[Advertisements⬇️]

JENNIFA CHAPTER 39 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Dafe kanshi dady yayi Sam bahaka yaso jiba, ya kalli President fuskarshi da damuwa,

    Yanxu ba yadda xa,ai mu hadu kenan?

Jim President yayi eh to akwai wata tattaunawa dana keso muyi dashi kasan shi Idan kana son ganinsa sai ta hanyar taimako akwai wani filinshi ana cikin abuja Ina son ya bamu filin xamu gina gidan marayu, akan hakan xai iya xuwa kasan shi adaline yana taimakon marayu sosai, damuwar shine vana tunanin xai xo da wuri sbd baifi 3 weeks da barin 9ja ba yaxo kano shida iyalinshi, dan ministern tsaro ya  fadamin cewa ched’e yana son abashi mutanen da xasu masa tsoro, da sauri dady ya kalli President, yana tuna lbrn da jannat ta bashi na taga wata mata tabbas duk yadda akayi matar tana da alaka babba da jannat din,

Kayi hkr bashir xanyi waya dashi Adam ched’en duk yadda mukayi xakaji ka jirani nan da 3 dys,

Dady yace bakomai xai jira suka cigaba da hirar yau she rabo,

Bayan kwana 3 din suka dawo wajan President, yana ganinsu ya girgixa kai,

Su ka gaisa,

Bashir kaga abinda na fada maka ko ?

Wllh babban yaronshi ya turo wai duk abinda xa ai ga shi nan ya turo wakili ayi,

Dady ya girgixa kai shima ranshi ajagule bai so haka ba a daddafe suka gama hirar da President ya dawo gidan shi na abujan yana jin takaici kala kala bai son wanne kalan rarrashi xaiwa yaran nan ba tunda ya taho safe da rana cikin kiranshi suke duk sun kagu ya furxar da iska xuciyarshi ba dadi, baiyi tunanin haka abin xai cabe ba, kafin asansu an wahala anganosu kuma xa a kuma shan wta wahalar ? Ya rabbi, Allah kawarware mana wannan hadin Allah ka haka yai ta addu’a yana tnanin yanda xaije wa da iyalin shi wannan maganar Mara dadin ji

Bai kwana ba sbd ji yai garin ya isheshi  jirgin yamma yabiyo ya dawo gida suna ganinshi suka taso da murna da jindadin ya kallesu tausayinsu ya kamashi kamar yai musu kwalla tunanin shi wanne irin yanayi xasu shiga in sukaji cewa ba a dace ba,

Tun kafin ya huta sulthana da Hindu suketa tambayarshi jannat ce kawai batayi mgn ba itama yasan kunya ce ta hanata  ya basu hkr su bari yai sallah, ya idar da sallah ya ya tarasu duka a babban falo da nasiha ya fara sai da ya tabbatar jikinsu yai sanyi sannan ya fada musu avinda ya faru ga mmkin sa sai yaga sunyi tawakkali basu tada hnklinsu ba, ya khaleel ya kalli dady,

      Dady uwargidan ched’e tana da alaka mai girma tsakaninta da masarautar garin nan dan kakanta yai  mulki yanxu haka sarki yayanta ne Dan kakan ninsu d’aya mai xai hana aje wajan sarkin ai mishi bayanin komai tunda nasan ba xa a samu matsala da ga b’angreshi ba, murmushi dady yayi nan da nan ya nemi bacin ransa ya rasa, sbd shawarar da khaleel ya kawo shi Sam bai son da haka ba, hakane khaleel Allah yai mk albarka,

Amin dady xanyi wa prince A,K Garkuwa mgn yai mk jagora wajan sarkin tunda shima suna da babbar alaka duk dangin sune, dady ya saki fuska, mashaa Allah in shaa Allah kuwa gobe nakeso naga sarkin mutattauna dan nafison yaran nan suga iyayensu su huta da wannan bakin cikin,

In shaa Allah dady xankira A.K Garkuwan anjima kadan basu bar wajan ba sai da dady yai addu’a akan Allah ya basu nasara sannan suka tashi suna jin dadin wannan shawarar da ya khaleel ya bada,

Washegari dady tun 2:00 na rana yaje gidan sarki dan tun safe ya khaleel yake kiran A.K Garkuwa wayarshi akashe rabonshi da shi tun jiya da sukayi waya da daddare ya fad’a masa yace badamuwa kai tsaye ba’n garensu A.K Garkuwa sukaje suka tadda shi shida mahaifinsa bayan sun gaisa suka fadawa mahaifin A.k, kabeeru Garkuwa na suna son ai musu iso wajan sarki,

Alhaji kabeer Garkuwa yace, yasalam anyi sab’ani sarki ya jiya jiyan nan ya tafi umara sai yayi kwana 12 xai dawo sai dai kuyi hkr Ku jirashi nan da kwana 12 jikinsu asanyaye suka dawo nan ma lallashinsu yayi yace kwana 12 kamar gobene in  Allah yasa muna da tsawon rai, jikinsu yai sanyi Dan gani suke kamar baxa suga iyayensu ba, dady ya kwantar musu da hnkl da nasihohi,

Bayan kwana 9

Saura kwana 4 d’aurin auren ya khaleel da jidda, kullum cikin fita unguwa suke dan tunda sukaxo itada ummanta basu koma ba sauran ne suka koma suma jiya suka dawo aka fara shirye shiryen biki, kullum kafin dady ya fita sai yai musu nasihan kada su biyewa k’annansa Dan yasan mafad’a tane kullum sai sun yadda musu da mgn, babu mai kulasu sulthana ce mara hkr dalilin dayasa momy tace ta dawo b’angarenta duk inda ta xauna sulthana na kusa da ita sbd gudin rigima,

Jannat na kwance adakinta xuciyarta cunkushe tarasa me ke damunta tun safe ta kasa fita jikinta duk yayi sanyi, turo k’ofa akayi tayi tunanin ko su Hindu ne shiyasa bata waiwaya ba, fusgo hijab din jikinta taji anyi da sauri ta waiwayo had’e da mikewa ta kallesu hantar cikinta ta kad’a sbd tsoro ta bisu da wani irin kallo cike da firgici,

Jidda ce zahra da umman jiddan, suna mata wani matsiyacin kallo,

Umman Jidda tai guda ta dingure mata kai, to Yar tsintuwa jikar bola kin mike agado kamar na ubanki, kin kwaso tarkacen bola irinki y’an’uwanki kin kawo gida sbd kuna son maidamin Yaya irinku to shi Dan asaline kowa yasan kakan nin kakaninsa, Jidda tace hmm, ummana ni kadai nasan bakin cikin dana keji inna kalli wannan a matsayin kishiyata Mara galihu wacce bata da asali gayyar tsiya, wllh momy sam yarinyar nan bata dace da ya khaleel ba da su danjuma ta dace talaka irinta,

Zahra ta katseta, ina bakin cikin ace wannan itace matar ya khaleel dole na yadda asiri sukai masa, ummanmu plx ki karya sihirin nan ya rabu da shegiya mu huta nifa na fison ace yayana ya auri Yar wani k’usa a garin nan ko Anty Jidda amma ya b’ige a Mara galihu mtsww,

Umman tace barni da shegu ni ce maganinsu sai na karya bakin asirinsu, Jidda ta karasa da sai ako mawa danjuma dan tun farko shi naso ki aura, suka fice bayan sun gama mata cin mutunci,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tagumi tayi tana xubar da hawaye masu xafi da kuna, kuka mai daci ya kufce mata taitayin shi har sai da  kanta ya fara sarawa ta dauki kur’ani tana  karantawa a hnkl a hnkl tafara jin saukin radadin da xuciyarta takeyi, ta Dade tana addu’a akan Allah ya kawo mata sauki cikin al’amuran rayuwarsu, karar wayar ta taji ta kalli screen din wayar ta ga ya khaleel ne haushi ya kamata taga duk danshi ake mata wannan cin kashin ta kyale taki dagawa har wayan ta yanke, ta tsurawa wayan ido tana tunanin any’a kuwa ta kyauta ? Tasan ba shi yai mataba, tayi ajiyar xuciya tana ganin tayi babban kuskure na  k’in  d’aga wayarshi da tayi motsin bude kofa taji anyi da sauri ta kalli kofar atsorace, ya shigo, yana kallon fuskarta da tasha kuka, tayi jaja jaja ya karaso inda take ta sunkuyar da kanta ya xauna kusa da ita, ya janyota jikinshi ta saki ajiyar xuciya, cikin muryar lallashi, me ya sameki ? Tayi shiru tana tunanin amsar bashi, kuka ya kufce mata da ta tuno bakaken magangun da su jidda sukai mata, lalashinta yayi yana tunanin ko damuwar rashin iyayenta ne, shi kanshi yana cikin damuwa ta rashin ganin iyayen nasu daurewa kawai yakeyi, nasiha ya cigaba da yi mata, har sai da jikinta yai sanyi ta daina kukan ya xamota daga jikinsa ya shafa cikinta, kinci abinci kuwa ? Kai ta daga masa, anya kuwa beautyna cikin nan naki baiyi kama da Wanda ya ci abinci ba, ya mike yana kallonta, ina jin yunwa ki kawomin abinci hade da coffee ina jiranki ya fita, ta mike jikinta asanyaye ta tashi ta tafi kitchen,

Jidda ce take ta safa da marwa daga sama xuwa dining ganin momy da sulthana sun hau sama yin sallah sai Hindu kad’ai suka bari a falo yasa ta faki idonta ta d’ebe abinci a flask cikin sauri ta fita waje da shi ta d’auko d’aurin maganinta ta barbarda tai b’angaren ya khaleel kai tsaye ta shige dakin cikin bacin rai ya kalleta, meke damunki Jidda ? Meyasa vaki iya sallama ba in xaki shigowa mutane daki ? Da sauri ta juya aranta tana fadin xaka gane kuranka na kusa rama wulakancin da kk min in dai kaci abincin nan sallama tayi ya amsa kamar bayaso ta shigo ta ajjiye abincin yana tsaye kusa da kofar toilet dinshi, ta kalleshi ya khaleel abinci naka wo maka,

Ok ajjiye wanka zan shiga kije ngd,

Tayi narai narai, ya khaleel na dawo to anjima?

Kan sa ya daga mata ya shige toilet bata so ba ta fice daga dakin tana murnan yau xata sami kan ya khaleel da murna ta hau sama dan tabawa ummanta da sauran yan’uwanta lbrn ta xuba maganin

Bayan ta xuba masa abincin ta wuce kitchen ta hada masa coffee ta nufo bangarensa tayi sallama ya amsa hade da xubawa k’ofar ido ta shigo dai dai lokacin daya ke xuba abincin da Jidda ta kawo masa a plate ganinta yasa ya ajjiye, ta kalli abincin tasan Jidda ce ta kawoshi ta b’ata rai had’e da turo baki, dad’i ya kamashi ganin tayi kishinsa sosai, sorry beautyna ina jin yunwa ne sosai, bata ce masa komai ba ta xuba mishi nata avincin ta mika masa ya amsa ta xuba masa coffee sai da ya fara shan shi sannan yaci abincin suna hira jefi jefi, kwatsam kamar an jehota ta shigo ta gallawa jannat harara ganin yana cin abincin dake duk iri d’ayane yasa ta lumshe ido tana jin dadi, tsawa ya khaleel yai mata, baki da hnkl ? Ki dink’a shigowa d’akin mutane ba sallama, murmushin samun nasara tayi ta fice batace masa komai ba,

Bayan yagama cin abincin jannat ta d’auki flask din da plate da cups din da tashigo dasu ta fita tabar abincin Jidda anan, murmushi yayi ya bita da kallo dan tunda ta shigo taga abincin jiddan take bata rai daukar abincin yai ya fito harabar gidan dashi ya ci karo da danjuma dayake wanke kayansa,

  “Danjuma Dan Allah ga wannan abincin kabawa almajirai,

Jikin danjuma na rawa ya amsa Dan dama yunwa yakeji ya ajjiye wankin a ransa yana fadin gani kuma wanne almajiri xan nema, sbd gaggawar yaci abincin ko bissmillah baiyi ba ya fara cinshi da sauri da sauri kamar wnda xa’a kwace mishi ya cinye abincin tass dai dai da kashin naman sai da ya taune da kyar ya xubar da dusar k’ashin yasha ruwa yai hamdala ya shige d’akinsa ya kunna redio yana sauraro wani nannauyan bacci yai awan gaba dashi

Bai farka ba sai gab da sallar magrub, yana farkawa yaji duk duniya babu wacce yake son gani irin Jidda ya mike da sauri daga kwancen dayake ya fito kai tsaye falon gidan ya shige suna falon dukansu ita da ummanta ta yayyan mahaifiyarta su Hajiya Aisha yana hada ido da jiddan yaji kamar Ankara masa sonta kai tsaye kusa da ita yaje, ya takarkare ya fashe da wani irin axababben kuka da sauri suka kalleshi, umman Jidda tace lafiya kuwa kake danjuma yak’i mgn ya cigaba da rusa kuka da k’arfi haka ysa ya janyo hnklin y’an gidan sukayo k’asa dukansu harda dady da yayi alwala xai fita sallah shida khaleel, da sauri dady yake tmvyr danjuma dalilin kukan fur yaki mgn sai da khaleel yai mishi tsawa, cikin kuka danjuma yace INA MASIFAR SON JIDDA IDAN NA RASATA WLLH MUTUWA ZANYI, arikice suke kallonshi kamar tababbe, Umma tace kan uvancen, danjuma waye sa’anka anan ya rushe da wani savon kukan dayafi Wanda ya fara tun farko Hajiya hadiza ki taimaka min ni kad’ai nasan me nakeji da gudu ya nufi center table ya dauko wukar da ake yanka tuffa ko lemo ya ce, muddin kuka hanani Jidda kashe ta xanyi na kashe kaina caraf ya ruko ta yasa wukar dai dai wuyanta, Jidda ta fashe da wani mahaukacin kuka gaba d’aya sukayo kanshi, ummanta na kuka sosai, Dan danjuma babban hauka yakeyi, dady yai shiru yana naxarinsa, da muryar lallashi yace, tun yaushe kafara sonta ? Ya kalli dady hawaye na xuba yace yanxu bayan na tashi daga bacci,

Mmkin su ya karu nan da nan suka yadda danjuma ya haukace,

Dady ya kuma cewa, kafin ka kwanta kayi shaye shaye ?,sanina baka shan kwaya danjuma,

Girgixa kai danjuma yayi ko kad’an alhaji bana shaye shaye abinci kawai nasan naci kuma megida khaleel ne ya bani shi,

Wani k’aton ashar umman Jidda tayi ta kalli khaleel, a kidime shi kabawa abincin da Jidda ta baka? D’aga mata kai yayi cike da mmki dan duk sun rikici, d’ora hannu tayi aka wayyo na shiga uku ni hadiza, itama Jidda kuka tasaki da k’arfi, ummana  naga da sunan Ibrahim a kai aikin, nan kowa ya fahimci abinda ya faru cike da bak’in ciki Mara misaltuwa dady yace innalillahi wa inna ilaihi raji’unn, danjuma meye sunanka na gsky,

Muryarshi na rawa yace iro Ibrahim sunana, da mugun bacin rai dady yace yaci sunan sihirin da kukayi yayi aiki dame irin sunan  wllh sai Jidda ta aureshi, ya kalli shi danjuma anbaka ita

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]