[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 17 - Bankinhausanovels
Wed. Nov 30th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kaka yace eh nasan komai sabreen, mamminkine tace karna gaya miki ita zata gaya miki da kanta shiyasa nayi shuru😰. Sabreen tace to kaka amma dukda kasan hakan shine kabarta tazo guna akan me zatazo guna bayan ita da iyayentane nasadiyar kasancewata marainiya, juyawa tayi afusa ta sake hankad’a salma tana cewa kibar gidannan banason ganinki kuma bana buk’atan jin sauran bayaninki kawai ki fita a gidannan karki sake zuwa inda muke adalilinki mahaifina ya sadaukar da ransa😭, salma ma kuka takeyi tace kiyi hakuri sabreen ki saurareni, sabreen tace bana buk’atan jin komai kawai ki fita nace😰, salma tace haba sabreen nasan dama hakan zai faru amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe mana hakan shiyasa nad’au alk’awarin taimakonki kota wani hanyane dan ki yafe mana, sabreen shiyasa na saudaukar da budurcina dan in taimakeki a hannun wannan MUTANE UKUN a tunanina hakan zaisa ki yafemin sabreen dan Allah😰. Murmushin takaici sabreen tayi tace kina nufin zan yafe mikine, to ai shi mahaifina RANSA ya baki saboda da haka ban yafeba kuma kibar gidannan salma😭. Shi kaka dayake yasan wacece salma da sauri yaje ya janyo sabreen yana cewa haba sabreen kefa musulmace bai kamata ki dinga fad’an hakanba mahaifinki kwanansane ya kare koda hakan bai faruba to a wannan ranan zai mutu. Da sauri sabreen ta cewa kaka da bazai mutuba kaka ka dena bin bayanta nidai ban yafeba salma kibar gidannan😭, kaka yace salma yi hakuri kije karki damu zata yafe muku dama bakuyi komaiba jeki kinji mun gode sosai banaso ‘yan gidan su dawo suji me muke ciki. Kuka sosai salma takeyi sannan ta tafi tana fita daga wajen gate d’insu seta b’ace.
Kuka sosai sabreen takeyi kaka yana ta rarrashinta tana cewa wayyo Abbana wayyo mammaina Allah ya jik’anku da rahama😭. Kuka tayi mai isarta sannan tayi shuru ta wuce d’akinta tanata tunanin abin a ranta, toilet ta shiga ta wanke fiskanta sannan ta fito zataje kichin ta d’aura abinci dare, wayartace ta fara kara ta duba taga yah kamal ne, ta dauka tare da cewa hello, kamal yace hello sabreen ina fata dai kin dena kukan yanzu? Murmushin karfin hali tayi tace EH nadena, yace to shikenan mun fitane dukkanmu hardasu mum amma zuwa anju kafin magrib zamu dawo kinji, to yah kamal sekun dawo nagode, yace sabreen kawar naki ta tafine? Eh tafi😠, ko to shikenan semun dawo, toh sannan ta katse wayar.
Itadai bats ganewa yah kamal ba alamu dai ya Nuna sonta yakeyi, kuma gaskya yah kamal mutum ne nagari Wanda ko wace mace zatayi fatan samu a rayuwarta. Yana da kyawawan halaiya ga nutsuwa da Sanin darajan mutane, bugu da k’ari kyakkyawane shi sosai Dan yafi SUHAIL kyau gaskya, kawai dai shi SUHAIL farine tas kamar balarabe, shi kuwa kamal bak’ine sannan yana da saje mai kyau Wanda shi suhail Sam bayi da saje se gashin kai mai laushi. Kunsan kuma farin mutum da d’auke ido da kuma d’aukan hankalin ‘yan mata gashi sun iya dressing sosai da iya d’aukan kamshi😘 kuma suhail yafi kamal tsayi sannan suhail baida yawan dariya kamar kamal, wannan shine bambancinsu. Sabreen tanata tunani a zuciyarta tana had’a abinci har ta gama tuwo miyan kuka yaji DRY FISH. 6:20pm su mum suka dawo gida lokacin sabreen tana kwance a d’akinta, mikewa tayi dan taji dawowarsu ta karasa Palo tace HAJIYA sannuku da dawowa, mum tace yawwa sabreen sannunki da gida ya fama da aiki, sabreetayi😊 tace alhamdulillah sannan tace ya kamal yah suhail sannunku da dawowa, sukai mata 😊sukace yawwa sannu da aiki, ta kalli HAFSAT sukaiwa juna murmushi tace sannu da dawowa, HAFSAT tace yawwa sannu sanna itama ta shige d’aki. Suhail yace muyi alwala ko semu wuce masallaci, kamal yace to Kaje ina zuwa sannan suhail ya wuce ya barsu a tsaya, sabreen ta juya zata koma d’aki se kamal yace sabreen inasonyin magana dake, sabreen ta juyo tana kallonsa tace toh yah kamal ina sauraronka, daga Inda yake tsaye yace baridai muyi sallan magrib tukunna kinji, tace to badamuwa, murmushi yayi mata sannan ya wuce d’akin suhail ita kuwa tanata binshi da kallo harya shige sannan tayi ajiyar zuciya ta wuce d’akinta.
Bayan sun dawo daga masallacine suhail yace toni bari in ciga ciki seka shigo, OK kamal yace dashi sannan ya kira sabreen a waya yace mata yana tsakar gida acikin mota, tace to ina zuwa shi kuwa ya shige mota ya zauna yana jiran fitowarta. Saida ta sake fesa turare sannan ta fito bakowa a Palo ta wuce gun Motansa ta bud’e gaba tare da sallama bayan ya amsa sallamarne seta shiga ta zauna tare da rufe kofan tace gani yah kamal kanta na kallon gate d’in gidansu shi kuwa yana kallonta yayinda take ganinsa da gefen idonta.😜37/38

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]