[Advertisements⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TANA RAINA CHAPTER 13

 

 

Ayaune sabreen zasu koma gidansu suhail, bayan ta gyara ko ina ta kimtsane tayiwa ya kaml girki ta ajiye a daining, da yamma yazo ya tarar dasu a palo suna zaune. Bayan yaci abincine yace to bari ind’an watsa riwa semu tafi koh, sabreen tace to sannan taje ta d’auki plate d’in ta wanke ta dawo ta zauna, daidai lokacin kamal ya fito daga d’akinsa se kamshin turare yakeyi yace toh kaka muje ko sannan ya d’auki kayan kaka ita kuwa sabreen ta d’auki nata suka tafi. Maigadi baiso rabuwansu da kakaba harma da sabreen domin mutanen kirkine suna da dad’in zama sosai. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai se wayan kamal ya fara ringing, ya d’auka tare da cewa hello abokina ya akayine, suhail yace ka d’aukosu kakan kuwa, eh na d’aukosu yanzu hakama muna dab da shiga gidane, suhail yace”thankyou dud” pls ka gaishemin da kaka, kamal yace kaka yana jinka, se kaka yace ina amsawa Allah ya dawo dakai lfy, suhail yace ameen kaka nagode, kamal yace to abokina zan kiraka anjuma, ok sena jika sannan ya katse wayar, dai dai lokacin kamal yayi hon aka bud’e gate suka shiga, tun daga wajen gidanma kasan gidan manyane bare kuma inka shiga ciki, bayan sun fitone kamal ya d’auki kayan kaka yana musu jagora har suka k’arasa da sallamarsu, mum ce da hafsat zaune suna kallon “THE GARDINERS DAUGHTER” wani series film ne mai dad’in gaske. Tun shigowarsu suka sawa sabreen ido suna ganin irin kyawunta ai atake kirjin hafsat ya buga da karfi, bayan sun zauna ne suka gaggaisa hafsat tace bro kamal kardai ince sune bak’in namu? Kamal yayi murmushi yace kwarai kuwa sis sune, wannan itace sabreen wannan kuma kakanta, shi zaici gaba daba flawer ruwa ita kuma zata dinga yin girki, mum tace Allah sarki sannu sabreen ya hakurin mahaifiyarki kuma, sabreen tace hakuri ya zama dole, mum tace to Allah ya jikanta ya jikan dukkan ‘yan’uwa musulmai, gabad’aya suka amsa da ameeen. Se mummy tace toh hafsat tashi ki nunawa sabreen d’akinta ko, hafsat tayi murmushi tace taso muje, mikewa sabreen tayi tare da d’aukan akwatinta tabi bayan hafsat, shi kuwa kaka masaikin bak’i dake tsakar gidan ta gefe aka kaisa, d’akin harda AC da komai dakomai dai gwanin sha’awa. Bayan hafsat takaita d’akinne ta bud’e wall drop sannan ta karb’i akwatin sabrren ta ajiye mata a ciki ta juyo tace nan shine d’akinki, sannan ga toilet naki nan, idan akwai wani abu da kike buk’ata toki sanar dani kinji😊, sabreen taji dad’i sosai tace nagode hafsat😊. Bayan hafsat ta fitane sabreen ta k’arewa d’akin kallo tas d’an daidai ne bayi da girma sosai amma an zuba kayan duniya, kwanciya tayi tana ta tunanin yah kamal, tace oh yah kamal yau shi kad’ai a gidan bazaiji dad’iba hakama mai gadi. Bayan isha hafsat tazo ta kira sabreen wai kizo kici abinci, a baya take biye da hafsat har suka k’arasa daining, kamal na zaunne kusa da mum suna cin abinci, hafsat ta zubawa sabreen ta ajiye tare da cewa bisimillah zauna muci, sabreen tace zanje inci a d’aki, mum tace meyasa zakije d’aki bayan gamunan anan kodai kunyan d’an nawa kikeyine kamal, kamal yace kunyana kuma mum meyasa zataji kunyata kawai dai k’ila kunyanki tajeji, mum tace toh shikenan hafsat mik’a mata ta tafi d’akin tunda hakan tafiso, sabreen ta karb’a tare da cewa nagode emm kaka fa? Kamal yace kaka yana d’akinsa yanzu na kai mishi nashi abincin jekici abincin seki dawo muyi hira kinji, toh tace sannan ta wuce d’akinta taje ta zauna tana cin abincin, abincin yayi dad’i sosai dan haka taci sosai sedai bata cinyeba. Wani murya taji kamar daga sama an SABREEN, d’ago da kanta tayi tana kallon bakin kofan shigowa😳 wannan MACEN tagani a tsaye tana kallonta tana mata murmushi, itadai sabreen sam bataji an bud’e kofaba kawai ganin mutum tayi a tsaye, ahankali MACEN take takowa inda sabreen take, 😳😳🙆🏻ihu mai karfi sabreen ta sake tare da wurgi da plate d’in abincin hannunta tasss kakejin fad’uwan shi a k’asan tiles take ya tarwatse. Ganin yadda sabreen ta tsoratane yasa MACEN tayi saurin b’acewa segasu mum da kamal sun shigo da saurinsu, kamal dake waya da suhail yace abokina bani 2minit zan kiraka, da gudu sabreen taje ta rungume mum tanata kuka tare da waige waigen bayanta🙄😳🤔

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]