FULANIN TASHI CHAPTER 11

cikin asibityn suka shiga basu tsaya ko ina ba sai ɗakin da Samha take, sallama su kayi Dr. Mubarak dake zaune ya tasa jarida a gaba yana karantawa ya ɗago ya kallesu, da sauri ya miƙe haɗi da ajiye jaridar a sama tebur ya taho ya rumgume Dr. Jalaluddeen saka ya sakeshi ya rumgume Mallam tukum ya waiwayo ga Iya ita ma ya rumgumeta haɗi da sakin tikum ya kaiga ƙasa ya gaishesu.
Amsawa Iya tayi cike da so da ƙaunarshi ta ɗagoshi fuskarta ɗauke da fara’a tana faɗin “shine sai da ka wani duƙa kuma”,

“E Iya aikin cancanci fiye da hakan ma, in ana kwanciya ma mutum to tabbaskin cancanci a kwanta miki, fatana da burina bai wuce inga na kyautata muku”,
sosai Iya taji daɗin maganar Mubarak, jinjina kai tayi alamar gamsuwa sannan Mubarak ya saketa ya koma ga Mallam ya rumgumeshi tukum yaje ga Dr. Jalaluddeen shuwa.
Rumgumeshi ya yi yana faɗin”ɗan uwa na gode da wannan karamcin da ka mani Allah ya saka da Alkhairy ya biyaka da gidan duniya dana lahira ya kuma ƙara kaifin basira ya yin aiki.”

Girgiza shi Dr. Jalaluddeen shuwa ya yi yana faɗin “kai dallah Mallam bansan bariki, sakeni inje in duba patient ɗina kabi ka wani kanainaye mutum kamar wata mage”,sosai maganar Dr.Jalaluddeen Shuwa ta bama su Iya dariya aikuwa suka dinga darawa sannan suka ɗumguma zuwa wajen da Samha take kwance, duddubata Dr. Jalaluddeen kenan kana ya kalli Dr. Mubarak yace “Au shine baka saka mata wani drip ɗin ba?”.
“A’a ranka shi daɗe patient ɗinka ce, sannan in kuna kusa ai mu yara ne a harkar kaga ni tafiya ma zanyi inje in huta saboda duk daren jiya banyi bacci ba ina aikin dubata”, Dr. Mubarak ya faɗa yana ƙoƙarin saka kai ya tafi.
“Ok toh sai Allaah ya kaimu an jima, in kaje gidan akwai komi na buƙata ba sai ka girka ba ko Maɓa?”, ya faɗa yana kallon Iya da alamar tambaya.
Ɗaga maaa kai Iya tayi saboda ta kasa furta komi, ji take kamar a mafarki idan aka kira ta da Mama, lalle Dr. Mubarak Anas Gombe, da Dr. Jalaluddeen Shuwa suna cikin mutanen da ba zata iya mantawa dasu ba komi tsawon rayuwarta.

Bayan Dr. Mubarak ya tafi ne suka ɗan taɓa hira kaɗan sannan suka fito wajen asibityn suka zauna dan Dr. Jalaluddeen yace su barta haka nan ba’a son masu lalura irin ta ta suna jun hayaniya, kwakwalwarta tayi sanyi da yawa tana buƙatar hutu sosai.

*ABUJA*
Gudu sosai take zabgawa a saman titin da babu wata halitta sai kuka tsuntsaye da ka keji jefi-jefi, sosai take gudun fitar hankali cikin ƙanƙanin lokaci ta ɗauke hanyar tafa, Ni’imatullah dake kusa da itace tayi saurin kallonta haɗi da faɗin “Momi ina zamu ne muka ɗauke hanya haka harfa mun fita daga cikin garin ma gaba ɗaya”,
Kallon banza Momi ta watsa ma Ni’imatullah, haɗi da faɗin “idan baki zuwa ki fita ki bani wuri sha sha sha kawai”, tsit Ni’imatullah tayi har suka shiga cikin garin tafa sannan suka ɗauke hanyar wani jeje.
Ba suyi wata tafiya mai nasa ba, sai gashi sun kawo wani ƙaton gida, parking Momi tayi tukum ta kira sunan Ni’imatullah, ɗago ido Ni’iɓmatullah tagi cike da tsoro ta amsa, hannunta Momi taja tana faɗin “ki nutsu kar kiyi wani kwakwaran motsi sannan zan ruƙe miki hannu tare zamu tashi zuwa cikin gidan,” cikin bin umarnin abinda Momi ta faɗa Ni’imatullah ta riƙsma Momi hannu gam! wasu suruitai Momi tayisai gashi sun ɓace ɓat kamar an yi ruwa an ɗauke.

babban ɗakin taro ne wanda ya ƙawatu yaji kayan alatu da kyale-kyale, zaune suke suna tattauna wasu muhimman abubuwa sai ga Momi ta duro daga sama, sannan Ni’imatullah itama ta duro kamar an jehuta, gaba ɗaya jama’ar dake ɗakin miƙewa su kayi suka dinƙule hannu alamar jinjina tukum suka koma suka zauna.
Father dale zaune akan wata kujerar ƙarfe ya ɗago ya kalli Momi cikin faɗa-faɗa ya fara mata magana.
Momi bata tanka masa ba ta nemi waje ta zauna tukum ta zaubar da Ni’imatullah kusa da ita, “meke tafe dake”, faza ya faɗa idonshi na kanta.

Numfasawa Momi tayi tukum tace “Maganar dai da mu kayi da kaine ta waya Hajiya Babba ni keso a kashe sannan a baiwa dodanni jinin su shanye kyauta”,

da sauri Fada ya kalleta cikin zuciyarshi yana tunanin anya zasu iya kashe Hajiya Babba, saboda lokacin da Momi ta shiga ƙungiya ba Ibrahim mijinta ta basu ba Hajiya Babba ta bada amma sun kasa kasheta dole cikin ɗaya zata zaɓa Ni’imatullah ko Ibrahim mijinta, shiyasa ta bada Ibrahim kawai aka zuƙe jininshi.
Gyara zama da kyau Fada ya yi tukum yace “Naji ƙudirinki akan Hajiya Babba, bakya ganin idan aka samu matsala mai ze biyo baya? dole sai dai ki zaɓa ko ke, ko Ni’imatullah”,
Ɗagowa Momi tayi da sauri cikin zuciyarta tana faɗin ko ni, ko Ni’imatulla, lalle akwai jarfa kenan, amma a fili kuwa cewa tayi “Gaskiya Fada za canza wata shawarar ama ba wannan ba, dan bazan iya bada kaina ko Ni’imatullah ba, ita kaɗai ta ragemim da da wasu yaran ne da sai na bada amma ina son Ni’imatullah”, Momi ta idashe maganar da alamun gajiya tartare da ita.
shiru wajen ya ɗauka na wasu lokuta tukum Fada yace “To shikenan, zaki bada Baban mijinki?”,
Da sauri Momi ta ɗago ido ta kalli Fada, Ni’imatullah ma haka, saboda gara a bada Hajiya Babba da a bada Kaka.
Amma bari taji abinda Momi za tace,
Seda Moɓi ta kalli yanayin Ni’imatullah, sannan ta ɗago ta cema Fada, “Na amince ba ɗauki Alhaji Salihu”, ta faɗa murmushi kwance a saman fuskarta.
Da sauri Ni’imatullah ta ɗago ta kalli Momi bakinta har rawa ya keyi tana faɗin “Momi dan girman Allaah kiyi haƙuri indai a kaina za’a kashe Kaka ki barshi kawai mu canza wani wajen,” ta faɗa hannayenta haɗe alamar haƙuri.

Daka mata tsawa Fada ya yi yace “Dan Ubanki ba a magana biyu anan, dan haka ki shiga taitayinki kuma ki hankalta dan ba’a magana biyu.”
Daradaran idonta ta ɗago ta zuba ma Fada sannan tace “Ni nace na yafe a barshi”, kafin ta idashe maganar Momi ta watsa mata wasu tagwayen maruka, dafe ƙuncinta tayi tukum ta nu nata da yatsa, “ki shiga taitayinki Ni’imatullah, ba’a ma Fada musu sannan ba’a magana biyu anan, abinda na faɗa sji za a aiwatar kuma wallahi ko ba yau ba, ba gobe ba naji wamnan ɓaganar ta fito waje sai nayi matuƙar saɓa miki, idan baki sani ba ki sani yau”, Momi ta idashe maganar tana miƙewa haɗi da ɗaukar jakarta bata ko tsaya sinyi sallama da Fada ba juya a fusace ta wuce, ita ma Ni’imatullah miƙewa tayi ta fice a wajen,
gaba ɗaya mutanen dake ɗakin suka hautsine da surutu kowwa na faɗin abinda ke bakinshi,
seda Momi ta jira Ni’imatullah a daidai inda suke ɓacewa, tana zuwa kusa da ita ta kama hannunta ba tare da ta mata magana ba suka ɓace ɓat.

Washe gari da sassafe Ammar ya shiga part ɗin Ummi, zaune ya taddata da Al-ƙur’ani mai girma tana karantawa, har ya zauna da niyyar jiranta ta gama dan magana yazo suyi amma sai Ummi tayi masa alama da hannu akan ya ɗauko Alƙur’ani su karanta tare. ɗaukowa ya yi yazo ta zauna kusa da Ummi suka fara karantawa tare har suka gama tukum su kayi Addu’a suka shafa a tare, ɗagowa tayi ra kalleshi cike da tausayin yadda ya koma cikin kwana biyu kacal kawai tace mishi “Son ina jinka, naji kayi shiru”, dabur-dabur Ammar ya fara, dan shi yama manta da maganar da yazo ya faɗa mata amma bari ya yi mata maganar Ni’imatullah, cike da kwarin gwiwa yace “Momi dama akan maganar Ni’imatullah ne, dan Allaah kiyi ma Daddy magana na amince, wallahi Momi ina son Ni’imatullah tamkar raina dan girman Allaah ku lallashi Hajiya Babba ina sonta ina son aurenta”,
Da sauri Ummi ta ɗago tanakallon Ammar, yau shi yake faɗa mata yana somɗn Ni’imatullah da kanshi kafin Ummi tayi wata magana Ammar ya riƙe hannunta dukka yana ƙara roƙonta, shi idan be auri Ni’imatullah ba mutuwa zeyi, ya ya zeyyi da rayuwarshi duk duniya yafi ƙaunar Ni’imatullah fiye da komi da kowwa.
Ammi ce da shigowarta ɗakim kenan cikin shirin zuwa aiki, ta dakata da tafiyar ta ta keyi ta tsaya tana jin maganganunshi, jinjina kai tayi cike da ɓacin rai ta juya za ta wuce ta jiyoshi yana cewa, Ummi dan girman Allaah ki roƙi Daddy inda hali ma a sauko da bikin, ina sonta, wallahi tallahi Ummi ko Ammi bata isa ta hana a ɗaura min aurw da Ni’imatullah ba, balle Hajiya Babba, ki faɗa ma Hajiya Babba ni na turoki wajenta saƙo na bada a bata ki mutuwa za tayi sai na auri Ni’imatullah ita ɗin banza da wofi,
Da wani kalan zafin nama Ammi ta taho ta tsinkama Ammar wasu maruka guda ukku, tafe ƙuncinshi ya yi ya ɗago a razane yana kallonta, gani yake kamar ba Ammi bace a gabanshi kuma har ta mareshi, shafa inda ta mareshi ya yi kana ya buɗe idonshi dukka akanta, Ammi ce dai, ita ta mareshi amma hakan bazai sa ya gajiya ba, cike da kwarin gwiwa yace “Ammi dan Allaah ki temaka min na auri Ni’imatullah…..” kafin ya idashe maganar da yake yi Ammi ta ƙara masa wasu marukan, cikin zallar baƙin cikin daya dabaibayeta ya mata ɗaurin goro Ammi tace “wallahi! tallahi thumma tallahi game da zancen auren Ni’imatullah dakai, in dai ka aureta Allaah ya isa Nono na daka sha, Allaah ya isa ɗawainiyar cikin da nayi da kai, Allaah ya isa ɗawainiyar daka sanyani cikin halin ciwo ko lafiya sannan zaka gani”, Ammi ta faɗa tana yarfa hannunta tukum taja hannun Ummi suka fice daga ɗakin,
Da sauri Ammar yabi bayansu shima ba tare da nadamar ko da second ɗaya bane ya bisu falo inda dukka illahirin jama’ar gidan ke zaune.
Cikin ƙonar zuciya Ammi ta ɗaga kai ta kalleshi haɗi da faɗin “ubanwa ka kebi”, ta huwa ya dingayi ba tare da ya saurare abinda Ammi take faɗi ba zai fara magana kenan Ammi ta waiga da niyyar ɗauka abin jifa bata samu ba, idonta ne ya faɗa akan takalmin Amra mai shegen tsini, ɗauka tayi ba tare da ta saurari abinda Ummi ke cewa ba ta jefeshi dashi aikuwa tace babbar sa’ar samunshi a goshi, cakan goshin shi takalmin ya yi dandanan goshin nashi ya fashe ba’a jima ba sai ga jini ya fara zuba sosai, dafe wajen Ammar ya yi ba tare da ya kula da jinin dake zuba masa ba ya yi wajen Hajiya Babba dake saboda taji hayaniyar dake tashi, beko bari ta sauko ba yaje wajen stairs ɗinbya tsoguna, tana idashe saukowa ya duƙursa ƙasa kamar zai tsala ihu ya fara roƙonta akan ta temaka ta sanya baki akan maganar aurenshi da Ni’imatullah. baki sake Hajiya Babba take kallon Ammar cike da Al’ajabi take tafa hannu, leƙa fuskarshi tayi da kyau tana so ta tabbatar da shine ɗin ki bashi bane, buɗe dadaran idanuwanta tayi tana kallonshi kana ta ƙara tafa hannu ta fara sababi itama, jama’a na shiga uku mai zan gani da sassafen nan, mi nike gani haka Ammarul-Islam kaine kuwa,

“Wallahi nine Hajiya Babba abinda kawai zaki mim in tabbatar da kina ƙaunata shine ki temaka ki roƙi Ammi da Ummi su yafe min ayi auren nan, wallahi ina son Ni’imatullah, ina mata soyayyar da bana yima wani mahaluƙi kalarta, Hajiya Babba kince kina sona ina so in tabbatar da soyayyar da kike min, idan har baki amince da auren nan ba wallahi zan iya haukacewa in kashe kaina kowwa ya huta”, sosai Ammar yake wasu kalan maganganu kamar taɓaɓɓe, Hajiya Babba duk tsiwarta ta kasa ceea komi sai uban kallonshi ta keyi kamar yau ta fara ganinshi Al’ajabi ne ya da baibayeta ya hana mata sukuni har sai da ta kalli Amra dake tsogune tana kuka saboda tausayin yayanta, da kuma jinin da taga yana zuba goshin shi gashi yaƙi bari a taɓashi balle a wanke masa, data matso kusa da shi zai matsa gefe yana faɗin ta kyaleshi ko ya hallakata.

About Ismail

Check Also

KHAIREEYAH CHAPTER 15

Yau neh ranar da Khairiyya zata shiga Jami’a, Ita da kanta ta tashi batare da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *