[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 14

 

Mum ta d’ago da sabreen tace lfy sabreen, menene, sabreen ya rasa me zatace se tace musu mammina na gani anan mammina tana nan d’akin naganta, kamal ya matso kusa da mum yace ki kwantar da hankalinki sabreen mamminki ta rasu ai ba yadda za’ayi ki ganta anan wanda ya rasu baya dawowa kinji “may be dai kin razana ne kawai” har yanzu dai sabreen waigawa takeyi tanata k’arewa d’akin kallo. Mum tace shikenan hafsat kwashe plate da abincin can, sabreen muje daining kici abinci.
Da sauri tabi mum suka isa daining ta zauna mum ta zuba mata abincin, kad’an sabreen taci tace ya isheta, ruwa mum ta mik’a mata yasha sannan tace nagode mum, hafsat ce ta k’araso tace mum ko zamu kwana da ita a d’akina idan ta dena tsoron seta koma d’akinta, mum tace toh hakanma yafi sabreen ku kwana tare kinji, kai sabreen ta d’ago batare datace komaiba hankalinta yana gun wannan MACEN. Wayan kamal ne ya sake yin kara ya d’auka hello abokina, suhail yace meke faruwa ne a gidan? Kamal ya gayawa suhail komai, sannan suhail yace ina sabreen d’in bata wayan, sabreen da tayi nisa cikin tunani kamal yana ta mata magana tare da mik’a mata wayan amma sam bata jinsa, hafsat dake zaune a gefentane ta tab’a kafad’arta tace sabreen tunanin me kikeyi haka akanata miki magana bakyaji, se a lokacin ta dawo hayyacinta a zabure ta kalli hafsat sannan ta karbi wayan tasa a kunne tare da cewa hello, suhail yace sabreen naji abinda ya faru amma inaso kisani shi mamaci baya dawowa k’ila dai kinsa tunaninta arankine har kike ganinta a naki tunanin yakama ki d’auki kaddara kisa a ranki cewa ta rasu ba kuma zata dawo garemuba har abada kinji? Shuru tayi tana had’iyan kukanta batace dashi komaiba, suhail yaji tayi shuru batace komaiba seya kira sunanta “sabreen are you there”? Se alokacinne tace “yeah naji kuma na gode” sannan ta mik’awa yah kamal wayan, lokacin suhail nacewa sabreen muryaeki yamin kama dana wata yarinya, karaf a kunne kamal amma seyayi kamar baiji yace hello abokina yane, suhail yayi ajiyar zuciya yace bakomai nan dai sukaci gaba da hiransu har kamal yayi musu sallama ya tafi suma suka wuce d’akunansu donyi bacci. Kamal dai tunda ya koma gida tunanine cike a zuciyarsa game da sabreen da kuma abinda yaji a bakin suhail, da kyar bacci ya d’aukesa. Shima suhail acan pakistan kasa bacci yayi yanata tunanin wannan yarinyar mai nik’af, tabbas yanzu da yayi magana da sabreen seyaji irin wannan muryance datace mishi “Thankyou so much SUHAIL” yace toh kodai kawai dan nasata a rainane shiyasa naji muryanta irin na sabreen, da wannan tunanin shima yayi bacci. Itama sabreen kasa bacci tayi dukda kashen wutan d’akin da hafsat tayi amma sam ta kasa bacci, fiskan MACENNAN dai shiyake mata yawo a kwakwalwarta, tace dama na sani dabanyi ihuba tunda dama na dad’e inaso in sake ganinta domin inyi mata godiya, insha Allah duk randa na ganta bazan sake tsorataba zanso inji metakeson gayamin sannan nima kuma inyi mata tambayoyi, ta wani gefe kuwa dad’in kalaman suhail takeji har cikin ranta tana ta murmushi tare da mamakin suhail tana zamcen zuci, yanzu shi suhail kota muryata bazai ganeniba😊, murmushi tayi tana tuna lokacin da suke shak’ar numfashin junansu yayinda suke kallon idanun junansu, kyakkyawar fiskarsa take gani a idanunta tare da murmushin yayi mata😌 dad’i sosai take ji har cikin ranta tace koda wasa bazan sanar dashiba, kuma bazan tab’a bari ya ganeniba😊 da wannan tunanin itama bacci yayi gaba da ita.
Bayan sunyi breakfast ne taje gun kakanta sunata hira har azahar kafin ta shigo dama bata sallah. A palo suke zaune sunata hira da mum da yah kamal da kuma hafsat sabreen dai dariya kawai takeyi tana sauraron tsokanar da yah kamal yakeyiwa hafsat, har la’asar bayan sunyi sallah ne kamal yace zai fita se dare zai dawo, mai girkinsu tana gama abincin dare d’anta yazo ya d’auketa, alkhairi sosai mum ta mata harma da hafsat sannan suka tafi. Bayan isha yah kamal yayi cefene sosai ya kawo gida saboda gobene alhamis sabreen zata fara girki. Washegari ta shiga kichine ta fara girki, dama kunsani base na k’ara maimaitawaba. Kowa yaji dad’in girkin nata harma da masu gadin gidan sunata cewa ai tafi nadama iya kirki wlh, dad’i kaka yaji har cikin ransa don yadda aketa yaba girkin jirarsa😊. Haka tayi na rana dana dare mum farin cikine a fiskarta sosai danko gaskya girkin sabreen bakarya, sun yaba sosai harda hafsat tana cewa gaskya zaki koyamin girki sabreen, yah kamal yace da lalacinkinne zaki koyi girki? Hafsat ta b’ata rai mum kinji abinda bro kamal yake cewa ko, mum tace rabu dashi zaki bashi mamaki kuwa, sabreem tace zan koya miki hafsat karki damu. Haka sukaita ta hira har suka gama cin abinci se yah kamal ya mik’e tare da cewa mum nizan tafi seda safenmu, mum tace yau da wuri haka babu hira kenan, kamal yace mum kinsanfa gobene abokina zai dawo, dan haka bazan samu zuwa da safe bama sedai zuwa yamma. Mum tace to shikena Allah ya bamu alkhairi, kamal yace ameen sannan ya wuce gun kaka sukai sallama seya tafi, su mum kuwa sun d’an tab’a hira sannan suka wuce donyin bacci, Hafsat se murna takeyi gobe bro suhail d’inta zai dawo, ita kuwa sabreen binta kawai takeyi da kallo tana mamakin hafsat, dan sam basa wani hiran kirki da hafsat d’in, amma gashi yanzu tanata murna tana cewa sabreen zakiga d’ayan bro na gobe kinji, sabreen tayi murmushi tace to Allah ya kaimu goben Allah kuma ya dawo dashi lfy😊, hafsat tace ameen sannan ta kashe wuta suka kwanta kowacce da tunaninda takeyi a ranta da haka har bacci ya d’aukesu…29/30

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]