FULANIN TASHI CHAPTER 12

ƙara dunfaroshi tayi aikuwa ya kawo mata duka, kaucewa tayi tana fasa ƙara wanda ya yi dai-dai da shigowarsu Daddy da Abu, tsayawa suka yi suna kallom abinda ke faruwa yadda Ammar ya haukace akan maganar auren Ni’imatullah,
“Ammar”, Daddy ya kira sunanshi, gaba ɗayansu da suke tsaye curko-curko suka wai ga saboda tunda suke da Daddy basu taɓa ji ya kira sunan Ammar kai tsaye ba,
Da sauri Ammar ya taho wajen Daddy ya durƙusa a ƙasa ya kama hannayenshi, kwantar masa da hankali Daddy ya dungayi akan maganar auren, babu gudu babu ja da baya za’ayi auren dai-dai lokacin da aka sanya bikin, sannan ya shirya duk abubuwan da zeyyi na shagulgula maganar akwati kuɓa ya barshi dan Daddy dama tuni ya yi maganar akwatin za’a aiko dashi a haɗe.
Sosai Ammar ya ji daɗin maganganun Daddy har sai da ya rumgumeshi, Ammi da Ummi kuwa dukkansu wucewa ɗaki su kayi, Amra ma ɗaki ta wuce, mtsw taja tsaki saboda haushin kanta da taji akan ƙoƙarin lallashin shi da tayi, miƙewa Ammar ya yi yabi Ummi ɗaki aikuwa tana ganinshi ta miƙe tsaye haɗi da shigewa bedroom ta saka key ta koma ta kwanta zuciyarta bata mata daɗi sam! jiki a sanyaye Ammar ya fita daga ɗakin Ummi ya nufi ɗakin Ammi.
Zaune ya taddata tayi tagumi da hannu biyu, fuskarta babu alamar walwala sai hawaye dake biyowa yana saukowa samun fuskarta, sosai hawaye suke zuba kamar famfo wani na bin wanu, daka tsalle Ammar ya yi ya isa gareta, durƙusawa ya yi akan gwiwuwinshi zai fara magana kenan Ammi ta saka ƙafa ta shureshi, nuna shi da yatsa rayi haɗu da faɗin “Wallahi Ammar ka sale ka ƙara raɓar inda nike ban yafe maka ba duniya da lahira, sannan daga yau magana dakai ta haramta a tsakaninmu kai na yanke duk wata alaƙar dake tsakaninmy dakai ba ni ba kai, kayi gagawar tashi kabar min part kafin nayi matuƙar saɓa maka”, Ammi ta faɗa tana miƙewa tsaye ta shige bedrom tabar shi a wajen azaune.
ba tare da wata nadama ba Ammar ya miƙe tsaye ya wucewar shi,
Ammi dake kallonshi ta taga, ganin ya miƙe ba tare da wata nadama ba yasa ta ƙara fashewa da kuka, lalle Ammar ta faɗa tana share hawayenta a fili tana furta daga yau ba zata ƙara shiga shirginshi ba, sannan zata manta dashi kamar matattace, mataccen ma mara galihu.
Ƙarƙashin zuciyarta kuwa ba haka bane ba,

Hajiya Babba kuwa, kallon Daddy tayi tukum tace “Wallahi Jibril idan ka ƙulla auren nan Allaah ya isa ɗawainiyar da nayi dakai, ta faɗa tana miƙewa ita ma ta haye sama, dai-dai lokacin da Hajiya Babba tayi maganar Ammar ya sauko da sauri yabi bayanta ya fara roƙonta, sandar dake hannunta ta ɗaga ta buga masa a tsakiyar kai, wani kalan ƙara ya saki ya ɗago idanunshi da su kayi matuƙar rinewa ya kalleta zuciyarshi na masa zafi kamar zata faso ƙirjinshi ta fito.

Dafe kanshi da yake matuƙar juya masa ya yi, saukiwa daga stairs ya fara yi yana tafe yana tangal-tangal kamar ze kife, yana taka step ɗin ƙarshe ƙafarshi ta goce saboda duhun da yaga ya dabaibayeshi ya faɗi ƙasa babu numfashi a tartare dashi, Daddy da ya yi ƙoƙarin tareshi be samu damar hakan ba saboda suna da ɗan tazara cikin zafin nama ya isa gareshi ya rumgume, abunka da manyan sojoji idonshi ya fara rinewa zuwa jajawur kamar an zuba masa borkono, kallon Abu ya yi da yake ƙoƙarin wucewa cike da halin fulani wato kunya kasancewar Amnar ɗa na fari awajenshi, “Tanim”, Daddy ya kira sunan Abu.
Cak Abu ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba, saboda ba ƙaramin mamaki ya yi ba jin rana ɗaya tal Daddy ya kira sunanshi da Tanim, dan tun tasowarsu be taɓa jin Daddy ya kira sunanshi kai tsaye ba sau yau,
Daddy da ya ƙufala sosai ganin Abu be juyo ba ya ƙara kiransa “Tanim”,
Juyawa Abu ya yi mamaki kwance a fuskarshi yace “Ina jinka Ranka shi daɗe”, cikin rashin gwarin gwiwa Daddy yace “ba ka ganin halin da ɗana ya shiga ciki, ka taimaka min ka fitar da mota muje zuwa asibity,” Daddy ya yi maganar idonshi yana kan Abu.
Ɗan murmushi Abu ya yi, tukum yace bari dai in taimaka maka ka fitar dashi waje ku tafi, amma ni bazan bika zuwa asibity ba,” sallamar da Ahmad ya yi ne ta dakatar da Daddy daga magabar da yake ƙoƙarin yi,
Ahmad na ganin halin da Ammar ganin halin da Ammar yake ciki, cikin rawar jiki ya ƙaraso wajenshi haɗi da faea jijjigashi, Daddy ne ya ɗago ido yace Ahmad ka mata ya yi ka temaka a sanyashi a mota zuwa asibity ba jijjigashi ba,
Ahmad kuwa sabo da ruɗu bai bi takan abinda Daddy yake faɗa masa ba, sai ma wurga ido da ya keyi, idonshi ne ya kai kan fridge ɗin dake falon aikuwa cikin azama ya nufeshi, bulewa ya yi cike da zafin nama ya ɗauko ruwa mai sanyi yazo ya durƙusa ya juyema Ammar, ko gizau Ammar be yi ba, ba tare da gajiyawa ba Ahmad ya ƙara ɗauko goran ruwa ya juye masa, seda ya juye masa gora uku kafin Ammar ya sauke nannayar ajiyar zuciya.
sai yanzu Daddy ya farga da ashe akwai fridge a falon, ya ma manta shaf saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki,
a tare dukkansu suka furta “Alhamdulil Lah”, saboda ganin Ammar da su kayi ya miƙe da ƙarfi haɗi da ƙwalla ma Ammi kira, riƙeshi Daddy ya yi ya koma ya kwantar dashi akan kujera 3seater, ƙara yinƙurowa Ammar ya yi zai tashi Daddy ya ƙara kwantar dashi,
Ahmad kuwa zuba masa ido ya yi tamkar yau ya fara ganinshi, cike da tausayin ɗan uwan nashi bakinshi har rawa ya ke wajen tambayar Daddy me ye faru, Daddy be ɓoye masa komi ba ya faɗa masa duk abinda ke damun Ammar ɗin da kuma abinda ya faru yau da safe har zuwa wannan lokacin.
jinjina kai Ahmad ya yi sosai cikin zuciyarshi ya yi na’am da zancenta da lalle akwai abinda ke faruwa, jiya an tashi meeting akan Ammar beson aure yanzu, yau kuma antashi Ammar ya tubure yace sai Ni’imatullah, girgiza kai kawai Ahmad ya yi haɗi da tambayar Daddy ina Ammi.
nuna masa hanyar da zata sadashi da part ɗin Ammi ya yi, saboda beson magana ma sosai kuma ga dukkan alamu Sojojin ne aka yau,Ahmad kuwa hanyar part ɗin Ammi ya nufa da zummar ya bata haƙuri amma sai yaci karo da Abu a tsaye ya naɗe hannayenshi, nufar Abu Ahmad ya yi yana zuwa ya durƙusa a gabansa yanayinshi gaba ɗaya ya ƙara sauyawa zuwa zallar baƙin ciki.
ɗagowa ya yi ya kalli Abu tukum ya fara magana cikin rashin kuzari “Abu” Ahmad ya kira sunan Abu.
jijjiga kai kawai Abu ya iya yi saboda bazai iya magana ba, shima sai yanzu ya kula da ciwon dake goshin Ammar in dan kwata-kwata be bi takanshi ba, saboda ya ga Daddy na wajenshi be kamata ace shi yaje ba, ɗan uwa yafi gaban wasa.
haba Abu yanzu kana kallon halin da Ya Ammar yake ciki ba zaka taimaka masa ba, Abu ina soyayyar da kake masa taje? dan Allaah Abu kayi ƙoƙari ka cika masa burinsa, kar ka sanya hannu wajen durƙushe rayuwar ɗanka, ba tare da Ahmad ya jira cewar ta Abu ba, ya wuce zuwa part ɗin Ammi, buga ƙofar ya yi ya jita a datse, Ammi dake kwance tana rizgar kuka saboda taga sanda Ammar ɗin ya faɗi kuma duk abinda ya faruwa tana gani amma tayi Alƙaqari Ammar ko mutuwa zeyi ba zata taɓa zuwa wajenshi ba,

Ahmad ya daɗe yana bugun ƙofar ɗakin Ammi ba’a buɗe ba tukum ya haƙura ya tafi part ɗin Ummi, bugawa ya yi sai gashi tazo ta buɗe kamar jira ta keyi,
kallonta Ahmad ya yi zuciyarsa ba ta masa daɗi, a hankali ya tako inda take tsaye kanar ab dasa ta, tukum ya kama hannunta ya shiga da ita ɗakin.

 

“`dan Allaah kuyi haƙuri kwana biyu bakwa samu sosai wallahi bana zama ne wannan ma a gaggauce nayi shi“`

About Ismail

Check Also

KHAIREEYAH CHAPTER 15

Yau neh ranar da Khairiyya zata shiga Jami’a, Ita da kanta ta tashi batare da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *