[Advertisements⬇️]

FULANIN TASHI CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Wed. Nov 30th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Yace “Mama zaku kwana a cikin asibityn nan ba tare da kun biya ko sisi ba, sannan zan muku hanyar ganin likita acan Aminu kano ɗin, kuyi haƙuri da halin da ƴarku tace ciki In Sha Allaahu zata sami lafiya da yardar Allaah sedai kuma kaina ya kulle da wani abu, menene a jikin yarinyar nan kamar shedan belt wani mara imanin ne ya daketa haka”, shiru Iya da Mallam su kayi daga bisani kuma Iya ta faɗa ma Dr. Mubarak komi bata ɓoye masa ba.

Ba ƙaramin mamaki Dr Mubakar ya yi ba jin labarin Samha lalle wannan mijin nata ya cika marar imani da rashin tausayi amma Allaah ya fishi kuma yana tare da ita, sannan ze bi mata haƙƙinta, haƙuri ya dinga basu Mallam akan magangunun da suka faɗa musu wanda ba susan gaskiyar lamarin meke faruwa da Samha ba har suka yi musu faɗa cikin rashin sani.

“Babu komi komi ka gani yana da sanadi shi kuma da ya zalinceta yaje shi da Allaah”, cewar Iya,

Atare dukka suka miƙe suka fita zuwa ɗakin da Samha take, duddubata Dr ya yi tana nan yadda take babu inda yake motsi a jikinta sai zuciyarta da take harbawa fat fat, ga wani kalan hasle da ta ƙara fuskarta tayi shar da ita kamar sabuwar amarya, kusa da ita Iya taje ta zauna, Mallam ma bin bayanta ya yi ya zauna a gefen gadon ya kama hannayenta ya mata Addu’a sannan ya cema Iya “Ya kamata muje muyi sallah”, miƙewa Iya tayi tsam ba tare da tace dashi ƙala ba ta fice abinta saboda ita gaba ɗaya haushin Mallam ɗin take ji, komi ya faru tana ganin kamar sune sila.

Cikin zuciyarta kuma tana faɗin taya za’a yi ka ɗauki auren ƴarka ka bama mutumin da baka san daga inda ya fito ba a yadda duniyar nan ta zama sai hamdala kawai, sam wannan abu be mata daɗi ba.
Fita Mallam da Dr Mubarak su kayi suka jera zuwa masallaci, bayan sun gama sallolin da ake binsu sannan suka fito inda ake seda abinci,
Abinci mai rai da lafiya Dr Mubarak ya siya ma su Iya shima ya siya nashi sannan suka koma cikin asibityn, Iya suka tarar a ɗakin ta idar da sallaah tana lazami, Dr Mubarak ne ya ajiye mata abinci a kusa da ita haɗi da faɗin “Mama dan Allaah kici abincin nan, karki zauna da yunwa nasan kina cikin wani hali na rashin lafiyar Samha, kiyi haƙuri In Sha Allaahu zata sami lafiya kamar kowwa”, ya idashe maganar yana jinjina kai.

Itama Iya jingina kai tayi alamar gamsuwa cikin dashashiyar murya tace “In Sha Allaahu! na gode Allaah ya bar zumunci”,

*ABUJA*

Zaune yake awajen wani haɗeɗɗen wurin shaƙatawa, sanye yake da ƙananan kaya red & black, ƙafarshi sanye take da takalmi *merlians* kanshi ya ɗaura hula pacing cap idonshi sanye da baƙin glass hannunshi kuma sanye da agogo wanda kallonshi kawai kayi sau ɗaya zaka tabbatar da naira tayi kuka wajen siyanshi, wayarshi ya ɗauko ya kara a kunnenshi, babu ɓata lokaci mai kiran tace “Hello guy kana ina ne?”

“Au tambayata kike ina ina ne? to gani na iso ke nike jira”,

“to shikenan gani nan fitowa”, ta faɗa tana kashe wayar.

Sanye take da atamfa lemon green wacce tayi matuƙar da cewa da jikinta ta zauna mata sosai, ƙafarta sanye take da takalmi high hill sai jakarta dake maƙale a kafaɗarta, cikinsanɗa take saukowa daga stairs har ta gama saukowa, tafiya take a hankali har takai bakin ƙofar da zata sadata da waje, ta murɗa hannun ƙofar kenan zata fita Ammar dake saukowa daga stairs shima ya dakatar da ita ta hanyar faɗin “Ni’imatullah! ina za kije cikin wannan daren”, cak taja ta zatsa zuciyarta na matuƙar bugawa kamar zata fasa ƙirjinta ta fito hankalinta ya yi ƙolokuwar tashi, juyuwa tayi a hankali zuciyarta na bugawa sosai take kallonshi, rasa abinda za tace ne ya sata fara susan kai, ya yinda Ammar kuma ya kafeta da ido yana tambayarta, ganin tayi masa shiru ne yasa shi daka mata tsawa haɗi da faɗin “Dan Ubanki ba tambayarki ni keyi ba ina zaki da wannan daren kika min shiru ko ba kida baki ne?”, jikinta na rawa kamar mazari ta fara maganar kamar me koyar magana daga baya kuma ta fashe da kuka, jiki na rawa Ammar ya matsota haɗi da matseta a jikinshi gam! yasa hannu ya fara dukan bayanta a hankali yana hura mata iskar bakinshi a cikin kunnenta, lumshe ido tayi sosai tana shaƙar ƙamshin turarensa sai a sannan wata kalar nutsuwa tazo mata.
Cikin rashin kwarin gwiwa Ammar ya ɗagota haɗi da kallon fuskarta da idanuwanshi da su kayi ja suka rine kamar garwashin wuta, “ni ne ko?”, ya faɗa yana nuna kanshi ɗaga masa kai kawai tayi ba tare da tace dashi komi ba, tukum tace “Momi ce fa ta aikeni gidan Anty Rahina”, ta faɗa tana ƙoƙarin komawa jikinshi ta kwanta,
Cike da mamaki yake kallonta sannanya ɗago yace “Mmo da kanta ta aike ki gidan Anty Rahina da wannan daren muje na raka ki ko”, ya faɗa yana jefa idanunshi cikin nata, da sauri ta tsogunar da kanta ƙasa zuciyarta na bugawa da ƙarfi sosai kamar zata faɗo ƙasa”my soul ka barshi kawai ai kwana zanyi kuma ka ga dare ya yi, idan ka biyo dare kace zaka dawo gida yadda hanyar nan ta lalace ai kaga da akwai matsala kawai ka barshi idan Allaah ya kaimu gobe se kaje ka ɗaukoni daga nan kwa gaisa da itama”, jinjina kai Ammar ya yi, tabbas kuwa hanya ta lalace ya faɗa cikin zuciyarshi dan tabbas wajen haske be wadata ba, ga kuma ɓarayin hanya su na ƙasa ka abanza a wofi ba tare da sunji ɗar a ransu ba, “muje to na raka ki bakinta”, Ammar ya faɗa yana amsar jakarta.
Wani kalan daɗi ne ya ziyarceta lokaci ƙanƙani ta washe baki zuciyarta fes suka fita tare.

Raka ta ya yi har bakin titi ya tabbatar da ta hau motar unguwarsu Anty Rahina sannan ya juya zuwa gida zuciyarshi fal tunanin kala-kala, koh da ya shiga babban falo Ummi ya tarar zauna tana aiki a system ɗinta, waje ya samu kusa da ita ya zauna haɗi da kwantar da kafaɗarshi akan nata.
Ɗagowa Ummi tayi ta ajiye system ɗinta gefe guda sannan ta dubeshi cike da so da ƙaunar dake tsakaninsu tace “Ammar”, ɗago kanshi ya yi, ya kalleta ba tare da ya iya amsawa ba, saboda yasan idan Ummi zata masa magana mai muhinmanci ce take kiran sunanshi, Ummi bata damu da rashin amsawarshi ba, tasan ƴan mulkin ne suke kusa dan tun yana yaro har girmanshi babu wanda ze nuna mata karantar halinshi ta karanceshi tamkar yunwar cikinta wani lokacim yana da wuyar sha’ani ga wanda besan shi ba kuma sai ayita samun matsala,

“Ammar”, Ummi ta ƙara kiran sunanshi akaro na biyu, ganin be amsa mata ba, kuma baya da niyyar amsawa sai ma jinjina mata kai da ya yi alamar yana saurarenta yasa ta ci gaba da cewa.
“Ammar dama ina so in tambayeka ne, tunda ka dawo gida ka kira Baffanku na Kaltingo kun gaisa kuwa?”,
Gaban Ammar ne ya faɗi ras, tsakani ga Allaah ya manta ma ya yi rayuwa da wasu mutane a Kaltingo, shiru yayi kamar beji abinda Ummi tace ba har seda ta ƙara maimaita tambayar da ta masa, ras ya ƙarajin gabanshi ya faɗi, dafe kanshi ya yi da yaji dandanan ya fara masa ciwo sannan ya ɗago ya zuba ma Ummi ido tukum yace “Ummi na kirasu kusan kullum sai munyi waya dasu, yau ma da mu kayi waya dasu harda Kuka tace a gaisheku”, Ammar ya faɗa yana murmushin da iyakarshi ƙasan leɓe.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Ok to dan Allaah zuwa gobe idan ka kirasu ka bani waya mu gaisa sannan in musu godiya”, Ummi ta faɗa ita ma tana murmushi.

“To Ummi”, kawai ya iya cewa ya miƙe zumbur kamar an mintsineshi ya shige ɗakinshi dake ƙasa.
Itama Ummi miƙewa tayi ta sshige ɗaki saboda dama ta duba wasu abubuwa masu amfani ne kuma ta gama babu abinda zata tsaya yi kowwa yaje ya kwanta.
Kwanciya ya yi a saman katifa ya fra juye-juye sai yanzu ya tuna da Samha da kuma halin da ya barta ciki, “Mtsw”, ya buga tsaki yana zancen zuci, to ni meye ruwana da itama ta mutu mana babu abinda ya dameni da ita, ya koma ya kwanta.
Kusan minti talatin kenan da kwanciyarshi amma bacci yaƙi zuwa masa yasa ya miƙe haɗi da ɗauko jakar da ya dawo tafiya da ita, ciro kayan cikin jakar ya fara yi a hankali yana neman takardar da ya ajiye, ganin ya duba inda ya ajiyeta be ganta bane yasa ya zazzage kayan gaba ɗaya a ƙasa hankalinsa tashe ya fara dubawa,

_free page ya kusa ƙarewa, makaranta ku hanzarta biya ku karanta cikin kwanciyar hankali, akan farashi mai sauƙi nera ɗari biyu, masu buƙatar posting sau biyu a rana safe da dare kenan zaku turo ɗari huɗu, ko da kuɗinka sai da rabonka_

sai da ya bincike jakar nan zab be ganta ba, hankalinshi ba ƙaramin ƙara tashi ya yi ba, wayarshi ya zaro da ya barta tana caji ya kunna haɗi da dialing lambar Jalaluddeen.
Cikin bacci Jalaluddeeen yaji wayarshi na ringing ya ɗaukota cike da magagi ya karata a kunne yana faɗin “Hello wake magana”, ya faɗa haka saboda renin wayau dan yasan wayake kiran tsabar ya ƙular dashi ne,
“Kai dan Ubanka ka farka daga barcin da ka keyi shege kasa kawai tambayarka zanyi”,

“Ok ina jinka”, Jalaluddeen ya amsa masa a gajerce.

“Dan Allaah ka shiga ɗakin dana kwana ka duba min wata takarda ko na ajiye anan fara ce a cikin ambilon”,

“Gaskiya yanzu na kwanta sedai ka bari zuwa safiya in Allaah ya kaimu”, cewar Jalaluddeen ya zare wayar a kunnenshi ya kasheta gaba ɗaya.

Ammar yana ta magana jin ba’a amsa masa bane yasa ya zare wayar a kunnenshi haɗi da kallon fuskar wayar,ganin an datse kiran ne yasa ya ƙara kira, jin wayar a kashe take yasa ya buga tsaki ya koma ya kwanta be gyara kayan ba.

seda ta ɗanyi nisa da gida sannan ta lalubo wayarta dake cikin jaka ta kira Salim,
Salim dake zaune ya haɗa rai sosai ƙarasowar Ni’imatullah kawai yake ya sauke mata ruwan bala’i amma ganin kiranta kawai ya sagar masa da gwiwa ya ɗauka jiki na rawa, “Hello S boy ina hanya kazo ka ɗaukeni”,

“Amma baby tun ɗazu fa nike jiranki anan shiru sai yanzu zaki ce dani kina hanya nazo na ɗaukeki? ba komi gani nan ƙarasowa ai bakya lefi”,

“A’a S boy ba zaka gane bane, wannan shegen yaron ne ya dawo wanda nike baka labari ɗinnan shiyasa nayi dare da yawa kuma ya kama ni hannu biyu, kai badan na yi masa ƙarya da Momi ce ta aikeni da ya kake gani?”,

“no baby kibar zancen wannan yaron tunda ina kusa gani nan zuwa kina dai-dai ina ne?”,

“an gama S boy ina mararraba”,

“to ki tsaya dai-dai nan gani nan zuwa”, ya faɗa yana shigewa mota dan dama a tsaye yake yana ɗauka ta iso ne yazo ya shiga da ita baya so ya shiga shi kaɗai gashi kowwa ya halarta su kawai ake jira a fara farti ɗin.

ba wata tafiya mai nisa S boy ya yi ba ya ƙaraso mararraba inda Ni’imatullah take, tsayar da motar ya yi ta shiga ba tare da yace da ita komi ba yaja motar, itama ba tace dashi komi ba haka su kayi zaman kurame har kusa isa babban hall ɗin, fitowa Ni’imatullah tayi ta shiga ɗaki na musanman ita da S boy suka canza kaya zuwa wasu ƴan iskan kaya, nima bangani ba seda aka gama shirya Ni’imatullah!.
Sanye take ta rigar net light blue kana iya hango bra da long trouser ɗin da ta sanya wanda dashi gara babu saboda kana hango komi na jikinta, kanta ya sha gyara har ya gaji an ɗaireshi da maɗauri fari sai baƙin tabarau dake matsakaicin idonta wanda ya zauna ya yi ɗas dashi, ƙafarta sanye da farin takalmi mai igiyoyi, fuskarta tasha kwalliya kamar wata sarauniyar kyau, ba ƙaramin haɗu Ni’imatullah tayi ba,

Ana gama mata kwalliya aka fito da ita, S boy ne ya kama hannunta na dama ya sarƙe cikin nashi sannan ya ɗauki hannunshi ya sagale a kafaɗarshi a haka suka dunfari ɗakin taron.

Tun daga nesa idan ka ɗaga ido ka kalli wajen zaka tabbatar da dukiya tayi kuka sosai, a jikin glass ɗin ɗakin kasancewar wajen na ƴaƴan masu kuɗi ne yasa akayi amfani da glass anyi rubutu da manyan baƙi inda aka rubuta *HAPPY BORN DAY S BOY* daga gefe guda kuma ga wasu flowers masu kyan gaske, tsayawa faɗar haɗuwar wajen ɓata lokaci ne haka suka shiga cikin ɗakin taron.

Gaba ɗaya mutanen dake wajen suka miƙe tsaye suna tafa hannu saboda Ni’imatullah da S boy baƙaramin bada kala su kayi ba, bayan wajen ya yi shiru ne suka gudanar da abinda ya kawosu aka yanka cake suka yi raye-rayensu sannan suka shige ɗakuna,
ganin S boy zeja Ni’imatullah ɗakin da yafi kowwane haɗuwa ne yasa ta kalleshi, ido ya kaɗa mata alamun “E”, saboda a bige yake baze iya magana ba, girgiza masa kai tayi tana sonyi masa turjiya amma sai ya matseta gam a ƙirjinshi har ta kasa wani motsin kirki, tana ji tana gani S boy ya jata ɗakin ya mai da ƙofa ya rufe.

*GOMBE STATE*

_SATURDAY ASHIRIN DA ƊAYA GA WATAN OGUSTA SHEKARAR DUBU ƊAYA DA ASHIRIN DA ƊAYA DA MISALAN KARFE BIYAR DA RABI NA ASUBA_

Shiri sosai Mallam da Iya su kayi na tafiya da Samha asibityn *MALLAM AMINU KANO* Dr Mubarak ne ya ɗauko Samha cak a kafaɗarshi ya sanyata a motarshi gidan baya, sannan ya umarci Iya da ta shiga gidan baya kusa da Samha sannan shima ya shiga ya zauna mazaunin direba tukum Mallam ya shiga ya zauna a gaba, seda su kayi Addu’o’in kariya daga sharrin ƙarfe kamar haka,
_ADDU’AR
NEMAN TSARI DAGA
SHARRIN ABIN HAWA:.
bismillahi majraha wa
mursaha inna rabbi la
gafurum rahim_

Tukum Dr Mubarak ya kira Dr *JALALUDDEEN SHUWA* Dr Jalaluddeen na cikin shirin zuwa asibity cikin shigar fararan kaya yaji wayarsa na kuwwar neman temako, dakatawa ya yi ya ɗauki wayar haɗi da karata a kunne,

“Assalamu Alaikum likita bokan turai barka da war haka”, cewar Dr Mubarak,

“Wa’alaikas-salam barkan mu, ranka shi daɗe”,

“Na’am tare dakai In Sha Allaahu, kana magana da Dr Mubarak Anas Gombe”, cewar Dr Mubarak.

murmushi Dr Jalaluddeen Shuwa ya yi wanda ya ƙara fito da ainihin kyanshi cikin zuciyarshi yake ayyana ko zai manta da kanshi bazai manya da mutane biyu masu karamci da muhimmanci a rayuwarshi ba, Dr Mubarak Anas Gombe, tare da Engineer Ammar Tanim Bature, burun ya yi yaƙi cewa komi yana faɗaɗa murmushin shi har seda Dr Mubarak Anas Gombe ya kaɗa baki yace masa kana jina,

“Yes ina kan layi kana magana da Dr Jalaludeen Shuwa”,…………

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]