[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 40 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

zaro ido umman jidda tayi cike da kad’uwa da mgnr da dady yayi, da rarrashi dady yace, ajjiye wukar danjuma,

jikin danjuma a sanyaye ya ajjiye har yanxu hawaye na xuba daga idonshi danji yake xai iya yin komai akan soyayyar jidda, dady ya kallesu ranshi ab’ace

     gaba d’aya kowa yaje yai sallah xuwa gobe xamu tattauna,bana son naji kowa yakara wannan mgnr

    ya wuce, jikin kowa asanyaye suka bar wajan, daren ranar kam kad’an ne na gidan suka iya cin abinci sauran kam xuciyoyinsu kamar wuta jidda kuka take sosai,tana jin wani irin tuk’ik’i a xuciyarta,

washegari tun da sassafe baban jidda yaxo gidan dady dan tun jiya dadyn ya kirashi akan yana son ganinsa da gaggawa, haka ya taso hajja mahaifiyarsu wacce bata da lfy tana fama da hawan jini ba kowacce mgn ake fad’a mata ba,

   dady ya tara mutanen gidan kaf a babban falon k’asa, kowa ka kalla yana cikin mmk, jidda har lokacin kuka take musamman dataga mahaifinta ita kanta umman jiddan arikice take ganin mijinta yasa ta shiga wani sabon tashin hnkln, danjuma yana xaune agefe ya takure cikin xuciyar shi yana jin takaicin yadda ya tsinci kanshi a wannan halin, cikin takaici mara misaltuwa dady ya fara mgn,

      Alhaji musa nasan kayi mmkin kiran gaggawar da nai maka sbd jibi ne ranar da ta kama daurin auren Ibrahim da jidda,

kuka danjuma yasaka Alhaji kataima kamin,

dady ya xuba mishi ido cike da tausayawa, ya kalli umman jidda da harara,

sai kiyiwa mutane bayanin abinda kikayi,

sunkuyar da kanta k’asa tayi hawaye na xuba kunya sosai takamata tarasa ta ina xatai bayanin wannan abin kunyar,

ya daka mata tsawa a firgice ta d’ago kai jikinta na karkarwa wani b’akin ciki mai xafi ya tokare mata kirji,

sam takasa bud’ar baki tayi mgn,

cikin kuka hjy Aisha yayarta ta fara mgn xuciyarta akarye, kayi hkr yaya bashir kuskure ne da kuma kad’dara, shekaranjiya ne mukaje wajan wani malami akan ana so jidda ta mallake Ibrahim, tayi jim cike da danasani muryarta k’asa k’asa had’e da kuka ta cigaba,

shine yai aiki mai karfi ya bamu yace ta xuba masa a abinci ko a lemo in dai yasha to sai yadda tayi dashi dan ko uwarshi tace kada ya kara gaisheta  baxai k’ara ba xata maidashi kamar d’anta sai abinda tace,

    salati Alhaji musa yayi ya cire hula yana girgixa kai gumi yaji ta ko ina,

momy ma salatin tayi hawayen farin ciki ya sauko mata na Allah ya mayar musu da mummunan k’udirinsu,

jannat ma hamdala tayi ta godewa Allah xuciyarta cike da tsoron Allah, hajja kuka tasaka tana yiwa yarta mugun kallo,

         hadiza ina bak’in cikin mugun halinki yanxu ko makiyinki xaki masa haka ? balle Ibrahim daya ke d’anki ? innalillahi wa inna ilaihi raji’unn kin cuceni hadiza kin gama da rayuwarki,ya khaleel daya ke kusa da ita ya riko mata hannu plx hajja yi hkr ki yi shiru, ta rik’e hannunshi sosai sannu khaleel kayi hkr kaji nasan kana da tausayi da imani da taimako shiyasa Allah yake tare da kai, d’aga mata kai yayi, ki daina kuka hajja,

tabe baki dady yayi yana yiwa hjy hadixa mugun kallo cike da tsanarta,

        kinga yadda Allah ya nuna ikonsa ko ? Allah baya barin xalunci, Ibrahim d’ankine hadiza idan kin maidani d’an’uwanki kaf d’inku kun tsani firdausi mahaifiyar shi wai ta shanyeni, yar bin bokaye ce da malamai yanxu tsakaninku waye mai bin bokan ? tunda yaran nan suke xaune cikin gidan nan kuke xaginsu kuna aibatasu kuna ce musu yan asiri sbd kawai sun rab’eni,

sam bakwason kowa ya rab’u da jikina,

       wannan shine babbar sakayya daga ubangiji yanxu sai ku gane abu d’aya duk wanda yake xaune dakai da kyakkyawar xuciya ubangiji baxai baka sa’ar ka cutar dashi ba,

Alhaji musa ya kalli dady,

Dr bashir yau yaxama dole na fadi abinda ke raina akan hadixa da y’ata hauwa’u ka gansu nan babu wanda na isa dashi hauwa’u ita kadaice mace tilo da Allah ya bani amma sai na shafe wata ko shekara ban sata a idona ba danayi mgn uwarta tace min tana gidanka bawai zan hanata xuwa gidanka ba amma amatsayina na ubanta yadace ace duk inda xataje a fad’amin, amma sbd ammai dani buje dantofi ya jinjina kai ban isa ba sai dai na xuba musu ido, hadixa ta rabani da yan’uwana tace duk mak’iya nane

    Dr bashir na fad’a maka hakane dan kagane wannan kad’an daga cikin mugun hali irin na hadiza ta xamemin masifa bala’i a ratuwata narasa yadda xanyi da ita,

innalillahi wa inna ilaihi raji’un lokaci daya dady da hajja sukayi hajja ta k’ara rushewa da kuka , da kyar khaleel ya rarrasheta tayi shiru,

      sai a yanxu dady ya tabbatar da hadiza ba k’aramar makira bace gdy yaiwa Allah daya tsare d’ansa daga makircinsu,

cike da jimami dady ya cigaba da mgn,

           aikin gama ya gama khaleel Allah ya tsareshi daga wahala baici abincin ba cikin tsautsayi ya bawa danjuma ya nuna danjuman daya ke arab’e yaci abincin sai akayi dacen shima sunanshi Ibrahim,

dalilin haka ya shiga wani mayuwancin hali na kaunar jidda har yana ikirarin muddin aka hanashi  xai iya kashe kanshi ya kasheta,

     xaro ido hajja tayi hade      da    murmushin yake  tace alhamdulillah Allah nagode maka,

Alhaji musa shima murmushin takaici yayi ya kalli danjuma, kwantar da hnklinka d’ana na baka auren ta kuma yau yau dinnan xa a d’aura maka aure da ita, wani ihu jidda ta kurma hajja ta kai mata rankwashi,rufewa mutane vaki makira ba uban da ya isa ya hana wannan d’aurin auren haka ba wanda ya isa yace baxa d’aurashi ayau ba, ngd maka musa nagd mk musa, haka akewa mutane masu mummunan xuciya ta fashe da kuka, wllh ban wa hadiza wannan tarbiyyar ba cen y’an bariki suka b’atamin ita Allah ya shiryar min dake, kuka hadizan take sosai dana sani na xiyartar ta ta ko’ina,

Alhaji musa ya kalli danjuma fuskarshi na nuna tausayinsa,

kana da sadaki a hannunka ?

asanyaye danjuma ya shafo aljihunsa dan bashi da kudi sai wasu yan canji, da sauri ya khaleel yace xan biya mishi sadakin,

   dan shi ya fi kowa farin cikin wannan hadin waskewa kawai yake yana nuna ya damu amma xuciyarsa cike take da farinciki,

danjuma

ya kalle shi ngd oga khaleel

Alhaji musa yace  ka katuro wakilinka

kana da mata ?

kanshi a k’asa yace  mahaifina ya rasu sai mahaifiyata datake xaune da matata acan garinmu gexawa,

nan garin bani da kowa idan kuma xa’a jira wakilan nawa zan kirasu awaya, dady yace in dai wakiline zan zame maka Allah ya baku xaman lfy,

nagode dady,

kada kadamu danjuma kaima kazama namu tunda xaka auri yarmu,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Alhaji musa yace kana da inda xaka ajjiyeta ?

girgixa kai yayi jikinshi asanyaye sai dai gidanmu na gado na cen gexawa d’aki biyu ne anan matata da mahaifiyata suke xaune,

Alhaji musa yace  nabaka gidane da yake rijiyar xaki nan kano ku xauna aciki,

idon danjuma fal hawaye yake gdy,

dady yace zan canxa maka aiki kadawo companynmu Allah ya baku xaman lfy,

fashewa yayi da kuka lokaci daya Allah ya axurtashi ta dalilin wannan auren yai gdy sosai, hajja tace saura waccen ja’irar ta nuna zahra, dady ya gallawa xahran harara itama cikin satin nan zan aurar da ita ga duk wanda na ga dama sbd itama na fuskanci wani irin hali gareta, da sauri hajja tace bakin hali kai,

  kai dai baka dashi uwarta ma bata dashi xama da wannan ta nuna hadixa yasa tana k’ok’arin komawa ita sak Allah ya shirye ku addu’ar da xan muku kenan, zahra ta fashe da kuka hajja tabige mata baki yi mana shiru munafuka,

     Alhaji musa ya kalli agogon hannunsa inshaa Allah yau ana idar da sallar axahar za’a daura auren ya mik’e tsaye dady yayi addu’a suka tashi ya khaleel ya mik’e shima had’e da kiran danjuman yabi bayansa dakinsa yaje kayan shi da dady ya dinko masa sbd bikin shi da jidda set 30 ya d’auko ya had’a masa da hula da takalma harda agogonsa wannan dady ya siyo masa ya bashi, danjuma gashi nan aje ayi hidimar biki dasu, gdy sosai danjuman yakeyi, shikam ya khaleel farin ciki fal ranshi shiyasa ya had’a kayan da aka siyo masa dan d’aurin auren ya bada su dan ko kallonsu bai son yi tunda Allah ya rabashi da alak’a k’ai

ana idar da sallar axahar aka d’aura auren danjuma sani gexawa da amaryarshi hauwa’u musa kan sadaki nera dubu d’ari biyar wanda ya khaleel ya biya sbd farin cikin daya keji ko miliyan nawa ne xai iya biya Allah ya rabashi da jidda bai tab’a jin soyayarta aransa ba yana kulatane kawai sbd yar’uwarsa ce, wani vangare na xuciyarshi yana wa Allah gdy akan tsareshi da yayi da makircinsu yau jinta yake kamar sallah

tunda saka bar falon hajja take ta musu fad’a da nasiha,

hajiya amina da hjy Aisha da umman jiddan lokaci d’aya suka fita hayyacinsu dan sun bala’in kad’uwa da abinda ya faru lokaci d’aya Allah ya nuna musu ishara hajja tana xubar da hawaye tace,

kun bani mmki dukanku, kun xubar min dak’imata ngd wa  da ubangiji da yasa mahaifinku bai ga wannan masifar ba duk irin soyayyar daya nuna muku da yanda ya koya muku kaunar juna, ace har daya daga cikin xai yi yunkurin cutar dan daya innalillahi

          da kyar momy ta lallasheta tayi shiru, ta kamata tai bangaren ta da ita sbd rashin lfyr ta ba’a son ranta ya dink’a b’aci,

hjy amina ta kallesu nikam wannan abin yasa ni dana sanin da bantab’a jinshi ba hawaye ya sauko mata sbd haka hajja take xubar mana da hawaye nayi nadama, haka suka dinka tattaunawa a tsakaninsu kowacce tana dana sani k’arara

daki jannat ta shiga ta xaune gefen gadon ta tagumi tayi tana tuna abin kamar mafarki ko shirin film lallai Allah shine mai kare bayansa abincin da ta fita tabar shi adakin ya khaleel ashe bashi da maraba da tarwa tsa farin cikin raywarta ? tasaki ajiyar xuciya sulthana ta shigo jikinta asanyaye tana xama hindu ta biyo ta, sulthana tace wai naga drimer mai ban mmk,abinda ya bani mmk ba wannan ne karo na farko ba lokacin data fara barbaden ni naganta na sauya abincin, sbd bata daddara ba sai da ta kara ni wllh banso asirin ya tsaya akan danjuma ba naso ace wani tutturna baki mai katon ciki da katon baki da mummunan fuska ta samu danjuma dayake bafillace me kyau da yaji wanka murjewa xaiyi, hindu tace, kina da matsala sulthana wananna fa ishara ce kiyi addu’a kawai daga Allah yake ba awajan dan’adam ba, murguda baki sulthana tayi

eh kaikayine ya koma kan mashekiya,

knocking door sukaji a hnkl aka bude kofar suka kalleta jikinta asnyaye ta karaso kusa da su fuskar ta tasha kuka, cikin rawar murya tace anty jannat plx ki ya femin nayi danasani sosai yanxu na tabbatar da dan’uwa suna ya tara wani dan ‘uwan naka bashi da abin nema sai jin ka wulakanta wani baren sai ya kaunace ka kaunar da dan’uwanka bai nuna maka ita ba, ki dubi halin da umma taso saka ya khaleel wai ahaka kanwar dadynmu ne, ta fashe da kuka yanxu na gane ku yan’uwane na yadda ku yafemin plx,

ayatsine sulthana tace munji anyafe atashi a k’ara gaba saura ke dan kema sai kinga naki isharan wanda ya tuba dan wuya ba lada, hindu tace, me ye haka sulthana ? ba inda xata dan duk duniya in banda ku bani da wata bayan su, jannat tace bakomai zahra Allah ya yafe mana gaba d’aya, kasa tashi tayi dan kunya ce ta kamata yara kanana sun fita hnkl tasan ko kad’an su jannat ba sa’anninta bane da kyar ta mike jikinta ba kwari ta fice xuciyrta cike da xullumin itama wa xa’a daura mata aure dashi ?

momy tana komawa d’aki ta saki ajiyar xuciya tai hmdl tun farkon soyayyar jidda da khaleel ba so take ba sbd halin uwarta cikin ikon Allah sai gashi Allah ya raba, ta d’ago hannu sama tanawa ubangiji gdy kan tsare mata danta da yayi wayarta ta dauko ta kira kanwarta hjy safiyya ta bata lbrn komai sun dad’e suna hira suna jajanta lamarin sannan sukayi sallama ta tashi ta dauro alwala tai sallar la’asar

da daddare gidan tsit kowa ka gani da abinda ke damunshi

jannat tana zaune gefen gado sulthana tana kusa da ita hindu na xaune kan stool suna hira,

sallama tayi suka amsa mata da mmk suke kallonta, gaba d’ayanta asanyaye take idanuwanta sun kumbura sbd kuka fuskarta tayi jaa ta xauna kusa da jannat ta kalleta tayi wani mugun murmushi kana kallonsa kasan na bak’in ciki da takaicine,

jannat kinga yanda Allah yayi dani ko ?

girgixa mata kai jannat tayi,

kada kice hk jannat wannan abin daya sameni ishara ce babba, dan wannan ya xame min babban darasi wasu guntun hawaye suka sauko mata, ta kare mata kallo, ina mmkin yarinya karama dake amma kin san rayuwa tunda dad’ewa nasan ya khaleel yana sonki,

xaro ido jannat tayi,

plx ina son ki bani shawara dan ni yanxu daga jiya xuwa yau na dauki wani babban darasi arayuwata,

rik’o hannunta jannat tayi, ki daina kuka anty jidda komai kika gani daga ubangiji yake gaba d’aya rayuwar nan a tsare take gun Allah ki godewa Allah kina da iyaye suna gabanki kina kallonsu kina da rabin jin dadin duniya, jidda ta share hawayenta, hakane anty jannat ina son kibani shawarar yanda ya khaleel yake sonki duk da na san rik’akk’en ra’ayi irin nasa,

jim jannat tayi tana tunani a sanyaye tace anty jidda kema kin san shi sai dai mutuna sar da juna dan duk wata mace tasan da wannan,

*biyayya*

itace ke saurin jefa kauna axuciyar mutun idan har xakiyi biyayya ga wanda yake sama dake to tabbas xai k’aunace ki k’auna bata wasa ba,

rashin biyayya shi ke kawo kiyayya da tsana axuciyar mutun

meyasa xakiga wasu matan suna kula da kansu da tsabtace jikinsu da shan magani dan gyara da iya abinci duk wani abu na jan hnkl ta iya tana ganin ita ta cika mace lokaci d’aya mijinta ya kuntata mata yai mata abinda inkikaji sai kinyi mmk, idan kika binciketa sai kinga ne bata masa biyayya amma fa tana kyautata masa

akwai banbanci sosai, duk yadda kike kyautata wa mijinki muddin bakya masa biyayya tofa kyautatawar nan abanxa take,

misali ko baki da miji kina da kanne acikin k’annanki duk wanda yafi miki biyayya kinfi sonshi kinfi son ki kyautata masa haka ma ayayanki wanda yake miki biyayya kinfi kaunar sa haka dangantaka take arayuwa mata plx adage da yi miji biyayya kada ki manta Allah da kansa yace da ace xa ayiwa wani sujjada bayan ni dana umarci mata taiwa mijinta,

77/78

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]