[Advertisements⬇️]

SAKACI KO HALIN MAZA CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Juwairiya zaune a gefen Mama ta na yi mata kitso,Ibrahim ya na zaune a gefenta ya na wasa.Baba ya buɗe labulen ɗaki ya fito dai-dai lokacin da Baba Sani ya kwaɗa sallama daga nesa da su.Ganin sa Juwairiya ta zabura kamar za ta gudu,tun lokacin abin ya faru ta ƙara matuƙar tsoron shi ganin shi take kamar kumurci.

Baba Sani ya kalle ta da wani irin kallo wanda shi kaɗai ya san ma’anar sa,sannan ya miƙa ma Baba takadda yace.”Gashi na gaji da biyan kuɗin wuta ni kaɗai,yau za su zo  ka biya ko kuma a yanke na ka.”Ya faɗa ya na kallon bangaren Juwairiya da ta rintse idanunta tun bayan da lamarin ya faru ta yi katanga da shi,ko ina ba ta zuwa islamiya ma ta haƙura gara ta din ga zama a gida da ta gan shi.

Baba ya yi kasaƙe ya na kallon sa na tsawon lokaci sannan yace.”Ka sa su yanke nawa in dai baza ka iya biya ba,bani da shi kuma na ga ko waya babu wanda yake da shi a cikin mu hasken kawai muke amfani da shi.”

” Oho ko ma me zaka ce kace na gaji da wahala.”Ya sa kai ya fice ya na bambami.

” Ikon Allah na rasa me ke damun shi ya canza gabaki ɗaya.Allah ya ganar da shi.”Yace sannan ya ɗauki gatarin sa ya fita.Juwairiya ta yi shiru ta na tunani a ranta zuwa can ta miƙe tare da shiga  bayi ta saka kuka.

Mama ba tace komai ba illa baƙin cikin halin da yake nuna musu,wanda ta san tsananin ƙiyaryarta ya sa yake nuna musu hakan.Idanunta suka kawo ruwa amma sai ta yi ƙoƙarin sharewa,ba tare da Ibrahim ya gani ba.

Juwairiya ba ta fito ba sai da ta sha kukanta ta ƙoshi sannan ta wanke fuskarta ta fito,a ranta ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki.Duk da Mama ta gane kuka ta yi ba tace mata komai ba,domin ita ma da za ta samu dama kuka za ta yi ko zuciyarta ta rage raɗaɗin damuwar da take ciki.

Yanayin rayuwar da Juwairiya take ciki babu daɗi ji take kamar ta na rayuwa a gidan kurkuku!Kusan kullum sai ta yi kuka ta na matuƙar bakin cikin halin da iyayenta suke ciki,burinta bai wuce ace ta samu aiki ta na taimaka ma iyayenta ba.

Tsakanin ta da Baba Sani tun faruwar lamarin take jin wani tsanar sa mai tsanani ya na ƙara shiga cikin ranta,ko muryar shi ta ji sai ta yi ta’awizi a cikin ranta tsananin mamakin mugun halin sa take.

Duk yadda ta so ta taimaka wa iyayenta abin ya ci tura har takai su kwana basu ci ba,tashin hankalinta yadda Ibrahim yake yi,amma ƙiri-ƙiri Baba Sani ya hana matar sa basu abinci.

Ganin halin da suke ciki wani lokacin ta yi kuka kamar numfashin ta zai rabu da gangar jikinta.

Mahaifin Juwairiya na tsaye ya rataye gatarin sa a kafaɗa hankalinsa baya jikinsa,tunani yake sosai a cikin ransa ga wata irin yunwa dake ƙwaƙularsar.Tunani fal a cikin ransa ya na tunanin kuɗin aikin da za’a yi ma Ibrahim aiki a ƙafar sa.

Ya daɗe a tsaye ya na tunanin mafita daga bisani yaci gaba da saran iccen da yake yi cikin rashin kuzari,tare da rashin madafa sai tsaƙa da warwara yake a cikin zuciyar sa.

Ya ɗaga gatarin sa a sama ya na can ya na tunani bai ankara ba sai ji ya yi gatarin ya dawo tsakiyar kansa! “Innalillahi wa inna ilaihir ra ju’un.”Iya abin da yace kenan ya zube a ƙasa a sume jini na ta zuba kamar famfo!

Hankalin Malam Audi dake gefen icce ya na bayar da iccen ya fahimci abin da ke faruwa, da sauri ya iso garesa ya na salati cikin tsananin razana tamkar zai fasa ihu ganin halin da yake cikin.

Mutanen dake gurin suka yo kansa suna salati ganin abin da ke faruwa,kama shi suka yi aka saka shi a cikin mota suka nufi a sibiti da shi.

Lokacin da labari ya riske Juwairiya hannunta saka a ka sai kuma ta yi ƙoƙarin daƙile zuciyar ta da take ninyar kwarma ihu,ta fara salati ta na faɗin.”Inna lillahi wa inna ailaihir raji’un.”Sai hawaye bayan ta yi nasarar faɗin haka ta yi koyi da faɗe na ubangiji da ya umurci bayin sa da su faɗi haka duk lokacin da wata musiba ta same su.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Wayyo Allah rayuwa ta me ya sa daga wannan sai wannan?”Ta tambayi kanta cikin tsananin ruɗani.Gabaki ɗayan su sun ruɗe ganin halin da yake ciki kai ya kumbura kamannin sa ya canza,sannan an ɗaure kansa da bandeji duk ya ɓace da jini.

A lokacin da suka je ko magana baya yi idanunsa a rufe ba ya iya ko buɗe idanunsa,daga ganinsa ya na cikin wani hali babu alamun numfashi tare da shi sai bugun numfashin sa da yake sauka a hankali a cikin tsananin wahala.

Rintse idanunta ta yi a jikinta take jin kwatankwacin zafin ciwon dake jikin Baba,ta kasa kuka sai hawaye da yake gasar sauka a ƙuncinta ba tare da sanin ta ba.

Suna zaune har tsawon wani lokaci amma bai farka da ga baccin da yake ba,saboda allurar baccin da aka yi masa.Har misalin tara na dare sai a lokacin Baba Sani ya shigo ya na ta zare ido,a cewar sa yanzu ya dawo gida ya ji labari.

“Ni na rasa wannan lamari na ka Yaya kamar wani mai bakin uwa,kullum rayuwarka ƙara taɓarɓarewa take.Haba wannan wane irin musifa ne! Tun ba yau ba nake maka maganar kabar yin faskare amma kaƙi ga shi nan abin da ka jawa kanka.”

Ire-iren kalaman da yake faɗi kenan ba tare da nuna tausayi a fuskarsa ba,sai dai nuna rashin damuwa da faɗin maganganu mara tsari.Juwairiya da ta kifa kanta da akan gadon asibitin ta na wani irin kuka.

Hankalin su ya yi matuƙar tashi ganin halin da yake ciki,Juwairiya kamar ta mutu haka take ji,ƙiri-ƙiri in aka buƙaci kuɗi Baba Sani yake ƙin bayar ba kullum da uzurin sa da yake faɗi.

Da ga baya Baba Sani yake zuwa ya na kwana da Baba.Baba Sani tsaye akan Yayan na sa da misalin ƙarfe ɗaya na dare,kallon sa yake da mugun nufi a ransa.Filo ya janyo tare da danne masa kai.

Allah Sarki bawon Allah da yake kwance a cikin mawuyacin hali ya fara mutsu- mutsu da ƙafafun sa,bai jima ba ya yi dip alamun babu numfashi a jikinsa.

” Gara ka mutu kowa ya huta kullum cikin wahala nake da kai da iyalan ka,sannan ɗan buƙata ta da nake son na biya na rasa.Kaje kawai Allah ya haɗa mu a kiyama!Abin da yace kenan ya kwanta da ninyar da safe ya fasa ihun ya mutu.

Washegari da safe Juwairiya tun da asuba take azalzala wa Mama da su je asibiti,irin mugayen mafarkin da take yi akan mahaifinta ya sa hankalinta ya tashi sosai.Mama ce ta ɗan ƙarfafata har suka dama koko suka sha,duk da dai Juwairiya ƙurɓar kokon take wanda ko siga babu hankalinta na gurin mahaifinta.

Ko wanka ba ta yi ba ta ɗauki ruwan kokon ta na addu’ar Allah ya sa ya iya sha,Mama dai ba tace mata komai ba duk da ranta babu daɗi.Ko da suka isa asibitin gaban Juwairiya ya yanke ya faɗi ras!Sai ta kira sunan Allah ta riƙe kofin kokon ta na wani irin tafiya zuwa ɗakin da yake tamkar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki.

Gabaki ɗayan su suka yi mutuwar tsaye ganin Baba Sani tsaye, a ɗakin ya ɗora hannu a kansa ya na ƙwala ihu, da kuruwa tamkar yadda jahilan farko suke yi yayin da wata musiba ta afkawa ɗayan su.

Sautin kukan sa yake tafiya tare da bugun zuciyarta,ta rintse idanunta ta na addu’ar kar Allah ya sa mafarkinta ya zama gaskiya!In kuma da gaske ne ya za suyi da rayuwar su a duniya bayan ba mahaifin su?

Sai kawai ta fara ja da baya ta na girgiza kanta tare da nuna mahaifinta, ta na faɗin dai-dai lokacin da Mama ta saka kuka domin ta tabbata ya riga mu gidan gaskiya.”A’a bai rasu ba wallahi mafarki ne!Don Allah kar kuce min mafarkina ya zama gaskiya.Mahaifina ya na raye bai mutu ba.”

Sai ta ruga za ta fita waje tashin hankalin ta ta ya ya mahaifinta zai mutu ya bar ta da azzalimi!Mutuwar sa na nufin ya yi nasara akan ta zai cika mummunan nufin sa kenan?

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]