FULANIN TASHI CHAPTER 8

Advertisements

_____

Murmushi sosai Dr. Mubarak ya yi sannan yace “Dr Jalaluddeen Shuwa muna tafe a hanyarmu ta zuwa kano yanzu motarmu zata tashi, muna da oatient da *GENERAL HOSPITAL suka rubuta mana takarda zuwa *MALLAM AMINU KANO* naji ance yau zaka diba mararsa lafiya acan shine yasa na yace bari mu ɗauko hanya mu taho yau, saboda patient ɗin namu tana cikin wani haline wallaahi”, Dr. Mubarak Anas Gombe ya idashe maganar yana waiwayen sit ɗin baya inda Samha da Iya ke zaune.

“Na’am”, cewar Dr. Jalaluddeen Shuwa sannan ya ci gaba da cewa.
“Dr. Mubarak Anas Gombe kenan ku kawota, In Sha Allaahu zan bata duk wani temako daya kamata na bata Allaah ya kiyaye hanya”, ya idashe maganar yana katse kiran murmushi kwance saman fuskarshi, saboda ya ga Dr. Mubarak Anas Gombe be nuna masa sani ba shiyasa shima ya yi buris abinshi, kowwane cikinsu naji da aji da kuɗi uwa uba sarauta.

Belt Dr. Mubarak ya sanya sannan ya tada motar ya fita da ita asibityn gaba ɗaya suka hau titi, tafiya a hankali su keyi har suka fita daga cikin garin gombe gaba ɗaya, sannan Dr. Mubarak ya ɗauke hanyar Bauchi, gudu kawai yake shararawa a babban titi-titin cikin lokaci ƙanƙani suka isa garin bauchi wanda tafiyar awa ɗaya ce take kai mutum Bauchi daga Gombe amma shi se gashi tafiyar minti arba’in da biyar ta kaishi Bauchi saboda tsabar gudun da yake tiƙawa akan kwalta.

Kasuwa ya shiga ya faka motar a gefe tukum ya dunfari wani babban shago, siyayya ya yi ma su Iya da Mallam, danginsu Madara Indomie kwai da sauransu, saboda yana si su ɗan jiɓa a garin Kano lokacin Samha ta ɗan samu sannan su dawo cikin Gombe dan ya yi Alƙawari su da zaman Kaltingo sedai suga anayi, wannan rashin daraja har ina, kuma yana nan yana jiran mijin nata ya rantse da Allaah seya saketa komi daɗewa.

Advertisements

_____

buɗe boot ya yi ya loda kayan da ya siyo sannan ya shiga mota ya ƙara bata wuta suka ɗauki hanya jos.

*KANO STATE*

Shiri ya yi sosai cikin shigar manyan likitoci tukum ya fito ya faɗa mota be tsaya ya yi breakfast ba, saboda yace adadin marasa lafiyan da zai duba yau yafi gaban abincin da zaici, doreba ne yaja motar suka nufi asibityn *MALLAM AMINU KANO*.
Tun daga ƙifar asibityn har wajenshi an saka tsaro na musanman sojoji ne da ooeration yaƙi gasu nan a ko ta ina, saboda bashi kariya, wajen da ake ajiue motoci direba ya nufa ya yi fakin sannan Dr. Jalaluddeen ya fito ya taka sa ƙafa zuwa cikin asibityn.

*ABUJA*

Sosai S boy ya mutsiki Ni’imatullah san ranshi, tun tana noƙewa daga baya ta fara karman saƙon da yake bata sai gashi cikin lokaci ƙanƙani sun faranta ran juna, S Boy kuwa mamaki ne fal a ranshi yana tunanin shine ze fara sanin Ni’imatullah a mace ashe ba haka bans, lallle Ni’iɓatullaah iskanci ya gawurta, kwana S boy ya yi yana kallon Ni’imatullah dake ƙanƙame a jikinshi duk wata juyawa ta ta yana kallo yana kuma tausayin yarinyar saboda daga gidan da ta fito har ya fara dana sanin gurɓata musu tarbiyyanta, yasan dai shins mutum na farko da ya fara ɗinkira mata ƙwaya amma shi be taɓa amfani da ita ba sai a time ɗinnan kuma da farko ita ta nuna ta masa alƙawarin bashi kanta, ta jarma wasu kaɗaɗe a wajenshi daya nuna mata beda ra’ayin lalata yaran mutane shi dai ɗan rayuwa ne kawi sai tayi masa hakin ƴam bariki ta nuna duk duniya babu wanda yafi ta mutunci da kamun kuma ta dunga wayencewa.
Washe gari da sassafe S boy ya sallami Ni’imatullah wanda shine ya tada ita daga bacci sannan ya bata wasu kuɗaɗe a hannunta yace ta riƙe da cake da kayan shaye-shayen da suka yi amfani dasu, yasan halin Ni’imatullah sarai akwai kwaɗayin bala’i zuwa jibi ma zata iya kiranshi tace dubu hamsin ɗin da ya bata sun ƙare ya ƙara turo mata da wanu saboda san vanzan bala’i.

Sosai Ni’imatullah ta naniƙema S Boya tana nemanshi da wata lalatar kafin su rabu amma sam yaƙi amincewa da ita, sai ma komawa ya yi ya kwanta yace da ita baya jin daɗi ta tafi kawai, kallon agogon dake maƙale a ɗakin tayi taga shida da rabi na safiya shiyasa ta zabura ta tashi haɗi da yima S Boy godiya ta tafi amma ba dan ranta na so ba, sai dan tunawa da tayi Ammar ya dawo yana gari komi ze iya faruwa.

Mota ta tara ta shiga ta faɗa masa inda zata, a dai-dai ƙofar gidan Anty Rahina ya sauketa tukum ta zari kuɗinsa ta biyashi sannan ta shige cikin gidan.
Zaune ta tada Antu Rahina ta zabga uban tagumi ga sai ƴan biyunta Salim da Salima waɗan da suke sa’ar Ni’imatulla suna bata haƙuri ita kuma taci kuka harta godema Allaah, Sallama tayi bayan ta shiga wacce ba’a yita a waje ba sai a ciki, samun kujera tayi ta zauna daga gefw tukum ta gaida Anty Rahina, cikin dasashewar murya Anty Rahina ta farka tukum Ni’imatullah ta fara tambayar Anty Rahina lafiya take wannan kukan, amsar da Anty Rahima ta bata shi ya yi matuƙar bata mamaki cikin manyance da rawar baki ta kaɗa baki tace “Anty wai wannan mijin naki wani kalan la’ananne ne? ya rasa me zeyyi sai bin mata? gaskiya halinshi beda kyau ko kaɗan idan ka ganshi kamar na Allaah amma a ɓoye yafi ɗan shege shegantaka”, ta ƙarashe maganar tana kama bakinta alamar mamaki fal ranta.

Harara Salim da Salima suka watsa mata, kasancewar Salim yafi Salima zuciya da kuma faɗa ya ɗaga hannu ya nuna Ni’imatulla dashi sannan yace “Ni’ima wallahi tallahi! kinji na rantse da Allaah idan baki fita gidan nan ba sai nayi mummunan ɓata miki, sakarya kawai idan ba zaki yayyafa ma ƙurar ruwa ta lafa ba ce miki akayi ki ƙara mata, sannan kinsan ko da goma ta lalace ai tafi biyar Albarka ko”, ya ƙarashe maganar yana huci kamar zaki.

Sumi-sumi Ni’imatullah ta tashi zata fita Anty Rahina ta dakatar da ita da hannu, gaisawa su kayi sannan ta bata saƙon da Momi ta aikota tukum ta ƙara gaba tana harara Salim.

Daidaita ta tara ta hau ya kawuta har bakim gate sannan ya juya ya tafi ita kuma ta shige cikin gidan, sanɗa ta dungayi tana tafiya kamar ɓarauniya saboda kar wani ya ganta, karya kwana tayi za tabi ta ƙofar baya harta fara tafiya ta ɗanyi nisa Ammar dake bayanta bata sani ba ya kira sunanta “Ni’imatullah!”, ras gaban Ni’umatullah ya faɗi, hannu biyu tasa ta dafe ƙirjinta dashi cikin zuciyarta tana faɗin amma dai wannan anyi mugu, wato babu qanda ya ganni amma shi saboda tsananin bin diddiƙi seda ya ɗagoni, ta ƙarashe zancen zucin tana juyawa, tahuwa ta farayi tana dawowa da baya ya tsayar da ita cak yana faɗin “sai yanzu kika ga damar dawowa?”, jin tambayar rainin wayon da ya matane yasa ta juyawa a fusace zata faɗa masa magana amma idonta na faɗawa cikin nasa tayi sauri ta rumtse ido haɗi da kallon ƙasa tana wasa da hannayenta, ba ƙaramin cika mata ido Ammar ya yi ba yau ɗinnan musanman da ya yi shiga cikin manyan kaya sai ya fito kamar wani babban mutum.

“Daga ina kike?”, ya ƙara tambayarta yana daka mata tsawa,

Dabur-dabur ta fara yi bakinta na rawa haka jikinta wanda sai ka kalleta sosai zaka tabbatar da hakan, da ƙyar ta iya seta kanta wajen faɗin “Ya Ammar na faɗa maka inda zanje jiya”, ta faɗa idonta na kawo ruwa.

tsawa ya ƙara daka mata yana ƙara maimaita tambayar da ya yi mata amma amsa ɗaya take bashi itace ta faɗa masa inda zata jiya da dare, ganin zare idon da yake mata ya yi yawane ya sanyata rushewa da kuka saboda tasan tabbas Ammar kaɗan da aikinshi ya yi mata dukan tsiya shiba wata damuwarshi bane kuma bazai duba shaƙuwa da soyayyar dake tsakaninsu ba, ba ruwanshi da wannan shi dai burinshi ya daki mutum a gaban kowwa ya kuma gaggasa maka magana.

Ganin ta rushe da kuka ya yasa Ammar gwiwowin Ammar gaba ɗaya suka sage, sosai Ni’imatullah take kuka kamar ranta ze fita da sauri Ammar ya yo kanta haɗi da riƙe mata hannaye dukka biyu ya haɗata da ƙirjinshi yana bubbuga bayanta, nannauyar ajiyar zuciya Ni’imatullah ta sauke jikinta har rawa ya keyi wajen damƙeshi sosai, sassauta mata roƙo ya yi ya saketa dukkansu suka fara mai da numfashi, ɗagowa ya yi ya zuba mata ido na tsawon sekon hamsin da biyar sannan yace da ita “jeki ciki,” murya a shaƙe.

Ni’imatullah ba tace komi ba ta juya haɗi da share hawayenta dukka sannan ta fara tafiya zuwa cikim gidan,

Shi kuma Ammar komawa da baya ya yi kamar ɗan maye ya kwanta a akan kujerun dake wajen yana mai da numfashi, lumshe ido ya yi dukka cikin zuciyarshi yana ayyana abubuwa da dama.

Sallama tayi ta shiga cikin falon ba tare da ta jira an amsa mata ba, gaba ɗaya ahalin gidan ta tadda zaune suna breakfast saboda dukka babannin nasu na gari, wannan al’adar gidance indai suna gari dukka to haka zasu haɗu a babban falon gidan azauna cin abinci tare, Momi na ganin Ni’imatullah ta faɗaɗa murmushinta,
Kusa da ita Ni’iɓatullah taje ta zauna sannan ta gaisar da mutanen gidan ɗaya baya ɗayan, da kyar Ammi ta amsa gaisuwarta saboda sam basa shiri da ita tunda ta fara canza hali,Amra ce ta kalli Ni’imatullah haɗi da faɗin “Anty Ni’imatullah sai yanzu kika dawo?”, Amra ta faɗa tana jawar da kanta gefe saboda sam ta tsani halin da Ni’iɓatullah ta tsiro dashi yanzu.

“E yanzu na dawo kina da magana dani ne?”, Ni’imatullah ta mayar mata da amsa tana sunkuyar da kai saboda kalar kallon da Abu ya bita dashi.

“A’a kawai…..”, Ammi ce ta dakama Amra tsawa tana faɗin
“Ke Amra wa ya tambayeki ba yayarki bace?”,

“Kiyi haƙuri Ammi”, cewar Amra tana cire hannunta tsam a cikin abincin ta haye sama.

da kallo Ammi ta bita har ta ɓace ma ganinta cikin zuciyarta tana faɗin dole ta shiga tsakanin Amra da Ni’imatullah dan taga take-taken Amra, itama tana so ta ysiro da tata rashin kunyar.

Tunda suka fara maganarsu cikin Mahaifan nasu babu wanda yace wani abu har seda suka gama yin breakfast dukkansu sannan Daddy ya kalli Ni’imatulla da dawowarta daga ɗaki kenan ta canzo kaya, cikin hali da dattako yace da ita “Ni’imatullah! an jima da misalin ƙarfe tara da rabi na safen nan da akwai zama na musanman ki faɗa ma ƴan uwanki maza da mata kowwa ina so ya halarta”,
Ya ƙarashe maganar yana kawar da kai daga kallon da Ummi take masa,

“To Daddy”, Ni’imatullah ta furta sannan ta miƙe zuwa ɗaki.

Waya ta ɗauka ta dinga kiransu ɗaya bayan ɗaya tana faɗa musu akwai zama da misalin ƙarfe tara da rabi, da yawa daga cikin yaran gidan da basa nan suka fara shirin dawowa asu aure kuma suka fara shirin zuwa gida dan jin abinda za’a tattauna.

Bayan Ni’imatullah ta tashi ne Abu ya kalli Abba da Daddy yace “ƴan Uwana kumin afuwa akan rashin sanar daku maganar zaman da za’ayi ba, ba wani abu bane illa akan Ni’imatullah da Ammar……
Dakatar dashi Abu ya yi da hannu sannan yace “kana da damar da zaka zartar da komi akansu mu dai fatanmu duk abinda zai zame musu Alkhairi”, murmushi Daddy ya yi tukum suka ɗan taɓa wasa tsakaninsu da suka saba yi harda Babban Oga Alhaji Salihu da ya hakimce yana kallonsu.

*KANO STATE*

Ƙarfe tara da minti goma sha biyar su Dr. Mubakar Asan Gombe suka isa garin kano, ba ƙaramin gudu Dr. ya zuba a kwalta ba shiyasa su kayi isowar wuri, direct asibityn *MALLAM AMINU KANO* ya nufa dasu Iya,
Babban Asibity ne nazo a gani, yana ɗaya daga cikin asibitocin da ake ji dasu a arewancin Nigeria, tun daga bakin asibityn zaka tabbatar da yau ɗin ranace ta musanman saboda yadda mutane suka cika maƙil asibityn.

Bayan Dr. Mubarak ya yi fakin a cikin asibityn sannan ya ɗauki waya ya kira *DR. JALALUDDEEN SHUWA* ringing ɗaya biyu ya ɗauka ya kara a kunnebeko tsaya kallon fuskar wayar ba dan yana tsammanin kiran daga ɗaya daga cikin likitocin ne, sallama ya yi, jin muryar da aka amsa sallamar da itane yasa ya zabura ya miƙe tsaye yana faɗin “Dr. Mubakar Anas Gombe ba dai har kun iso ba”, ya faɗa yana faɗaɗa murmushin shi wanda yake ƙara fito da ainihin kyanshi.

“E mun iso Jalaluddeen gamu a wajen asibityn”, Mubarak ya bashi amsa, sosai Dr Jalaluddeen ya ƙara wanshare baki cikin zuciyarshi kuma yana mamakin wannan abu kamar almara, tabɗijon lalle Dr. Mubarak ashe har yanzu yana nan yana zuba gudu a kwalta kamar yadda ya sanshi a da,
Jin Dr. Jalaluddeen Shuwa ya yi shiru ne yasa Dr. Mubarak cewa,
“Kana kan layi kuwa”,

“E ina kan layi, kawai nayi mamakin yadda akayi ka zuba wannan gudun cikin lokaci ƙanƙani sai gaka a garin kano,”

Murmushi Dr. Mubarak Anas Gombe ya yi, saboda shi kanshi yasani kuma ya tabbatar da Allaah ne kawai ya kawosu kano lafiya, dan be taɓa gudu kamar na yau ba koma ya taɓa to tabbas da daɗewa.

“Ok to mu shigo ne ko zaka zo ka same mu?”,

“A haba bari in fito in sameku dan Allaah,” Dr. Jalaluddeen Shuwa ya faɗa yana kashe wayar, kallon wacce yake gani ya yi yace da ita ta ɗan jirashi bari yaje ya dawo.

Fitowa ya yi har haraban asibityn nan idonshi yaci karo da motar Dr. Mubarak Anas Gombe, wacce akai nata tambarin sarauta a bayanta, da kaga motar bama sai an faɗa maka daga gidan da ta fito ba, seda yazo kusa da motar sanan yasa hannu ya ƙanƙwasa motar da yake tinted ce shiyasa Dr. Mubarak be ganshi ba,
Jin ana ƙwanƙwasa motar ne yasa Dr. Mubarak yakai hannu ga handle ɗin motar ya buɗe,

Daga Dr. Mubarak har Dr. Jalaluddeen babu wanda ya cema wani ƙala sai ma kallon kallo da suka tsaya yima junansu wanda zai tabbatar maka da an jima ba’a haɗu ba.

 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Advertisements _____ Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *