SALON SO CHAPTER 20 END

Advertisements

_____

SALON SO CHAPTER 20 END

 

 

 

Ranar da Bomboy da Kausar suka dawo da

Advertisements

_____

ga tafiya, ‘yan aikinta suka gabatar mata da sakon

iyayenta. Kausar har kuka ta yi don bakin ciki gashi wayarta da lambobin iyayen nata suke ciki ta fadi a

wannan tafiyar da ta yi, don haka ba wata hanya

da zata ji su ba damar ta yi musu waya kenan, ko

su yi mata?

Ga shi bata san address din su a American ba, bare

wata rana ta kai musu ziyara dole ta dauki dangana da hakuri ta na me fatan Allah sa su zo nan kusa

don ta ji cikakken address dinsu ko ta bisu su tafi

tare. Ba dadewa Kausar ta gama da laulayin ciki me

wahalar gaske bata iya cin abinci sosai ga azabar

ciwon ciki da ciwon kai. Hankalin Bomboy

ya tashi da ganin rashin lafiyartata. Ya kwashe ta suka nufi asibiti akayi mata tes da

gwaje gwaje daga karshe likitan ya dauki fitsarinta

ya ce, gobe a dawo a karbi ruzol suka taho a hanya

ya yi mata siyayya fal irin na marasa lafiya ya dawo

da ita gida.

Da gari ya waye Bomboy da kansa ya je ya karbo sakamakon gwajin da aka yi mata hankalin

Bomboy yayi fari da ganin wannan sakamakon

Murna a gun shi da Kausar kuwa kamar su hadiye

juna don murnar samun ciki Kausar ta fara

kawowa Bomboy tsarabe-tsarabe, ta ce

wannan ta ce wannan haka Bomboy zai je ya kwaso mata. **** **** ****** *****

Sannu sannu rayuwa ta juya ta juyawa

Bomboybaya domin kudin hannunsa tas sun kare

‘yan aikinta wuya ta ishe su duk sun gudu sun

barsu, sai ga Kausar ta je ta na rokon matan yayun

Bomboy da su taimaka su rinka sammata abincinsu, su kuma suka ce muddin tana so ta

rinka cin abincinsu sai dai ta fito ta rinka girkawa

don babu bawanta da zai rinka dafawa yana bata

tana ci.

Dole Kausar ta fito tana girkawa da safe koko ne

za’ayi shi tsilulu saboda babu wadatacciyar gasara, rafin kofi ake rabawa kokon ga ba kosai da rana a

jika garin kwaki a yayyafa a kasan roba yaro ma

baya koshi bare babba.

Da daddare datsar dawa za a tuka bakikkirin da

koriyar miyar kuka wadda daga daddawa sai

barkono a ciki. Kausar ga fama da ciwo ga shi yanzu cikin nata ya

kai wata shida ya yanzu cin abinci ne da ita saboda

cikin yana sata masifaffiyar yunwa. Ga abincin da

ake bata baya isarta, ga rashin dadi haka take

hakura ta tattura, ga shi duk ta yi baki ta rame ta

kanjame ke ba kya ce ‘yar hutu Kausar din da ba ce.

Duk ta bushe sai kashin wuya da tsinin ciki gashi

bata iya yin tuwon ba duk ranar da ta yi sai yai

danye ko ya yi gudaji.

Ga matan yayye da ‘yansu si yi mata masifa sun

dungure mata kai suna yi mata ba la’i, dole ta jure ta hakura take zaune don bata da gurin zuwa in ma

ta fita ga iyayenta har yau bata samu labarin su ba,

to ina zata samu kudi xuwa American ma bare ta

binciko in da suke.

Don kayan dakinta kaf ta sai da su ta ci abinci

duniya kenan me juyi juyi. **** ****** ****** Jawahir watanta biyar kenan da haihuwa ita da ‘ya

‘yanta sun kara kiba da haske sun yi kyau jajir da

su kamar ‘ya ‘yan Turawa. Kowa ya kalle su sai ya

yi sha’awar cewa da ma dai iyalinsa ne.

Haidar arziki ya ci uban na da, ya tanfatsa musu

wani tsantsareren gida na gani na fada wanda duk wanda yaje gidan kallo abinda yake fadan shi ne

aljannar duniya.

Gidan ya

tsaru iya haduwa ya hadu, yanda Haidar ya

hadewa jawahir falonta da dakunanta ko na

sarauniyar indiya albarka Dakin ‘yan uku kuwa ke kya ce kamfani ne

tsadadde na kayan wasan yara saboda kayan alatu

da suke ciki, Haidar ya kara girman da murjewa ya

zama Alhaji me tsananin kyau da kwarjini.

Jawahir ta zama big madam cikakkiyar mace ga

kyau ga hutu ga kwarjini ‘yan ‘ya’yayansu guda uku abin sha’awa tubarkalla, bul bul da su jajir da

su gashinsu akanannade kamar ‘ya’yan turawa.

Mijinta ya sakar mata naira sosai don duk wasu

takaddun kamfanoninsa da gidajensa da filayensa

da duk wasu kadarorinsa suna hannunta. Baya yi

mata geji akan komai duk wani abu daya kamata ya yi na game da biyan ma’,aikatansa

albashi na kamfanoninsa zuwa na gidajensu, ya ce

Abbansa ya kwanta ya huta shi yake komai na

gidansu.

Jawahir ta kasance me taimakon talakawa da

kaskantattu wadanta basu da watada, don haka gidan nasu kullum yake cike da ‘yan neman

alfarma.

‘Yan uku suna da shekara daidai ta yaye su sun yi

girma sunyi wayo gudunsu suke yi ko ina ga

surutu kamar Aku. Suma hadadden falonsu duk

sun ci kwalliya kamar masu shirin zuwa fati, Haidar yana ta wasa da ‘ya

‘yansa ya ta da kai da cinyar jawahir Salim da Sadat

shiga iri daya akayi musu ta jins da T shirt fara da

aka yi rubutu da ruwan gwal a gaban rigar.

Salma ma tana sanye da dan jins dinta da ‘yar riga,

kunnanta da wuyanta yana sanye da yari da sarka kirar daimond ‘yar xire, kanta ya sha kananan

kalba da kanan ribon a jiki yaran sun yi kyau

kamar ‘ya ‘yan turawa.

Gaba daya yaran suna kan Haidar suna ta tsalle

tsallensu a jikinsa, wayar ku sa da jawahir ta yi kara

ta daga ta kara a kunnenta, “Hello yauwa Anty jawahir wallahi wata bakuwa ce tazo ta kafe lallai

tana son ganinki.

Jawahir ta ce “Okey ba damuwa kawo ta muna

falon sama

Ta dire wayar, bakuwar da tun shigowarta ta saki

baki tana ta kalle kalle a cikin gidan babu abin da ya fi kayatar da ita irin tsantsara tsantsaran falon da

suka rinka wuce su, jikinta bai kara yin sanyi ba, sai

da suka shiga wani tsantsareren falo wanda ya

hadu da kayan kyale kyale sai wata hadaddiyar

matattatakalar bene wadda aka yi ta kamar da

ruwan gwal. Kasan matattakalar shimfide yake da kafet, suka

hau suka yi sallama falon suka shiga.

Jawahir ta dago kai tare da amsa sallamar ta zuba

wa matar ido, tana tunanin ina ta santa. Matar ta

zube a gabansu tana kuka Haidar kuwa yana ta

wasa da ‘ya ‘yansa be ma dago kai ba bare yasan wacece.

Jawahir ta ce a’a baiwar Allah me kuma yake

faruwa daga zuwa sai kuka ba tare da kin yi wani

bayani ba.”

Ta kwanto yan kwananniyar’yarta daga baya

wadda shimi ce kawai a jikinta saboda rashin sutura matar kuma atamfa da take jikinta duk ta

kode ta jeme ga hadin baki a jiki matar ta ce “Ban yi

mamakin yanda baku gane ni ba ni ce Kausar.

Jawahir ta

yi zumbur ta mike tana rike da baki cikin mamaki ta

ce “Kausar ke ce rayuwa ta maida ki haka me ya faru dake Kausar ina iyayenki da mijinki.?”

Kausar ta goge hawayenta ta shiga basu labarin

iyayenta da halin da take ci, ta juya tana kuka tana

rokon Haidar gafara Haidar ya ce “Ni wallahi ba

komai don rabuwa da ke alheri ya zamar min don

da ina tare da ke da ban sami zaman lafiya da kwanciyyar hankali haka ba.” Ya mike goye da

Salma ya dauki Salim da Sadat a kafadarsa ya shige

ciki.

Kausar ta bisu da kallo tana me sha’awarsu shi da

‘ya ‘yansa da matarsa da ta yi hakuri da yanzu

itama tana cikin wannan daular. Jawahir ta girgiza kai zuciyarta cike da tausayin

halin da ta ga Kausar. Lallai duniya zancan banza ce

kana takama kai wani ne lokaci daya sai Ubangiji

ya mayar da kai ba komai ba.

Jawahir ta ce Kausar “Ki yi hakuri lamarin duniya

kenan don haka ba a son daukan duniya da zafi. Ta mike ta shiga daki ta debo sababbin riguna kala

takwas da turamen atamfofi kala hudu da

dinkakku kwance kala shida, da kudi naira dubu

hamsin ta kawo mata ungo wa’yannan kije ki yi

amfani da su zan kuma sa abinciko min koda

lambar wayar iyayen naki ne kin ji ko.” Kausar ta rissina ta rinka godiya tana kukan murna.

Jawahir sai da ta sa aka hada mata kayan abinci fal

bayan but din mota tasa direba ya kaita har gida.

Kausar tana komawa ta sai rishonta ta sai kananzir

galan guda ta kai dakinta take girkinta ita kadai ita

da mijinta suna ci ta daina kula abincin gidan Nan fa matan gidan da ‘ya’yan gidan suka tusa ta

agaba da habaici da bakaken maganganu ita dai

bata kula kowa sai ta rinka kulle wajenta ma ta

daina sauraronsu.

Sati biyu a tsakani jawahir ta ba wa direbanta waya

sabuwa da kudi dubu goma a ciki da lambar wayar iyayen Kausar ta ce ya kai wa Kausar.

Direba ya kama hanya ya kai wa Kausar ta rinka

murna tana kwarara wa direba godiya ta ce ya

mika mata godiya wajen jawahir din kafin tazo.

Direba yana tafiya, Kausar ta kulle dakinta ta buga

wayar bugu uku ana hudu aka dauka. Muryar babanta ta ji ta fashe da kuka, “Dady, Dady

nice Kausar kun gudu kum barni cikin halin kunci

da wahala.

Tana kuka tana gaya masa halin da ta ke ciki da ita

da mijinta tace yanzu mijinta bashi da komai suna

cikin kuncin rayuwa hatta lokacin da ta haihu bai yi mata komai ba, da yunwar da ta sha da bautar

girkin da take yiwa matan gidan da irin tsangwama

da cin mutuncin da ake yi mata har kawo irin

taimakon da jawahir take yi mata da binkicen da

jawahir ta yi ta samo mata lambarsu ta kawo mata

sabuwar waya da kati na dubu goma a ciki duk ta gama gaya masa.

Hankalin

babanta ya tashi ransa ya damu ya ce mata kiyi

hakuri da man kwanan nan muke son mu zo mu

duba ki ganin mun shekara daya da baro Nigeria.

Amma kisa idonmu a cikin satin nan muna tafe.” Hankalin babarta da ‘yan uwarta ya yi masifar tashi

da jin halin da Kausar ta ke ciki, ai basu iya hakuri

ba kwanakin ba cikin kwana uku suka dira a

Nigeria.

Iyayenta da ‘yan uwanta har kuka suka yi jin halin

da Kausar ta shiga, nan fa aka shiga bata kashi tsakanin Bomboy da iyayen Kausar da kyar

suka samu ya sake ta.

Bayan ya sake ta ne, ya shiga daki yai ta kuka har

da ihu shi ya shiga uku. Yanzu yaya za ayi ya kuma

wani auren?” Da kyar su Amal Junior da Jauhar M.

Nas suka rarrasheshi. Suka zo suka ta yiwa jawahir godiya tare da sa

mata albarka.

Suka roki kuma Haidar gafara a bisa abin da Kausar

ta yi masa ya ce “Ba komai ai ya yafe mata.

Nan fa kyakkyawar alaka da zumunci ya kullu

tsakanin jawahir da Kausar da kuma iyayensu. Satinsu uku a Nigeria suka daga da Kausar da

‘yarta da iyayenta zuwa America.

Cikin lokaci kankani Kausar ta murmure ta murje ita

da ‘yarta ssuka shiga shafe shafen da ya bayyanar

masu da kyansu. Bata dade da gama idda ba

manema suka fito mata in da ta sake auren wani mai mata daya da ‘ya’ya uku.

Ya riki kausar da ‘yarta cikin gaskiya da amana in

da suke zaman lafiya da abokiyar zamanta.

Haidar da jawahir linkafa ta ci gaba sun zamo abin

kwatance da sha awa a Nigeria suna da ‘ya’ya biyar

kenan ‘yan uku Salma, Sadat, Salim sai Nana khadija da Mohammad auta.

Rayuwarsu me burgewa da ban sha awa kowa ya

shiga gidan baya son fita don ganin irin

rantsattsiyar SALON SO, ya yarda suke shimfidawa a

gidan. KASH DAMA ANCE LAIFIN DADI KAREWA.

DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA UBANGIJI DA YA BANI DAMAR KAMMALA KAWO

WANNAN LITTAFI KAMAR YADDA MUKA FARA.

TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA SHUGABA

ANNABIN RAHMA (S.A.W), ALAYEN SA DA

SAHABBAN SA. DA FATAN MUN KARU DA DARUSSAN

DA MUKA GANI A CIKIN WANGA LITTAFI, ALLAH YASA MUYI KOYI DA MASU KYAWAWAN HALAYEN

DAKE CIKIN SA YA KUMA TSARE MU DAGA AIKATA

MUNANAN AYYUKA MAKAMANTAN NA WASU DA

MUKA JI A CIKI. TOHHH!!! INA FATAN NIMA XAKU

TAYA NI ADDU’AN SAMUN WATA MATAR TUNDA

MAFARKI NA TA SUBUCE MIN WATO KAUSAR. SAI MUN HADE A WANI SABON LITTAFIN INSHA ALLAH..

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

BAKAR INUWA CHAPTER 23

Advertisements _____ Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *