun da aboki”Dariya mom tayi ta ce “Muje ka rabu da wanna Uwar tsokanar”Ransu Kal suka wuce gida.

“Sabren ko bayan Gidan su Janna suka wuce ita da ita mate dintace Daman Sosai suka hau wasan guje guje da tsere tsere tare da Kanin Janna suna cikin yin Lilo Sabren Taji kanta Yayi wani irin sarawa kafin tafarajin duniyar gabaki daya na juya Mata wani Kara ta fasa Wanda Saida ya kaurayewa ilahirin Gidan ta ce.

“Dad “Kafin ta sulale a wajen sumammiya sosai hankalin su Janna ya Tashi da gudu suka je suka sanarwa mamansu hankali tashe suka sungumi Sabren Basu zarce ko Ina ba Sai boshom clinic hankalin maman Janna duk ya Tashi ta rude yo ba Dole ta rude ba ankawo Mata Diya lafiya qalau ta sume a gidanta Dukta rude number mom ta Kira a Lokacin shigarsu Bedroom kenan hankali tashe ta ce.

“Kina ina maman Khady ku maza ku juyo Boshom clinic “hankali tashe mom ta ce “Subhanalla waye ba lafiya kuma yanzu fa muka rabu”Sabren ce wlh suna wasa da Yara ta sume Yanzu haka suna ciki tare da Dr”.

Ai mom bata karasa sauraron abunda zata fad’a Mata ba ta fashe da kuka”Dad a rude ya ce “Lafiya meya faru”Cikin kuka ta sanarwa da dad ai finta rud’ewa Yayi hankali tashe ya figi makullin mota da gudu mom ta bisa Lokacin da suka Isa clinic din. Dr din Daya shiga duba Sabren ya fito kalllon maman Janna Yayi ya ce .

“Duk gwaje gwajen da zanyi Mata na yi Babu abunda ke damunta watakila taga abunda ya firgitata Ne Amma insha Allah zata farfado Nan kusa”.

“Dukansu Ajiyar zuciya suka sauke har su Mom da suka shigo kafin su d’unguma d’akin Dad ya rungumota jikinshi,ba ayi 20 minutes ba ta farka Tana ganin dad ta makalkaleshi tare da Fara kuka.

“Lallashinta dad ya Fara Yana Daddab’ata bayanta har ya samu tayi shiru “tambayarta suka shigayi meta gani Me ya sameta “Ba Wanda ta iya ba Amsa saidai tace bakomai,Sosai Kan mom da dad ya Kara daurewa har suka Isa gida.

Washegari Tana zaune jikin dad Tana buga game wayarsa tayi ringing cikin Fara a ya Daga wayar tare da gaishe da yayan nasa Cikin mutuntawa kallon dad tayi ta ce.

“Dad uncle Ahmed ne bani Shi”Murmushi dad yayi tare da Kara Mata wayar a kunnenta “hello Mamanmu yakike”Ya fada Daga bangarensa Tana dariya ta ce “Lafiya qlau uncle Ina Yaya Faruq kace nayi fushi dashi Yanzu yadaina zuwa gidanmu”.

“Ciikin muryar dattako ya ce “to ai ke yakamata kizo Mana hutu tunda Shi aiki ya hanashi zuwa ko”Turo Baki gaba tayi tare da make kaf’ad’a kamar Tana gabansa ta ce “Ni bazanzo Lagos ba Uncle saidai ku kuzo Ka gaishemun da Yaya Faruq da Aunty Hafsat Sannan yaushe zakuzo” .

Yar dariya Daga bangarensa yayi ya ce “To shikenan zasuji ai kunma kusa zuwa tunda bikin auntynki ya kusa”wani tsallen murna tayi Tana ihun zasu Sha biki janye wayar a hannunta Dad yayi Nan Dan uwan nasa ke shaida Masa bikin Y’arsa Hafsat da aka Sanya wata biyar masu zuwa ,dad yayi farinciki sosai Kuma ya Sanya Albarka tare da addu’ar Allah ya kaisu Lokacin da Rai da lafiya.

Lokacin da dad ya koma wajen aikinsa sannan mom ta Fara Shirin Tafiya katsina ita da sabren tunda tayi J’s c e taga y’an uwanta dukda sabren ba Dan ta so ba ita ala Dole mom takura mata zatayi Dan batason tayi missing friends d’inta tunda safe sukayi wanka tare suka shirya Ganin Sabren ta shirya cikin kananin Kaya ne Riga da wandon Jiens masu kyau tayi parking gashinta tsakiyar ka tare da Sanya karamun beil blue sosai tayi Kyau ta fito kamar Wata baturiya ya Sanya mom harararta ta ce.

“Da wanna shigar zamu tafi koma ki sauya “Lokaci guda ta tubure tare da tirjewa a kasa tahau birgima ta ce .

“Ni wlh bazan sauya kayan Nan ba idan ba haka ba saidai ki tafi ke Daya Ni Daman bason zuwa wannan garin naku nake ba”banza mom tayi ta kyaketa har tagama tirje tirjenta Saida tagama shiryawa tasa kayanta akwati kafin ta kalleta ta ce.

“Zoki saka kayanki na sati “Tana turo Baki ta Sanya kayanta Wanda duk k’ananun Kaya ne Har suka fito mom batace Mata kala ba Drivern dad ya jasu a motar ta Suka wuce Saida suka dauki Hanya kafin mom.ta kalleta ta ce “Saura muje ki dinga yimun sakarci cikin mutane keda Baki sanin kin girma ba”

Turo Baki gaba tayi tare da kwantawa kafadar mom sosai suka hau Tafiya kowa yasan tsakanin yola da katsina ba karamar Tafiya bace “Sabren kamar zatayi kuka ta ce “Mom garinku nisa ni bazan sake zuwa ba “Kyaleta mom tayi sai chocolate din data taho Mata da ita ta Mika Mata cikin murna ta amsa Tana Dariya ta ce.

“Thanks my dear Mom”Tana cikin Shan chocolate d’inta tanayiwa mom surutun hanya duk inda suka wuce Saitayi tambaya mom ta Bata Amsa kafin a kafadar mom bacci ya dauketa mom na ganin haka ta g’yara Mata kwanciyarta akan cinyarta….

*Katsina*

“yakamata ace ka baro Lagos dinnan Anwar ka Dawo Nan saboda shekaru suna ja baya yakamata ace ka Fara sanin abubuwan da suka shafi sarauta banason kana nesa da Gidan Nan”.

“Mai martaba ya karasa fad’a Yana shafa Kan Dan Nasa “Murmushi Yayi ya ce”chan d’inma suna Bukatar irinmu a wajen Abba Aikine mukeyiwa k’asarmu tare da Kare hakkin alummarmu Matsalolin chan sunfi na Nan Amma tunda kafi Bukatar Hakan Zan jaraba Naga transfer idan zata yiwu”

“Zama ta yu ma muma din muna bukatarka gwarzona fiye da chan amincewarka kawaii nake bukata idan yau nayi waya sai anyi maka transfer an kaika duk inda kakeso kasan muna da wannan alfarmar a k’asar nan”Dan Murmushi Yayi ya ce “Abba a Bari ba yanzu ba duk sanda na shirya baro chan da kaina Zan maka Magana.”,.To shikenan Allah Yayi maka albarka “Ameen Abba”.

Daga wajen Abba bai zarce ko Ina ba Sai part din mama Talatu,tundaga dosowarshi Palourn yakejin warin babban abunda ya tsana watau sigari ,zaune ya tarar da ita sanye cikin alkyabba Tana bawa hadimai umarni daga d’ayar kujerar Kuma Haidar ne zaune ya Dora kafa Daya kan Daya Yana zukar sigari”.

” Ka karaso Mana son”a a mama Nan ma Yayi biyowa nayi Daman na gaisheki na wuce “Yana Gama fad’ar haka ya juya hararar Haidar Mama talatu tayi ta ce.

“meyasa baka gaisheshi ba,sannan kaga kaja ka korarmun Shi na tabbata wannan warin sigarin ya hanashi karasowa sau nawa Zan fad’a Maka Haidar ka daina shamun sigari a part Amma dayake kunnen kashine dakai Bakaji”ta karasa fad’a Tana Jan kunnansa”.

Dan kara yayi tare da Mik’ewa ya ce “Ke kikejawa mutane raini Wlh Aunty wannan yaron da na girmesa zaki dinga Cewa na gaisar”To ai Yana gaba dakai tunda dai Dan sarki ne Kuma magajin sarki Kuma sarki Nan gaba kadan”.

“Ai Bai Zama sarkin ba” ya fad’a Yana mik’ewa tare da barin part din ya wuce club Hajiya TALATU ko mayafi ta yafa tare da ficewa tare da direba a mota ta Kira number Kulthum bayan ta Dauka Taji muryar wani Yana Mata magana ta ce.

“kina ina Dan ubanki naji muryar namiji kusa dake “Tsagat Kulthum ta Mike tare da yiwa na kusa da ita nuni da Hannu da Yayi shiru ta ce “a kallo ne Aunty kina ina “ki sameni Gidan Hajiya Saude zamu koma wajen bokane akan maganarki da Anwar banga wani cigaba ba”Ai Lokaci guda Kulthum ta mike har tuntube take ta ce.

“Gani Nan Aunty yanzunnan”Kayan jikinta ta mayar batama k’ara waiwayarsa ba da yake mata magana ta ce ” sai anjima Baby yau bazan kwana a Nan ba karma ka jirani’tana Gama fadar Hakan ta Yayi gyalenta tare da barin hotel d’in gaba Daya ta nufi Gidan da zasu had’u da Auntyn Ta ta”,.

Durkushe suke gaban wani garsakeken Boka Fuskarnan tasa bakikkirin ba alamar imani a tattare dashi Kafin ma Suyi magana ya dakatar dasu cikin muryarsa marar dad’in sauraro ya ce.

“Nasan abunda ke tafe daku Maganar Nan ce dai Akan Yarima ,
Har Yanzu hankalin Shi yaki karkata gareku ,sannan ya Fara ja Miki baya ba kamar da ba da yake daukarki uwa ” .
sannan ya Fara wasu abubuwa irin na Yan tsubbu kafin ya kuma Cewa “Aiki Bai lalace ba Hajiya yaron ne Yana da taurin Kai sannan mahaifiyar sa tsaye take dayi Masa Addua Karki damu zamu zuba sabon Aiki Wanda Dakanshi zaizo yace yanason kanwarki da Aure,zata auresa Dole Kuma zaku juyashi,kije Nan da sati biyu ki dawo akwai Mashahurin aikin da zamu gabatar da manya manyan Aljannunmu da na ketare”.

Godiya sosai Hajiya Talatu sukayiwa bokan kafin ta aje Masa bandir din 1k suka tafi a hanya Kulthum sai farinciki take Gidan Kawar Hajiya suka sauka rungumeta tayi ta ce “Nagode nagode Aunty kedin Yar uwace da kowa zaiyi alfaharinki kina sonmu Aunty kina son farincikinmu,kin kula damu,”Hajiya Talatu ta ce “To idan banyi muku ba wazanyiwa Umma,Ina da wasune bayanku ,Karki Manta mu ukku iyayenmu suka Haifa har Allah yayi musu rasuwa to akanme bazan maye muku gurbin iyayenmu ba keda Haidar kukenan garan kamar yanda Allah ya daukakani da Auren daukakken miji to haka kema nake maki fatan kiyi Auren hutawa da kece sa’a Ni nayi Miki alkawarin Auta Indai ina Raye saikin Auri Anwar ,sai kinzama matar sarki kamar yanda nazama”ta karasa fad’a Tana sakin shu’umun murmushi kafin ta ce “Hajiya Aisha Wasa Farin girki”.,

 

 

_____Gajiya da Tafiya Sabren tayi Hakan yasa ta sanyawa mom Kuka ta tubure Mata kamar ta satota Sosai mom tahau lallashinta Amma kamar zugata Ake har suka Isa gidansu kuka take Mata Saida suka Isa kafin su fito tana makale jikinta kamar za’a saceta Suka Isa cikin Gidan irin na Manyan masu Hali Kallon Gidan kakannin nata tayi ta wani turo Baki Kai tsaye babban Palourn Gidan suka nufa.

Maman Mom Bak’ar dattijuwa Bata wani tsufa Sosai ba a Ido Kasancewar hutu da take samu cikin Fara a da Tsantsar murna ta Fara Cewa “Lale marhaban oyoyo mutanen yola ne a Gidan namu sannunku da zuwa ,Amina Zuwan bazata haka ,Gaskiya kinyi mana bazata badai Kubra ce ta girma haka ba,.

Ta karasa fad’a Tana kame Baki”Kallon mom Sabren tayi kamar ta fashe da kuka ta ce “mom Ji tsohuwarchan nace Mani kubra saikace wata Yar kauye ni ba suna na Kubra ba suna na Sabren “.

ta karasa fad’a Tana murguda Baki”Harararta mom tayi kafin Hajja tayi Dariya ta ce “ikon Allah Y’ar Nan Taki Tana Nan dai Bata sauya ba Amina”Murmushi mom tayi Tana dukursawa ta gaishe da mahaifyartata cikin girmamawa,.

kafin kace me an cika musu gabansu da abubuwan ciye ciye Sabren ko duk ta gaji jikin mom ta shige ta kwanta har bacci ya kwasheta kowa kannen mom da yaransu suka shigo saisunyi mamakin girman Sabren Dan rabonsu da ita tun Tana 8years ,.

Washegari suna zaune a Palour sabren duk Taki sakewa da mutanen Gidan tana like da mom Sai mitar Taki sakin jiki da mutane take Mata ita ko hankalinta gabaki daya Yana wajen Friends din wasanta gashi gaba Daya babu wasu Yara gidan ita da ko yaro NE ma ta sama da sauki”Shigowar Hajiya Aisha NE ya Sanya Mom Mik’ewa Tare da tarbar juna cikin fara’a da dokin ganin juna Kallon Sabren dake ta harhade Rai Mamy tayi tare da ware idanu ta ce.

“Wa nake gani haka kamar y’ata “Sai sannan Sabren tayi Dariya tun sanda sukazo ta ce “Maman katsina kinzama tsohuwa Ni harna ganeki ke Baki gane niba”ta karasa fad’a Tana Dariya”Dariya Mamy tayi tare da ware Mata Hannu da gudu ta fad’a jikinta Tana murna”Kame Baki Hajja tayi tayi ta ce.

“Watau mu duk rainamune tayi Kenan”Dariya mom kawaii tayi”surutu Sosai Sabren ta dinga yiwa Maman katsina yayinda itama ke biyeta Saifa wajen Tafiya ne mama ta ce “Muje ki kwana gidana kiga Yan uwanki suma suna son ganinki “Hakan ya sanyata make kaf’ad’a ta ce “umm umm mama Ni bazanje Gidan sarki ba wannan dogoran su dakeni “bazasuyi Miki komai ba daughter tare kike Dani fa”Duk yanda Mamy taso tafiya da Sabren kiyawa tayi.

Kwanansu hudu yau a katsina wanda Sabren jinta Take kamar a k’aya,yau ta fito farfajiyar Gidan daga Ita sai Riga da Wando sai hular da ko Rabin gashinta bata rufe ba irin ta yaran nan,kallle kalle kawaii take har ta samu ta fita daga farfajiyar gidan duk leken da zatayi tayi amma ba kowa tsaki taja ta koma ciki ga haushinta na manto wayarta da tayi a gida ,Tana komawa ta kalli mom ta ce .

“Mom ki bani Dubu Biyu Dan Allah”me zakiyi da Dubu biyu”Wani abune Zan saya a k’ofar gida Dan Allah mom”Shine har na Dubu biyu ,to bazan bayar ba tafi kibani waje Uwar cin kud’i”Fashewa da kuka tayi tare da Fara diddira kafa Tana ihu ta ce.

“Allah saikin bani ko ki kiramun dad yazo ya daukeni Ni banason garin Nan naku ki bani kudina,ai dad yace yabaki kudi kome nakeso ki dinga bani shine kike cinyemun bakya bani wallahi saikin bani kudina”.

“Maman katsina da shigowarta Kenan Kame Baki tayi Mom ko duk ruwa ya cinyeta wannan Yana daga babban dalilin da yasa Bata son yawo da sabren koya saita kunyatata ,Shakota mom tayi za taci ubanta maman katsina ta amsheta tare da Girgiza Mata Kai ta na rungume da Sabren ta ce.

“Meye haka Zaki wani daketa Ai duk laifinkune tun farko”Kafin ta zage Jakarta ta dauko 2k din ta bata ta ce Amshi jeki sayo kardai ki wuce ko ina Yanzu Yanzu ki dawo”Lokaci guda tabar kukan tare da sakin murmushi ta ce “Nagode maman katsina Kafin ta juya tayiwa mom gwalo ta wuce a guje.,

Hajja ce ta ce”Daman Amina Baku bar sangarta yarinyar Nan ba,macece fa Yar Gidan wani Sannan Koba mutuwa da rabuwa Yanzu fisabillahi asa halin rayuwa waye zai iya Zama da yaarinyar Nan idan Babu ku,kudinma da kuka haifeta kunja batajin maganarku ina Ga wani, fisabillahi wa kike tunanin zai iya lankwasa yarinyar Nan ta lankwasu ,Ina amfanin haka Dan Tana ita D’aya Allah ya mallaka muku Kuma saiku sakartata”.

,Fad’a Sosai Hajja ta shigayiwa mom Wanda k’ala batace ba saboda Kota fad’a musu Dad dinta ne kadai ya sangartata ba yarda suke ba sunfi Bata laifi har Hajja ta Gama fadanta ta Mike tabar musu Palourn.

,maman katsina na ganin tashin Hajja ya sa ta koma kujerar da Mom take tare da kamo hannunta ta ce.

“Daman Ina son muyi magana dake Amina wai meke damunki naga kin rame ,kamar Baki cikin walwala tun wancen Zuwan naki na fahimci Haka Amma Yanzu na tabbatar da Tabbas akwai Abunda ke damunki idan Baki fadamun Abunda ke damunki Ba Ni Yar uwarki kuma wacce tamu tafi zuwa D’aya wazaki fad’awa Amina Dan Allah meke damunki ko ina da Shawarar da Zan Baki”.

Numfashi mom taja Harga Allah ta shirya fad’awa yayartata abunda ke damunta ko ta taimaka Mata da wata shawarar………Sosai Maman katsina tayi mamakin al’amarin Nan ace Shekara Har Biyu ,Sosai tashiga kogin tunani to me Hakan yake nufi kafin ta ce “to meyasa sai kuna tare Take Cewa ana tsorataka din?nifa ban yarda da ana tsoratataba Aunty kawai nafi daukar Hakan a shakiyanci ta ne”,.

Girgiza mata Kai tayi ta ce “Ba Haka Bane Amina Da chan meyasa Bata tab,a Cewa an tsoratataba sai Lokacin,sannan ki kula da maganar da Kika fadamun na sumar da tayi bayan Kun barota Gidan Kawar Taki nanma akwai alamar tambaya,Shiru mom tayi tana nazari Tabbas kuma hakane to me Hakan ke nufi?ta tambayi kanta”Gaskiya akwai magana,,!Mamy ta fad’a tana shiga kogin nazari..

___Sabren Tana fita daga Gidan ta Fara waigen inda zata samu adaidaita harta samu Kallon Mai adaidaitan tayi ta ce .

“Kasan inda Ake Shan Ice cream anan garin me Dadi?Eh na sani Akwai Lady m Shi yafi kusa da Nan”okay chan zaka kaini “ta fada Tana hayewa har suka Isa Tana kalle kallen gari suna Isa ya tabbatar Mata da sun iso wajen .
Kallon wajen tayi kafin ta fito ta ce “To nawa Zan baka”200 ya fada “Dubu ta bashi ya Bata chanji kafin ta shige robar ice cream na 1k ta hada da meat pie zaunawa tayi Kan chairs ita daya ta Fara ciye ciyen ta ta kalli wannan ta kalli wancen masu shige da fice.,

Harta kusa Gama Sha nanfa hankalinta Yayi gida Gashi babban tashin hankalinta na batasan sunan unguwar su Mom ba bare ta tari adaidaita tace ga Inda sai kaita sosai ta Fara muzurai duk Wanda suka shigo su fita har magriba masu wajen dai basuce da ita kala ba ganin duhun magriba ya Fara ya sanyata Fara hawaye Ta sadda kanta tana kuka.

Bangaren mom ba k’aramun Tashi Hankalinsu Yayi ba musamman Maman Katsina ko gida Bata koma ba wasa wasa magriba isha’i ba Sabren ba labarinta Gaba daya unguwar ba inda ba ajeba Amma Bata Nan hankalin su gaba daya Yayi mugun tashi musamman mom Kadan ya Hana Bata fashe da kuka ba ta ce “yarinyar Nan karta jamun masifa ta bace na shiga ukku Daman nasan yawo zata tafi yasa na hanata kudin Nan Ina ta sani a garin Nan “.

____ lura da ita ya sanya ma aikatan wajen nufar wajenta suna tambayarta Lafiya take kuka Kuma tun dazu Taki Tafiya.

“Kuka ta Kara Fashewa dashi ta ce “Nima bansan Gidan mu ba”Kamarya bakisan gidanku ba to wa ya kawoki?nina kawo kaina Amma bansan inda Zan koma ba ”

ta karasa fada Tana rushewa da Kuka Duk tambayar duniyar Nan sunyi Mata Amma bata Basu amsa ba ,sai Kuka take a jikin wata arniya Sama sama Taji shigowar wani wajen gaba daya Taji ma aikatan wajen sun b’ige da gaisheshi cikin girmamawa dagowar da zatayi ko ‘karewa saurayin kallo batayi ba ta saki arniyar ta ruga wajenshi ta baya ta makalkaleshi tare da Fashewa da Kuka ta ce.

 

“Yaya shine ka tafi ka barni “Mamaki ne ya Gama cika Anwar shi kuma Ina yasan wanna yarinyar da zata makalkaleshi har Tana kiranshi da Yaya,kafin Yayi magana d’aya daga cikin ma aikatan ta ce “Sorry ranka ya Dade ai bamuyi tunanin sister ka bace Bata sanar Mana ba ce Mana kawaii tayi ta bace”.

 

“Baice uffan ba sai kokarin ture Sabren yayi Kara makalkaleshi tayi Dan ba zata sakeshiba ya tafi ya barta zaune cikin arnan Nan da Bata sansu ba su Saida ita”.

“tsawar Daya daka Mata ce ya sanyata sakinshi ba shiri kamar ta fad’i k’asa saboda rud’u ganin Yayi hanyar fita Ne ya sanyata binshi da gudu Yana Shirin shiga lafceciyar motarshi ta riko rigarshi ta baya Lokaci guda ya juyo fuskarsa murtuke ya watsa Mata harara ya ce “me Zan Baki kike Bina sanina kikayi?

“Lokaci guda ta fashe da Kuka tare da Kara rike rigarshi ta baya sosai ta ce “Ni bansanka ba Amma Allah bazaka tafi ka barni ba a saceni Bansan kowa ba ”

“Mamaki gaba daya ya Gama cika Anwar Karewa karamar yarinyar kallo Yayi kafin yaja tsaki ya shiga da gudu ta zagaya ta bude wajen zaman banza ta shiga cikin sweet voice dinsa ya ce “Ke wai ina Zan kaiki Zaki shigomun mota haka kawaii Bansankiba”?

turo Baki gaba tayi cikin shagwaba ta ce “To Gidan da nazo zaka kaini Mana Ni bansan gidan ba?da zakizo Nina kawoki?

“a a a bakai ka kawoni ba Amma Kai zaka maidani “ta Fad’a Ta na turo Baki”Shi tsawon Rayuwar Anwar baitaba ga ikon Allah irin haka ba ya lura yarinyar matsala take Neman bashi “meye sunan unguwar?.

Ya jefo Mata tambayar”jujjuya idanu tayi kamar zatayi tunani kafin ta juyo ta kalleshi Tana kwabe fuska ta ce.

“Nima bansan sunan unguwar ba katsina ne dai saika tambaya kace Gidan su Mom d’ina ko Kuma kace Gidan su Maman Katsina kayi sauri Dan Allah Yaya Choculate Nasan mom Dita nachan Nata nemana please yawwa kuma sunan maman mom din tawa Hajja,sunan Baban Nata Ne ma na manta Naji ance ya mutu Da dadewa……..✍️

*Tofa sabren wannan kwatance haka dalla_dalla*😛

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

 

“`MALLAKAR“`

 

*HAJARA L SADEQ*

 

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

 

🅿️………….*15 & 16*

 

“Saida bayanin nata ya so bawa Anwar dariya ya fusge ya ce”waye zai gane kwatancen Nan naki,,ki fad’amun yanda Zan gane kina batamun time”.

Shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka ta ce “To nima Bansan sunan unguwarba Yaya beauty Amma muje zangane bi hanyar chan ta fad’a ta na nuna Masa bayansu”

Duk yanda Anwar yaso fisgewa Saida ya danyi murmushi sosai yanayin yarinyar da yanda take magana ya basa Dariya ,kafin yabi hanyar da ta fad’a ,.

Hanyoyi ya dinga bi da ita sai sunyi nisa ta ce ba Nan bane a sauya sosai Anwar ya Fara gajiya ya lura shiriritar dashi yarinyar keson yi Parking Yayi tare da juyowa ya kalleta fuska ba wasa ya ce.

“Saukarmun a Mota tunda bakisan Inda zakiba Ina da aikinyine.”Sabren najin haka ta fashe da kuka tare da Fara Masa diddire_diddiren kafarta a Mota Tana kukan sangarta ta ce.

” Allah bazan saukaba saika maidani gidanmu so Kake a saceni a yankani ayiwa mom Dina da dad asara nidai saika kaini gida”.

sakato Anwar Ya yi Ya na Kallon ikon Allah ,Ya na ganin sangartattun Yara Amma tunda yake bai taba ga Mai sangartar wannan yarinyar ba tsaki Yaja a ranshi Dan ya tsani yaga Yara na sangarta”To Ni sani na kikayi,idan fa nidinma D’an yankan Kaine haka kawai kin makalemun to Bari na kaiki wajen yankan Kan ba shikenanba”

Ta tsinkayi muryarshi Lokaci guda ta hadiye kukan kallonshi tayi sosai ta Kare Masa kallo kafin ta turo Baki gaba ta ce.

“Ai nasan Kai ba D’an yankan Kai bane bakayi Kama dasu ba “ohh Daman har Kama garesu”ya Fada Yana tada Mota ya bi wata hanyar ko Allah zaisa a dace”Eh Mana Ni ai Dana gansu Ina ganesu “.

shiru Yayi Mata Jin hakan ya sanyata itama yin shirun”tsit motar ta dauka bakajin Komai sai sautin Gidan radio kallonshi ta dingayi haka kawai saita dinga ganin Yana yanayi da mom d’inta musamman idanunsa chocolate skin dinsa kasayin shiru tayi a hankali ta ce “.

“Yaya Beauty kaima D’an Nan garin Ne?Eh”ya Bata Amsa a takaice”To Kai inane gidanku?”duniyar sama”ya sake Bata amsa”kenan Yanzu Samar zaka koma?”Eh ko kina zuwa?Mak’e kaf’ad’a tayi ta ce “Umm umm injema ko Kai aljani ne “ya sunan mamanka wlh kanamun yanayi da mom d’ita ?

 

ta Kara jefo Masa tambaya”Dan tsaki yaja ya ce “kin fiya surutu parrot “harara ta galla Masa Tere da juya Dara daran idanuwanta “daidai ya juyo wara idanu yayi ya ce”Ni kike harara”Kauda Kai gefe tayi ta ce “Ni bada Kai nake ba “cigaba yayi da driving dinsa Daidai zai gitta ta wajen wasu masu gashin kaza idonta ya Kai wajen cikin d’aga murya ta ce.

 

“”wayyo Yaya Beauty Dan Allah kaza ka sayamun “ganin Yana Shirin wucewa ya sanyata rirriko hannunsa Kadan ya Hana ta chaza musu accident ba shiri ya taka birki cikin d’aga murya ya ce “Waike Baki da da hankali,da Kika kadamu fa”ya Fada Yana sakar mata Tsawa “Kuka ta fashe dashi kamar ya daketa ta ce “To ba Saida nace ka tsaya ka sayamun kaza ba”tsaki yaja ya ce.

“ba a saya Ajiyar kud’in Kika bani,wlh idan bakiyi wasa ba Zan saukeki a tsohon Daren Nan daga haduwa dake kin likemun saikace na had’a dangi dake Duk kin chazamun Kai sai gararamba kike sanyani inayi a gari”.

“cikin shagwaba ta ce “To Daman nace Kai danginane mema zai had’ani dakai Had’uwar joint kawai Ni ka saimun kazar bashi idan mukaje ba biyanka zanyi ba daga Rance ai ba kyauta nace ka sayamun ba?.

“,Oh haka kikace to bazan ranta ba Kuma daga wajen Nan indai har Baki gano Gidanku ba Zan saukeki ki nema ke kadai”naji Yaya Beauty wlh indai ka saimun kazar sannan Zan gano Gidan sannan ma Rance Ne zakaban da munje gida Zan amsa wajen Mom d’ina na baka”.

Banza Anwar yayi Mata Tare da fita ba ayi minti ukku ba ya dawo tare da leda batare da ya kalleta ba ya aje Mata Kan Cinya cike da murna ta ce.

“Thnks Yaya Beauty”cigaba da driving yayi ya nufi wata hanyar ko Allah zaisa a dace Yana tuna sunan da ta lakaba Masa Yaya beauty ko gidanwa ya Zama yayanta in Banda kawaii macece idan Ya sauketa baisan wani Hannu zata fad’a ba da tuni ya sauketa shawara ya Yanke in har Bata gano ba gidan ganin 11pm harta wuce gwara kawai ya kaita Gidan Radio.

Sabren bude kazarta tayi tahau ci sosai naman yayi Mata dadi har wani lumshe Ido take ta gefen Ido Anwar ya kalleta ya GirGiza Kai Yana jinjina wautar yarinyar kawai batasanshi ba ta makale masa to da ace shidin mugu Ne fa ya tabbata da Bata fada hannu ba gari ba da komai zai iya faruwa,.

Tana cikin ci taga zasu wuce wajen da ake Saida Fruits da juice marairaicewa tayi ta na kallonshi ta ce “Uhm Yaya beauty Dan Allah ga fruits Nan ka sake rantamun sai ayi lissafi”wata harara ya banka Mata ganin haka ya sanyata Fashewa da kuka ta Fara diddira kafa “tsaki yaja baisan Lokacin da ya sakar Mata tsawa ba Wanda haka ya Kara rudar da ita ta Kara Fashewa da kuka “.

.OMG ya Fada Yana dafe saitin kansa tare da duba agogo yaga karfe Sha Biyu saura tsaki yaja ya fita ya sayo Mata tare da cilla Mata cikin sauri ta amshe tare da aje naman kazar fakar idonsa tayi tare da yi Masa gwalo,tunani yayi kawai gwara ya kaita Gidan radio Dan ya gaji da gararanba da ita a gari karta jaza Masa masifa,wani tunani ne ya fad’o Masa kallonta yayi ya ce “Baki da number wani naki da kika hardace a Kira”.?

Tana Shan gwanda ta ce “umm na haddace ta mom” ta Fada muryarta Bata ma fita sosai sakamakon cika Mata Baki gwanda da tayi,”.

“Daman kinsan Akwai number a kanki kikayi ta sanyani gararanba sai kace kin samu driver”mancewa nayi fa Yaya beauty “ta Fada hankalinta kwance tuni damuwarta ta gushe tunda ta samu abunda takeso”karki Kara cemun wani Yaya beauty “ya Fada Yana Had’e girar sama da ta kasa tare da Mika Mata wayarsa ya ce Sanya ki Kira ki tambayeta unguwar”.

Amsa tayi ta Sanya numbobin mom ringing biyu mom ta daga lokacin ta gaji da kuka Dan har Gidan radio an tafi badawa cigiyarta “Hello mom baby ce “Lokaci guda mom ta zabura ta Mike ta ce “Baby Ina kikaje ,kika tayarmana da hankali kina Ina”Bata bawa mom amsa ba sai Cewa tayi “Ya sunan unguwarku mom”Cikin sauri mom ta ce “Layout”layout”ta Fada Masa Masa kafin ta katse wayar ta goge number mom ta Mika masa.

Cigaba da ciye ciyenta tayi har batasan sunzo unguwarba ,kina iya gane gidan Yanzu ko sai an kirata tunda na Kula kwalwar Taki chunkushe take bakya ganewa daga gani ko a class”Harara Sabren ta balla Masa tare da turo Baki gaba wara idanu yayi Yana nuna kanshi ya ce.
“Ni”?
To menayi a cikin Daren Nan harma idonka yagane maka”

ta Fada Tana turo Baki tare da karewa unguwar kallo Kasancewar akwai hasken glove ya sanyata gano k’ofar Gidan su Mom wata Nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke gabanta ne ya fad’i tuno bashin da taci na uban sayayyar da yayi Mata kayanta ta Had’e a leda guda Tare da bude murfin motar ta fita da gudu kafin ta juyo da karfi ta ce.

“Yaya beauty Daman wayau nayi maka naci banza ,na koshi,sannan kayi yawo Dani a gari Daman so nake Naga gari kuma Kayimun sayayya da kudinka nagode saimun had’u a lahira Dan bazaka Kara gani na ba har abada ba garin nake ba “Tana Gama fadar haka ta Kara kwasawa a guje.

Anwar ya rasa Dariya zaiyi ko haushi ,baitaba haduwa da wacce tayi wasa da hankakinshi ba irin wannan yarinyar babban haushinshi na dagangan ta Bari ya dinga yawo da ita,Wanda baisan ta fada Masa ne kawaii saboda tsabar shakiyanci,sannan maganarta ta taci banza ita ma taso bashi Dariya ga haushin shi na ashe layin su Hajja ne ma tun farko Rashin sani juya Kan motarshi yayi Ya wuce Kai tsaye spare Gidansa Dan baya shiga cikin masarauta muddin dare yayi.

Sosai mom sukayi mamakin ganin Sabren Ita hankalinta kwance Su kuma gaba Daya ta tayar musu da hankali Dan maman katsina ko gida Bata tafi ba koda suka tambayeta Bata boye musu komai ba sosai maman katsina ta Kara jinjina wautar da rashin ji irin na Sabren kawai ta makalewa wani batasanshiba danma Allah ya taimaka mutumin kirki ne da ta hadu da na banza ya lalata Mata rayuwa fa Fada sosai maman katsina tayi Mata akan yawo,da Kuma yarda da wadanda Bata saniba kafin mom ta Dora nata Tana ganin haka ta shigewarta daki ta kwanta ta jima Tana dariyar wayan da tayiwa mutumin Nan yayi Mata sayayya Tana ta Dariya har bacci yayi awon gaba da ita.

 

Washegari Anwar ya wuce Lagos wajen aikinsa bayan yasamu Sanya albarka daga wajen iyayensa Bangaren hajiya talatu ko bataso hakan ya faru ba saboda Akwai maganin da Boka ya Bata akan tilas ya cisa a abinci kafin mako guda maganin zai daina aiki to gashinan Kuma ya tafi Dan ko bankwana baije yayi Mata ba sai text yayi Mata saboda Kiran gaggawa Daya samu daga wajen aikinsa.

Mom rage kwanakin da zasuyi tayi Dan ba k’aramun tsorata tayi da b’atan Sabren ba tasan ba saduda take ba hakan yasa kwanansu shida ko gidan Yan uwanta Bata zagaya ba tayi musu bankwana driver’ da Daman Yana Nan ya wuce dasu Wanda murna wajen Sabren har baka suna Isa gida ko ciki bata shige ba ta ruga Gidan su Affan sosai suka hau murnar ganin Juna suna rungume juna Affan Yana Fada Mata yanda yayi missing d’inta Shi ya rakota har gida bayan yayiwa mom Sannu da zuwa dashi ya Taya mom ta gyara Gidan da ya danyi datti abun Tafiya da sukayi Dan Sabren Cewa tayi ta gaji.

Wannan karinma da dad yazo satinshi biyu haka yakoma ba abunda ya shiga tsakaninsu da matar tasa sai Dan wasanni Dan Sabren ta k’asa ta tsare babu ta yanda zasu kebe sannan ko bacci take indai sukayi niyyar wani Abu sai ta farka cikin satin Ne mom ta Fara rashin lafiyar zazzabi da ciwon ciki.

Yauma kwance take sosai ciwon cikin nata ya matsa Mata gashi Taki fad’awa dad Sabren da ta hado Mata tea ta zauna gefenta cike da kulawa ta rungumota ta tadata zaune ta ce

 

“Sannu mom ga tea din “GirGiza Mata Kai tayi Ta ce “jira ya Dan lafa”Aje tea din tayi ta ce “Wai mom ciwon cikin me kike kwana biyun Nan sannan jikin kima da zafi fa ko dai ciki gareki kani zakiyimun Daman Ina sane tun ina karama idan nace kiyimun Kane kikecewa zakimun Allahsa Kanin ne zakimun mom shine ko?”

“Saida ciwon cikin ya lafa mom ta Gama had’a zufa kafin ta dauki ruwan tea din Tasha “Kwabe fuska Sabren tayi ta ce “Mom Baki bani Amsa ba “Dan Allah yimun shiru Sabren please banason surutu”.cewar mom.

“Sannu to?yawwa Baby”momy Saura wata nawa ki haihun Dan na Fara shirya dinner da zamuyi da friends dina”dafe Kai mom tayi ta ce “Zaki dameni baby cemiki nayi haihuwa zanyi”turo Baki gaba tayi ta ce”Ai nasani Mana bakyason ki fadane Kuma Bari naje nayiwa dad albishir ta Fada Tana rugawa tare da janyo wayarta Ta dannawa dad Kira.

Yana Dauka cikin d’oki ta ce “Dad Albishirin ka”Goro babyn dad”Mom nada ciki zata haifamun k’ani “Wara idanu dad yayi sosai cike da farinciki ya ce “da gaske baby wannan babban albishir ai kin chanchanci tukuici Mai tsoka Ina mom din Taki maza Kai Mata wayar ‘”Tana Dariya ta ce.

“Ai dad tukuicina kawai shine ka kaini Dubai da England da Paris tare da India mu hadu da aditi sharma saboda ita ce best actress d’ita “ta Fada Tana mikawa mom wayar daga Bangaren dad ya ce “Sweetheart Daman Akwai wannan babban albishir din Baki fad’amun ba ,wannan abun farinciki haka”.

“Mom ji tayi kamar me wani gamin saita rasa Wanda yafi wani tsakanin sabren da dad “Hmmmmm ya wajen aikin”.

kawai tace “Kamarya hmm ya Zaki chanza magana please wata nawa,kinje hospital an dubamun lafiyarki kuwa?waiko baka karya ba dadyn Sabren Kai Yanzu ko ce maka akayi Ina da ciki saika yarda ,ana haihuwa ba mahaifa Daman?Sannan kodai a Ruwa akeshan cikin ban sani ba kamanta shekara biyu da wani abu rabona dakai?”.

Lokaci guda murnar dad ta koma ciki A sanyaye ya ce”sorry na Manta hakane sweetheart Gaskiya Nima Hakuri na yazo karshe Jibi ki shirya tarbar mijinki Ina Nan zuwa jibi saimu shirya yanda zamuyi da daughter”.

Sosai mom Taji wani Dadi a ranta suna Gama waya da dad ta mikawa sabren wayarta.

kamar yanda dad ya Fada ranar ya dawo Sabren da mom sosai sukaci kwalliyarsu kamar ko yaushe idan zai dawo an shirya Masa lafiyayyun abinciccika Sabren na lik’e jikinsa Tana da dokin ganinsa Yana shafa kanta suna ta hirar y’a da uba mummy tayi serving dinsu wanda a Baki ya dinga feeding din Sabren harta Koshi kafin itama tayi feeding dinshi mom ce ta ce.

“Nima ban yarda ba to oya ayi feeding Dina “Dariya sukayi Sabren ta ce “To Mom Bari mijinki yayi feeding dinki”.

dakuwa mom tayi Mata yayinda dad da ita suka sa Dariya cikin farinciki suka Gama dinner dinsu kafin Dad ya kalli agogo Karfe Tara na dare ya gani da Ido yayiwa mom sign ta ankare Kallon Sabren tayi ta ce.

“Babyna Muje na kaiki Gidan Su Affan Samira tayi maki kitso saiki kwana a chan”Jin zata kwana gidansu affan ya sanyata murna haada tsalle ta ce.

“To mom muje”Ajiyar zuciya mom ta sauke har dad dad ya ce Bari na rakata ke zauna “Dad ya rakata har gidansu Affan kafiin yayi hug d’inta tayi mishi bye bye tare da Saida safe ta shige cikin Gidansu Affan .

Affan shine matsayin sallamarta Tana shiga suka Taba ta ce “Albishirka besty yau gidanku Zan kwana zamu jima muna game a tab yau saina gwada maka kwarewata “Dariya yayi ya ce.

“Wayarki dai Akwai charge ko “Ehmana tun safe na cikata “Maman su Affan ce ta ce “Au ba kitson da mamanki tace a Miki ba zakiyi ba kenan ta game ma kike”Dariya tayi ta ce “Mama kitso da Daren Nan saidai gobe Tana Gama fadar haka taja hannun Affan suka zauna a k’asa suka Fara buga game Hankalinsu kwance ,girgiza Kai mamansu Affan tayi Tana jinjina wannan kawancen tun yarinta zataga ranar da aure zai raba tasan dai ansha kuka.,

 

Kashe wayoyinsu mom sukayi saboda gudun wata matsala……bayan komai ya lafa kamar sarar mom Koda yaushe Bata kwanciya ba tsarki wanka ta maza taje tayi tare da dauro alwala dad ko Wani baccin dadine da ya Jima baiyi irinsa ba ya kwashesa ba irin yanda mom bata tasheshiba Akan ko alwala ce ya Tashi yayi Amma ya k’iya haka dai ta hakura suka kwance like da juna.

Bangaren Sabren harsun kwanta karfe Sha Daya ita da samira Taji ta kurma wani uban ihu yayyun affan manya Dakyal suka rirriketa zabura kawaii take Tana wasu maganganu da basusanma wani yare ne ba gashin kanta gabaki d’aya ya warware zabura take sosai Tana neman fusgewa mamansu affan da Ihun ya tasheta da ita aka hadu aka dinga tofa Mata adduoi tare da Sanya Karatun alkur’ani wani irin gunjin kuka take Tana jujjuya Kai Tana hawaye adduoi sosai aka shiga tofa Mata Dakyal suka samu wajen 1:00am abun ya lafa ta Fara sauke ajiyar zuciya kafin ta lafe jikin Maman Affan ta koma bacci kamar ba itace ta Gama fisge fisgen Nan ba”.

____Da wani irin masifaffen zazzabi Mai zafin gaske dad ya Tashi Gaba Daya hankalin mom Duk ya Tashi baitaba ciwon da ya hanashi yin sallar asuba ba sai wannan sosai jikinshi yad’au kerma,Yana kakkarwa ya ce.

“Rufamun bargo Amina sanyi nakeji,”Hankali tashe mom ta ce”To Dadyn sabren please ka Tashi Muje asibiti “Ki Rufamun zan samu sauki “Tana rufa Mai ya Kara cewa ta rufa Masa wani Saida ta rufa Masa bargo har ukku chan Cikin muryarshi da Bata fita ya ce “yayemun bargon Nan Amina zafi nakeji har Cikin Kashi na ji nake kamar ana huramun wuta a Cikin jikina zafi Aminaaaaa”ya fadada Cikin dauriya Yana Jan Aminaaaaa da karfi”.

Iya rikicewa mom ta rude batasan sanda ta fashe da wani irin kuka ba ta ce “innalillahi wa Inna ilaihiraji’un meke faruwa dakai Mustapha?………✍️

*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_ 🤙
[12/9, 9:17 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

 

“`MALLAKAR“`

 

*HAJARA L SADEQ*

 

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

 

 

🅿️……….*17 & 18*

 

Dad bai iya bata amsa ba sakamakon gushewar da hankakinsa ya fara saboda tsananin azabar da yakeji Gaba d’aya mom ta rikice a matukar rudewa ta Haye gadon tare da tallaboshi Taji jikinshi zafi rauuuu kamar wuta “sunanshi kawai take Kira Tana jijjigashi saikuma ta fada jikinshi ta fashe da matsanancin kuka.,

Tunda Sabren ta Tashi takejinta sai a slow fir tak’iya ta karya ita gida takeso Ba yanda Maman Affan ta iya sai rabuwa tayi da ita ta wuce gida a ranta Tana nazarin Daman sabren nada iskokokai kuwa?iyayenta sun sani kokuwa?.

Ba k’aramun Tashi Hankalin Sabren yayiba a yanda ta tarar da iyayennan nata Bata ta’ba ga kukan mom irin haka ba ga dad a sume jikinta “wani k’ara ta fasa Wanda shiya dawo da mom hankalinta da gudu ta ruga tare da rungumo dad ta fashe da kuka ta ce “Mom what happened to my dad mom meyasamu dad Dina jikinsa kamar wuta “.

Sai sannan mom ta lura da dad a sume yake Dan numfashi ne kawai zai tabbar da Yana Raye “Dakyal mom ta iya jarumtar mik’ewa ta janyo wayarta Cikin sauri,rasa Wanda zata kirama tayi aje wayar tayi tare da janyo gyalenta a rude. Ta ce “Taimakamun Mu kaishi asibiti baby bar kukan zai samu lafiya yi sauri “Sabren da ta Mak’alk’ale dad Ta na kuka ta ce “To mom Dan Allah mom Kar dad Dina ya mutu Nima mutuwa zanyi mom Ina sonshi sosai karki Bari mu rasashi”.

Ta karasa fada Cikin wani irin kuka da tunda take Bata Tab’a irinshi ba da taimakon get man aka saka dad Mota mom tayi driving dinsu Basu zarce ko Ina ba Sai FMC Fedaral Medical center har suka Isa hospital din Sabren kuka take mom ko tashin hankalinta da take ciki Baya musaltuwa da komai mijinta mafi soyuwa a ranta uban yarta Kuma babban masoyinta Cikin halin mutuwa ko rayuwa Idan tatuna irin soyayyar da sukayi da dad saita fashe da kuka ba addu’ar da take in Banda Allah ya Tashi kafadunshi.

Emergency aka nufa dashi Sabren rungume mom tayi ta na kuka Mom Bata iya lallashinta ba sai kukan ita ma take,basuyi tunanin Kiran kowaba saboda Gaba Daya kansu ya fasu Wasa wasa Tun safe likitoci suke Kan dad Duk wani gwaji da za ayi Masa anyi Masa Amma basu ga Komai ba game da abunda ke damunshi Gado suka bashi tare da bashi Yan taimakon da ba a rasa ba,bayanin Dr yayiwa mom Akan basuga abunda ke damunshi ba Amma Sun kwantar dasu za a cigaba da gwaje gwaje har Allah yasa a dace da ganin ciwon.,

Yinin ranar asibiti suka yini cikinsu ba Wanda ya iya Shan ko ruwa Sabren ko kuka kawai take gwarama yanzu mom ta dake Tana lallashinta,Around 8 suna zaune sunyi jugum Sabren na gadon da Dad yake Mom na Kan kujera tayi tagumi,Cikin kuka Sabren ta kalli mom ta ce.

“Mom yaki Tashi har Yanzu please kice ya Tashi Ina son magana dashi mom “Bata iya Bata amsa ba sai hawaye kawai take ganin haka ya Sanya Sabren Fashewa da kuka ta fada jikin dad “Sai Lokacin mom ta iya daga Baki Cikin muryarta da ta gaji da kuka ta ce.

“Ki daina Hawa kansa kina Masa kuka baby zaiji sauki insha Allah ki dinga tofa Masa Addua sannan ki Tashi muyi salla mu roki Allah Shi kadaine zaiyi Mana maganin damuwarmu”Cikin sauri ta ce “To mom “tare sukayi Salla sun Jima suna Addu’ar Allah yabawa Dad lafiya kafin mom ta janyo wayarta “Mom wazaki Kira?cewar Sabren”Su Baba Zan Kira Nafada musu halin da Ake ciki?Bata Rai tayi sosai ta ce.

“Mom karki Kirasu Ni banason ganinsu,banason su da dad d’ina Allah ko kin Kirasu saina koresu”?Saboda me baby me yasa Wai bakya son Su baba bayan kinsan dai yayace wajen kakanki kuma kusan ita ta Riki Babanki tun bayan rasuwar iyayensu matsayin kakarki take Sarai kinsan da Haka Meyasa wai bakison dangin babanki?Ni ba kakata bace Allah kiyaye tazama kakata ,Maman Dad ta rasu tun Yana yaro yabani Labari bayan Nan mahaifinsa ya rasu Taya ta Zama kakata “.

Girgiza Kai kawai mom tayi tana dannawa mahaifiyarta Kira ta sanar da ita rashin lafiyar mijin nata Akan su tayasu da Addua sosai Hajjar mom ta rude ita kanta Jin Wai ba asan Kan ciwon ba.

Washegari mutane Duk sun Fara sanin halin rashin lafiyar dad sosai mutane ke tururuwar zuwa dubiya mom takira baba ta fada musu halin da ake ciki tun a Cikin wayar take kuka ba ayi ko awa guda ba sai gata Ta na kuka da shaftar majina Tana ganin dad ta fashe da kuka ta ce.

“Shikenan Na shiga ukku Ni lami D’ana Mai taimakona shine.a Cikin halin Nan?Na shiga ukku na lalace Shikenan asirina ya tonu Mustapha Kaine ci na kaina Sha na ,Kai NE suturata,kaine rufin asirina Dana y’ay’a na idan ka mutu Bansan wani Hali Zan shiga ba?.cike da masifa Sabren ta hayayyako ta ce .

“Kece dai Zaki mutu badai Dad Dina ba da Allah yiwa mutane shiru kinzo Kin ishi mutane da ihu Wama ya kawoki Asibitin Nan?tsawa mom ta daka Mata ta ce Zan B’ata Miki Rai baby dan Baki da kunya Babar kike fad’awa Haka “.

Baba ko Cewa tayi “Ba Cewa nayi zai mutu ba y’ar Nan Mutuwar Mustapha ai tonon asirina ce Kiyi Hakuri”Dogon tsaki Sabren taja tare da Kauda Kai tana ballawa Baba harara dake ta shafce majina “Sadiya ce ta shigo itama Da nata kalar haukan Zubewa tayi a k’asa Tana wani irin kuka ganin Masoyin nata da take da burin mallaka tun yarinta Cikin wani Hali batasan sanda Tafara sabbatu ba Tana cewa.

“Karka tafi ka barni Mustapha Dan Allah bakasan kalar son da nake maka ba ,nidin masoyiyarkace ta Hakika ,karka mutu ban cika Burina na aurenka ba “kafin ta fashe da wani irin kuka marar dadin sauraro ,ba Sabren ba hatta mom Saida ta firgita Jin kalaman Sadiya Ganin Tana Shirin yin gadon dad zata rungumoshi mom batasan sanda ta zabura ba Tare da zuwa ta bangaje sadiya Tana aika Mata da harara ta ce.

“Meye Haka fad’awa jikinshi zakiyi ko me?Sadiya Gaba daga hankalinta Baya gabanta Saida ta Tab’a wuyan dad Taji sanyi k’arai “wata irin zabura tayi ta ce “Amina Jikinsa ya fara zafi kafin yayi sanyi yanzu”Mamaki dauke da fuskar mom ta ce “Ya akayi Kika San jikinsa Ya Fara Zafi?”wayyo Allah na sadiya Innalillahi innalillahi”ta fada Tana Dora hannu a ka kafin ta fita daga d’akin a matukar rude gabaki d’aya da Kallon Mamaki suka bita “.

D’iyan BaBa magidanta maza biyu ne suka shiga Shamsu da Balarabe “Mom har Lokacin ta daskare a zaune Sabren ko Wani irin tafarfasa takeji zuciyarta nayi kamar zata tsage gida biyu a duniya idan da Wanda ta tsana Basu wuce su BaBa ba, Gaishe da mom sukayi Cikin ladabi tare da yi Mata ya Mai jiki “Suna yiwa Sabren magana Dakyal ta iya bude Baki tace “Sannunku”Baba ce ta ce “Ko gida kike zuwa ki Shirya Ki Dan huta’ Amina tunda gamu Kuma ga Yan uwansa sun kula dashi”.

Girgiza Kai Mom tayi ta ce “A a a baba Zan zauna Zan aika a dauko Mana abunda muke bukata “ganin baba Taki Tafiya NE ya Sanya Sabren Jan tsaki tare da Tashi tabar d’akin Gaba Daya ta koma waje ta zauna Kan chairs ta Had’e Kai da gwuiwa ta. Na hawaye.

Daren ranar mom ta Kira Uncle Ahmad don ta fada Masa halin da ake ciki Koda ta fada Masa Rashin lafiyar dad sosai ya nuna tashin hankalinshi tun a cikin wayar saidai yacewa mom Yanzu Haka yana Shirin b’arin kasar zuwa Australia wani muhimmin aiki Amma idan yadawo zaikira yaji halin da ake ciki”.

Washegari Y’an yola sukazo duba dad Ciki hada maman katsina da maman Mom da Kuma yayyu da kannan ta sosai sukaji dadin zuwansu kowa yazo Saiya tausayawa halin da dad yake ciki numfashine kawai zai tabbatar da Yana raye Dan abincima da ruwa ta na’urori ake basa gashi babban tashin hankalin har Yanzu an Gaza gano abunda ke damunsa.”.

Aunty sadiya ko tunda ta tafi basu Kara ganinta Asibitin ba ,sosai mom take kashe kud’i a hospital dinnan a aljihunta Gaba Daya harta rame Ga rashin cin abinci ga tashin hankali kwanansu Yan yola biyu Suka juya Banda Maman katsina da tace zata zauna Suyi jinyar Tare bazaiyu a bar y’ar uwarta ita kadaiba da wannan jinyar tunda Daman sunsan dangin dad ba wani kula dashi suke ba Abun hannunsa suke so sosai hakan yayiwa mom da Sabren Dadi Dan Koba Komai Tana kwantar musu da hankali itake tilasta musu da sai sunci abinci.

Daga Sabren sai mom Sai maman katsina a d’akin kallon Sabren maman katsina tayi ta ce “Baby bamu waje zamuyi magana”ba musu ta Mike Ta fita da wayarta a hannu”Kallon mom maman katsina tayi ta ce “Wai Meye farkon silar faruwan ciwon Nasa”Shiru mom tayi kafin tayi k’asa da kanta Ta ce.

“Daren dai ranar wani Abu ya shiga tsakaninmu to washegarin ranar ya Tashi da ciwon”nazari sosai maman katsina ta shigayi kafin ta ce “Khadija na Gidan Lokacin?a a a Bata kwana gida ba makotanmu ta kwana “Gaba Daya kan mama katsina ya kulle Tabbas Akwai lauje Cikin Nadi”ta fada Tana jinjina Kai”Lauje Kuma Aunty”Tabbas Kuma Kiyi nazari sosai “Kafin ta janyo wayarta ta ce..

“Bari na Kira Wani likitan Mai martaba a Abuja yake a sauya masa asibiti mukaishi asibitinshi mutumin Yana da zurfin ilimi sosae Sannan idan ba Maganin asibiti bane da kansa zai fad’a inason mu tabbatar da ainahin ciwon na gida Ne ko na asibiti”

“To Aunty nagode sosai Allah yabar zumunci”Mom ta fada “Magana Maman katsina tayi da likitan Mai martaba na Abuja washegari aka sauyawa Dad Asibiti aka mayar dashi na Abuja Gaba Daya suka tafi har mom da Sabren tare da maman katsina Kasancewar fly suka hau Duk wani gwaje gwaje Dr yayiwa Dad baiga Komai ba.

Kwanansa biyu ana Masa gwaje_gwaje Kanshi tsaye ya fada musu ba larurar asibiti bane.

sosai hankalinsu ya Kara tashi matuk’a ganin hakan ya sanyashi kwantar musu da hankali ta hanyar cewa.

“Ku kwantar da hankalinku Insha Allah zai samu sauki Zan muku hanyar wani asibitin musulunci mai suna “PRINCE MUHAMMAD BIN ABDULAZIZ MADINA HOSPITAL a kasar Saudi Arabia Shima asibitine da likitoci da Komai da Manyan malamai suna kwantar da mutum har tsawon Lokacin da zai samu lafiya ko shekara nawa kuma tare da majinyacinshi mutum D’aya ,Akwai mutane da dama da nayi musu hanya Kuma an dace saidai Akwai kishin kud’i sosai da sosai Dan Gaskiya a kalla mafi karanci ku tafi da ,20 millions,saboda ci shanku Sanan dakine za a Baku kamar hotel ba irin gadajen sauran asibitoci bane rayuwace zakiyi tamkar a Gidanku da Palour da toilet Sannan da masu kula daku idan Kuna da Hali Kuma Kuna da ra’ayi zanyi muku hanya Zan hadaku da Likitan dake aiki Asibitin”

“Cikin sauri mom ta ce “na Shirya Dr ko Yanzu indai mijina zai Samu lafiya kayi Mana hanyar Dan girman Allah”to shikenan Badamuwa zamuyi waya zuwa gobe kome Kenan saiku Fara tanadar kudin Sannan bazamu sallameku ba zai zauna a Nan har zuwa Lokacin tafiyar”Godiya Sosai sukayi mashi kafin sufito farfajiyar Asibitin Gaba daya idanun mom.harsun jike da hawaye kallon Yayartata tayi ta ce “Aunty Dole na koma yola saboda naje na had’o kud’ad’an da ake bukata bazan jure ganin Mijina ya cigaba da Zama Cikin wannan halin ba”.

Ta karasa fada Tana hawaye “kamo hannunta Maman katsina tayi ta ce “Ki nutsu Amina Komai da kikaga ya Samu bawa daga Allah ne Kiyi Hakuri da damuwar Nan Yanzu nawa ne yake dashi a account dinshi?Numfashi mom taja ta ce”ba sirrin Mustapha Wanda bansaniba Aunty ,Kudin account d’insa basu wuce 15 millions ba Zan hada dasu kawai na sayar da Gidan da muke Ciki tunda na tabbbatar zaiyi 15 millions an Mana tayin wulakancima Kinga saimu tafi da isassun kud’i idanma Basu Isa ba Kinga saina hada da gwala gwalaina”Girgiza Kai maman katsina tayi ta ce.

“Allah ya kiyaye ku sayar da Gidanku Amina ,me amfaninmu,kenan ma bamu da wani amfani tunda har larura ta samu irin wannan bamu share Miki hawayeba ,wasu ma suke kawo Mana kokensu muyi musu bare jinina Ba zaku sayar da Gidanku ba Sannan ba zamu Tab’a sisi na account dinshi ba Bari muyi waya da Mai martaba “Take ta Kira Mai martaba ta fada Masa halin da ake Ciki dukda ya san rashin lafiyar tunda shine ma yace karta taho ,Mai Martaba ya ce ya dauki nauyin komai na Asibitin sosai mom da maman katsina suka shiga yi mashi Godiya mom hada kukan farinciki rungume Yayartata tayi Tana kukan farinciki da Sanya Mata albarka.,

Shirye shiryen fitar da dad Saudi Arabia aka farayi a yini guda mom taje yola ta hado musu Duk wani abun da zasu bukata Sabren Ita a tunaninta da ita za a tafi harta Fara murnar tare zasu tafi dad zaisamu lafiya sai murnarta ta koma Ciki sakamakon Cewa daga mom sai dad zasu tafi Dan har an hadasu da Likitan chan zuwansu kawai ake jira Daren ranar Sabren Tayi kuka kamar ranta zai fita Dan jikin dad ta kwana Tana kuka Tana ita Dole sai an tafi da ita tun su Mom na Lallashinta har suka gaji a jikin dad bacci ya kwasheta.

 

_____Karfe takwas na safe a Nnamdi azikiwe international Airport tayi musu dad,mom,Sabren,maman katsina,Hajjar Mom Sai Uncle Yusuf Kanin mom sai direbobin motocin masarautar Guda ukku da sukazo musu bankwana Babu sautin da kakeji saina kukan Sabren sosai ta rungume mom Tana kuka Tana cewa.

“mom Dan Allah karku tafi ku barni mu tafi tare Ina zaku barni “Duk yanda mom taso daurewa Saida ta goge hawaye Rungume yartata tayi Tana jin wani iri a ranta Tana hawaye ta ce “Kiyi Hakuri baby saboda Makarantarki bazaiyu ki bimu ba Sannan Ai ga Mamankinan ga Kuma Hajja Wajen iyaye na Zaki zauna har Allah yayi Mana dawowa kedai kawai ki dinga Mana Addua Allah yasa a dace a tafiyar ya bawa Babanki lafiya ko Sannan ai zamu dinga waya”Kuka ta Kara rushewa dashi ta ce “Ni mom bazan zauna katsina ba Su Affan suna yola Ni banason katsina mom “.

Ganin jirginsu na Shirin tashine ya Sanya mom bin Daya bayan Daya tayi bankwana da mahaifiyarta tare da kaninta Saida tazo Kan Maman katsina kafin a hankali ta faki idon Hajja ta ce ‘Aunty karkibar baby Wajen Hajja Kinga dai yanda take baji take ba Hajja bazata iya rike Sabren ba Dole sai babba Mai zafi Tazauna a wajenki Dan Allah Aunty idan tayi ba daidaiba a horeta Gatanan dai a hannunki har Allah yayi Mana dawowa Aunty Dan Allah kiyimun kokari Wajen ganin ta shiryu ta daina abunda take Sannan na fada maki matsalarta Akan yawo Shima wannan Dole Saida kula nasan kina da kokari a fanni Nan Shiyasa nake son ta zauna a wajenki”.

Murmshi Maman katsina tayi ta ce “karki damu Amina Daman banyi niyyar barinta Wajen Hajja ba insha Allah zanyi iya bakin kokarina Wajen ganin na rik’e Maki Amanarta Allah ya bashi lfy ya dawo daku lfy”.

Koda jirginsu zai Tashi Mak’alk’ale su sabren tayi dakyal aka Samu aka rabasu suka tafi dan Hawa jirgi mom na hawaye Tana daga musu hannu ihu Sabren ta Fara ta durkushe a wajen Tana wani irin kuka A haka har jirginsu ya d’aga sararin samaniya….✍️

*page d’aya ya rage mu kammala free page hajiya kiyi saurin mallakar naki ba girmanki bane ace sai an sata an kawo miki ki karanta Littafi ne da sakinshi ya banbanta da kowanne salon Labaran da nake zuwa muku dashi labari ne da zai tabo bangarori da dama ,bamu fara komai ba a khadijatul sabren ba wannan din duk sharen fagene bamu shiga ainahin labarin ba karki bari a barki a baya y’ar uwa 300 kachal ta biyaki karanta kasaitaccen littafin nan Mai dogon zango Da ya tafi book 1 book 3 book 3 book 4 book 5 dukansu Akan 300 kachal Karki bari a baki labari y’ar uwa Bazan cika ku da surutu ba ance waka a bakin mai ita yafi dadi domin neman Karin bayani ku tuntub’eni akan number wayata kamar haka 07026166536 Kardai ku manta duk lokacin da yazama complete zai tashi daga 300 ya koma 500 sainajiku masoyan Gaskiya da Gaskiya*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_
[12/10, 1:08 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

 

“`MALLAKAR“`

*HAJARA L SADEQ*

@Miss Hajo✍🏿

*END OF BOOK ONE 1* 👆🙇

🅿️……….*19 & 20*

 

Sosai aka Sha dagu da sabren kafin ta yarda ta shiga Mota Saida ta gaji da kukanta kafin bacci ya kwasheta a jikin maman katsina har suka isa katsina Tana bacci.

Kai tsaye masarauta suka nufa saboda motarsu daban dasu hajja Suna Isa maman katsina tahau tadata a hankali ta bude idanuwanta Tare da Karewa inda suke kallo Lokaci guda ta Had’e fuska kamar zatayi kuka ta ce .

‘”mamy Ni banason masarauta ,”Cikin sigar lallashi ta ce “Kinga kwantar da hankalinki ba abunda za ayi Miki Anan din kinji y’ata”Make kafada tayi kamar wata Yar goye ganin Tana neman ‘Bata Mata Lokacin NE ya sanyata nuna Mata wani dogari Daya b’ullo ta ce “Kinga Baki fito ba yanzunnan zan hadaki da dogari ya zanemunke”.

Jin Haka ba shiri Sabren ta fito tare da Mak’alk’ale maman katsina ta ce “Kiyi Hakuri mama karkisa a dakeni wlh na fito”To shikenan bar kukan muje ko Yata”Kama hannunta tayi har suka isa part d’inta duk inda ta wuce ana kawo gaisuwa Sabren dai rarraba idanu kawai take har suka isa katafaren Palourn Wanda Ganinsu ya Sanya Mufida Tashi da sauri tare da rugowa ta rungume Sabren cike da zallar farinciki ta ce

“oyoyoy my sis Sannunku da zuwa kafin ta kalli mamy ta ce “Sannu da zuwa mamy”Yawwa Mufeda ya Gidan”Alhamdulilah kafin ta kalli Sabren dake kwakwabe fuska ta ce”Ga sister ki Nan baby kuje dakinta ki saki jikinki kinji nandin gidankune “Make kaf’ad’a tayi Tana Shirin Fashewa da kuka ta ce.

“Mama ni banason Nan din ki maidani wajen mom da dad “to naji za a mayar dake Amma yanzu kuje Ki huta’ ko?kafin ta kalli mufeda tace “ga Yar uwarki Nan Kuma kanwarki Nasan kinganeta tunda Kuna Dan gaisawa za a shigo da kayanta ki kaisu dakinki kuje ki Bata Abinci tayi salla tayi wanka”.

“tohm Mamy ?ta fada kafin ta kalli Sabren ta ce “Muje ko sis?Zata Sanya kuka mamy ta Had’e fuska ta ce “Kika sanyamun kuka Zan fasa maidake ?Cikin sauri ta hadiye kukan Tana goge hawayen ta ce .

“Na daina”Kama hannunta mufe tayi suka shiga bedroom d’inta ita ta ha’da Mata ruwan wanka da kanta bayan ta fito daga wanka kallon mufe tayi ta ce “Ina kayan nawa”Akwatinta da tun zuwan mom yola suna Asibiti ta had’o mata kayanta aka shigo dasu ta janyo tare da budewa ta ce.

“gasunan”Budewa tayi Daman duka kananan kayane cikinsu ta Sanya wasu mararsa nauyi Tana gamasa ta Haye gado Tana kallon gefe ta Lula duniyar tunani”Mufe ita ta rufe kayan kafin ta ce “Bazaki Tashi Kiyi salla ba Sabren Mamy tace a hanya la’asr tayi muku ga magrib itama har anyi”ba ayin sallar ta fada Tana rufe idonta “Dariyar mufeda tayi ta ce “sallar ce bakiyi kome?ba a saniba Yar ba’ka kawai”Dariyar mufe ta Kuma sawa ta ce “Au a kaina Zaki huce fushinki kenan to Yi Hakuri yar Farar danginmu “.

shiru Sabren tayi na Yan wasu Lokaci Jin mufe Bata Kuma magana ba ya sanyata juyowa kallonta tayi Tana salla Tashi tayi zaune Saida mufe ta Gama sallar kafin ta ce.

“waike kadai na gani a Gidan ko duk anmusu aure?a a a Yaya Maryam Taje bikin wata friends d’inta Shiyasa Baki ganta ba “To ina Aunty Farida wadda mom ta Tab’a ban muka gaisa da ita tace itace first born din Mamn katsina .

“Tana gidanta Kano take Aure kardai itama Baki Santa ba”zaro idanu tayi irin a mamakance ta ce “kaiii Wai har anmata aure”Dariyar mufe tayi ta ce “Eh Mana koni Lokacin da akayi bikinta Banda wayau ke Kuma Lokacin ko yayeki ba ayiba Yanxu Haka babban d’anta yayiki tsawo”Allah da gaske?Eh mana lokaci guda ta washe fuska ta ce.

“Kice Ina da abokin wasa”Dariya sosai mufe tayi ta ce “ke Yanzu Baki wuce wasa ba Sannan ma da d”an zumunki zakiyi wasan”Harararta Sabren tayi ta ce “Ehmana Ina ruwanki”To naji Amma yanxu Tashi Kiyi salla kinji Yar kanwata”.

Tilla Mata pillow Sabren tayi ta ce “ba ayi din Tashi muyi game a wayarki Dan Allah”bazan bada ba indai bakiyi salla ba Kuma Ina dasu Amma sai kinyi sallah jin haka ya Sanya Sabren mik’ewa faka_faka tayi sallar ta salamce tahau gado suka hau buga game sosai mufe tayi mamakin kwarewar game irin na Sabren duk game din da suka shiga ta iya Shi ita kanta a Dan zaman da sukayi na yan montuna ta tabbatar da ba k’aramun Wasa bane a ranta Suna Cikin game Daya daga Cikin hadimar Mufe ta shigo ta shaida Mata Hajiya na kiransu suje suyi dinner da to mufe ta amsa Mata Sabren hankalinta Yana wajen game Dakyal mufe ta samu ta Amshi wayarta suka fito tare da Sabren d’in.

a tsararren dining area din dake shake da manyan kuloli na alfarma suka tarar da mamy da Maryam Suna dinner karasawa wajen sukayi tare da Jan chairs suka zauna “Kallon Sabren Mamy tayi da Fara a fuskarta ta ce “Kici abinci sosai kinji “.

“Dan murmushi Sabren tayi ta ce “To Mamana”Maryam ce ta dakata d’aga cin abincin da take tare da Kame Baki ta ce.

“Mamy kardai Yar aunty Amina ce ta girma Haka ,Rabona da ita fa tun Tana 8years ko 5 “ai Dole kice bakisan Yar uwarkiba mararsa zumunci Wai Kuna cousin sister’s Amma bakusan juna ba ai hada laifin Aminar da Bata zuwa da ita kuma again ba zumuncin zuwa inda suke ba Kuke “.

Sosa Kai maryam tayi ta ce “Ba Haka bane Mamy Yanzu ai inshallah zamuyi zumuncin kafin ta kalli Sabren ta ce “sannu ko kanwata kinsanni Ai Ni ko?Make kaf’ad’a Sabren tayi tare da kallon mufe ta ce “Kice Bazanyi magana da ita ba yanzu”.

Dariyar Maryam tayi ta ce “To menayi”Tana tuttura Baki Gaba ta ce “Bake Ce kikace Baki gane niba bayan Ni Ina zuwa Saida na tambayeku”Sorry my kanwa Nina Isa nak’i ganeki Wasa nake maki my sweet sisterta dawo nanma ayi kaunar zumunci”.

ta fada Tana janyo hannunta tare da zaunar da ita kujerar gefenta “Lokaci guda Sabren ta saki fuska tare da yin Murmushi Dan a rayuwarta ba abunda takeso sama da Yan uwa idan taje gidan friends d’inta taga yayyunsu da kannansu sosai abun ke burgeta sabanin ita da take ita daya Tana kallon Maryam ta ce.

“Aunty Kema Ai yayata ce ko?eh Mana yayarkice ni Mai matukar kaunarki my sister “Cike da farinciki Sabren ta ce “yeee Nima Ashe Ina da yayyu kamar su Affan Amma meyasa bakwa zuwa Inda muke”Murmsuhi Maryam tayi Mata ta ce “muna zuwa Lokacin Baki wayau shiyasa Amma Yanzu ai kindawo Cikin mu ko ?Make kaf’ad’a tayi ta ce.

“a a a wajen dad Dina zan Koma saidai idan ku kun yarda ku bimu”Amma ai zakiyi Mana kwana biyu indai kina son muma mu bikin?shiru tayi na Yan mintuna kamar Mai tunani kafin ta ce”To na yarda Amma gidanmu zaku Koma da Zama”Mamy Ce tayi murmushi sosai take so da kaunar Sabren a Cikin ranta yarinyar nada shiga Rai over ta ce.

“Yanzu dai ki Barmun daughter taci Abinci ai kuna tare saikuje kuyi ta hirar Taku”Mufe ce ta kalli Maryam ta ce “Aunty daga zuwanki harkin kwacemun fada wajen sis”Dariya Sabren tayi tare da yi mata gwalo ta ce “Ke ai kanwata ce”Duk Dariya sukayi kafin su Fara gabatar da dinner dinsu Sabren taci wannan taci wancen Har Saida ta KoshI kafin ta mike Tana kallon mamy ta ce.

“Mamyn katsina Ki kiramun Mom d’ina”Tirkashi Mamy ta fada a ranta kafin a fili ta ce”Bata sayi layi ba Amma dazu ta kirani a wayar wani Dr sun Isa lfy Suna ma Asibitin gobe za a Fara duba lafiyar dad din naki kije ki kwanta gobe da safe kunyi wayar”.

Nan fa Sabren ta ce Bata San wannaan ba kuka ta fashe dashi tare da bajewa Kasan tiles tahau diddira kafa sai an Kira Mata mom d’inta ba lallashinta da ba ayi Mata ba Amma ta tubure ta ce.

“indai ana son na hakura sai an sayamun ice cream”Dakuwa many tayi Mata ta ce “Gidanku keda ice cream din katuwar wofi kitashi kije ki kwanta ko na zaneki “.

“to ki maidani gidanmu Nidai Allah sai ansayamun ice cream”ta fada Tana cigaba da diddira Kafa Maryam da Mufe Dariya kawai suke Mata dansu Basu tab’aga Sangarta irin wannan ba katuwar budurwa na acting din Yan yaye.

“Maryam ce ta ce “chab akwai aiki Gaba Keenan to Nidai na tafi saida safenku”ta nufi sashenta Tana Dariya yayinda Mufe itama Tana dariyar ta shiga lallashin sabren Amma kamar zuga ta ake Mamy ganin ba sarki sai Allah yarinyar tayi nisa ga wani ihu da take Tana Shirin Tara Mata mutane a dauka ba lafiya ba ya sanyata lallashinta tare da aikawa a sayo mata ice cream Din.

ana kawowa ta Mike kamar ba itace ta Gama murje murje ba ana Mika Mata ta goge hawayen tare da Fara Dariya Ta kalli mamy ta ce “Thnks Mamy na”kafi ta Ruga da gudu d’akin Mufe “girgiza Kai Mamy kawai tayi tare da kallon Mufe ta Mika Mata d’ayar robar ta ce.

“Saida safe ki tabbatar Tana cika salla nauyin Dana Dora Miki kawai akanta”Dariya Mufe tayi ta ce “to Mamy inshallah Zan kokarta Naga kamarma batasonyin salla Dan dakyal tayi dazu”Haka Uwar tacemun batason yin sallah Sai taga dama Shiyasa na Dora Miki Bangaren Nan naji da sauran “Tana Gama fadar Haka ta shige sashenta yayinda Mufe ta wuce sashensu itama Tana ta Dariya ita Daya Dan ita Gaba daya maganar Sabren ma yanda take komai a sangarce Dariya yake Bata.

Cikin sati guda Sabren ta Fara sabawa da Yan uwanta soboda irin yanda suke janta a jikin da nuna Mata kulawa musamman Mufe Sannan hankalinta yadan Fara kwanciya kasancewar kullum sai sunyi waya da mom ta wayar Mamyn katsina tanajin lafiyar dad d’inta Sannan Suna video call ,dangane da shiriritarta ba abunda ya ragu Yanzu babu abunda yafi damunta Daya wuce Zama waje Daya yanda ta Saba da yawo jinta take kamar a Kaya take,.

Sanye take Cikin blue din jiens tare da farar t-shirt ta Sanya farin combost d’inta hula Ce kawai a kanta ganin ba kowa a Palour mufe da Maryam Suna school Mamy Kuma Bata fito ba ya sanyata Cikin sauri ta fita d’aga part din, wani lumshe Ido tayi Koda taji hasken Rana sosai take karewa masarautar kallo Wanda sai Yanzu take Gama ganinta,kowa harkar gabanshi yake hakan ya sanyata Fara zagayawa Yawo ta shigayi ta shiga Nan ta fita Chan .

Tana Cikin Tafiya Taji tayi Karo da mutum Kadan ya hana ta fad’i cike da tsabar masifa ta ce “uban uban wani shegen ne ya Bugeni”Haidar dagowarshi kenan cike da zafin nama niyyarshi ya wanke wacce Yar rainin wayan ce har da Zata zageshi “.

Saranda yayi ba shiri Cin Karo da kyakyawar fuskar da tunda yake tsawon rayuwarsa Bai taba cin Karo da kyakyawa ba kamar yarinyar da yake gani gabansa, sakato yayi Yana kallonta kamar wani statue,irin kallon da yake Mata Ne ya Kara kular da Sabren cike da masifa Ta fara jaraba “Kai makahone ko baka da hankali da Zaka Bugeni Sannan ma shine ka tsaya kana kallona ko?.

Murmushi Haidar ya sakar Mata tare da. Cewa “Am sorry pretty ban gani ba Kiyi Hakuri”wata harara ta Dalla Masa tare da Had’e fuska sosai ta ce “Ai bansan wani Abu Hakuri ba malam ,sai ka biyani diyyar Bugeni da kayi Kasan dai ko a kotu kudinka sun haura dubu dari biyu ko?.

Ta fada Tana tsatsareshi da manyahn Idanunta “Barema Ke kyakyawa ai sai dubu dari biyar”ya fada Yana Dariya”Harararsa tayi ta ce “ba wani dadin bakin da zakamun nayi maka ragi ka biyani diyyar da Robar ice cream guda ukku tare da gasashshiyar kaza ,da Kuma Kwallon kwakwa ukku”Dariya sosai haidar yayi kafin ya ce “Su kawai Kike bukata pretty ?Tana Harararsa ta Ce”Eh idan Kuma baka siyamun ba Kara Zan kaika wajen Sarki “.

“Ah ah yi Hakuri ba akai ga Haka ba kyakyawa tare zamuje ko Kuma jirana zakiyi na dawo”Tana Zama wani dakali ta ce “Jeka dawo Ina Nan”Haidar har ya Isa Mota yana juyowa Yana kallonta har kusan faduwa yayi sosai yarinyar ta shiga ransa lokaci guda bai taba ga yarinyar da ya kamu da tsananin sonta cikin kankani lokaci ba kamar wannan yarinyar ,ga dressing dinta ma yayi mugun Tafiya dashi”.

Sabren ko Yana Barin wajen ta hau Dariya tare da cewa “Banza gara hotiho kawai har na Masa wayau”Tana Nan zaune Har Haidar ya dawo sosai tayi mamakin hada abunda Bata fada ba ma ya saya Mata “Amsa tayi Tana Shirin Tashi ya ce “Baki fad’amun ba to sunanki pretty”Tana wani yatsine fuska ta ce “Shima na kud’i ne”To nawa za a sayarmun”ban shirya saidawa Yanzu ba “binta Haidar yayi ganin Tana neman b’arin wajen tare da Cewa “kina son na dinga saya Miki wannan abubuwan kullum?.

Dan ya lura kwata kwata Bata da wayau “lokaci guda ta juyo Ta ce “Da gaske?Da gaske Mana Amma Sai kin yarda kin Zama kawata “Kare Masa Kalo tayi kafin ta ce “Amma ai Kai babba ne Ni friends Dina duk ba manya bane”To ba so kike na dinga saya Miki kayan Dadi ba ko su kananan friends din naki suna saya Miki”Shiru tayi Jim kafin ta dago ta kallesa ta ce “a a basa sayamun na yarda to “Good girl My friends wani Bangaren Kika zo Wai Dan Nasan dai ke bakuwace a Gidan Nan”

“Bangaren su Mufeda Ni diyar sister mamansu ce”Okay nagane to mu dinga haduwa a Nan ko gobe ma da la’asr mu hadu anan zanyo Miki sayayya?Sannan karkicewa Hajiyar Ni friend dinki ne”Harara ta Galla Masa tare da Cewa.

“To sannu Daddyna kake bani wani umarni kamar wani uba na”Kafin tayi Gaba “wani dogon numfashi Haidar Yana gabaki Daya kafafuwanshi gagaranshi dauka sukayi bai bar wajen ba har saida yaga bacewarta wani sanyayyen murmushi ya saki cikin kasalalliyar murya ya ce ” I love you so much my pretty…

A dakinsu ta baje ta dinga ciye ciyenta Tana ci Tana dariya ta ce “Gaskiya garin Nan duk Basu da wayau,jifa garan ya zaci da gaske nake yayo mun wannan sayayyar ,Allahsarki ko Ina Yaya beauty Shima da nayi mashi wayau yayi ta sayamun abubuwa Rance “Kafin ta kwashe da dariya.

Wanda Zata iya ci taci kafin ta Sanya wasu Fridge wayarta ta janyo tare da Kiran affan sosai suka Sha hira cike da kewar juna affan ne ya ce.

“Ina wannan Babar da kika cemun ba Kakarki bace ,kusan kullum sai sunzo suyi ta buga Gidan inaji jiya Mai gadinku ya ce musu bakowa Gidan karkiga jarabar da ta dingayi Tana ta zagin mom dinki Wai Zata sayar Mata da d’a Kinga zagin da suka dingayiwa mom dinki ita da wannan lutetiyar”.

“tsohuwar banza ce ai Dan Allah Affan idan ta Kara zuwa Ni na sanyaka ka harbeta da kwari da baka ko ka kad’e shaggu a kekenka Sannan karku sake ku fada musu inda su Mom da dad suke”Dariya sosai Affan yayi ya ce “Kai besty Kakartaki Nidai ba ruwana”Uwar kakata Allah kiyaye wannan munannar ta Zama kakata, banza Ni har ka batamun raima sai anjima”,
Baccine ya kwasheta bayan Gama wayar.

 

Tunda Sabren ta Tashi taga ana ta Shirye Shirye part din na musamman tare da girki kala kala ita dai taga Shirin wannan yasha banban da Wanda ake kasa Shiru tayi hakan ya sanyata kallon Maryam dake gefenta Tana Danna Laptop ta ce .

‘”Aunty Wai Shirin me ake tayi Naga tun safe gashi Yanzu har kusan la’ars ba a gamaba “Yaya Anwar ne zai shigo gari shiyasa”Waye to yaya Anwar din?.

ta tambaya “Shima yayankine daga Aunty farida saishi saini sai mufe Shima Nasan Baki sansa ba”Shima Kuma d’an mamyn katsina NE?Cike da kosawa da tambaya Maryam ta ce “Eh jekiyi salla ko azahar bakiyi ba “Make kafada tayi ta ce.

“Banyi to sai anjima”Wai meyasa Kika fiya Wasa da salla baby kefa ba Yarinya bace kin Isa ki fad’awa wasu “Turo Baki Gaba tayi ta ce “To Nidai nace Miki Yanzu bazanyiba kafin ta Haye gado ta janyo wayar Maryam tahau buga game,sanin ba yin zatayi ba ya Sanya Maryam kyaleta taci gaba da aikin da take.

Kamar ko yaushe duk zuwan da zaiyi tofa sai yasha bushe_bushe da kiraye_kiraye Wanda tun bayason abun harya hakura Dan ba yanda zaiyi Dole ,Sanye yake cikin manyan kaya irin na gidan sarauta masu tsananin masifar kyau saboda fad’an da mai martaba yake masa akan zuwa da kananun kaya ya sanya yanzu yake zuwa da manyan kaya kamshi ko duk inda ya gitta sai wajen yajima Yana kamshi Kai tsaye Bai zarce ko Ina ba Sai part din Ammynsa ,.

*Hajiya Talatu*

Ganin irin Shirin da ake a masarautar ne ya tabbatar Mata Yarima Anwar Yana tafe hakan ya sanyata fita tun safe ita da Ummul kulthum Tafiya sukayi Mai nisa Saida suka shiga har kasar Niger domin zuwa wajen sabon malamin da sukayi,.

magunguna ya Basu sosai ya ce”d’aya kina komawa Gidan ki turare d’akinki dashi Gaba Daya muddin ya shaki hayakinnan tofa aiki ya Gama sai yanda kikayi dashi ko uwarsa Bata Isa ta fad’a Abu ya tsallake ba”.

“Kafin ya fiddo wani ruwa a kwalba ya mikawa Ummul khairi ya ce “Ke Kuma wanna Lokacin da zai shigo ki wanke fuskarki ki tabbatar Kunyi Ido hudu dashi tofa zance ya kare da kanshi zai dinga bibiyarki harsai kinja Masa aji ,Kafin ya dauko wata kwalbar turare ya ce “Wannan Kuma ki shafa sa Shima ki tabbatar ya shaki kamshin ba k’aramun Aiki muka Sha ba wajen hada magungunan Nan Sha Yanxu Ne magani Yanzu da kanku zakuzo Kuna mini godiya Amma akwai sharad’i guda Kar a sake maganin ya Tab’a k’asa Koda Wasa Kar ya ta’ba k’asa Dan k’asa itace makarin hadin magungunan muddin ya taba k’asa Aiki ya b’aci”bama zai Taba ba malam nagode Allah saka da alkhairi kafin ta dauko makudan kud’i ta Aje masa ta ce “tukuicinka Yana Gaba malam sai aiki yaci Yanzu muna sauri na tabbatarma da Kila ya iso saimun dawo.

____”Irin tarbar da yake samu a Koda yaushe ita ya Samu a wajen mamyn Nasa da kanta ta dinga b’ara Masa ayaba Tana basa Hira suke sosai irin ta d’a da uwa,Daga ita saishi a Palourn mamy ce ta ce “Wai ya maganar transfer taka kuwa gwarzona nifa nafison ganinka kullum kusa Dani bana son nesan Nan”Yana murmushi ya ce “Mamy keda Abba kunki Hakura da transfer Nan,Inajin Dadin aiki a chan ne shiyasa ,ya mai jikin tun Kuna abujar naso naje na duba sa Sha anin Aiki ya Hana Yanxu Suna madinar har Auntyn?

“E to da sauki za ace Amma har Yanzu dai Bai farfado ba”Cikin nuna rashin Jin dadinsa ya ce “Allahsarki Allah ya bashi lfy Ina Yartasu kuma”Amen ya Allah khadija Tana Nan na taho da ita Tana ciki Daman Ina tason kazo muga wace Makaranta yakamata a kaita saika kaita s s one tunda tayi jsce”.

“inaga ammy kowace ma da an kaita da a jira zuwana ba ma “ya fada cike da ladabi”Girgiza Masa Kai tayi ta ce”a a a Kasan harkar karatu Dole saida namiji ai ba kurewa lokaci yayi ba “To shikenan mamy inaga mezai Hana a hadata da Mufeda kawai kamar zaifi”?Eh Daman Dole a hadasu Makaranta Daya da wani Dan y’artawa dai Har Yanzu akwai Saura”to shikenan’ gobe Saita Shirya tare da Mufe naje na kaita din tunda Gobe Tuesday”.

Tunawa da har la’asr ta wuce ya Sanya Sabren tunowa da maganarsu da Haidar ya ce zai yo Mata sayayya yau Aiko ba shiri ta Aje laptop din Daga ita sai hula ko takalmi Babu ta ruga a guje Mamy ganin fitowarta da gudu Cikin daga murya ta ce.

“Ke Khadija Ina zaku haka Cikin gudu “Ina Sabren bama ta saurareta ba tuni tayi Gaba Hankalin Anawar na kan mamy baima ganta ba yaji dai ‘Karan gudu Sabren gudu ta dingayi Tana haki a zatanta mamy ta Sanya an biyota Daidai Mama Talatu ta shigo Tana niyyar nufa Bangarenta rike da kullum magungunan Data rike a hannu gudun matsala Daidai Sabren dayo wajen ji kake Gam ta tunkudeta Gabaki Daya magungunan suka baje a k’asa sabren ko bama ta tsaya tabi takantaba tasandai ta Buge mutum Amma batasan ko Meye ba.

“wani irin ihu mama talatu tayi tare da Dora hannu aka tsundumawa Sabren zagi tahau kutuntumawa Wanda babu dadin ji Takaici Daya ishi kulthum kuka ta fashe dashi ta ce shikenan duk tafiyar da wahalar da mukayi ta tafi a banza Kai Amma Allah tsinewa tsinanniyar yarinyar chan ko Yar gidan uban wacece,”Mama talatu ko Zaman Yan bori tayi .

Sabren Saida takai inda suka hadu da Haidar kafin ta tsaya Tana haki ,Haidar Daman Yana wajen Cikin sauri ya taso Yana tambayarta meyasa tayi gudu Haka Dan yasan tazarar tsakanin Part din Mamy da Nan nasu hakan yasa basama wani haduwa Dan idan ba dalili ba wani ma saisuyi wata Basu hadu ba Tana haki ta ce “Mamy Dan karta Sanya a biyoni shiyasa nayi gudun”Ohh sorry my pretty ya fada Yana son taba hannunta Yana tsoron karta masa jaraba dan ya lura jarababbiya ce.

“Saida ta Gama hak’in kafin ya Bata sayayyar da yayo Mata tun a Nan ta bude robar ice cream tare da Fara Sha har wani lumshe Ido take Dadi yakai Mata Karo da wannan abun Haidar ya samu damar kamo hannunta a hankali cike da barikanci ya ce.

“Wow pretty hannunki laushi me kike shafa Masa Nima ki sammun na dinga shafawa “kwata kwata hankalin Sabren Bai kawo Mata komai ba ta ce “Ba Komai Fa Nake shafawa wlh Haka yake “sosai Haidar ya dinga janta da hira Wanda a Haka yadinga murza hannunta ita kuwa Sakaran ko a kanta Dadi yakai Mata Karo Saida ta Gama ciye ciyenta kafin ta Mike wajen 5 tace Zata wuce.

“Saida yarakata gab da part din kafin ya juya yanajin wani Dadi a ransa ya Samu daman yanda yakeso yayi da yarinyar da tunda yaga yarinyar ya kwadaitu da ita dukda ba wata babba bace shida yake Hulda da manyan babies Amma Gaba Daya baitabajin yanayi irin Wanda yake shigaba idan gashi ga yarinyar sigarinshi ya fiddo ya kunna tare da komawa ciki,.

Dadi Sabren Taji sosai da Bata iske Mamy a Palour ba Kai tsaye dakinsu ta wuce Tana Jin Dadi ta samu Wanda zai dinga Mata sayayya,around 9pm Suna dining Suna dinner Mamy ta kalli Sabren ta ce”Gobe ki Shirya tunda safe Tare zaku tafi school da mufeda yayanku zai kaiki ayi Miki register “Batare da gardama ba Sabren ta ce”To mamy”Dan Koba komai ta samu hanyar da Zata dinga ganin gari.

Washegari tunda safe Saida ta riga ma mufe shiryawa Around 7:30 sungama shiri har break fast sunyi d’akin mamy suka biya sukayi Mata sallama kafin su fito Kai tsaye inda Yayan nasu yake Tsayawa da motarsa Mufe tajata suka nufa Lokacin Yana ciiki back seat Mufe ta shiga Sabren na niyyar shiga baya mufe ta ce “ki shiga gaba Mana ba kowa”.

Daman ita sabren tafison zaman Gaba a Mota ba musu ta bude murfin motar tare da shiga ba laifi ta danyi shigar kirki tunda ta Dora hijab a jiens din dake jikinta dukda Bata Kai Mata gwuiwa ba ,”Good morning Yaya”Cewar mufe daga Baya”Morning too how was your night”Alhamdulilah”ta bashi amsa”.

Jin kamar tasan Mai muryar ne ya Sanya Sabren juyawa tare da kallonshi Daidai shima ya juyo Dan ya kalli ta rufe k’ofar yaja idanunsu ya sartse Cikin na juna ,wara idanu sosai Sabren tayi Dan son tabbatar da shi dinne shima kallon mamaki yake Mata cike da tsoro Sabren ta wara manyan idanunta ta ce “Yaya Beauty Kaine da gaske……….✍️

*Alhamdulilla anan na kawo karshen free page kuma karshen book one na wannan littafin nawa Mai take khadijatul sabren kamar yanda na fad’a Wanda suka biya ne kawai suke da daman cigaba da karanta gawurtaccen Littafi da yazo daga cikin gawurtattu biyar salon wasan littafin khadijatul sabren yanzu zai fara zaku biya kudin ku ne ta hanyar da muka rubuta muku a kasa Ki saya da zuciya daya Ba dan ki fitar ba y’ar uwa shi Allah baya yafe hakki duk kankantarsa saimun hade a paid group masoyan Gaskiya da Gaskiya masu ci da guminsu domin neman Karin bayani a tuntub’eni akan number wayata kamar haka 07026166536 Miss Hajon ce dai da ta nishad’antar da ku a littafanta irinsu ,Ni da yaya Arman,Auren wata Tara da sauransu*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

07026166536 what’s app

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]