ALJANU, Aljanufa kace kaka, kana nufin salma aljanace shine nayita hankad’ata jiya? Kaka yace kwarai kuwa shiyasa naketa dakatar dake, danma kinyi sa’a salma tana sonki a ranta ne tace ranan tazo gunki a d’akinki ganin,yadda kika tsoratane yasa ta canja salon zuwa ta yadda kowa zai ganta dan karki tsorata, amma wannan maganan ya zama tsakaninmu mu uku kinji? Sabreen ta sauke tsorataccen ajiyar zuciya tace to kaka shikenan nizanje in karya, yace toh sannan ta fito har zata shiga palo se taji hon, bayan maigadi ya bud’ene se taga motar kamal ne yake shigowa, hon yayi mata tare da kunnan wutan motan yana hankata, murmushi tayi sannan ta k’arasa gun motan ta tsaya ta gefensa, fitowa yayi cikin farin shets da blue jeens yayi kyau sosai ga kamshi da yake tashi, “good morning my luv” yace da ita yana murmushi?, kunya taji sosai ta kauda kanta gefe tace morng ya kake?, lfyta lau kin fito gurin kakane? Eh nakai mishi abincine, ok to muje ciki kafin ya gama cin abincin se indawo gunsa. Ayate suke tfy yana kallonta tare da cewa gaskya wannan wankan yayi kuma na yaba?, dariya tayi dai dai lokacin sun shiga palo tare da sallama, wani irin abu ne ya tokari suhail a k’irkinsa ayayinda ya hangosu suna tahowa, sabteen ta karasa ta gaida hajiya sannan ta wuce ciki sunaya binta da kallo dukkansu?. Bayan kamal ya zauna ne suka gaisa sannan hafsat ma ta gaishesa tare da had’a mashi tea, suna sha suna hira. Anan ne kamal yake sanar da mum k’udirinsa akan sabreen, mum taji dad’i sosai kuma tayi farin ciki tace to ai gara dai kam kuyi aure zaifi, kaima suhail yanzu kam lokaci yayi da za’ayi aurenku da hafsat kamar yadda iyayenku sukeso. Wani irin dad’i hafsat taji a ranta tace kamar kina raina mum?, suhail ya kalli hafsat yace mum tunda tana karatu a dai bari seta gama tundama saura 1year ne ta gama. Mum tace to shikenan Allah ya nuna mana, yace ameen, kamal yace to gaskya nidai zan rigaka dan banaso in wuce nan da 6 month, suhail yayi murmushi yace to Allah ya sanya alkhairi, sukace ameen.
Ita kuwa sabreen tunda ta shiga d’aki taketa tunanin maganan da sukayi da kaka, nan ta kira munira ta gaya mata komai a waya. Munira tayi mamaki sosai tace yanzu bakya tsoro sabreen gaskya ina son ganinta, kuma inaso ta zama kawata wlh?, sabreen tace lallai kam to idan ta sake dawowa zan had’aku. Munira tace to yanzu shikenan kin hakura da suhail d’in? Sabreen tace eh nahakura munna kawai zan auri yah kamal tunda ma kinga ga abinda hafsat tace min, munnira tace to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agareki k’awata, sabreen tace ameen ina abbakar sadiq d’inki? Munna tace yanan shimafa ya dage wai miyi aire se inci gaba da karatuna, sabreen tace eh tundai zai barki ai shikenan nima hakan zanyi, munna tace eyye ashe fa kina son kamal d’innan?, sabreen tayi dariya tace bakida kyau fa munna nikam se anjuma ki gaida su mama?, munna tace to nagode zasuji ki gaidamin “ango to bee” hmm zaiji sannan ta katse wayar tana dariya?.
Bayan su mum sun gama cin abincine kamal da suhail sukaje gun kaka kamal ya gaya masa buk’atarsa akan sabreen, kaka yaji dad’i sosai kuma ya tabbatarwa kamal cewa yabashi tunda dai sabreen d’in ta amince, murna sosai kamal yayi sannan sukayiwa kaka godiya suka tafi. Suhail da kamal ne suke tfya a cikin motansu suna hira, suhail yace abokina ka kusa ka zama angon sabreen, kamal yace bawannanba tukunna, kasanfa matsalata suhail yanzu in gayawa sabreen ne ko dai inyi shuru? Suhail yace ina kace nanda 6month kake son auren, kaga daidai kenan kafin lokacin auren komai zai daidaita kamar yadda doctors sukace insha Allah. Daganan kuma shikenan seka jah kaya abokina gaskya zaka morefa da wannan sabreen d’in naka??, ??duka kamal yakai masa yana dariya tare da cewa kaima ai k’i kayi damunyi tare. Suhail yace abokina kafi kowa sanin cewa ban tab’a “SON” hafsat a matsayin matar aurenaba sedai “SO” amatsayin ‘yar’uwata na jini, nidai wannan yarinyar “TANA RAINA” itace nake “SO” a matsayin matar aurena dan haka sedai in auri mata biyu a rana d’aya wannan shine burina, da zab’in mahaifina da kuma zab’i nah. Kamal yace “ar u serious?” Suhail yace wlh abokina shiyasa nake so ka tayani da addu’a Allah ya sake had’ani da “TANA RAINA” kamal yace tofa harka lak’ana mata suna kenan toh ai semu sake komawa k’auyen gobe ko Allah zaisa mu dace, suhail yace hakan za’ayi kuwa, kamal yana kallon abokinsa kallon mamaki da irin son da yakewa wanda akaiwa fyad’e, yace sekayi angon “TANA RAINA” dariya suhail yayi? yace eyyy angon sabreen sannan suka tafa✋?suna dariya nima “SAD-NAS” na tayasu???
Check Also
KHAIREEYAH CHAPTER 15
Yau neh ranar da Khairiyya zata shiga Jami’a, Ita da kanta ta tashi batare da …