[Advertisements⬇️]

DOGON YARO BY JAMCY - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

*🌴DOGON YARO🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 1*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

30/6/2022

Bismil-lahirrahma-nirrahim.

Matashin Yaro ne wanda be wuce shekaru 19- 20 ba, sanye yake cikin ƙananun kaya jar riga da baƙin wando sai hula hana sallah da ya kifata tayi masa rumfa akan fuskar sa, pink lips ɗinsa ne sukafi ɗaukar hankalin me kallonsa a daidai lokacin saboda yadda yake motsasu yana yin fito a hankali.

Wanda ke gefensa ne yace, ” DOGON YARO wannan jan ajin naka fa bashida ma’ana anan gurin dan ba’a gaban ta bane”

Sassayan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa yayi taku uku cikin nutsuwa da kuma cika, sannan ya fara magana, “idan ban dawo da rai ba fa karkiyi kuka”

a ɗaya bangaren Zeety tace, “bana son irin wannan maganar a bakin ka Jan nasan ba’a nasara akanka karka manta fa koda yaushe tsawo kake ƙarawa baka gajarcewa haka a kowane lokaci sama kake ƙarawa a wannan karon ma idan kabari, Na’im yayi nasara akanka?? ai kasan kwanan zancen ko??”

ƴar Dariya yayi kafin yace, “idan kuma nayi nasara wace kyauta ce tawa???”

Murmushi me sauti tayi tace, “sai ka dawo”

Murmusawa yayi yace, “ban yarda ba”

Daidai lokacin ya isa gurin motarsa abokansa dake gurin suka buɗe masa motar ya shiga mazaunin direba, Na’im ya bashi hannu sukayi musabaha yace, “Dogon Yaro gudun kere sa’a yau za’ayi dan haka karka bari wannan koɗaɗɗiyar yarinyar ta hanaka ƙoƙari”

Dariya yayi yace, “ashirye nake, haba ai ko tana motar kasan mahaifiyata ce kawai zan ɗauka a motata na saurara duk dattin kanka baka kaini kasada ba kaima ka sani, (na rabaka)”

Ihu suka sa tareda faɗin “sai da kai DOGO Jancy”

Shikam dariya kawai yakeyi sai da ya rufe motar ya gyara zama sannan yace, “wai kina saurare na kuwa??”

tace, “ina jinka suna ta fasa maka kai ko?? shiyasa kake wani ƙara jin kanka”

yayi dariya kafin yace, “Shikenan Naji kuma na yarda sai na dawo ko?”

Tace, “Allah ya tsare”

Wauta da zallar ƙuruciya suke gwadawa akan babban titin wanda babu mutane sai tsilli tsillin ababen hawa haka suke zuga gudu tareda ƙiriniya ba tareda tunanin rai da lafiyarsu ba,
Yau ma kamar kullum Jancy ne ya take wasan ta hanyar yiwa Na’im fintinkau.

ko tsayawa ya saurari surutai da koɗashin da sukeyi beyi ba ya wuce gida dan kuwa hankalinsa yayi can.

Da gudu ya shiga layinsu ba tareda ya saurara ba kai tsaye ƙofar gidansu ya dosa, wata ƴar budurwa ce take tafiya a hankali kanta a ƙasa. ba tareda tunanin komai ba yayi kanta da motar tareda danne ƙararrawa. ihu ta fasa tareda dafe kai ta rintse ido da ƙarfi.

Ƙiris ya hana yayi sama da ita sai yayi gefe ya tsikara parking ya fito ya nufo inda take cikin ƙasaitaccen takunsa.

Jin shiru bataji ta a lahura ba yasa ta buɗe ido a hankali tana son fuskantar inda matsalar take, tafa hannuwan sa yayi a bayanta tareda cewa, “gani nan”

firgigit tayi ta tsallake zuwa gefe tana zazzare ido, ya tuntsire da dariya kafin yace, “matsoraciyar banza sai shegiyar yanga a titi yangar kwalba ba mai”

Murguɗa baki tayi tace, “lallai ma wallahi kaci mutunci kaci zarafin ka raina kima da daraja ka latsawa tsorona basirarsa”

Gaba yayi yana dariya yace, “idan kin gama gaya musu sai ki shigo ciki ko?”

Bin bayan sa tayi tana murguɗa baki, a falon Ummi tana tsaye cikin kiɗima tana zarya, ganin sun shigo suna raha yasa ta sauke ƴar ajiyar zuciya fuska a tsuke tace, “halama ba a hayyacin ki kike ba?? kin dokawa mutane ƙara haka kinsa hankalina ya tashi na zata ma wanine ya taɓa ki”

Ta turo baki tareda cewa, “Ummi wallahi Jancy ne yayi kaina da mota saura ƙiris ya buge ni kuma gudu yake ko shafata yayi da ita inaga bazan rayu ba”

Maida kallonta tayi kansa cikin sanyi tace, “Jannah kasan adadin ƴaƴan da na haifa suka mutu kuwa?? ku biyu ne kawai nasan daɗin ku banaso ku dinga wauta da rayuwarku dan nima inason na dinga buɗe ido in ganku”

Jancy ya murmusa tareda ringumeta yace, “Nan? mu rabonki ne tinda har muka kawo yanzu, da ace ba me tsawon rai bane ni Ummi kin fini sanin adadin shekarun mutuwa ta a yanzu, ina fatan na sameki lafiya”

Taja numfashi ta sauke tana murmushi tace, “madallah da kai Jannah ina lafiya lau”

Yace, “to ki dena damun kanki da ihun Magen Ummin nan”

da sauri tace, “eh kai kuma Muzurun Aba ko??”

Dariya yayi yace, “amma dai kinsan Mage tafi kalar mayu daman”

Zatayi magana Ummi tace, “Natiee zo ki kalmashe min gashin nan dan Allah na gaji da rashin kitso”

Kafin Natiee tayi wani motsi tini Jan ya dira a bayan Ummin yana cewa, “me zakiyi da kitsonta Bayan ina nan Ummi salon ta gwaguye miki gashi”

Ummi ta murmusa tace, “naga ai ka ƙi tsayawa kayi min ne shiyasa”

a tsiwace Natiee tace, “gaskiya Ummi ya tashi nayi miki da can da kike son yayi mikin ba ƙi yayi ba sai yanzu ze dawo yace zeyi ai kuwa baka isa ba, kullum fa shine yake miki kitso idan nace zanyi sai ace aa gaskiya nidai Ummi yau nizanyi miki”

Jancy ya harare ta sama da ƙasa tareda cewa, “iyee???? eh lallai to bazakiyi ɗin ba idan kuma kinada ƙarfi kisamin duka”

Ummi tace, “kunga banason kace kacen nan naku Natiee jeki ki kawo masa abinci”

Juyawa tayi tana cewa, “ai kuwa lokaci nagaba nice zanyi mata kama dena murna”

Kafin tayi nisa yace, “kinga ni bazanci komai ba sai Abana ya dawo dan haka ki dawo ki zauna”

Komawa tayi ta zauna tana kumburo baki.
Ummi ma taɓe baki tayi dan tasan dama ba lallai ya cin ba.

Shiru ce ta biyo baya har na ɗan wani lokaci. Jan ne ya katse shirun da cewa, “Ummi wai da yaya kikafi wannan ɗiya gashi subhanallah ko ni na zuciya sai na tara gashin da ya ninka nata oohh ga son iyayi ga muni Allah yaban mata kyakkyawa kamar Ummi na ba kamar ta hannun dama na ba”

Ummi dai dariya tayi tace, “Allah ya shiryeka Jannah ka fiye neman fitina”

Natiee kuwa ƙara murguɗe baki tayi tace, “barakallah masha Allah maye yaci kansa, kuma wallahi kasan babu matar da zaka aura wadda zata fini kyau”

Yace, “haba ƙanwati yawa ne kike wallahi kinsani dai”

Tace, “ba wata yawa ko a mafarki bazan yarda ba, ko ita wannan diddigar larabawan da ka mayancewa kasan wallahi na fita komai kuma a banida gashin dai nawa ya ninka nata sau uku amma a hakan ka ganta ka ƙyasa bare kuma ni”

Dafe kai yayi tareda cewa, “ahh? Natiee abun kuma tonon silili ya koma??”

Ummi tace, “ina gida a zaune ashe har kafara jawomin magana??? bari to Aban naka yazo zan gaya masa aure kake so”

da sauri Yace, “Ummi dan Allah kiyi haƙuri kuma yarinyar nan ƙarya take kawai dan ta haɗa mu faɗa ne”

Ido Ummi ta zubawa Natiee, kawai sai ta sunkuyar da kai dan kuwa duk abunda ze ɓatawa ɗan uwanta da mahaifiyarta rai bata ƙaunarsa.

Ummi ta murmusa sannan tace, “Jannah!! sa albarka akanku shine muradina a koda yaushe, ina fatan Allah ya haɗa ka da abokan mu’amaka nagari”

Natiee ce kawai ta amsa da “amin” shi kuwa shiru yayi dan kunya ta gama ritsa shi yasan dai Ummi ba yarinya bace ya tabbata ta gane komai kawai tayi musu kwance kwance ne”

Da yake kitson nata ba wani aiki bane manya manya ne guda shida kawai yayi mata dan haka ba wani ɓata lokaci ya gama ya tashi.

Kai tsaye ɗakinsa ya nufa kan gado ya faɗa tareda sauke numfashi ya lumshe idonsa yana ambaton “La’ilaha’illallah” ya kai tsawon minti biyu yana kwance kafin ya miƙe cikin sanyin jiki ya nufi ɗakin wanka yana tafiya yana lumshe ido.

koda ya fito a gaban madubi ya zauna yana ƙarewa kansa kallo murmushi yayi tareda shafar kansa sannan ya fara shiryawa cikin nutsuwa da kamala tareda tsantsar haiba,
mayuka da turaruka ya mulka sannan ya nufi ma’ajiyar kayansa ya fito da wata riga iya guiwa me maɓallai sai ɗan guntun wandonta.
Sai da yaƙara fesa turare sannan ya koma bakin gado ya zauna tareda janyo wayarsa yafara dannawa cikin nutsuwa, ɗan bakin nan nasa a tsuke kamar ba shine ya gama surutu ba.

Natiee ce ta shigo tana cewa, “kun fara jarabar ko??”

Ba tareda ya kalleta ba ya murmusa cikin muryarsa me matuƙar ɗaukar hankalin me sauraronta yace, “bamu fara ba tukunna”

Tace, “ai nasan bakuda aikin da ya wuce waya ne narasa ma me kuke cewa”

Yace, “ina ruwanki?”

Tace, “na shanye”

Yace, “banida damuwa da hakan”

Banza tayi masa ta dawo kusa dashi ta zauna, a hankali tace, “Jan? yau ma tsere kaje kayi ko?”

Sai a lokacin ya ɗago fararen idanunsa ya ɗora akanta tareda motsa pink lips ɗinsa yace, “eh”

Tace, “ai dama na sani ɗan kasada kawai”

Murmushi yayi gami da maida hankalinsa kan waya kamar baze magantu ba sai kuma yace, “babu wanda ya neme ni??”

kafin ya gama rufe baki tace, “eh kuɗi ne kai da za’a wani neme ka?? me za’ayi da kai??”

Jinjina kai yayi yace, “wai me nayiwa ƙanwata ne yau??”

Gyara zama tayi tana cewa, “anzo gurin hakan nakeson ji, wato ainafin sharaɗi zan saka nan gaba idan Ummina ta warware gashinta nice zanyi mata kitso sannan kuma yau banaso kaje wajen Zeety ka zauna a gida karkaje ko ina”

Shiru ya ɗanyi kafin yace, “haka ne?”

Tace, “eh ɗin”

Yace, “zanyi hakan”

tace, “yauwa ko kai fa? yanzu dai babu wanda yazo nemanka amma nasan zasu zo yanzu ma kuwa ka shirya”

dummm dumm dumm zuciyarsa ta shiga harbawa a take yanayinsa ya canja cikin sanyi yace, “Natiee kin tabbata?”

Cikin tausayawa tace, “abunda ya zama wajibi ne shiyasa kaji na faɗa”

Lumshe ido yayi tareda jan numfashi, ko saukewa beyi ba kuwa yaji ana ƙwala masa kira DOGO!!!! DOGO!!! DOGO!!!!!!.

Shafar kansa yayi tareda rintse idonsa da ƙarfi yana ambaton sunan Allah a cikin zuciyarsa.

Natiee tace, “Jan ka tashi kaje tin kafin yazo ya sameka”

Girgiza kai yayi tareda cewa, “aah bazani ba”

Cikin marai-raicewa tace, “Dan Allah Jannah katashi”

Ummi ce ta faɗo ɗakin kamar anjefo ta, a kiɗime tace, “Jannah tashi kaje mana!! ko kafi so azo aci zarafinka a gabana????”

Miƙewa yayi tareda girgiza mata kai alamar “aa”
Kamar zata fashe da kuka tace, “Jan? me kayi yau kuma? meyesa baka gujewa ɓacin rai?”

Rungumeta yayi tsamm cikin rawar murya yace, “Naan”

tace, “kayi sauri fa”

janye jikinsa yayi daga nata ya nufi waje, yana fita daga sashin yayi karo dashi.
Cikin hargowa yace,………….

 

 

 

Share fisabililah.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem.
*INDO CE..*
[10/20, 2:38 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 2*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

“Ban hanaka zuwa kayi mana parking ɗin banza ba?? kai ba’a isa a faɗa kaji ba ko??”

Ƙasa yayi da kai cikin ƙunar zuci yace, “mantawa nayi”

Wasu kyawawan maruka ya zuba masa lafiyayyu har uku sannan yace, “ni zaka gayawa ka manta?? ni zakai wa rashin kunya kai ga ɗan iska ko?”

wani marin ya ƙara haɗa masa yana huci Fauzy da take gefe tace, ” ƙara masa wallahi Faisal mara tarbiya dama ya gama yimin rashin kunya ɗazu”

Jancy da yayi ƙasa da kai cikin son kare kansa yace, “kayi haƙuri dan Allah”

a harzuƙe Faisal ya ƙara hawa kansa da tafka har saida gefen bakinsa ya fara jini saboda azabar marukan da yake watsa masa na rashin tausayi da rashin imani.

Sai da ya gaji da dukansa sannan yace, “ba zakaje ka gyarata ba kuma?? saboda kai kaɗai ne ɗa a ɗauki wannan danƙareriyar motar anbaka, sai nasa an faffasa ta ma kowa ya huta”

Jiki na rawa Jancy yayi waje a kiɗime ya manta ma yabar mukullin a ɗaki, Natiee ce ta miƙe tana sharar ƙwalla tace, “Ummina bari na kai masa mukullin”

Ummi kasa magana tayi kanta na ƙasa tana wasa da zubukan yatsunta idanunta da suke zubar hawaye ma kawai sun isa nuna irin raɗaɗi da zugin da takeji, maganin kar ya shigo tayi ido huɗu dashi sai ta tashi ta koma sashinta, a bakin gado ta zauna ta fashe da kuka me tsanani ban tausayi.

kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Natiee take tafiya har ta isa gashi, shima ya tawo da nufin ɗaukar mukullin suka haɗu, karɓa yayi da sauri ya koma ya shigo da motar.
yana ajiyeta Kai tsaye ɗakinsa ya wuce sai da yasa mukulli ya kulleta gam sannan ya zame a gurin ya fashe da kuka me tsuma zuciya.
Allah me yadda yaso bashida wata damuwa a duniya wadda ta wuce ƴan uwansa mahaifinsu ɗaya amma sun maidashi kamar shaiɗan sun tsaneshi basa ƙaunar ganinsa kowannen su bashida burin da ya wuce ƙaga masa sharrin da ze jawo masa ƙuntata da ɓacin rai shi kuma tashi ƙaddarar kenan.

Ya daɗe yana kuka a gurin har ya gaji ya dena sai kansa da yake masa wani azababben ciwo, sai da aka kira sallar Magrib sannan ya tashi ya ɗauro Alwala.

Bayan ya idar da sallar ya ɗakko Alƙur’ani ya shiga karantawa cikin nutsuwa tareda fatan samun salama daga zafi da ƙunar da zuciyarsa takeyi.

Sai da yayi sallar isha’i a wajen sannan ya tashi yana ƙoƙarin kwantawa yaji murya Abansa yana kiran sunansa.
Da sauri ya tashi ya buɗe yana murna.

Hannu Aba yasa ya tallafo haɓarsa yana ƙare masa kallo cikin tausayawa yace, “Yaro!!! fuskarka tayi jajur shatin yatsune sosai akanta waye???”

Ƙasa yayi da lumsassun idanunsa hakan ya bawa hawayen da suka cicciko damar ɗigowa.

Aba yace, “mahaifiyarka ta kasa gaya min kaima haka??, Meyesa kuke son ɓoyemin abunda ya shafeni? ƴan uwanka ne ko??”

Faɗawa yayi jikinsa ya ƙanƙameshi sosai cikin harshen fulatanci yace, “Abana meyesa basa sona wane laifi na aikata musu da suka tsane ni? kenan kuskure ne kasancewata ƙaninsu??”

cikin sanyi Aba yaja hannunsa ya zaunar dashi sannan yace, “ba kuskure bane sune dai suke aikata kuskuren kayi haƙuri ka jure komai wata rana sai labari, ka gaya min waye ya taɓa ka yau?”

Girgiza kai yayi yace, “aa Abana dani dasu duk abu ɗaya ne suyi komai kawai lokacin su ne karkace musu komai, amma kasani akwai ranar da zata zo wadda ko yatsa ɗaya daga cikin su ya nuna min sai na karya yatsan”

Ya ƙarashe maganar cikin shashshekar kuka tareda tsananin ƙunar zuci.
Ummi da ta shigo yanzu ce ta daka masa tsawa da cewa, “kulll Jannah!!!!! karka bari naƙara jin makamancin irin wannan furucin daga bakinka, ko Jaafar shine autansu kuma kasani sama yake da kai ban yarda kayi rashin kunya wa yayyen ka ba koda da minti ɗaya suka girmeka, banaso”

Aba yace, “bazeyi ba ma dan ba halinsa bane amma ni zanyi ruwa da tsaki a ciki tinda ni na isa dasu”

da sauri tace, “banaso fa idan kayi musu faɗa duk akansa zasu juye raina ne ze ƙara ɓaci a banza”

Jinjina kai Aba yayi yace, “Yaro!! bana son ganin kana kuka kayi haƙuri ka dena ai na dawo”

Lafewa yayi a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya akai akai, Aba ya goge masa ƙwallar da tayi shaɓe shaɓe akan fuskarsa yana yi yana hura masa iskar bakinsa a hankali, hakan da yake masa kuwa ba ƙaramin daɗi yakeji ba ajiyar zuciya har har bibbiyu yake haɗawa kamar ƙaramin yaro.

sai da ya samu nutsuwa sosai har bacci yafara shirin ɗaukarsa sannan Aban yace, “tashi muje kaci abinci”
Ba tareda yayi magana ba ya tashi..

lokacin da suka fito Ummi ta gama shirya musu abincin dan haka suka zauna kawai,
Kamar kullum a baki Aba yake bashi yana ci kaɗan kaɗan yana yi yana shagwaɓa.

 

 

Share fisabilillah.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:39 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 3*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

Sai da Aba ya tabbatar ya ƙoshi sannan shima ya ci, bayan sun kammala Aba yace, “Yaro ina fatan dai ba wani abun?”

Yace, “Abana bana rabo da ƙorafi wallahi fita nakesonyi kuma waccan farar yarinyar ta hanani ”

Aba yace, “wa kenan ba dai Fauziya ba?”

Da sauri Ummi tace, “wace fa idan ba karkatacciyar kuka ba? tayi ma bacci ita idan zaka fita ka fita idan kuma bakai niya ba to, ko gurin wa ma zakaje a daren nan oho”

yayi ƴar dariya sannan yace, “Nan!! ina namiji idan ban fita ƙarfe taran dare ba waye ze fita?, Aba bar zancen kawai bazan fitan bane saboda nayi mata alƙawari kuma banason saɓawa”

Aba ya murmusa cike da farin ciki yace, “masha Allah ina matuƙar farin ciki da jin daɗin irin kulawa da ƙaunar da kake bawa ƙanwarka Harma da yayyen ka guda uku wanda sune suka kasance fansar sauran ƴan uwan naku a gurina, inada tabbacin ko bana raye zaka iya kulamin dasu indai da ranka da lafiyar ka, ina ƙara jaddada fatan alkairi na gareku baki ɗaya Allah ya yi muku jagora a duk lamuran ku”

Cikin jin daɗin addu’ar ya amsa da “amin Abana abun alfahari na, insha Allah bazaka mutu kabarni ba zamu rayu tare”

Aba yayi murmushin manyance ba tareda yayi magana ba .
cikin harshen buzanci Ummi tace, “Jannah! kaje ka kwanta dan Allah gobe litinin fa zaka tashi da wuri”

beyi musu ba ya tashi rungume Aba yayi yace, “Allah ya tasheka da rai da lafiya Abana”

Aba ya shafa kansa gami da cewa, “Amin Allah ya amsa tareda kai Yaron kirki”

Yana murmushi ya koma wajen Ummi itama rungumeta yayi yace, “Ummina karki manta kimin addu’a”

Tace, “Jan bazan manta ba”

Dariya yayi sannan ya nufi hanyar sashinsa yana tafe yana waiwayen su.

Ummi sai da ta tabbatar ya tafi sannan tabawa kukan da yake cinta damar fitowa.
Aba ya dawo kusa da ita ya zauna cikin tausayawa yace, “Aaminatu? meyesa zakiyi kuka? ni kuma yaya zanyi kenan idan ke da kika kasance ƙwarin guiwata kikayi kuka??”

Share hawayen ta shigayi tareda ƙoƙarin tsagaita kukan.
Janyota yayi zuwa jikinsa yayi mata masauki cikin sanyi yace, “Aamina kin jure kinyi haƙurin zama dani har lokacin nan, lokacin da mukejin ranar kukan mu ta wuce Allah ya azirta mu da ɗa kamar MUFTAHUL”’JANNAH amma ki zubda hawaye? meye ya ragewa rayuwar mu wanda ya wuce mu godewa Allah da ya bamu su? shine ya bamu kuma yasan halin da suke ciki kuma dukan mu muna gareshi ne duk abunda ya faru dani dake dashi dasu duka ma duk Allah yana sane kuma yasan me gaskiya yasan mara gaskiya koda ba a gidan duniya ba wata rana zakiga lokacin da Allah zeyi mana SAKAYYA (Littafin Gimbeeya) akan duk wanda ya zalumce mu, ƙwarara masa zuciya yakamata mu dinga yi ba mu raunana masa ita ba, dan Allah Aaminatu”

Shiru tayi tana sauraren sa har ya kammala sannan tace, “a koda yaushe idan da ɗan adam zeyi nazari? tabbas da ze gane lokacinsa kaɗan ne lokacin farin cikinsa ƙalilan ne, jiya ta wuce ɗazu ta wuce ko anjima bamu san ya zata kasance mana ba bare kuma gobe wannan sai Allah, kuma muna manta cewa mutuwa rigar kowa ce idan baka mutu ba to za’a mutuwar maka, za’a mutu a barka ko kuma ka mutu kabari bakasan halin da kabar baya ba, ina tunanin goben mu da ƴaƴan mu tabbas zuciyata tana gaya min akwai babban ƙalu bale da ɗanmu ze fuskanta a rayuwar sa ta gaba bayan na baya da ya fusjanta koma nace yake ka fuskanta kaga kuwa ni kuka ya kama idan kayi nazarin kalamai na zaka fahimci hakan”

Aba ya numfasa sannan yace, “wannan gaskiya ne Allah yasa mu dace ya iya mana akan duk abunda bazamu iya ba ”

Jancy.
har ya gama ƙalular sa da tunane tunane ya kwanta bakinsa ɗauke da addu’o’i yana shirin bacci yayi awon gaba dashi yaji wayarsa tana ƙara , kamar baze ɗauka ba tsoro da shakka yasa shi ɗaukar dan dole cikin sanyi ya kara a kunne tareda yin sallama.

A ɗaya ɓangaren Fahad yace, “kai Dogo zo kaimin wankin ƙananun kaya dallah,

kamar zeyi kuka yace, “nafa kwanta har nafara bacci ka bari sai gobe”

Cikin isa da gadara yace, “yanze nake so kuma idan kanajin ka kai kace ba zakai ba”

share ƙwalla yayi gami da cewa, “ina zuwa amma kana ina?”

Yace, “kayan suna sashin Hajiya Murja kuma kazo sashin mu kayi wankin banaso kasa a injin wanki kuma”

“to” kawai yace sannan ya tashi ya nufi sashin Hajiya Murja yana tafiya yana sharar ƙwalla, raɓewa yayi ta hanyar da yasan bazeyi karo da Aba ko Ummi ba.

Sallama yayi a falon babu wanda ya amsa har sai da yayi sau uku sannan Fauzi tace, “gafara dallah kazo ka cikawa mutane kunne da sallama kamar wani maroƙi ubanme zakai anan??”

Ƙasa yayi da kai sannan yace, “Yaya Fahad ne yace inzo inyi masa wanki”

Tace, “sai dai kaje ɓangaren su dan bayanan bazaka shigo ba”

Hajiya Murja ta murmusa a ƙasaice tace, “barshi ya shigo Fauzi me ze iya ɗauka koma me ze iyayi?? zo ka wuce ka ɗauka sai ka shiga sashin nasu yana ciki”

Cikin sanyin jiki ya shiga yana tafiya a hankali cikin tsoron yayi takun da ba dai-dai ba ya faɗa ruwa.

Jaafar da yake zaune yana danne dannen waya ba tareda ya kalleshi ba yace, “kai maza ka kawo min 30k idan ka koma”

Cikin ƙarfin hali yace, “saboda me?? me zakai dasu??”

Yayi ƴar dariya sannan ya cigaba da danna waya.
har ze wuce ya dakatar dashi da cewa, “dakata!!”

Tsayawar yayi yana sauraron abunda ze ce, sai da ya gama danne dannen sannan yace, “shagali zanje nayi nida budurwa ta kai harma da abokaina bani 50k kawai ina jiranka gobe kafin ka tafi makaranta zan karɓa kuma idan ka bari tsohonka ya hana sai na saɓa maka kamanni”

da ” to” kawai ya amsa dan baze iya yin jayayya dashi ba musamman anan da ya shigo tsakiyar su, wucewa yayi inda Fahad ya kwatanta masa ya ɗauki kayan sannan ya wuce sashin Hajiya Saratu.

Haka sukai ta ciccira shi har 12:00am sannan suka barshi ya koma sashin su lokacin bacci ya gama cin galabarsa.

Washegari da ƙyar ya tashi saboda bacci me nauyin da ya danneshi, sai da yayi addu’a sannan ya tashi ya nufi ɗakin wanka shower ya sakarwa kansa ruwan yafara dukansa yana ratsa shi a sannu a sannu ajiyar zuciya ya sauke gami da lumshe ido sannan ya shiga shafa sumar kansa ya a yamutsa ta, tunanin mafarkin da yayi a daren ne yake ta yimasa yawo aka ya rasa ina abun ya dosa ko kuma yake son zuwa amma yasan mafarkin ba shawai ɗin mafarki bane me hujja ne, ya rasa meyesa baya taɓayin mafarki me daɗi sai dai mummunan mafarki kullum, yana ganin abubuwa da yawa wanda ya kasa fahimta kuma baya son sanarwa wani irin munanan mafarkan dan yana matuƙar gujewa damuwar su.

ya daɗe yana tunane tunane kafin yayi wankan ya fito ya kintsa, lokacin da ya fito tini Natiee ta gama shiri dan kuwa tana tsoron barazanarsa idan ya rigata shiryawa ƙarshe ma baze bari tayi shiri me kyau ba.

Sai da ya tanadi kuɗin da ze bawa Jaafar sannan ya samu ƙwarin guiwar fita a wajen motarsa ya tarar da Jaafar ɗin yana jiran fitowarsa kuɗin kawai ya bashi ya shige mota dan bayason hayaniya bare tashin hankali duk abunda ze zamo matsala ba ƙaunarsa yake ba.

Zaune take a gaban madubi tana ƙarewa kanta kallo fara ce sol kyakkyawa sahun farko ƴar duma duma hannu tasa ta kwashe gashinta da ya bazu har kan fuskarta tayi baya dashi ta cigaba da kallon fuskart, Masha Allah, tana da ƴan saffa saffan idanu ba manya ba ba ƙanana ba farare sol sai ƙwayar idon da tayi sirki da brown color sai dogon hancinta irin wanda ake kira hanci har baka ɗan bakinta ɗan madai-dai-ci.

Cikin shauni tayi ƴar kwalliya mara yawa daga kwalli sai manbaki sai hoda.

Zahra ce ta shigo tana kiranta, ta amsa sannan ta cigaba da cewa, “na rasa ma da yaya zanje makaranta yau Zahra bani shawara mana”

Zahra tace, “kai Queen gaskiya Allah ya fiddake dai kawai, amma wannan kwalliyar duk akan wanda ko kallonki ma ba lallai yayi ba bare ya gani, Shawarar da zan baki kawai ki dena kwalliyar ma”

tace, “wallahi bazan dena ba son gaskiya nakewa Jan dan haka zan juri ko me zeyi min na rashin mutunci wata rana sai labari idan na mutu sai dai ace ai da Zuhra ta So Jancy sosai, to irin wannan tarihin nakeson kafawa a rayuwata”

Zahra tace, “banajin wata rana ma Jan ze kalle ki a matsayin mace, kinfiye zaƙewa da yawa ki tsaya iya matsayin ki tinda ya riga ya nuna miki iyakar ki”

Tace, “dena wannan maganar Zahra, banida iya tsakanina da Jancy babu wani layi da ze shata wanda ze shiga tsakani na dashi sonshi ba? to Yanzu na fara”

Zahra tace, “to naji amma ya zakiyi da masoyiyar sa da ya mutu akanta”

Zuhra tace, “Zeety!!!!!!…………”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:42 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 4*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

bazan iya cewa, “itace katanga tsakanina da Jancy ba dan na lura akwai rashin jito tsakanina dashi kawai ita ɗin tana matsayinta na wadda yake so ni kuma ina sonshi dan haka babu ruwa na da ita kawai bana yanke ƙauna da sa rai akansa”

Zahra ta jinjina kai tace, “Allah ya bada sa’a nidai ki tashi mu tafi kar kisa mu makara dan ke ba asara ce dake ba ni zaki cuta”

murmushi tayi ta tashi ta ƙarasa shirin a gurguje.

Idanunsa a lumshe ya kwantar da kai jikin makarin kujerar motar duk hankalinsa ya lula duniyar tunani.
Natiee ta cewa direba, ” yau ba sai ka ɗauki wannan matar ba kawai ka wuce”

Ba tareda ya buɗe idon ba yace, “Natiee wai meye abunda tai miki ne?? jiya kin hanani ganinta yau kuma kar a ɗauketa to akanki zata zauna??”

kallonsa tayi sama da ƙasa sannan ta taɓe baki ta basar.
murmushi kawai yayi batareda yayi magana ba.

Direba yace, “hajiya za’a dakko ta ko kuwa?”

tace, “eh kayi sauri dan Allah”

Suna isa gidan su Zeety suka tarar ta gama shirinta su kawai take jira dan haka babu ɓata lkaci suka cigaba da tafiya.

Tin a parking space sukayi katari da juna, tana ganinsa tayi saurin komawa ta laɓe a jikin mota,
Shi kuwa yama manta da ita a duniya tafiyarsa kawai yake yana tunanin abunda ya dameahi.
Zuhra kuwa tsoro ne ya lulluɓe ta da sauri ta ɗage hijab ɗinta rufe fuska dashi hakan ya bawa jikinta damar fitowa saboda hijab ɗin ba wani babba bane.

Dogon Yaro kuwa ɗaga idon da zeyi ya sauke su akanta duk da besan ko wacece ba amma abun ya bashi haushi sosai sai da yazo saitin ta sannan ya saki wani dogon tsaki wanda yasa hantar cikinta juyi.

A kiɗime tace, “kayi haƙuri wallahi banaso ka ganni ne nasan idan ka ganni ranka ɓaci zeyi”

Cakk ya tsaya ya dena tafiyar yayi jimm sannan ya juyo ya kasheta da rikitattun idanunsa, da sauri tayi ƙasa da kai jikinta har tsuma yake.

Ɗan tsaki yayi sannan yace, “ke bugaggiyar ina ce da zaki ɗage sittirar ki ki rufe fuska? halama kinfara hauka kuma? ai tinda na ga wannan shirmen nasan baya wuce ke buzur”

Cike da shakka tace, “kayi haƙuri dan Allah”

kallon baki kai ba ya watsa mata sannan ya cigaba da tafiya cikin takunsa na ingarman namiji, da ido ta rakashi tareda tunanin ranar da zata dena tsoronsa gashi yaro amma zubin matasan da suka bawa 29 zuwa 30 baya gashi da kwarjini kamar wani babba.
Murmushi ta saki bayan ya ɓacewa ganinta ita hakan da ta faru ma daɗi tayi mata dan wani lokacin sai tazo a bati ta koma a sadaka ba tareda ya ko kalli inda take ba duk da irin alayen da take masa.

Hajiya Saratu ce tsaye sai kai kawo take a falon cike da damuwa.
Hajiya Murja tayi sallama ba tareda ta jira an amsa ba ta nemi guri ta zauna,
Ganin Hajiya Saratu tarasa zaune tarasa tsaye yasa tace, “meke faruwa ne?”

dama jiran wanda ze ɓula mata take dan haka tayi saurin cewa, “meye ma baze faru ba Hajiya Murja? kullum yaron nan barazana yakewa rayuwata ina cike da tsoron lokacin da ze ida girma wallahi”

Tsamm tayi tana tunani zuciyarta ce ta buga da sauri ta kalli Hajiya Saratu tace, “wannan haka yake tabbas idan ya girma akan wannan tafarkin komai ya rushe mana”

Hajiya Saratu tace, “yanzu meye mafita dan gaskiya nafiki jin tsoronsa kinga wani irin kallon tsana da yake min kuwa? bazan lamunta ba gaskiya, gashi duk asirin da za’ai baya taɓa shi lallai Aamina ta haifa min ƙaddarata”

Hajiya Murja tace, “ya kamata kuwa mu ɗauki mataki dan yanzu ne yake tashen balaga wannan yaƙin ba namu ne mu kaɗai ba samun ƴaƴan mu zamuyi mu tattauna dasu yanzu sune yara sabon jini zasu fimu sanin makwanta dan haka zamu haɗa duk tuggu da zamu ga bayansa, ni baƙin cikina ma irin muguwar ƙaunar da Alhji yake nuna masa burina kawai na rabashi da uban nasa sai naga meye kuma ze rage masa dashi da uwar tashi, sai dai asiri ko tsafi ma baze musu ba, amma ina tunanin sharrin da baze fita ba zamu laɗɗafa masa wanda Alhji da kansa ze tsaneshi”

Farin ciki ne ya ziyarci Hajiya Saratu dariya gami da shewa tayi kafin tace, “shiyasa ina dake banada fargaba wannan yayi haka yakamata muyi tin farko amma bamuyi ba, yanzu ya kamata a buga wannan wasan kuwa wallahi.

Fauzy da ke gefe tace, “wallahi na tsani yaron nan ɗan iska kuma idon mutane gaba ɗaya akansa yake basa ta mu sai shi shi kaɗai ake ɗauka a matsayin ɗan Alhji ina baƙin cikin wannan wallahi”

Hajiya Saratu tace, “kwantar da hankaln ki yarinya ai tazo ƙarshe, maza ki sanarwa ƴan uwanki duk su hallara akwai tattaunawa”

Tace, “to”

Aba yana dawowa ya ɗauki wayarsa ya koma sashin sa ya samu guri ya kwanta akan kafet.

Cikin kulawa Aba yace, “YARO!!! idanunsa a lumshe batareda ya buɗe su ba yace, “Abana”

Aba yace, “baka gaya min meke faruwa a fannin kasuwancin mu ba”

tashi yayi ya zauna sannan yace, “Abana komai Alhamdulillahi yana tafiya dai-dai yadda ya kamata, ka duba Asusunka ɗazu na tura maka kuɗi”

Aba yace, “Masha Allah jajirtaccen Yaro bari na duba”

wayarsa ya ɗauka ya shiga dubawa ya bincika tsaff sannan ya kalli Jan a nutse yace, “ka tabbatar ka tura??”

Jancy yace, “ƙwarai kuwa Abana”

Aba ya sake yin nazari kafin yace, “zasu kai kimanin nawa?”

Cikin tsitstsinkewar magana Jancy yace, “Abana?? kar dai kace min baka gansu ba”
….

Aba yace, “eh hakane bangansu ba kodai ka samu kuskure ne wajen turawar?”

Yace, “aa Aba banyi ba gaskiya sai dai in wani ne yayi kutse cikin lamarin”

Hajiya Murja da take tsaye tana jinsu batareda sun san ta shigo ba tace, “madallah ɗannan lallai kanada ƙarfin hali ai kowa yaji yasan inda kuɗin sukayi waye yasan sirrin ku da zeyi muku kutse sai dai in kaine ka kutsa su a Aljihu ai kashe kuɗin da kake ma yayi yawa ina zaka same su in baka taɓa na wani??”

Alhji yace, “ya isa haka, banason fitina da tashin hankali ni ban haifi ɓarawo ba, ɗana ba haka yake ba sai dai in naki ɗan ba wannan ba, bansan ma menene ya kawo ki ba, ki wuce ki bamu guri keda bakyason zaman lafiya”

Tayi dariya sannan tace, “eh lallai yau naji kan Aba da ɗansa Allah ya sittira, gaskiya bakaji daɗi ba Dogon Yaro kai da tsohonka yana sonka yana baka kuɗin nan meyesa se kai masa sata?? wannan ai abun kaico ne sata bata dace da kai ba kaida ake nunawa ƙauna duk da dai dama irinku ɗin kunfi lalacewa, naji ance har ƴan mata gareka to ni dai Allah ya kiyaye min tawa karka lalatan ita tinda ka zama haka”

Tsawa Aba ya doka mata badan ta kai matsayar maganarta ba tayi waje ba shiri amma ko iya haka taji daɗi ko babu komai tasanya tsoro da ƙunci a zuciyar Jancy.

Cikin tashin hankali da razani Jancy yace, “wallahi Abana ni ba ɓarawo bane kuma ni ba lalatacce bane bansan ya akai ba amma ni ban taɓa kuɗinnan ba, kayi min komai dan haka banga dalilin da ze sa na zalumce ka ba Abana wallahi ba ni bane”

 

 

Comment and share saboda Allah.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:42 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

 

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 5*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

Aba yace, “hmm Jannah nasani sarai dan dai bakasan wacece wannan ba da bakai tunanin zan yarda da abunda ta faɗa ba, ka kwantar da hankalin ka mu fauwala wa Allah kawai karka shiga damuwa akansu”

Rausayar da kai kawai yayi ba tareda ya iya yin magana ba.
Jiki ba ƙwari ya tafi ya kwanta cike da tarin damuwa da tunane tunane.

A falon su Hajiya Murja kuwa sun gama hallara kaf mutum uku ne kawai babu FA’IZA HASSANA DA HUSAINA bayan su kuwa tin daga kan Salisu har kan Jafar sun gama haɗuwa.

Abdul ne yace, “wai Hajiya meke faruwa ne aka neme mu haka??”

Fauzy tace, “ɗan kutumar uba dama kana can kana shaye shaye taya zaka gane me ake nufi?”

Yace, “ke wallahi ki kama kanki ko na sama ki yanzu”

Ta gasa masa harara gami da jan dogon tsaki.

Hajiya Saratu tace, “kunga ba wannan ne ya kawo mu nan ba kun gane?? muna neman hanyar da zamu ƙwaci ƴancin mu ne ta hanyar da zamu ci galaba akan DOGON YARO”

Dariya Sultan da Haisam sukayi kafin Sultan yace, “sai yanzu kuka farga da hakan kenan? ai ni tin tini nagama tsarina akansa, a komai nasa gaba shine me tarwatsani yaron nan dan haka yanzu shi na sako a gaba, ko yanzu ma nayi musu kutse na mayar da kuɗin da ya turawa Alhaji zuwa banki na kunga yau anyi haka gobe anyi yau da kullum dole Alhajin yagaji sai kuma naga matakin da ze ɗauka akansa”

Haisam yace, “wannan yaron indai baka yimasa kare kare ba ai zaka mutu da baƙin ciki, Hajiya ni dai banaso ku takuri kanku ku cigaba da naku aikin ku barmu muyi namu”

Bomboi yayi tsaki sannan yace, ” ni tsohon nasa ma nakejin kamar na kashe wallahi, duk shine yake sangarta shi sai kace shi kaɗai ne ɗa wallahi da da yadda zanyi da tuni na ɓatar dashi”

Hajiya Murja ta rausaya sannan tace, “hee yaro kenan Dogon Yaro da ace shima me gajeren kwana ne kamar sauran ƴaƴanta da muka kashe da tini shima ba’a labarinsa, Allah ne kaɗai yasan abunda ya ɓoye a tareda yaron nan da har ya gagare mu wannan kaɗai idan na tuna yana bala’in tayar min da hankali”

Hajiya Saratu tace, “muna zaune ze tarwatsa mu ko a yanzu ya gaje komai bare ya kai lokacin da yakejin ya isa? ai abun baze mana kyau ba, dole mu tureshi kodan mu ji daɗin rayuwa”

Miƙewa Hawaz Yayi tareda cewa, “Sultan da Haisam fa sunai muku nuni da cewar karku damu dan haka ku barmu kawai ni nayi hanya ta”

Bomboi yace, “aikuwa zamu ƙare a haka wallahi haɗin kanmu shine mafi alfanu garemu a yanzu indai bamu haɗa kai ba babu yadda za’ai mufi ƙarfinsa shi mutum ɗaya ne amma yafi ƙarfin goma bare wasu ƴan tsirarin mutane, a shawarce mu haɗe kai wallahi”

Fauzy tace, “wannan gaskiya ce ba shakka idan bamu haɗe kai ba mu zamugani”

Hajiya Murja tace, “ai dalilin hakan ne yasa muka taraku, mu haɗe duk wanda yake son dukiyar ubansa yabamu haɗin kai”

Faisal yace, “kanmu a haɗe yake kuma zamu cigaba da hakan yanzu dai kowa yaji abunda aka faɗa dan haka mu watse tin kafin Alhaji ya shigo”

Da haka suka tashi kowa da irin mugun ƙudurinsa akan Jannarh.

Natiee tana zaune a falo tana kallo Jancy ya shigo yana sanɗa har ya wuce ta batareda ya lura da ita ba tace, “ina kaje???”

Ɗan firgita yayi ya zaro ido sannan ya juyo fuska a haɗe yace, “ina ruwanki??”

Ta kwashe da dariya sannan tace, “ga tsoro ga ban tsoro ai ni abun ne ya tashi kaina ka fita da sittirarka tsaf ka dawo da singileti da kamfai tsamo tsamo da kai ko suma kayi kyautar su?”

zama yayi kan kujera sannan yace, “eh meye amfanin su to? wani ne yace yana so shine nabashi kuma sai akai me? naki ne ko nawa?, marowaciya kawai ke in mutum ya biye muki bazeyi alkairi ba”

Ta taɓe baki tace, “ba nawa bane amma dai an bada maza da kayi karo da Yayyen ka ma cewa zasuyi daga gidan karuwai kake, kai dai garin bayarda abunka ga wasu wata rana ma har ranka zaka nema ka rasa”

A miskilance yace, “ranka kikace dama ba ranki ba dan haka ki rufen baki”

Tace, “naji ni dik ka isheni da magana kasa bana fahimtar ma abunda nake kalla ”

Yatsine fuska yayi kafin ya ciro wayarsa ya turawa Zeety kira ba jimawa kuwa ta ɗauka.

miƙewa Natiee tayi tana zumɓura baki tace, “idan kun gama na dawo ”

Dariya kawai yayi gami da ɗaga mata hannu.
Kai tsaye kicin ta nufa tafara taya Ummi aiki.

“Jannah yadawo ko?”
Ummi ta jefa mata tambaya.

Tace, “kinji motsin shi ne? ya wani zo ya addabeni”

Ummi tace, “aa kawai tinda naga kin tawo ɗungul ɗungul nasan da walakin”

Cigaba tayi da aikin murya ƙasa ƙasa tace, ” shi kowane lokaci nashi na wannan jar yarinyar ne”

Ita dai Ummi murmushi kawai tayi.

 

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..”*
[10/20, 2:43 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 6*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

 

: wurgi yayi da kwalbar turaren sannan ya ɗan gyara sumar kansa, Saɗaf saɗaf ya fito yana leƙe leƙe dan kar yayi katari da ƴar kanzagi cikin sa’a kuwa sai da ya gama ƙure falon yaje ƙarshe sannan yaji muryarta tana rera waƙa cikin harshen buzanci, tana zaune kan kujerar roba ta harɗe ƙafa.

Ido ya zuba mata cikin sarewa da fitar.
Dariyar Ummi ce ta katse masa tunanin sa, ya juya kanta cike da shagwaɓa yace, “Nan!! nifa abokaina ne suka gaiyace ni”

Ummi tace, “dama ai bance nice ko Natiee muka gaiyace ka ba kawai dai bama son kayi nesa damu ne”

Kafin yayi magana Natiee tace, “Ummi na? yau ina son fita siyayya ko Jancy na ze rakani??”

Ummi tace, “gaki ga shi, Jannah ka bata amsa”

Yace, “amma Ummi nafa gama shiryawa na tsara komai kawai shikenan sai suga banje ba? gaskiya yarinyar nan ta fiye jaraba”

Natiee tace, “zaka iya rantsewa zakaje wajen abokan ka ne??”

Ƙasa yayi da kai yana sosa ƙeya ya yace, “bana rantsuwa akan ƙarya kinji ko?”

Dariya sukayi kafin Ummi tace, “ya tabbata kenan ba da gaske kake ba?? shikenan ai Allah ya tsare”

Natiee tace, “hmm abokai abokai sai kace kaine ka ƙirƙiri abota a duniya, daga wannan yace Jannah yimin kaza sai wancan yace”

da sauri yace, “Nan kinji ko?? marowaciyar banza idan mutum ya biye mata baze taɓa yin abun arziki ba kalle ta dan Allah sai kishin tsiya ke dai ko matata ce ba lallai taimin wannan ƙididdigar ba”

Natiee tace, “to a jikinka ma meye na kishi? Babu wani abunda za a yiwa kishi a tareda kai”

Yace, “Ummi kina jinta tana neman maidani wani soloɓiyo kuma bayan bata ƙaunar ta ganni da masoyiya ta ƴar sa ido kawai sai na buge ki kar Allah ya haɗani ma da mata irin ki, da wata rana sai dai azo a tarar da gawa ta jarabarki ta kasheni”

Tayi dariya sannan tace, “insha Allahu wadda ta fini zaka aura wadda duk ma inda zakaje da ƙafar yawon nan naka tana tareda kai, dan ma Allah yasa kai ba mayen ƴan mata bane da abun baze maka kyau ba”

Tsaki yayi ya nufi hanyar fita yana cewa, “karki fito zauna masifa ki tarar bana nan”

Da sauri ta tashi ta mara masa baya tana cewa, “Ummi mun tafi”

Ummi ta murmusa gami da cewa, “Allah ya kiyaye ku kula dai kar kuyi wannan faɗan naku akan titi”

Kasancewar sauri yake yasa be lura ba sai jiyayi yayi karo da mutum sun bangaji juna,
da sauri yayi Baya yana zaro ido a tsorace .

Cikin tsawa Haisam yace, “kai dabban ina ne wai?? mara ɗa’a kai ko da yaushe baka ƙara hankali shashashan banza, da wane ƙwarin guiwar zaka bangaje ni? sai na tubirbiɗa ka a gurin nan, ita Aaminar bata koya maka girmama mutane ne??”

Ƙasa yayi da kai cikin sanyi yace, “kayi haƙuri, amma dan Allah ka dena zagin kimar mahaifiyata badan tana koyar dani girmama ku ba tabbas da yanzu ba wannan zancen ake ba”

Mari ya ɗaura masa cikin zafin rai ya shaƙe shi ya haɗa shi da bango ya matse shi da ƙarfi yana huci, sai da yaga yafara jigata sannan ya watsar dashi gefe yana cewa, “idan kaji zafi gobe karka kuma ɗaga min harshe idan yau iya shaƙe ka nayi gobe har sai ka mutu sannan zan jefar da kai mara amfani kawai”

Sai da ya wuce sannan Jancy ya miƙe ya kama hannun Natiee cikin ƙarfin hali yace, “kizo muje”

Cijewa tayi cikin kuka tace, “bazanje ba Jan ka koma cikin gida ka samu nutsuwa in anjima sai kaje gurin Zeety dan farin cikin da zata baka ni bazan iya baka ba”

Share ƙwallah yayi cikin rauni yace, “Natiee ba kina son zuwa ba? karki fasa saboda ni zan raka ki kuma yau bazanje ko ina ba tinda bakyaso na fita”

Jan hannunsa tayi zuwa ciki tana tafe tana kuka shima yana sharar ƙwalla.
Hajiya Saratu tayi dariya cike da farin ciki tace, “matsalar ja da manya kenan, Allah sarkin daɗi da ya tashi sai ya sako ka a ƙaramin su, tabbas da kaine babban su babu shakka da kaina zan kashe kaina saboda baƙin cikin ganinka baze barni rayuwa ba, karfa ka damu wannan fa kaɗan ne yadda kake ba zuciyar nan me kake ganin ze faru? ai yadda ka fito haka zaka koma bazaka taɓa cigaba ba, gashi kai akafi so sai dai kuma anfi ƙarfinka bawan su ma yafika daraja haka zaka ƙare a ƙarƙashin ikon su, idan ka shiga kace ina gaida tsohuwar ka”

 

Fincikarsa Natiee tayi suka shige ɓangaren su, shi dai binta kawai yake ƙafafunsa ne kawai suke jansa hankalinsa nutsuwarsa da tunanin sa duk basa jikinsa.

Kallo ɗaya Ummi tayi musu tayi ƙasa da kai sai da tayi da gaske sannan ta hana kukan da yake son kufce mata fitowa.

Zame hannunsa yayi yaja dogayen ƙafafunsa ya nufi ɗakinsa.
Natiee ta zauna kusa da Ummi cikin zafi da raɗaɗin da takeji tace, “Ummi kenan haka yayana ze kasance kamar mutum mara ƴanci?? shima fa ɗa ne a cikin gidan nan amma komai aka ɗebo sai a juye akansa? kenan baze taɓa samun nutsuwa ba? yanzu fa shi ba yaro bane yayi girman da yaci su dena wulaƙanta shi haka, ni nagaji Ummi idan shi baze iya ba ni zanyi tsayin daka dan ƙwatar masa ƴancinsa, zan iya jurar duk abunda za’aimin amma bazan juri a dinga cin zarafinsa ana tozarta shi ba dan shine ƙashin bayana shine jigo na shine wanda nake kalla naji daɗi shi tamkar magaji ne a gurin Abana dan haka tamkar uba nake ɗaukarsa, shi fa namiji ne amma sun maidashi kamar marainiyar mage Ummi me yayi musu?? me suke son maidashi a rayuwar nan? kullum sai dai suyi masa yayi kuka mu kenan bazamuyi farin ciki ba? kowane ɗa a gidan nan baya laifi sai Jan saboda shine ba mutum ba?, Ni kawai ki barni dan Allah Ummi nagaji sai dai ayi yadda za ai dani”

Taƙarasa maganar tana wani irin kuka me matuƙar girgiza me sauraronta.

Cikin dauriya Ummi ta danni zuciyarta sannan ta rungumo Natiee a jikinta, bayan ta goge hawaye tace, “Natiee bana son hana ku yin kuka amma yayi yawa, tabbas abunda suke yiwa Jan yaci yanzu su dena ƙwarai shi ba yaro bane amma a gurinsu har yanzu yaro ne, karfa ki manta shine autansu da ace ya girmi Jaafar koda da minti ɗaya? tabbas da ni da kaina zanyi tsara a tsakanin su dan na nema masa girmansa amma sai ya kasance shine ƙarami ni kuma ban kasance uwarda zata bari ƙani ya raina yayansa ba, idan kukai haƙuri komai ze wuce akwai lokacin da ze zo wanda ko sunyi masa ma baze damu ba, yanzun ma rashin gane hakan ne yasa kuke damun kanku”

shiru Natiee tayi tana sauke ajiyar zuciya, dama tasan shine ƙarshen zancen Ummi babu matakin da zata ɗauka wanda ya wuce hakan, bata ƙara magana ba har bacci ya saɓe ta,
Ummi ta kwantar da ita akan kujera sannan ta tashi.

Jancy duk ya rasa me yake masa daɗi yana so yayi kuka kashirɓan kamar yadda ya sabayi amma abun ya gagara, ƴan hawayen da suke zuba a idonsa ne kawai suke ɗan sassauta irin zafi da raɗaɗin da zuciyarsa takeyi,
Duk jinsa yake kamar ba’a nutse ba ga wasu zantuka marasa kan gado da tunaninsa yake bashi wanda kuma suke ƙoƙarin yin tasiri a zuciyarsa,
Tabbas Ummi takan gaya masa ya canja canjin kuma beyi mata daɗi ba, sam be ga canjin ba sai a wannan lokacin da yanaji yana gani yake irin wannan burkitaccen tunanin.

Yana cikin haka wayarsa tafara tsuwwa beyi niyar ɗagawa ba amma da ya tuna Zeety tana can tana jiransa sai ya ɗauka.

Cikin sanyi tace, “Jan? yau ma…”

Katse ta yayi da cewa, “kiyi haƙuri”

Murmushin tausayawa tayi sannan tace, “kai yakamata na bawa haƙuri dan kuwa nasan an ɓata maka rai ne”

 

 

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:44 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 7*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

jinjina kai yayi yace, “haka ne shiyasa ma yau bazan samu fita ko ina ba”

Tace, “Jan har yanzu kai kaɗai na sani sai yaushe zaka bani labarin ka?”

Murmusawa yayi sannan yace, “kamar bazan iya ba Zeety bana son fayyace abunda ya shafi ni da ƴan uwana”

tace, “kenan har yanzu ban kai matsayin da zaka ɗauke ni matsayin ɗaya daga cikin su ba? a gani na nima tamkar ƙanwa nake a gurinka dan mun zama ɗaya, kenan tunani na kuskure ne?”

yace, ” karkice haka mana, na yarda zan gaya miki amma ba yanzu ba”

Tace, “har sai yaushe kenan?”

Yace, “bansani ba banida tabbacin lokacin amma ki shirya cikin kowane irin lokaci zan iya tsinkayar ki da labarin”

Murmushi tayi gami da cewa, “amma bana so ka cigaba da kasancewa cikin damuwa fa”

Yace, “karki damu tinda naji muryarki ai komai ya wuce”

cigaba sukayi da fira cikin nishaɗi da matuƙar so da ƙauna.

Zaune take kan kujerar roba ta kashingiɗa a jikin makarinta sai murmushi take wani daddaɗan tunani ne yake mata yawo dan haka har ta manta ma a inda take.

“Queeen!!?? Queeeen!!!!!”

Cikin wata ƴar siririyar murya yake kiran ta.
Zaro ido tayi akansa tareda cewa, “kai??? ta ina ka shigo nan???”

Sai da ya zauna sannan yace, “daga sama kawai sai gani a gaban Queen”

Harara ta maka masa sama da ƙasa sannan tace, “kai a suwa?”

Yace, “kinsan dai ni mutum ne ai ba aljani ba sannan kuma ba sata na shigo yi ba bare kice bazan shigo ta hanyar da kowa yake shigowa ba”

tace, “Naji amma ai da dalili”

Matsowa yayi kusa da ita ya sassauta muryarsa cikin salon me jan hankali yace, “matuƙar kina gidan? me ze sa ki tambayi dalilin bayan kece? saboda ke nazo ina fatan zaki bani damar ganawa dake”

Maida kallonta tayi zuwa gefe ta murguɗe baki sannan tace, “kenan? meyesa kake son shiga rayuwar wani ne?”

Gyara zama yayi tareda cewa, “yauwa anzo wajen tambaya kawai zanyi miki”

Tsira masa ido tayi alamun tana sauraron sa,
a marai-raice yace, “Zuhra meyesa kina mutunta kowa kina sakarwa kowa fuska amma banda Zaheer meyesa duk irin son da nake miki bazaki tausaya min ba?”

Sai da ta sauke ƴar ajiyar zuciya kafin tace, “Zaheer Zuhra sunan ma ko dacewa beyi ba, Zaheer! Zuhra ba taka bace ka gane??”

Cikin tattausar murya yace, “meyesa??”

Ta murmusa sannan tace, “saboda ta riga tayiwa kanta zaɓi kuma ta sadaukarda zuciyarta wa soyayya, ba sauran inda zan iya raɓa ka Zuhra ta Jannah ce ba Zaheer ba”

Yace, “menene abunda Dogon Yaro yake dashi wanda ni banidashi? shi namiji ne nima kuma haka ina ganin dama ɗaya garemu dani dashi kamata yayi ya kasance ba wani cikakken bambanci tsakanin mu”

cikin ɗaga murya tace, “aaaa!! wannan maganar taka ai sai tasa mutum ya faɗi da yaya zaka haɗa kanka dashi?? shi fa dogo ne kai kuma ga ka nan dai shi kuma mutum ne me hankali da nutsuwa ga aji ba kamar kai ba, idan kuwa haka ne?? kaga babu yadda za’ayi kuzo ɗaya dole akwai bambanci”

Ya kwashe da dariya tareda cewa, “shashashar yarinya, wai banda ƙuruciya ina dalilin ki na maƙalewa wanda baya sonki baya ƙaunar ma ganin ki? bana tunanin akwai ranar da ze saurare ki fa”

Tace, “Zaheeer!!! wannan kalaman naka ɗaci garesu, kuma bi’izinillah da ranka zaka ga ranar da zan auri Jancy kanaji kana gani”

Yace, “mahaukaciya”

Yana rufe baki tace, “mahaukaci”

Yace, “shashasha”
Tace, “shashasha”

Yace, “sokuwa mara wayo”

A ɗan tsawace tace, “soko mara yawo manaa!!!!, jarababbe ina cikin tunani na me daɗi da fa’ida kazo ka rushe shi ka dami mutane”

dariya yayi sannan yace, “kin raina ni sosai Zuhra amma ba komai wata rana bazakiyi ba, naji zan dena takura muki amma fa bazan dena sonki ba sannan kawai kibani dama na cigaba da nuna miki ƙauna kuma karkiyi mita akan ina sonki kin yarda?”

Tace, “nace aa, idan baka so nayi mita to karka wani nuna min ƙauna ka cigaba da sona ɗin wannan kai ta shafa kaima ka yarda??”

Lallausan murmushi yayi gami da cewa, “na amince tinda hakan ya kasance hukuncin da zuciyarki ta yanke min”

Murmusawa tayi sannan tace, “Zaheer kasan me yake damuna? Jan! na kusa dena ganinsa dan mun kusa kammala makarantar shikenan yayi min nisa fa”

Zaheer ya jinjina kai sannan yace, “shine damuwar? zanyi tunani kafin lokacin sai mu nemo mafita indai hakan yai miki”

Cikin farin ciki tace, “yauwa Zaheer ɗina da kana haka ai da banyi faɗa ba a duniya dan indai kaji bakina to kaine ka tunzura ni saboda rawar kanka”

Yace, “ba wai!! damuwar tamu ƙuruciya ce kawai take damun mu duka amma naji kuma na ɗauka laifi na ne ”
..

Tace, “yauwa yanzu ka zama mutum da ka amsa laifinka”

Jancy
a kan hanyarsa ta dawowa daga wani ƙauye da Abansa ya saba zuwa duk sati domin bada tallafi ga mabuƙata, kasancewar baze samu zuwa ba yasa ya aikeshi,
tuƙin motar kawai yake amma hankalinsa baya tareda ita duk ya ta’allaƙa akan tunanin makomar rayuwarsa,
Kamar gilmin wani abu yagani ya gifta a gabansa ya wuce, gabansa yayi wata kyakkyawar faɗuwa har ƙasa,
Be ga komai ba sai dai kama da yagani da kuma bugawar da zuciyarsa tayi hakan yasa be sassauta gudun da yake ba dan kuwa burinsa a yanzu be wuce yaga Ummin sa da abar ƙaunar Natiee ba.

bayan yaƙara tafiya me nisa kamar daga sama yaga wani maciji baƙi siɗik murtukeke ya sako kai kan titin ya doshi ɗaya tsallaken da alamun tsallakawa yake son yi.

wani mugun burki ya sha wanda yasa motar ta ɗanyi tsalle tayarta da ta haɗu da kwalta ta bada wani farin hayaƙi sannan ta tsaya,
Rintse ido yayi da ƙarfi tareda furta “Hasbunallahu’wani’imalwakil”

Har ya buɗe idanunsa yaƙara ɗora su akan titin Macijin be gama tsallakawa ba gashi dai kansa ya wuce amma gangar jikin bata ƙare ba bare a ga ƙarshen sa,
Sosai Jan yaƙara firgicewa dan kuwa ko a tatsuniya be taɓa jin labarin macijin da ya kai wannan tsawo ba.

Juyawar da kansa yafarayi ne yasa ya ƙara rintse idon yana buɗewa kuma yaga ko ƙurarsa babu,
Lokaci guda kuma wata muguwar kasala da tsinkewa ta saukar masa kamar an zare masa laka jikinsa yayi wani bala’in sanyi tin daga tsakiyar kai har ɗan yatsan ƙafa ga wani mugun rauni da zuciyarsa tayi.
yakasa ko motsin kirki sai wasu zafafan hawaye da suke sintiri akan fuskarsa,
Duk da wannan yanayin da ya faɗa be fasa addu’o’i yana neman temakon Allah ba, har ya fitar da rai da komawa gida sai kuma yaji ƙwari ƙwari a jikinsa cikin sauri kuwa ya sake ɗora motar kan hanya jiki na rawa fatansa kawai ya ganshi a gida koma yaga ya shigo cikin mutane dan kuwa titin ba kowa kamar anyi shara.

Yana cikin tafiyar yaƙara ganin maciji kalar golden ya faɗo akan glass ɗin motar har sai da yayi tsawa yai ratsa ratsa, Jancy kuwa besan lokacin da ya juya motar ba saboda kiɗima da gigita yayi cikin jeji da ita saura ƙiris yayi karo da wata bishi Allah ya tsare motar ta tsaya.

Ko buɗe ido ya kasayi ga wata zuffa me zafi da take keto masa jikinsa sai ɓari yake, kawai ya saduda ya miƙa wuya jiran irin ɗanyen hukuncin da macijin ze yanke masa kawai yakeyi.

 

 

 

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:45 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 8*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

 

Zuhra gyara kwanciya tayi tareda cewa, ”
Zahra idan kin gama shirmen naki sai kiyi shiru nidai bacci zanyi”

Zahra tace, “da ranar nan??”

Zuhra tace, “kinga surutun naki ne fa ya hanani bacci kimin shiru”

taɓe baki tayi sannan ta fice daga ɗakin.
Zuhra kuwa bayan ta gama lissafin dokin ranon bacci yayi gaba da ita.

A firgice ta farka ta dire daga kan gado tayi waje tana ƙwalawa Zaheer kira, suna falo shi da Zahra da Momu suna hira ta iso a gigice kai tsaye wajen Zaheer ta nufa tana cewa, “Zaheer Jancy bashida lafiya dan Allah kazo ka kaini wajen shi so suke su kashe shi kayi sauri ka tashi”

da mamaki yace, “bangane ba fa Dogon Yaro ba lafiya to ke tayaya kika sani? kuma ni banida lambarsa kawai ruɗani ne ma irin naki amma mutumin da bakisan a duniyar da yake ba”

cikin son gazgata gaskiyarta tace, “da gaske nake ina cikin bacci naganshi yana ta kuka ka kiramin Alamee ka tambayeshi yana ina wallahi baya lafiya ka temake ni Zaheer”

Momu tace, “ikon Allah waye wanda take magana akansa ne Zaheer??”

Zaheer ya ɗanyi ƙasa da kai sannan yace, “abokin karatun ta ne”

Momu ta jinjina kai sannan tace, “tinda hakane ka kira kaji ɗin ai yana da kyau hakan”

Waya ya cira ya kira Alamee cikin sa’a kuwa ya ɗauka tareda cewa, “aboki yane??”

Zaheer yace, “kasan ƙanwata ai Zuhra itace ta rikice min wai Jancy ba lafiya yana ina ne??”

Cikin kaɗuwa Alamee yace, “kut to ai baya gida yaje wani ƙauye yau kuma yanzu yaci ace ya dawo gaskiya dan yace baze jima ba tinda ba tareda Alhaji suka tafi ba, bari na nemeshi naji”

Zaheer yace, “yauwa nagode”

Alamee yana kashewa ya kira wayar Jancy har sai da ta katse sau uku be ɗauka ba dan haka ya kira Sufyan yana ɗauka yace, “Sufee Jan be dawo gida ba ko?”

Yace, “eh da ya dawo ai ze sanar damu”

Alamee yace, “ai kuwa ba lafiya ya kamata mu bi sahun sa maza ka fito mu haɗu kuma ka sanarwa su Zuhair da sauran abokan mu”

Sufee yace, “shikenan yanzu zan fito kawai ka tawo sai mu haɗu ko?”

Yace, “ina zuwa”

Cikin sauri ya shiga cikin gida ya ɗakko mukullin mota ya ɗau hanya.

Jancy kuwa yana jin ƙarar wayar amma yakasa ɗauka yadda yake zaune idan ba zuffa ba ba abunda yakeyi sai jikinsa da yake karkarwa yana kallon macijin ya silale yayi ƙasa ya cigaba da tafiya, ya daɗe a cikin wannan halin kafin ya samu ya janyo wayar ba tareda ya duba me kiran ba ya ɗaga ya kara a kunne.

a kiɗime Sufee yace, “kana ina Jancy muna ta nemanka amma shiru”

a wahalce yace, “Sufee ina wata hanya banyi nisa sosai da futowa daga ƙauyen ba kuma bazan iya dawowa gida da kaina ba kuzo yanzu dan Allah”

Sufee yace, “muna kan hanya karka damu zamu zo amma karkayi wani wajen mu neme ka mu rasa ka tsaya anan ba abunda ze sameka da yardar Allah”

Kai ya gyaɗa tareda cewa, “to”

har suka iso beyi wani yunƙuri ba dan a matuƙar tsorace yake gani yake yana fita daga motar ze ƙarayin mugun katari da macijin a hakan ma be yarda tafiyar yayi ba.

Basu tsaya nemam ba’asi ba kawai suka maidashi ɗaya motar suka rufe waccan, sannan suka kama hanyar komawa gida, har suka dawo be ce musu ƙala ba, kai tsaye gidan su Alamee suka wuce dan sun san baya ƙaunar abunda ze ɗaga hankalin mahaifiyarsa.

Sai da yayi wanka ya huta ya dawo hayyacin sa sannan suka maidashi gida.

A falo ya tarar da Ummi da Natiee yana yin sallama duk suka bishi da ido Ummi ce kawai ta amsa sallamar tashi Natiee kuwa kallon tuhuma kawai take jefa masa.

Murmushin ƙarfin hali ya saki gami da zama a gefen Ummi yace, “sannu da gida Nan”

Tace, “yauwa amma baka da lafiya me yafaru ne?? ba Aba ne ya aike ba?”

Ya gyaɗa kai sannan yace, “hakane Ummina yanzu na dawo duk a gajiye nake wallahi”

Yaƙarasa maganar tareda yin miƙa, yaƙara da cewa, “ke Natiee yau me kukai mana ne? wai ma baki iya gaida mutane ba? kawo min ruwan bunu do Allah”

Tashi tayi tareda cewa, “ba dai kace bazaka dani ba gashi nan ka dawo a gajiye ai, sannu dai ba dan halinka ba ya hanya?”

Yace, “lafiya lau ba’a zo nema na ba?”

Natiee tace, “to za’a fasa ne?? kayi shiru da zancen su kawai ka huta ze fi”

Ummi dai kallonsu kawai take haka kawai takeji kamar ba dai-dai Jannah yake ba amma tasan ko zata mutu dan tambayarsa baze gaya mata gaskiya ba amsar dai itace ba komai”

ko alamun wani abu ya faru be nuna musu ba har dare yayi suka rabu da nufin ya tafi bacci, yaso yin baccin amma abun ya faskara da ya rufe ido macijin nan guda biyu su yake gani sai ya firgita, tin yana ɗaukar abun da wasa yaga har ya girmama ya kasa baccin gashi yanajin sa da ya rintsa sai yayi muguwar firgita gashi dare yayi sosai, tashi yayi ya ɗauki filonsa ya nufi ɗakin Ummi tana zaune tana lazumi da alamu ta gama nafila ne da sallama ya shiga ya zauna a kusa da ita ya ɗora kansa kan kafaɗarta.

Sai da ta kammala addu’ar ta shafa sannan tace, “Jannah meke damuwarka??”

Yace, “Ummi nakasa bacci”

Tace, “meyesa?”

Yace, “bansani ba nima kawai firgita nake”

Tace, “bakayi addu’a bane?”

Yace, “nayi amma ban dena ba kuma inajin baccin amma nakasayi”

yayi maganar cikin rauni kamar ze fashe da kuka.
Jinjina kai tayi tace, “ka cigaba da addu’ar tashi ka kwanta ”

Tashi yayi ya koma kan gadonta ya kwanta ita kuma ta zauna kusa dashi ta tayar masa da kai da cinyarta sannan ta shiga binsa da nata addu’ar tanayi tana shafa kansa,
A hankali nutsuwa tafara saukar masa yafara numfashi cikin kwanciyar hankali zuwa wani lokaci bacci yayi gaba dashi.

Ido ta zuba masa a zuciyarta tace, “lallai akwai abunda yafaru da Jannah yau ɗinnan kuma ya zama dole na sani dan na ɗauki matakin da ya dace”

 

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem

*INDO CE..*
[10/20, 2:46 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 9*

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

Sai da Aba yazo tashin shi su tafi masallaci ya tarar baya nan kai tsaye sashin Ummi ya nufa dan yasan baze wuce can ba yana zuwa ya tarar dashi yana ta shaƙar bacci, “lafiya? kuwa” itace tambayar da yafara jefawa Ummi.

Cikin sanyi tace, “nima tambayar da nayi masa kenan yayin da na ganshi sai dai kasan be zama lallai na samu gamsashahiyar amsa ba, amma banajin lafiya yake yace firgita yake amma be sanar min da abunda yake tsorata shi ba”

Ya ɗan numfasa sannan yace, “shikenan Allah ze mana tsari da koma mene tsashe shi muje mu gabatar da sallah”

koda gari ya waye ma babu irin tambayar da Alhaji da Ummi basuyi masa ba amma ba amsa.

a wunin ranar ko fita beyi ba gaba ɗaya babu wani ƙwari a tattare dashi.
Ummi ce ta kalli Natiee cike da damuwa tace, “zurfin cikin ɗan uwanki yayi yawa Natiee, jiya da daddare beyi baccin kirki ba ya dinga firgita kuma nasan dole akwai dalili amma yaƙi sanar dani baki lura da dawowar sa jiya ba? nasan baya cikin yanayi me daɗi sai dai shi baya cika amsa tambaya koda yasan abu amsar sa ɗaya ce ba komai, amma nasan ke ze iya gaya miki dan haka ki tambayar min shi, na ƙwallafa rai akan son sanin abunda yake damunsa”

Natiee tace, “Ayyah Ummi shiyasa naji jikinsa zafi rau tin jiya da ya dawo ashe bashida lafiya, Allah ya sauwaƙe ni kuwa zan tambaye shi sai dai nima ɗin sai yaga dama yake gaya min abunda yake ransa”

Ummi tace, “amin, eh amma dai ba kamar mu ba ai”

tashi Natiee tayi tana cewa, “bari naje gurinsa tin kafin ya fita”

Yana zaune kan kujera ya rufe fuskarsa da tafikan hannunsa duka biyun har ta ƙarasa inda yake be san tazo ba sai da ta dafa kafaɗar sa sannan ya ɗago idanunsa da suka sauya kamanni ya zuba akanta.

Cikin tattausar murya tace, “Yayana baka da lafiya ko??”

Kauda kai yayi gefe sannan yace, “zauna do Allah bana son ganin ki a tsaye kina samin ciwon kai”

Murmusawa tayi sannan ta zauna ta zuba masa ido tana binsa da kallon tuhuma, suna haɗa ido ya kauda nasa tareda girgiza kai a fizge yace, “bana son kallon nan Natiee”

Tace, “to na dena matsoraci yanzu faɗa min me yake damunka? anya kuwa yau ka ci abincin da muka baka ma kuwa??”

Ya gyaɗa kai alamar “eh” sai da ya furzar da wata zazzafar iska sannan yace, “Natiee dan Allah”

Da sauri tace, ” dan Allah me kake son cewa?”

Ya ɗanyi ƙaramin tsaki sannan ya cigaba da bata labarin abunda yafaru dashi a hanya yanayi yana rintse ido yana cije leɓe.

Kasa motsawa Natiee tayi saboda mamaki da Al ajabi duk ilahirin jikinta yayi sanyi zuciyarta ce kawai take bugawa da gudun gaske.

Dariya yayi tareda lumshe ido yace, “kenan??”

Cikin rawar baki tace, “kenan me Jan??”

Yace, “aa bafa wani abu bane kawai ina son cewa kenan da kece lokacin kawai mutuwa zakiyi saboda tsoro, na zata na fiki tsoro fa Natiee ashe ba haka bane”

Fashewa tayi da kuka tana cewa, “baka fini tsoro ba Jan tayaya ma? kaine garkuwata idan ina tareda kai banida wani haufi tayaya zaka fini tsoro kuma?”

Shafar kwantacciyar sumar kansa yayi yana dariya har fararen haƙoransa suka baiyana sai da yayi me isar sa sannan yace, “ba abun kuka bane Natiee gaskiya kin bada mata, kiyi shiru do Allah dan wallahi dariya kukan naki yabani”

Tashi tayi tareda cewa, “tafiya ta zanyi idan na gama kukan nawa sai kazo ka neme ni ko na dawo da kaina amma wallahi sai nayi, yanzu da ace ya kashe ka fa?”

ya ɗan ɗage kafaɗa alamar bata shafe shi ba, yace, “shikenan na mutu muradin ƴan uwana ya cika kinga an wuce gurin, damuwa ta a ciki kawai halin da iyaye na da ƙanwata zasu faɗa shine abunda ze dameni, nasan ko Abana a cikin yayye na ba kowane yake masa kallon uba ba duk ba ƙaunarsa suke ba abun duniya kawai shine suka sa a gaba, ina tsoron ranar da zasu juyar da akalar zalumcin su kan mahaifina”

Da gudu ta fice tana ƙara fashewa da kuka, ya murmusa gami da cewa, “Natiee kenan a dole dai sai kinyi kukan nan”

Zuhra kwance take kan kujera tayi lif a cikin bargo sai rawar sanyi take, Momu ce ta tsaya akanta tana cewa, “Queen? zazzaɓin nan duk akan wannan yaron ne wai?”

Tattaɓe baki tayi tana shirin fashewa da kuka tace, “Idan da ya mutu fa shikenan na dena ganin shi”

Tattausan murmushi Momu tayi ta zauna a kusaa da ita cikin sigar girma da manyance tace, “idan kika ga mutum ya mutu to ba ya mutu ne kawai dan a dena ganinsa ba kawai Allah yayi shi ba me tsawon rai bane bazamu rayu tareda shi ba, ba ya dawo gida lafiya ba? ki kwantar da hankalin ki babu abunda ze faru sai ikon Allah”

Gyaɗa kai tayi sannan tace, “to kicewa Zaheer ya kaini gidan su na dubo shi”

da sauri Zaheer yace, “Queen kinada hankali kuwa?? kinsan adadin sashin da zaki wuce kafin ki isa gareshi? haka kawai kisa ayi masa sharrin da har ya koma ga Allah baze manta ba to gaskiya ba dani za’ai wannan ba”

juyawa tayi ta gyara kwanciya taƙara tattakewa a cikin bargon sai zumɓuro baki take.

Natiee sai da tagama kukan sannan ta zaiyanawa Ummi abunda ya faru kamar yadda ya gaya mata.

Nazari sosai Ummi tayi kafin tace, “maza nema min wayar Ariee kice ya haɗani da Baffi”

Cikin sa’a kuwa tana kira ta sameshi, bayan sun gaisa Ummi tace, “Baffi meye haɗin Jannah da macijin iska?? kuma har yake neman hallakashi??”

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*INDO CE..*
[10/20, 2:47 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 10*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

Baffi ya ɗanyi nazari kafin yace, “ba komai bane macijin na gidan su ne ina nufin a gidan nan akai masa aikin, ba nufin kashe shi akai ba kawai anyi ne dan a firgitar dashi kuma sunyi nasara a yanzu haka sun jefa ruɗani da kokonto a tattare dashi, kiyi ƙoƙarin mantar dashi wannan labarin idan ba haka ba zasu cimma abunda suke muradi na zautar dashi”

Ta jinjina kai sannan tace, “zanyi hakan Baffi nagode matuƙa”

Daga haka ta yanke kiran sulluɓar da wayar tayi zuwa ƙasa ta zuba tugumi cikin sanyin jiki gami da damuwa”

Natiee tace, “kinji ko Ummi? na rasa me mukai musu suka tsane mu mahaifi ɗaya ne yayi silar zuwan mu duniya amma sun jajirce wajen ballagazar da rayuwar mu a matsayin su na yayyen mu nakasa gane meye ribar su da yin hakan”

Ummi tace, “Natiee da na fitar da rai daga duk wata ƙauna ta tsakanin mu da Aban amma yanzu na gane babban rashin adalci ne mu kaɗaita kanmu mu barshi, da nayi tunanin saboda shi ake mana haka amma yanzu na gane dan dukiyarsa ne kawai mu kuma shine namu ba abunsa ba dan haka bazamu sakar musu ba”

Natiee ta rausayar da kai sannan tace, “yanzu me zakiyi to Ummi?”

Tace, ba wannan ne ya kamata ba yanzu kije ki kira min shi dai-daita nutsuwar sa shine abunda ya dace dani”

tashi tayi ta kirashi ba jimawa suka dawo tare.
cikin sakin fuska Ummi tace, “Jannah yau bana jin daɗin jikina sosai kuma zan shiga kicin muje ka tayani aiki ko?, kodai baka da lafiya ne?”

Da sauri yace, “aa Nan lafiyata ƙalau kawai inaga dai zazzaɓi nakeyi”

Tace, “amma shine ka ƙi gaya min?”

ƙasa yayi da kai yana ɗan sosai ƙeya yace, “Ummi ai gani nayi ba wani babban abu bane bana so na tayar muku da hankali akansa”

Tace, “shikenan yana da kyau kasha magani, Natiee maza ki ɗakko masa maganin saura kai kuma ka ƙi sha, ni bari naje kicin ɗin idan kaji dama ina jiranka”

har ta ɗakko masa maganin yana nan zaune, sai da tace, “Jan gashi fa”
Sannan ya numfasa gami da lumshe ido yace, “Natiee zauna mana bana son ɗabi’ar nan taki ta miƙa min abu a tsaye”

Tace, “shikenan kayi haƙuri zan kula, karɓi kasha”

Karɓar yayi ya sha sannan ya ɗan kashingiɗa.
Natiee tace, “kenan? mu bamu da wani amfani a matsayin mu na ƴan uwanka? su ma iyayen ka kenan duk gara babu tinda baka ɗauke su a komai ba”

Baki buɗe yake kallonta kafin yace, “Natiee wai a ina kika koyi kwainane da manyance haka?? wannan wace irin magana ce kamar nayi amai?”

Ta gyara zama sannan tace, “dole nayi manyance mana tinda har yau ka kasa gane ka girma, fisabilillah Jan haka alƙawari yace?? kana tareda mu amma baza ka iya gaya mana ko abu ɗaya da yake damunka ba sai dai kaita ramewa ta ciki ba wanda ya sani, Aunty Fa’iza da Yaya Hassana Da yaya Husaina da ni ƙanwarka ko mu kaɗai mun cancanta ka gaya mana wani sirrin na zuciyarka bare azo ga mahaifanka, da gaske fa bana jindaɗin abunda kakeyi Jan kayi nazari ka gani zaka gane ba dai-dai bane, idan ni ban fahimci komai ba Ummi mahaifiyarka ce kallo ɗaya zatayi maka ta gane kana da damuwa dan ita ta raine ka tin baka iya magana ba har kafara, kuma zata so sanin abunda ya dameka kuma ka ƙi gaya mata baka tunanin jefa ta cikin wani mugun hali??”

Dafe goshi yayi tareda cewa, “wayyo Allah!! Natiee maganganun nan sunyi tsauri da yawa basar kawai dan Allah”

Tace, “naƙi gaya min dalilinka na yin hakan”

Yace, “babu, kawai bana son tayar da hankalin ku ne”

Tace, “ohh kai ka mutu kenan mukuma muyi ta jimami??, to shikenan dai bar wannan zancen yanzu bani labarin Antin tawa Zeety”

Murmusawa yayi yace, “yau kuma kece da tambaya ta?”

Tace, “kwana biyu ne bamuyi ba shiyasa naji nayi kewarta”

Yace, “duk a kwanan nan ne bana cikin yanayi shiyasa ma kikaji bana zancenta”

tace, “Ayyah har na tausaya mata gaskiya tana sonka sosai”

Yace, “to ya ranki?”

Tace, “yana lafiya tashi muje gurin Ummi ni, ai tinda na ɗago zancen nan sai ka dameni kuma”

Dariya yayi tareda miƙewa suka nufi kicin ɗin.

Hajiya Murja
dariya tayi sosai kafin tace, “ai babban goro sai magogin ƙarfe Aamina gashi yanzu na sauya labarin ɓangaren naki da abu guda ɗaya, Haisam? baka ga ƙanin ku ya fita daga hayyacinsa ba?”

Yace, “ƙwarai Momi na gani kuma nayi mamaki”

hhhh tayi dariya sannan tace, “na firgita ƙwaƙwalwarsa hakan kuma kaɗan ne daga cikin mummunan shirina akansa, duk da irin dafa’in nasu nayi nasara cikin ƴan kwanakin nan na kauda duk wani farin cikin su, kuma zan ɗora daga inda na tsaya wasan be ƙare ba”

Haisam yace, “wato a waje kina nuna duk ɗaya ne ke da Hajiya Saratu amma a gefe kawai kanki kike wa gyaran hanya”

Tace, “duniyar haka ta zama Haisam dagani sai ƴaƴa na kawai ina amfani da ita ne dan ta temaka min ta wani ɓangaren har na cimma matsaya, yanzu na gane lagon DOGON YARO”

Alhaji ne zaune a falo shida Ummi suna cikin fira yace, “Aaminatu nayiwa ɗanki laifi fa”

Da mamaki tace, “menene ya faru?”

Yace, “da fari dai kafin shi yana da kyau ki tausasa zuciyarki dan kema abun ze taɓa ki, ina son yaje ƙasar waje ne dan ɗaukar matakin karatunsa acan baze dawo gida ba har sai na tabbatar ya girma yayi hankali ”

katseshi tayi da cewa, “Alhaji meyesa??, idan yana tareda mu mukanji kamar muna ƙarƙashin wata garkuwa ne, idan ka fita fa daga ni sai Natiee mu kaɗai baka tunanin abunda ze same mu? Idan yana nan munajin daɗi inaga ace yayi nisa damu haka?”

“Kayi haƙuri bana son gardama maka amma bazan iya bari ya tafi ya bar mu ba”

 

 

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:50 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 11*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

Aba ya jinjina kai yace, “shikenan bazanƙi ta taki ba, ba abunda zan faɗa anan wanda ya wuce na baki haƙuri kawai”

Ummi tace, “to haƙurin na meye kuma?”

Yace, “Aaminatu yana da kyau ki daure ki fahimce ni dan Allah, nima kaina banason yin nesa da yaron da ba kasafai yake cin abinci ma idan ba tareda ni ba, tambayar da yakamata ki fara yimin dalilin da yasa na zaɓi hakan, ni anawa ɓangaren hakan sauƙi ne gareshi harma damu, zafin rashin ganinsa kullum sai yafi mana sauƙi akan zafin zalumci da cin zarafin da akeyi masa, shifa Jannah yaro ne har yau yana buƙatar rayuwa ingantacciya kuma nutsatstsiya kafin ya girma yana buƙatar dogon nazari kafin lokacin da nauyin mu duka ze koma kan kafaɗunsa, amma idan ya kasance a tsakankanin mu wasu su soshi wasu su ƙishi kinga koda yaushe ze kasance cikin ruɗani ne, baze gane asalin suffar sa ba har sai ya kaɗaice yayi nesa da duk wani ruɗani, amma kiyi haƙuri abisa faɗen hakan da nayi har na ɓata miki rai tinda bakyaso nima banaso farin cikin ki shine abun nema agareni”

Shiru tayi ta zurfafa acikin tunani har wani lokaci sannan taja numfashi ya sauke cikin sanyi tace, “na yarda”

cikin sauri Aba yace, “kin yarda?? da gaske?”

Murmusawa tayi tace, “eh da gaske mana kafini gaskiya zan jure rashinsa na wani lokaci amma lokacin da ze dawo gareni ze zamto ɗaya tamkar da dubu, tabbas yana buƙatar tunani da nazarin irin rayuwar da ze gina idan ya girma, nagode da ka tunatar dani hakan da nakasa tunawa, Allah ya tsare mana shi”

Aba yace, “Alhamdulillah ba ƙaramin farin ciki nayi da jin hakan ba Aaamina, amma akwai alfarma ɗaya, banaso yasani har sai komai ya kammala, idan ba haka ba kuma kinsan halin kayanki”

Tace, “ba komi”

Da sauri Meera ta riƙo hannunta tana cewa, “kiyo sauri ki ganshi wlh yanzu zasu fita”

ba musu ta mara mata baya cikin sauri sauri tana cewa, “da gaske Meera?”

Kafin Meera tayi magana idonta ya tabbatar mata da hakan, ido ta zuba masa tareda shuɗawa duniyar tunani, sai da Meera tace, “a iya kallonsa zaki tsaya bazaki matsa kusa dashi kiyi masa magana ba?”

Zuhra tace, “magana fa yake da abokansa ni wacece da zanje na katse masa hanzari banida ƴancin yin hakan”

Meera tace, “kenan Kina ji kina gani hakan ze gagareki? wane irin so ne wannan Queen? a ganina ki faɗa masa gaskiya ma ze fi”

Zuhra ta zaro ido tareda dafe ƙirji tace, “Meera kin haukace ne?? bazan iya ba gaskiya ki dena faɗe dan Allah”

Tsaki Meera tayi tace, “ai kuwa idan bakiyi da gaske ba zakiyi ukullala”

Zuhra tace, “nafi yarda da hakan akan nakai kaina inda ba matsayina ba”

Alamee ne ya katse mata hanzari da cewa, “nan ake aikin banza harara a duhu”

Dukan su suka zuba masa ido shi kuwa ya kauda kai yayi kamar ba dasu yake ba.
Meera tace, “Alamee? meyesa zaka jefo mu da magana haka?”

Cikin haɗe fuska yace, “Meera na taɓa shiga harkar ki ne wai? bana son shishshigi ba kwarjini, ba’a sa dake ba kina shirin ɗauka, ashe dai kunyi tinda har kuka tsargu dama ku mata aikinku kenan ku laɓe kuna maganar samarin wasu tirr dai”

Ƙasa Zuhra tayi da kai tafara sharar ƙwalla, Meera kuwa harara ta doka masa taja tsaki tace, “kai menene ma ajikinka wanda ze sa ayi maganar ka wallahi baka da wannan”

Zuhra ce ta katse ta da cewa, “aa Mera ko mene akace akaina ni najawa kaina, shi kansa Jan kallon mayya yake min inaga wanda suke kusa dashi? Alam kuyi haƙuri da zancenku da muke amma kasani ko me zakuce min akan sonda nakewa abokin ku baze sa na fasa ba kuma ba zanyi fushi ba zanyi kuka har zuwa lokacin da zuciyata zatayi sanyi na manta da komai”

Daga haka taja hannun Mera suka bar wajen.
Alamee ya shafa ƙeya tareda lumshe ido sannan yabar wajen.

yau ta kasance ranar jumu’at. rana ce wadda duk idan tazo Jancy yake jin daɗinta tamkar ta fiye masa ko wace rana a duniya, sukanyi wasanni sosai shi da abokansa ko acikin makaranta ko a wajenta wani lokacin ma baya komawa gida sai yamma saboda ƙiriniyar da suke wuni yi.

kowa yana sharholiyarsa amma banda Zuhra wadda ta raɓe daga nesa nesa ta zubawa Jancy ido, duk wani motsinsa idonta yana kansa.
Sallamar Zeety ce ta dawo da ita haiyacinta daga tunanin da takeyi.
Cikin fargaba da tsoro ta zubawa Zeety da tawagarta ido cikin tsammanin abunda suka zo mata dashi.

Zeety tana murmushi ta zauna kusa da ita tace, “tinda kin kasa amsa min sallamar ba komai, na same ki lafiya?”

Gyaɗa kai kawai ta iya yi dan kuwa matuƙar shakkar Zeety takeyi kasancewarta mace ɗaya da tauraron makarantar tasu ya taɓa saurara har ma ta zamo tauraruwarsa hakan yasa duk suke ji da ita babu wanda ya isa ya kai mata wargi shiyasa take sharafinta take taka duk wanda taso tasan tanada goyon bayan Jancy, Jancy kuwa na jama’a ne jama’a nashi ne.

Zeety taƙara faɗaɗa murmushinta cikin jin kai tace, “Tauraro mafi haske acikin taurari ɗaya tamkar da goma, tabbas yana da kyawun kallo daga nesa, sai dai idan ka matsa kusa dashi saboda tsabar kyawun nasa da cikar haibarsa bazaka banbance yanayin da kake ciki ba, amma tabbas kasancewa a kusa dashi yafi komai daɗi, idan ba damuwa ƙawata Zuhra inason muyi shawara”

Zuhra ta jinjina kai gami da cewa, “to”
Zeety tace, “a madadin kallon abunda ze disashe ganinka? me ze hana ka samu naka gwanin wanda idan kana kallonsa sai dai ganinka yaƙara ƙwari?, uhm basar da wannan maganar kawai, Zuhra dama wata shawara ce gareki, bana son yadda abubuwa suke faruwa marasa daɗi tsakanin ki da Dogon Yaro shine nace me ze hana ki haƙura da soyayyarsa ki karɓi ta wanda suke sonki?? na sani tabbas ke macece me matuƙar farin jini a makarantar nan, taurarinki sunada haske sai dai hasken na masoyina sun disashe naki, meyesa bazaki manta da jiya ki gyara gobe ba??, ina nufin ki manta da Jan ki bar min shi kema ki fidda naki gwanin”

ƙasa tayi da kai cikin tausayin kanta tace, “kiyi haƙuri Zeety dan Allah, ko nice na samu soyayyar nan bazan so wani yaso ta ba zanso ta zama mallakina ta har abada, sai dai narasa yadda zanyi nakasa gane meye masarrafin soyayyata gareshi, ki gafarce ni bana so ki ƙullace ni amma ni irin wannan rayuwar nafi jin daɗinta fiye da kowace rayuwa, idan na zubda hawaye ta dalilin Jancy jina nake tamkar ni nafi kowace mace sa’a a duniya, tabbas INA SONSHI So me tsanani kuma bazan iya denawa ba akan sonsa banida shamaki, nakasa sawa kaina linzami, idan babu damuwa ki barni na cigaba da gudanar da rayuwata a haka zan jure komai kuma banada sa ran wata rana ze saurare ni, kawai inai masa TSANTSAR SO NE”

Jinjina kai Zeety tayi sannan ta tashi hannunta goye a bayanta, ta furzar da huci sannan tace, ” tabbas komai ya kankama, wai yau an samu wadda take ƙoƙarin yin takara dani ina matsayin ƴar talaka kuma matar me kuɗi, hee!! Ashsha rashin sani yafi dare duhu, zaki ga ZARRAR TALAKA, fatan nasara abokiyar takarata”

Daga haka ta ratsa ta tsakiyar ƴan matan da suke kewaye da ita ta wuce cikin takun ƙasaita.

Haɗe kai da guiwa Zuhra tayi ta shiga rera kuka me matuƙar cin zuciya.

Tana cikin wannan halin muryar Sufee ta tsinkayeta, “ke bararoji???”

Rassss gabanta ya yanke ya faɗi, tabbas in kaji gangami akwai labari, basa yi mata irin wannan banzan kiran har sai idan suna jikin ogan nasu kuma da nufin tayi musu wani laifin.
Cikin nutsuwa ta ɗago koɗaɗɗiyar fuskarta ta zuba musu idanunta da suka zargage suka canja kama sabo da yawan koke koken da take yi.

Rabewa sukayi wasu sukai nan gefen wasu sukai nan, Jancy ne ya baiyana a tsakiyar su hannunsa salgafe da na Zeety sai raurau take da ido da alamu ma kuka tayi.

Bugun zuciyar Zuhra ne yaƙara tsananta take jukinta ya ɗau tsuma kakar kakar!!!.

Cikin ƙasaitaccen takunsa irin na wahainiya ya ƙarasa inda take.
Da sauri ta miƙe tana yin baya baya jin tayi karo da bishiya ne yasa ta dakata ta rintse ido kawai ta cigaba da tsammanin hukunci.

Sai da yaje daf da ita sannan yafara magana a kausashe yace, “Ummina da Abana sune Rayuwata, Ƙanwata kuma itace Duniyata, ita kuma Zeenart itace Zuciyata!! ina nufin itace jigo kuma ginshiƙina kinga kuwa ko waye ya taɓa su dole ne ya faɗa KOMAR WAHALA bana iya jurewa dan haka ki kula da kanki, bana fariya kuma bana gori amma nasan kuɗi da dukiyar mahaifinki ba komai bane akan nawa amma hakan besa na banbance talaka da me kuɗi ba, ni kowa nawa ne, amma har zaki kalli Zeety kiyi mata gori, ki faɗa min adadin dukiyar mahaifin naki ni kuma zan siye komai na biyaku duk akan masoyiyata, ki bi hanyarki ki iya takunki ni bana haɗa sahu da irinku kiji kuma ki gane”

Daga haka ba ƙari ba ragi ya juya ya kama hannun Zeety ya cigaba da tafiya.
Juyowa Zeety tayi tana kallon Zuhra, suna haɗa ido ta sakar mata wani shu’umin murmushi.

Zuhra ta kalli ko ina taga kowa kallonta ake ana nunata wasu suna dariya wasu suna tirr da irin soyayyar tata akansa, Durƙushewa tayi a gurin ta fashe da kuka me ƙarfin gaske.

Mera ce ta dafa kafaɗarta cikin rarrashi tace, “kiyi haƙuri Queen, komai yayi farko zeyi ƙarshe, ki tashi mu tafi gida kinga kowa kallon ki yake”

Sai da Meera ta ƙoƙarta sosai sannan ta tashi suka nufi gurin da direbansu ya ajiye mota.
Sai da Meera ta tabbatar sun kaita har gida sannan ta wuce nasu gidan.
Ganin ta shigo a burkice yasa Momu tambayar ba’asi, bata tsaya ta bata bayani ba tayi hanyar ɗakinta.
Momu tace, “Allah ya sassauta miki ƴarnan”

Jancy
Ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba wajen shawo kan Zeety dan kuwa rikici ta dinga yi masa kala kala.

yau yana zaune kan kafet a falon Alhaji yana buga game hankalinsa kwance.
Aba ne ya katse masa jin daɗinta da cewar, “Yaroo!!!”

Da kyar ya amsa da “Aba” dan kuwa gani yake ko motsin kirki yayi ze samu game over.
Aba yace, “ka fuskance ni nan ka dena wannan wasan dan magana ce me muhimmancin gaske”

 

(ba dai zancen tafiyar bane?😳😳. mu haɗu a fejin gaba😂💞❤️💔💖)

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:50 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 12*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

 

Jancy ya ce, “Abana wace magana ce kuwa wannan?”

Aba ya ce, “dawo kusa da ni ka zauna sai kafi fahimta ta dan hankalinka yanzu yana kan waya”
Tashi ya yi ya koma kusa da Aban nashi ya tattara masa hankalinsa guri guda sannan ya ce, “Abana ga ni fa”
Aba ya ce, “to Alhamdulillahi, Alhaji Abdussalam shi ƙaramin ɗan kasuwa ne kuma wanda yake buƙatar temakon-mu kuma ka sani hakan ba baƙon abune agaremu ba mun riga mun saba, dan haka ina buƙatar ka je inda yake gobe domin ku tattauna game da kasuwancin aji ta ina za’a shawo kan al’amarin”

Jannah ya ce, “amma Abana meyesa shi ba ze zo inda muke ba sai dai mu mu je? anya kuwa haka ya yi?”

Aba ya ce, “ayya Yarona ayya, ita wannan maganar taka ba ta dace ba, da ni da shi da kai duk abu ɗaya ne, ko ya zo , ko na je, ko ka je, duk ɗaya ne, babu banbanci dan ka je da kanka kuma ke temaka masa kar fa ka manta waƴanda ba su san ma ta ina za su samemu ba muna temaka musu ka ga kuwa hakan ai ba aibu bane”

Jinjina kai ya yi ya ce, “Abana Allah ya kaimu goben zan je ɗin, kuma ayi haƙuri a bisa maganata da ba ta kan hanya, afuwan Aba”

Aba ya murmusa ya ce, “ba komai a kula dai sabida gyara gaba Yaro!, am.. duk hukuncin da ka ga ya dace ka yanke kawai walau ka karɓi buƙatarsa walau ba ka karɓa ba abunda ya dace dai shi nake so kayi”

Jancy ya ce, “zanyi hakan in sha Allah”

Aba ya ce, “Allah ya yi maka albarka ɗana” ya amsa da “amin ”

Zuhra! cikin sanyin jiki taƙarasa inda Zaheer ya ke tsaye yana kallon ƙasa ta tagar da take gabansa da alamu yayi zurfi cikin duniyar tunani.
cikin tattausar murya ta ce, “Zaheer!!!”

Idonsa ne kawai suka ƙara girma alamun ya ji kiran kuma kiran ya zo masa a bazata amma ya kasa amsa domin kuwa ko da ya yi magana ba lallai ta fito ba.
Rausayar da kai ta yi ta ce, “Zaheer na sani duk wannan damuwar akaina ne”

Sai a lokacin ya juyo ya na fuskantarta ya ɗanyi gyaran murya sannan ya ce, “ba haka bane”
Ta ce, “ohh shi kenan to gaya min tunanin me kake?”
Kamar ba ze ce komai ba sai kuma ya ce, “soyayya: ita nake tunani, uhm Zuhra ni ina yi miki son da bani da burin da ya wuce faranta miki, ke kuma ki na yi wa wani son da yake tozarta ki”

Da sauri ta ce, “har an baka labari kenan? wai dan Allah waye ya ke gaya maka abunda ke faruwa a makarantar-mu?”
Ya ce, “shi fa Jan na mutane ne yawancin abokaina abokansa ne nima kaina abokinsa ne muna gaisawa ta mutunci da shi kin ga kuwa ai dole ne labari ze isheni har inda nake”

Jinjina kai ta yi kafin ta ce, “amma dai kasan…” katse ta ya yi da ce wa, “meyesa ba za ki amince da soyayyata ba? tabbas inajin raɗaɗin abunda Jancy yake miki kawai ina jurewa ne sabo da ina sonki”

Ta ce, “na sani ƙwarai kuma hakan da kakeyi ne ya sa nake jin banda kamar kai, sai dai kashshh so da ƙaunar dogon yaro sun gama haukata ni, amma inaso ka sani shi fa ba laifin shi bane, shi mutum ne me haƙuri da kawaici baya fushi da kowa indai ka ga ya yi min abu? to kawai ka ce laifina ne”
Ya ce, “na sani ai madam Queen!! yau da gobe ce ta fi ƙarfin wasa, acikin mutanen da yake tare da su ba za a rasa wanda yake buƙatar ganin kukanki ba dan haka sa shi yayi miki abunda ba dai-dai ba abu ne me sauƙin gaske, yarinyar da yake tare da ita ina itace ta gaya masa wani abun?, to kinsan me ta gaya masa? kar ki yi tunanin wani abu me daɗi zata kitsa masa dan ni nasan sharrin mace, tin ina yaro ban kai haka ba mace ta yi min sharrin da naji a duniya bayan mahaifiyata ba wadda zan ji ta a raina amma da yake so wawa ne sai gashi na mutu akanki”

Ta murmusa kafin ta ce, “dan Allah zaka iya yi min uzuri??, nima uzuri nake yi masa sabo da nasan zafin so kuma kai ma nasan ka sani, kai kana sona ni ina sonsa shi kuma yana son Zeety inayi masa uzuri sabo da yana da wadda yake so kaima ina fatan kayi min wannan uzurin, Dan Allah ”

Ya yi murmushi me cin rai sannan ya ce, “nasan zafin so sosai Queen hakan ne ma ya sa bana jin komai akan hakan abunda na sani kawai shine inajin ba daɗi a duk lokacin da Dogon Yaro ya tsinka miki zaren mutunci”

Ta ce, “amma dai ka karɓi uzurina ko Zaheer?”
Ya ce, “ba tin yanzu ba ma, ohh na gane, kenan shi Jan yana da ikon samun soyayyarsa ni kuma ko oho ko??”

Zuhra ta yi Dariya gami da ce wa, “wata zolayar zakai min? ka bari zancen ya wuce mana”

Ya ce, “shi kenan tin da ba kya so, ni zan wuce yau zan kwanan kusa da Ummata sai gobe zaki ganni dan kuwa bazan iya jure rashin ganinki ko da yaushe ba”

Ta ce, “da Daddy ze bari ai nima da na bi ka, amma ba komai wata rana zanje kace ina gaida Umman”

Ya amsa da “za ta ji”

Washe-gari.
Da daddare Jancy ya yi tattaki zuwa inda Aba ya aikeshi, lokacin da ya isa aka sanar masa da cewar Alhaji Abdussalam be dawo ba sai dai ya ɗan jira shi.
Ba dan ransa ya so ba ya zauna dan dai ba ya son ɓatawa mahaifin nasa rai.
Ya na nan zaune Zahra da Zuhra sukayo wajen suna wasan guje guje.
Ganinsa ne ya sa duk ta ruɗe ta shiga zaro masa ido yayin da shi ma yake zare nasa idon akanta, Zahra kuwa ƴar kallo ta zama dan kuwa ta kasa fahimtar abunda ya ke musu ciwo.

Sun kwashi ɗan lokaci a haka sannan Zuhra ta yi magana cikin rawar baki ta ce ,”ka yi haƙuri wallahi ban san kana nan ba”

Miƙewa ya yi rai ɓace ya ce, “tsabar haukanki har kina neman hayewa kaina, waye Abdussalam??”

Ƙasa ta yi da kai cikin sanyi ta ce, “mahaifina ne”
dogon tsaki ya ja sannan ya koma ya zauna ya dafe kai.
Cikin sauri ta yi gaggawar ɓacewa daga gabansa jiki na rawa ta koma cikin gida.

Bayan wani ɗan lokaci Alhaji Abdussalam ya yi sallama a wajen, a sannu ya tashi tsaye cikin fara’a ta ƙarfin hali ya ce, “barka da zuwa”
Alhaji Abdussalam yana murmushi ya ce, “ɗa na sannu da zama, na bari kana ta jirana kayi haƙuri dan Allah ”
A ɗan fizge ya ce, “ba komai ina do dai mu yi abunda za mu yi ina da abunyi”
Alhaji Abdussalam ya ce, “a’ah ɗa na sauri kake haka? to bismillah zauna mana”

Zaman yayi sannan suka shiga tattaunawa.

Zuhra tana zaune kusa da Momu Daddy ya shigo babu alamar annuri a fuskarsa ya nemi guri ya zauna ba tare da ya saurari kowa ba.
Momu ta ce, “lafiya kuwa? ya batun baƙon naka? ko dai be amince da haɗa hannun jarin bane?”
cikin ɓacin rai Abba ya ce, “eh haka ya ce ba buƙatar sai sun temaka mana shi ba ze iya haɗakar kasuwanci da ni ba, kuma bansan wane kuskure na aikata masa ba, amma nasan suna temakawa ƴan kasuwa sosai ko me yasa ba ze temaka min ba?, gani nake kamar idan na rasa damar nan komai zan rasa kamar kasu-wancina ba ze yi ƙarfi ba sai dai ya yi ƙasa ”

Momu ta ce, “haka ne?, ai shi kenan, Allah ya kawo mana mafita, amma kuwa abun akwai ban mamaki me yasa ɗannan ze yi mana haka kuwa?”

Alhaji Abdussalam ya ce, “sanin gaibu sai Allah”
Kukan da Zuhra ta fashe da shi ne ya jawo hankalinsu gareta suka shiga tambayarta abunda ya faru.
Kasa ba su amsa ta yi sai ma tashi da ta yi da gudu ta nufi ɗakinsu.
Momu ce ta bi bayanta cikin sauri tana fargabar abunda ke damun ƴar ta-ta.
Cikin sigar rarrashi Momu ta ce, “gaya min Zuhra me ya faru??”
Ƙara fashewa ta yi da kukan tana cewa, “laifina ne, na tabbata ganina da ya yi ne yasa ya ce hakan, bansan ya akai ya tsaneni ba haka har laifina ya shafi mahaifina, gashi yau ran Daddy ya ɓaci saboda wannan mugun son, wayyo Allah na Momu na shiga uku”

(Afuwan🤝 wannan na barka da dare ne🥰 wlh ban samu ishashshen lokaci ba😢 ina yinku duka💞😍

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:51 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 13*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
“me???” Momu ta faɗa tare da ƙura mata ido cike da son jin amsa.

Dena kukan ta yi ta saki baki tana kallon Momu a razane, sai yanzu ta tuna irin suɓul da bakan da tayi, girgiza kai ta yi gami da cewa, “a’a ba komai bane kawai ina tunanin saboda ni ne Jannah ya ƙi amincewa da Daddy”

Zahra ce ta katseta da cewa, “babu amfanin ɓoye ɓoye gareta Queen, ita mahaifiyarmu ce fa”
Cikin rashin ganewa Momu ta ce, “akwai abunda yake faruwa ne? na kasa ganewa meye kuke ɓoye min Queen?”
Zatayi magana Zahra ta ce, “ta yi magana akan so ko? to tabbas shine abunda yake ɗawainiya da ita, ta kamu da Son Jannarh Alhasan wato DOGON YARO mukan kira shi Jan ko kuma Jancy, wannan shine kawai Momu yanzu sai dai haƙuri da Queen kawai domin kuwa ta yi nisa tin da har ta na iya faɗa miki hakan a rashin sani, sai dai abunda ze ɓata miki rai shi fa ba sonta yake ba ita take abunta”

Momu ta kasa magana sai dai ta kalli Zahra ta kalli Zuhra da tayi ƙas da kai tana hawaye,
Halin da ta ga Zuhra a ciki ma kawai ya isa shaidar abunda Zahra ta faɗa dan haka Momu ta yarda.
Tashi ta yi tare da cewa, “Allah ya bada sa’a Queen dan nasan ko na hana ki ba za ki hanu ba”

Daga haka ta fice daga ɗakin, Zuhra ta kalli Zahra gami da cewa, “kinyi daidai kenan Zahra? yanzu kinga ran Mommu ya ɓaci me yasa kika gaya mata?”
Zahra ta ce, “ba sonsa kike ba?, to menene dan mahaifiyarki tasan da zamansa a zuciyarki? ai ba aibu bane yin hakan, Allah dai ya kawo miki mafita shine addu’a ta gareki”

Jancy da sallama ya shiga falon Ummi da Natiee suna zaune suna ƴar hira, ganinsa ne yasa duk suka haɗe rai sukayi kicin kicin, sakin baki ya yi yana binsu da ido kamar wani soko, cikin sanyi ya ƙarasa inda suke ya durƙusa a gaban Ummi cikin karaya ya ce, “Umminah!!!?”
Bata ko kalleshi ba sai ma ƙara ɗage kanta sama da ta yi.
Kamar ze yi kuka ya ce, “Ummih?? meke faruwa dan Allah ki yi min magana, na dawo zuciyata sam ba daɗi a gurinku nake sa ran farin cikina amma Ummi kun ƙi kula ni, dan Allah wane laifi na aikata miki Ya Ummiee?”

Kallon kallo Natiee da Ummi sukayi sannan suka kwashe da dariya.
sai da ya tabbatar tsokanarsa sukeyi sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya sai a lokacin dariyar da sukeyi tasa shima ya saki murmushi cikin sauri ya rarrafa gurin Ummi a shagwaɓe yana cewa, “naji tsoro sosai Ummina ku kaɗai ne nawa a gidan nan kuma yau ace duk kuna fushi dani ai bazan iya bacci ba”
Ummi tana murmushi ta ce, “ƙwaƙƙwaran ɗa ɗaya kamar kai taya zamu iya fushi da shi?, kasa a ranka kawai Umminka da ƙanwarka sun zolayeka ne ”
Ya yi murmushi sannan ya ce, “Ƴar mata ji mana”
Natiee ta yi farr da ido kafin ta ce, “mene?”
Ya ce, “kinga banson iyayi ko dan kin ji nai miki irin kira da samari sukewa ƴan mata?, a taɓ ai kuwa ki canja akala dan ko a tatsuniya bazaki samu kira daga zuƙeƙen ɗa kamarni ba”
Juyo masa ƙeya ta yi tare da cewa, “a hanci nafi ji”
Dariya ya yi tare da cewa, “Ummi kinga yarinyar nan ko? nifa ni kaɗai na shigo gidan nan fa ba da wani ba, ta fiye iyayi Nan kawai zamuyi gonjonta mu huta sai na zama ni kaɗai bani da kishiya”
Natiee ta ce, “zama da kishiya kuwa ya zamo maka dole kuma nice ƙarshe daga ni ba ƙari ehe, na dai lura yau da tsokana ka dawo gidan nan ni kuma bana jinta yau dan haka ka rufe bakinka, nima idan baka son magana hanani yi kake”
Ya ce, “ohh naji zancen ne ba’a so kuma ya zama dole”

Ummi ta ce, “Jannah? Abinci fa ko ka ƙoshi?”
Kafin ya yi magana Aba ya yi sallama, amsawa sukayi, cikin farin ciki Jan ya tashi yana cewa, “yauwa Abana har na tashi hankalina nayi zaton ba yanzu zaka dawo ba, Ummi tana cewa na ci abinci yanzu kuma na ƙoshi kawai ka zauna na gaya maka yadda mukai da wannan mutumin”

Zama Aban ya yi sannan ya ce, “to barka da dare Yaro”
Da sauri ya ce, “Abana kana lafiya?”
Aba ya ce, “eh ƙwarai ina lafiya sai dai ban fahimci dalilin da yasa ka ƙagara ka sanar min abunda kuka yanke da Abdussalam ba”
Jan yace, “yauwa naga kamar abun ba daɗi ne gaskiya ban yarda da kasuwancin da shi ba”
Aba ya ce, “to me yasa?? shifa ba wai mutumin banza bane bare ko ka ce ”
Jan ya ce, “nifa asalina Aba kasan bana son kasuwancin haɗaka, kuma da naje sai naga abunda be min ba”
Aba ya ce, “to gaskiya bazan tsawaita bincike akai ba dan ni na baka damar, yanzu ka zo ka ci abinci”
ya ce, “na ƙoshi fa”
Tashi ya yi tare da cewa, “yau baccin wuri zan yi”
Aba ya ce, “ka yi addu’a dai”

Natiee ta ce, “in zo in raka ka??”
da sauri ya ce, “a’a a’a haka kawai ki zo ki hanani yin abunda ya dace?”
tana dariya ta ce, “shi kenan gobe zamu haɗu ai”
Ummi ta yi murmushi gami da cewa, “karka manta da yin addu’a kafin bacci bayan ka gama abunda ya dace ɗin”
Ya ce, ” in sha Allah”

Abana!!! Abana!!!!!, kira yake ƙwalawa Aban nasa yayin da wasu mutane da suka rufe fuskarsu suke jansa a ƙasa wasu daga cikinsu kuma suna riƙe dashi yana ta kici kicin ƙwatar kansa amma ya kasa, yana kallo suka sa bindiga suka harbi Aban akai da ƙirji, wani razanannen kira ya ƙara yiwa Aban tare da fizgewa ya nufi inda yake kwance cikin jini sai dai kafin ya ƙarasa muryar wata budurwa ta dakatar dashi ta hanyar kiran sunansa kamar yadda ta saba, “Furena!!!!”
Cikin wani mugun razani ya juyo daidai lokacin harsashin da aka harbo masa ya sauka akan goshin budurwar da tayi shamaki tsakaninsa da harsashin.
zubewa ya yi akan guiwarsa tare da ƙwala mata kira “Natieee!!!!!!”

dai-dai lokacin ya farka daga mummunan mafarkin da yakeyi a matuƙar razane zuciyarsa kawai bugawa take da sauri sauri, zamewa yayi daga kan gadon ya zube a ƙasa kafin wani lokaci zuffa ta gama jiƙa masa jiki,
Kamar wanda aka zabura haka ya tashi cikin sauri ya nufi ɗakin Ummi dan duba lafiyar Natiee, Ummi tana zaune tana lazumi ta ganshi baga-tatan, da sauri ta miƙe tana cewa, “Jannah?? kana lafiya kuwa? meke damunka haka??”

Girgiza kai ya yi tare da cewa, “ba komai Ummi ina Natiee take? ki nuna min ita dan Allah wallahi idan suka kashe min ita nima mutuwa zanyi”

Hannunsa Ummi ta kama ta kaishi har inda Natiee take kwance tana baccinta cikin kwanciyar hankali, sai da ya tabbatar baccin take sannan ya nufi ɓangaren Aba.

A kwana a tashi ba wuya,
Lokaci yana ta tafiya. su Jancy suna kammala makarantar Aba yasa masa ranar tafiya ba tare da ya sani ba jiran lokacin kawai akeyi sannan a sanar dashi.

Zuhra kuwa kullum cikin kuka da ƙunci take bata da wani lokacin farin ciki, yau ma kamar kullum tana zaune ta sa abinci gaba ta zabga tagumi ga wasu ƴan hawaye da suke ta zirya akan kumatunta.
Zaheer ne ya katse mata tunanin da cewa, “Queen? me yasa wai damuwa da hawaye sune abokananki mu kuma ba mu da amfani?”
Ta ce, “Zaheer kar ka ce haka mana kasan dukan ku ba wanda bashi da amfani gareni, dan dai bansan yadda zanyi bane, amma kace zaka temaka min akan komai ko?”
Ya ce, “eh na ce”
Ta ce, “yanzu ma zaka temake ni?”

Ya ce, “ƙwarai kuwa me ze hana?”
Ta ce, “ka nemo min bayanan inda Jan ze kammala karatunsa da komai ina buƙatar sani, bayan haka inaso na kasance dashi kamar yadda muke da, ina fatan ka gane”

Duk da hakan be yi masa daɗi ba amma sai ya shanye cikin son kwantar mata da hankali ya ce, “wannan ai me sauƙi ce karki damu kinji ko?”
ta gyaɗa kai gami da cewa, “na gode Zaheer”
Ya ce, “to amma maza ki ci abinci”

Jan yana zaune ya yi fakare da alamu tunani yake, Natiee ce ta yi masa tafi a gefensa ya ɗan firgita amma da ya ga itace sai ya fuske,
Natiee Ta ce, “tunani tunani Jan? me yake sa yawan tunani ne??”
A taƙaice ya ce, “ina ruwanki??”
ta yi dariya gami da cewa, “ohh ya yi, ashe kenan kai ma kana tunanin? nifa tambaya nayi akan kaina ashe kaima kana yi?? to kenan kai tunanin me kake??”

Ya ce, “oho miki”
Zama ta yi a gefensa ta ce, “haba yayana na kaina gaya min mana ko nima baka so ka ji damuwa ta?”
Ya ce, “au tsufan naki za ki gwada min?”
Tace, “a’a gaskiya na gaya maka, ka ga ni a nawa ɓangaren bani da wanda zan faɗawa sirrin zuciyata sai kai kaɗai, amma kai sai kaita ɓoye mana”
ya ce, “hmm! Natiee tunani nake akan wata yarinya da take zuwar min a mafarki, na kasa gane wacece da nayi tunanin kece amma daga baya na gane ba kece ba, ko Zeety ce?? amma bana jin hakan, abunda yake sani damuwa kuma shine baƙar ƙaddarata banaso wani ya shiga cikin lamurana a rashin sanin waye ni har wani iftila’i ya faɗa masa ta dalilina, Zeety ta san ciki da wajena amma idan ya kasance ita wannan yarinyar wata ce daban zata shiga tsakanina da maƙiya na abun bazeyi min daɗi ba dan kuwa sakamakonta bazeyi kyau ba, Natiee ke ma kiyi tunanin ko zaki gano min ko wacece”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:52 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

 

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 14*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
Natiee ta ce, “to fa, ni kam kai da kake ganinta ka gaza ganewa ina ga ni wadda aka bawa labari?”
Ya ce, “ai kaji, do Allah ki tashi min anan ke da baki iya wani abun arziki ba”
Ta ce, “na yarda, idan ka gama Umminka na kira”
Tashi ya yi yana cewa, “jira ni mu je tare”

Hajiya Murja ce ta kalli Hajiya Saratu gami da cewa, “Hajiya! wai kuwa kina ganin ba muyi sanyi sanyi ba? a ganina kamar akwai abin da wannan matar take shiryawa”
Hajiya Saratu ta ce, “haba kwantar da hankalinki ai na gaba ya yi gaba, yanzu ba wata dubara da Aamina za ta yi mana a yanzu, amma idan ki na ganin akwai matsala to ki faɗamin ta ina zamu sha kan lamarin”

Hajiya Murja ta ce, “ban ga komai ba sai dai kwana biyu ban ji wani mummunan labari daga garesu ba kuma ina son ji”
Hajiya Saratu ta murmusa ta ce, “kar ki damu, akwai wani ɗanyen shiri da nake yi akansa”
Hajiya Murja ta ce, “menene?? gaya min ko zan ji daɗi”
Hajiya Saratu ta ce, “shirin nawa yanzu sharri zan yi masa wanda sai ya gwammace kiɗa da karatu, kowa ya ja da ni ai yasan ba ze kai ba, ganganci su ka yi daga Alhajin har Aaminatun kuma sai sun gane kurensu, sai sunyi dana-sanin haifar ƴaƴa biyun nan da suka yi, za su ce inama bamu haifi ƴaƴan nan ba”
Hajiya Murja ta tuntsire da dariya kana ta ce, “wannan abu ya yi, Allah ya bar min ke Hajiyata wallahi har na ji zazzaɓin da ya hauro min ya sauka”
Hajiya Murja ta yi dariya a ƙasaice ta ce, “ai ta yaro kyau take ba ta ƙarko Hajiya Murja”
Hajiya Murja ta ce, “wannan haka yake”

tashi ta yi ta fice daga ɓangaren Hajiya Saratun tana tafe tana murmushin mugunta a ranta tana ƙissima ranar da Hajiya Saratu za ta gama yi mata yaƙin ita kuma ta ɗaga tutar”

Hajiya Saratu kuwa da kallon yaro man kaza ta raka Hajiya Murja har ta ɓacewa ganinta sannan ta bushe da dariya har da tafa hannuwa, sai da ta yi me isarta sannan ta tsagaita cike da duniyanci ta ce, “ai bariki iyawa ce Murja, kina ganin duk wannan abun da nake yi dan ki amfana ne? inaa ai ba wannan maganar komai na yi kawai dan ni da ƴaƴana nayi, amfani kawai nake da ke Murja watan wata rana daga ke har Aaminar sai kun bani fagen”

Zahra ce ta kalli Zaheer cikin takaici ta ce, “kenan Yaya Zaheer haka kaima za ka biyewa wannan ƙaddararren son na Queen ko?, kai ne har zaka goyi bayan ta bi Jan inda ze yi karatu ko?”
Ya ɗan rausayar da kai sannan ya ce, “Zahra nifa ba maƙiyin Zuhra ba ne, sonta nake kuma son gaskiya ba na yaudara ba, dan ina sonta ba yana nufin zan tauye mata haƙƙi ko kuma na ƙi farin cikinta ba, hakan ba aibu bane Zahra dan haka na zaɓi hakan dan shine farin cikin silar farin cikina”
Zahra ta ce, “Allah Sarkin Baiwa kai kuma irin taka ƙaunar kenan, to Allah ya yi muku magani dukanku”
Zaheer yace, “amin kawai addu’a ya kamata mu yi mata dama, nasan Queen ɗita ba banzar mace bace dan haka banajin komai akanta Allah ze kare min ita daga dukkan wani kaidi”
Zahra ta ce, “to amma ai Daddy ya ce be amince ba gwara ta zauna ta koyi ƴan dabarun zaman gida na mata”
Zaheer ya ce, “eh haka ya ce amma na shawo kansa ai, kuma na sanarwa Ummata har ta yi masa magana a yanzun haka komai ya yi dai-dai”
Zahra ta ce, “to Allah ya bada nasara”
Ya amsa da “amin”

yau ma kamar yadda ya saba farkawa ya yi cikin zullumi sabo da wani bahagon mafarki da ya yi yana buɗe ido kamar wasa ya ga Ammar da Ameera ƴaƴan Yaya Fa’iza suna ta kai kawo a ɗakin nasa, da sauri ya gyara zamansa yana ƙara zaro ido tare da tunanin anya kuwa ba mafarki acikin mafarki yake ba?.
Lura da tashinsa da suka yi ne yasa suka yo kansa cike da murna suka ɗafe jikinsa, da kyar ya ce, “ƴaƴan-nan ku kam waye ya kawo ku gidanmu kuma ɗakina a yanzu?”

Ammar ya ce, “tare da su Ummata muke”
Haka kawai ya ji zuciyarsa ta buga ya kasa cewa komai sai ido da yake binsu da shi cikin sanyin jiki”
Natiee ce ta shigo cikin sanɗa tana cewa, “Ameera kar ku tashe shi mana kuzo mu je waje”
Ganin ya tashi ne yasa ta yi shiru tana kallonsa lokaci ɗaya zuciyarta ta yi matuƙar karaya, wasu zafafan hawaye suka shiga karyo mata, cikin ruɗani ya ce, “Jannatiee!! me yasa kike kuka kuma? ki faɗa min meke faruwa?”
Cikin rawar baki ta ce, “Jannah shi kenan zanyi nesa da kai kenan?”

cikin kaɗuwa da razani ya ce, “me???? Natiee kina haiyacinki kuwa? kodai har yanzu ban farka daga baƙin mafarkin nawa ba?”
Ta girgiza kai gami da sake fashewa da wani gigitaccen kuka me ƙarfi, da sauri ya diro daga kan gado ya riƙo hannayenta duka biyun a firgice ya ce, “tayaya Natiee?? tayaya za ki nesanta dani?? ki yi min bayani kafin zuciyata ta ida tarwatsewa Natiee ”
Cikin shashshekar kuka ta ce, “Jan zaka tafi karatu har na wani lokaci zamu dena ganinka”
Sakinta ya yi ya yarfa hannu ya dafe kai gami da rintse ido ya juya, sai da nutsuwarsa ta ɗan fara dawowa sannan ya ce, “ƙarya kike Jannatiee ba haka bane, don Allah ki ce tsokanata kike ba da gaske ba ne”

“gaskiya ba wasa acikinta YARO!!!”
Muryar Abba ce ta daki dodon kunnensa, ido warwaje ya maida kallonsa ga Abban bakinsa na kakkarwa da alama magana yake son yi ya kasa sai jujjuya kai da yake yi.

Sam ran Aba babu daɗi dan dai ba shi da zaɓin da ya wuce yin hakan, cikin danne ƙunar zuciyarsa ya ce, “ɗana komai na duniya da sannu ake binsa kar ka bari hakan ya zamo maka damuwa ni kuma hakan ze yi min illah, ni na yanke wannan hukuncin Yaro kuma ina son ka amince min ka yarda dani, ganin da ka yiwa yaran su Usaina to zuwa sukayi domin kuyi bankwana yau zaka tafi”

Baya baya ya yi yana tangaɗi har ya kai jikin garu sannan ya samu madogara ya jingina bayansa a jikin bangon cikin fitar haiyaci yake cewa, “Abana!! anya kuwa ba mutuwata ce take tinkarata ba?, Ummina Natiee Yaya Fa’iza Yaya Hassana Yaya Husaina Masoyiyata Zeety da abokaina da kai Abana duk ya zanyi na rayu ba tare da ku ba? Aba kasan cewa bana iya cikakken wuni ba tare da nasa Zeety a idona ba? Abana kasan cewa bana iya bacci me daɗi idan Ummina ba ta yi min addu’a ba? Abana ka sani ba koda yashe nake cin abinci idan ba tare da kai ba, Abana kasan cewa ganin Natiee a tare da ni shine yake yaye min ko wace irin damuwata?”

Zamewa ya yi ya zauna zaman ƴan bori a wajen sannan ya fashe da wani mugun kuka.

Ummi kam kasa ƙarasowa inda yake ta yi cikin sauri ta fice tana sharɓar kuka”
Hassana Husaina Fa’iza dukansu kukan suke yi sosai suma duk sun kasa magana,
Aba ne ya ƙarasa kusa dashi ya durƙusa a gabansa cikin sigar rarrashi ya ce, “yaro ka yi haƙuri, nasan hakan da ciwo sai dai ka yi haƙuri a matsayinka na namiji, kuma hakan ba umarni bane Alfarma ce nake nema daga wajenka kuma cike da ƙwarin guiwa da sa ran za ka yi min”

“ka dena kuka Muftahul’Jannah kai fa namiji ne ka ga ganin kukanka ya sa duk ahalinka da suke samun ƙwarin guiwa daga gareka duk sun sare, ka kalli yadda Yayyenka da tilon ƙanwarka suke kuka mahaifiyarka sabo da ba za ta iya jurar ganin kukanka ba ta kasa shigowa inda kake, kenan hakan shine girmanka? ba haka bane Jannah nasan za ka iya kai ba rago bane kuma nasan ba alfarmar da zan nema a gurinka ta gagareni bi’iznillah”

a hankali kukan nasa ya fara lafawa har ya yi shiru sai ciwon kai da ya kamu dashi a ɗan lokacin.
murya a cunkushe ya ce, “Abana ko da umarni ka bani bazan iya watsa maka ƙasa a ido ba bare alfarma, ni dai addu’ar ku nake so ta kasance a tare da ni a koda yaushe”

Abba ya yi ƙasa da kai ya goge hawayen da suka samu damar suɓutowa kan fuskarsa sannan ya ce, “na gode kuma na yi farin ciki Allah ya yi maka albarka ya yi jagora a dukkan lamarinka, yanzu ka rarrashi ƴan uwanka su dena kuka kar su yi ciwon kai”
Kai kawai ya iya gyaɗawa sannan ya tashi .

12:40pm jirginsu ya tashi, haka suka rabu cikin kewar juna shi yana kuka su suna yi.

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:53 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 15*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
“tunanin me kake kuma?”
Zahra ta jefawa Zaheer tambayar tare da kafe shi da ido.
Ya ɗan murmusa kafin ya ce, “tunaninta nake Zahra tabbas nayi kewarta kuma inajin ba daɗi kasancewar bata tare da ni, ko da nasan ba koda yaushe take da lokacina ba amma inajin daɗi idan tana nan dan nasa ina gaf da ita”

Zahra ta yi dariya sannan ta ce, “daga baya kenan ai yaya Zaheer, kaine kayi komai na tafiyarta sannan yanzu kana kewarta, wannan wane irin so ne?”
Ya ce, “son gaskiya kenan so na haƙiƙa shi nake yi wa Zuhra, kar fa wannan ya dameki Zahra kinsan komai yana ga Allah harmu ɗin kinga kuwa dogara gareshi shine mafi dacewa damu”
Ta ce, “wannan haka yake, ai kamar yau ne ma zaka ga ta dawo”
Ya ce, “in sha Allah”

Kai kawo Hajiya Saratu take faman yi tarasa inda za ta sa kanta, hankali tashe Hajiya Murja ta shigo ɓangaren nata tana ƙwala mata kira, Hajiya Saratu ta ce, “meye ne??”
Hajiya Murja ta ce, “shikenan an rusa shirinmu an karya alkadarinmu, wai ashe yaron nan ƙasar waje za su turashi a lokacin da muke son aiwatar da aikinmu akansa”
Cikin ɓacin rai Hajiya Saratu ta ce, “ba da ni ake zancen ba? to wallahi sai na jira ya dawo ya tarar da abin da na shuka masa kuma dole ya girba, sun yaudaremu mutanen nan kina kallo ko zama na kasa yi Hajiya Murja ai na fi ki shiga tashin hankali ji nake kamar zuciyata za ta tarwatse”

Hajiya Murja ta ce, “nasan dole za ki fi ni jin abun ai dan shirin komai naki ne temakawa ce kawai tawa”
Hajiya Saratu ta ce, “kar ki wani damu kanki Murja indai na haifu to fa sai nayi ɗai-ɗai da mutuncin Aamina da ahalinta”

Hajiya Murja ta ce, “za ki yi fin hakan ma, Allah ya dawo da shi lafiya”

Aba ne ya jinjina kai ya ce, “ikon Allah ashe bayanmu har da wata ce ta samu mazauni a zuciyar abokina”
Ummi ta yi dariya ba tareda ta kalleshi ba ta ce, “ƙwarai kuwa nima ɓoye min ake ba’a sanar da ni ba amma kasancewata uwa na iya fahimtar hakan tin ba yau ba sai gashi kuma a lokacin da ya fita daga hayyacinsa har ya furta maka sunanta, idan ka bibiya fa be sani ba kawai ruɗewar da ya yi ne”

Aba ya ce, “ba shakka a cikin zancenki ƙwarai, amma har yanzu na kasa gazgatawa”

Ummi ta ce, “ga kakakinsa nan ai ka tambayeta”
Da sauri Natiee ta ce, “wayyo Ummi me yasa za ki ce haka ”
Aba ya ce, “kenan ba za ki sanar dani gaskiya ba?”
Ta ce, “a’a Abana zan sanar da kai, kamar dai yadda ku kai tunani hakane ita ƴar makarantarsu ce kuma yana sonta sosai itama kuma haka”
Aba ya ce, “ma sha Allah zanje gidansu mu yi magana da mahaifinta sannan zan miƙa ban-haƙuri gareta a bisa hukuncin da na yanke akan Jannah kuma ya afku cikin gaggawa dan banajin ma ya sanar da ita kafin tafiyarsa”

Ummi ta ce, “to Allah dai ya dawo min da shi lafiya”

 

BAYAN WASU ƳAN SHEKARU.

cikin tsalle da murna Natiee ta shiga falonsu tana ƙwalawa Ummi kira, da sauri ta miƙe tsaye tana tambayar “lafiya?” Natiee ta ce, “lafiya ƙalau Ummi ki duba ki ga yadda na yi kyau dan Allah gaskiya nima kyakkyawa ce Ummina nasan idan ya dawo ba ze ganeni ba dan yanzu na ma fi da kyau”

Ummi ta taɓe baki ta ce, “uhmm Allah ya sauwaƙe shirme dai, kuma kinsani yabon kai jahilci ne ki bari a yabeki ba ki yabi kanki ba”

Natiee ta ce, “yi haƙuri Ummina nasani wallahi murna ce tasa duk na watsar da komai”
Ummi ta ce, “bakya yin koyi da ƴar’uwarki tin da ku ka dawo bayan sallama banji ta ce wani abu ba bare tace ta yi kyau”

Yaya Hassana da ta fito daga kicin yanzu ta shiga zancen da cewa, “wannan haka yake Ummi, Natiee duk da nasan kin haɗu amma tin da ki ka yabi kanki dolene Fatima ta fi ki kyau ko ƙanwata?”

Fatima ta yi murmushi gami da yin ƙasa da kai aranta tana tunanin shi wanda ze dawo ɗinnan har ake ta ɗoki da kwalliya da shirye shirye, zuwa yanzu itama har ta fara jin ta ƙagu ta ganshi fatan ta dai Allah ya kai ta goben da rai da lafiya.
Tunowa da ta yi bata gaishesu ba yasa ta yi saurin durƙusawa har ƙasa ta gaida Ummi bayan ta amsa ta gaida su yaya Husaina.

Yaya Fa’iza ta ce, “gaskiya dukanku kunyi kyau sai dai Umminmu duk ta fi ku, tasha lallenta ɗagwas dan ma dai ta ƙi kitso ta ce shine zeyi mata da kansa”

Natiee ta taɓe baki ta ce, “ai fa kishiyar tawa za ta dawo”
Suka yi dariya sannan su ka cigaba da fira.

Zaheer ya kasa zaune ya kasa tsaye sai sagaraftu shine wancan sashin shine wannan ƙetaren, daga falo zuwa waje daga waje zuwa ɗaki daga gidan Mammi zuwa gidan Umma.
jinjina kai Mammi ta yi ta ce, “tirƙashi wato Misbah yaron nan ba ƙaramin so yake wa Zuhra ba, ka duba ka ga yadda ya kasa zaune ya kasa tsaye sabi da dawowarta ƙarshe kuma idan ta dawo ɗin ta watsar da duk wannan hidimar ta shi ta cigaba da bautar wahala, gaskiya ina tausaya masa ainun”

Misbah ya ce, “bari dai Momu ina matuƙar takaicin abun na rasa ya ya zan yi ta ce bata sonshi shi kuma ya kasa denawa Mammi kinsan jarrabawar kowa da irin ta shi amma su kam tasu ba ta da daɗi da ita dashi ɗin duka”

Momu tace, “to Allah ya warware mana”
Ya amsa da “amin”

Misalin 03:00pm
Natiee sai sukur sukur ta ke ta buwayi kowa da tsalle tsalle duk ta gama shiri jira take ta ji ya kira ya ce ya iso ta nufi airport. tana zaune kan carpet kamar da wasa ta ji sallamarsa a falon, daskarewa ta yi saboda shakku ta ma kasa gane gaske ne ko mafarki.

“Alhamdulillah. Muftahul’Jannah barka da dawowa”
Ummi ta faɗa cikin tsantsar farin ciki yayinda idanunta suke kan Jancy.
Su Yaya Hassana ma duka miƙewa suka yi cike da murna.
Jancy yana dariya ya ce, “gaskiya Abana ka iya ba zata na gode dan Kuwa da bansan ta ya zan shigo musu ba”

Aba ya ce, “ai ba ni zaka godewa ba abokanka su zaka yi wa godiya dan kuwa sunyi maka kara sosai”
Sufee ya ce, “ai mune shi shine mu Aba wannan ai ba abin godiya bane abin da ya dace muka yi”

Murmushi Jancy ya yi kafin ya zame daga cikinsu ya nufi gurin Umminsa, kam ya rungumeta harda tsallensa yana dariya ita kuwa ba abin da take sai sanya ma sa albarka,
Kowa ya nuna farin cikinsa a lokacin amma ban da Natiee wadda har lokacin takasa motsawa gaba ɗaya ta rasa me ke mata ciwo”

Fatima kuwa ban da ido ba abin da take zuba musu tana daga gefe sai faman kallonsu take iyakaci idan ta gama ƙarewa Jancy kallo ta furta masha Allah a zuciyarta.

Kusa da Natiee ya zauna a marai-raice ya ce, “Jannatiee!! kenan baki ji daɗin ganina ba? ko dan ban gaya miki na iso ba? ki yi haƙuri ƙanwata ba dan saɓa miki hakan ta faru ba”

Ido ta zuba masa har wani lokaci kafin ta fashe da kuka tana cewa, “na rasa tayaya zan nunawa duniya farin cikin ganinka Yayana nafi kowa murna nafi kowa baƙin cikin tafiyarka, meyesa ka tafi ka barni Jannah? ba ka yi min alƙawarin kasancewa tare da ni ba? meyesa kuma ka tafi ba ka tafi dani ba?”

Ta ƙara fashewa da kuka tare da faɗawa jikinsa ta ƙanƙameshi, hannayensa yasa ya zagayeta gami da gyara mata zama, cikin tattausar murya ya ce, “Natiee idan baki manta ba bugun zuciyarmu tsere suke da juna tayaya wani ze wuce wani? kisa a ranki komai nisan da nayi ina tare da ke ko da kuwa mutuwa na yi bare kuma da sauran rayuwata gashi har na dawo gareki ƙanwata, kiyi haƙuri ki yafeni daga wannan bazan ƙara yin tazara me tsayi ba zan kasance tare da ku zan zamo muku tamkar danga ƙanwata, duk wani cin zarafin da akayi muku yanzu bazan bari ayi muku ba Natiee wannan alƙawari ne wa kaina zan mutu ina me kare martaba da kimarku”

kuka ne ya suɓuce masa me ƙarfin gaske, ba komai ne yake ƙara tunzura shi face ɗanyen aikin da yayyensa suka girbawa mahaifiyarsa da ƙanwarsa da ma duk wanda ya shafe shi, tabbas da ba yanzu ba ce akwai sauran hadari a ƙasa.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE*
[10/20, 2:53 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 16*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
a ɓangarensu Jancy kowa farin ciki yake yi. a ɓangaren su Hajiya Saratu da Hajiya Murja kuwa hankalinsu ya kai ƙololuwa wajen ta shi, musamman Hajiya Saratu ji take kamar ta yi hauka dan kuwa ko da wasa bata kawo dawowarsa a yanzu ba sai gashi ya dawo ba tare da ta shirya ba.

Zuhra kowa yana farin ciki da dawowarta amma ita ba ta yi, duk tunaninta da nazarinta suna ga Dogon Yaro, yanzu gani take tamkar ganinsa ma wahala ze yi mata dan kuwa ba ta da wata hanya da dalilin da zata ganshi.

Zaheer ya damu sosai da ya lura da yanayinta zuwa yanzu ya tabbatarwa kansa gaba ɗaya ba ta tunanin ma makomarsa har ya mutu ba lallai ya samu wata ƙauna bayan ta wa da ƙani daga gareta ba, amma duk da hakan ya ɗaukarwa kansa matakin sanyata farin ciki da ƙoƙarin nema mata abin da take so.

Zahra ce ta kalleta ta ce, “yanzu kuma me ya rage Yaya?, shin kin samu soyayyar ne? zaki rabu da Dogon Yaro ki rungumi ƙaddararki ko kuwa?”

Girgiza kai ta yi ta ɗan murmusa sannan ta ce, “abun da kamar wuya na iya rabuwa da Dogon Yaro, magana kike akan ƙaddarata kuma a iya sanina Jancy shine ƙaddarata dan haka batun rabuwa da shi bata tashi ba, ba na son ma irin zancen nan Zahra idan ma kin faɗa ba ganewa zan yi ba dan kuwa dubunki sun faɗa amma ba abin da ya sauya”

Zahra ta rausayar da kai tana ji kamar ta yi kuka, matuƙar tausayin yayar ta-ta ya kama ta.

Bayan kwana biyu.

Jancy yana zaune ya harɗe ƙafa yana danne dannen waya ya tsinkayi muryar Ummi tana cewa, “Fatima nemi guri ki zauna mana”
ɗago idanunsa ya yi ya zuba akan Fatiman yana tsammanin amsar da zata bawa Ummin, cikin sanyi ta ce, “aa zanje na yi kintsin kaya ne”
Ummi ta ce, “shi kenan ki hanzarta to”

Jan yana dariya ya ce, “Ummina wai waccan yarinyar wacece? ko dai Abana ne ya yo miki ta huɗu??”

Dariya Ummin ta yi ta ce, “kasan dai ɗiyata mace guda ɗaya ce, kenan bazan buƙaci ƙari ba?, iya tunaninka akan Abaka ya ƙare ko? ba ka yi tunani akan ƴar aiki ko dai wata ƴar uwa a gareka ba?, ta yuwu wata ƴar ɗan uwana ce”

Girgiza kai ya yi ya ce, “nasan Abana ba zai miki kishiya ba Ummina, to amma ke buzuwa ita bafulatana ta ya zata zama ƴar ɗan uwanki? kai a’a ƴar aikin dai Ummina nafi yarda da hakan”

Ummi ta murmusa sannan ta ce, “yana da kyau hakan, Abaka ya ce na sanar da kai yau ze yi baƙi abokinsa ze zo tareda iyalinsa domin su yi maka barka da zuwa”

Marai-raice fuska ya yi yana cewa, “ohh ni ɗa ɗaya tilo nifa duk harkar baƙi baƙin nan ba ƙaunarta nake ba, haba kawai salon a sawa mutum ido sai ace za’a wani yi barka da zuwa”

Natiee ta ce, “idan ba’a so abar gidan mana in ba tsoro ba?”
Kai tsaye ya ce, “tsoron ne to, kansakalar banza”
Natiee ta yi dariya ba tare da ta ƙara magana ba”

Tin da suka zo gidan take zazzare ido dan ta ganshi amma ya ƙauracewa ganinta har ta gaji ta haƙura, Kowa yana tofa albarkacin bakinsa a cikin firar da ake amma ban da ita sai ma ta yi ƙasa da kai kawai.
Tana cikin halin tunanin rashin ganinsa ta ji sallamarsa tare da abokansa, kasa ɗago kai ta yi saboda tsoro da shakkar haɗa ido da shi a wannan lokacin.

Shafar sumar kansa ya yi ya yarfa hannu tare da cewa, “kashshh, in ba na manta ance Abana ze yi baƙi wai harda iyalinsa dan abun takaici ban da haka da sai ɗayan dare zan dawo gidan”

Alamee ya ce, “fitar, ba wannan maganar abincin kuma da zan ci fa?”
Tsaki Jancy ya yi ya ce, “acici kawai”
Alamee ya ce, “ba komai na ji”

Ƙasa ƙasa Jancy ya yi da ido sannan ya ƙarasa falon yana shirin wucewa Ummi ta dakatar da shi da cewa, “Jannah ka zo ka gaishe su mana zaka wuce?”

ƙara sauke rumfar ido ya yi sannan ya nufo gurin, har ƙasa ya durƙusa ya gaishe su har Zahra dan kuwa be ɗago kai ya ga ko wacece ba.
Ze tashi Ummi ta ce, “ƴata tunanin me kike ne? ba ki ga yayan naki bane? ya kamata ku gaisa ai ko dan zumunci, Jannah ku gaisa da Queen mana”

“Queen??” ya maimaita sunan cikin sigar tambaya, sai da ta yi ta maza sannan ta iya ɗago idanunta ta juye akansa ko ƙiftawa ba ta yi, sai da ya gama nazarin inda yasan sunan sannan ya ɗago ya kalleta dan kauda tantamar da yake, “Subhanallah” ya faɗa lokacin da idanunsu suka yi arba da juna, cikin sauri Zuhra ta ce, “ina wuni”

Sai da ta ƙara mai-maitawa sannan ya yi ƙoƙarin gaske ya danne duk wasu tunanin da suka hautsino masa ya amsa da “lafiya”

Idanunta ne suka cicciko da ƙwalla gashi duk yadda ta yi ƙoƙarin dena kallonsa ta kasa, tana lure da yadda Zahra take zabga mata harara.

Miƙewa ya yi yana cewa, “Ƙanwati kawo min Bunu mana, yauwa ki haɗo da abinci saboda su Zuhair”

Da sauri Zuhra ta tashi tana cewa, “yauwa Natiee zan iya tayaki?”

Dogon tsaki Jan ya ja sannan ya wuce sashin sa tareda tawagarsa.

Natiee ganin damuwa ƙarara a fuskar Zuhra yasa ta ce, “kar ki fa damu akan wannan tsakin nasa shi dama haka yake akwai shi da son raha”

Murmushin ƙarfi da yaji Zuhra ta yi. suka runguɗa i zuwa kicin.

A memakon taya aiki sai ta raɓe a gefe tana sharar ƙwalla ba tare da ta bari Natiee ta gane ba,
har ta kammala abin da take ta ce, “to mu tafi ko?”
Sororo ta yi tana kallonta kafin ta ɗan murmusa ta ce, “idan ba damuwa inada tambaya Queen”

Zuhra ta ce, “bismillah”
Natiee ta ce, “mene tsakaninki da ɗan uwana?”
Rass zuciyarta ta buga, ta shiga zazzare ido cike da fargaba.
Natiee ta ce, “ki sanar dani mana, ko kuma so ne ko?”

Zuhra ta yi saurin cewa, “a’a”
Natiee ta ce, “yayana yana da wadda yake so shiyasa baya bi ta kan ko wace mace dan shi ba gama garin namiji bane, ni kuma ko soyayyar ma bana yi Queen, kinga kuwa ba zamu zo ɗaya dashi ba ta wannan fuskar idan kin gaya min ni zan yi wa maganarki kyakkyawan duba ne sakamakon shi da kai tsaye zai tuna masoyiyarsa, kinga Zuhra nima fa macece ko ban kai ki gayamin damuwarki bane a matsayina na ƴar uwarki mace?”

Zuhra ta girgiza kai gami da cewa, “a’a kiyi haƙuri, ba na ƙi bane amma..”

Natiee ta katseta da cewa, “temaka min ki ɗakko min fulas ɗinnan, ba komai ai kinsan kowa da nashi sirrin”

Zuhra ta ce, “amma ina Son Jannah SO me tsanani Natiee sai dai nayi rashin sa’a wata ta rigani, amma duk da hakan zan jurewa komai akansa ko me zeyi min bani da zuciyar da zan iya haƙura da binbini akansa, sabida na dinga ganinsa na tsallake komai na bi shi inda ya yi karatu nima na yi nawa acan, yanzun haka domin na ganshi ne nasa Yaya Zaheer ya takurawa Daddyna akan sai mun zo”

sosai jikin Natiee ya yi sanyi kalau, tausayin Zuhra ya kamata sosai, ba abunda take tunani sai tsananin so da ke tsakanin Jancy da Zeety tabbas me farraƙa wannan soyayyar sai Allah.

Zuhra ce ta katse mata tunani da cewa, “muje ko Natiee kar ya ga mun daɗe”
Natiee ta ce, “to”

Jancy. sanin ɗakinsa ne shi kaɗai yasa suka kutsa kai ba tare da tunanin ganin wani ba sai dai yana shiga ya yi tozali Da Fatima kwance akan gadonsa kamar na gadon gidansu.

Kai tsaye wajen ya nufa yana cewa, “kutt! ke uban waye ya kawo ki ɗakina?”

Da sauri ta miƙe cikin razani tana kallonsa da idonta da ya koma irin na munafukai. atake bugun zuciyarsa ya ƙara tsananta ya kasheta da kaifafan idanunsa masu matuƙar kwarjini da barazana.

Kamar za ta yi kuka tace, “Ummi ce tace na zo na kwanta ”

Ya ce, “kuma a naku ƙauyen mace tana kwana a ɗakin namiji ko??, fita daga nan ko na mammake ki, dama daga shigowa ta Allah ya haɗani da waccan bararojin me baƙaƙen idanu”

Kafin ya gama magana tini Fatima ta fice jikinta na tsuma sabida tsabar tsoratar da ta yi, ba ta ƙara tsinkewa da lamarinsa ba sai yanzu, lallai ta yarda Allah ya yanka mata kazar wahala yanzu yaya za ta yi da wannan ingarman mutum haka?”
Ta jefawa kanta tambaya sai dai bata da me amsa mata.

Zama ya yi a bakin gado yana jinjina kai cikin mamaki da juyayi yace, “nifa abun nata ma yarinyar nan tsoro ya bani, ko Natiee idan bana ɗakin nan bata shigowa bare ita bare, anya kuwa ba ta da taɓin kai?”

Jin sunyi shiru ne yasa ya kallesu a ɗan hasale ya ce, “ya ina magana duk kunyi shiru dan iskanci”

Sufee ya ce, “a’a to ai abun ne ya girmi kanmu shiyasa muka kasa magana, nima abun ya ɗauren kai”
Zuhair ya ce, “wai ma wacece?”
tsaki Jancy ya yi ya ce, “ƴar aikin Ummina ce fa, kawai dan ance ta je ta kwanta sai ta zo gadona ta kwanta tsabar hauka”

Alamee ya murmusa sannan ya ce, “anya kuwa yarinyar nan ba ta da dalilim zuwa ɗakinka ta kwanta??, nasan yarinyar tin kafin ka dawo dan muna zuwa mu duba lafiyar su Ummin kuma naga kamar tana da nutsuwa sosai kamar ma ba ƴar ƙauye ba, kuma ka yi tunani ka gani”

Zuhair ya ce, “kuma wallahi ka faɗi gaskiya Alamee da yuwuwar akwai wata a ƙasa, to amma mene??”

Sufee ya ce, “anya kuwa ba da wata manufa ma yarinyar nan take zaune da su Ummi ba??, yarinya da zubin munafukai haka?”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE*
[10/20, 2:54 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 17*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
Jannah ya ce, “naga alamun gaskiyarka Alamee nima da na yi tunanin tana da nutsuwa amma yau ɗaya na gane asalin mara kan gado ce”

Sallamar Natiee da Zuhra ce ta katse musu maganar da sukeyi, cikin haɗe rai Jancy ya ce, “abin da ba wani aiki ba amma sai kin nemi tayo kawai salon ki ɓata min rai”

Zuhra ta tari numfashinsa da cewa, “Allah ya huci zuciyarka Bawan Allah, ba itace ta nemeni ba nice na buƙaci hakan amma ka yi haƙuri”

Dogon tsaki ya zabga wanda yasa ta rintse dan kuwa sosai tsakin nasa ya bugi zuciyarta.
Zuhair ya ce, “kai da akaiwa gwaninta kuma kaine da faɗa, yawa ne fa Dogo ka barta da abin da yake damunta ma kawai ya isheta”
Jancy ya ce, “ba kuma zata tarkata ta bar min ɗaki in dena ganin farar fuskarta ba”

Zuhra ta yi murmushin tausayin kai sannan ta ce, “yanzun ma kuwa ba dan ka yi magana ba ma da tini na fita ai”

Wani shegen kallo ya kora mata sannan ya kauda kai tare da yin tagumi da hannunsa na hagu.
Alamee ya ce, “Zuhra idan ba damuwa ki koma do Allah kar abun ya fara yawa”

Ba tare da ta ce komai ba ta fice Natiee ta mara mata baya,
Suna fita Fatima ta dawo da sallamarta.
idanu ya waro akanta cike da son jin tsiyar da ta ƙara dawo da ita, kanta a ƙasa ta ce, “Ummi ce ta ce na sanar da kai Abaka na nemanka zaka gaisa da abokinsa”

Hannu biyun yasa duka ya zuba wani sabon tagumin ya yi tsamm.
Sufee ya ce, “ke wai a ina kika ga mace tana shiga ɗakin namiji kai tsaye?, yar wahala kai”
Alamee ya ce, “kashhh meye na wannan kuma? dalla basar kawai, ke kice yana zuwa”

Bayan ta fita Jancy ya ce, “da yaushe?? kuma da ya akai? me ya faru har Abbun yarinyar nan ya zama abokin Abana?, wayyo Tawa ƙaddarar”

Zuhair ya ce, “share mana haba, wai har yanzu kamar ba namiji ba? yanzu fa ka girma”
Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita ba tare da ya yi magana ba.

sai 10:00pm su Zuhra suka bar gidan, bayan nan shi kuma ya dawo daga rakiyar abokansa zuwa gida, kamar an sauke masa kaya a kai haka ya ji da ya tarar basa nan, kai tsaye sashin Aba ya wuce.

Dakatawa ya yi sabi da ganin Haisam da ya yi zaune kan kafet, sai motsin bakinsa kawai ake gani sai zarar zance yake Aba kuwa ya yi shiru yana saurarensa.
Har ze juya Aba ya ce, “ƙaraso Yaro magana ce wadda ta dangan-ceka”

Gabansa ne ya yanke ya faɗi, cikin Zullumi da fargabar abin da Haisam ya faɗawa Aban nasa ya ƙarasa ya zaune kusa da ƙafafun Aban, irin mugun kallon da Haisam yake jifansa dashi ne yake ƙara rikirkita shi.

“ya zama dole gareka ka iya sarrafa raunin zuciyarka da haka ne zaka tinkari duk abin da ya shige maka gaba kuma zaka yi gaba da gaba da duk wani gwarzon da yake son ganin bayanka, idan ka farfaɗo da zummar zuciyarka tabbas zaka yi wa maƙiyanka kwarjini ko da rundunarsu ta fi su dubu ba adadi”

Yarinyar da yake yawan mafarki da itace take yawan faɗa masa maganar da kuma makaman-tanta, ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido, dai-dai lokacin Aba ya ce, Yarona magana suke akan kasuwan-cinmu, ya ce akwai wani kamfani da yake son haɗa cinikaiya da mu”

Jancy ya gyara zama ya ƙara haɗe rai, cikin nuna isa ya ce, “ban amince ba Abana ba na ma buƙatar irin wannan shirmen zancen, a sanar dasu buƙatarsu bata shiga ba”

a hautsine Haisam ya ce, “kai ɗin wa? akan me zaka ce haka? ai ni zanji da komai ba wai kai ba”
Jancy ya ce, “na sani ai, akan bana son irin wannan kasuwancin ne yasa nace haka, bari na ƙara mai-maita maka ba za muyi ba, ina fatan ka gane sai a koma a isar da saƙona ”

Haisam ya harzuƙo ze yi magana Aba ya ce, “ba buƙatar ka ƙara cewa wani abu, ka sanar da su abin da Yaro ya ce, sannan ka gaggauta bamu guri zamu yi magana me muhimmanci”

Haisam ya tashi ya fice cikin fushi da ɓacin rai kamar me shirin yin faɗa da iska.
kafin Aban ya yi magana Jancy ya ce, “Abana wai ya akai Alhaji Abdussalam ya zamo abokinka?”
Aba ya ɗan murmusa ya ce, “mamaki kake? bayan ka tafi muka zama ɗaya, ta fannin kasuwan-cinmu muna temake-keniya wa juna, daga gareka ban samu ƙwararan hujjojin da zasu hana mu mu’amala da juna ba dan haka kawai na yarda da kai ne a lokacin dan bana son dakushe tunaninka, ɓacin ranka shine kawai bana so”

Jinjina kai ya yi sannan ya ce, “Aba wace maganar zamu yi ina ji”
Aba ya yi murmushi sannan suka cigaba da tattaunawa.

Tin sassafe ya ji alamun mutum akansa sai kurin kurin akeyi amma ya yi banza dan kuwa baccin be isheshi ba, be fi minti goma da jin hakan ba ya ji an fara ƙwala masa kira, a ɗan razane ya tashi saka-makon mafarki da yake, lokaci ɗaya ya ware idonsa yana neman me kiran sunan nasa cikin sa’a sukai ido huɗu da Fatima wadda take kallonsa kamar hoto,
Cikin sauri ya tashi ya zauna cikin ɓacin rai ya ce, “ke wai wace irin Kuɗɗe ce?? yanzu kuma me ya kawoki gurina? ko dai na ci miki bashi ne kike bibiyar haƙƙin ki?”

Ɗan ƙasa ta yi da kallonta tana murmushi sabi da jin abin da ya ce ɗin, aranta ta ce, “ina da haƙƙi akanka sosai Jannah dan dai ba ka sani bane, sai dai hakan bashi da wata fa’ida”
Mai-maita mata tambayar da ya yi ne yasa ta yi saurin ɗagowa tare da cewa, “na’am au dama gyaran ɗakin nake yi shine kuma nazo gyara gado”

Sai da ya kalleta sama da ƙasa kafin ya ce, “fita” ta ce, “amma ya..” katseta ya yi ta hanyar mai-maita mata abin da ya faɗa ɗazu,
Ba dan ta gaji da ganinsa ba ta fice daga ɗakin saƙwal, can wani ɗan loko ta koma ta raɓe sannan ta bawa kukan da yake cinta damar fitowa sarari tsananin tausayin kanta da tausayinsa ne yake ƙara karya mata zuciya a gefe guda kuwa ga wani abu me kama da so da ya yi mata kaka-gida a zuciyarta, lallai idan ya kasance ta kamu da son Jancy ba shakka ta faɗa matsala fiye da da.

Jancy kuwa Jallabiya ya zura sannan ya fito, tin daga falo yake ƙwalawa Ummi da Natiee kira, da yake suna kicin ba bacci suke ba yasa suka jero suka fito dan kuwa kira yake musu sama sama.

Cikin matuƙar ɓacin rai ya ce, “Nan ko za ku ɗauki ƴar aiki me yasa zaku ɗakko mahaukaciyar can, na tsani wanda ze shiga rayuwata ba tare da na gaiyaceshi ba, waccan bata dace da zama ƴar aikinki ba Ummi dolene a sallameta, ballagazar banza, kin ce ta je ta kwanta ta tafi gadona ta kwanta, yau tin ban tashi ba taje tana yi min ƙwale ƙwale aka wai da sunan gyaran ɗaki duk hakan be isa ba sai da ta tasheni, da na fito na sameta a falon nan sai na yi ƙasa ƙasa da ita shashashar banza”

Ummi ta buga tsaki sannan ta ce, “ya isa haka mana Jan, a tunaninka wai ƴar aikina ce? cikin maganar da na gaya maka akanta baka tsinci komai ba banda wannan kalmar?, to kar ka ƙara kiranta ƴar aiki domin kuwa matarka ce ni kuma sirikata ce tamkar ma ƴa nake kallonta”

Ido warwaje da alamun razani da kaɗuwa ya ce, “mata?? mata dai Ummi, ahh a’a gaskiya, ni?? kai haba da wasa kuke min”

Ummi ta ce,
“tabbas mun saba zolayarka da wasa amma ba mu taɓa yi maka maka-mancin wannan ba, ita ɗin matarka ce”

ya ce, “Ummi amma kun sani duk faɗin duniya ni Zeety kawai nake so, me yasa zaku yarda ku auramin wata? me yasa baku tambaye ni ba tayaya zan iya zama da wannan yarinyar bayan ina bala’in son Zeety?”

Ummi ta ce, “Ban sani ba Jancy iya abin da na sani shi na gaya maka, kaje ka tambayi Abanka ze gaya maka dan kuwa shine ya amince ya ɗaura aurenka da ita, kuma ma nice nace ta dinga kwana a ɗakinka dan kasan bazan barta ta dinga kwana a gidan nan ita kaɗai a ɗaki ba, Natiee ma tare muke kwana kuma tinda kana nan banga amfanin ni na kwana ni kaɗai ba gwara ita tazo gurinka tin da matarka ce dolenka ce ”

Juyawa ya yi ya nufi hanyar sashin Aba, Ummi ce ta dakatar dashi da cewa, “yau fa Abanka baya sashin nan, yana ɓangaren su Hajiya Saratu ka jira ya fito tukunna”

Neman guri ya yi ya zauna ya yi tsitt ya rasa ma bakin magana sai dai kallo.

Koda Aba ya shigo sashin nasu bayan gaisuwa be bari anyi wata maganar ba ya shiga jerawa Aba tambaya har da ta fitar haiyaci.

Aba ya gyara zama sannan ya ce, “mahaifinta babban mutum ne a ƙauyensu, ina matuƙar ganin mutuncinsa shima yana ganin nawa, kasancewar ita ɗaya ce yarinyarsa mace yasa yake ta tsoron sharrin mutane akanta Allah ne kawai yake kuɓutar da ita, daga bisani ya yanke hukunci bayar da ita wa ɗana idan na amince, ni kuma naga hakan ya yi shine na yarda, kana ƙoƙarin yin komai domin ni a wannan karon ma ba na so ka bani kunya ɗana”

Be ce komai ba ya tashi ya koma ɗakinsa, kamar ya yi kuka yake ji sai dai ya ƙoƙarta ya ƙi yin.

abokansa suna zaune suna hira ya iso wajen babu alamun walwala a fuskarsa, da tambayar abin da yake faruwa suka fara tarbarshi, a taƙaice ya ce, “wannan yarinyar”

Sufee ya ce, “eh wannan yarinyar sai akai me?”
ya ƙara cewa, “wannan yarinyar fa ta gidanmu”
Abubakar ya ce, “me ta yi wai?”
Ya ƙara cewa, “ita fa wannan yarinyar”
A ɗan hasale Zuhair ya ce, “ɗan iskan mutum kazo ka ishe mu da wannan yarinyar kana magana sai kace wani mace, budurwa ce za’ayi mata tambaya akan saurayi ta zauna tana shine shine amma ba namiji ba, ka ƙara cewa ita ɗinnan sai na baje maka baki dallah”

Alamee ya ce, “wai ƴar aikin Ummi?”
cikin ɗaga murya ya ce, “ba fa ƴar aiki bace ba MATATA CE”

haɗa baki suka yi dukansu wajen cewa, “MATARKA?????????”

 

 

Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/20, 2:54 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 18*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
Ya ce, “ƙwarai kuwa, ni ba hakan ne ma ya fi tsorata ni ba, bansan tayaya zan fahimtar da Zeety ba gaskiya sun sakani a wahala, har naji na tsani ma yarinyar nan wallahi”

Alamee ya ce, “gaskiya akwai damuwa amma kuma yin shirun ba shi da amfani faɗa mata gaskiya sai ya fi, ban da haka da sai mu ƙi gaya mata”

Abubukar ya ce, “ai ya zama dole ta sani, gwara ma a sanar da ita tin kafin ta ji a wani wajen”

Zuhair ya ce, “jarumta ce ta kamaka Jan dan kuwa sai ka daure”

Be iya cewa komai ba dan kuwa ko ya faɗa ba abu me ma’ana ze faɗa ba dan haka ya yi shiru.

Haisam ne ya kalli Hajiya Saratu cikin takaici ya ce, “Hajiya yanzu shi kenan mun rasa damar nan?, wai wannan yaro ya gaje mana komai gaba ɗaya dukiyar Alhaji ta zama ta shi”

Hajiya Saratu ta ce, “nasarar tawa ce, bazan taɓa yarda na karɓi faɗuwa ba dan haka tin da be yarda da hanyar da kaje da ita ba dole ya ya yarda da wadda zan je masa da ita, ba shakka sai munyi tsaye akan yaron nan idan ba haka ba wata ran za mu zama bayinsa ne”

Haisam ya ce, “na tsaneshi dukansu ma bana ƙaunarsu, kawai asan yadda za ayi a kasheshi Hajiya”

Hajiya Saratu ta ce, “kar ka damu Haisam, nima na yi wannan tunanin kasheshi shine ze kawo mana mafita ta haka ne komai ze dawo hannunmu”

Jaafar da ya shigo yanzu ya ce, “nima wallahi na tsani yaron nan mafi sauƙi kawai mu ɓatar dashi”
Hajiya Saratu ta ce, “faɗe ma ɓata baki ne ku dai ku zuba ido kusha kallo”

Jannah cikin sauri yake tafiya hankalinsa ya riga ya yi gaba be ankara da tafowar Bomboi ba sai dai yaji sunyi karo, Bomboi yasa iya ƙarfinsa ya bangaje shi da kafaɗa har sai da ya yi baya.

Cike da masifa da tsananin ƙiyayya Bomboi ya yi kansa da duka ko ta ina ya na cewa, “ni sa’anka ne da zaka zo ka bangajeni? baka san idan manya sun tawo ka dinga basu hanya ba?”

Zamewa Jancy ya yi zuwa gefe tare da cewa, “ya isa haka ai ka amfana”
Bomboi ya ce, “na amfani uban me??, rashin kunya zakai min?”
Jancy ya ce, “ba rashin kunya zan yi maka ba, ina nufin ka moreni a barni haka tin kafin na dawo da raddi”

Ƙara masa wani shigaggen mari ya yi yana cewa, “maza ka maido da raddin”
Cikin ɓacin rai Jancy ya ware dogayen yatsunsa guda biyar ya zabga masa marin da sai da wutar kansa ta ɗauke baki ɗaya, ya dafe gurin ya ɗan sunkuya idanunsa a rufe garam sabi da raɗaɗin azaba ya hanasu buɗuwa”

Jancy ya ce, “jiya ba yau ba Yaya Bomboi, kun riga kunyi sake da ku ka barni na girma, sai na saita zamanku ɗaya bayan ɗaya, masu son zuciya kawai”

Daga haka ya yi gaba ya bashi guri, Bomboi ya na buɗe idanu a idonsa ɗaya hawayen da ba na kuka ba na wahala suka zuraro zuwa kan kumatunsa, hannu ya sa ya shafa ya ƙara kallar hawayen, cikin zaro ido ya ce, “wannan yaron ne ya sakani hawaye haka? wallahi bashi ka ɗauka sai ka biya”

Tsaki kawai Jancy yake dokawa har ya isa gidansu Zeety, dama jiransa take yana zuwa ta fito ta shiga motar tashi,
Ganin shatin yatsu akan fuskarsa ne ya tashi hankalinta, a ruɗe ta shiga tambayar ba’asi, cikin taushi ya ce, “Zeetyna kar ki damu da wannan yanzu bana jin zafi sabi da na rama”
Numfashi ta sauke ta ce, “naji daɗi da ka nuna musu zarrarka nasan dole abun ze girgizasu”
Ɗan kauda kai ya yi sannan ya ce, “bazan iya yi miki ɓoye ɓoye ba Zeety shin za ki cigaba da sona kamar da idan ki ka saurari abin da zan gaya muki?”
Duk da abin ya zo mata wani baibaice amma sai ta shamuƙe dan kuwa ba wani dalilin da ze sa ta dena sonshi, a sanyaye ta ce, “ka ɗauka kawai kaine zuciyata Jan, yadda bazan iya fushi da ita ba har na ji na dena sonta haka bazan iya yi maka ba domin kuwa da kai da ita duk abu ɗaya ne, zuciya itace ginshiƙin mutum ni kuma kaine ginshiƙina”

Idanunsa masu ɗauke da zallar damuwa a cikinsu ya zuba mata kafin ya ce, “Abana ya yi min mata har ya auramin ita, dan Allah kar hakan ya sa ki dena ƙaunata idan ki ka barni ba shakka ni kuma duniyar zan bari”

Ido ta zazzaro akansa atake hawaye suka fara sakkowa daga cikinsu cikin rawar murya ta ce, “Jancy!! ka sani duk duniya na fi kowa sonka da kai kaɗai nake so na rayu kuma inaso in rayuwa da kai cikin farin ciki ba tare da wata damuwa ba, ni kaɗai nake so na fi kowa na duniya kusanci da kai, yanzu kenan wata ta yi min shamaki da kai, wayyo Allah na shiga uku na lalace”
Taƙarasa maganar tare da rushewa da kuka me tsanani, Jannah ze yi magana ta yi saurin ficewa da ga cikin motar ta koma cikin gidansu tana kuka.

waya ya cira ya fara kiran lambarta amma ta ƙi ɗagawa sai ma ta kashe wayar muɗus daga baya.
Ba yadda ya iya haka ya koma gida cikin tsananin damuwa har wani ɗan zazzaɓi zazzaɓi ne ya fara sakko masa.

Fatima ce kaɗai a falon tana ta ƴan gyare gyare dan kuwa akwai ta da tsafta bata so ta ga abin da ba dai-dai ba ga Natiee ita kuwa bata gajiya da ɓata guri itace shan alewoyi ta zubar da ledar itace ci wancan ci wancan.

Tin da ya shigo ta dakata da aikin ta zuba masa ido ba tare da tasan manufar kallon da ta ke masa ba, a ƙasan zuciyarta kuwa tunani ne kala daban daban a gefe guda kuwa ganinsa cikin matuƙar damuwa da ta yi ya taɓa mata zuciya sosai, lokacin ɗaya gabanta ya shiga faɗuwa da ta tuna wani abu guda ɗaya.

Har ya wuceta sai kuma ya juyo murya a cunkushe ya ce, “Ummina”
ba tareda ta dena kallonsa ba ta ce, “tana falonta”
Shima kallonta ya shigayi cikin mamakin irin wannan kallon ƙurillar da take masa ko kunya ba ta ji, kamar ya hau kanta da duka sai dai yasan yin hakan kuskure ne a matsayinsa na mijinta, sai da suka haɗa ido sannan ta zabura sabi da kaifin idonsa sai da ya danne nata ganin, cikin rawar baki ta ce, “ina kwana?”
Dogon Tsaki ya doka kafin ya nufi ɗakinsa.

Fatima ta bi bayansa da kallo tare da tunanin meke damunsa?.

Zuhra cikin damuwa ta ce, “Zahra magana nake kinyi mun banza ki gaya min wace hanyar zan bi na haɗu da shi?”

Zahra ta ce, “me zan ce miki kuwa? ai idan ba gidansu za ki je ba ba ki da wata mafita”

Wasu sabbin hawayen ne suka ƙara sukwanowa daga idanunta zuwa waje, cikin rawar murya ta ce, “ki yi tunani Zahra, ba ni da ƴar uwa mace sama da ke dan Allah ki yi tunani, idan ban gansa ba mutuwa zan yi”

Shiru Zahra ta yi cike da tausayawa take nazarin mafitar da za ta samawa ƴar uwarta, bayan ɗan wani lokaci ta ce, “ki je kamfaninsu idan za ki same shi dan ba ko da yaushe ne ya ke zuwa ba”

Da sauri Queen ta ce, “da gaske zan iya ganinsa acan?”
Zahra ta ce, “ba ni da tabbas amma kuma matsalar kamfanin nasu ba ɗaya bane ba biyu ba, yauwa kawai idan ba ki same shi acan ba ki tare kwanar layinsu ki dai-daici lokacin fitarsa sai ki ajiye motarki yadda ta shi ba za ta wuce ba kinga dole ze tsaya sai ki ganshi, amma gaskiya kin fiye zaƙewa da yawa Yaya wallahi nuna masa son da kike ma kawai ya isa ya wulaƙantaki kinsan wasu mazan akwai aji har sun fi wata macen ga shegen jin kai a gurin ɗa namiji, mace ce kawai za’a buɗi baki ace ana sonta ta yarda amma banda namiji, da zarar kin furta masa wannan kalmar gani zeyi kamar kin rasa makama ne ko ba ki da wanda ze so ki, maza ta wannan fuskar sun fi mu wuyar sha’ani, dan haka yana da kyau ki kula”

Tana gama saurararta ta ta shi tana faɗin tin da dai kin gama kinga tafiyata,
Zahra ta bi ta da kallo me cike da tausayawa, babu shakka yanzu ta yarda SO yana haukatarwa dan kuwa ya haukata yayarta.

Cikin sauri ta shirya cikin doguwar rigar leshi ko kwalli ba ta saka ba bare hoda ta ɗaura ɗankwali akan goshinta ko ɗaure gashinta da babu kitso ba ta yi ba dan haka ya samu masauki a gadon bayanta ya barbazu cikin sauri ta fesa ture, a falo ta ƙarasa yafa mayafi ta sa takalmi, mukullin mota kawai ta ɗakko ta yi hanyar fita da gudu gudu, “Queen!!!” cak ta tsaya sabi da kiran da Mammi ta yi mata cikin ranta tana addu’ar kar ta hanata fita.

Mammi ta ce, “saurin me ki ke kuma ina za ki je?? har za ki fita ba ki sanarwa kowa ba”

Cikin rawar baki ta ce, “zan..zan..zan. je”
Zahra ce ta bada amsar da cewa, “Dogon Yaro za ta je gani”

Mammi ta riƙe haɓa gami da cewa, “too? ikon Allah amma shine ba za ki gayawa kowa ba za ki fita?? kuma kiranki ya yi ne Har kike wannan karkarwar?”

Ƙasa ta yi da kai cikin rashin sanin amsar da za ta bayar, Zahra ce ta ce, “ai Mammi ta gaya min ni kuma zan gaya miki, Queen ki ta fi kawai sai kin dawo”

Dama jira take dan haka ta ce, “to sai na dawo Mammi sai na dawo”

Mammi ta rakata da ido kamar tai mata kuka, sai da ta fice sannan ta ce, “Allah sarki ni dai bazan hanaki ba Queen Addu’ar da nake miki kaɗai ta isa, Allah shine ya ɗora miki kuma shi ze yaye miki damuwarki”

Zahra ta murmusa cike da jin daɗin maganar mahaifiyar tasu yanzu ba ta da shakka akan Mammi tin da hakan be ɓata mata rai ba dama tsoron da takeyi kenan amma yanzu komai ya zo da sauƙi.

Kai tsaye kamfanin ta nufa cikin sa’a tana fitowa daga mota idonta ya sauka akansa yana ƙoƙarin shiga tashi, cikin sauri ta matsa kusa dashi tana tunanin ta inda za ta fara, ganin ze wuce ya barta yasa ta yi saurin cewa, “Jannah!!!!”

Cakkk ya tsaya yana nazarin muryar sannan ya juyo fuska a haɗe ya zuba mata idanu cikin harshen buzanci ya ce, “meye kuma??”
Ƙarasawa ta yi sannan ta ce, “dan Allah ka tsaya ka saurareni”

Kai tsaye ya ce, “dole ne??”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/21, 9:43 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 19*

 

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

(Yachin banyi EDITING sosai ba🤣🤭 sai kun kula da error typing)

 

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
ta ce, “ba dole bane amma ka ji tausayina dan Allah ka saurareni”

ido ya zuba mata da alamun yana sauraron abin da za ta faɗa, cikin sauri ta ce, “dan Allah za ka ɗaukeni aiki a kamfaninku?”

Shafar kansa ya yi tare da cewa, “ashsha, ke da kike likita amma tsabar ba ki san inda ke muki ciwo ba aikin kamfani za ki fara, to ki baza kunnenki ki ji indai saboda ni ne ki ma dema marmarin aiki a ƙarƙashin kamfani domin kuwa yanzu ina da mata, Faɗimatu itace zaɓin Abana a gareni ni kuma zaɓina Zeety ce ba kinga yanzu ba ki da gurin shiga ya kamata ki san inda ke miki ciwo”

Daga haka ya shige mota ya barta a tsaye, da ido ta raka shi har ya ɓacewa ganinta sannan ta koma cikin motarta ta rufe ta fashe da kuka.
Sai da ta yi me isarta sannan ta nufi gida ba ta bi takan kowa ba ta wuce ɗaki ta ƙara kullewa.

Jancy duk ya shiga damuwa sabi da fushin da Zeety take dashi kwata kwata ma ta ƙi saurarar shi bare har ya iya shawo kanta.

a ɓangaren Hajiya Saratu, Hajiya Murja ce ta kalleta tana dariya ta ce, “wato yanzu kuɗi muke buƙata ko Yayata?”
a ƙasaice Hajiya Saratu ta murmusa sannan ta ce, “ƙwarai kuwa dan haka na shirya yadda za’a sace ƴaƴan yayyensa”

Bomboi ya yi zaram ya ce, “wanne ya kamata a sace ne??”
Hajiya Murja ta ce, “manyan Ammar da Ameera”

Hajiya Saratu ta ce, “ba haka ba, idan kana son cin galaba akan maƙiyinka ana so ka taɓa wani abu wanda kasan dole sai ya girgiza shi har ya karya lagonsa ƙarashen aikin kuma naka ne, dan haka Mubeen da Mubeena ƴaƴan Hassana da Usaina su za mu sace, kunsan sabi da me?, jami’ar CID ɗinmu ta kawo min labarin cewa bayan mahaifiyarsa ƙanwarsa mahaifinsa da budurwarsa ba wanda yake so aduniya sama da waƴannan ƴa ƴa guda biyuya fi sonsu fiye da sauran ƴa’ƴan da kuka ambata dan haka takansu za mu fara bayansu sai mu yi tunanin takan waa za mu faɗo”

Bomboi da Haisam suka tafa suna dariyar farin ciki, Jafar ya ce, “wallahi Hajiya kin iya tsara komai yadda ya kamata”

Sultan ya ce, “wannan magana haka take, to amma baza’a cutar dasu ba?”

Hajiya Saratu ta ce, “iyayensu ƴa’ƴana ne dan haka na zaɓesu ma fiye da kowa dan kuwa yanzu su Hassana ba su da amfani a gurina tinda har za su iya zuwa gidan nan su tsaya iya sashin Aaminatu sabi da gurinta suka zo, ni kuma mahaifiyarsu ina nan ko zuwa su gaishene sai sun ga dama basa ɗaukar duk wata huɗuba tawa daga baya ma sai suka ƙi ni suka komawa maƙiyama dan haka ya zama dole su san ba’a taɓani a zauna lafiya sai na yi musu hukunci”

Sultan ya ce, “shiyasa nake son ki Hajiyarmu wallahi ko ba ki ce a taɓasu ba sai nasa anyi wani abun dan kuwa na tsani ganin Dogon Yaro cikin farin ciki”

Hajiya Murja ta ce, “yanzu to yaushe za’a sace su?”
Hajiya Saratu ta ce, “wannan duk ni zan yanke zan dai-daici lokaci mafi sa’a sannan a gudanar, ita kuma ƴar wasanmu za ta samu gwaggwaɓar kyauta dan kuwa aikinta yana kyau”

Jancy yana tsaye a ƙofar gidansu Zeety cike da zullumin abin da ze biyo baya duk da baya tsammanin za ta fito, yana nan tsaye kuwa ta fito fuska koɗai koɗai da alamu kuka ta gama yi, cikin sanɗa ta ƙaraso onda yake idanunta akansa yayin sa sshima nasa idon yake akanta, kamar ze fashe da kuka ya ce, “me yasa kike Fushi da ni? na shiga wahala sabo da kin ƙi saurarata amma hakan be sa na gaza ba nidai har yau ban dena ba ina matuƙar ƙaunarki Zeety amma ban san a naki ɓangaren ko har yanzu ina da wani matsayi ba”

Murmushi me haɗe da ƙwalla ta yi ba tare da ta ce ƙala ba, hakan kuwa ba ƙaramin karya masa zuciya ya ƙara yi ba, hawaye ne suka cicciko idonsa cikin tattausar murya ya ce, “da gaske nake kece raunina kuma kece ƙwarin-guiwata, kullum sai na yi kuka kafin baccina farin cikina ya samu tangarɗa sabo da ba kya tare da ni, shin da gaskene sabo da na yi biyayya ga mahaifina shime ze jawo rabuwarmu?”

Da sauri ta girgiza kai tana murmushi gami da hawaye cikin rawar murya ta ce, “bazan iya rabuwa da kai ba Jannah tsananin kishinka da nake ne yasa na kasa gane kaina, ba wani dalilin da ze sa na gujeka har abada Inasonka”

sai a lokacin hawayen da suka cika taf a idanunsa suka samu damar zirarowa, cikin muryar da baya fita sosai ya ce, “da gaske kin dena fushi da ni?”

ta ce, “ka dena zubar da hawayenka My Love domin suna da muhimmanci matuƙa hakan kuma yana ƙona zuciyata sosai”
“Na gode My Love”

Ya faɗa tare da sake kasheta da narkakkun idanunsa.

Zuhra tin da ta koma gida zazzaɓi me zafi ya rufeta, ba wanda ya sani har sai dare sannan suka farga da ta kulle kanta a ɗaki, hankali tashe Zaheer da be daɗe da zuwa gidan na yake bubbuga ƙofar ɗakin tareda kiran sunanta amma shiru,
sai da ƙyar ta rarrafo ta buɗe sabo da jin muryar Zaheer da ta yi dan kuwa shi kaɗai za ta faɗawa damuwarta ta samu sauƙi.

tana buɗewa ta faɗa jikinsa gami da rushewa da kuka me tsuma zuciy. shiru Zaheer ya yi yana sauraron sautin kukan nata wanda daga ji yasan a wahalce take yinsa.

Mammi ce ta ƙaraso wajen tana cewa, “Zaheer lafiya kuwa?”
Turuss ta yi da ta yi tozali dasu dukan ta buɗe baki tana kallonsu har na ɗan wani lokaci sannan ta yi magana cikin sanyi, “meke faruwa Zuhra? me ya yi miki Jannahn?”

jin ta yi shiru yasa Zaheer ya sauke numfashi kafin ya ce, “Zuhra kinsan ba na iya jurar kukanki, ki sanar damu abin da ya faru dan Allah”
Cikin shashshekar kuka ta ce, “mutuwa zan yi Zaheer, nasan wannan mugun son Shine ajali, zuciyata zata tarwatse ku ƙyaleni na mutu kawai dan Allah kowa ya fita daga rayuwata”

Dummm! dummm!! dummm!!!. bugun zuciyar Zaheer kenan yayin da yake kallon yadda take kukan kamar ranta ze fita, iya kaiwa ƙololuwar tashin hankali da fita haiyaci ya gama kaiwa ji yake kamar zuciyarsa zata fashe sabi da wata irin azabar ƙuna da raɗaɗi da take yi idanunsa kuwa kamar an ɗora ƙwayar idon akan wuta haka yake ji, kamar wanda aka shaƙe shi ya ce, “indai kin mutu to kwananki me ya ƙare, Dogon Yaro ƙarya yake ya zama silar mutuwarki idan kuwa hakan ta faru babu shakka zan yi HAUKA Haukan da ba zai taɓa yiwa kowa daɗi ba, ke rayuwata ce fa Zuhra na riga na yi zurfi acikin sonki har na nitse na zama wawa mahaukaci sabi da ke na kasa sarrafa duk tunanina INA TSANANIN SONKI Zuhra”

zame jikinta ta yi daga nasa cikin tsawa ta ce, “ya isa haka Zaheeer!!!!!!!”

Zafin zazzaɓin da yake jikinta ne yasa jiri ya fara awon gaba da ita ta yi taga taga zata faɗi, cikin sauri Zaheer ya ƙwala mata kira tare da yunƙurin riƙota amma sai ta yi saurin ɗaga masa hannu alamar ba ta so, da lalube ta kai ga bango ta jingina sannan ta fara magana, “na sani kana sona Zaheer amma me yasa zaka ƙara tafasa min zuciya a lokacin da rayuwata take cikin garari?, kasan me na ji kuwa?? Jancy yanzu ya zama mijin wata Mammi! !!, ya ce ita zaɓin mahaifinsa Zeety kuma zaɓinsa ni kenan ba ze taɓa sona ba Mammi??? kenan mutuwa zan yi? kenan ba ni da sauran farin ciki a rayuwata?, bazan iya ba dan Allah kar wanda ya ji ba daɗi idan na mutu amma tabbbas nasan dole mutuwa zanyi”

Da baya baya Zaheer yafara tafiya har ya dangana da bango sannan ya yi zaman daɓaro a ƙasa, ba um ba um um bakinsa ya rife sai dai kallo.

Mammi kuwa ba ta san lokacin da wani zazzafan kuka ya kufce mata ba ta shiga mazgar kayanta cikin tsananin……

 

(Yachin banyi EDITING sosai ba🤣🤭 sai kun kula da error typing)

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/22, 11:43 AM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 20*

*(Don yin magana da ni INDO CE kai tsaye ku antayo ta wannan lambar 👉🏽+234 907 988 5632 sai na ji ku🤝🥰💞)*

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
tausayinsu, cikin su biyun ta rasa wa zata fi tausayawa dan kuwa kowan-nensu ya cancanci a tausaya masa.

yaya Ameer ne ya ƙaraso cikin kaɗuwa yana tambayar abin da ya sa Mammin take kuka, goge ƙwallar ta fara yi tana cewa, “ba komai”
Ya ce, “haba Mommu ya ba komai gashi ina ganinku cikin damuwa?”

Rausayar da kai ta yi gami da cewa, “tohh, Ameer mu ba iya maganin matsalar nan za mu yi ba dole sai dai mu zuba ido”

Kafin ya yi magana Zuhra ta ce, “yaya Ameer dan Allah ku bari na mutu tin da nasan Jannah ba ze taɓa ƙaunata ba ya tsaneni”

Sai yanzu ya gane inda lamarin ya dosa, ya kalleta ya kalli Zaheer ya jinjina kai gami da sauke ƙaramar ajiyar zuciya sannan ya kamo hannunta ya zaunar da ita shima ya zauna dafa’an a nutse ya ce, “ki zauna ki saurari abin da zan faɗa miki Queen, DAN KA SO, ba shi yaske nufin dole za ka samu ba, amma idan abu rabonka ne to fa ba makawa wannan rabon naka ne, ina so ki kwantar da hankalinki kisa a ranki babu wata da ta isa ta rabaki da abin da kike so baki san cewa ƙiyayya tana komawa so ba? ki ta addu’a idan Allah ya yarda sai ki ga wata rana kamar ba ayi wannan ba komai ya wuce, ki roƙi Allah sassauci tare da neman zaɓin alkairi daga gareshi ba ki zauna kina kuka kina damun kanki ba watan wata rana sai ki ga ya so ki”

Da sauri ta ce, “da gaske Yaya wata rana ze so ni??”
Gyaɗa mata kai ya yi gami da cewa, “in Allah ya yarda hakan za ta faru burinki ze cika kinji ko?”
Goge ƙwallar ta shiga yi tana cewa, “idan kuwa hakane indai ban mutu ba zan kasance kullum cikin jiran wannan ranar, shin ban yi kuskure ba hakan?”

Ameer ya ce, “babu kuskure a cikin hakan amma fa ki dinga nemawa kanki sauƙi, yanzu dai kafin wannan maza maza ki tashi mu je ki ga likita”

Kafaɗa ta noƙe alamar ba ta so, Mommu ta ce, “sai ka yi da gaske fa dan kuwa cewa take mu barta ta mutu”
Yace, “mutuwa ai sai kwanan mutum ya ƙare kuma insha Allahu sai burinki ya cika kafin numfashinki na ƙarshe a duniya, yanzu maza maza ki tashi mu tafi”

Ta ce, “jiri nake ji bazan iya ba”
Temaka mata ya yi ta tashi sannan suka rankaya.
Wajen Zaheer Mammi ta koma ta durƙusa a saitinsa tana sharar ƙwalla ta ce, “Zaheer ɗana, inajin ƙuna sosai dan ganinka a wannan halin daɗin daɗawa idan na tuna ta silar ƴata ka shiga tsanani nakanji kamar bazan iya yafewa kaina ba, Zaheer dan Allah ka buɗe bakinka ka faɗa min duk hukuncin da ka yanke akan Zuhra ya yanku ba abin da zan yi na iya biyanka sai ta wannan hanyar indai kana son aurenta ka gaya min ni kuma bazan wuce kwana biyu ba za’a ɗaura maka aure da ita”

Sai lokacin wasu zafafan hawaye suka wanke masa fuska ya girgiza kai kana ya ce, “Mammi!! ina sonta kuma ina son farin cikinta idan mu ka yi hakan nasan baza ta ƙara yin farin ciki ba dan haka na haƙura zan cigaba da haƙurar da zuciyata har zuwa lokacin da Allah ze cire min dafin sonta”

Hannunsa Mammi ta riƙe cikin son tabbatar da gaskiyarsa ta ce, “ni tamkar abokiyarka ce Zaheer kar ka ji kunyata kar ka yi min kara tsakaninka da Allah nake so ka faɗa min gaskiya”
Ya ce, “Mammi iya gaskiyar kenan, rayuwata ba ta da fa’ida idan na kasa bata farin cikinta”
rungume shi ta yi cikin muryar kuka ta ce, “na godewa Allah na gode maka da irin gudun-mawar da kake bawa Zuhra kaima ina roƙon Allah ya baka wadda ta fi Zuhra kuma ta kasance mafificin alkairi a gareka”

bayan kwana biyu.

Zuhra ta ji sauƙi sosai sai dai damuwarce dai kullum ba fashi.
a ɓangaren Jancy kuwa sabuwar soyayya suka ɓare shi da Zeety yanzu ba shi da labari sai ita, zuwa yanzu har Aba yasan da zamanta fatan alkairi kawai suke yi masa.

Fatima. ko da yaushe zuciyarta ƙara kusantar Jannah take duk ta faɗa wani irin dabai-bayi me wuyar warwa-ruwa, tana matuƙar shiga damuwa idan ta ga shima yana cikin damuwa haka ganin farin cikinsa yake mugun sa ta farin ciki sai dai halin ko in kula da yake nuna mata shine yake baƙanta mata rai haka kawai ta tsinci kanta cikin matuƙar son ya saurareta koda da ido ne ya kalleta amma ko kallo ba ta isheshi ba ko gaisheshi ta yi sai ta bugi babbar sa’a sannan yake amsa.

yau ya na zaune kan 3seater da take daga gefe a ɗakinsa ya na danne danne cikin Laptop Fatima tana daga kan gado tana kallonsa, zuwa yanzu har ya saba dan kuwa ta kasa denawa shi abun nata ma har dariya yake bashi, wayarsa ce ta yi ƙara ya duba sannan ya amsa tare da cewa, “Ya-ya sannu kira da wannan daren haka?”

A ɗaya ɓangaren aka ce “ba ita bace ni ne mijinta, ƙanina muna cikin damuwa sosai mun yi niyar ɓoye maka amma hakan ba zai yuwu ba dan kuwa abun ba na wasa bane”

gyara zama ya yi cikn sauri ya ce, “me ke faruwa Ya-ya Aliyu?”

Aliyu ya ce, “ba mu ga Mubeen da Mubeena ba tin da suka tafi makaranta har yanzu ba su dawo ba mun yi iya yin mu ba’a gansu ba”

“innalillahi-wa-inna-ilaihirraji’un, Ya-ya Aliyu yanzu to ina su Yayan?, ka ce su kwantar da hankalinsu yanzu zan zo”

Daga haka ya katse kiran ya miƙe ya tattare ƴan komatsensa ya zura silifas,
Sosai Fatima ta girgiza ganin yadda ya kiɗime lokaci ɗaya ya fara zaucewa sai haɗa kan kare da na doki yake, ba tare da ta sa ran samun amsa ba ta ce, “ina zaka je? me ke faruwa?”

Tsayawa ya yi ya kalleta sannan ya ce, ” ba lallai na dawo da wuri ba, za ki iya kwana ke kaɗai?”
Gyaɗa masa kai ta yi ta ƙara da cewa, “amma ina tsoron wani abu ya sameka dan Allah ka kula”
Sosai maganar ta-ta tazo masa a waskace sai ma ya kasa tafiya ya tsaya kallonta tare da lulawa duniyar tunani, idan wani abun ya same shi ita meye damuwarta?, tambayar da ya jefawa kansa kenan sai dai ba shi da lokacinta ma dan haka ya cigaba da tafiya.

Koda ya isa gidan tararwa ya yi sun yi jungum jungum dukansu, su Yaya Hassana sai kuka suke yi, suna ganinsa suka tattashi tamkar ya shigo da yaran ne, jiki a sanyaye ya ce, “Yaya Imran wane mataki kenan aka ɗauka?”

Imran ya ce, “ai da ba ka zo ba ma Auta dan kuwa bana jin yau za’a ga yaran nan duk wani bincike munyi amma ba labarinsu abin da ya kamata duk mun yi sai dai mu zuba ido mu raka gobe mu ga abin da Allah ze yi”

Cikin matuƙar damuwa ya ce, “yanzu sai mu zuba ido? ba mu san halin da suke ciki ba fa, taya za mu iya kwana bayan bama tare da su?”
Aliyu ya ce, “ba mu yi musu komai ba ƙanina haka kuma yaranmu ina da tabbacin ba laifi sukai musu ba ka ga kuwa mu ne da gaskiya kuma ka sani Allah yana tare da me gaskiya shine ze kare mana su a duk inda suke, ku kwantar da hankalinku dan Allah”

Jinjina kai ya yi ya ce, “Ya-ya Hassana dan Allah ku dena damuwa”

Husaina ta ce, “damuwar ta zama dole ne Jannah don Allah ka temaka ka karɓo mana su”
Ta ƙarasa maganar tana kuka.
Jancy ya ce, “na yi alƙawarin zan dawo muku da su da yardar Allah amma ku dena kukan nan idan ba haka ba bazan iya komai ba Ya-ya”

Hassana ta ce, “nima na yi maka alƙawarin zan dena damuwa indai za su dawo”

Jinjina kai ya yi gami da cewa, “Ya Imran ba wanda kuke tunani akan hakan?”

Imran ya ce, “ba bu gaskiya”
Aliyu ya ce, “nima a ɓangarena haka”

Shiru ya ɗan yi sannan ya ce, “na fahimta da yuwuwar sabi da ni ne aka yi hakan amma ba komai kawai mu cigaba da adda’a”

Cigaba suka yi da tattaunawa dan gani yadda za su shawo kan lamarin har wani lokaci sannan Jan ya koma gida.

washe-gari shiru ba bu su babu labarinsu har akai kwana na biyu, duk Jancy ya gama ruɗewa har ya ɗan yi rama sabi da ko abinci baya zama ya ci ko da yaushe a tsaye yake kangal kangal dashi da abokansa.

Shigowarsa kenan cikin gida wayarsa ta fara ƙugi ganin ɓoyayyar lamba ce yasa shi ɗagawa cikin sauri, a ɗaya ɓangaren aka ce, “saurara ka ji ni Dogon Yaro ƴaƴanka suna gurina ba komai nake buƙata a gurinka ba kuɗi kawai nake so tsagwaronsu kimanin miliyan hamsin hamsin akan kowane yaro, indai kana son rayuwarsu to ka haɗo kuɗin daga nan zuwa gobe ka kawo mana, zan ƙara nemanka na baka misalin gurin da za ka zo sannan idan ka faɗawa wani ko ka sanarwa ƴan sanda sai dai iyayensu su ƙara haifar wasu”

Kafin ya yi magana aka yanke kiran, wani mugun gumi ne ya shiga keto masa, da kyar ya iya ɗaga ƙafarsa ya cigaba da tafiya, yana jin Natiee ta na tambayarsa abin da ya faru amma sai ya yi shiru ya wuce ɗakinsa, yana shiga sautin kukan Fatima ya fara yi masa marhabun, zamansa ya yi ba tare da ya bi takanta ba, ya zuba tagumi ya na tunanin ta abin da yake tinkaro shi, jin kukan nata ya ƙi ƙarewa ne ya sa ya tashi ya bar mata ɗakin dan kuwa abun ze yi masa yawa ga wata fitinar a gefe ga ƙarar kukanta.

Washe-gari
Misalin ƙarfe 02:34pm suka ƙara kiransa Suka ba shi bayanin inda ze samesu, ba tareda tunanin komai ba ya nufi inda suka ce ɗin, wata tsohuwar ma’aikata ce acan gefe inda ba mutane sosai a yankin babu komai a cikinta sai tarkacen ƙarafa da ƙura sai da ya shiga ciki ya tabbatar matattarar ƴan iska ce shaye shaye da wasu miyagun kayan maye duk anan suke tarawa kuma suke cinikayyarsu.

Wani daga cikinsu ne ya tare masa hanya yana cewa, “ance na nuna maka hanya”

“to” kawai ya ce, shi kuma matashin ya yi gaba, bin bayansa ya yi har suka isa can ƙololuwar ma’aikatar inda anan manyan ƴan ta’addan suke zama, sai da akuyar cikin Jancy ta yi kuka lokacin da ya yi tozali da ƙarin wasu abubuwan da be taɓa tunanin ma akwaisu a duniyar ba dan kuwa duk wata harkar Daba ko ta’addanci da ɓarnar a doron ƙasa basa gabansa basa taɓa burgeshi baya bibiyarsu baya bibiyar masu yinsu hanyarsu daban tashi daban, ya fi ƙwarewa ta fannin ABOTA da kuma SOYAYYA wannan su ne kawai shaukinsa a rayuwa, yana matuƙar son abokansa waƴanda suke da yawan da shi kansa besan adadinsu ba kuma yana ƙaunar kowan-nensu sannan yana temakawa matasa kamarsa ko da besan daga inda suka fito ba, yakan basu abin yi ko kuma fitar da su faga wata matsala idan sun shiga, ta fannin soyayya kuwa masoyiyarsa ɗaya sai kuma soyayyar tsakanin iyaye da ɗansu sai kuma so da shaƙuwar ƴan uwantaka bayan wannan ba shi da wata matsala a rayuwarsa kowa na shi ne amma banda mutanen banza.

Zazzare ido kawai yake a cikin su yana kallon yadda suke hidindi-munsu wasu na murza wiwi wasu na karkasawa wasu kuma suna harkar ƙwayoyi abun dai ba kyaun kallo.

 

 

*(Don yin magana da ni INDO CE kai tsaye ku antayo ta wannan lambar 👉🏽+234 907 988 5632 sai na ji ku🤝🥰

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[10/23, 10:36 AM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..
(Jaririyar ELEGANT )

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 21*

*(Don yin magana da ni INDO CE kai tsaye ku antayo ta wannan lambar 👉🏽+234 907 988 5632 sai na ji ku🤝🥰)*

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
“ai na yi zaton kuɗi sun fi ran yaran naka”
Juyawa Jancy ya yi inda ya ji sautin maganar,
yana zaune ya yi damfamfam akan kujera da alama yana ɗaya daga cikin oganni,
Cikin ƙarfin hali Jancy ya ce, “ina yaran suke?”

Dariya mutumin ya yi ya ce, “yaran suna hannuna mana, sai ka miƙo sannan za ka karɓa idan mun yi niyar ba ka, idan kuma ka yi wasa za ka ajiye kuɗin ne ka je ka yo ciko lokacin nima na gama abin da zan yi da ƴar kyakkyawar yarinyar nan”

rai a ɓace Jannah ya ce, “ko kunya ba ka ji ba wannan ƴar yarinyar da bayan iyayenta ba ta san komai ba kake irin wannan banzar maganar akanta”

ƙara tuntsirewa ya yi da dariya sannan ya ce, “mu a gurinmu mace sunanta mace ba banbanci tsakanin babba da yarinya, bansan ma jinkirin da na tsaya yi ba har kawo yanzu, ka samu ma ka tsira da ranka sai ƴaƴan naka su kuɓuta”

Jancy ya ce, “alƙawari ka ɗauka zan baka kuɗi ka bani yara, idan ka sake ka saɓa ka tabbata sai ka yi nadama mummuna dan kuwa bazan saurara maka ba, jahilin banza”

Ga mamakin Jancy sai ya ga ko a jikinsa sai ma cigaba da ɓalɓala dariya da ya yi, sai da ya ɗan ɗebi lokaci yana dariya sannan ya cewa yaransa su fito da su Mubeen, ba tare da ɓata lokaci ba suka fito da su duk a ɗaɗɗaure sunyi jeme jeme sun sha kuka har sun gaji.

Mutumin ya ce, “kalli nan Dogo idan fa naso a gabanka zan yi komai”
Cikin ƙunar zuciya Jannah ya ce, “ƙarya kake ba za ka iya ba”

Ya kuma yin dariya sannan ya ce, “ka basu kuɗin su kawo min idan sun zo hannun yarona to zan kwance su su tafo da ƙafarsu sannan kai ba za ka motsa ba daga inda ka ke idan ƴaƴanka sun riga zuwa gareka to sai ka tafi idan kuma yarona ne ya riga zuwa gareni kai zamu riƙe sannan mu saki yaran naka bayan na fyaɗeta, ka amince da hakan ko kuma in ɗauki matakin da na ga ya sace??”

Janncy ya ƙare musu kallo kusufa kusufa kafin ya ɗan murmusa ya ce, “cikin sauƙi zan yarda da sharaɗinka ka turo wanda ya fi kowa sauri da zafin nama a cikin yaran naka ni kuma na yi maka alƙawarin zan fita daga gurin nan tare da abin da na zo nema da yardar Allah”

“Hahhhhh” ya yi dariya sannan ya ce, “gaskya yanzu ka samu ƙwarin zuciya sosai ka zama namiji kai ma hhhhh to maza a fara wasan”

Da hannu ya yi wa wani yaronsa inkiya, ya diro daga kan wani ɗan ƙaramin gini fuskarnan tashi ba annuri baƙa ƙirin da ita sai wani hure huren hanci da harare harare yake ya nufi kan DOGON YARO gadan gadan”

Miƙa masa kuɗaɗen ya yi dai-dai lokacin suka saki su Mubeena shi matashin ya juya zuwa ga ogansa su kuma su Mubeen suka nufo kawunsu, cikin harshen fullanci ya ce, “ƴaƴana ku yi gudu irin wanda muke yi na wasa duk wanda ya riga zuwa gurina zan yi masa kyauta”

Duk da basa jin ƙwarin jikinsu da su ka ji yace haka sai suka bar abin a matsayin wasan da suka saba yi da shi dan haka suka shiga tsela gudu da iya ƙarfinsu.

duk yadda wannan matashi yake sauri dan ya riga zuwa ya kasa sabi da nauyin kuɗinma ba na wasa bane bare ya gama shaye shaye. jikinsa suka faɗa suna maida numfashi, ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa, “Alhamdulillah”
Mubeena ta ce, “Kawu mu yi sauri mu bar wajen nan idan ba haka ba za su kasheka” Mubeen ma ya ce, “sun ce sai sun kasheka Kawu ka tashi mu gudu”

Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce, “kuna dai lafiya ko?” kai suka gyaɗa masa ya ce, “haka nake son ji, ku kwantar da hankalinku ai gudu na rago ne mu kuma jarumai ne ko?”

Mubeena ta ce, “eh mu jarumai ne kuma ba za su yi mana komai ba”

ganin ta yi shiru tana zazzaro ido tana kallon inda ya juyawa baya ne ya sa ya yi saurin juyawa, da sauri ya ture su gefe shima ya yi gefe sabi da wani nannauyan baƙin ƙarfe da ya gani a hannunsu har mutum biyar ɗaya yana neman sauke masa ƙarfen akansa.

ya ce, “ku zauna guri ɗaya Mubeena kar ku je ko ina idan kun ga wani ze taɓa ku ku yi min magana”

Gefe guda suka koma suna kallon ikon Allah cikin firgici.
Jancy ya ɗan shafi ƙeyarsa kafin ya ce, “wasan baya sai rago ai guys ku shigo fage mana”

Tsageran cikinsu ya ce, “mu za ka cikawa baki anan?”
wani ya ce, “barsa ya yi na ƙarshe dan ba da rai ze fita ba”
Jancy ya ɗan yi dariya sannan ya ce, “ina da tambaya waye ya sa ku kasheni?”

tsageran ya ce, “oho me gidan me gidanmu ne yasa me gidanmu me gidanmu kuma ya sa mu”

Cikin tsawa Ogan nasu ya ce, “me kuke jira ku zare mai maƙogwaro mana”

yana rufe baki kuwa suka yiwa Jan ƙawanya, ɗaya ne ya kawo masa duka ya kauce cikin zafin nama ya tsugunna dukan ya wuce, kafin ya yi wani yunƙuri suka fara farmakarsa ta ko ina yana kaucewa, da dubara ya dinga jansu har zuwa inda ya hangi wani mulmulallen ƙarfe ya sham-macesu ya ɗauka kai tsaye ya hau kansu dashi danda-nan suka fashe Jancy kuwa be ƙyalesu ba ya bi su ɗaya bayan ɗaya yana moresu a kai da ƙafa da damtse yake dukansu har sai da suka yi laushi suka kasa kataɓus.

a fusace Oga ya ƙara taso wata tawagar sun kai su goma suka yo kan Jancy, cikin dauriya da ƙarfin hali ya cigaba da ƙoƙarin kare kansa tare da mayar da raddi har ya gama da su.

Zuwa yanzu lamarin ya fara tsorata Oga ba shiri ya ɗaga waya ya kira Sultan ya bashi labarin abin da yake faruwa nan fa su Sultan suka canja salon faɗan.

Wasu mutanen Oga ya tura masa dan su ɗauke masa hankali gefe guda kuma ya tura wasu gurin su Mubeena suka saka musu wuƙa a wuya, ihu suka fara ƙwallawa wanda ya dawo da hankalinsa garesu, a wahalce ya ce, “kar ku cutar da su dan Allah ni na yarda ku kasheni amma kar ku kashe yaran nan zan yi duk…”

maganarce ta yanke saboda zurma masa wuƙa da aka yi a gefen cikinsa, cike da rashin imani Bomboi ya zare ya kuma coka masa yana dariya,
murya a disashe Jancy ya ce, “Bomboi!! kai ne za ka kasheni da kanka??”

Bomboi ya ce, “hakan burina ne, kuma cika wannan burin mafarkina ne sannan ina buƙatar ya zama gaske”

Ɗan sauran ƙarfin da ya rage masa ya tattara ya hankaɗe shi ya nufi wajen su Mubeena, kafin ya ƙarasa Bomboi ya rotse masa goshi da wani ɗan matashin dutse lokaci ɗaya jini ya fara shatata, duk da hakan be gaza ba ya goya Mubeen ya ce ya riƙe shi sosai sannan ya ɗauki Mubeena a kafaɗa, cike da ƙarfin hali ya fara gudu dasu kafin ya yi nisa Oga ya sa ƙarfe ya buga masa a ka, jinsa da ganinsa sai da suka ɗauke na wucin gadi sannan suka dawo ya yi taga taga ze faɗi, rintse idonsa ya yi yana cigaba da karanta add’o’in da yake yi, girgiza kai ya yi gami da buɗe idanunsa wanda suka gama fita daga haiyacinsu.
A tunanin su Oga ba ze iya komai ba dan haka suka saurara su ga ya zube a sume kafin su ankara ya yi nisa da gudu, nan fa suka rufa shi da jifa masu binsa da gudu suna yi, da haka ya cigaba da gudun har ya isa motarsa cikin hanzari ya zuba su Mubeena sannan ya shiga mazauninsa ya tayar da ita.
rassssss dutse ya faɗo a kan glass ɗin ɓangarensa atake ya tarwatse yasan inda dare ya yi masa, be tsaya saurarar glass ɗin ba ya taka motar da mugun gudu yabar wajen.

Tafiyar kawai yake amma ko gani ba ya yi sosai Allah ne kawai yake karewa gashi mugun gudu yake yana faɗawa ko ina.

Zuhra, tana gama shiryawa ta ɗauki mukullin mota ta fito, a hanlali take jan motar sabi da ba wani ƙwari ne a jikinta ba tana cikin tafiya ta ji wata motar ta gogi motarta daga gefe hakan ya sa ta yi burki cikin sauri tana kalle kalle dan ganin waye da wannan aikin, kamar a wasa ta yi arba da Jancy fuskarsa duk jini kafin ma ta yi wani ƙoƙari tini ya wuce, cikin kaɗuwa da tashin hankali ta ƙarawa motarta wuta ta fara bin bayansa domin tabbatarwa kanta shi ɗin ne ko kuwa gane gane ta fara.

Ta na biye da shi har ya isa ƙofar gidansu sai a lokacin ta tabbatarwa kanta shine hankalinta ne ya ƙara tashi fiye da da ko gama ajiye motar a dai-dai ba ta yi ba ta fita da gudu zuwa inda ya ke lokacin da ta ƙarasa ya yi dai-dai da fitowarsa ya fito da su Mubeena sannan ya zagaya mazaunin direba yana shirin ƙara tafiya, cikin sauri ta buɗe murfin tana cewa “Jannah!!!”
Kasancewar kiran firgici ta yi masa ya sa ya waro idanunsa da suke lullulum-shewa cike da mamakin abin da ya kawo ta, a kiɗime ta ce, “ina za ka je kuma? ba ka ga abin da yake jikinka bane?? me yasa za ka kuma tafiya wani gurin?”

Idanunsa ya lumshe tare da kwanciya a jikin kujera cikin taushin da ya yi ya ce, “bazan juri ganin kukan mahaifiyata ba gwara naje can gefe ko da mutuwar zanyi na mutu a can”

Fashewa ta yi da kuka tana cewa, “ba za ka mutu ba ba za su iya kasheka ba Jancy ka zo na kai ka asibiti”

Girgiza kai ya yi alamar baya so, ba ta tsaya bin ra’ayinsa ba ta ture shi ta kutsa kai ta zauna a mazaunin direba, ganin ta fi ƙarfinsa ya sa ya koma ɓangaren ɗan zaman banza hakan ya bata damar jan motar a tsiyace ta nufi asibiti.

Suna barin ƙofar gidan su Ummi su ka fito cikin tashin hankali, Natiee da Fatima tini sun fara kuka Ummi kuwa addu’o’i kawai take zubowa.

 

(MASOYANA Zaku ga na saka suna a saman page ɗin JARIRIYAR ELEGANT sabon sunana ne😹💞💞)

*(Don yin magana da ni INDO CE kai tsaye ku antayo ta wannan lambar 👉🏽+234 907 988 5632 sai na ji ku🤝🥰)*

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
(Jaririyar ELEGANT)
*INDO CE..*
[10/25, 10:07 AM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..
(Jaririyar ELEGANT )

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE

*shafi na 22*

*(Don yin magana da ni INDO CE kai tsaye ku antayo ta wannan lambar 👉🏽+234 907 988 5632 sai na ji ku🤝🥰)*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
Zuhra ba ta zame ko ina ba sai a harabar asibitin, da gudu ta fito ta zagaya inda ya ke ta buɗe murfin motar gami da cewa, “za ka iya takawa ko in nemo malaman asibiti?”

Be ce komai ba ya daddafe ya fito ya jingina a jikin motar ya coge.
Hankali tashe Zuhra take ihun a kawo mata ɗauki a shigar mata dashi cikin lokaci kaɗan mutane suka fara taruwa a wajen, kasancewar shi sananne ne yasa ba’a sha wuyar gane shi ba dan da nan mutane ƴan jiran ƙiris aka fara sa kyamarar waya ana ɗaukar hoto da bidiyo.

Ko da Malaman asibiti suka isa cikin hanzari suke ƙoƙarin yadda za’a shigar dashi amma sai ya yi burus da al’amarinsu, banda cije leɓe da rintse ido ba abin da yake yi,
Cikin kiɗima Zuhra ta ce, “Jancy ka manta da komai dan Allah yanzu ba lokacin gardama bane ”

Katse ta ya yi da cewa, “na gode da ƙoƙarin ceton rayuwata da kikai amma ba da yawuna kika kawo ni asibiti ba, bana son kowa ya taɓani yanzu lokacin da zan bawa ƴan uwana farin cikinsu ya yi, ba dai duk akan dukiyar Mahaifina da kuma ƙaunarsa gareni ne yasa suke son kashe ni ba? zan bar musu har duniyar ma duka su haɗa da komai su riƙe zan cika musu burinsu sabi da haka bana buƙatar temakon kowa ku bari na mutu”

Cike da damuwa Zuhra ta ce, “ba wannan ba ne Jan lafiyarka ta na da amfani”
Maida kallonta ta yi kan malaman asibitin tana cewa, “ku shigar dashi mana jiran me kuke?”

Cikin ƙarfin hali da mazantaka ya ce, “duk wanda ya sake ya taɓani tamkar ya taɓo wutar ƙona shi ne, lallai ku bi ra’ayina bana son na samu lafiyar”

Da ganin yadda yake magana za’a gane abubuwa ne suka haɗe masa da yawa ga zafin rai da ƙunar zuciya da tafarfasarta ga tsanin zafin ciwo.

Sanin taɓa shin ze iya jawo musu matsala ne ya sa suka yi gefe suka bi shi da ido.

Tirzawar duniya Zuhra ta yi amma ko uffan bai ce mata ba sai da ta matsanta masa sannan ya ce, “ranki ze yi mugun ɓaci fa”

Tassss!! tasssss!!!!

Ƙarar kyawawan mugayen marukan da Zuhra ta zuba masa hagu da dama ne ya ƙara dawo da al’ummar gurin cikin hankalinsu, da yawan mutane mamaki da tambaya ke musu yawo, wacece ita ga Muftahul-Jannah Alhassan da har ta samu zarrar yi masa wannan marukan? shin meye dalilinta na marinsa?.

Sosai marukan suka ratsa shi har tsakiyar zuciyarsa lokaci ɗaya hawaye suka fara rige rigen zubowa daga cikin idanunsa.

a harzuƙe Zuhra ta ce, “ya isheni haka Jaan!!!!!, da na yi tunanin kai me hankali ne ashe kai mahaukaci ne? idan ka zaɓi mutuwa mahaifanka da ƙanwarka da ƴan uwanka fa???, duk duniya Natiee yaya ɗaya gareta kai, duk yawan ƴaƴan mahaifinka kai kaɗai ne rabon mahaifiyarka a cikinsu, me yasa duk duniya Zeety ba ta taɓa son wani namiji kamar yadda take sonka ba? Su Aunty Faiza da ka zamo musu yaya kuma ƙani fa?? duk ba ka taɓa tambayar kanka meye dalulun hakan ba? ba ka taɓa yin tunani akai ba?? to ka sani kaine bango kuma kaine jigonsu, Jannah idan ka mutu dubban al’ummar da suke ci suke hidimtawa iyalinsu ta dalilinka fa???, Ka manta da rayuwarka ka yi tunani akan rayuwar waƴannan bayin Allan”

Numfashi ya ja kafin ya fizgo maganar da ƙyar ya ce, “ki yi haƙuri na ga ranki ya ɓaci kuma na gode da kikai min wannan marin ta dalinsa hawayena sun sakko hakan shine tabbar zuciyata ta fara sanyaya hakan shine burin mahaifiyata a duk lokacin da raina ya ɓaci, na gode miki karo na farko ”

Kafin ta yi wani yunƙuri tini ya zame ya faɗi a gurin da yake tsaye babu Alamun numfashi a gangar jikinsa sai dai zuciyarsa da take wani irin bugawa da mugun gudu.
Cikin sauri akai ɓangaren bada temakon gaggawa dashi, likitoci ne suka rufu akansa kowa yana iya bakin ƙoƙarinsa.

Ba’a ɗauki lokaci me tsayi ba Aba da Abi suka iso sai su Alamee sai su Ummi, dan da nan asibitin ya cika da dangi da ƴan uwa da abokan arziki ta ko ina.

Zuhra kuwa a bakin ƙofar ɗakin da yake ta zube itama sai tsintar kanta ta yi a gadon marasa lafiya, ta na farkowa ta ƙarewa ɗakin kallo sai ta ɓere baki ta shiga ɓarza kuka tare da haɗa wata me kula da ita da Allah da Annabi akan ta kai ta gurin Jancy sai dai matar ta ce ba zai yuwu ba, haka suka danneta suka ƙara mata wata allurar ta yi bacci.

DR ne ya fito yana sharce gumi ya cewa Aba ya bi shi Office ɗinsa, bayan sun je Likitan ya ce, “to Alhamdulillah mun samu nasarar ceto rayuwar Jannah, JIGON ABOTA inji matasa, Alhaji Alhasan ina so ku fitar da damuwa daga rayukanku dan kuwa yanzu baya cikin haɗari”

Aba ya saki murmushin farin ciki gami da cewa, “Allah shine abin godiya, na yi farin ciki da wannan kyakkyawan albishir naka DR kaima na gode maka”

DR Kabir ya ce, “ai ba godiya a tsakaninmu Alhaji ai kuna yin fin haka ma kun cancanta ai muku komai, a gaskiya Alhaji akwai abubuwan al’ajabi a tattare da yaronka, maganar gaskiya Allah ne kaɗai yasan abin da ya ɓoye a tare da Jannah, ransa ba kara zube bane dan kuwa raunukan da ya samu ya ci mutuwa musamman da aka ɗauki lokaci kafin zuwa asibiti sai dai cikin ikon Allah ba wata illatuwa da ya yi sosai ƙarin wani abin mamakin ma a yayin da yake a sume amma zuciyarsa cike take taf da begen wani abu da takeso wanda ba mu iya gane ko meye ba gashi saurin bugun zuciyarsa ya ƙaru fiye da hallau ma tafasar jininsa ya ƙara ninkuwa akan da, a taƙaice dai Yallaɓai DOGON YARON da ya banbanta da na yanzu yaronka ya canja ɗari bisa ɗari, yanzu ba lallai ka fahimta ba amma za ku ga wasu baren ɗabi’un da ba nasa ba a tare dashi a yanzu, magana ta ƙarshe kuma in sha Allahu kafin wanzuwar sati ko kwanaki biyar zai samu lafiya sosai”

Aba ya jinjina kai sannan ya ce, “ba shakka ina godiya DR a cigaba da kulamun dashi mu ma za mu kula idan ya dawo hannunmu, a tsaurara tsaro a tare dashi”

Dr ya ɗan murmusa gami da miƙewa sannan ya ce, “Yallaɓai Alhassan Mai Temako yaronka yana tare da tsarewar Allah amma duk da hakan za mu ƙara ba da gudun mawarmu”

Aba ya ce, “na gode sai mun ƙara yin magana”

washe gari.
Cikin sauri Zeety take tafiya har ta isa ɓangaren da ta samu labarin Jannah yana can, hangen su Ummi da ta yi a wajen ne ya sa ta fasa ƙarawasa ta tsaya tana tunanin ta inda za ta bi dan ba ta shirya haɗuwa da su ba,
Tana nan tsaye kallonta ya kai kan Zuhra da ta goye hannayenta a baya sai zarya take ta kasa zama ta kasa tafiya, murmushi ta yi sannan ta nufi inda ta ke.

Sam Zuhra ba ta lura da ita ba sai jin muryarta ta yi tana cewa, “Hello Queen!”

Sai kuma ta bushe da dariya, kamar sokuwa haka Zuhra ta tsaya kallonta, dena dariyar ta yi sannan ta ce, “na ji labarin wai ke ki ka kawo Jan asibiti na ji daɗi kuma na gode da ceto soyayyata da ki kai sai dai ki sani hakan ba zai karkato da hankalinsa gareki ba domin shi ɗin nawa ne, ƙarya ki ke! ba ki isa ba! kin yi kaɗan na yi kishi dake sai dai ki turo wata amma ba ke ba Queen!!”

Ta ƙarasa maganar tana wani shegen murmushi wanda Zuhra ta kasa gane manufarsa, kamar ta yi kuka haka take ji amma sai ta danne cikin dauriya ta ce, “ba na yi ne dan kaina ba na yi ne domin mutane da yawa masu muhimmanci a gareshi ciki kuma har da ke”

Da sauri Zeety ta ce, “ahhh!! labari me taushi taushi, ƙarya ki ke Zuhra da dai bansan ke maiya ce ba, har yanzu ma an kasa gane abin da ya faru dashi wasu na cewa yunƙurin kashe shi akai wasu na cewa haɗari ya samu kuma abin mamakin kece ki ka fara ganinsa har ki ka kawo shi asibiti, ke ya kamata ayi bincike ma akanki ta yuwu kishi ne ya sa ki kai ƙoƙarin kashe shi, ki sani bazan ƙyale ba ba zan manta ba dole zan bibiyi wannan lamarin mayyar banza, kurwar Jan ɗina ta fi ƙarfin maiya bare ƴar mayyar kuma za ki ga abin da zan muki”

Da ga haka ta bar wa Zuhra gurin, baya baya ta yi ta haɗe da bango tare da rintse idanunta da ƙarfi, maganganun Zeety ne suke yi mata yawo ɗaya bayan ɗaya hakan ya sa take jin kamar kanta zai tarwatse”

Ganin sun kauce ne ya sa Zeety ta yi wuff ta faɗa ɗakin tana kuka shaɓe shaɓe.

Hajiya Saratu, zagaye falon take ta faman yi ba ƙaƙƙautawa da alama tana tsaka da wata muguwar damuwa ne, Fauza ce ta ce, “Hajiyarmu wai duk me ya kawo hakan? wa ye ya ce ci Dogon Yaro da ga hannun mutanenmu??”

Hajiya Saratu ta ce, “ɗan iskan rai ne wannan da ku ke ganinsa, tin yana ciki muke ƙoƙarin raba shi da ransa gashi har ya girma, da idona na ga bidiyon da Bomboi ya shuka masa wuƙa a ciki har sau biyu haɗi da irin dukan da sukai masa amma kinga be mutu ba, me yake so a dunya ne yaron nan?????, lallai yana buƙatar wani abu kuma ba komai bane face kuɗi da dukiyar da muke so dan wannan ne kawai ransa ya gagaremu”

Salisu ya ce, “ba shakka kin yi gaskya Hajiya akwai abin da ruhin wannan tsinannen yaro yake buƙata, wai ni wacece wadda ta kai shi asibitin nan har ake ta yaɗa bidiyonsu?”

Fauza ta ce, “wata maiyar yarinya ce tin suna yara take bibiyarsa amma ya ƙi sonta”

Jafar ya ce, “ita ai wannan yarinyar sifili ce dan kuwa ba sonta yake ba kuma hakan bazai sa ya sota ba kunga ba mu da matsala da ita”

Hajiya Saratu ta ce, “amma gaskiya ta yi gangancin shiga shirgina to amma tin da haka ne ba mu da matsala da ita, yanzu aikina zai koma wajen ƴar aikinmu ta ɓangarensu ita ce za ta kashe shi da kanta”

Bayan kwanaki bakwai.
yau farin ciki yake mara misaltuwa kasancewar ance za’a sallameshi tin safe ya gama ɗanawa ya shirya komai ana cewa an sallameshi ya nufi hanyar fita, abokansa ne suka ja shi zuwa gurin ajiye motoci a cewarsu su za su maida shi gida, a gurin ya yi kaciɓus da ƴan jarida suna jifansa da da surutai kamar haka, “alhamdulillah, Mallam Muftahul-Jannah Alhasan Mai Temako mun taya ka murnar samun lafiya da ka yi, kuma jita jita ta na ta yawo kan cewar wasu sunyi ƙoƙarin kasheka wasu sun ce haɗari ka samu to muna so mu fita daga kokonto”

Murmushi ya yi kafin ya ɗaga musu hannu ya ce, “sannuku na fa gode da taya murnar nan taku, kokonton da kuke kuma ku dena tabbas haɗari na samu akan hanyata ta zuwa wani guri, kowa ya kwantar da hankalinsa ba kasheni za’ai ba, ina ganin ma a duniya babu wani kaifin wuƙa ko tsinin takobi da zai iya rabani da raina”

Ƴar dariya ya yi sannan ya ce, “ahh da wasa nake fa mutuwa sai kwananka ya ƙare a koda yaushe idan ajali ya riske mutum ko me yake yi dole zai mutu kunga wani ba shi da hurumin ran wani fatanmu kawai mu cika da imani, na gode masu bibiyar lamarina kuma masu damuwa da damuwata ɓoyayyu da na sarari”

Hajiya Murja, tsaki ta zuƙa sannan ta ce, “wai har wata zarrar da zai ce ba wani takobi da zai kashe shi gareshi, ai ka riga ka shiga komarmu yaro ai idan ba takobi guba ce za ta yi aikinta”

Hajiya Saratu ta murmusa a ƙasaice ta ce, “gasky kika faɗa Hajiya Murja! gubar ma me yin muguwar illa ga ɗan adam, da anijima zan yi magana da ƴar aikinmu”

 

(wai wacece ƴar aikin nan ta su a ɓangaren su Jannah????? ku biyo ni domin jin ya zata kaya)

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareerm
Jaririyar *ELEGANT*
*INDO CE..*
[10/26, 12:47 PM] INDO CE: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*

NA INDO CE..
(Jaririyar ELEGANT )

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

Na kuɗi ne😂
200 kacal
VIP
300
last free page

*shafi na 23*

*SHAFIN ƘARSHE NA KYAUTA*

*(Wannan shine shafin ƙarshe na kyauta, domin samun karantawa har ƙarshe naira 200 Normal grp amma update ba kullum ba, VIP kuma naira 300 Update kullum, ga lambata +234 907 988 5632 )*

 

 

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
A sashin su Ummi kowa farin ciki suke ba ji ba gani, sai 10:30pm su Yaya Faiza suka ta fi gidajensu, sai a lokacin ya samu damar shiga ɗakinsa domin kuwa ko motsin kirki ba sa barin sa ya yi.
kasancewar a gajiye yake ba shi da burin da ya wuce bacci ya sa yana shiga ɗakin ya rage haske tare da nufar hanyar ɗakin wanka, cakk ya tsaya sabi da jin sautin kuka da ya yi, ya ɗan ja nufashi ya sauke gami da shafar ƙeyarsa, har ga Allah ya manta da Fatima a duniya dan kuwa kwata kwata be sanya ta a idanunsa ba tin da ya dawo idan ma ta je inda yake to fa hankalinsa bai kai kanta ba, be kammala tunanin ba ya ji ta rungushi ta baya, a hankali sautin kukan nata ya cigaba da tashi yana ratsa kunnuwansa, shiru ya yi yana sauraren bugun zuciyarsa wadda ta shiga raya masa abubuwa da yawa a lokacin, sun ɗan ɗebi lokaci a hakan kafin ya sauke ajiyar zuciya yasa hannu ya zagayo da ita ya yi mata masauki akan faffaɗan ƙirjinsa.

Ido ya tsura mata na wani lokaci kafin ya fara goge mata hawayen a tausashe ya ce, “Faɗimah!! me yasa kike kuka yayin da nake farin ciki? ba kina murna da samun lafiyata ba??”

Cikin sauri ta gyaɗa masa kai ta ce, “amma da sun kashe ka fa??”
Ɗan murmushi ya yiya ce, “ki kori ƙuruciya mana Matata! ke fa ba ƙarama bace ki gane mana bayan ina tsaye tangaras akan ƙafafuna ki ke yin kukan wasu za su kasheni? na fa samu lafiya ki kwantar da hankalinki”

Cikin shashshekar kuka ta ce, “dan Allah kar ka kuma zuwa inda suke ko sun ƙara kiranka”
da kallo ya bita yana wani lallausan murmushi ya ƙara karyar da murya sannan ya ce, “bazan kuma ba idan kuma na ƙara to ki yi min hukunci indai har ni ne da laifin, amma fa idan ba ki dena kuka ba zan hau sama in faɗo ko na shiga tsakiyar titi mota ta takani”

ƙara ƙanƙameshi ta yi gami da cusa kanta cikin ƙirjinsa tana cewa, “a’a na dena”
Ya ce, “to kalleni ki gayamin zan fi yarda”
a hankali ta ɗago idanunta ta zuba su cikin nashi haka kawai sai ta tsinci kanta da kasa dena kallon cikin ƙwayar idonsa wanda a zahirin gaskiya take ganin tsananin tausayinta a cikinsu, Jannah kuwa wata duniyar ya ji ya fara tafiya sakamakon kallon idanun da babu komai a cikinsu face so da ƙauna na gaskiya ba algus, hannu yasa ya ɗan tallafo haɓarta cikin wata narkakkiyar murya ya ce, “Faɗimatu!!!! da gaske kina sona?”

Sosai tambayar ta shi ta rikito mata ba tare da ta yi tsammanin fitowarta ba ta yi saurin sauke kallonta zuwa ƙasa ta fara ƙoƙarin zame jikinta da ga nashi sai dai ya ƙi bata dama, ba zato ba tsammani ta ji bakinsa akan nata ya kama leɓenta na ƙasa ya fara tsotsa cike da kulawa hannunsa ɗaya na kan ƙunƙurunta yayin da ɗayan yake kan tattausan gashin kanta idanunsa a lumshe, Fatima kuwa ji ta yi numfashin ya tsaya na ɗan wani lokaci idanunta a zazzare kamar su fito waje, danda nan zuciyarta ta fara bugawa a ɗari da casa’in.

Ƙarar wayarsa ce ta dawo da shi cikin hankalinsa da sauri ya janyeta daga jikinsa ya shafi sumar kansa tare da furzar da wani zazzafan huci, Fatima kuwa jiki na ɓari ta yi saurin komawa can bango ta lafe tana zazzare ido a firgice.

ganin lambar da bai sani ba ya sa ya ji kamar ba zai ɗauki kiran ba amma sai ya ɗauka, ya kara a kunne tare da yin sallama.

A ɗaya ɓangaren Zuhra ta ce, “Jannah ba ka yi baccii ba??”
Wani shegen tsaki ya doka lokacin da muryarta ta ratsa dodon kunnensa a tafashe ya ce, “kina da hankali kuwa? ni fa ba saurayi bane da za ki kirani a irin wannan lokacin ina tare da me ɗakina kin shigar min rayuwa, idan ki ka ƙara maimaita irin kuskuren nan fa zai kawo miki matsala meye haɗina da ke da za ki kirani ma?”

gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa da jin maganarsa a take jikinta ya fara kakkarwa sabi da mugun kishin da ya soketa, cikin rawar murya ta ce “ba ni da haɗi da kai amma ka sani dole na binciki lafiyarka kafin na samu nutsuwar da zan iya bacci”

ya ce “Zaheer shi da yake sonko shi za ki gayawa wannan ba ni ba mara hankali kawai”

Da ga haka ya katse wayar ya jefa ta kan gado ya wuce bayi yana cewa, “ke kuma ki tabbar kafin na fito kinyi bacci kar na ganki har na ƙara marmarin taɓa ki, kike wani zarewa mutane ido kamar tsohuwar mayya”

yana shigewa toilet ɗin ta haye gado ta yi liff tana neman bacci ido rufe.

Jannah, yana tsaye a waje na musamman da aka tana da domin hutawa an ƙawata shi da abubuwa na more rayuwa iri iri akwai yawaitar tsirrai a gurin kala kala masu matuƙar ɗaukar hankali, duk hankalinsa yana kan wayar da ke hannunsa yana danne danne, sama ta ka ya ji an duki ƙirjinsa har sai da wayar ta faɗi ƙasa, a razane ya ɗago ido dan ya ga wane gogan ne, arba ya yi da Bomboi fuskarsa ba annuri da kallo ɗaya za a gane cike yake da masifa da neman dalili.

A tunanin Bomboi ganinsa zai sa Jancy ya girgiza, sokototo ya yi yana kallonsa jin ya ce, “ohh Ɗan iya kake ko ɗan uwa ka kasa gane hanya ne da za ka zo ka bugeni ina tsaye?”

Cikin hargagi ya ce, “kar kai min rashin kunya yanzu na yi ƙasa ƙasa da kai a gurin nan, ya kamata ka gane ruwa ba sa’an kwando bane ka saduda ka miƙa wuya, wancan karon ka mereni na burma wuƙa a cikinka yanzu idan ka kuskure me kake tunanin zai afku?? ”

Dariyar rainin hankali Jancy ya yi kafin ya ce, “kallo nan Ɗan iya, ta baya ta rago ce ta gaba ta jagayya da mu gudu gwara mu faɗi ko mun faɗi mun fi yaro suna, to Bom ko duka za ku haɗe guri guda ba ku isa ku sa na miƙa muku wuyana ba ciki kuwa har da wanda su ka ɗora ku akan wannan banzar hanyar ta rashin imani da son zuciya”

Mari Bomboi ya kai masa ya na cewa, “dan uwarka ni za ka gayawa haka?”
Caraf Jannah ya riƙe hannun tare da cewa, “dakata!!!!! ko ka tina cewa ranar mari ɗaya kai min nai maka biyi?? yanzu idan ka ƙara irin wancan kuskuren ba ka tunani na yi maka biyu sau huɗu?? hmm kurarin banza ka ke yi a ganinka ka ci bulus ne? ba ka san inada muradin fansa akanku ba?, ware daga nan ko na saka a wahala”

Cikin tirjiya da nuna janwuyanci Bomboi ya ce, “bazan bari ba zo ka ja ni”

wata muguwar mahangurɓa Jancy ya kai masa gami da cewa, “na jaza ma na tsoma ka a uƙuba na janyo maka wahala na rikirkito maka jaraba”

Wata muguwar razana Bomboi ya yi ya ɗauka dukan gaske Jancy zai yi masa amma sai yaji shiru sai ƴan surutansa wanda suka ƙara sa shi cikin wani kogin firgicin dan kuwa ya ga mugun canji a tattare da Jancyn.

Kwashewa ya yi da dariya ya ce, samfurin firgita daga yaya Bom, da wasa fa nake bazan iya yin duk abin da bakina ya furta akanku ba domin da wannan zuciyar da ku ka yi ƙoƙarin fasawa da ita nake muku sahihiyar ƙauna ta ƴan uwantaka duk abin da ku kai min bazan yi tunanin wata ɗaukar fansa ba dan ba ta cikin tsarina, kuma har gobe ina yi muku fata da addu’ar ku gane gaskiya ku shiryu ku tsarkake zukatanku ku ji tsoron Allah tin kafin lokaci ya ƙure muku.

daga haka ya jame daga gurin ya bar Bomboi a tsaye kamar dashe.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a kowane ɓangare wani lokaci farin ciki wani lokaci akasinsa, su Hajiya Saratu kullum cikin shirin yadda za su ga sun muzgunawa Jannah suke sai dai Allah ya na kuɓutar dashi ba sa yin nasara akan abin da suke so.

kullu shaƙuwa ce take shiga tsakanin Jannah da Fatima duk da yakan nuna mata halin ko in kula hakan baya damunta ba ta fushi da halayen nasa dan kuwa ta riga ta karanci yadda yake.

Zuhra kuwa kullum ba canji aikinta kenan kuka da damuwa, sai Zaheer ya yi da gaske yake shawo kanta.

“Ari!!” Alamee ya kira sunan cikin sigar tambaya tare da ƙara waro idanunsa akan wayarsa wadda sunan Ariee ɗin yake yawo akanta, mamaki ya hanashi amsawa har sai da ta katse ya kuma kira sannan ya amsa gami da sallama.

Ko Amsawa Ariee bai yi ba ya fara cewa, “ina magana da Alamee Abokin Muftahul-Jannah ko?”

Alamee ya ce, “eh ni ne meke faruwa ne na ji ka a hautsine haka??”
Aree ya ce, “ba lafiya ba Alamee na kira wayar su Jannah duk ta ƙi shiga Ummi ma ba ta ɗaga ba har Alhaji Alhasan ɗin ma ban samu ba”
Alamee ya ce, “to fa ai kuma Jannah bai cika barin waya a kashe dan zai yi bacci ba, ko kuma dan mun takura masa da tsokana ne yau yasa ya yi hakan dan kar mu kirashi?”

Aree ya ce, “ko ma dai menene ina son magana dashi”
Alamee ya ce, “cikin gaggawa haka? ba za mu iya jiran gobe ba?”

Aree ya ce, “idan mu ka wayi gari ba shi fa ina amfanin jiran? kawai ka gaya min ta ya zan same shi, Baffi ya ce kar ya kwana a ɗakinsa a daren yau kuma cikin gaggawa ake so ya bar ɗakin”

Alamee ya yi shiru yana nazari kafin ya ce, “nifa gaskiya ba na jin akwai wata hanyar da za mu same shi, yauwa sai dai in ka kira Abdul Yayansa sai ka sa ya dakatar da shi”
Aree ya ce, “zai amince ne?”
Alamee ya ce “shi Jannah zai amince shi kuma Abdul ɗin dubara za mu yi masa ta yadda ba ma zai gane mu ne ba”

Hakan suka yi masa da ƴan dubaru yadda za su ja hankalinsa, kasancewar ya na da sauƙin kai ba kamar sauran yayyen nasa ba ya sa ya yarda da tsarin nasu cikin sauƙi kuma ya kira Jannah ya tilasta masa barin ɗakin.

Ciza yatsa Hajiya Saratu ta yi kafin ta ce, “lallai mun samu matsala a aikinmu na yau ba na fatan ganewa ya yi da ya gudu daga ɗakin”

Hajiya Mirja ta ce, “ba fa zai iya ganewa ba gaskiya kawai faɗuwa ce ta zo daidai da zama”
Hajiya Saratu ta ce, “shi kenan ba sai a yi fito na fito ba? yanzu zan ƙara wani shirin”

Fatima, acan ƙasan kayanta ta ciro wata waya ta kunna ta ƙare wa wayar kallo ta yi kafin ta saki murmushin shu’umanci, kira ta tura ba jimawa aka ɗauka, a ɗaya ɓangaren Hajiya Saratu tana murmushi ta ce, “Matar Dogo ya akai ne? na ce ki kirani tin ɗazu ba ki kira ba”
Ta ce, “lokacin yana nan be fita ba kiyi haƙuri Hajiya”

ta ce, “to ba komai nai miki afuwa ko dan aikin da ki ke min komai yana tafiya dai-dai yadda na tsara dan haka ki manta kawai, zan aiko Fauza ta baki abin da za ki zuba masa a abinci ko abin sha lallai ki yi hakan a yau”

Fatima ta ce, “an gama ranki ya daɗe”

yau bai dawo da wuri ba sai ƙarfe 09:30pm a ƙagauce ya amsa gaisuwarta sannan ya wuce banɗaki, yana fitowa ya ɗan kalleta ya ce, “Inna Wuro kawo min bunu mana”

murmushi ta saki sannan ta tashi ta tafi kicin, sai da ta ɗauki lokaci me tsayi kafin ta dawo, lokacin har ya kwanta ya na shirin yin bacci”

Kanta a ƙasa ta ce, “gashi”
Tashi ya yi ya zauna ba tare da wani tunani ba ya karɓi shayin, juyawa ta yi da sauri tana murmushin samun nasara shi kenan aikin su Hajiya Saratu ya kammala ita ma za ta samu abin da take so.

 

 

*(Wannan shine shafin ƙarshe na kyauta, domin samun karantawa har ƙarshe naira 200 Normal grp amma update ba kullum ba, VIP kuma naira 300 Update kullum, ga lambata +234 907 988 5632 )*

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
Jaririyar *ELEGANT*
*INDO CE..*
[11/3, 10:20 AM] INDO CE: *DOGON YARO*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*24*

 

ƙarewa shayin kallo ya yi sannan ya maida kallon gareta yana nazartar ta, cikin wata daskararriyar murya ya ce, “Fatima!!!!!”

A firgice ta juyo tana zazzare ido jikinta na kakkarwa dan da nan idanunta suka sake cikowa da wata sabuwar ƙwallar, murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce, “da madara zan sha kawo min ita ko ki je ki haɗo min”

Hannunta na kakkarwa ta karɓa har shirin yin tuntuɓe take yi ta nufi kicin, ajiyar zuciya ta sauke wadda ta yi dai-dai da kufcewar kukanta, ta durƙushe akan guiwoyinta ta cigaba da rusar kayanta, tunowa da ta yi Jannah yana can ya na jiranta ne ya sa ta tashi ta goggoge ƙwallar sannan ta haɗa shayin ta koma ɗakin, tin da ta yi sallama idanunsa akanta suke yayin da ita ma nata yake kansa, a take tunaninta ya sauya daga wanda take a baya, wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska ganin yana miƙo mata hannu alamar ta bashi, girgiza kai ta yi cikin sauri ta kai kofin bakinta da nufin shan shayin”

Jannah da zuciyarsa take dukan tara tara ya kira sunanta cikin tsawa “Faɗima!!!!!!!”

Hakan ya sa ta fasa kurɓa ta wararo masa idanunta, cikin zafin nama ya dire daga kan gadon ya nufi inda take ya ƙwace kofin ya ajiye gefe, shafar sumar kansa ya yi ya yarfa hannu gami da furzar da wata zazzafar iska, ya shiga kaikawo a tsakar ɗakin hakan ya sa Fatima ta ƙara shiga ruɗani da firgici.

da kyar ya iya dai-daita kansa sannan ya ce, “Faɗima!!, yanzu fa kina da muhimmanci gareni, za ki iya kwana akan nan??”

Ya yi maganar tare da nuna ƙirjinsa, Fatima kuwa ido da baki da hanci ta saki tana kallonsa tare da tunanin anya kuwa ba aljanu ne da shi ba?,
Katse mata tunanin ya yi da cewa, “ki kwanta ina zuwa na manta ina da magana da Abana, kar ki je wani gurin sannan kar ki yi komai idan ba bacci ba”
Gyaɗa kai ta yi alamar ta amsa, ya suri kofin shayin ya yi waje da shi.
Zaman daɓaro ta yi a bakin gado ta ƙara fashewa da kuka.

Jannah kuwa ya kasa shan shayin kuma ya kasa zubarwa ko ajiyewa ma ya kasa yi, yadda bai ajiye kofin ba haka shima bai zauna ya dinga sagaraftu a babban falo daga farkonsa zuwa ƙarshensa.

Tarin tambayoyi ne a cikin tunaninsa sai dai ba kowacce tambaya yake da tabbacin samun amsarta ba.
Ya kwashi lokaci me tsayi cikin wannan halin kafin ya iye zuwa ya zubar da shayin sannan ya koma ɗaki, yadda take sauke ajiyar zuciya jeri jeri da yadda idanunta suka nuna kumburi ne ya tabbatar masa da irin mugun kukan da ta sha kafin baccin ya ɗauketa, kwanciya ya yi a gefenta sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam, cikin raunanniyar murya me nuni da tsananin tausayinsu ya ce, “Faɗima zan so na ji damuwarki da har ta sa kika bi SON ZUCIYA kike ƙoƙarin kashe mijinki, nasan ba yin kanki ba ne kuma nasan ban yi miki laifin da na cancanci hukuncin kisa ba, tayaya za ki sanar da ni?? me yasa kuma kika zaɓi ki fara mutuwa kafin ni??”

Zazzafar ƙwalla ce ta gangaro ta gefen idonsa, ya ja numfashi ya sauke gami da lumshe ido, gyara mata kwanciya ya yi akan faffaɗan ƙirjinsa ya Cigaba da lallaɓata yadda za ta fi jin daɗin bacci.

washe-gari.

Ashar Hajiya Murja ta lunƙuma kafin ta ce, “danƙari maƙari, wato yarinyar nan yaudarar mu ta yi ga ɗan iskan ya tashi garau da shi ba abin da ya faru da shi”

Fauzah ta ce, “ban da abin ku Hajiya ai ba ko wace mace bace za ta samu damar auren wannan santalelen yaron kuma ta kashe shi”

hankali tashe Hajiya Murja ta ce, “wai me yake so mu yi ya mutu ne yaron nan?? me yasa ba zai sallama mana ba? gashi Bokaye sun ce indai ya na raye burinmu ba zai cika ba kuma zai ta rusa mana ko wane irin mafarki namu, wai ya yake so mu yi ne??”

Fauzah ta ce, “sai ku canja taku ita kuma yarinyar nan tinda ta kasa kashe shi ita ku kasheta kawai”
Hajiya Murja ta ce, “haka za’ai wallahi ko mu kasheta ko ta kashe shi, bari ma na je wajen Hajiya Saratu sai mun ci uwar yarinyar nan shi kuma mu ɗauki babban mataki akansa, wallahi na gaji da wannan cin mutuncin da ake min ace ko da yaushe ba ma nasara akan wannan watatstsen yaron? to da sake wallahi da sake”

Yadda take maganar ma kaɗai ya isa tabbatar da tana cikin matsanancin tashin hankali.

Ko da labarin ya iski Hajiya Saratu har ta fi Hajiya Murja ruɗewa gaba ɗaya ta fita daga haiyacinta tafara surutai har da na saɓo.

tana zaune ta yi tsugul a jikin gado tana tunanin irin tsatstsauran matakin da su Hajiya Saratu za su ɗauka akanta, gaba ɗaya a tsorace take ga fargabar abin da Jannah zai yi dan kuwa ta yarda ya gane abin da ta ke shirin yi, zaman da ta yi kawai ta yi shi ne cikin tsmmanin hukunci ta kowace fuska, kiran sunanta da ya yi ne ya sa ta firgita sai kuma ta ƙara ɓoye kanta a tsakankanin cinyoyinta.

Cikin kulawa ya ce, “Natiee za ta je gyaran gashi idan anjima za ki raka ta???”

Da sauri ta girgiza kai alamar “a’a” ya ce, “ohhh na fahimta kin fi son zuwa gidan Yaya Faiza ko? to dama zaɓi ne kuma kin riga kin ture rakiyar Natiee Yaya Faiza kuma tana nemanki dan haka kafin na dawo ki shirya za mu fita tare”

Bai jira amsarta ba ya tashi ya bata guri, bayan ɗan wani lokaci ya dawo ya tarar ta shirya sai dai ba kwalliya ta yi ba.
babu wata fira da ta haɗasu har suka isa sannan sukai sallama ya wuce inda zai je.

………………..

a kiɗime Alamee ya ce, “matarka ce take son kashe ka fa??”
Ya ce, “ba shakka idan kai ba ka yarda ba nasan Sufee da Zuhair da Abubakar har ma da sauran abokaina duk kun yarda da ni ko??”

Sufee ya ce, “gaskiya lamarin nan akwai ɗaure kai, shiyasa fa gaba ɗaya ni tsoron yarinyar nan nake ji wallahi munafukar banza”

Abubakar ya ce, “to yanzu meye abin yi?? inaga dama dan ta kasheka ne ta aureka”

Girgiza kai ya yi ya ce, “a’a babu lallai, na yarda da Abana akan duk abin da ya amincewa ya yi tarayya da ni to yasan ba me cutarwa ba ne, dole wani abin ne ya sauyawa yarinyar nan tunani amma ba yin kanta bane, Yanzu dai kawai ku yi abin da na ce, ba na so Abana da Ummina da ƴan uwana su sani”

Zuhair ya ce, “shi kenan Allah ya yi mana tsari da irinsu, amma ba ka tunanin yin hakan zai kawo wata ɓarakar??”

Ya ce, “ko kaɗan, ina sane ma na fito da ita daga gidan tin safe dan nasan ganina ƙalau zai tashi hankalin ƴan gidanmu har su huce akanta”

Alamee ya ce, “abu ne me sauƙi ai wannan kawai ka dai zuba ido za ka ga aiki”
…………….

Yaya Faiza ce ta shigo falon cikin fara’a ta ce, “Fatima kinji mijinki ya turo wani ya ɗauke ki na ɗauka zai bari ki wuni kinga tin yanzu ya ce a mayar da ke gida”

a gefe guda ta yi farin ciki da tafiyar a wani gefen kuma tsoro ne ya ɗarsu a zuciyarta, murmushin ƙarfi da yaji kawai ta iya yi dan kuwa nauyin Yaya Faizan take ji musamman idan ta tuna da kuskuren da ta aikata gani take kamar duk duniya ma tasan abin da ta aikata”

Ba ta tsaya jiran komai ba ta fita, gani ta yi motar ba ta yi kama da kalar ta Jannah ba ga direban motar kamar ɗan jagaliya ne ba irrin wanda Jannah yake tarayya da su ba, a matuƙar tsorace ta shiga motar, ta sa a ranta kawai ta miƙa wuya ko rayuwa ko mutuwa a cewarta babu amfanin rayuwarta idan har ba za ta iya ceton rayuka biyu mafi kusanci da ita a wannan duniyar ba.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
Jaririyar *ELEGANT*
*IINDO CE*
[11/3, 10:20 AM] INDO CE: *DOGON YARO*
*(Jancy)*

NA INDO CE..

*25*

a wani gida da babu kowa suka ajiyeta a wani ɗaki daga ita sai halinta ta yi tsuru tsuru tana jiran sakamako.
……..

Waya wani ya ɗauka ya tura kira yana cewa, “bari na kira Oga na sanar da shi abin da ke faruwa, bayan an amsa kiran ya ce, “Oga wallahi duk barazanar da mu kai mata ta ƙi faɗen komai mun rasa yadda za mu yi da ita ta ce sai mijinta za ta gayawa”

kashe wayar ya yi ya mayar cikin aljihu ya na cewa, “yarinya taki ta ƙare ga Oga nan zuwa, ki faɗa mana kafin yazo”

Girgiza kai ta yi tana kuka ta ce, “ko me za ai min ayi amma bazan faɗa ba”

Ya ce, “to sai ki jira hukunci”

Bayan wani ɗan lokaci aka sanar musu zuwan Ogan duk suka fita daga ɗakin saura Fatima kaɗai,
Cikin naɗi irin na buzaye ya shigo ɗakin, daga ɗan nesa da ita ya coge ya zuba mata na mujiya.
ganin mutum tsaye yana kallonta yasa ta ƙara tsorata ta yi lakur a jikin bango tana shashshekar kuka idanunta tsai akan nasa idon.

Cikin nutsuwa ya shiga takawa har inda take ya durƙusa sannan ya buɗe fuskarsa wadda take ɗauke da tarin damuwa, ya lumshe idanunsa da suka fara cikowa da ƙwalla kafin ya ce, “kince mijinki kawai za ki gayawa, to gani”

Farin cikin ganinsa yasa ta yi saurin shigewa jikinsa ta shiga sauke ajiyar zuciya.
Kamar zai yi kuka ya ce, “Faɗimatu! gaya min dalilin da yasa za ki kashe ni”

Rintse ido ta yi sannan tace, “ka yi haƙuri Jannah dan Allah ka yafe min nasan na aikata kuskure ka hukuntani ko da ta hanyar kasheni ne ni dai alfarmar da zakai min kawai ka yafe min kar ka barni na mutu da alhakinka”

Huci ya furzar kafin ya ce, “ba ki min laifin da zan kasa yafe miki ba Fatima, ki gaya min waye yake barazana wa rayuwarki”

Duk da tana tsoron abin da zai je ya zo dole ta sanar dashi dan haka ta tattar yawun bakinta ta haɗiye shi a wahalce sannan ta fara magana, “Hajiya Saratu da Hajiya Murja da yaransu su ne silar komai, mahaifina ni kaɗai ya haifa kuma shi abokin mahaifinka ne bansan ya akai suka san hakan ba rana ɗaya suka je suna yi mana barazana akan rayuwar, idan Babana bai amince da su ba su kasheni idan ni ban amince ba su kashe Babana, dukanmu ba za mu iya ƙin yardar ba dan haka Mahaifina ya yarda zai nemi alfarmar aurena da kai ba mu san meye manufar su akan hakan ba sai daga baya suke gaya min zan dinga yi musu aiki ne, mahaifina kuwa ya ce min indai akan na cutar da ku ne to ya fansar da rayuwarsa kar na yi tunani akansa ko da sun kasheshi fatansa shine na zama makamin kariya a gareka, SON ZUCIYA ya sa na banzatar da maganarshi sabi da tsorata nin da suke da cewar za su kashe shi shiyasa na karɓi guba na zuba maka a shayi da nufin bayan nan nima in kashe kaina, da ka ce in ɗakko maka madara kuma sai na yi wani tunanin, na yi ƙoƙarin fara sha domin ni na rigaka mutuwa nasan ma idan ka ga na cutu kai ba lallai ka sha ba, a yanzu haka Mahaifina sun ɗauke shi daga garinmu yana hannunsu dashi suke min barazana ni kuma nake yin duk abin da suke so dan shi kaɗai ne ya rage min ba ni da kowa”

Ta kai maganar cikin matsanancin kuka wanda yake ƙara ƙona masa zuciya.
Numfashi ya sauke sannan ya ce, “ba ki da kowa kalmar nan ba ta yi miki wuyar faɗe ba?? kin manta cewa yanzu kina da miji ne? mijinki ya na da iyaye har da ƴan uwa da masoya amma a hakan kike kiran kanki wadda ba ta da kowa?, uhm yanzu ki yarda dani kuma ki yi abin da zan yarda dake daga nan rayuwarmu za ta inganta, tashi mu koma gida”

Cikin kuka ta ce, “a’a Jannah ina jin tsoron abun da za su yi min”
Ɗan ƙaramin tsaki ya yi ya ce, “ba za ki gusa ko ina ba indai ba gidanmu ba, ki tashi ko na ɗauke ki da kaina umarni ne ba shawara ba ba kuma faɗe na yi dan mu yi muhawara ba”

……………..

Bayan kwanaki biyu.

Jannah ya yi iya bakin ƙoƙarin sa wajen ɓoyewa su Ummi abin da ya faru itama Fatima ya yi da gaske wajen kareta daga sharrin su Hajiya Saratu.

A ɓangaren Zuhra kuwa sai dai sauƙi amma har yanzu ba ta warke ba. Zaheer kuwa Allah ya rangonta masa mugun son da yake yi wa Zuhra har ya haƙura ya fara saurarar ƴar ƙawar Ummansa wadda suke son haɗasu.
………….

Haisam ne ya kalli Hisham ya ce, “na samu labarin garin da zai je yau dan haka sauran aikin kai da Sultan ne”

Hisham ya ce, “ai ka yi me wuyar, ni yanzu na ce ma su Hajiya su fita sabgar mu za mu ji da komai kawai”
Haisam ya ce, “ƙwarai hakan ya yi shine dai-dai”

Jannah cikin sanyi yake tafiya har ya fito falo ya samu Ummi da Natiee da Fatima zaune suna ƴan hidindi-munsu,
Kusa da Natiee ya zauna gami da cewa, “Ummina sannu”
Ta ce, “ka fito? amma sai na ga kamar ka yi dare da yawa Jannah ba fa kusa bane ƙauyen nan”
lumshe ido ya yi ya ce, “Ummina sam sai na ji tafiyar ma ba na son yi dan dai umarnin Abana wajibine gareni”
Ummi ta ce “Allah ya tsareka gaba da baya, kar ka damu ba abin da zai faru sai ikon Allah ka ji ko?”
Ya gyaɗa kai gami da maida kallonsa kan Natiee da ta tsura masa ido, zai yi magana ta katse shi da cewa, “kishiyoyi uku ni ta huɗu gaskiya duniya tai min atshawar tsaki”

Dariyar da bai shiryawa zuwanta ba ta ƙwace masa ya ce, “su waye kishiyoyin nan naki kuwa? sun san da cewa daga ni ba ƙari ko?”

Ta ce, “to ai kaine kai min kishiyar, a da lokacinka daga ni sai Zeety amma yanzu Ga ni Ga matarka ga Zeetyn sannan ga kai kanka, ya kamata ka barmin Ummi gaskiya”
Kai tsaye ya ce ” bazan iya ba”
Ta ce, ” to ba komai tashi ka tafi Allah ya tsaremu”
Ya amsa da amin Yana murnushi.

Har zai tafin sai kuma ya juyo a ɗan fizge ya kalli Fatima da take ta faman kallonshi ya ce, “ba lallai na dawo da wuri ba kar ki je ko ina ki zauna tare da Ummina”

Gyaɗa kai ta yi gami da cewa, “to, Allah ya dawo da kai lafiya”
Hannu kawai ya ɗaga mata gami da sakin lallausan murmushi.

kamar sanɗa hake yake tafiya ba ya son yin gudu dan kuwa duk jikinsa ba ƙwari ga wata tsinkewa da zuciyarsa take yi duk ya ƙagu ya gan shi a gida sai dai yana tafiyar kamar ba ya yi sai kace wanda ake mayarwa baya.

Yana cikin tunane tunane ba tare da tsammani ba sai gani ya yi wata ringimemiyar mota Tifa ta yo kansa gadan gadan, kafin ya yi ƙoƙarin guje mata tuni ta kantsameshi duka ba na wasa ba, motar ta yi majaujawa ta yi gefe duk ta lallotse.

shi kuwa me motar tini ya gudu ya bar wajen. da yake mutane suna ɗan wuce dan da nan aka taru akansa akai ƙoƙarin fitar da shi daga motar zuwa asibiti.

Zuhra ta na shirye shirye tafiya gida abokiyar aikinta a ɗan madai-daicin asibitin ta shigo Office tare da sallama, Zuhra ta ce “lafiyarki kuwa?? na ga duk jikinki rawa yake”
ta ce, “DR Ridwan ya na son ganinki, wani bawan Allah ne ya yi haɗari”

Dummm zuciyarta ta buga cikin sauri ta ajiye shirin gidan sannan ta nufi inda Abokiyar ta-ta ta sanar mata.
ta na yin tozali da fuskar Jannah ta yi baya cikin sauri tana zazzaro ido a matuƙar firgice.
Dr Ridwan ya ce, “Zuhra me yake faruwa da ke haka??”

Goge ƙwallar da ta fara tsere akan fuskarta ta yi ta tashi tana cewa, “ba komai lafiya lau nake”

Ganin duk ta firgice yasa Dr Ridwan ya ce ta fita kawai.
Ofishi ta koma ta haɗe ƴan komatsenta ta wuce gida.
Tin a falo ta ci karo da Mammi ta zube ta fara rusa mata kuka na tashin hankali.
Sai da ta lallaɓa ta ta ɗan dawo daidai sannan ta ce, “me ya faru kuma yau??”
Cikin kuka ta ce, ” Mammi Jannah kashe shi suke son yi fa wallahi indai su ka kashe shi nima sai na mutu, nasan haɗarin nan da ya yi su ne suka jawo masa”

Zahra ta zabga tsaki ta ce, “ke kika damu da banza ma, ke kin damu dashi amma shi ko sau ɗaya ba ya yi miki kallon mutunci amma dan rashin zuciya har za ki tashi hankalinki akan ya yi haɗari, ni da ya mutu ma ai da mun huta”

Mammi ta ce, “ya isa haka Zahra me yasa bakin ki ba sakata ne???, kamar ba ki da imani? tausayinsa ma kaɗai ai ya isa ya hanaki irin maganganun nan, kin ga Zuhra ni na ba ki dama ki dinga bibiyarsa kuma kina temaka masa a duk inda yake buƙatar temako, nima abin ya fara isa ta dan nima uwace na haifa kuma bazan so wannan mugun abu yai ta faɗowa kan ɗana ba”

Zuhra ta ce, “Mommu ban sani ba ma ko zai rayu ko zai mutu”
Mammi ta ce, “dena irin tunanin nan ƴata Allah ba zai basu ikon kashe shi ba insha Allahu zai rayu”

Ummi tin da labarin ya iske ta ba abin da take yi sai addu’a ko kukan ma ta kasa yi.
Natiee kuwa wani zazzafan zazzaɓi ne ya rufeta.
Fatima ce ma me ƙoƙarin zaman dirshan sannan ta dasa kuka.

Sai misalin 10:42 Aba ya yi sallama, da kyar Ummi ta amsa ya ƙaraso inda suke cikin sanyi.
Cike da damuwa ya ce, “Jannatiee ma ba ta da lafiya?”
Ummi ta gyaɗa masa kai. ya ce, “Allah ya bata lafiya amma ya kamata mu je ganin likita”
murya a cunkusshe Ummi ta ce, “lafiyar ɗan uwanta itace mafi muhimmanci, ba za ta amince da hakan ba”

Aba ya ce, “yanzu kam bana so ki dakatar dani ya zama dole na ɗauki mataki akan masu farautar ran ɗana, na gaji idan na zuba musu ido za su yi abin da ya fi haka”

Ummi ta ce, “sam ba na so ka dinga irin tunanin nan, sanin kanka ne ko me ka yi akansa zai ƙare, dan Allah na roƙe ka ka bar shi da iya wannan kar ka ƙara ɗakko masa wata fitinar, su gama zaluncin su amma ba su isa su yi masa abin da Allah bai yi masa ba, idan mukai haƙuri Allah zai mana sakaiya cikin sauƙi”

Aba ya ce, “dama nasan haka za ki ce” miƙewa ya yi gami da cewa, “ina Fatima?”
Ta ce, “ta na ɗakinsu”

Bai ce komai ba ya cigaba da tafiya.

Washe gari.
Zeety itace farkon zuwa asibitin, da an ganta an san ta yi kuka kuma tana cikin tsaka da damuwa me tarin yawa, ta rasa zaune ta rasa tsaye ko faɗan da suka saba yi ita da Zuhra ba su yi ba ko wacce da abin da ya dameta.
……………

sai da Jannah ya yi sati biyu ciff a ƙarƙashin kulawar asibiti a ɓangare na musamman wanda aka sa tsaro sosai sannan ya ji sauƙin da aka mai da shi gida.
gaba ɗaya ji yake duk duniyar ta ɗau ɗumi ya rasa meke damunsa ƙunci da damuwa sun ɗaura abota da shi.

Hajiya Murja da Hajiya Saratu har kuka sunyi kasancewar ƙullinsu bai yi tasiri ba sai dai ƴaƴansu sun yi musu alƙawarin kawo ƙarshen shi ta ko wace hanya, da haka suka kwantar musu da hankali suka haƙura.
A gefe guda kuma ƴaƴan nasu suka fara ƙoƙarin yadda za su kawo ƙarshen shi cikin sauƙi tin da ko wace hanya suka bi masa ba ta yin yadda suke so.

Cikin doguwar rigar shadda ɗinkin buzaye Ta shirya ta yafi mayafinta ta nufi gidansu Jannah.
Motar ta tana tsayawa ta yi ido biyu da Zeety wadda itama take shirye tsaf cikin shiga ta alfarma sai taku take tana kwarkwasa.

Ɗan tsaki Zuhra ta ja gami da cewa, “ko wace ƙaddarar ce kuma ta haɗamu yau ma?”

Ƙarfin hali ta yi ta nufi hanyar shiga ciki, Zeety ta dakatar da ita da cewa, “haba ƴan karo! ai ko barori za su shiga a bari masu abun su wuce, wai me kika taka ne da kike yi min shishshigi akan mijina??”

Zuhra ta ce, “saurayinki dai, idan kuma ya zama mijinki nima zan iya kiransa da hakan dan kuwa zai iya zama nawa nima”

Zeety ta ce, “na tsani in faɗi magana ki dawo min da martani hakan yana taɓa darajata”

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
Jaririyar *ELEGANT*
*INDO CE..*
[11/4, 10:54 AM] INDO CE: *D-YARO*

26

Zuhra ta ɗan yi murmushi gami da cewa, “ai ban san kina da wata daraja ba ma bare har na taɓa ta, a ganina ki tsaya iya matsayinki nima ki barni a nawa, meye amfanin mu zauna raba gari da juna bayan duk ɗaya muke? nema kike nema nake kinga ai ɗaya muke ba fifiko yanzu shi Jannah ya na da mata mu ne dai har yanzu me rabo ka ɗauka”

Rai ɓace Zeety ta ce, “dallah rufewa mutane banzan bakinki sannan ki ja ƙazamin jikinki ki koma inda kika fito domin kuwa ba abin da zai hana ki shan disgi a gurin Jannah, a shawara mafi sauƙi ki kama hanyarki tin kafin dare ya yi miki”

Zuhra ta ce, “bazan iya yin hakan ba”
Zeety ta ce, “ai kuwa za ki gani”

Daga haka Ta Shige cikin gidan tana takun ƙasaita, Zuhra ma bayanta ta bi tana ta faman haɗe fuska dan kuwa Zeety ta ɓata mata rai sosai.

Yana zaune kusa da me gadi suna ɗan hira kaɗan kaɗan ganinsu ne yasa ya tashi yana kallonsu cike da mamakin yadda akai suka zo tare.

Zeety kuwa canja salon taku ta yi ta koma tafiya a salihance ta raɓe fuska kamar me shirin fashewa da kuka har da ƴar cikowar ƙwallarta.

Da sauri ya isa inda take a kiɗime yana tambayarta abin da ke faruwa.
Cikin kissa ta ce, “ba abin da yake damuna face kai, ina da burin rayuwa tare da kai ni kaɗai amma Allah bai ƙaddarta min hakan ba yanzu lokacinka ya koma na matarka ni na zama ƴar gefe gashi wannan muguwar tana neman yi min tsakani da kai, da gaske ne soyayya kake da ita har Abanka ya amince za ka aureta?? idan har hakan ta faru ka sani mutuwa zan yi ba ni da sauran rayuwa a duniya”

Ta ƙarasa maganar tana kuka mara sauti sai dai cin rai da ƙunar zuciya.
A fusace Jannah ya zubawa Zuhra ido, ta saki baki tana kallonsu mamakin irin sharrin da Zeety ta lafka mata lokaci ɗaya yasa ta daskarewa.

babu alamun wasa a tare da shi ya ce, “ke ce kika gaya mata hakan?? a yaushe hakan ta faru? nima mugun sharrin naki za ki fara laƙƙaba min?”

Girgiza kai ta yi tana cewa, “a’a wallahi ba ayi haka ba ka tsaya ka saurare ni, tin da n…”
Zeety ce ta katse ta da cewa, “nasan dama ba za ta yarda ba ni dai ka gaya min indai har da gaske ne to zan je na mutu kawai zan haƙura da soyayyarka na bar mata, mutuwar ta fi min akan ganin baƙin cikin nan ka gaya min gaskiya Jannah na fara tantama yanzu anya kana so na kuwa ”

Wani sabon ɓacin rai ne ya ƙara turnuƙeshi a harzuƙe ya ce, “fita daga gidan nan Zuhra!!!! na gaya miki na kuma gaya miki bana son ganin jar fuskar nan taki yanzu kin ji daɗi tin da kin haddasa min fitina a cikin ƙaunata, me yasa kike son dole sai kin shiga tsakanina da wadda nake so? ke wace irin mara zuciya ce an kore ki amma kin nace ko ana SO DOLE ne???”

Kukan baƙin ciki ne ya ƙwacewa Zuhra, tana goge ƙwalla ta ce, “idan na faɗa Allah ya saka maka wallahi ni ban ce haka ba kuma ban taɓa tunanin shiga tsakaninka da ita ba iya abin da na sani kawai ni dai sonka nake kum….”

Cikin tsawa ya ce, “ya ishe ni haka!!! ba na son jin muryarki kwata kwata idan baki sani ba na tsaneki!!! tin da kin kasa fahimta yanzu na gaya miki na tsaneki ki yi harkarki inyi tawa, idan kuma ki ka sake na ƙara sanya ki a idanuna musamman a gurin da kika san tsagina ne sai na mugun ɓata miki rai bana buƙatar ƙara ganinki daga nan har bayan raina”

Za ta yi magana ya nuna mata hanyar fita gami da cewa, “ki kasata kawai, idan kuma kika ƙara magana sai na ɓata miki fuskar nan, ballagazar mace me zubin karuwan Nijar kawai”

ganin ya yi wata muguwar fusata yasa ta yi saurin ficewa ba tare da ta tsaya waiwayensa ba ta wuce gidansu tare da shan alwashin indai ta haifu kuwa za ta bi sharaɗinsa ba za ta ƙara bari su haɗu a yankinsa ba.

Zeety da ta tabbatar Zuhra ta tafi burinta ya cika sai ta goge ƙwallar a marai-raice ta ce, “nasan dama ƙarya take ba za ka yaudare ni ba ba za ka ci amanata ba, ina kishinka sosai Jannah Shi yasa nake matuƙar ɓacin rai idan naga wata ta kusanceka, kamar yadda na yi alƙawari bazan taɓa juya maka baya ba ina so kai min wannan alƙawarin kaima”

Zazzafar iska ya furzar sannan ya ce, ” na yi Alƙawarin A KARAN KAINA bazan taɓa juya miki baya ba komai wuya komai rintsi zan kasance me matuƙar ƙaunarki, ko kasheni za ayi akanki ba abin da zai canja sai dai na ƙara son ki wannan Alƙawari ne na rataya a wuyana”

Lallausan murmushi ta yi kafin ta ce, “na yi farin ciki mara misaltuwa, na gode da wannan Sahihiyar ƙaunar taka kyakkyawan masoyina”

yadda ta sako murmushin a sukwane yasa zuciyarsa ta yi sanyi har ya samu damar murmusawa ya ce, “ki zo mu je ki gaisa da Ummina”

ba musu ta bi bayansa tana murmushi sai yauƙi take kamar ɗanyar kuɓewa.
Abin da bai yi mata daɗi ba daga Ummi har Natiee babu wadda ta nuna zallar farin ciki da zuwanta sai dai ba yabo ba fallasa, duk sai ta ji ta tsargu musamman da ta lura da wani kallon za mu haɗe da Ummin take bin Jannah dashi.

Ba ta wani daɗe ba ta tashi ta yi musu sallama, Jannah ya yi niyar rakata har gida Ummi ta hana shi ta hanyar jona masa uzurinta Dan haka ya kaita iya bakin get ya dawo ciki.

Cikin ɓacin rai Ummi ta ce, “me jar fuska da zubin karuwai na Nijar idan haka ne ai Umminka ma ta cancanci wannan sunan dan kuwa abin da ya yi ta shi ya yi ni, yarena ɗaya da ita haka ƙasata ɗaya da ita ka ga dukanmu karuwan Nijar ɗin ne”

Cikin sauri ya ce, “a’a Ummina dan Allah ki yi haƙuri wallahi kawai ɓata min rai ta yi ba dan na so na ci zarafinta ne ya sa ni faɗe ba hasalima bansan hakan zai ɓata miki rai ba, Allah ya huci zuciyarki Ummin Jannah”

Ummi ta ce, “ba na son daɗin bakinka, ya zama dole ne rai na ya ɓaci ai so ba hauka bane yadda kake jin kana son wannan yarinyar itama haka take jin tana sonka amma sai hakan ya zama na cin mutunci da cin zarafi garemu, ba komai ai dama zan je Nijar ɗin sai ka zauna a ƙasarka nima in tafi tawa zan tafi da Jannatiee kuma ba na son ganin ƙafarka acan ko da bayan naje”

Turo ba ki ya yi a shagwaɓe ya ce, “Ummih!! to ida ba kya nan ke da Natiee waye zai dafa mana Abinci ni da Abana kenan??”

Ummi ta ce, “Aban naka ya dafa maka ai ya iya, ko dan kana da mata ma har ka zauna jiran abincina? sai ta yi ta baka ka ci”
Ya ce, “Ummi wai da gaske kike ? na tsorata fa sosai Dan Allah ki yi haƙuri bazan kuma ba ”

Ta ce, “oho maka kuma wannan ni ɓace min da gani”

Ransa ne ya ƙara ɓaci gaba ɗaya ya ta’allaƙa laifin akan Zuhra, bai ƙara cewa komai ba ya nufi ɗakinsu. karo ya yi da Fatima tana shirin fita, baya ta yi tana cewa, “lafiya kuwa?”
Murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce, ” ba komai wata yarinya ce ta ɓata min rai ta sa ma Ummina ta na fushi da ni”

ƙasa ta yi da kai cikin sanyin ta ce, “to ka yi haƙuri”
Kallonta ya yi har na ɗan wani lokaci kafin ya saki murmushi me sauti ya wuce ciki ya na cewa, “da ba na haƙuri da Yarinyar nan ai da tin kafin ki sanni na rufe babinta”

Ko ɗagowa ba ta yi ba bare ya sa ran ta ji abin da ya ce.
Ƙasa ƙasa ya yi da murya cikin salon jan hankali ya ce, “zo nan na ga kitson naki”
Ba musu ta matso ta zauna a gefensa ta sunkuyar da kan yadda zai fi gani.
Janta ya yi ya kwantar a jikinsa ya na wani tattausan murmushi cikin murya me kama da raɗa ya ce, “ya yi kyau ba kaɗan ba, gaya min meye abin da ke damunki? Abbanki fa yanzu yana ƙarƙashin kulawata na gaya miki kuwa??”
Da sauri ta ɗago ta kalleshi cikin matuƙar farin ciki ta ce, “da gaske? na ji daɗi sosai na gode maka”
Ya ce, “ohh iya godiya ma?”
Girgiza kai ta yi alamar “a’a” ya ce, “to gaya min”
Sake shigewa jikinsa ta yi gami da rintse ido ta ce “ai ban san me kake so ba amma ko menene zan yi maka”
“ba abin da nake so sai duk abin da kika bani, ni dai fatana na kula da mutunci da darajar aurenmu”

Ba ta ce komai sai murmushi kawai shi kuwa idonsa suna kanta, ganin yadda ta ƙanƙameshi ya sa shi cewa, “wai anya kuwa ke bafulatanar gaske ce??, ahh na ga Su Abana akwai kunya ne”
Ya yi maganar yana dariya cikin sigar zolaya.

Da sauri ta janye jikinta ta wantsala kan gadon ta rufe a cikin bargo ta na ƙifil ƙifil da ido gaba ɗaya kunya ta lulluɓeta. itama kanta ta rasa yadda akai ba ta jin kunyar baiyana tsantsar ƙaunar da take masa ba ta iya yiwa kanta linzami akan duk abin da ya shafe shi.
Jin sa a kusa da ita ne ya sa ta ƙara rintse ido maganin kar idanun nasu su yi arangama da juna.

………………..

Haka Rayuwa ta cigaba da gudana a wannan lokacin ta zo da sauyi sosai dan kuwa wasu abubuwan sun canja a wasu ɓangaren. a wannan ƙadamin ɓangaren su Hajiya Saratu da Hajiya Murja sun yi shiru sun Zuba masa ido ba su ƙara ƙoƙarin yi masa wani abu ba, hakan ya bashi damar sakewa ya fara gudanar da rayuwarsa cikin farin ciki dan kuwa shi mutum ne me saurin manta abin da ba na alkairi ba.

a ɓangaren Zuhra ba laifi ta yi ta maza sosai dan ganin ba ta ƙetare iyakarta ba ta danni zuciyarta ta haƙura da son ganin shi da take yi, Addu’a itace makamin da ta ɗauka kuma ta na samun nasara dan kuwa kaso 20 a cikin 100 na rashin hankalin da take yi akansa ya ragu, yanzu ta fi samun nutsuwa tana samun damar yin wani tunanin ba nashi ba tana gudanar da aikinta na likita dai-dai ba kamar da ba.

a fannin Zaheer kuwa soyayya ta ƙullu tsakaninsa da Aneesha har an tsayar da ranar aurensu yanzun haka sauran wata ɗaya da ƴan kwanikai ana nan ana ta shirye shirye.

a soyayyar Zeety da Jannah kuwa ba baya sai gaba take ƙarawa, duk da yana son Fatima kuma ya shaƙu da ita amma har yanzu ba ta kama ƙafar Zeety ba. ya na mugun nuna mata ƙauna kuma duk abin da ta ce a lokacin da taso ba ya jin komai wajen aiwatarwa, a yanzu neman yadda zai yi a aura masa ita kawai yake yi sai dai baya jin Abansa ya shirya yi masa wani auren.

Ummi ce zaune ta yi zugum tana tunani, har Jannah ya zauna kusa da ita ba ta sani ba sai da ya ce, “sannu da hutawa Nan, tunanin fa na mene?? ”
Numfashi ta ja ta sauke kafin ta ce, “Jannatiee ɗiya mace ce kuma burin ko wace uwa shine ta ga ta miƙa ɗiyarta ɗakin miji, amma ni abin yana neman gagarata Jannah, duk wanda ya zo ya nuna mata so sai ƴan uwanku su yi kicin kicin a cikin zancen su yi mata ƙage da sharrin da duk wanda yasan kansa ba zai ƙara neman inda take ba, abin yana damuna sosai sun ɓata mata suna yanzu ba me sonta gashi kullum ƙara girma take yi, ni da Abanka muna da muradin ganinta a ɗakin miji kafin ni na mutu ko shi ya mutu ko kuma mu mutu duka Amma ina ga hakan ba zai yiwu ba Dan komai daren daɗewa ba wanda zai aureta a hakan nan”

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/6, 10:31 AM] INDO CE: *D-YARO*

27

 

Duk da abin ya taɓa shi sosai amma sai ya danne, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, “Haba Ummi Natiee ɗin fa ba wata babba ce ba karki damu ba wanda ya isa ya hana cikar burinku Ummina in Allah ya yarda za ki ga lokacin har fin nan, duk wannan abin da su ke yi ba zai hana ta aure ba, Dan Allah Ummi ki dena damuwa haka na ai abin sai ya yi min yawa”

Ta share ƙwalla sannan ta ce, “Allah ya tabbatar da faɗarka, Zan fi kowa farin ciki da hakan”
Ya ce, “a ko da yaushe ma ki kasance cikin farin ciki kawai kar damuwar su ta dameki”
Ta gyaɗa kai alamar ta fahimta.

bikin Zaheer da Hafsat ya rage saura kwana uku, ana ta shirye shirye ta ko ina kowa yana nuna farin cikinsa.
A ɓangaren Zuhra dai ba yabo ba fallasa ba za ta ce farin ciki ba ba za ta ce akasinsa ba sai dai duk ta rasa me ya ke mata daɗi.

Ta na zaune ta zubawa masu kaiwa da komowa ido Zaheer ya zo ya zauna kusa da ita tare da cewa, “Queen!!!”
Juyowa ta yi ta kalleshi ta kauda kai ta ce, “ina jinka”
ya zuba mata ido har na ɗan wani lokaci kafin ya ce, “hakan dai ya na nufin ke ba rabona ba ce ko?”
Duk da ta gane inda ya dosa amma sai ta yi kamar ba ta gane ba cikin nuna ko in kula ta ce, “kamar ya kenan?”
Ya ce, “kamar yadda na so ke na aura amma kin ƙi yardar min gashi har zan auri wata, na kasa manta soyayyarki Queen dan dai ba yadda zan yi ne amma har yanzu da nake zaune anan ba me matsayi sama da naki a Zuciyar nan tawa, ina kallo kenan haka zan auri wata ba ke ba? anya kuwa soyayya ta yi min adalci?, ni fa a yanzu indai ki ka ce ki na so na to fa ke zan aura rashin samun hakan daga gareki ne dama ya sa Umma ta yi wannan haɗin”

Murmusawa ta yi kafin ta ce, “kai ma na musamman ne a wannan zuciyar da ta haukace akan soyayya, kai tsaye zan iya kiran kaina wadda so ya ci galaba akanta na kasa yin nasara a so gashi an so ni na ƙi kuma na so an ƙi ni, uhm sau tari na kan tambayi kaina a duniya akwai me irin wannan baƙar ƙaddarar tawa kuwa?? har yanzu na kasa yarda akwai wata bayan ni, Zaheer ba abin da za kai min ya zamo sadaukarwa a gareni a yanzu bayan na baya wanda ya wuce ka riƙe matarka da hannu bibbiyu kuma cikin lumana, ina buƙatar ganinka cikin farin ciki tare da ita a duk lokacin da ka ke tunaninta ka sa a ranka ni ce kake tunawa idan ma ganinta ka yi kawai ka ɗauka ni ce sannan ka so ta ninkin ba ninkin yadda ka ke sona hakan ne kawai zai sa na yarda ka na tsananin so na san ka yafe min kuskuren da na yi maka”

Murmushi me rauni ya yi kafin ya ce, “na yarda da hakan Queen! duk abin da zai sanya ki farin ciki zan yi shi komai wahalarsa”
ta yi murmushi gami da cewa, “Allah ya sanya alkairi ya albarkaci aurenku”
Ya amsa da “amin”

wayar Zuhra ce ta yi ƙara ba tare da ta duba ba ta kara a kunne gami da sallama.
a ɗaya ɓangaren Zeety ta ce, “ƙaramar ƴar yi yakike??”

Zuhra ta ce, “ina lafiya kuma cikin farin ciki sabi da na rabu da ganin ciwon kaina”
Zeety ta ce, “ba dogon bayani na ke buƙata ba na kira ki ne dan mu yi wata gasa ta IN KA CIKA shin za ki yi ne ko kuwa kwarjinina ya sa tin kafin ki gwabza kin karaya?”

Zuhra da gabanta yake ta faɗuwa ta danne razaninta sannan ta ce, “uhm, ba ki da kwarjinin da zai sa na karaya akanki ai Zeenatu”
Zeety ta ce, “Zeenatu kai tsaye? lallai kin samu ƙwarin guiwa amma ba komai in kin cika ki zo Fatin ƙawata wanda za’a gudanar a daren yau kuma ba tare da kowa ba ke kaɗai muke buƙata, ki nuna min ta ki cikar kamar yadda na ke nuna muki tawa”

Shiru Zuhra ta yi tana nazari kafin ta ɗau kasada “ki turo min adress da lokaci sannan ki jira ni”
Zeety ta ce, “sai na ganki”

Huci Zuhra ta furzar tare da sa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. ta ya za ta bar nasu bikin ta tafi na ƙawar wata? anya kuwa Mammi za ta bar ta?? amma tin da ta yi gangancin cewa za ta je dole ta yi duk yadda za ta yi.
Da wannan tunanin ta tashi ta koma ɗaki ta kulle sannan ta cigaba da nazarin idan za ta je ɗin ma a ya-ya za ta je? me ma suka shirya mata da har suke gaiyatarta?.

Zahra ce ta ja tsaki ta ce, “ai sai ki je tinda bikin ƙawarta ya fi na yayanki muhimmanci”
Zuhra ta ce, “a’a ba haka bane kawai dai ina son zuwa ne dan na ga iya ƙarshen gudun ruwanta”
Ta ce, “to ai sai ki san takun da za ki yi mata, ki tashi ki shirya lokaci yana ƙurewa”

nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta tashi ta fara shirya.
Ba wata shahararriyar kwalliya ta yi ba daga hoda sai kwalli da ya yi bajau a idanunta, hakan yasa ya ƙara fitowa da zallar kyaunsa farin cikin idon ya ƙara haske yayin da ƙwayar tsakiya wadda ba baƙa ba take wani irin sheƙi, man leɓe ta saka sannan ta nufi gurin kayanta.
ta ɓata lokaci kafin ta ɗakko wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar leshi baƙi me adon fulawa ja ta sha aiki tin daga samanta har ƙasa.
bayan ta saka ta nufi wajen mudubu ta tsaya tana kallon kanta tare da tunanin irin ɗaurin da za ta yi, murmushi ta saki kafin ta ware ɗankwalin sannan ta ninka shi har ya dawo ƙarami siriri yadda iya goshinta kawai zai rufe , ɗora shi ta yi iya goshin ta soke shi a baya ta gyarawa dogon gashinta da ya baje akan kafaɗunta zama sannan ta ɗauki jan mayafi ta ɗora, da turare ta feshe jikinta tsaf sannan ta sa takalmi ta fito.

Kowa ta yi karo da shi mita yake mata akan ta ƙi zama ayi bikin ɗan uwanta da ita ta tafi na ƙawar-ƙawa haka duk ta rufe kunnenta ta ƙi saurarar su.
wajen wata fitacciyar baƙar mota ta nufa ta buɗe ta shiga sannan ta ja ta cikin nutsuwa ta fita daga cikin gidan.

a wajen kwatance sai da suka bata wahala kafin su gaya mata ainihin inda suke.
a hankali ta fito daga mota tana ƙarewa fuskar gidan kallo. ɗan madai-daici ne sai dai ya ƙawatu ta wajen gininsa da fitulu da kuma adon da akai masa hakan yasa ya yi kyau.
Taɓe baki ta yi kafin ta ciro waya ta kira Zeety ta sanar da ita ta iso.
Wata tsagerar budurwa ce ta fito tana tafiya tana girgiza da karairaya. da an ganta an san ba kanwar lasa ba ce.

idon Zuhra na kanta har ta ƙaraso wajen.
Ga mamakin Zuhra ji ta yi tana cewa, “sannunku da zuwa ki yi haƙuri Hajiya na zo tarar wata baƙuwar ƙawata ce, ki shigo ciki, kece matar abokin yayan Hafsat ko? ai daga gani ma kece dan wannan shigar irin ta alfarma ce”

Girgiza kai Zuhra ta yi ta ce, “Sunana Zuhra ni na zo wajen Zeety ne”
Baya budurwar ta yi tana zazzaro ido ta ce, “me??? kenan kece matsiyaciyar da aka ce na shigar ciki?? innalillahi gaskiya na bada kai wallahi, a memakon ki yi shigar dai-dai da ke sai ki nemi fin amarya kyau?? to wallahi muje cikin sai kin canja hawa ba za ta saɓu ba muna dangin amarya ki fi mu haskawa”

Yadda take magana cikin tijara da iya gaskiyarta ya sa Zuhra ta ɗan dara sannan ta ce, “to muje cikin ko?”

Ƙwafa ta yi sannan tai gaba tana ci gaba da masifa har da yiwa Zeety Allah ya isa wai yadda take faɗa mata ba a haka ta ga Zuhran ba.

wani ɗan ƙaramin falo ta kai ta inda anan ne suke a tattare ko wacce jiran ganinta take yi.
Yadda su ka so ganinta ba haka su ka ganta ba musamman Zeety da ta ga sai fara’a take ba alamar shakka a tare da ita sai ta ji haushi ya kamata.

Zuhra kuwa da ta lura da hakan sai ta ƙara warewa ta danne duk wata fargaba, cikin sigar zolaya ta ce, “Zeety!! gaskiya a matsayinki na asalin ƙawar amarya wannan kwalliyar ba ta dace da ke ba”
A ɗan hasale Zeety ta ce, ” kin ga bana son rashin mutunci da wulaƙanci”
Zuhra ta yi dariya ta ce, “wallahi da wasa nake miki kin yi bala’in kyaau har kin so ki fi amarya bare mu ƴan karere, ke fa kyakkyawa ce kuma mallakin manya kin ga shigar alfarma dake ta fi dacewa”

Zeety ta lura baƙar magana Zuhra take son gaya mata a bai-baice dan haka ta yi shiru tana tunanin ta yadda za ta ƙuntata mata har ta ga babu wannan murmushin akan fuskarta, ta jima tana nazari kafin ta sauya taku daga ita har ƙawayenta suka shiga yarwa Zuhra magana tare da nuna mata kyara da wulaƙanci.

Zuhra kuwa ba ta nuna hakan ya dame ta ba duk da yana cin ranta, gaf take da fashewa da kuka ta ji ance abokan ango sun iso za su kwashi amarya dan haka ta tashi tai musu sallama ta salallaɓa ya shige motarta.

sai da taje gurin ta fara raina kanta dan kuwa har i lokacin ba ta ga fuska ba gaba ɗaya sai ta tsargu gani take kowa kallon bare yake mata ga ta ita kaɗai a cikinsu. tun da ta nemi guri lafiyayye ta zauna ta yi ƙasa da kai ba ta ƙara ɗagowa ba sai da ta ji ana ihun Muftahul-Jannah Alhassan Mai Taimako ya shigo.

Ɗago kanta ta yi zuciyarta na dukan Dubu ɗaya da tari tara da casa’in, a gefe guda kuma mamakin yadda akai duniya ta san shi take yi, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ga hannun Zeety sarƙe a cikin nasa suna takawa ɗai-ɗai tamkar su ne amarya da angon, ba ta san lokacin da ta miƙe tsaye ta dafe ƙirjinta da take jin yana mata wani irin raɗaɗi, komawa ta yi ta zauna dan kuwa yanzu ta tabbatar shi ɗin ne ba gizo idonta yake mata ba, jikinta har rawa yake sabi da tsabar shiga ruɗani da tashin hankali.
Tsoro ne ya ƙara sakko mata da ta ga mazaunin da suka zauna ya yi maƙoftaka da inda take zaune ita kaɗai kamar mayya, sanin halinsa ya sa ta kama kanta dan gudun tozarci.

Zety kuwa tana sane ta yo gurin dan kuwa tinda ta shigo ba ta mutanen gurin take ba ta inda za ta hangi Zuhra take yi da ta ganta kuma shine ta matso kusa da ita yadda komai zai fi mata kyau.

murmushi ta yi tare da kallonsa sannan ta ce, “kalli mutuniyarka da alamu zuwan fa naka ne ina ga ta na son ganinka, ka je ku gaisa”
Da ɗan mamaki ya ce, “anan kuma?? kai anya kuwa ta na da hankali ma wannan?”

Zeeyy ta ce, “iyakar hankalin nata kenan”

taɓe baki ya yi suka ci gaba da wata hirar cikin farin ciki ba tare da wani abu ya sha musu kai ba.

Tashi Zeety ta yi ta ce, “ina zuwa”
ya jinjina kai ya mayar da hankalinsa kan waya.

jikin Zuhra na ta kakkarwa har yanzu ta kasa ɗago kai sabi da tsoro. muryar Zeety ce ta katse tunanin da take yi “ba za ki je ku gaisa da abin son naki ba??”

Ɗagowa ta yi ta kalleta ta kuma sunkuyar da kai dan ba za ta iya cewa komai ba.
jin ta yi shiru yasa ta ci gaba da cewa, “da naga kin nuna jarumta a gidansu Hafsat na ɗauka yanzu ba abin da yake iya tsorata ki sai gashi yanzu kin jiƙe da gumi duk da ba zafi ake ba”

Ta kai maganar tare da ƙyaƙya-cewa da dariya irin ta mugunta.

Da kyar Zuhra ta ce, “ke ce fa ki ka gaiyace ni amma kina wulaƙanta ni, ko dan komai laifina ne tin da ni ce na kawo kaina”
“hhhh kin ɗauka dan na karramaki na nemeki?? a’ahh!! kawai dan na nuna miki iyakarki ne kuma nasan ko yanzu kin san sama ta yi wa yaro nisa, kar ki ɗauka wasan ya tashi fa yanzu ma aka fara hhhhhh”

Daga haka ta bar wajen.
zafi ƙuna raɗaɗi ba abin da zuciyar Zuhra ba ta yi gashi ko kukan ma ta kasa yi sai dai iya karɓar azabar da take. tana shirin tashi ta gudu taji an yi sanarwar shigowar amarya da ango dan haka ta haƙura ta tsakure anan har suka gama shigowa aka cigaba da gudanar da shagali da ta tabbatar komai ya dai-daita sai ta gyara mayafinta ta rufe fuskarta sannan ta fara tafiya ta na haɗa hanya dan kuwa kanta sarawa yake ya na wani irin juyi.

Ta na cikin tafiya ba tsammani ta ji an sa mata ƙafa ta harde ta faɗi, sai da hankalinta ya ɗan fara marowa sannan ta gane inda ta faɗa jikin mutum ne, saurin janye jikinta ta yi ta tashi tana zazzare ido.
Zeety ta saki wani shu’umin murmushi kafin ta ce, “wannan wane irin rashin kamun kai ne?? akan me za ki zo ki faɗo kansa?”

a kiɗime ta ce, “ku yi haƙuri wallahi ba a sani na bane”
Jannah kuwa ganin idanun mutane ya dawo kansu ya sa zuciyarsa ta ƙara tafasa, tasssss!!!!!! tasss!!!!! ya wanke ta da hasu kyawawan maruka hagu da dama, hakan yasa kukan da yake kunno kai ta na danne shi ya samu damar ƙwacewa da ƙarfi.

a Fusace Jannah ya fara magana cikin harshen buzanci “na raba ki da hanyata amma sabi da baƙar maitarki kin kasa rabuwa da ni, ya ci yanzu kin gane matsayinki da nawa akwai tazara me yawa sabi da ballagazanci har za ki zo ki faɗo kaina…”

Bai gama maganar ba ya ga Zaheer ya shiga gabanta ya yi musu tsakani fuskarsa a murtuke ba alamun annuri, mamaki ne ya kama Jannah ganin Ango guda a gabansa.
Ba iya Jannah ba ma duk mutanen da hankalinsu ya zo gurin abin ya matuƙar ba su mamaki Ango ya bar Amaryarsa ya tafi wajen wata.

Cikin ɓacin rai Zaheer ya ce, “ki tsaya mu tawo tare shine ki ka baro danginki ki ka shiga inda ake wulaƙanta ki??”

Rungumeshi ta yi ta baya tana ƙara fashewa da wani sabon kukan.
a kiɗime ya zagayo da ita yana share mata hawayen cikin yaren buzanci yake cewa, “me yasa za ki yi min haka Queen?? kinsan da a tozartaki gwara ni ayi min ko ma menene, me yasa ki ka zaɓi rayuwar ƙasƙanci Queen??”

cikin tsananin kuka ta ce, “dan Allah ka yi haƙuri Zaheer bazan ƙara ba, yanzu na amince da soyayyarka Zaheer nima ina sonka!!!”

Sake ƙanƙameta ya yi gami da cusa fuskarsa cikin wuyanta cikin wata susutacciyar murya ya ce “zan ba da rayuwata da komai nawa akanki, INA SONKI QUEEN!!!!! na fasa auren Hafsart”

Hannu Jancy ya ɗora bisa kansa ya shiga zarya a wajen cikin tashin hankali da ruɗewa. da yake ba da hausa yake magana ba Zeety ba ta fahimci abin da suke cewa ba dan haka ta tambayi Jancy.
Sai da ta mai-maita tambayar ya kai sau biyar sannan ya iya bata amsa cikin ɗaga murya ya ce “Zaheer soyayya yake da Zuhra kuma ya ce ya fasa auren ƙawarki!!!”

Hafsat da take tsaye ta gwale ido da kunne tana sauraren abin da Jannah zai ce ta fasa Ihuu da kuruwa da tirje tirje tana cewa, “kar kai min haka Zaheer wallahi mutuwa zan yi idan ba ka aure ni ba wayyo na shiga ukuna!!!!!!”

Sai a lokacin ya ɗago idanunsa da suka canja kala ya ce, “ki yi haƙuri Hafsa ƙawarki ta tozarta min Ƙanwata wadda na fi so fiye da kowa na duniya kuma ita ɗin Masoyiya ta ce wadda nake da burin mallaka mata ko wane lokaci na rayuwata dan kasancewa tare da ita har Abada, babu aure a tsakanina da wadda ba za ta mutunta min abar ƙaunata ba dan haka ki je ki Auri Jannah Alhasan Me Taimako”

Wani shagen mari Aunty Mariya ta zabga masa tare da jefa masa tambayar “ka na da hankali kuwa?? Kasan abin da ka ke faɗe???”

Cilak ya ɗage Zuhra ya rungumeta a ƙirjinsa sannan ya ce “Aunty Mariya ko me za ku yi komai tsananin hukuncin da za ku yanke min bazan aureta ba”

Daga haka ya ci gaba da tafiya.
ido kowa ya zuba masa gurin ya yi shiru kowa sauraren rikicin yake.

Amarya Hafsat kuwa da ta ji Zaheer ya mai-maita abin da Jannah ya faɗa sai ta silale ta sume.

Jancy ya rasa zaune ya rasa tsaye sai kaiwa da kawowa ya ke yi yana ciza yatsa gaba ɗaya ya fice daga haiyacinsa. abubuwa da yawa sun tare masa haka kawai ya ji wani mugun baƙin ciki ya tokareshi sabi da jin Zuhra da Zaheer suna furtawa juna kalmar so.

 

(Meke shirin Faruwa ne??🤔)

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE*
[11/8, 9:35 AM] INDO CE: *D-YARO*
28

Zaheer Bai saurari kowa ba kai tsaye ya nufi gidansu, ya na tsayar da motar ya ƙarƙa sunkutar Zuhra sai da ya dangana da ɗakin Umma sannan ya direta cikin mugun ɓacin rai ya ce, “Umma bazan iya jurar zama da duk macen da za ta wulaƙanta Queen ba, ki bawa aminiyarki haƙuri domin na riga na yanke hukunci, Queen ta karɓi soyayyata a daren yau dan haka ita zan aura”
“Innalillahi’wa’inna’ilaihirraji’un”
Umma ta faɗa cikin tashin hankali.
Umma Rahina ce ta tashi cikin sauri ta na jefo masa tambayoyi “me yasa? ka na da hankali kuwa Zaheer? ashe za ka iya bawa mahaifiyarka kunya ka tozarta ta a idon duniya??”
Ya girgiza kai gami da cewa “A’ahh!! ba ni da wannan manufar Umma Rahina kar ki sa Ummana ta yi fushi da ni akan gaskiyata, na san itama shaida ce tin da aka haifi Zuhra ba ni da wani muradi ko farin ciki a rayuwa sama da ita na kamu da sonta ne tin bansan kaina ba, Umma dan Allah kar hakan ya ɗaga miki hankali na san ba daɗi amma wallahi cin zarafin Queen ɗita su ka yi kuma kinsan ba na iya jurewa”
Cikin sanyi Umma ta ce, “meye haɗin Queen da Hafsa??”
“DOGON YARO, ta dalilinsa ne hakan ta faru yarinyar da yake so ƙawar Hafsa ce shine suka haɗa kai suka wulaƙanta min Zuhrata Umma”
jaɓar Umma ta zauna ta na dafe goshi “duk laifina ne Zaheer na san wannan ƙaunar ba za ta barka ka auri Hafsa ba amma na take sani na yi ƙoƙarin yi maka dole gashi yanzu dare ya yi min duhu, ba komai ku je Allah ya sanya Albarka ko ba komai na yi farin ciki kasancewar ka samu farincikin rayuwarka ba zan yi fushi ba Allah ya yi muku albarka, amma ka je ka sanarwa iyayenka maza da kanka dan bazan iya ba”
Da sauri ya ce, “na gode Ummata Allah ya saka da alkairi”
Da ga haka ya kama hannun Zuhra da ta zama kamar hoto sai ido ta ke bin su dashi, su ka yi waje.

Jancy ko Zeety bai saurara ba ya yi gaba kamar iska.
Ya na zuwa gida ya tarar da Ummi da Natiee da Fatima suna falo ko kallonsu bai yi ba ya wuce.
Fatima ce ta kasa jurar ganin halin da yake ciki ta ƙyale dan haka ba tare da ta shiryawa maganar ba ta ce “Jannah me ke damunka ne?”
Banza ya yi mata ta yi saurin tashi za ta bi bayansa. dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu.
Ummi ta ce, “ƴata ƙyaleshi ba lallai ya saurareki ba”
A ɗan kunyace ta zauna ta yi ƙasa da kai sai dai har yanzu hankalinta bai kwanta ba.
Cikin damuwa Natiee ta ce, “Ummi na rasa yaushe ɗan uwana ya zama haka a memakon idan ransa ya ɓaci ya yi kuka zuciyarsa ta yi sanyi yanzu sai dai ya yi ta fushi kamar kububuwa haka”
Ummi ta ɗan murmusa ta ce “ba wanda ya ke saurara a lokacin da ba ya cikin yanayi me daɗi kamar ke, ke ce yake gayawa sirrin zuciyarsa kafin kowa dan haka wannan aikinki ne”
Tashi Natiee ta yi gami da cewa “ina zuwa”

a tsakar ɗakin ta tarar dashi yana zagaye ya kasa zama, ta ƙarasa a hankali ta tsaya a gefe sannan ta ce “Jannah Yayan Jannah waye ya taɓa min kai lallai yau akwai badaƙala, gaya min waye???”
Cikin zafin rai ya ce “Natiee!! me yasa wani lokacin gaba ɗayana na karfa ne kuma mara amfani??”
“kashhhhh!!”
Ta faɗa kafin ta cigaba da cewa “Astagfirullah! na faɗa a madadinka amma faɗen hakan da ka yi tamkar izgili ne da nuna butulci ga Allah, me ka nema ka rasa a rayuwa Ɗan Uwana? kai mutum ne wanda Allah ya yi masa baiwa iri iri amma in ka ce haka ka butulce masa Jannah, a ko da yaushe manyanmu, iyayenmu, malamanmu, cikin gaya mana suke su na nusar da mu kar wani son zuciya ko wata jarrabawa ta gifta wadda za mu nuna butulci ga Allah, ka sassauta dan Allah yanzu ga ka ga ƙanwarka ka gaya min meye abin da ya sa ka ɓacin ran nan”
Dogon tsaki ya doka ya ce, “Zuhra!!! me yasa Natiee! ta dalilin ni da ita Zaheer ya ce ya fasa auren yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba, wai ma akan me ta na sona za ta haɗa soyayyata da ta wani?? me yasa ba za ta tsaya iya kaina ba har sai ta danganta soyayyata da wani? ba ta ji kunyar ƙasƙantar da ni ba ta ke gaya masa wai ta na son shi, ni fa ban yarda a haɗa soyayyata da ta wani ba indai sona take ba ƙarya ta ke ba”
Natiee ta jinjina kai gami da cewa, “too! danƙari lallai maganar babba ce, amma yayan fisabilillahi ba ka son yarinyar nan akan me ba za ta so wani ta samawa kanta salama ba?”
“amma dole sai ta shiga rayuwar yarinyar da ba ruwanta? hakan fa kuskure ne Nati”
Natee ta ce, “ka ga zauna Jan ka sassauta wannan fushin naka ka yi tunani sosai akan abin da ya dace da ita da kai da shi, ka ga yanzu Fatima ma ta na can cikin fargabar abin da ya faru da kai yanzu za ta ji daɗi ne idan ta ji abin da ya faru? dan Allah ka haƙura ka dena ta da zancen nan ya wuce”
“shi kenan” ya ce kafin ya tashi ya shige banɗaki.

Fatima ta na ganin Natee ta yi saurin tashi ta na tambayarta “ki je ya na nemanki”
Natiee ta faɗa tare da wucewa ta zauna.

Ya na fitowa ya yi tozali da Fatima ta yi tsuru tsuru da alamu ta daɗe ta na kallon saitin ƙofar bayin dan jiran fitowarsa.
Ɗan murmushi ya yi ya ce “Inna Wuro!!”
Ƙasa ta yi da kai ta na murmushi tare da ajiyar zuciya har cikin rai ta ji daɗin gani murmushi akan fuskarsa.
Jin hannunsa akan kafaɗarta ne ya sa ta yi saurin daɗo kai ta na kallonsa, kashe mata ido ya yi ya na murmushi ya ce, “ƳAR MANYA!!”
Ckin murya me ka ma da ta shagwaɓa ta ce, “na ji tsoro da ka shigo na ga ba ka farin ciki”
Ya ce, “Yar Manya anya kuwa yau kin je makaranta?”
Ta gyaɗa kai alamar “e” “a’a anya kuwa? ban ga alama ba”
Ta ce, “ka tambayi Natiee da gaske nake na je”
Ya ce, “to kar ki dinga makara”.

Tin bayan faruwar haka Zaheer bai ƙara bi ta kan Hafsa ba ko da aka sanar ta na asibiti bai je ya nemeta ba, haka aka ci gaba da gudanar da wasu ƴan shagulgulan ba tare da tabbacin WACECE AMARYAR ba.
Har ranar ɗaurin aure ta zo Zaheer bai sauke bakarsa ba duk da irin ba shi haƙuri da rarrashin da ake masa.
Haka akai ta tirka tirka, sai kusan azhar Alhaji Abdussalam (mahaifin Zuhra) su ka shawo kansa da kyar sannan aka ɗaura aurensa da Hafsat.
da Zuhran da Zaheer ɗin sun ci kuka kamar ba za a mutu ba, Zaheer kamar ba namiji ba haka ya koma sabi da tsabar karaya da raunata da ya yi, ya yi matuƙar kwaɗaituwa da auren Zuhra a wannan karon gashi kuma Allah bai tsara hakan ba.
Tausayinsa ya na ɗaya daga cikin abin da ya sa Zuhra ta daddage ta ci kuka ta shiga damuwa a gefe guda kuma ta kan ji kamar shi kenan an rabata da farin cikinta.

taro ya tashi lafiya Su Zaheer sun tare a gidansu shi da matarsa, har yau bai gama sakin jiki da ita ba ya kasa mantawa. ita kuwa abin ya na bala’in damunta dan dai ba yadda za ta yi.

Zuhra kuwa ƙarin shiga damuwa ta yi ga kewar Zaheer ga tunanin shi kenan ta rasa duk wata dama ta duniya da za ta kasance me kyau a gareta.

Natee ce ta ƙarewa Jannah kallo cikin sigar zolaya ta ce “Muftahul Jannah na Zuhra ni fa sai na ga kuna min kama ƙwayar idonku ma iri ɗaya”
tsaki ya ja ya juya mata ƙeya tare da cewa “a ka na fi ji”
dariya ta yi sannan ta ce, “Yayana na gaji da zaman nan a gida haka-nan shi yasa na ce zan cigaba da zuwa islamiyya tare da Ƴar Manya”
Kallonta ya yi cike da tausayawa “amma Natee! sai dai ki koyar”
Katse shi ta yi da cewa, “ai ilmi kogi ne Jan idan na ci gaba da nemansa ba laifi bane hasalewarka da sa albarkarka kawai na ke buƙata, idan ka amince gobe ka kaimu ni ma in zama ƴar makaranta Fatima ma za ta fi jin daɗin hakan”
Ya jinjina kai gami da cewa “Allah ya kaimu goben”
“amin”.

Hajiya Saratu ta yi shiru ta na saurarar baɗi ba ran da ƴaƴansu suke faɗe akan abin da ya kamata su yiwa Jannah a cikin shawar-warinsu ba wadda ta yi mata dan haka ba ta kula su ba, sai da taga abin nasu ba na ƙare bane sannan ta ce, “ya isa haka!!”
Duk su ka yi shiru suna kallonta dan jin abin da za ta faɗa.
Hajiya Murja ta ce, “Hajiya kin yi shiru kuma kin hana su magana”
A ƙasaice ta ce, “a cikin abin da suke faɗe ba abin kamawa dalilin da ya sa na hana su kenan, ku gaya min a cikinku waye zai iya yin komai waye ba zai iya ba? indai kun shirya ni zan gaya muku abin da za ai,, ina jiran ta bakinku”
Hisham ne ya yi saurin cewa “wallahil’azim Hajiya akan dukiyar ubana da ake neman cinyewa ba abin da ba zan yi ba dan ni kuɗi sun fiye min komai a rayuwa, Allah na tuba muke aikata abin da mu kanmu munsan zunubi ne akan samun duniyarmu yadda ya dace?”
“to wallahi ni ko kashe Alhajin da ƴaƴan nasa ne zan iya dan na tsanesu duka ƴan-wahala, na tsani me ƙaunar yaron nan duk inda zan yi masa lahani nan nake nema wallahi a kashesu ma duka” Faɗar Sultan kenan:
Haka su kai ta faɗen abin da yake bakinsu wanda ba komai a ciki sai RASHIN IMANI da SON ZUCIYA da BUSHEWAR ZUCIYA kamar ba ɗan uwansu ba hasalima kamar ba ƴaƴan musulmi ba.
“hhhhhhhh”
Hajiya Saratu ce ta bushe da wata muguwar dariya “yara kun zo bigiren da nake buƙatar ganinku akai ba shakka ko da ban kashe Muftahu ba na san na yi nasara akansa dan na gada muku ƙiyayyarsa wannan kawai ya isheni, gashi yanzu kun furta da bakinku shakka babu wannan lokacinmu ne, ya ku ƴaƴana ina buƙatar haɗin kanku baki ɗaya ba buƙatar nuna wariya ko ƴan ubanci a tsakaninku a dai-dai wannan lokacin, ko da yaushe ku kasance cikin shiri mu aiwatar kafin wani abin ya zo ya gifta ya ce-ceshi lallai mu yi da jiki kuma mu haɗe kai mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, Duk wanda ya amince da ni ya dawo bayana”
zanzarewa su ka yi su ka koma bayanta duk alamar sun amince kenan.
Ta ƙara sakin dariya sannan ta fara ba su bayani.

Jannah ne zaune kusa da ƙafafun Aba jikinsa sanyi ƙalau. Aba ya ce “ɗana kar ka ji na ce haka hankalinka ya tashi dukiyata halak malak ta ka ce kai da ƴan uwanka masu ƙaunata sauran kuma ba su halakta gareni ba”
Cikin sanyi ya ce “Abana yanzu ya ka ke so ayi??”
“zan sayar da wasu daga cikin kadarorin da na mallaka sannan zan sayi wasu da sunanka da na ƴan uwanka, ba wai aro ko jingina ba kyauta na baku sun zama na ku halak malak kuma ba na son wasu su yi muku barazana akan halak ɗinku ɗana, lallai ka nuna tsayayya akan haƙƙin ƴan uwanka domin kuwa dukkansu mata ne ka kare haƙƙinsu ka tsaya musu tamkar mahaifi, ka yi min alƙawarin za kai min hakan ko da bana raye”
Kukan da yake dannewa ne ya samu damar kuɓucewa da ƙarfi, rungume ƙafafun Aba ya yi cikin shashshekar kuka ya ce, “Kaicona Aba har ila’i yanzu da nake zaune kusa da kai ina son ƴan uwana ina yi musu sahihiyar ƙauna a matsayinsu na yayyena ina ma ace na samu ƴan uwa na gari Abana tabbas da na kasance ƊA Mafi gata a duniya tabbas da suna ƙaunata da na nunawa duniya sune Bangon wannan Yaro dake zaune a kusa da kai Aba, ba su taɓa ƙaunata ba amma ni ko da wasa ina baƙin cikin na ji an faɗi munanan magana akansu, ina ma za ku gane gaskiya ƴan uwana!!! Abana me yasa ba za ka basu lokaci ko za su fahimci kuskurensu ba??, Aba kana kirar wa kanka mutuwa amma har yanzu ba ni da ƴan uwan da za su jiɓanci lamarina a matsayina na ƙaramin yaro Kaicona ina ma ban zo duniya ba, inama na mutu tin ina cikin mahaifiyata! Aba me yasa nake ta tsallake tarkon mtuwar da ƴan uwana suke haɗa min? me yasa na kasa mutuwa dan na cika muradin ƴan uwana???????”
kuka me tsananin zafi da ƙuna da raɗaɗi ne ya danne maganar da yake yi.

 

 

TAKU HAR KULLUM..
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..”*
[11/9, 9:39 AM] INDO CE: *D-YARO* 29

 

“da ƴan uwanka sun so ka da na fi kowa murna da hakan Yaro sai dai dole dai ko an canja gaskiya wata rana za ta dawo dai-dai ba sa ƙaunarka, zuciyarsu ta riga ta bushe ta ƙeƙashe duk sabi da son zuciya da son duniya, A’uzubillah Allah kai mana tsari da wannan duniyar da za ta sa mu aikata zunubi, Muftahul-jannah ba kuka ne ya kamata ka yi wa ƴan uwanka ba indai har ka na sonsu addu’arka ita su ka fi buƙata ka nema musu yafiya a gurin Allah idan ya so sai ka ga ya yafe musu har ya shiryasu sun zama mutanen kirki, ka yi haƙuri ka kwantar da hankalinka yarona Allah ya na tare da me gaskiya ko da kuwa an yi haƙa ne a cikin ƙasa an birne shi to Allah ya na tare da shi, ka ci gaba da kyawawan halayenka da ɗabi’unka Allah zai ba ka nasara akan duk abin da ya gagareka ɗana, temakon da mu ka saba yi da ayyukan alkairi ko da yaushe so nake su ƙara haɓaka ba su yi ƙaranci ba ka riƙe wannan ma ɗana, ka dena kukan sai ka gaya min ka yarda da ni ne ko kuwa?”
bayan Aba ya yi shiru an ɗauki lokaci me ɗan tsayi Jannah ya na kuka kafin ya iya sassautawa, ya goge ƙwallar ya na sauke ajiyar zuciya a kai a kai, “Abana duk abun da za ka faɗa na san gaskiya ne kuma duk hukuncin da ka yanke akaina a shirye nake”
Aba ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce, “na yi matuƙar ɗora yaƙini akanka ɗana, Allah ya yi maka albarka yayi jagora a lamarinka”

Zuhra ta na zaune akan gado rungume da filo ta yi tagumi ta ji sallamar Zaheer, cikin sauri ta diro daga gadon ta nufeshi ta na murmushi cike da murna da farin cikin ganinsa.
Kamar wanda aka dasa a wajen haka ya tsaya ya na kallonta cikin tsananin tausayi da wani irin zafi da raɗaɗi.
tunowa da ta yi yanzu ba da bace ya sa ta Durƙushewa a gabansa ta re da rushewa da kuka me tsuma zuciya.
sai yau ya ƙara tabbatarwa kansa irin muguwar damuwar da take ciki duba da yadda ta ƙare ta lalace ta yi baƙi ta koɗe kamar ba ita ba. a hankali ya durƙusa saitin fuskarta cikin dauriya ya ce, “Queen!!! duk da nasan ba dan ni ki ke kukan nan ba amma ina roƙon afuwarki kasancewar na yi kamar bazan ƙara waiwayarki ba, na zaɓi hakan ne ko zuciyata za ta samu salama ki gafarceni”
Girgiza kai ta yi cikin kuka ta ce, “ba ka da laifi Yaya Zaheer ko me ya faru laifina ne, na yi asarar soyayyar gaskiya soyayyar da aka gina bisa tsafta-tacciyar ƙauna na yi rashin masoyi da na ba ri na rasaka Zaheer, na yi nadamar ƙin karɓar soyayyarka a lokacin da ya dace!! wai yaushe zan mutu na dena ganin baƙin cikin rayuwa? yanzu ya tabbata har na koma ga Allah ba ni da sauran farin ciki kenan??”
Lumshe ido ya yi gami da girgiza kai ya ce “a’a Zuhra!”
Buɗe idon ya yi ya zuba mata kafin ya ce, “komai da kika gani Allah ne ya tsara hakan a rayuwarmu ba yin kanmu ba ne ba wani ne ya hana ba, kin sani dai kowa na duniya ya na da mahaɗinsa bayan haka fa wuya ba mutuwa ba ce, akan iya asha wuyar kuma a dawo lafiya dan haka ki sa a ranki indai akwai haɗi tsakaninki da Jannah ba makawa sai kun haɗu idan kuma ya rubuta ni ne mahaɗinki to ba abin da ya isa ya dakatar”
“ba zan ƙara son Jannah ba tinda ba shi da imani Yaya Zaheer na yarda na ƙare rayuwata cikin wannan wahalar na san ba zai taɓa tausaya min ba”
kamar zai fashe da kuka ya ce, “ki yi haƙuri komai me wucewa ne wata rana sai ki ga kamar ba a yi ba ki dena kuka kin ji”
Amir da ya iso yanzu ne ya ce “ai sai dai haƙuri dan ba lallai ta taɓa fahimta ba”

rayuwa ta ci gaba da garawa a haka ta ɓangaren Zuhra.
Kamar yadda Aba ya ce zai yi bai fasa Ba duk ya haɗe kadarorinsa ya canja musu zama.

Jan ne zaune a ɗan madai-daicin Seatroom ɗin gidan su Zeety, hira su ke yi cikin kwanciyar hankali, Zeety ce ta ce “Jancy kullum zuba ido na ke yi na ji ka yi maganar aurenmu amma sai na ji shiru nifa gaskiya ya kamata mu wuce gurin, mutane har sun fara cewa wai dama ba so na kake ba”
ya ɗan murmusa kafin ya ce, “ohh dan Allah kar mutane su yi mana kutse cikin rayuwarmu mana kema dai kin san ina sonki…”
fasa maganar ya yi sabi da kiran da ya shigo wayarsa, ganin Ummi ce ya sa shi ɗagawa cikin sauri tare da cewa “Assalamu-alaikum Ummina!!”
Hankali tashe ta amsa sallamar ta ci gaba da cewa, ” ka zo gida yanzu ba lafiya Fatima ba lafiya ka yi hanzari ko me kake ka dena”
Da sauri ya miƙe ya na cewa “me ya sameta?? Ummina meke faruwa ne?”
Ummi ta ce, “idan ka zo ka fi fahimta dan Allah ka kawo mana ɗauki”
“to” ya ce sannan ya katse wayar.
Ganin yadda ya fara diriricewa ya sa takaici ya kama Zeety, cikin basarwa ta ce, “me yake faruwa ?”
Ya ce, “ki yi haƙuri Ummina ce ta ke nemana cikin sauri Fatima ce ba ta da lafiya, ina ganin sai Allah ya kaimu gobe”
Bai jira ta ce wani abu ba ya fice kai tsaye motarsa ya shiga ya bata wuta.
Zeety ta na tabbatarwa ya tafi ta fito ta shige maƙotansu cikin sauri.
a tsaitsaye ta gaida Umman su Sakina tare da tambayar ta ina Sakina.
Sakina da take a ɗaki ta ɗaga murya ta ce, “gani nan, shigo”
Kafin Sakina ta rufe baki tini ta afka ɗakin, tin kafin ta zauna ta fara cewa “akwai bala’i wallahi da sake Sakina!”
Sakina ta ce “ƙalau?? me ya kawo wannan fusatar ƙawata?”
“wallahi Sakina yanzu Jancy ya fara son matarsa a son da yake min cikin ɗari kaso talatin ko arba’in ta koma kanta, kin san fa ni kishi gareni ba zan iya gani ba wallahi ya zama dole na ɗauki mataki ki bani shawara me ya kamata na yi??”
Sakina ta kwashe da dariya kafin ta ce, “Allah ya ƙara zan ce Zeety ai tin farko sai da na gaya miki ta na gidansu tare suke kwana suke wuni idan ya na gida kuma fa ba wai ta gani a ƙyale bace, ina nufin ba finta kyau ko wani abu ki ka yi ba kinga ya zama dole ta shiga fadarki”
Zeety ta ce “na ji dan Allah kar ki ƙara min baƙin ciki, yanzu meye abin yi??”
Sakina ta ce, “ni fa ya ma fara ba ni tsoro anya kuwa zai aureki?”
“ni fa malama na san zai aureni dallacan”
Sakina ta ce, “Okey to indai kin tabbatar ya na sonki to wallahi ki fara nuna masa hanyar da kike so idan ke ɗin ke idan kuma matarsa matarsa kinsan maza fa yanzu ba a zuba musu ido ya zama dole ki samu makama, yadda ya ɓata miki rai ke ma ki ɓata masa dan wallahi idan ya na yi miki irin haka ki na haƙura to fa kece a wahale, gobe da safe zan shigo sai mu cigaba da magana kin ga yanzu Abbanmu ya isa dawowa”
Zeety ta ce, “to ina jiranki dan Allah ki fito da wuri”

Natee Ummi suna zaune cikin damuwa sunyi jugum jugum ya yi sallama, cikin sanyin jiki ya durƙusa a gaban Ummi kamar me shirin fashewa da kuka ya ce “Ummin Natiee me ya faru da Faɗimatu?”
ɗan goge ƙwallah ta yi sannan ta ce “ban sani ba amma ya fi kama da cutar iska, su na girki a kicin kawai Jannati ta ga ta yi shiru ta juya baya ta na yi mata magana ta shammace ta ta shaƙeta da kyar muka ƙwaceta bayan nan kuma a dole sai mun barta ta fita gashi ba mu san inda za ta mufa ba dan ba’a hayyacinta take ba, yanzu dai mun samu da temakon Allah da addu’o’i bacci ya kwasheta, shi yasa na kira ka gashi Abanka baya nan mun ji tsoro sosai ka ga Natee har yanzu ba ta dawo dai-dai ba sabi da fargaba, ina ganin wannan wata sabuwar hanyar ce suka tsiro dan su hana mu zaman lafiya”
Jinjina kai ya yi ya ce “Allah ya fi ƙarfinsu kar ku damu za ta samu Lafiya in sha Allah, Natee ba komai fa ki dena kuka mana”
Cikin kuka ta ce, “Allah sarki wallahi na ji tausayinta duk a dalilinmu ne hakan ta faru da ita”
Ya ce “Allah ya tsara hakan dama ba danmu bane, na ce ki dena kuka ko so ki ke nima naita kukan ne??”
Ta girgiza kai alamar “a’a” ya ce”to ba na so ki dena”
Gyaɗa kai ta yi alamar ta fahimta.
Ummi ta ce “ka je ka duba halin da take ciki”
ya ce “to” sannan ya tashi ya nufi ɗakin nasu.

A bakin ƙofa ya ci karo da ita ta ta raba hanya ta yi kwanciyarta ta na ɗan wasa da farcenta.
Cikin murya me nuni da raunin zuciya ya ce “Ƴar Manya! meye na kwanciya anan kuma?”
Ɗago idanu ta yi ta zuba masa ta na wani shegen murmushi me cike da ma’anoni iri iri.
Durƙusawa ya yi saitin fuskarta ya ce “magana nake fa kin yi min shiru”
Yanzu ma shirun ce babu alamun amsa. hannu ya kai zai taɓa ta ta yi saurin matsawa ta na cewa “kar ka taɓa ni”
Ya ce “to sabi da me??”
Ta ce “ba ka san akwai dafa’i a jikinka ba??, hhhhhh” ta kwashe da dariya. Jannah ya zuba mata ido kamar soko ya rasa ma wane irin tunani zai yi. muryarta ce ta buwayi kunnensa “in faɗa maka gaskiya??”
Ya gyaɗa kai, ta ce “kai kyakkyawan gaske ne, shi yasa da aka aikota ta yi aiki ta zo ta kama soyayya, to yanzu ni akaa
turo domin na hallaka ka da kai da ita harda ɗan cikinta, hhhhh na ga ka razana ba ka san ta na da ciki ba ko? kar ka yi mamaki domin kuwata na da miji ɗanta ba shege bane kaine ubansa”
Murmushi gami da ƙwallah ne suka sukwano masa a lokaci ɗaya. ta ce “me yasa kuma kake murmushi a maimakon ka yi kuka? duk ahlinka fa zan kashe”
Ya ce “dole na yi farin ciki ko da yanzu zan mutu na san zan cika ne bayan na sanya Abana murmushi, bare ma ko ɗana ba za ki iya cutarwa ba bare matata da ƴan uwana ”
Ta ce “dama ɗanka ai ba zai taɓu ba, taɓa mahaifiyarka ya fi sauƙi akan taɓa ɗanka, duk abin da su Hajiya Saratu su ka yi akanku ba ya yuwuwa shiyasa su ka turo ni kan matarka duk da cewar itama ta na da nata amma na ku ya fi ƙarfi aljanu za su iya hawa kanta amma sihiri ba zai kamata ba”
Ya ce “ina son yin magana da matata”
ta ce ” ba zai yuwu ba”
bai ce mata komai ba ya tashi.
Har ya yi wanka ya fito ta na gurin a kwance sai wasu ƴan waƙe waƙe take, ita kaɗai tasan abin da take faɗe dan maganar ta-ta ba ta fita sai dai kaji ƙus-ƙus-ƙus.
Shammatar ta ya yi ya ɗagata cikal ya rungumeta a ƙirjinsa ya nufi gado da ita, wata muguwar ƙara ta ƙwallara tare da mimmiƙewa ta na wutsil wutsil sai kuma ta yi laƙwas.
Sharaf!!! ya zube ta akan gado kamar ba mutum ba, gyara mata kwanciya ya yi kafin ya kira sunanta dan yanzu ya tabbatar ta dawo dai-dai.

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/10, 9:52 AM] INDO CE: *D-Y*
30

a hankali ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi cikin muryar da ba ta fita sosai ta ce, “Ɗan Manya ka dawo?”
ya ce “e, sannu ina ne ke miki ciwo yanzu?”
wata zazzafar ƙwalla ce ta shiga tsiyaya ta gefen idonta da kyar ta ce “duk jikina ciwo yake yi, dan Allah ka kai ni na ga Baffa”
rungumeta ya yi yana hawaye cike da tausayawa ya ce, “zan kai ki amma sai gobe Allah ya baki lafiya, ki dinga yawaita addu’a ko da yaushe kin ji matata”
Ta gyaɗa kai, ya ce “sannan kar ki dinga nesa da Ummina ko Natiee, da ace ni mazaunin gida ne da ko da yaushe zan kasance tare da ke Faɗimatu, ki taya ni kiwon lafiyar ɗana dake cikinki dan Allah”
Cikin rashin ganewa ta ce “ka na nufin ina da juna biyu?”
Ƙara rungumeta ya yi gami da cewa “ƙwarai”
Kuka me ƙaramin sauti ne ya kufce mata, bai hana ta ba sai ma ta ya ta da yake yi.

washe-gari
tin wuri suka shirya suka nufi hanyar Garin su Baffa.
Tin da ya tashi ya ke kiran Zeety amma ta ƙi ɗagawa ya tura Message duk ta ƙi saurara, tin da ga nan ya gane fa akwai matsala, jikinsa ya yi sanyi sosai.
Suna dawowa bai zame ko ina ba sai gidansu. sai da ta gama ƙalelaji sannan ta fito sai wani basarwa take yi, har su ka rabu bai samu ya shawo kanta ba da ya ɓulle ta can za ta ɓullo ta nan, sai da su ka ɗebi kwanaki su na wannan wasan ɓuyar bayan ta gama ba shi muguwar wahala sannan ta dawo dai-dai, shi kuwa da yake ya na matuƙar sonta duk bai gaji da irin wahalar ta-ta ba.

Gyaran murya Aba ya yi sannan ya ce, “to Alhamdulillahi, kamar yadda na faɗa maka Muftahul-jannah yanzu na kammala duk abin da na ce zan yi, wato na sayar da kadarorina na sayi wasu na bayar da komai gareka yanzu ƙalilan ne suka rage su ne wanda suke mallakin ku duka, waƴan nan kuma su naka ne, ƴan uwanka su Faiza ma daban na saya da sunansu, na yi komai a gaban yardaddu kuma ƙwararan hujjoji wanda su ɗin iyaye ne a gareka, ALHUSAIN ABUBAKAR ILYAS ɗan uwan haihuwar ALHASAN ABUBAKAR ILYAS inkiya Me Temako ina nufin Husainina gashi nan a zaune, sai kuma ALHAJI ABDUSSALAM IDRIS, ALHAJI ABUBAKAR ƊAN ƘWARAI, ALHAJI USMANA ƊAN KASUWA, sun kasance shaƙiƙan abokai kuma Aminai a gareni, da saninsu da kuma sahalewarsu a matsayin shaidu na sayar kuma na sayi wannan kadarori, Allah ya tayaka riƙo Muftahu”
Gyaɗa kai ya yi murya a cunkushe ya amsa da “amin Abana”
Abi ne ya ce “bayanin ɗan uwana haka yake Ɗana ko waye ya nemi shaidarka to mu ne, Allah ya yi jagora”
Da “amin” ya amsa cikin sanyi da wata irin fargaba gami da tsinkewa.

Larurar Fatima ko da yaushe motsawa take har ta na neman ta’azzara, idan Jannah ba ya kusa ba ƙaramar wahala take bawa Ummi da Natiee ba dan haka Ummi ta umarceshi da tafiya Niger tare da ita domin neman lafiyarta.

Bayan sun dawo, ta ji sauƙi ta yi lafiya kamar ba ita ba, yanzu ba wani abin da yake damunta sai laulayi.
Zeety kuwa ba irin wulaƙancin da ba ta yi wa Jannah, duk da abin ya na ƙona zuciyarsa amma so ya rufe masa ido sam ba ya ji ba ya gani.
Zuhra, Kura ta yi lafiya ta rage damuwa da yawan koke koke har ta yi ɓulɓul ta ciko, a ɓangaren Zaheer ma hakan take shi ma ganin ta ware ya sa ya warware.

yau ta kasance ranar Lahadi.
tin da safe Ummi da Fatima su ka tafi gidan Abi, Natee kuwa cewa ta yi ba za ta je ba makaranta za ta je Ummi da tasan ba yarinya ba ce sai ta ƙyaleta.

da misalin ƙarfe 03:00pm ta na aji ta na ɗaukar darasi wani Malami ya shigo ya dakatar da su sannan ya ce, “Jannat Alhasan Me Temako!! yayanki Muftahul Jannah Alhasan Me Temako ya zo da uzuri cikin gaggawa ba sai an tashi ba ya turo abokinsa ya ɗaukeki dan haka ki tashi ki je sai Allah ya kaimu gobe sai a fito da wuri kar a makara”
Rasss!! gabanta ya faɗi har ƙasa, kamar wadda aka zarewa laka haka ta tashi sululu ta fice daga ajin zuciyarta cike da tsoro wane abu ne me muhim-mancin da zai sa Jannah ya ce a ɗauketa daga makaranta yanzu?? kamar ba ta yarda ba kamar ta yarda, gashi ta na jin tsoro amma ta na gudun ta ƙi zuwa ya yi ta jiranta dan haka ta bi bayan wanda ya zo ɗaukar ta-ta. sai da ya buɗe mata motar ta shiga sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa na direba.
su na fara tafiya ya tsaya wani matashin saurayi ya shiga, cikin mamaki Jannatiee ta ce “wannan kuma waye? ya ka ɗaukeni kuma za ka tsaya ɗaukar wani??”
Ya ce “ki yi haƙuri Madam”
Ta buɗe baki za ta yi magana ɗayan matashin da ya shiga daga baya ya shaƙa mata wani ƙyalle atake ta yi laƙwas ta zube kan kujerar motar.

Aba ya na tsakiyar gudanar da al’amuransa kira ya shigo wayarsa, bayan ya ɗauka aka yi sallama gami da cewa, “ka yi hanzarin zuwa gida Jannah ba lafiya ya ce a kira ka ni abokinsa ne”
Daga haka ɗiff aka katse kiran. wayar Jannah Aba ya shiga nema amma ba a ɗauka sai ta gama ringing ta katse dan kanta, cikin sauri sauri ya ture aikin ya nufi gida Hankali tashe.

Unguwa ce wadda babu gine gine da yawa bare a samu mutane gini tsilli tsilli ne shima yawanci ba kammalallu bane ana kan yin su ne, a bakin wani gida suka tsayar da motar sannan su ka yi cali cali suka shigar da Natiee ciki, ruwa suka yarfa mata ta farka sannan suka kira waya su ka sanar aka ƙara basu umarnin abin da za su yi.
Wani saurayi ne ya shigo ya na murmushi jikinsa har rawa yake yi, akan Natiee da take zaune ta na zazzare ido ya tsaya cikin rashin imani ya ce “kin san ni??”
ta girgiza kai ya ce “ni abokin yayanki ne, hhh yau zan yi abin da na daɗe ina muradi gashi na samu cikin sauƙi yayanki ya sallama ki gareni”
Cikin rashin fahimta ta ce “ban gane ba waye kai? wane yayan nawa??? na san yayana ba zai taɓa cutar da ni ba ka gaya min su waye su ka turo ka? me yasa za ku zalumceni? waƴannan azzaluman mutanen ban yi musu komai ba su ka ɗakko ni dan Allah ku bar ni na tafi”
Wani da ga cikinsu ya ce, “Ai na yi zaton ba kya magana da na ga kin yi shiru da ki ka ganmu da yawa ashe kina yi, za mu barki ki tafi amma sai mun gama cimma Abin da aka sa mu”
a mugun tsorace ta tashi da gudu ta taka da nufin guduwa sai ta ga sunyi curko curko a hanya. saurayin ya bushe da dariya sannan ya ce “ba za ki iya kuɓuta ba, ku riƙe min ita”
Cifketa su ka yi da iya ƙarfinsu, kiciniyar ƙwatar kanta ta shiga yi ganin ta ƙi nutsuwa ya sa saurayin ya shiga dukanta duka na rashin imani da tausayi ya buga ta can ya bugata can haka ya dinga katan-tanwa da ita har sai da ya ga ya buga kanta akan dutse jini ya fara shatata ta yi suman dole sannan ya rufar mata.

Kuka me tsanani Ummi da Fatima Har ma da Ammah matar Abi su ke yi, Ukasha ne ya yi sallama ganin suna kuka ya sa ya shiga tambayar ba’asi Yazid da yake zaune kamar butum-butumi ne ya miƙo masa wayarsa Ukasha ya karɓa yana warara ido dan ganin abin da suka gani ya sa su kuka.

Hoton Jannah ne ake yaɗawa a social media jikinsa duk jini hannunsa riƙe da wata muguwar wuƙa da ke suke a ƙahon Zuciyar Aba.
rubutun da aka yi a saman hoton shine.

Yanzu yanzu mu ka samu labarin Muftahul-jannah Alhasan Me Temako ya kashe mahaifinsa sabi da wata manufa da ba mu samu nasarar gano ko ta mene ba, sannan an nemi ƙanwarsa Jannati an rasa itama ana zargin ta faɗa hannun wannan ɗan ta adda. hakan kuwa ya yi matuƙar dunguzuma ƴaƴan wannan mamaci waƴanda uba kawai su ka haɗa da Jannah sun ce sai sun ɗauki matakin shari’a dashi kotu ce kawai za ta iya rabasu dan kuwa sai an bi musu haƙƙinsu na kisan mahaifinsu da sace ƙanwarsu wadda alhakin kulawa da ita ya rataya a wuyansu, mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Muftahul-jannah sai dai bai ce komai ba, sai hotunansa da muka samu nasarar ɗauka a lokacin da muke ƙoƙarin jin ta bakin nasa.

jifa Ukasha ya yi da wayar ya fice da gudu, a tsiyace ya figi motarsa ya na wani irrin gudu na fitar hayyaci, lokacin da ya isa gidan ya cika da mutane iri iri da masu farin ciki da masu jimami da masu alhini, har Sashin Aba ya dangana ya tarar da su Abi, Abi ne ya ce “Ukasha ka kira waya ka ce su Aaminatu su tawo”
Gyaɗa kai ya yi ya ce “ina Jannah Abi? me yake faruwa ne? kenan kun yarda Jannah ne ya kashe Aba ni fa wallahi ko kasheni za ayi bazan taɓa yarda ba kawai sharri su ka yi masa”
cikin dauriya Abi ya ce “ya isa haka Ukasha! kasan akwai mutane da yawa ba mu kaɗai bane ba amfanin tashin hankali, Allah zai bayyana gaskiya ni ma nasan ba shi ne ya aikata ba, ka je wancan ɗakin ya na ciki”
Da gudu gudu ya nufi ɗakin, Jannah ya na tsaye maƙale a jikin bango idanunsa a rufe garam, sabi da tsabar cizo da taunar da yake wa leɓensa har ya fashe ya fara tsatstsafar jini, kallo ɗaya za ai masa a gane irin tashin hankalin da yake ciki ba na wasa bane duba da yadda ya fita haiyacinsa lokaci ɗaya.
jin ƙarar waya a aljihunsa ya sa Ukasha ƙarasawa ya ɗauka gami da ƙaro murya sannan ya yi sallama, a ɗaya ɓangaren Alamee ne ya amsa a mugun kiɗime ya ce “meke faruwa haka Jannah? ankira ni ance na je wata unguwa na ɗauki Jannati yanzu kuma labari ya cika gari cewar ka yi mata fyaɗe kuma ka kashe Aba wannan wace irin baƙar rayuwa muke ciki anya kuwa za mu gama da duniya lafiya? me ka tarewa mutane da su ka dage wajen tarwatsa maka rayuwa? yanzu yayyenka sun ce sai sun yi shari’a da kai sabi da ba su san inda ke musu ciwo ba, babu shakka muna ƙazamar rayuwa a duniya Kaicona Allah ka gafarta min ya Allah ba dan ni ba dan mummunan halina ba Allah na san ni ba komai bane face wani bawa mara amfani a duniya, Jannah rayuwarmu ta ƙara shiga bala’i, duniya tana ƙarewa amma kullum muna ƙara nitso cikin kafirci da jahilci a’uzubillah, Jannah meye amfanin abotarmu bayan mun kasa cetonka daga wannan mugun nufin? mu ya kamata mu bawa Jannat kariya amma mun kasa duk yawanmu, Subhanallah! Hasbunallahu-wani-imal-wakil”
Wani zazzafan kuka ne ya biyo bayan maganar ta sa.
Ko motsawa Jannah be yi ba kamar bai ji abin da aka ce ba, tsabar dukan da zantukan Alamee ya yi masa ne ya sa ya ƙara sumewa a tsaye, ji yake inama ta shi mutuwar za ta riskeshi a dai-dai wannan lokacin.
Ukasha kuwa sai a lokacin kuka me ƙarfi ya yi nasarar ƙwace masa cikin shashshekar kukan ya ce “Alamee ashe kai ma ba ka yarda ba? na tabbata ɗan uwana ko ƙaramin rai ba zai iya kashewa ba bare na mutum mutum ɗin ma mahaifinsa sannan ya aikata mummunan zunubi wa ƙanwarsa shi da ko yaran wasu ma ba ya yiwa kallon banza bare ƙanwarsa, wallahi ba shi bane na san bai aikata ba, dan Allah ka ci gaba da kulawa da ƙanwarmu kai ma Allah zai baka lada idan ka yi hakan, yanzu gashi Jannah ko magana ba ya yi ko idanunsa ya kasa buɗewa so suke su kasheshi da baƙin ciki kawai”

 

 

(fejin yau fa sai haƙuri dan ya taɓa min zuciya sosai, Allah ka karemu da sharrin zuciya da son duniya)

Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/11, 11:02 AM] INDO CE: *D-YARO*
31

“Allah ba zai ba su damar hakan ba”
Alamee ya faɗa ya na kuka.
Har aka raka Aba gidansa na gaskiya Jannah bai cewa kowa komai ba.
misalin ƙarfe 02:00am, zamewa ya yi daga tsayuwar zuwa zama ya jingina bayansa a jikin bango, wani mugun yawu me ɗaci ya haɗiye tare da tanƙwara ƙafarsa wadda yake jin kamar ba ta shi ba har ta fara kumbura sabi da tsayuwar da yake ya kasa zama, har Fatima ta gama ƙwanƙwasa ƙofar ta tafi bai ƙara wani motsin ba.

Cikin kuka Fatima ta koma wajen Ummi ta na sanar da ita tinda ya shiga ɗaki ya kulle ya ƙi buɗe ƙofar, Haƙuri kawai Ummi ta bata dan kuwa ba abin da za ta iya yi wanda ya wuce wannan tasan ba zai iya buɗewa ba, haka Fatima ta ci gaba da rusar kuka har zuwa lokacin da bacci ya kwasheta.
Jannah kuwa a wannan zaunen da ya yi ya kwana idanunsa ƙaƙau in banda yaji da raɗaɗi gami da zugi ba abin da suke yi, sai da asbah ta fara kawo kai iska ta fara kaɗawa a lokacin ya ji idanunsa sun fara kawo ruwa zuciyarsa ta raunana, numfashi ya ja wanda sauke shi ya yi dai-dai da fitowar wani azababben kuka me cike da abubuwa na ban tausayi, “Abana me yasa ka zaɓi tafiya ka barni? waye zai zamo min jigo da ka tafi Abana? kai kaɗai ne za ka iya gayawa duniya ba zan iya aikata abin da take tuhuma ta akai ba, wayyo Allahna Aba ka dawo gareni da ma idan an mutu ana dawowa Aba”
Sambatu ya shiga yi cikin fitar hankali da nutsuwa.
kiraye kirayen sallah da aka fara yi ne ya sa ya rarrafa zuwa banɗaki, ruwa ya sakarwa kansa har wani lokaci kafin ya ɗauro alwala.

Washe-gari tin safe Su Sultan su ka iso da Police don a kama Jannah aje a tuhumeshi, haka su na ji su na gani aka tafi da shi,
ba irin kuka da magiyar da Ummi da Fatima da Umma Zaliha ƙanwar Aba ba su yi ba akan a ƙyaleshi sai bayan an yi uku amma su ka ƙi haka suka tasa ƙeyarsa.

Zuhra ta ci kukan har ta gaji ta dena sabi da galabaitar da ta yi, kamar wadda aka zarewa laka take tafiya tana ratsa mutane har ta isa ɗakin Ummi, itama ta yi kukan har hawaye sun dena fitowa sai kukan zuciya wanda ya fi na zahiri ciwo da ƙuna, a gaban Ummi Zuhra ta durƙusa cikin disashshiyar murya ta ce “Ummi!..”
Kallonta Ummi ta yi a take ta ji wani sabon kukan ya tawo, lumshe ido ta yi kafin ta ce “Zuhra rayuwar Jannah ta na cikin haɗari, bai saurare ki ba a lokacin da yake tsaka da gudanar da rayuwar da ta dace yanzu dan ya faɗa wani iftila’i ba zai zalumce ki ba, ki je ki gudanar da rayuwarki me kyau kuma cikin farin ciki, ba ni da tabbacin ɗana zai rayu yanzu na san hukuncin kisa za’a yanke masa kema ki guje shi kamar yadda duniya ta guje shi take zagin shi dan Allah ki fita sabgarsa kar ki ɓata goben rayuwarki”
hawaye ne suka wanke mata fuska cikin rawar murya ta ce “ban damu da hakan….”
Ummi ta ɗaga mata hannu gami da cewa “dan Allah, na haɗa ki da Allah ki fita daga rayuwar ɗana”
Miƙewa Zuhra ta yi tana tangaɗi ta fice daga gidan, sai da ta shiga mota sannan kuka me ƙarfi ya samu damar kufce mata.
Lambar Sufee ta shiga laluba cikin sa’a ya ɗauka ya yi sallama wadda take baiyana laushin da yayi da alama ya na cikin damuwa”
Cikin shashshekar kuka ta ce “Sufyan Ido za ku zubawa ɗan uwanku ku na kallo ana zalumtar shi??, anya kuwa hakan adalci ne? me yasa ba za mu yi tsayin daka wajen fito da gaskiyarsa ba?”
Sufee ya share ƙwallah sannan ya ce “gani nake kamar ba za mu iya yin komai ba Zuhra don maƙiya sun riga sun shirya mana ta ko wace siga sun kulle hanyar da gaskiya za ta baiyana sun yi hoton shaida sannan kuma sun yi masa sharrin yi wa Jannati fyaɗe muna sa ran idan ta farko za mu ji gaskiya sai gashi ta farka ba a haiyacinta ba ta manta rayuwar da ta yi ma a baya, sai yanzu da hakan ta faru muke ta ganin maƙiyanmu suna baiyana kai duniya abin tsoro ce a cikin abokansa wanda ya yarda da su ma akwai waƴanda su ke farin ciki da faruwar haka, muna tare da mutum ba mu san irin halinsa ba duniya ta lalace yanzu son zuciya ya yi yawa a cikinmu, ba abin da Jannah ya yi wa wani ɗan adam idan ba alkairi ba amma a hakan aka tsaneshi. Zuciyata ta karaya na riga na gaza Zuhra ji nake kamar ba za mu iya yin komai akai ba”
Zuhra ta share ƙwalla cikin fusatar zuci ta ce “ka bani kunya Sufee na yi tunanin ka na dakakkiyar zuciyar da za ka tinkari ko wane ƙalu-balen rayuwa sai gashi tin kafin a je ko ina ka kasa, to ni yanzu na fara ko da kuwa Jannah ba zai taɓa kallona da mutunci ba zan yi komai domin na fito dashi daga zargin da duniya take masa ko da hakan zai yi sanadiyar rasa raina, bazan taɓa ƙyalewa ina kallo a ci zarafin gaskiya a wulaƙanta wanda bai san komai ba, ka tuna fa mahaifinsa aka kashe masa sannan aka lalata rayuwar ƙanwarsa yanzu gashi an jefa shi cikin masifa da sharri, a’ahh idan na ƙyale hakan ta ci gaba da faruwa to fa rayuwata ba ta da amfani, zan yi yaƙi da iyakar ƙarfina har zuwa numfashina na ƙarshe”
Cikin jin daɗin maganarta ya ce “na ji ƙwarin guiwa sosai da maganarki nima zan yi yaƙin ƙwatar ƴanci, ki gaya min ta inda za mu fara”
Ta ce “ba sun ce shari’a za su yi da shi ba??, mu ma shari’ar za mu yi da su, mu tsaya mu fafata kar mu gaji har lokacin da Allah zai kawo mana ƙarshen ƙarya”
Suffee ya ce “yanzu a shirye nake ko yanzu a fara”
da haka su ka yi sallama sannan ta kama hanyar komawa gida.

a rana ta uku Abi ya yi ƙoƙarin da ya yi aka dawo da Jannah gida kafin lokacin da za’a fara shari’a.
Duk ya rame ya yi baƙi ya ƙojale ya koma kamar mahaukaci ko wani zautacce, halin da yake ciki bai hana shi tambayar Zeety ba Fatima da Umma Zaliha kuwa ba su ɓoye masa komai ba su ka sanar masa ba ta taɓa leƙo su ba tin da abin ya faru ko da sunan gaisuwa.

Bayan kwana goma.

gidan ya rage da ga su sai halinsu, Natee ta ji sauƙi an dawo da ita gida sai dai Fatima ta ƙara rikicewa lokaci zuwa lokaci abin yakan ɗan motsa, kullum cikin jimami gami da zullumi suke, Jannah kuwa kullum ba fashi sai ya ci kuka ya gode Allah, Addu’a Ummi ta ke yi ka’in da na’in domin nema masa mafita.

su na zaune sun yi jigum jigum kamar kullum, Fauza ce ta yi sallama ta haɗe cikin wata muguwar shiga ta rashin ɗa’a fuskarta ɗauke da murmushi.
Duk ido su ka sa mata har ta ƙaraso, Jannah ya ce “lafiya kuwa?”
Ta ce “a gurina lafiya ce amma kai ba lallai ya zamo maka lafiya ba, Hajiya ce take son yin magana da kai”
Ba tare da ya jira komai ba ya tashi tare da cewa “mu je”
Ummi da tsoro ya kamata ta ce “a’a Jannah kar ka je yanzu kai ne kaɗai bangonmu ba na son wani abu ya sameka”
ya ce “in sha Allah ba komai Ummi”
Rausayar da kai ta yi gami da cewa “Allah ya sa”

kamar yadda su ka saba haɗuwa yau ma sun cika falon kowa da ido yake bin Jannah da yake tsakiyarsu. Hajiya Murja ce ta ce “nemi guri ka zauna magana za mu yi da kai akan haƙƙinmu”
Bomboi ya ce “zauna mana haba marigayi, kai fa yanzu ka mutu hukuncin rataya za’a yanke maka”
Haisam ya ce “ni wallahi ba ma rataya ba so nake a ƙonashi da ranshi har sai ya mutu”
Hajiya Saratu ce ta katse su da cewa “ya isa ku bari mu yi abin da ya tara mu mana, kai Muftahu magana ce akan dukiyoyin Alhaji muna buƙatar a raba a sallami kowa, sannan idan ka na da wani fata na ƙarshe ka sanar mana ko za mu yi maka kafin rai ya yi halinsa”
“Fatimata ba ta yi muku komai ba, hasalima ta dalilina ku ka santa dan haka ko me za ku yi mata ni za ku yiwa ita ba ta da laifi, ina so ku janye wannan ƙazamin shirin naku akanta sannan ɗan da ke cikinta ina so ya zo duniya lafiya, sannan ƙanwata Ummina da ƴan uwana su rayu cikin farin ciki wannan shine fatana na ƙarshe, dukiyarmu kuma ba ta hannuna ta na gurin ABI”
a fusace Hisham ya ce “Abin uwarka ɗan iska, ina ruwanmu da wani Abi a hannunka mu ka santa kuma sai ka fito da ita, dan ka raina mana hankali sai ka ɗauka ka bashi sai kace karensa ne ya kama?”
ya ce “malam ba ni na bashi ba wanda ku ka kashe ne ya bashi tin kafin ku kashe shi, idan kuna buƙata sai kuje gurinsa idan ya yi niya sai ya baku”
Hajiya Saratu ta ce “hmmm! lallai ma wannan mutumin, wato duk inda muke tunanin ya kai ashe ya wuce, mun yi niyar jifan tsuntau biyu da dutse ɗaya amma sai gashi ɗaya mu ka samu, amma ai tarkonmu ya yi babban kamu, ka je kawai za ka gani ne ganin idonka ai ka riga ka shiga hannu yanzu ba na ta taka”
Hajiya Murja ta ce “sannan kar ka manta gobe ne za mu shiga kotu sai ka nemi hujjojin kare kanka”
Zuciyarsa na bugawa ya fita daga sashin nasu, gudun kar ya koma wajen Ummi a yanzu ya sa ya yi hanyar fita waje.
wajen me gadi ya nemi guri ya zauna ya dafe kai.
Me gadi kuwa kallonsa kawai yake yi.
Suna nan zaune Zeety ta shigo kamar an jefota, cikin sauri ya miƙe ya na kallonta cike da tunani daban daban har ta ƙaraso inda yake ta tsaya. kara tsaye ta ce “ya haƙuri? Allah ya yi masa rahma, na makara wajen zuwa gaisuwa ina da muhimman abubuwa ne shiyasa ban zo ba, bayan wannan bayanin kuma ina me baka haƙuri a bisa wanda zan ƙara kawo maka, kasancewar kai yanzu rayuwarka ma ba ta da tabbas ya sa na yanke hukuncin da nake ganin shine dai-dai da ni, ci gaba da soyayya da kai tamkar ci gaba da birne kaina ne dan haka yanzu ba ni ba kai na haƙura da soyayyarka ka je ka ji da abin da yake gabanka, wanda har zai iya kashe mahaifinsa ai kuwa babu amfanin ci gaba da biye masa”
kai kawo ya shiga yi A wajen Kamar zautacce cikin kiɗima ya ce “kar ki min haka Zeety wallahi ban aikata ba na zata kin fi kowa sanin ba zan iya ba Zeety wallahi ba ni bane kar ki rabu da n…”
Katse shi ta yi da cewa, “ya isa haka!! ba na son ƙara jin muryarka. ko da na san ba kai ne ka aikata ba amma kasan dai yanzu babu daula a hannunka komai ya rushe maka duk wani gata da kuɗi yanzu ya ƙare ni kuma maganar gaskiya idan ba ka da duk wannan me zan amfana a tare da kai?? shi yasa na canja sheƙa zan je na nemi ɗan gata me ji da kai da kuma kuɗi wanda damarsa take hannunsa ya ke juya duniyarsa a tafin hannunsa ba irin kai da ta gama ƙarewa ba ka je ka nemi wadda za ta iya soyayya da kai nima na nemi dai-dai da ni ina fatan ka fahimta”
Cakkk ya tsaya ya na kallonta baki buɗe sai yanzu ya gane inda jirginta ya sauka, cikin tsananin mamaki ya ce “Zeety ki na nufin ba ki taɓa sona da gaskiyarki ba???”
Ta yi murmushi sannan ta ce “ni ba irin matan nan ne da suke mutuwa akan wani ɗa namiji ba hasalima ni tamkar riga na ɗauki soyayya idan ta raya min in saka idan ta raya in cire, kai ne dai ka yi asarar son gaskiya na domin Allah, wadda kake cin zarafinta a kaina wannan itace irin matan da suke sadaukar da rayuwarsu akan wanda su ke so. na barka lafiya”
daga haka ta fice ba tare da ta ƙara waiwa-yensa ba.
Tafiya yake amma sam baya sanin inda ƙafarsa take takawa sabi da idanunsa sun rufe duhu duhu kawai yake gani ga kansa na wani irin sarawa da juyi jikinsa duk rawa yake, da lalube ya koma sashin su, cikin Sauri Fatima ta miƙe ta riƙo hannunsa ta na tambayar lafiyarsa, da kyar ya ce “kai ni gurin Umminahh!!!”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/13, 11:34 AM] INDO CE: *D-YARO*
32

Kamar wanda bai san hanyar ɗakin Ummin ba haka yake binta zungui-zungui, sai da ta kaishi sannan ta fito daga ɗakin ta koma nasu, ta na shiga ta faɗa kan gado gami da fashewa da kuka.

tsayawa ya yi ya na kallon Ummi wadda take fama da Jannati akan ta ci Abinci, ganinsa cikin wani yanayi ne ya sa Zuciyar Ummi ta ƙara karyewa, cikin rawar murya ta ce “Allah ne kaɗai ya san nufin da yasa su ka nemeka, yanzu gashi ka dawo ba daɗi ban san me yasa har yanzu ka kasa gane matsayinka a gurinsu ba, ka zo ka zauna ka huta Allah zai kawo mana ɗauki”
Ya Ƙarasa ya durƙusa akan guiwoyinsa runtse ido ya yi yana girgiza kansa da yake jin kamar zai tsage sabi da ciwo, cikin murya me nuna zugin da zuciyarsa ta ke yi ya ce “Ummina ashe dama haka duniya take??? me yasa mutanen cikinta su ka kasance haka Ummi? son zuciya rashin imani da tausayi ga rashin tsoron Allah, ban-san halin duniya ba sai a wannan lokacin da ta juya mun baya, da ba abin da na sani sai ku iyayena da ƴan uwana sai tarin abokai da kuma wasanni komai na rayuwata a ƙidaye yake ba na shiga sabgar kowa amma duniya ta damu da ni ba dan tana ƙaunata ba, Ummi ban taɓa tunanin hakan ba Idan gaya min aka yi bazan taɓa yarda ba ko a munanan mafarkan da nake ban taɓa yin wanda zai faɗa min Zeety za ta yaudareni ba, na san kema shaida ce akan irin son da nake mata Ummina amma yau ta gaya min ba ta taɓa so na ba duk don son duniya take nuna min ƙauna, anya kuwa Zeety Musulma ce? ba ta ji tausayina ba ba ta yi tunanin halin da za ta jefani ba haka ta gujeni ta juya min baya, tabbas ni mahaukaci ne kuma mutum mara amfani na tafka kuskure da na yarda da ita na riga na mutu akanta gashi yanzu ta ƙara kasheni, ta juya min baya sabi da wani tsautsayi ya faru da ni”
ba dan ya gama surutun ba Ummi ta dakatar da shi da cewa “ya isa Jannah kai ta yiwa amma ta yuwu na fika jin zafin don ni na haifeka amma abin da nake so da kai ka manta da labarinta ka ƙaddara ma ba’a taɓa yinta a duniya ba kar ka illata kanka sabi da wata bara-gurbi, ka sa a ranka hakan Alkairi ne garemu tin kafin ta zamo wani tsagi na cikinmu Allah ya nuna mana halinta kuma ta rabu da mu, yanzu ka yi tunani in da ace ta kasance kamar Fatima sannan kuma ta gujemu ba ka jin abin zai fi ciwo?, to idan ka yi duba da cewar wani hanin daga Allah baiwa ne sai ka gode masa, Muftahu ka barta da halinta, ka yi duba zuwa gareka kai da ba ka aikata komai na kuskure ba gashi duniya ta na zaginka bare ita da ta ɗibar wa kanta alhakin wasu ka ga lokacin da duniyar za ta yi mata juyin juya hali za ta fahimci gaskiya da akasinta, ko da yaushe cikin roƙa maka sauƙi da sassauci nake a gurin Allah duk da cewar muna cikin matsala ina so ka daure ka cigaba da rayuwa tare da walwala, kar ka bari maƙiya su gane lagonka ka ji ko?”
gyaɗa mata kai ya yi alamar ya ji.
ci gaba ta yi da lallaɓa shi tare da nasihu masu sanya nutsuwa da ratsa Zuciyar duk wani shiryayyen ɗan adam.

yau ta kasance ranar shiga kotu.
mafi yawa daga cikin mutane sun bada hankali da nutsuwarsu wajen jin yadda shari’ar za ta kaya, daga kan masu zuwa kallo zuwa masu tsumayin labarin a yanar gizo da masu saurara a Radio duk a shirye suke.

Bayan Alƙali ya nemi waɗanda sukai ƙara da su gabatar da bayaninsu suka gabatar sannan wanda ake tuhuma.
Bai iya cewa komai ba sai tsabar kuka kawai da yake yi,
Br Shamsuddin Lauyan su Hajiya Saratu ya ce “Ya me shari’a ina neman alfarma a gurin kotu da ta yi duba ga irin ƙwararan hujjojin da muka kawo wanda su ka tabbatar da gaskiyarmu a yanke masa hukunci dai-dai da laifinsa”
Me Shari’a ya ce “ba za’a yanke masa hukunci a bisa laifin da bai amsa ba”
Da ga haka ya ce ya ɗaga Shari’ar zuwa wani lokaci.

Kwata-kwata hakan bai yi musu daɗi ba, a zatonsu da hujjojin da suka bayar kawai hukunci za a yanke masa.
Da kyar ya iya hamɓare tambayoyin da ƴan jaridu su ke yi masa, da temakon su Alamee Sufi Zuhair da Abubakar ya shiga mota, Alamee ne ya ce “Zuhair ka tuƙa wannan motar ni kuma zan tawo da su Yaya Fa’iza”
Zuhair ya ce “in sha Allah, ka kula aboki kuma ku samu ku fito daga rintsin nan lafiya”
Kwata-kwata bai ji motsin mutum ba har sai da ta kira sunansa, dakatar da kukan ya yi ya tsura mata duk da ba komai yake ganewa ba amma ya gane yadda idanunta suka yi jajir daga kan fatar waje har cikin ƙwayar idon nata da alama itama aikin kuka take yi, kamar wanda aka tsikara ya yi saurin buɗe murfin motar ya sa ƙafarsa a waje da nufin fita, cikin zafin nama ta riƙo hannunsa jiki na rawa, cikin muryar kuka ta ce “ka samu nutsuwa Jannah ni ya kamata in fita ba kai ba ka zauna domin kuwa komai zai iya faruwa”
Zuhair ya ce “e ta faɗi gaskiya Jannah dan Allah ka zauna sai dai ni ban goyi bayan itama ta fita ba, ban san sai yaushe zaka fara haɗa inuwa da Zuhra ba kuma bansan laifin da ta yi maka ba”
Komawa ya yi ya zauna ya na jan ajiyar zuciya, cikin disasshiyar murya ya ce “mu tafi Zuhair ka cewa Abubakar ya je gida ya ɗauki Ummi ya mai da ita gidan da na saya zamanta a nan akwai matsala”
Zuhair ya ce “shi kenan, amma dan Allah ka dena nunawa baiwar Allahn nan kyara, yanzu ba maganar sonka ce ta kawota ba ta na ɗaya daga cikin mutanen da suke da burin ganin ka fita daga cikin wannan cakwakiyar yanzu ta shigo cikinmu wato rukunin abokanka kuma masu ƙaunarka, idan ka so za ka barta a matsayinta na abokiyarmu idan ba ka so hakan ba za ka iya ɗaukaka matsayinta ya fi namu”
shiru ya yi ba tare da ya yi magana akan abin da Zuhair ɗin ya faɗa ba.

Ɗan madai-daicin gida ne ba wani babba ba sai dai an tsara shi ya yi gwanin burgewa.
a falo Zuhra ta nemi guri ta zauna shi kuwa ya wuce cikin ɗaki.
Kallon Zuhair ta yi cikin damu “Zuhair ya akai ma mu ka yi tunanin Jan.. zai iya magana da kanshi? ka ga fa da tuni sun yi nasara tashin farko, abin yi nan gaba shine neman ƙwararren Lauyan da zai iya wannan shari’ar bayan wannan matakin sai na addu’a ya zama wajibi mu dage tuƙuru wajen yin addu’a da neman temakon Allah mu yi da kanmu kuma mu sa ayi mana sannan mu ƙara yawaita sadaƙa ninkin wadda muke yi a da, sannan ina ganin ku yi magana da Abi mu ji ta bakinsa”
Dai-dai lokacin Ukasha da Yazid su ka yi sallama, Zuhair ya amsa, bayan sun zauna Zuhair ya ce “muna magana ne akan ta yadda za mu sha kan zama na gaba gashi ba mu da ƙwaƙƙwarar hujjar da za ta gwada gaskiyarmu”
Ukasha “Gaskiya!!! ita ce babbar hujjarmu ko da an fi ƙarfinmu gaskiyarmu za ta ce-cemu”
Yazid “wannan gaskiya ne”
“miƙewa Zuhra ta yi tare da cewa “zan wuce gida Dan Allah ku kula da Jannah sosai ya na cikin maƙurar damuwa kar ku barshi da kewa dan Allah”
Yazid ya ce ‘in sha Allah za mu ƙoƙarta”
Ukasha “Maza ka rakata Yazid idan ka kai ta sai ka dawo”
Tashi ya yi gami da cewa “to”

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya.
su Zuhra sun dage sosai wajen zaƙulo duk wani abin da ya kamata kuma suna iya ƙoƙarinsu don sanya shi walwala da mantar dashi damuwarsa.
a ɓangaren su Hajiya Saratu ma ba banza su kai ba asire-asire da tuggu kala kala suke haɗawa duk abin da zai yi musu dai-dai sun haɗa sun shirya tsaf ko yanzu a ci gaba da shari’a.

a falon ƙasa yake zaune shi kaɗai ƙwatal idanunsa a lumshe ya kashingiɗa a hannun kujera, da sallama ta shigo falon tare da nufo inda yake cikin sanɗa, gyara zama ya yi cikin haɗe fuska ya ce “Me yasa bakya jin magana ne??”
“ba wai ji ne ba na yi ba, a duk lokacin da ka faɗa ina ji sai dai matakin da ka ɗauka ya yi min tsaurin da ko na ji maganarka ba zan iya aiki da ita ba, yanzu ba wannan ba, ka sha maganinka kuwa yau? ka na yawan ciwon kai fa kuma kasan ya na muguwar illah sannan Yaya Hassana ta gaya min a koda yaushe ta na lure da karsashinka ya na raguwa ga zazzaɓin nan da ka ke yi kana buƙatar kulawa sosai fa”
“ina da wanda za su kula da ni ba sai kin shiga lamarin ba ina da mata ina da mahaifiya ga abokaina da ƴan uwana kin ga ba huruminki anan”
“ni nake da hurumi kuwa bawan Allah, ina ɗaya daga cikin Abokanka sannan ni Ƙanwarka ce kuma ni ƴar uwa ce kuma likitar da za ta dinga duba motsinka ka ga kusan wuni da kwananka ma ni ya kamata in kula da su, kuma ko za ka ci gaba da wulaƙanta ni ba zan dena ba ka sha maganin ne ko sai na ɗura maka??”
Gyaɗa kai ya yi alamar “e”
zama ta yi dam-fam-fam ta ciro wayarta ta fara dannawa.
girgiza kai ya yi kamar wanda ake ce ya yi magana dole ya ce “ke fa ƴa macece”
Tsare shi da ido ta yi gami da cewa “sai me??”
“bai kamata ki shiga rayuwar wanda ta sanadinsa hawayenki su ka daɗe suna zuba ba yanzu ma ba abin da zai iya anfana miki sai ƙunci da shiga matsala, bayan wannan ta faru da ni maganar gaskiya na ƙi saurararki ne sabi da kar baƙin jinina ya ɓata ki, ki na da kyakkyawar zuciya bai kamata na lalata rayuwarki ta hanyar saurararki ba kuma ko ba komai lokacin da ki ke bina akan na saurareki na ture na ƙi na rufe ido na sa ki cikin damuwa yanzu kuma dan duniya ta gujeni sai na saurareki sabi da son zuciya bazan iya yin hakan ba, bazan fasa faɗe ba Zuhra dan Allah ki ƙyaleni ki je ki rungumi ƙaddararki a yadda ta zo miki”
ƴar dariya ta yi kafin ta ce “ba ƙaddara ka ce ba? ina ganin kaine ƙaddarata don kuwa bani da wani haufi sai kai ya ka kwana ya ka tashi ko da yaushe shi ne abin damuwata, a haka ƙaddarar ta zo min dan haka na tungumeta hannu bibbiyu dan ba zaka so ni ba ba wai yana nufin ƙaddarata ta sauya bane a hakan dai take na so ka ba dan ka so ni ba kuma na damu da kai ba dan ka damu dani ba wannan shine tsarin”
Zai yi magana ta yi saurin ƙatse shi da cewa “ina ganin fa yau ko abinci ba ka ci ba, ko shayin ma ba za ka sha ba?? to faɗa min me ka ke so zan yi maka yanzu sannan ka gaya min mene ne ya ke sanya ka farin ciki?”
“Zuhra yau ɗaya ki saurare ni kuma ki yi aiki da abin da zan faɗa miki, a cikin rayuwata babu farin ciki ko walwala a yanzu, matata ma wani lokacin idan ta ganni kamar ta ga dodo sai ta dinga firgita ƙanwata kuma idan ta ganni sai dai ido tsakanina da ita, ta zama ba me hankali ba kuma bansan ranar da za ta dawo dai-da ba Fatima yanzu ba ta yarda ta zo inda nake ta ma dena kwana a kusa dani ta koma ɗakin Ummi sai idan sun yi bacci nake zuwa na yi shimfiɗa a ƙofar ɗakin domin na dinga gadinsu dan duk su biyun ba a hayyacinsu suke ba idan suka turnuƙe kuma Ummina ba lallai ta iya da su ita kaɗai ba”
da sauri Zuhra ta ce “yauwa anzo wajen tin da haka ne to in dawo gidan da kwana mana!!”
Waro ido ya yi akanta bai san lokacin da ƴar dariya ta suɓuce masa ba, tagumi ta zuba gami da buɗe idanunta tana kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi, ta daɗe ba ta ga ko murmushinsa ba bare dariya hakan ya sa ta ganshi kamar sabon gani yadda murmushi ya buwaya a fuskarsa kuwa har rai ta ji sanyi yana ratsata, za ta iya cewa yau ne karon farko da ya yi dariya ta dalilinta. kallon ido cikin ido su ke yi wa juna ba tare da sun ankare ba, kamar daga sama wata magana da Natiee ta taɓa faɗa masa ta dawo cikin tunaninsa, ”ƙwayar idon ku ma iri ɗaya ce”
Rasss ya ji zuciyarsa ta buga a ɗan ruɗe ya ce “gaskiya ne!!! to amma me yasa haka? komai da komai kuma iri ɗaya”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/14, 9:36 AM] INDO CE: *D-YARO*
33

“Me ya faru kuma?”
Ta jefo masa tambayar ba tare da ya shirya ba” girgiza kai ya yi ya ce “a’a ci gaba da surutunki nima zancen zuci nake”
“to ya kamata ka dena barin komai a zuci ka dinga faɗa wa wanda yake kusa da kai, yauwa zan iya dawowa wajen Ummin ko?”
Ya rausayar da kai ya ce “ke fa ba yarinya bace kema ai Zahra ta na buƙatarki a kusa da ita”
“au dama kasan Zahra?”
“ke can da yawarki, kin cika min kunne”
“aikin da likita ya bani kenan na dinga ɗebe maka kewa, a ganina abin da muka rasa ba zai dawo ba idan muna damuwa da ɗorawa kai wata larurar haka kuma damuwa fa ba ta maganin wata damuwar sai dai su haɗu su haifar da cuta, ina ganin ka dinga mantawa”
“to likita na ji”
Cigaba ta yi da zubo masa surutu, jin kansa ya na neman gaza ɗauka ya sa ya ce ta je ta kawo masa abinci kafin ta dawo ya ɗan huta.

Yau lokacin da aka ɗiba na ƙara zaman Kotu ya zagayo.
Lauyan da su ka ɗauka ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo hujjoji da kuma kore ta su hujjar hakan ya sa yau ɗin ma aka gara Shari’ar zuwa wata ɗaya.

Watanni Bakwai aka ɗauka ana fafata Shari’ar ansha gwagwarmaya da ƙalubale iri iri sai dai tasirin Addu’a gami da temakon Allah ya hana su nasara akan Jannah duk zaman da za a yi sai dai a ɗaga Shari’ar.

Zagaye Hajiya Saratu ta ke yi a falon Ummi na da wanda yanzu ta mallekeshi, alamun ɓacin rai da damuwa gami da kuntu-kuntu da ƙulle-ƙulle duk sun baiyana a tattare da ita, Bomboi da ya kashingiɗa ya na kallonta ya ce “mun gamu da tamu ƙaddarar Hajiya yaro ya ƙi mutuwa kuma mun gaza nasara akan shi wannan wace irin masifa ce?? gashi batun dukiya babu shiru maƙatau ba a ta ta-ta ma gashi haƙar da muke har yau ba mu cimma ruwa ba”
Abdul ne ya ce “tabbacin gaskiya kaifi ɗaya ce kenan, na rasa ina imaninku ya tafi da ku ka yarda da komai sabi da duniya gashi kullum ci gaba yake ku kuna ta wahalarku, mutane ma da suke zaginsa yanzu sun koma suna karɓar tallafi da temakon da yake musu kamfanu-nuwansu kullum gaba su ke yi, ku ci gaba da kwance kwance ku za ku ga kwance”
Hajiya Saratu ta ce”Abdul!! tashi ka koma sashin uwarka tin da magan-ganun banza za ka gaya mana”
“Allah ya baki haƙuri”
Daga haka ya bar mata falon.
Ta maida kallonta kan Bomboi ta ce “kai ɗana ne na san za ka gane irin raɗaɗin da nake ji, mu yi ƙoƙari a zaman nan ko ta hanyar barazana ne mu kawo ƙarshen shari’ar a yanke masa hukuncin kisa”
“me ya kamata mu yi Hajiya Babba??”
“ku sace wani madan-gancin Alƙalin sannan ku yi barazana ga rayuwarsa akan ya yi abin da ku ke so, wai shi me tsauri mutum nawa muka sa aka yiwa canjin gurin aiki bare shi karan-kaɗa kwata? dashi da gaskiyar ta shi za mu haɗa mu hamɓare, ku yi aikin cikin hikima kamar yadda ku ka saba, kar ku bar shaida ko alamar da za ta sa a gane ku kunsan ƴaƴan manya za ku taɓa yanzu kar bincike ya biyo ta kanku, ka gane?? lallai ka yi musu bayani yadda za su fahimta nima zan zauna da su, sannan idan fa mun ci nasara kar ku bari fa waccan Ballagazar ta samu wani abu so nake komai ya zamto daga ni sai ƴa-ƴana amfani kawai nake da ita”
Bomboi ya ce “na fahimci komai Hajiya Babba Ki yi shagalinki kawai kamar an gama ne”
Ta saki wani shu’umin murmushi.

Hajiya Saratu, kallon Fauza ta yi ta ce “ina ganin Shari’a ta kusa ƙarewa dan haka yanzu ɗamba za mu yi mu shirya yadda za mu samu komai daga ni sai ku, Ita ta na ta haukanta ba ta san ba ƙaunarta nake ba kawai dan dai ta fini hatsabiban ƴa-ƴa ne yasa nake amfani da damata dan cikar muradina, to yanzu an zo gaɓa wajibi ne mu kula”
Fauza ta ce “wannan haka yake Mommy ki kwantar da hankalinki ai ba a Sarki biyu a fada ɗaya dolenta ta bar miki komai”
Hajiya Saratu ta shaƙata da murmushi kafin ta ce “yanzu ina tsumayinta dan na ji da me ta zo mana dan na san babban shiri za ta yi kuma za mu karɓa hannu biyu”
Fauza ta ce “ni ma dai na ƙagu in ji me za ta yi”
“ai za mu gani”
Hajiya Saratu ta faɗa tana wani yauƙi cikin shauƙin burinta ya kusan cika”

Abi, Ummi, Yaya Fa’iza, Yaya Hassana, Yaya Husaina, Fatima, Natee, Jannah, Yazid, Ukasha,
Zaune suke su na tattaunawa akan abin da ya shafesu, Abi ya ce “Yarinyar nan Zuhra ba ƙaramin ƙoƙari ta ke yi akan ɗanmu ba sai dai mu ce Allah ya saka mata da Alkairi”
Cikin fara’a Ummi ta ce “wannan haka yake godiyar ma ban san wace iri ya kamata in yi ba amma sai na ga yana da kyau ma mu yi tattaki zuwa gidan iyayenta mu yi musu godiya mu jaddada farin cikinmu garesu ko dan su san mu na jin daɗin abin da su ke mana”
“Alhamdulillahi wallahi Ummi nima so nake ki rufe baki na gaya muku hakan”
Yaya Fa’iza ta faɗa cikin nuna farin ciki.
Abi ya ce “to kuwa tin da haka ne duk ya kamata mu shirya mu je mu gana da su mu yi musu zuwan bazata ko??”
Ukasha ya ce “bazata kuma Abi mu gaya musu za mu zo dai”
Abi ya ce “amma kwatsam idan mu ka ce zamu zo ai ka ga mun yi musu bazata ko? ba ina mufin sai dai su ganmu kawai ba, ka san dai ko a yanzu ba za su yi tsammanin za mu je ba ko?”
Yaya Husaina ta ce “mugun ɗan yawa ne fa yaron nan Abi, in banda ƙuruciya ga abin da ake nufi amma shi wanda yake nufi daban”
Janyo kular abinci ya yi ya fara zubawa a filet cikin ko in kula ya ce “ni dai kwanona yaren ci kawai zan gane yanzu”
Su ka yi dariya kafin Yazid ya ce “Jannah shirun me ka yi ne wai? ka na da damuwa fa amma ba ka son faɗe”
Murmushin ƙarfin hali ya yi gami da cewa “ina jinku Yazid kawai ban-san me zance bane”
Yaya Fa’iza ta ce “damuwa kuwa shi ta kama Matarsa fa tsohon ciki gareta Kuma lamarinta sai Addu’a kawai ni ina tsoron ma kar su jawo mata matsala wajen Haihuwa”
Ummi ta ce “Allah zai kiyaye ai muna ta neman temakonsa kuma ita Addu’a ba ta faɗuwa ƙasa banza”
Ukasha ya ce “ga Natee ma ta dawo yarinya kalli dai yadda take rungume da Teddyn nan kamar wata ƴar gaske haka za ka ji ta na yi wa Teddys hira kamar da mutane take”
Abi ya ce “Allah i yaye mata shine fatanmu, yanzu duk ba wannan ba kun ga lokacin shiga Kotu ya kusa saura kwana Uku mu ƙara tsananta Addu’a, zan yi magana da Lauyan namu Zuwa Anjima Allah ya bamu nasara”
Jannah kamar zai yi kuka ya ce “Abi ni ban-san ya tayaya hakan ta faru ba kawai an kira ni an ce naje wata unguwa zan tsinci gawar Jannati idan na ɓata lokaci ma ko gawarta ba zan samu gani ba, cikin tashin hankali na nufi Uguwar na bi inda su ka ce na bi kuma na duba amma ban sameta ba, hankalina ya kai ƙololuwar tashi sai ga wani kiran wai Abana zai mutu, haka akai ta yi min wasa da hankali har na kasa gane me yake shirin faruwa da ni”
Da sauri Yazid ya ce “kana nufin ba ka san su waye ma su ka aikata ba????”
Ido duk suka zuba masa cikin son jin amsa dan kuwa duk cikinsu har yau ba wanda ya san gaskiyar abin da ya faru,
Jimmm ya yi ya na Nazari kafin ya rausayar da kai cikin karyewar Zuciya ya ce “wannan dalilin ne ma ya sa na yanke hukuncin karɓar laifin a wannan zaman, ban-san ko su waye ba an rarraba hankalina ne ta yadda ba zan iya fahimta ba ina tsakiya ne su kuma suna gefe da gefe ɓangare ɗaya Nati ɓangare ɗaya Abana, shin Mutum ɗaya ne?? daban-daban ne?? wanene? me yasa su ka aikata? duk ba ni da waƴannan amsoshin dan haka ba zan yi nasara akan ƴan uwana ba su akan gaskiyarsu suke dole ne su ɗau fansar ran mahaifinsu, komai daren daɗewa da duk tsawon da Shari’a ta yi a ƙarshe ni ne mara gaskiya dole kisa ya rataya a wuyana”
Ya ƙarasa maganar cikin tsananin raunin zuciya gami da ƙunci da tausayin kansa da waƴanda zai bari idan an kashe shi”
Shiru gurin ya yi kowa ya shiga duniyar tunani, Fatima ce ta katse shirun da cewa “ai biri ya yi kama da mutum da alamu kaine ka aikata komai, dama in ba kai ɗin ba waye zai yi?”
Idanunsa da suka cicciko taf da hawaye ya zuba mata kafin ya ce “ba zan ji komai ba dan kun faɗi haka, ƴan Uwana ma tuhuma ta suke bare ku da ba jinsin mutane ba”
ta fashe da wata mahaukaciyar dariya irin ta Jinnu, cike da mugunta ta ce “oho ina ruwana ni dai aikina shine hana matarka zaman lafiya kuma yau zan sakota daga saman bene ta faɗo su mutu ita da ɗan nata”
Cikin ɓacin rai Ukasha ya ce “Azzaluma mara imani ki ji tsoron Allah dan ba ya halicceku bane dan ku dinga zalumtar mutane, kar ki manta ku ma fa kamar mu ku ke Allah ya haliccemu ne dan mu bauta masa mu yi biyayya ga sharuɗan addininmu mu kasance masu adalci da jinƙai da tausayin junanmu, amma da ku Jinnu da Bil Adam ɗin yanzu ɗai-ɗai ne masu tsoron Allah, ina me shawartarki da ki zama adala ki dena cutar da wani sabi da son Zuciya”
wani shegen kallo na baka isa ba ta watsa masa gami da ɗaukar ƙafarta ɗaya ta ɗora akan ɗayar cikin tantiranci da duniyanci ta ce “na ji kalamanka kuma sun ratsa zuciyata kuma fa ba kai ƙarya ba, hhhh amma ka riƙe shawararka ba na buƙata wannan itace rayuwar da na zaɓa kuma ba uban da ya isa ya hanani”
A harzuƙe Yazid ya yunƙuro zai sharara mata mari Jannah ya yi saurin dakatar da shi da cewa “tsaya Yazid!!!! ka barta da halinta kawai akwai ranar da Allah zai yi mana sakaiya”
Ƙara hautsinewa ta yi da dariyar mugunta.
Banza su ka yi mata su ka ci gaba da tattaunawa.

Zuhra, murna da rawar jiki kawai take yi ta kasa zama sai kurin-kurin take yau su Ummi za su zo, ita da Zahra su ka zage su ka haɗa musu lafiyayyen Abinci Bayan sun kammala shirye- shirye su ka zauna jiransu.
kiran Jannah ne ya shigo Wayarta ta yi saurin ɗauka tare da sallama to kawai ta ce gami da miƙewa ta ajiye wayar, kallon Zahra ta yi ta ce ” zo mu shigo da su ciki sun zo”
Zahra ta tashi suka nufi hanyar fita. a falon saukar baƙi a ka sauke su cikin karramawa da mutuntawa.
Bayan sun gaggaisa Mammi ta ce “yana nan shigowa ya ce ku yi haƙuri”
Abi ya ce “ba komai ai idan ma ba mu samu gaisawa ba shi kenan a miƙa masa saƙon gaisuwa da godiyarmu”
Mammi ta ce “za ku gaisa ma In Sha Allahu”
Sallamar Dadin Zuhran ce ta katse musu maganar, Mammi ta ce “ga shi nan ma”

Miƙewar da Ummi ta yi zumbur ne ya dawo da hankalin kowa kanta, hannunta akan ƙirjinta alamar firgici da razani sun baiyana akan fuskarta cikin rawar murya ta furta “A.. Abb.. Abdussalam!!!!!!!!!!”
Alhaji Abdussalam ya waro ido akanta suka shiga yiwa juna kallon mage da ɓera har na ɗan wani lokaci kafin ya ƙaraso inda take tsaye. durƙusawa ya yi akan guiwoyinsa cikin wata raunanniyar murya ya ce “Aaminatu!!”
sai kuma ya haɗe hannunsa guri ɗaya alamar roƙo wasu zafafan hawaye suka wanke masa fuska, da kyar ya ce “Aaminatu ki yafe min dan Allah”
share ƙwallar da ta shararo kan kumatunta ta yi ta ja numfashi kafin ta ce ” Zuhra ɗiyarka ce Yaya Abdussalam??”
Ya gyaɗa kai alamar “e”
Komawa ta yi ta zauna cikin muryar kuka ta ce “hakan ya na nufin ba Aure a Tsakanin Jannah da ita????”
Zamewa ya yi daga kan kujera ya zubo ƙasa sabi da jin maganar da Ummin ta yi ta mugun girgiza Zuciyarsa gami da barazana ga numfashinsa.
Cikin fitar haiyaci ya ce “ina ta mamakin ta yadda akai idona da na Zuhra ya kasance iri ɗaya sakkk sai yanzu na Fahimta Ummi ashe Abana da nake kira kullum ba shine mahaifina ba?? na kasa gane me hakan yake nufi dan Allah ki ganar da ni Ummina”

Cikin son jin amsar tambayoyin Muftahul-Jannah kowannensu ya yi Zuru-zuru da ido yana kallon Ummi da Alhaji Abdussalam wanda har lokacin a durƙushe yake ya na sharɓar kuka.
Zuhra kuwa tin maganar Ummi ta farko kanta ya yi mummunar sarawa ta rintse ido har zuwa lokacin ba ta buɗe ba.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/15, 1:57 PM] INDO CE: *D-YARO*
34

A sanyaye Ummi ta ce “duk yadda ku ka yi zato ba haka bane, ni da Abdussalam ƴan uwan juna ne, tuna labarin ba ya yi min daɗi sam musamman a wannan lokacin, ku tashi mu koma gida, Zuhra Ƴata Allah ya yi miki zaɓi mafi Alkairi”
Jannah kamar zai yi kuka ya ce “Ummi dan Allah!, ko da ni na iya yi miki kyakkyawar Fahimta to fa wasu ba lallai su fahimci inda ki ka dosa ba, don Allah ki gaya mana ko da ba za ta yi mana daɗi ba”
Abi ne ya tari numfashinsa da cewa “Haba Muftahul-jannah ya za ka ce haka? akwai kyakkyawar fahimta tsakaninmu da Aamina ba yadda za’ayi mu yi wani ragon tunani akanta, kuma tsananta tambayoyin nan ba su da amfani”
Numfashi Ummi ta sauke kafin ta ce “zan ma sanar da ku komai amma na so sai mun koma gida tin da ya ce haka to ku saurareni”
Shiru ta ɗan yi kafin ta ci gaba da cewa “ni da Abdussalam ɗan wa da ɗan ƙani muke kamar dai yadda Jannah da su Ukasha suke, sai dai labarin namu ya sha ban-ban kuma labari ne me tsayi amma zan taƙaice shi, kafin Allah ya haɗani da Alhasan mu yi Aure mun so juna sosai ni da Abdussalam, gidanmu Babban Gandu ne a gida ɗaya muka taso kuma cikin shaƙuwa sosai duk da cewar mahaifina da mahaifinsa ba sa jituwa Gaba ce a tsakaninsu tin asalin-asali suka taso da Gaba me zafin gaske kamar ba ciki ɗaya suka fito ba, daga bisani shaƙuwarmu ta koma ƙauna, mun ƙaunaci juna kamar iya rayuwa za mu yi ba mutuwa, da Iyayenmu su ka fahimci mun yi matuƙar shaƙuwa sai suka shiga tsakaninmu, rana ɗaya kawai Mahaifina ya ce zai min Aure da ɗan Abokinsa ni kuma na nuna ba na so, Kakarmu wato Mahaifiyarsu ta yi da gaske ta shawo kansa ya amince sai dai ɗan uwansa wato Mahaifin Abdussalam ya ce bai san zancen ba, juyin duniya ya ƙi amincewa mu ma mun kasa haƙuri da juna kullum cikin damuwa, Abdussalam ya yi min alƙawarin ba zai taɓa rabuwa da ni ba ni kuma na ɗora raina akan faɗarsa da sa ran zai tsaya min a ko da yaushe, kwatsam rana tsaka Abdussalam aka wayi gari babu shi, faruwar hakan ya ƙara Assasasa wannan Gabar ta Iyayenmu, shi mahaifinsa ya ce Babana ne silar ɓatan ɗansa Babana kuma ya ce dama ɗansa watsatstsene haka in da ya bashi ƴa ma zai gudu ya barta ko ya tafi da ita inda ba ta da kowa ya banzatar, wannan rigimar ce ta yi silar rushewar Babban Gandunmu sai ya zamana kowa ya ware ƴa-ƴansa ya yi gefe, Babana da Baba Ƙarami kuwa ko ƴa-ƴansu ba sa yiwa juna magana ko kusa da katangar ɗayansu ba wanda ya ke zuwa har i yanzu da nake nan ina magana, tin ina sa ran wata rana zan ƙara ganin Abdussalam har na dena sai yau da Allah ya tsara gashi mun haɗu, kuma ya na zuwa wajen Alhasan amma Allah bai sa zan ganshi ba sai yau”
Mai da kallonta ta yi kansa ta ce “Yaya Abdussalam soyayya ta yi sanadin tarwatsewar Danginmu gashi yanzu wata soyayyar ta ƙara haɗamu sai dai nasan Iyayenmu ba za su amince ba shiyasa nace babu Aure a tsakanin Ƴa-ƴanmu dan sun riga sun la’anci duk abin da zai haɗa zuri’arsu guri ɗaya”
Alhaji Abdussalam ya goge hawaye kafin ya ce “ba shakka laifina ne, da ban yi ragon azancin tafiya ba da wani abin ya zo da sauƙi, na kasa jurewa kafiyar Mahaifina ne shiyasa na yanke wannan hukuncin don sama miki nutsuwa nasan in kina ganina ba za ki amince da zaɓin Baba ba shiyasa na yi hakan, ki yi haƙuri don Allah ki yafe min Aamina na yi Alƙawari kuma na kasa cikawa na tafi na barki cikin wani mugun hali, amma yanzu zan gyara kuskuren da na aikata ta hanyar haɗa ƴa-ƴanmu ta yuwu Allah ya haɗa su ne dan dai-daitar wannan rashin Jituwa dake tsakanin Ahlinmu, na ji ƙuna sosai da na cutar da ke ba zan iya dena ba ki haƙuri da neman yafiyarki ba har sai kin yafe min”
Abi ne ya ce “Alhamdulillahi Ma sha Allah, mun ji daɗin wannan ƙarin bayani da muka samu, Subhanallah meke damun Bil Adam ne?? suna ƴan uwa amma su ke nunɗa ƙiyayya wa juna haka? ba su da sanin cewa Gaba Haramun ce, ba su san cewa babban kuskure suke tafkawa ba?, da Alamu Jannah da Zuhra su ne silar gyaruwar wannan kuskure da Manyanmu suke kai, ina so ku kwantar da hankalinku In Sha Allahu komai ya zo ƙarshe, Allah ya kiyayemu da duk wata fitina wadda take akwai da wadda ba mu san da ita ba”
Ummi ta murmusa gami da cewa “Amin ya Rabbil Alamin, Yaya Abdussalam ai ba kuskure ka yi ba tin da kana da kyakkyawar manufa tsakaninmu ko da yaushe yafiya ce komai ya riga ya wuce sai dai fatan Alkairi”
Alhaji Abdussalam ya ce “Ma Sha Allah, na yi godiya sosai Allah ya saka da Alkairi, Goben nan zan je Nijar ɗin In Allah ya Yarda zan nemi amincewarsu”
Ummi ta ce “dama kana zuwa?”
Ya ce “e ina zuwa dan dai ke ba a can kike da zama ba kuma har yanzu babu wata dangantaka tsakanin Iyayenmu”
Abi ya ce “to aikuwa da ni Mahaifin Jannah za’ayi wannan tafiyar dan haka ina ganin ka ƙara mana lokaci, bayan anyi wannan zaman Kotun idan mu ka ga hukuncin da Allah ya yanke mana sai mu ga meye abin yi ko?”
Abi ne ya yi ƙoƙarin kawar da waccan hirar ya sako wata. ba wani daɗewa su ka yi ba Jannah ya takura akan su tashi a koma gida.

Jannah yana tsaye hannayensa goye a bayansa ya na ɗan zagayawa a hankali, ya yi nisa sosai a duniyar tunani, Ummi ce ta kira sunansa hakan ya sa ya sauke hannuwan nasa tare da sauke wata matashiyar ajiyar Zuciya sannan ya amsa kiran cikin sanyi. “tunanin me kake yi? ko har yanzu ba ka gamsu da gaskiyar da na faɗa muku ba??”
“ba haka bane Ummi ina tunani ne akan goben rayuwar Zuhra, na zamo me cutar da ita cuta ba kaɗan ba, na so na hana kaina shaƙuwa da ita dan tsoron irin ranar nan amma na kasa, ko ba komai Ummi ni Mutuwa zan yi”
“me yasa?”
“ban sani ba kawai ina jin hakan ne a jikina”
“bai zama lallai ace dole abin da kake ji zai faru ba ta yuwu kuma ba a kanka bane, ba na so ka dinga min zancen za ka mutun nan in kuma so kake kafin ka mutu ni na fara mutuwa sai ka bani labari”
“a’a Ummi ba na so na rasaki na yarda zan dena, gobe ba ni da tabbacin zan dawo gida a raye, ki yafe min Ummina”
“Ba ka yi min laifin komai ba, In Allah ya Yarda za mu ci gaba da rayuwa tare”
ɗan murmushi ya yi kafin ya ce “sai da safe”
Daga haka ya koma ɗakinsa, yana shiga ya rufe ƙofa gami da fashewa da kuka.

Washe-gari.
a cikin Abokansa da Ƴan Uwansa Ba wanda bai yi kuka ba kafin lokacin shiga Kotu dan kuwa ya ce yau ba abin da zai hana shi amsa laifin da ake tuhumarsa.

Da yake Alƙalin ya na ƙarƙashin barazanar su Hajiya Saratu cikin sauƙi ya gazgata Hujjojin da su ka kawo tare da kore na Jannah, Lauyansu kuwa ya dage wajen tilastawa Jannah akan ya amsa laifin.
Suna ƙoƙarin yanke Hukunci ta hanyar jibgawa Jannah laifin wani ya shigo Kotun Fuskarsa a rufe, ya ce “a gafarceni ya mai Shari’a na san na makara na ɓata lokaci kuma na wahalar da Shari’a to yanzu a shirye nake domin karɓar hukunci, wannan Kisan da aka yi ni ne wanda na aikata Abokina kuma shine wanda ya yiwa Jannati fyaɗe”
ya ƙarasa maganar yana nuni da ɗan uwansa dake a gefensa.
Kafin Mai Shari’a ya yi wani yunƙuri wasu biyu suka ƙara shigowa har suna rige-rigen fara bayaninsu na cewar su suka yi laifin daga nan muhawara ta wanzu tsakanin su huɗun kowa yana cewa shi ne, suna cikin haka Mutum uku suka ƙara shigowa bayan su sai ga Mutum Huɗu duk suka amsa laifin, Mai Shari’a ya na ƙoƙarin yin magana wata budurwa ta shigo ta na takawa cikin nutsuwa fuskarta ba walwala, itama a inda waƴancan Mutanen suka tsaya ta tsaya, cikin Nutsuwa ta miƙa gaisuwa ga Mai Shari’a sannan ta fara koro masa cewar itace ta sa ayi kisan.
Gwauruwar ajiyar Zuciya Mai Shari’a ya saki gami da furta “Alhamdulillah” farin ciki ya ziyarce shi ganin ƴarsa ɗaya tilo a gabansa kuma cikin lafiya da kwanciyar hankali, duk da bai san ta ya akai ta baro hannun ƴan ta’addan ba amma ya sa a ransa Allah ne ya kawowa me gaskiya ɗauki, dan kuwa zai yi amfani da wannan damar wajen kuɓutar da Jannah daga sharrin ƴan ta’addar dan ya riga ya yi iya binciken da zai yi ya gane Jannah ba shi da hannu a cikin al’amarin tsabar ƙwarewarsu a sharri ce ta sa ba wanda ba zai yarda cewa Jannah ne ya aikata ba”
Dakatar da Mutane ya yi daga ce-ce-kucen da suke yi bayan anyi tsitt ya ce “wannan zama ya zo da ruɗani kuma lamarin masu ƙara ya zama kame-kame dan haka Kotu ta Kori wannan Shari’a”
Farin ciki ne ya kewaye duk wani me so da Tausayin Jannah.
Haka aka fito daga Kotun daban-daban wasu farin ciki wasu baƙin ciki.
Jannah yana cikin tafiya Jaafar ya tare masa hanya Zuhair zai yi magana Jannah ya dakatar da shi, Jaafar da yake riƙe da hannun Zeety ya ƙare masa kallo sama da ƙasa kafin ya ce “na tayaka murnar korar ƙara da aka yi, sai dai ka manta kaidi irin na Hajiya da kuma ƙarfin ikonmu, za mu iya ɗaukaka ƙara za kuma mu iya tuhumarka akan wani laifin, sannan tsohuwar budurwarka wato masoyiyata ta na yi maka fatan Alkairi” suka kwashe da dariya sannan suka yi gaba”
Cikin tausayawa Jannah ya bi Zeety da kallo “ba ta san halin Mutanen ba shi yasa ma ta fara soyayya da Jaafar ba abin da bai ɗauka ba a halayen Mahaifiyarsa ina jin tausayinta sosai”
Dogon tsaki Zuhair ya buga kafin ya ce “dallah wuce ka shiga mota akan ƴar iska da ɗan iska za ka zauna ɓata lokacinka, abin da ta yi maka ma ai bai kamata ka ƙara kallon inda take ko halin da take ciki ba bare ka ji tausayinta, idan ba ka sani ba bai fi sati ɗaya da rabuwarku ba suka haɗe suka fara soyayya, abin duniya take so kuma ta samu, kai ina ruwanka?”
rausayar da kai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya yi gaba.

Hajiya Saratu ce tsugunne a tsakiyar Ƴa-ƴansu tana kuka kashirɓan akan rashin nasarar da suka yi, Kukan da take kuwa ya ƙara tafasa Zuciyar kowannensu a take wani zafin ƙiyayyar ya ƙara shiga tsakaninsu. Hajiya Murja kuwa in banda firfita ba abin da take yi, duk da cewar ba zafi ake a lokacin ba amma hakan bai hana ta gumi ba.
Haisam ne ya kallesu ya ce “ni fa wallahi duk wadda Za’ayi sai dai ayi dan na lura sai mun ƙarar da dangin yaron nan kaf tin da shi ya ƙi Mutuwa, kuma wallahi sai mun ƙara shigar da wani ƙorafin, haba wallahi bai isa ba ya yi kaɗan”
Bomboi ya ce “me za mu yi wanda ya wuce wannan? ai wallahi nima hakan na gama tsarawa kuma ya jira hukuncin da zai biyo baya dan ba’a taɓamu a zauna lafiya”
Sultan ya ce “wajibi ne mu ƙara zuwa wata Kotun dan a ƙwatar mana haƙƙinmu, Sannan mu lalubo ko su waye suka ɓata mana wannan ranar mu kashe tsinannu”
Jaafar ya ce “nifa kamar na so ɗaukar muryar ɗaya a cikinsu, wallahi in dai ba kashesu ɗin akai ba za su iya jawo mana matsala”
Haisam ya ce “kana ma, kisa ai ya rataya a wuyan duk wanda ya shiga gonarmu ya yi mana ɓarna”
Haka suka ci gaba da tattaunawa tare da tsaida matsaya akan matakin da za su ɗauka.

A ɓangaren su Jannah kuwa har ya je gida mutanen da suka temake shi a Kotu suka bi bayansa suna neman tattaunawa da shi, tsayawa ya yi yana saurarensu bayan sun buɗe fuskokinsu ɗaya a ciki ya ce “maganar gaskiya mu yaran su Sultan ne kuma mun ga irin zaluncin da suke maka ne shine muka yanke hukuncin temakonka domin kuwa suna sa mu ɗaukar mummunan zunubi shiyasa muka ce ya kamata a karo na farko mu yi temako, yanzu nasan in suka ganemu ma kashemu za su yi, amma kar ka damu da hakan mun yi abin da ya dace ne, Ƴar wanda yake muku Shari’ar ma su ne suka saceta mu kuma muka kwantota daga hannun waƴanda aka bawa ita dan in bai ganta ba ba zai yarda ya wankeka ba, Alkairin da kake yi ya wuce komai dan haka mun sadaukar da rayukanmu”
Jannah ya Murmusa gami da cewa “na gode sosai Allah ya tsareku da sharrinsu, to yanzu ku ya za ku yi? ko guduwa za ku yi??”
Ɗaya ya ce “Fitar!! haba Oga ta yaya zamu gudu? ai da mu gudu gwara mu faɗi ko mun faɗi mun fi yaro suna, muna nan ko za su kashemu ɗin, kuma indai mun samu tsallakewa za ka dinga jin sirrinsu da duk abin da suke tsarawa”
Jannah ya ce “na gode Allah ya yi muku Albarka, yanzu ba wani abin da kuke da buƙata?”
Babbansu ya ce “mu fa don Allah mu ka yi kawai ka manta, mu bari mu ci gaba da tafiya”
Yana nan tsaye suka shiga motarsu, sai da suka ɓacewa ganinsa sannan ya koma cikin gida.

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/16, 6:06 AM] INDO CE: *D-yaro*
35

 

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, kowanne ɓangare da abin da ya damesu.
kamar yadda su Hajiya Saratu su ka faɗa za su shigar da wani ƙorafin, sun shigar kuma an karɓa jiran ranar da za’a zauna kawai su ke yi.
a ɓangaren su Jannah kuwa sun samu ƴar nutsuwa sai dai suna cike da tsoron abin da zai biyo baya shiga Kotu da kuma hukunci su Hajiya.

Zaune ya ke shi kaɗai a falo yana danna Laptop, har Fatima ta ƙaraso ta zauna bai sani ba sai da ta kira sunansa, ɗagowa ya yi ya kalleta tare da amsa kiran, cikin sanyi ta ce “ina son ganin Baffana, dan Allah ka kaini in ganshi har ma da mutanen garinmu ina so mu gana”
nazari ya yi kafin ya ce “anya kuwa zan iya hakan Ƴar-manya? ina jin tsoron fitarki dan duk wani motsinmu a idon duniya yake nima dan dai namiji ne fita ta kamani dole ban da haka da na zauna a gida tare da ke”
fashewa ta yi da kuka ta na cewa “Don Allah ka kaini in ganshi yanzu duk Wannan wahalar da nasha ta rashin lafiya ban ga Mahaifina ba amma ba za ka temaka min ba? gashi na kusa haihuwa idan na mutu fa?, Don Allah ka temaka min na ganshi kafin na mutu”
kukan da take ya yi matuƙar karya masa Zuciya tausayinta ya kama shi, ya kamata ya kwatanta Adalci gareta don kuwa tin da ya mallaketa bai fi sau biyu ya taɓa kaita ba sabi da kullum ba lafiya daga wancan sai wancan, cikin salon kwantar da hankali ya ce “ba damuwa zan kai ki in Allah ya kaimu gobe, sai ki shirya musu tsaraba amma fa ban da kwana hasali ma ba za mu daɗe ba da an gaisa za mu dawo gida tin da kin ga ba ki da lafiya”
goge ƙwallar ta shiga yi ta na murmushi cike da farin ciki ta ce “na yarda, in dai zan ga Baffan shi kenan ko ba za mu daɗe ɗin ba”
ya yi murmushi gami da cewa “To Sarƙa me rikicin gan-gan har an gama kukan?”
ta ce “e mana tin da ina kusa da kai ai batun hawaye babu, me zan kai wa ƴan garinmu?”
“ohh ki basar kawai zan ji da lamarin zuwa gobe, yanzu ki je ki yi bacci dan nasan ɗoki zai sa ki tashi da wuri”
murmushi ta yi gami da juya idanu ta ce “in ba ka kwanta ba nima ba zan kwanta ba, yau ba’a ɗakin Ummi zan kwana ba”
ajiye Laptop ɗin ya yi a gefe ya miƙe tare da riƙe hannunta ya ce “mu je in dan ta nine ai ba matsala”
ba son kwanciyar take yanzu ba shiyasa ta tsiro masa da hakan sai kuma ya ɓullo mata ta baya, babu yadda ta iya dan haka ta miƙe, cikin takunta irin na me tsohon ciki take binsa har su ka isa Ɗakin.
sai da ya lallaɓata ta yi bacci sannan ya janyeta ya gyara mata kwanciya ya fice ya nufi ɗakin Ummi domin duba lafiyarsu.

washe-gari.

lambar Zuhra yake ta zabgawa kira ba ta ɗauka ba har zai haƙura sai kuma ya ƙara kira, ta kusan tsinkewa sannan ta ɗauka cikin sauri ta ce “Allah ya baka haƙuri wallahi ba na kusa ne sai yanzu Zahra ta sanar min”
ta yi maganar ta na maida numfashi sabi da gudun da ta sha kafin ta zo ta amsa kiran.
“ba komai dama zan kai Fatima gida za ta gaida Baffa ne shine zan sanar miki ko za ki raka ni”
“ba za ni ba”
“kai tsaye?”
“e, tafiyarka kai da matarka shine zan wani je? to na ƙi ɗin”
“ba komai na haƙura sabi da nasan za ki min Addu’a dama ita kawai na ke buƙata”
“wannan kuma wajibi ne ai, kai dai Allah ya dawo da kai lafiya kawai kazo akwai labari”
“ki bar kayanki ba na so in na dawo ɗin”
“haba kai kam har ka ɗau ɗumi? to shi kenan bari in gaya maka yanzu”
zai yi magana Fatima ta dakatar da shi ta hanyar riƙe hannunsa ɗaya ta na murmushi ta ce “tawo mu tafi”
gyaɗa kai ya yi, bayan sun yi sallama da Ummi suka nufi mota.
tin da suka fara tafiya bai ce mata komai ba duk hankalinsa ya na kan Zuhra da take zubo masa surkullen surutu, kallonsa ta yi gami da kiran sunansa a marai-raice, kallo me alamar Ya akai ya watsa mata, ta ɗan sunkuyar da kai kafin ta ce “don Allah na iya wannan lokacin ka ba ni kulawa ta musamman har mu je mu dawo, sai na ke jin kamar…”
da sauri ya katseta da cewa “kar ki gaya min maganar da za ta tsaida numfashina mana”
goge ƙwalla ta yi kafin ta ce “ai dole ne Ɗan-manya ni dai idan da hali ka yi min abin da na ce”
sallama ya yi wa Zuhra ya ajiye wayar sannan ya mai da hankalinsa gareta.

sun isa lafiya kowa ya ji daɗin ganinsu Musamman Baffa ya nuna farin cikinsa sosai da sosai, kamar yadda ya ce ba za su daɗe ba ba su daɗe ɗin ba suka kamo hanya, haka su ka rabu Da Baffa yana ta binsu da sa Albarka.
a hanyarsu ta dawowa motar ta yi shiru kowa da tunanin da yake yi.

Zuhra tin da su ka yi sallama da Jannah gaba ɗaya hankalinta ya ƙi kwanciya sai ta ji duk ba ta yarda da tafiyar ba haka kawai Zuciyarta take tsinkewa tin tana iya sarrafa tunaninta har ta kasa, ba shiri ta shirya ta bi bayansu.

ƙarar fashewar tayar motar ce ta firgita Fatima ta farka daga ɗan baccin da ya kwasheta a tsorace ta zubawa Jannah da Zuciyarsa take wani mugun tsalle ido.
kafin ya bambance me yake shirin faruwa duk an harbe tayoyi huɗun motar hakan yasa dole ta tsaya ba tare da an tsayar da ita ba,
Kallon Fatima ya yi ga mamakinsa sai ya ga ta zuba masa ido tana murmushi ga kuma hawaye da suke tseren sakkowa daga idanunta.
cikin kiɗima ya ce “shi yasa na ce ba zan fito da ke ba Ƴar-manya, na daɗe ina mugayen mafarkai gashi yau na tashi zuciyata ta na ta tsinkewa jikina ya na bani akwai abin da zai faru sai dai bansan ko mene ba, kin ga yanzu tayoyinmu duk sun fashe, bari na duba meke faruwa”
gyaɗa masa kai ta yi hawaye na ƙara sharara ba za ta iya ce masa ko uffan ba a yanzu.
fita ya yi yana hange-hange amma Allah bai bashi ikon ganin kowa ba, ya na shirin komawa mota ƙarar bindiga ya ratsa kunnuwansa, juyawa ya yi dan ya ga ta ina ne, Fatima ce ta ƙwala masa wani gigitaccen kira juyowar da zaiyi harsashi ya sauka akan ƙirjinta ta yi ƙasa luuuuu ta faɗi.
“Fatimaa!!!!!”
ya kira sunanta da ƙarfi tare da durƙusawa ya rungumeta tsamm cikin tashin hankali ya ke cewa “Fatimata kar ki barni don Allah kin min alƙawarin haifa min ɗana me sunan Abana fa don Allah ki buɗe idonki Fatima ”
cikin sassarƙewar murya ta ce “na san ba zan yi tsawon rai tare da kai ba Jannah, ni tawa ta ƙare burina ya cika na ƙare rayuwata tare da kai gashi zan mutu a hannunka, kar ka damu a kaina dama ba ni ce abokiyar rayuwarka ba Zuhra ce kuma nasan za ta kula min da kai fiye da ni, kar ka yi ku….”
maganar ce ta maƙale sabi da harbi biyu da makashin ya yi mata a kanta lokaci ɗaya rai ya yi halinsa, wani ragon kuka Jannah ya saki tare da miƙewa da nufin yaƙar mutanen da suka harbeta suna daga cikin wata mota a ɗayan tsallaken Titin.
cikin rashin imani suka saita harsashin gareshi tare da sakin harbi biyu a jere, sai da suka tabbatar ya kai ƙasa ba alamun numfashi a tare da shi sannan suka gudu.

Zuhra cike da tsoro take jan motar sabi da Titin babu kowa ga wasu zantuka da Zuciyarta take gaya mata hakan ya haifar mata da tsananin tsoro, zuciyarta ce ta buga da ƙarfi lokacin da idonta ya sauka akan motar Jannah da ke tsaye akan Titi, wani sabon tsoron ne ya ƙara dirar mata ta yi sauri gangarawa gefe ta ajiye motar ta fito da gudu gudu ta nufi inda wasu ƴan tsirarin Mutane su ka yi ƙawanya, zubewa ta yi har ƙasa tare da kurma ihu ta fashe da kuka tana cewa “duk yawanku amma an rasa wanda zai ce-ci rayuwar Jannah, Innalillahi’wa’inna’ilaihirraji’un!!! shi kenan na rasa farin cikina nima mutuwa zan yi bazan ƙara rayuwa ba kowa ma sai ya Mutu tin da aka kashe min Jannah wallahi kowa sai ya Mutu, wayyo na shiga Uku na boni”

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/18, 6:28 AM] INDO CE: *D-YARO*
36

Wani ne ya kalleta cikin tausayawa ya ce “Baiwar Allah kin san su ne??”
kasa magana ta yi sabi da kuka ya hana ta damar yi, wani dattijo ya ce “Ai temako ba sai ka san Mutum ba tin da Allah ya sa an sami Mota ai sai ayi ƙoƙarin kai su asibiti kafin Ma’aikatan su zo ko?”
Matashin ya kalli Zuhra gami da cewa “Baiwar Allah kin amince kuma za ki iya jan motar?”
mukullin kawai ta miƙa masa tare da tashi ta nufi inda Motar take.
Asibiti mafi kusa aka kaisu , da kyar Zuhra ta iya kiran Abi da Alamee ta sanar musu.
ba ɓata lokaci su ka kama hanya tare da Dr Saadiƙ.
Alhamdulillah! an yi Nasarar shawo kan matsalar Jannah sai dai ya faɗa doguwar suma.
Abi ne ya kalli Dr Saadiƙ cike da damuwa ya ce “Ba ka sanar da ni halin da yake ciki ba sai ka na zuwa ka na zuwa ka ke ce min, an samu matsala ko?”
ya ƙarasa maganar cikin karyewar Zuciyar kamar zai fashe da kuka.
Dr Saadiƙ ya girgiza kai alamar “A’a” sai dai da kallo ɗaya za’a gane ya na cikin matsananciyar damuwar da ta so ta ninka wadda Abi ya ke ciki dan kuwa shi fargaba ce shi kuwa Dr shi ne ya fi kowa sanin muguwar matsalar da ke tare da Jannah.
Abi ya ce “Yanzu ma ba za ka ce komai ba? ina jin tsoron abin da zai faru da ɗana”
Dr ya ce “Wannan ba ita ce abin tattaunawa a yanzu ba, mu je mu ɗauki Fatima mu wuce daga can sai mu rakata gidanta na gaskiya”
shiru ce ta biyo baya kafin Dr Saadiƙ ya ce “Allah kenan me yadda ya so, wato Alhasan Abokina ne sosai Alhusaini! a iya sanina da shi ban taɓa ganin ya aikata wani babban kuskure wanda ya amsa sunan Zunubi ba, ya na da tausayi ya na temakon talakawa da duk wanda ya ke buƙatar temako ya na ibadarsa kamar yadda Addininmu Muslinci ya tanada ya na cika ƙa’idodi kyawawa, duk inda Mutum na gari na ƙwarai ya ke to Alhasan ya amsa wannan sunan, haka ɗansa ya biyo halinsa, ɗansa ba mutumin banza bane, tabbas ita Jarrabawar Allah ba ruwanta da imanin Mutum sai dai mu yi fatan Allah ya sa ta zo mana da kyau, Haƙiƙa yaron nan ya fuskanci ƙalu-bale me tarin yawa a rayuwarsa kuma ya na kan fuskanta, da ace idonsa biyu ya ga mummunan kisa na rashin imanin da aka yiwa Matarsa ai kuwa da ya yi kamar ya haukace to dan dai akwai tawakkali Allah ka ƙara mana imani da haƙurin jure kowace irin Jarrabawa”
da kyar Abi ya ɗaga harshensa ya furta “Amin”

Yau kwana na huɗu kenan da rasuwar Fatima.
gidan shiru babu ko alamun motsi duk da cewar duk suna falon a zazzaune amma jimami ya hana su ko motsin kirki
a hankali sautin kukan Natiee ya karaɗe kunnuwansu, cike da kulawa Yaya Fa’iza ta ce “Jannati meke faruwa?”
cikin shashshekar kuka ta ce “kamar yadda Fatima ta Mutu nima haka za su kasheni, da tini ma na mutu, nima na so ban rayu ba da hakan ya fi min farin ciki da irin wannan mummunar rayuwar, sun ci zarafina sun rabani da mutuncina”
Yaya Fa’iza ta ce “ba komai Janniee kar ki damu Allah zai yi mana sakaiya, in Allah ya yarda lokacin wannan baƙin cikin duk ya kusa wuce, ki dena kuka kina ambatawa kan ki mutuwa yin hakan tamkar butulcewa Allah ne akan hukuncin da ya yanke miki, mu godewa Allah da hankalinki ya dawo da ba mu san ya za mu yi ba, abin ya yi mana yawa, ki yi ta Istigfari sannan a duk lokacin da ki ke tunanin wani abu mara daɗi ki yawaita ambaton sunan Allah da yiwa Annabi (S.A.W) Salati”
Umma Zaliha ce ta zagayo ta zauna a kusa da ita ta janyota jikinta ta ci gaba da rarrashinta gami da kwantar mata da hankali tare da Nasihu.
Ummi ko ɗago kai ta kallesu ta kasa yi dan kuwa hakan zai iya sawa Zuciyarta ta ƙarasa bugawa.

Abi da Dr Saadiƙ ne zaune suna zantawa akan rashin lafiyar Jannah Dr Saadiƙ ya ce “Alhamdulillah, Alhinin Rashin da mu ka yi ya ɗan ragu a yanzu dan haka zan sanar da kai gaskiya akan Muftahul-jannah, shi ba ku taɓa lura cewa ya dena sunkuyawa ba? misali idan zai ɗauki abu a ƙasa ya sunkuya sakk! kamar yadda kai me lafiya za ka yi, ka lura da hakan ba ta yuwuwa a gurinsa??”
Abi ya girgiza kai gami da cewa “A’a fa ba na ce haka ba gaskiya, amma tabbas kullum ina ganin karsashinsa ya na janyewa, har Mahaifiyarsa ma ta yi min magana akan hakan sai dai in mun tambayeshi sai ya ce ba komai, mu kuma mun yi duba da hankalinsa shi ba yaro bane shiyasa ba mu tsawaita bincike akai ba”
Dr ya ce “Madallah, to banda abinku ina Muftahu ina hankalin da za ku yi masa turin jeka ka mutu? ko dan ba ku da laifi akan ni, a matsayina na Likitan da yake kula da lafiyarsa na iya gane cewa ya na ɗauke da matsala a ƙashin bayansa wanda shi mu ke kira maɗaukar Dan-adam, tin abin bai kai hakan ba na so a ɗauki mataki amma ya yi ta roƙona ya haɗani da Allah akan kar na sanarwa kowa, ni kuma na biye masa na ƙi sanarwa kowa gaf da Rasuwar Alhasan, a cewersa ba ya son ɗaga hankalin iyayensa da ƴan-uwansa ba yadda na iya dan haka na zuba masa ido, ana cikin haka kuma sai wannan tsautsayi ya faɗo na cewar shi ya kashe Mahaifinsa daga nan ba kwanciyar hankali
tausayin halin da za ku ƙara faɗawa ma kaɗai ya hana ni sanar muku, ashe ƙin faɗen da nayi shine kuskuren gashi yanzu lamarin ya haɗu da harbin da aka yi masa ya ƙara rincaɓewa, ina me shawartarku da ku yi duk cuku-cukun da za a yi a fitar dashi ƙasar waje, idan ka amince min a yau ma sai mu fara ƙoƙarin hakan, Alhaji Abdussalamu ma ya nemi hakan, tin jiya mu ka yi maganar da shi ya ce Yarinyarsa ta damu a fitar da shi neman lafiya har da cewa ita za ta iya ji da komai, to amma ai ba za mu zuba ido ba tin da dukanmu ɗanmu ne ita kuma in da rai da rabo Matarsa ce to dan haka ita nata kawai idan mun kammala shirye-shirye sai ta zama ƴar rakiya”
Abi ya numfasa kafin ya ce “Dukanmu ma mun yi kuskuren Dr da kai da ka ƙi faɗe da shi da mu da muka kasa gane lalurarsa mu ka kasa tilasta masa ya sanar da mu gaskiya, to a hakan ma dai sai mu godewa Allah sannan mu ci gaba da roƙo da neman temakonsa,
me yasa ma ba ka fara gudanar da komai ba tin da Alhaji Abdussalam ɗin ya nemi hakan? ai ba mu da burin da ya wuce samun lafiyarsa za mu yi komai domin inganta rayuwarsa dan haka yanzu ma a shirye nake”
Dr ya ce “To Alhamdulillah zan yi nazari akan asibitin da ya kamata a kaishi”

cikin kwana uku aka kammala duk wani shirin da za a yi a daren ranar jirginsu ya ɗaga, Abi da Aunty Fa’iza da Zuhra da Alamee.

MEDANTA HOSPITAL
NEW DELHI

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/19, 10:19 AM] INDO CE: *D-YARO*
37

Da yake an shirya komai tin kafin zuwansu, ba wani ɓata lokaci Jannah ya shiga ƙarƙashin kulawar likitocin Asibitin.
Alhamdulillah an yi aiki cikin nasara ba tare da wata matsala ba, lafiya ta samu sai dai ƙarashe sai kuma ƙunci da ya ke damunsa, duk yawan mutane a guri ko me za su ce ba zai tofa ta bakinsa ba, ba ya magana idan ba “To” da “Uhm” ba su ɗin ma sai an matsa masa yanzu yaren kai ya ke yi gyaɗa kai ko girgizawa.

Yaya Fa’iza da Abi ne zaune suna ɗan taɓa hira, Yaya Fa’iza ta ce “Yanzu Abi haka rayuwar Jannah za ta ƙare cikin ƙuncin nan?, gashi dai ya samu lafiya amma har yanzu Alhinin abin da ya faru bai sakeshi”
Abi ya ce “Mun godewa Allah da ya dawo cikin hankalinsa ma, dan kuwa wannan tashin hankalin da ya gani ma kaɗai ya isa ya sa Mutum ya zauce”
Yaya Fa’iza ta ce “Ya na da kyakkyawar Zuciya, Ya Allah ka kawo mana ƙarshen wanman zalumci da ake mana da wannan ƙuncin rayuwar da muke ciki”
Abi ya ce “Amin Amin Allah ya amsa, ni ma kaina idan na nutsu nakan rasa ta ina za mu shawo kan matsalar, gashi sun rattaɓa ni a Kotu a bisa cewa na cinye musu kadarorin Mahaifinsu da ya bari, gashi sun ɗaukaka Shari’ar Jannah, tin mu na yi kan-jiki kan-ƙarfi har ƙarfinmu ya ƙare, Allah ka kawo mana ɗauki Allah ka kawo mana temako ta inda ba mu taɓa tunani ba, Allah ka kawo mana ƙarshen wannan tashin hankalin cikin sauƙi ya Allah”
Yaya Fa’iza ta goge ƙwalla gami da cewa “Allah ya amsa Addu’a Abi, ni ai yanzu na tashi tsaye ba na baccin banza kawane dare ina raba shi ne da Nafiloli ina roƙon Allah da neman Agaji a gareshi, haƙiƙa shi ne yasan abin da ya ɓoye a cikin wannan lamari kuma ga shi za mu dogara”
Abi ya ce “Wannan haka yake ɗiyata, Allah ya saka muku da Alkairi a bisa ƙoƙari da riƙon amana da ku ka yi, dan Muftahu-jannah Amana ne a gurinku tin farkon zuwansa duniya, ba wai dan kuna yayyensa ko ma wanda uba kawai ku ka haɗa sai ya zama ba ruwanku dashi ba, a’a dole naku ne in kun riƙeshi Amana Allah ya fi kowa sani, idan kun banzatar dashi Allah ya sani, ku kam ba ku yi wannan asarar ba, Allah ya baku ikon ci gaba da riƙon Amana har ku koma ga Allah”
Ta Amsa da “Amin ya Rabbil-izzati!”

Da sallama Zuhra ta shiga ɗakin da Jannah ya ke jinya cikin taku me kama da sanɗa. Har ta ƙarasa ta zauna a bakin gadon da yake kwance idanunsa suna kanta.
Kiran sunansa ta yi cikin tattausar Murya hakan ya sa ya lumshe idanun nasa gami da kauda kai.
Kamar za ta yi kuka ta ce “Jannah ya kake ji yanzu?”
“Sanar da ke ɗin me zai amfana miki?”
“Ko ba komai dai ai zan san halin da kake ciki, gaya min meke damunka?, kasan dai mawuyacin abu ne na iya jurewa ganin ƙuncin nan naka, nima Zuciyata ƙuna take, ba ka san cewa na kamu da ciwon Zuciya tin lokacin da ka ƙi karɓar Soyayyata ba?, so ka ke ciwon ya kasheni ko??”
ɗago idanu ya yi ya na kallonta cike da mamaki, ba ta taɓa faɗa masa ba ko da wasa sai yanzu, ashe dai dole kowace irin Masifa ma ta faɗo masa dan kuwa ya aikata babban kuskure da ba zai iya gyarawa ba.
Katse masa tunanin ta yi da cewa “Ba ka yarda ba ko?”
“Na yarda mana, hakan ne ma ya ƙara gazgata min na aikata kuskuren da ya ke ta bibiyata, Zuhra in ki ka ga yadda aka kashe min Matata da ɗan cikinta za ki so ace na Mutu ban rayu ba, idan ina tuna wannan sai na ji tsananin tashin hankali da ƙunci, na rasa wane irin baƙin ciki zan yi ji na nake kamar na zauce, a gaban idona su ka kashe Fatima kuma na kasa cetonta”
“Haba Jan, ka gane mana, na daɗe ina faɗa maka Ba fa a gyara ɓarna da ɓarna, ina nufin dan ka sa kanka cikin wata damuwar ba za ta yi maganin wata ba”
“Nasan ba lallai ki fahimce ne ba Queen, ki yi min shiru dan Allah, in da dama ki fita ki bani guri”
girgiza kai ta yi gami da cewa “Allah ya baka haƙuri, amma ba…”
ɗaga mata hannu ya yi tare da cewa “Don Allah!”
rufe bakinta ta yi sannan ta miƙe gami da fashewa da kuka ta nufi hanyar waje.

Ta na fita daga ɗakin ta jingina a bango ta ci gaba da sharɓar kukanta, ta na cikin haka ta ji an dafa ta, tsayar da kukan ta yi sannan ta juyo dan a tunaninta Yaya Fa’iza ce, ganin ɗaya daga cikin masu kula da Jannah ce ya sa ta janye jikinta.
Cikin yaren turanci Budurwar ta ce “Sunana Aysha, ana kirana Jana, ni haifaffiyar Pakistan ce aiki ne ya dawo da iyayena da ni nan, ni Musulma ce kamar ke, na ga kuna cikin wani hali na damuwa shine na tambayeki ko akwai temakon da zan iya yi akai”
Ajiyar Zuciya Zuhra ta sauke sannan ta ce “ba za ki iya yin komai ba, na gode da kulawarki”
ta na gama faɗen haka ta yi gaba da nufin barin gurin. Cikin sauri Jana ta riƙo hannunta tare da cewa “ki saurareni, ba ki sanar min ba ai ba za ki gane ko zan iya ba, Don Allah ki faɗa min”
Zuhra ta ce “tsautsayi ne ya faru da shi, shi kenan?”
Jana ta ce “A’a, akwai wani abin dan kuwa na ji ƴan uwanki suna magana akai, na yi Alƙawarin zan temaka miki in dai zan iya, ina matuƙar tausayin Mara lafiyanku ne, da manufa ta Alkairi na ke miki magana”
Nazari Zuhra ta yi kafin ta gyaɗa kai ta ce “Mu samu zama zan sanar dake”
Murmushi Jana ta yi sannan ta ce “Mu je mu zauna yanzu”
ba tare da wani tunani ba Zuhra ta Amsa.

Dalla-dalla Zuhra ta bata labarin abin da ya faru har zuwa halin da ake ciki yanzu.
Jana ta sha kuka sosai, da kyar Zuhra ta iya rarrashinta.
Bayan ta gama kukan ta miƙe tare da cewa “zan je NEW YORK”
da sauri Zuhra ta miƙe tare da Maimaita kalmar “New York?” cikin sigar tambaya.
Jana ta gyaɗa kai, cikin sanyi ta ce “ina da babban Lauya a can, ya so na amince masa tin ba yau ba amma na ƙi yarda sabi da Addinina ya haneni da aikatawa amma yanzu na shirya yin komai domin na temakeku, na san ina sallama masa kaina zai yarda ya temakeku, babban Lauya ne sai dai baya aiki da hakan ya yi karatun ya yi karatun amma duk hakan bai sa ya yi aikin ba, aikinsa kullum shine shaye-shaye da ƴan-mata kala-kala”
girgiza kai Zuhra ta yi gami da cewa “A”a ni kuma ban amince ba, sabi da mu ba zan bari ki yi kuskuren da Allah zai miki Hukuncin mazinaci ba, ki bari kawai Allah zai kawo mana mafita”
Jana ta share hawaye kafin ta ce “Ko rayuwata zan iya shimfiɗawa tin da har na yi niyya, kuma ko ba ki amince ba zan aikata dan kuwa nima Ina son ARSALAN Ina son abin da zai Alaƙanta ni dashi”
ba ta tsaya sauraren abin da Zuhra za ta ce ba ta yi gaba ta barta da sakakken baki.

bayan kwana biyu.

Falo ne na Alfarma wanda ya gaji da haɗuwa. Jana ta na tafiya ta na kalle-kalle har ta isa tsakiyar falon, a tsakiyar da’irar wasu saitin kujeru ta tsaya kanta a sama ta na tunanin ta in da za ta ɓulla, ƙasa ƙasa ta fara jin ƴan surutai hakan ya sa ta maida kallonta in da take jin Surutan. Arsalan ne a zaune tare da wasu fitsararrun ƴan-mata su biyu sun sa shi a tsakiya sai aikata Alfasha suke, dukansu ba me sitturar kirki a jiki.
A tsorace Jana ta yi baya tare da Furta “A’uzubillah”
Kamar da ga sama ya ji Muryar abar marmarinsa dan haka ya yi saurin ture ƴan-matan ya na warara ido dan ya tabbatarwa kansa ba yaudararsa kunnuwansa su kai ba.
Ganin yadda ta rirrintse ido ne ya sa shi sakin dariya, ya miƙe ya nufi inda take, ƙasa-ƙasa ya yi da murya ya ce “My Heart!!”
a hankali ta buɗe idanunta a cikin nasa a take ta lula duniyar tunani.
riƙo hannunta ya yi ta re da cewa “menene ya kawo ki gurina??”
haɗiye yawun da ya tsaya mata a maƙoshi ta yi kafin ta ce “Na kawo maka kaina, amma ka yi min Alƙawarin za ka temaka wa wasu Musulmi da suke buƙatar temakonka”
cikin rashin fahimta ya ce “fahimtar da ni”
zame hannunta ta yi daga riƙon da ya yi mata ta juya masa baya sannan ta ce “Ina so a kaina ka yi aikinka na Lauya a karon farko, na yi alƙawarin temaka musu ne kai kuma ni kaɗai ka ke buƙata dan haka na kawo maka kaina amma don Allah ka temake su, Mahaifinsa aka kashe sannan aka yi masa sharri”
girgiza kai ya yi kafin ya fincikota ta faɗa jikinsa ya rungumeta ya na kallon kyakkyawar fuskarta cikin shauƙin wani abu da ya kasa gane ko menene ya ce “ba na ce kar ki ƙara yi min magana in ba da yaren Hausa ba??”
kuka ta saki cikin harshen turanci ta ce “Ka yi haƙuri, na gaya maka ban iya ba, dan Allah kar ka wahalar dani, ka yi min duk abin da za ka yi in dai za ka temakesu”
“ohh Asshah!!! na sauya muradina akanki yanzu ba zan yi miki komai ba har sai na Aureki, amma dai gaya min meke faruwa da su??”
cikin sanyi ta ce “To mu zauna”
jan hannunta ya yi zuwa kan kujera ya zauna gami da yi mata masauki akan cinyarsa cikin kulawa ya ce “ina jin ki”

Kamar yadda Zuhra ta ba ta labari haka ita ma ta sanar masa.
mugun sanyi jikinsa ya yi lokaci ɗaya kamar an zare masa laka, in banda kallonta da yake yi ba abin da ya ke iyawa. Sai da ta ƙarƙare labarin sannan ya yi ta-maza ya ce “meye cikakken sunansa??”
“MUFTAHUL-JANNAH ALHASSAN”

idanunsa ne su ka ƙara girma sabi da zazzaro su da ya yi, da sauri ya miƙe ya shiga zarya a wajen cikin firgici, ruɗani, da tashin hankali.
cikin ɗaga murya ya ce “Tashi mu tafi Jana!!!!”
da mamaki ta ce “ina za mu je?”
ya ce “New Delhi, yau ɗinnan nake so mu tafi, ki shiga ki haɗa min kayana da duk abin da ki ka san zan buƙata”
daga haka ya fice daga falon cikin sauri.
mamakin abin da ya sauya shi lokaci ɗaya ya turnuƙe Jana amma sai ta manta ta wuce Bedroom ɗinsa dan yin abin da ya Umarceta, don ta san halinsa in ya dawo ba ta aikata ba zai iya yi mata abin da bai kamata ba.

 

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/20, 9:58 AM] INDO CE: *DOGON-YARO*
38

Cikin kwana ɗaya ya gama shirin tafiyarsu tsaf, a kwana na biyun ƙarfe 07:00am a Airport ta yi masa zuwa 07:15am jirginsu ya ɗaga zuwa sama.

Zuhra da Yaya Fa’iza ne zaune kusa da Jannah sun yi jugum-jugum kowacce ta luluƙa duniyar tunani. Jannah kuwa ya haɗe rai ya yi ƙasa-ƙasa da ido sabi da ransa a ɓace ya ke hakan ne ya sa duk ya hanasu magana da maida yadda akai shine su ka yi wannan tagumin.

Abi ne ya yi Sallama gami da kaɗa ƙararrawar ƙofar. Jannan ya ce “Abi shigo mana”
shigowa ya yi ya na maimaita sallamar.
Ya-ya Fa’iza Ta amsa kafin ta ce “Abi sannu da isowa, na ɗauka zan ganku tare da Alamee”
Abi ya ce “Yauwa sannu ɗiyata, mun yi dai magana da Alamee ɗin yanzu, ya ce min ya na zuwa ya je Kasuwa ne”
durƙusawa Zuhra ta yi ta gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska ya bita da sa Albarka.
bayan wani ɗan lokaci Alamee ya ƙaraso, Abi da Alamee ne su ka yi nasarar mantar da shi ɓacin ran nasa ta hanyar janshi da hira irin wadda ya fi so, Zuhra kuwa ko uffan ba ta cewa har gwara Ya-ya Fa’iza takan ɗan jefa ta-ta.

Suna cikin haka Jana ta yi sallama, da sauri Zuhra ta miƙe ta na kallonta kafin ta nufi inda ta ke suka rungume juna, Zuhra ta fashe da kuka ta na cewa “Ina fatan kina lafiya”
wata Murya wadda take jin kamar ta san me irinta ta katse mata maganar. “Ni zan gaya miki”
da sauri ta zame daga rungumewar da ta yiwa Jana ta na kallon ƙofa, Arsalan ne ya shigo ɗakin kansa a ƙasa bakinsa ɗauke da sallama, bai jira aka amsa ba ya raɓewa su Zuhra ya wuce ya na cewa “Lafiyarta ƙalau ban yi mata komai ba”
ba iya Zuhra ba kowa na ɗakin ma kallonsa kawai yake, bai san su na yi ba don kuwa idanunsa suna ƙasa hanyar da yake takawa kawai ya ke kalla, kai tsaye wajen gadon marasa lafiyan da Jannah yake ya nufa sai a lokacin ya ɗago idanunsa ya zubawa Jannan suka shiga kallon juna.
Jannah bai ce komai ba shi ma Arsalan bai yi magana ba sai ma sa hannu da ya yi akan cinyar Jannah ta dama ya ɗan janye wandonsa, sai a lokacin Jannah ya ce “menene hakan? waye kai?”
da sauri ARSALAN ya sake zubawa Jannah ido a karo na biyu sai dai wannan karon kallo ne me cike da ma’anoni iri iri ga wani irin rauni da ya baiyana a cikin idanunsa, zuwa yanzu ya tabbatar da komai da yake son tabbatarwa. cikin murya me nuna zallar karyewar Zuciya gami fa mamaki da Al’ajabi ya ce “YARO! MUFTAHUL-JANNAHHH!!!!!”
da sauri Jannah ya tashi ya zauna cikin tsananin mamaki yake ƙara kallon Arsalan jikinsa har rawa yake sabi da ruɗanin da ya shiga.
Arsalan ya ce “Muftahu hakan ya na nufin na rasa Mahaifina???? ashe Mahaifina aka kashe????”
Abi ya ce “Muhammadu-Mustafa!!!!”
sai a lokacin Arsalan ya kai kallonsa kan Abi sai kuma ya fashe da kuka ya na cewa “ina Ummina Ina Jannati?? kenan Jannatinmu ce wadda aka wulaƙantawa rayuwa??”
cikin ruɗani Jannah ya ce “ni fa ban gane me kuke nufi ba”
matsawa kusa dashi Arsalan ya yi cikin kuka ya ce “ni ɗan-uwanka ne Ya-yanka ne ni, ni ne na rubuta maka farkon sunanmu wato MMH a jikin cinyarka ta dama, ba dan komai ba sai dan na ganeka a duk inda na ganka sai gashi da ga jin sunanka jikina ya bani lokacin da zan dawo gareku ya yi!!”
kukan da yake ne ya ƙara ƙarfi ya hanashi maganar.
Cikin mamaki Jannah ya bi Abi da kallon YA ABIN YAKE?? (Littafin Nazeefah Jikar Nashe)
Abi ya gyaɗa masa kai yana murmushi ya ce “Ba lallai ka iya tuna lokacin da ya ke tare da mu ba, gaskiya ne ka na da Yaya Muhammadu-Almustafa me sonka da ƙaunarka daga baya kuma sai mu ka wayi gari babu shi ba tare da mun san laifin da mu ka yi masa ba”
Arsalan ya ce “ba ku yi min laifi ba Abi, baƙin halin Mahaifiyata da take son jefani a masifa ne ya sa na gudu bayan na saci kuɗaɗenta, na zo na gina rayuwata ni kaɗai na barku dan ina tsoron wata rana na ɗauki muguwar huɗubarta, Jannah ni na yi maka wannan Shaidar MMH Muftahul-jannah, Mustafa, Hassan, sunan Mahaifinmu, ko Umminmu ba ta san dalilin da ya sa na yi hakan ba, ta ji ba daɗi sosai har ta yi tunanin mugunta ce ta sa na yanka jikinka amma inada manufata na san zan gudu daga gida kuma na san wata rana zan nemeka shiyasa na yi maka shaida,
ka ga yanzu sabi da son Zuciyarsu sun kashe mana Mahaifinmu”
Murmushi me haɗe da hawaye Jannah ya saki, wani farin ciki ya lulluɓeshi cikin tausasawa ya ce “Ya-ya ka dena kuka don Allah, farin ciki ya kamata ka yi tin da yanzu ka dawo cikinmu”
Arsalan ya goge hawayen ya ce “Na dena tin da ba ka so Ƙanina, daga yau zan yi farin ciki har zuwa numfashina na ƙarshe”
Murmushi Jannah ya saki gami da cewa “Ya-ya kenan wannan Matarka ce??”
da sauri ya kalli Jannah ya kalli Jana wadda ta ke tsaye kusa da Zuhra duk sun zubawa sarautar Allah Ido, suna haɗa ido Jana ta sunkuyar da kai.
Arsalan ya ce “A’a ban yi Aure ba tukunna”
miƙewa ya yi ya koma kusa da Abi cike da farin cikin ganinsu ya ce “Abi ka yi shiru”
Abi ya murmusa ya ce “Maganar Wa da Ƙani ai ba kowacce ake shiga ba, ka ga ƙanin naka kuwa ban da Allah ya yi Matar tashi ba me tsawon rai bace da tuni yana nan da Ɗansa ko Ƴa”
Arsalan ya yi ƙasa da kai tunanin abin da yake aikatawa ne ya fara faɗo masa shi bai taɓa yin tunanin Aure ba a cewarsa duk abin da macen Auren za ta yi masa ya na da ƴan-matan da suke yi masa, sai a kan Jana ya ji yana muradin rayuwa tare da ita har Abada”
Abi ne ya katse masa tunanin da cewa “Tunanin me ka ke ne? kar ka wani damu kaima lokaci ne, ai ni na fi farin ciki ma da hakan dan na fi so mu yi komai da kanmu”
Arsalan ya murmusa, Abi ya sosa masa inda ke masa ƙaiƙayi dan haka ya yi saurin kawar da waccan maganar.

bayan wani lokaci.

Jannah ya samu lafiya sosai sun dawo gida Nigeria tare da ƴan sharruɗa da Likitoci suka kafa masa.
Ummi da Natiee su kaɗai ne a gida sai Ukhasha Sufee da Zuhair da Alhaji Abdussalam su ne masu kulawa da su, sosai kowa ya yi farin cikin dawowarsu Jannah da samun lafiyarsa.

Kwana biyu da dawowarsu Jannah Arsalan da Jana da Wuskha suka sauka a sirrance ba tare da kowa ya sani ba..

 

Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/21, 10:34 AM] INDO CE: *D-YARO*
39

Ummi da Natiee da su Yaya Hassana suna zaune suna hira Jannah da Arsalan su ka yi sallama a tare.
zumbur Ummi ta miƙe ta na bin Arsalan da ido ta na murmushin farin ciki.
ƙarasowa ya yi ya durƙusa har ƙasa cike da farin cikin ganinta ya ce “Ummi ɗanki ya dawo ki sa min Albarka”
hawayen farin ciki ne suka fara tseren sauka kan kumatunta, murmushinta ya ƙara faɗaɗa cike da ƙaunarsa ta ce “Yanzu ɗana zai san ya na da yayye ya na da gata, Allah sarki Mustafa nasan da kana nan da Muftahu bai zubda hawaye har haka ba, nasan da kana nan komai zai zo masa da sauƙi”
hannunta Arsalan ya riƙe kamar zai yi kuka ya ce “Ummi har yanzu lokacina bai ƙure ba zan yi masa abin da ban yi ba a baya, sa Albarkarki kawai muke buƙata da ni da shi”
Ummi ta goge ƙwallar gami da cewa “Allah ya yi wa rayuwarku Albarka ya kareku daga dukkan wani sharri ko na mutum ko na wata halitta”
Amsawa ya yi da “Amin” sannan ya miƙe ya janyo Hannun Jana ya kawota gaban Ummi ya ce “Gata Ummi ita ce wadda zan Aura ban tawo ba sai da na smmu izinin Aurenta”
“masha Allahu” Ummi ta faɗa gami da janyo Jana jikinta cikin kulawa. “Allah ya sanya Alkairi ya inganta rayuwarku”
Jannah ne ya katse musu magana da cewa “wato Ummi kin ga babban ɗa kin manta da Auta ko?”
ta yi dariya gami da cewa “kai Do Allah, zo ka zauna ka yi mana tsaye aka”
ya ce “ai fa shikenan na samu wata kishiyar”
dariyar da Natee ta ke yi ce ta sa ya maida kallons gareta, harara ya zuba mata gami da cewa “baki kamar an yanka gwanda ”
duka suka sa dariya amma ban da Natee da ta zumɓuri baki.
Arsalan ya zauna kusa da ita ya na cewa ‘ƙyaleni da shi Ƙanwata ai shi yanzu ya na tsaka tsaki kece Autar ni kuma Babba”
Murmushi ta saki lokaci ɗaya ta ji hankalinta ya kwanta da yayan nata duk da ba ta san shi ba amma a yanzu da ta ganshi ta ji sonshi har cikin ranta.
Yaya Hassana ta ce “Barka da dawowa Yaya”
tattausan murmushi irin na manyance ya yi gami da cewa “Allah sarki tagwayen Hajiya kun yi shiru abinku, har yanzu ba ku da surutu kenan ba irinmu ba, na sameku lafiya ya iyalinku? Jannah ya sanar da ni cewar duk kun haifa masa Ƴa-ƴa”
Suna murmushi Ya-ya Husaina ta ce “Duk ga su nan ba Ka lura da su ba”
ya ce “Allah sarki, sai na ga komai ya canja, kai gaskiya duk wanda ya bar gida gida ya barshi, Mubin Mubina ku zo nan”
Ya-ya Hassana ta ce “Kasan sunansu dama?”
ya ce “Eh Jannah ya gaya min ai”
hira suka shiga yi ta yaushe gamo, Arsalan ya na basu labarin irin gwagwarmayar rayuwar da yasha kafin ƙafafunsa su tsaya ya zama wani bayan ya bar gida.

Washe-gari.
Har gida Hajiya Murja da Hajiya Saratu su ka zo wai Sun zo yi wa Jannah barka da dawowa, Hannu bibbiyu Ummi ta karɓesu ba tare da ta nuna musu komai ba, da za su tafi suka jaddada mata ranar Litinin za’a zauna a Kotu dan ci gaba da shari’a yau saura kwana Huɗu kenan, Allah ya kaimu kawai Ummi ta ce musu da haka su ka yi sallama suka kama hanyarsu.

Arsalan da Alamee da Sufee da Jannah suna zaune su na tattaunawa dan shawo kan lamarin kowa ya na tofa albarkacin bakinsa shi dai Arsalan ya yi shiru ya na saurarensu.
Sufee ne ya ce Ya-Ya ka yi shiru mu na ta shirmenmu”
sai a lokacin ya gyara zama gami da cewa “Ai na ji aikin naku na manya ne shiyasa na tsagaita, waye mafi sauƙin kai a cikin Yayyen naka Jannah?”
da sauri Sufee ya ce “Jaafar ko??”
Jannah ya ce “Kai ware!!, Abdul ya fi sauƙin kai nesa ma ba kusa ba, shi Jafar kawai takunsa ya iya dama Ummansa ta fi Shu’umanci ai”
Arsalan ya ce “Ya yi kyau, dashi za mu yi amfani wajen gano gaskiyar abin da ya faru”
Jannah ya ce “Ya-Ya kayi haƙuri fa amma Abana ya sanar min kafin ya cika, ina ta ɓoyewa ne sabi da har yau ban dena ƙaunar ƴan-uwana ba, Ummanka Hajiya Saratu itace jagorarsu, Yayyena da kansu suka kashe Aba kuma su ka sa wani saurayin Ya-Ya Fauza da saɓani ya taɓa shiga tsakanina da shi ya yi wa Natee fyaɗe, sun aika da Mota Islamiyyar su Natee sun ce na ce a ɗauketa, su ka kira Abana su ka gaya masa ba ni da lafiya ya zo gida, sannan su ka kirani na je wata unguwa na ɗakko Natee, na je ban ganta ba, shi ma Abokina su ka kira shi su ka ce ya je wata unguwar daban, sai daga baya suka ƙara kirana wai na dawo gida Abana ya na nemana, kafin na zo sun yi masa raunuka sosai, suka soka wata wuƙar a ƙirjinsa da haka suka laɗɗafa min sharri, abin da Abi ya iya faɗe kawai ya sanar min su ne su ka aikata sai kuma ya ce ɗan-uwana zai zo ya temakeni sai kuma amanar Ƴan-uwana mata ya bani”
idanun Arsalan sun kaɗa sun yi jajir sabi da zafin da zuciyarsa ta ke yi, da shi kaɗai ne a gurin ba abin da zai hana shi sakin kuka ko zai ji Zuciyarsa ta yi sanyi, ba ya son karya Zuciyarsu shiyasa ya yi ƙoƙarin dannewa.
numfasawa ya yi kafin ya ce “Ina son haɗuwa da Abdul”
Alamee ya ce “Taɓ ba ya bari mu haɗu”
Arsalan ya ce “Zan ji da lamarinsa zuwa gobe, amm.. da waɗanne mutane suke amfani wajen aikata wata ɓarnar kuma a ina suke? ina son bayanin komai daga yanzu zuwa dare”
daga haka ya tashi ya nufi Bedroom ɗin da aka ware masa.

kaiwa da kawowa ya ke yi a tsakar Ɗakin Zuciyarsa na tafasa, idan ya tuna halayen ƴan-uwansa da Mahaifiyarsa sai ya ji kamar ya mutu dan baƙin ciki, ya sha wa kansa Alwashin tarwatsa su da tona asirin duk wata ɓarna da suke aikatawa kuma zai tsaya a tsaye dan ɗaukar mataki akansu.

Washe-gari…

Abdul ne zaune kan ɗaya daga cikin kujeru biyun da suka zagaye wani ɗan-madai-saicin Tebur, ido kawai yake bazawa dan ganin ta inda wadda yake jira za ta ɓullo.
bayan wani lokaci Arsalan ya iso gurin fuskarsa a rufe da farin Hirami ya yi rawani da shi, ba tare da ya yi magana ba ya zauna tare da kafe Abdul da ido rabonshi da ganinsa tin bai gama yin wayo ba gashi yanzu har ya yi girman da ya zauna jiran budurwa”
hankalin Abdul kwata-kwata bai yo kan Arsalan ba ya na can kalle-kalle.
numfashi ya ja ya sauke sannan ya yi masa sallama, ya amsa a ɗan fizge, Arsalan ya ce “Ka na jiran wani ne??”
kallon sama da ƙasa Abdul ya yi masa ya ce “Na ɗauka shishshigin naka na iya zama akan kujerar da ba taka ba ne ashe har da son shiga sharafin da bai shafeka ba”
Arsalan ya buɗe fuskarsa ya na murmushi ya ce “Ta na da uzuri shi yasa ta ce ni na zo”
Ido Abdul ya tsira masa cike da mamaki, bayan Haisam da Jannah yau ya ga Mutum na uku da ya ke bala’in kama da Mahaifinsu, tunanin waye wannan ya shiga yi.
Arsalan ya katse masa tunanin da cewa “Ba buƙatar ka yi dogon nazari ƙanina, ni ne dai yayanku Babban cikinku wato Muhammadu-Mustafa, sanadin kisan gillar da ku ka yi wa Mahaifinmu gashi yau na dawo gareku, yanzu ka ganeni? ko dama ba ka yi wayon da za ka sanni ba?”
girgiza kai Abdul ya yi cikin sanyi ya ce “Na sanka, wallahi ni ba ruwana duk abin da suke yi ban cika shiga ba kuma ka tambayi Jannah ma zai gaya maka”
Arsalan ya ce “Haba yaro kwantar da hankali mana, amma nasan kasan duk abin da su ke yi da wanda su ka yi ko? to ina so ne ka baiyana min gaskiyar komai sai ka ce-ci kanka daga hukuncina dan kuwa ba ɗaya da zan ƙyale a ciki har da kai idan ba ka gaya min gaskiya ba”
jikinsa ne ya hau rawa ya yi tsilla-tsilla da idanu, ya na matuƙar tsoron matakin da za su ɗauka akansa idan ya tona musu asiri dan haka ba ya jin zai iya faɗe”
Arsalan ne ya katse masa tunanin da cewa “Abdul ina ganin mutuncinka hasalima na zaɓeka ne a matsayin ɗan-uwana sabi da nasan kana da sauƙin kai, amma a yanzu idan ka yi min gardama zan sa ka baiyana gaskiyar cikin uƙuba, imanina ya gushe ba zan yi duba da jinin da muka haɗa ba, tin da akan duniya za ku iya kashe mana Uba ai kuwa ba irin azabar da ba zan yi muku ba”
da kyar Abdul ya iya tattare busashshen yawun bakinsa ya haɗiye sannan ya ce “Ina jin tsoron abin da za su yi min ne amma wallahi nima ina neman hanyar da zan gyara kuskurena, Aba bai yi mana laifin komai ba ya na iya bakin ƙoƙarinsa dan fita haƙƙin kowa haka Jannah shi da ko yatsa aka sa masa a baki ba zai iya ciza ba amma mu ka zalumcesu, in dai za ka hanasu yi min komai idan na faɗa na yarda”
Arsalan ya murmusa gami da cewa “Wanda ya yi min laifi shi nake yi wa hukunci, indai har na tabbatar gaskiya ka gaya min ba abin da zai hanani ɗaukeka na maida ka bayana duk ƙurar da aka watso ta fara sauka akaina, kamar yadda na sha Alwashin zamowa Jannah Bango kai ma haka zan yi maka dan kai ma ƙanina ne, ina jinka”
sai da ya ɗan mumfasa sannan ya ce “indai akan kisan Alhaji ne ina da cikakkiyar shaida, na kunna Camerar wayata na ajiyeta a lokacin kuma ta ɗauki komai sannan na adana bidiyon ta yadda ba wanda zai sani, kuma na yi ne dan nasan a gaba zai yi min amfani ta kowace hanya, idan ka na so ga wayata ma ka tafi da ita duka, amma dan Allah ka cewa Jannah ya yafe min duk abin da na yi masa ina bin huɗubar Ummata ne sai daga baya na gane kawai za ta ɗorani a keken ɓera ne shi yasa na ji na tsani duk halayen nan nasu”
Arsalan ya jinjina kai gami da cewa “Umm!!! to ba komi na gode da hakan, amma bayan haka sai me ka sani?”
Abdul ya ce “duk wanda ba ya goyon bayan abin da suke aikatawa cireshi suke daga sabgarsu kamar yadda aka ware su Ya-Ya Hassana da Ya-Ya Faiza duk sun tsanesu, nima da su ka ga na dena goyon bayansu sai su ka dena yin komai da ni, iyakar abin da na sani shine ba iya mutum ɗaya suka cutar ba, suna harkar baƙaƙen kuɗi da mugayen ƙwayoyi, sannan suna da yara ƴan fashi”
Arsalan ya ce “In na fahimta dai-dai kana nufin manyan tantirai ne dai”
Abdul ya ce “Shaiɗanu ma kuwa, ni rasa ma abin da za su yi da kuɗi nake yi, wai sai su ce in kana da kuɗi ba wanda ya isa ya nuna maka yatsa shi yasa suke neman kuɗi ta kowace hanya”
Arsalan ya ce “Meye ma cikakken sunanku?”
Abdul ya ce “Ni dai Abdulmajid Alhassan amma Abdul ake kirana”
Arsalan ya ce “In kana son ganin Wuskha ka bari komai ya tafi min dai-dai har Aurenta ma zan iya baka, ƙanwar wadda zan Aura ce, bayan nan za ka ganta za ka ga Jannah sai ku yi magana, daga nan ma shi kenan kai ma ka zama ɗan Ummi”
Murmushi Abdul ya yi ya ce “na gode”
Arsalan ya ce “Zan koma inda na fito, bani bayanin wayar taka”
miƙa masa wayar ya yi bayan ya dawo da bidiyon sarari.
da haka su ka yi sallama kowa ya yi nashi guri.

yau ta kasance ranar shiga Kotu.
Hajiya Saratu da Hajiya Murja sun gama shirin komai lokaci kawai suke jira.
suna zaune sun yi ɗame-ɗame su na jiran Haisam ya zo da mota ya ɗaukesu, Fauza ce ta shigo da gudu ta na cewa “Mun shiga uku mun lalace, Hajiya!!!! Hajiya ku kunna TV ku ga abin da ke faruwa”
yadda take maganar cikin tashin hankali ne ya sa Bomboi ya yi saurin miƙewa ya na cewa “Me yake daruwa ne??”
Hajiya Murja ce ta kunna ta na faɗin “Allah ya sa abin kirki ne ma ta ke yi wa wannan ruɗe….”
kasa ƙarasa maganar ta yi sabi da ganin bidiyon da Abdul ya bawa Arsalan ya na yawo a kan fuskar TV ɗin.
ba abin da aka rage a cikin abin da su ka aikatawa Aba lokacin da su ka kasheshi, bayan shi aka shiga hasko yaran su da suke amfani da su wajen yaɗa ta’addanci su na yin bayanin irin mugayen laifuka da ɓarnar da su ke yi.

Kururuwa Hajiya Murja ta yi ta durfafi Hajiya Saratu da duka ta shaƙeta tamau a cewarta ko ma meye ita ta janyo.
ƴaƴan Hajiya Saratu kuwa ganin za’a kashe musu uwa ga baƙin cikin abin da ya faru su ka fara lubiɗar Hajiya Murja da duka.

cikin ƙan-ƙanin lokaci Falon ya runguntsime da faɗa da bala’i har ta kai ga sun yi wa juna raunuka.
Hajiya Murja duk da ta jikkata jaraba ta hanata haƙura, fita ta yi ta samo wata lafiyayyar Wuƙa ta shigo Falon da ita, kai tsaye kan Hajiya Saratu ta yi dan ba ta da burin da ya wuce ta rabata da duniya, Sultan ne ya ankare da ita kafin ta ƙarasa wajen Hajiya Saratu ya murɗeta ya ƙwace wuƙar ba tare da wani tunani ba ya bubburma mata ita a gefen wuyanta.
ƙasa ta zube ta na shure-shure da make-make gami da wani irin kakari mara daɗin ji.
idon kowa ya dawo kanta sai dai an rasa me zuwa inda take a haka har ta yi laƙwas alamar rai ya yi halinsa.

ganin ta mutu ya sa ƴaƴanta suka ƙara durfafar Ƴaƴan Hajiya Saratu.
suna cikin wannan Badaƙalar matakan tsaro suka afko cikinn gidan ta ko’ina. ba wanda ya samu damar guduwa duk aka kamesu.
Hajiya Saratu kuwa tin da ta yanke jiki ta faɗi sai kinkimarta a ka yi ba baki ba rabin jiki.

Kai tsaye gidan fursuna aka wuce dasu kafin a yanke musu hukunci.
labari ya cika ko’ina lungu da saƙo, kowa Alawadai ya ke da tofin Alatsine akansu.
Bayan kwana biyu aka yankewa kowannensu hukunci.
dukansu hukuncin kisa aka yanke musu domin rage yawan ta’addanci. Fauza da Jafar kawai aka bari a gidan Fursuna su ma ɗaurin ba beli. duk yaransu masu taya su an kama su an yi musu hukunci dai-dai da abin da su ka aikata.

“Alhamdulillah”
Arsalan ya faɗa gami da sauke ajiyar Zuciya, ci gaba ya yi da cewa “Allah ya yarda yau Ƙanina ka yi free”
Jannah ya ce “Na gode da temakonka da ba ka zo ba da ban san yadda zan yi ba”
Arsalan ya ce “Godiyar da za ka yi min itace ka manta da su kawai mu ci gaba da rayuwarmu, nasan zama za ka yi kana tunaninsu”
ƙasa ya yi da kai ya ce “Ba zan yi ba tin da nasan za ka mantar da ni komai”
Arsalan ya murmusa gami da cewa “Mu je ka ci abinci”
da “To” ya amsa sannan suka shige cikin gida.

bayan kwana biyu.
Zeety ce durƙushe a gaban Jannah ta na kuka wurjanjan, roƙonsa ta ke yi akan ya yi haƙuri akan abin da ta yi masa sannan indai ya yarda ta amince za ta gyara halinta in zai sota.
Murmushi ya yi gami da cewa “Allah sarki, ni ai a haƙure nake, na yafe miki, amma ba na son ƙara ganinki don Allah kar ki ƙara zuwa inda nake ko inda ki ka san za mu haɗu”
daga haka ya miƙe gami da cewa me gadi ya buɗe mata ƙofa ta fice, cikin gida ya koma cike da mamakin fitsara irin ta-ta.

 

Bayan watanni Biyar.

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[11/22, 8:00 AM] INDO CE: *D-Y*
40

END

Shirye-shiryen bukukuwa ake yi ta kowane ɓangare, gidan su Zuhra haka gidan Ummi haka gidansu Alamee, ko’ina kujiba-kujiba ake yi.

Cikin sanɗa Jannah ya raɓewa inda su Ya-Ya Hassana suke suna ta famar surutu har ya wuce Husna ta ƙwala masa kira cikin sigar zolaya ta ce “Ango!!! wannan ai rashin mutunci ne Fisabilillahi mu na zaune sai ka wucemu ko kallo ba mu isheka ba? yanzu ka na yi mana haka ta ya Matar taka za ta dinga kulamu?”
sosa ƙeya ya shiga yi cike da kunya gami da takaicin yarfa shin da ta yi, har ga Allah kunya ya ke mugun ji gashi gidan nasu ya cika maƙil da baƙi daga na Nijar har Dangin Aba har da waɗanda bai sani ba.
Zainab ce ta shiga zancen da cewa “Ke kuwa Husna ya na jin kunyar tamu amma sai kin tone shi?”
Ya-Ya Fa’iza ta ce “Ke a wa zai ji kunyarki?, Jannah kallesu da kyau ba’a kunyar abokan wasa duk wadda ta tanka na baka dama ka wanke min ita suɓul”
in banda Murmushi Ba abin da ya ke yi dan kuwa ba zai iya ce musu ƙala ba, ganin surutu da ce-ce-kucen ya koma kan Ya-Ya Fa’iza ya sa ya yi saurin wucewa in da yake son zuwa.
Hayaniyar da ta cika ɗan-madai-daicin Falon ta hana su jin sallamar da yake yi dan haka ya ƙarasa ya nemi gurin zama kusa da Arsalan sai ƙara sauke rumfar ido yake yi”
ganinsa sukuku ya sa Arsalan ya ɗauke hankalinsa daga kan Abokan nasa ya maida kan Jannah, cike da kulawa ya ce “Lafiya ka ke??”
kwantar da kai ya yi akan kafaɗar Arsalan ya na cewa “na gaji ne gashi gidan ko’ina mutane”
Arsalan ya ce “Ka yi haƙuri to, lokaci ne da an gama bikin shi kenan ba me takura maka, i yanzu ma ka na can tare da Queen ɗinka”
wani sassanyan murmushi ne ya suɓuce masa ya rintse ido ya na turo baki alamar shagwaɓa.
Arsalan ya ce “Ohh!! Me kunya, ba ka ci abinci ba ko? mu je na haɗa maka ruwan wanka ka yi sannan ka ci abinci ka kwanta”
noƙe kafaɗa ya yi alamar baya so.
Arsalan ya ce “Daure dai, maza gaya min me za ka ci? ko dai in kaika wani gurin ka huta kai kaɗai?”
girgiza kai ya sake yi kafin ya ce “Ni fa Bacci kawai nake ji”
Miƙewa Arsalan ya yi hannunsa riƙe da na Jannah ya ce “Tashi to”
Tashi ya yi suka nufi Bedroom. kamar wani Ƙaramin yaro haka ya dinga zubawa Arsalan shagwaɓa, shi kuwa sai tarai-rayarsa ya ke yi, ya san halinsa tin ya na yaro sai da lallami da lumana dan ba ƙaramar shagwaɓa ya ke zubawa Aba ba, yanzu kuwa da babu Aba dole shine zai yi masa komai dan wata rana sai labari.

Kwanaki shida aka ɗiba ana shan shagalin bukukuwan a ranar na bakwai aka ɗaura Aure.

Abi da Ummi
Jannah da Zuhra
Alamee da Jannatee
Arsalan da Jana
Ukasha da Zahra

washe-gari aka yi Dinner daga nan Amare sai ɗakinsu.
Ummi a gidanta Sabo da Jannah ya Mallaka mata ta tare.
Arsalan da Jannah da Alamee kuwa maƙoftan juna ne amma akwai ƴar tazara tsakanin su biyun da Alamee, Ukasha kuma ya na daga gefe shi kaɗai.

Taro ya tashi lafiya an yi komai cikin ƙayatarwa da burgewa gwanin sha’awa.

“Queen!!!”
Jannah ya kira sunanta cikin tattausar murya me saukar da nutsuwa, sai da ta ja numfashi ta sauke kafin ta amsa.
ya yi murmushi gami da cewa “Magana da kyar haka? meke faruwa?”
ya yi maganar cikin sigar zolaya, turo baki ta yi cike da shagwaɓa ta ce “Ba kai ne ba?, Zan gayawa Ya-Ya fa”
da sauri ya ce “A’a na dena maza ki yi baccinki na dena tsokanarki”
ya yi maganar gami da gyara mata kwanciya akan faffaɗan ƙirjinsa.
sassanyam Murmushi ta saki wani daɗi ya na ratsata har cikin rai, wasu ƴan siraran hawayene suka fara biyo fuskarta, kamar da wasa gashi ta zama Matar Jannahn da har ta yanke ƙauna daga gareshi, Allah me yadda ya so, ba ta taɓa tunanin wannan ranar ta farin ciki a rayuwarta ba.
tunanin abubuwan da suka faru a baya ya fara dawo mata, ba tare da ta sani ba har kukanta ya yi ƙarfi harda shashsheka.
sai da ta ji ya na yi mata magana cikin kiɗima sannan ta dawo haiyacinta, ta tsayar da kukan kafin ta ce “Tunani kawai na ke yi fa”
huci ya furzar kafin ya ce “Na ji tsoro sosai, dan Allah karki kuma yin tunanin abin da zai sa min ke kuka, lokacin da za mu rayu cikin farin ciki ne wannan, ina son na baki farin ciki daga yanzu har ƙarshen rayuwata My Queen!”
Ta na Murmushi ta ce “Na Tuna irin rayuwar da mu ka yi a baya ne tamkar babu wannan ranar, kar ka damu in Allah ya yarda in dai ina tare da kai ba abin da zai sa ni kuka, kaine cikamakin farin cikin rayuwata kuma ina tare da kai ka ga idan na yi kuka to na shagwaɓa ne”
ya murmusa gami da cewa “Har ba na son tunowa da baya dan kuwa na cutar da Zuciyata, ina ƙara neman Afuw..”
da sauri ta ɗora hannunta akan bakinsa gami da cewa “Aff!! Kai kam ba bacci za mu yi ba ne?, ka yi mana Addu’a sannan aga wanda zai riga yin bacci”
Tattausan Murmushi me ratsa Zuciya ya saki gami da cewa “Allah ya tasheki cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali Matata”
ta amsa da “Amin” Addu’o’i ya shiga jerowa har zuwa lokacin da bacci ya ɗaukeshi lokacin Zuhra har ta Haure ƙasa a nata baccin.

Zaune take a gaban Madubi ta na ƙoƙarin yin kwalliya, ta rasa ta inda za ta fara ta ɗauki wancan ta ajiye ta ɗauki wancan, ganin kamar Mutum a cikin Madubin ya sa ta yi saurin juyowa, ya na tsaye hannunsa harɗe a ƙirjinsa ya zuba mata idanun ta cikin Madubin ya daɗe a gurin yana kallonta ba tare da ta sani ba duk nutsuwarta ta na ga abin da take yi.
Murmushi ta yi gami da cewa “Ka bani tsoro fa, Yauwa kwalliya na ke son yi kuma na rasa ma ya zan yi”
ƙarasowa ya yi inda ta ke ya dafa kafaɗarta cike da ƙauna ya ce “Kalli Madubin nan ki gani”
ta ce “Mene?”
“Wata kyakkyawar Halitta ce, me matuƙar haske da walƙiya tamkar Tauraruwa, idanunta tamkar Farin wata sabi da kyawun Kallo Murmushinta maƙura wajen ɗaukar hankali da saukar da farin ciki da nishaɗi, Ƴar-baiwar Halitta wadda samun kamarta a Duniya Mawuyacin Abu ne, Mutum Ɗaya Allah ya bawa damar Mallakarta, ya kasance Mutum mafi sa’a a Duniya haka yake ɗaukar kansa, Kalli ki gani za ki tabbatar da abin da nace”
sai a lokkacin ta samu damar ɗauke idonta daga kallon da ta ke yi masa ta lumshesu tana murmushi ta buɗesu akan Madubin, Murmushinta ne ya ƙara faɗaɗa har Haƙoranta suka baina, cike da shauki ta ce “Wai da gaske ni kyaklyawa ce??”
durƙusawa ya yi kan ƙafafunsa ya riƙo hannunta cikin tsananin so da ƙaunarta ya ce “Asalin kyakkyawar Mace itace wadda ba ta taɓa yarda ita kyakkyawa ce bare har ta yabi kanta, ko da duk Duniya za ta faɗa ba lallai ki yarda ba, amma ina so ki kwatanta yarda da ni a karon farko, Ke kyakkyawa ce, Kyawu na haƙiƙa na gaskiya, kin tara Asalin Cikakken kyau Queen kina da kyawun Fuska sannan ki na da kyakkyawar Zuciya, SARAUNIYA ME ZUCIYAR ZINARE!!! wannan shine asalin sunanki My Queen!!”
Ta kasa rufe baki sabi da Murmushi, daɗi ne yake ratsata ta ko’ina, zamewa ta yi daga kan kujerar ta rungumeshi tsananin ƙaunarsa ke ƙara ratsa dukan ƙofofi da saƙo-saƙo na Zuciyarta, ƙanƙameshi ta ƙara yi tamau gami da cewa “Ina sonka Fiye da So Mijina, Ina Ƙaunarka fiye da kaina da komai na duniya Zan rayu da kai har Lokacin Mutuwata, kar Allah ya kawo tsautsayin da zai ratsa tsakanina da kai kyakkyawan Mijina”
Hannayensa ya sa ya zagayeta a jikinsa ya rungumeta gami da cusa fuskarsa cikin wuyanta, cikin tattausar murya me ratsa Zuciya da sanya Nutsuwa ga me sauraronta ya ce “Bakina ba zai iya fasalta irin tsananin ƙaunar da nake miki ba, kin zamo komai na Rayuwata, Farin ciki da samun kwanciyar hankalina shi ne kasancewarki lafiya Abar Ƙaunata, Ina sonki fiye da raina da rayuwata Matata”
Ajiyar Zuciya ta sauke ta na ƙara lafewa a jikinsa gami da lullumshe ido.

Bayan Wani Lokaci.
Rayuwa su ke cikin farin ciki da kwanciyar hankali cikin tsantsar so da kulawa ga juna,
Kowa ya na nuna wa Jannah da Zuhra soyayya sosai da sosai. A ɓangaren Natee ma Alamee ya riƙe Amana ba ya barinta da damuwa ko kaɗan bare ya bari ta yi kuka, daga wajen danginsa ma tana samun ƙauna da kulawarsu ba tare da wata matsala ba, a yanzu haka ta na ɗauke da Juna Biyu.
cikin Lumana Rayuwar Arsalan da Jana take tafiya duk wata shiririta ya ajiyeta a gefe ya ɗauki akinsa na Lauya ka’in da na’in tin daga kan Jannah ya zama Lauya me kare gaskiya tare da baiyanar da ita kuma ya durƙusar da ƙarya da masu yinta.

Bayan Shekaru Biyar.

Natee Ƴaƴanta biyu duk mata Aaminatu da Zainab sunan Mahaifiyar Alamee Ana kiransu Ameera da Inaya.

Zuhra haihuwarta ta farko ta haifi Mace mai sunan Mamminta, Maimunat ana kiranta Moon a ta biyu aka smu tagwaye, ba’a canja musu suna ba amma ana kiransu Abi da Aba.

Jana, Haihuwarta ɗaya Namiji Arsalan ya raɗa sunan ƙaninsa Muftahul-jannah, ya yi masa laƙabi da Akhee.

Abdul ma ya yi Aure shekara ɗaya kenan Matarsa ta na da ciki ba ta kai ga haihuwa ba.

yau duk suna gidan Ummi har su Ya-Ya Fa’iza da iyalinsu, yara sai tsalle-tsalle su ke yi manyan kuwa hirarsu suke sha.
Abi ne ya yi sallama, suka amsa gami da yi masa sannu da zuwa, Su Abi Ƙarami iyayen fitina suna ganinsa suka yo kansa gaba ɗaya suka zagayeshi ma su yi masa surutu su na yi masu tambayarsa su na yi.
sai da Arsalan ya yi musu tsawa sannan suka ɗan nutsu har suka samu damar gaishe da Abin, cike da farin ciki yake amsa gaisuwar ƴaƴa da surikan nasa ya na binsu da sa Albarka.
Ummi ce ta numfasa kafin ta ce “Allah sarkin Baiwa, yau ga Aaminatu da Jikoki Masu Albarka har da masu tayon aiki da abokan hira”
Abi ya yi dariya ya ce “Shi yasa ake cewa tsammaci abin da ba kai tsammani ba, ba mu yi zaton hakan ba gashi kuma mun gani, Alhamdulillah, Allah ya yiwa kowa Albarka”
da “amin” suka amsa kafin Jannah ya ce “Wai fa da tini na mutu ko??”
Arsalan ya ce “Rufe min baki da labarin bara anci waken nan naka, maza ka ce Alhamdulillah”
Ya saki Murmushi gami da cewa “Allah shi ne abin godiya, ALHAMDULILLAH!!!”

 

 

(Alhamdulillah!!! anan na kawo ƙarshen wannan labari me suna DOGON YARO, Na godewa Allah da ya bani ikon fara shi lafiya na gama lafiya cikin kwanciyar hankali, ina miƙo Dubu Dubun gaisuwata a gareku Masoyana haƙiƙa ina Alfahari da ku kuma kullum kuna raina)

SAI NA JI KU A LITTAFINA NA GABA MAI SUNA *(BAYA BA ZANI)* DA YARDAR ALLAH, INA FATAN ZA KU NUNA MIN ƘAUNARKU NINKI-NINKI.

*(Sarat Alƙasim, (MAMAN NUSAIBA) Gaisuwa ta ban girma a gareki, Allah ya saka miki da mafificin Alkairi, ina matuƙar godiya a bisa ƙoƙarinki akaina, Allah ya yi miki jagora a cikin lamarinki, Allah ya kareki daga dukkan wani sharri, Allah ya yi riƙo da Alƙalaminki Ya-Yata ta kaina, daga Ƴar ƙaramar Ƙanwarki INDO CE)*

 

*MOONASH!!!!!*
Alƙaluma Huɗu tamkar da dubu.
Ina Matuƙar ƙaunarku Aminai na.
*AYUSH*
*SHAAHD*
*MAIMOON*

 

Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]