[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 18 - Bankinhausanovels
Tue. Jan 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kamal yana komawa gida ya watsa ruwa a jikinsa sannan yayi shirin bacci, wayarsa ya d’auka ya kira mummynsa ya gaya mata komai akan sabreen. Farin ciki sosai tayi mishi tare da addu’oi tace kaga se’a had’a aurenku dana suhail, kamal yace insha Allah mummy sannan sukayi sallama seya kira sabreen.
Ringing d’aya ta d’auka hello, murmushi yayi yace hello sabreen kardai har kinyi bacci, a’a idona biyu ka tafine? Eh natafi kodai kinaso in dawone, a’a kawai dai na tambayane😊, yace bakinki fitowa muyi sallama ba, bahaka bane yah kamal kawai dai… se kuma tayi shuru, yace kawai dai me, tace bakomai ka isa gida lfy, lfya lau mummyna tace ingaisheki sosai, murmushi tayi tace nagode ka gaisheta, zataji me kikeyi yanzu? Bakomai ina kwamcene, har zakiyi bacci kenan, eh tace dashi, yace ok to shikenan bari in barki ki huta kinji, to nagode seda safe, ehen “I luv you so much sabreen” kunya taji sosai bata ce komaiba, yace sabreen, tace na’am a hankali, ya sake cewa “i luv u” itama tace “i luv u too” cikin wata irin murya wanda yaji dad’insa, murmushi yayi yace “ok good night” tace ok sannan tayi saurin katse wayar tare da sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Mikewa tayi ta fito palo da niyan d’iban abinci dama bata ciba, anan taga su mum sunata hira inda yah suhail yake cewa hafsat yakamata ki dinga zuwa kichine kina ganin yadda sabreen take girki dan kinsan bazata dauwama agidannanba dole wataran zatayi aure, mum tace ai nima yanzu na samu sauki dan haka zan dingayi. Sabreen tace dasu sannunku hajiya, mum tace yawwa sabreen se yanzu zakici abincin? 😊eh hajiya, sannan ta wuce inda ya suhail ya mike yayi gun daining d’in dan d’auko wayansa. Bayan ta gama d’iban abincinne ta juya zata koma se kafanta ya zame a tiles din saura kadan ta fad’i suhail ya tallafota da hannunsa biyu inda ta rike plate d’in da kyau suna kallon idon junansu🙄, sabreen taga kamar suhail yaso ya gane idanunta, da sauri ta mike tate da janye jikinta ta sunkuyar da kai tace nagode sannan ta wuce d’aki yanata binta da kallo🤔. Sabreen tana shigewa d’aki ta sauke wani ajiyar zuciya tare dayin murmushi tana jin dad’i a ranata😇 ta d’ayan b’angaren kuma kallon da suhail yake mata alokacin daya tallafota kamar kallon sani yake mata, tace to yanzu idan yah suhail ya gane idanuna fa, gaskya nayi kuskure bazan sake yarda mu had’a idoba. Shi kuwa suhail bayan ya d’auki wayansa ne seya fita waje zuciyarsa cike da waswasi akan sabreen, dan gaskya idanunta sunyi mishi kama dana wannan yarinyar🤔, kaka ya hango a tsakar gida suna hira da maigadi, ya karasa gunsu yace kaka nazo gurinkane. Kaka ya mik’e tare da cewa to muje daga can koh, gefe suka koma tagun ajiye motoci suka zauna a fararen kujeran roba, suhail yace kaka inaso in maka tambaya akan sabreen ne, kaka yace ina jinka. Suhail yace wato kaka gaskya bazan b’oye maka aduk lokacin dana kalli sabreen se inga kamar itace wannan yarinyar da neke nema mai nik’af d’innan dan gaskya bazan tab’a mancewa da idanuntaba, kakaji yaji k’irjinsa ya buga dan SALMA ta gaya masa komai kuma ta tabbatar mishi da cewa suhail shine wannan saurayin, kaka ya dawo daga duniyar tunani yace gaskya d’annan nidai jikata bata taba sa nik’af ba kuma ba’a mata fyad’eba sannan kasan babu yadda za’ayi ace an mata fyad’e kuma tab’oye mana kai kanka kasan bazai tab’a b’oyuwaba tunda kace MAZA ne harsu UKU kuma manya. Shi kansa suhail yabinda yake basa mamaki kenan yacewa kaka kwarai kuwa hakane to k’ila kamannine kawai idanunsun yayi, kaka yace eh zaiyu amma kai meyasa ka damu hakane d’annan? Suhail yace kaka bazan b’oye makaba wlh tun a wannan lokacin yarinyar “TANA RAINA” Allah ya d’auramin SONTA kaka fatana shine in sake had’uwa da ita dan in gaya mata sak’on zuciyata. Kaka yace kana nufin zaka aureta a hakan? Kwarai kuwa kaka don haka zuciyata take gayamin, kaka yaji dad’in hakan a ransa yace lallai sabreen tayi sa’an samun suhail a rayuwa gashi zai rik’eta tsakaninsa da Allah kuma jikarsa zata huta dan haka gobe zai sanar da sabreen komai sannan kuma zaice ta gayawa suhail d’in cewa itace wannan yarinyar kuma ba’a mata fyad’eba. Suhail ne ya katseshi da cewa shikenan kaka nizan shiga ciki seda safe, tare suka mik’e sannan kaka yace toh Allah ya tashemu lfy, suhail yace ameen sannan yayiwa maigadi sallama seya shiga cikin gida. Koda ya shiga su mum sun shiga bacci, sabreen ne ta fito da plate d’in abinci kanta ko d’ankwali babu dan tasan babu kowa a palo ta nufi kichine bata lura da suhail ya shigo palon ba, shi kuwa suhail gashin kanta kawai yakebi da kallo mai tsayi sosai dan batasa ribom ba yana baje a bayanta. Kichine d’in ya bita lokacin tana wanke hanunta akan sink yaje dab da bayanta ya tsaya, bayan ta gama wanke hannuntane seta juyo dan komawa d’akinta aiseta tsorata ganin mutum a bayanta har hannayenta sun tab’a kirjinsa inda ruwan hannunta ya jik’a mishi rigansa tana kallonsa cikintsoro😳 suhail yace wlh kece kece wanan yarinyar daga razanarki na gane kece dan bazan tab’a mantawaba😇

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]