JENNIFA CHAPTER 24

Advertisements

_____

 

 

Ya xuba mata ido yana  kallonta ranshi abace cikin muryar tsawa kadan yace daga ina kike ? Shiru tayi kanta akasa , ya matso kusa da ita dago kai ki ban amsa , ina kika je ? Asanyaye ta abshi amsa gidanmu . girgixa kai yayi , naje gidanku Maman David tace bakije ba, gabanta ya fadi , tarasa ydda xatayi gashi ya tsareta da manyan idanuwansa,

       Naje gidan yayata ne. Tabashi amsa tana addu’ar Allah yasa ya amince, ina kenan ?? Ya kuma tambyrta muryarta na rawa ta amsa

Advertisements

_____

        Hotoro, Ok dago kanki ki kalleni

  A kunyace ta dago fuskarta kwarjinin fuskarshi yasa takasa jurewa tai kasa da kanta, hannu yasa ya dago da fuskar ta ta xubawa kyakkyawar fuskarshi  ido, shima idonshi akanta yana kallonta , kin San irin yaran da suke barin gida batre da wani dalili kwakkwara ba ?? Kai ta girgixa masa, nop kiyi magana, Asanyaye tace bansani ba,

     Kwafa yayi yaran dabasu da tarbiyya,

Xaro ido tayi atsorace

     Daga yau in ba dady ko Momy ne sukai miki mgn kada ki kuma varin gidannan jina jina? Kai ta daga hade da fadin naji zan kiyaye, Yayi Kyau, ya saki fuskarta sannan ya xuba hannayensa a aljihu, ki kiyaye.

  Inshaa Allah zan kiyaye,

  Ya fice daga dakin tabi bayanshi da kallo tana murmushi hade da jin dadin ganinshi ta fuskanci ya rame kadan,

          ************

Dakinsa ya koma ranshi yai mishi dadi na ganin ta dawo gida ya ga abubuwa da yawa afuskarta, tayi missing dinshi, murmushi yayi kadan, kofar aka bude hade dayin sallama mmk ya kamashi ganin Wanda ya shigo  hannu suka bawa juna, sagir ? Yaushe ka dawo ? Ba sanarwa? Dariya sagir din yayi, jiya na dawo,

Hamdala khaleel yayi  kaxo a time din Dana ke bukatarka, xama yayi ya kalli khaleel man naga ka rame kadan me ya sameka, kallon sagir din yayi da mmk, rama ? Ya maimaita, kana mmk ne sagir ya tmbyshi hade da janyo laptop din khaleel ya bude pix din jenny akai, sagir yace wow, wannan wacece? Ina kasamo kyakkyawa haka ? Karka cemin komai akanta nasan da Jidda aka saka maka rana, plx khaleel ina kamun wannan,

    Bata rai khaleel yayi bai bashi amsaba, ta hadu matsalar kawai karama ce, amma nayi mmkin ganin pix din nan sbd nasan wannan ba tai kama da danginku ba, aslima yanda nasanka banajin xaka iya son karamar yarinya, shiru yayi khaleel bai amsa masa ba sbd ya kulu, dago kai yayi ya kalli khaleel yaga yayi kutukutu, shekewa da dariya sagir din yayi lallai fuskarka ta tabbatar min da son yarinyar nan kake, ya kuma kallon pix din wow ! Kyakkyawar fuska manyan ido, karamin baki, ya isah haka sagir, bana son maza su dinka yaba min ita, bana so da mmk sagir yake kallonshi, menene dan na yabi mai Kyau, ranshi bace yace ban hanaka ba itace kawai bana so ka yaba, rufe laptop din yayi, abokina me ya sameka ?? Jingina yayi da jikin kujera sagir ina son Jennifer,

   Jennifer? Sagir ya maimaita, Kristen ce ita ? Suka hada ido khaleel ya daga mishi kai, haba khaleel duk matan Hausa Fulani ? No ! Sagir, ya daga mishi hannu, kasan hakan ba haramun bane, dan tana Kristen bazan ki aurenta ba addinina bai haramtamin  ba, idan na aureta kamar nayi jihadine, ajiyar xuciya sagir yayi hakane khaleel, kwafa khaleel din yayi ba wannan bace matsalar,

    Taurin kai gareta taki ta sanar min tana sona, da sauri sagir ya kalleshi khaleel wai har yanxu kana nan da wannan tunanin naka? Wani kallo khaleel ya wurgawa sagir, kana ganin zan canzane? Naja ra’ayin yarinyar sosai kuma tana sona taurin kanta ya hana ta fadamin, dariyar shakiyanci sagir yayi, khaleel wato kai na daban ne mgn daya kake baka canxawa, tayaya karamar yarinya xata yi maka abinda manyan big gals irinsu nabila, amatullahi, jidda, suka kasa ?  Murmushi yayi ina son Jennifer sosai ban San yadda akayi hakan ta faru ba, bakayi mmkin fada maka hakaba? Wata irin dariya yayi sagir mmkin ne yasa nabawa zancen serious, wai shin ya akayi kake sonta ? Kai da kace sai dai mace ta soka ? Bazan iya tunawa ba kawai na tsinci kaina cikin tsananin sonta, itama tana sona bazan iya gane waye yafi son wani tsakanin mu ba,

    Khaleel mafita kawai kacewa yarinyar nan kana sonta,

  What ? Sagir ni din ?? Ina bazan iya ba banta ba yi ba bakuma zan fara akan karamar yarinya ba, kasani sagir ban taba cewa budurwa ina sonta ba su suke sona, ban yadda da wannan tsarin ba xuwa wajan mace kace kana sonta sagir babban raini ne, ka ja ra’ayin yarinya da dabaru taxo da kanta sbd takasa jurewa tace tana sonka shikenan, lol khaleel kana nan da halinka kai din na manyan yara ne irinsu Jidda, Nabila, wai ina Nabila ne ? Tsaki khaleel din yayi ina ga ko tana Singapore ne ? Meyasa baka son yarinyar nan,

     Iska ya fitar daga bakinshi bazaka ganeba Nabila bata da kamun kai dalilin dayasa nake son jenny yarinya ce karama akansu bata kaisu ilmiba har yanxu a 0 label take wannan year din tagama secondary fa amma tafisu aji  da kamun kai babu jan ra’ayin da man mata ba amma har yanxu takasa ce min tana sona yai tsaki bana son mace ta dinka hauka akaina koda tana masifar sona nafison ta dinka Jan aji haka nakeso, hakane khaleel wasu matan soyayya tana Sa su manta kansu,  yanxu ya xakayi da auren Jidda ka Jennifer ? Gyara xama khaleel yayi yace jenny is too young kona aureta yanxu renonta zanyi, dariya sagir yayi ko kuma ita tare neka ba, dariya shima yayi kasan dai zahra itace autar mu ko ? To nesa ba kusaba ta girmi jenny, kaga dole sai reno, sagir ya buce da dariyar keta ina jiye mk abu daya ranar da yarinyar nan xata rikita ka, wani kallo ya jefa wa sagir anfada maka ni mayen matane irinka kajira kaga abin mmk nan da wata daya zata furtamin tana sona da kanta, wata dariyar sagir ya kumayi, ko kuma kai ka fada mata kana sonta ba, sagir bana son iskanci kaifa shege ne tayaya da girma na da ajina zancewa yarinya karama ina sonta ? Kana ganin xan sauya ne yadda nake ? Kaxuba ido xaka sha mmkina,

     Sorry abokina yanuna idonsa wannan shine nawa, amma fa kasani soyayya ba’a yi mata alwashi,

      Tsaki khaleel din yayi ya janyo musu wata hirar

       ***********

Bayan ta fito da ga wanka ta sauya kaya Momy tashigo dakin jenny kin shirya ? Eh Momy, OK in shaa Allah anjima malan Dr Ahmad Sani ningi xai xo kamar yadda muka tsara xai baki Kalmar shahada,

     Wani dadi ya kama Jennifer, toh Momy ina jiranshi, tare suka jero suka sauko kasa babbn parlourn gidan suka xauna, Jidda da zahra suna aika mata harara, ta lumshe ido bata damu da kiyayyrsu ba sam dan tasan rayuwa baxta yiyu kowa ya sokaba dole akwai makiya, suna nan a falon suna hira jefi jefi ya khaleel yai sallama shida wani babban mutun gaba daya falon suka mike suka gaishe shi cikin farin ciki da fara’a ya amsa ya xauna yai sallama suka amsa masa,

    Wacece acikin ? Suka nuna ta kanta akasa, baiwar Allah meyasa xaki musulunta ? Hawaye ya taru a idonta cikin rawar murya tace sbd nayi imanin shine addinin gaskiya sbd adalcinsu da mutuncinsu da taimakokon juna tun ina yarinya karama nayi imani da Allah na kuma yadda addinin musulunci shine addinin gaskiya,

Alhamdulillah, mungodewa Allah yanxu xan baki Kalmar shahada kafin nan zan fada miki rkunnan musulunci da kuma ahikanshi imani, addinin musulunci addinine na amince da salama da taimakon juna da kaunar junanmu, rukunann musulinci ya kasu kashi biyar Wanda dolene sai ka amince dasu xaka shiga addinin Allah

1 shahadatu an LA ilaha illalha wa’anna Muhammadan rasulullah

2 tsaida sallah

3 bada zakka

4 yin axumin watan Ramadan

5 da xiyartar dakin Allah .

A keeda ta muslunci tushenta shine imani da Allah, da mala’ikonsa, da littattafansa, da manxanninsa, da kuma ranar lahira, da yadda da akddara me Kyau ko mummuna

Lallai wannan magana da kika fadamin ta cewa tun kina yarinya kikai imani da cewar addinin Allah shine addinin gaskiya sai kika tunamin da hadisin manxon Allah (s.a.w)  daya ke cewa, maa min mauludin illa yuladu alal fidrah, babu wani abin haihuwa face an haifeshi da imani ga Allah, fa abawahu, har sai iyayensa yuhawwidani au yunassiranihi aw yumajjisanihi, sun kasnce yahudawa ko banasare ko majusawa,

Wannan ba abin mmk bane dan dan malaman tauhidi sun kawo wannan, fa inna kulla maklukin kad fudira alal imani bi kalikihi min gairi sabqi tafkeer au ta’alim, Allahu akhbar, haka Allah ya ke halittar kowa da imani dashi batre da wani tunani ko koyarda shi ba, Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah. Ikon Allah ya wuce komai dan shiyake shiryarwa kuma shi yake fidda haske daga cikin duhu, baiwar Allah duk kin amince da hakan ? Cikin gwarin gwiwa tace eh Malan na amince, yai murmushi yace to Alhamdulillah, zan fada miki Kalmar shahada kamar yanda nai miki bayani afarko, duk abinda na fada sai ki maimaita Ash’hadu an la ila ha illallah ta bude baki da murna hade da imani harshen ta ya karye taji wani irin abu ya rufe mata ido da kyar tayi kokarin juya harshenta ta kasa bata San lokacin data mike tana kakari tana son maimaita wa gaba daayansu sukayo kanta luuuu tai kasa kafin ta karasa kasa ya khaleel ya riketa yana jijjigata dif yaga idonta ya rufe numfashinta ya tsaya cak cikin tashin hnkli suke jijjigata

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Advertisements _____ Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *