[Advertisements⬇️]

SAKACINA KO HALIN MAZA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Duk yadda Juwairiya ta so ta kwantar da hankalinta akan mutuwar mahaifinta, abin ya ci tura!Da ta tuna mugun nufin Baba Sani sai ta ƙara rikicewa,irin yadda ta nuna na rashin tawakkali ya so ya fara tunzura Mama tun ta na ba ta haƙuri, ta taushe tashin hankalinta domin Juwairiya ta natsu amma ta kasa,sai uhu take ta na furta sunan Baba.

Ganin irin abin da take yi sai Mama ranta ya ɓace matuƙa,ta saki hannun Juwairiya dake son a kyaleta ta fita da gudu kamar wata kamun aljanu tace.”Ku kyaleta ta yi duk abin da ta ga dama,ban san baki da tawakkali ba sai yanzu Juwairiya!Na ɗauka saboda ƙarfin imanin ki ni zaki din ga ba ma haƙuri,tare da jawo min aya akan na ɗauki haƙuri domin duk mai rai mamaci ne.”

Juwairiya ta duƙa tare da ƙara sakin wani kuka dai-dai lokacin da Baba Sani ya ƙaraso gun ta ya na mata wani kallo,mai kama da tausayi ko akasin haka tare da sausauta murya yace.”Ku kyaleta rashin mahaifi abu ne mai ciwo na tausaya miki matuƙa,domin hakan da kika yi sai kika tuna min lokacin da mahaifin mu ya mutu ina kuka mahaifinki Yaya Ahmed shi ya dinga lallashina!”

Sai ya saka kuka ya na faɗin.”Allah Sarki!Allah ya jiƙan ka Yaya.”Ya nufo Juwairiya dake kuka tamkar ranta zai fita,da nufin zai riƙe ta ya lallasheta.

Da sauri ta matsa ta na wani irin kuka kamar za ta shiɗe,ja da baya take kamar ta ga dodo.Ganin haka sai ya kyaleta a ran sa kuwa murmushin mugunta yake mata.Bayan an gama cuku-cuku aka ba su gawar Baba da har ta fara sandarewa.

Hankalin Juwairiya bai ƙara tashi ba sai da suka dawo gida ta ga inda yake kwanciya,wani ƙarin abin tausayi tun da Ibrahim ya ji mutuwar mahaifinsa ya ɗauke numfashi ko motsi ba ya yi.Lamarin sai ya jagule ma Mama ta rasa in da za ta sa kanta ta ji sanyi,ga wani irin kuka da Juwairiya take yi taƙi ta yi shiru.

Bayan an yi wa Baba sallah aka kai shi gidan gaskiya gidan da ko wane bawa yake da gadon sa domin ba’a wahala gurin mallakar sa.Cikin dare Juwairiya ta na kwance ta kasa bacci!A ranta ji take kamar mahaifinta kashe shi aka yi musamman yadda ta ga Baba Sani bai nuna tashin hankali game da mutuwar sa ba.

Ta na lura da shi har shinkafa ya siyo a dafa ma ƴan zaman makoki,wanda ko mutuwa za su yi ba zai taimaka musu da shi ba.

Kwana ishirin da rasuwar Baba amma har yau sun kasa manta shi a kullum ta ranar duniya sai sun yi kukan rashin sa,musamman Juwairiya da yake sokanar ta duk san da zai fita ya na cewa Allah ya nuna mi shi ranar auren ta,a she ba shi da rabon gani.

A lokacin da Baba ya yi arba’in Juwairiya ta saka ma ran ta za ta yi fito na fito da Baba Sani duk abin da ya shirya a shirye take ita ma.Tun lokacin  da Baba ya rasu bai ƙara shiga sabgar ta ba,duk da cewar ba ganin ta yake ba don ba ta fita ko ina.

Ganin ba su da cin yau bare na gobe sannan Mama ita ma kwana biyu ba lafiya take da shi ba,ya sa za ta gaya ma Mariya ta nema mata aiki ta din ga yi don da yunwa ya kashe ta gara dukan Baba Sani ya kasheta ita kaɗai.Ta san ya na hana su abinci ne don kawai ya cutar da rayuwar su ko ya samu biyan buƙatar sa,amma ba wai don ba shi da kuɗi ba tunna aikin gwannati yake yi.

Ranar da Baba ya yi arba’in sun sha kuka bayan sun yi mishi saukar alkur’ani suka haƙura da kukan suna mishi addu’ar Allah ya jiƙan shi.

Cikin sa’a bayan kwana biyu da gaya ma Mariya ta nema mata aikatau,ta zo da murnar ta an samu saboda ta na samun aikatau da dama kusan ita dillaliyar masu aiki ne.

Tafiyar da Baba Sani ya yi sai hakan ya ba Juwairiya damar ta fara aikin ta cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya sani ba.Duk da ita Mama taso ta bari ya dawo su tambaye shi amatsayin sa na mahaifi,amma taƙi ta kafe daga karke wasu irin maganganu ta jefa ma Mama wanda yasa ta ji babu daɗi,a yadda take gaya mishi magana duk da ta san dama ba sa shiri,amma ko ba komai yanzu shi yake da matsayin mahaifinta kuma ko aure za ta yi shi yake da alhakin komai.

Faɗa sosai ta yi mata don ganin ta a maganganunta har da rashin kunya,wanda hakan bai dace ba musamman shi da yake da matsayi mai girma a ranta.Juwairiya ta ji maganganunta amma yadda ta faɗe su haka ta watsar da su a gurin a ranta take faɗin.”Ta ya ya za’ai na mutunta mutumim da yake da burin ɓata min rayuwa,ko da mahaifina ne ya bijiro da wannan iyakan abin da zai yi mishi kenan Mama,domin babu biyayya ga abokin sabon halitta!Kema da zaki ji abin da yake so a gareni sai kin yi mishi fiye da nawa.”

Matar da Juwairya za ta yi ma aiki likita ce a shika ta na da yara uku,a kwai wata mace tsohuwa wacce take mata girki ita kuma Juwairiya aikin ta kula da yaranta mata biyu da namiji ɗaya,in da za ta din ga mata aiki ta na tafiya har islamiya ta saka su tare da yaranta.Ranar da kuma take da aikin kwana za ta kwana da yaranta da safe ta shirya su ta tafi makaranta,wanda ta ba ta zaɓi in ta gama shirya su za ta tafi gida duk da ita matar makaranta ta ba Juwairiya zaɓi ta koma ta zana jarrabawar fita sakandiri.

Juwairiya ta ji matuƙar daɗi na samun aikin duk da ta na jin tsoron abin da Baba Sani zai yi mata in ya fahimci ta na aikin.Taƙi amince mata kan shawarar da ta ba ta da ta koma makaranta,duk da ita ma ta na da buƙatar haka amma ta san Baba Sani ba zai bar ta ba.

Sai dai cewar da matar ta yi za ta dinga kwana da yaranta in ta na aiki ya so ya ɗan tsorata ta,amma da ta gaya mata a kwai Baba tsohuwa sai hankalinta ya kwanta don ta yi tunanin tare za su din ga kwana.

Juwairiya ta ƙara son ta yi aikin jin an ambaci kuɗi mai tsoka,sannan da suka tashi za su tafi sai ta ba ta kayan abinci da kuɗi naira dubu ta sallami Mariya da tsoka,saboda ta yaba da hankalinta musammam da ta ganta ba ta da ƙazanta.

Mama da ta ji aikin har da kwana sai ta fara yiwa Juwairiya faɗa kuma tace sam ba za ta yi aikin ba,ta na ta faɗa in da take shiga ba nan take fita ba.Ganin hakan sai ta saka kuka ta miƙe domin ta yi sallar magariba.”Ba gara na zauna a gidan Anty Naja ba tunna na ji Mariya tace mijinta ustazi ne me gamu,akan ƙanin mahaifina dake son ya ɓata min rayuwa.

Juwairiya ta yi tunanin za ta shawo hankalin Mama,amma sai ta ga ta kafe a dokin naƙi in da ta ƙara mata da cewar sam ata fau ba za ta yi aikin ba.

A ranar da suka shirya da Anty Naja za ta fara aikin,Mama ta kafe ko da Mariya tazo suka lallashi Mama shi ma bai yi wani tasiri ba ganin haka sai ta haƙura,akan ta nema mata wani kawai wanda ba za’a din ga kwana ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Da maraice ta na zaune akan kujera ta na wanke-wanke sai suka ji sallamar Mariya da wata a bayan ta,da sauri ta ɗaga kanta  duk da cewar ba ta yi ma Anty Naja kallon kirki a ranar ba,amma ta sheda ta.

A kunyace ta amsa mata sallama tare da yi mata jagora zuwa ɗaki,ta ibo mata ruwa a kofi ta ije mata sannan  ta fice daga ɗakin ta na jan numfashi ta riƙe turaren Anty Naja da ya baɗe ɗakin na su,wanda Juwairiya ta so ya dauwama a ɗakin saboda daddaɗar ƙamshin sa.

“Ba ki sanni ba ko Mama?”Anty Naja tace bayan ta ɗauki ruwan da Juwairiya ta kawo mata cikin sakin fuska,kuma ta sha ruwan sosai ba tare da nuna ƙyanƙyani ko tafi ƙarfin shan ruwan randa,wanda hakan sai ya yi matuƙar burge Mama wani ƙarin burgewa ta baje akan tabarma har ta na cire hijabin ta da ɗankwalinta.

Hakan ya yi matuƙar ƙara burge Mama sai ta ƙara jin ta saki jiki da ita tace.”Bam ma sanki ba yarinya,amma da na ganki da Mariya ƴar maƙocin mu na gane kece wacce aka yi maganar aiki da Juwairiya…”

“Ni ce Mama tabbas ni ce ina ta jiran ta ba ta zo ba,sai da ga ba ya Mariya ta zo tace min kin hana ta “Tace tare da ƙatse Mama ba tare da ta kai aya ba.

“Haka ne gaskiya aikin nan ki nemi wata kawai.”Mama tace ta ɗan canza fuska kaɗan,ganin haka sai jikin Anty Naja ya yi sanyi amma saboda ya ba hankalin da ta yi na Juwairiya ta kasa haƙuri tace.”Don Allah Mama karki hana ta wallahi ba ni da matsala da ga ni har mijina,kuma in kina tunanin kwanan da za ta yi ne mijina ba zama yake ba wani lokacin ni kai na sai na yi bacci yake dawowa.”

Ta matsa kusa da Mama tare da riƙe hannunta ta yi rau-rau tace.”Don Allah Mama kar kice a’a ban ɗauki Juwairiya a matsayin me aiki ba ƙanwa ce a gareni,kuma duk ranar da kika ga wani  abu ya faru mara daɗi a tsakanin mu ki hana ta zuwa.”

Ta yi shiru ko Mama za ta ce wani abu amma sai ta ga ta kauda kanta ta na tunanin wanda ba za ta iya cewa ta yanke ta barta ko a’a.”Kin ji Mama ki amince don Allah!Na yi masu aiki da dama amma basa iya riƙe min amana,bayan haka sace-sace suke min.”

Duk maganganun da take yi ba ta ce mata komai ba,aranta ta na tunanin karta amince a za a sami matsala da Baba Sani duk da shi ma ya na da laifi,in da ace ya na taimaka musu da ba za ta yi aiki ba.

‘Ki na ji Mama da ban so na gaya miki wani sirrina ba,amma nuna amincewar ki ya zama dole na sanar miki domin ki taimakeni ki ceci aurena.Mai aikina mijina ya kama ta da yarana tana basu kirjinta suna tsotsa ita kuma ta na saka musu hannu a gabansu.Hankalinsa ya tashi ƙwarai ba yan ya miƙa ta ga hukuma ya kawo su asibitin da nake aiki,hankalina ya tashi ƙwarai na yi kuka kuma mun yi rikici da shi daga ba ya yace dole na bar aiki ko mu rabu.Ina son aikina saboda da shi nake taimaka iyayena,sannan ina son aurena na yi-na yi a dai na saka ni aikin kwana amma ba zai yiwu ba.

Mijina ya bani zaɓin na bar aiki na kula mishi da yaransa ko ya rabu da ni,domin yaƙi barin na ƙara ɗaukar me aiki.Mun yi rikici da shi sosai daga baya ya haƙura na samu mai aiki amma daga wannan ya kama ta da wani matsala zai rabu da ni.”Tace cikin hawaye ta ja numfashi sannan ta ɗora da cewa.

“Mariya ita ta ja ra’ayina akan Juwairiya saboda ta gaya min ta na da hankali,da ƙyar na amince da na ganta na yadda da maganar Mariya ki taimake ni Mama in har kika amince zan zama tamkar ƴarki,zan taimaka ma rayuwar ku.”

Jikin Mama ya yi sanyi sosai har ba ta san sanda ta amince ba jin aure na shirin mutuwa,duk da watarana ita ma aure za ta yi.”Na amince Allah ya kyuata amma ƴar nan ya kamata ku din ga kiyaye wa,ni ma matsalar ba daga gareni ba ne a kwai ƙanin mahaifinta ba lai-lai ba ne ya amince amma ta fara mu gani.”

Sosai ta ji daɗi ta buɗe jakarta ta ciro dubu ishirin da biyar tace.”Ga kuɗin ta na wata biyu dubu ishirin sai ki fara koda sana’a ne,sannan dubu biyar na baki kyauta kuma gobe in Allah ya sa tazo za ta taho da tsaƙo.”

Mama ta ji daɗin kuɗin da ta bata ta na ta murna da saka mata albarka har ta yi mata sallama,ta kama hannun Juwairiya tace.”Sis sai kin zo gobe ko?Don Allah ki zo da wuri ƙanninki suna ta maganarki.”Tace tare da shafa kanta.

“Gaskiya ta na da kirki sosai.”Mama tace ta na juya kuɗin da ta bata,sai kuma ta aje kuɗin ta kalleta tace “Kin san me ba zan taɓa kuɗin nan ba sai mun ji me Baban ku Sani zai ce.”Da sauri ta miƙe kawai ta na faɗin.”Ki ba ni naje na yo miki sare-sare ki fara sana’a ni fa ko me zai yi sana yi aikin nan,tunna shi ba taimakon mu yake yi ba don haka ba shi hurumin da zai hana mu.”

Ta yi maza ta fice daga ɗakin kafin Mama tace komai sam ba ta jin tsoron abin da zai ce in dai ba kasheta zai yi ba ta rantse sai ta yi aikin.

Kamar yadda ta gaya mata mijinta ba mazauni bane haka kuwa ta gani,don tun da ta fara aiki ba ta gan shi ba sai tanƙamemen hoton su da yake manne a falon wanda tun da taje ranar da Mariya ta kaita ta gan shi a hoto,wannan dalilin ya sa hankalin ta ya kwanta ko da ta ga Baba me aiki aikin ta take yi ta tafi ba ta kwana.

Ta na aikin ta cikin kwanciyar hankali ga abinci da take ci kullum taci mai kyau ta sha mai kyau,don Anty Naja ba ta da rowa ko nama taci sai ta rage mata saboda yadda Juwairiya take kula da yaranta ga ta da tsafta ko ina na gidanta tsaf ya na tashin ƙamshi.

Kusan sati biyu ta na aiki cikin jin daɗi kuma har zuwa wannan lokacin Baba Sani be dawo ba,kullum in dai za ta dawo Anty Naja na sawa a yi girki da su ta saka mata a kula kuma da yawa,don haka ba sa matsalar abinci ga ɗanye da take badawa a  kai ma Mama in dai za ta yi aikin kwana.

Ranar Juma’a da safe bayan ta gama aikin ta ta shirya musu abincin karyawa ta ibi nasu kamar yadda ta yi mata umurni,kasancewar ta gama aikin kwana za ta yi hutu har ta bawa Juwairiya hutun kwana biyu.

A hanya Juwariya ta na tafe ta na ta yi mata addu’a don tsakanin su Allah ne kawai zai biya ta,saboda irin kyautata mata da take yi fara aikin ta ta bata kaya masu kyau sosai da abin alheri ko hijabi kala biyar ta bata,sannan ko baƙi ta yi bata ce mata me aiki sai dai tace ƴar’uwanta ta na da matuƙar kirki sam bata nuna wani abu ko rashin mutunci.

A dai-dai ƙofar gidan su ta tsaya cikin firgici ganin Baba Sani ya ɗare kan motar sa ya na riƙe da ƙatuwar bulala,sai juya ta yake ya na zare ido ransa a ɓace da ga ganin yadda ya ɗaure fuska alamun ba mutunci.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]