[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 19 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Murmushi sosai suhail yakeyi yana kallon idanun sabreen, da sauri ta matsa baya tana cewa me kake cewane yah suhail wata yarinya kenan kake magana akai, cicefa sabreen ba wata yarinyaba. Suhail ya dawo haiyacinsa tare da sosa k’eyarsa yace kiyi hakuri sabreen idanunkune sukayi kama sosai da nata kiyi hakuri kinji😔, kai zanba hakuri yah suhail dana jik’a maka riga😊, karki damu ba komai seya juya zai fita se sukaga hafsat tsaye a kofar kichine d’in🙄. Suhail ya tsaya yana kallon hafsat yace hafsat me kikazo d’auka, ta d’an wayance tace nazo d’aukan ruwane se naji murya a kichine shine na shigo ashe kune, tana kaiwa nan ta juya da sauri ta koma d’akinta, suhail yasan hafsat tasa wani abu a ranta, ita kuwa sabreen jikinta a mave yake dan hafsat ta gansu da suhail a kichine gashi da daddare, da sauri tazo gun kofan inda suhail yake tsaye tace dashi barin wuce, juyowa yayi yana kallonta ita kuwa kanta a sunkuye ya matsa mata yana kare mata kallo harta wuce sannan shima ya wuce d’akinsa da damuwa sosai a ransa. Hafsat ranta se tafasa yakeyi ita dai batan me sukaceba amma to me yah suhail yakeyi a kichine gurin sabreen bayan sam shi bayama shiga kichine😠 lallai zan koyawa sabreen hankali idan dai har tayi kok’arin shigewa suhail d’ina, kai ina bazai yuba gobe zanyiwa mum magana akan aurenmu da suhail😠. Ita kuwa sabreen mamaki takeyi akan ganeta da suhail yaso yayi, lallai akwai aiki gobe zan sanar da kaka lbrn soyayyata da yah kamal gara kawai ayi aurenmu kar azo a samu matsala, sannan ita kanta taga yadda ran hafsat ya b’aci tace toko son yah suhail d’in takeyi oho, kishine ya tokarin sabreen a k’irjinta tace Allah sarki yah suhail shikenan zan rasaka, kuma na tabbatar daka fara sonane yanzu nima kuma ina sonka wlh😥.
Washe gari da safe sabreen bata fitoba dan basa karyawa da wuri kuma bata sallah. Harse 8:00am tayi wanka tasa riga da siket cikin kayan da kamal ya saya mata material ne blue ya mata kyau sosai ta fesa turare sannan ta yafa gyale a kafad’arta ta fito ta wuce kichin toasted bread tayi musu wanda tasa saidin a ciki se kamshine yake tashi ta sake soya egg sannan ta tafasa ruwan tea da kayan yaji taje ta shirya komai a daining sega hasat tayi wanka tasha english wears riga da siket tayi ado tazo har daining tana k’arewa kayan jikin sabreen kallo ita kanta tasan mai t’sadane dukda tasan cewa itama kyakkyawace amma kuma tasan bazata had’a kanta da sabreenba ko kusa. Ta k’arasa tace ke sabreen me kukeyi da yah suhail jiya a kichine? Sabreen ta juyo tace ina kwana hafsat, 😏hafsat tace ba wannan na tambayekiba ai, sabreen tace bakomai hannuna naje wankewa shi kuma bansan meyaje yiba, daidai lokacin suhail ya shigo palon lokacin hafsat tana cewa to wlh ki kame kanki ina gayamiki suhail shine mijin da zan aura dan haka ki dena wannan rawan kan naki😚sannan ta juya suka had’a ido da suhail ta wuce d’aki ko gaishesa bata yiba yanata binta da kallo. Jikin sabreen yayi sanyi dan maganan ya b’ata mata rai ta kalli suhail tace ina kwana yah suhail sannan ta wuce batare data jira amsarsaba ta d’auko abincincin su kaka dana mai gadi takai musu. Shi kuwa suhail yana tsaye agun yana binta da kallo harta fita sannan yayi sallama a kofar d’akin hafsat tazo ta bud’e yana tsaye fiskarta a had’e yace yau bazaki gaisheni bane hafsat, shuru tayi nad’an lokaci sannan tace ina kwana😏, yace lfy fushi kikeyi dani kenan ko? Ta marairaice murya tace gaskya yah suhail inaga lokaci yayi daya kamata muyi aure indai har kana sona😠, suhail yace to shikenan ki denayin fushi zanyiwa mum magana kinji, 😊murmushi tayi tace to nagode muje muci abinci to, shima murmushin😊 yayi mata yace to muje sannan suka nufi daining inda mum take zaune agun tana karyawa, dad’in ganinsu tare taji sosai suka zauna suna gaisawa. Sabreen kuwa bayan ta kai musu ta zauna agun kaka tana gaya masa yadda sukayi da kamal kuma ta amince. Kaka ayi ajiyar zuciya sannan yace sabreen shikenan tunda dai kina sonshi kema, amma shi suhail ya riga fara sonki tun lokacin da kuka fara had’uwa, sabreen SALMA ta gayamin komai kuma jiya da darema suhail yazo min da zancen yarinyar akan yanaga kamar kece ni kuma Sam ban gaya masa cewa kece d’inba, dukda dai shi atunaninsa an miki fyad’ene ahakan kuma yake sonki sosai sabreen. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tace kaka wlh Nima ina sonshi amma kuma yah kamal fa, kuma kaka hafsat tana son suhail sosai nan taba kaka lbrn abinda ya faru tas. Kaka ya tausayawa jikarsa sosai yace to shikenan sabreen shima kamal d’in ai mutumin kirkine Allah ya zab’a miki mafi alkhairi, tace ameen kaka maganan me kukayi da salman? Kaka yace mun dad’e Muna jiran zuwan salma da iyayenta tun bayan rasuwan mahaifinki da kwana 7 suka dawo suka gayamana gaskyar yadda mahaifinki ya rasu kuma suka bamu hak’uri sannan suka tabbatar mana da cewa duk lokacin da Muke buk’atar taimako zasuzo garemu nan kaka ya gaya mata cewa wannan macijin daya sari mamminkima salman CE ta kasheshi ba jama’an gariba babu Wanda yasan hakan saboda suba mutane bane ALJANUNE😳🙄😱

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]