[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Wed. Nov 30th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Bayan su sabreen sun shiga d’akine MACEEN tasa key ta rufe, da sauri sabreen ta juyo tace meyasa kika rufe kofan? MACEN tace karki damu sabreen bazan cutar dakeba nazone dan inyi magana dake. Bayan sun zaunane macen ta rik’e hannayen sabreen dukka biyu ta fara magana suna kallon junansu.
Sunana SALMA kuma ni kad’ai ne agun iyayena, tun kafin a haifeki mahaifinki ya rasu ata dalilin cetona.
Wata rana nida iyayena muna zaune a cikin jeji suna koyamin harbi da kwari da baka, ina zaune daga nesa su kuwa iyayena suna tsaye agu d’aya mahaifina ya saita kwari da baka a daidai inda nake zaune akan zai gwada kona iya kwaucewa kamar yadda yake koyar dani, nima jira nake ya harbo in nuna masa kwarewata na kaucewa. Kawai sega wani bafulatani yana wucewa se idonsa yakai gun iyayena kuma yaga suna da niyan harbinane, bafulataninnan ya kalli lokacin ina zaune bazan wuce shekaru 7 ba, dai dai lokacin da mahaifina ya harba kwarinne se wannan bafulatani yayi sauri tare dayin tsalle danya tareni, amma se wannan kwarin ya sameshi a daidai setin zuciyarsa, nan take ya fad’i. Iyayena dani dukkanmu mukazo kansa lokacin jini nata zuba sosai daga jikinsa, hannuna ya kamo yana magana da kyar yana cewa haba bayin Allah wannan yarinyar kuma metamuku da zaku kasheta dan Allah ku kyaleta sannan ya juya yana kallona yace yarinya tashi ki gudu kinji ki gudu zasu kasheki, mahaifina ya share kwallan fiskarsa yace bawan Allah ba kasheta zamuyiba, hasalima ‘yarmuce wannan na cikinmu gwaji kawai muke mata akan koyar da ita danayi, gashi abisa rashin sani na cutar dakai gurin kokarinka na ceton ‘yata😰, dan Allah ka yafemin bawan Allah ba’a son rainabane. Bafulatanin yayi murmushi yace bakomai na fahimta, haka Allah ya tsaramin nikuma, ta wannan hanyar zan koma ga mahaliccina, nayafe maka har cikin zuciyata, sedai ina neman taimakonku, mahaifina yace taimakon me kenan? Bafulatanin yace matata tana gida d’auke da tsohon ciki ita da surukina suna can gida a wannan kauyen da yake gaba danan, inaso ku taimaka ku k’arasa dani gidana dan baajin zan iya karasawa da kaina dan yadda nakeji ayanzu. Dukda cewa mahaifina ya cire kifiyar daya soki bafulatanin, amma sam jini bai dena zubaba gashi daga gani yana shan azaba, haka mahaifina ya d’aukeshi mukaje har kauyenku, nan mutane suka taru a kanshi agun mai unguwa. Matarsa da surukinsa aka kira sukazo tana ganinsa ta fara kuka sosai, mai anguwa yace meya sameshi haka? Har mahaifina ya bud’e baki zaiyi gaya musu abinda ya faru, kawai se bafulatanin ya fara magana da k’yar yana cewa ina cikin tfy ne se nayi tuntub’e da wani abu, kafin in ankara se naji na fad’i akan wani abu mai kaifi kuma mai tsini, ban iya tashiba se naji mutane na zuwa, shine nace su taimakamin su kawoni kauyenmu, bafulatanin ya nuna mahaifina yace wannan shine wanda ya ciremin kifiyar data sokeni kuma ya kawoni gida. Hawayene sosai a fiskar iyayena dajin lbrn da bafulataninnan ya fad’awa yan kaiyensu. Matarsa da surukinsa suka fara kuka gashi asibiti se cikin garin, mahaifina ya d’aukesa yace muje asibiti, nan aka tashi da wuri domin zuwa asibiti, se mata mai cikinnan ta rike hannunsa tanata kuka tana cewa maigida karka tafi ka barni tun bakaga abinda zan haifa manaba, banaso abin cikina ya zama maraya dan Allah karka barmu. Bafulatanin ya rik’e hannun matarsa yana kokarin magana amma se mukaji yana salati tare da cikawa😰. Kuka sosai matarsa takeyi da kuma jama’an dake gurin musamman iyayena dani, matarsa kuka takeyi tare da rungume gawan mijinta kowa ya tausaya mata, da kyar mahaifinta ya janyeta ya kaita gidan makota inda nida mahaifiyata mukabi bayanta, bayan mahaifinta yakaitane seya koma gunsu mahaifina akayi mishi wanka tare da suturceshi akai masa sallah se gidansa na gaskya😭. Salma ta tsaya da lbrnta anan tana kallon sabreen da idanunta yayi jah dan kuka datakeyi😭 SALMA ta dad’a matse hannayenta acikin na sabreen tana kwalla itama tace sabreen bakowa bane wannan bafulatanin illa MAHAIFINKI dan Allah ki gafarcemu nida iyayena😰👏🏻. 😳🙄😭😭 idanu sabreen ta bud’e tare da tsananta kukanta sosai ta hankad’e Salma tare da mikewa tabud’e kofa ta fita a guje segun kakanta yana baiwa flawer ruwa, tunkafin ta karasa gunsa ya juyo ya tareta dan yasan komai. Sabreen tana kuka tana cewa kaka itacefa sanadiyan rasuwan mahaifina wannan ita da iyayenta sune sila kaka😭😭😭. Salma ta k’araso gunsu tana cewa sabreen kakanki yasan komai ke kad’aice baki saniba dama, sabreen da take kallon salma seta juya tana kallon kaka tace kaka wai kasan komai😡😰😭??

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]