[Advertisements⬇️]

SALON SO CHAPTER 19 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SALON SO CHAPTER 19

 


Ya debi makudan kudi wanda ba zan iya cewa ko

na wane ba ya zuba a jaka ya fice ya kulle ko ina na

gidan ya fito ya kara gaya wa megadi ya kula da

gida sosai

Ya shiga mota da kansa yake jan motar cikin farin

ciki da annushuwa wani tsadaddaen hadadden kanti yaje wanda duk kayansu da ga waje suke

shigowa da shi. Nan da bude bakin aljihu ya runka

jidar kayan jarirai su tawul, da shawul da riguna

famfas su safa da takalman jarirai komai iri daya

guda uku yake kwasa, sai da ya cika but da kayan

jarirai har da gadaje set me uku na jarirai. Haidar ko ya manta ne da dinbin siyayyar da suka

yo daga kasar waje ta jariran ne? Oho.

Ya je ya siyo katon ragonsa wanda za a yanka

saboda naman gashi ya siyo kwandunan tattasai

da tumatir da attaruhu albasa da kaji da zabi

saboda girkin ‘yan barka ya yiwa direbansa waya ya taho da wata motar kwashe wasu kayan suka

nufi gidan su jawahir.

Tirkashi! Wani aiki sai masu da shi, aka rinka jidar

kayan da Haidar ya kawo ana kaiwa sashen momy

Haidar ya shigo yana ta gaisawa da jama’a suna yi

masa barka. Ya karasa falon Momi ya gaida su Momi su Anti

Babarsa da su Inna da kannansa ‘yan biyu. Dangi

dai rankacakaf kowa ya zo, jariran suna hannunsu

sun sha ado, da tsadaddun kaya ‘yan kantuna

masu kyau.

Sayyada ce take gaya masa ai jawahir tana sashenta ta ce kada abar kowa ya shiga bacci zata

yi, shi yasa aka kwaso jariran ma aka yo nan da su,

saboda yan barka.

Haidar ya ce ai suma jariran suna bukatar hutu da a

kyale su aka yi a jikin uwarsu suna jin diminta suma

suyi vaccin iya in an jima su ka tashi duk me son ganinsu sai ya gansu.

Anty babarsa ta watso masa harara yayin da ya

mike sum-sum ya bar falon ya nufi sashen da aka

ware wa jawahir.

Ya tura kofar falon ya shiga ko ina a gyare sai uban

kamshi da yake tashi, yana kai cikin dakin wani kalar kamshin ya ja mai dadi da sanyaya zuciya.

Ya hangota kan makeken gado tana ta baccinta

hankalinta kwance.

Ta yi kwanciyarta cikin jar sup me zanen ganye ta

kara kyau da haske sai dai ta rame. Ya karasa bakin

gadon ya sumbace ta yana shafa fuskarta tare da hura mata iska a kunnanta.

Ta bude ido

tare da fadada murmushinta “Lah, Honey ka daina

fushin ka zo? Ta tashi ta jingina a jikinsa ya

rungume ta yana shafarta tare da shakar

ni’imtaccen kamshin da yake jikinta. Ya ce “Bebyna ai ba zan iya fushi da ku ba, ina zan

iya bacci ba tare da naji diminki ba, ai ba ni da

kwanciyar hankali in banga ‘yan ukuna ba.

Aka kwankwasa kofar jawahir ta yi saurin kwace

kanta ta matsa can gefe, ta yi izinin a shigo.

Inna ce da sajida suka shigo dauke da kwanukan abinci.

Inna ta sakko mata da filo kasa ta ce zauna anan ta

bude mata kwanon tuwon dawa yana turiri ta

bude miyar kubewa danya da aka burge kaza ciki.

Daya kwanon kuma gasasshen nama ne ya ji

kayan kamshi da yajin daddawa. Sai kunun kanwa a kwanon sha Inna ta debo man shanu ta zuba

mata amiyar ta ajiye mata yajin daddawa, ta ce

“Sakko ki zauna maza ki cinye.”

Idon jawahir ya yi rau rau zata yi kuka, Haidar ya ce

“Haba Inna daman dan ki yi mata izaya da badin

tuwo da kunu shi yasa kika dage sai ta taho nan.? Inna ta ce, “Da Allah i min shiru ku me kuka sani

wannan ai shine gatan me jego shi zai sa mata

koshi ta sami wadataccen ruwan nono da ‘ya ‘yan

zasu sha su koshi ko kasan har yanzu yaran basu

sha komai ba sai zam zam da dabino?

Cikin tashin hankali Haidar ya ce “Inna saboda me? Bayan an siyo musu katon din madara.? Inna ta ce,

“Ai duk wani abu da za’a basu shi yanxu shirme ne

in dai va su fara shan nonon uwarsu ba, nonon

uwa shi ne abu mafi mahimmanci ga jariri. Don shi

yake sa su kuzari yake kara musu lafiya kuma don

haka ki sauri ki ci ga ruwan wanka can yakusa tafasa, idan an daki nonon da ganye zai temaka

wajen zuwan ruwan nonon da sauri

Haidar ya ce “A to ta so maza ki ci tuwon nan ki sha

kunun.

Jawahir ta kalli Haidar a marairaice alamun tsoro a

faskarta. Haidar ya kamo hannunta “Yi hakuri ta so na taya

ki ci kin ji kada ki damu.

Ta zauna kan filon shi kuma ya zauna kan kafet din

suka zuba yajin daddawa da man shanu suka fara

cin tuwo.

Yanda suka za ce shi ba haka suka ji ba, ashe dai shima tuwon dawar da dadi.

Tun suna ci suna hira har abin ya kaisu da shiru sai

dai gyada kai, kawai suke yi suna kai loma tare da

zuba santi.

Inna tana zaune tana kallon su sai da suka kusa

cinye tuwon nan, Inna ta zazzuba musu kunan a kofina ta tura musu gasashen naman shima sun ci

amma ba da yawa ba saboda koshin da suka yi.

Cikin kwana biyu ruwan nonon jawahir ya watada

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

tana shayar da ‘ya ‘yanta su koshi sosai.

Daddare dai ba sa shan nono sai madara yau

kwana hudu da haihuwar an kawo kayan barka akwati biyar na me jego da jirajirai.

Bayanin kayan da suke ciki zai cika min dan lattafin

nawa ban gama ba, hade da mukulun dankareriyar

mota jif, me ruwan ganye wadda Haidar ya yiwa

jawahir kyautarta da takardun dankareren gida da

yake a Nasarawa GRA shima gift ne ya bata duk saboda haihuwar ‘yan uku.

Sai takardun filaye guda uku kowacce da sunan

yaran mallakarsu ce kyautar ubansu Haidar da

yake ba su.

Kowa ya kalli kayan sai ya yi murna tare da son

barka da wannan hidima da Haidar ya yi. Ranar suna an sa wa jariran mazan sunan baban

Haidar da baban jawahir macen kuma an sa mata

sunan Inna.

Amma duk an boye musu sunan ana kiransu da

Salim, Sadat, Salma, Alhamdulillahi taron suna ya yi

kyau ya kuma kayatar ya burge kowa da yamma aka je dan Haidar da jawahir sun yi shigar kaya iri

daya jawahir ansha gwala gwalai hannu da wuya

da kunne har da sarkar kafa, sai sun jero a gurin

fatin suna rike da hannun juna suna tafiya sannu

sannu suna murmushi tare da hira kasa kasa a

tsakaninsu sai sheki suke yi kamar taurari, Bayan su

kuma Sayyada ce da Sajida sai Auwalu a tsakiyarsu

suna dauke da jariran yaran an yi musu kwalliya ta

ke ce raini Salma ta sha adon gwal har da siririyar

sarka ta kafa da ta hannu masu bidiyo da hoto sai

haskasu suke yi Sa’adu Bori ya saki kida yana wake su cikin wakar soyayya ta yi dadi Jawahir da

Haidar.

Allah ya raya Salim, Salma, Sadat, ‘yan uwa kuwa

suka balle bakin jaka sukai ta yi musu ruwan kudi.

‘Yan uwa da abokan arziki suka rinka ba wa

jawahir kyauta iri iri ta kayan jarirai da kudi da sauran su da haka taro ya watse.

Kowa ya nufi gida, jawahir tana zaune a gidansu ita

da jariranta da Inna sai kakar babarta wadda ita

take yi mata wanka.

Anty Maryam kuwa ta dage da sake hada wa

jawahir sababbin sinadarai na matse ‘ya mace da kara mata ni’ima mace ta koma kamar bata san

namiji ba.

Haidar kuwa kwana kawai yake yi a gidansa da

safe da ya gama shirinsa gidan su jawahir zai taho

ita zata hada masa break ya ci ya dauki yaransa ya

yi musu wasa sannan ya tafi office. Haka in ya dawo ma nan zai zo jawahir ta shirya

masa abinci ya ci ya yi kat yai ta rainon ‘ya ‘yansa ya

na yi musu wasa sai shadayan dare sannan zai

koma gidansa.

**** **** *****

Bari mu waiwayi Kausar don muga wace rayuwa take y ne.”

Kausar tun ranar da ta bar gidan Haidar ta sauka a

gidansu Abuja.

Iyayenta sun tare ta da murna amma ganinta da

shirmin akwatuna sai jikinsu ya yi sanyi suka shiga

tambayarta da lafiya? Kausar ta gaya musu karya da gaskiya na ciwon

Haidar sannan ta mika musu takardar sakin da ya yi

mata. Ba su ji wani zafin sakin da ya yi mata ba don

su a ganinsu gwanda hakan da ‘yarsu ta takura,

‘yan aikinta suka shiga gyara mata wajen zama.

Kwanaki kalilan a tsakani mahaifanta suka tura kano gidan Haidar don kwaso kayan Kausar suka

tarar da gida a kulle sai megida ne yake yi musu

bayanin ai ba kasar, sai gidan su Haidar din suka je

suka yi wa Anty bayanin zasu kwashi kaya.

Anty ta yiwa Yaya Abba waya yazo ta bashi

mukullayen ta ce ya je ya bude musu gidan ya tsaya su kwashi iya kayansu.

Haka kuwa aka yi, ya je ya bude musu ya jira suka

gama kwasar kayansu ko tsinke basu bari ba,

bayan yin iddar Kausar ta bude shafin zawarci in da

manema kuwa suka yo mata ca! Ganin ta fito daga

gidan mekudi ga ta kuma ‘yar mekudi. Kausar abinka da goggiyar tuni ta kuma wanke

fata ta tsunduma cikin zawarci. Manema da yawa

sun firfito mata sai dai rashin sa’ar da ta yi, duk

cikinsu babu saurayi, daga me mata daya sai me

mata biyu.

Hakan ne yasa ta riki Bomboy dinta. in da ya fito ya kawo

kudin aurenta ba dadewa ba aka sa ranar biki an

sha shagali da casu kamar na budurwa.

Ta tare a gidan ta dake nan K/Maiyaki. Bomboy dai ya dauki matar sa kauthar kamar wata sarauniyaba abin da be ajiye mata ba na jin dadin rayuwar

dan Adam. Ba ruwanta da girkin gidan kullum sai

dai ya dauke ta zuwa hotal su ci abin da ransu yake

so, ruwa sai da na roba wato swan.

Kowanne lokaci firji dinta cike yake da kalolin

abincin gwangwani da kalolin lemummuka. Tuni Kausar ta kara gogewa jin dadi da hutu ya

kara samun mazauni kome sai dai ‘yan aikinta su yi

mata bata katabus koda yaushe aikinta kwanciya

ko ci.

Ana cikin haka ne aiki ya kuma mayar da iyayen

Kausar kasar America. A lokacin kuwa Kausar da Bomboy ba sa kasar don haka bata sani ba

don iyayen nata sun ta lalubenta a wayarta ba su

same ta ba, sai sallahu suka bar mata gun ‘yan

aikinta suka daga zuwa America.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]