[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 31 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Bayan yayi wankane ya shirya tsaf, bayi breakfast sannan ya wuce kauyen su sabreen ciki da tunaninta a ranshi harya isa. Wayan hafsat ya kira tace to suna zuwa, basu jimaba suka fito dukkansu sunyi wanka sunyi kyau😘, tunda suka fito suhail yake kallon sabreen a sace yana maganan zuci😒inama da abinda ya faru a mafarkina zai faru yanzuma, sabreen ne ta katseshi da cewa sannu da zuwa uah suhail, mirmushi yayi yace yawwa sabreen ya kuke sukace lfy lau itada munira😊, yace ya mutanen gida, sukace lfy lau, sabteen tace ya mum? Uace mum lfyanta k’alau tayi kewarki, mirmushi tayi tace nima nayi kewarta wlh😊. Hafsat ta gaisheshi cike da so, ya amsa yana mata murmushi yace toya kwanan garin, tace wlh dad’i yah suhail kamar in sake kwana😜, yace to shikenan bari in koma😉, dariya sukayi dukkansu sannan yace kaka fa? Sabreen tace wlh sun shiga gari amma dai inaga sun kusa dawowa, ok yace sannan sukace bisimillah ka iso, yace a’a tfy zamuyi dama nazo d’aukantane. Hafsat tace yah suhail girki na musamman fa sabreen ta maka na dambun kuskus, suhail ya kalli sabreen yace to shikenan muje, gaba sukayi ita da munira suka barsu a baya har suka shiga ciki ya gaisa da mmn munna sannan suka isar dashi zauren baba. Wani yarone yazo yace wai ana kiran munira a waje, munna tace to kaje kace ina zuwa, sannan tace hafsat abbakar ya iso zomuje, hafsat tace ok muje sannan tace yah suhail bari inyi magana da angon munira akan shirin bikin ina zuwa, ok yace ta ita, azuciyarsa kuwa dad’i yaji yace zansamu inyi magan da sabreen. Bayan sabreen ta kawo mishi abincine seta zauna tana zuba mishi abincin yanata kallonta yana tuna mafarkinsa😊, yah suhail bisimillah ta ajiye mashi a gabanshi, murmushi yayi yace nagode sannan ya faraci suna kallon juna, wani sabon k’aunarshi ne yake shigan sabreen seta sunkuyar da kanta k’asa, suhail yace kunyi waya da abokina? Tace eh, yace gaskya naji dad’in wannan dambun nagode sosai, murmushi tayi tace akwai wani a kula seka tafi dashi, yace a’a ina kunyan mama, dariya tayi tace wlh bakomai dama nasamaka dewa dan nasan mum ma tana so, yace to shikenan sabreen? Tace na’am batare data kalleshiba, yace menene “SABSU”? Tace zan turo maka da ma’anarsa a waya, yace noo nidai ki gayamin anan, tace to ina zuwa sannan ta koma d’aki ta d’auki wayanta ta mishi texs.
“SABSU” yana nufin sabreen nd suhail, tunda bazan samekaba wannan suna zai zauna a raina har abada kuma dashi zan dinga kiranka a raina😔😔.
Bayan suhail ya gama karanta texs d’inne seya tsunbaci texs d’in nata tare da rufe idanunsa yana mai tausayamusu dukkansu😔. Da sauri ya mayar da phone d’insa aljihu danyaji shigowar hafsat gidan, gunsa ta wuce tace kayi hakuri yah suhail nabarka kai kad’ai yace bakomai ina abbakar d’in? Hafsat tace yana waje yana jiranka dan munce mishi kana cin abinci. Suhail ya mik’e yace mujeto nagama, tare suka fita yayiwa mama sallama alokacinne sabreen ta goge kwallan idonta ta fito tace yah suhail har zaka tafi😊, zan tafi sabreen sannan suka fito dukkansu. Bayan sun gaisane sukayi hira sosai kamar sunsan juna sannan sukayimusu sallama sabbreen taje ta d’auko musu kuskus din suka tafi suna kewar hafsat itama haka.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]