[Advertisements⬇️]

DEEN MARSHAL BY MAMUGEE - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

_*DEEN MARSHALL*_
_Mamuhgee_

*_ZAFAFA BIYAR_* 🔥🔥
_*So Da Zuciya*_
Miss xoxo
_*Halin Girma*_
Hafsat Rano
_*Dabi’ar Zuciya*_
Safiyya huguma
_*Takun Saka*_
Billyn Abdul
_*Deen Marshal*_
Mamuhgee

_Pay @08184017082 Or 09134848107_

*1*

*_BismillahirRahmanir-Raheem_*

Ahankali ta dago kanta dake ‘dan Sara Mata ta kalli kofar office din nata da aka kwankwasa batareda ta motsaba ta dauke idonta akan kofar tana sake boyayyan numfashin dake bayyanarda qosawarta da halin ABBAS LAMIDO sbd ko ba’a fada ba tasan koba shi bane to koma waye to al’amarine daya shafi sunan Abaas aciki.
Turo kofar akai tareda shigowa ko Bata dagoba Jin takun takalma yasa ta fahimci Sarah ce Dan Haka ta sake lumshe ido tana dago Kai ahankali tareda dauke hannunta daga kan aikin datakeyi a laptop ta aje gefe tareda gyara zama ta Kai hannu ta dauki ruwan data fitar a fridge tun dazu sbd su huce daga sanyi ta bude robar ruwan Tasha kusan rabi ta ajiye sauran tana cewa”

Sarah akwai wani abune?

Sai alokacin Sarah ta matso ta zauna kan kejerar hutawar dake kallon wadda  *_NAJMA_*  ke zaune tana jiran abinda zata fada,
Saidata Dan sauke numfashi itama kafin Kai tsaye tace”

Naj dazu kafin isowarki zuwan chairman Abaas biyu office dinnan Kuma Banga alamar lafiyaba a yanayinsa
Zan iya cewa dai yanayin da aka Sabane.

Sai alokacin _*NAJMA ABDULLAHI BELA*_ ta dago da fararen idanuwanta dasukai laushi da gajiya tareda damuwar Jin abinda aka fada din ta kalli Sarah tsawon lokaci kafin ta sauke nata numfashin itama ta bude Baki da muryarta me taushi dake kokarin boye damuwarta tace”

Meyene matsalar Abaas Kuma yanzu?

Cikeda kulawa Sarah tana kallonta tace”

A yanda nakega inaga bazai wuce akan maganar jiya bace da Dr Sa’id yazo gurinki sbd zuwansa biyu Ana cewa kunfita tareda Dr Sa’id din.

Sai alokacin ta tuno da zuwan Dr din jiya da fitar da sukai zuwa taron makarantar yaronsa a wata private school dake kusa bama nesa ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana daukan wayarta Dan kiransa Dan kuwa ma wannan karon yayi kokarin rashin binta gida tun Daren jiyan yayi abinda ya Saba.

Ringing wayar ta ringa yi harta katse Bai daga ba ta sake saka Kiran Bai dagaba har lokacin
kusan Kira uku Tai Masa baya dagawa ta kashe wayar tareda ajewa gefenta ta waiwayo ta kalli Sarah tace”

Bai dagaba
Baya office dinsa ne?

Banajin yafita Dan ko kafin nashigo Naga wucewar secretary dinsa hanyar zuwa office dinsa.

Juyar da fararen idanuwanta tayi ta maidasu kan wayarta da tadau ringing taga sunan Hanifa ne akai ta lumshe idanu ahankali tana sauke ajiyar zuciya tareda Jin sanyi aranta sbd Hanifa Marshal Alfa Bata Bata lokaci komai kankantarsa batareda takirata ba idan taji wani Abu yafaru da ita.
Kallon Sarah tayi da alamar tambayar cewa”
Kinfada Mata yawon da Abaas yayi na nemana yanzu da safe kenan?

‘yar dariya Sarah tasaki tana miqewa ta nufi hanyar fita tana cewa”

Sorry ma’am itace takirani da kanta ta tambaya.

Ficewa tayi tareda rufo kofar office din har lokacin da sauran dariya akan fuskarta saidai ta baro jikin kofar sukai kusan Karo da Abaas daya qaraso office din sanye cikin suits ash dasukai Masa kyau matuka kasancewarsa kalar ruwan tarwada Kuma cikakken kyakkyawan namiji meji da lokaci da kuruciya da nera.

Da sauri Sarah ta matsa gefe tana sake sake fuska da tace”

Barka chairman.

Ko kallonta beyiba ya bude kofar office din dake daukeda sunan NAJMA BELA ajiki ya shige tareda rufo kofar.

Tana zaune a inda Sarah ta barta bakuma ta juyoba sbd tariga tagane shine yashigo Dan Haka saima Dan lumshe ido datayi Wanda yake tamkar dabi’a gareta.

Kureta yayi da kallo daga tsayen kyawunta da dabi’unta masu sanyi suke taruwa su sace zuciyar mutum wainda shima sune suke dawo dashi gareta Koda yace ya rabu da ita,
Duk neman matansa yakasa samun wadda tafi Masa Naj kyau da sanyin dabi’u tareda wani irin aji Wanda ko jinin sarauta zai shafa Mata lafiya
Daya samu da tuni ya rabu da Naj sbd gabaki daya tagama Cinna Masa hauka bayan yanada tarin mutunci da dukiyarda yake iya shimfida duk abinda yakeso Amma gashinan yaqare da aiki a ALFA’S sbd ita ‘yar  daba ‘yar kowaba face wadda ke amatsayin babbar Aminiya ga ‘yar Marshal alfa Wanda sbd hakan ne take anan din shikuma yafiso ko ruwa idan zatasha tafada Masa Amma duk yabi yazama wani zararre akanta Wanda abin ke matuqar Kona Masa Rai duk da yasan tana tsananin hkr da dauke ido akan abubuwan dayake Mata Amma shima duk son dayake Mata bazai zauna Yana zuba ido tana yanda takeso ba Dan gwara ta Saba ko bayan aurensu tasan dokarsa baya daukan reni.

Jin shirun yayi yawa yasa ta dago ahankali ta Dan kalli gefensa da idanuwanta ta bude Baki cikin muryarta me taushi da nutsuwa tace”

Akwai wani Abu ne?

Rintse ido yayi wani takaici na taso Masa ya budesu akanta tareda qarasa matsowa gabanta ya fige wayar hannunta ya dangwareta kan kejera da qarfi cikin bacin Rai yace”

Akaro da danban adadiba Ina sake tambayar meye asalin boyayyar alaqarki da wannan likitan sbd bazai yiyu ko yaushe nayi tambayar mu’amalarku kinamun shiru sbd bansan meyake bakiba Wanda Ni bazan iya bakin ba da kinkasa rabuwa dashi,
Kyanki kike rudarsa dashi?
Kokuwa wani abun ne Wanda bansaniba ni……

Kashesa tayi ta hanyar zuba Masa manyan idanuwanta farare dasukai jajir atake da zallar takaicin kalamansa da basuda mutantawa ko darajantata amatsayinta na wadda zai aura din.

Miqewa tayi tsayi tareda daukan wayarta ta batareda tace Masa ko kala ba ta nufi table din office din da Jakarta ke Kai ta dauka ko kallon inda yake bataiba ta nufi kofa ta bude ta fice tabarshi tsaye Yana bin bayanta da kallo zuciyarsa na Kuna Kamar zai cinnawa kansa wuta yakeji.

Tana fitowa Sarah ta taso daga kan table dinta na matsayinta na secretary dinta ta qaraso tun kafin Tai magana ta lura da yanayin Naj din Wanda tasan dama za’ai Haka indai Abaas ne Wanda kullum ne qaida sai sunyi fada da Naj da Abaas din duk da dai kullum fitinar da tashin hankalin na Abaas din ne.

Batareda ta kalletaba da murya me ‘dan nauyi tace”

Sarah ki tattara takardun Dana Bari a table da laptop Dina ki kawomun gida idan kintashi.

Ok Naj Allah yatsare hanya.

Tana saukowa qasan building din ta nufi gate zata fita tahau taxi sbd dama Abaas din yawanci ke daukota daga gida Kuma idan sun tashi ya maidata idan Kuma suna fada taxi take hawa wadda dama tafi hawanta shiyasa ma takeda me taxi dinta na musamman Wanda kiransa kawai takeyi yazo Dan kuwa ranaku daddayane basa samun matsala da Abaas Wanda take Jin wani lokacin Kamar zuciyarta zata Gaza bazata iya cigaba da hakuri tana hadiye halayen Abaas ba dan kuwa gabaki daya Babu inda sukai dace da juna dazasu iya rayuwar aure bayan aurenba,
Ta Yaya zata auri mutuminda baisan darajarta,mutuncinta,qimarta ba tareda mutunta alaqarsu,
Tariga tasani tsananin kyawuntane yasa Abaas yake son aurenta Dan tazama tasa abin ado agaresa Wanda Bata saniba ko tsananin zafin ransa da zafin kishinsa zai Bar kyan nata ta tsufa da abunta Dan ita shakkar aurensa yafara mamaye zuciyarta sbd a dukkanin halayensa Babu Wanda baya Bata mamaki.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana sake shanye damuwarta Kamar yanda ta Saba akan al’amarin Dan kuwa fasa auran Abaas gareta babbar matsalace dazata sake sako Kai tsakaninta da mahaifiyarta dama Dada kakarta uwa uba Dattijo Wanda yake mijin mahaifiyarta Kuma tawainiyan mahaifinta daya auri mahaifiyarta bayan rasuwar mahaifinsu.
Fasa aurenta da Abaas idan tayi shine zai zama Karo na hudu biyar kenan Ana fasa aurenta…

Mun iso hajiya” me taxi din yafada daidai Yana parking bakin Babbar kofar gidan Marshal Alfa Wanda sojoji  hudu ke zaune kofar gidan suna gadi.

Fitowa tayi ahankali cikin nutsuwa wadda zallar ilimi da wayewartane tareda ajin datake dashine yasa komai nata yake cikin nutsuwa ta bude jeka ta fiddo nera dubu daya ta miqa Masa tana cewa”

Nagode Mal Hafiz.

Juyawa tayi ta nufi gefen gidan daya bangaren dake gefen gidan Alfa wani ‘dan madaidaicin gidan gado Wanda yakeda Dan zurfi daga cikinsa sbd ‘Dan yawan dasuke dashi a gidan danma kusan duk Yan Matan gidan sunyi aure duk da bawai yawane dasuba sosai.

Cikin sabo sojojin dake zaunen dasukaga dawowarta sukace”

Welcome Ms Naj.

Dan murmushi tasaki tana waiwayowa tace”

Barkanku da aiki da hutawa.

Gidansu ta qarasa Wanda yake gefen da ‘yar tazara da gidan Alfa din ta shige Wanda ba gate bane koface irin ta gidan me ‘dan rufin asiri.

Gefen Dattijo ne a farko Dan Haka ta wuce Kai tsaye kuryar gidan inda taci Karo da Umma habiba zaune a kofar nata sashen kan kujera tana duba kayan ‘yan kananan atampopinta datake saidawa tana waya autarta Asmau na gefenta tana jera kayan cikin qatuwar ledar da aka kawo kayan.

Cikin girmamawa asma’un ta dago tana cewa”

Anty Naj sannu da dawowa.

Yauwa sannu Asmau
Ina yiwa umma sannu idan tagama wayar.

Hannu kawai umma habiban ta daga alamar amsawa tana bin bayan Najma din da kallo tana yamutsa Baki cikeda shaguben Naj din sbd aikin datakeyi Amma aure ya gagara.

Tana Isa sashen mahaifiyarta ta taddata a tsakar gida zaune itama tana lissafin nata kudin na turarukan wuta datake saidawa duk kwalaben turarukan a gabanta baje sai wani irin kamshi Mai qarfi ke tashi ta kalli umman tana nufar dakinta tace”

Ummi sannu da aiki.

Itama Bata wani dagoba tanaci gaba da aikinta gabanta tace”

Yawwa,
Lafiya dai Naga kin dawo yau da wuri.

Tana qarasa shigewa dakin nata tace”

Lafiya kalau hutawa nakeson Yi jiya bansamu bacci sosaiba.

Dama Ina Zaki samu maganar bacci me Dadi bakida abokin Hira acikin gida kowa Yana dakin aurensa,
Dayake Kuma ga wata babbar kwabon Nan kinsamu” taqarasa fada tana kallon gefen Anty Amina dake gefe tana yiwa babbar ‘yarta zainab bayanin karatunta da Bata ganeba.

Kallon umman tasu anty Amina tayi tana cewa”

Umma Dan Allah ki daina cewa”

Naqi zaman auren Nan a gaban zainab zata ringa daukan abin aranta tana ajewa da wata fassarar.

Wani mugun kallo ta watsawa Anty aminan kafin tace”

To Yaya kukeson na bayyanarda damuwata da halinda nake ciki akanku?
Ke zaman auren ya gagara kin tattara kindawo gida da budurwar ‘ya,
Ita wannan aurenma ya gagareta Yi kwata kwata ta koma ta zama wata ma’aikaciya mutane na qarqashinta ta Yaya zata iya auren
Shiyasa nake sake cewa Hanifa wannan aikin na Najma bazai Bari tayi aureba matuqar tana ganin mazan daidai take dasu..

Lokacin auren ne baiyiba umma” cewar Hanifa data shigo gidan tana qarasowa gurin umman fuskarta daukeda murmushi tace”

Umma Naj zatai aure kamar kowa lokacine kawai Allah Bai kawoba.

Cigaba da aikinta umman tayi tana cewa”

Duk da hakan dai ta rage ganin girman kanta ta sallamawa duk namijin daya samu tayi aure Dan shine mutuncinta da nawa Nima Dan ko Nima na huta da gorin dattijo da Dada dasuke ganin da saka hannuna a  riqewar datai Kamar rake.

Murmushi Hanifa ta saki tana barin gurin umman tana cewa”

Umma Naj zata auri namijin daya kamaceta bawai ko wanne ba gskia
Kumafa ba riqeqa tayiba kawai dai Wanda zai Mana ciki da itane Bai bayyana ba haryanzu
Idan ya bayyana shikenan muma mun huta da damunta da kowa keyi da maganar aure,
Ni wlh bansan meyasa kuka sakamun Naj Dina a gaba ba duk kun damarmun ita.

Qarasawa kofar dakin tayi ta shige tana cewa”

Anty Amina barka da hutawa.

Da ‘yar dariya anty Aminar tabi hanifar sbd ganin Kamar ta kunna umma databi kofar dakin da harara kamar zata hadasu su duka Tai musu duka ko zasu fahimci ciwon ranta na rashin auren Naj din wadda ita Sam kamarma abin baya damunta.
#Mamuh#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DEEN MARSHALL_*
_Mamuhgee_

2
Da wani irin kallo Hanifa kebin Naj dake tsaye bakin wardrobe daure da towel me kauri da girma brown color fuskarta fayau Kamar ko yaushe Babu wata damuwar abubuwan dake addabe da rayuwarta Kamar fitinar ummanta data su dattaji uwa uba ta Abaas datafi ta kowa zama abin baqin ciki da takaici.

Sake kallon fuskarta Hanifa tayi tana zaunawa kan gadon tareda ajiye wayarta gaban madubi tana cewa”

Nayi waya da Sarah dazu.

Batareda ta juyoba tana zare Yan kunnayenta tace”

Kada ki damu da abinda tafada Miki
Idan Akan Abaas ne zuwa yanzu kema kinsaba da halinsa,
Abinsa ya daina damuna yanzu saidai kawai yanda Naga kamar abin nasa kullum rikidewa yake zuwa ga zargi
Zarginma me muni Wanda nake dannewa Ina sharewa sbd Umma dasu Dattijo…

Sai alokacin Hanifa ta katseta da cewa”

Meyesa Zaki daure sbd su umma bayan su dinma da zasu bude ido da kyau su duba dabi’u da wasu abubuwan tako Ina Abaas Bai cancanta ba bama Haka ba yaushe Kika fara damuwa da abinda ake fada na cewan kece Kika qi aure da har Kika zabi auren Abaas lamido Wanda Ni kwata kwata baima kwantaminba
Gabaki daya Banga halayen maza masu hakuriba ko iya tattala mace atareda Abaas.

Ajiyar zuciya Naj din ta sauke Jin ran Hanifan yafara baci da zancen ta waiwayo ahankali ta kalleta tareda sakin wani irin lafiyyan murmushi Wanda kusan Arayuwarta tunda tazama budurwa cikakkiya kaf kannenta sukai aure aka sakota gaba tako Ina Hanifan ce kawai take iya ganin murmushinta me fidda asalin kyawunta Wanda yafito daga ainihin cikin zuciyarta sai kuwa Dr sa’id Wanda yake tamkar ‘dan uwa Kuma aboki agareta shima idan tana tare dashi takanji nutsuwa da kwanciyar hankali sbd ya fahimceta tareda sanin halayyarta fiyeda ‘yan uwanta na jini duk da kuwa Bata hada komai dashi ba face kasancewarsa likitan Hanifa tun suna yara har yanzu dasuka girma.

Zama tayi gefen Hanifan tana kallonta tace”

Ba abun damuwa bane basai kin saka damuwan Abaas ba aranki
Mubar maganan ma sunan Harya fara sakamun ciwon Kai.

Hanifa Sam ko sunan Abaas din tafi kowa takaicin saurara sbd tun ranar farko da zancen Yana son Naj din ya sauka a kunnenta ta qarewa background dinsa da halayyarsa bincike bataga ta inda ya cancanta Naj ba kafin daga baya taji fara aikinsa da zuba hannun jarinsa a ALFA’S dinsu Wanda Sam bataso hakan ba Amma sbd zagayen da yayi akai Masa Hanya ya bullo ta gurin JALALUDDEEN qaninta Wanda dukiyarsa tafi ta kowa yawa acikin ALFA’S din hadda kuwa mahaifinsu da shine me asalin companies din na Nan portharcourt dama na wajenta.

Miqewa Naj din tayi tana cewa”

Bari nayi wanka nafito zamuyi mgna akan Isma’eel ya kirani dazu akan maganar zuwanki ganin likita A Jamaica.

Kallon kyakkyawar fuskarta Hanifa tayi tana murmushi tace”

Allah sarki Zawj.

Da yanayi na sanyi Naj ta kalleta zuciyarta na yin sanyi da dukkanin wata damuwar Hanifa ko ciwonta.

Toilet din dakin nata ta shige Dan dama wanka zatayi Hanifan ta shigo.
Bayan shigarta wanka miqewa Hanifan tayi ta sauko daga kan gadon ta zura flat slippers dinta na _Jimmy choo_ ta fita dakin ta nufi gurin umma dake zaune har lokacin tana aikin zuba wasu turaren wuta masu tsananin qamshi ta zauna gefen umman tun kafin ta qarasa zama umman tace”

Kun gamo shawaran yanda zaku fuskanci Dattijo da Dadah idan Maganar aurenta da Abbas ta fasu Dan nasan wannan doguwar fuskar da Kika shigo da ita bata lafiya bace Dole akwai abinda yake faruwa tsakaninta da Abbas.

Dan guntun murmushi Hanifa ta sauke tana Taya umman rufe kwalaben turarukan tace”

Umma meyesa kuka kasa gane irin taurin zuciya da qarfin imanin da Naj take dashi sbd ba kowane zai iya hadiyewa ba yakuma danne irin Gori da takura tareda cin fuskan da ake Mata akan rashin yin aure ba?

Umma kowa Yana yiwa Naj kallon taqi aure sbd zurfin ilimi da karatun bokon datayiba a cikin gidan Nan hakama Ana Mata kallon wadda ta Raina maza sbd ganin Kamar matsayinsu da nata daya ne Wanda umma keda Kika haifi Naj kinsan ba Haka takeba kawai dai ita Allah Haka yayita miskila me halin ko oho ga abinda ake fada akanta bayan Haka shi fa aure nufi ne na Allah Kuma ba lallai ne ita lokacin nata auren yayi ba idan lokacin yayi zatayi.

Hmmn Hanifa nagaji da bin bayan Najma akan maganar fasa aurarrakin Nan nata da akeyi kusan Kashi biyar tun Ina yadda da qaddarane a gaskia yanzu na yadda da hadda halinta na miskilanci Wanda kesa mazan ganin Kamar tafi karfinsu ne kokuma tana tuna tafi karfin nasu,
Kunfi kowa sanin yanda Dadah da Dattijo suka sakoni gaba a cikin gidan Nan akan Najma
Kullum fa qara shekaru akeyi ba ragewa ba yanzu ke da Allah yakawo rabo na haihuwa aurenki da yanzu ba kinada yara biyu ko ukuba koma hudu idan anyi haihuwar ritsa Amma Sam Naj ko ‘yar damuwar Nan Bata nunawa kullum itace a nutse a kammale saikace wata lissafi ahaka takeson qarewane saidai aiki kawai..
To ku zauna ku dasa sabuwar shawara wannan karon wlh Dattijo rantsuwa ce a bakinsu shida Dadah matuqar aurenta da Abbas ya fasu to wlh bazata rufa sati ba agidan zasu aura Mata duk Wanda ya samu ciki kuwa hadda sojojin dake gadin gidanku yace zai kaiwa tayi idan hakan ta faru Ni kaina danake mahaifiyarta wlh zuciyata zata iya bugawa bare ita Dan Haka ki zaunar da ita kuyi shawara koma menene matsalar su zauna suyi sulhun abarsu itada Abbas din asamu ayi auren Nan ta tafiyarta ta huta Nima na huta da zancen kullum din.

Batasan wane bayani zata yiwa umman ta fahimta ba sbd matsuwar su dattijon tariga tasaka umman itama gajiya tana kasa fahimtar ‘yar tata,
Tana tsananin qaunar Naj tamkar ‘yar uwarta ta jini dasuka fito ciki daya Dan kuwa tsananin qaunar datake Mata har kasa tantance cikin su biyun tsakanin ita da marshal batasan waye tafiso ba duk da shi din jinintane dasuka fito ciki daya,
Bazata iya Bari Naj ta cutu takowane irin Hanya ba Dan Haka ita da kanta zata nema Ganin Abbas lamido suyi magana idan har yanason Naj da dukkanin zuciyarsa da gaskia to yakamata ya sauya su fuskanci rayuwar aure zasuyi su fahimci juna tun yanzu.
Idan har zai qaunaci Naj da gaskia zaifi Mata ace Dattijo yabada auren Naj wa duk Wanda yasamu.

Wanka ta fito taga Hanifan Bata dakin tasan tana gurin umma ko anty Amina Dan Haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror ta zauna ta kalli fuskarta zuwa kirjinta da kafadunta dake bayyane suna wani qyallin haske da samun lafiyar fata ta maida kallonta kan fuskarta datafi komai kyau da daukan ido atare da ita ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tareda sauke numfashi kadan kafin ta janyo lotion na jagggins tana shafawa kadan kadan Dan batason Mai da yawa Ta miqe bayan ta shafa turaren POSSES ajikinta tareda mist na Rednight ta zare band din kanta ta gyara daurin gashinta tayisa sako sako sbd Taji dadin kan nata ta nufi wardrobe ta Ciro doguwar riga Mara nauyi zata saka wayar Hanifa data bari kan mirror din nata takawo haske tana vibrating ahankali ba qara sbd Wanda Dabi’arsune rashin sakawa waya qarar ringing Dan kusan itace ta koyawa Hanifan hakan qarar waya na damunta shiyasa Sam wayarta Bata qara idan Ankira saidai vibrating shiyasa itama Hanifan ta koya sbd Naj din.

Ahankali ta waiwayo ta kalla wayar taga sunan dayake Kai _MARSHAL_
dauke Kai tayi tana cigaba da saka kayanta Dan tunda takeda Hanifa Bata taba daga wayar ‘dan uwanta ba idan yakira Wanda shi kadaine kawai Bata daukan wayarta idan shine yakira idan har Bata kusa tun kuwa tasowarsu suna qananu haryanxu.

Sanin baya Kira biyu ‘daya yakeyi yasa ta sake waiwayo wayar tana kallon sunan destination dinda caller ID ta rubuto _HAWAII US STATE_
Hanifa Babu wani Abu a duniya dayafi Mata qanin nata Wanda su biyu kacal mahaifiyarsu ta Haifa ta bar duniya Wanda tazarar shekara uku ce a tsakaninsu yanayin aikinsa da girman matsayinsa yasa baya tareda ita wayama sai yasamu lokaci suke iya Yi Dan Haka Babu abinda Hanifan Bata Wasa dashi irin waya da marshal din Dan Haka bazata so ta rasa kiranba takai hannu a natse ta dauka tareda nufar kofa ta bude ta fito ta kalli zainab dake kusa tace”

Miqawa Hanifa wayarta Ana Kiranta.

Karba zainab tayi ta nufi Hanifan da sauri ta miqa Mata cikin sa’a kuwa har lokacin Kiran Bai katseba tana ganin me Kiran ta dauka tana Kiran sunansa cikin tsananin kaunarsa da kowa ya shaida kaunace me girman gaske a tsananinsu.
#MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

 

*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_

 

3
Komawa Naj din tayi Dan tayi sallah tana Shiga dakin tun kafin Hanifan ta qaraso dakin ta tayar da sallarta Dan tasan Babu ranar da zasuyi wayan Hanifan Bata hadasu ba suka gaisa Wanda daga ita harshi din basa buqatan gaisawar sbd shi dai Bai taba gaidata ba hakama itama batajin zata iya gaidashi din tun koba komai shine qani Amma gabaki daya matsayi dayake dashi da jin yazama billionaire yasa baya iya gaida mutane kokuma tace wasu mutanen tunda Yana gaida Hanifa da hajjo kakarsu,itadaima gabaki daya Bata wani buqatan shiga rayuwar kowa musamman irin tasa rayuwar wata iri kamar ta Mara kowa komai nasa yawanci kafin suji sunfara gani a labarai kullum koken hajjo da Hanifan rashin dawowarsa akai akai duk da dai taga kamar yafara sauyawa Dan yanzu Yana Dan yin kokari a shekara yazo so uku ko so biyu Haka.

Harta kammala sallar azahar data la’asar da aka gama idarwa lokacin Basu Gama wayarba wadda fiyeda Rabin harshen zancen turanci ne Hanifan keyi Dan Kamar yafi Kama bakinsa yanzu fiyeda hausarsa bugu da qari ma duk rayuwarsa yanzu idan Basu yakira bama baida Wanda zai Kira suyi yaren hausan sbd dad dinsu dai Yafi zama yanzu a Angola sbd tun wasu shekarun aiki da yayi acan bayan rasuwar mahaifiyarsu ya auri wata Yar can wadda gabaki dayama Bata wani Jin hausa Saida tahadu dashi ne ma tafara koya harta iya bayan auren danshi yasa ko dad din yakira sbd duk sun sama zama da yare yanzu Basu wani cika Yin hausar ba sai dai idan sun Kira su Hanifan da hajjon.

Kwashe dadduman tayi ta nade tareda zare milk hijab din datai sallan ta ajesu cikin wardrobe ta juya ta nufa water dispenser dake dakin nata Dan Shan ruwan dumi kawai ta matso ruwan dumi cikin cup tadawo ta zauna kan kujera tareda bude laptop dinta tana Sha tana duba saqon datace Sarah taturo Mata ta email.

Tana cikin aikin wayarta takawo haske tana vibrating ta dan kalla wayar ahankali da idanuwanta dake bayyanarda Bata buqatan Kiran kowa a lokacin taga sunan Dr sa’id ajikin wayar take ta saki ajiyar zuciya siririya sbd bazata iya sharesa ba kokuma nuna qosawarta dashi din sbd tsananin mutuncinsa datake gani dakuma yanda shima yake matuqar mutunta dakuma kulawa da ita.
Kallon Hanifa dake waya har lokacin tayi kafin ta dauki wayar tana amsa Kiran cikin taushin muryarta me zallar daukan hankalinsu sbd nutsuwa wadda sukafi daukanta da Jan aji tace”

Barka Dr sa’id.

Murmushi yasaki me Dan qaramin sauti daga nasa bangaren sbd yasan iya gaisuwarta kenan akoda yaushen
Ita bame hayaniyar surutu bace Dan Haka cikin taushin murya shima yace”

Kinbar office kokuwa na biyo na kaiki gida?

Ajiye cup din hannunta tayi bayan ta qarasa shanye ruwan tana kallon screen din laptop din gabanta tace”

Nadawo tun kafin time din tashina yayi sbd Ina fama da Dan ciwon Kai
Thank you.

Ajiyar zuciya ya sauke boyayya kafin yace”

Sorry,
Ki huta to idan natashi Zan biyo na dubaki…..

Cikin nutsuwa ta katsesa da cewa”

No kadaka wahalan da kanka gurin zuwa ba stress ne kawai na Dan meeting din danayi Amma yanzu yariga ya wuce.

Ko Naj Bata fadaba yasan damuwan fitanar Abaas ce bataso Dan ya tabbatarda fitarsu jiyan saita kusa zautarda Abaas din Wanda shi tuni ma yake Masa kallon Mara lafiyar qwaqwalwa Dan wasu abubuwan dayakeyi sunfita daga dabiun lafiyayyun mutane,
Kishinsa na hauka ne bana mutanen dasukasan kansu bane,
Fitinarsa ta marasa ilimi da wayewa ne kamar wanda baida ilimin da wayewar,
Shi gabaki dayama ya rasa ta Yaya Macen datake da tsananin aji da sanin darajar Kai tareda wayewa irin Naj ta yadda da auren namiji kaman Abaas lamido,
Ta Yaya Allah yabashi irin wannan sa’ar me girma ta samun Naj amatsayin Mata.,
Shi Yana tsananin son Naj tareda sanin qimarta Dan Haka bazai taba cire Rai ga samunta ba matuqar ba aurenta aka daura din ba da Abaas shiyasa ma duk haukan Abaas din Bata damunsa Dan bayama gabansa shi Naj din ce kawai a gabansa Dan kuwa irin son dayake Mata idan ya aureta zai maidata sarauniyar rayuwarsa Dan kuwa zai tattaleta tamkar ita kadai yakeda ita a duniya.

Kashe wayar tayi tana ajewa daidai itama Hanifa na aje tata wayar ta dawo gurin Naj din ta zauna tana janye laptop din gefe tareda rufewa tana cewa”

Naj zamuyi mgana akan Abaas.

Fararen idanuwanta ta zubawa Hanifan tana cewa”

Wai Ni rayuwata shikenan kullum akan maganar rashin aure yake?

Ahankali Hanifa ta girgiza Mata Kai tana riqo hannayenta duka biyu cikin kulawa da tsananin qaunarta tace”

My beautiful Naj tasan cewa bantaba damuwa da rashin aurenta ba sbd nasan aure lokacine dashi Kamar mutuwa ta yanda idan lokaci yayi Babu mai hanawa ko tarewa,
A zuciyata dakuma adduata kullum shine Allah yasa wannan jingikirin yazamo babban alkhairi agareki,
Wlh banajin dadin yanda su dattijo da su Dadah suka sakomin ke gaba akan rashin auren Nan gashinan umma itama tabisu tana tsangwamanki da rashin aure.

Sai alokacin tasaki wani kyakkyawan murmushi tana kallon kyakkyawar fuskar Hanifan tace”

Bana damuwa da dukkanin zancensu na rashin auren
Koba komai Baga Abaas Nan ba tunda sun saka auren 4month masu zuwa ai zancen ya mutu yanxu Ina Dan samun sauqinsu.

Bata fuska Hanifa tayi tana cewa”

Abaas lamido bazai taba auren Naj Dina ba matuqar bazai sauya hali ba.

Murmushi me sauti Naj din tayi tana riqota da murmushi akan fuskarta tace”

Kuma Kinga as long as Hanifan Naj bata Aminta dashiba Naj bazata taba aurensa ba.

Dariya suka saki lokaci daya sbd yanda haryanxu suke irin wannan wasar wa junansu
Hanifa tace”

Alqawarine ai kidainma Wasa da zancen,
Inshallah nice Zan tayaki zaban mijin danasan zai darajanta min ke tunda idonsu umma ya rufe Akan kowa Kika samu ki aura nikuma bazan yadda ba taqarasa tana ‘yar dariya,
Kinga dama shima Marshal nafada Masa Ni Zan tayasa tantance Matar dazai aura sbd shima shine ya tsaya akan nayi aure da wuri sbd yanayin qarancin lafiyana kema kece Kika tsayawa Isma’eel sbd lokacin amininsa arfat yakawo kudin aurenki Kika ci amanata Kika bi bayansu Saida ya aureni da yanzu lukuman ne mijina ko?
Dariya suka kwashe da ita su biyun suna tunano lokacin musamman yanda Hanifan Bata wani so auren Isma’eel din ba Amma da hajjo da Naj din suka hade Mata Kai gurin Dad dinsu akai auren sbd dama ya dade Yana Sonta tun suna secondary school sbd ‘dan yayar dad din nasu ne
Shima Marshal Isma’eel din yafi kwanta Masa sbd yasanshi sosai Yasan halayensa ba laifi Kuma shi Dama Wanda zai iya kulada Hanifan da lalurarta yake muradin ta aura din shiyasa.

Dan qaramin mayafi Naj din ta Dora akanta suka fito daga dakin har lokacin Fuskokinsu dauke suke da yanayi na dariyar tuna baya dasuka samu kansu
Anty Amina ta kallesu tana cewa”

Hanifa ki fadawa hajjo yau ba hirar dare saidai gobe kayan umma dazata aika sako abekuta zamu hada.

Anty Amina wannan fira taku keda hajjo ai yau kuwa zatayita mitan rashin firar Daren nan dakuke.

Fita sukai umma dai da guntuwar harara tabisu da ita Dan sun kasa gane abinda yake cin ranta,
Tsakani da Allah ‘yarta Kamar Naj wadda kaf gidan tafisu ilimin Boko da wayewa tareda abun duniyama ace anyi sadakarta ga duk me rabo idan Batai aureba wlh zata mugun cutatuwa Dan kuwa ciwon zuciyama kamata zaiyi Amma hanifar datakeson ta karkato Mata Naj din tamafi naj din kasa fahimtarta tana ganin Kamar sun takurawa Naj din.

Dakin Dadah suka nufa tun Basu qarasa ba ta tsuke fuska Dan tana zaune kofar dakin kan kujerar roba da qaton farin glass dinta.

Dariya Hanifa tasake tana qarasawa gabanta da cewa”

Dadah my love.

Uwar harara dadar ta sakar Mata tana hararar gefen Naj tace”

Yaudarata za’a kenan?

Da sabuwar dariya Hanifa tace”

Mezaisa na yaudari Dadah me ran qarfe¿
Kawai dai dama……

Cikin hanzari dakuma zallar Kokonto Dadah ta katse Hanifan da cewa”

Wlh idan har kikacemun matsala yarinyar Nan tasamu da Abbas to wlh yau daga ita har uwarta kwanan bacin Rai zasuyi mummuna kuwa
Kuma wlh gobe zuwa jibi suga ‘danyan hukuncin dazansa Dattijo ya yanke Inga qarshen Boko da wayewa…

Zubawa Dadah fararen idanuwanta Naj tayi tana sauraron kalaman bacin Rai na fada na fitowa daga bakin dadar take tahau fada me tsanani Wanda yasa umma yin tsit daga aikin datakeyi Dan tana jiyo fadan Wanda aketa zubawa har ita ba’a ragawa ba qarshe ma korarsu tayi daga gabanta tana tabbatar musu da cewan aure da Abaas anyi angama idan Kuma shiyace yafasa da kanshi wlh auren sadaka zasuyi Mata can ta qarata da kyawun idanma shine take korar maza akansa.

Jiki a mace suka bar gurin suka fice gabaki daya Kai tsaye suka shige gidansu Hanifan Wanda gabaki daya Anguwar Babu kamarsa ga girma da kyau dakuma wani irin tsaro na musamman na sojoji Dan cikin gidan ma gate biyu kafin ka Isa ainihin cikin harabar gidan Wanda ke daukeda motoci na alfarma wainda ake sauyawa akai akai kusan guda shida a ajiye,
Uku na Marshal ne sai guda daya ta Dad dinsu sai daya ta Hanifan ce dayar Kuma ta hajjo ce wadda Bata cika hawa ba sbd Bata fita Sam Sam sai Dole Kuma driver ne yake tuqa ta,
Hanifa ma Sam Bata Jan mota sai Dole sbd yanayinta Wanda yasa dad dinta dashi marshal din suka qarfafa dokan rashin tuqin itama driver ne da ita sai Kuma idan zasu fita da Naj sai Naj din tayi driving.

Suna Shiga qaton palon su ruqayyat da Khadija dake palon suna gyaran yamma Wanda yake kamar Dole koba komai qaida sai sunyi gyaran safe Dana yamma suka Dan durqusa suna musu sannu da shigowo.

Kai tsaye palon dazai isar dasu dakin hajjo suka nufa suna shiga tana zaune makeken palonta me ado na qyallin arzikin duniya da Allah yabasu sanyin ac Dana qamshin turarukan wutan umman Naj daya Gama Kama koina na palon kujeru da curtains duk qamshin sukeyi me Dadi da sanyi
‘yar dattijuwar na zaune fara tas da ita me zubin hasken larabawa tana sanye da doguwar jallabiyar mutanen Kuwait me Fadi tana dagowa ta kallesu tasaki wani irin nutsatsen murmushi tana kallon kyakkyawar fuskar Naj da ako yaushe take sanyata murmushi Dan Kamar yanda take tsananin so da kaunar Jokokinta biyu rak Haka take tsananin so da kaunar Naj din musamman daya zama Naj din tazama tamkar jinin gidan itama danma Naj din taqi dawowa gurinta gabaki daya saidai yau ta kwana gidan jibi Kuma tace gidansu zata kwana danma Allah yasa Hanifa ko bayan datai aure Bata barsuba tana nan gidan saidai idan Isma’eel yazo gari ya dauketa su koma gidansu Yana komawa ta dawo Nan gida sbd duk da akwai Yan aikinta Hanifan hankalinsa Bai kwantaba daya barta ita kadai da masu aiki Dan yanayinta.

Zama gefen hajjo Naj tayi tareda kwantawa ta kwantar da kanta kan cinyar hajjon ta lumshe fararen idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya ahankali tace”

Hajjona yau akan shimfidarki zanyi bacci.

Shafa kanta hajjo tayi cikin kulawa tace”

Kiyi hkr NAJMA kinji komai lokacine dashi rashin aure ba wata mummunar kaddara bace idan su dadan sun gaji da zamanki a gidan Ni subani inaso.

Murmushi kawai Naj din tayi tana cewa”

Hajjo idan aka baki Ni kema Zaki gaji da zamana ba aure wataran.

Murmushi kawai hajjon tayi tana kallon Hanifa da duk yanayinta bayada Dadi har lokacin akan fadan Dada Wanda akwai cin zarafi masu ‘daci da yawa aciki.
#MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_

 

4
Anan gurin hajjo tayi niyar kwana Dan Haka Babu wata damuwa Kamar yanda tasaba rayuwarta na rashin riqe damuwan Abu ta sakewarta musamman dayake tanada daki daki me zamanta agidan a cikin babban palon hajjon wanda dakin Babu abin daya rasa najin Dadi da tsari musamman irin na rashin hayaniya da akasan Naj din batada ita Wanda hanifa ma anan dakin take yanzu idan tana gidan sbd tabaro part dinsu Dad dinsu tunda Babu kowa a part din.
Tanada Yan wasu kayan sawa a gidan Dan Haka Kai tsaye bayan sun Gama cin abincin dare Bata tsaya doguwar Hira ba Shirin bacci tayi bayan tayi sallah ta kwanta sai lokacin tabi misscalls din Sarah da Kira cikin nutsuwa tagama sauraran bayananta na aikin data bar Mata kafin ta Dora da cewa”

Ummm Naj dazu bayan tafiyarki Abaas yasake dawowa yasa an fiddo Masa da dukkanin record dinmu na aiki tun na January ya soke wasu daga ciki tareda fidda Kura kuren dazasu Iya bamu matsala Kuma Yana maganar a sauyani daga gurinki.

Dan sanyi muryarta tayi cikin bayyanarda rashin Jin dadinta tace”

Naj kiyi magana dashi please abarni agurinki sbd Ina barin gurinki na tabbatarda korata aikin zaiyi gabaki daya.

Ajiyar zuciya Me sanyi Naj din ta sauke tana tareda bude Baki cikin muryarta me Dadi Kai tsaye tace”

Karki damu zanyi magana dashi gobe
Kawai dai ki ringa kiyaye Masa tunda Kinga yanayin kalar fushinsa baya tunani me kyau idan ransa ya baci.

thank you Naj.

Ok then see you tomorrow”Naj din tafada tana kashe wayar tareda ajewa gefe tana Dan zamewa daga jingine datake akan gadon ta kwanta tana lumshe fararen idanuwanta ta rufe tana Dan yin bacci.

Hanifa dake zaune tana kokarin Kiran wayar mijinta tana sauraron wayar da Naj din keyi ta Dan saki guntin tsokin baqin cikin Abaas din datakeson koyawa zuciyarta Aminta dashi amatsayin mijin ‘yar uwar tata tun yanzu.
Kashe wayarta tayi tareda miqewa ta zagayo tahau gadon ta kwanta tunda takasa samun Isma’eel din ga Naj shegen miskilancinta wani lokacin baya barinsu yin wata doguwar fira.

Qarfe 8 na safe ta fito wanka daure da towel me kauri tanaji wayarta na ringing Taki ko kallon inda take ta nufi gaban madubi tafara shafa Mai Wanda dama kusan komai product daya suke amfani dashi itada Hanifan.
Shiryawa tayi cikin doguwar riga maroon ta daura qaramin gyale akanta ta fito tana qamshin turaren Vivian rosalle har lokacin Hanifa na kwance sbd ciwon wuya data tashi dashi Wanda dama kullum cikin ciwuka take sbd sikla ce lafiyarta qarantacciyace sun Saba da rauninta shiyasa qaninta marshal baida wani abinda yafi komai so a duniyarsa bayan ita sai kakarsa tukuna mahaifinsa.

Dakin hajjo tafara zuwa har lokacin hajjon Bata farka ba itama Dan Haka Kai tsaye ta wuce kitchen su ruqayyat na ganinta cikin girmamawa sukace”

Ina kwana Anty.

Lafiya kalau ruqayyat
Please ku hado breakfast din Hanifa akawo daki batajin dadi.

Fridge ta qarasa ta bude ta dauko madara ta zuba a cup tareda zuba ruwan zafi aciki tayi dumi ta zuba Zuma kadan aciki ta dauka ta shanye ahankali tareda aje cup din ta koma ta diba dabino uku taci ta fice daga kicin din su ruqayyat suka bita da kallo Kamar dai yanda suka Saba sbd mamakinta har kullum Baya sakinsu na yanda take komai nata cikin wani irin burgewa da qaidojinta da nata ita ta shardantawa kanta su sbd maintaining rayuwarta.

Kalar abincin datake duk da gidansu ba masu halineba ta qayyade abinda take ciwa cikinta Wanda yake kamar dieting ne takewa kanta sbd gabaki daya rayuwarta batason abinci me nauyi tun tana yarinya Haka take idan taci abinci me nauyi sosai Yana wahalar da ita shiyasa data girma ta San yancin kanta tanada abubuwan datake ci kawai da wainda bataci Wanda shima yake qara bayyanarda miskilancinta da burgewarta da wasu ke gani acikin gidansu kuwa suna daukan hakan amatsayin nuna wayewa da nuna kudi Wanda yasa mazan ke ganin tafi karfinsu Ana samun matsalar fasa aurenta Kashi Kashi Kuma Sam Bata nuna damuwar hakan shiyasama ta tabbata dai itace Bata tashi aurenba inji su Dadah da Dattijo.

Cikin kulawa ta taimakawa Hanifa da wuyan ya riqe Mata sosai kamar ba lafiya ta kwanta ba tasamu ta danyi breakfast sai alokacin takira Dr said Wanda shine likitan Hanifan ta sanar dashi.
Dayake yanason ganin Naj din sai yace zaizo yakawowa Hanifan magani kafin ya wuce aiki.

Kafin Dr said din yazo taje dakin hajjo ta gaidata tareda Hado Mata ruwan dumi da Zuma Wanda itace hajjon ta koyawa Naj din Sha kasancewan itama abincin masu nauyi Basu cika Bata lafiyaba.

Bayan ta dan sha ta dago ta kalli Naj din tace”

Zaki tafi office ne?

Da fararen idanuwanta ta Dan kalli hajjon ta maida kallonta kan agogon dake daure a hannunta tana cewa”

Eh Amma ba yanzu ba Ina jiran Dr sa’id ne zai kawo maganin Hanifa wuyanta ya riqe Bata iya motsawa.

Dan numfashi hajjon ta sauke tana Dan jinjina Kai irin na manya tace”

Yau Kuma da riqewan jijiya ta tashi
Allah yabata lafiya.

Amin Naj din tace tana miqewa sbd ganin Kiran Dr sa’id akan wayarta.

Kamar dai yanda yasaba da gidan da dukkanin iyalan gidan tareda farin sani da securities na gidan sukai Masa amatsayin likitan Hanifan yasa Yana zuwa Kai tsaye aka bude Masa qaton gate din gidan yashigo har ciki da motarsa Amma iyakacinsa gate din farko baqi basa shigowa da motocinsu gate na biyun Dan Haka Yana parking ya fito yasake gaisawa dasu Mike ya wuce ciki Kai tsaye.

A babban palon farko na gidan ya tsaya Wanda yake matsayin na baqi ya zauna bayan su ruqayya sun kawo Masa ruwan black tea suna tiriri sun ajiye Masa kenan saiga Naj din ta fito ta qaraso tareda zama kujeran dake kallon tasa Tai Masa kallo daya ta Dan dauke Kai tana cewa”

Barka da safiya Daddyn Naufal.

Wani irin kyakkyawan murmushi ya sauke sbd a duk lokacinda takirasa da dadyn Naufal zancen na tsumasa sbd hakan na nuni ne da kusanci a tsakaninsu har wani lokacin Jin yake inama ace itace mahaifiyar Naufal din.

Kwarjininta yasa duk yanda mutum yaso baya iya Mata kallon qurulla Wanda shima wani lokacin hakan nasashi Jin fargaban zai iya mallakar Naj din kuwa Dan dai gskian magana bakowane namiji ne zai iya cika idon Naj din ba haryayi Mata irin kallon tsaf kona qurullaba saidai kuwa idan shima nasa kwarjinin ya take nata ne hakan zai iya yiyuwa.

Dan numfashi ya sauke Yana janyo qwazonsa na namijin daya ciki ya sake kallonta yace”

Barka da fitowa Naj.
Ya hajjo ta tashi lfy?
Yasu umma ma?

Alhmdlh” tafada a taqaice tareda sake kallonsa tace”

Maganin Hanifan.¿

Miqa Mata qaramar ledan maganin hannunsa yayi Yana cewa”

Kada a shafa Mata komi agurin Tasha maganin kawai saita gasa jikinta da ruwan dumi shikenan zai sake.

Ok bari nabata maganin yanzu coz tana buqatansa yanzu Nan.

Ta dauka lokaci sosai kusan awa daya kafin tafito cikin shirinta tsaf na zuwa office ta fito daga gidan gabaki daya tashiga gidansu cikin sa’arta Dattijo baya Nan bare maganar fadan jiya na Dadah ya tashi Dan Haka Kai tsaye sassansu ta nufa
Ummanta na daki tana ayyikanta taje ta gaidata umman ta Gama yimata Gore goren da tariga tasaba dasu ta fito suka hada ido da anty Amina dake zaune tsakar gidan tana waya Ta taso tana kashe wayar suka shiga dakin Naj din tana sake bayyanar Mata da kada kalaman umman su daga Mata hankali tacigaba da rayuwarta cikin salama sbd Haka Allah ya tsaro Mata ba komai bane rashin auren da wuri tunda su ganshinan sunyi sun fito din.

Murmushi kawai Naj tayi tana cewa”

Anty Amina Ni wlh kinmafi bani tausayi sbd fadan umma akan fitowan Nan Taki.

Kiji yarinya ke bakiga tausayin kankiba
Duk rigimarsu gwarani nayi harna tara yara nafito
Gwara dai kiji tausayin kanki kisamu kiyi shine rufin asirin.

Wani murmushin kawai tasaki tareda daukan abubuwan dazata dauka ta fito ta fice
Tana fitowa ga mamakinta Dr sa’id na Nan waje Yana jiran fitowarta ya ajeta office Dan batason doguwar hayaniya yasa kawai tashiga suka wuce Amma cikin ranta tana Dan fatan kada su tadda Abaas a ALFA’S din sbd bazata iya daukan hayaniyarsa da fitinarsaba ciwon Kai kawai zai sakar Mata na Wunin gaba daya.
#MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_

5
Duk yanda Dr sa’id yaso suyi mgn Bata yiyuba sbd ganin motar Abaas lamido na cikin gurin hakan ke tabbatarda Yana Nan Kuma ko ayanzu Haka yasan Yana iya ganinsu daga sama ta office dinshi
Shi kansa baya buqatan iya zallan wulaqancin Abaas din a bainar jama’a bakuma Dan komai ba sai Dan Naj dayasan tana iya kokarinta gurin tolerating din Abaas din Wanda gabaki daya Bai cancancetaba Kota Ina Sam sam Allah ne kawai ya bashi babbar sa’ar samunta idanma shine ya aurentan kenan Dan shima Bai cire raiba yanama Dan ji a jiki jikinsa Kamar shine ma me sa’ar aureta din kowama ya huta.

Fitowa yayi ya zagayo zai bude Mata ta bude da kanta ta fito da Dan guntun murmushi akan fuskarta tace”

Thanks Dr.

Jinjina Kai yayi Yana kallonta yace”

Atashi lafiya.
Ya juya ya koma cikin motarsa ya tada yabar gurin bayan tuni ta shige alfas din Sarah dake jiran isowarta ko Dama Bata hayeba tana qasa tana Nan reception tana jiranta sbd bazata fara isaba it’s kadai Dan shakkar Abaas zai iya Mata komai kafin Naj din taqaraso bazata iya ba gskia Dan yanda ya qware agurin cin zarafin mutum ta yanda duk hakurinka da dannewarka sai ranka yayi mummunan baci zata iya kasa hkr ta maida Masa mgna saidai ya koreta aikin Amma sbd Naj yasa itama take kokari tana hadiyewa tareda jinjinawa jarumta da qarfin zuciya irin na Naj datake hadiye maganganunsa.

Ma’aikatan dake gurin na qasa da Naj din gaidata suka hau yi suna Mata barka da isowa ta amsa musu tana wucewa kaman yanda ta Saba suka wuce Sarah na gefenta tana fada Mata Abaas yariga ya iso yau tunda safe ya iso office din.

Suna Isa cikin office dinta ta ajiye handbag dinta tareda waiwayo ta kalli Sarah dakyau kafin ta bude Baki tace”

Sarah daga yau banason maganar Abaas a office please
Zuwansa da rashin zuwansa duk bana buqatan sani okay??

Yes ma’am.

Juyawa tayi tana Shirin zaunawa aka turo kofar aka shigo
Sarah ce kawai ta juya tana ganin Waye ta Dan matsa gefe tana cewa”

Good morning chairman.

Ko kallonta baiyiba ya qaraso ya zauna kan sofa dake office din tana ganin Haka ta sulale ta fice bayan ta ajewa Naj laptop dinta.

Har lokacin Naj dake tsaye Bata juyoba tana hankalinta nakan wasu takardu dake hannunta ta sai qamshinta me sanyi da Dadi dayaketa sake gauraye office din Hadi da sanyin AC Wanda suke qara qona zuciyar Abaas din.

Dagowa yayi ya kalleta tareda zubawa fuskarta dakeda wani irin sanyin kyawu da nutsuwa tareda wani irin fizgar mutum ido kafin ya taso ahankali ya dawo gabanta ya tsaya Kai tsaye yace”

Meyasa Dr sa’id ne kawai zai kawo office?

Dan dagowa tayi ahankali ta kallesa tareda rufe takardun hannunta din ta ajiye ta koma ta zauna a natse tareda fiddo wayarta daga jaka cikin muryarta me kamewa tace”

Yaje duba Hanifa ne ya wuto Dani.

Rintse idanu yayi cikin qoqarin controlling zuciyarsa yace”

Kullum bashida aikine saina zuwa dubata kokuwa itace kullum batada aiki saina kwantawa ciwon dashine zaije Yana dubata ta yanda ke Kuma zai ringa kasancewa dake kokuwa nine da akewa kallon Mara hankali akeson shashantarwa da wannan zancen kullum”” ya qarasa fada Yana Dan daga murya sbd maqura da bacin ran nasa yake qara kaiwa.

Wannan karon kallon mintuna biyu cif tayi Masa tanason fahimtan idan Abaas din Yana lafiya kokuwa sbd kalamansa sun Sosa ranta Dan kuwa kamar Yana cin zarafinsu ne daga ita har Hanifan.

Kamar bazata tankasa ba saita dauke kallonta daga kanshi tace”

Zaifi idan ka tsaya da rashin fahimtanka a iya inda ka Saba kawai.

Cikin fushi yace”

Alaqarki da likitan Nan ta wuce dukkanin hakurina sbd Naga kin sabarwa kanki iya zama cikin motarsa Dan Haka tunda kin yanke zama taxi motar kowa saiki zaba tsakanin Ni ko shi waye Dan bansan ya alqarku zata cigaba da kasancewa ba bayan munyi auren….

Jajir idanuwanta sukai saidai har lokacin Bata dago ta tankasaba saima hakan yaqara qunan zuciyarsa yaci gaba da fada cikin maganganu masu dacin sauraro Amma taqi sake ko dagowa ta kallesa hakan yaqara lalata duk wani sauran hakurinsa ya fice ransa amatuqar bace.

Harya Gama ya fice tana zaune a inda take da wayarta a hannunta tana dubawa,
No Hanifa takira Bata daukaba Dan Haka takira no hajjo taji Yaya Hanifan take hajjon ta sanar da ita cewan wuyan dai Bai sakiba har lokacin.

Sama sama tasamu tayi wasu ayyukan ta tattara tabar office din Takoma gida sbd hankalinta gabaki daya yakoma kan Hanifa sbd tasan yanayin ciwukanta yanzu a Haka saita share kwanaki wuyan a riqe.

Tana Isa Kai tsaye gidansu Hanifan ta sauka Koda ta iso jikin yadan qara tsanantawa Hanifan Dan Haka kamar dai koyaushe itace tareda ita,itace tasan ciwonta da damuwarta da kulawa da ita bayan hajjo wadda itakuma tsufa yazo Mata bazata iya wani abun ba.,
Tun suna secondary Naj tasaba da kulawa da Hanifa sbd duk gata da tarin dibbin dukiyardasu Hanifan suke dashi basa tareda kulawa ta wani Dan uwa,
Masu aiki sune komai nasu sai hajjo wadda itama dai komai masu aikin ne keyi idan har Hanifa na buqatan kulawa da soyayya irin ta uwa to agurin umman Naj ne take samunta sbd umman da mahaifiyarsu aminai ne Suma tun yarinta shiyasa ma Suma suka taso Kamar umman ce uwarsu,
Umma na tsananin qaunar Hanifa Wanda yasama Hanifan kejin qarancin rashin uwa fiyeda DEEN Wanda shi asalima ko uwar tasa Bai saniba sbd gurin haihuwarsa ta rasu shiyasa ta taso a wani irin miskilallan mutum na qarshe sbd bai taso cikin hayaniyar taron mutane ba tun fara high school dinsa yabar qasar Yana Hawaii acan yayi karatunsa acan yake rayuwarsa ta matsayin babban Navy marshal Wanda zallan iliminsa da yakaisa acikin shekarunsa da basuyi yawa ba hakan Kuma yasa da yawa manyan mutanen Nigeria dake can harma Dana wasu qasar suna kawo sha’awan son hada zuria dashi saidai haryanzu kaman Shirin aure baya gabansa Dan baitaba sha’awan aure yanzu ba duk da hajjo da Hanifa sun fara nuna damuwarsu akan hakan Amma Yana dakatar dasu baya buqatan su takurawa junansu shiyasa ma basa matsa Masa sosai da maganar Dan sanin bayason yawan nanata zance.

Umman Naj itace ta raini Deen din tun bayan rasuwar mahaifiyarsu har Saida ya girma yakai shekaru biyar kafin yafara kwana gidansu ahaka ahaka harya koma gidansu gabaki daya sbd lokacin dad dinsu yayo aure shiyasa a duniyarsa bayan hajjo da Hanifa da dad dinsa umma itace uwa wadda tabashi so da qauna ta uwa duk da itama umman ta Saba sosai da halinsa na ko inkulan tun Yana yaronsa saidai duk yadawo Yana zuwa har cikin dakinta ya zauna tayita kulawa dashi danma yanzu sbd yawan gidan nasu yasa ya daina Shiga idan yazo saidai tayi girkin abincin dayafi so ta aika Masa daga baya taje har palon hajjo acan suke Yar firarsu ta uwa da ‘da.

No din Dr sa’id Naj takira saidai Bai daga ba Dan Haka tayi tunanin Yana aikine kokuma yashiga CS Dan yawanci hakan kesashi barin waya office Dan Haka Bata Bata lokaciba tasake hada ruwan dumi ta gasawa Hanifan jikinta tareda sake Bata magani gashi duk yanda taso Hanifan taci abinci takasaci qrshe dai da kanta ta hado Mata ruwan dumi da Madara da Zuma tasamu ta iya Sha tayi bacci.

Saida Hanifan tayi baccin tasamu ta tube tafada toilet tayi wanka tayi sallah tafito palon hajjo ta nufi dining ta zubo spaghetti kadan da salad tadawo ta zauna gurin hajjo suna Yar firarsu akan rashin lafiyan Hanifan da tuni Dad dinta yafara Kira sbd hajjon data fada Masa
Shima Isma’eel mijinta tun Naj na office yake Kira sbd Hanifa Bata daukan wayan kowa.

Tana Gama cin abincin kicin kenan saiga ummanta tashigo tareda zainab Yar gaban goshinta ayanzu kenan ‘yar anty Amina.

Zama umma tayi ita Kuma zainab Naj ta miqa Mata plate din hannunta tana cewa”

Ki Kai kitchen.

Sosai umma ke girmama hajjo tamkar mahaifiyarta Dan Haka firarsu suka Dora daga nan Naj na gefe tana aiki a laptop dinta saiga Kiran Abaas yashigo wayarta ta dauke ido daga kan wayar tana cigaba da aikinta yasake Kira Bata daukaba har so uku ko kallon wayar Bata sake yiba.

Sai yamma sosai bayan ma Hanifa ta farka su umma suka tafi Takoma gurin Hanifan wadda video call din marshal yashigo wayarta daidai shigowan Naj din.

Qarasowa tayi gurinta tana Kiran sunanta cikin taushin muryarta tana cewa”

Yaya wuyan?

Nuna tayi Mata da wayarta ahankali tana cewa”

Please ki amsa mun Kiran.

Kallon wayar Naj tayi taga sunansa baro baro ajiki takai hannunta ta dauka wayar tana dawowa gefen Hanifan ta zauna ahankali tareda daukan Kiran ahankali kyakkyawar fuskarsa ta bayyana akan wayar Yana zaune palon gidansa dake _Honolulu Hawaii US_ sanye cikin black three quarter da black armless shirt dasuka matuqar bayyanarda hasken fatarsa data Gama renuwa acikin hutu da lafiya sai daukan ido fatar jikinsa takeyi sbd yanayin kayan dake jikinsa dauke Kai Naj tayi tareda miqawa Hanifa wayar tana tashi daga gurin Dan gidansu takeson Shiga Dan Haka Kai tsaye ta fice.

Wayarta ce kawai a hannunta ta fito daga gidan ta nufi kofar gidansu ta shige ta nufi sashensu Kai tsaye saidai tana Shiga ta tadda Dattijo tsaye ga Dadah a zaune hakama ummanta dukkaninsu suka zubo Mata ido Banda ummanta da abun duniya ya taru yayi Mata yawa idanuwanta sun kada sunyi jajir da alama dai ba lafiya ba.

Qarasowa tayi cikin nutsuwa tace”

Dattijo Ina wuni,
Dadah barka da yamma.

Ko kallonta dadan bataiba sbd wannan karon tsaf tagama shirya duk wani rashin arziki da Naj din Bata tunani akan wannan maganar.

Kallonta Dattijo yayi da kyau Yana gyara tsayuwa da gyaran murya yace”

Ki saurareni da kyau kiji abinda Zan fada Miki sbd nafadawa mahaifiyarki kalma bayan kalma Amma Naga kamar ke din kinason watsar da maganar Kamar yanda kike watsi da masu neman aurenki,
Nafada naqara fada wallahi tallahi wannan karon kika Kori abbas da halinki yace yafasa auren Nan wallahi duk Wanda nasamu aura Miki zanyi bazaki maida wata a gidan Nan ba,
Yafara gajiya da halinki yazo ya sameni dazu ransa amatuqar bace na bashi hakuri akan za’a matso da bikin Nanda wata daya ma ayi a huta Dan Haka acikin watan Nan daya Kikai Masa abin dayasa yafasa wannna auren keda mahaifiyarki ku shirya hukuncina dazai biyo baya.

Daga fadar Haka ya juya ya fice Bai qara da komaiba sbd bacin ran al’amarin auren Naj din dayake kaisa maqura.
#MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 6_*
Shiru ummanta tayi zuciyarta na suya da bacin rai da damuwa hadda sirkin takaicin Naj din wadda take ganin duk itace take qara tsimar da duk wani bacin Rai dake faruwa tsakaninta da Dattijo da Dadah wadda ita kaf duniya Bata ganin laifin kowa akan rashin auren Naj face ita mahaifiyarta sbd ganin suke idan su Naj tana Shure maganarsu ta lalacewar da neman aurarrakinta keyi it’s uwarta ta tsaya ta ganar da ita Amma Ina ganin suke itacema take qara daure Mata acewarsu hamshaqin dayayi mugun ci ya tada wuya suke jira Wanda Allan daya halicceta yafita sanin cewan wlh a duniya tafi kowa farin ciki da qaunar ace yau taga ‘yarta Naj tayi aure kodan irin daukan ido da fizgar maza datake dashi Amma saigashi qaddara ta Allah tasa duk kyawu datafi Yan zuriar gidan kowa yayi aure yabarta hatta qannenta da dama wainda suke Yan uba dama na dangi sunyi aure sun barta.

Ahankali Naj din ta juyar ta nufi dakinta ta Murda kofar ta bude tashige a Karo na farko dataji zancen Dattijo akan rashin aurenta ya daketa badan komaiba sai Dan yanda ako yaushe ake Dora laifin akan ummanta wanda keda kalamai na cin zarafi.

Bakin gado ta zauna ahankali tareda sauke numfashi tana Dan dafe goshinta ta lumshe ido tana tunanin itafa duk yanda akaso tayi aure da yanda ake ganin kamar taqi auren bazata jawo namiji da aura ba da qarfi Amma meyasa su basa gane hakan?
Shin menene akewa maza su tsaya su aureka Wanda ita Bata saniba ko shine yasa ake fasa auren nata bayan dai tasan acikin wainda sukai neman aurenta suna fasawa kowanne tana Dan iya nata kokarin gurin kulasa da Yar sake fuska tana iya kokarinta gurin aje miskilancinta ta kulasu yanda ya kamata Amma duk da hakan suke fasa aurenta bayan kowannensu Saida ya Aiko magabatansu dayanma har fara bikin anyi aka fasa sakamakon Wai yagano gabaki daya taba sonsa Bata taba sonsaba kawai aurensa zatayi Dan Ana cewa Bata aure.
Wannan shine yafi konawa Dattijo Rai aduk cikin masu neman aurenta suna fasawa sbd har Gama komai anyi Amma zancen ya watse tun akan wannan al’amarinta yaqara baqanta ransa shiyasa yanzu ya dage ya tsayawa Abaas sbd kada shima ya fasan duk da kuwa yagama karantar halayen Abaas sunada matuqar wuyar zama sbd zafin ransa yasa wani lokacin harshi rufe ido yakeyi Yana fada Masa magana musamman daya Gama gano sun Kai maqurar matsuwa a son aurarda Naj dayasa suke lallabashi shiyasa yasamu damar yimata duk kalar abinda yaga dama sbd yasan kome zaiyi baza’a fasa auranba tunda auren akeso ido rufe.

Anty Amina ce tashigo dakin ranta Babu Dadi itama sbd tsakani da Allah suna Jin zafi da ‘dacin dukkanin wani fadan cin zarafi da akewa mahaifiyarsu saidai Kuma Babu yanda zasuyi tunda mijine agareta hakama Dadah uwace to Amma Kuma meye laifinka Kai idan anqi aurenka¿

Cikin nutsuwa anty Amina ta zauna kan kujeran madubin dakin ta kalli Naj din a natse tace”

Najma hakuri Zakiyi ki daure ki Kuma qara daurewa da halayen Abbas ayi auren Nan ki huta da wannan fitinar umma ma ta huta da wannan fitinar muma masu gani zuciyoyinmu na daci mu huta,
Idan Kuma kina ganin bazaki iya auren Abbas din ba ki dakatar dashi Kai tsaye saiki bawa Dr sa’id damar fitowa sbd yamafi Abbas din cancanta da mutunci tareda nutsuwar aura tako Ina,
Auren Abbas tabbas idan ba wani rahaman ubangiji babu ta inda zaku samu nutsuwa tako Ina Dan zafinsa yayi yawa kekuma miskilancinki yayi yawa zaku wahala ku duka.

Kallon anty Amina ta dago tayi da fararen idanuwanta dasuka Dan sauya Wanda iya Nan kake iya ganin damuwarta sai Kuma ahankali ta saki Dan guntun murmushi tareda bude Baki tace”

Nagode anty Amina.

Shiru sukayi tsawon mintuna biyar kowa kowa da abinda take tunani cikin ransa kafin ta miqe ta fice daga dakin Kai tsaye ta nufi dakin ummansu dake zaune kan kujera shiru da alama damuwace take cinta bakuma yanda zatayi tunda itama tayi iya yinta bazata jawo mijiba ta daurawa Naj din aureba duk abinda sukeji Dole Haka zasuyita daurewa suna hadiyewa har Allah yakawo ranar auren.

Qarasowa tayi gaban umman wadda sai alokacin ta dago a sanyaye ta kalla Naj din ta dauke Kai tana cigaba da tunaninta.

Zama Naj tayi gaban umman tareda riqo hannayenta tana kallon fuskarta ta bude Baki ahankali tace”

Umma kiyi hakuri kadaki saka damuwa aranki,kinada ilimin addini umma kinsan cewa aure lokacine da ubangiji ya dibar maka wlh idan lokacin Nan baiyiba bazakayiba meyasa kike damun kanki da abinda su Dadah ke fada bayan kinsan kinamun addua Kuma insha Allah zanyi auren kila Wanda Allah ya zabarmun ne a mijin Bai bayyana ba kokuma kila lokacin ne haryanxu baiyiba da saura idan Kuma auren ne Allah baice nayiba harna bar duniya Yaya zakuyi da hukuncinsa?
Umma addua kawai Zakiyi Allah yasa hakan shine mafi alkhairi gareni dakuma iyayena.

Kallonta umman tayi idanuwanta na kadawa jajir sbd tabbas su yayanta basusan irin mugun zama da cusgunawa tareda tozarci da hantarar datake samu daga dattijon har Dadah akan wannan al’amarin,
Ta dauka,ta hadiye,ta danne,ta shanye,ta boye duk wani mugun wulaqanci da tozarcin dasuke Mata akan al’amarin Wanda matsi da fitinarsu yasa taji Kota Yaya sotake Naj din tayi auren kowama ya huta kishiyoyi masu Mata dariya su daina Yan gidan masu zundenta su daina,yan matan gidan masu cewa ilimin Boko da aikin office yasa Naj taqi auruwa duk kowa ya daina a zauna lafiya,
Da wanne zataji gata da tsohuwar bazawara a Naj din.

Sake kallon Naj tayi da idanuwanta dake jajir har lokacin ta bude Baki Kai tsaye da sanyin murya tace”

Najma nasan aure lokacine Amma Kuma Allah yakawo Miki mijin meyasa bazaki lallabashiba har ayi auren tunda dai haryanason auren naki¿
Abbas dinnan duk halinsa dakike gani idan anyi auren lallabashi Zakiyi zai sauya shikenan kowa ya zauna lafiya.

Zubawa umma ido tayi akaro na farko tana Jin dacin hukuncin ummanta ahankali ta bude Baki tace”

Umma halayen Abaas ba masu lallabuwa bane…..

Ta Yaya Zaki yanke hukuncin ba masu lallabuwa bane tunda Baki auresan kin gani ba saidai idan shima kinada Shirin sakawa ya fasa auren Dan shima kina ganin bekai bane kaman yanda mutane suke fada.

Da mamaki ta sake zubawa umman ido tace”

Umma idan Kuna tunanin naqi aurene Dan akwai abinda nakeso agurin namijin dazan aura Kuna kuskuren fahimatar halayena da kuka sannu dasu duk da karatun danayi da da wasu cigaban Dana samu hakan Sam bayada alaqa da rashin aurena…

To ki amince da Abbas kawai ayi auren Nan idan ba hakan bane Najma sbd idan dukiya da rayuwa ne Abbas din yanadasu Kuma Yana tsananin sonki idan harkin daukeni mahaifiyarki…..

“Umma kadaki Bari fushi yasa ki lalata rayuwar Naj mana.” Anty Amina ce ta fada hakan tana isowa gaban umman Wanda idanuwanta suka rufe gabaki daya.

Naj kasa cewa komai tayi sai idanuwanta dake kan umman sunyi jajir ahankali ta dauke idonta ta bude Baki tace”

Zan aura Abbas idan har hakan Kika zabarmun.
Juyawa tayi ta fice daga dakin gabaki daya tana shiga dakinta wayarta kawai ta dauka ta fito ta fice.

Dadah dake zaune tsakar gidan tana Jin duk hayaniyar tasu farin ciki yacika ranta tunda tasan yanzu Kam Naj din bazata bada matsalaba tunda Zuciyarta ta karye da abinda umman tayi Dan Haka ta tashi Takoma dakinta a Daren zata fadawa Dattijo ya sanarda Abbas ya sanarwa iyayensa za’a matso da bikin Nanda sati uku ko biyu ayi ayi kowa ya huta Dan kaf zuriar gidan Naj din ce kawai ta riqe a gabansu batai aureba da wuri.
#MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

 

*_DM 7_*

*_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_*

https://youtube.com/c/sudaiskura

_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur’an at a very young age._

_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy._

_PLEASE SUBSCRIBE_

 

**********
Kodata dawo Hanifa tasamu komawa bacci Dan Haka Kai tsaye toilet ta Shiga tayo alwala tafito ta tayarda sallah.
Tana idarwa Shirin kwanciya tayi Dan batajin tanajin yunwa har zata kwanta ta fito ta nufi dakin hajjo
Tana Shiga kallo daya hajjon tayi Mata ta karanto yanayinta cikin kulawa dakuma tsananin qaunar data kewa Naj din tayi Mata hannu datazo ta kwanta kan cinyarta
Naj din ta qarasa ta kwanta qasa tareda Dora kanta kan qafafun hajjon ta rufe ido ahankali tanajin zuciyarta na samun nutsuwar data kasa samu daga gurin iyayenta.

Saidata fara bacci ahaka kafin hajjon takira sunanta ahankali tace taje ta kwanta a godonta
Ta bude idanuwanta tareda tashi zaune ahankali ta miqe tana cewa”

No hajjo zanje na kwanta da Hanifa sbd jikinta.

Shikenan kije Saida safe kiyi bacci karki saka damuwan komai aranki Allah ya tashemu lfy.

Amin”tace tana ficewa dakin.

Washe alhmdlh daga ita har Hanifa lafiya kalau suka tashi Hanifa wuyanta ya sake Takoma garau dinta dama Haka take yanzu lafiya yanzu ciwo,kokuma yanzu ciwo yanzu lafiya.
Itama sakayau ta tashi ba wani yanayi na damuwa kokuma dake nuna tana cikin wani hali sbd ta riga ta yarda ta yanke shawaran auran Abbas Dan Haka ta kauda bayyana damuwa a fuska da yanayinta sbd hajjo da Hanifa dasuka samu saqon an saka ranar auren an maida sati uku masu zuwa Wanda dad din Hanifan ne yakira hajjon ya sanar Mata sbd Dattijo ya kirasa ya sanar dashi Dan komai na harkan auren Naj da dad din akeyi sbd suna basa girmansa da matsayi na uba agareta sbd baitaba banbantataba da yarsa Hanifan tun daga karatun primary kuwa har zuwa yanzun.

Ranar bataje aiki bama Koda hajjo ta zaunar da ita akan maganar auren ta tambayeta akan tafada Mata gaskia idan batada ra’ayin auren Abbas din tasa dad yayi mgn dasu Dattijo a fasa
Tacewa hajjon ta amince da auren Abbas da raayinta ba Dole su dattijon sukai Mata ba.
Hanifa ma tayi tayi akan suyi maganar Amma tace Mata subar maganar ayi auren ahuta.
Dole suka haqura sunaji suna gani aka hau fara shirye shiryen auren gadan gadan.

Tunda aka fara wannan maganar Bataga ko shigowar saqon Abaas dinba a wayarta bare kiransa Wanda Bai wani dameta ba sbd tasan dama za’ai hakan Dan Haka ta tattara dukkanin alamarinsa ta cire akai ko a office Basu hadu ba sbd dama gabaki daya Bata zuwa office dinsa shine me zuwa nata to tunda yaga tagama shigowa hannunsa tunda zata zama matarsa saiyayi watsi da ita shima saima wani basarwa yakeyi a yanda Sarah take fada Mata yasa dokar shigar maza office dinta matuqar ba’a zo anfara tambayarsaba Koda kuwa aikine.
Hakan ya Bata mamaki sbd kaman rashin tunani yashigo al’amarin nashi Dan hakama Ana saura sati biyu bikin tafara hutun bikin auren dazatayi ta daina zuwa office.

Gidansu kuwa sosai da sosai aka hau shirin wani irin gagarumin hidima sbd bikinta kowa yasaka Masa burin holewa tunda sunsan za’a kashe dukiya sbd alaqarta da gidan tsohon marshal Alfa shiyasa suka hau shiri da anko anko na biki kala kala Wanda ita amaryar ma gabaki daya komai baya gabanta mamakinta daya har lokacin Abaas Bai taba kirantaba.

Dadah kuwa farin cikinta da murnarta a bayyane suke ba wani shamaki sai ji takeyi da Naj din tana lallabata hakama Dattijo manyan kudi tako Ina sai shigosa sukeyi sbd Alfa ya sakar Masa kudin hidamar auren fiyeda tsammani ga hajjo ma data tanadarwa Naj dukiyar aure ta musamman shiyasa kowa sai qara rikicewa yakeyi da harkan bikin.

Ummarta tuni tahau aikin gyaran ‘yarta sbd dama gyaran amare aikintane Dan Haka yanzu da Abu yake nasu ba kissa ko kadan gyaran Naj din takeyi ta ciki ta waje abinka da kyakkyawar farar mace tuni tafara sauyawa sosai Dan kuwa har wani daukan ido takeyi.

A duniya qawayenta biyu ne daga hanifanta sai Sarah Dan Haka kullum Sarah na gidan sunata shirye shirye Wanda Hanifan ce ke komai itadai nata ido da Kuma Dan murmushin yaqe Wanda babushi ko kadan cikin zuciyarta.

Saida akai saka lallenta kafin aka kawo kayan lefe mota biyu Wanda yasa gidansu yasake daukan bidiri suna sake yadda da Naj dama me kudin ta tsaya jira duk da hakan dai sudai sunyi murna musamman ummanta data ringa sadaka tana ciyar da mabarata sbd Allah yasa wannan karon ‘yarta tayi aure.

Ba gidansu Naj din kawaiba ya cika da baqin nesa Dana kusa ba hatta gidan Alfa yasamu saukar isowar Dad Alfa din tareda matarsa da sabbin masu aikinta datazo dasu har guda biyu sai babba ‘yar yayarta datake riqo tun tuni wato _HANNA_ Wanda take wata irin wayayyiya datake ji da kanta da Kuma kyau da Allah yayi Mata itama wadda asalin irin son datakewa  Marshal Deen ne yasa tadawo hannun mum Malika saidai hakan be wani taimaka ba sbd takanyi shekara Bata ganshi ba duk da kuwa iyayen nasu sunsan da maganar so a tsakaninta da marshal din Dan Yana kulata ba laifi shiyasa akeda maganar da yiyuwar aurensu gashi Kuma yanzu sun dawo gida gabaki daya da zama tasan yana zuwa Nan akai akai fiyeda can gurinsu sbd Hanifa da hajjo Dan Haka Suma gidan yanzu zai rayu tunda su dad din sun dawo.

Sai yamma sosai Naj tasamu damar fitowa gidansu ta tafi yiwa dad Alfa sannu da zuwa kodata fita mutanen dake waje sai binta da kallo sukeyi sbd yanda tasake wani irin washewa
Tsakani da Allah dai kowa ya kalleta saiyace Abbas yayi dace da kyakkyawar sa’a.

Tare suke da Hanifa dan haka Kai tsaye sashensu dad da mum Malika din suka nufa.

Babban lafiyayyan palon farko suka yadda mum Malika zaune tana waya tana ganinsu ta saki murmushi tana sallama da Wanda take wayar ta miqa musu hannu tana cewa”

Oh our beautiful bride is here
Naj you’re looking morethan beautiful.

Murmushi me qayatarwa tasaki tana cewa”

Thank you mum Malika kun iso lafiya?
Ya gajiyan hanya?

Alhmdlh alhmdlh hanya alhmdlh.

Kallon Hanifa tayi dayake ita tunda suka iso tazo tana tareda dad Alfa tace”

Hanifa I’m so happy for Naj
Allah yasa albarka a wannan auren.

Amin mum.

Congratulations Naj.

Thank you mum Malika.

Hannah ce ta fito sanye cikin doguwar riga Mara dogon hannu kanta daure da wani Dan qaramin scarf da tsadaddiyar wayarta a hannu tana dubawa tana ganinsu ta qaraso da murmushi akan fuskarta tana zama gefen Hanifa tace”

Sister in-law Hanifa barka da shigowa I’ve been looking for you tun dazu hajjo tace kuna gidansu Naj.

Murmushi Hanifa tayi tana kallonta tace”

Dazu nashigo kina ciki kina wanka
Ya hanya?

Lafiya kalau sis Hanifa.

Maida kallonta tayi kan Naj dake duba massage din Sarah akan Wai Abaas ya  dakatar da ita daga aiki.

Fuskar Naj din ta zubawa ido tana kallon kyan fuska Dana jiki da Allah yabawa Naj din ta gangara da idonta kan hannayenta dake farare tas kamar Bata aikin komai dasu gashi Tasha gyara tako Ina fatarta sai glowing takeyi
Dama can Naj na tsananin burgeta sbd tanason Abu me kyau ita shiyasa take tsananin son Marshal dinta ga wani aji da Naj din takedashi kamar ba Yar masu rufin asiri ba Dan Haka ta saki qayataccen murmushi tana kallonta cikin tayata murna tace”

Naj mijinki dinnan yayi sa’a
Congratulations to you Allah yabaku zaman lafiya.

Murmushi Naj tasaki tana kallon Hannah din tace”

Amin nagode Hannah.

Palon dad Alfa suka nufa inda suka samesa zaune Yana waya Dan kusan jama’arsa da yawa zasuzo daurin auren Yana ganinsu yasaki murmushi Yana kallon Naj datake murmushin Dole sbd saqon Sarah yabata matuqar mamaki shiyasa ta yanke shawaran Kiran Abbas din zatayi tana fita taji dalilinsa na korar Mata Sarah.

Zaunawa sukai Banda ita Naj din data zauna a qasa cikin biyayya da farin cikin zuwansa tace”

Dad Alfa barka da zuwa,ya Hanya?

Alhmdlh Najma ya hidiman?
Babu dai matsalar komai ko?

Babu komai Inshallah.

To shikenan Allah yasawa auren albarka yasa agama taron lafiya.

Hanifa ce tace Amin kafin suka Dora da zancen tahowar da Marshal zaiyi Wanda tun kafin suyi nisa Naj ta miqe tana cewa”

Zan Dan karba waya” ta fice.

No Abaas din ta Nemo Kai tsaye tareda Danna Masa kira tahau ringing.
Harta katse Bai dagaba ta sake Danna Masa Kiran sai akaro na uku ya dauka da cewa”

Hello.

Kai tsaye da muryarta me taushi tace”

Maganar office ce zanyi dakai akan Sarah ko Zan iya sanin abindaya faru ka dakatar da ita?

Takaicin zancen nata yaji Dan dama Yana sane yayi hakan Dan kuwa idan ba hakan yayiba yasan wlh har abada Naj bazata taba kiransaba har ayi auren kuwa to Amma yanzun data Kiran sai abin yabasa takaici ko gaidashi bazata iyayiba sai magnar Sarah Dan Haka cikin baqin ciki Kai tsaye yace”

Bana wannan maganar sai a office”

Kashe wayarsa yayi Yana sakin numfashi me zafi tareda komawa jifa da wayar Yana Jin tafasar zuciya.
Jin bazai iya hakura ba yasa ya zari key din motarsa ya fice daga palon mahaifinsa Kota cikin gidansu Bai bi ya fice sbd gidan Suma cikeda jama’ar biki.
Itama akaro na farko dataji bazata dauka wannan wulaqancin nasa ba cikeda takaici ta fasa sake kiransa ta wuce gidansu ranta a Dan jagule.

Washe gari akai gagarumar taron walima kawai sbd gabaki daya Naj din batada raayi na biki sbd komaima yafita kanta har akai waliman aka gama Bata cikin wani dadin zuciya sbd batasan me Abaas din yafadawa Dattijo ba yakirata itada ummanta a Daren yayi musu wani irin fadan cin zarafi duk da ummanta na cikin farin ciki na hidimar bikin Saida tayi kwanan bacin Rai.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 8_*
Washe gari kodata tashi miscalls din Dr sa’id biyar tagani a wayarta da text na cewan zaizo yau din yanason Mata fatan Allah ya Sanya alkhairi batai replying nashi ba sbd ganin massage din tun safe yayi Dan Haka ta share akan sai ya zo din.

Yau Bata leqo gidansu ba tunda tatashi tana tareda Hanifa data tashi da ciwon qafafu Dan Haka sai yamma tasamu fitowa ta da dogon hijab har qasa ta mask a fuskarta ta nufi gidansu inda acan tayi wani wankan ta shirya cikin wani brown lace riga da skirt saiga kiran Dr sa’id ta yafa gyale ta fito fuskarta ba kwalliyan komai sai Kohl dake cikin fararen idanuwanta.

Ko data fito Kai tsaye gidansu Hanifa ta shiga sbd tasan Yana ciki baya tsayawa waje musamman irin yanzu da komai zai iya faruwa.
Sabbin qarin securities tagani a waje da cikin gate na farko na gidan tareda ganin sabuwar motar gidan dake rufe a fili da alamun anfita da ita hakan yasa ta fahimci cewan DM na iso kenan ta Dan waiwaya hanyar sashen dayake matsayin nasa acikin gidan kafin ta dauke Kai ta qarasa sashen hajjo daidai shigowar Kiran Abbas tana gani taji bazata daukaba Dan Haka ta kashe wayar gabaki daya tana Shiga palon Kai tsaye.

Hajjo ce zaune a palon sai Dr sa’id shima suna maganar qafafun Hanifan daya duba ta kallesa tana cewa”

Dr barka da zuwa.

Kallon quralla yaso yimata Amma sbd hajjo na gurin yasa ya taqaita kallonsa fuska a sake yace”

Barka Amarya,ya hidima?

Murmushi kawai tayi tana qarasa dakinsu Kai tsaye tashige tana kokarin sake kunna wayarta Bata tsaya koina ba sai bakin gado ta zauna tana Kiran sunan Hanifan batareda ta dagoba.

Dakatawa tayi da abinda takeyi Jin shiru tareda Kuma qamshin turaren _TOM FORD Tobacco Vannile_ daya Gama gauraye dakin sanyin qamshinsa ko Bata dago ba tabbas tasan kodai DM Yana dakin kokuma yashigo ya fita sbd tsadar turaren kawai yasa Babu Wanda zata canka bayan shi Dan Haka ta miqe ahankali tareda juyowa akaro na farko idanuwansu suka shiga cikin na juna a bazata Yana zaune kan sofa gefen Hanifa da farin cikinta yasa ta daina Jin ciwon gabaki daya daga ita har shi Naj din suka zubawa ido
Ta dauke nata idon tana Dan dauke Kai daga kallonsa ta bude Baki Kai tsaye cikin dan sake fuska tace”

Barka da zuwa JALAL.

Dauke idanuwansa yayi daga kanta cikin muryarsa me Kai tsaye yace”

Ya hidima? Allah ya Sanya alkhairi.

Amin” tace Kai tsaye tana juyawa ta fice tana cewa”

Hanifan zanyi magana da Dr sa’id kafin kigama okay.

Tana fitowa palon Dr sa’id ma yagama mgna da hajjo suka fito zuwa harabar gidan inda suka tsaya suna mgna tsawon mintuna suna Shirin fita saiga taga Dr sa’id na kallon bayanta ta waiwaya ahankali daidai qarasowarshi zai wuce zuwa sashensa lafiyayyar fatarsa tana haskawa hakama qaqqarfan jikinsa dayake geaming yagama budewa tako Ina ta yanda duk qwaqwarka bazaka gano shekarunsaba sbd mugun miskilancinsa da kamewarsa dasuka shige da shekarun nasa Dan kuwa ko Dr sa’id daya girmesa da kusan shekaru shida koma fiye Yana ganin tsananin kwarjininsa da cika idonsa Wanda yasa manyansama suna bashi girman hakan.

Dauke Kai tayi suka nufi gate suka fito har jikin motar Dr sa’id din ta rakasa Tai Masa godiya harya wuce ta juya zata shiga gidansu saiga motar Abaas Tasha gabanta tana ganin hakan ta rabe ta shige gidansu sbd akwai jama’a sosai a waje musamman sbd securities din DM dasuka qaru suka cika layin gashi goben ne daurin aure batason hayaniya tasan tsaf Abaas din zai iya Tara musu mutane a wajen.

Cikin soron gidansu ya fincikota a matuqar hasale yace”

Me wancan likitan yazo Yi gurinki a Daren gobe aurenki shiyasa kenan naketa Kira kina qin dauka karshe Kika kashe min waya kokuwa abinda ba’a qarasa bane aka qarasa kokuwa hankalina da Kuka Saba rainawa  wayo keda gidan riqonki dasuka koya Miki rayuwar qarya zaki sake cemun wadda tafi kowa ciwoce yauma batada lafiya yazo…….

Cikin tsananin bacin ran data dau lokaci tana dannewa ta Kira sunansa ta Dan daga murya idanuwanta dasuka sauya akansa tace”

Abaas kasan abinda kake fada sbd tsawon lokaci Ina kokarin daukan jahilcinka a matsayin kuskure da bacin Rai amma abinka Yana yin yawa
Kana qetare iyakarka da yawa
Kaje kawai banason Yin wata magana dakai karka Tarawa kanka mutane anan sbd idan halinka ya bayyana anan banajin iyayen nawa da kake bugun gaban su suka baka aurena zasu aurar maka Dani din so please just leave from here.

Juyawa tayi idanuwanta jajir zata bar gurin ya fizgota da qarfi take rigar jikinta tayi mummunar yagewa saiti da kirjinta Navy blue bra din dake ciki ta ta bayyana gabaki daya tana waiwayowa ta daukesa da wani irin mummunan Mari idanuwanta na cikowa da wasu irin hawayen baqin ciki
Hanifa dasuka iso tareda DM data janyo Dan zuwa gurin umman sunkirata a waya zata fito soron DM yanason ganinta itama idanuwanta cikeda hawayen bacin Rai ta sake saukewa Abbas din Mari tana daukewa umman Naj din ta sauke Masa nata barin itama hawaye na gangarowa daga idanuwanta.

Marshal kuwa dauke idanuwansa yayi daga gefen sbd jikin Naj din dake bayyane koda Abaas ya dago jikinsa haryana rawa sojojin DM sukai Masa muguwar damqa suka jasa waje Yana fizge fizge suka wuce dashi daidai dawowar Dattijo ya qaraso soron ganinsu cirko cirko
DM na ganin Haka ya juya ya fice sbd yasan hayaniya za’ayi.

Aikuwa Dattijo da idanuwansa suka Gama rufewa sbd dai ko iya abinda yagani yasan Babu shakka wannan auren sunansa Babu
Baqin ciki da takaici daya Gama dunqulesa ko magana baiyiba ya kalli ummanta da idanuwanta sukai jajir yace”

Bazance komaiba Amma wallahi tallahi ku sani matuqar gobe tayi Abbas suka fasa auren Nan wlh duk Wanda nasamu daura Miki aure dashi zanyi.

Juyawa yayi ya wuce tsabar bacin Rai idanuwansa ko gani basayi Sosai.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_DM 9_*

*_MG’s SKINCARE_*
*_Ina manyan Mata da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau kuzo ga mg’s skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki,_*
*_mg’s skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*

*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne,_*

*_Saikuma beauty kit gbdy nagyaranjiki su cream dakomai ne acikin shi,_*

*_Then akwai bridal kit shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za’a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*

Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
Location:kaduna buh we deliver Nationwide
Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift

_*sannan sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_
_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks,juices nd so on*_
_*Kindly chat with us via 08062991549.*_

 

************
Rungumeta Hanifa tayi idanuwanta zuciyarta na tafarfasa ta zare gyalen jikinta ta yafawa Naj din ajiki ta Jata ahankali zasu shiga cikin gida ummanta da idanuwanta sukai jajir zuciyarta na Mata wani irin tsananin nauyi Dan Bata buqatan tabbaci tasan auren Naj yasake rushewa kenan da nauyin murya tace”

Kuyi can gidan Hanifa kada kishiga Nan da ita akwai mutane zasu fahimci abin daya faru Kuma komai zai iya faruwa sbd wannan abun daya faru yanzu kuje can kawai tana buqatan kadaici Nima Ina buqatan nutsuwa.

Kallon umman Hanifa tayi cikeda damuwa tace”

Umma ke fa?
Ran Dattijo ya baci kada cikin mutane yayi Miki fada.

Bakomai kuje kawai kuje.

Juyawa tayi ta shige Dan ko kallon Naj takasa sbd tsananin baqin cikin halinda Naj din take ciki.
Sake rufeta Hanifa tayi tajata suka fice tana gani waje kowa ya rabe Yana kallo sojojin DM suka ja Abbas din daga cikin gate na biyu sukai Masa wani irin mugun duka sai gashi Yana ihun ceton Kai Dan azaba gashi me gidan nasu tuni yashige abinsa bare yace su barshi Haka Dan Haka sukai Masa iya Yinsu Saida akaje da gudu aka sanarda Dattijo ya fito cikin tsananin tashin hankali har Yana mugun tuntube zai kife ya ceci Abaas din Wanda baqar zuciyarsa batasa yayi nadamar abin dayayiba saima kallon kawu da yayi da bakinsa fal jini cikin tsananin baqin ciki yace”

Naj ce tasa amun wannan” daga Haka Bai qaraba ya juya ya fada motarsa Yana dafe gefen cikinsa dake Masa mugun ciwo yakasa Jan motar sbd ko gani bayayi sosai Dan take fuskarsa tayi wani irin tashi Kamar burodi Dole jiki na rawa kawu yakirawo jamilu dansa dake cikin gida yazo ya Kama mishi Abbas din suka maida baya jamilu yaja motar kawu na gaba suka nufi asibiti da Abaas din Dan kuwa tuni ya kumbure musamman bakinsa daya baje.

Tunda suka Iso palon hajja Kai tsaye Naj daki ta wuce idanuwanta jajir Bata buqatan komai da kowa a yanzu tunani kawai takeso abarta Dan hakan yasa Hanifa Bata bita dakinba ta zauna Palo tareda sauke wata nannauyan ajiyar zuciya ranta amatuqar jagule itama.

Kallonta hajjo tayi tace”

Meya farune naganku haka? lafiya kuwa?

Kai tsaye Hanifa ta fada Mata abindaya faru tana qarawa da cewa”

Dattijo shi laifin umma yagani
Ummanma tanacan cikin tsananin damuwa ko wannan karon dai anfasa auren Naj.

Hajjo sosai itama zancen ya mummunan Bata ranta tace”

Ina yiwa Najma adduar alkhairi akan aurenta aduk sallata Dan Haka inaga hakan shine mafi alkhairi gareta Allah yakawo Mata mijin daya fisa.

Amin”Hanifa tace jikinta amatuqar sanyaye idanuwanta sai cikowa sukeyi da hawaye tana maidawa sbd Allah yasani batason Abaas da Naj to Amma Kuma da aka fara hidimar bikin nan bazataji dadin wargajewar auren Naj dinta akaro na maimaci.

Har dare Naj na kwance a daki idanuwanta rufe kaman me bacci saidai ba baccin takeba Dan Babu ta yanda zata iya bacci duk cikin aure aurenta da ake fasawa Babu Wanda ya dasu ta Hanya mafi Muni Kamar wannan.
Har dare Babu me dadin Rai acikinsu anan gidansu Hanifa Abu komawa yayi Kamar na zaman makoki Dan kuwa murna da farin ciki sunkoma damuwa da baqin ciki amma dai lokacin basusan menene zai farun gobe ba yiyuwar auren kokuwa¿
Hajjo data Kira Umma ta Dan Mata maganganun kwantar da hankali tareda sake tunatar da ita daukan qaddara me kyau da sabaninta Yana daga cikin zaman cikakken me mumini me Imani Dan Haka kada ta damu sosai tayi addua kafin safen Allah yasa suji alkhairi idan fasawarce alkhairi idan Kuma yin auren.
Cikin rauni da tsananin damuwa Umma tace”

Na yarda da qaddara hajjo Amma tayaya Dattijo zai lalata rayuwarta ta hanyar aura Mata wani cikin fushi idan ikirarinsa yazama gaskia rayuwarta zata iya lalacewa a qarshe dai auren da aka dage da sai tayin baiyi Rana ba kenan.

Inshallah rayuwar Najma bazata lalace Alfa bazai Bari a lalata rayuwar Najma ba zanyi magana dashi idan har sun fasa auren a hakura Allah zai kawo Mata wani.

Sai alokacin Anty Amina dake dakin Naj da Babu mutane tareda umman taji abin daya faru hankalinta yayi mummunan tashi cikin damuwa da Dan tsoro ta kalla idanuwan umman dake son cikowa da hawaye a raunane tace”

Umma Dan Allah kada kiyi kuka wannan jarabawace Allah kewa Naj Inshallah zata cinye.

Sauke Kai umma tayi tana girgizawa ahankali cikin tsananin baqin ciki da damuwa tace”

Wannan jarabawatace Nima sbd Ina cikin wani hali na tsananin baqin ciki da damuwar rashin auren Naj
Dadah bazata qara Bari nasha ruwa gidan Nan ba cikin kwanciyar hankali
Ga Dattijo Yana rantsuwar aurar da ita ko duk Wanda yasamu wannan karon tayaya Zan iya kwantar da hankalina da hakan?.

Zama Anty Amina tayi itama tana rafka tagumi cikin tashin hankali da tsoro ta bangare daya tana adduar Allah yasa kada Abbas din yafasa sbd duk halinsa gwarashi an sanshi idan yafasa ba’a San wa dattijo zai aurawa Naj din ba tunda yayi rantsuwa to tabbas kowa yasamu zai iya daura mata Dan Haka ita dai anata gwara Abbas din dai ko yayane.

Ta bangaren Dad Alfa hajjo takirasa yazo tayi Masa bayanin komai ta dora da cewa”

Auren wannan yaro ga yarinya Mara hayaniya da nutsuwa Kamar Naj Sam baiyiba Kuma hakan ya nuna Babu da’ar sanin darajar mace data aure atare dashi Dan Haka idanma su Basu fasa din ba kayi magana da Dattijo a hakura afasa bashi auren.

Shiru Dad Alfa yayi Yana nazarin maganar wadda ta Sosa ransa matuqa shima sbd yanajin Najma tamkar Hanifa Dan Haka Aure Kam kosu Abbas Basu janyeba babushi Dan idan har zai iya yaga Mata rigar mutunci Haka acikin gidan iyayenta tun kafin aure bayan aure al’amarin bazaiyi kyau da dadin ji ba Dan Haka take ya yanke shawarar neman Dattijon tun Daren suyi magana hajjo ma tace”

Idan ka aika kiransa zakuyi magana ka kirani Nima zanyi Masa mgn Dan kada ya qarfafa abin sbd hankalin Fatima umman Najma din ya tashi matuqa da hukuncin dazai yanke.

A asibiti su kawu sai kame kamen zancen ban haquri yakeyiwa mahaifiyar Abbas da qanin babansa Dan mahaifinsa ya rasu Yana Basu hakuri da Basu tabbacin bayan daurin auren gobe za’a zauna ayi magana.
Hajiyar Abbas da ranta yagama mummunan baci ganin yanda kamannin danta ya sauya lokaci guda take ta rufe ido tace wallahi tallahi ko ‘yar gwal ce Naj danta bazai auretaba Kuma bazasu yarda ba saisunyi shari’a dasu dattijon akan wannan dukan da akaiwa Abbas dan kuwa zata saki dukiya iya dukiya sai an hukunsu.

Kawu najin Haka wani irin dunqulallen baqin ciki ya tsaya Masa a zuciya ba Dan qarar datace ba sai fasa auren da akai Wanda dama jikinsa yabasa za’ai hakan.
Danne baqin cikinsa yayi yaso qanin mahaifin Abbas din yabashi dama suyi magana ta maza a fahimci juna idan yaso bayan an daura auren ayi maganar wannan Amma Sam shima abin Bai Masa ba ace anyiwa ango duka a gidansu amarya wannan al’amarin babbane.

Kallon Dattijo alhajin yayi a natse yace”

Alhaji Ibrahim katafi kawai maganar Nan bazata yuyuba yanzu sbd halinda shi Abbas din yake ciki maganar auren Kuma a goben dai gskia bazai yiyuba saidai ko kila gaba.

Shiru Dattijo yayi zuciyarsa na quna da tarin baqin ciki,
Shi shikenan kullum cikin gayyata yake Yana Tara mutane Ana fasa aure har sai yakai ya gayyata ba’a zuwa.
To anyi na qarshe da yardar Allah.

Juyowa sukai suka fice daga asibitin suka tari adaidaita sahu suka shiga Babu me cewa qala dagashi har jamilu Wanda shima fasa auren Bai Masa Dadi ba sbd baiga abin fasa aurenba idan an zauna anyi magana Amma sun dauka zafi har suna maganar qara da shari’a Wanda zaice Dan basusan a Ina akai dukan bane da bazasuma fara kawo maganar qara da shari’ar ba Dan kuwa yanasa ran sojojin Marsha ne sukai dukan bama na Alhaji Alfan ba bare ace da sauki.

Koda suka iso gida Saida Dattijo sukai sallar ishai a masallaci kafin yashiga gida dake danqam da hayaniyar Yan biki dasuka zozzo cikinma da yawa zuriar wasu Basu zoba sbd sunsha zuwa bikin Naj din Ana fasawa shiyasa ba kowane yasamu zuwaba.

Gurin Dadah ya aika jamilu yace yakirata sbd zancen bazai yiyu acikin gidanba dayake da mutane ko Ina.

Dadah dake zaune tana Shan radionta cikin kwanciyar hankali ta kalli jamilun daya fada Mata Dattijo na son mgna da ita ta kalli fuskarsa tsaf taga ba wata annushuwa jikinta yabata ba lafiya Allah yasa ba abinda yasaba faruwa bane,ta kashe radiyon tareda miqewa da hijabinta dake jikinta ta nufi kofa tana tafiya ahankali irin ta tsofin da qafafunsu Basu cika wata isashiyar lafiya ba ta nufi waje batareda kowa yasan ta fitar ba.

Dattijo dake tsaye Yana jiran isowarta Kiran alhaji Alfa yashigo wayarsa dama shima gurin nashi suka nufa ayi maganar gabaki dama Dan Haka Dadah na qarasowa yace”

Dadah muje can gurin Alhaji Alfa ayi maganar sbd Nan akwai mutane yanacan Yana jiranmu.

Dadah najin Haka tun Basu qarasaba take cewa”
Ibrahim maganar auren Naj din ce Babu ko?

Shiru yayi zuciyarsa a jagule Bai amsaba har Saida suka Isa cikin babban palon gidan na baqi suka zauna dama Alfa na palon shida hajjo suna Kiran isowarsu.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 10_*

*_MG’s SKINCARE_*
*_Ina manyan Mata da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau kuzo ga mg’s skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki,_*
*_mg’s skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*

*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne,_*

*_Saikuma beauty kit gbdy nagyaranjiki su cream dakomai ne acikin shi,_*

*_Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za’a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*

Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
Location:kaduna buh we deliver Nationwide
Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift

_*sannan sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_
_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks,juices nd so on*_
_*Kindly chat with us via 08062991549.*_

**********
Cikin girmama Alfa ya kalli Dadah bayan sun zauna a mutunce yace”

Dadah barka da zuwa ansaki fitowar dare ko¿Sannu da kokari.

Ba dole nafitoba Alhaji Alfa tunda dai Haka Allah ya rubuto Dani na tsufa lafiya da ‘yayana Amma matsalar jikoki na neman sakamun ciwon damuwa.

Gaisawa sukai da hajjo tana sake Mata sannu da hayaniyar taron jama’a kafin shima Dattijo ya gaida hajjon ya maida kallonsa kan Alhaji Alfa damuwarsa na bayyanuwa gabaki daya yafara magana da cewa”

Alhaji Alfa duk da bansan dalilinka na son magana daniba a a Daren Nan Ni Ina daukeda magana me girma dazan fara fada maka akan daurin auren gobe.
Bansan menene taqamaimai abindaya faruba a dazu Amma dai a yanda nasamu bayani daga bayan Nan shine Najma da mahaifiyarta sun taru sunyiwa yaron Nan Abbas wulaqanci hakama sojojin JALALUDDEEN sukai Masa duka yanzu Haka Yana asibiti a kwance a taqaice zance dai iyayen yaron Nan sun fasa auren Nan.
Naso su fahimceni mu tsaya ayi maganar fahimta Amma ita mahaifiyar yaron ta dauki zafi sosai qarshe dai qanin mahaifin nasa Alhaji Abubakar yace ayi hakuri da maganar auren Nan yanzu Bai sanarwa gaba ba Wanda Ni nasan Babu wata gaba Dan kuwa bazasu taba dawowa ba Dan Haka qarshen maganar zance dai aure babushi ya fasu ba maganar daura aure gobe da Abbas.

Shiru dukkaninsu sukai gurin yadauki tsit na wasu mintuna kowa zuciyarsa ba Dadi musamman shi Dattijo da tasa zuciyar quna takeyi tana ‘daci.
Sauke Kai Dadah tayi tareda fashewa da kukan da baya fita sosai tace”

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun
Wannan jarabawa nada nauyi ya Allah kabamu ikon cinyewa yasa Allah Fatima da Najman Susan kansu suke cutatarwa tareda mu da Allah ya Dora Mana nauyinsu.

Karkice Haka dadah sbd hakan Suma ba laifinsu bane musamman Fatima zatafi kowa farin cikin ganin ‘yarta tayi aure Dan Haka bazata Rusa auren yarta da ganganba musamman da aka kawo wannan gabar ta auren kawai ake jiran daurawa gobe” hajjo ce me bawa Dadah hakuri da wannan kalaman.

Shidai Dattijo shiru yayi yakasa cewa komai sbd tunanin shawarar abinyi goben.

Gyaran murya Alhaji Alfa yayi tareda tattaro nutuwa yace”

Dadah hakurin da aka Saba da tawakkali shi za’a sake dauka sbd shima Abbas din Allah baiyi shine mijinta ba Wanda a hakikanin gaskia harda wasu halayensa dana samu labarinsu yanzu yasa saidai kawai muce Allah yazaba Mata mafi alkhairi,
Sai maganar itace kokuma mahaifiyarta suka lalata auren wannna duk bashine abin dubawaba kawai Allah ne baice yazama mijintaba Dan Haka Dan Allah ayi hakuri a dauka hakan kawai a matsayin wata jarabawar
Sai maganar taron jama’ar da aka gayyato na nesa Dana kusa na daurin auren goben sai a sanar da cewar an daga auren abawa jama’a hakuri….

Sai alokacin Dattijo ya bude Baki Yana dagowa daga soken da kanshi yake tun dazu yace”

Maganar taron gobe Inshallah za’ai daurin auren tunda Allah Bai qaddari anyi dashi wanda aka tsaro dashiba na yanke goben Zan daura Mata da Mubarak sbd tun farko ma hakan yakamata muyi tunda auren na waje Bai samuba sai ayi na zumunci a rufawa Kai asiri dama shine qarin abinda dayasa nace Zan nemaka a Daren Nan na sanar da kai hukuncin Dana yanke sbd Kota bangarenka idan akai dubi da irin manyan jama’ar qasar nan dazasu zo daurin auren gobe Dominka idan akace anfasa bazasuji dadiba Dan Haka wannan shine nawa hukuncin.

Share hawaye Dadah tayi tana cewa”

Wannan hukuncin yayi gwara ayi Dana gidan Allah yasanyawa abun albarka….

Cikeda bayyanarda damuwa hajjo tace”

Mubarak yaushe akai aurensa da za’a Kuma daura Masa wani auren inace iyakacinsa wata t
Bakwai da aure hakama Najma din gabaki daya Bai kamata ayi Mata aure irin wannan ba Dan ba laifinta bane itama tanason tayi auren Amma Bata hakaba.

Numfashi Dattijo ya sauke Yace”

Mubarak ne me aikin Yi me Dan girma acikin mazan gidan Kuma tunda kamawa tayi Haka zai hadasu su biyun da matarshi ya riqe Amma Kam da yardar Allah Najma tagama zama tana Kore mazan aurenta rantsuwace akaina da alqawari danai Mata daga ita har mahaifiyarta akan wannan karon Inshallah wlh natara jama’a aka fasa aure bazan Bari ayi abanzaba Zan aura Mata duk Wanda ya samu da wannan rantsuwar akaina Amma suka taru suka shure maganata Dan Haka auren Najma gobe da yardar Allah ba fashi za’a daura.

Cikin sanyin murya sbd jikinta daya Gama mutuwa gabaki daya da al’amarin Dadah tace”

Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Amma dai banason ayi abinda zai Kuma kawo matsala idan aka fita wannan Dan Haka daga waya ka Kira Mubarak a fara sanar dashi zancen aji ta bakinsa kada ayi abinda zai janyo wata fitinar.

Zallar bacin rai ne da takaici suka Danni zuciyar hajjo ace yarinya Kamar Naj Ana Shirin yimata auren wulaqancinda sai Ankira Mubarak an tambayeshi bayan kowa yasan cewa zaiyi bayaso tunda duka duka yaushe yayi aure da matarsa wadda take yarinyace qanqanuwa sosai bayan cin zarafi da tazarci Babu abinda kishi bazaisa tayiwa Najma wadda take mace me tsananin kamewa da sanin qima da darajar kanta cikin bayyanarda bacin ranta a fili tace”

Basai Ankira Mubarak ba Alfa biyawa JALALUDDEEN sadakinta a daura auren dashi gobe.

Cikin sauke numfashi Alhaji Alfa ya  kalli hajjon wadda kowa yasan ranta yariga yayi mummunan baci akan al’amarin shi kansa Alhaji Alfan ransa  yabaci da hukuncin Dattijon saidai kawai Yana iya kokarinsa gurin dannewane sbd kada ya nuna isarsa da yawa bayan sunfisa iko da Isa akan Najman Kuma shima da hukuncinda yayi niyar yankewa kenan na nemawa Marshal auren amaimakon Mubarak dasukace Dan shikuma aikin Mubarak din ne Bai yarda dashiba Dan harka yakeyi da yan siyasa saikuma maganar Hannah da duk sunsan da maganarta da jalal din saigashi hajjo ta rigasa yanke hukuncin Dan Haka take ya maida kallonsa kan Dattijo dayayi tsit Yana soke Kai sbd ganin ran hajjo ya baci sosai cikin girmamawa ya kalleta zaiyi magana tace”

Aurenta da jalal zai kawo qarshen matsalar komai Inshallah tazarar shekarun ba komai bane tunda duka duka baifi shekaru uku ne tabashi ba dan Haka wannan ba matsala bane.

Wani kukan Dadah takuma fashewa dashi tana cewa”

Ni kulu dame zamu saka mukune da koyaushe kuke binmu da alkhairi¿
Tunda mahaifin yarinyar Nan ya rasu kuka zama gatanta kuka ginata akan kyakkyawar rayuwa yanzu Kuma gashi kun amince da ita adaidai lokacin datake cikin irin wannan tsaka me wuyar ya Allah yasaka muku da mafificin Alkhairinsa Kuma maganar ba ko anbawa jalalu ko ba’a bashiba babuta Dan kuwa Alhaji Alfa kaima mahaifintane Kai tsaye zaka iya cewa kawai kazaba Mata jalalun adaura dashi Kuma ayi hakan sbd ka Isa indai akantane.

Jinjina Kai yayi Yana kallon Dattijo yace”

To Ibrahim me kagani akan hakan??

Jiki mace Dattijo ya girgiza Kai Yana saukewa sbd shi wata irin kunyace ta dabaibayeshi sbd irin qaunar dasu hajjo kewa Najma yasa bazasu iya Bari ayi Mata auren tozarciba daya dage akan sai yayi din Dan Haka kasa kallon hajjo yayi ya kalli Alhaji Alfa yace”

Allah yasa hakan shine alkhairi.

Tashi hajjo tayi tafara ficewa kafin Suma suka fito Dadah hankalinta kwance murna fal cikin ranta tunda damuwarta Bata Kwana da itaba an kaudata Dan kuwa yanzu auren ya sauka inda Babu halin fasawa bare tashiga shakku shidai Dattijo duk ransa har lokacin a jagule yake Dan Haka Babu Wanda yasanda maganar sauyin auren aunbarshi akan sai goben.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 11_*
Acikin Daren Koda hajjo tadawo palonta Hanifa na zaune Palo tana waya da Isma’eel dinta dazai qaraso goben tunda safe sbd yasamu daurin auren cikin sanyin jiki Dana murya tareda damuwa tace”

Zawj ko yanzu wannan karon Babu auren Naj.

Subhanallh”yace cikin mamaki da firgici yace”

Meya faru Kuma wannan karon?
Yaya Naj din tana lafiya kuwa?
Innalillahi Wannan labarin bamai Dadi bane.

Kasa cewa komai tayi saima damuwarta akan Naj dake qaruwa sbd wannan karon Naj din abinda Abbas yayi ya daki zuciyarta Dan ba’a taba cin Mata mutunciba kamar Haka yaga Mata sutura a waje dasu Hanifan da ummanta Basu isoba alokacin batasan Yaya zatayiba da jikinta.

Ko palon hajjo Bata zaunaba ta nufi dakinta ruqayyat dake jiran dawowarta tayi Mata gashin qafafunta Wanda ake Mata kullum da daddare kafin ta kwanta sbd nauyin qafafu tana ganin hajjon ta shige taje ta dauko kayan aikin zata nufi dakin Hanifa ta tsayar da ita ta karba kayan tana cewa”

Jeki Zan Mata da kaina.

Karaban kayan tayi ta tura kofar dakin ta shige ta tadda hajjo zaune tasake ajiyar zuciya sai alokacin taji nutsuwa da fushinta ya sauka sbd koba komai shikenan Naj din tazama tasu ta har abada Babu me sake takurawa rayuwarta ta bangare daya Kuma tuno jalal da irin girman miskilancinsa da Kuma yanda girman matsayi yasamesa a cikin shekarunsa na samartaka dan Haka ba lallai hadin nasu yayi ba Dan kuwa shi yanzu yaro da kudine abokin manya itakuma idan ba Allah ya rufa asiriba kallon qani zatamai Wanda zai kawo musu matsala a tarayyar Amma dai koma yayane za’ai auren Kuma Inshallah zai zama alkhairi hakama bazasu takurasuba ko bayan auren za’a barsu ahankali komai zai daidaita Dan Haka ita ko ahakan komai yayi Mata.

Kallon Hanifa tayi tana nuna Mata kusa da ita tace”

Zo ki zauna kusa Dani mu Taya juna murna da Allah ya Sanya alkhairi sbd kema Zakiyi sirika a goben amatsayinki na yayar ango.

Hanifa Bata gane me hajjon ke nufiba ta qaraso ta aje kayan hannunta tana zama gefenta tace”

Naji dadin da auren Abbas da Naj Bai yiyuba Amma hajjo ai bazamuyi murna ba Kuma tunda Naj din na cikin damuwa duk da itama nasan Bata fasa auren bace ta abin daya faru ne.

Tunda safiyar ranar ta waye sai alokacin hajjo ta Dan saki guntun murmushi tana miqar da qafafunta kan qaramin sofa table dake gabanta tana cewa”

Gasamun qafafun ko da Dan sakemin gobe nasamu damar Dan zagayawa dasu cikin gidan kodan jama’a
Gobe Allah yayi damuwarmu akan rashin zuwan Marshal ta qare Dan kuwa yanzu tunda yanada Mata anan taredamu Dole zai ringa zuwa,
Mahaifinki ya nemawa Marshal auren Naj a Daren Nan Dan Haka ankai qarshen duk wata fitina gobe da Marsha za’a daurawa Najma aure Aminyarki ta zama sirikarki yanzu ita din tamuce halak malak.

Ruwan zafin da ba’a sirkaba ta tsunduma qafar hajjon aciki sbd rudewa cikin mamaki dason tabbatarwa tace”

Hajjo Aure tsakanin Naj da marshal??

Zare qafa hajjo tayi tana cewa”

Qonani kike Shirin yine kome?
Bari Naga auren nasu harma da ‘yayansu idan Allah yace kafin ki qona qafafun na rasa na zuwa.

Da dai hajjo tayiwa Hanifan bayanin komai Jin tayi wani farin ciki da Bata tabajinsaba anan kusa ya dabaibata tako Ina duk da can qasan zuciyarta tanajin akwai qalubale a tsakanin yardarsu da auren su biyun Dan kuwa Babu me sauqin saukowa wani acikinsu ga maganar aurensa da Hannah gefe daya Amma Kuma tana danne hakan da farin cikin hadin Dan kuwa wannan shine perfect match agurinta ita da Marshal dinta da Naj dinta
Miqewa tayi tana cewa”

Alhamdulillah ya Allah mungode maka da wannan zabi naka.

Ficewa tayi da sauri ta nufa dakinsu da Naj din take kwance tayi sallah ta saka kayan bacci tayi kwanciyarta da gudunta taqarasa ta fada kanta tareda rungumeta tana cewa”

I love you Naj
I love you Naj

Da idanuwanta dasukai laushi ta Dan kalli Hanifan tana maidasu ta lumshe batareda tace komaiba sbd har tafara Jin bacci sai kawai ta maida idanuwan ta rufe da muryarta me taushi tace”

I love you too Amma bacci nakeji barni Dan Allah.

Dariya Hanifan ta Dan sake cikin tsananin farin ciki tace”

Yi baccinki Lafiya MRS DEEN MARSHAL ALFA.

Bataji abinda Hanifan taceba sbd baccin daya fizgeta.
Daganan Hanifa fita tayi dakin Takoma palo ta miqe a kujera ta Danna Kiran mijinta tafada Masa Nan take cikin Daren tafara Dora sabbin shirye shiryen komai danma kamar yanda hajjo tafada Mata a yanke auren kawai za’a daura baza’a daga maganar takurasu tarewaba yanzu sai kowannensu ya Dan nutsu Dan wannan alamari na gaggawar daya riskesu musamman sbd yanayi na yanda suke kallon junansu na tazarar shekarun.

Ta bangaren ummanta da anty Amina kuwa a Daren Basu rintsa ba sbd tsananin damuwa da rashin sanin mezai faru mezai biyo baya ga Dattijo har lokacin umman Bata sake sakashi a ido ba bare tasan da maganar auren a gobe ko babu ga anty Amina zuwanta biyu yinin tana dubo Naj Wanda tunda abun yafaru take daki kwance Bata buqatan ko tada maganar ayi.

Koda akai sallar asuba kusan daga Dadah har Dattijo da Hanifa Basu rintsaba sbd zumudin safiya tayi ta waye a daura auren Nan kada wani abun ya gitta afasa Dan Haka daqyar kowannensu yaga anyi sallar asuba gari ya waye aka hau sabuwar hidima gadan gadan.

 

***********
Tsaye yake daga bakin qatoton window na cikin geam room dinsa dake cikin flat dinsa Wanda Babu kalar tsadadden lafiyayyan geaming machine dinda Babu aciki Wanda duk inda yake yasaba amfani dasu shiyasa jikinsa kallo daya macen datasan asalin jikin namiji me kyau qaqqarfa bazataji ta mutu a sonsaba take musamman idan tsautsayi yasa kasamu ganinsa ba riga.

Tsaye yake Yana amsa waya sanyeda black three quarter da black armless riga Wanda suka fidda hasken fatarsa sosai dama Kuma black shine kalar kayan dayafi so kila Kiran kalar tana Masa tsananin kyau ne.

Gama wayar yayi daidai knocking kofarsa da akai Wanda hanifa ce kawai yasan tana zuwa ta buga kofarsa Kai tsaye saidai akirasa a waya sbd sanin shi ba mutum bane Mai son hayaniya.

Kashe wayar yayi ya fito daga geam room din ya nufi Palo ya ajiye wayarsa akan kujera ya nufi kofar cikin nutsuwa ya saka hannu ya bude tareda juyawa Yana cewa”

Menene Kuma tunda safe Nan?kinsan bana ganin kowa fa tunda safe is too early now Hanifa.

Muryar Dad Alfa yaji yace”

Munsani Marshal Deen Dan hakan before anything ma we are really sorry to disturb.

Waiwayowa yayi tareda kallon Hanifa dake gefen dad din kafin ya maida kallonsa kan dad din ya na Nuna Masa kujera Yana cewa”

Sorry Dad banyi tunanin ganinkaba Ina tunanin haniface sbd itace tafi iya damuwa musamman da safe.

Zama yayi bayan dad din ya zauna Yana cewa”

Good morning Dad antashi lfy?

Lfy Alhmdlh.

Hanifa ya kalla ahankali yace mata”
Gud morning madam.

Murmushi tayi tana ajiye kayan data riqowa dad tana miqewa tsaye da farin ciki shimfide kan fuskarta ta kalli qafafunsa dake sanye da slippers na Gucci farare tas kaman baya tafiya dasu sai qafafun Naj dake tsaf fes fes Kamar hakan suka fado mata tace”

Inada aikin Yi Zan tafi Anjima dai nasan zamuyi magana idan kayi lokacina.” Ta juya ta fice.

Baibita da kalloba sbd yawan kallo ba dabi’arsa bace ya Dan kalli dad da fararen idanuwansa shima dad din shi ya kalla kafin ya nuna Masa kayan dake ajen da hannu Yana cewa”

As you know yau akwai taron daurin aure So ansamu matsala anfasa daurawa da wancan din saidai za’a daura da Wanda na Isa dashi ga Kaya Nan su babban rigane kayi amfani dashi anjiman sbd mutane zasu taro akwai kuma media you’ll more comfortable in it tunda daurin aure ne na hausawa.

Kallon kayan yayi kafin ya kalli dad din Kai tsaye yace”

Thank you.

Gingina masa Kai Dad din yayi Yana cewa”

Ok then see you.

Tashi dad din yayi ya nufi kofa marshal din na bayansa har harabar gidan kafin ya juya zai wuce saiga Hannah Wanda ta fito daga sashensu hajjo data sakawa ranta zuwa gaishesu kowace safiya da Rana da yamma sbd sake samun damar kame zuciyar Marshal tana ganinsa ta qaraso gurinsa tana sake wani irin qayataccen murmushi jikinta sanye da wata doguwar straight English gown ta roba data Dan lafe a jikinta kyakkwan shape dinta a bayyane.

Good morning Marshal” tafada tana tsayuwa agabansa.

Dan kallonta yayi tareda dauke Kai Yana kallon hanyar sashen hajjo da Hanifa ta fito ta koma cikin sauri tana waya da alama dai gabaki daya tama manta da ita din ba wata lafiyayya bace take irin wannan kaida kawon sbd hidiman bikin Naj din.

Juyawa yayi ya wuce Yana cewa Hannah din”

I will talk to you later zankoma bacci yanzu.

Daukeda murmushi a fuskarta tace”

Ok love” tana bin bayansa da kallo Kamar zuciyarta zata narke gabaki daya akansa,
Tana yiwa marshal so me tsanani Dan ita ba Shirin aure gabanta a da Amma yanzu sbd shi aure takeso Kai tsaye ba Jan lokaci shiyasa zata dage da Binsu hajjo ko zata samu a saka ranar bikin nasu tunda ansan da maganar auren nasu.

Alhmdlh Koda Naj ta tashi safiyar lafiya kalau ta tashi kamar koyaushe data Saba tanada qarfin zuciya Kuma tasaba da hakan tunda ba yanzu ne hakan ta taba faruwa da itaba Dan Haka dataga Suma su Hanifa da hajjo dasuke damuwa koyaushe maganar aurenta ta fasu taga wannan karon Suma Basu nuna damuwaba saima farin ciki dasuke da hakan yasa ta qara cire abin a ranta tayi wankanta ta fito sanye da riga da skirt na atampa Maroon data yiwa kalar fatarta kyau tazo palo ta zauna gefen hajjo daketa faman waya tasha ruwan dumi da Zuma da Madara ta koshi ta tashi taje ta dauko qaramin gyale ta yafa kanta ta fito tareda wayarta a hannu tana kunnawa ta nufi gidansu bayan ta biya gurin mum Malika ta gaidata Dad baya Nan jama’arsa nata isowa so baya gida.

Ko data Shiga gidansu Haka ta ringa Dan gaggaisawa da mutane harta Isa dakin Dadah da yau farin cikin duniya tana cikinsa bakinta Sam baya rufuwa sbd farin ciki danma Dattijo ya kwabeta akan kada ta fadawa kowa komai sai sunsamu an daura auren lafiya sunga aure ya dauru tukuna Dan Haka Babu Wanda yasan da maganar bayan ummanta da Dattijon yafadawa yau bayan sallar asuba aikuwa gari na wayewa sadaka me yawa umman ta Tara almajirai tayi tareda duqufa da adduar auren ya dauru taga ya dauru itama Dan har lokacin daga ita har Dattijo gabansu Bai daina faduwaba sai sunga anshafa fatiha aure ya dauru.

Kodata Isa can cikin gida gurin ummanta dasu anty Amina sai hidima akeyi sai hakan yaso Bata mamakinsu saidai Tai musu uzurin basusan Babu maganar aurenba sai anjima idan lokacin daurawan yayi sunji ansanar anfasa Dan Haka batai wani yunqurin maganar da kowannensuba Dan dama ba halinta bane yawan maganganu musamman irin wannan Dan Haka dakinta ta shige tana hada sauran kayayyakin lefen Abbas dake dakin Dan tasan maida Masa za’ayi Allah yasa ko takarmi daya Bata sakaba a kayansa duk aurenta idan za’ayi hajjo ke hada Mata lefe na musamman sbd gudun irin Hakan.

Har qarfe daya da rabi tana gidan inda tana gamawa Kai tsaye ta fice Takoma bayan tabar musu kayan shirye tsaf a tsakar dakin ta fito tana waya da Sarah Dake sanar da ita gatanan a Hanya tana zuwa.

A waje Babu kowa maza tsit duk an tafi gurin daurin auren da za’ayi dama a babban masallacin juma’ar da Alhaji Alfan ya Gina acan farkon layinsu jami’an tsaro da securities kuwa koina cikin layin akwaisu
Sojojin Marshal ne a kofar gida tsatsaye jikin motarsu da alama jiran fitowarta sukeyi ta wuce Kai tsaye ta shige gate suna bude Mata da sauri
Ahankali tace” thank you” tana wucewa hankalinta a waya.
Tana saka Kai a palon hajjo Yana fitowa sanye cikin wata navyblue hilton filtex da rawar da yakeyi kawai zai bayyana kudi me yawa ya lashe
Sai hular daya saka wadda ke nuna Bai Saba sakawaba Dan yanda ya sakatan ta Dan Yi gefe Amma sai hakan yayi wani irin yiwa kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani irin qyalli na kwarjini da cika ido ta dauke idanuwanta akansa tana rabewa ya kalli Dan qaramin siririn gyalen dake kanta Wanda iyakacinsa kafadunta ya dauke kai Yana wucewa sbd lokacin daurin auren yayi saura mintuna basufi goma sha uku ba ita Kuma tana shigowa tsakiyar palon hajjo da wasu baqinta da Basu Dade da isowaba sukabi Naj din da idanuwa gabaki dayansu.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 12_*
Ganin duka idanuwansu akanta yasa ta sauke idanuwanta tareda qarasowa a natsenta cikin taushin murya da rashin karauniya tace”

Ina wuninku Baabah barka da zuwa.

Sake Mata kyallon qiri qiri su baabar keyi wato yanne da qannen mahaifiyarsu Jalal dinne suka qaraso yau sbd tun a Daren jiyan hajjo da Alhaji Alfa suka sanar dasu auren jalal din daya Kama na gaggawa saidai Ba’a sanar dasu yanda akai auren ya yiyuba dakuma girmarsa datai sbd idan ba’a fadaba zakacema ta girmenta sosai Sosai sbd yanayin jikinta datake me kyau da burgewa da nasa jikin daya bude sosai sbd exercise dakuma tsayi daya fita sosai Dan Haka cikeda yabawa suke kallonta fatarta na daukan musu ido sbd zallan gyalan dilka da wasu abubuwan da akaita Bata tana Sha Dana mulkawa.
Baabah tace”

Lafiya kalau alhmdlh,ya hidimar kike ‘yar Nan? Ya hidimar jama’a?
Allah ya Sanya alkhairi kinji,
Allah yayiwa wannan auren naku albarka.

Da sauke Kai tayi shiru batareda tace Amin din ba tunda tasan abinda yake Nan ba aure.

Hanifa dake daki tagama shiryawa cikin Ado na shigar alfarma tana qamshi sbd mijinta da tuni ya iso suna gurin daurin auren
Fitowa tayi takama hannun Naj sukai dakin tana cewa”

Naj zo ki sauya shirinki inasa ran yanzu kowane lokaci za’a daura auren
Zo kiyi ado A ranar farko mijinki ya ganki da ado na musamman.

Zama kan sofa dake dakin Naj tayi tana aje wayarta da kallon Hanifa cikin Dan basarwa tace”

Nasan kinsan anfasa auren Nan just drop your drama.

Murmushi me girma Hanifa tasaki tana cirowa Naj din wani tsadadden navyblue lace me tsananin taushi da rashin ado na hayaniya Wanda yaja kudi sosai gurin siya tareda wani transparent emboidery veil ta aje gabanta tana cewa”

Dan Allah ki shirya kadaki Bari asan abinda yake faruwa musamu Mana a watse lafiya basai kin nuna musu Abbas yafasa aurenki ba ki nuna ko babushi Zaki iya rayuwarki ta walwala da farinki.

Da gangan ta fada hakan Dan Naj din ta shirya da farko qin yadda tayi sai daga baya ta saka kayan ta zauna bakin gado sbd zuciyarta data fara harbawa da sauri da sauri Kamar zata Fado ta Dan dafe kirjinta tana sauraron bugun zuciyarta daya sanyata lumshe fararen idanuwanta ta rufe tanajin kamarma hadda faduwar gaba.

Miqewa tayi ahankali takoma Palo inda hayaniyar baqin gidan take Anata fira
Tana fitowa dukkanin idanuwansu suka sake dawowa Kanta suna Yana baiwar kyawu da Allah yayiwa Naj din qamshin wani irin fitinannan turaren da ummanta ke Mata gyara dashi daya Gama Kama jikinta Dana kayanta tareda kayanta da aka turara ya gauraya palon cikin nutsuwa da farin ciki a fili hajjo tace”

Masha Allah, Allah na gode maka da ganin wannan Rana Allah kasawa aurensu albarka da farin ciki me dorewa.

Amin Hanifa ta amsa idanuwanta akan Naj da ko itama dasuka taso tun yarinta tare sukai rayuwa tare koyaushe tana yabawa.

Qarasowa tayi gefen Hanifan ta zauna tana duba wayarta hankali kwance ba damuwar komai su Kuma suka cigaba da sha’anin gabansu.

*****
An daura Auren JALALUDDEEN MARSHAL ALFA da NAJMA ABDULLAHI BELA akan sadaki naira dubu dari cif Wanda duban jama’a suka shaidar cikin mamakin sauyi da aka samu ciki harda jama’ar su Abbas da yawa sun halarta sbd basusan cewan an fasaba duk da hakan dai kowa tanata fatan Allah yasanya alkhairi Wanda aketa bawa Marshal hannu Ana tayasa murna shidai bin kowa yake da mayun idanuwansa sai hannu dayake bawa manyan mutanen dasuke miqa Masa hannu Dan tayasa murnar aurenda Saida ya iso gurin yasan nasane.
Isowarsa gurin yasa mahaifinsa daketa dakon jiran isowarsa ya qaraso gabansa Yana kallonsa Kai tsaye yace”

Za’a daura auren Najma dakaine Ina roqon alfarman ka amince da hakan sbd wancan ya fasa adaidai lokacinda Babu wani mafita shiyasa a matsayinsa na mahaifinka Kuma itama Ina matsayin uba gareta na hadaku ta hanyar nema maka aurenta Ina fatan zakamin biyayya.

Fararen mayun idanuwansa ya zubawa Dad din kafin ya Dan sauke Kai cikin miskilar murya yace”

Ok Dad.

Hakan dayace yasa Dad din Jin wani irin sanyi da nutsuwa sbd yanata nazarin yanda zai fahimtar da jalal din hukuncin dasuka yanke Kai tsaye akansa batareda Jin shawararsa ko raayinsaba tunda ba yaro bane yanada iko da yancin zabarwa rayuwarsa abokiyar rayuwarsa da kansa duk da yasan karba Masa Marshal din yayi sbd yariga yazo gurin bazai iya komawaba yasa Dad din kunya Amma yanayinsa kawai ko Bai fadaba Dad yasan anyi Masa shigar sauri Dan kuwa Babu tsarin aure agabansa yanxu musamman da wannan din da za’a daura da ita Dan kuwa a yanda suke dinnan ba lallaiba ta kwantar Masa da Kai shikuma bayasa ran macen dake qarqashin ikonsa zatana Masa kallon qani ko wani Abu Dan kuwa shi mijin macen dazata bisa ne Amma tunda su dad din suka zaba auren dama agurinsu zata zauna so ba damuwarsa bane sosai aciki tunda shi bataredasu zai zaunaba a taqaice ma yaji bazai iya dogon zamaba komawa zaiyi.

Dan Haka Ana gama daurin aure akai gagarumin reception da akai liyafar alfarma shidai ko ruwa Bai Sha ba aka fara watsewa ya zame yayo gida kansa na ‘dan sarawa Dan Haka Koda ya iso gida Kai tsaye flat dinsa ya wuce ya zare babbar rigar jikinsa da hula da komaima ya cire ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi ta shower Yana sauke ajiyar zuciya.

Sai dayayi wanka yafito yaji ya Dan samu nutsuwa da saukin ciwon kan ya saka guntayen qananun Kaya yaje fridge yasha ruwa kadan yadawo yashige daki ya kwanta Yana kashe wayarsa cikin nutsuwa bacci ya daukesa.

Saida ‘yan daurin aure suka dawo kowa yaji da Wanda aka daura auren zallan mamakin al’amarin yasake yayata gidansu Naj da hayaniya saidai Kuma tunda dai ansamu andaura Mata auren ba’a fasaba gabaki dayaba a watse a banza yasa aketa sabuwar murna Allah yayi lokaci yayi tayi aure duk da wasu da yawa sun manta da banbancin shekarun sbd matsayinsa da yanayinsa yasama har wainda suka kusan haihuwarsa suna basa tsananin girma sbd matsayi da kamewa shiyasama ake mantawa da wani banbancin shekaru sai murna sukewa umma Allah yabasu Wanda yafi abundama suke buri tako Ina.

Dadah kuwa Banda sadaka da godiyar Allah tana washe bakin babu abinda takeyi yau Jin takeyi wani irin sakat daga ita har Dattijo da sai baza babbar riga yakeyi Yana gaisawa da manyan mutanenda yasan Albarkacin auren Naj da jalal ne yakeci Dan kuwa ganinsu Koda appointment ne shi bazai samuba Dan Haka sai farin ciki yakeyi Yana baje babbar rigarsa ta tsadaddiyar shaddar da Alhaji Alfan ne yake dinka Masa daman.

Yana dawowa gidan yakira Naj a waya yace maza tadawo gida yanzu.

Da mamaki ta fito zuciyarta ba Dadi sbd dai ga dukkan alamun data gani agun mutane andaura auren kenan
Ta hadiye wani Abu me daci da nauyi daga maqogoranta Dan kuwa auren Abbas shine mafi mumman al’amari daya sameta a wannan rayuwar.

Ko data shiga gidansu sama sama takejin Ana mata adduar Allah yawa aure albarka Saikuma tafarajin Ana Kiran sunan Jalal da cewan mijinta
Kanta ne taji ya dauka ciwo sbd komaima ita yanzu a duhu yake Mata Kai tsaye dakin Dadah ta Isa sbd tasan Dattijo daya aika kiranta Yana can tana Isa tashiga da siriryar sallama ta nufi gefen Dadah daketa washe Baki cikin farin ciki ta zauna ahankali tareda bude Baki cikin taushin muryarta tace”

Barka da jumaa Dattijo.

Gaida Dadah tayi itama duk da dazun sun gaisa data shigo.

Kallonta Dattijo yayi dakyau yana Dan kame fuska yace”

To Najma Kamar dai yanda Kika sani yau ne ranar daurin aurenki da Abbas
Amma sbd rubutowa ta ubangiji Allah baiyi shine mijin ba Dan kuwa a jiya suka sanarda sun janye sbd abindaya faru a jiyan da safe.

‘dan shiru yayi kafin yacigaba da cewa”
Sakamakon hakan yasa Babanki Alhaji Alfa da hajjo suka bayyanarda buqatarsu tason nemawa JALAL aurenki muka amince atake sbd Babu wani zabin kokuma mafita Daman cigaban dayafi hakan Dan Haka dai a taqaice andaura Miki aure da JALAL yanzu ke matarsace halak malak saidai Hajjo ta nema alfarmar kada a takuraki da maganar tarewa gurinsa kokuma wani abun yanzu duba da yanda akai auren Dan Haka Zaki zauna gurinta kafin daga baya idan an natsa Kya koma sashen mijinki kokuma ki bisa can qasar dayake.

Akaro na farko a rayuwarta data kafe Dattijon da ido idanuwan nayi jajir ko qyaftawa batayi zuciyarta ta tsananta dokawa har batasan lokacinda ta bude bakiba tace”

JALAL qanin Hanifa?
An daura auren kokuwa dai za’a daurane yanzu??

Gano inda ta dosa da Aniyar bijirewa auren yasa ya tsuke fuska cikin bori yace”

Andaura Kuma wallahi kibar maganar Nan dakikeson fada acikinki Dan kuwa kisani kikaje Kika dagawa bayin Allahn Nan hankali akan banzan tunaninki na girman Kai suka raba auren Nan dake da mahaifiyarki zaku bar gidan Nan Dan kuwa Banga amfanin rashin godiyar Allah ba,
Dukkanin masu fasa aurenki Babu Wanda yakaisa bare yafisa ba’a ma hadawa ga qauna da mutunci da mahaifinsa da kakarsa dama ‘yar uwarsa dasuke Miki har kin Isa kice bakyason auren,
To kiji da kyau Dadah kizama shaida wlh taqi auren Nan bani ba ita Kuma Tak banyarda tasake cewaba.

Miqewa yayi Rai bace ya gyara rigarsa zai fice yace”

Kuma duk abinda kikeyi kiyisa ki hada kayanki anjima Zaki koma gurin hajjon da zama afadawa kowa ba yanzu zata tareba kowa ya watse daga gobe banason zaman tsegumi”
juyawa yayi ya fice daga dakin Rai bace Dan baiyi tunanin zata musanya din ba yanda yasanta da komai yace hakane sbd rashin iya ja’injarta Amma wannan karon zata iya turjewa shiyasa ya rufe idon yayi Mata me gabaki.

Jajir idanuwanta sukai zuciyarta ta dauki wani irin mummunan ‘daci da nauyi dataji tana marmarin mutuwartama Dan kuwa a rayuwa ta Jima tana kunsar baqin cikin maza Dana fashin aure Dana tsangwamar iyaye da ‘yan uwa Amma Bata taba Jin an Mata tozarci da baqin ciki irin wannan,
Aure tsakaninta da Wanda ta girma Wanda yake matsayin qanin Aminyarta ta Yaya ake tunanin tayi aure da rayuwar aure da JALAL Wanda bayan sannu ta gaisuwa Babu abindayake hadasu….

Najma karki damu godiya zakiwa Allah jira da zaman gida ya qare Allah yakawo lokaci kema kin aure,
Tsananin Rabon dake tsakaninkine da JALAL din yake Kore waincan aurarrakin naki da ake fasawa,Rabo ne me qarfi na haihuwa kesa irin wannan auren Dan shi Koda aure ko Babu sai ansamu Rabon Dan Haka muke qara godewa Allah da Akai hadin, Allah ya kawo……Wani irin kukan baqin ciki Mai qarfi ta saki sbd maganganun Dadahn dasuka fasa wani qoqon baqin ciki cikin zuciyarta ta miqe tashige kuryar dakin Dadahn tareda zamewa qasa ta zauna tana wani irin kukan da tunda take rayuwarta Bata taba yinsaba.

Tun abun na Wasa Dadah hankalinta ya tashi da halinda Naj din tashiga saitaji murnarta na Shirin komawa ciki Dan kuwa matuqar Najma taje gaban hajjo ko Alhaji Alfa tana wannan kukan na tashin hankali da zallan baqin ciki zasu iya warware auren sbd gudun damuwarta Dan Haka hankali tashe tasa akai Mata Kiran Dattijo da Umma ta fasa musu kuka tana cewa”

Matuqar Najma taqi wannan auren aka warwareshi to Nima barin gidan Nan zanyi bazan zaunaba dan zuciyata harbewa zatayi da kunyar Alhaji Alfa da hajjo Dan Haka gatanan ki fada Mata gwara ta dangana da wannan tashin hankalin ta rungumi auren.

Ko kallon Najman Dattijo baiyiba ya kalli ummanta yace”

Ki saka Mata hankali cikin kanta tadawo tunaninta Dan kema nasan bazaki so auren ya warwareba Dan idanma ya warware na fada Mata hukuncina bazaiyi Mata Dadi ba Dan bazamu zauna da qatuwar budurwaba kamarta muna rarrashinta akan aure bayanma tuntuni yakamata muyi Mata auren Dole mu huta.

Kallon Najman umma tayi tareda miqewa tsaye ta Isa inda take ta janyo hannunta tana cewa”

Inshallah zata fahimta aure Amma yariga ya dauru ma maganar warwarewa tunda ai Dan an Isa da itane akai Mata auren maganar taje gaban hajjo tana wannan kukan Ni kaina bani ba ita Dan Haka Najma ki nutsu kidawo hankalinki rayuwar aure zakiyi a gidan yanzu ba wadda Kika sababa, su din yanzu dangin mijinkine Kuma kinsan son da suke Miki bazasu taba cutatar dakeba hakama jalal ki yadda ko kiqi yadda mijinkine yanzu bashi girma yazama Dole.

Kinga Fatima jeki da ita can kuyi sauran abinda zakuyi na tsakaninku ganinan zuwa na maidata gurin hajjon da kaina shikenan.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 13_*
Zaunar da ita bakin gadon dakinta umma tayi tana kallon yanda fuskarta gabaki daya tayi jajir sbd kukan tashin hankali musamman dogon hancinta yafi yin ja ta zauna gefenta tana tausasa murya cikin kulawa da tausayi tareda kewar rabuwa da ita dazatayi duk da kusa suke tace”

Najma Dan Allah ki daina daga hankalinki akan abindaya kamata kiyi farin ciki akansa,
Farin ciki mukeyi kowama shiyake Dan tayaki murnar aure da Allah yabaki ikon Yi Wanda kinsani auren rahamace tunda kin dau lokaci da gwagwarmaya kafin kisamu kiga hakan.,
A shawarance matsayina na mahaifiyarki Ina Baki shawaran karki watsawasu hajjo da Alhaji Alfa qasa a ido kodan tsananin qaunar dasuke Miki wadda itace ta Sanya hakan,
Hakama Yaya kike tunanin Zaki iya kallon Hanifa kice bakyason Dan uwanta datafi so fiyeda komai a duniya wannan tunanin baiyiba ki ajiyesa Anan gida ki barsa zaman qarqashin ikon mijinki zakije kiyi bakida wani majagorancinki bayansa Dan Haka biyayya da bin umarninsa dole ne….

Wannan kalmar tasa wasu hawayen baqin ciki da ciwo masu zafi suka gangaro Mata tana sake sheshekar kuka ahankali, umma taci gaba da cewa”

A umarni Kuma na matsayina na mahaifiyarki Ina Baki umarnin ki aje maganar Araba aure anan ki barta Dan duk ranarda kikaiwa wani acikin gidan Alfa maganar daga ranar zakisan asalin kalan fushi da bacin Raina Dan Haka Dan Allah Najma na rokeki daki dauka dangana kiyi biyayya kaman yanda Kika Saba yiwa qanin mahaifinki Dattijo daya dauki damuwar tsakani da Allah yasakawa kansa akan al’amarinki,
Qanin mahaifinki ne Kuma Miji gareni Ni mahaifiyarki Dan Haka ya cancanta kiyiwa hukunsa biyayya Koba Dadi sbd baitaba nuna banbanci ko gazawaba a tsakaninku da nasa ‘yayan daya Haifa tun bayan rasuwar mahaifinku da wannan biyayyar kawai Zaki iya saka Masa kodan yanda yake Shiga tashin hankali da damuwa ba dare ba Rana aduk lokacinda neman aurenki yasamu matsala Dan Haka kiyi hkr ki dauki dangana Allah ya sanyawa rayuwar auren albarka.

Amin anty Amina tace tana qarawa da nata nasihar da rarrashi Dan kuwa duk Wanda yasan Naj baitaba ganinta a mummunar yanayiba irin yanxu Dan kukan datakeyi harya zama abin kayar da gaba.

Ganin idan aka biyeta sanyi jikin kowa zaiyi yasa aka qyaleta quryar dakin umman ta dunqule a gado cikin mummunan yanayi na qunci da baqin ciki hawaye Kuma sun kasa tsayuwa daga idanuwanta.

Hidimar Wunin biki akaci gaba dayi har dare masu tafiya gida suka tafi akabar baqin nesa kawai wainda Suma washe gari Dattijo yace kowa ya watse yakoma ‘dakinsa.

Mummunan yanayin da Naj din take yasa Dadah tacewa Dattijo yaje ya sanarwa Alhaji Alfa abar Naj din ta kwana gida har gobe tadawo sbd sudai duwarsu da tashin hankalinsu kada hajjo ko Alhajin sugan Naj a wannan halin komai zai iya faruwa Ana fadawa Alhajin yace bakomai abarta ta nutsu tukuna tazo Koda fiyeda goben nema zai fadawa mijin nata,da wannan aka barta gidan ta kwana.

Har safe tana dakin umma Nan takwana ko ganinta batason mutane nayi sbd tsananin kunyar kanta da wannan aure ga idanuwanta dasuka kumbura tsabar kukan data kwana tayi a Daren.

Hanifa na sane taqi zuwa sbd tana gidanta tun jiya da daddare mijinta ya dauketa suka tafi takuma qi kira Dan taji labarin kukan da Naj din keta faman Yi a bakin Anty Amina,
Taji tausayinta matuqa hakama tana iya kwatanta jin yanayi na damuwa da Naj din take ciki na auren Kai tsaye da Wanda ko taqamaimai kalma biyar Bata taba shiga tsakaninsu ba duk suka hadu tsawon shekaru kuwa Dan Haka take tausayin Naj din ga sanin halin JALAL datai na tsagwaron kamewa da basarwa Dan kuwa kafin Naj taganewa komai sai anga wuya.

Koda qarfe goma Sha biyun Rana tayi baqi kowa ya hada jakarsa ya kama hanyar komawa gida Dan Haka gidan su anty Amina dasu Khadija da zainab din Anty Amina sai aikin gyaran gidan suke Dan Haka Koda la’asar tayi gidan koina yayi fes fes sai mutan gidan kawai Kamar ba’ai taron biki ba dan ma da Dattijo Bai tsaya akan kowa ya watse yau ba da akwai wainda sai sunqara sati kila kafin su koma.

Bayan sallar isha tayi wanka tareda Shirin bacci tasaka riga da wando masu tsantsi na baccin kalar maroon ta janyo wayarta datun jiya data shiga tashin hankali take kashe ta kunna tareda ajewa gefe batareda tabi takan wayarba ta Haye gadonta tana Shirin kwanciya ummanta tashigo daukeda wani ruwan turaren humra me shegen qarfin qamshi ta ajiye gaban madubi tana zubawa a hannunta tahau shafawa Naj din akoina ajikinta tana cewa”

Sauko Dadah na Kira kutafi gurin hajjo duk da wannan baza’a kirashi da tarewaba Amma dai tafiyar kenan kila sauko ki sauya Kaya Mana.

Bata dago ta kalli ummanba tayi kamar bazata saukoba tsawon mintuna kafin dai ta sauko tana zura slippers dinta dake bakin gadonta ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko wata sabuwar jallabiyarta me Fadi kalar coffee brown ta warware ahankali ta saka kan kayan baccin Dake jikinta kafin ta jawo qaramin Chantelle veil ta yafa akanta Dan Bata daura ko dankwanlin jallabiya
Umma kuwa binta tayi tayi tana watsa Mata turaren harya ushers Yana Mata yawa murya a shaqe tace”

Umma Dan Allah ya Isa
Yana min yawa cikin Kai.

Dainawa umma tayi tana murmushi cikin kulawa tace”

To shikenan ai na barshi Haka Amma bazaki sauya kayaba…..idon da Naj din ta zuba Mata yasa ta waske zancen da sakin murmushi tana cewa”

Ko hakan ba laifi muje ku tafi gobe Amina zata kawo Miki kayanki Dattijo ma na gurin Dadah suna jiranki.

A dakin Dadah abun takaici agareta sabuwar nasiha da lallashi suka Dora Mata da dadin Baki da komai itadai tana jinsu batace komaiba sai sauraro  kawai sai Kuma zuciyarta dake Mata zafi da baqin ciki har lokacin Haka suka Gama ta ta fito itada Dadah da Dattijo Wanda ya fito da Kaya niqi niqi shida Anty Amina da Umma habiba kishiyar ummanta zasu maida gidansu Abbas acikin Daren.

Suna isowa bakin gate da wani irin sauri sojojin Marshal suka taso suka bude Mata kofa suna Mata gaisuwa cikin tsananin girmamawa dayasa Dadah sakin wata sabuwar hamdala cikin ranta abun na Mata Dadi sabanin Naj da “thank you” kawai ta iya bude Baki ahankali tace tana wucewarta kamar ba Amarya ba Kai tsaye gurin sashen hajjo suka nufa gidan tsit Suma duk baqi sun tafiyarsu.

Itace a gaba Dadah na bayanta da kallon ikon Allah da wannan Alamari saidai dayake lallabata sukeson Yi sai batace komaiba suka Isa babban palon gidan dazai isar da ita bangaren hajjo.

Kai tsaye ta shigo palon hajjo idonta dasuka kumbura suna kan kofar dakinta datakeda niyar shigewa ta rufe ta kwanta data shigo Dan Haka Bata lura da mutum dake zaune a palonba Yana cin abinci kan dining ta shige tabar Dadah dake shigowa da zama tana washe Baki ganin Jalal din zaune yanacin abinci tareda hajjo.

Cikin sakewa da farin cikin ganin Naj hajjo ta taso tana yiwa Dadahn barka da zuwa suka zauna suna sake gaisawa.
A ‘dan taqaice ya taso yaxo suka gaisa da dadah yakoma dining din Dan baima faraba yanzune zai fara cin.

Hajjo na kallon kofar dakin da Naj tashige tasaki murmushi tana cewa”

Inshallah ahankali zata sake ai tamayi kokari da biyayya ko ahakan Dan Haka baza’a takirata ba zatai zamanta taredani har su daidaita da mijin.

Zare jallabiyar jikinta tayi tabar kayan baccinta har zata kwanta ta fasa ta fito Dan zuwa gurin hajjo Dan Bata Saba fushi da hajjon ba duk kuwa yanzu tanajin kaman antaru an Mata rashin kyautawa da adalci.

Tana fitowa dukkaninsu suka kalleta hajjo na murmushi tace”

Zo ki zauna Nan Najma Babu Mai takuraki akan auren Nan Inshallah,
Zaki zauna Dani har sai lokacinda kikaji da kanki kinason komawa gurin mijinki…. Da sauri Dadah tace”

Ba maganar saita buqata da kanta tunda ba itace me ikon kanta da yanda takeso ba,
Idan Kika biyeta tunda ba tunani cikakke akantaba da Haka zata qare rayuwar auren bare tana ganin cewan ta girmesa Wanda girmewar ta zama ta banza da wofi dankuwa yanzu a qasanshi kike.

Murmushi manya hajjo tayi tana kallon Najman dake gefenta zuru tace”

Bazata tareba saita buqata hakan da kanta inshallah,
Ina Kuma da tabbacin zata buqaci hakan Inshallah.

Kasa wata magana Dadah tayi sbd takaicin Najman datai shiru alamar hakan shine yayi Mata daidai ta miqe tana cewa”

To na tafi Ni Saida safenku Allah ya bamu alheri Dan dai Naga alamar a sashenki kila za’a haif….katseta hajjo tayi da cewa”

Amin ya Allah Dadah Saida safe” saboda sanin Dadah zata iya yanko zancenta tsakani da Allah.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 14_*
Bayan tafiyar dadah hajjo ta kalli Najma da kallo daya zakai Mata kasan Kuka ta kwana ta yini tanayi duk da hakan fuskarta is so fresh sbd wankan da Bata Jima dayiba ga qamshinta tunda tafito ta zauna yake gauraye palon maida kallonta kan hanyar dining da jalal ke gurin har lokacin yanacin abinci Kamar wani sarki Wanda har lokacin Naj batasan da Yana palon ba ta miqe tana nufar hanyar dakinta tace”

Jeki ki kawomin ruwan dumi daki da Zuma zansha na kwanta ‘yar gajiya nakeji.
Shigewa dakinta tayi tabar Naj na lumshe ido ahankali cikin sanyin jiki ta miqe ta nufi dining hanyar dining Dan dauko zuman tana tafiya a natse har saidata shiga dining area din da kyau taga Wanda ke tsaye agurin hannuwansa sanye cikin aljihun guntayen qananun kayan dake jikinsa zai bar gurin tana isowa.

Mayun fararen idanuwansa ya ‘dan zuba Mata sbd yaji maganar Dadah ta banbancin shekarunsu data kawo Wanda yasashima ‘dan kallon nata Dan ganin abinda ake ikirarin ya girmesa a jikin nata Wanda a iya ganinsa baiga komaiba sai kayan baccin dake jikinta riga da wando ba bra ajikinta sai idanuwanta dasukai nuni da kukan datai ya kalli iya tsayinta da shafaffen cikinta ya dauke Kai ahankali Yana barin gurin yabarta tsaye tanajin wani irin damuwa da ‘dacin zuciya me qarfi duba da kallon tsaf sama sama da yayi Mata ya dauke Kai ya wuce yabar gurin da qamshinsa na _Tom Ford, Tobacco vanille_ daya zama Kamar maita tasan qamshim kamar me sbd shikadai tasani me amfani da turaren Dan tsadarsa.

Numfashi me zafi ta sauke tareda shaqaqqen tsokin dabai fitoba taji duk komai ya fice Mata a sukwane ta hadowa hajjo ruwan takai Mata ta fito ta wuce daki ta kwanta tanajin wani Abu toshe a maqogoranta da qyar tasamu bacci ya dauketa.

Qarfe Tara na safe ta fito Palo sanyeda doguwar straight gown ta atampar super exclusive maroon dataiwa farar fatarta kyau fuskarta fayau ko kwalli Bata sakaba saidai qamshinta daya zama na koyaushe dayake tashi jikinta idan ta kusantoka.
Da slippers a qafarta ta nufi kicin ta hado tea me zafi sosai tadawo Palo ta nufi dakin hajjo tana sha ta zauna kujerar dakin tana cewa”

Ina kwana hajjo.

Amsawa hajjon tayi tana cewa”

Kinyi waya da Hanifa kuwa?
Tun jiya Isma’eel yakira batajin Dadi Wai hannunta na dama ya riqe Yana ciwo kamarma yakira wayarki a kashe yace.

Miqewa tayi tana cewa”

Bari na dauko wayar tun jiya na kunna inaga Banda caji ne Bari nasaka nasamu ko kadan ne saina kirasu kafin na Isa.

Kallonta hajjo tayi tana cewa”

Ki Isa Ina da sabon aurenki akai Najma¿
Kinga hakuri Zakiyi tunda Isma’eel din na Nan Kuma Dr sa’id ma yaje tun jiyan Dan Haka basai kinjeba yanxu Bari a kwana biyu tukuna.

Shiru tayi yanayinta ba Dadi idanuwanta na sauyawa da ciko hawaye kafin Tai magana Hannah tashigo dakin da sallama muryarta a shaqe,hajjo na ganin fuskarta tasan itama kwana tayi kukan Dan kuwa a kumbure idanuwanta suke jajir.

Naj ta qurawa ido zuciyarta na wani irin harbawa da zafin radadin kishinta me qarfi saidai kamar yanda mum Malika ta hudubar da ita akan danne fushi da boye bacin Rai shine matakin nasarar komai tunda dai kowa yasan daga Naj din har marshal ba son juna sukeba aurene kawai na Hadi na huce takaici da fita kunya Dan Haka fushi da qunci ba nasu bane samun zama Matar JALAL da rabuwarsa da Naj ba wani Abune dazai Basu wuyaba ko daga musu hankali Dan Haka dole zasu danne ‘dacin zuciyarsu.

Dan yaqen dole tayi tana qarasowa ciki ta zauna kusada Naj tana cewa”

Hajjo Ina kwana?
Ya gajiyan taro?
Allah yasanya alkhairi.

Hawayen datake dannewa suka gangaro ta qarasa gaban hajjo ta durqusa tana sake siririn kuka ahankali tace”

Dan Allah karkiga laifin kukana hajjo zuciyatace ke zafi bansan yazanyiba naji sauki bayan kukan sbd abin yazomin a bazatane.

‘dan tausayinta hajjo taji Kuma tasan Kam Dole hannah zataji damuwar abin musamman datasan ayanzu Kam babu ranar auren Hannah din da jalal sai taga Najmanta tasamu zama dakyau tukuna Dan Hakan takejin tausayin Hannah ta dafa kanta tana cewa”

Kiyi hkr shi aure muqaddarine Kuma Allah yayi itace zata zama Matar ayanzu Amma kadaki daga hankalinki Matar mutum kabarinsace kema lokacin ne baiyiba ki kwantar da hankalinki kinji.

Shiru tayi tanajin wani qaton takaicin tsohuwar Yana tsaya Mata a maqoshi datake Mata zancen wani lokaci bayan ba Haka takeson ji ba.

Share hawayenta tayi tana miqewa a sanyaye ta juyo gurin Naj datake Shan tea dinta batareda ta maida hankalinta kan zancensuba ta Dan saki yaqen murmushi tace”

Naj Allah ya Sanya alkhairi da fatan bazaki ringa Jin damuwar alaqata da Marshal ba.

‘dan kallonta Naj tayi kafin Kai tsaye tace”

Thank you” kawai taci gaba da Shan tea dinta Dan ita abundama zai ringa alaqantata da Marshal din Bata buqata Dan Haka Hannah ma na cikin abinda zata nesa kanta dasu.

Kallon tsaf Hannah taqare Mata tana ayyana wannan shariyar ta Naj datake Kamar wulaqantawa gareta kafin ta juya ta fice idanuwanta na sake kadawa da Jan baqin ciki da takaicin hajjo da Naj din.

Cajin wayarta Takoma daki tayi takira Hanifa sukahau wayarsu duk da taqi Bari Hanifan tayi Mata maganar auren itama Hanifan data fahimci Haka saita bar yimata maganar suka hau zantukansu.

Saida tayi sallar azahar ta ‘dan ci abinci kafin taje gurin gaida Dad Alfa datun jiya Basu haduba tafara zuwa gurin mum Malika ta gaidata Kamar yanda suka Saba Babu komai a fuska mum din ta tarbeta suka gaisa Tai Mata addua da fatan alkhairi Hannah na daki tanajinsu taqi fitowa sbd ayanzu kyakkyawan fuskar Naj tafasa zuciyarta yake itakuwa Naj Kai tsaye palon Dad din ta nufa tana duba wayarta ahankali tashiga da sallama ta tura kofar palon tana kashe wayarta Yana zaune kuwa a palon suna magana da jalal dake gefensa sanye cikin farar jallabiyar datasa takasa ganesa sosai Dan kuwa hardasu qaramar farar hular tabani kaji hadisi datai Masa wani irin kyau sbd kayane dabai cika sawaba sai yazo Nan Dan acan kayansa idan ba suit ba sai uniform din aikinsa sai kuwa qananun kayan Shan iska dayafi sakawa idan baya aiki komai Wanda suna cikin kayan dasuke Masa kyau sbd kyan fatar jikinsa.

Dauke Kai tayi daga gefensa tanajin idanuwansa na yawo a jikinta ta qaraso ta zauna a qasa tana gaida Dad din cikin nutsuwa.

Amsawa yayi Yana Mata barka da gajiyar biki cikin farin ciki kafin ya Dora da yimusu nasiha musamman ita akan dole tabi umarni da hukunci JALAL kowane irine cikin biyayya.

Shiru kawai tayi batareda ta dagoba har yagama ta Dan dago tace”

Nagode Dad” ta miqe ta fice batareda Tama nuna tasan da akwai wanzuwar wani a palonba bayan su.

Bayan fitarta waiwayowa dad yayi ya kallesa batareda yace komaiba ya Dan saki gajeran murmushi Yana mamakin qarfin girman Kai irin nasu su duka biyun Wanda bazai taimakesuba.
##MAMUH#

 

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 15_*
Washe gari sanin a daki ta wuni taqi fitowa sbd fahimtar dai a sashen hajjon yakecin abinci abinda Bata saniba shine baya fitowa zuwa cin abincin Rana acan ake Kai Masa sbd baya fitowa da ranar sai dare yake fitowa cin abincin Daren Dan masallaci kawai yake iya fita cikin Rana Amma bayan sallah Babu abinda yake sakashi fitowa cikin Rana Wanda hakan ne yasa skin dinsa yake fresh koyaushe.

Hajjo na sane da dalilin qin fitowar tata Dan Haka itama Bata damuba tunda lallabata takeson Yi Dan Haka Bata dametaba ta qyaleta,
Sai dare ta fito sanye da riga da wando na bacci farare masu tsantsi kanta sanye da qaramar hular da Bata Gama rufe gashintaba hannunta riqe da waya tana sai qamshi takeyi me sanyi ta nufi kicin ta dauko fresh milk Mara sanyi sosai tafito tanasha ta nufi dining tana shiga idanuwanta suka sauka kansa Yana zaune cikin fararen qananun Kaya hannunsa riqe da cup din ruwa marasa sanyi yanasha ahankali.

Dauke kanta tayi tana kokarin juyawa hajjo dake zaune taredashi tace”

Zoki zauna.

Dakatawa tayi tareda Dan rufe idanuwanta kafin ta bude ta juyo tareda kallon hajjon fuskarta Babu wani sauyi daga straight din datake cikin muryarta me nutsuwa Kai tsaye tace”

Banajin yunwa freshi milk din ya isheni bacci zanyi Dan natashi da wuri gobe zankoma aiki office.

Dan kallon Marshal hajjo tayi taga ko dagowa baiyiba bare yanuna yasan da zuwan wani agurin saidai tasan yanajinsu,
Ta maida kallonta kan Najma cikin kulawa da tausasawa tace”

Wane aiki bayan Baki Gama hutawa daga hidimar biki ba Kuma saikun zauna da mijinki kunyi magana akan aikin idan yaji zai Bari kici gaba.

Dagowa Najma tayi da idanuwanta dasuka sauya Nan take da maganar ta kalli hajjo sai Kuma takasa magana tayi shiru tana hadiye wani daci daya danne zuciyarta ta Dan rufe ido tabude ahankali tace”

Kaina Yana ciwo zanje na kwanta Saida safe hajjo.

Juyawa tayi zata wuce hajjo tace”

Dawo Najma zoki zauna.

Dakatawa tayi tafara sauke numfashi kadan kafin ta juyo tadawo taja kujera ta zauna batareda tace komaiba sbd Jin numfashinta ma takeyi Kamar siqe zamanta agurin da Wanda har lokacin Bai nuna yasan da wanzuwar wata halittar Dan Adam agurinba Wanda Kamar Ana sake sukar martabartane na mace dakuma girmanta.

Ahankali ya dauka tissue yana goge bakinsa Dan yagama cin abincin sai alokacin ya dago ya kalleta Yana kallon hajjo datake lallabata da alama zatai taurin Kai da taurin zuciya
Ya dauke Kai ahankali tareda miqewa tsaye ya zuba hannuwa a aljihun wandonsa ya bude Baki Kai tsaye a gajarce yace”

Saida safe hajjo” ya juya ya wuce yabar gurin harya fice itama Bata dagoba bare ta nuna tasan dashi,

Kallonta hajjo keyi tana Jin qaunarta da tausayinta tareda jinjina taurin zuciyarta Dan kuwa sosai ta hango tsanar auren da qinsa cikin idanuwan Najma da zuciyarta,
Bataji dadin hakan ba Amma Kuma Dole za’a dubawa Najma din tunda aurene na Babu shiri Babu sanarwa Babu amincewa musamman yanda take yiwa auren jalal din auren ci baya qarara amatsayinsa na qanin qawarta Wanda Kuma takejin bazata iya russunawaba ya juyata kamar yanda maza ke juya matayensu.

Hajjo da kanta ta janyo plate ta zubawa Najman abinci kadan iya Wanda tasan tana iya ci ta turo Mata gabanta cikin kulawa tace”

Ci abinci kafin kije ki kwanta din karki kwanta Babu wani Abu me Dan nauyi a cikinki kinji.

Bata iya gardamaba Sam musamman a yanzu da zuciyarta ke cikin wani hali Dan Haka ahankali tadauki spoon tafara cin abincin hajjo na kallonta tana sake Bata Baki akan karta damu Babu Wanda zai takurata akan komai.

Daqyar tayi spoon shida ta dauki ruwa Tasha ta ajiye ta kalli hajjo cikin nutsuwa tace”

Na koshi zanshiga daga ciki.

Tare suka miqe saidata raka hajjo har dakinta ta sake gyara Mata gadon kwanciyarta kafin Tai Mata Saida safe ta fice.

Tana Shiga daki toilet ta wuce tayi brush tafito ta hau gado ta kwanta tana rufa da bargo wasu hawaye suka gangaro Mata saiga kuka ya kufce Mata ahankali ta rufe idanuwanta tana sakin kukan ahankali tanajin wani irin radadi a zuciyarta,
Bayan qaddarar rashin aure data fasawa qarshe dai qaddarar irin wannan aurence take jiranta,
Auren Wanda ta girma,Wanda ko kallo Bata isarsa bare ya nuna sanin da ita a duk haduwar dazasuyi tayaya zatai rayuwa ahaka a gurin Wanda tafi Amma agurinsa ita ba komai bace face ta qarqashinsa,
Bata buqatar soyayya Amma dai tayi fatar yin aure inda zatai rayuwar ‘yanci da mutuntawa tareda Bata kulawa da qaunar data rasa samu tun tashinta,
Batada shaquwa da mahaifiyarta sosai sbd miskilancinta,batada shaquwa da ‘yan uwanta da kowa nata face Hanifa wadda itama itace me kokarin riqe shaquwar tasu sbd miskilancinta Dan Haka tayi fatar jinkiranta ya zamar Mata alkhairi tasamu mijin dazai rusa miskilancinta ya cike gurbinsa da soyayyarsa da qaunarsa Amma Haka qaddara tazo Mata Wanda ta gwammaci zamanta Babu me aurenta da wannan auren dazai ringa quntata rayuwarta a zahiri da boye.

Washe gari Haka takuma wuni a daki Bata fito ba a dakin ruqayyat takai Mata abinci Wanda hajjo tasa akai matan.
Koda daddare Bata fitoba saidata tabbatarda ya bar sashen ta fito taje tayiwa hajjo Saida safe Takoma takwanta.

Saidatayi kwanaki tana kiyaye duk wani Abu dazai hadata dashi ko a hanya ne dan ko Dad Alfa idan zataje gurinsa saita Gama tabbatarda Rana tagama tsagowa lokacinda taji baya fitowa kenan a bakin hanifa take zuwa gurin gaidashi su mum Malika ma tana Dan shiga sama sama sbd lurada Hannah Kamar tana Dan Jin zafinta Wanda Sam gabaki daya daga Hannan har Wanda takeyi dominsa basa gabanta Bata Kuma buqatan su shiga gaban nata.

Daqyar taga sati biyu tacika Isma’eel ya koma Hanifa tadawo gidan sai alokacin taji hankalinta yadan dawo Mata musamman yanzu da Bata ganinsa Babu me Mata maganar auren saitake mantawa tana fitar da abin a kanta ta tattara maganar auren ta watsar gefe tafara kokarin son komawa aikinta Amma Kuma Bata buqatan kowa yasake tada mata maganar Saida izinin wani ko damar wani zata fara fita aiki hakan yasa taketa dannewa.

Ta bangaren Marshal kuwa kamar yafita mantawa da maganar auren Dan kuwa gabaki dayama ya daina shigowa ko cin abincin akai akai wani lokacin Hanifa ce ke kaimasa suyo firarsu da maganganunsu dasuka shafesu acan duk da yawanci nasa sauraro ne sai kadan kadan yake saka doguwar magana tanason sako Masa maganar Naj Amma tana Hana kanta kamar yanda suka yanke da hajjo bazasu takuraba akan zancen ahankali komai zai daidaita.

Lokacinda tasamu labarin komawarsa abakin hajjo da Hanifa Sam Bata nunama tajiba Dan ba abune daya shafetaba Dan ita yanzu tabar auren akan hanyar data sauya Mata na uzzurawarsu Dattijo dasu Dadah da ummanta ma hakama dai tana gidane bawai wani gurinba hakama Wanda ake Kira da mijin da auren duk basa gabanta itama Bata gabansu Dan Haka hakanma is okay tunda tasamu yancinta ta wani bangaren.

Yau ciwon baya Hanifa ta tashi dashi me ‘dan qarfi Dan Haka bayan zuwan Dr sa’id yadubata yabata wasu magani da wasu treatment dayasa sukai mata na Nan gida tasamu sauki Sosai ba laifi musamman datai bacci Sosai har yamma kodata farka alhmdlh taji sauki saidai Dan sanyin jiki na rashin qwari na wuni datai kwance Dan Haka wanka Naj ta taimakata Mata tayi tayi salloli taci abinci sai alokacin ta dan sakewa ta dauki wayar mijinta dake Kira tun dazu yanajin Yaya jikin.

Sai alokacin Naj tasamu nutsuwa tafito taje taci abinci tadawo tayi sallar ishai da aka Kira tana idarwa ta tube ta shige toilet wanka Dan bacci takeji Sosai.

Tun safe baya gida Yana gurin wani sabon company da Dad Alfa zai bude rashensa anan Wanda Marshal din zai sake zuba hannun jarinsa me kauri kamar yanda shares dinsa sukafi yawa a wancan company din da Naj take gudanarwa.
Sai kusan magriba suka dawo Dan Haka sallar magriba yayi ya shige Saida ya huta yayi wanka yayi ishai kafin ya nufo sashen hajjon qamshin TF tbc daya Gama Kama jikinsa Yana tashi jikinsa Hannah datakai Masa fruits salad daya ‘danci kadan suka fito tare zuwa sashen hajjon tana gefensa tana Masa fira cikin wayewarta da sonsa daya Gama cire Mata kunyar kowa itama sai qamshi takeyi tana sanye da doguwar free grown me guntun hannu dayake bayyanarda tattoo dinta me dauke da sunansa a gefen kafadarta.

Babu kowa a Palo sai qatuwar LG TV dake aiko Dan hajjo na dakinta Kai tsaye suka nufi dakinsu Hanifan hannah na daukeda sauran fruits salad din dazata kawowa Hanifan Dan nuna kulawarta da damuwarta.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 16_*
Hannah ce tayi Dan knocking dakin so biyu kafin ya tura kofar suka shigo tana Dan nuna kulawa ta qarasa gurin hanifan tana ajiye bowl din hannunta kan table tana cewa”

Ohh sister in-law sannu da jiki tun dazu naso shigowa kaina Yana Dan ciwone shiyasa ban shigoba ya jikin?

Gyada Kai Hanifa tayi tana cewa”

Alhmdlh naji sauki thank you.

Dagowa tayi ta kalla Marshal din Yana tsaye da hannu cikin aljihu ganin hanifance kawai a dakin yasashi zaunawa ahankali kan sofa Yana kallonta da fararen idanuwansa ya bude Baki cikin kulawa yace”

Yaya jikin?
Ina tare da dad yau duka sai yamma nasamu kaina,
Dr sa’id yamun bayanin komai Yace hadda sanyi yana Miki yawa meyasa bazaki daina kwana da AC ba?

Murmushi ta ‘dan saki tana kallonsa yanda koyaushe yake tamkar shine yayan sbd irin tasa kulawar.

Gyara zama tayi tana kallonsa da sauran rashin kuzari a muryarta tace”

Ina kiyayewa Marshal.

Jeho kanta Hannah tayi cikin zancen da cewa”

Sister in-law Allah yabaki lafiya duk mundamu dake bamason ganinki cikin irin yanayina ciwo musamman Marshal he cares for you so…….katsewa zancenta yayi yawu na neman zubo Mata daga Baki tayi saurin hadiyewa sbd idanuwanta dasuka sauka Kan kofar toilet da aka bude Naj ta fito daureda towel sky blue me haske cinyoyinta dasukafi komai tada hankalin Hannan sai daukan ido sukeyi tayi sama da idanuwanta kan qirjinta dasuka fito Dan fito ta saman koina jikinta daukan ido yakeyi gashinta daure a tsakiyar kanta ta dauresa da Banda gabaki daya Bata lura dasuba Dan batasanda suna dakinba Dan hakan taqarasa fitowa Kai tsaye ta rufo toilet ta nufi closet tana cewa”

Hanifa ruqayyat takawo wankin kayan da aka dauka jiya??

Tsit dakin yayi musamman Hannah data waiwayo da sauri ta kalli marshal din taga idanuwansa basa kan Naj suna kan wayarsane ta kalla Hanifa da ita Kuma Jalal din take kallo Dan kuwa akan idonsa sak Naj ta fito Kuma ta tabbatarda ya qarewa Naj din kallo sak kafin ya basar ya dauke Kai.

Da sauri Hannah ta miqe tana cewa”

Umm Naj Ashe kina ciki bamu saniba sorry Bari mukoma Palo zamu jira ki Gama shiryawa tukuna.

Wuta Naj ta dauke tareda waiwayowa cikin tsananin mamaki da takaici ga sabon baqin cikinta ba Hannah ce kawaiba akansa idonta ya sauka daidai ya dago zai miqe ya fice idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke idonta suna sauyawa kin wani irin baqin ciki da kunya da takaici lokaci daya suna taso mata ta juya Kai tsaye Takoma toilet din daukeda kayan barcin data fitar zata saka a hannu.

Kodata Gama shiryawa ta fito basa dakin sun tafi har Hanifa Bata dakin tana dakin hajjo taredashi da hajjon suna magana sbd gobe zai koma duk yanda taso kasa Masa maganar Naj din kasawa tayi ta kalli fuskarsa dake fresh Kamar wani Dan baby hankalinsa nakan hajjo Yana sauraron bayanin datake Masa akan dawowarsa yanzu akan lokaci sbd akwai nauyin iyali akansa.

Marshal bazakai magana da itaba kafin ka wuce?
Kaji koda akwai wani abun datake buqata?

Shiru sukai suna jiran Jin amsarsa saisukaga ya miqe Yana kallon agogon hannunsa yace”

Zanje na kwanta gobe zantashi da wuri.

Kofa ya nufa hajjo tace”

Goben ka tabbatarda kayi mgn da ita kafin ka wuce.

Da umarni tayi maganar ba wani Wasa acikinta shiyasashi Dan dakatawa batareda ya juyoba kafin ya taka yafice Hanifa na bayansa tana sake Dan saka Baki a maganar.

Sam ba irin wannan auren yasoba Wanda kowa zai ringa shiga tsakanin mu’amalarsa da matarsa sbd yanason yayi nutsatsiyar rayuwar aure Mara hayaniya da soyayyarda baya buqatan shigan wani zancen,
Ya lura zata ringa hada Masa tarin mutane acikin rayuwar auren Wanda baya buqatan hakan Amma zaiga tsarin dazai dauka.
Koda ya Isa sashensa Saida yakuma wanka da ruwan dumi kafin yayi Shirin bacci ya kwanta.

Bacci me qarfi da dadi itama yau tayi shiyasama tayi lattin tashi sallar asuba Dan sai guraren qarfe bakwai ta bude idanuwanta dake tareda sauran bacci ahankali tana Dan motsawa ta lumshe ido sbd Jin sabon qamshin daya Shiga hancinta ta tashi zaune tana ‘yar miqa botiran gaban rigarta uku na sama suna budewa sbd miqar datai ta zuro qafafunta qasa tareda miqewa tsaye idanuwanta suka sauka Kan mutum a tsaye cikin dakin Yana kallonta jikinsa sanye da _Prada-gabardine straight leg trouser _ brown sai White spread collar long sleeves gabaki daya dakin ya gauraya da qamshinsa fararen idanuwansa ya zuba Mata akaro suna yawa ajikinta sbd tunda aka daura Masa aure da ita ake maimaita kalmar girmansa datai Wanda haryau yakasa ganin wani Abu dayake tunanin ya girme Masa
A taqaicema kallon dayake Mata yasa yake qara ganin zamtowarta qasanshi.

Kallon dayake Mata yasata dakatawa daga wucewar datasoyi ta shige toilet saita nufi kofar ficewa daga dakin zata fice bacin ran dake ranta Yana bayyanuwa kan fuskarta akaro na farko da mace ta wucesa tabarshi tsaye
Kai tsaye ya damqi hannunta tareda dawowa da ita baya ya tsayar da ita gabansa fuskarsa a hade tsaf ya kalli hannunta datake kokarin fuzgewa a fusace batareda tace komaiba Dan bazata iya bude Baki Tai Masa mgna ba Sam,
Ba wani riqo yayi Mata ba Amma gabaki daya takasa qwacewa ta dago a fusace ta kalli fuskarsa idonsa cikin nata ta janye idonta Kai tsaye tace”

Meye hakan?
Kabar hannuna.
Wannan auren ba wani aureneba kamar kowanne dazai baka Daman tabani so can u get your hands off me.

Sabon kallo yayi Mata Jin abindata fada daya basa mamaki Dan baiyi tunanin zata iya magana Haka ba.
Fizgota yayi ta Fado jikinsa ya dago shanyayun idanuwansa ya zuba Mata Yana kafin ya kalla kirjinsu daya manne Dana juna tana ganin hakan ta qwace da qarfi cikin tsananin bacin rai tareda turesa da iya qarfinta yayi baya ya zube kan gadon dakin kafin ta juya ya janyota tafado jikinsa daidai turo kofar Hanifa data shigo dakin Hannah na bayanta Jin shiru sbd dama itace ta fito din tace yashiga Naj din na ciki Dan wucewa zaiyi.

Da sauri a firgice Naj ta waiwayo kofar tana kokarin tashi daga jikinsa idanuwanta na cikowa da hawayen baqin ciki da bacin Rai
Hanifa kuwa juyawa tayi da sauri tana cewa”

Sorry sorry.
Hannah kuwa da sauri ta qaraso gurin tana Kama Naj dakeson tashi tana cewa”

Bari na taimaka Miki.

Sakinta yayi yana tashi daga kan gadon Kai tsaye ya fice daga dakin Yana duba agogon hannunsa sbd lokaci dayaso shige Masa Bai luraba.

Hajjo Kamar koyaushe idan zai tafi har mota take rakasa itada Hanifan Haka suka fito Hannah na gefensa tana fada Masa irin yanda zatai missing dinsa a can harabar gidan ya tararda Dad Alfa dazasu fita tare tareda mum Malika daketa zuba nata iyayin na zatai kewarsa matsayinta na uwa.

Gidansu Naj yashiga tareda Hanifa yaje yayiwa umma bankwana tareda bar Mata abindaya Saba Bata duk yazo idan zai koma hakama Dadah wannan karon kyautar dataso firgitata yayi Mata kafin yafito tareda Dattijo suna maganar Yana sanar dashi abar Naj din taci gaba da aikinta idan tanada ra’ayin.

Motarsa data sojojinsa lokaci daya suka tashi sukabar kofar gidan wasu na ‘yar murnar zasu samu ‘yancin unguwa zakai iskancinsa cikin anguwa yanda kaga dama ka tada hayaniya da rigima son ranka tunda sojojin Marshal sun tafi sojojin dake tsoron gidan basuda muguwar fitina da ikon wahala Kamar na Marshal din matuqar Yana gari ko Rigima da fada andaina a layin Dana bayansa sai Kuma suntafi Dan Haka yau kowa yayi yanda yaga dama.

Toilet tashige saidatai kukan baqin ciki Mai isarta kafin ta iya alwala ta fito baqin ciki da kunyar kanta na kamata tayi sallah tana idarwa tun kafin Hanifa tadawo dakin Takoma tayi kwanciyarta ta rufa tana rufe ido Dan komawa bacci saidai tasan halinda zuciyarta take ciki bazata iyaba.
Hanifa data dawo dakin Bata wani jawo zancen komaiba itama Takoma ta kwanta tana murmushin abinda itace kawai tasan metakeji aranta.

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 17_*
Koda tagaji da kwanciya da kame fuska taga hakan zai sake cutatar da itane sai kawai ta watsar da al’amarin ta sakewarta taci gaba da abun dayake gabanta tayi wanka ta shirya cikin riga da wando na Shan iska tafito ta nufa kicin ta hado abin datake buqatan ci tadawo dining ta zauna tanaci Hanifa ta fito itama a shirye cikin atampa doguwar riga tayo gurinta tana cewa”

Zanci Nima yunwa nakeji.

Qarasowa tayi ta zauna tana kwada Kiran ruqayyat tace”

Ki kawomin abinci Nima inajin yunwa sosai.

Sunacin abincin tanata jawo fira da zantuka kala kala Wanda dama tasaba itace me janyo Hira a tsakaninsu itace me zancen itace me Hira.

Palo suka dawo suka zauna bayan sunyi sallar azahar da akai suka dasa Hira hajjo na daki yau batajin Hira karance karancen Islamic books dinta takeyi.

Da yamma sosai saiga Sarah takawo Mata wasu files da ake buqatan tayiwa signing Nan ta maida hankali kan takardun tana dubawa Sarah na qara koro Mata sauran bayanan ayyukan dasuke zaman jiranta a office din tanason ta sanar da ita Abbas yadawo aikin da kowa yayi tunanin zai ajiye Amma Kuma ganin Hanifa yasa takasa fadar maganar tunda yanzu Naj din surukarsu ce kawo Mata maganar wani ba daidai bane zata Bari sai Takoma office din zata sanar Mata.

Ganin hankalin Naj yakoma kan aiki gabaki daya dama ita abida yasa takeson aikinta sbd shi kadaine zata zauna tayi batareda wani surutu ko hayaniyaba shirun tana aiki Yana bada nutsuwa Dan Haka Hanifa tabarta Takoma kicin gurinsu ruqayyat suna aikin abincin dare dama ita tana aiki cikinsu lokuta da dama sbd tanada sha’awan girke girken.

Sai bayan magriba tagama duba ayyukan da Sarah din takawo Mata suka tashi sukai sallah kafin Sukaci abinci Sarah tayi shirin tafiya gida suka fito tare ta rakota har waje tareda miqa Mata 10k tace tadauka drp na taxi taje gida.
daidai ta juya zata shige ta hango Hannah tafe tun Bata qarasoba tayi wucewarta Dan bazata iya da sauraren maganganuntaba.

Tana Isa daki ta wuce saidatai sallar ishai kafin tayi wanka tayi Shirin bacci takwanta sbd tana jiyo hirarsu Hanifa har lokacin Hannah na sashen.

Washe gari Haka ta wuni tana aikin wasu takardun data saka Sarah kawo Mata tun tanayi sama sama kwanaki suka Dan fara ja kusan tadawo da aikin office dinta gida takeyi saidai Sarah Dake faman Shan yawo tsakanin office da zuwa gidan kullum.
Hajjo data lura da aikin na Sanya Naj din samun nutsuwa sai tafadawa Dad Alfa akan maganar komawar Naj din aiki duk da Bata wani so Naj din Takoma aikinba Amma Haka ta hakura tabari saidai tasan JALAL zaiyi wuya yabari tunda ita din yanzu matarsace.
Dad alfa dakansa yayiwa Marshal magana cikin nasa mamakin yaji Kai tsaye yace abarta taje
Shikuma kawai bayason arinqa nanata Masa maganar auren da nauyinta dake kansa Dan tunda ya dawoma yamanta da maganar auren yake aikinsa da rayuwarsa yanda ya Saba ko tunota sai Yana waya dasu hajjo yakeyi idan sun jeho Masa maganarta.

Ta bangarentama tunda aka Bata damar komawa aiki tafisa mantawa da auren musamman da Dad Alfa ya siya Mata lafiyayyar sabuwar motar datake hawa Dan Haka yanzu aiki takeyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,
Babu damuwa da tunanin fada da gorin dattijo, Dadah da ummanta akan rashin aure saima kulawa da qauna dasuke nuna Mata a yanzu din Wanda yake na lallabawa kada ta bijire auren ya kwabe lissafi yadawo musu sabo,
Ta bangaren office kuwa yanzu girman datake samu gurin ya zarta na kowa dake ALFAS din sbd yanzu tana amatsayin Matar me company dinne sbd sanin da kowa yayi Marshal shikeda 60% shares a company din.

Abbas duk wani Abu dazai hadasu bayan meetings batabi sbd har lokacin Yana sauran ‘danyar haukarsa atare dashi Dan kuwa kallo yake Mata harna qurulla wani lokacin Kuma harda ‘yan maganganu Amma Bata taba ko kallon inda yakeba Dan dama wannan tun suna tare yasan halinta dabi’artane rashin tankawa da kulawa.
Qarshe sbd nunawa da son nuna rashin gazawarsa da kausar yafara soyayya receptionist dinsu Kuma cikin gaggawa suka fara gabatarda komai lokaci qanqani saigashi Ana sanarwar aurensu Nanda wata biyu masu zuwa.
Duk wannan sha’anin nasane yakeyi shi kadai Dan kuwa ko hankalin saurara Bata badawa idan Sarah na kawo Mata zancen abindayeke faruwa bare ta fahimci menene dinma yake faruwa.

Sosai yanzu takejin dadin rayuwarta Babu takura Babu wani damuwa Haka take gudanarwa,
Kullum zata tashi tayi Shirin office tafito tasa masu aiki suyi Mata abinda takeso taci taredasu hajjo da Hanifa, tafito taje gurin dad Alfa tai Masa gaisuwar safe kafin tafito ta wuce aiki,
Idan tadawo zatai wanka tayi sallah taci abincin tayi baccin yamma kafin tatashi tayi sallar magriba sai suyi firar dare dasu hajjo wani lokacin idan Batai baccin yammaba gidansu take zuwa acan take baccin dakin ummanta kokuma firarta dasu duk da ba itace me firarba Yi akeyi tana Dan amsawa da eh ko aa sai ido datafi sauraron hira dasu.

Ahaka lokaci Mai Dan tsayi yaja tasamu sauyi sosai na jiki da rayuwa Dan kuwa fatarta ayanzu tafi samun qarin hutu da lafiya tareda kyau.
Tayi fresh sosai sbd har wani irin haske take qarawa kullum musamman dayake itama Bata cika Shiga Rana ba Dan rayuwarta bazata iya yaushene zuwanta kasuwaba kokuma siyayya irin gurare masu Rana sosai haka yawanci siyayyarta online shopping takeyi akawo Mata har gida sai idan sunso su fita da Hanifa zuwa manyan malls Haka siyayyan Yan abubuwan amfaninsu kaman su turaruka dasu Mai sai undies da qananun Kaya Haka
Musamman ita Naj indies basa isarta kullum cikin siyansu take.

Gabaki daya rayuwarta ta manta da auren dake kanta sbd rayuwar data samu kanta aciki ta rashin takura shiyasa ta sake sosai tana gudanar da rayuwar yanda takeso.

Kamar dai yanda Dr said yasake hadawa Hanifa appointment da Dr Kenneth a Sweden yanzu lokacin zuwanta ya qaraso Dan Haka suke cikin damuwa musamman Hanifan Wanda tasaka ran samun haihuwa sosai a ranta.
A yanda suka bibiyi likitoci tun shekarun aurensu na farko an tabbatar musu da cewa Hanifa bazata iya daukan ciki da kanta ba ma’ana zaiyi wuya saidai ayi Mata dashensa Wanda ta daga hankalinta sosai tashiga damuwa Suma sumshiga damuwa sbd halindata shiga qarshe akai dashen cikin na wata biyu ya fita shima tashiga wani mawuyacin hali na tashin hankali da shiga qunci da addua da komai aka samu ta dangana tayi tawakkali tadawo daidai saidai sun dibar Mata lokacinda zata dawo asake Mata dashen Wanda shine lokacin yayi yanzu saidai Kuma damuwa da tsoron ko zata samu ko bazata samuba ya Hana zuciyarta sukuni duk yanda takeson danne damuwar kasawa takeyi Wanda yake sake sakawa hajjo tausayinta sbd tana cikin jarabawa ta lalurar lafiya yau gobe Babu ga wannan jarabawa ta rashin samun haihuwa Dan ma tanada tawakkaline soda dama Koda damuwar abin ta taso Mata tana dannewa da rokon sassauci gurin ubangiji gashi a zuriar gidan basuda iyali da yawa sune suke fatar su cika gidan da nasu yayan Amma batajin za’a samu daga gareta kila saidai ‘dan uwanta JALAL.

Damuwar da Hanifa take ciki tasa gidan kusan kowa damuwar yakeji ita kanta Naj din tunda aka tsaida ranar tafiya Sweden din ta nema hutu office ta daina zuwa koyaushe tana tareda Hanifar wadda damuwa tasaka ciwon gefen ciki ya kamata cikin lokaci qanqani ya kwantar da ita Nan hankalinsu yakuma tashi ga tafiyar nata sake qarasowa Dan saura Kwana biyu su wuce wannan karon tareda Naj din zasu sbd zasu hade da Isma’eel acan sai Hannah data nace akan zataje itama sbd ta tabbatarda Marshal zaije can daga Hawaii.

Kwana biyu Ana fama da jikin Hanifan ansamu ta ‘dan ji sauki ta warware Haka suka lallaba suka tafi tareda Dr sa’id din Wanda yake likitanta.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 18_*
Koda jirginsu ya sauka Ana ruwan sama Dan hakan Isma’eel ne yazo da mota ya daukesu Kai tsaye suka wuce _copperhill mountain Lodge_ inda marshal yake zama matuqar Yana Sweden din,Koda suka Isa room cards din dakunansu suka karba suka wuce
Dr sa’id gabaki daya ba’a Lodge din ya saukaba nasa masaukin ya nufa Wanda yasaba zama Dan shima Yana Dan zuwa qasar akai akai Dan Haka dakin Isma’eel da matarsa Yana farkon floor din saina Hannah agaba tukuna na Naj acan qarshe Wanda dakin Marshal ne Isma’eel yabata card din batareda yayi tunanin komaiba tunda dai yasan zasu iya zama daki daya.

Dama sai asuba suka sauka qasar Dan Haka Koda suka shiga dakunansu har qarfe Tara na safe ta kusa Dan Haka wanka ajiye luggage dinta tayi cikin wdrp ta tube kayan jikinta ta jefe laundry ta nufi toilet ta sakarwa kanta ruwan zafi tana lumshe ido sbd Jin dadin saukansu a jikinta ta gasa koina nata tafito daureda towel qarami tana goge jikinta sai alokacin take qarewa dakin kallo da irin tsarinsa daya burgeta Dan kuwa komai haduwarsa a tsarance da natse take musamman komai na dakin is white ta nufi wrdrp ta fiddo qaramar akwatinta ta fiddo kayan shafarta ta ajiye gaban mirror ta dauki wasu kayan bacci riga da wando ta dawo gaban mirror sama sama ta shafa body mist ta saka kayan baccin ta dauko wayarta ta duba alkiblan sallah ta Dora jallabiya kan kayanta tayi sallolin da ake Binsu Ana idarwa ta cire jallabiyar ta maida ta Haye gado tashige bargo sbd wani irin bacci da gajiya takeji gabaki daya jikinta ba qarfi,
Wani irin bacci me Dadi da nauyine ya dauketa cikin nutsuwa gashi har lokacin ruwan saman akeyi Bata farkaba sai qarfe biyu da mintuna shima knocking kofan da akeyine ya tada ita ta bude idanuwa ahankali tareda tashi zaune ahankali taji Ana cewa”

Ur Lunch is here Sir.

Saukowa gadon tayi ahankali ta zura slippers din dake dakin masu taushi ta nufi kofar tana Dan mamakin Jin Sir din data ambaya ta bude tana amsa gaisuwar waitress din data kalleta da mamakin ganin mace sbd qarqashin sunan Deen Marshal akai booking dakunan Kuma a iya saninta wannan dinne nasa shigowa tayi ta nufa dining ta jere mata abincin tareda ruwa da drinks masu qarfi ma’ana energy drink Wanda Marshal din Kesha dama sune ake kawo Masa aduk lokacinda za’a kawo Masa abinci indai Yana lodge din ta juya ta fice bayan tagama tunda Babu ruwanta da sanin waye Naj Kuma Ina me dakin.

Brush tayo tafito ta nema wayarta ta zare layinta ta saka layin qasar da tun kafin su iso Isma’eel ya siya Mata dama itace kawai batadashi Amma dukkaninsu suna dashi har Hannah wadda dama tasaba yawon qasashenta da qawayenta ita dinma ta Dan fita wasu qasashen Amma ba dayawaba gurin aikinta da yawon ganin likitocinda Hanifa keyi tun kafin tayi aure Dan Haka itama sosai take waye da harkan qasashen na waje musamman ma dayake tafisu zama a miskilancen dayake bayyanarda ajinta sai hakan yake fin yimata kyau da fitarda wayewarta.

Bayan ta saka layin yahau massage din Isma’eel yashigo Mata akan shida Hanifa sun fita zuwa wani gurin Hannah ma ta fita zuwa gurin friends dinta saisun dawo.

No hajjo tafara Kira suka Dan Jima Suna magana kafin takira ummanta suna Gama magna ta ajiye wayar ta nufa dining din ta zauna tana duba abincin
duka ba taste dinta bane Amma Haka ta Dan ci kadan Tasha drink dinda Bata tsaya dubawaba sosai tafin ta miqe tabar gurin tana duba chats a wayarta tsawon mintuna saiga room service suka sake gyare gurin aka fitarda kayan abincin sauran drinks din Kuma aka saka a fridge bayan fitarta ta rufe dakin tashiga wanka.

Sai dare Su Hanifa suka dawo Hannah kuwa da alama acan zata kwana
Koda suka dawo tuni ta kwanta saidai sukai Saida safe a waya sbd ciwon Mara dake damunta yanda Hanifa taji muryarta yasata zuwa dakin ta dubata saidai ta Dan daure ta nuna Mata ba wani Abu kawai Dan ciwon marane hakanan Hanifa ta tafi tabarta saidai ta tafi da room card din dakin sbd zuwa dubata idan taji shiru da yawa ta fice ta tafi bayan ta rufo Mata dakin,tun yamma yafara yimata ahankali yanzu yafara yimata tsanani Dan kuwa sosai take jinsa gashi tasan lokacin period dinta baiyiba da sauran lokaci.

Daqyar tasake lallabawa tayi wanka da ruwan zafi sosai ta ‘dan gasa Marar ta fito ko miqewa tsaye Bata iyayi sosai ta daddafa daqyar ta Isa gadon ko kayan bacci Bata iya sakawaba ta fada gadon ta dunqunqune cikin duvet cover tana rufe idanuwanta dasukai ciki ciki sbd azaba.

Qarfe goma Sha biyu jirginsa ya sauka Bai tsaya jiran Azo daukansa ba yadauka taxi ya qaraso Lodge din tun daga reception aka sanar dashi katin dakinsa Mr Isma’eel Khamis ya karba Baice komaiba ya wuce ma’aikatan gurin na biyedashi da luggage dinsa.

Bangaren dasuke Yana daya daga cikin kebantaccen bangare da ba’a aje mutane da yawa yawanci ma sai couples sbd rashin hayaniya da tsaruwarsa Kai tsaye wayarsa ya fidda yayiwa Isma’eel text cewan gashinan hanyar dakinsu ya miqo Masa katin dakinsa.

Cikin sa’a katin na hannun Hanifa Dan Haka Kai tsaye ya karba ya fito suka hade a Hanya ya miqa Masa Yana Masa barka da isowa suka rabu ya wuce dakin duk da baya tareda gajiya sbd Babu wani nisa sosai daga can din zuwa Nan.

Kai tsaye bude dakin yayi da katin ya shige tareda karban luggage dinsa ya qarasa shigewa dashi ya rufe kofar Yana nufar Yana kunna wuta Mara haske ya aje wayarsa Yana Dan motsa fuskarsa sbd qamshin dayake gauraye da dakin na turarent possess dakuma humrah me sanyin qamshi.

Yamutsa fuska yayi Yana nufar fridge ya bude yaga har drinks dinsa ansaka a fridge din ya dauka daya ya bude ya shanye ya juya yabar gurin ya nufa toilet yashige tareda tubewa ya sakarwa kansa ruwan zafi yayi wanka da brush ya fito duk lokacin Bai lurada fararen panties din dake shanye a hanger na toilet din ba yafito daure da towel ya shirya cikin fararen _Fred Segal pyjamas_ ya kashe wayarsa gabaki daya ya nufi gadon ya Haye Yana yaye bargon zai shiga Yana ayyanawa aransa tabbas Hanifa tashigo dakinsa shiyasa yake ganin komai ba daidaiba da safe zasu sauya Masa kusan komai na dakin qamshin Nan na matane Yana Masa yawa.

Jin jikinsa yayi ya hadu Dana mutum da sauri ya tashi zaune Yana Dan yaye duvet din yakai hannu kan side lamp ya kunna Yana waiwayowa idanuwansa suka sauka Kan fararen cinyoyinta dasuke bayyane towel din jikinta ya zame saura kadan yabar jikinta
Ya dauke idanuwansa Yana maidawa kan fuskarta dake fayau tana baccin wahala Wanda ya takeyi tana farkawa sbd tsananin azaba.

Saukowa yayi gadon Yana Dan rintse idanuwansa cikeda mamaki da takaici ya dauki wayarsa ya kunna Kai tsaye no Hanifa yayiwa text cewan waye a dakinsa.

Karanta massage din tayi yafi so biyar tana maimaitawa cikeda mamakin tambayar Wai waye a dakin nasa bayan yaga ko waye dinne.

Kai tsaye da takaicin tambayarsa ta rubuta masa “itadin daice wadda kagani ko kanada wata matarne bayan ita?”

Kashe wayar yayi ganin abindata rubuto Yana sake boyayyan tsaki ya shafa sumar kansa sbd baya iya kwanciya da wani a gado daya baimasan ta Yaya zai kwanta da ita a gadon.

Hawa yayi gadon ya kwanta gefe daya tareda rufeta sbd jikinta dake bayyane ga towel din ta saman kirjinma yakusa zamewa Yana rufeta ya kashe wutar dakin ya kwanta Yana rufe ido dandai shi bazai iya kwanciya a sofa ba yabar Mata gadon.

Cikin bacci yaji mutum cikin jikinsa gabansu daya tana fidda wani irin numfashi me zafi da ‘duminsa yake sauka cikin wuyansa yanasashi Jin wani iri ya bude idanuwansa ahankali ya zubawa fuskarta dake cikin wuyansa tana Nishi ya daga hannunsa ahankali yakai jikinta zai janyeta hannuwan ya sauka Kan shafaffen cikinta dake Mata ciwon zuwa mararta take tasaki wani irin numfashi da ajiyar zuciya wadda tasashi janye hannun Yana rufe ido sbd dumin numfashinta Yana Masa wani iri.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 19_*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*********************
Juyowa yayi Yakuma kallonta da idanuwansa da bacci yagama sakinsu yafara karantar yanayinta ahankali sai ya lura da kaman tanada matsalane Dan kuwa ko ayanda yasanta sama sama yasan bazata shiga jikinsa a hayyacinta ba,
Qaramin numfashi da yasaki Yana waiwayawa ya duba agogo yaga Daren yaraba sosai Babu ta yanda zai iya Kiran Hanifa yanzu ya lumshe idanuwansa Yana Kuma kallonta kafin Kai tsaye ya saka hannuwansa biyu ya juyota daidai Yana kallon fuskarta dake Dan tsatsafo zufa duk da sanyin aircon daya Kama dakin.
Baisan ya zaiyiba tunda ba Saba irin wainnan abubuwan yayiba aikine kawai su Hanifa suka hadosa dashi kawo Masa ita dakinsa gabaki daya.

Shafa fuskarta yayi tareda bude bakinsa ahankali cikin nutsuwa akaro na farko daya Kira sunanta.
Bata motsaba sbd wani irin rawa da jikinta keyi zufa na keto Mata
Ganin irin zufan yasa ya yaye musu bargon gabaki daya Yana dauke idanuwansa akan jikinta dake bayyane yakai hannu Yana janyota jikinsa Yana sake Kiran sunanta wannan karon da ‘dan sauti saidai har lokacin Babu wani alamar tasan wayema yake tareda ita bare kiransa.
Dayaga baisan meyake faruwaba Kuma gadai zafi tanaji tunda tana zufa shikuma bazai iya kallonta ahaka ba Kaya jikintaba sai towel Wanda shida Babu duk daya sai kawai ya kwanta ya rufe jikinta da nasa ta hanyar sanyata cikin jikinsa ahankali yaji dumin jikinta na shigewa jikinsa.

Qamshintane yafi komai takura Masa sbd qamshine daya riga yagama kame jikinta tun Yana Dan rufe ido Yana budewa yanajin wani irin rashin sukuni ahakan Kuma baccin dole me daukeda ciwon Kai me qarfi ya daukesa Dan kuwa a rayuwarsa kaf baya iya tuna ranar dayayi baccin takura irin wannan Mai cikeda rashin sukuni na komaima.

Qarfe bakwai da arbain ta bude idanuwanta dasukai Mata mugun nauyi da kanta ma dayake Sara Mata sosai ta lumshe idanuwanta dasuka Dan kumbura tasake budewa tareda juyawa gefen gadon Dan lalubo wayarta taga karfe nawa gabaki daya batada qarfin jikin daqyar ta daga hannun tana lalubowa ko Ina taji bataji wayarba saita sauke numfashi Mara karfi tana tashi zaune ahankali ta zauna dakyau tsakiyar gadon tana bude idanuwanta da kyau suka sauka kan mutum zaune akan sofa Yana aiki da laptop a gabansa jikinsa sanyeda kayan geaming daya dawo jikinsa dake daukan ido duk kusan a bayyane sbd rigar jikinsa batada hannu hakama wandon jikinsa three quarter ne sai slippers din Gucci masu taushi a qafarsa gabaki daya hankalinsa nakan abinda yakeyi duk da yaji tashin nata Amma Bai dagoba abindake gabansa kawai yakeyi.

Wani irin mummunan faduwar gaba da firgicine ya shigeta lokaci daya tasake kallonsa da idanuwanta dake neman sauyawa da shakkar Shidin ne kuwa kokuwa?
A firgice cikin tsananin tashin hankali ta kalli jikinta da Babu komai har towel dinma Babu Yana cikin gadon
Mummunan faduwa gabanta yayi tashiga wani irin tashin hankali da baqin cikin dayake neman danne numfashinta jikinta ya dauki rawa ta janyo rigar baccinta dake kan kujeran mirror hannuwanta duka rawa sukeyi ta saka rigar tareda lalubo towel din ta daura ta sauko gadon ko cikakken qarfin jiki batada taqaraso gabansa murya a shaqe da tsananin baqin ciki da tashin hankali tace”

Menene yafaru anan?
Menene kakeyi anan?
Yaushe kashigo?ta Yaya kashigo Nan?
When?How? and why????”” Ta qarasa da fushi me tsanani acikin muryarta sbd dukkanin inda tsoro da tashin hankali yake tashiga so take taji menene yafaru,fatanta komai Bai faruba a tsakaninsu Dan kuwa Babu abindatake iya tunawa sbd drink din bayan qarfi da yayi Mata daya Bata reaction har fitarda ita hayyacinta yayi she just can’t remember anything.

Dagowa yayi akaro na farko ya zuba Mata idanuwansa fuskarsa a matuqar hade ya qare Mata kallo saiyaga bazai iya tsayawa Mata mgna ba sbd yafara Mata kallon Bata hayyacinta ciwon Kai zata saka Masa kamar yanda ta sakawa kanta.

Ganin kallon rainin dayayi Mata ya dauke kansa baida niyyar tanka Mata hakan yasake Cinna Mata hauka Rai bace ta dauke laptop din dayake aikin ta dire gefe tana kallonsa da idanuwanta dasukai jajir Kai tsaye tace”

Banyi Kama da mahaukaciyaba inaga
Zan bude maka zance akan maganar aure dayake tsakaninmu Wanda haryanzu ban amince dashiba maganar Miji da Mata a tsakaninmu bakada wannan rights din akaina sbd bana maka kallon miji idan akwai abin dayake tsakaninmu shine Kai qanin Hanifa ne,
Bakada iko ko wani izini dazai baka Daman kusanci Dani can you leave this room now please tafada tana nuna Masa kofa idanuwanta na cikowa da hawaye sbd kukan datakeson fashewa dashi da tsoron ko wani abun yafaru.

Bai dago ya kalletaba ya miqe tsaye tareda damqar hannunta ya nufi kofa da ita tana fizgewa tana qwacewa ya tsaya jikin kofa da ita ya kalleta da fararen idanuwansa dake bayyanarda  bacin Rai qarara acikinsu ya saki hannunta ya bude Baki yace”

Babu abin daya faru anan Kuma Babu abin dazai faru din ko ba’a yanzuba sbd Babu abindake jikinki dazaisa wani abun yafaru idanma akwai ajikin naki to Ni yamun kadan so kidaina tunanin wani abun yafaru sbd bana sha’awan macenda bata iya banbance tsakanin namiji da muna maza Dan kuwa idan har wani abun zai faru bakinki bazai tambayaba da ajikinki Zaki tabbatar, mganar karban aure ko tashin karbansa wannan nine Zan sanar Dan a hannuna yake get that to your dumb Head and get out of my room now.

Ballewa hawayen idanuwanta sukai takasa daga ko qafarta sbd tsananin qunci da baqin cikin daya rufe zuciyarta kukan dakeson subuce matane yasata nufar toilet tashige tana rufo kofar da qarfi hawayenta suka qarasa ballewa suna gudu kan fuskarta.

Meya sametane?
Wace irin rayuwace wannan?
A rayuwarta kila Bata taba magana da fushiba irin yau din,
Ta Yaya za’a gane damuwarta da wannan auren,
Tayaya zasu gane Bata so da qaunar wannan auren har cikin zuciyarta.
Kuka sosai tayi idanuwanta dasuke a Dan kumbure suka qarasa kumburewar daqyar ta danne tayo wanka tareda alwala ta fito sanyeda kayan data shiga dasu tana fitowa ta dauki Kaya Takoma toilet din ta sanyo ta fito ta tayarda sallah har lokacin Yana zaune Yana aiki a laptop Babu alamar zai nuna dayasan da akwai wata halittar a dakin aikin kawai yakeyi Amma gabaki daya ransa har lokacin a bace yake Dan kuwa baitaba  saka bacin ran kowabama aransa Amma yau ta kunnasa ta yanda yakejin ko ganinta baya buqatan yi.

Tana idarwa ta miqe ta tattara kayanta ta maida cikin akwatinta duka ta janyo akawatin ta dauka wayarta da handbag ta nufi kofa ta bude ta fice.

Dakin Hannah ta nufa Kai tsaye tayi Knocking tana jiran abude har lokacin idanuwanta a Dan kumbure suke.
Jin shiru yasa ta fiddo wayarta takira Hannah din.

Hannah dake bacci taji ringing wayarta na tashi ahankali ta lalubo tareda bude ido tana dubawa taga sunan Naj tasaki wani tsokin takaicin Naj din kafin ta dauka cikin bacci tace”

Yes Naj menene?

Kintafi da room card dinkine ko Yana reception ko hannun Hanifa?

Tashi zaune Hannah tayi tana bude ido dakyau Dan kuwa idan har Naj na neman Mabudin dakinta kenan Marshal ya iso kaman yanda tasani they can’t share a room.
Cikin farin cikinta da Bata boyeba tace”

The card is here with me Amma kiban  10min koma kiban 6min ganinan zuwa na bude Miki you are most welcome Naj.

Kashe wayar tayi tana dirowa gadon dakin gidansu Sofia dasuka kwana ta dauki Jakarta da kayanta a hannu tareda daukan key din motar Sofia ta fice da sauri sauri gudu gudu tana Isa inda motar take tafada tareda tadawa taja da qarfi ta fice.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 20_*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************
Batason Kiran Hanifa sbd batason damunta tunda tana tareda Isma’eel shiyasa ta takura kanta tayi tsayuwar jiran Hannah bakin kofar dakin tanajin gabaki dayama gida takeson komawa Amma sbd bazata iya barin hanifar ba ayanzu datake buqatarta akusa da ita shine kawai zaisa ta tsaya Amma da baby abun dazai hanata barin qasar a ranar gabaki daya toshewar numfashi takeji a garin gabaki daya.

Da kayan bacci riga da wando sai jacket data doro a sama jikin Hannah Babu kunya ta iso lodge din tayi parking tareda fitowa taqarasa reception ta wuce da sauri sauri
Tana qarasowa tahau bude dakin tana cewa”

Sorry nabarki kina jira,shiga
Shigo ki aje kayanki Zaki iya zama daganan har mu bar Sweden zanyi farin cikin zama taredake.

Bata cewa Hannah din komaiba ta shiga ta aje kayanta tareda nufar toilet tashige sbd tasan zatai matuqar wahala zama da Hannah sbd banbancin halayensu da rashin Jin juna dasukeyi,
Sam Hannah batai mataba sbd yanayin rawar kanta da iyayi dama komaima ita gabaki dayama Hannah is suffocating her Amma yanxu Haka zata zauna da ita kamema takeji akanta.

Wanka tayo tafito ta saka doguwar riga Mara nauyi ta zauna kan sofa tana shan tea me zafi ahankali tanajin Hannah dake cikin farin ciki shigewa toilet wanka,tana gamawa ta Haye gado ta kwanta ta rufa tana rufe ido.

Qarfe biyu zasuje asibiti Dan Haka biyu saura ta tashi tayi alwala tayi sallah ta shirya cikin _Pal zileri drawstring_ straight skirt navy blue da milk long sleeves sai milk scarf data daura ta fito daga ita sai wayarta a hannunta daidai Hanifa na qarasowa dakin zatai knocking suka kalli juna tana mamakin ganinta dakin Hannah ta waiwaya ta kalli hanyar kofar dakin Marshal tasake dawo da kallonta kan Naj din Kai tsaye tace”

Me kikeyi Anan Naj?

Kallonta Naj tayi Kai tsaye kafin ta Dan dauke tana cewa”

Nan nadawo.

Kallon mamaki Hanifa tabita dashi kafin ta kalli Hannah dake shiryawa cikin Adonta na daukan hankali ta Kama hannun Naj din tajata suka fita gabaki daya zuwa gurin motocin da zasu fita dasu ta saketa suna fuskantar juna cikin fara gajiya da halin Naj din tace”

Naj banso shiga cikin zancenku ba sbd ku duka biyun Ina sonku Ina qaunarku banason dayanku yashiga takura ko damuwa shiyasa nake dakatar da kaina ga fada Miki gskia duba da yanda akai Miki ba daidaiba ta hanyar daura Miki aure da Wanda kike ganin kin girma Amma Naga kinason yiwa kanki illa Dan kuwa shekarunki sun tashi sunbi iska daga lokacinda aka shafa fatihar aurenki da Marshal Dan kuwa yanzu shine me ikonki,
Duk ba wannan ba meyesa Zaki ringa bawa Hannah damar dazata ringa qara samun kusanci da mijinki bayan kinsan zata iya Jan raayinsa tunda ita mace ce Kuma itama din kyakkyawace kina ganin Jin kan Nan naki bazai damekiba agaba idan Baki dakata wannan shirmenba koni da hajjo bazamu iya taimaka Miki ba agurin Wanda kike rainawar sbd namijine wani lokacin Kaine zaka sauke Kai kabisa Amma bazaki gane hakan yanzuba sbd Baki Gama sanin meye auren ba kokuma nace kinsani zuciya ta hanaki fahimta.

Da yanayi na rashin me zatace ta kalli Hanifan idanuwanta akanta da damuwar meyene abin tattaunawa anan ta bude Baki zatai magana idanuwanta suka sauka kanshi Yana tahowa sanye cikin _Escada jeans_ blue da farar _Saint Lauren_ long sleeves sai _Shiels Emerald_ sunglasses dake fuskarsa daya Gama fito da fuskarsa dake wani irin daukan hankali Hannah ce taredashi tana sanye da jeans da Lois chiffon shirt sai qamshi take fitarwa suna tafe tana Masa firar outing dinta da friends dinta gabaki daya ta cika Masa kunne Amma baiyi yunqurin dakatar da itaba.

‘dauke idonta tayi akansu tana fasa maganar dazatai ta Dan dauke Kai,
Waiwayawa Hanifa tayi tagansu ta juyo ta kalli Naj din data dauke Kai cikin kawar da zancen dasuka fara tace”

Muje wainda ake Kira sun fito.

Isma’eel yafadawa su hadu a asibitin kawai ya nufa motar dayasa aka kawo Masa ya karba key yashiga Hannah tashige gaba ya tayar suka bar gurin batareda ko kallon inda suke yayiba har it’s har Hanifan Bai nuna yasan dasu dinba ya wucewarsa.

A motar Isma’eel su suka wuce motar shiru Babu Wanda yake magana sbd kowa da abindayake ransa musamman ita datake qara Jin duk garin yafita kanta.

Hanifa duk yanda takejin damuwarsu tata damuwar tafi damunta sbd tana cikin hali na tsananin damuwane Dan kuwa wannan karon idan akai Mata dashen baiyiba shikenan tasan batada Rabon zamtowa uwa da samun ‘dan kanta.

Koda suka Isa asibiti Dr sa’id na can already Dan Haka shine ya tarbesu suka wuce zuwa ganin Dr Kenneth din Wanda ke fifth floor.

A reception ta zauna jiransu sbd Hanifan ce kawai zata shiga sai Dr sa’id Isma’eel Yana kofar office din Yana jira.

Kusan awanni hudu suka shafe kafin suka fito suka sauko daidai isowar marshal dake waya cikin nutsuwa har lokacin Hannah na gefensa Kamar wasu sabbin aure.

Dauke kanta tayi daga kansu tana kallon Hanifa cikin kulawa ta riqo hannunta tana cewa”

Are you ok sweetie?

Kallonta Hanifa tayi da idanuwanta dasukai jajir sai kawai takasa magana ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciya sbd batason yin kuka tana neman qwarin gwiwane.

Kamo hannunta Isma’eel yayi Yana shafa kanta cikeda kulawa da bayyanarda tsananin Sonta dayake cikin zuciyarsa yace”

Hanifa Inshallah komai zaitafi lafiya
Zaki dauka cikin lafiya ki haihu lafiya
Duk gamunan muna taredake I am here,Marshal is here, Naj is here too and Dr sa’id ma Yana Nan inshallah Zaki samu lafiya da abin dakikeso.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa”

Thank you Zawj.

Murmushi yayi Yana cewa”

Muje to kina buqatan hutawa.

Kallon Marshal yayi Yana cewa”

Gobe za’a fara processing aikin.

Lodge suka koma tun a hanya Naj din ke Dan sake kwantarwa da Hanifan hankali Koda suka Isa daki ta wuce ta fada kan gado tana sauke nannauyan numfashi kanta na Dan sarawa sai daga baya ta samu ta lallaba tayi sallar la’asar Bata wani jimaba akai magriba tayi sai alokacin tasa aka kawo Mata abinci taci ta koshi iya cikinta ta tashi tayi sallar ishai tayo wanka tayi Shirin bacci ta kwanta har lokacin Hannah Bata dawoba.
Washe garima kusan a asibiti suka wuni sai dare suka dawo Banda hanifar wadda akai admitting sbd aikin.

Kwana biyu suna yawon asibiti kafin akai aikin nasara suna fatar cikin ya tabbata Dan Haka Koda aka sallamota suka dawo sabuwar kulawa take samu daga kan dukkaninsu Banda Marshal Wanda kobai nuna ba tasan yafi kowa jinta cikin ransa takumasan sbd Naj ne yake nesanta kansa dasu baya buqatar abin dazai hadasa guri daya da Naj din.

Ta warware gabaki daya Dr sa’id harya koma shi tuni su kadai suka rage Marshal dinma yariga yayi booking ticket na tafiya washe gari Dan Haka ranar tareda Hanifan suka fita dagashi sai ita Basu dawoba sai dare bayan ishai lokacin Naj na tareda Isma’eel a bakin pool din gurin suna fira Yana sake tausarta akan maganar auren ta Dan kallesa tana maida kallonta kan ruwan dake gabansu a natse tace”

Isma’eel banajin aurena aurene Kamar kowane sure sbd bana hango ranarda zai zama aure kamar yanda akai fata har aka hadashi.

Rufe idanu tayi ta bude zuciyarta na Shiga qunci daya bayyana cikin sautin muryarta tace”

Andai yimin fata fa matsin aure Kuma nayi saidai banajin daga sunan auren zai wuce ko Ina har abada bazan daina yiwa Wanda ake Kira da mijin kallon mijin ba……

Daga bayansu Hanifa tace”

Zawj mundawo.

Juyowa sukai gabaki dayansu ita nata idon akansa suka fara sauka Yana sanye da kayan dasuka fitarda samartakarsa sosai sai cika ido dayakewa mutane da kwarjininsa da ingarman jikinsa ta dauke Kai tana juyawa ahankali ya tako ya Isa har inda take ya durqusa ya dauketa gabaki dayanta
Ta zabura da qarfi tana qwacewa saidai riqon gaske yayi Mata a kirjinsa me Fadi ya dago ya kalli Hanifa da Isma’eel yace”

Wannan qawar Taki inason nuna Mata wani Abu ko zata Dan dawo daga shock da tarin shirmen samarinta na dah suka Bata.

Zillewa take neman yi cikin qarfi da baqin ciki Tama kasa kallon inda Hanifa take sbd tsananin baqin ciki da kunya take idanuwanta sukai jajir
Isma’eel ya kallesa Yana cewa”

Saida safe Naj Zan fadawa Hannah karta jiraki ta rufe kofa.

Akaro na farko da Marshal din yayi murmushin dayafi Kama Dana mugunta ya juya ya wuce da ita tana dukan kirjinsa cikin tsana da takaici.

Rufe dakin yayi Bai direta koina sai tsakiyar lafiyayyan gadonsa Yana kallon kyakkyawar fuskarta data koma ja take sbd tashin hankali da baqin ciki hakan yasake kunnasa ya ranqwafo yayi Mata rumfa da kirjinsa daya rufeta gabaki daya qamshinsa na shiga hancinta direct ta rintse ido da qarfi tana turesa iya karfinta Amma Kamar garu take turawa sbd ko gezau baiyiba saima matso da kyakkyawar fuskarsa yayi ahankali ya cusa cikin wuyanta ya shaqi qamshinta daya fara Dan sabawa da hancinsa tsawon kwanakin sbd gabaki daya koina dakinsa qamshinta yakeyi har gadon da bargon da komaiba kusan ko ina yasa kansa a dakin qamshinta yakeyi daqyar yake iya shaqar numfashi batareda qamshintaba tun ranar dayazo Sweden din Dan Haka ya manna hancinsa kan fatar wuyanta dake bayyane Ya shaqa qamshin Yana rintse fararen idanuwansa duk da bayajin komai game da ita Amma hancinsa sun Dan Saba da qamshin
Ya dago fuskarsa ahankali Yana kallon fuskarta dake cikeda tsanarsa yakai hannu ahankali ya fincike botiran gaban rigarta gabaki dayansu farar lace foam bra din dake jikinta ta bayyana kan fuskarsa ya kalli kirjin nata zuwa shafaffen cikinta dashima yake bayyane ya daga hannunsa Yana kallon fuskarta da hawayen baqin ciki suka fara gangarowa ya Dora hanun kan cikinta yayi wata irin shafawa data Sanya su biyun kusan dauke wuta sbd abune dabai taba faruwa da kowannensuba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 21_*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**********
Bude idanuwanta dasukai ja tayi ta yunqura kanta tareda daga hannuwanta takai zata turasa ya Dora hannunsa kan hannunta daya sauka Kan qirjinsa yana zuba Mata idanuwansa Kan fuskarta yakai bakinsa Kan kunnenta Saida ya sakar Mata numfashi me dumi dayasa tsikar jikinta suka tashi gabaki yace”

Meyasa kike yawan nanata auren Nan ba aure bane?
Idan bakijisa bane ajikinki daga yau Zaki ringa jinsa tunda kina saurine da alama.

Bude idanuwanta tayi dake tsiyayar hawayen baqin ciki ta kallesa cikin ido shima ya zuba Mata nasa idon Yana dauke gira daya yakai hannunsa Kai tsaye Kan bra Dinta dakeda hook a gaba ya balle idanuwansa Kan fuskarta a razane tayi saurin ware idanuwanta cikin idonsa tana girgiza Kai da qarfi sbd yariga yayi Mata runfar dabazata iya tashiba ta rintse ido hawayenta na tsananta gudu ta bude Baki muryarta na rawa cikin fushi tace”

I hate you,I hate you for this…ka barni…this is wrong..

Kirjinta yaqarewa kallon tsaf kafin yakai hannu kan wuyanta Yana shafawa zuwa cikinta ya qarasa zare bra din ya jeho qasa Yana qarasa shigar da ita jikinsa gabaki daya ya kamo fuskarta yayiwa bakinta wani irin kallo kafin ya Dora nasa yana Bata wata irin tsotsa Yana cusa hannunsa daya cikin kirjinta
Take tahau mutsu mutsu tana jujjuyar dakai saidai Babu ta inda take samun motsawar musamman daya dago fuskarsa ahankali Yana kallonta ya dagata yayiwa rigarsa kyakkyawar yagar data rabata biyu daidai ya zare yayi wurgi da ita Yana kallon wandon jeans dake jikinta tafashe da kuka me sauti tana girgiza Kai idanuwan akan fuskarsa datai ja kadan alamar sha’awarsa ta ‘dan motsa tabbas idan tabari wani Abu yafaru tsakaninsu rayuwarta tagama lalacewa bazata iyaba ta rintse ido tana sake girgiza Kai zuwa lokacin ko qarfin jiki batada dazata iya turesa tunda Kota turan baya turuwar.

Mayarda kansa yayi tsakiyar kirjinta Yana shaqar qamshinta yasake dagota ya hade bakinsu yana kissing dinta yanda yaga dama hannuwansa na yawo cikin jikinta gabaki daya tsikan jikinta sun Gama tashi nako Ina Banda kukan baqin ciki tana dukan bayansa Babu abinda takeyi Haka yabi dukkanin jikinta ya hargitsa Mata shi kafin ya saketa tareda sauka gadon batareda ya waiwayo ba ya nufi toilet ya shige yabarta agurin kwance daga ita sai farin pant dinta dake jikinta da qyar ta daga hannunta takai tajawo duvet ta rufe jikinta idanuwanta jajir zuciyarta Kamar ta fashe Mata ta huta da abin datake ji cikinta.

Dunqunqunewa tayi tareda rungume jikinta datakejin Kamar har lokacin hannuwansa da bakinsa yawo sukeyi jikinta wasu sabbin hawayen suka gangaro Mata ta rintse ido tana dafe zuciyarta dake Mata tsananin zafi da ciwo.

Daure da milk towel a qugunsa yafito jikinsa na tsiyayar ruwa alamar wanka yayi ko inda take bai kalla ba ya nufi mirror Yana goge jikinsa yagama yashafa egg yolk cream kadan ya fesa spray na _Creed Aventus_ ya shirya cikin black riga da wando na bacci guntaye ya dauko drink yasha ya dauki wayarsa da aka tarawa misscalls kusan guda Tara hadda na Hannah data dawo bataga Naj ba tana kuma tunanin Babu inda Naj zata fita tunda ita ba mutum bace me karauniya da rawar qafa.
Zaunawa yayi Yana waya da wani Marshal din gurin aikinsa cikin turancinsa dayafi Kama bakinsa dakayau akan yarensa hankali kwance.
Baibi takan misscalls din Hannah ba ya kashe wayar ya nufi gadon Yana zare slippers din qafarsa ya Haye yayi kwanciyarsa.

Saidata tabbatarda yayi bacci ta laluba rigarta a qasa ta rufe jikinta ta nufi wadon jeans dinta dake yashe shima ta dauka ta saka ko bra Dinta Bata tsaya nemaba ta zura rigarta ta dauki scarf dinta tafice dakin tana kamma jikinta da har lokacin tsikar jikinta Yi take tana tashi.

Bugu daya tayiwa dakin Hannah data kasa kwanciya ta taso da sauri ta bude Mata tana Mata kallon qurulla tana cewa”

Ina Kika tafi?
Daga Ina Kika dawo?
I mean tuntuni kina Ina?dare fa yayi sosai yanzu.

Batada lokacin sauraro ko kula Hannan zafi da radadi jiki da zuciyarta ke Mata Kai tsaye toilet ta nufa tayo wanka ta fito rigar bacci kawai ta saka ta hau gado ta kwanta tareda rufe ido tana sauke numfashi.

Kasa kwanciya Hannah tayi ta zauna kan sofa tareda rafka uban taguma tanajin itama tata zuciyar na daukan radadin rashin sanin taqamaimai inda Naj take tun farkon Daren fatarta dai ya tabbata Naj din taba gurin Marshal,ita gabaki dayama taji haquri nta na jiransa yagama qarewa kuka zata fasawa Dad Alfa adubi Allah da girmansa a daura musu aure sbd Jin take Kamar Naj zata zama barazana agareta gabaki daya Bata qaunar kusanci a tsakaninsu ko yayane.

Washe gari qarfe goma jirginsa zai tashi Dan Haka qarfe tara da rabi yafito a shirye cikin _Roberto cavalli_ straight trouser and shirt brown fuskarsa sanye da _Prada_ sunglasses black hannunsa sanye cikin aljihun wandonsa Hanifa dake tsaye tareda Isma’eel sai Hannah dake zuba qamshi Dan tuni tayi wanka suna jiran fitowarsa ta kallesa cikin kulawa da kewarsa da zatayi tace”

Marshal kamun alqawarin zuwa kodan baby right?

Kallonta yayi ya sakar Mata murmushinsa dakewa Hannah wuyar gani Yana gyada Mata Kai ahankali kafin ya Dan waiwayo ya kalli Hannah datake Masa kallon tsananin so da burgewa harma da sha’awa ya kalli kofar dakinta ahankali yace”

Tana ciki?

Bata gama fahimtar me yafadaba ya nufi dakin yayi knocking Kai tsaye duk suna tsaye suna kallonsa.

Ahankali ta tashi daga zaunen datake kan kujera idanuwanta da fuskarta gabaki daya a kumbure ta nufi kofar ta bude sbd tunanin ko hannace tadawo Dan Bata fita da card din dakinba.

Cikin idanuwansa nata idanuwan suka sauka ta dauke Kai take fuskarta na sauya zuwa wani mummunan yanayi ta juya zatabar gurin ya riqo hannunta Kai tsaye tareda Ciro abindake aljihunsa ya saka Mata a tafin hannu ta kalla da sauri ganin bra Dinta ta dago a fusace wata fitinanniyar kunyar Hanifa dake kallonsu tana dabaibayeta ta qwace hannunta tareda juyawa ciki a fusace.

Juyawa yayi baice komaiba shima yabar gurin ya nufi gurin Isma’eel dake jiransa a mota Hanifa da mamaki da wani boyayyan murmushi yagama kamata tabi bayansa tana waiwayan dakin
Hannah kuwa kusan mutuwar tsaye tayi ganin fitowar bra din mace daga aljihun Marshal dinta daqyar ta iya daga qafa tabi bayansu suka nufi airport kaisa.

Bayan dawowarsu Babu Wanda yaga wani sakin fuska daga Naj din sbd sosai ta fuske Dan Bata buqatar wani magana dazai danganci JALAL din Dan Haka Bata Bari Koda Wasa Hanifa Tai Mata wata maganar ba ahaka suka lallaba suka qarasa kwanakinsu bayan anyi gwaji an tabbatarda cikin ya tabbata.

Da farin cikin nasarar da aka samu suka dawo gida inda aketa murnar cikin Hanifan musamman umma da duk maraice da abinda zata aikowa Hanifa hakama Dadah,
Ta bangaren Dad Alfa ma Yana tsananin farin ciki da cikin uwa uba hajjo data qwallafawa ‘yayan da Marsha Rai shida yake namiji sai gashi na Hanifan zasu fara samuwa ta dauki buri da qauna tasakawa cikin itama duk da hannuwansu a gabansu suke da cikin sbd yanayin lafiyar Hanifan suna fatar dai Allah yasa adace wannan karon.
##MAMUH#

 

_*DM 22*_

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*****************
Ba sosai take jimawaba yanzu a office sbd yanayin Hanifa da hankalinta yafi kwanciya idan taga batayin nesa sosai da ita Dan kwanakin tana Dan samun laulayi masu wahala dan yanzu cikin Yana wata na hudu harya fara Dan tasawa Ana hangensa.

Yau Bata samu damar zuwa office ba sbd yanayi na ciwon Mara data tashi dashi na period dayazo Mata dama Kuma tana ciwon Mara sosai idan zatayi period duk wata saidai wannan karon ciwon yafi tsananta Mata Wanda takejin Kamar ba yanda tasaba bane Dan Haka da yamma hajjo da kanta takira Dr sa’id yazo ya dubata sbd ganin duk Naj din tayi wani iri Babu qarfi sosai ajikinta.

Herbal tea hajjo tasa ruqayyat ta dafo Mata da Zuma kadan aka kawo Mata ta gyara zamanta daga takuren datake dunqule Kan kujerar kusada hajjon ta karba tana kallon cup din ahankali kafin takai bakinta tafara kurba tana Dan rufe ido sbd ‘dandanon da baya Mata ko kadan a Baki ta kalla Hanifa dake Mata sannu tace”

Bani tissue akusa dake.

Hannu Hanifa takai ta zaro Mata tissues din dake gefenta na ‘dan Tara  yawu datakeyi sbd cikinta ta miqawa Naj din cikin kulawa tana cewa”

Sorry sweetie.

Gyada Mata Kai Naj din tayi tana dan lumshe idanu sbd saukar herbal tea din da zafinsa cikin cikinta yasa taji tana Dan Jin Kamar ciwon na Dan fadawa ta goge bakinta da tissue tana cigaba da kurban tea din harta shanye ta ajiye cup din hajjo na Mata sannu cikin kulawa.

Ahankali ahankali ta danji ciwon Yana fadawa Yana ragewa hartaji taji Dan saukinsa ba laifi sai alokacin ta miqe ahankali ta nufi dakinta Wanda take ita kadai yanzu aciki bayan an sauya Mata komai na dakin zuwa sabin furnitures dasukafi wainda aka sauya komai na dakin fari kamar yanda Hanifa ta bada zabin kalar sbd jalal ma yawanci komai na part dinsa farine,
Raba daki sukai da Hanifa sbd yanayin laulayin cikin hahifan dayakeda tsanani da zabe zabe Dan kuwa gabaki daya batason qamshin turare Wanda Naj Kuma ko zama tayi kusa dakai saita bar maka qamshinta me sanyi da dadi Wanda kamarma yariga yakama jikinta,
Hakama hahifa yawu takeyi wnda itakuma Naj takurane gareta,
Sai qamshin toilet din dakin nasu shower gels dasu feminine wash da bataso Wanda Suma Naj ke amfani dasu shiyasa Hanifan ta tarkata takoma dayan dakin dake palon aka sauya Mata wasu abubuwan dakin wainda bataso da sabbi.

Wanka tasamu tayi da ruwa masu zafi sosai tasake Jin Dan Jin qarfin jikin ta shirya cikin riga da wando masu Fadi sosai marasa nauyi ta saka hula ta Dan kwanta Dan samun bacci Bata Farkaba Saida Dr sa’id yazo aka tadota tafito sanyeda mayafi me Dan kauri rufe da jikinta ta qaraso palon tana tafiya cikin nutsuwa ahankali ta nufi kujera tana kokarin zama anty Amina na shigowa Nan suka zauna tare itama tana gaisawa da Dr sa’id din cikin sanayya da mutuntawa kafin ta miqe ta nufi dakin hajjo dake mutuniyar hirarta Dan suna qasan Kaka sosai da hajjon.

Kallonta Dr sa’id yayi kadan tareda Dan taqaitawa daga kallon Kai tsaye yace”

Menene matsalar?
Yaya kike jin ciwon Marar?

Numfashi ta Dan sauke tana dubansa a natse tace”

Wannan ne Karo na farko danake Jin wannan kalar ciwon duk da dai Ina ciwon Mara dama Amma wannan inajinsa dabam.

Kallonta yasakeyi Yana jeho Mata tambayoyi dabam dabam tana basa amsa tsawon lokaci Yana saurarenta ya hada amsoshinta Yana nazarinsu kafin ya dago Yana kallonta dason fada Mata abinda yake tunanin yasaka ciwon fin koyaushe wannan karon yace”

Ciwon mararki ya sauya yanayin tsarin ciwonsane ta hanyar tsananta da wani launin ciwom kamakon sha’awarki ta mace da aka motsa Wanda ke nuni da Baki taba ji ko aikata wani Abu daya taba motsa sha’awarki Wanda dakin Jima ahakan batareda an motsa Miki itaba kokuma yanayi yasa ta motsa da kanta Kika dauki shekaru ahaka kofofin sha’awan naki zasu rage qarfi matuqa kokuma suyi rauni sosai ta yanda zuwan sha’awan zaiyi Miki wuya.

Wani irin nauyi kanta ya dauka akaro na farko a rayuwarta da wata irin mummunan kunyar da Bata tabajiba ta Gama rufeta tako Ina har bazata iya kallonsaba saidai ta dago ahankali ta waiwayo duba Babu Wanda yafito bare yaji wannan mugun al’amarin daya sameta sukai ido biyu da Anty Amina data fito daga dakin hajjo takumaji abinda Dr sa’id din yafada Amma sbd ragewa Naj din nauyi da kunyar data hango tareda ita saita dauke Kai tana fuskewa tace”

Zan wuce nabarowa umma aikin hada sakon turarukan daza’a Kai mota gobe zuwa wani gari,Dr sa’id sai anjima.

Wucewa tayi batareda ta jira amsar Naj din ba sbd tasan bazata samu amsawar daga garetaba sbd halin datake ciki na tsananin Jin nauyi.

Babu wata kunya ko nauyin maganar dayaji sbd shi likita ne Babu kunya a tsakaninsa da patient dinsa Dan Haka Kai tsaye yabata shawaran ringa Shan ruwan dumi akai akai tareda bada shawaran zama guri daya da mijinta.

Tagane ma’anarsa ta cewa ta zauna guri daya da mijinta Dan Haka ko kallonsa bataiba tace”

Ngd Dr sa’id” tana miqewa daga zaunen shima ya miqe sukai sai anjima ya fice ita Kuma ta nufi daki tana dafa mararta datai nauyi.

Kwana biyu tagama period dinta ciwon Mara ya wuce Dan Haka ko maganar Dr sa’id Bata sake tunawaba bare sakawa arai taci gaba da sha’anoninta hankalinta kwance Babu tunani ko damuwar komai.

Yau da yamma sosai tadawo aiki sbd wani meeting da sukai me mahimmanci Wanda yasa take cikin farin ciki sosai sbd project ne dasuka Jima Suna buqatansa sai yanzu Allah yasa suka karbe.
Tana sanyo kan motarta cikin layin ta hangi qarin sojoji a kofar gidan Wanda yasa gabanta mummunan faduwa akaro na farko data tuna zai iya yiyuwa shine yadawo.
Sake faduwa gabanta yayi taji kaman tana neman shiga damuwa Amma dai ta danne ta qaraso suka bude Mata gate tashige da motarta tana amsa gaisuwar dasuke Mata daga ciki ta hanyar jinjina musu Kai da daga hannu.

Parking tayi tareda kashewa ta fito riqe da handbag dinta tasamu kanta da qin ko kallon daya daga cikin motocinsa dakeda alamar da ita akaje daukarsa airport ta dauke Kai ta nufi cikin gidan Kai tsaye tana nufar sashensu ma’ana na hajjo.

Da siririyar sallama ta shiga palon Kai tsaye tana kallon Hanifa dake zaune palon da tissue dinta ta yawu,
Gurinta ta qaraso tana sauke qaramin numfashi tace”

Maman baby Yaya??

Murmushin farin ciki Hanifa ta saki tana cewa”

Sannu da dawowa sirikar maman baby.

Naj din Bata tankata ba sbd yanzu tasaba da wannan neman fitinar da Hanifa keyi yanzu Dan Haka Kai tsaye daki ta nufa tana cewa”

Bari na tube nayi sallah yau na gaji sosai jikina na ciwo sosai.

Shigewa tayi daki tareda rufo kofar ta tana aje handbag dinta tareda Dan mayafin dake kanta ta tube tareda Kai kayan cikin laundry ta janyo towel ta daura tashige toilet.
Jin Ana Kiran sallar magriba yasa tafasa wankan tayo alwala tafito ta Sanya doguwar riga ta tafara yin sallolin Dake kanta saidata gamasu kafin ta miqe tana tubewa wayarta tahau ringing batabi ta kanta ba ta nufi toilet tashige.

Wanka tayo tafito ta shafa Mai kadan sai body mist da khumrah ta Sanya doguwar riga me qaramin hannu ta Sanya hular da Bata Gama rufe kanta gashin kanta dukaba tana kokarin fitowa taga lokacin sallar Isha yayi ta tsaya tayi abarta kafin ta dauko wayarta ta fito tana duba Kiran da aketa Mata tun dazu ga zallar mamakinta sai taga no din kamar ta santa ta sake dubawa taga 9misscalls Dan Haka sai mamakin Kiran ya Dan kamata ta nufi palon da hajjo da Hanifa ke zaune a dining ta nufa gurinsu Kai tsaye tana cewa”

Me maman baby keyi a dining hajjo itada baby bayason cin abinci a dining San……kasa qarasa maganarta tayi sakamakon Wanda idanuwanta suka Shiga cikin nasa Yana zaune kan kujerar da Bata hangosaba saidata iso gurin gabaki daya fararen idanuwansa masu rikitarwa a zubasu akanta jikinsa sanyeda jallabiya fara qal tana qyallin daya tabbatarda tsadarta,
Samun kanta tayi da kallon hajjo ahankali kafin ta maida kallonta kan Hanifa dake kallonta da murmushi a fuskarta sai kawai ta juya zatabar gurin Kai tsaye taji muryarsa a kame yace”

Dawo ki zauna.

Wani mamakin gaskene ya kamata dan ganin isar dayakeson nuna Wanda ita Bata basa wannan damar ba Dan Haka Bata dakataba ta wucewarta saidai ko taku uku bataiba taji an dauketa sama an qarasa cikin dakinta da ita tareda rufo kofar ya direta tareda manneta jikin bango Yana kallon fuskarta Yana Kuma controlling zuciyarsa dama kansa ya lumshe idanuwa ahankali yasake budesu akanta ya bude Baki cikin nutsuwa da kamewarsa yace”

Next time Kika Kuma Haka Zakiyi mamakin abinda Zan Miki agaban hajjo dama qawar Taki da kike Jin girma agabanta.

Qin kallonsa tayi tasa hakai hannu zata turesa daga jikinta dayake manne taji bazata iya Kai hannunta ajikinsa Dan kada wani tunanin ya shigesa ta dago ahankali ta kallesa da fararen idanuwanta shima idon nasa na kanta ya daga gira daya Yana jiran abin dazata fada ta Dan hade fuska tana dauke idonta daga cikin nasa murya a kame tace”

Bana buqatan sharadi ko doka akan waye Zan kula waye Zan gaida so can you just excuse me please.

Wani kallon daya tayar da tsikar jikinta batareda tasaniba yayi Mata kafin ya juya ya fice yabarta da qamshin turarensa daya maqale a kayanta takasa bin bayansa da kallo zuciyarta a Dan bace.

Kasa fitowa tayi lokacin saidata tabbatarda yabar sashen ta fito fuskarta a kame Dan kada Hanifa tasamu damar yimata wata magana
Tana fitowa cikinsu Babu Wanda yabi takanta taje dining din taciyo abinci kadan tagama ta taso tadawo gefen hajjo ta zauna tana Dan fuskewa dayin kallon wata Mexican drama the forbidden love A tashar telemundo suna fira.
Dai qarfe goma da arbain ta shige lokacin tuni hajjo ta shige daga ita sai Hanifa kusan tare suka shige dakunansu.
##MAMUH#

*DAN ALLAH ZAKU RINGAMUN UZURI KWANA BIYUN NAN ZUWA RANAR SATURDAY HIDAMAR BIKIN QANWATA MUKEYI ZANYI KOKARI NA RINGA BAKU INSHALLAH IDAN KUMA HIDIMA TA RIQENI ZAN RINGA SKIPPING HAR MUGAMA BIKIN RANAR SATURDAY INSHALLAH*
_NAGODE🙏_

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

 

*_DM 23_*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************
Kwanciya tayi bayan tagama duk abubuwan dazatayi ta rufe idanuwanta Nayan ta rufe Rabin jikinta da bargo me taushi takai hannu ta rage hasken wutar dakin sosai.
Tsowon mintuna hudu ta juya kwanciyarta tana sake rintse ido saidai har lokacin qamshinsa dake maqale a kayan jikinta Bai daina Shiga hancintaba Yana damunta gabaki daya ta rasa sukuninta ta tashi zaune tana sake Dan qaramin tsaki tareda dan yamutsa fuska tana sauka daga kan gadon ta nufi closet tana zame rigar jikinta ta jefa cikin wardrobe ta Ciro wasu riga da wando na bacci guntaye masu santsi ta saka tareda komawa ta kwanta tana lumshe ido bayan tayi adduar bacci.

Karar vibrating wayane ya tada ita da safen bayan tayi sallar asuba Takoma bacci,
Hannu takai ahankali tafara lalubo wayar tana bude idonuwanta dake tareda sauran bacci ta dago wayar ta duba taga no din jiyane da akaita kiranta da ita ta tashi zaune tana Dan sake sakewa daga baccin ta dauka Kiran cikin muryarta me taushi tace”

Hello,aslm alkm!

Shiru taji ba’ai magana ba cikin nutsuwa tasake cewa”

Hello.
Jin shiru ba magana yasata kashe wayar tareda ajiyewa tana kallon agogo taga qarfe Tara da minti uku.

Saukowa tayi Kan gadon tareda zura bedroom slippers dinta na dolce and Gabbana ta nufi toilet da sauri tafada wanka sbd tayi kafin ta Isa office tasan zatai latti.

Tana fitowa wanka tafara shiri cikin nutsuwa tashafa Mai da body mist kawai sai khumrah ta shirya cikin Givenchy floral chiffon skirt navy blue da milk blouse dinsa sai veil datai rolling ta fito daukeda wayarta da _D&G_ handbag dinta tafito Palo cikin sa’a duk suna dining suna breakfast daga hajjo sai Hanifa bandashi Dan Haka ta jiye handbag din a kujera tana qarasawa dining din cikin nutsuwa da sakewa tace”

Barka da safiya hajjo,
Ina kwana?

Taja kujera ta zauna tana kallon Hanifa dake kallonta cikin yabawa da samunta da ‘dan uwanta yayi amatsayin Mata tace”

Good morning maman baby, how’s our baby?

Murmushi Hanifa tasaki tana cewa”

Morning Auntie din baby.

Sama sama taci slice biyu na toasted bread da tea Mara shugar ta miqe tana cewa”

Hajjo zantafi saina dawo.

Adawo lafiya Amma yau ki dawo da wuri sbd kece Zaki ringa Mana dinner daga yau.

Murmushi tasake tana wucewa tace daga yau kuwa Zaki ringa cin dinner me Dadi hajjo,
Maman baby saina dawo,take care.

Fitowa tayi Kai tsaye ta nufi hanyar sashen Dad Alfa tana duba wayarta ta qarasa shiga da Hannah tafaracin Karo ta fito daga kicin fuskarta shafe koina da face scrub data shafa tana jiran yayi mintunan dazaiyi kafin tashiga wanka ta wanke Dan Marshal na gari Bata Sanya da qarin gyare gyare.

Kallon juna sukayi Naj tana ganinta ta Dan basarda fuska tana wucewa palon Dad Alfa din bayan ta amsa “morning” dinda Hannan Tai Mata cikin qure ido akanta sbd har yau tana shinshinowa kanta barazana daga Naj shiyasa take buqatan ayi gaggawan aurenta da Marshal Dan kuwa kyawu da kyan jiki tareda daukan idon Naj na daban ne duk da Bata wani qyale qyalen kwalliya Dan zata iya cewa Naj Bata taba shafa su jambakiba musamman masu shwty kala shiyasa komai nata yake unique and natural.

Tsoki hannan taja tana dauke Kai daga bin inda Naj ta shige da kallo ta nufa dakinta tana Jin tsanar Naj har Dan kuwa tashiga gabanta Kuma ta hanyar wainda Babu abinda zata iyayi bayan ta danne duk abin datakeji tabisu da yaqen dole tunda sune dolen Marshal dinta Dan tasan suna tsanarta to har abada bazai auretaba sbd yanda yakejinsu a ransa.

Fitowa Naj tayi bayan sungama magana da Dad din Dan ba gaisuwa kawai ta kawotaba harda magana akan ALFA’S company Wanda suke buqatan meeting dasu na saka hannunsa Dana Marshal akan wasu takardu na wani babban project da zasu fitar.

Fitowa tayi bayan sunyi magana Akan zasuzo ALFA’S din gobe gurin meeting din.

Tana fitowa daga sashen wayarta tasake daukan vibrating ta bude handbag dinta tareda Ciro wayar tana nufar motarta ta dauka tareda cewa”

Hello Aslm alkm!

Shiru takuma ji ta daga wayar daga kunnenta ta duba taga tana aiki ta Mayar kunnenta tana sake cewa”

Hello.

Mrs DEEN MARSHAL zankiraki dashi kokuwa Antyn JALALUDDEEN MARSHAL?
To koma dai wanne duk dayane basuda wani amfani tunda bashine dalilin dayasa nakiraba,
Akwai meeting qarfe goma da rabi gashi Banga alamar kintuna da hakan ba Dan bama iya jira idan lokaci yayi sbd munada iyalan da mukai auren soyayya bana cushe ko sadakaba dasuke jiran dawowarmu gidan Kan lokaci.

Cire wayar tayi daga kunnenta tareda kashewa Kai tsaye batareda tasamu damar cewa maganarsa ko kalma dayaba ta maida wayar jaka tana Shirin Shiga mota ta hangosa tsaye a balcony dinsa da mug a hannunsa Yana kurba ruwa masu dumi kadan da Zuma kadan aciki Wanda yake dabiarsa kullum Shan ruwan zafi masu Zuma kadan aciki.
Sanye yake da three quarter black da armless shirt sai slippers brown a qafarsa yafitone sbd fresh air ya shigesa Dan exercise din dayayi gabaki dayansa yasashi zufa shiyasa ya fito Yana Shan fresh air din jikinsa sai daukan ido yakeyi acikin baqaqen kayan dake jikinsa.

Dauke Kai tayi tana ciro keys na motarta ta bude ta shige tareda tada motar tana Danna horn aka bude Mata gate ta figeta ta fice daga gidan
Cigaba da abinda yakeyi yayi batareda yabi inda motar tata taficeba da ido sbd tun fitowarta daga sashen Dad Alfa idonsa ya sauka akanta ya qarewa kayan jikinta idon Yana tsayar da idonsa Kan Dan qaramin qugunta da skirt din jikinta ya zauna akai daga sama ya Dan rintse idonsa Yana daukesu daga kanta.
Ciki yakoma kawai sbd Jin iskar ta sauya zuwa wani yanayi mara Dadi.

Tana Isa office tayi parking ta fito ta nufi ciki Sarah na qasa tana jiran isowarta Dan Haka kai tsaye tan isowa gurin meeting din suka wuce San sama hanyar office din chairman wato Abbas.
Ko data Shiga shareholders din companyn duk sun iso ita zatai representing Alfas,Marshal da Dad Alfa.

Sai qarfe biyu da arbain suka fito meeting din Dan Haka Kai tsaye ta wuce office dinta Dan duba wasu takardu tanayi tana duba agogo sbd komawa gida da wuri tunda tasan aikin dake jiranta a gidan.

Sai qarfe uku da hamsin da uku tasamu kanta ta fito tana sanarda Sarah Dake biye da ita takardun dazata kaiwa Abbas ya duba kafin goben a zauna next meeting.

Wayartace tahau vibrating ta Ciro tana dubawa cikin Dan yamutsa fuska ta kashe wayar tareda maidawa cikin jaka tana kallon Sarah tace”

Ki tabbatarda kin kaiwa chairman duka takardun da ake buqatan ya duba kafin goben sbd bana buqatan wani aiki dazaisa yaringa kirana.

Ok Inshallah.

Fitowa tayi tafada motarta tabar companyn gabaki daya tana sake duba agogon hannunta.

Tana Isa bataga motorsaba a harabar gidan hakama sojojinsa Dan Haka tasawa ranta sun koma kenan ta fito ta Kai tsaye ta nufi sashensu.

Bakowa a Palo hajjo na sallar la’asar a dakinta, Hanifa Kuma na daki tana baccin yamma.

Dakinta ta nufa Kai tsaye saidata Dan zauna ta huta kafin ta tashi tasauya cikin doguwar rigar roba Mara nauyi tayo alwala tayi sallah kafin ta fito ta nufi dakin hajjo.

Sai yamma sosai ta fito ta Isa dakin Hanifa har lokacin bacci takeyi ta Dan tayarda ita cikin kulawa sbd maraice yayi ta kamata ta tashi ta nufi toilet kafin it’s ta nufi kicin Dan aikin abincin dare da itace yau zatayi.

Aiki suka hau yi itadasu ruqayyat masu kama Mata wasu ayyukan
Suka Dora tuwon semo da miyar waterleaf da nama kadan aciki sbd Jin daga bakinsu ruqayyat cewan idan Marshal na gari ba’a saka nama de yawa a abinci bayason nama sosai duk da dai bawai dansun fada tayiba itama Naman Bai wani dameta bane sosai hakama Hajjo itakuma sbd tsufa da manyanci.

Fruit salad tayi sbd Hanifa me juna biyu sai normal peach drink da black lemon tea me zuma data dafa Dan gidan gabaki daya kusan kowa mayen tea da zumane duk hajjo ce ta koyar dasu hakan tun suna qananu.

Basu Gama aikinba ta fito kicin sai bayan sallar magriba Dan Haka tana fitowa Kai tsaye ta nufi dakinta tafara tubewa gabaki daya ta nufi toilet yin wanka.
Ta Jima ciki kafin tafito daureda towel me girma blue tazo tafara saka doguwar riga tayi sallar magriba Da Isha kafin ta zare rigar ta zauna gaban madubi tashafa Mai kadan da spray din _Chanel_ ta sako doguwar riga Mara hannu ta fito daukeda wayarta lokacin hajjo da Hanifa tuni suka Isa dining Dan Haka Kai tsaye itama can ta nufa tana ajiye wayarta Kan kujerar palon.

Bata ganshiba Amma hancinta ya shaqo Mata qamshi _Tom Ford_ turarensa Dan Haka ta rage takun tahowar tata tana Dan Kai idanuwanta kujerar dayake zama a dining din wadda ba’a hangota sai ankawo cikin dining area din tana Kai idonta gurin tagansa zaune da tea gabansa Yana tiriri cikin Dan qaramin cup,Bai dagoba bare ya nuna yasan da zuwanta saidai ta tabbatarda yaji zuwan mutum agurin ta ‘dan dakata kadan zata koma saikuma ta fasa ta qaraso ahankali tana Dan fuskewa batareda itama ta kalla inda yakenba tace”

Sorry nabarku jirana.

Bata zaunaba ta zubawa hajjo abincin kafin tazubawa Hanifa fruit salad da tuwon Dan kadan sai ta zuba itama Dan kadan Takoma ta zauna sai alokacin ya kalleta baice komaiba ya qarasa Shan tea dinsa ya miqe ahankali hajjo ta kallesa tace”

Abincin fa?
Najma kiyi serving mijinki abinci yagama Shan tea din.

Wani irin kallo yayi Mata dayasata kusan sarqewa duk da Bata dagoba Amma tanajin kallon ajikinta ga rigar jikinta duk tasata Jin haushi da takaicin fitowa ahaka.

Da muryarsa me kamewa yace”

Takaimun abincin acan ba anan zanciba.

Yana Gama fadar Haka ya wuce yabar gurin batareda yasake kallon inda takeba yabarta da wani irin takaici,baqin ciki da takaicin rashin gane meyake nufi da “Takaimun”
Wa yake nufi da kalmar Dan Bata tunanin da ita yake Dan kuwa bataga ranarda hakan zata faruba takai kanta sashensa to tace tazo ubanme.

Ganin idon hajjo akanta dake nuni da zallar rashin Wasa na tayi abinda yace din yasata sarqewa tana sakin tari ahankali
Hanifa ta dauki ruwa ta miqa Mata ta a cewa”

Sorry sweetie,sannu bi ahankali kije kidawo tukuna saiki qarasa.

Da manyan idanuwanta ta dago ta kalli Hanifa wannan karon Kamar sun sauya da yin Dan ja da Kamar hawayen takaici dasuka Dan ciko aciki sbd halinda take Jin zuciyarta aciki na takaici saidai Kuma Bata hango ranarda zata iyayiwa hajjo gardamaba.

Hanifa dakanta ta miqe taje ta dauko Kaya ta hada Masa abincin da komai aciki tasaka a basket ta miqawa Naj din tana cewa”

Bari na dauko Miki wayarki da hijab.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 24_*
Da wani irin kallo tabi Hanifa dataje dauko Mata wayar da hijab din datace zuciyarta na wani irin tsallen takaici da bacin Rai.

Miqewa tsaye tayi tareda Dan shafa kirjinta dake Dan Mata zafin sarqewan datai tabar gurin qafafuwanta a harde
Hajjo dai kallon mamaki tabita dashi kafin ta miqe daukeda basket din Takoma Palo ta zauna tareda ajiye basket din Kan table tana jiran fitowan Naj din.

Mintuna shida zuwa bakwai ta Bata tana juyayin zuciyarta dake cikin bacin takaici gashi dai batada wani zabin bayan na zuwa Dole Amma sbd hajjo kawai.

Jin shiru yasa hajjo daga muryarta da babban sauti tace”

Naj kifito ba kafin abincin Nan ya rage zafi ki Kai masa sbd lokaci na tafiya bayacin abinci idan dare yayi sosai.

Fitowa tayi sanyeda hijab har qasa fuskarta a kame Babu wata alamar dazata baka damar sanin halinda zuciyarta ke ciki Kai tsaye ta dauki basket din ta fice batareda race komaiba,ko Hanifa dake cewa ga wayarki Bata tsaya tankawaba ta fice.

Kai tsaye hanyar sashensa ta nufa
‘daya daga cikin sojojinsa dasuke tsaron second gate na gidan Yana hangota ya taso da gudunsa Yana Mata barka da fitowa
Batareda ta kallesaba ta amsa yana qarasawa kofar Marshal din da saurinsa ya bude Mata kofar Kai tsaye ahankali sbd sanin Marshal bayaso Ana buga Masa kofa cikin sa’a Kuma dayake yasan zata kawo abincin Bai saka key a kofar ba.

Dan dakatawa tayi tana kallon kofar ahankali kafin ta Dan juyo ta kalla Wanda ya bude Mata kofar yayi saurin matsawa daga jikin kofar cikin girmamawa Yana cewa”

Good night ma’am.

Juyawa yayi yabar gurin ta rintse idanuwanta tana furzar da numfashi me dumi ta saka qafa Kai tsaye tashige tareda rufo kofar ta tsaya tana kallon inda zata ajiye abincin ta juyawarta sbd gabaki daya Babu numfashin da mutum zai shaqa Babu qamshin turarensa daya Gama kame koina na sashen nasa Dan Haka sanyin Aircon ma Dake tashi Kamar da qamshinsa yake feso mata.

Qarasowa ciki tayi ahankali ta nufi dining dinsa dake can kusada hanyar bedrooms dinsa tana kaiwa ta Dora basket din akai ta juyo sai ganin mutum tayi a bayanta tsaye daf da ita sanye da kayan bacci Yana kallonta da fararen idanuwansa dasuka sanyata dauke nata idon akansa tana matse fuska tareda juyar da Kai zata wuce
Taji yazura hannuwansa yariqo qugunta ya cirata duka ya nufi kujera ya zauna tareda zaunar da ita Kan cinyarsa Yana kallonta ahankali ya bude Baki yace”

Ina wayanki?

Kallonsa ta waiwayo tayi fuskarta a tsuke tana miqewa da qarfi daga jikin nasa
Ya dawo da ita ya zaunar Yana riqe qugunta da kyau cikin salon dayasata Jin zazzabi na neman kamata tasake miqewa Amma riqon da yayi Mata bazata iya kwacewa ba Dan Haka tasake juyowa ta kallesa da fuskarta a matuqar daure zatai magana ya matso da fuskarta daidai tasa suna shaqan numfashin juna takasa maganar tana juyar da kanta gefe ya juyo da kanta ahankali Yana hade goshinsu cikin nutsuwa yace”

Kina sane Kika kawomin abincin latti sbd bakyason naci.

Miqewa tayi gaba daya daga jikin nasa tana nufar kofa da Dan sauri saidai ko kofar Bata kaiba ya dawo da ita jikinta Yana dauketa gabaki dayanta ya nufi bedroom dinsa da ita Yana Kai bakinsa kusada kunnenta yace”

Idan bakiyi mgna Zaki kwana a dakin Nan yau.

Da sauri ta kallesa tana zillewa batasan lokacinda ta bude Baki zatai mgna ba ya kwantar da ita Kan lafiyayyan gadon Master bedroom dinsa cikin fushi tace”

Wannan abin dakakeyi yana wuce gona da iri please stay within your limits….

Bai kalletaba ya zauna bakin gadon Yana janyota ya zaunar Kan qafarsa Yana zare Mata hijabin ya jefar Kan kujera Yana kallon rigar jikinta kafin ya dago ya kalleta Yana Kai hannu kan hannunta dake kokarin banbare nasa akan jikin nata ya juyar da ita Kan gadon suka kwanta Yayi Mata rumfa da jikinsa Yana kallon wuyanta zuwa kirjinta dayake bude sbd rigar jikinta da Babu hannu,
Numfashi me zafi ya sakar Mata a wuya dayasata rintse idanuwanta dasukai jajir da baqin ciki.
Jin dumin bakinsa tayi Kan wuyan nata ya sakar Mata wani irin kiss bayan yagama shinshinarta qamshinta na shiga kowace kusurwan hancinsa zuwa gangar jikinsa batasan lokacinda ta qanqamesaba da qarfi tana rintse ido da qarfi hawaye na gangaro mata,
Hannuwanta dake jikinsa sukasashi kallon kyakkyawar fuskarta ahankali kafin ya tsaida idonsa kan idanuwanta dake rufe yakai bakinsa ya Dora Kan wuyanta Yana sake ruda jikinta da kisses dinsa dasukasata qoqarin turesa daga jikinta tana neman tashi
Tana yunkurowa ta tashi fuskarsu ta hade ya hade bakinsa da nata Yana Bata wani irin sumba data sakata fashewa da wani irin kukan baqin ciki
Ganin hakan yasan abin datakewa kukan Dan Haka saiya fasa sakinta yakai hannu ahankali yazare daurin rigarta daga baya rigar ta zame take jikinta ya bayyana musamman dayake Babu bra a jikinta take yashiga ruda Mata jiki yanda yakeso tun tana kuka har taji Yana neman haukatar da kanta daya kasa daukan abinda yakeyi ta sake fashewa da kukan baqin cikin dayafi na farko tana turesa.
Dagowa yayi da idanuwansa dasuka sauya ya kalleta Yana wani tunanin kafin ya juya ahankali ya sauka daga kan gadon ya nufi toilet ya tube yasakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwa.

Daure da towel yafito iya qugunsa ya kalli gadon har lokacin tana kwance cikin bargo tana hawayen yanda zata iya komawa bayan su hajjon sunga irin jimawar datai.

Wasu kayan baccin ya sauya ya fita zuwa fridge ya dauki drink yasha yakashe komai na palon ya nufi bedroom din Yana kashe wayarsa daya dauka a Palo daya Bari.

Yana shiga tana fitowa sanye da kayanta data maida tsaf ya kalleta tana wucesa
Bai ce Mata komaiba shima ganin yanayinta ta nufi kofa ta fice yabita shima suka jera Batama nuna tasan da mutum tareda itaba duk da tasan tanajin tsoron fitowa dagacan din zuwa Nan yanxu da daren.
A kofar shiga ya dakata saidata shige ta rufe kofar ya juya yakoma Yana duba agogon wayarsa daya nuna karfe goma Sha daya da arbain.

Sai datai wanka ta iya kwantawa jikinta na Mata Ba Dadi ta samu ta kwanta tanajin nauyi da radadin zuciya har wani wahalallen bacci ya dauketa.

Qarfe Tara da rabi ta fito shirye cikin Luis chiffon shirt da pallazo trouser me shegen Fadi daya koma kaman skirt saidai daga gurin qugun a kame yake sai D&G scarf me Dan girma datai rolling tana ganin yanda Hanifa ke kallonta ta kame fuska sbd Kar Tai Mata zancen komai
Hajjo kuwa Kota kansu batabiba abincinta taci Takoma aikin karatun littafan addininta.

Kodata fito Bata tsaya biyawa gurin dad Alfa ba tunda zasu hadu office din yau sauri takeyi sbd tayi latti tunda zasuyi shirye shirye kafin shareholders dinsu su iso qarfe goma da rabi daza’ai meeting din.

Kafin ta Isa ahanya tana ganin no din data tabbatarda itace ta jiyan da Abbas yakirata yanata kiranta taqi dauka Amma Bai daina kiranba Dan Haka Kai tsaye tasaka wayar flight mode gabaki daya sbd tasan koyaushe Abaas cikin neman fitina da tashin hankali yake.

Ko data Isa Kai tsaye office dinta tashige tacewa Sarah duk Wanda yazo karya shigo tana buqatan duba wasu files cikin tsanaki.

Dukkanin wani Shirin meeting dinsu sun Gama har shareholders dinsu sun iso Dan Haka ta miqe zata fita saiga Abbas yashigo office din ta kallesa tana dauke Kai tace”

Lafiya?
I mean gani Nan zuwa can yanzu basai kazo ba kaje gani abayanka tareda Sarah.

Qarasowa yayi gaban table dinta Yana kallonta dakyau yace”

Meyasa naketa Kira bakya dagawa?
Kinsan dalilin dayasa nake kirane?

Matse fuska tayi tana matsawa tareda kaucewa ta nufi kofar fita tana cewa”

Idan kafito ka rufe kofar.

Shan gabanta yayi tayi baya tana kallonsa cikin fara quluwa da dabiarsa ta kallesa cikin tsana da qyamar halayensa da Basu sauyaba tace”

Mr chairman behave yourself please kana neman wuce limits dinka
Hurumin wani kake neman shiga da wannan dabi’ar taka ka kiyaye.

Wani irin murmushin takaici yasaki Yana Mata kallon daya sake suqeta Yana tsananta Mata tsanarsa yace”

Wai kina maganar ke Matar aurece yanzu kokuwa kina nufin hurumin na waye akanki.

Sanin dama ba cikakkiyar hankaline dashiba yasata sake rabesa zata wuce yasake matsowa gurinta sosai zaiyi magana Wanda ke bakin kofar tun dazu yayi gyaran murya suka waiwayo gurinsa
tana ganinsa taji faduwar gaba akaro na biyu kenan data gansa gabanta na faduwa, dauke Kai tayi ganin yanda fuskarsa tayi ta rabashi zata wuce ya riqo hannunta tareda dawo da ita ya kalli Abbas dake kallon hannunsu a hade zuciyarsa na tafasa yanajin kamar ya Ari hauka yajuyewa Marshal din ita
Cikin muryarsa me kamewa ya kalli Abbas yace”

Zaka bamu guri ko” yaqarasa fada Yana nuna Masa kofa da idanuwansa dasuka saka Abbas din mufar kofa ya fice zuciyarsa na tiriri.

Bayan fitar abbas Dan rufe fararen idanuwansa dasuka sauya yayi kafin ya bude ya kalleta Kai tsaye yace”

Bayan wannan meeting din kafin kibar Nan ki tabbata kin rubuta resignation letter, daga yau na soke zuwanki aiki gabaki daya harda fita ma.
Yana Gama fadar hakan ya juya ya wuce sbd ita kanta tana iya jiyo tsantsar da gaske yake maganar Babu Wargi acikinta yabarta tsaye tana binsa da kallon mamaki Dan kuwa kasa dogon motsi tayi ganin yanda yau idanuwansa sukafi kullum nuna Isa da hadewa.

Daqyar ta iya tattara kanta takai gurin meeting din inda ita kadai ake jira
Tana shiga Abbas yabita da ido Yana satar kallon Marshal Wanda gabaki daya fuskar Nan tasa Babu wani sauqi ko rahama atareda ita Dan ko ita din Bata ishesa kallo ba.

Meeting din suka fara tsawon lokaci kafin aka kammala suka fito ko office Bata nufaba Sarah ta qaraso da sauri cikin sassauta murya tace”

Marshal na jiranki yanzu a mota.

Kallonta tayi tana dauke Kai ta qarasa office dinta tashige tana cewa”

Zankoma da kaina idan nagama.

Kasa juyawa Sarah tayi sbd tsoro da fargaban tunkarar Marshal da zancen Dan sanin ba Wasa ko reni bare sakin fuska.

Sake kallonta Naj din tayi tana cewa”

Me kike jirane?
Kije ki sanar Masa nasan hanyar komawa gidan da kaina.

Ganinsa bayan Naj din yasa Sarah Dan sauke Kai tana ficewa daga office din batareda tasake cewa komaiba.

Tana fita Naj dataji isowarsa ta hanyar Jin qamshin turarensa ta tamke fuske tana wucewa zuwa gurin handbag dinta zata fiddo wayarta.

Akaro na farko da bacin ransa yafara fita akan taurin kanta da rashin tunaninta Dan Haka Kai tsaye ya fizgo hannunta da handbag dinta a hannunsa yafice da ita.
Cikin Motar yasata kafin yashiga yaja motar sukabar gurin.

Itama Bata hakurin yakai maqura cikin bacin Rai ta juyo ta kallesa tace”

Ka tsayar da motar bana buqatan zuwa gidan ahaka sbd bana buqatan kowa nashiga rayuwata yayi abin dayaga dama aduk lokacinda yaga dama inaga hakan ya Isa so just stop the car Zan sauka.

Ciki tsananin bacin Rai yayi wani mugun parking da motar ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasuka sakat gabanta muguwar faduwa da muryarsa data sake kayar Mata da gaba yace”

Zan banbanta Miki tsakanin iko da dama dakuma ganin dama Wanda Duke suke a hannuna na rayuwarki gabaki daya ta yanda gaba Zaki San waye mijinki waye tsohon saurayinki
And Kika sake magana agurin zakisan waye Wanda igiyar aurenki yake a hannunsa.

Fasa nufar gidan yayi ya juyarda motar da wani irin speed yakama hanyar qaton gidansa dake cikin anguwarsu ta sojoji wadda duka manyan sojojine acikin anguwar shiyasa tsaronta yafi kowace anguwa a garin.
Tun a checking point din farko da sojoji ke gadin anguwar taji gabanta yafara faduwa sbd tasan yanada sabon gida a anguwar wanda zai zauna da Hannah bayan aurensu
Idan tashiga anguwar Nan tasan Babu me fitar da ita idan bashiba Dan tsananinta taji hankalinta na neman tashi Amma sbd taurin zuciya taqi cewa komai bare kallonsa.

Suna Isa gaban makeken gate din gidan aka wangale Masa sbd kurtun sojan dake gadin gidan Yana zaune kofar gate din Kan kujera Yana waya.

Parking yayi gefen wata Mercedes Benz beymach dinsa wadda take gidan tunda ya siyeta take gidan ko hawanta Bai tabayiba.

Fitowa yayi batareda yabi takantaba ya nufi kofar shiga wadda keda code tana ganin hakan tasan ko zatai shekarun duniya agurin bazai dawoba Dan Haka ta fito tabiyosa Dan Jin dalilinsa na zuwa Nan din da ita Dan tanada abin Yi idan shi batadashi.

Tana Shiga palon ta kallesa lokacinda yake shigewa hanyar bedrooms ta dauke Kai tana Jin zuciyarta na zafi da kalar nasa cin ran ta nufi kujera ta zauna Dan kuwa kozasu shekara anan itama bazata bisa ta rokesaba akan ya maidata gida tunda taga a sama yake.

Agogo tafara kalla ganin lokaci na tafiya Dan kuwa tunda yashiga Bai fitoba taga magriba tayi har lokacin Babu motsinsa
Ta fiddo wayarta daga cikin jaka tana dubawa saigashi taji qamshinsa Yana dosowa ta dauke Kai daga kallon inda zai fito din ya qaraso ta gabanta sanye da farar jallabiyar data qara Masa kyau sai qamshi yake zubawa ya kalleta da idanuwansa datakejinsu suna yawo akanta ya wuce ya nufi kofa ya fice zuwa masallaci sallar magriba.

Wayarta ta duba Dan Kiran hajjo sai taci Karo da saqon Hanifa data rubuto Mata”

_Sarah tace tafiyar office ta gaggawa ta kamaku Allah ya tsare adawo lafiya sirikita karki damu nariga nafadawa hajjo_

Da alama da wata manufa hanifar Tai Mata text din Dan Haka sai kawai ta aje wayar tana miqewa dan yin alwala a toilet din dake palon farkon kafin yadawo.

Da dubara da kame kame tayi sallar magriba da ishai da kayan jikinta Takoma kujera ta zauna tana jiran dawowarsa.
Bai dawoba sai qarfe goma na Daren lokacin wani wahalallen bacci ya dauketa Amma sbd tariga tasawa ranta rashin yadda dashi da sukuni tanajin motsi ta farka tareda bude idanuwanta ahankali dasuke cikeda baccin bacin Rai da gajiya tagansa gabanta tsaye Yana kallonta cikin yanayi na Dan tausayawa sbd ganin taurin kanta yasa ko ruwa batashaba duk da yaga alamar tayi salloli sbd ganin toilet din daya gani tayi amfani dashi na palon.

Sunkuyawa yayi ya dauketa gabaki dayanta ya nufa dining da ita ya zaunar tareda nuna Mata kayan tarkacen abinci da drinks daya shigo dasu da ido ta miqe tsaye tana kallonsa da cikin masifa zatai magana Amma batama da qarfin yin masifar
Yana ganin Haka ya dauka yoghurt me sanyi kadan ya bude ya zaunar da ita yabata abaki ba musu ta bude bakin ta Sha sosai sai alokacin tasamu damar kallonsa tana qwacewa daga jikinsa.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 25_*
Miqewa take kokarin Yi ya ajiye cup din dake hannunsa ya kalleta da mamaki akan fuskarsa datake sata dauke idonta daga kallonsa ya mayarda ita zaune kan qafafun NASA tareda zura hannayensa ya rungumota ta baya Ya zuro kansa ta wuyanta daidai kunnenta ya bude Baki ahankali ya furta”

Me kike yiwa gaggawa na guduwa bayan kin shanyemun yoghurt¿
Kinsan me hakan ke nufi kuwa?””” Ya qarasa maganar Yana shafa fuskarta da tasa.

Yi tayi kamar bataji abin daya fadan ba taci gaba da kokarin kwacewa daga jikin nasa yasake shigewa da ita jikinsa Yana kallon wuyanta dayake shaqo qamshi daga gurin ya lumshe fararen idanuwansa ahankali kafin ya saketa ahankali Yana Dan dauke kallonsa daga kanta ta miqe tsaye fuskarta a daure sosai duk da tanajin takaici da kunyar kanta data Sha yoghurt din gashi Yana kawo Mata wani zancen kunya da takaici Dan kuwa tasan fassarar kalmar daya fada ta cewan” tasan me Shan yoghurt dinsa yake nufi”

Miqewa yayi shima ya Dan kalli fuskarta dake daure ba sassauci ko kadan,
Juyawa yayi ya nufi kujera ya zauna Yana kunna tv tareda daukan remote yakai _Aljazeera_ Yana maida hankalin shi 4 akai.
Yana kallonta tagajinda tsayuwa batace ko kalma daya ba sbd qin yadda ta saukar da Kai tace ya maidata gida fuskarta har lokacin a daure Takoma Kan kejeran dining din ta zauna tana jiran yagama yabar palon.

Baibi takanta ba sbd shima bawai rigimar ya iyaba dakuma daure daurenta shiyasa yashareta yaci gaba da kallon labaransa Yana duba agogo akai akai har Sha daya(11:00) tayi ya miqe tareda kashe switch na komai ya nufi hanyar bedroom dinsa batareda yabi takanta ba sbd yaga har lokacin tana zaune daram ga idanuwanta dasuke nuna tsantsan baccin dake cinsu Dan Haka Yana shigewa ta taso a galabaice ta kwanta kan kujera tana rufe ido Dan kuwa tasan baccin wahala ne zatayi gabaki daya batajin zata iya bacci a sofa sbd uban gajiya da takurar datakeji na rashin wankan dare na kafin kwanciya data Saba uwa uba kayan jikinta Suma batajin zasu barta ta iya bacci Amma Haka ta kwanta tana rufe ido.

Wanka yafito ya saka riga da wandon bacci masu Dan kauri na rugby ya zura slippers ya fito palon Yana duba agogon dake bangon tsakanin Master bedroom dinsa da bedroom dinda zai zama na Matar gidan yaga 11:37.

Bacci wuyane yayi gaba da ita me Dan nauyi Dan kuwa harda yunwa na tareda ita,
Idanuwansa ya zuba Mata ya kalleta da kyau yanajin tausayinta dakuma mamakin taurin zuciyarta tareda bakinta dayake zaro ko wace irin magana ya fada.

Sunkuyawa yayi ahankali ya dauketa gabaki dayanta ya nufi dakinsa da ita Yana sake kallon fuskarta datafi komai tsaya Masa.
Bude dakin yayi yashige tareda rufowa ya nufi sofa ya kwantar da ita ahankali ya zare Mata qaramin mayafinta da iyakacinsa wuya zuwa kafada kadan yayi wurgi dashi Yana sawa aransa bazata sake saka ire iren mayafanba sbd qarancinsu yayi yawa.

Maballan rigarta yabi Yana cirewa ahankali gaba daya kafin ya zare Mata rigar idanuwansa suka sauka Kan fara tas bra din dake jikinta wadda take showing sosai sbd lace dinta transparent ne ya dauke Kai Yana Dan hadiye abin data tsaya a maqoshinsa ya zare Mata pallazo trouser dinta take yaji kamar zaiji zufa ya miqe tsaye tareda daukanta ya kwantar tsakiyar gadonsa yaja bargo ya rufeta tareda qarasa jikin qaramar bedroom fridge din dake dakin ya dauki ruwa me Dan sanyi ya bude yasha ahankali kafin ya maida sauran ya dawo bakin gadon ya zauna tareda lumshe idanuwansa dasukaso sauyawa ya Haye gadon gabaki daya Yana kwantawa gefenta tareda rufe Rabin jikinsa ya zura hannu ya kashe musu wutar dakin.

Bacci me nauyi yayi daqyar ya samu yatashi sallar asuba da ake gaf da tayarwa ya Dan waiwaya ya kalli fuskarta dake daf da tasa suna shaqar numfashin juna ya yakai bakinsa ahankali yayi kissing bakinta dayafi komai kunnasa idan ya jeho magana kafin ya zare yafita bargon ahankali ya sauka gadon ya nufa toilet.

Da alwalarsa ya fito ya sauya Kaya zuwa jallabiya da hula ya fice zuwa massalincinsu dake tsakiyar kamar estate din.

Harya dawo bacci takeyi sosai Dan Haka Saida ya maida kayansa na bacci kafin ya hau gadon yashige bargon ya kamota jikinsa ahankali ya shigar da ita qirjinsa Yana kallon fuskarsa yakai hannu ahankali ya shafo wuyanta cikin yanayin daya sata motsawa sbd Jin baqon lamari.
Sake shafa wuyan nata yayi tareda hura Mata iskar bakinsa a hankali cikin kunne take ta bude idanuwanta dake cikeda bacci suka sauka Kan kyakkyawar fuskarsa ta kafesa da idanu tana kallon fuskar tasa batareda ta saniba.

Gira daya ya daga Yana Mata alamar tambaya da ido da wata irin muryar daukan hankali can qasa ya furta”

Karki damu da yawa sun riga sun fada da kallo daya suke fadawa soyayyana me qarfi Dan haka naki ba damuwa bane tunda ke kinriga kin samu fadawanki son mijinki ba illa bane Ina tayaki murna.

Wani qaton takaicin kanta da baqin cikin maganarsa tareda kunya suka suka taru suka danne maqoshinta ta dauke Kai tana tashi zaune fuskarta a bace.
Kallon jikinta tayi ganin daga ita sai bra da wando da sauri ta rufe jikin nata da bargon tana kasa dagowa ta kallesa akaro na uku kenen Yana samun damarta,
Wannan wace irin jalalace take gani abin kunya da takaici kullum qaruwa yake a rayuwarta.

Kwanciyarsa yayi tareda rufewa ya rufe ido Kamar bashine yagama magana ba yanzun.

Duddubawa tafara yi Amma takasa ganin kayanta a koina cikin dakin gashi bangarenda closet dinsa take daban bazata iya zagayawa tabi bangarenda fuskarsa ke kalloba ahakan,
Sabuwar damuwa da baqin cikine yakuma dabaibayeta lokacinda idanuwanta suka sauka Kan jallabiyar daya cire daya dawo sallar asuban,
Batada wani zabin dayafi Mata daukan rigarsa ta Sanya sbd bataga kayanta ba Kuma bazata taba iya tambayarsaba Haka zalika bazata taba iya zama ahakan ba daga ita sai undies din Dan Haka ta Dan taka ahankali ta dauki rigar dake zuba wani irin qamshinsa me sanyi da dadi ta yamutsa fuska tana dauke kallonta kan rigar sbd idan tana kallonta zafin zuciyarta qaruwa yakeyi ta zura rigar datakai qasa ta zube sbd mugun yawan datai Mata ta daga hannuwan rigar dasuka rufe gabaki daya hannuwanta ko yatsanta daya ba’a gani ta dauke Kai tana sakin boyayyan tsoki ta tattara gaban rigar ta ‘dan riqe ta nufa kofar dakin ta fice Kai tsaye ta nufa toilet din palon Wanda Tai amfani dashi tashige.

Da alwalarta tafito ta rasa abun rufawa tayi sallah Dole Takoma dakinsa acan tasamu qatuwar hijab din sallah cikin shopping bags dinda yashigo dasu jiyan da daddare ta Sanya akan jallabiyar ta tada sallah.

Tana idarwa tayi Azhkar ta miqe ta fito tadawo palon ta zauna tana bincike Jakarta sbd wayarta data kasa gani.
Duddubawa tashiga Yi Amma takasa ganin wayar gashi wayar takeson Yi kamar me dan kuwa Sarah zata Kira tasamo mota tazo ta dauketa kota Yaya bazata iya sake ko wuni anan din ba bare wani kwanan gashi babbar damuwarta da baqin cikinta bazata iya Kiran hajjoba ko Hanifa bare Dad Alfa tace suyi Masa mgn ya dawo da ita gidan ba sbd bazata taba son ma Susan cewar har yasamu kebewa da itaba Dan kada adauka rayuwar aure suke bazata iya daukan wannan kunyarba bazata iyama Bari Susan tana taredashiba koma Nan gaba bazata Bari wani yasan sun taba kwana gurin dayaba shiyasa takeson Kiran Sarah ta lallabo ta dauketa subar Nan tun ba’a ganeba Amma takasa ganin wayar Kuma tanada tabbacin tazo gidan da wayar.

Rashin mafitar wayar da madafa gareta yasa Takoma palon ta zauna bayan ta hada tea da shortbread biscuits Tasha ta koshi ta dunqule guri daya tana rufe idonta Dan tana Jin sauran gajiya da bacci har lokacin
Ahaka kuwa wani sabon baccin me nauyi ya dauketa.

Bata Farkaba sai Sha daya saura na Rana Dan Haka a kasalance ta bude idanuwanta tana tashi zaune gabobinta na Dan Mata ciwo sbd yanayin kwanciyar datai a kujeran Babu wani sakewa.

Agogo ta kalla tareda miqewa ta nufa toilet tashiga tayo fitsari ta wanko fuskarta tafito tanajin Kamar ta Dora hannu akai tayita rusa ihu sbd baqin cikin wannan al’amari daya sameta na zama Kamar a kurkuku.

Jin shiru Babu motsinsa yasa ta nufa dakinsa Nan ba baya Nan ta fito Palo ta duba harabar gidan motarsa daya batanan ta tabbatarda fita yayi Dan Haka ta tube tashige toilet din dayan dakin Wanda yadauka sanyin AC da qamshin Rosalle roomfreshner da alama shine ya kunna AC din dakin tunda Babu kowa,
Komai na dakin golden ne ita batada wani lokaci ko sha’awan Bata lokacinda kallon dukkanin wasu abubuwan burgewa na gidan Dan Haka wanka tashiga toilet tayo da ruwan zafi ta gasa jikinta koina ta Dade tana wankan saidataji ta sake sosai kafin ta fito ta kalli gaban mirror din dakin taga turaruka kusan guda biyar Kuma dukkaninsu wainda take amfani dasu ne sai qarin Tom Ford Oud wood Wanda tasan tsananin girman kudinsa sbd girman tsadarsa.

Sama sama ta fesa turarukan kafin ta nufa jakar siyayyar data gani a dakin ta bude taga duk cikin siyayyar kayan dayayi jiyan ne ta fiddosu tana dagawa taga wata fitinanniyar rigar baccin data sanyata maidata da sauri cikin jekar tana yamutsa fuska da zallar mamaki da qin gasgata me tunanin hakan ke nufi?
Yagama wulaqanta rayuwarta tako Ina idan har ya siyo wainnan kayan baccin ne Dan Yana tunanin ita tasaka.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 26_*
Akwai riga da wando three quarter red Wanda Suma kadaine kayan sawar ta fitar ta Sanya daqyar sai alokacin ta lura hadda bra da panties acikin siyayyar ta dago bra din ahankali tana dubawa cikin tsoro da mamakin ganin dukkaninsu size dintane,
Cikeda takaici da qin yadda da ya akai ya San sizes din nata ta maida kayan ta fice daga dakin tana Jin koina na gidan siqe Mata numfashi yake sbd tsananin kosawa da tsanar komai na gidan datake ji.

Sallar azahar Tai Takoma takuma hada tea tana cikin sha aka Danna doorbell ta waiwayo tana kallon hanyar kofar tana ayyana bashi bane
Idan shine baya buqatan doorbell din Dan Haka ta tashi da tunanin ko waye zai taimaka Mata ta nufa kofar bayan ta Sanya hijab ta bude Kai tsaye.

Sojace mace sanyeda uniform ta kalleta cikin tsananin girmamawa tace”

Good afternoon mah.

Qaton basket din hannunta dayake daukeda food warmers kusan guda uku sai ledojin fresh fruits ta nunawa Naj din tana cewa”

Marshal yasa akawo Miki wannan Yana meeting tareda sauran Marshals dinnmu dasuka zo.

Ahankali ta bude Baki ta furta”

Thank you” tana miqa hannu ta karba ta shige dasu sojar tabar gurin tana cewa”

Idan kina buqatan wani Abu Ina daga Nan waje tareda dayan soldier dinmu mune muke gadin Nan.

Tana ganin kulolin tasan na gidane take taji hankalinta a na neman tashi da fatar basusan tana Nan dinba gurinsa, daqyar ta iya takura kanta taci abincin sbd batason taqici takasa samun qarfin Hana kanta bacci yau bare yasamu damar kaita dakinsa.
Tana gamawa ta Kai kayan kicin tadawo ta zauna a palon lissafinta na neman mafita na ninkuwa Dan kuwa zuwa yanzu din tana ganin zai iya Kai hakurinta da rashin maganarta maqura Kuma batasan kwanaki nawa zai jata anan dinba tunda tasan ko ajikinsa tunda kamar tozarcine yakeson yimata Dan Haka kawai ta yanke hukuncin idan yadawo zatai masa magana Dan idan ya manta matsayinta na qawar yayarsa to ya tuna ita batada abin Yi dashi.

Hankalinta ko daya baya Kan TV dake aiki zuciyarta a cunkushe take bayan komawarta gida Babu abinda take buqata.
Sake daga Kai ta duba agogo tayi tana Jan numfashi me zafi ganin karfe hudu harda mintuna ashirin ta miqe takoma dayar dakin tayi sallar la’asar tayi zamanta Bata fito tana karatun wani littafin yaren French data gani a palon har akai sallar magriba Bai dawoba Dan Haka ta sake fitowa palon ta nufa dining ta zuba abinci kadan taci Tasha lemon tea da Zuma tana kicin taji dawowarsa taqi fitowa sai daya shige tafito ta nufa dakin tashige ta rufe kofar tana tayarda sallar ishai.

Baya tareda wata doguwar gajiya Dan Haka kayansa yafara rabuwa dasu duka ya daura towel a qugunsa ya nufa toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe ido sbd Jin kansa dayake yau din free Dan meeting dinsa na yau din ya kammala aikin daya dawo dashi dan lokacin dayake dawowar baiyiba.

Fitowa yayi yana goge jikinsa ya tsaya gaban madubi Yana sake goge kansa ya dauki Neutrogena oil kadan ya shafa ajikinsa kafin ya shafa body spray na _Creed Aventus_ yabar gaban madubin ya qarasa closet ya Sanya kayan bacci farare masu tsantsi ya zura slippers yafito Yana waya da Hannah a natse cikin qowa da surutunta nason zuwa Nan gurinsa tagansa.

Direct dining ya nufa Yana zaunawa ahankali yaci abinci kadan ya taso riqeda _Red Bull energy drink_ yanasha yazo ya zauna palon Yana kallon labarai.

Ya Jima zaune a palon Yana kallon labarai tareda amsa waya akai akai.
Bude kofar dakin tayi ta fito sanyeda hijab din datai sallah ta nufosa fuskarta a Dan hade ta qaraso tsakiyar palon ta Dan tsaya daga gefensa ta Dan kallesa tana taqaita kallon nasa Kai tsaye da muryarta mara hayaniya tace”

Inada abubuwan dasuke jirana a gida da gurin ai….shiru tayi tareda waiwayowa ta kallesa har lokacin Bai juyo ya kalletaba idanuwansa na Kan TV da waya ahannunsa ta dauke Kai tana tamke fuska Kai tsaye taci gaba da cewa”

Inada abinyi Babu wani dalili ko amfanin zamana anan pass na shigowa anguwar kawai nake buqata inada inda zansa Azo daukana acikin Daren Nan Dan bana buqatan qarin ko kwana daya anan.

Juyowa yayi ahankali ya zuba Mata fararen idanuwansa Yana qarewa fuskarta kallo zuwa hijab din dayayi Mata kyau tsawon seconds kafin juyar da kansa Yana duba Kiran daya shigo wayarsa yaga sunan Hannah ya dauke Kai Yana sake maidawa kan tv ya bude Baki Yana waiwayowa kadan ya kalleta da wani irin kallo yace”

Kije ki kawomun ruwa marasa sanyi sosai zansha.

Da mamaki me girma ta kallesa ganin yanda yayi maganar Kai tsaye fuska a kame ba alamar tsokana ko wani Abu Mai Kama da hakan,ranta ya ninka baci ta juyo gaba daya gabansa ta kallesa cikin gajiya tareda kosawa da duka wannan abubuwan dake faruwa tsakaninsu kai tsaye tana bayyanarda bacin ranta tace”

Inaga ai kaji abin Dana fada farko right?
Menene wannan kakeson nunawa?
Mijin ko me bada umarni? kokuma me?
Banda lokacin duka wainnan ban buqatan fada maka Amma ai kasan matsayinka da matsayin auren so please just quit all this kaban pass Ina buqatan barin Nan.

fararen idanuwansa ya dago ya zuba Mata dasuka fara saka maganarta gargadan fita ta dauke idonta akansa tana Jin idanuwansa akanta suna neman hanata fadar abubuwan datake fadar ta juya cikin takaici zata bar garin ya riqo hannunta ahankali tareda janyota tadawo baya ta Fado jikinsa zaune yayi Mata wani irin riqo Yana kallon fuskarta dake kaucewa kallonsa cikin muryar data sanyata waiwayowa ta kallesa batareda ta saniba yace”

Meyasa kikeson nanata kalmar girman ikona akanki?

Ahankali ya zare Mata hijabin ya aje Yana sake shigarda fuskarsa cikin wuyanta Yana shinshinawa cikin ya zura hannuwa ya shafo cikinta Yana cewa”

Abin dake nuna kansa basai nafadaba shine nine mijin,nine me ikon,nine me bada umarnin Kuma nine Zan zamo me damar Amma yanzu bazaki gane hakan ba sai Nanda watanni Inshallah result din damata zai bayyanarda kansa Amma dai shi bakin Nan daga yau zai daina magana akan iko da dama…

Bata ankaraba taji hannuwansa cikin wuyanta Yana juyo da fuskarta ya hade bakinsa da nata yana lumshe fararen idanuwansa cikin nutsuwa.

Qwacewa tafara kokarin Yi Amma takasa sbd irin shigar da itan da yayi ajikinsa gabaki daya ya rufeta bayan sarquqan numfashinsu saitaji bugun zuciyarta na tsanantuwa da fargaba ta bude idanuwanta akan nasa idanuwan dake rufe takai hannuwanta biyu Kan fadadden kirjinsa zata turesa daga jikinta ya cirata gabaki daya ya nufi dakinsa da ita Yana sake Bata kyakkyawar runguma cikin jikinsa.

Tun Bai qarasa gadonsa da itaba Yana rufe dakin ya kashe wutar dakin Yana qarasawa Kan gadon da ita ya kwantar ahankali tareda zare rigar jikinsa ya Kuma janyota jikinsa sbd tuni ta sauko gadon qafafunta na rawa zata fice dakin.

Rigar jikinta yake kallon cikin yanayin dayasa bugun zuciyarta qaruwa hannuwanta na daukan rawa ya hade Fuskokinsu Yana shaqar numfashinta da ‘duminsa yake tado Masa da wata irin tsimammiyar yanayi da akanta kawai yake jinsa ya lumshe ido Yana zare rigarta cikin wani irin salon da Bata saniba yabarta da bra wadda ya zubawa ido Yana yimata fitannan kallo sake tabbatarda baiyi kuskuren riqe size dinta ba yakai hannu Yana shafa wuyanta cikin nutsuwa da salon dake sake Sanya jikinta rawa da fargaba tana neman kwacewa duk da jikinta Babu inda Bai dauki rurin abin dayake matanba,ta yunqura da qarfi tana neman turesa
Yunqurinta ya basa damar balle hooks na bra Dinta ya zare Yana jehowa qasan gadon jikinta da Babu riga ya mannu da kirjinsa da Babu rigar shima take ya kusan rabuwa da numfahsinsa sbd haduwar kirjinta da nasa take control dinsa ya balle yakasa riqe kansa Ya hade bakinsu yana zura hannuwansa zuw kirjin nata.

Wani irin kukan baqin ciki da tsoron abin dazai iya faruwa tasaki tana turesa da qarfi Amma takasa ko motsasa daga jikinta daya Gama rabata da komai Yana Mata wasu irin abubuwan dasukafi qarfin tunaninta da kwanyarta Dan kuwa abune dabai tana faruwa da itaba Arayuwarta musamman dataga wannan karon sosai yake yanda yakeso da jikin nata tun tana iya daga hannuwan tana hurasa harsaida yagama tarwatsa duk wani qarfinta ta hanyar bin jikinta da wasu irin romance masu kunyar fada bayan wani irin Nishi Bai sake tsoratata Babu abin Dake tashi a dakin saikuma sheshekan kukanta daya kasa dannuwa
Ahankali taji Yana adduar data sanyata tattaro Dan qarfinta tana neman kwacewa da wani irin kuka Amma Babu wata damar hakan Dan kuwa ahankali yafara rabata da budurcinta Wanda tayi shekaru tana kame kanta ga kowane namiji dakuma qazanta.
Azabar datake Jin tana dosarta me tsananin da Bata taba jiba yasata fashewa da kukan dabatasan tanada qarfin yinsaba tafara roqonsa ta Kiran sunansa saidai ba wannan maganar Dan kuwa tuni komai yafara kammaluwa har batasanma lokacinda taji Kamar numfashinta yabar jikintaba.

****
Qarfe bakwai saura na safe ta bude idanuwanta datake ganin dishi dashi sbd tsananin kumburinsu ahankali ta saukesu akansa Yana zaune bakin gadon yana waya ahankali cikin yanayi na basarwa wanda ke nuni da yin wayar na damunsa
Ta maida idanuwanta ahankali ta rufe a wahalce da sanyaye hawaye suka gangaro Mata tafara kokarin juya baya daga inda yake sai alokacin ya lurada farkawarta ya kashe wayar tareda ajiyewa ya birkitota tareda dorata jikinsa Yana kallon fuskarta dake tsiyayar hawayen dasuka kasa tsayuwa ahankali yakai bakinsa yayi kissing idon ahankali da wata murya me kamewa da taushi yace”

Good morning Anty NAJMA JALALUDDEEN MARSHAL.

Wani sabon qululune ya taso Mata ta fashe da wani sabon kukan ahankali idanuwanta a rufe sbd bazata iya bude ido ta hada ido dashiba bayan wannan qaddararren daren.

Jin kukanta yake Yana masa wani iri ya kalleta Yana Kai hannu kan fuskar ya shafa ta turesa da qarfi tana kokarin saukowa daga kan gadon Amma takasa sbd gabobin jikinda da qafafunta Babu inda baya Mata wani irin azababben ciwo da tsamin jiki ta bude idonta dasukai jajir ta kalli kanta ko Kaya Babu ajikinta ta zuro qafafunta da qyar zata miqe Amma takasa
Baice Mata komaiba ya zagayo ya dauketa gabaki dayanta yakaita toilet ya aje zai kunna Mata ruwa ta fizgo towel ta rufe jikinta tana nuna Masa kofa da hannunta dake rawa sbd wuya.

Ficewa yayi yabarta ta lallaba daqyar ta iya fara gyara jikinta tanajin gasawa da ruwan zafi sosai duk da har lokacin hannuwanta rawa sukeyi sosai ta rasa meyasa.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

 

*_DM 27_*
Kamar zataji sauqi idan tagyara jikinta tayi wanka da ruwan zafi sosai Amma sai zazzabi me qarfin gaske ya sauko Mata Wanda dama tanajinsa tunda ta farka din Amma ta dauka idan tayi amfani da ruwan zafi sosai zai tafi.
Bayan fitowarta wankan da qyar ta iya Kai kanta bakin kujera ta zauna qafafunta na rawa sbd tsananin azabar ciki da wajen datakeji batabi takan qaramin towel data fito dashiba hakama kanta dake digar ruwan wanda yafi komai sake daukan hankalinsa ya taso ahankali cikin kulawa ya ranqwafa ya dauketa yakaita gaban madubi ya zaunar ya dauko wani towel din Yana goge Mata gashinta da duk ruwa suka digo daga cikinsa saitaji kamar ta kurma ihu.

Da hand dryer ya busar Mata da Kan sama sama ta lallaba tayi sallah tun kafin tagama jikinta ke rawar sanyi sosai Dan Haka kodata Gama Kan gadon ya maidata bayan ya Sanya Mata wata shirt dinsa datai Mata yawa da wandon baccin kayan baccin daya siyo Mata ya rufeta Yana fita.

Tea Mara shugar ya me kauri sosai ya hado Mata yakawo ya tadata zaune yabata kadan da dubara saidai yanayinta da yayi tsanani yasa yakasa nutsuwa damuwa ta shigesa sosai ya Ciro waya ya Nemo no din Dr sa’id ya saka kiransa ya sanar dashi yana buqatarsa anan.

Massage yatura na pass daga garesa yayiwa security check point dinsu na shigowa anguwar Da sunan Dr sa’id din Dan Haka Koda yazo suka duba sunansa da pass dinda Deen Marsha din yatura aka bude Masa ya wuce.
Dayake yasan gidan Marshal din Kai tsaye ya nufa gidansa yana zuwa aka bude Masa gate yashige yayi parking yafito daidai fitowar Deen din daga kofar babban palon Yana sanyeda three quarter kalar Navy sai shirt mara hannuwa me hula qafafuwansa sanyeda slippers na Brian Atwood marasa nauyi hannuwansa cikin aljihun wandonsa ya qaraso Yana cewa dr sa’id ya qaraso.

A Palo suka zauna ya kalli Dr sa’id suna sake gaisawa ya kallesa Kai tsaye yace”

NAJMA tana fama ne da zazzabi me qarfi plus gabobinta na ciwo sosai kaita asibiti zai sake wahalar da ita banason hakan I hope akwai taimakon da za’a iya Bata anan gida batareda an wahalar da ita zuwa asibitin ba?

Kallon tsanaki Dr sa’id yake Masa jikinsa na matuqar yin sanyi zuciyarsa ta saki sbd idan ya karanci yanayin Marshal din dakyau zai iya cankar cewan ciwon Naj din yanada alaqane da kila marshal din ya kusanceta Wanda dama hakan a gurin wasu matan is normal ciwon zazzabi Dana gabobi a ranar farko da aka fara kusantarsu.

Sauke boyayyan numfashi yayi Yana Dan taqaita kallonsa ga Marshal din Kai tsaye yace”

Pain relief Zan Bata kawai Inshallah zai sassauta zazzabin da ciwon gabobin zuwa gobe Inshallah duk zata warke
Idanma jikin baiyi saukiba zuwa goben idan tasamu karfin jikin zaku iya zuwa asibitin sai aduba jikinta acan din.

Mota yaje ya dauko maganin ya bawa Marshal din Yana cewa”

Hot milk zai taimaka Mata shima da abinci Mara nauyi shima dai me Dan zafin, Allah yabata lafiya.

Thank you” ya furtawa Dr sa’id din Yana juyawa shikuma ya fada mota ya fice jikinsa a mace Dan kuwa Deen Marshal ba namijin da mace zata iya rabuwa dashi bane duk da yasan Naj dinma Babu Wanda zai sameta yayi gangancin rabuwa da ita idanba Abbas da Allah yayi Mara rabo ba a duniya.

Da kansa yabata maganin Tasha ya maidata ta kwanta baccin wahala na sake daukanta ya miqe yakoma kan sofa Yana duba saqonni a laptop dinsa daya dawo da ita jiya daya dawo.

Yana buqatan komawa Hawaii zuwa jibi Dan aikin dayake gabansa dakuma tafiyar dazasuyi Cyprus akan wasu sabbin sojojinsu da za’a qaddamar….
Dagowa yayi ahankali ya kalli gadon datake kwancen tana bacci ya Dan zubawa fuskarta datake kumbure ido ya Dan lumshe idon Yana daukesu daga kanta Yana rufe laptop din ya miqe ya fice zuwa balcony dinsa na qatoton windown dakinsa Yana amsa wayar Hanifa dake tambayarsa Naj ya bude Baki a natse Kai tsaye yace”

Tana bacci batada lafiya ne?

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa”

Please Marshal ka kuka da ita tanada rauni.

Yaya jikinki?
Fatan keda babyn lfy?

Murmushi tayi Jin ya basar da zancenta Wanda tasan lokacin amsarta ne baida hakan Kuma na nuni da itace kenan zata fada Masa abin daya kamata da matarsa.

Kashe wayarta tayi tana cewa”

Ku kula da kanku I love you both bye.

Sai bayan sallar azahar sosai Ana gaf da la’asar ta farka lokacin zazzabin ya rage tasake yin wanka da ruwan zafi sosai ta fito tayi sallar azahar tana kokarin miqewa yashigo ta dauke Kai daga kallonsa tana komawa bakin gadon Bata qarasa zamaba ya dauketa Yana cewa”

Zo kici abinci tunda kinyi sallah.

Abincin da Hanifa ta Aiko musu ya zuba Mata white rice da kidney sauce dataji kidney din sosai dasu carrot ta miqe tana cewa Bata ci
Ya janyota tana qwacewa cikin masifa da qyar yasa taci kadan Tasha tea me zafi sosai takuma Shan magani batareda ta kalli duk inda yakeba tabar gurin tana tafiya ahankali ta Isa daki ta dauka hijab din datagama sallah tasaka ta fito tana Shirin nufar kofa ya rungumota ta baya Yana sauke ajiyar zuciya a hankali yakai fuskarsa Kan wuyanta Yana cewa”

Karkiyi wahalan tafiya Zaki qarawa kanki ciwone basai kintafiba nasan irin fushi da masifan dake cinki zo ki zauna ki huta idan kin warke Zaki iya sauke duka fushinki ba damuwa bane.

Daukanta yayi yadawo da ita palon ya zauna Yana kwantar da ita a jikinsa yace”

Ki daina Bata ranki Babu Wanda zaisan me qanin qawarki yamiki bare a rainaki Kiji kunya nasan duk wannan ne damuwar ko???” Yafada Yana shinshina wuyanta da sauke Mata numshinsa me dumi da qamshi tanajin hannunsa na yawo Kan shafaffen cikinta Yana shafawa tafara kokarin miqewa ya riqeda Yana kwantar da kansa a bayanta.

Yamma nasake dosowa zazzabinta ya dawo me qarfi ya sake Bata magani tareda kwantar da ita cikin jikinsa ya rufe zafin jikinta na shiga jikinsa nasa Dan daga ita sai qaramar shimin daya Sanya Mata kuka yadawo sabo dama Kuma tunda garin ya waye take tsiyayar hawaye Bata dainaba baqin cikin duniya ganin takeyi yau yaqare acikin zuciyarta da rayuwarta datake ganin ta rushe saidai har cikin ranta bazata iya wannan rayuwarba dashi sbd Babu Randa matsayinsa na qanin qawarta zai goge a ranta yanzu Kuma yakai kololuwar wuce hurumin haquri da juriyarta Dan Haka yakai maqura bazata Bari wannan abin daya faruba yabasa damar ji da daukan kansa cikakken miji me iko agareta,
Bazata Bari yasake samun wannan damarba dan Haka ya dauka hakan amatsayin kuskure zata sanarda iyayensu araba auren kawai Koda hakan zai kawo bacin Rai tasan zai wuce.

Koda gari ya waye ta bude idanuwanta akan fuskarsa suka sauka ta juyar da Kai tana cire jikinta daga nasa ta sauka Kan gadon tareda ficewa dakin ta koma dayan dakin tayi sallah tahirya cikin hijab ta fito palon da niyar ficewa saigashi tagansa a tsaye cikin jallabiya da waya da laptop dinsa a hannu sai key din mota ya kalleta da fararen idanuwansa kafin ya tako ahankali ya qaraso gabanta Yana kallon fuskarta ya ranqwafa ahankali yakai bakinsa saitin kunnenta ya furta”

Yanzune kike Kama da matan sure cikkaki Dan Haka be very careful idan bana nan,
Maganar aikinki Kuma Zaki iya komawa kafin wani dalilin na hanaki zuwa ya bayyana.

Kallo ma Bata samu damar binsa dashiba ta nufi kofar ta fice Allah yasa driver zai jasu Dan Haka tana fitowa motar ta nufa ta shige Koda yafito fuskarsa a matuqar kame sai zuba qamshi da kwarjini yake kamar bashine yagama maganaba aciki yanzu ta hade fuska sosai tana kallon gefe harya shigo aka tada motar suka bar gidan Babu Wanda yasake magana acikinsu suna barin anguwar suka hau titi ta bude Baki tareda Dan kallon drivern ta dauke Kai tana cewa”

Kayi parking Zan sauka anan.

Ta madubi ya kalla uban gidansa yaga ko kallonsa baiyiba yasan ba wannan maganar Dan hakan Bai tsayaba yaci gaba da tafiya har Saida suka Kai gida ta kallesa cikin bacin Rai zatai magana Deen din ya waiwayo ya kalleta Kai tsaye yace”

Bakya gane shiru ne idan anmiki?
Koba yau ba duk ranarda na samu labarin anganki a hanya bazaki Kuma marmarin ko fita ba.

Anayin parking ta fito ta daidai fitowar Hannah zata fita a mota ta gansu zuciyarta na wata irin bugawa da ganinsu tare suda akace musu Naj tayi tafiyar aiki tareda Sarah ko hajjo ma Haka Hanifa ta fada Mata to daga Ina suka hadu suke tahowa gida tare da sassafen Nan bayan shi Daren yau jirginsa zai tashi na komawa.

Dannewa tayi tana qarasowa gurinsa cikin wani irin yanayi na Jan hankali tana cewa”

Good morning my Zawj.

Kota kansu batabiba tayi hanyar sashen hajjo tana tafiya ahankali Dan har lokacin Bata Gama warkewaba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 28_*
Da wani irin kallo yabi bayanta da fitinannin idanunsa Yana karewa tafiyar datakeyi ahankali kallo wadda ke sake tabbatar Masa da ita din tasace tako ina,wannan hurumin nasane iya shi daya.
Saidata shige ya dan sake kamewa Yana kallon Hannah kadan wadda tagama shagwabe Masa tana cewa”

A hanya ka hadu da Naj ne ka rage Mata Hanya?
Sbd nasan dai cewan tayi tafiyane tareda secretary dinta yakamata ace tare suka dawo.

Wucewa yayi hanyar sashensa batareda ya Bata amsar tambayar dataiba cikin muryarsa datake bayyanarda kamewarsa Yana tafiya tana biye dashi yace”

Tambayan nada mahimmanci ne?

Zatai mgna ya bude kofar palonsa tareda waiwayowa kadan sai alokacin ya kalleta dakyau tana sanyeda Gucci pencil jeans da farar long sleeves me yankakken hannu sai scarf qarami dake kanta daure ya dauke Kai Yana nuna Mata kofar da ido da alamar kosawa da ita yace”

Kinada abin yi ne idan kinbini ciki?

Dakatawa tayi tana kallonsa cikin tsananin sonsa dayasa Sam batajin haushi ko zafin duk abinda zai Mata ta saki wani yalwataccen murmushi tana kashe Masa ido daya tace”

A yanzu dai banidashi Amma zuwa gaba nice nakeda abinyi aciki
Zan fita,bye,take care I love you.

Juyawa tayi ta bar gurin tana murmushin farin cikin ganinsa Dan kwananta biyu rabonta da ganinsa saidai waya shima idan ta nace da kirane yake dagawa.

Rufe kofarsa yayi bayan ya shige ya aje wayarsa da key din mota ya nufa hanyar bedroom dinsa Yana zare jallabiyar jikinsa.

Maimakon ta nufi motarta datai niyar fita saita juya ta nufa hanyar sashen hajjo tana ayyanawa ranta son sanin meyake faruwa.

Naj ko data shiga palon Babu kowa saisu ruqayyat dake aikin gyara koina hajjo na daki,hanifa ma tana dakinta tana bacci Dan Haka Kai tsaye dakinta ta wuce tana amsa gaisuwar dasu ruqayyat ke Mata da Kai Dan bazata iya bude bakin ba Yar tafiyar datai tasa tanajin Kamar ciwon datakeji ya dawo sabo ta lallaba ta shige dakinta tareda rufowa.

Hijab dinta tafara cirewa kafin ta zare kayansa dake jikinta takai cikin water ta jefa ta shige toilet tareda hada ruwa masu shegen zafi ta shige tana sauke ajiyar zuciya tareda rufe ido ahankali sbd Dan sauki da rahamar dataji sai hawayen dasuka balle suna tsiyayo mata ta rasa Ina zata saka ranta taji saukin abinda takeji a zuciyarta Dan bazata iya wannan aurenba,suqeta al’amarin keyi gabaki daya.

Ta Jima sosai acikin toilet din kafin tafito bayan tayi hadda wanka Wanda yasa jikinta sakewa sosai saidai fuskarta da zuciyarta cike suke da zallar damuwa da baqin ciki
Ta shafa Mai kadan ta shirya cikin riga da skirt na atampa dark purple dataiwa farar fatarta kyau sosai musamman yau din da fuskarta tayi fresh duk da kumburin idanuwanta datasha kuka Yana nunawa ta fesa turare ta fito kanta ba dankwali sai qaramar hular da Bata rufe gashinta duka ba hakan Kuma ya qara Mata kyau ta nufa dakin hajjo tana kokarin nutsar da kanta Dan kada agano halinda take ciki.

Saida takai tsakiyar dakin ta tsaya cak ganinsa zaune gefen hajjo gabaki daya dakin yadauki qamshinsa yayi wanka yana sanyeda riga da wando na farin yadin filtex me laushi da tsada
Yaji shigowarta da dakatawarta Bai juyoba hankalinsa na Kan hajjo dasuke mgn Amma ganin Naj din itama saita tsaya kallonta cikin mamaki tace”

Najma kindawo ne?
Yanzu kuka dawo kokuwa cikin dare?
Qaraso mana,
Sai tafiya Kuma takamaki daga office Baki dawoba,
Anya wannan aikin yakamaceki kuwa yanzu Najma?
Shi wannan na tambayesa tun ranar da kukai tafiyar yace da saninsa Kika tafi,ga wayarki akashe haniface kawai tace tana samunki Kuna mgn.

Daqyar ta iya qaqalo wani munafukin murmushi tana kallon hajjon a natse tace”

Da safen nan nadawo duk Kuna bacci Bari naje gurin Hanifa kafin ki Gama.

Juyawa tayi ta fice batareda tajira wani zancenba Dan
Batareda ya waiwayoba yasaki wani irin murmushin dayasa hajjo kallonsa da dukkanin nutsuwarta cikin mamaki dan ba abune daya fiya yiba ta maido hankalinta kansa yace”

Yaushe ka shirya tafiya da matarka?

Bai kalletaba hankalinsa nakan waya yace”

Saita shirya Bina da kanta.

Bana tunanin zatai hakan sbd haryanxu Bata amintaba da auren
Kuma Sam banason a takurata Akan komai.

Wani shegen guntun murmushin yakuma saki Yana cewa”

Kar a takurata abarta harta Aminta dan kanta.

Tsoki hajjo tasaki cikin quluwa dashi tace”

Tashi ka ficemun sbd kedai haryau zance dakai bayada Dadi
Mutum saiya zage yamaka mgn me tsayi ko mahimmanci ka jeho Masa kalma daya amsa,banason kayan takaici tashi kaje kafin na qarasa quluwa da wannan muguwar dabi’ar taka mara Dadi.

Bai tashiba saima kallonta da yayi yanaci gaba da duba wayarsa Yana cewa”

Ahaka fa kike damuna yaushe Zan dawo idan bana nan.

Murmushi tasaki tana cewa”

Ta Nan ka bullo Kuma.

Naj Kuma tana fitowa dakin ta nufa dakin Hanifa ta tura kofar Kai tsaye ta Shiga saiga Hannah zaune a kejarar dakin tana Taya Hanifa yanka qatuwar guava data tashi tunda safen da marmarin ci
Da mamaki Hanifan ke kallon Naj fuskarta na yalwatuwa da farin cikin ganinta ta ware Hannu tana cewa”

Hey sweetheart sannu da dawowa nayi kewarki sosai sirikata.

Tsuke fuska Naj din tayi tana Mata kallon daya sanyata rufe Baki tana cewa”

Sorry sorry.

Qarasowa tayi tana zama bakin gadon kusada Hanifan ta bude Baki cikin kulawa tace”

Ya ya?ya babyn?

Lafiya kalau muke,ya Hanya? Da gajiyan tafiya?

Alhmdlh” kawai ta furta tana basar da zancen ta hanyar Dan kallon Hannah datace”

Naj sannu da Hanya?
Inane kukaje aikin ne hala?

Yi tayi kamar bataji Hannan ba ta miqe tana nufar kofa tace”

Zanci abinci a dining.

Miqewa Hanifa tayi tana cewa”

Nima yunwar nakeji,
Hannah ko Zakiyi breakfast damu?muke ko.

No nariga naci abinci bana buqatansa qarawa Zan fitanema nace Bari nashigo na dubaki tun shekaran jiya banshigoba.

Dining suka nufa ita Kuma ta fice daga sashen batareda tasan Marshal na sashenba Dan da Babu inda zata.

Tea kawai ta iya Sha sai doya kadan da aka soya da egg sauce ta miqe tana kallon Hanifa dakecin doyar sosai tace”

Inajin Dan ciwon Kai da gajiya zanje na kwanta ko zansamu bacci kafin lokacin sallah.

Ok ki kula, Allah ya hutarda gajiya.

Daki Takoma ta Isa gadon ta kwanta tareda qarawa AC qarfi sbd zufi takeji na zazzabi dake hawa Yana sauka ajikinta ta rufe cikin bargo tareda rufe idanu ahankali bacci me qarfi ya dauketa.

Bacci Sosai tayi Bata Farkaba sai guraren la’asar ta tashi zaune ahankali tanajin tasamu sauki Sosai ko Ina nata ya sake ba laifi ta sauko gadon tareda cire kayan jikinta ta nufi toilet tadake wankan ruwan zafi sosai ta fito da walwalarta tafarayin sallar azahar da la’asar kafin ta Dan shafa Mai ta Sanya doguwar rigar atampa ta fito.

Daga hajjo har Hanifa na zaune palon Hanifa na kallo hajjo na karantunta data Saba da medical glass dinta a fuskarta,
Naj din na fitowa duk suka bita da ido hajjo Kai tsaye tana cewa”

Najma lafiyarki kalau kuwa?Naga duk kinyi wani iri kamar bakyajin Dadi?
Anya Baki debo sanyi a tafiyar Nan ba fuskarki duk ta kumbura,kodai bakyajin Dadi ne?

Hanifan ma zuba Mata idanuwa tayi tana jiran amsar da Naj din zata Bata Dan itama dai taga alamar Kamar batada lafiyar duk fuskarta a kumbure Dan ko yanzu data shiga wanka saidatasha kukan qaqa nikayi kafin tafito.

Dan murmushin Dole tasaki tana qarasawa dining tace”

Lafiyata kalau hajjo kawai dai garin akwai sanyi ne sosai shine yake damuna matuqa Amma zankira Dr sa’id saiya kawomin maganin sanyin Inshallah Kuma ma zuwa gobe Inshallah Zan warware tunda nadawo gida.

Zama tayi ta diba abinci tafara ci bayan Tasha ruwan zafi Dan tafijin dadinsu fiyeda abincin,
Saidata koshi ta taso tadawo gurinsu palon ta zauna Hanifa na janta da Hira sosai tana Dan qoqarin sakewa da amsawa
Hajjo kuwa saiyi takeyi tana kallonta sbd hankalinta kamar Bai kwanta da lafiyar ba ganin take Najma din batada lafiya boyewa takeyi sbd kada ta daga musu hankali idan taga ankwana biyu Bata warware ba zata Kira Dr sa’id da kanta yazo ya duba musu ita.

Ba laifi ta Dan sake sunata hirarsu akan babyn Hanifa da duk suka qwallafa Masa Rai har akai magriba suka shige sallah
A dakin Hanifa sukai sallar acan tayi zamanta har ishai Hanifa nata Koro Mata bayanin scanning dasukai shekaran jiya da Kuma dawowar da Isma’eel zaiyi qarshen wata.
Saida sukai sallar ishai suka Gama zantukansu da Naj daurewa kawai takeyi tana danne damuwar halinda take ciki kafin suka fito cin abincin dare.

Dukkaninsu suna zama Kan dining din ko fara cin abincin basuiba saiga qamshinsa ya fara tunkaro dining din tanajin hakan tasan waye ke zuwa Dan Haka ta Dan hade fuska tana daurewa Dan Hana kanta miqewa tabar gurin sbd hajjo dake gurin gashi tariga tana zaune ne da a tsaye take saitabar gurin..

Muryar Hannah taji cikin wani irin salon nemawa Kai gurbi tana cewa”

Hajjo anan zanci abinci Nima yau can masu aikin mum Malika abincin dasukai yayi Mai sosai zaisani zafin Zuciya.

Da Yar kulawa hajjo tace”

Eh gskia karki ci idan zai saki damuwa zoki zauna kici anan din.

Da sauri ta qaraso taja kujerar dake kusa data Marshal din ta zauna tana jifansa da wani irin kallo
Shikuma hankalinsa gabaki daya baya kanta Yana Kan abincin da Naj ta zubawa kanta taqi ko dagowa ta kalla inda suke Dan Jin take cikinta yagama cika da wani irin takaici.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 29_*
Hannah da kanta ta miqe tariga kowa zuba Masa abincin duk da tana iya kokarinta na riqewa da kiyaye duk wani abin dayake so dakuma ya shafesa Dan Haka abincin iya daidai Wanda tasan yanaci ta zuba masa tareda lemon juice me zuma datasan bayan _RED BULL Blue edition Energy drink_ shikadai yakesha.

Zama tayi tana zuba nata abincin kadan sbd Babu wata yunwar datakeji taci abincinta tun dazu sbd Marshal din yasa tace zataci anan din duk da zuwa yanzu da Naj ke sake zamar Mata abin takaici da baqin ciki Sam said Dole take iya zama guri daya da Naj din Dan dai kawai tana mum Malika nasata dannewane tana boyewa.

Naj cin abincin takeyi a hankali duk da yariga ya gundureta cin kawai takeyi a natse batareda ta kalla kowaba sai hajjo data kalleta cikin kulawa ganin yanda takecin abincin cikin nutsuwa ahankali duk da tasan sanyi da komai a natse hali da dabi’ar Najman ne Amma ita dai tafiyar Nan duk tasake sakurkuce Najman,
Cikin kulawa tana kallonta tace”

Najma jikin ne haryanxu?
Nace ruqayyat ta dafa Miki Ginger tea da Zuma sbd da alamar wannan sanyi ya kamaki sosai a wannan tafiyar,
Gobe Dr sa’id zaizo ya dubaki.

Dagowa tayi ta kalla hajjon tana aje spoon din hannunta cikin nutsuwa tace”

Naji sauki fa Kuma bawani ciwo bane sanyi ne kawai basai Dr sa’id din yazo ba zansha Ginger tea din zuwa gobe Zan qarasa warwarewa.

Zanfi samun nutsuwa idan Dr sa’id yazo yadubaki” hajjo tafada Kai tsaye tana kallon Najman kafin taci gaba da cin abincinta.

Shiru Naj din tayi tana daukan spoon taci gaba da cin abincin tana ganin irin kallon da Hanifa ke binta dashi tayi Mata banza Bata bi ta kantaba.
Hannah ta karba zancen da cewa”

Naj inane kukaje da Sanya zai kamaki Haka?

Sai alokacin ya dago ya ‘dan zubawa Naj din ido wadda tun dazu dasuke zancen Bai dagoba Yana jinsu tambayar hannah tasa ya dago yana kallon Naj din.

Ahankali taji idanuwansa akanta Dan Haka ta sake kame fuska tanacin abinci tana share tambayar hannah da shirun yasake habbaqa tsanar Naj din aranta ta dauke Kai daga kanta ta juyo gurin Marshal din zatai mgn ya aje tissue dinda ya goge Baki Yana miqewa tsaye ahankali alamar yagama ya zuba hannayensa ahankali ya tako zuwa inda take zaune ya sunkuya ya saukar Mata da wani irin lafiyayyan kiss a kumatunta na hannun dama ya Kai Bakinsa kan kunnenta ahankali qasan maqoshi da wata irin murya me tsananin taushi ya furta”

Ki tabbata kinsha ginger tea dinnan sbd wani sanyin dazai iya kamaki.

Dagowa yayi ya kalli su hajjo Kai tsaye cikin attitude yace”

Goodnight,Mu kwana lafiya.” Ya juya ya wuce yabar gurin.

Mutuwar zaune tayi abincin dake cikin bakinta na neman dawo Mata da qarfi sbd mummunan yanayin mutuwar zaunen datai,wani irin tari ya taso Mata Hanifa tayi saurin daukan ruwa tana Bata daqyar ruwan suka wuce Mata ta dauki tissue tana goge bakin idanuwanta na yin ja sbd wahalar sarqewar datai dakuma ta halin data shiga na tsananin kunya da takaicinsa,
Ta dago ahankali ta saci kallon inda hajjo ke zaune taga abincinta take ci kawai tayi kamar batamasan menene ya faruba agurin sbd JALAL tasan zaiyi fin hakan agaban ko uban waye tunda rayuwar daya tashi acikine yake Kuma rayuwa aciki gabaki daya rayuwarsa irin ta ‘yan can yake ta Dade da sanin kaai tsaye yake.

Ruwan juice Hannah ta zubarwa Naj ajiki ta hanyar ture cup din cikin tsananin bacin Rai da baqin ciki dukkaninsu suka kalleta Naj na miqewa sbd sanyin juice din na shigarta ta dago ya kalli Hannah data miqe itama tace”

Sorry ba da ganganbane hannuna ne yayi santsi cup din ya subuce, sorry.

Hanifa dake goge jikin Naj din tace”

Hannah tana fama da sanyi Zaki qara Mata wani juice din nada sanyi sosai fa ki ringa kulawa ko gaba please,
Naj kije ki cire kayan Kar sanyin ya shigeki.

Hajjo ma kallon Hannah tayi barin barin Naj gurin cikin yanayi na manyanci tace”

Hannatu wannan baida kyau kwata kwata kiyi gaggawan aje shashanci ki saka kula.

Barin gurin hajjo tayi Hannah tabi bayanta da wani irin mugun kallon tsana zuciyarta Kamar zata cinnu da wuta sbd baqin ciki da takaicinsu duk su dukan, Ahankali ta furta”

Munafukan Allah ta’ala.
Juyawa tayi ta bar sashen gabaki daya idanuwanta ko gani basayi Sosai sbd baqin ciki.

Naj na shiga dakinta Kai tsaye tube kayan jikinta tayi duka ta jefasu cikin kwandon kayan wanki ta daura towel ta nufa toilet ta bude Kai tsaye ta wanke jikinta tasake Dan watsa ruwan zafi tafito ta saka kayan bacci masu kauri riga da wando ta fito ta nufi kicin Dan Shan Ginger tea dinta da aka dafa Mata.

Tana fitowa palon taji qamshin Tom Ford turarensa taso dakatawa Amma sbd Bataga alamar kowaba a palon saita wucewarta kicin ta zubo tea din a cup me Dan girmata fito ta nufa dakin hajjo Dan batai Mata Saida safe a Kai tsaye tashiga dakin da cup dinta a hannu saidata rufe dakin ta juyo tagansu zaune a kujera daya shida hajjo Yana riqeda hannunta sai Hanifa dake Kan gadon hajjon kwance tana facing dinsu da alama duk su dukan magana suke.

Juyarda fuskarta tayi daga kallon dayake Mata zuwa gefen Hanifa a tausashe tace”

Zanje na kwanta saida safenku.
Juyawa tayi ta fice batama tsaya sauraron abinda hajjo ke fadaba na tambayarta jikin nata.

Dakinta ta koma ta zauna ahankali tafara shan ginger tea din Yana tiririn zafi harta shanye duka
Take zafi yataso Mata tako Ina taji Kamar tana cikin Rana ta miqe tsaye tana cire kayan baccinta masu shegen kauri ta sanya rigar bacci me Dan tsayi Mara nauyi ta qara qarfin AC sai alokacin taji tanajin daidai Kuma taji jikinta yasake sakewa sosai ta nufi gadonta ta Haye ta shige bargo tana kashe wuta Dan yau Kam baccin wuri zatai Dole tunda abokanan firarta nada abokin fira.
Bata Jima da kwanciya ba bacci ya dauketa.

Qarfe goma Sha daya saura yashigo dakin ya qaraso bakin gadonta ya tsaya kanta Yana qare Mata kallo cikin wani yanayi dashi kadai yasan sirrin abinsa.
Fuskarta zuwa bakinta dayake yanka wuyanta ya tsayar da idanuwansa kafin ya cire hannuwansa daga aljihun wandonsa ya zauna bakin gadon Yana gyara Mata rufarta data Dan bude rigar baccin red color na Dan daukan hankalinsa sbd kalar hot red ce ba transparent bace Amma ta lafe ajikinta ta kwanta,ya ‘dan rufe ido ahankali Yana budewa ya shafa fuskarta da har lokacin Bata koma daidaiba da kuka da zazzabin datai.
Qarfe bakwai jirginsa zai tashi gobe shiyasa kawai yashigo gurinta saidai samunta da yayi tayi bacci yasa yafasa tafiya ya Haye gadon ya kwanta gefenta tareda shigar da ita jikinsa Yana sake gyara musu rufa.

Asubar fari alarm din gefen gadonta ya tada ita ta bude idanuwanta ahankali tana kokarin Kai hannu ta kashe taji mutum tareda ita
Gabanta ya buga da qarfi cikin sauri takai hannu gefen gadon ta kunna wutar dakin Mara haske daidai Yana bude idanuwansa ahankali ya kalleta da yanayin daya sake kayar Mata gaba da ganinsa ta yunqura da qarfi zata tashi ya girgiza Mata Kai ahankali Yana maidata jikinsa cikin kasala yace”

Banason farkawa da hayaniya Yana sani ciwon kai,ki riqe hakan.

A hasalce da bacin Rai da mamaki tana qin daga murya danma Kar tsautsayi yasa aji tace”

Meya kawoka Nan?
Menene hakan?
Banason wuce wuri fa,Abinka yayi yawa….

Bude idanuwansa yayi da kyau akanta har lokacin tana cikin jikinsa ya shafo bayanta da hannunsa dake cikin rigarta yace”

Ke bakinki baya mutuwa ne?
Just shut up ok¿Nafada Miki banason farkawa da hayaniya.

Turesa tahau Yi tako Ina sai hannuwanta daketa turesan suna Masa wani irin waiwayi dayasashi dagowa ya kalleta da mayun idanuwansa cikin kunnenta ya furta”

Kinsan me kikeyi kuwa?

Da sauri tasake turasa batareda ta kalli fuskarsa ba sbd Jin muryarsa data sauya.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 30_*
Riqe hannunta yayi ahankali yana sake kallonta da yanayinda yasake fadar Mata da gaba yace”

Ya Isa haka,kece Kika jawo wannan yanzu..

Shinshinan wuyanta yashiga Yi Yana sake shafa bayanta zuwa wuyanta da hannunsa dake cikin rigarta har lokacin,tsikar jikinta dasuka tashi gabaki daya sbd wani irin fitannan kiss daya sauke Mata a wuyanta da Babu komai,
Tasake daga hannuwan zata turasa can qasan maqoshinsa ya furta”
Kinayi Zaki Zaki ja na rasa jirgina Kuma wlh na rasa jirgina saimun bar gidan Nan ayau.

Bata tsaya sauraronsaba sbd idonta dasuka Gama rufewa taringa turasa Wanda hakan yake qarasa sauya yanayinsa ya juyar da ita gabaki daya Yana Mata rumfa tareda dago fuskarta yana hade bakinsa da nata hannuwansa Kuma na zare rigar baccinta ya jefar da ita Yana hada jikinsa da nata da Babu riga shima dama Bai Kwana da riga jikinsa dagashi sai dogon wandon baccinsa rigar sanyice yazo da ita Kuma yacire.
Saida kukanta ya daina fita gabaki daya kafin ya taqaita aikinsa daya mugun shagala ayi musammam yau daya samu hanyar da kyau
ya dauketa da kansa ya nufi toilet da ita,
Yana sauketa ahankali duk da batada qarfi da kuzari Haka tabi bango ta fito ko gani batayi sosai duk wani rauninta ya fama matashi zallar azaba takeji tana fitowa toilet din ta zube qasa da Jan jiki ta qarasa gadon ta kwanta bakin gadon hawaye na tsiyayo idanuwanta dasuke a matuqar kumbure.

Kamar zai biyota yasan Rigima kawai zatai Kuma batada qarfin yin rigimar Dan Haka ya barta kawai yayo wankansa duk biyu da yafito daureda qaramin towel dinta dayayi Masa kadan yahau goge jikinsa Yana duba agogon sallar asuba da aka tada tuni ya kalleta Yana qarasawa inda take bai tsaya komaiba yakuma daukanta duka ya nufi toilet da ita ya aje ahankali,
Zata qwace jikinta ya saketa a hankali Yana cewa”

Relax fita zanyi.

Juyawa yayi ya fice ya saka kayansa ya fice da sauri zuwa masallaci.

A palon kuwa Yana fitowa daga dakin ruqayyat na fitowa daga kicin data shigo ta kofar baya ta kicin din Dan fara aikace aikacensu dasuke farawa tun qarfe shida da rabi Amma yanayin ciki da Hanifa take dashi yanzu tun asuba take shigowa Dan hanifar tun asuba tana tashi saitaci abinci tayi sallah Takoma bacci kafin Kuma ayi breakfast da ita.

Tana ganinsa tayi saurin sauke Kai cikin tsananin girmamawa tana dakatawa daga inda take harsaida ya fice tukuna.

Ahankali ta gyara kanta tayi wanka da ruwan zafi sosai tasake shiga cikinsu sosai kafin tayi wankan Dole jikinta yayi Mata daidai tsamin jikin ya Dan tafi ta fito ahankali ta saka kayan data fara sawa jiyan ta cire riga da wando masu kauri tayi sallah ta koma gado ta kwanta sbd zazzafan zazzabin datake Jin Yana saukar Mata.

Qarfe shida da rabi ya fito shirye tsaf cikin Roberto cavalli jeans da white Armani rugbay shirt sai qatuwar tsaddadiyar rigar sanyi jacket daya Dora me tsayi sai qamshinsa ke tashi tuni aka fitarda motarda zata kaisa airport ya kalli hajjo cikin kulawa yayi Kama hannunta Kamar yanda yasaba cikin kulawa yace”

Allah ya sadamu da alkhairi,saina dawo Inshallah.

Dafa hannunsa tayi tace”

Allah yacigaba da yiwa rayuwarka albarka,
ALLAH ya tsare yakai lfy.

Kofar dakinta ya kalla kafin ya nufa kofar dakin ya tura yashiga yaganta kwance baccin wuya yayi gaba da ita ya qarasa ahankali ya sunkuya ya shafa fuskarta tareda Bata light kiss ya Ciro katinsa na banki daya tareda paper me daya rubuta password ya ajiye Mata gefen pillow ya fice.

Yana fitowa shida Hanifa suka fito zata rakosa mota a bakin motar suka tararda Hannah shirye cikin kayan sanyi itama sbd safiyace Sosai akwai sanyi zata rakasa airport Kamar yanda tasaba duk zuwansa
Suka Shige motar driver yaja suka fito motar mutanensa na waje suka Mara musu baya suka harba titi.

Bayan dawowar Hanifa ciki Kai tsaye dakin Naj ta nufa Dan ita Kam Hannah ke wasu abubuwan itakeji wa Naj din ba Dadi tunda Naj din Bata yiwa kanta fada da karatun ta nutsu ta amsa aurenta tun kafin ayi Mata sagegeduwa tun Bata ganewa komai a aurenba.

Bacci ta taddata tanayi ta qarasa bakin gadon tana tunanin kilama ko sallar asuba Bata tashi tayiba
Tana Kai hannu jikin Naj din taji yadauka wani irin zafi sosai.

Da sauri ta kalleta tana sake taba jikin nata da har wani Dan guntun Nishi takeyi cikin sauri da damuwa tace”

Naj,Naj kina fama da zazzabi me zafine Haka?

Bude idanuwanta tayi ahankali cikin siriryar murya tace”

Nasha magani idan nayi bacci Koda Zan tashi Inshallah ya sauka.

Da kulawa Hanifa tace”

Wane magani Kika Sha?
Bari naje na sanarwa Dr sa’id a waya.

Girgiza Kai tayi ahankali tana cewa”

No please karki fada Masa ki Bari nayi bacci Dana tashi Inshallah shikenan.

Badan tasoba tace”

Shikenan Bari na kwanta anan din mugani zuwa anjima idan kin tashi daga baccin.

Duk da tana cikin zafin zazzabi saidata yunqura ta tashi zaune tana cewa”

Aa kije karki damu Inshallah nafada Miki ba wani ciwo bane.

Kallonta Hanifan take da mamakin ganin tashinta zaune Kai tsaye tace”

Naji Amma dai Zan kwanta anan ko natafi dakina bazan iya bacci ba idan nabarki ahaka.

Riqo hannunta Naj tayi da sauri tana Dan rufe ido ta bude sbd zafin zazzabin ta qaqalo murmushin daya sake sawa Hanifa zargin boyon wani abun Naj keyi tace”

Hanifa dan Allah kije dakinki
Na Miki alqawarin Ina lafiya Inshallah.

Naj is there anything you’re not telling me??

Like what Hanifa?” Naj din tafada cikin Dan mamaki.

Hanifa tace”

Like abin dayasa bakyason na kwanta anan din sbd na tabbatarda ba sbd karna damu bane wannan din.

Ajiyar zuciya Naj ta sauke tana rintse ido sbd rashin sanin yanda zata Hana Hanifan kwanciya a gadon Dan duk Wanda yasan Jalal farin sani to Yana hawa gadon saiyasan jalal din ya kwana a gadon Dan kuwa daga bargon har zanin gadon da pillows din qamshin turarensa sukeyi.
Tasan Hanifa na hawa saitace qamshin JALAL takeji,
Me zatace idan ta tambayeta hakan?
Wannan wace irin masifa ce ta sameta ta kame kame,
Wlh dai angama da rayuwarta.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 31_*
Ahankali ta sake hannun Hanifar tana komawa ahankali ta kwanta sbd Jin hanifar tafara tunanin akwai dalilin dayasata batason ta zauna din tareda ita,
Har cikin zuciyarta tana Jin zafi da takaici tareda tsananin kunyar Hanifa ta Dan samu alama ta fahimta koma hasahsen wani Abu yafaru a dakin,bama dakin ba kawai a tsakaninta jalal din gabaki daya
Abune mafi kunya da tozarci gareta idan Hanifa tasan wani Abu gameda hakan,bazata taba Bari wani yasan wannan tsausayi da qaddarar data hau kantaba.

Ajiyar zuciya Hanifa ta sake cikin kulawa ta tako ta matso gaban gadon ahankali ta gyara Mata rufarta tana cewa”

Shikenan kiyi baccin zanje Nima na kwanta Dana tashi zandawo na dubaki.

Gyada Kai tayi ahankali tana rufe idanuwanta tareda gyara kwanciyar kanta a pillow.
Sai dataga fitar Hanifan ta saki Dan qaramin numfashi tana sake komawa baccinta dayake idanuwanta har lokacin.

Bacci tayi Sosai Bata fitoba Wanda yasa hajjo nacewa zancen tabbas Naj ba lafiya take ba Dan Haka Babu sanin Naj din tasa Hanifa takira Dr sa’id Wanda baizo gidan ba sai yamma bayan yataso daga asibiti.

Dagashi sai ita ya Mata Yan tambayoyi tabasa amsa a Dan gaggajarce sbd son qin bada hanyar dazata saka koshi ya Dan gane wani abun
Shima Bai wani zurfafaba sbd gane zazzabin tun ranarda Marshal yakirasa acan gidansane Bai Gama sakinta musamman idan sake kusantarta akai Wanda hakan ke nuni da Bata taba saduwa da kowane namijiba hakama Bata budeba ta hanyar tsallake tsallake da yawace yawace Wanda yake ragewa budurcin mace qarfi shiyasa take wannan wahalar Dan Haka Bai zurfafa tambayaba ya Bata maganin dazasu taimaka Mata nasu zazzabi da pain relief ya miqe Yana Dan kallonta yace”

Inshallah zaki warware zuwa gobe ko jibi idanma dai kinji bakyajin daidai har lokacin Zaki iya kirana kokuma ki sameni asibiti saimuyi waeu dube duben mugani Amma dai Inshallah ma Zaki warware din zuwa gobe.

Hajjo takira Masa ta fito tana kallonsa tana qarasowa tana cewa”

Dr sa’id zaka tafi?
Kagama dubatan?
Bansan menene wannan zazzabin sanyin dayaqi sakinta ba tun dawowarta na fahimci batada lafiya Amma tace sanyi ne,
Kuma anyi maganin sanyin kwana biyu yau Kuma abin yadawo.

Dan murmushi yayi Yana cewa”

Nabata magana Inshallah zata warware zuwa gobe
Ba wani ciwon daga hankali bane zazzabine kawai sai gabobi da zasuyi ciwo dama, ALLAH ya Bata lafiya Zan tafi hajjo idan kwana biyu zazzabin Bai tafiba nace ta sameni asibiti.

Ok Inshallah Dr sa’id,
Agaida gidan dasu hajiya.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Zasu shi Inshallah.

Ficewa yayi daidai fitowar Hanifa data fito daga kicin tagama ciyo wainar fulawar dataji kwai wadda umma ta Aiko Mata,ta qaraso palon ta zauna gefen Hanifa tana kwadawa ruqayyat Kiran takawowa Naj Naman Hantar datasa ta dafa Mata dazu tareda ruwa Tash magani.

A gabanta ta ajiye Mata Kan table Takoma takawo Mata ruwa marasa sanyi sosai Dan kaidar Naj dinne Bata Shan ruwan sanyi sosai.

Ahankali takeci sbd ya ‘dan yimata Dadi dan yajin da ya ‘danyi sbd bakinta da baida apatite na zazzabin,
Taci sosai Saida cikinta yacika Tasha maganin da Dr sa’id yabata tasake dorawa da Ginger tea me zafi
Ahankali taji jikinta ya Dan Yi Mata Dadi tasamu kuzari dakuma zazzabin daya sauka.

Ahankali ta kalli ruqayyat dake dauke kayan data Gama cin abincin tace”

Ruqayyat idan kinkai kije dakina ki dauke zanin gadon Dana cire Yana Nan Kan kujera kikai laundry.

Yes Ma.” Ruqayyat din ta furta tana Kai kayan kicin tadawo ta nufa dakin Naj din ta kwaso zanin gadon ta fito.

Miqewa hajjo tayi ta nufa hanyar dakinta sbd kiran sallar magriba da aka fara daidai ruqayyat na kawowa da kayan zata wuce Hanifa tadawo daga dakinta dataje dauko Abu ruqayyat na giftawa gabanta ta kalleta cikin mamaki tace”

Ruqayyat wannan beddings din Marshal ne?me sukeyi a hannunki?
Ta Yaya sukazo hannunki?” Taqarasa fada tana sake shaqar qamshin Dake tashi ajikinsu kamar yanzu ya kwanta akai.

Hajjo ma dakatawa tayi tana kallon ruqayyat Jin abinda Hanifa ta fada Dan dai tasan Babu me shiga sashen nasa a taqaicema namijine me aikinsa dayake Masa gyaran sashensa da wankin kayan zanin gadonsa da komaiba.

Da sauri cikin tsananin tsoro da girmamawa ruqayyat ta kalli Hanifa tace”

Anty wannan da dakin Ma’am ne tace akai laundry ba na Sir Marshal bane.

Rintse ido Naj tayi zuciyarta na Shiga takaici wannan al’amari gashi ba damar tasa Baki tabada kanta dan Haka Tai shiru tana fatan ruqayyat din ta wuce ga hajjo ma datake saurarensu sbd Jin sunan Marshal Dan gskia ba’a Wasa da harkan Marshal ko bayanan ba’a yin abinda akasan bayaso.

Qamshin turensa ne yake tashi a kayan Nan sosai kin tabbata Wanda Naj tace ki dauko ne a dakinta,
Bafa sashensa tace kijeba a dakinta take nufi……..

Da sauri ruqayyat tana sauke Kai tace”

A dakinta na dauko wlh
Acan ya kwana shine zanin yake qamshin,
Wlh banje sashensaba a dakin Ma’am na dauko.

Wata irin wuta Naj ta dauke zaune agurin wani zafi na huro Mata tako Ina ta dago ahankali zuciyarta na gaurayuwa da daci ta kalli inda hajjo take taga Bata gurin Dan tunda taji Ana neman tada sallah ta shigewarta Bata tsaya Jin zancenba tunda ga Hanifa.

Rufe ido tayi wani Dan sauki saukinda baida wani amfani na shigarta ganin hajjo bataji me ruqayyat din tafadaba
Taqi waiwayowa ta kalli Hanifa datai Kamar bataji me ruqayyat din taceba duk da ta girgiza matuqa dajin zancen ruqayyat din ta fuske tana cewa”

Wuce kije aikin gabanki kardai ki kuskura Koda aike kije sashensaba batareda iziniba.

Ruqayyat na barin garin hanifar Bata waiwayoba tayi dakinta tana cewa”

Naj Bari nayi sallah kafin na zauna.

Rufe ido Naj tayi tana dafe Kai cikin tsananin hali,gabaki daya zuciyarta ta cike da damuwa da bacin Rai tana zamanta cikin kwanciyar hankali da rufin asiri kame kame da boye boyen bacin Rai yaganta,wane tashin hankali da damuwa ne wannan¿Bazata iya cigaba a hakaba kunya da baqin ciki zasu iya illatata kawai zata daukarwa abin mataki wlh kanta bazai iya daukan wannan ba.

Miqewa tayi ta nufa daki a sanyaye itama tayi alwala tayi sallah tana idarwa ta miqe ta nufi gaban madubi sbd abinda ta hango.
Sai alokacin idanuwanta suka gane Mata katin bankin Dake daukeda sunansa JALALUDDEEN ALFA da wayarta a gefe aje.
Wani sabon mamakinsane ya kamata ta kalli takardar dake daukeda pin na katin ta yamutsa fuska tana rintse ido tareda dafe goshinta sbd kanta dake sake daukan ciwon haukatata da komai nasa ke Naman yi,
Me hakan ke nufi daya bar Mata katinsa?
Ya dauki nauyintane da dawainiyarta sbd ya karbi auren kokuma zai karba kuwa matsayinsa Miji yake son nunawa?to ita Bata karba ba Kuma batajin zata iya Dan Haka ta hada katin da paper din ta nufi wardrobe ta bude safebox dinta ta bude ta jefa ciki ta rufe tareda rufe wardrobe din gaba daya tadawo ta zauna da wayarta a hannu tana kunnawa saiga massages suna shigowa kusan duk na Sarah ne saina Abbas Wanda ko budesu bataiba ta gogesu tana Danna Kiran Sarah.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 32_*
Da daddaren ta daurewa tayi ta fito sbd nuna taji sauki Dan kada hajjon tacigaba da matsa cewan Bata warkeba Azo Ana tsananta bincikawa.

Suna cin abinci Hannah ta shigo ko dining room din Bata qaraso ba hangosu sunacin abinci tayi zamanta Palo tana jiran su qarasa wasu kayan zaqine takawowa Hanifa tsaraban shopping dataje.

Koda suka Gama a palon suka zauna fira sama sama Banda hajjo data shige qaramin palonta dake hanyar gefen dining room suna magana da Dad Alfa dayazo gaisheta kamar yanda yasaba matuqar Yana gari kullum saiyazo gaisheta.

Ganin wani irin dogon surutu da Hannah ke janyowa Wanda duk rabi na firar Marshal ce Dan nuna irin kusanci da soyayyar datake tsakaninta dashi,
Hanifa sai basar da zancen take sbd Hannah ta barshi Dan Naj dake zaune Amma sai sake jansa takeyi cikin salo da nuna isar matsayinta agurinsa.

Miqewa Naj tayi tabar gurin sbd surutun ya isheta musamman indai akansa ne Bata buqatan ji ta nufi hanyar dakinta tana musu Saida safe tashige.

Tana shigewa Hannah ta saki murmushi tana sauya zancen da cewa”

My in-law kinyi waya da Marshal ya Isa lafiya ko?sbd nakasa samunsa tun dazu,bazan iya kwanciyar hankali ba sainajisa,
Please idan kunyi waya ki sanar dashi inata neman wayarsa, please.

Ya Isa lafiya inshallah saidai Bai Isa qarasawa gidaba bare ya huta harya kunna wayar sai zuwa gobe Inshallah,idan ya Kira Zan sanar Masa Inshallah..Zanje na kwanta ko,Saida safe.
Miqewa tayi ta bar Hannah din a zaune ta nufi dakinta sbd tasan idan ba tashi tayiba Hannah Bata gajiya da magana.
Bin bayanta Hannah tayi da kallo tana Dan yamutsa fuska itama sbd tamafita Jin gundura dasu dukan dannewa kawai takeyi.
Miqewa tayi itama ta fice daga sashen.

Washe gari ba laifi ta tashi lafiya kalau sai Dan qananun abinda baza’a tasaba Dan hakama tana tashi wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na lace me tsada Mara nauyi ta fito sukai breakfast daga Nan sukai Shirin zuwa asibiti scanning din Hanifa da akeyi akai akai.
Koda suka Isa asibiti Dr sa’id na jiransu Dan Haka Basu wani Bata lokaci ba suka baro.
Driver ne yakaisu sbd Hanifa Isma’eel da Marshal sun hanata tuqi itama Naj din sbd Bata Gama warwarewaba hajjo tace itama Kar tayi tuqin.
Driver daga waje yayi parking daidai kofar shiga gidansu Naj din suka fito Kai tsaye suka shige gidansu Naj din kafin driver ya shige da motar can gida.

Tun a hanyar qarasawa cikin gidan suka hadu da Asmau zata fita ta qaraso tana cewa”

Anty Naj Ina wuni?gurinki fa zani yanzu,
Ta kalli Hanifa tana cewa”
Anty Hanifa Ina wuni?
Ya hajjo?

Lafiya kalau Asmau,ya karatu?Ina Umma habiba tana ciki?

Eh.

Wucewa Hanifa tayi Gama ta nufi sashen umma habiban suka gaisa kafin ta wuce sashen ummansu acan ta tadda Dadah zaune tsakar gida tana Shan radio da qatuwar sabuwar butarta a gefe sauraron Shirin hantsi.

Qarasowa tayi tana cewa”

Dadah hantsi akesha Bari nazo na tayaki Sha idan Zaki sanmun goronki.

Kallon Hanifan Dadah tayi tana washe Baki cikin farin cikin ganin cikinta daya fito tace”

Goro Kam Zan sanmiki kici Amma karki zauna Nan iska yayi yawa Zaki kwasa sanyi tafi gurin ummanku nasan dama can kikai gulmar na sanmiki goron ne yasa za’ai zaman Shan hantsi Dani.

Miqa Mata qaramin farin goro tayi tana cewa”

Allah ya nunamun NAJMA tazo tambayar goron Nan ranar nayi kwanan niyar azumin godiya ga Allah.

Najma dake qarasowa taji abinda Dadahn tace ta kame fuska matuqa rashin Jin dadin zancen da qyamarsa na bayyana fili a fuskarta tafasa zama gefen Dadahn ta gaidata kawai ta wuce dakin ummanta
Dadah tabita da fadin”

Duk mugun halinki sai Naga ‘yayanki da yardar Allah,
Mara godiyar Allah.

Daka tawa tayi ahankali ta waiwayo zatai magana gabaki daya ranta ba Dadi Anty Amina data fito daga dakinta ta riqo hannunta tana girgiza Mata alamar kada tafada koma menene tayi niyar fada.

Juyawa sukai suka nufa dakin ummansu dake zaune dakinta tana hada khumras masu shegen qamshi da kame jiki Kamar na _*YERWA INCENSE*_ tana jinsu takuma San da Amina Bata Hana Naj din mgn ba zata iya fadar abinda Dadah yau zata Hana uban kowa bacci a gidan sbd zaunarda Dattijo zatayi ta hada masu gurminda zai fatattaki kowa da bacin Rai.
Naj tareda Aminar ne suka shigo kafin Hanifa dake bayansu suka zauna Naj na cewa”

Umma barka da aiki,
Ina wuni?ya gidan?

Amsawa umman tayi batareda ta kalletaba sbd A qule take da ita akan wannan taurin Kan da muguwar zuciyar sbd Hanifa kawai ta kyaleta Dan batason tayi Mata fadan rashin son datake nunawa auren jalal a gaban Hanifa Dan kuwa tasan ko Dadah sbd Hanifan na gidan ta taqaita tata masifar.

Kusada umman Hanifa ta zauna tana daukar kwalban khumrah daya tana shinshinawa tace”

Umma wannan khumrahn wankane ko?
Eh Hanifa,Yaya jiki jikin?
Ankai Miki wainarki Kan lokaci kuwa?

Eh umma naci kafin mufita anjima alalan manja nakeso umma ko gobe da safe ruqayyat Basu iyaba idan sunyi qarfi yake.

Anjima Inshallah Zainab zata kawo Miki yanda kikesonta.

Yawwa Ngd ummana.

Ganin yanda umman fuskarta ba asakeba da alama ranta bace yake akan Naj hakama anty Amina ma Babu wani dogon magana ita kanta Naj din duk tayi wani iri ranta ba Dadi itama kowa sai kame kamen yaqen Dole yake Kuma duk tasan sbd itane ba’ason tada maganar Dan kada asa taji ba Dadi saidai ita Bata damu sosai da duk qin auren da Naj keyina sbd tasan Dole bazata iya karban aure irin wannan lokaci daya ba tunda har bata fitina ko fada akan auren ko ahakan ai ba laifi tasan wata Rana zata Aminta da auren.
Kallon umma da anty Amina tayi cikin nutsuwa da sanyin murya tace”

Umma kuyi hakuri ku sake bawa Naj lokaci Inshallah komai zai daidaita tunda na tabbatarda itama kasa amsar abin ne Kai tsaye yasa takejin bazata iyaba Amma ai komai lokaci yakeso.

Da kallon takaici umma tabi Naj din hakurinta na qarewa tace”

Kinji abin datake fada ko?
Fahimtarki takeso ayi abaki lokaci akan abinda kece aka rufawa asiri da kuwa da Bai aurekinba da yanzu kinanan kina zaman wulaqanci da matsuwa agidan wani,
Shine namiji shine yakeda damar cewa bayaso sbd shine me riqe auren Amma kece kike rainin wayon da kikaga dama sbd sun nuna suna sonki.

Dagowa Naj tayi da idanuwanta dasukai jajir suna neman cikowa da hawaye tace”

Umma…..

Katseta anty Amina tayi da cewa”

Naj bakida gskia ko kadan
Kuma wallahi kunya kike bani da wannan dabi’ar Taki sbd banyi tunanin ko Dan su hajjo ba ki nunawa wannan auren tsana haka,
Menene matsalarki?

Kukan baqin cikin datake dannewane tsawon lokaci ya kufce Mata tana cewa”

Wallahi bazan iyaba,
Nakasa,
Shin meyasa da aka tashi taimakon nawaba Amin taimakon da akasan Zan iya dauka,
Zuciyata zafi take,
Ciwo take,radadin hakan nakeji Dan Allah Araba wannan auren koba komai Ni bazan iya da Wanda yakeda wadda yakeso ba…..

Au bayan girman da kike ganin kinmasa yanzu Kuma hadda wadda yakeso tazama dalili kenan?

Sake fashewa tayi da wani kukan tana cewa”

Ni koma menene Dan Allah Araba auren Nan…..

Wani irin salatin Dadah sukaji data shigo tana kallon Najman bakinta na rawa gurin magana saikuma kawai ta fashe da kuka tana cewa”

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun
Wace masifar ce zata kunno Kai rayuwarki Najma,
Wace tsanace kikewa wannan auren dako shekara daya baiyiba za’a kidawo zawarci,
Najma Dan Allah ki duba tsufana da mutuncin Dattijo ki hakura ki cirewa ranki masifa ki runguma aurenki….

Irin kukan da Najma da Dadah keyi yasa umman sake Shiga wata mummunar damuwa da baqin ciki ta tashi cikin tsananin fushi tayi Kan Naj din Hanifa da duk hankalinta itama ya tashi ta tashi da sauri ta janye Naj din tana kasa mgna sbd ganin cikin qanqanin lokaci Abu yazama tashin hankali.

Ba shiri Dadah tasa aka Kira Mata Dattijo tun kafin ya qaraso sashen yake jiyo fadan umma da ranta yayi mummunan baci qololuwa dakuma kukan dadah daya Gama daga hankalin kowa.

Anty Amina ce tayi Masa bayanin abin Dake faruwa tana dasa Aya ya kalli Naj cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin daya rasa abin dazai Mata
Tana durqushe gefe har lokacin kuka takeyi me qarfi na rashin sanin mafitar abindayake cin ranta.

Kallon umma yayi cikin fushi da bacin Rai me tsanani yace”

Najma dai takai matakinda tafi qarfin umarnina Dan Haka ke dakika haifeta bakifi qarfin umarnin nawaba saiki shirya kayanki dan wallahi tallahi tana dawowa gidan Nan da sunan aurenta ya mutu bazata zaunaba tare zaku bar gidan nan.

Kallonsa umman tayi cikin baqin cikin koyaushe yayanta sukai laifi aurentane yake barazanar rawa,
Ta maida kallonta kan Najma tace”

Kinji ai saikije ki hado kayan naki mubi duniya tunda shine sakamakon dazaki bani.

Dadah cikin kula tace”

Najma Dan Allah ki dubi girman Allah kiyi hkr ki dangana wlh na zubarda makaman yaqina na yarda anmiki ba daidaiba ki dangana ki runguma aurenki wlh gaba Zakiyi farin ciki da yardar Allah.

Cikin fushi Dattijo yace”
Ki daina rarrashinta Dadah wlh ko ta tashi ta fice Kona nema mugun ice nai Mata dukan da bazata iya komawa da qafafuwantaba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

 

*_DM 33_*
Janyeta anty Amina da Hanifa sukayi ta suna sake bawa su dattijon da Umma hakuri Dadah kuwa kamata tayi tayi dakinta da ita ta zaunar tana kallonta tace”

Ki dauka dangana ‘yar Nan kibi umarnin mahaifinki da mahaifiyarki tunda dai kinsan bazamu zabar Miki mugun abu ba,
Banda abinki Najma kinyi aurenki kina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa meyafi hakan,
Dan shekarun da Kika basa waye yasani tunda idan aka kalleku ma sai adauka sa’an babban yayanki ne,
Shin menene illar auren qaninka tunda?
Shin kin manta Nana Khadija ko data aura Manzon Allah ya girmesa da shekarun dasukafi Wanda kikaiwa naki mijin ita datafi daraja ma ko farin ciki da wannan koyin bazakiyiba ki faranta Mana?
Mu idan bakya Yi danmu munada fada da takura to kiyi Dan hajjo da Alfa Mana,ga Hanifa Nan haryanxu Bata ganin laifinki tana bayanki sbd irin qaunar datake miki
Dan Allah kiyi hkr kiyi zamanki gidan aurenki tunda har daga mijin harsu hajjon sun amincew zamanki ba takura sai kinji kin samu nutsuwa da auren.

Haka Dadah ta ringa Bata rarrashi da maganganu sbd ganin fadan ba inda zai kaisu saiga tone tone har Azo abata goma biyar Bata gyaru Dan ita da wannan aure ya mutu gwara aje ahakan tana zaune gurin hajjo indai da auren yafi musu zasui jira har Allah yasa auren yazama Kamar kowanne auren.

A dakin Dadah tayi zamanta saidata nutsu kafin Dadahn da kanta ta rakasu har palon hajjo suka Kuma taruwa suka rarrasheta kafin Dadah ta tafi
Har dare hajjo da hanifa na tarairayarta Dan tasake Haka suka Kwana
Ko Dad Alfa da kansa Saida yakirata suka sake zama da hajjo suka ringa rarrashinta cikin kulawa hartazo tanajin kunyar abin qarshe Dole ta sake Dan ganin yanda duk suketa sake lallabata shiyasa ta sake sosai ta koma bakin aikinta,

Hannah da mum Malika Koda sukaji abindaya faru Dadi Kamar me musamman suka sake maida himma gurin ganin auren Hannah da MARSHAL din ya tabbata,
Duk yanda Hannah taso fadawa marshal din rigimar Bata samu damaba sbd baida lokacinta busy yake sosai gashi yanata tafiye tafiye acan din Dole ta hakura harta samu lokacinda zata fada Masa.

Umma da Dattijo Basu duk da zancen yayi kwanaki sosai Basu daina fushi da itaba sama sama suke amsa gaisuwarta idan tashigo gidan Dadah ce dai take lallabata dataga fushin ba yayi sai anty Amina daketa aikin dawainiya da duk abinda Hanifa keso sbd cikinta daya fito sosai yanzu.

Takoma aikinta gadan gadan sai yamma take dawowa musamman da ayyuka sukai Mata yawa na ‘yar rigimar da ake wadda ta tarar Marshal ya fige Abbas daga ALFAs Amma sauran shareholders din Basu yardaba shikuma sbd yafi kowa hannun jari aciki yace hukuncinsa kenan.
Rigimar tasa ayyuka sun Mata yawa sbd dukkanin ayyukan office din president na companyn yadawo office dinta tunda Abbas an dakatar dashi say angama rikicin gashi Marshal din yatafiyarsa saiya dawo Kuma.

Da mamakin wannan qarfin halin nasa take aikin office din kullum sbd ayyukan sun Mata yawa ko yawon meetings yasa har wata Yar rama ta taso mata.
Saidatai wata daya da sati biyu tana fama da ayyuka kafin ayyukan suka Dan daidaita tafara samun kanta har tana dawowa gida da wuri.

Yau tunda tazo office din batai komaiba sbd jiri datake gani tun jiyan tafara jinsa yanayi Yana tafiya.

Dafe kanta tayi tana Dan rufe ido ta bude ahankali ta dago tana kallon Sarah data shigo office din ta bude Baki ahankali tace”

Sarah please bani ruwa me sanyi nasha.

Kallonta Sarah tayi da mamaki tace”

Me sanyi ko me Dan sanyi kadan?

Batareda ta dagoba tace”

Me sanyi sosai.

Da mamakin Sarah takuma kallonta sanin Bata Shan ruwan sanyi zatai mgn saikuma ta fasa ta nufa fridge ta bude ta dauko Mata ruwan roba masu sanyi sosai ta kawo Mata ta miqa Mata.

Karba tayi ta bude Kai tsaye takai bakinta tana Sha Sarah na kallonta da mamaki.

Ajiyar zuciya kadan ta sauke bayan tagama sha ta ajiye sauran ruwan tana cewa”

Sarah zanje gida yanzu kaina na ciwo Ina buqatan hutawa ko zai sake.

Tare suka fito da Sarah din itace take tuqin takaita gida suka nufa cikin gidan tare.

A Palo suka tararda Hanifa zaune tareda anty Amina data kawo Mata sabuwar Awarar da Umma ta Aiko Mata wadda akaiwa sauce din kayan miya dasu carrots da kwai.

Kallo daya Naj tayiwa Awarar taji tana son ci abinda Bata taba yiba shine ko dakinta Bata shigaba ta qaraso gefen Hanifan ta zauna ahankali tana cewa”

Yunwa nakeji sosai har kaina Yana ciwo.
Ta dauka plate tana miqawa Hanifan tana cewa”

Samun zanci.

Zuba Mata Hanifa tayi tana cewa”

Lallai yau ‘yar gaban goshin hajjo yunwa takeji tunda ko daki bazaki iya qarasawaba.

Batace kalaba saidataci Awarar a bakinta taji kanta dake sarawa ya daina ta dago ta kalli Hanifan ahankali tace”

Thanks.

Sai alokacin ta kalla anty Amina tana cigaba daci suna gaisawa anty Amina na kallonta dakyau cikin nazari tace”

Naj bakida lafiyane Naga kamar kin fada.

Kallonta Hanifa tayi tana cewa”

Ramar aikice Amma duk da hakan Ni Banga ramarba haske dai Naga tayi sosai kodai bakida jini ne Naj?” Taqarasa fada tana Dan zare ido.

Batareda ta dagoba tace”

Lafiyata kalau stress ne kawai amma zanshiga hutu sbd komai yakoma yanda yake a office din Inshallah.

Saidata qoshi kafin ta qarasa dakinta tabarsu a palon ta tube ta shiga toilet wanka.
Sai datai wankan taji jikinta ya sake sosai ta fito daureda towel ta nufa jikin mirror kenan taji wayarta na ringing ta juyo ta nufa wayar dake Kan gado ta dauka sai kawai taga No din qasar waje destination id dinta ya nuna Mata United States of America.

Kai tsaye ta dauka batareda ta tsaye tantance kiranba Wanda yake Vidcall sai ganin mutum tayi ya bayyana kan screen din wayarta Yana zaune cikin lafiyayyan palonsa sanyeda uniform dinsa na sojojin America dasukai Masa wani irin kyau uwa uba hutu da nutsuwar daya samu ta bayyana ataredashi Ya zuba Mata fararen idanuwansa har zuwa kirjinta dake daureda towel Tsananin hasken data qara yasashi sake zuba Mata idanuwansa,
wannan ne Karo na farko data gansa cikin uniform ta dauke kainta ganin irin kallon dayake Mata sai alokacin ta tuna da towel ne jikinta ta kashe wayar tana jefarwa Kan gado ta tafi tahau shirinta.

Baccin maraice yayi sai magriba ta tashi ta fito bayan tayi sallar magriba sbd yunwa me tsanani datake ji.
Kicin ta nufa sbd sanin lokacin cin abincin Daren baiyiba tasan Hanifa na kicin sbd Bata jimawa bataci ba shiyasa take zuwa kicin taci ta koshi Kuma ahau dining aci da ita.

Tana Shiga kicin din ba kowa sai ruqayyat dake qarasa aikin abincin Daren ta nufa fridge ta bude ta dauko milk drink tasha sosai ta dauko cake guda hudu ta cinye ta qara da apple biyu kafin taji ta dan samu nutsuwa ta fito suna hadewa da Hanifa dazata Shiga kicin din neman abinda zataci itama tace”

Naj yunwa nakeji cake zanci da Madara tunda kin cunyemun awarar da Umma takawo min dazu.

Batace komaiba Takoma Palo ta zauna tana duba wayarta tana jiran agama abincin akawo dining.

Sallar ishai taje tayi tana fitowa hajjo na fitowa suka dunguma dining Hanifa tuni ta riga kowa Isa.

Naj din ita tazubawa hajjo abinci takawo Mata ruwa da komai ta kalli Hanifa da Bata harta zuba abincinta tafara kaiwa Baki.

Zama tayi itama tareda zubawa ta zauna suna binta da ido ta dago ta kallesu ganin irin kallon dasukewa abincinta yasata kallon abincin sai alokacin taga ta zuba da yawa ba kamar yanda ta Saba ba dama kwanakin gabaki daya cin abincinta ya sauya ta Dan fuske tana cewa”

Yunwa nakeji sosai duk yau banci wani abincin kirkiba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

 

*_DM 34_*
Hajjo kallon abincin takuma Yi kafin ta kalli Naj din cikin kulawa da nutsuwa tace”

Najma ki daina zama da yunwa Haka sbd zata iya Miki illa yanzu wannan abincin zai iya qulle Miki ciki,Kisha tea kafin ki ci abincin cikinki ya sake tukuna.
Kallon Hanifa tayi tana cewa”

Miqa Mata tea din ta zuba ta Sha.

Qaramin flask din dake cikeda black tea dinda yaji kayan qamshi da hadinsu lemon da Zuma wanda koyaushe dashi ake jere abincin safe Rana da dare Wanda qaidar hajjo ne wadda ta Saba da Shansa Kuma al’ada da dabi’ar Shan nasa ya Kama duk Wanda yake gidan ko baqi akai idan za’a kawo musu ruwa sai an tambayesa ko akawo Masa tea din.

Miqawa Naj Hanifa tayi tana cewa”

Kin riga kinfara cin abincin kinsha tea din daga baya” ta aje tana daukan spoon tafara cin nata abincin.

Kamar yanda tasaba cin abinci a natse ta cinye abincin tas tasha ruwa kadan ta zuba tea din Wanda kurba daya Tai Masa ta ajiye tana cewa Alhmdlh ahankali.

Kallonta hajjo tayi tana sake cewa”

Idan Zaki ringa zama da yunwa irin Haka Zaki sa ciwofa ya kamaki karki sake hakan daga yau.

Guntun murmushi tasaki ahankali tana kallon Hanifa da har lokacin abincin takeci tace”

Yaune kawai hakan bazai Kara faruwa Inshallah hajjo.

Barin gurin tayi ahankali tanajin nutsuwarta ta dawo ta dawo palo ta zauna sai alokacin ta dauka wayarta tana dubawa har Hanifa da hajjon suka Gama suka baro dining din hajjo tayi dakinta sbd qafafunta da ruqayyat zata gasa Mata da ruwan dumi.
Hanifa Kuma gefenta ta zauna tana daukan tata wayar itama tace”

Naj gobe umma zata faramun sabon gyara Isma’eel zai dawo next week fa.

Juyowa Naj din tayi ta kalleta tana sake maida hankali kan abinda take dubawa a wayar tace”

Shine kike Zillo Haka?
Cemasa zanyi yayi zamansa sai zaki haihu yadawo muga qarshen gyaran.

Dariya Hanifan tasake tana cewa”

Zillo ma ai kadan ne zille zille zanyi ma idan ya dawo tunda bansan kalar zille zillen da matan duniya ke can suna Masa ba tunda bana kusa Dana Haka idan yazo nawa lokacin ne nayi haukama idan Zan iya,
Hannah kina ganin duk ranarda tasamu auren Marshal wannan rawar kan datake ai uwar ubansa zamu gani akan wannan datakeyi Yan…….

Hade sauran maganar tayi tana rufe bakinta Jin Naj din tayi shiru sbd gabaki daya ta manta da Naj take maganar,ta Dan kalli fuskar Naj din data juyo itama ta kalleta tareda sake wani irin guntun murmushi tana basarwa da cewa”

Ashe kinada qarfin yiwa miji zille zillen Kike makure Mana fuska ki nade muna dawainiya da matarsa.

Haba sirikita idan bakiyi hidima daniba waye zaiyi….

Dan kame fuska Naj din tayi Hanifan tasaki dariya tana cewa”

Sorry my Naj.

Wayar Hanifan ce tayi ringing ta waiwayo tana kallon wayar ta maida kallonta kan Naj da kallo daya tayiwa wayar taga sunan me Kira ta dauke tana maida hankali akan tata wayar.

Dauka Hanifa tayi cikin murmushin ganin video call ne ta dauka Kai tsaye tana cewa”

Hey Deen Marshal,ya kake?

Kallonta yayi Yana Dan gyara crossing qafafunsa da yayi wayar na ajiye saiti dashi a gabansa Yana zaune acikin office dinsa sbd sun safiyace har hantsi ma yafara,
Ya bude Baki ahankali yace”

Lafiya kalau,ya baby?
Kinje scanning din kuwa?
Nayi mgna da Dr sa’id,ki turamun scanning din I want to see it.

Ok,ok,Baby is fine,and iam fine also” satar kallon Naj tayi tana cewa”

And Naj ma tana Lafiya.

Jingina yayi baya Yana folding hannuwansa fararen idanuwansa akan wayar cikin muryarsa data Gama Isa cikin kunnuwanta yace”

Bata wayan.

Kallonsa Hanifa tayi tana Dan kame fuska da murmushi akan fuskarta tace”

JALAL karka damu qawata da wannan kamewan naka,
Wani irin kallo yayi Maya Wanda yasata harararsa tana cewa”

Kome ka zama karka manta dai Ni yayarkace.

Dan rufe idanuwansa yayi ya bude da wata muryar yace”

Matan auren dake gefenki Zaki bawa wayar.

Naj dake zaune duk takasa ma qarasa abinda take a waya sbd zancen a bayyane yake fita ta miqe zata bar gurin lokacinda Hanifa ke kokarin miqa Mata wayar Kai tsaye taji muryarsa ba Wasa aciki yace”

Kika bar gurin Zakiyi mamakin hukuncin hakan.

Dakatawa tayi tareda waiwayowa ta kallesa ta cikin wayar zatai magana saita kasa ta fuske tana kokarin wucewa tabar Hanifa ta riqota tareda maidata zaune tana cewa”

Dawo ki zauna Bari Ni natashi kicin zanima.

Miqewa tayi tabar gurin bayan ta aje wayar saiti da Naj din.

Dauke Kai Naj din tayi tana cigaba da duba wayarta tanajin idanuwansa na yawo akanta duk sai hakan yasata kasa nutsuwa ta dago ahankali fuskarta a hade suka hada idanuwa ta dauke Kai kafin tayi wani motsi a natse yace”

You look sexy in that dress.

Da wani irin yanayi na kunya da takaicin kayan dake jikin nata ta motsa zata kashe wayar yasakar Mata wani kallon daya sata hadiye wani yawun dake neman sarqeta yace”

Ok goodnight jeki kwanta.

Kashe wayar yayi sai alokacin ta sake daure fuska tana dauke idanuwanta daga gefen wayar tana kallon kayan jikinta da gaban rigar take a Dan bude Ana hango tsakiyar kirjinta da condom bra Dinta ta rabasu ta miqe tabar gurin ta nufa dakinta.
Tana shiga tubewa tayi Bata sake wankaba sbd Dan sanyi datakeji ta saka kayan bacci tayi kwanciyarta take bacci ya dauketa.

Washe gari sallar asuba kawai ta Gama ta fito taje kitchen Tasha tea me zafi tana lumshe ido sbd rashin shansa a Daren jiyan yasa takejin yunwa Kamar hakan.

Da cake Tasha tea din ruqayyat data fara ayyukanta tana binta da satar kallo sbd sanin gabaki daya Naj din batada ciye ciyen abinci qaidarta taci lokacin cin abinci tagama takuma shikenan.
Har tagama tafito Hanifa Bata zoba Dan Haka Takoma daki ta kwanta wani sabon baccin me nauyi yakuma dauketa.

Sai qarfe goma da mintuna ta farka tana kallon agogo ta saki wani qaramin numfashi tana dafe Kai sbd ganin irin lattin datai Wanda Bata Saba lattin ba irin Haka.
Zuro qafafunta tayi ta sauko gadon tana nufar toilet Kai tsaye tayo wanka ta fito.

Babu Bata lokaci ta shirya cikin doguwar jallabiya Maroon da qaramin mayafin data nade kanta dashi Wanda kalar abayar ta fitarda tsananin hasken data qara ta fito qamshin khumrah kadan Yana Dan tashi a jikinta..

Kai tsaye gurin hajjo dake zaune palon ta qarasa ta zauna gefenta cikin kulawa tace”

Good morning hajjo, muntashi lafiya?

Kallonta hajjo tayi cikin kulawa tana cewa”

Lfy kalau,yau kinyi lattine?

Eh,zanci abinci na wuce.

Dining ta nufa ta zauna tareda Kiran ruqayyat takawo Mata ruwan sanyi tafara cin abincin kenan saiga Zainab din Anty Amina tashigo da sallama ruqayyat data bude Mata kofar palon tana biyeda ita zuwa dining din.

Anty Naj Ina kwana?

Lafiya kalau zainab yasu umma da anty Amina suka tashi da Dadah?

Lafiya kalau,ga wainar Anty Hanifa Nan Zan koma aikin su daughnuts mukeyi da ummana da aka kawo Mata na wani bikin idan Anty Hanifa ta fito Ina Mata Ina kwana.

Juyawa tayi ta qarasa gurin hajjo tana gaidata har hajjon na Bata sako gurin umma kafin ta wuce.

Qamshin wainar ya ringa Shiga hancinta Amma dayake Sam waina Bata dametaba saita dauke Kai tana daukan hakan amatsayin rashin damuwa da bataiba da waina
Amma qamshin sai sake Shiga hancinta yakeyi Yana sata Jin wani iri ba shiri ta miqe tabar gurin tana goge bakinta da yawunta keyi Kamar zasu tsinke Dan Haka Kai tsaye handbag dinta ta dauka tana cewa”

Hajjo na tafi office saina dawo.

Ok ki kula,saikin dawo.

Sai data Shiga motarta ta sauke wata irin Ajiyar zuciya tana sauke numfashi ahankali.

Sai data samu nutsuwa kafin ta tayarda motar ta fice daga gidan ta nufi office.

Isarta office taji abinda take no yakuma taso Mata da qyar ta daure ta iya kaiwa office dinta tana Shiga ta nufa toilet da sauri wani irin amai me qarfi da wahala na kufce Mata.

Da sauri Sarah tabiyo bayanta ganin irin yunqurin Aman datake me wuya da qarfi.

Daqyar Aman ya tsaya ta wanke fuskarta tareda dagowa ahankali tana miqewa dukkanin Rabin qarfinta ya tafi ta kalli Sarah tana cewa”

Bani ruwan sanyi zansha.

Cikin kulawa da damuwa Sarah tace”

Naj kinci wani Abu ne?
Ko Zan Kira Dr sa’id ne yazo ya dubaki idan bakyajin Dadi.

Girgiza Mata Kai Naj din tayi tana fitowa toilet ta zauna a kujera tana karban ruwan sanyin ta bude Tasha ahankali tana ajewa tace”

Basai kinkira Dr sa’id ba inaga naci abinci da yawane kawai zanji sauki yanzu tunda na same na rage kawai dai karki Bari a dameni banajin Dadi Kuma.
Lumshe idanuwa tayi tana dafe kanta dake Dan juyawa sbd Aman, Sarah ta fice tana sake Mata sannu.

Wunin kasa gane kanta tayi gabaki daya a office din Haka dai ta tattara Takoma gida wani Dan zazzabi na damunta.
Ko a gidan data Isa abinci kawai tasamu taci ta kwanta saikuma taji daughnuts din dazu da Zainab tafada Mata takeson ci Dan Haka ta daga wayarta takira anty Amina tace”

Anty Amina kibawa zainab daughnuts takawomin nakasa cin abinci cikina ya qulle.

Kash wlh wainda akaiwa harsun Aiko an karba duka saidai ko samosa akwai sauranta Bari akawo Miki.

No ki barshi banasonta zanci cake kawai.

Tana kashe wayar taji zazzabinta na neman qaruwa Haka dai ta lallaba har dare shima tanacin abincin dare ta kwanta gabaki daya Aman ya sakar Mata da mutuwar jiki da guntun zazzabi.

Ko washe gari wani sabon uban latti ta buga dayasa fita ko abinci bataciba
Sai data Isa office Tasha milk drink aikuwa tana gamasha Amai ya biyo bayansa Wanda yafi na jiya take hankalin Sarah ya tashi ta zubawa Naj din data Gama galabaita tana cewa”

Naj please kibari nakira Dr sa’id.

No tattara min kayana gida zankoma jiri nake gani.

Tsayawa Sarah tayi tana kallonta cikin tsananin shakkun tunanin daya shigeta da mamaki me tsananin qarfi tareda kasa gasgata tambayar dazatayin tace”

Naj are you pregnant?

Wani kallon mamaki da takaici tayiwa Sarah din duk da tana Dan jin jiri ta yamutsa fuska a hade tace”

Are you stupid?
Ta Yaya zakimun wannan tambayar inada Wanda zaimun cikine?
Sarah please karki karamun ciwon Kai just leave,kije ki dauki key din motar muje ki kaini bazan iya tuqin ba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 35_*

Albishirinku mata💃shin Ina ma’abota ado da kwalliya🗣️Ina team no makeup🗣️Mata gareku inamai tabbatar muku dacewa duk wnd takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar marari agurin kowa😍Mata inamai tabbatar muku dacewa kujaraba kayan mg’s skincare Koda gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki🧚🏻‍♀️ domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki😘Kuma wani abun jindadin ma shine duka kayansu organic ne Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b💁‍♀️mekike jira hjy maza garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi kwalliya inzaki fita😃kifita aganki da zallar kyawunki hjy😍kanawa mutanenmu ina godiya Kuna nunama mg’s one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg’s na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu🥺Yar shawarmannan karta gagareni🤧😂
Henajiku lvs🤭
Meso should chat
08062991549
07046881166
Call 08064532391
Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare

Team glow✅

Masu buqatan makeup ma duk mgs skincare suna kulawa da wannan ko a makeup studio dinsu kokuma a gidanka.
08062991549

 

************
Sarah binta tayi da ido tana sake qure kallonta akanta Dan kuwa duk da ita ba likita bace Amma ta taba aure harma da bari na ciki harso biyu kafin suka rabu da mijin Dan Haka tana iya ganewa ko hasashen ciki ajikin mace Amma Kuma Kamar yanda Naj din tafara batada Wanda zai Mata ciki bayan mijinta Dan kuwa tare sukai karatu da Naj qawartace ita din cikakkiyar sheda daga Nan har koina zata iya bayarwa akan nutsuwa da kamun Kai irin na Naj din to Kuma Marshal Wanda yake matsayin mijinta kowa ya iya yanda ya tabbata Babu ko gaisuwa a tsakaninsu bare su Aminta da zamansu ma’aurata a taqaice dai Babu ma wani maganar ciki da zai yiyu ajikin Naj din itama din tayi banzan tunani data Yi tunanin hakan harta fada din.

Kallon Naj din tasake Yi cikin kokarin kawar da dukkanin alamun da idanuwanta da zuciyarta ke nuna Mata a natse cikin kulawa tace”

Sorry Naj,Nima bansan tunanin daya shigeniba nace hakan kawai dai ganin yanda kike yawan Amai a kwanakin Nan ne dakuma wannan jirin dashima yake yawan kamaki,duk da hakan please Naj ki daure kiga Dr sa’id sbd Kar wani ciwon ne yake damunki yazo yayi qarfi.

Ahankali ta girgizawa Sarah din Kai suna fitowa daga office din tace”

I will be fine Inshallah,nafi tunanin ko stress ne yamun yawa so daga yau zanshiga hutu na huta sosai idan Naga Bai daina bane Inshallah Zan sanarwa Dr sa’id kokuma zanje asibitin sbd karna kirasa yazo su hajjo hankalinta ya tashi ta dauka wani babban ciwon ne.

Mota suka Isa ahankali ta bude gaba ta zauna ita Kuma Sarah ta shiga gurin driver ta zauna tareda Dan sake kallon Naj din data jinginar da Kai a rufe idanuwanta sbd baccin datakeji Yana cika idanuwanta ta sauke numfashi tana sake Kore tunanin tsananin hasken da fatar Naj din taqara zuwa kirjinta da Kamar sun Dan qara cikowa,tayi saurin girgiza Kai tana Kore tunanin abinda itama tasan bazai yiyunba wato ciki ajikin Naj bayan kowa yasan ko Gama daidaituwa auren baiyiba bare har asamu kebewa babba irin wannan dazatasa ciki a yanda Naj Babu ko alamar auren acikin kanta Dan Haka gskia ba ciki bane kawai sauyin yanayi ne.Tayarda motar tayi ahankali ta ja suka bar ALFAs.

Suna cikin tafiyar ta bude idonuwanta dake cikeda bacci ta kalli Sarah din tace”

Mu biya Bakery zansiya daughnuts idan na Isa gida Zansha da tea cake Yana dannemun zuciya idan naci yanzu kamar kwanan Nan ruqayyat idan zasuyi cake din suna cika butter ne ko kwai¿Nadai gaji dashi Zan gwada Sha da daughn din.

Ok,kokuma kisa suyi Miki ko Anty Amina tai Miki sponge cake shi bazai Miki nauyiba.

No daughnuts din nakeso dai yanzu.

Biyawa sukai wani babban bakery Basu shigaba suka nada ordarsu daga cikin Motar aka kawo musu doughnuts din cikin qaramin farin kwali me dauke da sunan gurin suka wuce.

Suna Isa gida Sarah daga harabar gidan ta juya Ta fito ta hau taxi Takoma office Naj dince kawai tashigo cikin sa’a kuwa tana shiga Dad Alfa na fitowa daga sashen hajjon ta qaraso gabansa ta gaishesa cikin girmamawa yana amsawa tareda tambayarta wasu ayyukan yace idan tasamu lokaci zasuyi mgn akan Marshal daya tsaya akan zai Saida shares dinsa a companyn matuqar Abaas yadawo.

Tana sane da wannan rigimar Dake kwance a ALFAs Dan kuwa Marshal din na janyewa Babu wani sauran nauyi sosai a ALFAs din Dan kuwa kusan Rabin uwar dukiyar tasace aciki saita mahaifiyarsu wadda kasonsane shida Hanifa sai sauran ta Dad Alfa da wasu abokanan kasuwancinsa su uku.

Ok tom Inshallah” kawai tacewa Dad din,Yana wucewa itama qarasa ciki.

A palon ta tadda Hanifa harma da hajjo data kalleta ganin lokacinda ta dawo cikin kulawa ta dago daga karatun datake a wani littafi _The sacred path to islam_ cikin kulawa tace”

Harkin dawo ne?
Lafiyanki dai ko?
Naga idanuwanki Kamar bakyajin Dadi,qaraso zoki zauna Nan.

Kusa da ita ta nuna mata tana kallon yanayinta da duk ita ya sauya Mata a ido Nan tasake tabbatarda ba lallai lafiyar Naj din kalau ba.

Kallon Hanifa hajjo tayi tace”

Kira mun Dr sa’id.

Zama Naj tayi tana hanawa da cewan”

Hajjo lafiyata kalau wlh kawai dai rashin hutune yake damuna na wahalar aiki Amma Inshallah Zan huta kwana biyu saina ji duk wata gajiya ta sakeni Dan Haka ba buqatan Kiran Dr sa’id.

Aje qaramin kwalin hannunta tayi tana budewa tareda kallon Hanifa tana cewa”

Maman baby ga doughnut me chocolate nasan baby nason ci.

Kallon daughnuts din Hanifa tayi tana  murmushi tace”

Baby batacin me chocolate saidai next time kila yanzu nagama cin fatan wake da doya da Umma ta aikomun.

Kallonta Naj tayi tana miqewa taje kicin tafara wanke hannuwanta da kyau tadawo ta zauna tana faracin daughnuts din dasukai Mata Dadi sosai.
Guda biyar ta cinye tabar biyar dan guda goma be Tasha orange juice da ruqayyat takawo Mata me sanyi har hajjo na maganar yaushe tafara shan sanyi Haka tace”

Zan daina hajjo Nima bason sanyin nakeba Sarah ce tafara koyan Sha sanyin Nan inaga a office.

Miqewa tayi ta nufi daki tana cewa”

Bari naje nayi sallar azahar nayi bacci ko kaina zai sake.

Tana Shiga daki handbag dinta tafara ajewa kafin ta nufa toilet Kai tsaye tashige tayi alwala da komaima ta fito ta dauki hijab ta saka ta tayarda sallah.
Tana idarwa hijab din kawai ta zare ta Haye gado wani irin bacci me Dadi ya dauketa take.

Bacci Sosai tayi sai yamma ta farka bayan zirga zirgar da hanifa tayita yi a dakin na zuwa dubata ganin baccin yaqi qarewa Dole ta tadata lokacin har qarfe biyar ta Dan gota cikin mamaki Hanifa tace”

Naj da gskiar hajjo fa Anya lafiyarki kalau kuwa?
Wannan baccin me lafiya bazaiyisa ba saidai me ciwo gskia.

Saukowa gado tayi ta nufa toilet bayan ta duba agogo ta shige tana Dan dafe kanta dake sarawar baccin Bai Gama isartaba.
Alwala tayo tafito har lokacin Hanifa na dakin tana zaune kan sofa tana waya mijinta.
Qarasowa tayi ta dauko hijab ta inda zata tayarda sallar ta tayar har lokacin Hanifa na waya.

Ko data idar kicin tafara zuwa ta debo abinci a plate tareda ruwan sanyi na roba a hannunta tadawo dakin ta zauna lokacin Hanifa ta Gama wayar tafaracin abincin ahankali tana cewa”

Yau bakije gyaran bane gurin umma?

Naje dazu kina bacci Amma zankoma yanzuma da yamman Nan gamaci muje Dan Nima Ina buqatan kiyi gyaran Nan tunda kema Amarya ce duk da haryanxu dai Baki zama cikakkiya macen aure ba.” Taqarasa maganar tana Yar dariya.

Qin kallonta Naj din tayi taci gaba da cin abincinta Dan sanin neman maganarta kawai Hanifan keyi Wanda ko tankawama bazataiba Dan ba zancen tankawar bane.

Tana gamawa wanka tayi ta Sanya jallabiya kawai suka nufi gidansu bayan sun sanarwa da hajjo dake dayar palon da baqi datai.

Tunda suka shigo gidan Dadah dake zaune tsakar gida ta zubawa Naj din ido tana cewa”

Masha Allah,
Wannan Ya Allah yaqara tsare Mana ita daga Baki da ido Tubarkalla Masha Allah,
Gatanan sai qara santalewa takeyi Kamar abiya kudi a taba wannan aure da ace lafiya lafiya ake da ita akan auren Kuma da ace ta tare agurin mijin ne da Babu abinda zai Hana tace cikine a jikinta Amma Ina wannan magana datake Kamar babban sa6o me zunubi agurin Najma zata fadu ko kwatantuwa Dan Haka sbd ma karsu Bata da maraicen ta tsuke bakinta ko fatarta Bata fitarba a fili ta hadiye abarta ta kallesu tana amsa gaisuwar Hanifa data wuce gaba zuwa gurin uwarta Naj kuwa gefen Dadahn ta zauna Tama cewa”

Dadahn wannan kallon badai wani laifin nawa za’a tadoba?

Wata qaramar dariyar tsofi Dadah tayi tana dauke idonta daga kan Naj din zuwa Kan Amina dake zaune tana hada odar snacks din wasu dasuka kawo dazu da Rana tace”

Yayarki nake kallo Ina kallon santaleliyar budurwarta zainab gatanan Allah yabata sai fatar ganin aurenta bada jimawaba zaku samu siriki Amma ke Banga alamar zanga naki ‘yayanba.

Kallon dadar tayi fuskarta n sauyawa ta kame fuska tana dauke Kai tareda share zancen ta hanyar miqewa tana cewa”
Bari na qarasa gurin umma na gaisheta.

Bayanta Dadah tabi da muguwar harara tana cewa”

Wannan Yar baqin cikin Allah ya tausasa zuciyarta tasamu tabawa auren Nan dama itama tasamu nata ‘yayan kanta,
Tausayinta nakeji Amma Sam ita ba tausayin kanta a zuciyarta Dan kuwa bansa ran zata sauko Nan kusa bare muji alkhairi.

Gurin umma ta qarasa ta gaidata tana zama gefen Anty Amina tana cewa”

Anty Amina yauma Zakiyi snacks din kenan?
Idan kinyi ki ciremin daughnuts please.

Kallonta Hanifa tayi kafin Anty Amina tabata amsa tace”

Duk me Zakiyi da daughnuts bayan ga Wanda Kika siyo can ma Baki cinyeba?
Wancan din baiyi Dadi bane Hala?
Dama kayan kasuwa Basu cika dadin Kamar na gidaba.

Wancan din su ruqayyat su cinye na anty Amina yafi Dadi Zan karba din.

Sai dare suka baro gidan bayan sunci ruwan semo da miyar zogale me Dadi sosai ba Anty Amina ba ko umma sai datai mamakin abincin da Naj taci kafin suka fito suka nufi gida.
Suna Shiga Kai tsaye daki ta wuce bayan ta Dan tsaya zance da hajjo a dakinta tayi wanka ta sauya Kaya sai alokacin taji sakat ta fada gado sai bacci.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 36_*

Albishirinku mata💃shin Ina ma’abota ado da kwalliya🗣️Ina team no makeup🗣️Mata gareku inamai tabbatar muku dacewa duk wnd takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar marari agurin kowa😍Mata inamai tabbatar muku dacewa kujaraba kayan mg’s skincare Koda gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki🧚🏻‍♀️ domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki😘Kuma wani abun jindadin ma shine duka kayansu organic ne Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b💁‍♀️mekike jira hjy maza garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi kwalliya inzaki fita😃kifita aganki da zallar kyawunki hjy😍kanawa mutanenmu ina godiya Kuna nunama mg’s one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg’s na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu🥺Yar shawarmannan karta gagareni🤧😂
Henajiku lvs🤭
Meso should chat
08062991549
07046881166
Call 08064532391
Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare

Team glow✅

 

***************
Washe gari ki data farka da jiri ta tashi sai Bata damu sosaiba tasan warwarewar da Bata Gama Yi bane Dan Haka breakfast kawai tayi taredasu hajjo Takoma daki tayi kwanciyarta Hanifa kuma tayi gurin umma.

Sai Rana ta farko shima ko yau din hanifa ce ta tadata sbd lokacin sallah daya wuce sosai bayan ta idar Koda Hanifa ke sake tambayarta lafiyarta kalau itama zuwa yanzu tafara jin kamar ba lafiyaba Dan Kamar tanajin komai nata batajinsa daidai ta dago ta kalli Hanifan dake jiran amsarta tasaki wani qaramin numfashi tareda murmushi sbd kada tasa sufara Kiran sunan Dr sa’id hajjo tabi ta damu tace”

Lafiyata kalau dama bana fada Muku zanyi hutuneba kwana biyu shine naketa kokarin ganin nasamu hutun yanda ya kamata,Yaya harkin dawo daga gidan.¿

Ajiyar zuciya Hanifa ta sauke tana cewa”

Nadawo Amma please Naj idan dai kinji akwai abinda yake damunki ki fadamun sbd Kar abin yayi qarfi ok??

Gyada Mata Kai tayi tana kallonta cikin kulawa tace”
Yes madam.

Daughnuts din da anty Amina tabata tazo Mata dashi ta miqa Mata tana cewa”

Ganshinan Bari naje nayi sallar nima.

Karba tayi tana budewa qamshinsa na shigar Mata hanci ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tana daukan daya tareda kaiwa bakinta tana fara Ci.

Sai dataci sosai kafin ta fito da sauran ta miqawa ruqayyat a kicin ta aje Kai tsaye ta nufa dakin Hanifa acan suka zauna Yar fira datakeson ta wartsake sbd Dan zazzabin yamma datake ji.

Da daddare suna zaune suna fira a dakin Naj din Dake kwance Kan gado daga ita sai riga da wandon bacci gajeru hankalinta na Kan wayar datakeyi da Sarah data Kira tana sake jin Yaya jikin nata wayar Hanifa tayi ringing tana dubawa taga sunan Marshal akan wayar Kamar yawanci yanda yasaba dai video call ne Dan Haka earphn dake kusa ta dauka tayi connecting sbd kada Naj taji muryarsa ta dauka kirana tana kallonsa Yana gidansa yau ba gurin aikiba cikin kulawa da farin cikin ganinsa tace”

Hi.

Wani irin qayataccen murmushi ya saki Yana kallonta shima sbd yanda ta maidasa baturen gaske ganin rayuwar dayafi sabawa kenan.

Cikin nutsuwa da sauti me dadi yace”

Assalm alaikm.

Qaramar dariya Mara sauti tayi tana kallonsa tace”

W slm,how are…kasa qarawa tayi ganin Naj Dan kallonta da fararen idanuwanta Jin tana wayar da turanci Wanda tasan shi kadaine baturen gidan Wanda kowa ke waya dashi da turancin fiyeda hausarsa.

Basarwa Hanifa tayi tana maida zancen cikin hausa tace”

Yaya aiki?

Ahankali ya bude Baki yace”

Alhmdlh,hw are you and The Baby?
And the other baby next to you?

Satar kallon Naj dake waya har lokacin tayi tana murmushi tace”

Duk lafiyanmu kalau kawai dai the other babyn is not that ok,I mean she’s not..kasa qarasawa tayi sbd Naj dake kokarin Gama wayar karta gane maganarta takeyi Dan Haka ta basar da zancen da kallonsa tace”

Duk lafiyanmu kalau sai Dan zazzabin da ba’a rasabane kawai.

Sakamun ita Zan ganta” yafada Kai tsaye Yana aje cup din lemon tea me zafi dayake Sha.

Cire cameran daga front tayi tana maida Masa cameran wayar ta baya
Naj dake kwance akan gado ta bayyana kan screen din iPad dinsa dayake vidcall da ita,kwance take tana waya fuskarta fresh da alama Bata Dade da yin wankan bacciba ya tsayar da idanuwansa Kan fararen cinyoyinta dogaye dake bayyane suna sheqin haske da lafiyan fata da Allah yabata.

Lumshe fararen idanuwansa yayi ahankali Yana jinginarda bayansa jikin kujera ahankali Hanifa tayi Masa sauti da wayar akan Naj ya aje wayar ta miqe ta fice tana cewa Naj din tana zuwa zata dawo.

Bayan fitarta gyara kwanciyar Naj tayi bayan tagama wayar da Sarah ta juyo da idanuwanta kan sauran boiled plantains da Hanifa tabari acikin plate take taji zuciyarta ta motsa ta dauke ido daga kan plate din sbd zuciyarta data fara tashi akan Amai datakeji
Yana kallonta yakumaga abinda ta daukewa kan,
Duk da ta juyarda Kai zuciyarta takasa daina tashin ta sake juyowa tareda tashi zaune ta zuro qafafunta qasa ta miqe ta tako da niyar dauke plate din ta fita dashi saidai tana qarasowa kafin ta dauka wani irin amai me qarfi yataso Mata da gudu ta nufa toilet tana rufe Baki tashige tafara zuba Amai me qarfi.

Rintse idanuwansa dasukai wani iri yayi tareda dauke Kai daga wayar bayan ya kashe ya Nemo no din Hanifan yasake Danna Mata wani Kiran wanda ba video ba Amma ba’a daukabaya saki wani guntun numfashi me Dan zafi tana jefar da wayar gefensa Kan kejera ya lumshe idanuwansa ahankali.

Amai tayi Sosai Wanda ya mugun galabaitar da ita ta sake watso ruwan zafi sosai ta fito ta saka Kaya masu kauri sbd zazzabin daya taso Mata ga mutuwar jiki ta Haye gado tareda shigewa bargo tana rufe idanuwanta.

Baccin rashin lafiya ne ya dauketa Koda Hanifa tashigo daukan wayarta Bata tashetaba ta dauka wayar ta fice sai alokacin taga misscall dinsa ta saka kiransa saidai Bai dagaba Dan Haka itama ta wuce daki Kai tsaye tafara Shirin kwanciya tana gamawa ta kwanta.

Washe gari sosai Naj din ta tashi da zazzabi, hankalin hajjo ya ‘dan tashi sbd dama tasan Najma batada lafiya boyewa kawai takeyi sbd duka alamun Bata daidai ya bayyana.

Dr sa’id aka Kira yazo dubata Dan ko abinci daqyar aka samu ta iya ci sai Amai takeyi Wanda duk ya qarar Mata da qarfin jiki.

Koda Dr sa’id ya iso Anty Amina na gidan itama harta shigo duba Naj din Dan Haka itace ta kamota suka fito Palo bayan ta sanyo doguwar hijab akan kayan baccinta.
Zama sukai Dr sa’id ya Dan zubawa Naj din ido Yana yimata kallon tsaf.
Dauke idonsa yayi tareda Ciro paracetamol ya miqawa Hanifa yace”

Inaga Tasha paracetamol sbd wannan Dan zafin zazzabin ya sauka tukuna Dan gskia inaga saitaje asibiti saina dubata acan Dan inason Zan Mata wasu test musan asalin menene yake damunta.

Cikin kulawa hajjo dake kallonta tace”

Babu wani maganin wannan Aman datajeyine?duk qarfinta ya qare,kodai food poison ne yake wahalar da ita?

Eh zai iya yiyuwa hakan ne Amma dai saimun gwadata zamu sani.

Bayan tafiyar Dr sa’id aka kawo Mata abinci taci ko kadan Amma takasa cin komai,
Kallonta Anty Amina tayi tace”

To akwai abinda kikaji Zaki iyacin sai akawo kici ko kadan ne Kisha maganin.

Ahankali tace”

Aban orange drink ma kawai is ok.

Kawo Mata akai Tasha sosai Tasha maganin sai alokacin tasamu damar watsa ruwan zafi tayi salloli kafin ta iyacin white rice da miyar busasshen kifi.

Tana gamawa anty Amina dasu biyun ne kawai suka rage a dakin ta kalleta dakyau hat zuwa yatsin hannayenta dasukai wani irin fresh ta maida kallonta zuwa Kan fuskarta data Dan ciko kadan Kai tsaye cikin mamaki da shakku idanuwanta cikeda kasa boye mamakin tambayar tace”

Naj ciki ne dake?????

Dukan zuciyarta da qarfi maganar tayi harsaida kanta ya Sara ta dago ahankali ta kalli anty Aminan data tsareta da ido a waje tana jiran amsarta ta dauke Kai Yana sauke wani irin numfashi me wahala na gabanta daya dauki faduwa da tambayar sbd Karo na biyu kenan Ana Mata wannan tambayar,Sarah tayi yanzu Kuma Anty Amina.

Girgiza Kai tayi Kai tsaye tace”

Tayaya zakice ciki ajikina Anty Amina.
Cikin fa haihuwa kike mgn,Ina Zan samesa.

Da wani sabon mamakin anty Amina tace”

Kinada Miji kike tambayar Ina Zaki samu Miji duk da dai ansan auren baigama daidaitaba Amma yanayin naki ne da sauye sauyen danaga duk kin samu a Yan kwanakin Nan yasa nayi tunanin hakan sorry.
Duk da hakan kije asibitin gobe Dr yadubaki ciwo Haka batareda kasan menene yake damunka ba Dadi wuya zakiyita Sha.

Gyada Kai tayi ahankali zuciyarta na wani irin daukan nauyi da maganar Anty Aminan ta farko,
Ta Yaya za’a ringa tunanin ciki ajikinta?
Shin ciki zai iya shigartane a mu’amala biyu da akai bama da so ko yardartaba?
Rufe idonta dasuka sauya tayi tana girgiza Kai da cewan bazai yiyuba wannan masiface me girma,
Aa aa Bata fata, Allah ya tsareta daga wannan abun kunyar me girmanda bazata taba iya kallon ko kanta a madubi ba bare wani.

Bayan tafiyar Anty Amina daurewa tayi ta cije tafara nuna tasamu sauki Sosai sbd abar wani maganar zuwa asibitin Dan kuwa da kanta zata samu zuwa asibitin ita kadai saita fara Jin abinda yake damunta.

Haka ta tilastawa kanta dauriyar ciwon Wanda take matuqar jinsa Amma ta daure tana kannewa ta nuna taji sauki Sosai da wannan tasa aka bar zancen zuwanta asibiti har aka kwana biyu anty Amina ma data saka Mata ido Dan ta basar da ita akan zancen kullum tare suke zuwa gidan da Hanifa gurin gyara da ake Mata na zuwan Isma’eel itama wani lokacin takanyi wani lokacin Kuma batayi sbd qamshin su kurkum da bataso.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 37_*
A gidansu duk wani Abu dazai sake bawa Anty Amina damar sake saka ido akanta tana kokarin kauce Masa
Sbd gabaki dayama ta rasa tunanin Yi abinda dai tasani shine cikin Marshal ajikinta bazai zama gskia ba.

Washe garin ranarda taji abun yafara Mata yawa ta yanke shawaran komawa aiki ranar Isma’eel ya dawo suna zaune Palo tareda hajjo Hanifa na daki tana sake shiryawa ya iso da sallama ya shigo palon bayan ruqayyat taje ta bude Masa kofa ya qaraso fuskarsa daukeda murmushi ya nema gurin ya zauna Yana gaida hajjo cikin tsananin girmamawa
Naj kuwa kallonsa tayi murmushi akan fuskarta tace”

Sannu da dawowa dadyn baby da maman babyn.

Dariya yayi Yana kallonta yace”

Sannu da zaman hutawa Amarya Kuma uwar gidan Marshal,
Hajjo ta daure Miki kina zuba ikonki akan Marshal.

Basarwa tayi tareda sauya zancen da cewa”

Yanzu dauke matarka zakayi ko kunyar hajjo bakwaji.

Satar kallon hajjo dake duba sako a waya yayi Yana maida da kallonsa kanta Yana hadiye dariyarsa Dan kuwa ta shammacesa agaban hajjon yace”

Zan Rama ne kinci bashi Naj.

Murmushi tayi tana maida kallonta kan Hanifa data fito cikin Ado sai daukan ido takeyi sbd fatarta datai kyau Tasha gyaran umma dakuma cikin daya qara Mata kyau sbd ya fito sosai.

Zaunawa tayi tana Masa sannu da isowa daganan suka koma dayar palon hajjo kafin aka gama jere abinci Sukaci abincin dare kafin suka wuce Naj din ta rakasu har mota bayan Isma’eel yaje gurin Dad Alfa ya dade Kuma acan din suna mgna.

Bayan tafiyarsu a hanyarta takomawa sashensu ta hadu da mum Malika da Hannah zasu nufa part din zuwa gurin hajjo
Mum Malika na ganin Naj din ta zuba Mata ido tana Dan bude idanuwanta akanta sosai tana qare Mata kallo a sirrance,
Dan shiga tunani tayi tana sake kallon Naj har Naj din ta iso gabansu cikin nutsuwa tace”

Barka da maraice mum Malika.

Washe Baki mum din tayi tana Dan dawowa daga tunanin data shiga ta kalli Naj din suna qarasawa tace”

Naj Yaya kike?yaya jikin naki kinji sauki kuwa?
Ki daure kije asibiti,idanma bakyason zuwa akwai wani babban likita Dan uwan baban Hannah dake Nan ko Zan kirasa yazo ya dubaki harma da kayan dibar samples na awon idan ya Kama kokuma Hannah ma zata iya kaiki ki gansa.

Da Dan wani yanayi na kame fuska Naj din ta kalli mum din kadan kafin ta dauke Kai batareda ko inda Hannah take ta kallaba tace”

No thank you mum Malika ba buqatan hakan,Dr sa’id ma ya Isa.

Wucewa take kokarin Yi Hannah da tuni Naj din tagama isarta data bar gurin ta daga wayarta tana dorawa a kunne tace”

Hey sweetheart harka qara missing Dina yanzu fa muka Gama waya.

Ko dakatawa Naj bataiba ta wuce sbd Kota kanta zancen baibi ba Dan Haka ko data Isa palon Bata tsayaba ta wuce dakinta Kai tsaye Dan tasan fira suka kawowa hajjo Kamar yanda sukeyi akai akai.

Washe gari Haka ta shirya Takoma aikinta sbd rashin Hanifa ma agidan duk kadaici takeji sbd hajjo ko yaushe karatun littafantane a gabanta.

A office ko dataje kasa samun sukuni da nutsuwa tayi ta ringa zuba Amai Wanda yasa hankalin Sarah tashi Haka dai suka lallaba harta tashi Takoma gida,
Tana Isa gida abinci taci sosai tayi wanka tayi kokari ta zauna Palo sbd Kar hajjo tasan batajin Dadi.

Hakama washe gari a office Bata ganewa komaiba Haka ta jera kwanaki tana zuwa office Amma Babu wani sauki qarshe dai haka taji kamar qamshin office din ne yake sata wannan yanayin Haka tasa Sarah aka kusan sauya Mata komai na office din tasamu Dan saukin abinda take ji Amma duk da hakan gabaki daya tana cikin wani irin yanayi me wahala sbd yawan cin abinci akai akai ga yawan zazzabi da jiri dasuka sakota gaba uwa uba Amai dayafi komai wahalar da ita,
Takasa Kai kanta asibiti sbd tsoro da shakkar Jin wani ciwone ke damunta zuciyarta na cika da wani irin mummunan yanayi idanma tunanin hakan ya shigeta wato na zuwa asibitin.

Sarah duk tabi ta damu akan rashin lafiyan Naj din gashi tana boyewa hajjo sbd Karta damu Dan Haka ta takurata akan Dole suje asibiti kokuma ta sanarda hajjo rashin lafiyan.

Itama al’amarin ya isheta tana buqatan ganin Dr Dan Haka ta yanke shawaran zuwa asibitin,
Daga office batareda sanin kowaba suka nufa asibitin itada Sarah wadda itama tata zuciyar ke harbawa da abinda zasu jiyo sbd zuwa yanzun tagama tabbatarwa kanta cikine da Naj din Wanda tasan akwai tashin hankali idan har hakan ta tabbata agurin Naj,qarin mamakinta Kuma yaushe har hakan yafaru duk da dai ba abin mamaki bane tunda tanada aure Amma auren da mijin Kuma…..

Isowarsu asibitin yasa ta dakatarda tunaninta suka fito Kai tsaye office din Dr sa’id Wanda takira a waya suka nufa.

Tana buga kofar yasan itace Dan Haka ya taso ya bude Yana kallonta yace”

Kafin mu zauna muje a dauka sample dinki ko?

Gyada Masa Kai kawai tayi ahankali suna juyawa zuwa Lab yana sake Mata tambayoyi akan yanayin datakeji tana basa amsa ahankali sbd jikinta dake amace.

Bayan an dibi jininta a lab din suna fitowa daqyar suka Isa office dinsa ta ringa Amai a toilet dinsa daqyar ya tsaya Mata ta dawo ta zauna Sarah na shafa bayanta tana Mata sannu cikin kulawa da tausayawa.

Ruwan roba Dr Sa’id ya dauko daga fridge ya kawo ya miqa Mata Yana Mata sannu cikin kulawa saiga result din ankawo.

Karba yayi Yana budewa ya nufi kujerarsa ya zauna Yana fara karantawa.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali bayan yagama dubawa ya dauki biro yayi signing ahankali ya miqa Mata Yana cewa”

Well kamar dai yanda nayi tunanin ciwon shine kina daukeda juna, You’re pregnant Naj.
Yanxu zanmiki scanning sai muga ko wata nawa ne.

Daukewa numfashinta yayi cak sbd wutar jikinta tako Ina data dauke ta zubawa bakinsa dake bayanin ido tana daina fahimtar abinda yake fada.

Da sauri Sarah ta dafata tana shafa bayanta tareda bude Mata ruwan tana kaiwa bakinta cikin kulawa da tsoron yanayinda Naj din tashiga tafara Kiran sunanta tana cewa”

Naj, Naj, Naj are you okay?
Please ki saki numfashinki Mana,
Say something Naj.

Buga bayanta tayi da Dan qarfi sai alokacin numfashinta yadawo da qarfi ta dago ta kalli fuskar Dr sa’id din da idanuwanta dasukai jajir Nan take sbd firgici da tashin hankali Babu tunanin komai sbd kanta da tunaninta dasuka cushe Kai tsaye tace”

Banason sanin ko wata nawa ne ka ciremun cikin.

Wani kallon tsananin mamaki da Dan qaramin firgici Dr sa’id dama Sarah sukai Mata atare yasake kallonta Yana cewa”

Ciki fa nace Miki kinadashi Naj.

Rintse ido tayi wasu irin hawaye na balle Mata tace”

Ka ciremun kawai Dan Allah bana buqatan kowama yasan da cikin Nan.

Ajiyar zuciya ya sauke sbd abinda yakeson fada Mata ba lallai ta fahimtaba ya kalli Sarah da itama shi take kallo tana fatar karya amince din ya maida kallonsa kan Naj din cikin nutsuwa yace”

Kije gida yanzu kina buqatan hutawa tukuna zuwa gobe ko jibi zamu sake mgna sbd Dole saina Miki scanning dinnan kafin wani maganar Amma dai cire cikin shine abinda bazai faruba.

Miqewa tayi Sarah na riqeta ta zame ta fice ahankali result din awon na hannunta ta share hawayenta ta Isa mota ta bude ta shige sai alokacin tasaki wani irin kukan daya daga hankalin Sarah takasa tada motar Kuma batace kalaba sbd karata damu Naj din Dan kuwa ko ita Jin wannan Batu yasa taji hankalinta ya tashi da yanda cikin zai bayyana ga maganar cirewa da Naj din keyi Wanda bazata bartaba gskia saidai suyi fada kowama yaji abinda yake faruwa.

Tada motar tayi suka nufi hanyar gida Naj din ta dauka tissue ta goge fuskarta datai ja sbd kukan datai din
Saikuma zuciyarta dake doka wani irin tsalle.
Suna shigowa layin gida Sarah ta hango sojojin dasuka saka gabanta faduwa itama Dan kuwa da yiyuwar Marshal ne yadawo.

Naj Bata lura dasuba Saida suka Shiga harabar gidan taga motarsa dake quryar rumfar motoci a fili sai sheqi takeyi ta dauke ido sbd gabaki halinda take ciki baya barinta bi takan tunanin komai ta fito ta nufi ciki bayan Sarah ta wuce batareda ta Shiga cikiba itama.

Kai tsaye ta shigo palon ahankali cikin yanayi na son boye halinda take ciki ta qaraso cikin palon ba kowa sai hajjo dake waya hankalinta Kuma duka Yana Kan wayat ta nufi hanyar dakinta takai hannu zata bude taji an rungumota ta bayanta ahankali hannuwansa na sauka Kan takardar dake hannunta har lokacin
Ya sako fuskarsa wuyanta ahankali tareda sakar Mata wani irin numfashin daya sakata juyowa da sauri bugun zuciyarta na tsananta
Idanuwanta suka sauka cikin nasa Ya qaro wani irin haske da fresh na hutun gske da rayuwarsa take ciki ahankali yakai bakinsa kunnenta ganin irin kallon datake Masa zaiyi mgn hawayen idonta suka balle tana sake damqe result din a hannunta.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 38_*
Dagowa yayi ahankali daga jikinta Yana kallonta a natse ganin hawayen dake gangarowa daga idonta fuskarta na sakewa kamar wadda dama take nemansa ta saka Masa kukan.
Fuskarta yakai hannuwansa Yana kallonta sosai da idanuwansa dake cikeda Tsananin qaunarta data kasa boyuwa daga cikin idanuwan ya shafo hawayen ahankali Yana janyota jikinsa cikin taushin murya da girman kulawar da baya fitarwa yace”

Lafiya?
Zo Nan,inace kukan na kewata ne ba gani ba¿

Maganarsa tasa hawayenta tsananta gudu tana sake damqe result din a hannunta sbd yariga yakaita ya barota batasan ta Yaya zata iya kallon kowa na duniyarba da cikin Wanda Bata karba ba amatsayin miji Wanda Kuma ko tarewa bataiba amatsayin Matar aurensa to ta Yaya kowa zaiyi kallon ta samu cikin¿
Bazata iya wannan kunyarba Tai Mata girma me tsananinda bazata iya daukaba Dan Haka tunda Babu Wanda yasan da cikin zata ciresa batareda kowa yasaniba arufe zancen.

Kama hannunta yayi ya bude kofar dakinta yayi ciki da ita ya qarasa bakin gado ya Isa ya zauna tareda zaunar da ita Kan qafafunsa ahankali Yana kallonta kafin ya maida kallonsa kan takardar dake hannunta datake sake riqewa da kyau.

Cikin nutsuwa yace”

Ok ok,ok hawayen ya Isa Haka Zakiyi ciwon kai,”
Handkerchief dinsa me qamshi ya fitar daga aljihunsa ya Kai Kan fuskar tata yafara share Mata hawayen dasuka kasa tsayuwa har lokacin saima sake ballewa dasuke Mata kuka me qarfi takeson Yi ta fitarda tsananin quncin da zuciyarta ke ciki Amma takasa.
Miqewa tayi daga jikinsa tareda nufar tashige ahankali tareda rufowa.

Lumshe fararen idanuwansa yayi tareda miqewa tsaye ya fice daga dakin a palon har lokacin hajjo na zaune tana abin Dake gabanta yafito ya fice zuwa sashensa Kai tsaye.

Yana shiga koina nasa yadauka qamshi da sanyin AC sbd gyaran dame aikinsa yagama ya nufa bedroom shima Kai tsaye toilet din ya nufa Dan wanka sbd yasamu nutsuwa Dan gabaki daya kansa ya juye da wannan kukan datake.

Wankan ya fito ya saka jallabiya fara qal Yana zuba qamshi me sanyi ya tada sallar la’asar yayi Yana gamawa yafito palonsa daukeda wayarsa ya nufa fridge ya dauki Redbull drink dinsa ya balle yakai Baki yashanye tareda jefarda gwangwanin cikin ledar shara yafito Palo Yana kokarin zama da wayarsa daya saka Kiran Hanifa akai knocking kofar ahankali Wanda yasashi dan rintse ido Dan kuwa ya tabbatarda Babu me zuwa gurinsa ayanzun bayan Hannah wadda bayan ciwon Kai Babu abinda zata sakar Masa Dan Haka yaci gaba da wayar dayakeson Yi Hanifa data dauka wayar cikin farin cikin ganin numbernsa ta Nigeria alamar yadawo ba sanarwa kenan tace”

Hey Marshal,
Wannan zuwan bazatane kokuma kaida matanka kuka hada.

Kai tsaye yace”

Ya kike?ya baby?

Alhmdlh tafada Kai tsaye tana cewa”

Yaya dai? Naj na lfy kuwa?

Dan shiru yayi na sakanni kafin da murya me nutsuwa yace”

Menene yake damunta?
Dr sa’id yace Yana damunta?

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali kafin tace”

Jikin yadawo da ciwon ne?
Dr sa’id baice komaiba kawai dai bayan zazzabin rashin hutu sai Kuma cewar da yayi idan tasamu time taje asibiti yayi Mata su gwaji Amma banasa ran taje asibitin gskia Amma za’a tambaya Sarah sai aji ko sunje asibitin daga office.

Ok ki turo no din Sarah din zanyi magana da kaina da ita.

Ok.

Kashe wayar yayi tareda miqewa ahankali ya Isa kofar da har lokacin Hannah na tsaye tana jiransa daukeda basket din snacks da Tai Masa taci ado cikin riga da skirt na atampa abinda Bata cika sakarwaba.

Shigowa palon tayi da murmushin farin cikin ganinsa dauke a fuskarta ta rufe kofar tana Isa dining ta aje qaramin basket din tadawo ta zauna palon tana kallonsa cikin shauqin ganinsa da farin cikinta dake bayyane tace”

Sannu da dawowa Marshal
Nayi kewanka sosai,
Ina maganan zuwa hutu qasarku saigashi ka dawo.

Wayarsa da Sarah ta dauka yasata dakatawa da maganarta sbd jin alamar da mace yake wayar.

Kai tsaye sarah tanajin muryarsa ta ganesa cikin girmamawa tace”

Barka da dawowa.

Thank you” yace Kai tsaye da kamammiyar muryay dayake mgn da ita da kowa bayansu hajjo sai matarsa yace”

NAJMA tasamu zuwa asibitin ganin likita????

Faduwa gabanta yayi tanason yin Shiru saidai Kuma Marshal din ba irin Wanda zataiwa Shirun bane ta bude Baki ahankali cikin nutsuwa tace”

Eh munje asibiti taga Dr sa’id.

Ok thank you,zan nema Dr sa’id din da kaina naji.
Katse wayar yayi Yana ajewa tareda Dan rufe idanu ya budesu ahankali Kan Sarah datai tsit tana saurarensa zuciyarta na Shiga qunci,
Kenan dai ciwon Naj ne yasashi dawowa da alamar datake gani,
Ciwon yayi tsananine Haka kokuwa dai Raina musu wayo Naj din zatai sbd janyowa kanta attention dinsa?
Aikuwa saitaji menene yake damun Naj din idanma qarya take saitaji dan ta sanarwa da Marshal din.

Kofa ya nuna Mata Yan sanarda ita hutawa zaiyi yanzu.
Badan tasoba ya miqe ta fice Kai tsaye ta nufi sashen hajjo tana ayyanawa aranta tagama Kai maqura akan Naj data shige tsakaninta da Marshal dinta.

Ba kowa a palon Dan Haka ta saki wani wulaqantaccen tsoki ta juya ta fice daga sashen tana Jin zafin zuciyar Yaya zatai da baqin cikin Naj.

Da daddare Haka ta lallaba tayi wanka ta saka riga da wandon bacci masu tsayi ta fito cin abincin sbd cikinta dake kukan yunwa.

Kicin tafara zuwa ta hado tea me zafi data zubawa madara sosai da Zuma ta fito ta nufa dining inda ba kowa ta zauna ahankali tana Shan tea din har sai data shanye kafin ta zuba abinci kadan taci ta qoshi ta miqe ta koma dakinta ta Haye gadonta tana Shirin kwanciya taji anturo kofar dakin Ana shigowa ta dago kanta ahankali sbd Jin qamshin turarensa daya fara qarasowa hancinta idanuwanta dasuka kumbura sbd kuka suka Shiga cikin nasa taji jikinta na saki ta dauke idon daga kan nasa tana kokarin kwantawa Kan gadon har lokacin tanajin idanuwansa na yawo jikinta.

Takowa yayi ahankali ya qaraso bakin gadon
Ta qarasa kwanciya tana rufewa batareda ta kallesa ba sai zuciyarta dake Dan bugawa da sauri sauri.
Ahankali ya zauna bakin gadon ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa hannun tareda sauke qaramin numfashi yayi shiru ahakan dumin tafukan hannayensu suna shiga cikin na juna.

Dan rintse idanuwa tayi tareda budewa sbd yanda dumin tafin hannun nasa ke saka jikinta kokarin sanyi ta Dan motsa tana kokarin zare hannun nata sai alokacin ya Dan waiwayo ahankali ya zuba Mata idanuwansa dasuka sata dagowa ta kallesa.
Wani kallo yake Mata ta dauke idonta tana sake kokarin zare hannunta
Ya riqe hannun tareda tayarda zaune Yana janyota jikinsa ya rungume,
Bayason hayaniya nutsuwa kawai yakeson Yi sbd kansa na Dan Masa ciwo kadan sbd damuwar ciwonta daya zo dashi dakuma kukanta daya qarasa damar da nutsuwar cikin kansa.

Qwacewa take kokarin tana turasa ahankali ya kalleta Yana sake yimata kyakkyawar runguma ya bude Baki a natse cikin yanayi na rashin son hayaniyar yace”

Ki nutsu banason hayaniya,
Kema bakida lafiya,idan Kika qi nutsuwa Zan saki baccin gajiya.
Daure fuska tayi tareda son sake qwacewar amma Bai Bata damar hakan ba sbd irin rungumar da yayi Mata idanuwansa a rufe.

Qarfe biyu da Rabin dare ta farka ahankali tareda bude idanuwanta sbd yunwa da qishurwan daya tada ita
Ta motsa ahankali jinta cikin jikin mutum ta dago da sauri ta kalli fuskarsa sbd ta manta gabaki daya da zuwansa dakin da daddaren.

Fuskarsa ta kalla da qaramin hasken wutar gefen gadon tana Dan dauke Kai daga kan fuskar tasa bugun zuciyarta na qaruwa ta zare jikinta daga nasa tana kokarin saukowa gadon ya bude idanuwansa Yana kallonta a Dan kasalance kafin ya tashi zaune Yana kallonta yace”

Lafiyanki kuwa?

Ko kallonsa bataiba ta miqe ta nufi kofa tana kokarin fita ya tashi a natse ya riqota Yana kallon idanuwanta da bacci yagama sakinsu yasake tambayarta cikin kulawa Yana kallon cikin idonta dasukai laushi.

Dan rintse ido tayi tana rasa abin Yi Kai tsaye ta sake zamewa tana nufar kofa ta bude ahankali ta fice Yana binta a gefe da mamakin Ina zata cikin Daren.
Kicin suka nufa Yana sake kallonta da mamaki Yana kallon kitchen din sbd bazai iya tuna ranarda ya taba shigowa kicin din ba sai yau.

Fridge ta nufa ta dauko orange juice me sanyi ta zuba a cup ta maida sauran ta nufa inda cake yake ta dauko guda biyu ta fito Yana biyeda ita Yana kallonta da mamakin cin Abu cikin tsakiyar dare.

Karban cup din yayi daga hannunta sbd sanyin juice din Yana kallonta da ido yayi Mata alamar sanyin zai qara Mata zazzabi.

Zaunar da ita yayi a palon tagama ci da kansa yakawo Mata ruwa Tasha tana qin kallonsa tagama ta miqe ta nufa daki ta shige.

Tsayawa tayi tsakiyar dakin cikeda mamaki da tsoro ta kallesa bayan yashigo da ido shima yaka Mata wani irin kallo sbd gabaki daya kayan baccinta daketa damunsa da wani irin qamshi tuni
Tana bude Baki da niyar nuna Masa kofa ya ranqwafo ya hade bakinsa da nata Yana fara Bata wani kiss me sanyi da nutsuwa ta rintse ido da qarfi tana son qwacewa Amma takasa sbd jikinta dake mutuwa ahankali ahankali.
Ahankali hannuwansa suka sauka cikin rigarta ta dauke numfashi tana qanqame hannuwansa da qarfi sbd yanda tsikar jikinsa suka miqe ta bude idanuwa daqyar zata kallesa ko zata iya hanasa da idanuwanta Amma kallon dayake Mata yasa idanuwanta neman makancewa jikinta na saki
Ya dauketa gabaki dayanta Yana dorawa Kan gado bakinsa cikin nata har lokacin sai hannuwansa dake yawo cikin jikinta suna barazanar rabata da numfashinta.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 39_*
Qarfe shida tayi wanka tayi sallah daqyar sbd tsamin jiki da bacci me nauyi dake cikeda idanuwanta tareda kasala Takoma ta kwanta wani bacci me nauyi ya dauketa sbd tun asuba daya fita sallah Bai dawoba Yana sashensa shima baccin yakeyi me nauyi sbd tunda ya iso Bai samu hutuba da nutsuwa sai bayan asubar.

Hannah tunda uwar safiya ta tashi tana aiki hada Masa kayan breakfast a sashensu duk da gabaki daya hankalinta na Kan yanda zatai tasan meye manufar Naj akan Marshal dinta Dan kuwa wlh bazata yardaba Naj ta cike gurbanta a rayuwarsa.

Sai guraren goma tagama ta nufi dakinta tayi wanka tafito ta zauna gaban madubi tana shiryawa cikin adon kwalliya da turare masu qarfi da tsada ta nufi kayanta ta fidda wata doguwar riga me fadin wuya da roba roba ajikin yadin dayasa ta Dan lafe jikinta ta sake saka wasu turarukan ta daura qaramin scarf daya Gama fitarda gashinta me Dan tsayi ba laifi sbd itama kyakkyawar ce ta fito daukeda basket ta nufi sashen hajjo sbd tafi saka ran zuwa yanzu Yana can din sbd kusan Sha daya tayi.

Tana shiga hajjo na daki Babu kowa a palon bayan ruqayyat dake sake jere abincin Rana da aka fara gamawa.
Aje basket din hannunta tayi a dining ta juya ta nufi dakin Naj datake Jin shedan na ayyana Mata taje tunda Naj din Bata Nan zuwa yanzu tasan tana office.
Tana Isa jikin kofar ta Murda ta bude ahankali zata shiga taji Naj din na waya da Sarah cikin damuwa da rashin sukunin data tashi dashi akan cikin,gabaki daya hankalinta ya juye Tama rasa Ina zata saka ranta da tunaninta komai nata ya tsaya cak
A yanda ta yau din ta ringa Jin abubuwan da jalal yake Mata har cikin ranta ta tabbatarda aikin cikin jinintane sbd abinda yafaru a Daren yau din sosai jikinta ya karba hakan Wanda ta tabbatarda hakan yaci gaba tozarcin datake gudarwa kantane zai sameta sbd yanayi na cikin Wanda shima dakansa ya fahimci a Daren jikinta ya karba saqonsa tako Ina,
ta rintse ido tanajin wani irin kunya da takaicin kanta da ma na cikin Kai tsaye cikin damuwa tace”

Sarah ki shirya kizo yanzu Zaki daukeni muje wani asibitin ayi scanning Zan biya ko nawane a ciremun cikin Nan,
Kunyar zancen Nan ma yafita nakeji,kizo yanzu,gani Zan fara shiri.

Kashe wayar tayi tana kokarin saukowa daga gadon da gabaki daya qamshinsa yakeyi ta yamutsa fuska tareda miqewa tana gyara zaman towel din dake daure ajikinta Wanda Takoma bacci dashi bayan tayi sallah
Ta inda ta ajiye takardar jiyan ta dauko tasake budewa ta karanta zuciyarta na tsalle da quncin rashin sanin Yaya zatai da wanann qaddara ta cikin data sameta Kuma tsoron cirewar na Dan shigarta Dan Bata taba kwatanta hakan akantaba.
Shafa cikinta dake shafe ahankali tayi tana sauke numfashin dayake sake shigar da ita damuwa ta maida takardar cikin envelope dinta ta saka cikin handbag dinda zata fita da ita kafin ta daga qafafu ahankali ta nufi toilet yashige tareda rufo kofar.

Wani irin tsalle zuciyar Hannah keyi na shiga cikin wani razanannen yanayi na kaduwa da tsoro tsoro dakuma farin cikin Jin wannan muguwar tonuwar asirin dazai samu Naj Wanda zai taimaka Mata shikenan qarshen Naj da Marshal yazo,
Bama Marshal ba ko iyayenta saisun tsaneta bare familyn Alfa Dan kuwa ba tantama idan har yanda taji Naj nada ciki to cikin tsohon saurayinta dasuke aiki guri dayane Abaas lamido.

Da sauri ta bude kofar ahankali ta shige dakin ta isar jakar da Naj tasaka result din ta bude ahankali tana kallon kofar toilet din ta dauki envelope din tareda rufe jakar ta silale ta fice tareda rufe kofar ta bar sashen gabaki daya da sauri.

Sashensu ta qarasa hannuwanta na rawa da jikinta tun a Palo ta tsaya hannuwanta na rawa tafara kokarin Ciro takardar daga envelope din
Mum Malika dake zaune ta miqe itama ta matso cikin mamaki da son ganin menene take cewa”

Menene kiketa rawar jiki haka kina zare idanu.

Bude result din tayi dakyau tana karantawa zuciyarta na tsallen wasi wasi duk da shedan na saka Mata tabbacin cikin wani guri ta samosa
Saidai Kuma tunanin sanin wacece Naj da girman kamun kanta da sanin darajar kai nasata tunanin ba cikin kowa bane saina Marshal.
Cikin wani mummunan yanayi na fita hayyaci tace”

Uban waye yayi Mata ciki?Dan kuwa Babu wani kusanci a tsakaninta da Marshal bare ace cikinsa ne,
Wannan cikin bana Marshal dina bane,Sam Sam,
Zan nuna Masa wannan Dan yasan wacece Naj da irin rayuwar datake da wasu mazan…

Da sauri mum Malika ta qwace takardar tana karanta cikeda mamaki da firgici itama,
Ta dago tana jinjina Kai cikin Shiga tunani tace”

Tun kwanaki Naga alamar ciki ajikin yarinyar Nan Amma ban kawo hakanba araina sbd sanin Babu wani kusanci ko mu’amalar kusa dake Shiga tsakaninta da Marshal Kuma banajinma kowa yasan sunada kusanci kowa yasan Babu wata mu’amalar kusa tsakaninsu to Ina wannan cikin ya fito???

Qwace takardar Hannah tayi idanuwanta na sauyawa da tsananin baqin ciki da tashin hankalin rashin sanin taqamaimai cikin Ina ya fita cikin tsananin baqin ciki da zafin Zuciya tace”

Koma Ina ya fito nasan bana Marshal bane,
Ko Ni Marshal Bai taba yiwa kallon sha’awa ba nida nake Masa shigar daukan hankali kala kala tareda bayyanar Masa da duk wasu sigar daukan hankalin maza Amma Bai taba Bina da kallon sha’awa ko so dayaba bare ita da Bai taba ganin wani kayan daukan hankaliba ko jikinta a bayyane bare har ya iya kusantarta Dan Haka Marshal bayada alaqa da wannan cikin shiyasa Dole Zan nuna Masa Dan yasan waye Naj da halinta ko zai sawwaqe Mata taqara gaba.

Zama mum Malika tayi tana janyota ta zauna itama cikin nata baqin cikin tace”

Ba kince tace abortion zataiba?
Kibari saimun samun tabbacin abortion din saimu samu hanyar sanar dashi ta yanda idan yaji tayi wannan abun qyamar Kuma tana kokarin zubarwa Dan Kar wani yasani zaifi daukan zafi mukuma mu samu abinda mukeso,
Amma dai yanzu ki Adana takardar Nan ba yanzu zamuyi amfani da itaba karki Bari zafin Zuciya da rashin hakurinki ya Bata Mana aiki nasan halinki bakida dangana ko kadan.

Zafin da zuciyar Hannah ke Mata yasata miqewa tana maida takardar cikin envelope ta nufi daki ta dauko mukullin motarta ta fito ta fice zuciyarta na wani irin nauyi Dan dai ita tarasa yadda da zancen inda zata saka cikin.

Motarta ta nufa ta bude tashiga tana kokarin tayarwa Naj ta fito Sarah na tareda ita tana sanyeda doguwar rigar jallabiya ash da gyale black datai rolling Jakarta na hannunta Sarah ta karba key suka Shiga motar suna kokarin tadawa ta fito Tata motar zuciyarta na sake tafasa ta nufi sashen Marshal da tashinsa bacci kenan yayo wanka Yana sanyeda qananun Kaya ash da sukai Masa kyau ya dauki wayarsa zai saka Kira Hannah Tai knocking kofar.

Kallon kofar yayi tareda Dan dauke Kai sbd baya buqatan damuwar kowa yau shiyasama yau zai tafi gidansa dake anguwarsu ta sojoji zai Kira Dr sa’id can ya samesu ya duba Masa Naj din acan yanason sanin menene matsalarta Dan ko yau da asuba tayi Amai kafin yafita sallah.

Bude kofar yayi tareda zuba Mata idanuwansa fuskarsa a kame ta kallesa tanajin zuciyarta na qara mamayuwa koina da sonsa,
Bazata rasashiba Kota halin Yaya, Marshal natane Dan bazata iya rayuwa babusaba.

Juyawa yayi yakoma ciki ganin irin kallon datake Masa da dukkanin idanuwanta abinda yafi tsana kenen agurin Mata yawan kallo.

Idanuwanta rufewa sukai da takaici da baqin ciki da tsananin kishinsa ta fitarda envelope din hannunta ta qaraso ta ajiye Masa a gabansa ta juya zata fice saikuma ta dakata tareda juyowa ta dawo cikin marairaice fuska hawayen data Dade tana dannewa tun dazu na radadin da zuciyarta keyi zuciyarta na zafi tace”

Marshal ina maka son da bazan iya cin Amanarka ba Kamar Naj sbd Haka nakasa boyewa abinda naji nakuma ga tana kokarin Yi,
Abortion take kokarin……..

Wani kallon daya dago Yana Mata yasa maganarta maqalewa tana kallonsa zuciyarta na harbawa da fatan yayi mummunar fusatar dazata tashi kowama ayi duk abinda za’ai.

Idanuwansa ya maida Kan takardar data aje yakai hannu Kai tsaye ya dauka ya bude.
Sunan asibitin yafara kalla yaga asibitinsu Dr sa’id ne ya gangaro da idanuwansa zuwa cikin takardar Yana karantawa.

Shiru yayi idanuwansa zube akan takardar wani irin yanayi na rashin tabbaci da Kuma abinda Hannah tafada yasashi aje takardar tareda miqewa ya nufi dakinsa ya dauko key din motarsa ya fito lokacin Hannah tuni ta fice ta nufi motarta itama ta fice Suma su Naj tuni suka fice daga gidan suka nufi wata private hospital dinda wata yayar Sarah ke aiki.

Scanning aka fara yimata bayan sister farida Tai Mata dogon bayanin illar abinda takeson ayi din na cire Mata cikin tana sake cewa”

Ki koma gida kiyi tunani wannan abune me girma ba’ason gaggawa.

Sarah da duk hankalinta yake atashe tanajin zuciyarta na turata data Kira Marshal ko Hanifa ta sanar musu tunda takasa Hana Naj din da idanuwanta suka rufe da kunyar aji zancen cikin bayan itama din tana iya ganin hankalinta ba akwance yakeba da al’amarin.

Ahankali tace”

Naj Dan Allah mukoma gida ki sake zaunawa kiyi shawara akan hakan.

Cikowa idanuwanta sukai da hawayen dake bayyanarda tsananin damuwar da zuciyarta ke ciki ta girgiza Kai ahankali tana kallon takardar scanning din dake nuni da cikin watansa biyu da sati biyu harda kwana uku ahankali tace”

Sister nagama yanke shawaran Yi din kawai.

Da kansa yake tuqa motar zuwa asibitin Dr sa’id sbd Yana buqatan mgn dashi bazai iya jiran saiya tashi aikiba yazo gidan Dan Haka Kai tsaye can ya nufa.
Kirane yashigo wayarsa ya Dan kalli wayar Yana ganin sunan Hanifa ya share Kiran Dan baya cikin mood na magana da kowa yanzu sai zuwa anjima.

Ko daya Isa asibitin sai alokacin ya nema wayar Dr sa’id cikin sa’a Yana office zaune Dan Haka koda yashigo cikin mutuntawa Dr sa’id ya nuna Masa kujera Yana cewa”

Barka da zuwa Marshal,
Hope lafiya Naga kazo da kanka asibitin Kai tsaye?
Badai jikin Naj ko Hanifa bane ko?

Dan rufe fararen idanuwansa yayi ya bude Yana kallon Dr sa’id fuksarsa a kame kamar koyaushe Kai tsaye yace”

Dr ka duba Najma akan ciwon dake damunta inason sanin taqamaimai menene matsalar,Ina nufin akwai abin daya kamata nasani?

Kallonsa Dr sa’id yayi Yana sauke ajiyar zuciya a fili tareda gyara zama cikin nutsuwa yace”

Ciwonta ba komai bane face laulayi na ciki datake dauke dashi Wanda dama Dole zata ringa irin wainnan qananun ciwon kafin cikin yafara qwari.

Rufe idanuwa yasake Yi ya bude ahankali yanajin wani irin yanayi na shigarsa ya sake kallon Dr sa’id zaiyi mgna text din Sarah yashigo wayarsa Kamar hakan”

_please kana buqatan zuwa wannan address din Naj tanason aikata abinda yake hadari ga rayuwarta._

Sake karanta saqon yayi zuciyarsa na kasa fahimtar zancenta duka ya dago ya kalli Dr sa’id cikin yanayi na ransa dake neman baci yace”

Tasan cewa tana daukeda ciki ne?

Eh munyi mganar da ita saidai gskia zancen cikin kamar Bai kwanta Mata.

Ta maka maganar cire cikin kenan????”” Yafada Yana kafe kallonsa kan Dr sa’id din daya fara kame kamen boye zancen da yayi.

No,yes I mean ta nuna bataso Amma ai na Mata mgn Kuma inaga tabar zancen…..

Miqewa yayi idanuwansa na sauyawa ya fice daga office din ya nufi motarsa Yana kokarin shiga idanuwansa a juye da wani irin mummunan yanayi saiga motar Isma’eel yashigo asibitin da gudu Yana Kiran nurses saiga dr sa’id yafito take sukai kansu sbd Hanifa da ake kokarin fitarwa motar jini ya balle Mata gabaki daya Bata hayyacinta.

Wayar Isma’eel dayaketa Kiran Marshal Bai dagaba itace tashigo wayarta daidai lokacinda zata saka hannu a takardar abortion din tana dauka cikin tsananin tashin hankali yafada Mata mugun labarin dayasata sakin takardar tana miqewa cikin tsananin tashin hankali ta fice da sauri Sarah tabita tana tambayar lafiya Amma Bata tsayaba ta karba keys din motar da kanta taja cikin tsananin gudu sukabar asibitin zuwa asibitin su Dr sa’id.

Suna parking taga motar marshal agurin Bata tsayaba sukai ciki da sauri tana Jin qafafuwanta na neman sagewa da tunanin halinda kowa zai Shiga idan Hanifa ta rasa cikinta.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 40_*
Isarta bakin gurin yayi daidai da isowar anty Amina itama hankalinta tashe,
Idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin damuwa da tsoron halinda Hanifa zata shiga ta juyo ahankali tana kallon Isma’eel da duk yagama ficewa hayyacinsa sbd damuwa saidai tawakkalinsa yasa yaketa kokarin natsar da kansa ya kalli Naj din kafin ya juya ya kalli Marshal dake magana da Dr sa’id cikin wani irin yanayi na tsananin zafi biyu daya hadu akansa fuskarsa amatuqar hade Babu rahama ko daya akai.

Shigewa Dr sa’id yayi da sauri yana cewa su Dan kwantar da hankalinsu Inshallah zasuyi iya kokarinsu.
Kasa zama tayi sbd tsananin tsalle da bugawar da zuciyarta keyi ta rintse ido cikin yanayi na sagewa Dan Bata fatan wani Abu ya samu Hanifa ko babyn,
Tana roqon Allah yasa Hanifa cikin Nan rabonta ne Dan tafi shaidar yanda take tsananin son haihuwa da samun baby Amma wannan ne karo na uku Wanda dagashi idan har ta rasa batajin za’a Kuma yimata wani dashen.
Matsowa Sarah tayi qafafunta a sanyaye ta kalli Naj cikin kulawa da Dan qaramin sauti tace”

Naj ki zauna Kuma ki Dan kwantar da hankalinki kema kinsan ba’a son kishiga damuwa sbd yanayinki please.

Satar kallon Marshal Sarah tayi taji gabanta yasake bugawa cikinta na Dan kadawa ta dauke Kai sbd ganin wani irin mummunan hadewar fuska da wani boyayyan fushi dayake cikin idanuwansa Yana zaune ya harde qafa Babu Wanda yacewa kala sai jiran tsammani dasukeyi.

Qin zama Naj tayi tana Dan kaida kawo ahankali idanuwanta na neman kuka Amma yaqi zuwa sbd tashin hankalinta biyu ya kasu tanajin tashin hankalin halinda Hanifa ke ciki ga nata tashin hankalin sbd sosai take sake jin tsoro da shakkar cire cikinta dayake neman mamayarta Wanda ke sake cusar Mata da kai gabaki daya ta rasa wane tunani zatai,ta rintse ido tana dafa bango sbd sarawar da kanta ke dauka Yana neman sakar Mata da jiri.

Anty Amina dake kallonta cikin kulawa tace”

Naj ki zauna Mana tunda kema zazzabin da kikai Ba gama sakinki duka yayiba karki qara Mana wata damuwa Anan idan Kika shiga cikin wani hali.

Sai alokacin ta kalli Anty Amina tanason fashewa da kuka yaqi zuwa ta Dan sake dafa bango Sarah na kamata ahankali ta qarasa kujerar kusada Marshal ta zauna tana sunkuyar da Kai har lokacin hankalinta duka baya jikinta.

Gabaki daya Babu wata alamar data nuna Marshal dake gurin yasan da wanzuwar dukkaninsu a gurin bayan anty Amina data Dan basa bakin komai zai daidaita inshallah Akan Hanifa itama bayan Kai daya gyada Mata ahankali bai samu cewa komaiba sbd a yanayinda yake ciki idan ya fitarda fushinsa da tsananin bacin ran dayake ciki kowa bazai iya tsayawa agurinba.

Ismail ma miqewa yayi yafara safa da marwa yana Dan bubbuga hannayensa dake nade a kirjinsa,
Yanason Kiran Yan gidansu ya sanar musu Amma bayason tayar musu da hankali tukuna sai ansamu Kan matsalar.
Hannuwan Naj rawa suke ta damqesu tana Dan rintse idonta daketa cikowa da hawaye Amma kuka da hawayen sun kasa saukowa tsoro ne fal aranta,
Hannu ta daga ahankali takai Kan cikinta ta dafe tana sake Shiga wani sabon yanayi,anty Amina dake lure da ita ta matso ta dafata Anatse tana kallon fuskarta da duk take bayyanarda damuwarta a natse tace”

Naj,kina Lafiya dai?

Kasa mgn tayi ta sauke Kai ahankali tana sake dafe cikin ta gyadawa anty Aminan Kai.

Dr sa’id ne ya bude kofa yafito ahankali tareda wani Dr Adebayo
Dukkaninsu suka kallesa suna kallon idonsa da bakinsa jiran Jin abinda zai fada Dr Adebayo kuwa wucewa yayi zuwa office dinsa.

Kallon Marshal Dr Sa’id yayi Yana sauke numfashi tareda ajiyar zuciya ahankali kafin ya maida kallonsa kan Isma’eel a natse yace”

Hanifa ta rasa cikin sbd ta haifi babyn da Bai Isa haihuwaba kwata kwata hakan ne yasa babyn baizo da raiba sbd baima Gama zama cikakkiyar halittaba,
Jinin ya tsaya duk da ta zubarda jini sosai Amma bama buqatan qara Mata wani jinin sbd munduba pcv dinta is normal,
ayi hakuri Haka Allah ya nufa,wannan jarabawa ce idan anyi tawakkali za’a cinyeta Kuma za’a ga ribar hakan, Allah yabata lafiya,an bi kofar baya anfita da ita zuwa dakin hutawa zaku iya samunta acan.

Sake kallon Isma’eel yayi Yana cewa”

Zaka jira mu hado maka babyn sai aje a rufe ko.

Kallon Marshal da idanuwansa suka qarasa sauyawa gabaki yayi cikin kulawa yace”

Sorry Marshal,Allah yabada hakuri yabada rayayye,
Ita Hanifan kwata kwata Babu wata matsala atareda ita yanzu saidai damuwa Dan Haka tana buqatan ku dukan.

Juyawa yayi ciki yakoma Dan hado gawar ‘dan babyn yakawo.

Kowa agurin kasa kuka yayi sai Naj dakejin kukan nason taso Mata Amma yaqi fitowa ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Isma’eel da qarfin imaninsa yasa ya daurewa zancen sosai Yana jiran fitowar Dr sa’id
Kasa kallon gefen Marshal tayi tanajin nauyin zuciyarta na qaruwa ta miqe Kai tsaye ta bar gurin ta nufi hanyar dakin datasan can za’a Kai Hanifan a  Amenity Sarah na bayanta anty Amina kuwa matsowa tayi cikin kulawa da tsananin tausayawa tana sake bawa Marshal hakurin wannan rashin shida Isma’eel dake gyada Kai cikin wani yanayi Yana cewa”

Bakomai anty Amina nagode.

Marshal kuwa Kai kawai ya gyada Mata har lokacin Yana zaune a inda yake idanuwan Nan tamkar zasuyi Aman wuta sbd baqin ciki,bacin Rai dakuma damuwar Hanifa.
Tsayawa tayi itama har akawo babyn.

Da tsananin sanyin qafa Naj ta tura dakin tashiga fuskarta na narkewa da ganin hanifar wadda tana ganin Naj din ta sauke Kai wani irin gigitaccen  kuka na zuwar Mata da sauri Naj din ta qaraso ta zauna tana rungumeta itama Bata hawayen na gangarowa alokacin.

Kuka Hanifa keyi Sosai Wanda yake fitowa daga tsakiyar ranta tareda dibbin ‘daci da ciwon rashi na cikinta,
Sosai takejin wani irin radadi da zafi dama ciwo Wanda takeson kokesa idan zai fito shiyasa take kukan sosai zafin zuciyar Amma yakasa raguwa saima tsananta da quncin keyi.

Kukan Hanifan har cikin zuciyarta Naj ke jinsa sbd kukane da Bata taba irinsaba,kukane me cin Rai na Shiga zuciya,tanason Bata hakuri Amma takasa bude Baki sbd tanajin ciwon da Hanifan keji,tasake rungumeta nata hawayen na sake gudu.

Kukan datakeyi tuni yafara daga hankalin Naj din ta dago tana kallonta ta bude Baki murya a yamutse taka cewa”

Hanifa Dan Allah kiyi hkr ki daina kuka Haka Inshallah Zaki samu wani babyn,
Dan Allah ki daina kuka Haka Kinga Baki Gama warwarewa kada wata damuwar ta shigeki…….

Wani kukan me qaramin sauti yakuma zuwar Mata tana girgiza Kai cikin dasashiyar murya tace”

Naj Ina tsananin son babyna Amma Allah baiyi Zan zama uwaba.

Hanifa karki cire Rai daga rahamar ubangiji Dan Allah…”Naj tafada hawaye na gangarowa idanuwanta dasukai jajir.

Naj bakowane yakeda rabo da Sa’ar zamowa uwa ba kila Ina cikinsu duk da na dandana zamowa uwa me renon ciki ko ahakan na godewa Allah
Amma zafi nakeji da qunci cikin zuciyata sosai……kakane yaci qarfinta ta sunkuyar da Kai tanayi.

Gabaki daya jikin Naj mutuwa yayi da Tsananin tausayin Hanifan Dan kuwa ko Hanifan Bata fadaba kowa yasan zatai qunci sbd tsananin soyayyarta da son haihuwa Amma Allah ya qaddara hakan,
Sake mutuwa jikinta yayi da wannan yanayin na Hanifa ta dafa cikinta tanajin shin idan ta cire cikinta zata iya Shiga irin wannan halin na Hanifa na kuka da baqin cikin rasa nata babyn¿
Dafata Sarah tayi ahankali,Bata dagoba ta rufe idanuwanta hawayenta na gangarowa akaro na farko taji kamar qaunar cikinta ta motsa aranta tasake kallon yanayin quncin dake Kan fuskar Hanifa ta rufe ido tanajin qaunar cikinta amatsayinta na uwa,
Uwa mahaifiya zata zama,idan ta cire cikin tazo kukanta yafi na Hanifa.

Dafe kanta tayi tana rasa tunanin Yi sai tazama kamar Hanifan ta zuru zuru da ita sbd rashin sukunin zuci Dana fili ga na Hanifa.
Bude Baki takuma Yi a kasalance tana son rarrashin Hanifan Amma takasa sai shafa Mata bayanta take tana gyada Mata Kai alamar tausayawa har lokacin hannunta daya na Kan cikinta datakejin Kamar zai zube sbd tsoro da firgicin datake ciki,
Tunanin hakan Kuma shiyafi komai sakata rudu a daidai yanzu a wannan lokacin.
Shigowan marshal ne yasata dagowa ahankali ta kalli kofar sbd Jin qamshinsa daya fara Shiga hancinta ta sauke idanuwanta akansa zuciyarta na harbawa da wani irin bugu tana qure kallonta akansa akaro na farko tunanin wannan shine mahaifin cikin jikinta,
Shine uban ‘da ko yarta,
Wasu irin zafafan hawayene suka gangaro Mata,ita tata qaddarar kenan kuma ta abun kunya cikin qanin qawarta ajikinta,
Tayaya zata iya kallon kowa da wannan cikin bayan kullum cikin tashin hankalin ta qi Aminta da auren ake,
Duniya ta shaida rashin yardarta da Aminta da auren ta Yaya zata iya kallonsu da cikinsa ajikinta bayan ko tarewa bataiba, ta ina?ta Yaya suka samu kebewar data samu cikin?
Da wane ido zata kalla hajjo da ma Dadah datasan bazatai shiru ba,harma ummanta da Hanifa duk batasan ta Yaya zata iya kallonsu da wannan cikinba gashi Kuma yanzu bazata iya cutatar da kantaba ta cire cikin sbd jinsa data farayi ayau akuma Nan asibitin sbd gani ga wane datai.
Yanayin fuskarsa da Babu wani sauki acikinta kamar dai ayanda yake kame koyaushe saidai yau muguwar kamewar tafi ta kullum Wanda takewa kallon yanayinda Hanifa take ciki ta dauke idanuwanta ahankali daga kansa din ta sauke Kai tana miqewa daga gefen hanifar ya qaraso Yana kallon Hanifa da ganinsa keson dawo da kukanta Wanda yafi komai cin ransa ganin hawayenta Dana wadda yanzu yafi komai takaicin kansa daya Bata lokacinsa.

Riqeda hannun Hanifa yake Yana kallonta da idanuwansa cikin kulawa yace”

Soon Zaki Kuma samun wani Inshallah just have faith ki dauka wannan jarabawa Allah zai duba zuciyanki ya Baki wani ok????stop this tears now.

Handkerchief dinsa yaciro daga aljihun wandonsa ahankali ya fara share Mata hawaye Yana Dan kokarin sake kwantar Mata da hankali fuska kame.
Anty Amina ce ta qaraso itama tana sake Bata nata rarrashin suna cikin hakan saigasu umma da hajjo sun iso motarsu daban ta dad Alfa da mum Malika dabam sai ‘yan gidansu Isma’eel dasuka iso mum dinsa da qannanesu biyu sai qaninsa namiji daya na dakin ya cike da Yan uwa kowa Yana fidda kalar jimaminsa sbd Babu wanda abun Bai taba zuciyarsa Dan dukkaninsu sun qwallafa Rai a cikin bama kamar hajjo da Dad Alfa sbd rashin ‘yaya a familyn Alfa din sunason ‘yaya su hayayyafa a cikin zuriar ko Dan a morewa dukiyar da aketa tarawa.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 41_*
Yanda kowa ya damu yake Kuma bayyanarda damuwarsa yasa Hanifa daina kukan saidai fuskarta Kam Bata dubuwa ta kumbura sosai tayi jajir daqyar mumyn Isma’eel tasata Dole lallabata Tasha tea dasu magani aka hada ruwan zafi sosai anty Amina ta taimaka Mata tayi wanka ta gasa Mata jikinta suka fito tasaka doguwar riga Mara nauyi lokacin maraice yayi sosai kusan kowa ya tafi sai anty Aminah da Naj din sai Sarah Yar hannun damar Naj Isma’eel ma lokacin yasake dawowa daga gida dayaje ya sake kintsowa cikin wasu kayan sbd waincan sun baci.

Kallon Naj da idanuwanta sukai laushi Sarah tayi ta kalli Anty Amina tace”

Anty Amina kice tazo na maidata gida Mana ko abinci taci itama ba isashiyar lafiya ne da itaba gashi idanuwanta sun nuna ta galabaita Amma taqi zuwa
Hanifan ma gatanan alhmdlh taji sauki ki daure muje gidan kici abinci kiyi wanka ki Dan nutsu saiki dawo asibitin.

Kallonta Hanifa tayi da idanuwanta dasukai mugun nauyin kumburi ta bude Baki ahankali cikin kulawa a natse tace”

Naj kije gida Mana ki huta gaba daya kinyi na kyan gani sbd damuwa da gajiya,naji sauki banajin komai yanxu kije banson ganinki ahaka zanji ba dadi.

Dagowa Naj din tayi tana kallon Hanifa jikinta na sake sanyi ta dauke idanuwanta daga kanta tun yanzu tanajin kunyar hada Idanuwa da kowama kafin aji aikin dake jikinta cikin sanyin murya tace”

No banajin yunwa ko naje gidan bazan samu nutsuwaba zan zauna din anan…

Naj karki kamanta fa tunda safe Kika fita ba daga gida kikayo Nan ba Dole kina buqatan samun hutawa….

Sarah please nace Zan zaunsa Anan…

Anty Amina ce ta katseta da cewa”

Akace kije ki dawo mana.

Marshal ne ya shigo dakin tareda Isma’eel da Dr sa’id lokacin har anyi sallar magriba kowannensu Yana zuba nasa kalar qamshin turaren Amma gabaki daya nasa ya take nasu qamshin ya cika dakin Yana sanyeda jallabiya fara qal da alama wankan maraice yayi ya nufa masallaci dagacan yayo asibitin idanuwansa na Kan Hanifa datake zaune Kan gado duk jikinta a mace tayi sanyi.

Wasu maganunan Dr sa’id yakuma rubutawa cikin folder dinta tareda Masa wasu tambayoyin yana rubutawa cikin folder din yayi signing ya rufe Yana ajiyewa ya kalleta cikin kulawa da Bata qwarin gwiwa yace”

Ki sake Inshallah rabo na zuwa agaba,ki qara hakurine Hanifa okay???

Gyada Masa Kai tayi ahankali tana cewa”

Thank you Dr sa’id.

Dan murmushi yayi Mata kafin ya maida kallonsa kan Naj datai mugun laushi sbd har wani irin jiri me qarfi take gani daga zaunen cikin kulawa da mamaki yace”

Naj yakamata fa kije gida kisamu hutawa da abinci,you don’t you look good kinsan Kuma yanayinki kema masu ciki ba’a son suna saka damuwa irin haka,”””kallon Marshal yayi Yana cewa”

Inaga yakamata ka kaita gida yanayinta ya nuna ta galabaitu sosai.

Tsit dakin sukai kowa wuta na dauke Masa musamman Hanifa da anty Amina dasu kadaine Basu San da cikinba sai Isma’eel Amma shi me cikin yasani yau din sai Sarah datafi kowa sanin komai.

Batareda anty Amina tasaniba tace”

Waye me cikin??

Kallonta Dr sa’id yayi sai alokacin ya lura da yanayin kowa yake fahimtar ba kowane kenan yasan da maganar cikin ba ya Dan juyo Yana kallon Naj datai zuru takasa dagowa jikinta amatuqar sake yayi Dan gyaran murya Yana kallon Anty Amina yace”

Tana buqatan zuwa gida koma yayane.”ya juya ya nufi kofa zai fice Marshal ya dago sai alokacin ya kalleta lokacinda take bude Baki jiki ba nauyi tace”

Lafiyata kalau banajin komai Zan zaun…..

Akaro na farko da kowa yaji tsawar Marshal Da ba Naj din kawaiba Hanifa ma da anty Amina Saida suka Sha jinin jikinsu suna kallonsa cikin tsananin mamakin ganin bacin ransa shima akaro na farko da wani irin kallo dake sake saka Mata shakkar halinda take ciki Yana dauke Kai daga kallonta yace”

Kitashi ki koma gida yanzu,
Anty Amina ku maidata gida karta sake dawowa asibitin ta zauna gida.

Yana fadar hakan ya miqe ya nufi kofa ta dago tanabin bayansa da kallo zuciyarta na tsalle ahankali ta bude Baki zatai mgana Anty Amina ta tareta da cewa”

Tashi muje kinji abinda yace.

Hanifa kuwa kasa shiru tayi ta kalli Naj din data miqe Tasha gabansa zatai magana jiri ya dibeta tayi baya zata Fadi anty Amina da Sarah suka zaburo zasu tareta Amma yariga ya tareta ta hanyar riqota yana Mata wani kallon Yana sake boye fushinsa akanta yace”

Ke kanki baya daukan magana daya me sauki?
Ki aje wannan shirmen kije gida idan kuma kina shirin komawane gurin cire cikin daganan toh let me be very clear with you,
Idan wani Abu yasamu cikin Nan zakisan wayeni,nayi tunanin banzan tunaninki baikai kiyi tunanin cire ciko ajikinki ba Amma har Zaki iya zuwa wani asibitin daban tunda Nan Dr sa’id yaqi yarda da manufarki sbd kece Kika fi kowa shekara a duniyan Dan Haka kisa aranki wani Abu yasamu cikin Nan zakiga abinda bakyaso now get out of my sight.

Cikin rudu da mamaki Anty Amina take kallon Naj data Gama jiqa fuskarta da hawayen baqin cikin tayaya yasan da cikin har yasan tayi niyar zubar a hasale anty Amina tace”

Naj cikine dake kike son zubarwa?????

Cikin tsananin hawaye ta dago tana kallon fuskarsa dake a hade Babu sauki tako Ina ta bude Baki tace”

Ban aikata……wani wanan Mari ne ya sauka fuskarta Wanda yasata faduwa zaune da sauri hanifa ta sauko gado ta qaraso ta riqe ummu da basusan da isowarta ba Saida tayi Marin.

Dr sa’id ma da Isma’eel matsowa sukai suna bawa umman hakuri duk da kowa yashiga mamakin jin abinda Naj din taso aikatawa.

Wasu sabbin hawayene suka tsinkewa Naj takasa dagowa tana sake qaramin kuka ahankali
Ya rintse idanuwansa tareda Dan sake kame fuska ya kamo hannuta daya ya damqa cikin na anty Amina Yana cewa”

Ki kaita gida kawai.
Baiso zancen yafita Haka ba yaso yabarshi a tsakaninsu Amma taja zancen yafita sbd rashin Jin ta.

Umma kallonta take zuciyarta na zafi ta tiriri Tama kasa cewa komai sbd zuciya data Gama cinta
Hanifa ta Kama hannun umman suka Isa bakin gadonta ta zauna tana bude Baki ahankali tace”

Umma Dan Allah kiyi hkr karkiyi irin wannan fushin addua zamu taru muyi Mata,tayi lafi babba Kam wannan karon Amma Dan Allah Kar ayi fushi da ita tashiga damuwa kuma wani ciwon yashigeta tunda har dai akwai cikin.

Fuzgarta anty Amina tayi Dr sa’id da Isma’eel yabita Yana cewa”

Kibita ahankali sbd yanayinta Mana.

Kala Bata samu cewa ko wannnensuba sbd zuciya data Gama cinyeta itama.

Sarah da duk tagama Shiga rikita rikita ita ta Isa motar Naj dasuka zo da ita da sauri,
Anty Amina ta bude baya ta tura Naj din da lokacin take kuka sosai na abun duniya daya rufto mata tonon asiri cikin dare guda.

A mota Babu abinda Anty Amina keyi sai tsokin baqin ciki akai akai
Tanajin badan cikin ba Kamar ta rufe Naj din da mugun duka da zagi.

Suna Isa gida Sarah na parking suka fito Naj tayi gaba tashige gidansu tanajin bazata iya Shiga gidaba ta hada ido da hajjo da maganar cikin.
Bayanta anty Amina tabi Sarah Kuma da motar ta nufi gidan Alfa tashige tayi parking tafito itama jiki duk a mace da yunwa da damuwar halinda Naj take ciki.

Sashen hajjo ta nufa Kai tsaye cikin sa’a hajjon na Palo tana jiran Alfa dazasu asibiti tare,Sarah ta qaraso tana gaidata cikin girmamawa kafin ta miqa Mata key din motar Naj din tace”

Hajjo ga key din motar Naj zantafi gida Saida safe.

A asibitin Kika barotane?bazata dawoba ta huta tun safe.?

Shiru Sarah tayi tana Dan Jin nauyin fadawa hajjon saidai gwara ta fada Mata sbd a yau idan wani baijeba Dattijo zai iya yiwa Naj dukan fulawar biredi,ta daure tace”

Aa tare muka dawo tana Nan gidansu akwai matsala ne,tun asibiti ummanta tafara….shiru tayi tana kasa fada.

Da zallar mamaki hajjo ke kallonta tana cewa”

Meya samu Najman?
Matsala Kuma wace iri?

Miqewa dai tayi ganin yanda Sarah ke qaf qaf da ido tana qin fadar abinda Najma tayi ta nufi kofa tana cewa ruqayyat tashiga gidansu Najma.
Sarah Bata bita ba ta wuce gida tana fitowa.

Koda su anty Amina suka shiga gida Naj dakin ummansu take neman shigewa anty Amina ta jawota Bata tsaya koina ba sai gaban Dattijo dake zaune tareda Dadah suna maganar auren Asmau da za’a zo tambaya.

Dattijo ya dago yana kallon Naj din dake kuka har lokacin kafin ya kalli Anty Amina yace”

Ita Kuma wannan ya akai da itane?
Tasake gudowar ne batason auren?

Numfashin takaici anty Amina tasaki kafin tace”

Cikine da ita shine taje cirewa batareda sanin mijintaba yau dai harta Kai qarshen hakurinsa sai daya bayyanar.

Wani irin kallo Dattijo yayiwa Naj din Yana Dan gyara zama ya maida hankalinsa Kan Anty Aminar Yana sake tambaya cikin rashin gane bayaninta na farko yace”

ta samu cikine kokuwa?sake mun bayanin.

Dattijo cikine ajikin zata zubar bada sanin mijinba hakama bada sanin su hajjo ba……

Wani irin salati me qarfi Dadah tasaki tana kallon Naj da idanuwanta waje cikin daga murya da mamaki yagama suqeta tace”

‘yar Nan ciki gareki?
dama Ashe kingama daidaitawa da mijin kike zuwa Nan Dan kin Gama rainamu kike zuba Mana hauka kullum bakyaso bakyaso to uban waye yayi Miki cikin?
Kokuwa shima mune mukai Miki Dole?yau ga ‘yar banzar yarinya.

Hajjo data iso takuma ji abinda ake fada tayi saurin janye Naj tana kallon Dattijo daya Gama siqewa da wani irin mummunan baqin ciki da takaicin Naj din ta kallesu su dukan tace”

Haba Hana Dattijo wannan ba abun daza’aita tonawa bane Dan Allah abar maganar har asamu zuciyoyi su lafa Najma muje gida.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 42_*
Kasa motsawa Naj tayi sbd tsananin nauyin da kunyar dasuka riqe qafafun nata,ta sake soke Kai hawayenta dake tsiyaya masu yawa suna qara gudu Akan fusakarta datai jajir tarasa ta Yaya zata dago ta kalli hajjo.
Miqewa tsaye Dadah tayi tana sake kallonta har lokacin da bayyananen mamakine a cikeda da ita Bata iyayin shiru da magana ta matso gaban Naj din tana Mata kallon kinci Amanata tace”

Da tuni da kike bori da yamutse yamutsen bakyason mijin da auren,qanin qawarki dama Ashe kingama daidaicewa da abinki Kika barni inata faman lallabaki Ina ranqwafar da duk masifata sai abinda kikaso nake Miki Dan kawai musamu ki hakura Ashe duk kallon Mai saman ruwa uwa kike Mana har kinsamu Dan rakiyarki a dakin hajjo¿

Kallon hajjo Dadahn tayi tana cewa”

Kinada labarin wannan salalar da akai Miki kokuwa kema bakida labarin Raina Miki wayon take?
Dattijo maza wanke fuskar Nan tata me Kama da wankakken karas da Marikanda saita nema hanyar asibitin makafi da kanta,
Dukan Yanda taci Amanar rarrashi da kwantar da Kan danake Mata zakamin Dan kuwa ta Jima tana zambatata,
Yarinya ido a kafe amma ta….

Cikin damuwa da Dan takaicin maganganun Dadah hajjo ta kalli Dattijo da baqin cikin duniya da takaicinsa yasashi qamewa gefe Yana kallon Naj din Dan kuwa dukan wankin bargo yakeson Mata Amma hajjo ta tareta shiyasa yakejin tafarfasar zuciya da kunyar yanda zai kalla su hajjon musamman Alhaji Alfa akan wannan mugun tunanin da niyar data shiga Naj din.

Har lokacin tana rakube Kai a soke takasa dagowa ta kalla kowa sai zuciyarta dake raunana da girman kunya da kukan kunyar Dan kuwa tonon asirin da Dadah ke Mata yasa kusan duk sauran jama’ar gidan suka fito tanaji Umma habiba data iso gurin da mamakin hayaniyar fadan Dadah daya dayake tashi cikin mamaki take kallon bakin Dadah dake fadar ciki ajikin Naj,ta Dan fito da idanuwa cikin kaduwa da mamakinta itama daya kasa bayyanuwa tace”

Najman ce da ciki?
To¿Lallai aure yayi albarka tunda har ansamu rabo kafin tarewa.

Da wani sabon takaici Dadah ta kalleta tana Mata mugun kallo tace”

Bar Nan tunda daman ke bakya fadar alkhairi.

Juyawa tayi ta tana barin gurin tana cewa”

ALLAH dai yasa a sauka lafiya tunda Naga kamar cikin ya kwana biyu da Samu.

Kamo hannun Naj hajjo tayi tareda kanta Kai tsaye suka wuce tana cewa”

Sai da safenku” suka wuce.

Tunda suka fito gidan hajjo ta saketa ahankali tana gaba Naj din na bayanta qafafunta na tafiyar da kyar sbd yanda takeji a zuciya da jikinta.

Suna fitowa waje motar Marshal na tsayawa da Umma aciki tafito fuskarta a matuqar daure hajjo na ganin hakan ta waiwayo ta kalli Naj da har lokacin kanta a qasa yake takasa dagosa a natse tace”

Najma wuce gidan Ina zuwa.

Daqyar ta daga kafafu ta taka ahankali ta wuce ta nufi gate din gidan securities na wangale Mata tashige.

Sai data Shiga harabar gate na biyu na gidan tasamu ta Dan dakata tareda Dan dagowa tana share hawayenta dasuka cika Mata ido ko gani Sosai batayi.
Wucewa zatayi ta qarasa ciki hancinta ya shaqo Mata qamshin turarensa ta dakata ahankali tareda Dan juyowa gabaki daya ta zuba Masa idanuwa Yana tahowa ya fito daga motarsa fuskarsa amatuqar kame Kuma da alama Baigada tsayuwarta agurinba Dan ko kallon gurin datake baiyiba ya wuceta kadan saiga Hannah ta fito tana ganinsa ta qarasa gurinsa da sauri tana wani irin karya jikinta da shape dinta yake bayyane cikin wata straight English gown data kwana jikinta sosai sai qamshi takeyi cikin kashe murya da kulawa tace”

Kasa hankalina ya tashi tun Rana nake kiranka baka dagawa asibiti ma ko danaje duba Hanifa bakacan duk sai ahankali na yasake tashi,Yaya kake?

Wucewa yayi tana binsa a gefensa ahankali ya furta” Hannah kaina na ciwo bana buqatan abin dazai qaramin ciwon kan ok???

Ahankali Naj data dauke idanuwanta daga kansu ta daga qafafunta tafara tafiyarta ta wucesu batareda taji abinda suke fada ba Kai tsaye sashen hajjo ta nufa ta shige,

Shima hanyar nasa sashen ya nufi yabar Hannah tsaye agurin tana binsa da kallo zuciyarta fal farin ciki ahankali tace”

Koma dai menene Kai nawane tunda nasan yanzu kowa yasan da maganar cikin zanjira gobe naji sakamakon inda cikin yafito.
Juyawa Tai itama ta wucewarta.

Naj na Isa palo Bata tsayaba Kai tsaye dakinta ta wuce tareda rufowa ta qarasa Kan kujera ta zauna sai alokacin yasake sakin sabon kuka Mara sauti tana dafe zuciyarta dake tsananin zafi da bugawa.
Sai datai kukan hartaji sauran qarfinta ya qare ta share hawayenta tareda miqewa ahankali ta nufa toilet ta shige bayan ta cire kayanta.
Wanka tayo sosai tasamu jikinta ya Dan sake taji qarfi qarfi Bata shafa komaiba ta saka riga da wandon bacci masu kauri da hula tana sallame sallar ishai ruqayyat na shigowa daukeda abinci ajere harda orange juice da kwanakin akaga ta maqalewa Sha sai yanzu da zancen cikin ya fita suka fahimci dalilin Shansa kenan.
Ajiyewa ruqayyat tayi tana gaidata kafin ta juya ta fice.

Tsananin yunwar datakeji tasata cin abincin sosai bawai Dan tanada appetite na comes din ba Tasha orange juice din ta miqe ta nufi gado ta Haye ta kwanta tanason fita Amma bazata iya kallon hajjo ba ta kwanta tareda rufe idanuwanta bayan ta rufa.
Tanaji ruqayyat tayi Knocking kafin tashigo ta tattara kayan abincin ta gyare gurin ta fice bayan ta kashe Mata wuta.

Washe gari tun da wuri ta tashi tayi sallah Takoma bakin gado ta zauna tana tunanin yanda zata iya fitowa Palo ta nufa kicin neman abinda zataci sbd cikinta dake wani irin kukan yunwa,batasan da wane ido zata kalla su hajjo ba.

Daurewa tayi takoma ta kwanta bayan taci wani short bread biscuit dake cikin handbag dinta wani sabon baccin wuya yakuma dauketa.
Bata Farkaba sai qarfe Tara shima yunwarce takuma tada ita ta sauko gado nufi toilet takuma yin brush ta fito Kai tsaye ta nufi kofa ta bude ta fito palon sbd tunanin zuwa lokacin hajjo tana asibiti taje.

Dining ta nufa Kai tsaye ta zauna babu kowa a palon da dining din duk saitaji jikinta yaqarayin sanyi ta zuba abincin ahankali tafara ci wayarta na hannunta tanason Kiran Hanifa taji Yaya jikin nata Amma takasa sbd Jin nauyi da kunyar,
Ita yanzu shikenan abin daya sameta kenan na kayan kunya da to Nan asiri.

Kofar dakin hajjo aka bude gabanta ya buga da qarfi jikinta na mutuwa ta dago ahankali tareda waiwayowa idanuwanta suka sauka Kan kyakkyawar fuskarsa dakeda cika ido yafito dakin hajjon ta dauke Kai ahankali daga kansa ganin Babu alamar zai nuna yaganta kokuma yasan da ita a palon ya nufa kofa ya fice yabar palon da qamshinsa daya sanyata Dan rufe ido tanajin cikintama yacika da abincin ta miqe tabaro dining din takawo tsakiyar palon saiga hajjo ta fito fuskarta ba wani alama na bacin Rai ko fushi ta kalli Naj din cikin kulawa tace”

Najma kinci abinci kuwa?

Batareda ta dagoba ta bude Baki bayan ta sauke Yar ajiyar zuciya tace”

Eh.

Ok kije ki kwanta ki huta Babu maganar sake fita gareki umarnin mijinki ne daya gindaya Wanda Nima na Aminta da hakan Dan Haka ki nutsu hutu kawai Zakiyi.

Komai bataceba bayan gyada Kai datai tana wucewa dakinta sbd ita kunya da wannan tunanin da kowa keyi akan cire cikin yagama dama Mata lissafin Kai sbd batasan ta Yaya zata iya sanar dasu cewan tariga tafasa cire cikin,zata bar abunta tun kafin komai ya faru,
Shi takeson ya fahimci hakan Amma batajin zata iya yimasa wannan bayanin na bafa zubar da cikin zataiba yanzu sbd da alama baya buqatan bayani ko iya sauraran wani abun.

Wuni tayi a daki ko palon takasa fitowa saidai ruqayyat dake yawon Kai Mata abinci da fruits wanda hajjo tace aringa Kai Mata dakin tunda bazata iya fitowarba tana sane da tsananin kunya komaice ke dawainiya da Naj din Wanda itama har cikin ranta Bata daina mamakin yaushe har suka samu wani kusanci da fahimtar data kaisu har ga mu’amalar aureba saidai sukaji ciki suna Nan suna jiran saukowar Naj din Ashe tuni suka San yanda sukai suka kebewarsu kilama Kamar yanda Dadah tafada acikin sashenta aka samu cikin tana Nan tana dakon bin dare da adduar Allah ya kawo kusancinsu ga wannan aure.,
Lurada tsananin kunya da girman kunyar dake dawainiya da Naj harta yanke shawaran cire cikin dakuma yanzu da kowa yasani yasa ta bar nata fadan da zancen cikin ranta ba yanzuba sbd Kar abin yayiwa Naj din yawa damuwa ta shigeta ga juna biyu a tareda ita badan hakan ba na Dadah zatai Mata taji suna Ina akai wannan babban aikin ga Marshal din yadauki zafi gabaki daya yakoma Marshal dinsa ko maganar yace Kar kowa yayi Masa baya buqatan ji.

Har dare Haka ta wuni Babu wani doguwar walwala sbd daga daki sai daki asibitin ma takasa Kiran kowa nauyi da kunyar kowa takeji qarshe Sarah takira a waya ta tura asibitin ta dubo Mata jikin Hanifan.
Dukkaninsu wainda Sarah ta tarar a asibitin suna ganinta suka San Naj ce ta aikota Amma Babu Wanda yayi maganar saima Hanifa data kalleta cikin kulawa tace”

Sarah Yaya uwar dakinki?

Murmushi Sarah tayi tana Dan satar kallon inda Marshal yake zaune Hannah na gefensa sai wani basarwa takeyi itama tunda tasamu Marshal din ya taho tareda ita bayan ta nace Masa akan motarta nada matsala.

Kallon kyakkyawar fuskarsa dake Kan wayarsa tayi tareda dauke idon ta maida Kan Hannah dake gefensa tamkar wata sabuwar amaryarsa ta dauke Kai tanajin zafin Hannan ta Dan kalli Hanifa tana miqewa tsaye tareda qaqalo murmushi tace”

Tana gida Ina saka ran Kuma tana Lafiya sbd banje ba saidai gobe kila zanje nadubota,
Zan tafi, Allah yaqaro lafiya.

Amin anty Amina tace tana cewa” ki gaida umma Jamila.

Zataji.” Juyawa tayi ta fice batareda ta sake kallon inda Marshal din yakeba Dan har cikin ranta take jiwa Naj dinta kishin Hannah da kusancin datake samu dashi.

Da maraicen ranar aka sallami Hanifa suka tattara suka dawo gidan sbd taqarasa warwarewa a gida kafin Takoma duk da dai Isma’eel din tafiya zaikuma Yi idan yadawo zai fara Mata Shirin su koma gabaki daya can qasar da yake tare kowa ya huta.

Tana daki taji dawowarsu gabaki daya harda ummanta da anty Amina sai hanifar da Isma’eel daya fice bayan shigowarsu.
Fuskewa tayi ta fito sanye cikin doguwar riga Mara nauyi sosai ta wani English material fuskarta tayi fayau kowa yabita da kallo sbd zuwa yanzu da zancen cikin ya fito kowa yasani sai dukkanin alamomin cikin suka bayyana da kyau tanajin zuciyarta na narkewa cikin kunya me girma da tsanani Amma ta fuske ta qaraso tsakiyar palon ta nufi gefen Hanifan ta zauna tana satar kallon ummanta data miqe tana cewa”

Zata shige gida.

Anty Amina ce ta kalleta bayan tafiyan umman tace”

Uwar biyu angama kukan borin kunyar?
Yanzu kowa ya daina biyewa kukanki da borinki tunda angano kukanki da borinki daban aikin da kike dabam.

Qaramar dariya Hanifa tayi Mara sauti tana kallon Anty Amina tace”

Please Anty Amina karki saka tafasa zaman Takoma daki Mana.
Kallon Naj tayi a natse cikin kulawa tace”

Maman baby Yaya?ya jiki jikin?

Banza tayi musu duk su dukan tana sake daurewa tana Hana kanta komawa daki,
Hajjo ta katse zancen da cewa”

Kar Wanda yakuma yimata maganar daba ita takesoba,
Kubarta taji da laulayi daya dameta.

Itadai har lokacin Bata ce komaiba saima sake fuskewa datai tana tambayar Hanifan Yaya jikin.

Anan gidan Anty Amina ta wuni sunata firarsu itadai Bata wani saka Baki sbd gabaki daya bakinta ya mutu a gidan,
Ko dataji Dadah tashigo sulalewa tayi ta shige dakin hajjo sbd Kar Dadah taqara Mata wani tonan asirin Dan kuwa tasan Dadah tafara kenan daga yanzu.

Da daddare su kadai Sukaci abinci batareda Shiba Hanifa Kuma duk wani abinda tasan Naj din ta nacewa ci a kwanakin Haka tasa aka kawo Mata duk da tana cikin radadi na rashin nata cikin Amma tana farin ciki dana ‘dan uwanta da Aminyarta.

Washe gari ma Haka suka wuni tana ta kokarin kawar da Jin nauyinta sbd ganin hajjo ta share maganar laifinta na maganar cire cikin Kuma ta Hana kowa tada maganar,
Kwana biyu tana Jin nauyi zuwa gaida Dad Alfa qarshe dai Haka ta hakura taje har palonsa gaishesa jiki ba nauyi ta fito
Tana fitowa taci Karo da Hannah tafito sashen Marshal suna tare fuskarsa tayi wani irin fresh sbd hutun dayake samu kwana biyun da baya fita koina Yana part dinsa gabaki daya skin dinsa yasake kyau,Yana sanyeda fararen Kaya qafafunsa sanyeda slippers na gucci
Hannah na ganinta ta sake matsowa kusadashi sosai tana sake karya murya tana cewa”

Marshal please zanbika Nima akwai program dazan attending acan tunda sati biyu ne zuwa uku zaka dawo I really want to go with you.

Dan kallonsa Naj tayi tayiwa fuskarsa kallon seconds kafin ta dauke idonta tana dauke kanta tana wucewa sukuma suna bayanta har cikin palon hajjon
Tana Shiga ta nufi hanyar dakinta batareda ta tsaya gurinsu Hanifa dake zaune palonba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 43_*
Tana shiga dakin nata jin tayi numfashinta na toshewa ta nufa windows din dakin da ba’ata taba budewaba ta yaye curtains dinsu ta bude tana shaqar iska Dan Kamar zata sanqame takeji.

Iska ta shaqa sosai agurin har sai daya fara Mata yawa sbd Ana Dan iska sosai agarin da sanyi,
Shiru tayi tareda fadawa tunani me zurfi na yanda komai ya sauya a rayuwarta tadawo yanda take yanxu,
Ahankali takai hannu tana dafe cikinta bugun zuciyarta na sauyawa da tsananin so da qaunar jariri ko jaririyarta,
Tabbas tanajin shauqin kauna irin ta uwa ga cikinta ta lumshe idanuwanta dasuke ta cikowa da hawaye tana maidawa ahankali sbd qamshin turarensa daya shiga hancin nata ta bude idanun suka sauka akansa ya wucewa ta makeken windon kyakkyawar fuskarsa datafi komai cikawa mutane ido tana a Dan sake Hannah nataredashi har lokacin.

Dauke kanta tayi daga kallonsu tana rufe windows din Takoma Kan sofa zata zauna saikuma ta fasa ta nufi toilet tana wanke fuske fuskarta datake Jin idanuwanta na yaji yaji.

Da daddare Koda suka zauna cin abinci da wani irin yanayi na sanyi tafito sbd gabaki dayama zazzabi taji tanaji me qarfin gaske Amma ta daure ta fito sbd abinda aka tambaya tanason ci shi aka dafa
Cikeda kulawa hajjo ta kalleta tana cewa”

Najma Lafiyanki kalau ko?
Banason ganinki wani iri,akwai abinda kikeji ba daidai ba?

Dan qaqalo murmushi tayi tana Hana kanta kallon inda yake zaune gabaki daya hankalinsa baya kansu Babu alamarma zai nuna yasan da qaruwar mutum agurin ta girgiza Kai ahankali tana zaunawa tace

Lafiyata kalau hajjo.

Hanifa ce ta zuba Mata abinci ta aje Mata gabanta tana cewa”

Orange juice din ko tea???

Ruwan sanyi kawai,thank you” tafada muryarta Bata fita Sosai sbd abinda takeji a zuciyarta.

Ruwan Hanifa ta zuba Mata masu sanyi zata miqa Mata sai alokacin ya dago fararen idanuwansa ya yiwa Hanifan wani kallo Kai tsaye ya bude Baki yace”

Bazata qara Shan ruwan sanyi ba ko bana nan, okay???

Qin saka Baki hajjo tayi sbd gskiyarshi ce Kuma tunda shine me Matar da cikin Dole ya fada yanda yakeso ayi din tunda lafiyanta Dana cikin yake karewa.

Hannun datakai zata amsa cup din ruwan ta dagakata daga karban tana Jin wani irin nauyi a zuciyarta na shikenan tata taqare tunda ga komai Nan Yana sauyawa Babu Kuma yanda ta iya.
Janye hannunta tayi tana Dan cigaba da tsakurar abincinta tana ci zuciyarta na harbawa sbd gabaki daya takasa takasa Jin idanuwansa akanta,aje cokalin hannunta tayi tareda daukan tissue ta goge Baki Yana miqewa,
Hanifa ce tafara kallonta zatai mgn hajjo ta rigata da cewa”

Najma lafiya kuwa?
Kin qashine?
Ko ruqayyat zata dafa Miki wani abun ne idan bakyason wannan din?

Na koshine zansha tea anjima kafin na kwanta karna ciki cikina da yawa shiyasa.

Ok Zan dafa Miki tea dinma da kaina Hadi na musamman Zan Miki” cewar Hanifa dake kallon Naj din cikin kulawa sbd lurada yanayinta na rashin sukunin datake ciki sbd Marshal din daya daina cin abinci taredasu kwana biyun sai yanzu.

Tana shiga daki wanka taso Yi Amma tanajin sanyi Sosai Dan Haka sauya kayanta kawai tayi ta zauna tana kokarin duba wayarta Amma gabaki daya batada Jin Dadi Rai tayi jefa da wayar a gefenta tana rintse ido.

Hanifa ce tashigo daukeda tea din a Trey cikin cup Yana tiriri sai cake da daughnuts guda guda uku uku a plate ta qarasa gefenta ta aje Kan table tana zaunawa ta janyo Mata tana cewa”

Hey sweetie ga tea dinki harda daughnuts ma nakawo Miki.

Kallon Hanifan tayi ahankali tareda sauke numfashi da ajiyar zuciya ahankali ta dafa hannunta cikin sanyi tace”

Hanifa banajin dadin zuciyata.

Kallonta Hanifa tayi tana daukan Mata tea din ta miqa Mata cikin kulawa tana cewa”

Komai zai daidaita kawai ki cire damuwar komai ki nutsu ki karba wannan rayuwar Haka Allah yariga ya tsaro Miki,
Jalal shine zabi mafi kyawu da alkhairi da Allah yayi Miki Kuma bana tunanin hakan zai sauya duk da dai nasan kinyi ba daidaiba tunanin zubar da cikin Kuma da boyemun,shin harminyi nisa Haka da Zaki kasa sanardani sirrin abin dayake faruwa a rayuwarki?
Nasan nauyin fada hakan kikaji sbd abune dayazowa kowa da mamaki da shock tunda duk Babu Wanda yayi tunanin kebewarku Nima danasan Kuna kebewan banyi tunanin kun samu kusanci da junaba irin Hakan,
Duk da hakan kowa yayi farin ciki da wannan qaruwar,muna farin ciki da wannan cikin Naj,
Shin kinsan irin tsananin so da qaunar da MARSHAL kewa cikin Nan naki?
Yana son na haihu sbd yanada son yara duk da kamewarsa da miskilancinsa saidai Ni Allah Bai baniba shiyasa yanzu yake yiwa cikin Nan naki qauna me girma duk da baya nuna hakan ne sbd me din dakika bayyanarda tsanarki akansa da cikin ta hanyar yunqurin zubarwa, Naj gskia bakiyi tunani anan ba.

Rufe idanuwanta tayi ahankali tanajin ‘dan sanyi na sauka a zuciyarta data samu tayi mgn da Hanifa ta rage damuwarta da nauyin zuciyarta ahankali tafara shan tea din ta kalli Hanifa tace”

Thank you.

Murmushi Hanifa tayi cikin kulawa tace”

Anytime my baby maamah.

Har dare sosai Hanifa na dakin Naj din tana tayata Yar fira da taimaka Mata Tasha maganin da Dr sa’id yace abata Saida Naj din tayi bacci kafin ta fice tayi Nata dakin
Tana fitowa palon har lokacin Yana zaune Yana duba wayarsa ya dago ya zuba Mata idanuwansa ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda qarasowa gurinsa tace”

Kaman yanda kafada akwai zazzabi sosai ajikinta Amma ya sauka tayi barci.

Gyada Mata Kai yayi tareda miqewa ya nufi kofa ya fice bayan yace Mata goodnight ahankali.

Ajiyar zuciya tayi bayan ficewarsa sbd ko Babu fada tasan irin so me qarfi dake cikin zuciyarsa,ita kanta Naj din wahalarda kanta kawai takeyi tana cutar kanta sbd tunanin girman banzan da shedan ke saka Mata.
Daki ta nufa ta shigewarta tareda rufo kofar.

Washe gari tunda safe Hannah ta shirya Masa breakfast zuwa karfe Tara da rabi harta kammala komai ta nufa dakinta tayo wanka ta shiryo cikin riga da skirt na atampa dasukai mata kyau sbd shape dinta daya fito Ras aciki ta feso turaruka ta fito kanta yafe da Dan qaramin gyale sosai Wanda ko gashinta Bai Gama rufewaba sbd Bata daura dankwalin Kayan native idan tasaka.

Ta fito Kai tsaye ta nufa sashensa tana Isa ko knocking bataiba aqeel me aikinsa daya bude kofar zai fito da kayan wankinsa dazai tafi dasu yace Mata baya ciki Yana sashen hajjo.
Ko tankasa bataiba ta juya ta wuce sashen hajjon tana Jin baqin cikin zuwansa can din tunda safe.

Da sallama tashigo palon bayan ta bude kofar tashigo batareda tayi Knocking ba
Da Dr sa’id idanuwanta suka fara yin Karo ta kallesa tareda kallon Marshal dake taredashi suna mgn sbd tunda safen yakirasa akan yazo ya duba Naj din sbd zazzabin data samu jiyan.

Baishigoba sai da Dr sa’id yagama dubata takoma daki kafin yashigo sashen.

Qarasowa tayi tareda nufar hanyar dining ta ajiye basket din data shigo dashi tadawo tana wani irin juyarda ido tace”

Good morning Marshal¿

Batareda ya kalletaba yace”

Kinga inada baqo ko?

Kallon Dr sa’id tayi tareda Dan qaqalo murmushi tace”

Ina kwana Dr?
Waye ba lafiya Naga Dr a gidan tunda safe?”tafada cikin nuna damuwar qarya.

Hanifa data iso gurin tace”

Uwar ‘yayansa ce ba lafiya.

Waiwayowa tayi cikin wani irin bayyananen yanayi na mamaki da rashin fahimtar zancen tace”

Uwar ‘yayansa? Yanada wata uwar ‘yayance dama bamuda masaniya?

Murmushi Hanifa tayi tana cewa”

Seriously Hannah???
Zakice bakisan matarsa nada ciki ba bayan kece Kika fara sanar Masa da maganar cikin idan natuna maganar danai da Dan uwana daidai.
Idan bakisan uwar yayansaba ai kinsan matarsa ita nake nufi.
Kiyi Murna Hannah Zaki zama Aunt.

Wani mugun ashar ta saki batareda tasaniba Allah yasa marshal baijiba sai Hanifa kawai datace”
Nagode.

Waiwayawa tayi tana kallon Marshal dake sallama da Dr sa’id zai tafi
Idanuwanta suka fara ganin wani dishi dishi sbd yanda zuciyarta tadauki zafi take tana bugawa kamar ma ta fara fashewa take ta yanke jiki agurin ta zube jikin Marshal daya tareta batareda yasan meyake faruwaba tsakaninta da Hanifa Dan gabaki daya hankalinsa nakan Dr sa’id suna maganarsu basusan me su Hanifan ke fadaba.

Dan jijjigata yayi Yana kallon Hanifa yace”

Meya sameta?

Naj data fito daga daki Kamar wadda aka Kira Hanifa tafara kalla ganin ta tsaya kallon Marshal da Hannah ke jikinsa a sume Yana Kiran sunanta.

Juyawa Hanifa tayi ta nufi kicin ta dauko robar ruwan sanyi tana fitowa ta bude ta zubawa Hannah din gabaki daya a fuska take taja wani irin numshi tana bude idanuwanta ahankali tana ganin Marshal ne ke rungeme da ita wani irin kukan girmammen baqin ciki ya kufce Mata tana qanqame hannunsa take ya zuba Mata ido kafin yayi mgn saiga mum Malika da Hanifa tasa ruqayyat taje tafadawa dan tazo ta tafi da Hannah.

Cikin tsananin tashin take cewa”

Babyna me nake gani?
Meya sameki?
Lafiya?
Dan Allah kufan meya sameta.

Sai alokacin Marshal ya zareta daga jikinsa mum Malika ta rungumeta ganin irin tsananin kukan datake dayake basa mamaki shima sbd baitaba ganin Hannah a irin wannan yanayin na damuwaba harda kuka me tsanani irin.
Cikin kulawa ya dubeta zaiyi mgn sai alokacin ya lurada tsayuwar Naj agurin tun dazu wadda itanuwanta sukai wani iri sbd abinda takeji na toshewar numfashi ta dauke Kai daga kallon gurin da abin ke faruwa ta juya  takoma dakinta tareda rufo kofa Bata tsaya koina ba sai toilet tana sake wanke fuskarta sbd zafin dataji Yana sauka koina a garin.

Fitowa tayi ta qarawa AC dinta qarfi kafin ta Dan rage kayan jikinta sbd zafi takeji Sosai ta kwanta sanyin ACn na shigarta koina.

Hannah kuwa daqyar suka koma sashensu zuwa lokacin hankalin mum Malika yagama tashi tako Ina sbd kukan da Hannah keyi ya wuce Wasa ko abun sauki Dan Haka itama gurin dad tanufa Kai tsaye ta sakar Masa kuka tana sanar dashi halinda Hannah ke ciki akan Marshal da afarko ita zai aura yanzu Kuma ko tada zancen anqiyi itadai tanason ayi maganar auren Nan asan me yiyuwa.

Dad alfa Bai wani damu ko daga hankalinsaba akan zancen mum Malika din ya kalleta cikin kulawa da nutsuwa yace”

Ki rarrasheta ki fahimtar da ita bawai alqawarin aurene akai ba Amma dai zaiyi magana da marshal din yaji ra’ayinsa akan zancen,idan yanada niyar aurenta sai a saka lokaci ayi auren,idan ma Babu sai abawa masu neman Hannah din Dama su shigo aga Wanda za’ai dashi.

Wannan maganar tasa baqin cikin mum Malika ninkuwa tazo tafadawa Hannah yanda sukai da Dad Alfa din wani sabon baqin ciki me girma yaqara rufe Hannah tasake Jin sabuwar qiyayyar Naj na shigarta
Cikin baqin ciki tace”

Wlh mum Malika idan har Marshal yace Bai zaba aurenaba bazan Bari Naj ta Haifa cikin Nan ba saina zubar dashi tareda fatar tabi cikin zuwa inda zasa.
Da wannan Hannah da mum Malika suka daga hankalinsu suka Shiga tashin hankalin abinda zai biyo baya gashi dad Alfa din Kuma baice dasu komaiba har zancen na maganar sati
Gabaki daya Hannah ta rasa nutsuwarta akan ta qwallafa ran wannan karon auren takeso Kota Yaya,
Gurin Marshal da kowa na gidanma cewa sukai Hannah batada lafiya sosai sai Marshal din yadan rage kamewarsa akanta Yana Dan kiranta a waya yaji Yaya jikin nata sbd yariga yasan irin Nacin sonsa datake sbd hakan yasa baya wulaqantata Dan koba komai Wanda yace Yana sonka yafi Wanda yace baya sonka.

Hakan Dake faruwa yataru yasake sakarwa Naj wani ciwon rashin sukuni da walwala ta Rasa inda zata saka ranta gashi ummanta Bata daukan wayarta idan zata shekara tana Kira sbd fushin datake da ita har yanzu.

Shikuma Dad Alfa Yana sane yaqi yin maganar sbd duba da yanayi na juna biyun Naj din bayason taji maganar auren Marshal da Hannah ta fita tashiga wani hali ga ciki ajikinta gefe daya Kuma ga mum Malika ta daga hankalinta ta damesa da koke koken rashin lafiyan Hannah Wanda yake na qarya Dole ya yanke shawaran magana da marshal da niyar zancen bazai fitaba sai bayan haihuwan Naj.

Yau da daddare Zaune suke a dining suna cin abinci gabaki daya Naj cin abincin kawai takeyi batada wani appetite,
Hajjo ta Dan dago ta kalli Marshal din dake Shan Ginger tea me Zuma ahankali,
Cikin nutsuwa da maida dukkanin hankalinta akansa tace”

JALAL dazu mahaifinka yamun maganar Aurenka da Hannah shin……
Wata mummunar sarqewa Naj tayi tana jero wasu wahalallun tarin dake fitowa da qarfi da zafi…
Da sauri hajjo tace”

Hanifa maza Bata ruwa tasha,
Abincin yamiki yaji ne Najma??

Ruwa Hanifa ta zuba da ssauri tana kaiwa bakinta tana bata,
Kadan Tasha ta janye hannun Hanifan
Idanuwanta sunyi jajir take sbd zafi da radadin tarin sarqewar dan wani irin zafi takeji a kirjin nata
Ta dago jajayen idnauwan ta kalli Inda yake zaune har lokacin Bai dagoba tea yake Sha ahankali,
Ta miqe tsaye tareda barin gurin taqarasa dakinta ko gani Sosai batayi sbd zafin da kirjinta ke mata
Tana shiga daki toilet ta nufa direct ta sakarwa kanta ruwan sanyi a shower sbd abun Dake ciko Idanuwanta da batason su sauko.

Tana barin gurin ya dire cup din hannunta tareda miqewa batareda ya bawa hajjo amsar tambayarta ba gabaki daya zuciyarsa zafi take dauka da abinda ya farun.
Hajjo kuwa da wani kallo tabi inda dukkaninsu sukabi tana girgiza Kai tareda sharesu tana cigaba da cin abincinta hankali kwance dan tana sane tayi maganar.
##MAMUH#

Na shekaran jiyane da banyiba na biya bashinsa🙏

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 44_*
Bayan fitarsa Hanifa kasa nutsuwa tayi da yanayin Naj saidai batace komaiba sbd ta fahimci dalilin hajjo na hakan sbd wannan rayuwar dasuke tsaf dadin bakin mum Malika da ikonta na zama Mata agurin Dad Alfa zai iya sawa aure tsakanin marshal da Hannah ya yiyuwa Wanda bawai suna qiyayya da hakan bane har cikin ransu itada hajjo basa kaunar Marshal yayiwa Naj kishiya sbd ko auren Mata Gama tantacewaba da dadinsa da komai ayi Mata kishiya yanzu bazai yiyuwa ga ciki ajikinta wata damuwar zata iya kamata Dan Haka itama Bata bayan auren Marshal ko wane iri bama na Hannah kawaiba da koma waye.

Tana Gama cin abincin ta miqe zata wuce hajjoma data rigata miqewar cikin kulawa tace”

Je kidubo Mana ita tana Lafiya kuwa¿

Hanyar dakin Naj Hanifa ta nufa ta bude Kai tsaye ta tura tashige tareda rufowa tana kallon dakin ganin Naj din Bata ciki taji motsin ruwa a toilet tasan tana toilet ta nema guri Kan gadonta tana kokarin hawa ta dakata tunanin ranarda Naj din ta hanata hawa Kan gadon na dawo Mata,
Ta dan ja baya tana sake kallon gadon abun daya faru ranar Yana dawo Mata,ranar da gskiyar ruqayyat kenan anan dakin Marshal din yakwana???
Kenan….
Girgiza Kai tayi tana Hana kanta cigaba da tunanin sbd Bai kamata ba tafasa hawa gadon tareda koma Kan sofa ta zauna tana sakin boyayyan murmushi sbd mamakin cikin Naj daya shigi kowa sbd abune da ko a mafarkin lulaye Babu Wanda yataba hasko hakan zata taba faruwa a yanzun,
Ki ita datasan wasu abubuwan na kebewansu da lokacinda ya dauketa daga office sukai tafiya Bata taba tunanin wani Abu zai Gama haduwaba a lokacin yanzu iya tunaninta laifi Naj din Tai Masa ya dauketa sbd ya hanata zuwa office amatsayin hukuncinsa Ashe babban aikine yasamu Naj dinta.

Jin Abu yayi yawa shiru Shiru yasata aje tunaninta ta juya tana kallon kofa cikin mamaki kafin ta miqe tsaye ta Isa jikin kofar tace”

Naj, Naj wankan da yawa fa baiyiba kinsan yanzu sanyi ba Wasa ya kamaki sbd cikin jikinki,
Idan sanyi ya kamaki zai illata babyn please kibar wankan Haka ki fito kokuma nashigo na kashe ruwan.

Komawa tayi tana kokarin zama taji Naj din Bata kashe shower ba ta fasa zaman ta nufi toilet din Kai tsaye tana budewa daidai Naj din na Gama daura towel da qyar sbd rawar sanyin da dukkanin jikinta keyi Dan ruwan sanyine ta sakarwa kanta.

Da wani irin kallo Hanifa ke binta cikeda mamaki ganin har kanta tayi wankan sai tsiyayan ruwa Kan keyi ta janyo wani towel da sauri tana Dora Mata akai ta jawota kamar wata qaramar yarinya suka fito toilet din dukkanin jikin Naj rawar sanyi yakeyi sosai zaunar da ita tayi bakin gado tana goge Mata kanta cikin kulawa da damuwa take cewa”

Naj menene hakan kikaiwa kanki?
Kinsan hakan zai iya saki ciwo
At least yanzu ki ringa tunanin abindake jikinki kafin kiyi wani abun hi sanyi gashinan a fili ya kamaki
I have to call Marshal sbd yakira Dr sa’id bakida Lfy gskia.

Aje towel din hannunta tayi ta nufi waje Dan dauko wayarta sbd rawar sanyinda Naj din keyi yayi yawa ko mgn takasa yi sai idanuwanta dake cikowa da hawaye suna komawa.

Tana fita dakinta ta Isa da sauri ta dauko wayarta tadawo palon inda hajjo ke kokarin shigewa dakinta ta saka Kiran JALAL din kamar bazai daukaba sbd gabaki daya bayajin mgn da kowa a yanzu tunanin halinda cikinsa yake ciki yakeson samun nutsuwar Yi,
Daukar wayar yayi batareda yace komaiba ita Bata tsaya Jin miskilancinsaba Kai tsaye cikin damuwa tace”

Naj nata rawar sanyi kamar ma dai sanyin yariga yashigeta ta sakarwa kanta ruwan tsayi ta tsaya cikinsu,
Bansan yayama zance ba ko zanyi ka Kira Dr sa’id ka……

Kashe wayar tayi lokacinda tayi ido biyu dashi Yana shigowa palon cikin kamewa Yana sanyeda shirt ash kala da farin three quarter sai slippers din Gucci dake qafarsa ya qaraso tsakiyar palon fuska a kame kamar Babu damuwar komai aransa na Kiran da Hanifan Tai Masa ya kalli Hanifa dake kallonsa Kai tsaye yace”

Tana Ina?

Ha hannu ta nuna Masa dakin Naj din tana cewa”

Tana dakinta” kafin tai wata maganar ya juya ya nufa dakin yabi ta gaban hajjo data tsaya Jiran Hanifa tagama wayar tafada Mata ‘dumi zai ragewa Naj din sanyi da tea me zafi basai Ankira Dr sa’id ba.
Hajjo na ganin ya nufa dakin ta juya ta shige dakinta bayan tacewa”

Hanifa kisa ruqayyat ta dafa Mata tea me zafi takai abata Tasha.

Shigewa Tai dakinta sbd ita yanzu al’amarin nasu su keyi itace me Jin nauyi tunda cikin Nan ya bayyana takasa yadda da a sashenta duka wannan hidimar ke wakana Dan Haka gwara tana basar dasu sbd Kar taga abinda yafi qarfin tsufanta tunda Marshal shi ko ajikinsa
Cikinma Naj kawai ke dawainiya da kunyarsa shikuwa saima ikonsa na uban cikin dayake nunawa.

Kicin Hanifa ta juya ta nufa da kanta tahau dafawa Naj tea din Wanda zata saka Masa ginger kadan.

Zaune take bakin gadon har lokacin daureda towel din tana rawar sanyi idanuwanta a rintse sosai takejin sanyin har cikin qamshinta,
Ana zuba sanyi a garin sosai ga ruwan da matuqar sanyi Kuma ta saukesu tun daga kanta takuma Jima aciki.

Bude kofar dakin akai aka turo tareda rufewa ya tsaya a gurin tareda zuba idanuwansa akanta Yana Mata kallon dayayi kwanaki Bai mataba.

Ahankali taji qamshin turarensa na gauraya dakin yana shiga hancinta,
Dan motsawa tayi ahankali tareda bude idanuwanta dasukai ja ahankali ta kalli bakin kofar zuciyarta na narkewa da wani irin Jin tanason yin kuka idanuwansu suna Shiga cikin na juna batareda kowannensu ya dauke nasa idonba.

Cikowa idanuwanta keyi da hawaye suna neman gangarowa ta lumshe idanu jikinta na sake daukan rawar sanyin.

Dan dauke Kai yayi tareda sauke numfashi ahankali kafin ya zare hannuwansa daga aljihun three quarter wandon dake jikinsa ya tako ahankali ya qaraso inda take zaune Yana isowa gabanta baice komaiba ya sunkuya zai dauketa ta dago a Dan hawalce ta kallesa daidai fuskarsa datake daf da tata fuskar numfashinsu na haduwa sosai zuciyarta taqara tsananta bugu har kirjinta dake daure da towel Yana yin sama Yana komawa qasa.

Kirjin nata ya kalla da fararen idanuwansa sbd towel din Bai wani dauru sosaiba juyi daya zai iya sawa ya zame ya dauke idonsa akai tareda kallon fuskarta dashi take kallo itama
Ya dauketa Kai tsaye tareda nufar gaban mirror da ita ya zaunar Kan kujeran gaban madubin tareda janyo hand dryer saiga Hanifa tayi Knocking kofar dakin tana cewa” ga tea din takawowa Naj.

Aje dryer din yayi tareda komawa sofa ya zauna sai alokacin yace Hanifa ta shigo.

Shigowa tayi tana kallon Marshal din batareda ta kalli inda Naj takeba sbd Karta qara Mata jin nauyi ta aje Trey din da cup na tea din ke Kai tana cewa”

Ga tea zai taimaka tasamu dumin ciki dakuma rage sanyin.

Lokacin ta juya tana cewa”

Zanje nayi waya Allah ya sauwaqa.” Ta fice tareda rufe kofar dakin.

Daukan tea din yayi ya dawo inda take ya miqa Mata sai alokacin ya bude Baki yace”

Kisha.

Ahankali ta dago hannunta dake rawa ba musu ta karba takai bakinta tabude ta Dan kurba taji zuciyarta bataso zata iya Amai ta aje tana Dan rufe ido
Baice komaiba ya dauka dryer din Yana duddubawa sbd baisan ta Yaya zai iya busar Mata kanba tunda ba aikin maza bane.
Ajewa yayi dayaga zata Bata Masa lokacine kawai ga sanyin yana sake shigarta,
Wayarsa ya fidda ya saka Kiran Hanifa tana dauka yace”

Kizo ki Mata wannan drying din
Sanyin na sake shiganta banason nayi nayi nasata Jin zafi bansan ya akeba.

Dawowa Hanifa tayi dakin tana waya da mijinta har lokacin Dan Haka sama sama ta Dan busarwa da Naj din Kai sbd zuwa lokacin zazzabi me qarfi da zafi ya kamata daqyar take zaune a agaban madubin, Hanifa na gamawa ta fice ya taso yadawo ya Kama hannunta ya miqar yaga ko tsayuwar Bata iyayi sosai yakuma daukanta ya nufi Kan gadon dakin da ita ya kwantar tareda gyara Mata towel din jikinta ya nufa wardrobe dinta ya dauko Mata wata shirt me Dan kauri ya dawo bakin gadon ya tayarda ita zaune yana zare towel din jikinta zai saka Mata.
##MAMUH#

*KUYI MANAGE YAU UZURI YA DAN KAMANI ZAMU KAMA GOBE INSHALLAH.*

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 45_*
Rintse idanuwanta tayi ahankali tana Dan juyar da kanta gefe kadan ta riqe hannunsa da hannunta da babu qarfin jiki tana Dan girgiza Masa alamar zata iya sawan da kanta.
Ba musu ya miqa Mata rigar tareda sakinta Yana komawa Kan kujera ya zauna tareda folding hannayensa Yana Dan dauke Kai daga kallonta zuwa Kan wayarsa dake vibrating na shigowar Kiran Hannah da sunanta Yafito Kan screen din wayar.

Idanuwan Naj sun sauka akan wayar takuma ga sunan me Kiran tadauke Kai tana qarasa zura rigar ajikinta ta zame ta kwanta tana rufe ido cikin tsananin azabar zazzabi me qarfi.

Tasowa yayi bayan ta kwanta yaja bargo ya rufe Mata jikinta bayan yasakawa dakin key yadawo ya zauna bakin gadon Yana Dan dafe kansa sbd sarawan dayake Dan masa.

Bai kwanta ba Sai dayaji zafin jikinta na qaruwa gashi dare yayi bayason Kiran Dr sa’id Dan Haka ya zare takalman qafarsa tareda kwanciya gefenta Yana jawota jikinsa ya shigar ya rungumeta sosai bayan ya zare rigar jikinsa itama ya zare Mata tata sbd su samu body contact din dakyau zafin jikinta ya rage.

Lumshe fararen idanuwansa yayi lokacinda ta zagayo da hannuwanta biyu masu taushi ta qanqamesa sosai tana fitarda numfashi me zafi sosai Wanda shima zafin numfashin nata sauka yakeyi a qirjinsa Yana shigarsa har cikin zuciyarsa,
Komai nata jinsa yakeyi cikin jini da jikinsa shiyasa yakejin qiyayyar data nuna Masa shida da ‘dan alhakin magajinsa har cikin ransa.

Kyakkyawar fuskarta dake cikin kirjinsa ya zubawa ido yana sakejin kowane bugun zuciyarta da numfashinta Dake sauka jikinsa suna sake Shiga zuciyarsa Kai tsaye suna Masa illa.
Rufe idanuwan yayi Yana Dan juyar da Kai ahankali kafin yasake rungumeta da hannayensa dake zagaye da qugunta da bayanta.

Sai tsakiyar dare cikin bacci zazzabinta ya sauka zufa ya ‘dan zuwar Mata,numfashintama ya sauya yafara fita ahankali ahankali,jikinta ma yasake saki gabaki daya ajikinsa har lokacin hannuwanta na rungume dashi nutsuwar baccinta ya sauya yanayinsa cikin kwanciyar hankali da samun sauki.

Ahankali ya Dan bude idanuwansa da ‘dan bacci acikinsu Yana sake kallonta tsawon seconds kafin ya gangaro da hannunsa ya Dora Kan mararta data fara Dan qarfin da tasowar cikin kadan,ya shafa cikin tareda sakin wata irin sahirtacciyar ajiyar zuciya akaro na farko dayaji ‘dumin inda ‘dansa yake kwance,farin ciki da nutsuwar hakan yasashi sake kallon fuskarta har lokacin hannunsa na Kan mararta yanajinsu itada cikin akoina na zuciyarsa,ya matso da fuskarta ahankali yakai bakinsa yayi kissing goshinta Yana lumshe idanu.

Saukar dumin kiss dinsa a goshinta tajisa cikin baccinta dayake dab da warwarewa dama sbd yunwa,
Ta bude idanuwanta ahankali batareda ta motsaba shikuma lokacin idanuwansa na rufe ta dago idanuwanta dake wani irin lumshewa ta zubawa fuskarsa tareda sauke wani siririn numfashin Jin hannunsa akan mararta,gashi ba rigunan ajikinsu su dukan.
Kasa motsawa tayi ta maida idanuwanta ta rufe tana kokarin saita numfashinta dake qara gudu zuciyarta na bugawa.

Ajikinsa yaji alamar ta tashi sbd numfashinta Dake sauka ajikinsa yaji ya sauya,sai hannuwanta dake zagaye dashi datake dan motsawa tanason janye hannuwan Amma Kuma takasa sbd motsinta zai iya tadasa Kuma Bata buqatan hakan sbd rashin kayan dake jikinta.

Bude idanuwansa yayi suka sauka cikin nata dake kansa
Ta janye nata idon tana juyar da Kai ahankali.

Dafe goshinsa yayi Yana Dan fitarda numfashin ciwon kan dake damunsa sbd gabaki daya baisamu bacciba ya janyeta daga jikinsa Yana tashi zaune.

Agogon gefen gadon ya kalla yaga time yanajin lokacinda ta sauka gadon ahankali ta dauko riga ta saka ajikinta ya zuro qafafunsa qasa tareda zura takarmansa ya miqe tsaye Yana gyara tsayuwa ya kalleta fuskarsa na bayyanarda ciwon Kan dayakeji ya bude Baki a natse yace”

Akwai abin Dake damunki yanzu?
Ba wani matsala?

Batareda ta juyo ta kallesaba ta ‘dan gyada Kai tana bude Baki cikin yanayi na taqaita mgn tace”

Am fine.

Numfashi ya sauke ahankali kafin ya sake kallonta yace”

Ki koma ki kwanta Hanifa zata kawo Miki abinda zakici,take care.

Juyawa yayi ya nufi kofa ya fice Yana saka Kiran Hanifa a wayarsa kusan Kira hudu Ana biyar ta dauka sbd bacci Kai tsaye yace”

Please abata wani Abu taci yunwa ya tasheta idan taci Takoma bacci.

Kashewa yayi Yana qarasawa sashensa ya bude yashige palonsa tareda nufar bedroom dinsa Kai tsaye gado ya nufa Yana kashe wayarsa yayi wurgi da ita ya hau gadon ya kwanta Yana rufa idanuwansa a rufe.

Bayan fitarsa dakin kofar tabi da kallo da Dan mamakin yanda ya iya fahimtar yunwa takeji,
Meyesa kusan komai nata Yana fahimta bayan ko kulawar arziki Bata samu daga garesa tunda gashi har zaiyi aure,
Baqin ciki goma da Shirin qanin qawarta cikinsa ajikinta,zai nunawa duniya matsayinta ta hanyar auren wadda yakeso,ita shikenan tagama tashi aiki ba aure,ba miji,ba aikinta,ga fushin ummanta da Dattijo akanta..
Ji tayi idanuwanta na cikowa da hawaye sbd batada inda zata tafada damuwarta,
Anty Amina ce da Hanifa suke sanin damuwarta,Hanifa Kuma Dan uwantane ba Daman Mata mgnnan anty Amina Kuma zatai Mata Allah yaqara.

Shigowar Hanifa dakin daukeda plate din indomie da dafaffen kwai yasata maida hawayenta tana dagowa ta kalla plate din tana Dan sake fuskarta daga yanayin na damuwa.

Aje Mata plate din Hanifa tayi cikin kulawa tana cewa”

Yaya jikin?
Gyada Kai Naj din tayi tana dawowa kujera ta zauna tana daukan spoon tafara cin indomien tana cewa”

Thank you Hanifa.

Anan dakin Hanifa takoma tayi kwanciyarta akan doguwar sofa sbd sosai baccinta ke cinta indomin ma daqyar taiya hado Mata ita Allah yasa akwai dafaffun kwai a fridge ta jefa Mata daya aciki.

Taci indomin bawani sosaiba sbd tayi Mata yaji Tasha ruwa ta miqe ta nufa toilet tayo wani brush da fitsari tadawo ta kwanta bacci yakuma dauketa.

Qarfe Takwas tasamu ta tashi daqyar ta lallaba toilet tayo alwala tazo tayi sallah tana istigfar na lattin datai itama Hanifa tayi lattin sallar sbd tashin dasukai tsakar Daren.
Tana gamawa Takoma ta kwanta Amma baccin baikuma daukantaba sbd jiyo maganar mum Malika da Hannah datai a palo sunzo gurin hajjo Kuma idan kunnenta ba zautuwa yayiba sai takejin Kamar kalmar sunan biki na fitowa daga palon.

Qarfe goma da wani Abu suna sashen Basu tafiba Kuma itama Bata fitan ba tana dakinta
Tayi wanka ta shirya cikin doguwar Turkish gown Mara ado da yawa coffee kala Takoma ta zauna tana amsa wayar Sarah datace tana tafe.

Haniface tashigo dakin tana cewa”

Naj har qarfe goma da rabi fa bazaki fito kici abinci bane?
Ko ruqayyat zata kawo Miki daki ne?
Lafiyanki kalau kuwa?
Akwai matsala ne?

Miqewa tsaye tayi tana nufo kofar a natse tace”

Lafiya kalau,naji hayaniya ne a palon nayi tunanin baqine.

Murmushi Hanifa tayi tana cewa”

Sabuwar sirikar hajjo ce sukazo gaisheta kinsan yanzu gaisuwar sauyawa zatai ta ninku tunda da uwa da ‘ya duk sun zama sirikan gida daya.

Qin kallon Hanifa Naj din tayi saima Dan qaramin yaqen datai tana qarasa fita kofar dakin zuwa palon.
Mum Malika ce zaune ta sake tana zubawa hajjo zancen fira kala kala abinda batayi tunda tazo gidan Dan iyakacinta da sashen hajjo gaisuwa tanayi Kuma take komawa sashenta Amma yanzu Kwana biyun sosai take bajewa a palon ta zauna tana isar hajjon da firarrakinda basa gabanta.

Hannah na zaune gefen mum din jikinta sanyeda riga da skirt na lace Babu dankwali akanta sai qaramin mayafi tana Dan saka Baki a firar duk Dan su burge hajjo da Hanifa wadda ita tashin fitowar Naj ne yake gabanta shiyasa ta miqe taje dakin.

Batareda Naj din ta kallesuba ta qaraso gurin hajjo ta zauna kusada ita cikin kulawa tace”

Good morning hajjo,
Kintashi lfy?

Da tsananin kulawa hajjo ta kalla Naj din tana cewa”

Lfy kalau natashi,Yaya jikinki?
Karki qara Shiga ruwan sanyi Najma,kin tashi hankalin mijinki ba gaira ba dalili gashi baisamu bacciba ya tashi da ciwon Kai me tsanani yau haryanxu baisamu yazo yayi breakfast ba inaga ma tunda kintashi kema bakiyiba Hanifa tayata ku hada abincin suje can sashensa suci din tunda Nan akwai mutane ma……

Mum Malika da Hannah dake kallon ikon Allah cikin takaici da baqin ciki
Mum din tayi saurin cewa”

Aa hajjo ai mu ba baqineba tayi zamanta anan taci abincinta tunda itama jikin sai ahankali sbd juna biyu sai shi Hannah takai Masa nasa din can tunda duk dayane ai.

Sai alokacin Naj ta dago ta kalla mum Malika din Kai tsaye tace”

Ina kwana mum Malika?

Da yaqe mum Malika din ta amsa tana cewa”

Lafiya kalau Naj,Yaya jiki jikin naki?
Ashema da zazzabi Kika kwana banjiba ai danice zanzo nayi jinyar sirikata da kaina,
Me ciki ba’ason tana yawaita yawo da aikin wahala ki zauna kici abincinki anan..

Hajjo shirunta tayi kamarma maganar mum Malikan daidai Tai Mata,itama Hanifa shiru tayi duk da mamakin mum din yagama cikata ba kunya ta Hana matarsa zuwa garesa Amma tana tura tata ‘yar saidai bazata tankaba itama sbd fadan na Naj ne idan bazata tsayawa kanta agurinsu ba ta Karba mijinta sukam sune shirye ne da niyar karbesa su riqewa kansu.

Naj ma shirun tayi tana jiran Jin abinda hajjo ko Hanifa zasu ce akan hakan duk da Babu niyarta na zuwa sashen nasa cin abinci dashi Amma taji Babu Wanda ya tanka saima kokarin tashi da Hannah tayi tana gyara qaramin gyalenta daya zame daga kanta ta nufi kicin din sashen tana Dan Kiran sunan ruqayyat da wani irin salon bada umarni.

Numfashinta ne ke qara gudun fita ta Dan danne tana kokarin miqewa tabar gurin mum Malika da Dadi yagama cikata ta kalli Naj din tana cewa”

Muje dining Naj Dita da kaina zanyi serving naki,ki daina Wasa da abinci is not good for your health…

Kai tsaye tana Dan daidaita kanta a natse tace”

No,thank you mum Malika banajin cin abinci zansha tea kawai ya isheni.

Juyawa tayi tana kokarin barin gurin anty Amina tashigo dauke da basket din abinci ta qaraso tana cewa”

Mum Malika kina Nan yau Ashe¿Ina wuni?
Ya jikin Hannah?Allah yaqaro lafiya.

Amin mum din tace cikin washe Baki.

Gurin hajjo ta qaraso tana cewa”

Hajjo barka da hantsi,
Antashi lfy?

Lafiya kalau Amina,Yaya Fatima dasu Dadah?

Lfy kalau hajjo,
Hanifa ta miqawa basket din hannunta tana cewa”

Ga breakfast din marshal dayace yau umma tai masa Zainab na makaranta Dole sainice nakawo.

Kallon babban basket din dake daukeda kuloli uku masu kyau da tsafta dukkaninsu sukai Banda Naj data saki numfashi ahankali tareda kallon Anty Aminar ta bude Baki jiki a sanyaye tace”

Anty Amina Ina kwana?

Tausayinta dukkaninsu su ukun sukaji sbd yanayin datai gaisuwar muryarta ta bayyanarda damuwarta da sanyin jikinta,
Kasa riqe tausayin Yar uwarta anty Amina tayi ta kalleta cikeda kulawa tace”

Lafiya kalau,Yaya jikinki?

Gyada Kai kawai Naj din tayi tana son tambayar ummanta amma sbd mum Malika dake gurin yasata dakatawa tana kokarin nufar dining ba kwana kwana Anty Amina data Dan fahimci abindake faruwa sbd taji maganar Hannah a kicin tana hada kayan breakfast din tace”

Naj ki dauka abincin ki Kai masa sbd nasan acan gurinsa zaici tunda yace umma ta hado masa.

Hannah ce tafito daukeda plates da qaramin flask na tea me zafi dayaji Zuma da kayan qamshi harda lemon kadan Anty Amina ta kalleta cikin sake fuska tace”

Hannah keda bakida lafiya kike aikin dawainiya Haka?
Ga wadda yakamata tayi Nan tunda mijinta ne Amma tabarki kina fama gaki Baki Gama warkewaba,
Naj ki karba ki wuce ki kai kintsaya kina kallo wani na Miki aikinda kece kike Dole kiyi,son jiki yamiki yawa hajjo da Hanifa sun sangartaki.” Taqarasa maganar tana kallon Hanifa dake basar da dariyarta ta hanyar fuskewa tana cewa”

Hajjo ce Bata Bari Naj na aiki a gidan Nan.

Hajjo qin Shiga tayi zancen tana kallon mum Malika tana cewa”

Me kike cewa Malika akan Kaya da Hajiya nafisat takawo?
Zankirata ta hado min set biyu na kayan kwatinan kayan biki Inshallah……

Duk da a rude mum din take da abinda Anty Amina tayi saidata juyo tana kallon hajjon cikin farin ciki tace”

Eh,eh, Haj nafisat tadawo daga UK kuna kayanta na Dubai ba duk sun iso komai akwai available kayan komai na sawa hidimar biki duk akwaisu latest wlh.

Hanifa data lurada halinda Naj tashiga ta miqe tareda karban kayan hannun Hannah ta saka cikin basket din abincin ta dauka basket din ta Kama hannun Naj suka nufi dakinta anty Amina ma na bayansu suna shiga dakin suka rufo anty Amina ta kalleta ganin yanda idanuwanta sukai jajir ta kalla Hanifa dake zaunar da Naj din da mamaki tace”

Kishinsa take kome?
Hannah na sonsa zata kula dashi fiyeda yanda ake tunani to menene na kishin hakan tunda bason….

Hawayen datake riqewane suka balle Mata ta rintse idanuwanta siririn kuka na balle Mata.

Cikin kulawa Hanifa tace”

Please Naj karkiyi kuka nasan kina cikin damuwa ta kowane bangare Amma kema kinsa aje hankalinki da tunaninki guri dayane ki rungumi aurenki,
Bansan meyasa kikejin zafin maganar auren Hannah ba idan anyi Amma Kuma Ina tabbatar Miki da idan aka cigaba a hakan komai zai iya tabbatuwa tunda ko yanzu din alamu sun nuna da maganar yiyuwar auren gashi Hajjo na maganar hada lefe.

Cikin kuka ta bude Baki tace”

Babu ruwana da aurensa Ni kawai idan zaiyi ya rabu Dani to.

Cikin zare idanu Hanifa ta bude Baki zatai mgn anty Amina ta katseta tana hanata da cewa”

To shikenan ma anhuta kifada Masa hakan,tashi kije kikai Masa abincin dakacan saiki fada Masa abindake ranki kuyi mgnr kukai karshe ko zaku Kai gobe zan jiraki anan saimu koma gida tare idan ya sallamokin.
Ga mamakin Hanifa kuwa miqewa Naj din tayi tareda goge fuskarta,
Anty Amina ta dauko turare taqara saka Mata tana cewa”

Qamshin abincin Nan kike Bari narage Miki.

Hanifama gyara Mata hularta da Bata Gama rufe gashinta tayiba tana miqa Mata qaramin siririn mayafi ta daukar Mata basket din suka fito suka fice hajjo tayi kamar bataga wucewarsuba tana magana da mum Malika wadda hankalinta yatafi gabaki daya gasu Naj din dasuka wuce itada Hanifa tana cewa”
Wannan hanifar anyi tsohuwar munafuka mara Imani.
Hannah kuwa kasa hakuri tayi ta miqe tabi bayansu da niyar itama zata dubo Marshal din tunda bayajin Dadine.

Suna kaiwa bakin sashen Kai tsaye Hanifa takai hannu ta bude kofar palon da wani irin sanyin AC da qamshin Rosalle roomfreshner da qamshin turarensa daya gauraya dashi suka daki Fuskokinsu zuciyarta na harbawa ahankali akaro na farko kenan tana saka ran dazata shiga sashen idan ba mantawa Tai ba.
Kama hannunta Hanifa Tai ahankali suka Shiga har cikin tsakiyar palon ta nufa dining ta ajiye basket din kafin ta juyo ta fito tareda rufe kofar.

Hanifa na fita bugun zuciyarta ya tsananta qamshinsa kawai take shaqa tako Ina a palon ta rintse ido tareda Dan dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi taji bazata iya abinda yakawota din ba ta juya zata nufa kofa ta buge da center tablet dake palon take tayi gaba zata kife taji hannunsa dakeda sanyin ruwan wankan daya fito yayo palon yayi Mata kyakkwan riqo Yana dawo da ita jikinsa da babu riga sai towel.
Daidai lokacin hannah tayi Knocking tareda Kiran sunansa cikin salon shagwaba da daukan hankali Wanda yasa Naj din qanqamesa batareda tasan tayi hakanba.
#MAMUH#

####################
*DATA!!DATA!!DATA!! PROMO😍😇🤗💃💃*
*Assalamu Alaikum*
*Batools Net.S
*muna sayarda DATA bundle akan farashi mae sauki, tuntubemu dumin yin subcription dinku*
*💃💃
*📶MTN DATA🌕*
*500MB 👉₦140
*1GB 👉₦ 240
*1.5GB 👉₦ 400*
*2GB 👉 ₦500*
*2.5GB 👉 ₦650*
*3GB 👉 ₦750*
*3.5GB 👉 ₦900*
*4GB. 👉N1000*
*5GB 👉₦1250*
*6GB 👉₦1500*
*10GB. 👉N2500*
*15GB. 👉 N3800*
*20GB. 👉 N5000*
*30GB. 👉N7500*
*(Valid for 30days)*
Balance, *461*4#* OR
*131*4#*
💃
Airtel data plan
1gb—550
1.5gb—750
2gb—1100
2.5gb—1350
3gb—1550
4gb—2100
5gb—2400
6gb—2750
10gb—3300
Balance*140#

Glo Data price
1.gb—550
2.9gb—1000
4gb—1500
5.8gb—2000
7.7gb—2300
10gb—3000
Balance *127*0#

9mobile Data price

1.5gb—1000
2gb—1250
3gb—1550
4.5gb—2250
11gb—4750
15gb—5500
Balance *228#
(All valid for 30days)
*CALL/SMS/WHATSAPP -* *08034450108
👇👇👇
*MTN 1GB @ 240

*Ana biyan kudi ta✔Bank*
*ACCOUNT NUMBER:*
1130713591
*ACCOUNT NAME : Fatima Abubakar Ibrahim,
*BANK NAME :Polaris BANK👇*
*
*PLS BA BASHI ❌❌❌*
One to tell Ten and Ten to tell others💃💃
Pls Don’t forget to share with family and friends🤝🤝
################

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 46_*
Ahankali ya saukar Mata da idanuwansa Yana kallonta Jin tafukan hannayenta ajikin nasa ta zagayosu bayansa,
Ta rufe idanuwanta tana qin kallonsa duk da tanajin Idanuwansa na yawo akanta gabaki daya ta Gama daga zafin jikinsa da dumin tafin hannuwanta….
Sake Dan buga kofa Hannah tayi tana Kiran sunansa cikin yanayi na sake shagwabar da murya,ya kalli kofar kafin ya maido da kallonsa kan Naj din dake jikinsa har lokacin Bata motsaba,Akaro na farko datake jikinsa batareda tafara kokarin kwacewa ba.

Zameta yake kokarin Yi ta sakar Masa jikinta gabaki daya daya Gama mutuwa da nutsuwar dataji tasamu a ‘yan sekannin sbd qamshin shower cream dinsa da yayi wanka dashi dake tashi ajikinsa na _TomFord Neroli portofino shower gel_ dayake shiga hancinta yana sata Jin dadinsa.

Kokarin budo kofar tashigo Hannah tafara kokarin Yi Naj din ta bude ido tana kallonsa da fararen idanuwanta tana sake kallon jikinsa da Babu Kaya sai towel,ta sauke Kai tana kokarin kawarda yanayinta dake sauyawa har lokacin hannuwanta na jikinsa,
Tsaf ya lurada yanayinta dakuma nutsuwarta ajikinsa ya sake kallon fuskarta datake juyarwa, ahankali yasaki wani murmushin mamaki da takaicin rigimarta baice komaiba ya dauketa cak ya juya daidai shigowar Hannah wadda bayansu kawai tagani da wucewarsu zuwa dakinsa.

Rufe idanuwanta tayi tana girgiza Kai da qarfi sbd Bata fahimtaba harma da yadda da abinda taganin,
Uban me Naj zataje dakin Marshal din tayi yanzu da Rana tsaka daga kawo abinci bayan ga antynta can tana gidan Bata tafiba,
Wani wawan jirine ya debeta ta zube kan kujera tana zaman Yan bori kanta takoina da zuciyarta suna daukan zafi da tiriri,
Wane bala’i da masifa da kata’i ne wannan take gani Yanata qara kusanto aurenta dama soyayyarta da marshal dinta.

A bedroom dinsa kuwa Yana Shiga bayan ya tura kofar dakin da qafarsa makeken lafiyayyan gadonsa daya gama cakuda da qamshinsa ya kwantar da ita Yana kallon fuskarta da idanuwanta ke rufe ta kasa budewa ta kallesa sai hakan yasake kunna abin dayakeji akanta,
Ya sunkuyar da kansa ya ranqwafo fuskarsa daf da tata numfashinsu Yana sarqewa Dana juna, bugun zuciyarta ya tsananta bugu ta sake rintse idanuwanta tana Jan wani irin wahalallen numfashin data fixgo da qyar sbd hannunsa me sanyi daya shiga cikin rigarta ya shafo cikinta zuwa mararta ta qanqamesa da ahankali tana sake riqe numfashinta Dake neman fin karfinta sbd hannun nasa shafa cikinta yakeyi.

Riqon datai Masa yasashi kallon fuskarta yaqasa hade fuskarsu cikin qaramin sauti ya bude bakinsa da qamshin _AfferVescent Mint mouth wash_ ya Shiga hancinta ahankali ya furta”

Kina buqatan mijinki ne????

Kunya da takaicin zancensa yasata yunqurowa zata tashi fuskarsu ta qarasa hadewa Bai tsaya komaiba ga bude bakinsa yana hadewa da nata suka saki ajiyar zuciya kusan alokaci daya duk da tata ajiyar zuciyan ta sanyin jikinsane daya hadu da nata Yana qarasa hawowa gadon gabaki daya Kuma har lokacin bakunansu na manne Dana juna yana kissing dinta cikin sanyi da nutsuwar Dake tayarda dukkanin tsikan jikinta.

Ahankali ya Dan bude idanuwansa dasukai ja ya Dan kalli fuskarta a wahalce idanuwanta har lokacin a rufe ya sake shigar da ita jikinsa Yana zare zip din doguwar rigarta ya zame Yana jehowa qasa tayo saurin shigewa jikinsa tana boye nata jikin tsoro na cika zuciyarta na abin dazai iya faruwa dan kuwa Bata manta irin jigatar dataiba a so biyun daya kusanceta wancan ba’a saniba tayi jinyar kanta yanzu idan wani abun yafaru kowa zaigane menene yafaru…..
Wuyanta dayake sakarwa numfashinsa me dumi ta Dan motsa tana neman rasa nutsuwarta har batasan tana sake manna Masa qirjinta ba dayashi sake hade bakinsu Yana binta da hannuwansa na yawo jikinta koina musamman wuyanta zuwa kirjinta da cikinta dayakejin kamar a haifo Masa abinsa yau.

Sosai al’amarin yayi nisa, tsoronta Kuma Yana qaruwa akan yanda zata kalla su hajjon idan Takoma sbd tabbas zasu ganeta sbd sanin yanda zata jigatu,kowama zai San metayi,
Ahankali ta dafe hannunsa dake Kan cikinta tareda Dan rintse ido ta budesu ahankali takasa kallonsa sbd wata irin kunya me girma datake ji
Ta dakatar dashi ta hanyar Dan janye jikinta kadan tana kasa kallonsa.

Wani irin boyayyan numfashi ya sauke tareda rufe jajayen Idanuwansa ya bude ya miqe Kai tsaye ya nufi toilet yashige ya rufo kofar yabarta kwanci tsakiyar gadon idanuwanta na cikowa da hawaye.

Ya Dan dauka mintuna sosai kafin yafito da sabon wankansa fes Yana sake zuba qamshin gel din wankansa fuskarta fresh Babu wani alamar bacin Rai ko damuwa
Kai tsaye gaban madubi ya nufa yafara shiryawa kaman yanda yasaba turaruka da oil kawai yashafa ya Sanya three quarter navy blue da farar designer polo shirt ya dauki wayarsa yafito Palo Kai tsaye
Yana zuwa ga mamakinsa Hannah na zaune a palon ya Dan yamutsa fuska cikin mamakin zamanta Kai tsaye Yana nufar dining yace”

Me kikeyi anan?
Ina nufin, how did you get in here??

Da jajayen Idanuwanta Dake tsiyayan hawaye ta kallesa saikuma takasa mgn ta fashe Dan siririn kuka tana dauke Kai daga kallonsa zuwa kallon hanyar bedroom dinsa da Batama tana sanin Yaya takeba ga Naj da Babu zato Babu tsammani hartayi Mata tazarce ta rigata Isa.

Dan dauke Kai daga kallonta yayi cikin Yar kulawar dayake Mata yace”

Akwai matsalane?
Kina lafiya?

Girgiza Masa Kai tayi tana share hawayenta dake sake tsananta gudu tace”

Matsalana shine Aurenka Marshal,
Rashin lafiyana son kane yake neman yimun illa, gskia nidai Nima auren nakeson ayi nasan matsayina agurinka.

Wani irin kallo yayi Mata na mamakin rashin sanar dasu da Dad Alfa baiyiba akan ra’ayinsa na rashin buqatan qarin aure zaiyi mgna bude kofar bedroom din Naj yasashi Jin ba zai fadawa Hannah dinba hakan yanzu ya kalleta cikin irin ‘yar kilawan daya Saba Bata Yana nufar dining yace”

Zanci abinci idan nagama Zan fita zakixo Dani.

Jin hakan yasa Hannah din hallonsa tana qarasa share hawayenta cikin Jin Dan farin cikin hakan da yayi Mata a gaban Naj wadda tafito sanyeda shirt dinsa datai Mata mugun yawa sbd bataga inda ya jefar Mata da doguwar rigartab…

Wani mugun yawu Hannah din ta hadiye zuciyarta na neman bugawa tana kallon dogayen fararen cinyoyin Naj din Dake fili bayyane suna daukan ido da haskensu sbd rigar da iyakacinta tsakiya zuwa Rabin cinyoyinta.

Naj kuwa Saida takawo tsakiyar palon ta lura da Hannah a palon cikin tsananin mamakinta daya kasa boyuwa a fuskarta duk da batai mgna ba take kallon Hannah din kafin ta Dan juya ta kalla inda Marshal din ke zaune a dining Yana cin abincinsa,
Juyawa tayi Takoma daki sbd yanayin kayan dake jikinta zuciyarta na ‘daci,
Kai tsaye tana Shiga ta ringa duba rigarta ido rufe sbd ta sanya tabar sashen kafin takaicin zuwanta ma tun farko yasan yanda yayi da ita.

Bataga rigartaba Dan Haka ta zare rigarsa Dake jikin nata ta Sanya wata jallabiyarsa fara data sauka sosai ta zube har qasa,ta tattara rigar ta rige ta nufi kofa ta fito.

Tana isowa palon ko kallon inda suke bataibata ta nufi kofa zata fita harta riqe handle na bude kofar taji anriqota tareda dawo da ita ahankali…
Ko Bata dagoba tasan shine tunda zuwa yanzu ta haddace qamshinsa da taushin jikinsa.,
Dan qwacewa takeyi tana mutsu mutsu Yana kallonta batareda ya kalla Hannah ba idanuwansa akan fuskar Naj din data bayyanarda matuqar bacin Rai da fushi yace”

Hannah Zaki iya bamu waje,
And next time karki sake shigowa Nan din,idan Zakiyi mgn Dani ne just call me basai kinzo Nan ba……

Sabbin hawayen baqin cikin Naj ne na dazu datake riqewane suka Dan gangaro Mata ta goge tana miqewa tsaye idanuwanta akan Naj data dakata da mutsu mutsun datake Jin abin daya fada ta juya zata fice ta tsaya tace”

Fitar dazamuyi fa???

Je ki shirya ganinan fitowa.

Tana rufe kofar bayan fitarta ya kalli Naj din data dago itama shi take kallo idonta wani iri ya Dan kame fuska ya bude Baki a natse yace”

Like seriously????
Ahakan Zaki fita daganan ki ratsa haraban gidan Nan ki Isa sashen hajjo?
Sake kallon wuyanta zuwa kirjinta yayi dasuka fito sosai sbd yawanda rigar Tai Mata yasake kallon qafafunta fili data Dan tattare rigar ya dan saketa Yana dauke Kai yace”

Kina buqatan tunanine acikin kanki?
Sbd nakasa gane Kan yara gareki kokuma na tsofi daya Gama tashi aiki.

Maganarsa tasata Bata fuska tana dagowa ta kallonsa kamar zatai kuka ta bude Baki zatai mgn ya zubawa bakin ido maganar takasa fitowa tahau hadiye numfashi,
Ya kalla cikin idonta Yana cewa”

Uhum fada abinda Zaki fadan??

Juyar da idanuwanta tayi dasuka kusan sakashi loosing balance ya dafa kujerar dake bayansu Yana Mata kallon mamaki duk da ita batamasan tayi ba..

Ta sake bude bakin ahankali Cikin wata qaramar murya me taushi tace”

Stop looking….sake loosing balance yayi suka zube zaune kan kujera tana Kan cinyoyinsa ya Dan rufe ido yana sauke ajiyar zuciya ya bude ya kalleta cikin yanayi nason tabbatarda wani Abu ya matso da fuskarta zuwa tasa ya hade goshinsu Yana kallon idanuwanta data kasa dagowa ta kallesa dasu yasakar Mata iskar bakinsa data Kuma kashe nata jiki da yanayin datakeji akansa
Ahankali ya hade bakinsu Yana kissing nata tareda zagayo hannuwansa qaramin qugunta ya rungumota suka matse sosai tana sakar Mata jikinta gabaki daya.

Daqyar ya iya controlling kansa ya saketa tareda dagowa ya kalli fuskarta datai ‘dan ja sbd yamutsarta da yayi
Ta sauke Kai tana kokarin miqewa cikin kunya ya riqota tareda dawo da ita yabata lafiyayyan light kiss a kumatu kafin ya bude Baki ahankali yace”

Kinason hanani fitane???

Dan kallonsa tayi tana rabuwa da jikinsa ahankali ta bude Baki tace”

Bansan me kake mgn akai ba.

For the first time daya sakar Mata murmushin dayasata kasa dauke ido akansa harsaida ya riqo hannunta yakai bakinta bakinsa yayi kissing cikin yanayin daya sake Hargitsa zuciyarta da wasu sabon feelings yace”

Karki damu zata bar Miki space dinki na baby maamah dina…..

Wani Dan qaramin numfashi ta hadiye daqyar ahankali kafin ta juyo ta kallesa da idanuwanta dasukai wani iri….

Kama hannunta yayi ya nufa dining da ita ya zaunar cikin kulawa yace”

Kici abinci Hanifa texted me cewan bakici komaiba.

Zuba Mata faten Irish da Naman kaza Babu qashi ko daya sai cabbage dasu carrots Dake ciki.

Kallon agogon dake hannunsa yayi sbd akwai inda zaije yayi wani aiki sbd tafiyansa dazaiyi jibi Dan Haka ya miqe ahankali ya nufi kofa Yana cewa”
Kici a natse okay??

Ficewa yayi yabarta zaune tana cin abincin badan hankalinta na kaiba.
Sosai taci abincin kafin ta miqe ta tattara kayan tamaida basket tadawo palon ta zauna tana tunanin yanda zata koma can cikin gida gurinsa hajjo sbd rashin suturar arziki Kuma gashi takasa tilasta kanta akan ta bijirewa maganarsa ta tafi a hakan,
Idan ma taje bazata iya shigaba I data fito da kayanta tsaf yanzu Kuma Takoma da wasu daban tace Ina nata sukeje??

Wasa Wasa sai gata har kusan la’asar a sashensa danma baccin qaqanikayi ya dauketa Amma Bai wani jimata ta tashi
Cikin sa’a ana la’asar saiga Hanifa takawo Mata wayarta da aketa Kira tana ganin Hanifan bayan tayita knocking tazo ta bude Mata kofar saitaji sabuwar kunyar kanta da takaici ya kamata ganin kallo daya Hanifa Tai Mata tana murmushin neman mgn tace”

Bacci kike Naj Kika bar anty Amina tanata jiranki haryanxu.¿

Kasa cewa komai tayi ta karbi wayarta tana komawa ta zauna cikin damuwa tace”

Dan Allah Hanifa kije kikawomin wata doguwar rigar nasaka tuntuni inason dawowa Bazan iya komawa da wannan kayanba.

Mayafin jikinta Hanifa ta zare ta Bata tana cewa”

Ki yafa wannan akan wuyan rigar saiya rufe shikenan.

Karba tayi ta yafa suka fito Naj din nata Kama jikinta kunyar hajjo na dawainiya da ita tun Basu qarasaba.
Suna shigowa palon Allah ya taimaketa hajjo Bata palon sai anty Amina data fito daga kicin sbd yau itace tayiwa hajjo tuwan Alkaman datakeso da miyan zogale tana ganinsu ta qarasa aje kulan dake hannunta kan dining tana fuskewa tace”

Bari banqarasa nazo mu tafi ko Naj?
Tun dazu nayita jiranki namayi tunanin ko kinwucene daga can.

Banza tayiwa anty Aminan sbd tagano kunyar dasuke Tula Mata itada Hanifan tareda ingizawa.

Dakinta tashige ta rufo tareda sakin ajiyar zuciya tana lumshe idanuwanta qamshinsa na shigar Mata hanci sbd rigarsa dake jikinta.

Sallah tafarayi har lokacin rigar tasa na jikinta takasa cirewa ta sanyo doguwar hijabi akai ta fito ta nufa kicin ta dauko cake da samosas da aka gama soyawa daga fridge taci tadawo dakinta tashige tana jin Anty Amina da Hanifa na mgna taqi tankawa ta shige sbd hajjo ta fito lokacin Kuma tasan ta fahimta komai itama.

A gidan Anty Amina ta wuni har dare sukai sallar magriba da ishai kafin suka fito cin abinci Wanda da qyar ta iya danne kunyarta ta fito zuwa dining din.
Tana zama taji shigowarsa a jikinta sbd qamshinsa da idanuwansa dataji ajikinta ta sauke wani boyayyan qaramin numfashi tareda ajiyar zuciya tana daukan cup din ruwa Tasha sbd bugun zuciyarta ya daidaita.

Sanye yake da wata jallabiyar fara sol dake sheqi Yana fitar qamshi me sanyi
Fuskarsa tana cika ido da kwarjini ya qaraso dining din ya zauna Yana kallon qatuwar hijabin dake jikinta
Ya saki wani sirrantaccen murmushi sbd gane har lokacin rigarsace ajikin nata.

Suna fara cin abincin Hanifa tace”

Tafiyan na Nan jibin kuwa?

Gyada Mata Kai kawai yayi Yana cin abincinsa cikin nutsuwa.

Hajjo dataji amsarsa ta Dan kallesa tana cewa”

Hannah ma tafiyar nata nanan kenan?

Itama gyada Kai yayi ahankali batareda yabude bakin ya amsaba..

Dagowa hajjo tayi gaba daya tana kallonsa tace”

Idan har Hannah zataje inaga zakaje da matarka itama koba komai zataga wani likitan acan tunda tafiyan bame dadewa bane..

Sai alokacin ya dago tareda kallon hajjon kadan kafin ya kalli Naj da cin abincin kawai takeyi ta Rasa appetite dinta.
Maida kallonsa kan hajjo yayi cikin nutsuwa ya bude Baki yace”

Bana tunanin hakan idan har ba itace da kanta tafada zataje dinba.

Kusan atare dukkaninsu suka kalla Naj wadda itama shi ta dago tana kallo zuciyarta na harbawa sbd batai tunanin ya fada hakanba tana tunanin umarnin hajjon kawai zaibi.
##MAMUH#

 

#############################

*DATA!!DATA!!DATA!! PROMO😍😇🤗💃💃*
*Assalamu Alaikum*
*Batools Net.S
*muna sayarda DATA bundle akan farashi mae sauki, tuntubemu dumin yin subcription dinku*
*💃💃
*📶MTN DATA🌕*
*500MB 👉₦140
*1GB 👉₦ 240
*1.5GB 👉₦ 400*
*2GB 👉 ₦500*
*2.5GB 👉 ₦650*
*3GB 👉 ₦750*
*3.5GB 👉 ₦900*
*4GB. 👉N1000*
*5GB 👉₦1250*
*6GB 👉₦1500*
*10GB. 👉N2500*
*15GB. 👉 N3800*
*20GB. 👉 N5000*
*30GB. 👉N7500*
*(Valid for 30days)*
Balance, *461*4#* OR
*131*4#*
💃
Airtel data plan
1gb—550
1.5gb—750
2gb—1100
2.5gb—1350
3gb—1550
4gb—2100
5gb—2400
6gb—2750
10gb—3300
Balance*140#

Glo Data price
1.gb—550
2.9gb—1000
4gb—1500
5.8gb—2000
7.7gb—2300
10gb—3000
Balance *127*0#

9mobile Data price

1.5gb—1000
2gb—1250
3gb—1550
4.5gb—2250
11gb—4750
15gb—5500
Balance *228#
(All valid for 30days)
*CALL/SMS/WHATSAPP -* *08034450108
👇👇👇
*MTN 1GB @ 240

*Ana biyan kudi ta✔Bank*
*ACCOUNT NUMBER:*
1130713591
*ACCOUNT NAME : Fatima Abubakar Ibrahim,
*BANK NAME :Polaris BANK👇*
*

 

######################
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 47_*
Kallonsa take tana juya maganar tasa a zuciyarta kafin ta Dan dauke Idanuwanta daga kansa tana kokarin basarda yanayin data Shiga akan tafiyar tasa da Hannah.
Cigaba tayi da cin abincinta ahankali cikin sanyi da nutsuwa
Tanajin idanuwansa akanta Amma taqi dagowa tana cigaba da cin abincin,
Hajjo ta kalleta Kai tsaye itama tana cigaba da cin abincinta tace”

Najma?
Zaki iya binsa kuwa?
Ko Dan sbd yanayinki kinji??
Kije can kiyi awon cikinki acan kafin kudawoma Zaki Dan samu hutu me kyau.

Hadiye ruwan data kurba abakin ahankali tayi tareda dagowa ta ‘dan kalla gefen gefen Hanifa data zuba Mata ido tana jiran Jin amsarta,
Shikuwa maida hankalinsa Kan cin abincinsa a natse yayi fuskarsa na bayyanarda wani sahirtaccen murmushin dabai bayyana ba duk da hakan Yana jiran yaji amsar tata.

Ahankali ta gyadawa hajjo Kai tana Jan numfashin Dake sarke Mata sbd kunyar zancen ta bude Baki ahankali ta Dan ‘dora da cewa”

Zanga likitan acan tunda kince.

Wani lafiyayyan murmushi ya sake ahankali lokacinda tagama fadar hakan,
Hanifa ma murmushin tasake tana boye dariyarta hajjo kuwa komai batai ba taci gaba da cin abincinta tana cewa”

Eh nace Kam,
Kije can kiga likita ki Dan huta.

Qarasa shanye ruwan cup dinta tayi tareda miqewa tsaye ahankali tabar dining din ta nufi dakinta tashige tareda rufo kofa tana sauke ajiyar zuciya da numfashi.

Zare hijabin daya isheta tayi ta aje tareda nufar kujera ta zauna tana Dan lumshe fararen idanuwanta ta bude ahankali tana Jin kunyar kanta sbd tuno irin amsar data Bata Kai tsaye batareda tayi nazarin maganar ba,
Yanzu shikenan kowa zaiji Kuma Ana gani zatabisa zuwa wata qasar bayan ansan idan sunje gida daya zasu zauna daga ita saishi….
Ita Kam Yaya zatai da wannan kunyar¿
Tun ranarda aka daura Mata aure dashi take Shan kunya kala kala musamman da cikin Nan ya bayyana shikenan gidansu yazama abin tsoron zuwanta sbd Dadah har ko yaushe taqi daina fadar taci Amanarsu tasakasu rarrashin banza suna tada jijiyan wuyan fada akan taqi auren saiga ciki,
Zancen mummunan hali na kunya me girma yake sata Amma Dadah taqi Bari.

Miqewa tayi ta zare jallabiyar jikinta ta daura towel ta nade rigar ta ajiye cikin wardrobe ta nufi toilet ta shige Dan tayi wanka ta kwanta da wuri ko zata samu baccin.
Bata wani jimaba acikin toilet din ta fito jikinta koina da ruwan wankan datai da ruwan zafi Wanda suka saka jikin nata har dumi yayi ta qarasa gaban mirror tana Dan tsane ruwan jikinta da qaramin towel ta shafa _Revitalizing body oil_ na _Tata Herper_ ta shafa khumrahs masu sanyin qamshi ajikinta ta nufi gurin kayanta ta bude wrdrb ta dauko kayan bacci riga da wando guntaye ta saka ta nufi bakin gado ta zauna tana daukan wayarta dake vibrating alamar Kira tana dubawa no dinda tagani yasa gabanta Dan faduwa tana sake kallon no din sbd idan har ta canka daidai Kamar Numbern marshal ne Dan yabata kiranta dashi tana office lokacinda akai rigimar Abbas.

Ajiyan zuciya ta sauke kaman bazata dauka ba saikuma ta dauka ahankali ta Dora a kunnenta batareda ta iya bude Baki tace komaiba.
Numfashinta Dake sauka cikin kunnensa yasashi jingina da kujeran dayake zaune a palonsa ya dago kansa ya kalli agogo yaga time ya sauke Dan numfashi kadan tareda kashe wayar Yana ajiyewa gefensa.

Cire wayar tayi daga kunnenta tana kallonta da yanayi na Dan basarda da yanayinda tashiga na blushing.

Numbern ta qurawa ido tana kallo zuciyarta na neman ingizata ga saving no din,
aka turo kofar dakinta ahankali cikin nutsuwa Bata dagoba sbd tunanin Hanifa ce
Sai daya tako Yana tahowa gurinta taji qamshin turarensa yashiga hancinta ta dago da sauri ta kallesa shikuma wayarta yake kalla Yana dauke girarsa daya ganin yanda take zaune a natse ta qurawa numbern wayarsa ido..

Basarwa tayi tana shigar da wayar key ta aje gefenta tana dauke idonta daga kansa tana Dan kame kamen fatan Kar yayi mgn ko wani tunani akan hakan,
Ta bayanta ya ranqwafo da fuskarsa ya zuro kansa ta cikin wuyanta ya Dora bakinsa Kan kunnenta cikin wani irin sauti me tsananin taushi da son qara Mata kunya sbd kunyarta na kashe dukkanin nutsuwarsa yace”

Basai kin saka kiranba gani nazo.

Kasa dagowa tayi ta kallesa tana kokarin miqewa tabar gurin sbd tafara fahimtan koyaushe da gayya yake Mata wasu maganganun.

Hannunta ya riqo yadawo da ita Yana zaunawa ya zaunar da ita Kan qafafunsa Yana kallon fuskarta dake cikeda kunyar datake basarwa har lokacin ya riqe hannunta Yana sauke numfashi me sanyi na samun nutsuwar dayayi bayan zuwansa gurinta ahankali ya kwantar da kanta kan kafadarsa ta lafe tana sauke ajiyar zuciya boyayya itama
Bude bakinsa yayi cikin nutsuwa har lokacin hannunta na sarqe da nasa yace”

Yaya yarona ko yarinyata?
Lafiya kalau right?

Wani yanayi na mutuwar jiki tambayarsa ta sakata aciki sbd wannan shine Karo na farko da maganar cikin nasu take shiga tsakaninsu bayan wancan tashin hankalin dasukai a asibiti,
Ta Kai hannunta kan cikin ahankali ta Dora tana qaunar cikin naqara mamayeta ta dago ta kallesa daidai lokacinda ya Dora hannunsa akan nata hannun Dake Kan cikin yasake cewa”

Kin shirya zama uwar babyn?

Zame hannunta tayi tana barin nasa hannun akai ta dauke idonta daga kansa ahankali ta furta”

Meyasa Jake tambayan hakan yanzu?

Kwantar da kansa yayi a jikinta cikin nutsuwa yace”

Ina tsananin son cikin ne bayan yakushi da dukan danasha gurin Samar dashi…

Bata taba sanin yakai hakaba a gurin iya magana me nauyiba sai yanzu taqara tabbatarwa takasa danne girman kunyar maganar tasa ta miqe tsaye tana barin gurin ta nufi bakin gadonta tana kokarin hayewa ta kwanta ta shige bargo ko ta rage Jin girman kunyar zancen
Yabi dogayen cinyoyinta Dake fili bayyane sbd gajeran wandon kayan baccin Dake jikinta da wani mayen sanyin kallo Yana tasowa ya riqota Kai tsaye ya juyo da ita Yana kamo fuskarta ya hade bakinsu guri daya Yana sakar Mata qamshin mint mouth wash dinsa kafin ta sauke Kai tuni ya dauketa Yana hayewa gadon da ita hannuwansa na cire dukkanin botiran rigar baccinta ya jefar qasa Yana binta da zafafan romance dinsa data kasa qwatan kanta.

Asubar fari da kansa ya taimaka Mata tayi wanka sbd sabon yanayin data Kuma shiga ko ayau din daya Kuma kusantar tata taji jiki matuqa
Bayan tayi wankan Kaya masu Dan kauri ya dauko Mata tasaka sbd sanyin asuba yakuma kashe AC na dakin yakoma yayo nasa wankan yafito daureda towel dinta a qugunsa qaqqarfan jikinsa a bayyane ruwa na diga ta sauke Kai ahankali tana daukewa daga gefensa ta tayarda sallah dan dama akan dadduma take.
Bayan fitarsa sallar asuban tanata fatan kada yadawo sbd karsu hajjo su fahimci kwanansa anan din tana Gama sallah tayi adduointa ta miqe ahankali ta nufa gado ta Haye ta kwanta tana sauke numfashin wahala kafin ta rufe idanu ahankali tanajin baccin na zuwar mata.

Bacci Sosai tayi har batasan lokaci yajaba sosai sai qarfe goma Sha daya da mintuna arbain ta tashi jikinta duk ba qwari ko kadan
Kasalar data tashi da ita tasa Hanifa da hajjo daketa yawon duba lafiyar wannan baccin datake sukai tunanin batada lafiya Dan Haka tana saukowa gado wanka tafara Yi Dan tasamu qarfin jikinta yadawo,
Tashirya cikin riga da skirt na atampa me coffee brown ta fito Palo
Ruqayyat ta kawo Mata Cocoa Krispies dayaji madarar ruwa data gari sosai Babu sugar sbd batason zaqi cikin farin glass bowl ta karba tana gefen hajjo data damu da yanayinta da tunanin batada lafiyane akwai wani matsalar Kuma.

Ki kawo Mata samosas dinda anty Amina ta Aiko mata dazu” Hanifa dake zaune tafada tana kallon yanda Naj din ke Shan Cocoa Krispies din ahankali kamar baya Mata Dadi bayan itace tace akawo Mata shi zatasha.
Samosas din aka kawo cikin plate manya manya da ita tacika da nama Amma batajin cinta taci gaba Shan abinda takesha tana amsa tambayoyin hajjo ahankali na cewan lafiyanta kalau…

Shigowarsa palon ne yasata tsarguwa taqi dagowa duk da tanajinsa gefenta ya zauna Yana kallon hajjo da itama shi din take kallo ganin fuskarsa na wani sheqin annuri duk da fuskarsa yawanci koyaushe a kame take yau dinma a kame take saidai tana iya hango nutsuwar da zuciyarsa ke ciki a fusakarsa cikin tambaya tace”

Ka fitane yau kaima baka fito da wuriba ko breakfast baka samu zuwaba kaci?

Kafin yabata Hanifa ya kalla da hankalinta Yana Kan qawarta yace mata”

Zanci wannan yanzu da normal drink Mara gas.

Maida hankalinsa Kan hajjo yayi yana cewa”

Bansamu bacci bane da wuri jiyan shiyasa yau da safen na kwanta nasamu hutawa.

Tissue Hanifa taje ta dauko Masa tareda orange juice dinda Babu abinda matarsa Kesha a drink bayanshi takawo Masa ya karba Yana cewa”
Thank you.

Zama tayi tana cewa”

Anjima Zan shiga gurin umma na dubo anty Amina ta kone a hannu Amma inaga ba sosai bane tunda itacema da kanta take fadamun.

Cikin mamaki da ‘yar damuwa Naj ta kalli Hanifa din da muryarta me sanyi tace”

Yaushe ne ta kone?

Dazu da safe tace,taface ba wani sosai bane Dan konewa ne a yatsanta ahaka gurin aikin snacks dinta.

Zanje Nima na dubata nagani….

Kallon Marshal hahifa tayi Dake cin samosas dinsa tayi Yana jinsu Yana Kuma kallon yanda take juya abincin Bata wani ci Hanifa zatai mgn ya katseta a cikin Isa da nutsuwa da cewan”

She’s not going anywhere until she finish all the Krispies Dake cikin abindake gabanta.

Tsit tayi tana son satar kallon yanayinsa Amma kunyar hajjo ta hanata ta share tana cigaba da sha tabatareda tasan umarninsane take cikawaba,
Hajjo kuwa cewa Tai”

Idan kunje Ina gaisheta anjima zanjira Dr sa’id yazo ya duba Mata hannun tunda konewa ce ba’a Wasa da ita.

Babu Wanda yayi tunanin zata iya shanye bowl din duka sbd yanayin cin abincinta dasuka sani Amma saigashi ta shanye hajjo batasan lokacin mamakinta yasata cewa”

Sannu Najma,yasaki Dole kin…

Girgiza Kai tayi ahankali tana cewa”

Dama adadin Wanda Zan iya shanyewa ne.

Sabon mamakine yakuma Kama hajjo dama shi kansa uban gayyar Hanifa kuwa qaramar dariya tasaki tana cewa”

To yanzu zamu iya zuwa tunda kace idan ta shanye Kuma ta shanye din.

Kamar jira Naj din keyi Yana cewa suje din ta miqe ta nufi dakinta tashige.
Saidata zauna abincin ya Dan fada cikinta dakyau sbd yawan dayayi Mata taji cikinta yamata daidai kuma jikinta ya Dan sake ta miqe ta dauko mayafi ta fito riqeda wayarta Hanifa Daman a jallabiyace ajikinta da qaramin mayafinta.

Hajjo saimun dawo tafada tana nufar kofa ahankali ta riga Hanifa ficewa Yana bin tafiyarta da wani irin kallon dayasa hajjo sauke ajiyar zuciyan kada kawaicinsu yaqare aringa abun kunya agabanta wata rana shiyasa zataso su tafi taren sugama zazzage Amarcinsu acan Dan taga alamar tunda aka samu ciki a sashenta batada labari komaiba zai iya biyowa baya.
Suna fita ta Dan sauke boyayyan numfashin da ajiyar zuciyanda Hanifama Dake kusada ita batajiba suka nufa gidansu Kai tsaye.

Suna shiga Dattijo zai fito Yana sauri yana sanyeda farar shadda da babbar riga da hula cikin girmamawa Naj ta gaidatasa tana basa hanya ya kalleta har Cikin ransa Yana Jin dadin ganinta da albarkar aure data samu saidai Bai Gama saukowa dukaba akan laifinta ya amasa gaisuwar Yana kallon Hanifa ma Dake gaishesa ya tambaya hajjo Yana cewa a gaida Masa ita ya wuce sbd jiransa ake
Naj tabisa da kallo bayan sun wuce tana tunanin gurin neman neman aure kokuma saurin auren zashi Dan kullum Dattijo agurin harkar aure hidimarsa tafi yawa.

Suna Shiga sashen umma habiba suka fara leqata Naj ta gaidata ta fito Asmau na biyeda ita suna mgana Hanifa na gabansu.
Suna Shiga sashensu Dadah dake zaune zainaba na Danna Mata qafafu ta kallesu bayan ta amsa gaisuwar hanifa tana kallon Naj dake qarasowa gurin fuska hade sbd Kar Tai Mata maganganun datake Mata akan cikin tace”

Wani borin kikazo gidan Yi bakyason auren da mijin kike hade mun fuska?
Tun wuri ki saki fuskarki zai fi Miki Dan Ni kingama cin Amanata da sakani koke koken wahala akan ki hkr tunda dai dama ihu muke bayan Hari,
Na are na yafe akan baza’a takurakiba lallabaki za’ai Ashema naquda nake bayan haihuwa,Kika kasa ko Jin Dan tausayin tsufana da kukan danake ki fadan na daina kingama daidaitawa…..

Anty Amina ce ta katse Dadahn da cewa”

Dan Allah Dadah kibar Naj akan maganar Nan tunda ta wuce,
Kiyi hkr ansan taci Amanarki yanda kike cewa.

Naj data rasa ina zata saka kanta sbd takaici da kunya ga qanwarta Asmau a gurin ga zainab din Anty Amina harda ma umma na gurin
Dakin ummanta ta wuce Kai tsaye tana Jin dadar na kwabe Anty Amina tanaci gaba dayi ummansu duk da Bata wani sakarwa Naj fuska haryanzu Saida zancen yasata dariya ta girgiza Kai tana Yi sbd Dadah Bata dagawa kowa kafa basuba da jikokin ba.
##MAMUH#

################################

*DATA!!DATA!!DATA!! PROMO😍😇🤗💃💃*
*Assalamu Alaikum*
*Batools Net.S
*muna sayarda DATA bundle akan farashi mae sauki, tuntubemu dumin yin subcription dinku*
*💃💃
*📶MTN DATA🌕*
*500MB 👉₦140
*1GB 👉₦ 240
*1.5GB 👉₦ 400*
*2GB 👉 ₦500*
*2.5GB 👉 ₦650*
*3GB 👉 ₦750*
*3.5GB 👉 ₦900*
*4GB. 👉N1000*
*5GB 👉₦1250*
*6GB 👉₦1500*
*10GB. 👉N2500*
*15GB. 👉 N3800*
*20GB. 👉 N5000*
*30GB. 👉N7500*
*(Valid for 30days)*
Balance, *461*4#* OR
*131*4#*
💃
Airtel data plan
1gb—550
1.5gb—750
2gb—1100
2.5gb—1350
3gb—1550
4gb—2100
5gb—2400
6gb—2750
10gb—3300
Balance*140#

Glo Data price
1.gb—550
2.9gb—1000
4gb—1500
5.8gb—2000
7.7gb—2300
10gb—3000
Balance *127*0#

9mobile Data price

1.5gb—1000
2gb—1250
3gb—1550
4.5gb—2250
11gb—4750
15gb—5500
Balance *228#
(All valid for 30days)
*CALL/SMS/WHATSAPP -* *08034450108
👇👇👇
*MTN 1GB @ 240

*Ana biyan kudi ta✔Bank*
*ACCOUNT NUMBER:*
1130713591
*ACCOUNT NAME : Fatima Abubakar Ibrahim,
*BANK NAME :Polaris BANK👇*
*

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 48_*
Tana Shiga dakin umma ta zauna kan kujera tana Dan rintse ido ta bude tareda sauke boyayyan numfashin damuwa da takaici me girma na Dana sanin zuwanta yanzu data sani a waya takira anty Aminar sbd Dadah tasamu ta daina Mata wannan mugun gorin kafin tasamu ta manta abar tada maganar tukuna tazo cikin rufin asirinta.
Shigowar umma tareda anty Amina da Hanifa ne yasata Dan dagowa kadan batareda ta kalla ummanba sosai sbd girman kunyar zancen Dadah da har lokacin tana tsakar gidan tana jeho zancen Bata Bari ba,
A natse cikin sanyi tace”

Umma ya gida?
Ina wuni?

Zama umman tayi Kan kujerarta datafi zama a palon tana cewa”

Lfy kalau,ya hajjo?

Wata sabuwar ajiyar zuciya ta sauke ranta na samun sauki da sanyi me yawa Jin umman ta amsa Mata cikin yanayi me Dadi batareda bacin raiba acikin zancen
Sbd wautarta saita kasa yin shiru ta kalla umman da farin ciki bayyane a fuskarta tace”

Umma kin yafemun?
Kin daina fushi Dani?

Wani kallon sakarya umman Tai Mata tana cewa”

Albarkanci mijinki kikaci daya kasa sukuni sai daya nema Miki gafara agurinmu,
Mutuncinsa yasa muka yafe Miki yanzu Amma gaba Kika Kuma makamancin Haka wlh Najma Ni kadai nasan hukuncin dazan Miki,
Yanzu meye amfanin wannan tonan bankada asirin na Dadah duk Dan sbd kinki yiwa kanki fada ki yadda da qaddara ki runguma aurenki Kuma umarnin iyayenki ko nace zabin iyayenki,Kika ringa borin bakyaso anata tashin hankula gshi Nan Dadah tanata Miki bankada Kuma wlh idan ba Allah Kika roqaba yasamata rikicin mantuwar wannan alamariba har tsufa taringa Miki fadensa,
Dan Haka kiyi wa kanki fada ki runguma aurenki sbd kinsamu mijin Dake tsananin sonki da qaunarki Sam bayason damuwarki,
Haka ya ringa zarya a gidan Nan Saida Dattijo ya sauko tas akan fushinsa Dake badan hakaba da yanzu dagake harni muna cikin bacin ransa da fadansa a kullum.

Cikin son bawa umman hakuri da kawar da damuwar zancen Dake neman dawowa sabuwa Hanifa ta kalla umma tana cewa”

Umma ai ta tuba tuni wannan ya wuce yanzu hakama binsa zatai tare zasu koma inasa ran sai takusa haihuwa zata dawo.

Anty Amina Yar dariya ta sake tana cewa”

Naj Wai binsa Zakiyi??

Shareta Naj din Tai kamar bataji me tafada ba ta basar da zancen tana kokarin yiwa umma mgn anty Amina takuma cewa”

Umma Dan Allah kiyi Mana gyaranta na amare masu ciki….

Wani kallo umman Taiwa anti Aminar tana cewa”

Amina kin Gama rainani ko?sbd Kinga muna goga kafada acikin gidan nan.

Dariya Hanifa da Anty Aminar sukai anty Amina na cewa”

Yi hkr umma Amma Allah gskia nake fada ayi Mana Dan gyara……

Jefa Mata sabuwar tissue din hannunta datake kokarin budewa Tai tana cewa”

Yaushe nafara Wasa dake.

Hanifa ce tace”

Dan Allah umma kiyi Mata,
Itama fa Kinga Amarya ce wancan na farko da akai na auren Abbas ne yanzu na auren ‘danki Zakiyi umma.

Hanifa kema zama da Aminar kwana biyun Nan yasa kin lalace da rashin kunya ko??

Naj dataga zasu kasheta da sauran ranta da zantukansu ta miqe zata bar dakin umma tace”

Gwara Miki kunyar nan da wadda Dadah zata ringa sakar Miki a tsakar gidan.

Fasawa tayi tadawo ta zauna tana hadewa Hanifa da Anty Aminar fuska ko zasu bar zancen umman tasu ma dayake dama ba ruwanta akwai sakewa sosai a tsakaninsu Banda matsalolin rashin auren Naj din dasukaita shigowa rayuwarsu.

Fira suka hau sunayi suna jeho maganar tafiyarsu Naj din Wanda duk kusan sanarwace suke Mata tareda gargadi akan saken datake dashi akan girman banza data dauka ta sakawa kanta bayan itama Hannah din bawai girmanta Marshal din yayiba kusan shekarunta daya dashi idanma itama Bata girmensa ba sbd kamar shekarunta daya da Hanifa Kamar yanda Hanifa ta taba ji agurin hajjon Amma dai ba maganar shigarsu bace Dan Haka koma dai yayane ta aje abinda takeji ta Kama mijinta da aurenta idan ba uwargida takeson zama da wuri wuri ba,
Cikin neman mgn Anty Amina tace”

To ai bawai fasa auren akaiba nashi da Hannah din kamar ji nai hajjo tace idan sun dawo za’ai Auren.

Murmushi Hanifa tayi tana kallon Naj tace”
Eh to kusan hakanne Amma ganin nake sukai tafiyar Nan Naj kafin kudawo ki sauya ra’ayinsa akan auren Nan kawai.

Umma dataga rainin wayon dasukewa Naj din tace”

Kyalesu Naj,
Kawai dai kiyi kokari ki kafa zamanki a gidansa da zuciyarsa maganar aure Kuma ai basai kin hanaba shi da kansa yace………

Umma kibari ta tashi tsaye akan mijinta da kanta Mana basai kin Bata kwarin gwiwan zama da kishiya ba.”” Anty Amina ce ta katse umman da hanata fadawa Naj ba maganar aurensa da Hannah,
Umma ta sake kallon fuskar Naj datai wani irin kalar tausayi duk jikinta yayi sanyi da maganar
Take tausayin Naj din yakama umman ta dafata cikin kulawa tana murmushin farin ciki tace”

Inshallah Zaki zauna gidanki ki Mori rayuwar aurenki ke daya ba takurawa,
Kishiya idan ba alkhairi bace agareki Allah ya nesanta mijinki da Miki ita,
Karki saka damuwar wainnan biyun Dake zugaki aranki kibi mijinki kawai ki Masa biyayyar data kamata ahakanma saiki riqesa,
ALLAH yayiwa auren Albarka ya saukeki lafiya.

Amin suka amsa gabaki daya Banda Naj da zuciyarta ce ta amsa da Amin din Amma Bakinsa yakasa furtawa.
Kunun gyada da Madara Umma tayi masu sbd Naj
Kuma tashasa sosai sai bayan sallar magriba suka fito gidan bayan umma ta hadawa Marshal lafiyayyan Macaroni salad da kunun gyadar shima aka jerasu a basket ta miqawa Naj wadda ta karba daqyar tana Jin kamar ta kwanta agurin tayita ihu ko zataji saukin halin kunya da takaicin datake ciki sbd Dadah data Kuma bude Mata wani babin data karba basket din harsaida takasa jurewa ta miqawa Hanifa kwandon tana dan dauke fuska.
Hanifa taqi karba tana cewa”

Ba nauyi Zaki iya riqewa ai.

Gaba ta wuce bayan tayiwa umma Saida safe sbd masifar Dadah duk da hakan tanayin gaban Dadah tace”

Eh ai Zakiyi sauri ki koma sbd duk ranarda Kika Kuma kawo zancen banza akan rashin yarda da auren wlh zagewa zanyi na kwada Miki Mari,
Ana tareki akan kiyi hkr kina zuba rashin arziki kala kala akan bazakiyi auren qanin kawarkiba gashi Nan Zaki haifawa kawar Taki ‘da a bakyason, za’a gida kina wucewa kece a gaba,jibi idan shegen haukarki ya motsa kidawo kice bakyaso mijin da auren to anshani na warke fes nake kallonki keda Fatiman Dan itama ban yarda dabatasan da cikin ba kuka barmu nida Dattijo bawan Allah muna gwara Kai gurin tunanin mafitar ki hakura ki zauna da auren.

Naj dai gaba tayi Bata waiwayoba tanajin su Anty Amina na shiga maganar suna tausar Dadahr da bakinta yaqi shiru Hanifa ma Saida safe Tai musu ta wuce Tani bayan Naj din suka fito tana ‘yar dariya tace”

Naj kin shiga Tara da goma gurin Dadah.

Bude Baki tayi tana cewa”

Dadah ai dama yanzu tasamu abin fada kenan,dama kwana biyu Bata samu Wanda ta maqalewaba duk yashigo ayita Jan riqe magana anayi yanzu tasamu ta maqale mun.

Kofar gate aka bude musu tun kafin su qaraso suka Shige securities din na gaidasu cikin girmamawa musamman Naj din datake Matar ogansu Kuma sunsan yanzu yashige Yana harabar gidan.

Hankalinta na Kan gabanta tana sauraren zancenda Hanifa ke Mata fuskarta daukeda Dan qaramin murmushin zancen me neman auren anty Amina da Hanifa ke fada Mata yanda akai jiya shida Dattijo kaca kaca Wai tsohon class mate dinsane.

Wani sabon murmushi tasake dayayi Kama da ‘yar dariyarta me burgewa har tana Dan dagowa sbd sosai labarin ke Bata dariya Dan anty Amina da Hanifa sukai zancen ita Bata samu sunyi zancenba.

Akansa idanuwanta suka sauka dagowar datai,
Yana sanyeda farar jallabiya data qara Masa kamala da kwarjini
Idanuwansa akanta sbd yaune Karo na farko dayake ganin murmushinta harma da dariyarta tun bayan lokaci me tsayi daya Santa,
Waya yakeyi Amma gabaki daya hankalinsa yakoma kanta tunda suka shigo harabar gidan,
Hannah dake gefensa tsaye cikin riga da skirt na atampa itama ba dankwali akanta sai wani Dan siririn mayafi data yafa akan tana ganinsu ta Dan dauke Kai tana saka Kiran qarya a wayarta tafara wayar itama Dan batason su tsaya ko da nufin gaisawa da ita gwara su wuce ciki tasamu yau zata dage saisunyi fira da Marshal din da Allah yasa tagansa yanzu tana dawowa daga anguwa shima Yana dawowa.

Dan sauke Kai Naj tayi daga kallon dayake Mata,
Tana ganin Hannah gefensa ta Dan sake kawar da Kai tana tafiyarta cikin nutsuwa batada Niya ko tunanin tsayawa Dan Babu dalilin yin hakan Dan Haka ta wucewarta Kai tsaye sabanin Hanifa data Dan kallesa tana daga Masa hannun itama tana wucewar ganin waya yake.

Riqo hannunta Wanda baya riqeda basket yayi tana gap da wucesu.
Dakatawa tayi ahankali batareda ta juyoba sbd tasan shine ba kowaba.
Dawo da ita yayi gefensa har lokacin Yana waya ya kalli Hanifa data tsaya kallonsa itama ahankali yaja hannun Naj din suka nufa hanyar sashensa Yana cewa Hanifan”

Zanci abincin Umman a part Dina anako mun tea da snacks sbd yunwan dare na baby.

Kasa magana Hanifa tayi sbd Dadi da mamakin daya Gama cikata hannu kawai ta daga Masa alamar ok angama,ta juya ta wuce tana Dan dagawa Naj hannu ahankali tace”

See you.

Hannah dake wayar qarya batasan ma Ashe upside down take riqeda wayarba ta bisu da kallo dukkanin jikinta na saki har suka Isa babbar kofar palonsaba suka shige ya rufo kofar duk da har lokacin waya yakeyi.

Daqyar ta iya durqusawa ta dauka key din motarta daya Fadi daga hannunta ta daga qafafunta dasukai nauyi ta nufi hanyar nasu sashen.

Suna Shiga palon Kai tsaye kicin ya nufa da ita har lokacin hannunta na riqe cikin nasa Kuma Bai Gama wayar ba har lokacin.
Da ido ya nuna Mata ta aje kwandon.
Ta dago kwandon ta aje suka fito suka nufi hanyar bedroom dinsa ta Dan kallesa da sauri tana neman zamewa ya girgiza Mata Kai suna qarasawa ya suka shige ya nufi sofa ya zauna tareda zaunar da ita gefensa Yana sake sarqe hannayensu Yana cigaba da wayar dayakeyi akan aikinsa
Yanayi Yana Dan juyowa ya kalleta da Idanuwansa da duk suka hanata sakewa sai sauke Kai takeyi tana kallon hannuwansu Dake sarqe.

Ya Dan Jima Yana wayar kafin yagama ya kashe wayar tareda ajewa ya waiwayo ya kalleta taqi dagowa ta kallesa ya Dan matsa hannunta kadan Yana sakin boyayyan murmushi yace”

Zanci abincin Umma kafin ya huce,muje.

Miqewa sukai suka fito tare yakaita kicin har gaban basket din data shigo dashi din kafin yasaki hannunta ya Dan rankwafo yayi kissing kumatunta ya fito Yana cewa”

Ina jira.

Dining ya nufa ya zauna Yana jiranta.
Numfashi ta sauke ahankali tareda Jin nauyin kanta gabaki daya da tata rayuwar auren tazo ahakan,
Batada zabin daya wuce dauko plates da spoons dasu cups da serving spoon ta Dan sake daurayesu duk da fes suke a jere,ta goge da sabon qaramin towel ta fito dasu a sanyaye ta aje a dining din Takoma kicin din ta dauko kayan abincin daya bayan daya ta jere Masa tana Jin yanda idanuwansa ke yawa ajikinta Yana binta da wasu irin kallo Amma taqi dagowa ta kallesa Dan idan ta kalli idanuwansa zata iya kifewa agurin Dan hakan taqi kallonsa harta Gama zuba Masa komai cikin sanyin jikinda yake sake kashesa Dan daukan hakan yake amatsayin yangar datake masa.

Janyota yayi ya zaunar akan cinyarsa Yana kallon hannuwanta dasukai aikin ya kamo yakai bakinsa yayi kissing nasu ahankali yace”

Maman junior Alfa tagaji ko??

Dagowa tayi ta kalli bakinsa da yayi maganar sbd Sam shi Babu ruwansa komai fada yakeyi Dan yasata Jin kunya…..

Matsoda fuskarta yayi kusada tasa sosai har numfashinsu na haduwa yana kallon tsakiyar idonta da wata murya me tsananin rashin fita sosai yace”

Go ahead,kiss me as much as you want, I’m all yours,ki daina kallon bakin kiyi abinda kikeso kawai.

Tsabar tsananin masifar kunyar dataji batasan lokacin data daga siririn hannu zata daki kirjinsa ba ya riqe hannun yana kallonta da wani irin murmushi Yana cewa”

Ok,ok sorry nine Mara kunyar zanyi duk lokacinda kikeso basai ke kinyiba.

Tashi tayi daga jikinsa tana barin gurin batareda ta waiwayoba ta nufi kitchen tashige da sauri,sai data Isa bakin fridge ta tsaya tana sauke numfashi da Ajiyar zuciya wani boyayyan murmushi nason saukar Mata tana tarewa sbd kunyar kanta.

Sai data dauki mintun biyu zuwa uku tasamu daidaita nutsuwarta duk da har lokacin tana blushing kafin ta bude fridge din taga gabaki daya REDBULL energy drink ne a fridge din sun dauka sanyi ta dauko guda daya da robar ruwa daya ta fito takawo Masa lokacin yafara cin abincinsa a natse kamar wani babban Dattijo sbd yanda yake cin abincin a natse.

Hajjo dataga lokacin cin abincin dare yayi bataga fitowar Naj ba tunda suka dawo Dan Koda suka shigo tana dayan palonta da baqi ta kalli Hanifa tace”

Lafiyan Naj kalau kuwa?
Kidubota ko lafiya haryanxu Banga ta fitoba.

Batareda Hanifa ta kalli hajjoba tana zama Kan dining tace”

Tana gurin JALAL acan zasuci abincin inaga Dan umma ta Aiko Masa da abinci,
Idan mungama Zan Kai Mata snacks tea Dan yunwar dare.

Shiru hajjo tayi duk da mamakin zancen sai dayasata sakin murmushinda Bata shiryaba ta zauna tana cewa ok kawai suka bar zancen daga Nan.

Daya Gama cin abincin barin dining din yayi yakoma Palo ya zauna yana duba sako a waya ta tattara gurin tamaida kayan kicin ta gyara gurin tana hada na kicin din Hanifa tayi Knocking kofa yabata izinin shigowa batareda ya tashi ba tana shigowa Kai tsaye ta nufi dining takai kayan hannunta ta aje kafin ta nufa kicin gurin Naj tana dariya tana cewa”

Mrs DEEN ALFA aiki kikeyine?

Banza Naj tayi Mata lokacinda tagama hada kayan umma a basket dinta ta wanka hannuwanta ta goge da towel tana kallon Hanifa tace”

Nagama mutafi naje nayi sallar ishai nayi wanka na kwanta.

Fitowa sukai ta nufi wayarta da mayafinta Dake kusa dashi zata dauka Hanifa ta zauna a kujera tana kallonta lokacinda ta dauka wayarta tana kokarin daukan mayafin ya jawota ahankali ya zaunar kusada ita Yana kallon Hanifa yace”

Yarana bazasuyi halin qawarki ba zasu dauko dadynsu suyi wayo sbd idan suka biyo mamansu zasu zama Kaman….

Kallon datai Masa yasashi kallonta Yana fasa fada ya saki murmushi Yana cewa”

Shikenan ya isa.

Maganar tafiyarsa sukeyi da Hanifa dakuma maganar wani qanin mum dinsu da Marshal din ya dauka nauyin rashin lafiyan data samesa zuwa ganin likita India sukeyi
Taso tafiya tabasu guri Amma ya hanata ta hanyar riqe hannunta cikin nasa Yana cigaba da magana da hanifar da itama ta kallesa tace”

Bayan kun yafi ma Nima munyi mgn da Zawj akan Zan koma can gurinsa gabaki daya shima an maidashi LA so munyi mgna min yanke shawaran nabisa can Zan ringa ganin likita Nima.

Cikin farin ciki Naj ta Dan kalleta tana Jin tausayin kadaicin juna da zasuyi tun yanzu da ido Tai Mata Ina tayaki murna sweetheart.

Gyada Mata Kai Hanifa tayi tana cewa”
Nayaki murna kema da fatan rayuwar farin ciki me albarka da ‘dan uwana.

Shi kuwa hakan yayi Masa Dan dama yanason tabi mijin nata Koba komai zasufi kusa idan tabi mijinta acan zaifi saurin zuwa ganinta hajjo ma idan ta yarda yanason takoma Hawaii kodan sbd manyanci zatafi hutawa acan.
Miqewa tayi tace zatai waya ta nufi kofar fita Hanifa tace”

Kishiga ciki kiyi wayar kafin nagama din saimu tafi tare,
Ba musu ta nufi hanyar dayan dakinsa Dake palon ta shiga tana amsa wayar Sarah data shigo wayarta.

Bata ankaraba ta Bata lokaci sosai gurin wayar tabarsu suna magana dama tayi niyar Basu gurin suyi maganganunsu na tsakanin ‘yan uwa shiyasa tasaki jiki suna waya da Sarah ko data kashe taji Kamar tana jiyo maganar Hanifa har lokacin sai tayi alwala a toilet din tafito tayi sallar ishai tana kallon koina a dakin dayake komai na dakin shikuma golden ne ba kamar na dakin baccinsaba Dake komai milk.
Jin tanajin bacci bacci yasata miqewa ta fito Kai tsaye da niyar tafiya ko Basu gamaba ga mamakinta Hanifa Bata palon saishi kadai yagama rufe kofa yadawo ya kalleta ganin tana kallon palon da mamakin rashin ganin Hanifa ta daga kafa zata nufa kofa ya miqa Mata hijab babba da jallabiya tareda kayan baccinta da Hanifa ta kawo Mata Yana cewa”

Kin gaji,kinajin bacci muje ki kwanta
Hanifa tawuce tuni.
Kama hannunta yayi suka nufa dakinsa tana son magana Amma ya girgiza mata Kai da alamar shima yagaji hutawa zaiyi Banda hayaniya.

Suna Shiga bedroom din nasa ya rufe kofa tareda rage hasken wutar dakin sosai yana aje kayanta Dake hannunsa ya nufi toilet yashige.

Wanka yayo yafito daureda towel tana ganin hakan ta dauke ido hankalinta gabaki daya ba akwance yakeba da kwana anan din,tafison ta komawarta saidai Kuma duba lokacin dayaja sosai tanajin tsoron fita ita kadai.

Da kansa yabata yakaita toilet tayi wanka tasako kayan baccinta tun acan toilet din saidai ganin kayan da Hanifan ta kawo Mata yasata tsayawa a toilet din tana yiwa kanta kallon mamaki da mamakin Hanifa data iya kawo Mata wannan shegun kayan tasaka.
Rigar baccin gabaki daya Babu abinda ta rufe ajikinta tun daga kan zamanta transparent dakuma qarancinta dako cinya daqyar takai.
Cikin bacin Rai tace”

Meye wannan Hanifa takawo?
Inama ta samo wannan kayan?

Tsoki tayi ahankali tareda cire rigar tana jefarwa qasa Yana bude toilet din yashigo.

Kallonta yayi daureda towel kafin ya kalli rigar data jefar din yana gani ya fahimci komai ya basar Yana cewa”

All okay???

Gyada Kai kawai tayi tana fitowa toilet din ta nufi jallabiyarta zata saka ya hanata ta hanyar dauko Mata shirt dinsa Mara nauyi da dogon hannu ya Bata.
Karba tayi takoma toilet tasako ta fito tana Jin wani iri Dan kusan itama duk cinyoyinta a bayyane
Bai tsaya Bata lokaciba ya dauketa suka nufi gadonsa ya kwantar da ita shima ya kwanta Yana ja musu abun rufa ya lumshe idanuwansa sbd baccin dayakeson ya daukesa.
Itama rufe idanuwanta tayi tana Dan sake rufe kirjinta da bargon ahankali bacci yadaukesu duk su dukan.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 49_*
Washe gari tun 7 na safe Bata qarasa bugawaba tadawo sashen hajjo bayan ya rakota har bakin kofar palon tashige ta Hana Masa shigowa ta hanyar rufe kofar bayan tashige sbd karyace zai bita dakinta yayi baccin safe hajjo tagansa,
Lallabawa Tai tashige dakinta tareda rufo kofar dakin ta Isa gadonta tafada sbd baccin dake idonta take bacci yadauketa ba Bata lokaci Dan yau din Kamar wadda wani Abu ya sameta tashinta kusan biyu cin abincin dare na farko cake da yoghurt Tasha na biyun Kuma kishirwane kawai ya tada ita duk shine yayi yawon dauko Mata daga kitchen zuwa bedroom shiyasa baccin nasu yake guntu guntu.
Bata farka ba Sai guraren karfe goma lokacin hajja batanan ta fita tareda Dad Alfa zuwa wani gurin,Bata fitoba Saida tayi wanka ta Sanya dogon skinny jeans daya lafe jikin siraran cinyoyinta da farar free long sleeves riga ta sako qaramar hula ta fito tana qamshin body mist kawai da bayama tashi sosai,yunwa takeji Sosai Dan Haka Kai tsaye dining ta nufa tana Dan qwala Kiran sunan ruqayyat ahankali Anatse.
Tana Isa dining din ruqayyat na isowa gabanta cikin tsananin girmamawa tace”

Gani Ma.

Ruqayyat ki bani tea me zafi sosai ki hadomin da sauran samosas din jiya.

To”ruqayyat din tace tana juyawa ta nufi kicin
Ita Kuma zama tayi tana janyo plate tareda zuba soyayyan dankali da aka hada da kayan miya ta kidney ta saka fork tafara ci tana Jin matsuwar akawo Mata tea din tafara Sha cikinta ya sake da ruwan tea din masu zafi.

Haniface ta fito daga dakinta tana kallon Naj din tace”

Barka da tashi Matar Marshal.

Da ido Naj din ta amsa Mata tana qin amsawa.

Dariya Hanifa tayi tana fasa wucewa ta dawo gurin Naj din tana cewa”

Da ido fa Kika amsa Uwargidan Marshal.

Kallonta Naj tayi bayan tagama Kai fork din Irish bakinta ta Dan bude Baki tace”

Wayene Amaryan to??

Daga bayanta taji an ranqwafo ya zuro Kai yayi kissing gefen fuskarta da kamammiyar muryarsa Yace”

Kece,
The only Mrs DEEN ALFA.

‘yar dariya Hanifa keyi tana cewa”

Karka yaudari qawata fa JALAL,
Kafada Mata gskia,
Hannah na…..

Kallon da Naj Tai Mata na yaushe Kika daina Sona yasata dakatawa tana dariya tace”

Ban daina sonki ba my Naj gaskia nake fada Miki fa.

Zama yayi a kejeran dake kusa data matarsa Yana riqo dayan hannunta ya sarqe da nasa Yana kallon Hanifa yace”

Zaki hanata cin abinci ne?
koda wata ko Babu she is the only one a zuciyan JALALUDDEEN MARSHAL ALFA….the only Mrs DEEN ALFA.

Atareda Hanifan suka kallesa alokaci daya zuciyan kowannensu daukeda yanayi na farin ciki daga Hanifa,ita Kuma mamaki ne me girma da wani sabon yanayi Dake shigarta wadda takasa gane farin cikine kokuwa?

Kallonta yayi kamar bashine yagama maganarba Kai tsaye yace”

Sakamun abincin zanci Zan fita.

Sai data Kuma kallonsa kafin ta dauke idanuwanta daga kansa sbd yawan kallonsa Yana karya dukkanin qwarin qarfin halinta na kame kanta.
Zare hannunta tayi daga nasa ta Dan miqe tana daukan wani plate din tazuba Masa daidai ruqayyat na kawo tea din ta karba ta zuba Masa itama ta zuba Takoma ta zauna tana cigaba da cin abincinta zuciyarta cikeda sabon yanayi data kasa fassara hakan da komai face nutsuwar zuciya datake ji.

Yanda takecin abincin a yanayi na sanyi da tunanin da zuciyarta tayi nisa akai yasa harya Gama ya miqe ya Dan kalleta cikin kulawa yace”

Nafita ki kula.” Ya wuce Yana daga wayarsa da ake Kira sbd harkan maganar Visa dinta ne na tafiyarsu Wanda shine yakawo Masa delay na tafiyar da tun jiya zai wuce Amma yanxu Sai jibi su tafi.

Bayan tafiyarsa ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda Dan rufe ido ta bude tana daukan ruwa Tasha itama ta miqe tabar gurin ta nufi dakin Hanifa tana zuwa ta zauna gefenta tayi shiru tsawon mintuna ba mgn kafin ta Dan motsa tareda bude Baki a natse tace”

Hanifa kina ganin Zan iya?

Sauke numfashi Hanifan tayi ahankali kafin itama a natse tace”

Naj idan kinason samun nutsuwar aurenki da rayuwar kwanciyar hankali tareda riqe zuciyar mijinki Zaki saka kanki Dole iyawa,
Zuciyarki na son mijinki meyasa bazaki bawa kanki qwarin gwiwaba da qarfin hali ki aje komai ki gwada sakewa kuyi rayuwar aure me cikeda kulawa da soyayya ahakan Zaki samu dukkanin soyayyarsa wadda ma bakinsa bazai iya fadaba.
Hannah na Tsananin son Auren Marshal Kuma zata iya maida kanta komai akan ya sota ya aureta Amma hakan bazai samuba sbd sonki da yayi Masa mugu shigarda har baya iya ganin laifinki ko fushi Dake akan duk abubuwan dakike Masa tun a farko,
Bansan yaushe,Kuma a Ina yafara sonkiba Amma dai ayanzun shine Yana tsananin sonki saidai irinsu idan baka riqe abinka ba zaka iya rasasu sbd yanada masu sonsa,masu jiran irin damar da kika samu ta zama matarsa,
Ina fada Miki hakan ne amatsayin qawarki Kuma Yar uwarki ba amatsayin Yar uwarsaba,
Samunki da yayi shima yayi dacenda wasu basuyiba Amma gskia wasu daga halayenki zasu Hana rayuwar aurenku sakewa idan har Baki daure kin ajeba,
Marshal kinsan a inda yatashi yake Kuma rayuwa acan yasaba da rayuwar sakewa ta turai shiyasa baimasan wani yin kawaiciba idan yatashi yin abubuwansa akanki
Dole kema Zaki Ari rayuwar dayakeson din ki sake jiki kuyi rayuwan kwanciyan hankali.

Bata iya cewa komaiba saima sake Shiga tunani datai sbd babban abin dayake juyi a zuciyarta shine kalmar sonta agurinsa,har tun yaushe yafara sonta?dama soyayya zata iya Shiga tsakaninsu me qarfi irin Hakan.

Sai kusan maraice hajjo tadawo lokacin suna can gidansu gurin umma suna cin abubuwa kala kala da anty Amina Bata fada musu Kona menene ba musamman Naj da idan taji zata iya qin cin duk da ba wani hadin me qarfi bane sbd ciki da Naj din takedashi Hanifa kuwa tun faraci tasan menene Amma itama tayi shirunta taqi fada,
Dambun Naman kaza ne da akaiwa Hadi da kayan gyara mace,sai kwakwa da aka soya itama da kayan gyaran dakuma lafiyayyan fura dataji fresh nono da yoghurt me shugar aka zuba wasu garin magani masu kyau da tsafta Kuma cikin sa’a Naj din Tasha sosai taci komai sosai sbd sun Mata Dadi abaki.

Tana sane dazasu tafi bayan sallar ishai ta sulale batareda sanin Dadah ba ta fito kafin taji Tai Mata abin data Saba.
Suna Isa gida hajjo Dake zaune Palo ta kallesu cikin kulawa tana cewa”

Fatima ta sakaltaku da qwadayi shiyasa kwana biyun Nan kuke yawon zuwa can Kuna dare,
Hanifa bakinki Nan Sam ko Babu ciki baya daina kwadayi.

Murmushi Naj tayi tana qarasawa kusada hajjon ta zauna tana cewa”

Hajjo barka da dawowa,
Da bakya Nan ne ba Dadi gidan sai muka fita,Amma dai Hanifa ce tajani Ni banmayi niyar fitaba.

Dariya Hanifan tayi tana zama tace”

Ciki dama harda sharri Yana sawa,
Dadah dai da gskiyarta kinci Amanarta gashinan Nima kin……

Matse fuskar da Naj tayi yasa hajjo Hana Hanifan qarasawa ta katseta da cewa”

Karna kumaji kina Mata tunin maganganun Dadah,
Dadan ma zanje na rufe Miki bakinta kinji Najma wannan gorin lagudan zancen ta taimaka tabarshi Haka.

Maganar hajjon tasake sakata Jin kunya ta fuske tana kallon Hanifa tace”

Hadda Hanifa hajjo kifara rufe bakinta kafin na Dadah din.

Hanifa Kika Kuma tada maganar Nan Zan Saba Miki kokuma ayau basai kin shiryaba ki tattara kibi mijinki.

Najma tashi kije ki dan gyara kizo ki kaiwa mijinki abinci yanacan yauma da ciwon Kai yadawo.

Sunkuyar da Kai Naj din tayi tana kasa amsawa hakama tana kasa tashi Saida hajjon takuma maimaita zancen  kafin ta miqe ta nufi dining zata dauka takai tadawo
Hajjo tace”

Aa kindawo a gajiye ahakan Zaki?
Kije ki Dan gyara duk qamshin kwakwa ma kukeyi
Tashi kema,kuje kuyi wanka kafin taje takai Masa.

Tashi tayi ta wuce dakinta bayan tagama fadan sbd Naj tasamu sakewar wucewa wankan dakinta.

Saida hajjo ta shige kafin ta juyo ta nufa hanyar dakinta tanajin Hanifa na cewa”

Saida safe Naj.

Bata kulataba ta shige dakinta dama Kuma wankan takeson Yi har cikin ranta.
Wanka tayi tana fitowa ta saka kayan bacci riga da wado dogo har qasa kafin ta saka doguwar hijab Nayan ta shafa khumrah me sanyin qamshi ko wayarta Bata daukaba ta fito ta dauka abincin ta wuce zuciyarta na ingizata ga son sanin halinda yake ciki na ciwon Kan.

Tana isowa kofar palon sashen nasa ta tararda Hannah tsaye tana Shirin buga kofar.
Tsayawa tayi sukaiwa juna kallon mintuna biyu kafin Naj ta dauke nata idon tana juyar da kanta zuwa ga kallon kofar Shiga zuciyarta data sauya tana ingiza kanta ga juyawa ta komawarta Amma zuciyar ta hanata hakan sbd rashin sukunin ta tafi tabar Hannah din agurin,
Hannah ta juyar da fararen idanuwanta tana yiwa Naj din kallon mamaki tace”

Lafiya dai kuwa??

Dan qaramin numfashi ta sauke a boye kafin ta sake kallon Hannah da itama tsoron Allah daya kasheta da mamakin Naj din a natse cikin sanyinta batareda tabi takan abinda Hannah din ta tambayaba tace”

Bayajin Dadi ko kinyi knocking ba lallai yabudeba.

Sake kallon kayan dake jikin Hannah din tayi sbd wata doguwar straight gown ce data lafe jikinta dakyau ta fidda da shape dinta ba laifi  kanta babu komai sai wata qaramar hula data saka wadda kusan Rabin gashinta ya fito itama qamshin take fitarwa Sosai.,dauke kanta tayi Anatse kafin ta qarasa jikin kofar takai hannu ahankali ta bude kofar Kai tsaye tashige tareda rufowa tasaka lock.
Jingina tayi jikin kofar tareda rufe ido tana Dan sauke numfashin dazai rage Mata nauyin da zuciyarta tayi.

Hannah kuwa kasa motsawa tayi agurin sbd al’amarin yafara Mata yawa, zuciyarta gap take da bugawa da halinda Marshal dama wannan Naj din suke sakata,
Cikin baqin ciki da takaici dama bacin ran daya qulleta tace”

Ubanwa ya tambayeki idan baida lafiya ko lafiyarsa kalau¿
Juyawa tayi Rai baqi qirin ta wuce tanajin Kamar tatashi kowa daga bacci gidan yafito sbd masifa.

Barin jikin kofar tayi ahankali tana Dan kallon palon da wutarsa take kashe saita gurin dining ce kawai a kunne Wai AC Dake aiki ta nufa hanyar kicin tana tafiya jiki amace
Takai Kan dining ta aje tareda sauke qaramin numfashi tana Dan rintse ido kafin ta waiwaya ta kalli hanyar bedroom dinsa tana juya yanda zata Kai kanta da kanta bedroom din.

Bama kanta qwarin gwiwa tayi tareda Dan taqaita Jin nauyinta da kunyarta ta nufi dakin zuciyarta na tsalle sbd haryanxu takasa sabarwa da kanta sakewa akan duk wani al’amarin daya shafesa ko yashigo dashi ciki.

Saidata Kuma sauke numfashi da ajiyar zuciya kafin takai hannu ta Murda kofar dakin a natse ta bude tana kallon Dan duhun daya gauraya dakin sbd wutan a kashe sai hasken bedside lamp na gefe daya dake kunne Wanda yabata Daman ganin fuskarsa Dake bacci cikin nutsuwa da alama baccin yasa ciwon Kan tafiya.

Kasa dauke idanuwanta tayi daga kan fuskarsa zuciyarta na gauraya da dukkanin nutsuwa da wata irin alkunya duk da bacci yake.

Bakin gadon ta tsaya saiti da kansa tareda durqusawa takai hannunta kan goshinsa ahankali ta Dan dafa saikuma ta dauke da sauri tana miqewa tsaye zata juya taji anriqo hannunta.

Kasa waiwayo tayi saima idanuwanta data rufe Jin kunya da mamakin ba baccin yakeba kenan.
Batareda ta waiwayoba ta bude Baki a natse cikin qaramin sauti tace”

Hajjo tasa akawo maka Abin……

Cikin muryar bacci da ‘yar kasala ya katse da cewa”

Kullum komai hajjo ke sakaki Yi,yanxu kiyi Wanda hajjon Bata sakakiba ki hadamun ruwan zafi zanshiga cikinsu nayi wanka tunda nayi bacci yanzu jikina zai sake.

Sakinta yayi Yana tashi zaune ya jingina jikin gadon Yana kallon qatuwar hijabin dake jikinta.

Kasa juyowa ta kallesa tayi ta bude Baki ahankali tace”

Hajjo zataga na Dade.

Batareda ya kalletaba ya zuro qafafunsa daga kan gadon yana zare qaramar shirt din Dake jikinsa dukkanin jikinsa ya bayyana ya nufi toilet din Yana cewa”

Ki koma gurin hajjon idan nagama zanzo da kaina gabanta na daukoki da hannuwa.
Shigewa toilet yayi yabarta tsaye tana bin kofar daya shige din da kallo
Ta kujera ta zauna tana tunanin tsaf zai aikata abinda yafada din Dan Haka zata jira yafito taji me zatai masa ta koma.
##MAMUH#

 

********************
*_MG’s skin care_*
Hi team no makeup
Ina kanawa mutanena🗣️
Shin Ina masoyan mg’s ina ma’abota ado da kwalliya kusaurara kuji dame nazomuku 💃
Nasan dayawa kunsiya kayanmu Kuma kunshaida yadda suke gyaranjiki cikin lokaci kalilan Koda iyasabulun kikayi anfani dashi sekinyaba balle kankat wato beauty kit dinmu toh inamaitabbatar muku cewa ynx kayanmu ankaramasu kayayyaki Wanda zasu Kara gyara fata fiye da tsammanin Mai tunani within 2weeks zakicanza kiga duk inda kikayi se anbiki d👀 domin ynd fatanki zaikoma Shar kamar madara bawanda zemiki kallo daya yadauke idanunshi😃😍
Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?
Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki
Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘
Soap:3k
Beauty kit:12k
Chat:08062991549
07066210195
Call :07046881166
08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra’ayi🥰
Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲
Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝
Nd guest what🤩
Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃
Pamper your skin🧖‍♀️
Shine like a bride👰🏻
Glow🧚🏻‍♀️

 

*********************************
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 50_*
Tunani tashiga na son tafiya Amma tana shakkar maganarsa datafi kowa sanin zai iya aikata abinda yafada din Wanda ba hajjo kawai ba kila ko Dad Alfa zai iya ganinsu ta samansa idan suka fito harabar gidan ahakan Dan Haka ta daure tasake bawa kanta danganar zaunawa jiran nasa..
Bude kofar toilet din yayi yafito daureda towel a qugu,ta dan dauke kanta tana kallon wani qaramin farin frame me kyau Dake gefen kujeran datake hotonsane tareda Hanifa aciki suna wata qasar turawan Wanda kayan jikinsu ne ya tabbar Mata da hakan ta qurawa fuskarsa ido tana sake qare Masa kallon da bazata iya yimasaba a fili dukkanin zuciyarta da gangar jikinta na tsayuwa akan Abu daya data kasa yadda yasameta wato shine SO,
Son JALALUDDEEN,qanin qawarta dasuka taso tare,
Tayaya?
Yaushe?
Kuma garin Yaya duk hakan ya shammaceta yashige……

Zama yayi kusada ita Yana zuro fuskarta kusada tata Yana kallon hoton data zubawa idon fuskarta na tona asirin zuciyarta ya bude Baki zai magana qamshin mouthwash dinsa na mint ya daki hancin Yana shigewa ta zuciyarta tasake raunana a hankali yace”

Ni din daine qanin qawarki aminiyarki Kuma mijinki uban babyn Dake cikinki,
Yaya??kin bada garine kokuwa inada sauran aikin daban qarasa?” Yafada Yana zura hannunsa cikin hijabinta ya Dora kan cikinta dayayi tauri ya Dan taso Yana shafawa fararen idanuwansa masu kwarjini Kan fuskarta Yana Jin qaunarta da Sonta daya riga yayiwa jarumtarsa da kemewarsa illar da Babu gyara.

Yanda yake shafa cikin cikeda kulawa yasata kasa jurewa ta dago ta kalli fuskarsa da har lokacin ita yake kallo cikin yanayi kulawa da so me girma.

Babyna yafara motsi?” Ya tambaya yaba kallon cikin.

Ahankali ta girgiza Masa Kai jikinta na mutuwa da yanda yake binta da wasu kallon kasalan da Bata Gama sakinsaba shima.

Amma Yana lafiya ba right?

Da mamakinsa take sake kallonsa Dan tarasa ta Yaya babu ruwansa Kai tsaye yake maganarsa duk yanda tazo Masa arai Kuma ko agaban waye.

Kama lips dinta yayi da hannunsa ya shafa Yana Dan daga mata ido alamar ta amsa Masa tambayarsa.
Dole ta bude Baki ahankali tace”

Lafiya kalau.

Kissing hannunta yayi Yana cewa”

Hakan nada kyau,yanzu muje kiban abinci inajin yunwa.

Miqewa sukai ya zare Mata hijabin ya aje a kujeran dasuka tashi suka fito Palo tana gaba Yana bayanta hannunsa riqeda Nata Yana biyewa tafiyar saibinta datakeyi a natse da sanyi Wanda ke sake shigarda ita ransa sbd a ra’ayinsa Yana qaunar mace me sanyi da nutsuwa shiyasa tayiwa zuciyarsa kamunda ba fili tako Ina.

Zama yayi Yana duba agogon yaga qarfe goma Sha daya takusa Dan Haka yace kadan zata saka Masa bayason nauyin abincin tunda dare yayi har Haka.
Kadan din tasaka Masa takawo Masa drink tana kokarin komawa ta zauna ya janyota ya zaunar a Kan cinyarsa Yana cin abincin da ita ahaka ta ringa binsa da idanuwa tako Ina Yana sake cikata da mamakinsa da girman abubuwan dayake Wanda basa boyuwa.

Koda yagama suka Gama samun bakinta tayi da kasa tambayarsa akan komawan datakeson Yi takama hannunta suka koma daki da kansa yakaita har toilet sukai brush suka fito ya hau gado ya kwanta tareda miqa Mata hannu da ido yace Mata zo Nan Kamar wadda aka daga hannunta aka miqa Masa Haka tasamu kanta da hannun nata akan nasa ya jawota ya kwantar gefensa Yana Dora kanta kan pillon da kansa yake suna fuskantar juna ahankali ya lumshe idanuwansa Yana rungume hannunta daya a kirjinsa yace”

Goodnight Mrs DEEN.

Lumshe nata idanuwan tayi itama tana sauke qaramin numfashi Dan baccin ya dauketa itama.

Bacci Sosai sukai musamman bayan sallar asuba dasukai sallah suka koma Dan kuwa yau Kai tsaye ya hanata guduwa sashen hajjo Kamar yanda take data nacewa komawan sai kawai ya sake yayi Making love da ita Wanda yadaukesu lokacin har gari yagama wayewa sukai wanka sbd tsananin gajiyan datai Dole tana kwantawa baccin wuya ya dauketa.

Bata Farkaba saida wata yunwa me qarfi ta tasheta,ta Dan motsa tana bude Idanuwanta ahankali tana Dan kallon gabanta ta tuno a inda take sai kawai taji jikinta yakuma sakewa da mutuwa sbd tariga tasan yanzu Kam hajjo tagama gane Bata Kwana acan ba.
Dan Haka yaye bargon datake rufe dashi tayi tana tashi zaune tareda zuro qafafunta qasa tana son sanin menene time.
Baya dakin ita kadaice
Ta Dan kalli wayarsa dake aje Kan drawer na gefen gadon ahankali takai hannunta ta taba screen din yayi haske Dan taduba time sai kawai tayi arba da hotonta akan wayar dayayi kyau sosai tana sanye da riga da wando da wula qarama dukkaninsu fararene Banda gashin kanta daya fito shikadaine baqi yayi kyau sosai da Dan boyayyan murmushi a fuskarta da tsananin mamaki take kallon hoton tanason tuna yaushe tayisa Amma takasa tunawa saidai tanada tabbacin koma dai yaushene ba yanzu bane Kuma a qasar turawane duba da yanayin shigarta dakuma mutanen dasuka fito bayan hoton,
A iya saninta kafin aurenta duka duka zuwanta qasashen waje baifi so uku suma duk sbd issues na ciwon Hanifa ne sai Wanda suka tafi kwanaki na dashen last cikin Nan nata daya bare Wanda shikuma bayan aurenta ne,
A dukkanin tafiyar Nan dasukai nataredashi sukajeba bayan wannan ta qarshen wadda Kuma tanada tabbacin Bata saka kayan nanba saidai idan ta mantane,
A Ina yasamu wannan hoton????

Koma dai a inane hakan yasaka zuciyarta cikin wani irin hali na kasa danne abinda yake ranta,fuskarta na bayyanarda sirrin ciki wanda yake saukarda wata walwala farin ciki akan fuskar.

Qarfe goma da mintuna ashirin da bakwai Kai tsaye ta miqe tana nufar toilet tabude tashige hankalinta nakan tunanin ko harya fita.
Brush din tayi tareda sake shiga ruwan zafi bayan tayi fitsari ta Danyi mintuna aciki kafin tafito tana gyara wuyan rigarta da har lokacin maballanta suke abude wasuma sun fincike sun fita sbd yanda ya ciresu bayan sallar asuba dazai rabata da rigar.

Tana fitowa ta hangosa zaune a palon Yana duba sako a laptop gabaki daya hankalinsa nakan laptop din ya aiki da ita Jin rufo kofar bedroom dinsa yasashi sanin ta farka Amma Bai tashiba baikuma dauke idanuwansa da hankalinsa Dake kan aikin gabansa ba saidai ya Dan bude Baki cikin kulawa da kwarjini tareda Kamala yace”

Good morning Mah lady,
Xo nan naji Yaya Kika tashi.

Ba musu ta qaraso tana kokarin zama gefensa ya kamo hannunta ya jawota ya Dora Kan cinyarsa Yana barin aikin dayakeyi ya maida hankalinsa kanta Yana shinshina gashinta daya tayata drying dake qamshin _Elvive extraordinary oil_ na _L’Oreal Paris_ ya gangaro da hannunsa ya Kama nata hannun ya Dora Kan cikinta natane aqasa sai nashi asaman natan cikin kulawa da tsananin son cikin dama ita dake daukeda cikin yace”

Hey little Alfa,good morning.

Bakinsa dake maganar take kalla kafin yasake mgna akai knocking ta waiwaya ta kalla kofar tana kokarin sauka daga jikinsa ya riqeta Yana hanata damar hakan sbd yasan haniface yayi waya da ita kafin yabaro bedroom cewan takawowa Naj din abincin Dan yasan takusa tashi baccin.

Ahankali ya ‘dan daga murya kadan yace tashigo kawai.

Hanifa najin hakan ta saki numfashi Dan kuwa tasan da wuya idan ba ajikinsa Naj takeba tunda taga Bai taso ya bude Mata kofarba da kansa,
Marshal bayajin kunyarta,ta kowama bayaji kila Banda iyayen Naj din Suma Babu ruwansu da yanayin rayuwarsa Amma Naj din dayake neman zararwa da kunya yakamata ya ringa raga Mata.

Murda kofar tayi taturo tareda shigowa ta maida ta rufe tana kallon Naj da tun tanajin kunyar Hanifan yanzu ta rage tunda ta fahimci shikuma Haka Allah yayisa da sakewar fuska batareda ta nuna taga zaman dasukaiba tace”

Barka da safiya sirikita.

Da wani irin kallo yabita Yana sakin boyayyan numfashin daya sakata sake baje idonta akansa Jin sunan da Hanifa takirata dashi yace”

Da gaske ke sirikartace?
Na dauka qawartace,
Hanifa sirikata na nufin matan dana right?

Aje kayan da Hanifan ta shigo dasu tayi a dining tana cewa”
Eh matan Dana ko matan qanin ko Matan yayana duka suna nufin sirikata.

Wani murmushin yakuma saki Yana Kai bakinsa kunnenta ahankali yace”

Kin zama sirikatanta kenan no more my qawa ko my aminya right?

Wani kallon daya kusan kashesa da mamaki Tai Masa ta bude Baki cikin taushin muryarta tace”

Zata cigaba da zama qawata Aminiyata har abada,
A alaqana da ita bandauketa sirika….

Murmushin dayan sakarwa zancen yasata kasa qarasawa tana miqewa da sauri tabar jikinsa ta nufi gurin Hanifa wadda ta juyo zata baro gurin ta nufi kofa tana cewa”

Inada abin Yi natafi.
Hajjo Kuma na gaidaki…

Ko tsayawa Jin abinda Naj zata fada bataiba ta nufi kofa tafice tareda rufowa.

Tasowa yayi yaqarasa janta zuwa dining din sbd sandarewan datai a tsayen Jin gaisuwar hajjo data Aiko Mata idan ba tsokanarta Hanifa keyiba da gaske ne tashiga uku da kunyar Hajjo.

Batasan lokacin data kallesaba cikin damuwa tace”

Yanzu shikenan hajjo tasan inda nakwana?

Zama yayi yana zaunar da ita yayi kissing hannunta Yana cewa”

Harma da Wanda Kika kwana taredashi tasani da……

Rufe Masa Baki tayi da sauri tana kallon idonsa Dan tasan zai iya fadar komai batareda shakka ba.

Zame hannunta yayi daga bakin nasa Yana nuna Mata abinci da ido.

Kusan shine yaciyar da ita abincin a baki duk da tana Dan kaucewa har Dole ta ringa ci daga hannun nasa suka gama yajata suka koma daki.

Cikin black _Balenciaga_ short sleeve da wando,
Sai agogon _Emporio Armani_ dake hannunsa Wanda yakeda tsananin tsada yafito Kai tsaye ya nufeta tana tsaye gaban mirror tana sake busar da kanta daya sakata Kuma jiqawa ya Dan kamota ta baya yayi kissing wuyanta ta lumshe ido Yana shaqar qamshin turensa daya shigeta sosai yace”

Zanfita saina dawo ki shirya gobene tafiyanmu da qarfe goma na safe.

Juyawa yayi yafice yabarta tsaye tana kallon fuskarta dake blushing ta cikin madubi kafin taci gaba da busar da kanta da dryer.

Riga da skirt na lace maroon tasaka Wanda hanifa takawo mata tayi sai turarensa datai amfani dashi tuna nata basa Nan din ta fito tana Jin kunyar kanta sbd yau kayan data saka din Kamar sun bayyanarda Dan kumburin cikin nata.

Palon tafara gyarawa kafin tadawo bedroom dinsa din tagyara takira Hanifa aka Aiko Mata ruqayyat ta taimaka Mata da gyaran kicin ita Kuma tayi sauran.
Qamshi koina ya dauka ta ragewa AC din palon qarfi ta dangana ta rungumi kunyarta ta fito bayan ta rufo ta zaro key din tayo cikin gida tunda dai Dole ta taho din komai kunya.

Cikin tsananin rashin sa’arta hajjo na Palo tareda Dadah datazo bankwanar tafiyar tasu gobe Dan shi Marshal din yashiga kafin ya fita zuwa inda zashi Dan zai iya dawowa kurarren lokaci shiyasa yashiga yayi musu sallama ya wuce shine Dadahn tazo sallama wa mutuniyar tata.

Tana ganin Dadah ta dauke Kai tana saddaqarwa da abinda zai biyo baya tafara qarasowa jiki amatuqar sanyaye.,
Cikin mamaki Dadah ke kallonta lokacinda ta bude Baki ahankali tace”

Hajjo Ina wuni?
Dadah sannu da zuwa.

Dadah da bakinta baya shiru da barin zance tace”

Wannan daga ita take cikin uwar ranar nan?
Badai haryanxu tana zuwa aikinba da sabon ciki?

Cikin kulawa hajjo take kallon Naj din tace”

Aa tadaina zuwa,
Aiki Kuma Kam yanzu ai saidai kila acan Qasar idan mijin zai Bari,
Yanzu daga sashen mijinta take…

Wata dariyar tsufa Dadah tayi tana maida kallonta kan Naj din tace”

ALLAH me iko,
Yanzu agaban hajjon bayan kalolin rashin arzikin dakika shimfida kala kala akan bakyason mijin shine tun kafin ayi tarewa ke harkin tare abinki,
Ai kuwa kin hutar da hajjo da afake sashenta Ana Mata Dan wake zagaye Bata saniba kuje can ku qarata Allah yasa yaqara dirko Miki wani cikin daga can….

Dariya Hanifa tayi tana cewa”

Dadah Ana samun wani cikin bayan akwai wani dama?

Hajjo kuwa dariyar zancen kawai tayi tana cewa”

Najma zoki zauna kusa Dani muyi firar bankawana kinji.

Qarasowa tayi tana Dan hararar gefen Dadah ta zauna.
Dadah tace”

Eh nagani kina hararata,Dattijo kikawai baniba.

Sai alokacin Naj ta kalleta tace”

Shikuma me yayi Miki?

Haihuwarki yayi.

Fira suke atsakaninsu ganin Haka itada hanifa suka bar palon suka nufa dakinta inda Hanifa tahau hada Mata kayanta cikin ‘daya daga cikin sabbin set din akwatinan da hajjo tasa Marshal din ya biya na gurin Haj nafisat da aka siyo.

Hanifa na hada Mata kayan it’s Kuma tana waya da Sarah akan takawo dukkanin takardun dazata sakawa hannu na damqawa sabon president dinsu aikin.
Sai kusan yamma suka fito tareda Dadah suka tafi gidansu Dan yimusu sallama.
A dakin umma habiba suka fara tsayawa suka Dan Jima acan tana Mata Yan nasihunta duk da kusan duk da Gori acikinsu kafin suka fito suka nufi sashen ummansu suka yada zango acan tareda umman da anty Amina suka hau nasu bakin.

Umma Tai Mata nasiha sosai tareda Yan maganganu na rayuwar aure da Kama miji kafin su anty Amina suka Dora da nasu Wanda suke hadawa na tsokana dakuma tunatar da ita hadarin kusancin Hannah da mijinta tunda aure zai iya shiga tsakaninsu.

Sai dare suka baro gidan bayan sunyi sallama da kowa umma ta hadota da tsaraba,suna dawowa gidan Kai tsaye a palon ta zauna tana fuskantar Sarah Dake jiranta ta zauna tana cewa”

Sorry Sarah nabarki jirana.

Karban files din hannunta tayi tana daukar pen tafara budewa tana kallon kayan drinks da aka kawowa Sarah da snacks tace”

Kici wani Abu Bari naduba nayi signing din sai driver ya maidaki gida tunda dare yayi.

Fira sukeyi sama sama tana duba takardun tana signing Sarah nafada Mata yanda abubuwan office din ke tafiya saita Dora da cewa”

Naj Abbas fa yanata yawon son adawo Masa da aikinsa anyi zama yafiso hudu Marshal ya tsaya akan hukuncinsa ya takura akan saina basa sabuwar number dinki Wai yanason magana dake Akan Marshal din kozaki Masa mgn dashi.

Bata dagoba abinda ke gabanta takeyi cikin rashin kulawa da zancen tace”

Duk indama zai samu Number na ki tabbatarda Baki Bari yasamuba
Maganar aikinsa Kuma bana tunanin ko hajjo zata sauya ra’ayin Wanda yake maganar akai bare Ni.

Qarasa signings din tayi tarufe file din qarshe tana hadawa ta miqawa Sarah tana cewa”

Thank you Sarah.

Naj zanyi kewarki gskia Amma Kuma hakan shine fatanmu ki kasance tareda mijinki kisamu hutawar gidan aure,Ina Miki fatan alkhairi a rayuwar aurenku.

Nagode Sarah,muje Naga Wanda zansa ya kaiki gida.

Miqewa sukai suka fara zuwa dakin hajjo sarah Tai Mata sallama suka fito suna kawowa harabar gidan Yana dawowa daga masallaci sallar ishai sanye cikin riga da wandon _Nike_ ash kala
Sarah ce ta gaidasa cikin mutuntawa da girmamawa matsayinsa name Companynsu.
Da kansa yasaka drivernsa yakai Sarah din gida da motarsa kafin suka nufo sashen hajjo tareda mutuniyar tasa tana gefensa Yana amsa wayar da aka kirasa lokacin har suka Isa ya wuce dakin hajjo Kai tsaye ita Kuma ta wuce dakinta.

Ya Jima sosai a sashen kafin ya tafi
Itama ta fito taje kicin ta dauko drink da snacks tadawo dakinta ta aje kafin ta Haye gado ta kwanta Dan tuni dama tayi Shirin bacci tana kwantawa bacci ya dauketa.

Washe gari qarfe Tara aka fito da kayanta aka Kai mota tafito sanye cikin doguwar English chiffon gown me Dan transparent sai blue skinny jeans daya lafe jikin cinyoyinta daga saman kuwa rigar ba transparent bace.
Handbag din _Calvin clein_ ce qarama a hannunta wadda wasu abubuwanta ke ciki qafarta kuwa loafers ne D&G.

Rungume hajjo tayi idanuwanta na Dan cikowa da hawaye ahankali ta furta” I will miss you hajjo.

Murmushi hajjo tayi tana shafa kanta tace”

Rayuwa mai albarka Najma,
Ki kula da kanki Kuma Kinga kinada ciki,munada buri da fata akan cikin Nan idan Allah yasa yazo lafiya yakuma Raya manashi.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa”
Inshallah hajjo.

Fitowa sukai tareda Hanifa suka Isa sashensu Dad Alfa Wanda ke jiranta shima.
Yan bayanai da nasihu yai Mata kafin ya Dora da cewan yasaka Mata kudi a account din _CPB_ account na qasar da aka bude Mata kafin yayi Mata adduar fatan alkhairi suka fito jikinta duk a sanyaye.

Koda suka fito tareda Hanifa da Anty Amina data kalli Dad Alfa daya fito shima zai fita cikin girmamawa ta gaidasa tana matsawa daga hanyar dazai wuce din ya amsa tareda kallonta Yana cewa”

Aminah Yaya ummanku da Dadah Ina gaidasu.

Zasuji” tace kafin suka wuce mum Malika na Bin su ukun da muguwar harara tana cewa” tsofin munafukai acikin ranta.

Suna Isa mota Yana zaune cikin bayan motar Yana waya a natse fuskarsa sanyeda _American optical_ goggles dayayi Masa wani irin kyau Dan gabaki daya tun anan din yakoma shigarsa ta can turai.

Hango Hannah sukai tafe a shirye cikin riga da wandon jeans na _Valentino_ tayi kyau sosai itama fuskarta sanyeda _Bulgari flora_ glasses dinta dama tuni aka saka akwatinta a mota.,
Baki sake Hanifa ke kallonta Anty Amina ma kusan kasa riqe mamakinta tayi Banda Naj dataji wani Abu yataso Mata ta juyo ta kallesa ta cikin glass din motar taga ko gefenda Hannah din ke tahowa Bai kallaba sbd hankalinsa nakan wayar dayake Yana Dan Yi Yana dagowa ya kalleta cikin kasa gajiya da kallonta.

Maida kallon nata takuma Yi Kan Hannah da kayan jikinta dasuka bayyanarda rayuwar turai gabaki daya atareda ita Allah yasama dad ya fice da kila shi zai iya Mata mgna Amma mum Malika Kam rungumeta tayi tana washe Baki tace”

My baby I will miss you, please ki kula da kanki karki wahalarda kanki akan program dinnan Amma kiyi kokari ki dawo min ta abinda zanyi alfahari dake, Allah yasamu abinda kikaje yi,
Dan qasa qasa tayi da muryarta yanda bazasujiba tace”

Idan kungama kwanakin program din kibar masaukinki kikoma gidan Marshal din kema kafin kidawo.

Gyadawa mum din Kai tayi tana murmushi tace”

I love you mum, muntafi saimun dawo.

Baya gefen Marshal su Anty Amina suka saka Naj dataji Kamar tafiyar tafita ranta Amma Kuma ayanda takeji ko cewa akai anfasa da ita ta zauna bazata zauna din ba matuqar da Hannah za’ai tafiyar.
Tana zama ya Kama hannunta ya sarqe da nasa Yana Dan kashe Mata ido daya har lokacin Yana waya.

Gaba Hannah tashiga badan tasoba aka tada motar suka fice daga gidan su anty Amina na bin motar da ido.
Ciki suka dawo bayan tafiyansu Naj din suka zauna palon jiki a mace sbd sunsan sai wani ikon Allah ne zai Hana qura tabiyo bayan wannan tafiyar tasu da Hannah tunda sunsan Naj din ita Kuma kayan haushinta sunfi na kirkin yawa zata tsaya fushi da basarwa har Hannah ta ringa Mata shishiginda zai iya kawo damuwa.

A airport suna Isa Babu Bata lokaci sbd time yayi akai duk abinda za’ai suka wuce.
Ticket din Economy class aka siyawa Hannah sabanin shida Naj dake first-class sbd Daman yanason sakewa da Naj din yanda zata sake Masa hannunta kuwa dama Yana cikin nata tunda suka zo airport din har suka Shiga jirgin suka zauna Wanda Hannah tayi zagi,tayi Allah ya tsine yafi so a qirga.
##MAMUH#

************************

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DM 51_*

*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
******************************

*_51_*
Saida asuba jirginsu ya sauka lokacin Naj tayi matuqar gajiya sbd yanayi na ciki ga Kuma yunwar datake damunta duk da snacks din dataita ci Basu Mata maganin yunwartaba abincin gske take buqata shiyasa duk jikin yake a sanyaye bawani qwari Koda suka fito zuwa gurin motar dazata daukesu zuwa gida sai sake lagwabewa takeyi Yana riqeda ita cikin jikinsa duk Rabin hankalinsa nakan Naj din harsuka Shiga mota ko yanzu Hannah dince agaba suna baya dukkanin farin cikin tafiyar data taho dashi ya bace ya maye da zallar baqin ciki da takaicin yanayinda idanuwanta keta game Mata suna ciki musamman yanda Naj din duk tayi wani laushi da sunan gajiya shikuma sai tarairayarta yakeyi Yana damuwa kamar wadda zatai nakudar cikin ta haife Masashi yanzu.
Tsoki taja me qarfi Wanda ya tunatarda Marshal tana cikin Motar ya Dan dago daga shafa fuskar matarsa dayakeyi ya kalleta Yana Dan kallon hanyar dasuka biyo kafin yace”

Kifadawa drivern inda za’a kaiki saimu ajeki mu wuce.

Ajiyar zuciya tayi tana kokarin danne baqin cikin datake ciki da bacin Rai ta bude Baki tareda waiwayowa ta kallesa kafin ta kalla Naj dake jikinsa idanuwanta a ‘dan rufe hannunta na riqe cikin nasa ta saki yaqen takaici tace”

Tunda Naj batajin Dadi da gajiya atareda ita hakama ga ciki tariga ta galabaita afara kaiku gida asamu akula da ita Ni sai a kaini daga baya.

Baice komaiba Dan shima isarsu gidance agabansa sbd halinda Mrs din take ciki.
Dan matsa hannunta yayi ahankali yana cewa”

Sorry wifey munkusa isa gida da kaina zanyi feeding babyna da mummynshi abinci.

Bude idanuwanta tayi ahankali ta zuba Masa idanuwanta dasukai laushi ta kallesa, take tsikar jikinsa ta tashi ya Dan bude idanuwansa akanta Yana rage murya Sosai yace”

Zaki kasheni ne?idan Kika sakemin wannan kallon bansan abinda Zan iyayiba acikin motar nan,ki ajemin kallon Nan zuwa gobe idan kin huta saikimun shi nikuma Zan nuna Miki qarfin tasirin dayakedashi akaina.

Duk da jikinta amace yake saidata Dan so barin jikin nasa sbd maganar dayake Yana sake Dan matsa hannunta da wata sigar.

Maida yayi takoma ta lafe ajikinsa din Yana cewa”

Shikenan bazan sake cewa komaiba.

Hannah tsabar hankalinta nakansu duk yanda yayi qasa da murya Saida kunnuwanta suka jiyo Mata abinda yake cewa,ta rintse idanuwanta tana damqe handbag dinta datakejin kamar ta rufe drivern dake tuqin da ita duk da kuwa baisan ma meke faruwaba a motar.

_North Beretania street,_
_Honolulu Hawaii_
_US._
Parking motar drivern yayi batareda yashigo da itaba har bakin kofar shigewarsu sbd Marshal din daya bada umarnin hakan Dan a tafi akai Hannah Dan ganin yake itama bazata rasa gajiyaba.

Kayansu aka fitar Mai aikinsa namiji Wanda Kuma Kuma shine cook shine me kula da komai na gidan bayan securities guda biyu na office da aka basa shine yadauki kayan Yana Masa sannu da dawowa tareda kallon Naj dake riqeda hannun mijinta har lokacin cikin girmamawa yace”

Welcome ma’am.

Thank you” ta furta ahankali kamar Mara lafiya.

Password din kofar yasaka kofar palon ta bude yafara shigewa ciki da ita brian na bayansu janyeda luggages dinsu,
Brian yayi saurin nufar switch na wuta ya kunna take koina haske ya kawo ya qarasa ya rage Aircon Dake aiki Wanda ya kunna dazu bayan yagama gyaran koina.

Tsaruwar palon da uban kayan kudin Dake cikinsa baya gabanta sbd yanayinda take ciki na gajiya da yunwa duk da komai na palon Dake milk da golden sun cika idonta Amma ba wannan time din yanzu
Kai tsaye hanyar dining room dinsa ya nufa da ita Yana Brian yakawo ruwa da black tea me zafi yanzu.

Zaunar da ita yafara Yi kafin yaja kujera shima ya zauna kusada ita Yana fara duba abincin dake Kan table din yaga chips ne dasu pasta salad sai qaton cake Wanda akai icing kadan.

Chips din yazuba Mata kadan da sai salad din dayaji red beef sausage kafin ya saka Mata fork aciki har Brian yakawo tea din a farin cup Kan trey Yana tiriri ya dauka tareda kaiwa bakinta Yana cewa Brian yaqara qarfin Aircon kadan sbd zataji zafi.

Ahankali take karban tea din daga hannunsa tanasha tana kallonsa yanda yakasa Bata cup din sbd karta kone sbd ganin Kamar batada qarfin riqewar.
Saidata shanye cup din tas ya aje cup din Yana kallonta da ido ya tambayeta ya Isa ko akaro?

Cikin Jin Dadi da samun nutsuwar kasancewarsu atare lokacin ta bude Baki ta furta”

Thank you.

Plate din gabanta ya nuna da ido Yana kokarin Kai hannu ta riqe hannun da nata ta kallesa kafin da ido ta kamar yanda taga dabi’arsace ta nuna Masa dayan cup din tea din tana cewa zataci da kanta.

Girgiza Mata Kai yayi Yana miqewa tsaye yace”

Zanje nafara watsa ruwa nayi salloli tukuna,Ki lura gurin cin abinci ok?
Kanta yayi kissing ya juya yabar gurin yana nufar hanyar dazata kaisa bedroom dinsa bayan ya Dan take steps biyar dasuka shiga cikin wata kofar wadda Nan ne hanyar dakinsa take bayan kayi Yar tafiya.

Tube kayan jikinsa yayi Kai tsaye bayan ya shigarda kwatinansu cikin qaton closet din kayansa daya cinye fiyeda Rabin bangon gefe daya na makeken dakin daya dauka sanyin Aircon da qamshin turarukansa masu tsada da qarfi dasuka Gama Kama dakin duk kuwa beddings din daza’a sauya dakin qamshinsa yake.

Toilet ya nufa yashiga yafara yin brush kafin yasakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe ido suna sauka jikinsa sbd nutsuwar dasuka fara basa ta warwarewar gajiyan zama.

Ya Jima sosai kafin yafito yabaro toilet din da qamshin shower gel dinsa Wanda jikinsa ma ke fitarwa.

Kai tsaye kofa ya nufa ya fito sbd sanin zuwa yanzu ta Isa Gama cin abincin Dan Haka Koda ya Isa palon a zaune yaganta Kan kujera tabaro dining din ya nufota ta zuba Masa idanuwa ganin dagashi sai towel iya qugu jikinsa da sauran ruwan wankan da yayo,
Yana qarasowa hannu ya miqa Mata Yana cewa”

Shall we¿

Cira hannunta tayi ta Kama nasa din ya miqar da ita Bai tsaya komaiba ya dauketa gaba daya suka nufa dakinsa.
Bai direta koinaba sai tsakiyar dakin Yana zare Mata Kaya ya dauko towel ya miqa Mata ta daura tana qarasa cire sauran kayanta ta nufa toilet dinda ya nuna Mata da ido tashige tareda rufowa.
Sabon brush tafasa cikin sabbin tarin brushes dasu shampoos masu tsada,dasu shaving cream da stick damasu kayan wanka dai duk masu kyau da tsada gasunan jere a makeken toilet din, tayi brush ta tattara gashinta ta daure tareda zaro wular wanka ta Leda ta Sanya tasakarwa kanta ruwan zafi itama tana lumshe ido nutsuwarta na qarasa dawowa taci abinci tayi wanka sallah kawai zata rage Mata.

Ko data fito yagama sallolinsa baya dakin ya fice zuwa dining inda yashawo tea me zafi da abinci yadawo dakin daidai Gama sallolinta da addua ta miqe tsaye ya qaraso Yana kallon yanda cikinta ya Dan taso kadan cikin doguwar rigar robar dake jikinta Mara nauyi ko kadan ya janyota jikinsa Yana tayata qarasa zare hijab dinda Tai sallah Yana miqa Mata cup din ruwan daya shigo Mata dasu ta karba Tasha kadan ta miqa Masa ya aje Kan table din Dake tareda kujeran dakin Yajata suka qarasa bakin gado ya yaye Mata tattausan duvet din dake Kan gadon Yana cewa ta kwanta da ido.

Hayewa tsakiyar gadon tayi kafin shima ya hawo Yana rufe musu Rabin jikinsu tareda Kai hannu gefen gadon ya kashe musu hasken dakin bai jimaba Yana shafa cikinta bacci yayi awon gaba da ita kafin shima yadaukesa.

Bacci me nauyi sukai sai yamma suka farka lokacin har qarfe biyar din yamman can ta Dan gota shine yafara tashi ya nufi toilet yasakeyin wanka jikinsa yasake sakewa dakyau kafin yafito ya shirya cikin riga da wando three quarter na _Catier_ farare tas dasuka matuqar qarawa farar fatarsa kyau da fitarta hutunta.

Wayarsa ya dauko ya maida layukansa na qasar tareda kunnawa lokacin ta tashi harta Shiga toilet wanka itama.
Bayan fitowarta daga bayin kallonta yayi daga qasanta zuwa sama fararen cinyoyinta Dake bayyane sbd qarancin towel din dake jikinta yaji tana neman kunce Masa notikan saiti ya kirata da hannunsa daya Yana sake kallon cinyoyin nata da tana tahowa,
Ko data iso gurinsa janyota yayi Kan cinyarsa cikin kunnenta ya rada mata”

Ki saka kayanda zaki barmun wainnan a bude”” yaqarasa fada Yana shafa cinyiyin.

Kallonsa tayi ya kashe Mata ido daya Yana cewa” yes” da ido.

Miqewa tayi fuskarta na bayyanarda murmushin data kasa riqewa ta nufi gaban mirror ta shafa Neutrogena oil cikin oils din data gani a gaban mirror din ta fitarda turaren khumrah me sanyi da tsananin qamshi ta shafa tareda tsayawa gaban closet din tana tunanin maganarsa akan abinda zata saka Masa din.

Duba kayanta tayi kaf taga babu ma wani abun kirki da Hanifa tasaka Mata a kayan sai jallabiyas guda biyar sauran duk jeans ne da blouse sai skirts sune kawai abun arziki bayansu gabaki daya kayan baccine na rashin mutunci dasu bumshort wainda batamasan a Ina Hanifan ta siyosuba harta sako Mata batareda tasaniba.

Jin tayi Bata wani damuba ta dauki wata free silk short gown purple tasaka bayan tasaka condom bra me taushi data lafe jikinta rigar iyakacinta Rabin cinyoyinta,take taji kunyar kanta na neman kamata Amma ta daure tabar rigar ta nufi inda ya aje Mata tata wayar bayan yasaka Mata wani layin ta dauka tana sake kallon kanta a mirror tanajin shakkar fita ahakan Dan tuni ya fice daga dakin Amma yunwar datakeji Dole zata fita dakin.

Da wayarta a hannu ta fito palon qamshin khumrahnta me tsananin qamshi na _*AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902*_ Wanda ummanta ta karbo Mata sbd hadin na musamman ne umma batada kayan hadin irin humran shiyasa ta siyo Mata agurin _*Amaryar kb global enterprise*_ na tashi daga jikinta Ahankali.

Waya yakeyi da hajjo Amma fitowarta yasa yayi shiru Yana sauraron hajjo kawai sbd hankalinsa yabar gurin hajjon Kuma,
Rigar jikinta yakewa wani irin kallo yana cewa”

Qawar Hanifa zata kasheni.

Qarasowa tayi gane da hajjo yake wayar ta karba wayar cikin farin cikinta daya bayyana kan fuskarta dake sakin murmushi cikin kewan hajjon tace”

Hajjo Ina wuni¿

Lafiya kalau Najma,Yaya kike?
Ya gajiyar hanya?
Ya jikinki Kuma?

Lafiya kalau hajjo,Yayasu Dad Alfa?
Ina Hanifa?

Karban wayar Hanifa Dake kusada hajjo tayi suna breakfast ta miqe tabar gurin hajjon tana fada Mata wata maganar data sanyata satar kallonsa itama tana Dan barin inda yake din sbd Hanifa zata iya zancen dazaiji tasata Jin kunya kokuma janyo Mata aiki.

Sun Jima Suna wayar harya gaji ya matso inda take ya kwantar da kansa Kan cinyoyinta Yana shaqar qamshin humrarta data shafa koina (08067558902) me sake kashe Masa jiki.

Ko data Gama wayar sallar magriba yajasu sukai tare kafin suka fito Sukaci abincin da Brian yagama dafawa suka koma sallar ishai tukuna yasata Tai brush ta kwanta shikuma ya janyo laptop Dan akwai aikin dazai duba.

Sai dare sosai kafin yagama ya kashe komai ya nufa toilet yayi brush da alwala yazo ya saka night suit ya Haye gadon tareda shigewa bargon ya shige jikinta.

Washe gari qarfe Tara na safe yayi Shirin fita cikin uniform dinsa na aiki dasukai Masa kyau matuqa qaqqarfan jikinsa ya bayyana acikinsu Banda cika Mata ido da kwarjini babu abinda yakeyi harsaida yagane irin kallon datake Masa ya janyota jikinsa lokacinda zai fita yakama bakinta ya tsotsa da kyau kafin yasaketa ahankali ya furta”

_I love you Najma_

Dagowa tayi da sauri ta kallesa kalmar na samun tarbon farin ciki a Zuciyarta har batasan lokacinda hannunta dake cikin nasaba tasake qanqamesa.
Ya kalli hannun Yana sakar Mata murmushi yace”

Ki kula kinji¿

Kai ta gyada Masa tana zare hannunta ya nufi kofa ya fice Yana sake sako Mata kiss ta bakinsa.

Tanajin tashin lafiayyar motarsa dako kukan engine bakaji ta sauke ajiyar zuciya tareda juyawa ta koma bedroom din tafara gyarawa ta dauko sweeper taqarasa gyaran Tai mopping ta kunna Aircon dasuka kashe da safen ta sauran dakunan gidan guda biyu da Palo da sauran duk Brian tunda safe yashigo yayi aikinsu yayi musu breakfast kafin ya wuce,
Dan Haka qaramar rigar baccin Dake jikinta ta zare kafin ta shige toilet tayo wanka tana fitowa ta shafa abinda zata shafa na kayan qamshi dasu Mai ta saka jeans blue da farar _Fendi_ sleeves tayi sallah yadawo Palo ta zauna tana waya dasu anty Amina da ummanta harda Dadah Saida aka Bata Tai Mata tsiyar saidai kawai tayi murmushi sbd yanzu kewarsu take bazataji haushin maganganun na Dadah ba qarshe anty Amina aka barwa wayar ta zauna Tai Mata bayanin daketa cin zuciyarta akan zuwan Hannah Dan Haka ta dorata akan hanyoyin da dama danta hanawa Hannah da kowama dama akan mijinta tunda Babu abinda ya saura kashi ya Dame da duwawu.

Bayansu da Hanifa takuma waya sunjima sunayi kafin takira Sarah itama daga qarshe takira Dattijo da dadin duniya ya ishesa yau Naj na gidan mijinta zaune.

Har bayan magriba Bai dawoba Dan Haka duk saitaji kadaici da kewa Kuma takasa cin abincin Daren ma sbd wata vegetable rice da egg aciki brian yayi ita Kuma taji batasonta Dan Haka cake da milk kawai Tasha tayi wanka tasaka rigar baccinta qarama tana idar da sallar ishai Yana dawowa dayake tayi locking kofar daga ciki bayan tafiyan Brian Yana Danna doorbell ta taso tafito bayan ta aje hijab dinta.
Tana budewa ya kalleta Yana yaba kayan jikinta yashigo ta tura kofar ta rufe Yana rungumota ta baya kafin yayi magana ahankali ta furta”

Sannu da dawowa.

Lumshe fararen idanuwansa yayi hannunsa kan cikinta ya amsa da murya can qasa kafin yace”

Kinci abinci?

Girgiza Masa Kai tana cewa”

Banason abincin daya dafa idan naji zanyi Amai.

Juyo da ita yayi Yana kallon cikinta yace”

Yanzu kina nufin bakici komaiba?

No,I ate cake.

Ajiyar zuciya ya Dan sauke Yana Kama hannunta suka nufa bedroom Yana cewa”

Bari nai wanka muje nakaiki kici abinci.

Wanka yayi ya shirya cikin black _H&M_ riga da wando ya tayata ta shirya itama cikin riga da skirt peach and white sai qaramin scarf da shine ma dakansa ya daura Mata akai suka fito hannunsa riqeda Nata yabude Mata gaban motar tashiga ya zagaya yashiga ya tada motar security ya bude Masa suka fice.

Wani babban five star Eatery suka Isa inda suka nufi can sama VIPs anan yayi Mata ordern abinci kala kala dasu snacks aikuwa kusan duk abinda aka kawo ta Dan ci
Takoshi sosai suka fito bayan yabiya shima yaci abincin yakoshi suka kamo hanyar gida.

Suna dawowa wanka taso Yi Amma tun amota ganin irin kallon dayake Mata da yanda yake kissing hannunta akai akai Dama tasan zaiyi wuya wani abun Bai biyo baya ba Dan kuwa tun a Palo suna shigowa ya janyota jikinsa yana sake shinshinan qamshinta dayafi komai yamutsashi ya sakar Mata wani sanyayyan kiss a wuya ta lumshe ido Yana waiwayowa ta kallesa ya rankwafo Yana Kama bakinta da nasa Wanda tun tanacin abinci acan yake bin bakin da qananun kiss yanzu kuwa na gasken yake buqata.

Dauketa yayi gabaki daya bakinta na cikin nasa ya nufi daki dasu ahaka ya kwantar da ita Kan gado bayan yasamu zare kayan dake jikin,
Saura kadan ya rasa numfashinsa lokacinda yaji tana kissing din bakinsa da kanta take ta qarasa kwance notikan kansa Dan kuwa yau ta ballowa kanta aiki Dan martanin datake maida Masa shiyafi komai haukatarda nutsuwarsa.

Saida suka kammala wanka ta saka kayan bacci ta kwanta bacci take ya dauketa sbd kasala da gajiya Dan kuwa duk lokacinda yayi kwanciya da ita wannan gajiyar saitazo Mata sbd ba qaramar dauriya takeba da yanayinsa na zama cikakken lafiyayyen namiji mai Jin karfi.

Washe gari ma agurin aiki ya wuni sai yamma sosai ya dawo lokacinma Brian yatafi Kuma yau dinma fita sukai suka ciyo abincinsu wani gurin daban kafin suka dawo.
Washe gari dazai fita Kai tsaye ya sanarda Brian ya daina abincin dare kuma kafin yayi aikin Komai na abinci yaringa tambayar Mrs dinsa
Brian yace to.

Da farko idan yatambaya tana fada Masa abinda zai dafa din Amma ko taci Bata wanijinsa yanda takeso Dan Haka dasukai waya da Hanifa tabata shawaran ta karba girkin tanayi kafin cikinta ya tsufa.
Hakan kuwa tayi ta karba girkin gidan daga hannun Brian Amma na yamma kawai sbd na safe MARSHAL din baya Bari tunda Yana Nan na Rana kuma yawanci cereals takesha tunda ita kadaice Saida yamma tayi na Daren idan yadawo suci tare.

Duk da kadaici da rashin zamansa sosai sai yamma bai Hana shaquwa me qarfiba Shiga tsakanin rayuwar auren nasu sbd baya fita aiki sai goma na safe ta wuce hakama karfe hudu zuwa biyar yadawo daganan Kuma shikenan bata wani motsi sai acikin jikinsa musamman da cikinta ya fito sosai Dan yanzu Yana wata shida haryana shiga na bakwai,
Tunda cikinya yafara tsufa kamar ansake jona musu juna sbd shi gabaki daya hannunsa koyaushe Yana cikin rigarta Kan cikin kokuma saman cikin duk yabi ya zare Mata cikin gidan bazaka taba cewama yasan yanda ake kame fuska ba duk da idan yanata tareda wasu kokuma suka fita kamewan dawowa take har itama Yana cika idonta.

Naj Bata samu kantaba Saida ya tabbatarda Babu wani sauran kunya a idanuwanta gurinsa musamman yanda ya mugun lalatata da saka ‘yan iskan kayanda dasu gwara Babu Wanda harta Saba Dan idan tasaka Masa wasu kayan kasa zuwa office yake Haka zai lalace acikin gidan suna zuba soyayyarda duk motsi daya idan tayi saiya furta Mata kalmar I love you.

Sayayya kayan baby kuwa harta gaji da kaiwa dakin da akaiwa jeren komai na baby,
Asibiti Kuma dama duk bayan 10 days suke zuwa Ana dubata.

Cikinta baizo Mata da matsalar komaiba shiyasa tananan ayanda take saidai haske data qara sosai na samun lafiyayyar rayuwar hutu da Jin Dadi ko kumburi bataiba saidai tsini da cikin kawai yakeyi Wanda koyaushe yake cikin daukanta hoto.

Lokacinda su Hanifa suka dawo US tareda Isma’eel a _Ala Moana_ sunkai musu ziyara inda suka sauka a wani babban hotel Amma a gidansu Hanifan suka wuni duk da Hanifan zata koma taqarasa shiryowa tadawo gabaki daya.
Kwanansu biyar a garin kafin suka tafi saidai ba Honolulu suka komaba New York suka tafi taron wani aikin sojoji da akai acanma Saida sukai kwanaba goma kafin suka nufo hanyar dawowa gida.

Da daddare sosai suka iso Dan Haka suna isowa wanka kawai tayi ta kwanta sbd Yar gajiyan zama jirgi duk da Babu wani nisa sosai.
##MAMUH#

*****************************
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902

 

*_DM 52_*

*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
******************************

*_52_*
Washe gari Bata Farkaba sai qarfe goma na safe shima sbd ya tada itane da dumin numfashinsa dayake sauke Mata a cikin wuyanta Yana yawo da hannuwansa cikin fingalalliyar rigar baccinta wadda Koda cikin daya tsufa Bata daina saka Masa ire irensuba.

Wani irin numfashi ta sauke tana ware idanuwanta masu sauran bacci akan fuskarsa Dake daf da tata Yana Mata wani kallon da ita kadaice tasan ma’anarsa.
Ta dan lumshe idanu ahankali tana sake numfashin kiss din daya sakar Mata a bayan kunne tareda sake cusa kansa cikin kirjinta duk da girman cikinta na hanasa manne Mata yanda yasaba ta bude idanuwanta tareda zura hannuwanta ta saqalo wuyansa tana nufar bakinsa da nata kafin ta Isa ya qarasa zuro kansa ya hade bakinsu sukahau kissing juna cikin nutsuwa da soyayyar dasukeji me qarfin gaske akan junansu daga nan lalabo rigar jikinta yayi yaqarasa zareta ya jefar Yana mannuwa da jikinta sunan cigaba da kissing juna.

Wanka tafito ta shirya tareda sakan gown Mara nauyi me Fadi sosai guntuwa wadda take ta masu ciki ce, ta daure gashinta da ko kafin barowarsu New York taje beauty parlor angyara matashi tafito tana qamshin Tom Ford dinsa da wani lokacin shi take shafawa wayarta Kan kunnenta tana waya da Hanifa dake sanar da ita komawarta Nigeria cikin satin Inshallah.

Hanifa Nima inason zuwa sbd na haihu acan din amma nasan bazai yadda ba.

Hanifa tace”

Tabbas bazai yardaba sbd Nima munyi mgna dashi din na tambayesa yaushe Zaki koma ki haihu agida yace Babu inda Zaki anan Zaki haihu kafin kuje gidan daga baya.

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa”

Dama nasan bazai yardaba yanzu ke yaushene ranar tafi……..kasa qarasawa tayi sbd cak muryarta ta dauke da abinda idanuwanta suka ganar Mata ahankali ta furta sunan Hannah tana kallon dining din da hannahn ke zaune sanyeda Jean and blouse na Burberry kanta da wula qarama Wanda ke nuni da kamar a gidan takwana,tasake maimaita sunan Hannah din tana qin yarda da itadince.

Hanifa dataji Naj takira sunan Hannah itama Saida gabanta ya Fadi cikin mamaki tace”

Wace Hannah Kuma?
Ba karatu takeba a qasar?yakamata ace tadawo tunda duka duka program din na 1year ne suna gabanin kammalawa me tazo Nan bayan ta tsaya tayi abinda yakaita qasar.

Cikin rashin sanin abin fada Naj tace”

Bari idan naji abinda tazo Yi zankiraki.

Kashe wayar tayi ta nufi dining din Kai tsaye
Hannah dataji tahowar qamshin Marshal ta waiwayo da sauri tana Kiran sunansa,ganin Wadda ke tsaye akanta yasata hadiye wani mugun abu daya taso Mata tana qurawa cikin Naj din data tsufa ido shedan na saka Mata fata da adduar Allah ya barar da cikin.
Daure fuska tayi Kamar yanda Naj ta Dan kame fuska ta dauke Kai Yana maida hankali kan abincin datake kokarin fara zubawa taci”

Kai tsaye Naj tabude Baki tace”

Zaki dakata sai maigidan yafito kafin kici komai,sbd koni danake Matar gidan banacin abinci saiyazo..

Isowarsa dining din Yana zuba qamshi yasa Naj sake Dan kame fuska ya Dan ranqwafa yayi kissing din gefen fuskarta kafin ya zauna Yana kamo hannunta daga tsayen datake ya zaunar a cinyarsa Yana kallon cikinta kafin ya kalleta cikin kulawa yace”

All ok??

Kallonsa tayi tana kasa hadiye zancen Dake ranta ahankali a natse tace”

Kasan da zuwantane??
Yaushe tazo??

Hannunta daya riqe yai kissing kafin yace”

Yes nasan dazuwanta,
Tazo jiyane,
Munacan takirani jiya akan ta kawo Mana ziyara bama Nan,inda taxo da nisa bazata iya komawaba a jiyan shiyasa nace Brian yaje ya daukota da mota ya kawo tunda muma a jiyan muka dawo.

Daga hakan baiqaraba ya kalleta Yana cewa”

Zauna kici abinci kinajin yunwa.

Gyada Kai kawai tayi batareda tace komaiba ko sake kallon Hannah din ta zauna a kujeran kusadashi tana fara cin abincin.

Har suka Gama bakin Hannah ne kawai ke tashi agurin Wanda duk da Marshal din take maganar Naj dai bayan kunnuwanta Dake saurare ko idanuwanta taqi Basu musamman dataga yanda yakeyi Yana kallonta akaikai.
Tana gamawa ta miqe tabar gurin Takoma bedroom ta zauna kan kujera tana sauraron yanda zuciyarta ke bugawa da zafi take idanuwanta suka cikoda hawayen baqin cikin barin Hannah ta zuwar musu harma da kwana gashi bataga alamar Hannah din zata tafiba ayau.

Saidata lallashi zuciyarta ta nutsu kafin ta miqe tasake fitowa lokacin tuni sukabaro dining Yana zaune Palo Yana waya Hannah din na zaune ta kafesa da idanuwa Kamar mayya tana kallon izzarsa da kamewarsa tareda ainihin sirrin kyau da kwarjini da Allah yayi Masa.

Qarasowa tayi fuskarta akansa tana sauya yanayinta zuwa bayyanarda nauyin da cikinta yayi Mata
Yana wayar ya dago yana kallonta tana tahowar ya miqa Mata hannunsa daya ta Kama ya zaunar da ita Kan qafafunsa da Yana kallon fuskarta da alamar lafiya dai ko?

Gyada Masa Kai tayi kafin ta Dan kalli Hannah data bala’in hade fuskar takaicin Naj da baqin cikinta Yana bayyane Kan fuskarta.
Cikin nutsuwa da muryarta me sanyi da Bata canjaba tace”

Hannah Yaya aiki zance ko karatu?

Banza Hannah din Tai Mata Kamar Bata jitaba saidataga Marshal din na kokarin Gama wayar kafin ta Dan kalli Naj din a wulaqance tace”

Ko wanne kike nufi lafiya kalau musamman yanzu dazan zauna Nan cikin na gida karatun zaifi tafiya kalau.
Gama wayar yayi tareda kallon Naj dake jikinsa ya kamo fuskarta da hannunsa dayan yakama bakinta yayi kissing kafin ya miqe Yana riqeda hannunta suka nufa kofa yakuma kissing hannunta yace”

Saina dawo,ki kula da kanki da Bby okay?????

Murmushi tasakar masa tana gyada Kai kafin tace”

Take care too.

Bayan fitarsa komawa tayi palonta ta zauna tareda daukan remote ta kunna TV tana kallo tana karba waya akai akai Bata sake bi takan Hannah ba.

Kamar yanda tasaba zuwan Hannah Bai hanata komaiba,data Gama abincin yamma taje tayin wanka ta sauya ado duk da ko lokacin ba wasu kaya masu takura tasakaba sai qamshinta takeyi tana fitowa Palo Yana dawowa,
Yana shigowa da Hannah dake zaune tana chatting a waya yafara cin Karo taci adonta Sama sama yake amsa gaisuwarta sbd Mrs dinsa daya hango tana tahowa gabaki daya tauke hankalinsa,
Wani murmushinda Hannah Bata taba gani a fuskar Saba taga ya sakarwa Naj din Yana Dan bude Mata hannu daya ta qaraso ta shige tareda rungumesa tana cewa”

Barka da dawowa.

Da ido ya amsa Mata suna wucewa zuwa bedroom dinsa Dan yayi freshen up.

Zuwan Hannah gidan Bai qareta da komaiba bayan gagarumin baqin ciki da takaici Dan tunda tazo babu iskan datake shaqa a gidan bana baqin ciki da takaiciba.

Naj gabaki daya ta iskance a gidan tagama lalacewa Marshal Wanda shikuma dama hakan yafiso shiyasa gidan yafara gundurar Hannah Amma ta nace taqi tafi,
Ko ina,kowane lokaci Naj cikin jikinsa acikin gidan,
Kiss kuwa a gidan Kamar ruwan Sha suka daukesa ya koyar da ita hakan,
Dakansa yafara gundura da zaman Hannah a gidan sbd sunsaba koina harkokinsu sukeyi Amma yanzu kamai ya dauko saidai bedroom dinsu.

Itadai Naj Bata bi takan Hannah sbd yanzu batada wani fargaba akanta damuwanta dayane yanda tayi tayi dashi akan Hannah din Takoma inda tafito Amma yace tabarta ta zauna harta tafi Dan kanta sbd kamar sun samu Dan break ne program din datake.

Hannah Bata fara kawowa Naj matsala ba sai dataga Naj dai dagake tako Ina tagama cike Marshal da rayuwarsa Baya iya ganin kowace mace sai ita Dan Haka taqi yadda da amincewa hakan tafara yiwa Marshal din shishigin son nuna itama matarsa zata zama Nan gaba.

Gabaki daya shi baisan abinda yake faruwaba a gidan sbd rashin zamansa dakuma koya dawo yanzu Bai cika zama Nan palonba Yana dakinsa wannan sabon tsarin Naj ne wadda Hannah takaita iya maqurar hakurnta Dan kuwa yanzu dai da qarfi da yaji take Kai kanta garesa musamman idan Yana dakin geamin acan tafi samunsa sbd lokacin Naj na baccin safiya.

Al’amarin yafara isar Naj takira Hanifa cikin damuwa take fada Mata maganar sbd Yan kwanakin har fada sunyi akan tace sai Hannah ta tafi shikuma can mum Malika takirasa tasakasa Masa tattausan lafuzan roqan alfarman Hannah ta zauna gidan taqarasa ‘yan kwanakin program na karatunta daya rage Mata.
Ya amince da hakan shiyasa yanzu zamanta gidan yakeda matsayi tunda ta tashi daga baquwar datace tazo weekend gashi yanzu kullum idan zai fita da safe kusan tare suke fita ya ajeta a Hanya taqarasa da taxi ko bus.

Numfashi Mai zafi Hanifa tasake cikin mamakin mum Malikan da Hannah dama takaicinsu tace”

Mezaisa qatuwar tsohuwar budurwa kamar Hannah tazo tazauna gidanku bayan ko haihuwar farko bakuiba,bayan hakan kowa yasan cewa son mijinki take batun yanzu ba.

Kalmar sonsa da Hannah keyi da Hanifan tafada ita tasake kashe jikin Naj din ta rintse ido kanta na neman sarawa zuwan Hannah gabaki daya ya hanata sukuni yanzu duk da Bata taba Bari Hannah din tagano rashin kunin nataba dashima kansa sbd karya gano zafin kishinta me tsanani.

Hajjo Dake zaune gefen Hanifa tanajin duk abinda suka tattauna tana Kuma iya jiyo damuwar dake cikin muryar Naj din itama al’amarin ya matuqar bata mamakin halin Malika Dan kuwa batai tunanin rashin tunanin nasu yakai can ba Dan Haka sai ranta ya soma baci da al’amarin tasan idan takira Marshal Tai Masa maganar ko yayane zaiji rashin Jin dadin Naj sbd ganin Kamar qararsa takawo akan wannan abun dazasu iya magana a tsakaninsu Dan hakan Bata kirasaba Saida aka kwana daya da maganar takira Dad Alfa ta sanar dashi komai tareda dorawa da cewan yasaka mum Malika takira Hannah tabar gidan Takoma masaukinta kokuma akama Mata wani gidan idan batason zama can.

Dad Sam baiji dadin al’amarinba musamman ya zaunarda Malika yafada Mata Marshal din yafada Masa baida ra’ayin auren Mata biyu kowace mace ma ba Hannah kawai ba,
Yayi Mata bayanin hakan yakuma fahimtar da ita ta zaunar da Hannah tafada Mata tabawa masu Sonta dama kawai tabar maganar JALAL din Amma shine ta turata sbd kawo fitina tsakanin Marshal din da matarsa.

Rufe ido yayi yai Mata fada sosai tareda cewa takira Hannah tabar gidan zai tura Mata isasun kudi takama wani gidan ta zauna Kuma tana gamawa ko sati Bai yadda taqara a qasarba Bata dawo gidaba.

Duk inda Rai yakai maqurar baci ran mum Malika yabaci sai kawai takira Naj tayi Mata fada tatas Wanda bayan Gori Babu abin daya qunsa Wanda duk yanda taso riqe kanta kasawa tayi Saida kuka yazo Mata ta kashe wayar tanayi.
Bayan Gama wayarsu mum Malika Marshal din takira shima tafada Masa irin fadan da Dad dinsa da hajjo sukai tareda Bata laifi tafada Masa takira matarsa tabata hakuri sbd ita Bata dauka abun zaizama abinda har Naj zata kasa tsayawa ayi maganarba anan tsakaninsu harsaita Kira hajjo da Dad Alfa tafada musu.

Zancen Bai Masa dadiba ko kadan musamman daya Kira dad dinsa yasake Masa maganar tareda sake bayyanar Masa da umarninsa na Hannah tabar gidan,
Hajjo ma fada Tai Masa sosai hakan duk saiya sakar Masa pressure sbd abinda Bai taba faruwa bane yau din yafaru sai yabawa Naj laifin rashin hakurinta data kasa fuskantarsa akan zancen harta kirasu hajjo da Dad Dan Haka daya dawo gidan dama itama kukan datasha zuciyarta tagama daukan ‘daci sai kawai shedan yashiga tsakaninsu suka samu sabani me girma Wanda yasata kukan da Bata taba yiba tun aurenta dashi.

Shima fita yayi gidan sbd kukanta Dake neman qarasa rusa zuciyarsa Dan har cikin ransa yake jinsa Amma Dolene yayi Mata fadan abinda tai din.
Yini guda tayi adaki tana kuka cikin tsananin damuwa,fuskarta ta kumbura tayi jajir ahaka saiga Kiran Anty Amina tana dauka sai kawai ta fashewa Anty Aminan da kuka tana kasa magana,gabaki daya hankalin anty Amina dake taredasu hajjo yatashi Suma hankalinsu yatashi musamman hajjo anty Amina cikin damuwa me girma tace”

Naj lafiya kike wannan kukan Haka?
Meyake faruwane??

Cikin kuka tafara fadawa anty Amina komai taqare maganar da cewa”

Anty Amina Dan Allah nidai Zan dawo gida zuciyata takasa dauka,
Da wanne zanji?
Da kishinta Dake cina kokuwa da wannan masifar dazsuyita haddasa tsakanina dashi,
Zan dawo gida kawai sbd idan ban Dan tafiba zasu cigaba da hada fitanarda zata kawo babban fada a tsakaninmu banaso…

Shiru Anty Amina tayi sbd zamansu hajjo da Hanifa dake gurin yasa bazata iya fadar wata maganar ba sai kawai tahau bawa Naj din hakuri tana tausarta Akan karta taho gidan,
Katsewa wayar tayi batareda kowa yace komaiba ta kalli hajjo cikin tausasa al’amarin tace”

Bawani abun damuwa bane ai zasu daidaitane Daman Dole za’a ringa fada irin Haka.

Qala dai hajjo bataceba saima wayar dad alfa data lalubo ta saka Kira Yana dauka ta sanar dashi tanason ganinsa da matarsa.

Anty Amina dai sake Dan tausar hajjon tayi sbd ko Batai magana taga alamar Kamar yadauka zafi ranta ya baci,
Ta Jima gidan sai maraice tana ganin shigowar Dad Alfa da mum Malika tasan Magana zasuyi da hajjo ta miqe itada Hanifa suka nufi dakin Hanifa ta dauko gyalenta ta fice bayan ta gaidasu cikin biyayya.

Zama sukai bayan sun gaida hajjon wadda Bata tsaya batawa kanta lokaciba ta kallesu Kai tsaye tace”

Nace Hannah tabar gidan JALAL Bata bariba gashi matsalar tashin hankali tafara shigowa tsakaninsu yarinya da tsohon ciki za’a sakata damuwa matsala tabiyo baya,
Dan Haka ke Malika tunda kekika turata da manufar cusa kanta akansa bayan anfada Miki shi me auren yace baya ra’ayi yanzu duk da bamu San me gaba ta tanadarba sanin gaibu sai Allah Amma kisani wlh karki bini bashin rantsuwa duk aka samu babbar matsala akan Hannah har Najma tabaro gidanta tadawo to wlh ko sati bazata cikeba da dawowa zansa naki mijin yaqara aure sai kema kisamu lokacin fuskantar matsalar gabanki Dan Naga hadda rashin zafin hakan yasa kikeson mijin wata koreta yaqara aure.

Mum Malika dataji saukar zancen kamar saukar Aradu a girgice take kallon hajjon tana son gane ko rikicin tsufa ne murya na Dan rawa da mamaki tace”

Hajjo meya kawo maganar qarin aure ga mutumin daya manyanta?
Maganar Marshal da matarsa Kuma ai tsakaninsu ne Ni menene nawa daza’a mun qarin kishiya akan sabanin dasuka samu…..

Hajjo dai Bata bi takan zancen mum Malikan ba ta kalli Dad Alfa tace”

Kaji abinda nafada Kai ko?

Inshallah hajjo za’ai yanda kikace.

Ja matarka kuje banson maimaicin zancen yanzu.

Suna fita mum Malika taso haukace Masa sbd maganar auren sai yanzu tasake tabbatarwa dataga ya amsawa hajjon a ladabce ma musantawa,
Qafafunta na rawar disco ta Isa dakinta tashige ta lalubo wayarta tashin farko Hannah takira murya na rawa cikin ihu tace”

Hannah ki tattara kayanki yanzu yanzu kibar gidan nan….

Cikin mamaki ta kalli wayarta Jin yanda mum din ke maganar hankali tashe tace”

Mum Kamar Yaya nabar gidan bayan yanzunema nakejin dadin gidan da masu gidan ke fada,Babu inda zani mum Malika gskia.

Kutumar uba,Ina cewa kibar gidan yanzu shine kike fadamun Babu inda zaki¿To saurara kiji maganar aurenki da Marshal ba kubarta yanzu babuta Dan kuwa hajjo tamun barazana da kishiya duk Kika kawo matsala ga aurensu……

Cikin zallar mamakin mum din Hannah tace”

Mum menene Dan anmiki kishiya idan har zansamu shiga gidan Marshal?Naga ai kin Gama manyanta Babu wani abinda yarage Dan anmiki kishiya akan farin cikina,nidai Babu inda zani yanzu danake ganin haske kiyi hkr kawai mum.

Zagi da fada Kamar mum zata tashi sama ta ringa jehowa Hannah din Amma Hanna ta kashe wayarta tana cewa”

Lallai mum tafara batan lissafi.

Mum dakejin Kamar ta Ari hauka akan al’amarin idan ba barin gidan Hannah tayiba batada nutsuwa Dan Haka Kai tsaye Marshal takira Yana ganin kiranta yaqi dauka sbd bayason wata damuwar akan wadda yake ciki da matarsa tsawon kwanakin ko dakin kwanciya sun Raba sbd tadaina kwana dakinsa.
Ganin ta dage da Kiran yasashi dauka sai kawai ta fashe masa da kuka tana fada Masa batasan me Naj din tasake fadawa hajjo ba Amma hajjo ranta yayi matuqar baci ta tursasa dad dinsa qarin aure baiyi niyyaba itadai yanzu yaje Hannah tabar gidansa.

Innalillahi yafada acikin ransa Yana rintse idanuwa gabaki daya baisan meyake damun kowaba musamman Naj gashinan ta gana musu azabar rashin juna dagashi har ita.

Koda yadawo gida Ashe mum takira Naj tai Mata tas akan hukuncin hajjon ta Dora da fadin idan ma Bai aura Hannah bakisan wazai iya auraba gaba..
Kiran yasa Naj sake shiga yanayi na damuwa me tsanani Tasha kukan bazataso hajjo tasa Dad Alfa yayi auren rashin niyaba da girmansa Dan Haka sai kawai taji ta yanke shawaran komawa gida sbd komai ya lafa zuciyoyin kowa su sauka Dan idan tabar gidan ne kawai zai iya binta subarwa Hannah gidan idan bazata tafiba itama tana ganin sunbar gidan zata tattara Dole tabar gidan koba komai cikinta yashiga watan haihuwa gida takeson haihuwan.

Koda yadawo Bai nema Naj dinba sbd bayason su sake samun damuwa akan maganar Kai tsaye yakira Hannah a waya yace ta hada kayanta driver zai maidata gidanta sai kawai tasaka Masa kuka ya kashe wayarsa Yana jifa da wayar.

Booking ticket da komai tayi na tafiyarta batareda tafada Masa ba sai Ana gobe jirginta zaintashi tasamesa har dakinsa Yana zaune Yana aiki a laptop ta kallesa shima ita din ya Dan kalla Kai tsaye tace”

Nasiya ticket gobe Zan tafi Nigeria Inshallah.

Takaicin maganarta yasa Bai dagoba ya kalleta cikin zafin Zuciya yace”

A sauka lafiya.

Juyawa tayi tabar dakin tata zuciyar na tafasa da zafi na yanda yaqi hanata tafiyar Dan Haka tana zuwa daki tahau hada kayanta kafin ta kwanta Dan tafiyar safe zatai.

Washe gari ko data fito yafita office da mota bayan yasa andauki Hannah data Sha kukan maganar daya fada Mata na Babu wani so ko Abu makamancin hakan aransa gameda ita shi matarsa Naj kawai yakeso bayan ita baya ra’ayin wata,shiyasa Koda aka kaita masaukinta Jin tayi qasar gabaki daya ta fita ranta dama dama danshi ta jona karatun yanzu Kuma tunda harya fito yafada Mata hakan bazata iya cigaba da zama anan dinba itama ticket din tasiya na barin qasar Amma gidan qanwar namanta dake Ghana ta nufa taqi komawa gida.

Taxi tahau takaita airport kaita airport idanuwanta sai cikowa da hawaye suke tana maidawa sbd kewarsa datakeji tun batabar qasarba,
Jirginsu na tashi ta rintse ido tana sakin hawayenta dasuka kasa tsayuwa.
##MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

 

*_DEEN MARSHAL_*
*_Mamuhgee_*

*_53_*
Jirginsu na sauka taxi ta dauka ta nufo gida fuskarta a kumbure da zallan kukan datasha acikin jirgin gakuma gajiyar zaman jirgi da tsohon ciki dan hakama Koda suka sauka kamarma batajin Dadi sosai Haka ta lallaba tabi taxi ta iso gida.
Securities na ganinta jiki na rawa suka dauka akwatinta zuwa ciki har gate na biyu daganan Allah yasa ruqayyat tafito kawo musu abincin Daren su sai ganin Naj tayi cikin farin ciki da girmamawa ta qaraso ta karba akwatin da handbag dinta tana Mata sannu da zuwa suka nufi ciki.

Hajjo da Hanifa ne zaune a palon suna fira sai ganin ruqayyat janyeda akwati sukai Naj na bayanta tafe da tsohon ciki fuska a kumbure
Da sauri hanifa ta tashi tarbota tana zaunar da ita gefen hajjo Dake kallonta kamar zata miqe.

Rungume hajjo tayi hawayen idanuwanta na gangarowa tana qaqalo murmushi tace”

Nayi kewarki hajjo da fatan nasameku lafiya?

Dafa kanta hajjo tayi tana qaqalo nata murmushin cikin kulawa tace”

Sannu da hanya Najma ke kadai Kika taho ko??
Kasa amsawa Naj tayi tana kallon Hanifa dake Mata sannu cikin kulawa.

Hanifa kaita dakinki tayi wanka akawo Mata abinci taci takwanta tayi bacci ta huta.

Miqewa tayi suka nufa dakin Hanifa lokacin tuni ruqayyat tabude dakin Naj din tafara gyarawa.

Bacci tayi Sosai Wanda ta manta rabonta dashi tun fara rigimarsu da mijinta.
Sai yamma ta farka lokacin tuni anty Amina tashigo suna murnar zuwanta duk da kowa yaqi tada maganar da akasan akantane dawowar tata kamar yanda Bata fadaba Suma Basu tada zancenba musamman hajjo har aka kwana biyu da dawowar tata.

Ranarda ta biyar da dawowa ranar aka daura auren Dad Alfa da anty Amina auren daya girgiza kowa sbd Babu Wanda yasan meyake faruwa bayan hajjo data saka dad din neman auren anty Aminan gurin Dattijo Kuma ta roqa alfarman adaura kawai Babu wani janye janyen saka Rana da shela.

Mum Malika hannu ta Dora akai ta ringa tsinewa Naj da Hannah akan sukeda laifin wannan muguwar qaddarar data sameta musamman Hannah sai kiranta take tana zunduma Mata zagi da fada Dan tarasa inda zata sauke haushinta.

Naj ma bataji dadin wannan aurenba Sosai daga ita har anty Aminan da ummansu sbd gujewa fitina Amma tunda andaura Babu yanda zasu iya Haka suka runguma qaddara anty Amina ta tare sashen Dad Alfa na qasa shikuma Yana sama.

Saida aka gama rikici da hidimar auren anty Amina tata damuwar tadawo sabuwa ta kewar mijinta sbd har cikin ranta batason ta haihu mijinta baya tareda ita.
Kullum wayarta ahannunta take tana jiran Kira ko massage dinsa Amma shiru Babu tun tana daurewa dai harta kasa damuwarta ta bayyanar Mata danma koyaushe daga hajjo har Hanifa da Anty Amina suna kokarin kulawa da ita ga Dadah ma da kusan lokaci lokaci tana shigowa dubata tunda yanzu ji da ita akeyi.

Yau zaune take a Palon hajjo tana Shan furar dataji nono sosai Hanifa na gefenta tana waya da mijinta
Hajjo Kuma tana cin apple din da anty Amina ke yanka Mata cikin kulawa.

Qamshin turaren dataji yashiga hancinta ko a mafarki tajisa tasan meyake nufi Dan Haka ta dago kanta ahankali ta kalli kofar palon idanuwanta suka sauka akan Wanda yake shigowa palon sanye cikin qananun kayan _Hermés_ navy blue yayi wani irin kyau da kwarjini fuskarsa a kame idanuwansa suka sauka cikin nata ya sauke wani boyayyan numfashi Yana dauke Kai daga kallonta sai alokacin dukkaninsu suka ankare da zuwansa cikin muran da farin ciki suka fara Masa sannu da zuwa.
Bai zaunaba bayan angama gaisawa sashensa da aka gama gyarawa ya nufa yasamu yayi wanka da sallah kafin yaci abinci kadan ya kwanta baccin nutsuwar ganintama kawai da yayi.

Acan bangarenta kuwa samun kanta tayi dashiga wani hali na nutsuwar zuciya da ganinsa,musamman da idanuwansu suka Shiga cikin na juna tana iya hango soyayyarta dake cinsa shima Dan Haka Koda dare yayi yanayinta ya nuna samun nutsuwar datai maimakon ita takai Masa abinci hajjo Hanifa tasaka takai Masa Dan yace bazai iya zuwaba Bai Gama hutawaba da gajiya.
Haka ta zuba ido tayi kwanan tunanin abinda yake yanzu har gari ya waye
Tunda safe tayi wankanta ta shirya cikin doguwar rigar Kuwait gown Mara nauyi sosai tana qamshinta Amma still baishigo breakfast ba kamar bazatai magana ba sai kawai ta daure ta tambaya Hanifa lafiyansa kalau kuwa?

Kije kiduba da kanki Mana Nima dai bansaniba iyakacina palonsa na dire Masa na dawowata.

Jin hakan yasa takasa samun nutsuwa Ana gama abincin Rana da kanta ta hada zata Kai Masa saigashi yashigo palon cikin guntayen kayan _Nike_ black dasuka fitarda haskensa sosai.

Kallonsa tayi tana ajiye basket din hannunta kan dining ta nufosa tana kallonsa da rauni sbd takai maqura gurin gazawa tana ta kamo hannunsa zatai magana ya Dan janye Yana dauke idanuwansa daga kanta zai wuce tasake riqo hannunsa tareda Shan gabansa Bata tsaya komaiba ta Dan daga qafafunta takai fuskarta saitin tasa ta hade bakinta da nasa tayiwa bakinsa wata irin tsotsa kafin ta sake tana kallon fuskarsa ahankali ta furta”

I’m sorry husband.

Kasa cewa komai yayi sbd tariga tagama sanin baya iya fushi da ita tareda sanin hanyayin kamasa tako Ina ya janyota jikinsa ya rungume ta gefe Yana sake Kama bakinta Yana kissing sbd cikinta daya tokaresu ya hanasu mannuwa da juna.

Gyaran muryan Hanifa ne yasa Naj zamewa ta waiwayo da sauri tana kallonta cikin fargaba saitaga ita kadaice Banda hajjo Dan ta manta da inda suke tuni.

Cikin Dan Jin kunyar kanta tace”

Ina hajjo??

Kallonta Hanifa tayi kafin ta kalli wanda yagama kamewa akan bayason tada maganarsa da Naj yanzu saita haihu ta kalla hannunsa dake riqedana matarsa tace”

Hajjo tafara fitowa taga abinda yake faruwa a palonta shine Takoma ta turoni akan ku tattara kubar Bata Palo Dan Allah.

Zaro idanuwa Naj tayi cikin wata irin masifaffiyar kunya tace”

Dagaske kike?

Da gaske nake Dan Haka kafin ku makantar Mana da ‘yar tsohuwa da wainnan hot romances din naku ku qara gaba.

Fuskewa yayi Yana mamakin yanda hanifa yanzu ta iya gulma da saka ido Yana matarsa Yana cewa suje dining zaici abinci.
Ba kunya suka taru suka fuske a sashen hajjo sai dare bayan sunci abincin dare suka ficewarsu Yana riqeda hannunta shine yayi musu Saida safe Naj kuwa sauran nauyin hajjo yaqi barinta iya mgn.

Saida suka biya sashen Dad Alfa gaisuwa kafin su wuce suka taddashi palon qasan zaune anty Amina na gefensa tana juya Masa tea din data dafo Masa Mai qamshi.

Sama sama suka gaida Dad din suka fito sbd ganin shima hutawarsa yake da amaryarsa.

Rufe kofar palonsu yayi Yana janyota jikinsa ya kalli bakinta Yana shafawa yace”

I love you wifey.

I love you too” tafurta Kai tsaye cikin siriryar muryar data sake yamutsashi suka kwasa sukai bedroom dinsa inda suka baje komai.

Asubar fari naquda me qarfi ta tadata hafara hawayen azaba Dana abun kunyar daketa binta kala kala tun aurenta yanzu Kuma daga zuwa kwana dakin mijin sai naquda kowa zaisan abinda ya tado Mata da naqudar karma Dadah taji shikenan.

Hajjo yakira Kai tsaye ya sanar Mata aikuwa hankali tashe tareda Hanifa suka fito lokacin har Anty Amina ma daya kira ta fito aka dauketa zuwa asibiti aka bar anty Amina tayi musu breakfast tazo daga baya.

Muguwar azabar datakeji yasa yau duk miskilancinta da sanyinta guduwa ta ringa Kiran sunayen Allah tana roqan gafarar mutuwa zatai
Aikuwa hankalinsa yayi mugun tashi yacewa Dr sa’id ayi Mata CS kawai tadaina Shan wannan wahalan dayake jinya acikin zuciyarsa na neman tarwatsewa.

Basa hakuri Dr sa’id yayi Yana cewa Kar ayi gaggawa zata haihu dakanta Inshallah.

Bata haihuwa sai gap da magriba lokacin tuni ta mugun galabaita Ana gama gyarata wani wahalallen bacci ya dauketa aka fitowa dasu hajjo da lafiyayyar jaririyar da Bata bar komai na Marshal ba sai bakin mamanta data dauko murna tasa iyalan gidan kasa barin asibitin Saida Naj ta farka daga dogon baccin gajiyar datai ta kalli fuskarsa Marshal din dake zaune dakin Kan kujera Yana rungume da ‘yarsa dayakejin Babu abinda yakeso aduniya yanzu Sama da ita musamman idan ta Dan motsa har cikin ransa yakejinta.

Murmushi Naj din tasaki lokacinda take kallonsa shida babyn shima ya sakar Mata nasa murmushin Yana tasowa yazauna kusada ita ya Dora Mata bbyn batareda ya damu dasu anty Amina dake dakinba umma dai sulalewa tayi tabar dakin gwara su hajjo sunsaba gani.

Washe gari aka sallamosu suka dawo gida inda suka tararda komai anyi musu tanadinsa adakinta inda zatai jegon Yan gidansu kuwa sai zuwa barka sukeyi Hanifa takasa saka ranta koina sbd farin ciki,
Dadah Kai tsaye ta sakawa yarinyar sunan _Anqi Allah yaso_ Naj najin sunan tasan da ita Dadah take saigashi yarinyar taci sunan hajjo suna kiranta da _Noor_
Bayan sunan Noor da sati biyu su anty Amina suka bar qasar itada Dad Alfa sukai tafiya zuwa umrah dakuma Malaysia da dad din zaije wani taron tsofin Marshals hahifa ma bayan tafiyansu anty Amina da kwana goma Hanifa ta wuce aka barsu sukadai sai hajjo da sabuwar tsohuwar Mai aikin hajjo Dake kula dasu bayansu ruqayyat dasu nasu aikin gyara dasu girki ne,

Mum Malika shiryawa tayi ta tafi Ghana tana cewa idan bataiwa Hannah dukaba bazata dainajin abinda takejiba dan haka ta tafi tayo Mata dukan tsiya tana kuka Hannah din na kuka suka dawo gida suka koma Yan kallon ikon Allah Dole Hannah din tafara bawa masu nemanta Daman zuwa gurinta badan tasoba sai Dan shafawa Kai lafiya dason maso wani tunda gashinan Bai kaita koinaba kotayi dinma baqin cikin zata kwasa gwara tayi aure tabar gidanma ta huta.

Watan Noor uku sabon ciki ya bulla jikin Naj batareda sanin kowaba tace Masa su tattara su koma kafin asan da cikin batason surutun dadah Dan Allah,
Dama shi hakan yakeso sukai Shirin komawa sukaje yiwasu umma bankwana da shigarsu kallo daya Dadah tayi Mata tace”

‘yar nan wani cikin Kika Kuma Yi da jaririyar ‘ya??

Kallonsa Naj tayi ganin murmushin da maganar Dadah ta sakasa ta dauke Kai ta wuce tana qin tanka maganar Dadahn sbd duk su umma da Dattijo na gurin
Sama sama cikin kunya tayi bankwana da iyayen nata tafito bayan umma ta hadota da kayan *_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902_* washe gari sukabi jirgin asuba suka wuce tareda barin ‘yan uwa da kewarsu.

Tunda suka koma wata sabuwar rayuwar Jin Dadi da kwanciyar hankali suka bude Mai tattareda tsananin so da qaunar juna gashi Kuma wannan cikinma baida laulayi Dan Haka soyayyarsu suke Sha Babu cikas ahaka tasamu cikin yakai wata bakwai lokacin Noor tayi 10month saita yayeta Hanifa tabiyo jirgi daga us tazo ta dauketa da dukkanin kayanta gabaki daya akan itace zatai riqonta.

Wannan karon Bata samu wahalar naquda ba ta haifo ‘danta namiji lafiyayye shima sukai bikinsu dagasu saisu Hanifa dasukazo da ‘yarta Noor sai anty Amina datazo tareda umma da hajjo Wanda Suma Dagan umrah zasu wuce da umman tayo kafin Hajj.
##MAMUH#

*_ALHAMDULILLAH YA ALLAH_*

*_DUKKANIN KURAKURAI DAKE CIKI ALLAH YA YAFEMANA GABAKI DAYA DANI DANA RUBUTA DAKU DAKUKA KARANTA,_*

*_DAN ALLAH KARKUCE BAI KAMATA YAQAREBA SBD BANSAN ABINDA ZA’A CIGABA DA RUBUTAWANBA IDAN BA’A TSAYA A GABARDA LABARI ZAI TAFIBA CIKIN MARMARI BATAREDA ANYITA JANSABA HARYA FITA RANMU MU DUKA, DAN HAKA KAWAI MUCE ALLAH YASA MU AMFANA GA ABINDA MUKA KARANTA,_*
*_IDAN AKWAI INDA NAYI MANTUWAR WANI ABU KU DAUKESA AMATSAYIN AJIZANCI NA DAN ADAM,_*

*_SAIMUN HADE AGABA,_*
*_ALLAH YABAR SO DA QAUNA NAGODE SOSAI._*
ZAFAFA BIYAR.

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]